Complete Hausa Novels

Busa A Mutu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Busa A Mutu Part 2 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 4 of 6

Nima Kuma na cika da mamakin Ganin Masoyiyata yau ta manta dani bata nemeni ba Kuma ta kasa aiko mun da sako hhh

Anan zamu dakata sai wani lokaci
BUSA A MUTU
Littafi Na Biyu (2)
Part D.
Na Abdulaziz Sani M/Gini
AA Misau ke Magana

Marubucin yaci gaba da cewa..

AIKO MA TA DA AGAJIN GAGGAWA A MATSAYINSA NA
GAGARUMIN MATSAFI.
Birimkan suka cì gaba da kutsawa cikin
kogon dutsen suna ta tafiya. Sai da suka yì yar
doguwar taiya mai tsawo sannan suka iso wanı
babban wuri mai cìke da bìshiyoyì da wata korama
a tsakiya wacce ruwanta ke gudana ta cikin dutse
yana kwarara izuwa cikin wanı kwararo.
Bishiyoyin da ke wajen duka sun yì 'ya'yaye
nunannu da danyu, kai da gani ka san cewa
wadannan Biimka suna jin dadin rayuwarsu a
Wannan wu.
Da isowar biimkan wannan wun sai aka
daure Husnaila a jikin wata bishiya da ke tsakiya
da wala inyar danyar jijiyar bishiya aka daureta
tamau, tayi ta wutsil-wutsil domin ta kwance kanta
ta kasa.
Nan fa tayi amfani da dukkan karfin sihirinta
domin ta kwance kanta amma sai ta kasa.
A sannan ne ta gane cewar babu wanì sihinin
tsafi da yake tasiri akan dabbobin da ke cikin
wannan dajì na Kirzula, dajin Bala'i da masifa!
Nan fa birirrik an suka kama dukan kirjinsu da
hannayensu tamkar ganguna- suke dogawa. Karar
bugun kirjin nasu ya cika dajin gaba daya
A wannan lokacı ne HuSnaila ta gane cewa
biririkan kirari suke yiwa shugaban nasu suna
zugashi akan ya alka ma ta.
Koda fahimtar hakan sai Husnaila ta ci gaba
da kwarara uban ihu. Shi kuwa birnin sai ya
durfafo kanta
Ya yin da ya rage bai fi saura taku uku ba
kacal a tsakaninsu sai kawai aka jiyo wani abu ya
taho da gudu ta baya. Lokaci guda gaba dayan
birirrikan suka juyo har shi kansa shugabansu.
Kafin daya daga cikinsu ya yi wani yun kuri
sai kawai suka ga mutum ya dako tsalle ya dira a
tsakiyarsu ya hausu da SARA DA SUKA.
Ba wani bane wannan mutum face yarima
Muraisu.
Al'amarin da ya matukar daurewa Husnaila
kai ke nan, domin a tunaninta tuni Muraisu ya dade
da konewa ya zama toka.
Abinda ya kara đaure ma ta kai shi ne, ko
alamar kuna babu ajikinsa.
Muraisu ya Wanzu yana mai sara da sukan
wadann an biririka su kuma suna kai masa
mangari, yakushi, calksa da cizo yana gocewa.
Duk sa'adda suka kai masa yakushi da faratan
hannayensu ya, goce ko dutse suka, karta sai ka ga
ya dare gida biyu saboda tsananin kailin faratan
nasu.
Shi kuwa Muraisu duk sa'adda ya sari jikin
Birirrikan ko ya sokesu sai ya ji kamar karle yake
sara. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke
nan, domin ya san cewa idan áka dade a cikin
wannan hali zai iya gajiya. Da zarar kuwa ya gaji
birirrikan za su sami lagonsa su hallakashi.
Nan fa ya fara tunanin dabarar da ya kamala
ya yi ya ccci rayuwarsa da ta Husnaila wacce ke
daure a jikin bishiya.
Haka dai aka ci gaba da wannan gumurzu har
tsawon rabin sa'a ba tare da wata dabara ta fadowa
Muraisu ba. A sannan ne kuma ya fara gajiya.
Ai kuwa sai shugaban biririkan ya shammaci
Muraisu ya gabza ma sa naushi a fuska.
