Buzu Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK2.txt
Chapter 2 of 2
Shafin Farko hoton Sultan ne, wanda ba dan yanayin shekaru da fuskarsa ta nuna ba, sai ka ce Imam Hammad ne, wanda tsananin kamannin har Muhsin da ta baro a gurin Nene.
Ta buɗe ɗaya shafin ta ga hoton wani, shi ma fari tas mai kama da su Sayyid sai dai shi ma babba ne. Kowanne a ƙasa da sunan sarautarsa.
Sai kuma ta shiga wani shafi mai ɗauke da hoton Sayyid a ƙasa an rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. Wani murmushi ya suɓuce mata ta ce "Ka fi kowa kyau a cikin album ɗin nan Shugabana." Ta furta cikin murmushi. Hotunan wannan matasan da suka yi wa girki a gidan Sultan su ma kowanne da sunansa a ƙasa. Amma a farkon sunan kowanne da Imam.
Nana ta din ga mamakin to kowa ma Imam ne kenan?.
Muryar Asal ta jiyo sun nufo cikin falon, ta hanyar da take kyautata zaton a nan turakar Imam take, kuma tana tunanin É—aya hanyar sashen Asal za ta mayar da kai, kai tsaye.
"Imam, wai ina zobenka ne?"
Ta yi maganar tana É—ago hannunsa, Nana kuma tana hango su daga inda take zaune.
"Ya karye yana gurin gyara"
"Gurin gyara kuma Imam? Ya za a yi dakakkiyar azurfa kamar wannan a ce ta karye? Ka san fa muhimmancin da zoben nan yake da shi a gurinka, ya za a yi ya karye?"
Daidai lokacin suka ƙaraso tsakiyar falon, ya ce "Zobe ya ɓata ban san inda yake ba, ina fatan kin gamsu yanzu. Kar ki sake yi mini maganarsa.
Yanzu zan fita, kar ki manta da saƙona"
Sai a lokacin suka ga Nana da ke zaune a cikin falon.
"Me ki ke yi a nan?" Asal ta tambaye ta.
"Babu komai, gyra É—akin na yi"
"Kuma sai ki nemi guri ki zauna sai ka ce ɗakinki? Imam yana da baƙi anjima, za ki sake dafa wani abin, kuma za su sha shayi, ba na son wauta ko makamancin haka" Nana ta jinjina kai ta kalle shi ta ce "Barka da yammaci Sayyid, in sha Allah zan yi"
Asal ta É—an yi shiru tana nazari jin ta kira shi Sayyid ba Imam ba.
A ɗan corridor ɗin ta tsaya tana zancen zuci, jin ana maganar zobe. Wane zoben kenan? Ko dai zoben da ya ɗauka ya ba ta ne? A'a ba ta tunanin haka wataƙila dai wani abin ne daban.
Gyaran murya da ya yi da ƙamshin turaren da ya cika gurin ne ya sanya ta farga ta waiwaya, sai ta ga a kan hanya ta tsaya.
Ta yi taku biyu ta ba shi guri, ya saci kallonta, zuciyarsa ta din ga raya masa son sanin wace ce ita, sanin na sosai ya yi mata tambayoyi game da wasu abubuwa.
Ya haÉ—iye yawu ya zo zai gifta ta, wani irin daddaÉ—an sanyi ya ratsa shi, sanyin da zai yi fatan dauwwama a cikin sa, saboda yadda ya saba da zafin jikinsa, wanda duk sanyin da yake guri, a cikin jikinsa yake jin wannan zafin.
Sai dai wannan sanyin da ya ratsa shi, har cikin ƙashinsa ya ji sanyin.
Ya sake waiwayawa ya kalli Nana, amma ya ga shi take kallo. Ji yake tamkar ya koma da baya ya ƙara samun kusanci da ita, sai ya fi jin sanyin sosai da sosai. Tun da Allah ya jarrabe shi da ciwon nan, bai taɓa jin sanyi mai daɗin wannan ya ratsa shi ba, kuma ya yi imani da Allah daga jikinta wannan sanyin yake, saboda sun samu kusanci sosai da sosai da zai gifta ta.
"Allah ya sa ba wani abin ake kuma shirya mini ko wani tarkon ake shirin yi mini da ke ba" Ya yi maganar a zuciyarsa.
Nana ta yi mamakin dalilin da ya sanya shi tsayawa haka.
Zuciyarsa ta din ga raya masa ya koma da baya, daf da Nana, ko zai fi kin sanyin yadda yake so.
AREWABOOKS
Nana ta ce "Sayyid ko wani abu ka ke buƙata ne?"
Sai da ta yi maganar sannan ya farga, bai ce mata komai ba kawai ya fice ya bar gurin.
