Complete Hausa Novels

Busa A Mutu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Busa A Mutu Part 2 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 6

Topah Wannan Zaki Ya Firgitani ta yadda bazan iya cigabaa da typing yanzu ba

Sbd haka sai Kuma wani lokaci...
BUSA A MUTU
Littafi Na Biyu (2)
Part E.
Takun Karshe
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke magana

Marubucin yaci gaba da cewa...

A DAI-DAI WANNAN LOKACI NE MURAISU YA
FARFADO DAGA DOGON SUMAN DA YA YI. KODA YA BUDE
IDANUNSA YA HANGO WANNAN ZAKI SAUKA DAGA KAN DUTSEN, SAI YA MIKE ZUMBUR YA RUGA
DA GUDUN TSIYA IZUWA KAN ZAKIN.
Kafin Zakin ya waigo tuni ya daka tsalle ya
dira a gadon bayansa, kawai sai ya shake wuyan
Zakin da hannayensa biyu, suka kama mirgin-
mirgin akan dutsen. Zakin ya yi iya kokarinsa akan
ya kufce daga hannun Muraisu amma ya kasa. Suna
cikin mirgi-mirgin akan dutsen nan suka rikito kasa
izuwa cikin wannan rami mai tsananin zurfin tslya,
Da Zakin da shi Muraisun sai suka hau ihu da
kururuwa bisa ganin hallaka muraran.
Tun a saman duk su biyun suka sume saboda
karfin iskar da ke kadawa wacce ta hanasu yin
numfashi. Ba su iso kasan ramin ba sai bayan cikar
rabin sa'a. In da Muraisu ya yi sa'a shi ne akan
Zakin ya fado. Ta ke gangar jikin zakin ta dagwar
gwaje, shi kuwa Muraisu sai ka farsa ta hagu ta
karye. Kansa ya bugu da jikin kan Zakin ya tsage
jini yai tsartuwa ya baje a kasa sumamme
Al'amarin Husnaila kuwa ya yin da taga
Muraisu ya shafe sa'oi shida bai dawoba cikin
kogon da ya barta sai hankalinta ya dugun zuma
ainun ta kasa zaune ko tsaye don haka sai ta fita da
gudu daga cikin kogon dutsen ta bazama a cikin
dajin na Kirzufa tana gudu da waige-waige tana
kwalawa Muraisu kira. Sai da ta shafe sa'a biyu
cur! tana yawo a dajin ba ta ga Muraisu ba ba ta ji
duriyarsa ba ya z:amana cewa ta gaji ainun da kyar
take iya tafiya tana hada kafafu tana tangadi
tamkar wadda ta sha giya ta bugu.
A haka ta hau kan wannan dutsen wanda
Muraisu da Zakin suka yi gumurzu akai. Tana isa
kan dutsen ta tsugunna kasa tana haki.
Kwatsam! Sai ta yi arba da guntun igar
Muraisu. Cikin rarrafe taje ta dauki guntun rigar ta
fashe da kuka ta aiyana a ranta cewa lallai Muraisu
ya fado kasan wa inan ami ya hallaka.
A haka dai ta mike tsaye ta karasa karshen
dutsen ta leka kasa sai ta ga ba ta iya gano abinda
ke can kasan saboda nisa. A guje ta juyo da baya ta
sauko kasan dutsen ta ruga inda wannan rami yake.
Husnaila tayi ta gangarawa kasa da gudu har
ta iso cikin wannan rami inda tayi arba da gawar
Zaki ta ga Muraisu kwance akan Zakin jini na zuba
daga kansa ko motsi baya yi.
Husnaila ta cuma uban ihu ta ruga izuwa kan
Muraisu ta ru:igumeshi ta fashe da sabon
matsanaicin kuki domnin à zatonta Muraisu ya
mutu. Tana cikin wannan hali ne taji Muraisu ya yi
dogon ajiyar num fashi.
Cikin tsanar in farin ciki ta ciro salkar ruwa ta
sa masa a baki yi kama kwankwada. Husnaila dai
ba ta san sa'adda ta bushe da dariyar farin ciki ba.
Ai kuwa Muraisu na gama shan ruwan suka sake
rungume juna.
Husnaila tayi sauri ta janye jikinta daga cikin
na Muraisu ta kama gefen rigarta ta yagi kyalle ta
daure kansa don tsaida jini. Kawai sai ta dubi
Muraisu ta
"Idan za ka iya ka cire kan wannan
Zaki ka bani yanzu domin an karba ka zamo
cikakken mijina".