Saboda karfin naushin sai da Muraisu ya yi
katantan wa sau uku a tsaye sannan ya baje kasa jini
na yoyo ta hancinsa da bakinsa a cikin matsanaicin
hali mai kama da suma da gushewar hankali.
Koda Husnaila ta ga halin da Muraisu ya
shiga sai ta saduda ta tabbatar da cewa itama ta ta
ta kare don haka saí ta sake kwalla ihu ta fashe da
matsanaicin kuka.
Shí kuwa wannan shugaban birrrikan sai ya zo :
kan Muraisu ya tsaya ya raba kafafu akansa ya.
surnkuyo kasa da nufin ya cire kansa ya cinye.
Ba zato ba tsammaní aka ga Muraisu ya
dunkule hannunsa ya gabzawa shugaban biririkan
naushi a ido. Take ruwan idon ya fashe jini ya
rinka kwararowa daga ciki tamkar an bude
IDANIYAR RUWA. Kawai sai birin ya sulale kasa
ya fadi rikica ya zama gawa.
AI kuwa sai sauran birirrikan suka yi caa!
akansa za su yagalgalashi.
yaki.
Nan fa aka ruguntsume da sabon azababben
Cikin zafin nama Muraisu ya ci gaba da
naushin birimikan a idanu suka rinka ihu suna
zubewa kasa matattu, amma saboda na ci basu fasa
kai masa muggan hare-hare ba.
A haka ne suma birimikan suka rinka yi masa
raunika a sassan jikinsa.
Kafin Muraisu ya sami nasarar kashe gaba
dayan birirrikan sai da ya sami raunika a jikinsa
sama da guda ashirin, ya zamana cewa gaba dayan
jikinsa yai fata-fata da jini.
Ai kuwa yana gama kashe birirrikan sai shima
ya kife kasa a sumamme.
Muraisu bai farfado ba sai bayan rabin sa'a,
sannan ya mıke zaune da kyar yana numfashi
sama-sama, kamar ransa zai fta. Koda ya dago kai
Ya hada ido da llusnaila sai ya ga tayi masa guntun
murmushi.
Kawai sai ya kau da kai ga barin kallonta ya
shiga yiwa kansa magani.
Bayan ya gana gyara raunikan jikinsa gaba
daya sai ya mike tsaye da kyar ya je yasa bakinsa a
ciin wannan koram a ya sha ruwa ya koshi.
Kawai sai yaj. Husnaila ta ce, "Ya kai wannan
jarumi ka taimakeni ka kwanceni nima na zo na sha
ruwan nan, domin ishirwa ta addabeni".
Koda jin haka sai Muraisu ya dago kai ya
dubeta ya Ce, "Ta ya ya kike tsammanin cewa zan
sake aminta da ke? Shin kin manta ne cewa sau
biyu kika yi yunkurin hallakani, kuma yanzu sau
biyu ke nan ina ceton rayuwarki.
Na sani cewa kin tsaneni fiye da komai a
duniya, don haka babu yadda za a yi na yarda da
ke. Ba zan kwancc ki ba daga jikin wannan bishiya
har izuwa kwana biyu, amma duk abinda kike
bukata zan yi miki".
Koda jin war nan batu sai hankalin Husnaila
ya dugunzuma ain un, ta ce. "To yanzu kuma idan
bukatar bawali ko bayan gida ta kanani fa?"
Murajşu yai numushi ya ce, "Ai sai dai kiyi
komai anan inda kike'.
Kamar yadda Muraisu ya fada haka al'amarin
ya kasance, sai da suka kwana biyu a cikin wannan
kogon dutse suna rayuwa.
Tsawon wadannan kwanaki Husnaila na
daure, a jikin bishiyar take kwana, a jikinta take
bawali, Muraisu bai yarda ya kwanceta ba.
A ranar kwana na biyu ne da yammaci daf da
magariba Muraisu ya kwance Husnaila daga cikin
wannan itaciya. Saboda tsananin gajiyar da tayi na
tsayuwa a tsaye, sai ta fadi kasa ta kasa mikewa
zaune.