****
Shukura ce a zaune ta takure jikinta, tana kallon kwanon abincin da aka kawo mata, Abinci mai rai da lafiya sai dai ko sha'awar kai wa bakinta ba ta yi ba, duk da uwar yunwar da take ji, tamkar ta ci babu.
Shiru ta yi tana tuna yadda bayan fitowarta daga Asibiti suka yi karo da wani mai adaidaita sahu.
Ya fito yana jarabar sai ta biya shi, duk da shi ne da laifi, amma ta kasa fitowa daga motar, ta sauke gilas ta ce ya gaya mata dammage É—in nawa ta yi masa ta biya shi. Daga sauke glass É—in nan ba ta sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa da ta yi ta ganta a wannan É—akin, da sai dai a zuro mata abinci kawai.
Ba ta iya banbance adadin lokacin da ta kwashe a gurin ba, sai dai ta kintaci lokacin salla ta yi.
Babu tsammani ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, hakan ya sanya ta kalli ƙofar da sauri.
Sai dai hasken fitilar mai wayarya haske mata ido, ba ta iya gane waye ba.
Sannu a hankali ya jingine wayar hannunsa ya zura mata ido.
Duk da ta É—an razana amma abin bai wani ba ta mamaki sosai ba.
Ya zuba mata ido sannan ya ce "Kin yi mamaki ko?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba sosai ba"
"Ko me yasa?"
"Saboda jikina ya daÉ—e da bani hakan"
"Ta yaya kenan?"
"Na daÉ—e ina zarginka ne, sai dai ana ta dankwafe ni, an hanani"
"Gaskiya ne, ban so ki zurfafa ki takura da son sanin abin da bai kamata ki yi ta bibiya sai kin gano ba, amma ban san me ki ka gani ki ka dage kina bin diddigina ba"
"Zarginka nake yi da kai da doctor Sharif na kasa yadda É—a na mutuwa ya yi, saboda har yau ina ji a jikina, mafarkin da na yi gaskiya ne"
Alhaji Zailani ya ce "Haka ne, lokuta da dama mafarki ishara ne, duk da ban san abin da ki ka gani ba, amma zarginki gaskiya ne duk da na yi iya yi na a kan na ɓoye komai, sai dai kashi kin zaƙe Shukura, soyayyar da nake yi miki ba za ta hana ni ɗaukar matakin da ya dace a kan ki ba"
Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Da gaske ka na da masaniya a kan batun mahaifar Mami?"
"Ina da ita, haka zalika ina da masaniya a kan jaririnki ma da ki ke ta zargina da Sharif a kai, duk da ban san me ki ka gani a mafarkin ba"
Shukura ta yi masa wani irin kallo, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.
"Tabbas mafarkinki ishara ne. Amma kafin na yi miki wannan bayanin ina son ki sani, talauci bala'i ne Shukura, babu yadda ban yi a kan na yi yaƙi da shi ba, amma abu ya gagara. Na faɗi na tashi na yi iya yi na amma na kasa nasara a rayuwata. Burina ya gaza cika na mallakar manyan motoci da gidaje da tara manyan kuɗaɗe yadda zan yi nesa da talauci.
'yar makarantar da nake taƙama da ita, abubuwa suka nemi ƙwace mini, bayan faɗuwa a jarrabbawa. A taƙaice dai a makaranta na samu ƙungiyar asiri na shiga, cike da burin na gama makaranta cikin sa'a da fatan cikar burikana na yin arziki mai yawan gaske ta hanya mai matuƙar sauƙi.
Bayan na auri mahaifiyarku, ta haifi Sadik, ƙungiya ta fara neman jini a gurina. Na bayar da babban ɗa na Sadik, na kaɗu na shiga tashin hankali, sai dai hakan ne zai ba ni damar taka babban matsayi a ƙungiyar, duk da na bayar da waɗanda ba jinina ba a ƙungiyar amma na ji zafin bayar da Sadik. Aka haifi Yusuf, aka haife ki, ba a sake neman kowa ba, sai da wata buƙata ta sake taso mini, wadda biyan buƙatar na buƙatar na ƙara taka wani matsayi a ƙungiyar.
Haka na bayar da matata ta fari, Hafsat da tsohon ciki, na saka mata ƙyallen jini a ƙasan shimfiɗarta ta tashi da ciwon naƙuda ta mutu a gurin haihuwa.
Hakan ya sanya dukiyata ƙara haɓaka, na yi kuɗi na yi suna. Duk fafutukar kasuwanci da muke yi tare da Fatuhu, shikaɗai yake abin sa, ni fakewa kawai nake yi da kasuwanci amma ta ƙungiyar asiri nake samun kuɗina.
Duk da ina samu ta kasuwancin ma, amma ga mamakina Fatuhu da baya ƙungiyar asiri, ya fi ni samun kuɗi, kuma duk inda muka je an fi son sa.