Ba lare da gardamar komai ba Muraisu na
daga zaune ya ciro wukar da ke daure a kugunsa ya
yanke kan Zakin ya mikawa Husnaila. Tana karba
sai ta soke kan Zakin a jikin mashinta sannan ta
dubi Muraisu ta ce, "Tashi mu tafi can kogonmu".
Maimakon Muraisu ya mike tsaye ko ya ce
wani abu sai ya nunawa Husnaila kafarsa.
Take ta ga cewar kafar tasa ta hagu ta fara
kumbura. don haka sai ta gane cewa ya samu
karaya.
Husnaila ta mike tsaye ta samo itatuwa
sannan ta zo ta gyarawa Muraisu karayarsa ta daure
Rafar da itatuwa da tsummokara. Wannan gawar
Zaki kuwa sai tà zamo abincinsu, domin wuta ta
hada ta gasa naman Zakin wanda tuni ma ya
dagargaje.
A cikin wannan ramí suka kwana har suka
more anarcinsu duk da cewa Muraisu na đauke da
karaya a kafarsa.
Sai da suka shafe kwana ashírin da daya a
cikin wannan rami Husnaila na jinyar Muraisu
kuma kullum ita ce take zuwa ta nemo musu abinci
da ruwan sha sannan Muraisu ya warke sumul suka
yi shiri suka fita daga cikin dajin Kirzufa.
Bayan sun yí nisa da baro cikin dajin Kirzufa
da kamar tazarar tafiyar zango biyu sai kawaí suka
yi kicibus da mutane uku a gabansu.
Ba wasu bane wadannan mutane face Barde
Kurzal, kuyanga Sabirat da boka Rufyan. Koda
suka yi arba da juna sai dukkanínsu suka cika da
tsananin mamaki, Sabirat ta ruga da gudu za ta
rungume Muraisu sai Husnaila tayi sauri ta sha
gabanta ta tsaí da ita ta ce, "Babu wata mace da za
ta sake ta6a jikin mijina".
Koda jin haka sai Sabirat ta zube kasa ta ce,
"Tuba nake ya gimbiya, ki gafarceni".
Nan take Muraisu ya baiwa su boka Rufyan
labarin duk abinda ya faru tsakanińisa da gimbiya
Husnaila a cikin dajin Kirzufa a tsawon kwarakin
da suka shude da rabuwarsu da su, sannan ya
tambayi boka Rufyan dalilin da ya sa suka ci gaba
da zaman jiransu har izuwa wannan lokaci alhalin
ka'idar lokacin da aka diba ta wuce?
Koda jin haka sai boka Rulyan yai murmushi
ya ce, "Ai na yi bincike ne na sm ai nasarar ganowa
kuna raye baku mutu ba,"
Koda jin haka sai boka Ruíyan yaí murmushi
ya ce, Yanzu bani labarin gida. A wanne hali
mahai fina da jama'arsa ke ciki?"
Koda jin wannan tambaya sąi boka Rufyan ya
hade fuska ya ce, "Bani da amsar wannan tambaya
a yanzu domin ban san komai ba sai dai ka yi
hakuri har mu isa can birnin Liruf inda za a yi
gagarumin bikin aurenka da gimt iya Husnaila".
Muraisu ya ce. "Bani da bukatar wani bikin
aure, ni dai kawai burina shi ne na isa gida lafiya
na iske mahaifina a raye kuma Ina sami damar
yin
wannan gagarumin yaki da za ay da abokan gaba".
Ba tare da 6ata lokaci ba su Muraisu suka
kama hanya suka durfafi birnin Lairus. Bayan sun
shafe tafiyar kwana da kwanaki ba tare da
fuskantar wata matsala ba gami da taimakon
gajarce nisan tafiyar da karfin s hiri sai su yarima
Muraisu suka iso birnin Lairus da farkon dare.
Tụn daga nesa suka jiyo sautin busa kaho da
tambura.
AA Misau ke magana Kawai sai yarima Muraisu ya fashe da
matsanaicin kuka domin ba a busa Raho da daddare
a cikin birninsu face an yi babbar mutuwa. Tabbas
yaji ajikinsa cewa Sarki Samral ne ya mutu.
Koda ganin Muraisu yana kuka sai su ma su
boka Rufyan suka kama kukan. Itama gimbıya
Husnaila sai ta rungume Muraisu a lokacin da ta
kamu da tausayin sa ta fashe da kuka.
Lokacin da su yarima Muraisu suką iso kofar
birnin Lairus sai suka iske kofar garin a kulle ruf
sai da suka kwan kwasa aka leko kuma aka haska
fuskokinsu aka shaida su sannan aka bude musu
kofa suka shiga.
Suna shiga cikin garin suka iske garin wayam
domin gaba dayan jama'ar sun tafi fada.