A wannan lokaci ne tausayin Husnaila ya
kama Muraisu ya dubeta ya ce, "Ki gafarceni ya ke
wannan ma'abociyar kyawu, ki yi sani cewa na ki
kwanceki ne daga jikin wannan bishiya saboda
tsoron kada ki sake yi mini abinda kika yì mini a
baya",
Bisa mamaki sai Muraisu ya ga Husnaila ta
juyo ta dubeshi tayi murmushi sannan ta ce,
"Hakika abinda ka yi min shi ne dai-dai, domin na
tabbatar a wancan lokacin ina jin kiyayyarka a
cikin zuciyata fiye da komai a duniya, amma a
yanzu ka kwantar da hankalinka ka saki jikinka
domin na fahimci, cewa bani da wani masoyi a
duniya sama da kai. Hatta dan uwana da ya
kasance jinina bana jin zai nuna mini irin kaunar da
ka nuna mini a cikin wannan daji".
Koda jin haką sai Muraisu ya yi murmushi ya
ce. "Na san da haka, kuma lallai ni yanzu na
tabbatar da cewa ba za ki cutar da ni ba",
Koda jin haka sai mamaki ya kama Husnaila
ta ce, "Mene ne tabbacinka cewar ba zan ta6a cutar
da kai ba?" Muraisu ya ce, "Saboda tun kafin na
fito nemanki na san cewar idan har muka kwana
uku a cikin wannan daji na Kirzufa sai kin daina
tsanata. Haka bokan mahai fina ya tabbatar mini".
Da jin haka sai Husnaila ta gyada kai tayi dan
tunani sannan ta ce,"Tabbas biri ya yì kama da
mutum. Hakika yanzu na gane cewa dan uwana
Sarki Ishmar ya tsafanceni ne da irin tsafin da zai
sa na tsaneka. Ina fatan yanzu za ka yi mini gafara
bisa abubuwan da nayi maka a baya".
Koda jn haka sai Muraisu ya yì murmushì ya
ce,"Ai duk abinda kika yi mini a baya na manta da
su, domin inda abin na raina ba zan biyoki nan
cikin kogon birimika ba na ceci rayuwarki."
Haka dai Muraisu da Husnaila suka yi ta hira
har dareya fara babu alamar jin barci a cikinsu.
Da lokacin cin abincinsu ya yi sai Husnaila ta
ki cin abincin da hannunta ta ce sai dai Muraisu ya
ciyar da ita da hannunsa.
Al'amarin da ya matukır baiwa Muraisu
mamakí ke nan.
Ba tare da gardamar komai ba kuwa Muraisu
ya fara ba ta abíncin da hannunsa.
Koda fara ba ta abincin sai ya ga ta kura masa
idanu tana murmushí tana yi m asa wani irin kallo
fnai nuna tsantsar kauna a zuci..
Haka daí Muraisu ya ci gaba da ciyar da
Husnaila har saí da ta koshi sarnnan shima yasa
hannu don ya ciyar da kansa. Sai tayi caraf! ta rike
hannunsa ta fara cíyar da shí da hannunta. Saí da ta
tabbatar ya koshí sannan ta bashi ruwa ya sha,
ítama ta sha.
Maimakon ta tashi daga kusa da shi ta koma
can gefe daya ta kwanta, saí ta kwanta daf da shi ta
dora kanta a cínyarsa tana kallon fuskarsa tana
murmushi irin wanda ke kuantar da hankalin
masoyi.
Shima sai ya kura ma ta idanu, tsawon 'yan
dakiku dayansu bai ce uffan ba. Daga can sai
Husnaila ta dubi Muraisu ta ce, "Yanzu me ka tsara
mana a rayuwa?"
Koda jin wannan' tambaya sai Muraisu ya yi
ajíyar zuciya sarnnan ya ce, 'So nake gobe da
sassafe mu bar wannan daji mu lafi izuwa birninmu
Domin a daura nana aure mu fara sabuwar rayuwa
la jin dadi da kwanciyar hankali",
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa
llusnaila, al'amarin da ya matukar baiwa Muraisu
mamaki ke nan, ya dubeta cikin tsananin damuwa
ya ce, "Ina dalilin zubar da wannan hawayc naki?"
Husnaila tayi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ina JI a
jikina Cewa abu nc mawuyaci mu yi rayuwa mai
tsawo ni da kai.
Ka tsaya ka yì tunani, a halin yanzu mutanen
birninku suna cikin tashin hankali na shirye-shiryen
yaki da za a yi.