Bayan na auri Amina, aka buƙaci duk wani ɗa da za ta haifa, zan din ga ba wa dodon ƙungiya. Lamarin ya yi mini nauyi, saboda ina jin ɗacin rabuwa da iyalina. Na nemi sassauci, sai aka dasa wa Amina wani jaririn aljani a cikin mahaifarta, duk cikin da ta samu ba ma ta sani yake cinyewa. Sai dai kawai ta wayi gari tana zubar da jini, babu ƙaƙƙautawa. Karo shida na shidan saura ƙiris ta rasa ranta, saboda jini take zubarwa ba kaɗan ba, sai dai a yi ta saka mata jini.
Ba a taɓa gane ɓari take yi ba, an zata larura ce kawai, Asibiti aka kasa gane abin da yake damunta, na kuma hana a yi mata na hausa, tana zaune lafiya kawai sai ta hau zubar da jini babu ƙaƙƙautawa.
Ta damu ta damu da matsalar rashin haihuwa, amma na hana ta zuwa Asibiti ta ci gaba da bibiyar lafiyarta.
Ni kaina na damu da wahalar da take sha, sai aka nemi na sadaukar da mahaifarta gaba É—aya ga wannan jaririn aljani, yadda ba sai ta ci gaba da samun ciki ba, cinyewar da yake tana azabtar da ita ba.
Haka na amince, cikin dare ta farka tana ihu da buge-bige, ina kunna fitila na haska, na ganmu a cikin jini male-male.
Na rirriƙe ta, amma ta fita daga hayyacinta, ihu kawai take tana riƙe mararta, a dole na ɗauke ta muka yi Asibiti, ganin za ta rasa ranta saboda zubar jinin nan. Ta fi kwana uku ba ta hayyacinta, jini kawai ake saka mata.
Aka tura mu scanic, domin a gano musababbin zubar jinin.
Na takurawa mai scanic É—in ya gaya mini me ya gani. Ya sanar da ni babu mahaifa ma a jikinta gaba É—aya, dan haka bai ma gano daga inda bleeding É—in yake ba a scanic É—in, sai dai a ci gaba da bincike.
Abin ya bani mamaki, duk da a cikin ƙungiyar asiri nake, ban taɓa tunanin za a ga abin a zahiri a yi scan a ga babu mahaifa ba.
Na biya mai scannnic kuÉ—i, ya rubuta sakamakon da ba daidai ba.
Muka koma gurin likita, aka din ga bincike ba a gane komai ba. Ita kuwa sai da ta shafe kwana goma ba ta tantance wanda yake kanta, har an fitar da rai da ita sai kuma ta warke.
Na daÉ—e ina tunanin abin da na yi mata saboda son da nake yi mata. Muka tattauna da malamina, da mamakin yadda a scanic É—in aka gane bata da mahaifa ma zata a zahiri bs a za a gane ba.
Sai ya ce mini idan na ce haka na ƙaryata kungiyar asiri gaskiya ce kenan, amma ya aka yi na yadda da kuɗin da nake samu a cikinta, har nake kashe su a zahiri? Ya ce mini dole na san duk yadda zan yi na ci gaba da rufe mata ba ta da mahaifa, dan kar ta ce za ta bi diddigi duk da ko ta bi diddigin babu abin da za ta iya ganowa.
Wannan aljani haryanzu yana rayuwa a cikin Amina, gurbin da mahaifarta take, kan addabe ta da ciwo wasu lokutan, sannan wannan aljani shi ne yake saka ta zubar da jini lokaci zuwa lokaci da take tunanin Al'ada take yi. Wasu lokutan ta zubar da jini fiye da kima wanda take tunanin duk su ne dalilin rashin haihuwarta."
Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.
Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.
Da ƙyar ta harhaɗo kalmomin da ta ce "Kai ka kashe Mummy, kuma ka bayar da mahaifar Mami? Da..da.dama aljani duk zai iya yin irin wannan abin?"
Yayi dariya ya ce "Ki na mamaki ne? Kodayake mutane duk abin da ba a kanmu ya faru ba, bamu fiye yarda ba, nima da fari kasa yarda na yi, abin ya ɗaure mini kai. Sai dai idan ki ka duba, ba a taɓa yi wa Amina aiki ba, kuma babu alamar tabo na tiyata a jikinta, dan haka ta yaya za ta rasa mahaifarta? Aljani muddin za ka yi masa biyayya, ka yi abin da yake so, to zai zama mai biya maka dukkanin buƙatunka. Da su ake sihiri, da su ake jifa, neman shugabanci, ɗaukaka kungiyoyin asiri da makamantansu. Duk wani siddabaru da za a ce miki sun yi ba abin mamaki ba ne ba" Ya yi maganar yana wata 'yar guntuwar dariya.