Babu kowa ma a kofar garin daga cikin face
Dakarun yaki nasu yawa don tabbatar da tsaro.
Su yarima Muraisu suka iso fada inda suka
iske ana bikin binne gawar Sarki. Koda jana'a suka
hango yarima Muraisu tare da amaryarsa sai aka
rugo gareshi gaba daya cikin tsananin farin ciki
bisa murnar ganin dawowarsa.
A wannan lokaci Muraisu ya daina kuka
amma hawaye na sartu akan kumatunsa.
Nan dai aka ci gaba da bikin binne Sarki.
Bayan an gama binne gawar Sarki Samral ne kowa
ya watse sai yarima Muraisu da gimbiya Husnaila
suka rungume kabarin Sarki Samral suka ci gaba da
zubar da hawaye, basu bar wajen ba saí da dare ya
raba sosai sannan suka mike suka tafi izuwa cikin
gidan sarautar.
Kashe gari da sassafe fada ta sake cika ta
batse aka dora Muraisu akan karagar mulki. Nan
lake Muraisu ya mike tsaye ya yi dogon jawabi ga
jama'ar birnin Lairuf kuma ya tabbatar musu da
cewa zai tafiyar da harkokin mulki kamar yadda
mahaifinsa ya yi kuma zai ci gaba da shirye-shirye
don tunkarar gagarumin yakin da ke gabansu.
Haka kuwa al'amarin ya kasance Sarki
Muraisu ya sa aka ci gaba da tanadin makaman
yaki kuma kullurn ana baiwa Dakaru sabbin dabaru
da horo na yakí har tsawon wata bakwai. A wannan
lokaci ne gimbiya Husnaila ta sami juna biyu ta
shiga laulayi.
A ranar da juna biyun ya cika wata takwas ne
babban bala'i ya zo birnin Lairuf domin kawai
wayar gari aka yi aka ji duwatsun wuta da
kibiyoyin wuta na fadowa cikin garin. Nan da nan
garin ya hautsine mutane suka firgice aka kama
iface-iface da guje-guje.
Nan da nan labari ya riski Sarki Muráisu
cewar abokan gaba ne suka iso AA Misau ke magana Nan da nan Sarki Muraisu ya yi damara ya
kwashi dukkan kayan yakinsa.
A dai-dai wannan lokaci ne ciwon nakuda ya
kama gimbiya Husnaila al'amarin da ya matukar
dugunzuma hankalin Sarki Muraisu ke nan ya rasa
abinda zai yi.
Kawai sai Sarki Muraisu ya tura aka kirawo
wadansu zaratan samari sadaukan gaske su dar
bakwai ya hadasu da malarsa gimbiya Husnaila
tare da wadansu mata tsofaffi da yara wadanda
gaba dayansu adadinsu ya kai dubu uku. Sarki ya
dubi wadannan zaratan samari ya ce, "Ga matata da
wadannan mata da yara na baku amanarsu. Duk
yadda za ayi komai RINTSI DA TSANANI ku fitar
da su daga cikin garin nan ta bayan gari.
Kada ku ajiye matata a ko ina sai a bakin dajin
Kirzufa, na yi imanin cewa matata za ta iya shiga
cikin dajin Kirzufa tayi rayuwa a cikinsa koda ita
kadai ce.
Sauran wadannan mata da yara kuwa ku yi
gudun hijira da su izuwa wata kasar dabam. Mu
kam zamu je mu fuskanci abokan gaba yanzu.
Ko za a karar damu gaba dayanmu ba zamu ja
da baya ba, dole ne mu tsaya mu kare mutuncin
kasarmu da jama'armu".
Koda gama wannan jawabi sai Sarki Muraisu
ya sallami wadannan zakwakuran zaratan samari
da tawagarsu suka tafi da su gimbiya Husnaila ba
tare da Husnaila ta sami damar yin bankwana ba da
mijinta Muraisu domin a wannan lokaci ba ta cikin
haiyaçinta sakamakon ciwon nakudar da take ciki.
Sarki Muraisu da sauran dakarunsa suka yi
hawa suka nufi kofar gari har a sannan ba a daina
harbo kibiyoyin wuta ba izuwa cikin birnin ba.
Koda Sarki Muraisu ya ga yadda gidajen jama'a
suka kama da wuta suka AA misau ke magana babbake kuma ya ga
gawarwakin jama'ar birjik a ko ina a kasa sai
takaici ya kamashi hawaye ya zubo masa.
A sannan ne ya tabbatar da cewa maganar
boka Rufyan ta tabbata gaskiya. Nan take Muraisu
da dakarunsa suka daga garkuwoyin su sama suka
rinka kare kibiyoyin da ake harbo musu.