Shin za su tsaida hankalinsu ne akan shagalin
bikinmu ko kuwa akan shirin yaki?
Shawarar da zan bamu ita ce, kawai mu
daurawa kanmu aure anan cikin dajin Kirzufa tun
kalin mu koma can birninku a fara yaki. Ka ga ke
nan da mun je sai mu fuskanci yakin a ci gaba da
tanadin yadda zaa fuskanci abokan gaba".
Lokacin da Muraisu yaji wannan shawara sai
ya yi shiru yana tunanı har izuwa tsawon yan
dakiku, daga can sai ya yi ajiyar zuciya ya dubi Husnaila ya ce, "Na yarda da shawararki, lallai idan
-gari ya waye za mu daurawa kanmu aure".
Koda jin wannan batu sai IHusnaila ta kamu da
tsananin farin ciki ta mike Zaune ta rungume
Muraisu ta kwanta akan kirjinsa, suka ci gaba da
hira a haka cikin murna da tsintar kansu a
Cikin sabuwar rayuwa wacce basu taba jin ba duk
su biyu.A haka barci ya sacesu basu sani ba.
Kashe garí kuwa da sassafe Muraisu da
lusnaila suka tashí daga barci,
Da yake IHusnaila ta fara tashi sai ta kwabe
kayanta ta shíga cikin wannan korama tayí wanka.
Bayan la fito ne daga wankan Muraisu ya farka.
Ba tare da įin kunyar komai ba kuwa IIusnaila
ta zauna ta goge danshin jikinta da kyallen mayafi.
Koda ganin haka sai shíma Muraisu ya kwabe
kayan jikinsa ya fada cikin koramar ya yi
wankansa sannan ya fito ya goge danshin ruwan,
amma bisa mamaki sai Husnaila ta ga Muraisu
yana sunkuyar da kansa kasa cikin alamun kunya,
ya kasa dago kaí ya kalleta,
Al'amarin da ya malukar bata manaki kc nan,
ta dubeshi ta ce, "Ya kai masoyin raina, ina dalilin
da ya sa ka ke dukar da kanka kasa baka son ka
kalli kyakkyawar surar jikina?",
Muraisu yai shíru kamar ba zai ce komai ba,
daga can sai ya ce, "Ya ke abar kaunata kiyi sani
cewa kunya na dagą cikin alamun karamci da sanin
yakamata.
Ilusnaila za ta fadi abu ne mai saukin gaske wanda
ba zal yi wuyar nemowa ba.
Koda llusnaila ta ga alamun camuwa a tare da
Muraisu sai ta sake bushewa da dariya sannan la
ce, "Kada ka damu ya kai masoyina, ka sani cewa
abin kunya ne a ce sadakin aurena abu ne mai sauki
a matsayina na kyakkyawar macen da babu
kamarta a wannan nahiya lamu, kuma wacce a ta
auri sadaukin da babu kamarsa yana da kyau mu
barwa dan da zamu haifa abin alfahari, abin tarıhi".
Koda IIusnaila tazo nan bayaninta, sai
Muraisu yaji dukkan tsoro ya kau daga zuCiyarsa,
wani irin gagarumin karfi ya shigeshi, kawai sai ya
mike tsaye ya dubi Husnaila ya ce, "Tabbas yanzu
zan je na kawo miki wannan sadaki".
Husnaila tayi murmushi ta ce, "Ina yi maka
fatan nasara da dawowa lafiya".
Gama fadin hakan ke da wuy a sai Muraisu ya
juya da baya ya fice daga cikin kogon dutsen ya
nausa cikin dajin Kirzufa yana farautar tsohon
Zaki.
Sai da Muraisu ya shafe sa'a biyar yana
farautar neman tsohon Zaki amma bai ga koda
macen Zaki ba. Al'amarin da ya girgiza hankalinsa
ke nan. Abinda ya matukar bashi mamaki shi ne,
duk dabbar da ta hangoshi komai girmanta sai ya
Ga ta ratse ta bashi hanya, ko kuma ta koma da
baya. Wata ma ta tsre da gudu kamar dodo ta gani.
Abinda bai sani ba shí ne, duk mutumin da ya
kwana uku a cikin dajin Kirzufa, duk halittar da ke
cikin dajin tsoronsa take ji.