Shukura ta ƙara rikicewa ta kiɗime. Ta ce "Yanzu Daddy, duk son da mahaifiyarmu ta yi maka kai ka kashe ta? Ga amanarmu da Mami ta riƙe ta kula da mu, ashe dama rashin haihuwarta da ciwon nan na zubar da jini da take yi babu gaira babu dalili, kai ne sila? Kai ka haddassa mata? Yanzu tayaya zaka nemi yafiyar su? Ka rasa imaninka saboda abin Duniya? Kai fa ka kashe su"
Ya ce "No in ji wa? Ai ban rasa imanina ba, ai annabi ya ce duk wanda ya ce La'ila ha illalahu zai shiga aljanna"
Cikin kuka ta ce "La'ila ha illalahu ba ta fatar baki ba Daddy, tayaya za ka shiga aljanna bayan ka kai buƙatarka gurin wanin Allah da ya buƙaci ka saɓa wa mahaliccinka dan ya biya maka buƙata. Me yasa ka ga buƙatar ka ta yi girman da ta gagari Ubangijinka ka dangana ga waninsa"
"Wannan wa'azin naki kin riga kin makara Shukura. Ina da yaƙinin zan tuba kan na mutu, kuma Allah zai yafe mini"
"Wa ya baka garantin ganin nan da awa É—aya ma?" Ta yi maganar tana kuka mai tsuma zuciya.
"Ina da shi, dan ko ciwon kai sai na shekara ban yi ba"
Ya miƙe tsaye yana faɗin "Ki mayar da hankali ki din ga cin abinci, saboda ke da abin cikinki nake sanya ran ku zama sadsukarwar ƙarshe da zan yi a ƙungiya. Sai dai kafin nan, ina roƙon afuwarki ko ba komai ke ma kin ci albarkacin dukiyata. Ɗanki da ki ka rasa ni na yi amfani da shi" Daga nan ya ɗauki wayarsa ya yi gaba abin sa hankalinsa a kwance, kamar bai aikata komai ba.
Wani irin gunji Shukura ta din ga yi tana kuka mai tsuma zuciya, ta din ga fatan ina ma mafarki ne ba gaske ba. Tabbas wannan babbar jarrabawa ce, a ce mutum irin mahaifinta shi ne mahaifinka, gara a ce an haife ka ba ta hanyar aure ba, ko makamancin haka. Amma uba irin Alhaji Zailani ba shi da wani amfani. Duk wata gwagwarmayar sa da faɗi tashinsa a kan iyalinsa ya zama na banza, a dalilin wannan mummunar hanyar mara ɓullewa.
Abubuwan da ya gaya mata sun shallake tunaninta, yanzu yadda ya tafi haka zai je ya ci gaba da rayuwa da Hajiya Amina duk da zaluncin da ya yi mata. Ta ji dama ta ba wa Sagir damar kai ta Asibiti wataƙila da ba a samu damar sace ta ba. Cikin kuka take roƙon Ubangiji Allah ya tona wa mahaifinta asiri, saboda a yadda zuciyarsa ta ƙeƙashe ɗin nan, babu wani abu na rashin imani da zalunci da ba zai iya aikatawa ba.
Can gida Sagir ko abinci ba ya iya ci. Yusra kuwa abin ka da ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, sai ta kwanta rashin lafiya, saboda yadda ta addabi kanta da ɗorawa kanta alhakin ɓatan Shukura, dan cewa take saboda ta dawo gidan Sagir Shukura ta tafi.
Haka Hajiya Amina ma, Addu'a kawai take yi a kan Ubangiji Allah ya bayyana Shukura a duk inda take. Sosai take jin tamkar 'yar cikinta ce ta ɓata, tun tana daurewa har ta kasa ta fara zubar da hawaye, kasancewar babu wani labari mai daɗin ji da zai nuna an kusa gano inda Shukura take.
****
Asal ta na tsaye a banÉ—akin cikin É—akinta, bayan tabattar da Imam baya É—akin, ta danna wata lamba ta kira.
Can aka É—auka mutumin ya ce "Na'am ina jin ki"
"Ina da labari ne"
"Ina sauraren ki"
Ta numfasa ta ce "Hannun Imam babu zobensa na tambari, na tambaye shi ya ce mini karyewa ya yi ya kai gyara, daga bisani kuma ya ce mini bai san inda yake ba"
"Kin tabattar da hakan, ba kuma ɓoye shi ya yi a wani gurin ba?"
Asal ta ce "Eh na tabattar ai zobe ne da ba ya cire shi, tun da ya dawo babu zoben a tare da shi"
Mutumin ya numfasa ya ce "Madalla, ki ci gaba da sanya ido da sanar da ni duk wani abu da yakamata na sani"
Ta jinjina kai tamkar yana ganinta ta kashe wayar ta fita.