A haka aka bude kofar birnin suka zaburi
dawakansu suka tasamma abokan gaba.
Kaico! Idan mutum ya ga yawan abokan gaba
akan yawan su sarki Muraisu dole ne ya tausaya
musu domin sun ninkasu sau uku.
Koda su Sarki Muraisu suka badu da su Sarki
Ishmar sai akakacame da azababben yaki.
Ana cikin gumnurzun ne Sarki Muraisu ya ga
dan uwansa Huraisu da sarkí Ishmar sun taso masa
su biyu a lokaci guda.
Ai kuwa sai ya tare su da dakakkíyar
zuciyarsa suka ruguntsume da azababben yaki ya
wanzu yana mai kai musu SARA DA SUKA cikin
tsananin zafin nama suma haka. Shí kansa Sarki
Muraisu ya san cewa sarkin yawa ya fi sarkin karfi,
amma sai ya jajirce iya karfinsa ya ci gaba da
wannan yakin ba tare da tsoron komai ba.
Duk da cewa Ishmar da Huraisu sun hada
karfi don su hallaka Muraisu sai ya zame musu
alakakai har ya sari kowannensu sau biyu. Koda
suka ga ya yi musu wannan rauni sai suka kara
zage dantse suka afko masa da dukkan karfinsu.
Da yake karfin sihirinsu da na sa ya zo đaya
sai kowannensu sihirinsa na tsafi ya lalace ya daina
aiki don haka sai suka ci gaba da yaki da tsagwaron
karfin dantse da kwarewa.
Idan mutum ya ga yadda ake ragargazar
dakarun birmin Lairuf suna zubewa kasa matattu
dole ne lausayi ya kamashi har ya zubar da hawaye.
Lokacin da Huraisu da Ishmar suka kara zage
dantse alkan Muraisu sai suka samo lagonsa suka yi
ta lafta masa sara, suka yi kaca-kaca da sassan
Jikinsa Jiri ya kwasheshi ya fado daga dokinsa ya
baje a kasa malacce.
A wannan lokaci ne aka busa kahon samun
nasarar yaki. Yarima Huraisu da Sarki Ishmar suka
cika da tsananin farin ciki.
Nan take aka 6alle kofar birnin Lairuf da
karfin tsiya aka kamo mutanen birnin gaba daya
aka tarasu a fada.
A sannan ne aka gano cewa wasu daga cikin
jama'ar garin sun sulale ta bayan gari sun gudu,
domin an ga sawayen dawakansu. Nan take yarima
Huraisu ya jagoranci wadansu dakarun yaki su
dubu arba'in aka bi sawun su gimbiya Husnaila.
Wannan shi ne asalin gudun hijirar da aka yi
daga birnin Lairuf.
Su yarima Huraisu sun riski wannan runduna
ta masu gudun Hijira inda aka kacame da sabon
yaki.
Da kyar da sidin goshi barde Kurzal ya sami
hanya ya gudu da gimbiya Husnaila akan dokinsa a
lokacip da take cikin mawuyacin hali na nakuda
har jini ya fara zuba a jikinta. Shi kansa barde
Kurzal a jikinsa akwai saran takobi sama da guda
ashiri.
Ko ina a jikinsa jini ne ke zuba amma saboda
naci da juriya sai da barde Kurzal ya kai Husnaila
bakin dajin Kirzufa sannan ya fado daga kan
dokinsa ya mutu,
Itama Hsunaila saí ta fado daga kan dokin ta
ci gaba da jan ciki har ta saní darmar shiga cikin
farkon dajin Kirzufa,
A dai-dai wannan lokací ne yarima Suraisu da
sarki Ishmar suka karaso bakin dajin suka hango
Husnaila a kwance tana nakuda
Huraisu ya yunkura zai Sada cikin dajin
Kirzula sai sarkí Ishmar yai wuf ya rikeshi ya Ce,
"Kana shiga cikín wannan dají shí ke nan sai dai a
dauko gawarka,"
Suna ji suna gani Husnaila ta haihu a gabans
ta yanke cibi da hannunta kuma ta gyara jikinta,
Nan take bakin ciki ya turnuke Sarki Ishmar
ya fashe da kuka ya dubi husnaila ya ce, "Ya ke
'yar uwata hakika kin cuceni.
Yanzu kí rasa wanda za ki haihu da shí saí
babban dan makiyina,"
Koda jin haka sai hawaye ya zuhowa husnaila
ta daga jaririnta sama ta nuno fuskarsa ga su
Ishımar ta ce, "Kwarai kuwa ku je ku mallaki birnin
Lairus, amma ku sani cewa komai dadewa wannan
yaro sai ya kurbi birninsa,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.