Haka dai Muraisu ya cí gaba da yawo a cikin
dajin Kirzufa har ya gaji sosai ainun guiwarsa tayi
sanyi kuma hankalinsa ya kara dugaunzuma domin
Idan ya koma wajen Husnaila bai san abinda zai ga
ya ma ta ba.
Cikin sanyin jiki ya juyo da baya domin ya
koma can cikín kogo inda ya baro Husnaila. Ba
zato ba tsammani sai kawai Muraisu ya ga wanı
Jibgegen Zaki a gabansa bisa wani katon dutse.
Koda Zakin yai arba da Muraisu sai ya tsaya cak!
Suka kurawa juna idanu suna nazari.
Shi dai Muraisu murna ce ta kamashi saboda
ganin cewar Zakin tsoho ne tukuf, irin wanda yake
ncma.
Shi kuwa Zakin ya tsoro ne ya kamashi domin
yana kallon Muraisu ya ga shima Zakin ne irinsa
kuma ya ninkashi biyu a girma.
Ashe sirrin dajin shi ne, idan har bil'adama ya
kwana uku -a cikinsa to duk dabbar da ke cikin
dajin da ta ganshi sai ta ga ya zama irinta kuma ya
fita girma da kwarjini.
Ya yin da tsohon Zakin ya ga Maraisu ya
durfafoshi ya hawo kan wannan dutse da yake bisa
sai Zakin ya juya da baya ya soma tafiya da sauri-
sauri.
Koda ganin haka sai shima Muraisu ya kara
sauri. Koda Zakin ya waigo ya ga Muraisu na sauri
sai shi kuma ya fita da gudu.
Wohoho! Nan fa aka kasa tsere tsakanin
Zakin da Muraisu. Duk sa'adda Zakin ya waigo sai
ya ga saura kiris Muraisu ya cinimasa.
Koda suka iso karshen dutsen sai Zakin ya yi
turjiya ya tsaya cak! Saboda gabansa wani rami ne
mai tsananin zurlin tsiya. Duk abinda ya fado
izuwa kasa sai dai ya zama gawa.
Masu iya magana sun ce, "Abinda ya koro
Bere daga Rami ya fada wuta, to labbas abin yafi
wutar Zafi!
Lokacin da Zakin ya leka ksan wannan rami
ya ga zurfinsa sai ya juyo da baya ya fuskanci
Muraisu ayi duk abinda za a yì.
Bayan sun yiwa juna kallo na isawon 'yan
dakiku sai kowannensu ya daka tsalle suka
rungumi juna a sama suka rikito kasa saka kaima
kokawa da birgimą. Muraisu ya shiga kokarin zaro
wata wuka a kugunsa domin ya lumawa Zakin, shi
kuma Zakin sai ya dinga turmusheshi yana kai
masa yakushi da cizo. Nan fa kowanncnsu ya kasa
samun nasarar komai.
Sai da suka shafe lokaci mnai tsawo suna
tumurmusa juna akan dutsen, duk sa'adda Zakin ya
karci jikin Muraisu ko ya cijeshi sai yaji kamar
dutse ya gatsa, ko kwarzancwa baya yi. Abinda ya
dugunzuma hankalin Muraisu shi ne, ya fara jin
alamun gajiya amma shi Zakin ko kadan bashi da
alamun gajiya.
Suna cikin wannan gumurzu ne Zakin ya
danne Muraisu kuma ya cafi wuyan Muraisu đa
hakoransa yana kokarin gatsawa. Kaifin hakoran
Zakin ya kasa huda wuyan Muraisun, amma kuma
sai Muraisu yaji ya shaku ainun.
Nan da nan idanunsa suka kada suka yi jawur,
kuma suka yi luhu-luhu kamar za su fado kasa.
Nan fa ya fara kakarin mutuwa, kafin ya
ankara ya suma.
Koda Zakin yaji gaba daya jikin Muraisu ya
sandare baya motsi sai ya yi wurgi da shi domin a
zatonsa ya mutu, don haka sai Zakin ya juya da
baya domin ya sauka daga kan dutsen.
A dai-dai wannan lokaci ne Muraisu ya
farfado daga dogon suman da ya yi. Koda ya bude
idanunsa ya hango wannan Zaki......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.