Jikin Nana tamkar an yi mata duka, saboda azabar gajiya da ta yi. Ta kammala aikinta tana ta gyaran kitchen, sai ga Balaraba ta shigo da ƙatuwar jarka. Ta ajiye ta ta ce "Gashi nan madarar raƙumi ce da Imam yake sha"
"To sannu da ƙoƙari Mama Balaraba"
Ta ce "Yauwwa kukun Imam, Allah ya taimake ki"
Nana ta yi murmushi ta ce "Kar ki ba ni kunya mana"
"Ba kunya zan ba ki ba, ai ke yanzu duk wata kuku a gidan nan a ƙarƙashinki take, ke kaɗai ki ke dafa abincin da zai ci, dole mu girmama ki saboda kema shugabarmu ce"
"A'a ni ba shugabarku ba ce ba, ni da nake bare ma a cikinku. Amma dan Allah Mama Balaraba wai su wa ake cewa Imam É—in nan ne? Dan na ga wanda ake kira da hakan da yawa"
"Eh su Biyar ne, galibinsu jikoki ne na gidan sarauta, su na cikin jerin waɗanda za su iya gadon kujerar Sultan. Shi Imam Hammad a gidansu su biyu ne da shi da Imam Abdallah, sai Imam Zahradeen shi ma jikan marigayi Sultan ne, akwai Imam Asadullah yayan Asal, sai Imam Omar, waɗannan su ne jerin waɗanda ake sanya ran za su gaji kujerar Sultan. Duk da su na ganin cewa Sultan na yanzu nuna son kai ƙarara na son Imam Hammad ya gaje shi a cikin yaransa. Imam Hammad yana da 'yan uwa da suke uba ɗaya amma su biyu ne suka cika ƙa'idojin zama Imam.
A ƙasar nan ana girmama duk wani Imam fiye da zatonki, mu na ƙasa mu na son Imam Hammad sosai mussaman baƙaƙen buzaye da fararen ke yi mana kallon kamar ba 'yan uwansu ne mu ba, bayinsu ne kawai.
Idan kin lura galibi hadiman gidan nan baƙaƙen buzaye ne, fararen kaɗan ne ƙarara yake ƙoƙarin yaƙi da kyamar da fararen buzaye suke yi mana, yana ta fafutukar nema mana 'yanci, da ƙoƙarin mu ma a din ga bamu dama a cikin shugabanci, bai kamata iyayenmu sun ƙare a bauta mu ma mu ƙare a haka ba. Amma manyan nan ba sa son shi sam, gani suke yana ƙoƙarin hana su rawar gaban hantsi. Ni tun da ya dawo ma duk ya canza mutum ne mai sanyin hali, amma kaifi ɗaya ne, ba sani babu sabo.
Shi ne shugaban majalisar duk Imam ɗin ƙasar nan. Duk da a cikin su akwai wanda suka girme masa, amma a haka dole su girmama shi kamar yadda yake a dokar ƙasar nan.
Tarihin masarautar Agadez yana da yawa da kuma faÉ—i Nana, bari na tafi na je na ci gaba da aikina.
Nana ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai da sosai"
Bayan fitar Balaraba Nana ta naɗe hannunta a ƙirjinta, tana nazari da tunani.
Jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, ta duba kayanta ta lalubo takardar nan da aka kawo saƙon aka ce a ba wa Sayyid. Ta ƙare wa takardar kallo.
"Ko a cikin Imams É—in nan ne wani ya aiko da wannan takardar?" Ta yi maganar tana tuna maganganun da ta ji suna yi ranar da aka kai su yin girki a gidan Sultan. Ta koma ta lalubo zoben gurin Sayyid ta din ga jujjuya zoben ta ce "Ko kai a ke nema ne? Idan kai ne ta yaya zan ba shi abin sa, tun da ban san iya adadin muhimmancin sa a gare ka ba, idan na baka ka manta ni ta yaya zan yi bayani a yarda da ni?" Ta din ga surutai ita kaÉ—ai ta gaji ta nannaÉ—e kayan ta buÉ—e jakar sarkin baka ta watsa takardar da zoben ta rufe ta ajiye a cikin kayanta.
Bayan sallar magariba aka sanar mata baƙin Imam sun iso, su na can sashin karɓar baƙin sa wanda ɗaki ne a can wajen lambun gidan.
A kwanduna ta shirya kulolin Abincin, É—aya daga ma'aikatan gidan, ta taya ta kai wa.
Su na zazzaune a ɗakin, gaban su shaƙe da kayan marmari da uban soyayyen nama.
Duk wannan Imam Imam É—in ne, gaba É—aya zaune a gurin.
Ayabar hannun Sayyid ta kalla, da ya kai bakinsa ya gutsura fuskarsa ɗauke da murmushi. A take ta ga jini yana bin bakinsa, ayabar ta koma baƙa ƙirin, wasu abubuwa masu tsini tamkar ƙayoyi suka tsiro a jikinta.
Ayshercool
08081012143
77
Rikicewa ta yi, amma ta fara ƙoƙarin daidaita nutsuwarta dan ta san idan ta yi wani gangancin a gurin, babu lallai ta sha ta daɗin rai duba da girman mutanen da suke gurin a zaune.
Ganin ta tsaya ta zuba masa ido, ya sanya ya sauke hannunsa a hankali yana kallon ta shi ma.
Ta ƙarasa shigowa a hankali ta ajiye musu kwanukan abincin.
Zuba mata ido suka yi, gaba É—aya suka yi shiru daga hirar da suke yi.
Ta ce "Shugabana, ga abincin ko zan jira ku duba idan da abin da bai yi ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Za ki iya tafiya"
Sai dai ta kasa tashi, ta ci gaba da rarraba ido.
Ya sake cewa "Za ki iya tafiya"
"Dan Allah ka taimaka mini da ayabar hannunka, yunwa nake ji"
Imam Omar ya ce "Imam Hammad, wai wace ce wannan É—in? Ta san waye kai kuwa abin hannunka za ka ba ta?"
Ya kalli ayabar ya kalle ta, bai kai ga yin magana ba, ta saka hannayenta biyu ta miƙa masa.
Tamkar soko haka ya miƙa mata ayabar, ba tare da musun komai ba.
Ya ce "Ga wata nan ki É—auki yadda za ta ishe ki"
Ta girgiza kai ta ce "Wannan kawai ta ishe ni, na gode sosai da sosai"
Duk su ka bi Nana da ido, wasu cike da takaici, wasu kuma mamakin tsaurin idonta, duk da ba abin mamaki ba ne sosai, tun da ba ta san irin girmansu da matsayinsu ba, kasancewarta bare ba ƙabilarsu ba, kuma ba 'yar ƙasarsu ba.
A hankali ta saci kallon hannayensu, sai ta gan su sanye da zobunan nan irin na hannun Sayyid da ya É—auka ya bata.
A take ta koma gefe ta cinye ayabar, sannan ta yinƙura ta tashi.
Imam Asad ya fara masifar wace mahaukaciyar haka, da za ta zo ta yi musu wannan rashin hankalin, su zuba ido su na kallonta.
Hammad ya ce "Ina mai baku haƙuri, baƙuwa ce a cikin lamarin gidan mulki, ku yi mata afuwa"
Nana tuni ta fice daga É—akin, aikuwa fitarta ke da wuya, jiri ya fara É—ibanta, bango ta dafa tana bi a hankali, sai dai kan ta kai inda take so ta yanke jiki ta faÉ—i.
Faɗan Ƙaisar ne ya sanya ta buɗe ido, a matuƙar galabaice.
"Waye ya ce da ki ka karɓa ki ci? Kin san abin da aka yi a jikin ayabar? Ban da na riga na buɗe miki ido ki na ganin abubuwa, da ba zan sake bari ki ga komai a kansa. Sai kin kashe kan ki a banza a kan mutumin nan, gaba ɗaya kin ƙarar da ƙarfinsa a kan ki, wanda ko tabbacin idan ya tuna ki zai miki irin wannan son ba ki da shi"
Nana dai kasa magana ta yi, saboda yadda jikinta yake a mace, duniyar take juya mata.
Ɗaga bakinta ya yi ya zuba mata wani abu mai kama da turiri, ta yi wani yinƙuri ta hau amai ta hanci da bakinta.
Ba ƙaramin galabaita ta yi ba, jin yadda ƙayoyin da suka tsiro a jikin ayabar su na sukar ƙirjinta gurin yinƙurin aman da ta yi.
Cikin fusata mutumin yake magana, "Wane irin wawanci ne haka da shirme da rashin hankali, ta yaya zamu shirya abu ka je ka bari ya ɓaci?"
Cikin damuwa matashin ya ce "Wallahi Tafawa ba laifina ba ne ba, dan har ya fara ci wata yarinya ce ta hana shi ci, wai ya ba ta yunwa take ji"
"Wace yarinyar ce a kaf faɗin Agadez za ta je tsakiyar ku, har Imam zai ci abu ta ce ya bata? Ɗaya daga cikin mugwayen ɗabi'unsa kenan da ya sanya yake zubar da kimar ku a idon mutane maƙasƙanta, har su samu zarafin raina ku. Ban da raini da wulaƙanci har baiwa ta ga abu a hannun Imam na ƙasar Agadez ta ce za ta ci."
Ya buÉ—e baki zai yi magana ya ce "Ka ga tashi ka bani guri ni kafin na mangare ka" Haka ya ja bakinsa ya tashi ya fice jikinsa a sanyaye.
*****
Alhaji Zailani ne a zaune a falon Hajiya Sa'a, ya je yi mata ta'aziyyar mutuwar Abba.
Ya numfasa ya ce "Wai dama Abban ba shi da lafiya ne?"
Ta girgiza kai ta wassafa masa dukkanin abin da ya faru.
Cikin kaɗuwa yake jin bayanin nata. Ya ce "Ban da ke Hajiya Sa'a, ina ke ina gayyato yarinya da rana tsaka ki janyo ta jikinki, ga shi ta zame miki masifa, haba Sa'a. Ke kin san ba kowa a ke fallasawa sirrin ƙungiya ba, Allah ya kyauta, ya yi mata gaisuwa ya tafi.
*****
Hammad tun bayan tafiyar sauran 'yan uwansa yake tunani daban-daban a ransa.
Tuni aka saita masa wayarsa, ya ci gaba da amfaninsa da ita.
Wayewar gari yana ta jiran Abinci amma shiru, ya gaji da jira saboda yana jin yunwa, ya tafi ya tashi Asal da take ta bacci.
"Imam lafiya kuwa?"
"Ba a kawo mini Abinci ba, ina jin yunwa zan fita"
Kamar ta yi tsaki, saboda ta ji daÉ—in baccin, haushi ya kama ta, tare da tunanin uban abin da ya hana Nana tashi ta yi masa girki ko ta makara haka.
Ga shi duk hadiman sashen ta kore su, dan haka ta tashi da kanta, ta fita.
A zaune ta tarar da Nana ta jingina da bango, idanunta duk sun faÉ—a kamar ta kwana tana amai da gudawa.
"Wani wulaƙancin ne ya sanya ba ki tashi kin yi wa Imam girki ba, har ki ka saka na biyo ki nan?"
Nana ta numfasa ta ce "Ba ni da lafiya ne"
"Ba ki da lafiya kuma Imam ba zai ci abinci ba? Kin san ba kowane Abinci yake ci ba"
Wani malulun takaici ya ƙule Nana, wato lafiyarta ba abin da yake gabanta ba ne, kawai fatanta ta yi wa mijinta girki tun da ga baiwa.
"Magana nake yi miki kin yi mini shiru"
"To me zan ce miki, ba ni da lafiya, ai ban taɓa ƙin yin girki ba. Ko wani abu da ki ka saka ni ba, amma yau ba ni da lafiya babu abin da zan iya yi. Idan ke ba za ki yi mini uzuri ba, ki gaya masa kukunsa babu lafiya na san, shi zai iya yi mini uzuri"
A hasale Asal ta buɗe baki za ta yi magana, Nana ta yi mata wani irin kallo, da a dole ta haɗiye maganganun da ta yi niyyar caɓa wa Nana.
Ta haƙura ta juya ta fita, tana tunanin me ta ji ne ko ta gani, ta kasa yi wa Nana rashin mutunci.
Tana komawa ya kalle ta ya ce "Ina Abincin?"
"Wai ba ta da lafiya"
"Me ya same ta?" Ta girgiza kai jiki a mace ta ce "Nima ban sani ba"
Ya so sake wata tambayar, amma sanin halin Asal ya sanya shi ta shi, zai fita.
Ta ce "To ina za ka je ba ka karya ba?"
"Zan samu abin da zan ci, zan je na ga Mahmoud ne" Daga haka bai kuma cewa komai ba ya fita.
Bakin Imam Hammad fal maganganu kamar yadda bakin Mahmudu yake fal maganganu, amma kowanne ya kasa furta wa kowa.
Hammad ne ya numfasa ya ce "Mahmud ina son na koma kan ayyukana, amma Sultan ya ce mini na dakata, akwai abubuwan da nake son yi da yawa."
Mahmoudu ya ce "To ka yi haƙuri, wataƙila akwai dalilin da ya sanya ya ce ka dakata tukuna"
Ya numfasa ya ce "Haka ne, wai yaushe za ka shigo gida ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Ba na son shiga gidan nan naku"
"Saboda me?"
"Kai ma ka sani ai"
Imam ya ce "Ban san komai ba. Jiya Imams sun kawo mini ziyara. Ranar Lahadi za mu yi zagayen raƙuma da shan shayi, ka zo mu je tare"
"Imam, ka na manta waye ni, da ƙoƙarin kai ni matsayin da Allah bai kai ni ba, ni dai dan Allah ka yi haƙuri"
"Mahmoudu, idan ba kai ba wa ka ke so na janyo jikina? Ka san komai fa? Shikenan haka ni zan zauna?" Yayi maganar muryarsa É—auke da rauni.
"Haba jarumin shugabana, ka na fa da wanda ku ka shaƙu, ku ke da kusanci tsakaninku sosai da sosai"
"Waye?" Ya yi maganar yana kallonsa.
"Zan haɗa ku kwanan nan, aure zan ƙara yi maka kwanan nan, ka na son 'yar Nigeria?"
Ƙanƙance idanunsa ya yi yana kallon Mahmoudu. Ya ce "Ga ka nan ga Asal ai"
"Ahh yi haƙuri, kar ka gaya mata sai ta saka a fille mini kai"
Hammad ya yi murmushi yana gyara zamansa.
Sai da Nana ta shafe kwana uku ba ta aikin komai, haka kurum Imam ya ji abin ya tsaye masa ya dame shi, ko ya yi ƙoƙarin mantawa sai ya kasa. Kwanakin nan uku kame-kame kawai yake yi gurin cin abinci, duk abin da zai ci sai ya ga kamar abin zai cutar da shi. Ga uwa uba rashin ɗanɗanon abinci da ba ya ji gaba ɗaya.
Yau da Nana ta lallaɓa ta fito, ta ji ana ta zancen hawan zagayen da za a yi a kan raƙuma.
Har ya yi shirinsa zai fita, ya tarar da Abinci a falo.
Cikin zaƙuwa ya ƙarasa ya buɗe, tabbas ƙamshin girkinta ne. Wani murmushi ya suɓuce masa cike da farin ciki.
Sai dai sam ba su haÉ—u ba.
Har yau jikinta babu ƙwari sosai, bayan fitarsa ta shiga ta gyara abin da za ta gyara, kawai ta nemi guri ta zauna, tana hutawa wani irin bacci ne ya ɗauke ta a gurin.
Ba ta jima da fara baccin ba, sai ga ta a Libraryn Ƙaisar.
Waiwaye ta fara yi taga ta ina za ta gan shi, sai dai ba ta gan shin ba, sai wata guguwa da ta taso, ta watso mata littafin nan da ta ce ba za ta karanta ba. Ta kalli littafin a gabanta amma ba ta motsa ba, ba kuma ta É—auka ba. Kawai littafin ya buÉ—e kansa da kansa, sai mudubin nan ya haska inda ya buÉ—e É—in.
Sayyid ta gani a tsaye a cikin sahara ana ta harbo masa kibiya ta ko ina, Sultan ta ta gani yana ƙoƙarin tare masa, shi ana samun sa da kibiyar. Har ya fara gazawa aka fara samun Sayyid.
Ya na tsaka da tarewar aka janyo shi aka nufi wata wuta da shi, da cin ta yake gwanin ban tsoro. Ba ta iya ganin fuskar wanda yake jan na shi, saboda ya rufe fuskarsa da rawani.
Gaba É—aya Nana ta gigice ta rintse idanunta tana addu'a kar Allah ya ba wa mutumin nasara, can jin shiru sai ta buÉ—e idonta a hankali.
Sai ta daina ganin wancan lamarin, sai wata taguwa da ake ta É—urawa wasu abubuwa.
Sayyid na zuwa ya kama taguwar ya hau, yana hawa ta din ga walagigi da shi, ta nufi kan wani rami da shi. Zumbur Nana ta tashi, tare da miƙewa tsaye a falon. Zuciyarta sai bugawa take yi da sauri.
Waje ta yi da wani irin hanzari, ta nufi inda ake shirya raƙuman da za a yi hawan da su.
Raƙuman duk jajaye ne, an yi musu wani irin ado, ga su ƙosassu.
Gaba É—aya ta ji ba ta yarda da lamarin ba, ta juya ta sake kwasar hanya ta koma sashen su.
Tana zuwa ta ci karo da shi ya fito, sanye da makamanciyar shigar da ya shigo É—akinta bayan auren su.
Takobinsa na soke a gefen ƙugunsa, babbar rigar jikinsa ta sha aiki.
Kallon Nana ya yi, fuskarta ta nuna rama sosai da sosai.
Nana so take ta yi masa magana amma yana tare da Asal da ta sha kwalliya ita ma, sai hura hanci take yi.
Gaba É—aya yanayinta ya nuna masa a rikice take, kuma magana ce a bakinta.
Har za su gifta inda Nana take ya ce "Sayyid excuse me"
Asal ta waiwayo ta kalli Nana jin ta ce masa Sayyid maimakon Imam.
Ya kalli Asal ya kalli Nana, sai kuma ya yi taku biyu ya matsa daf da Nana, ya sunkuyo daidai tsawonta.
Gaba É—aya sauran barorin da suke gurin ma zubo musu ido suka yi.
"Dan Allah kar ka hau Taguwar nan" Ta yi maganar cikin tsoro muryarta har tana rawa.
Ya ɗaga idonsa ya saka a nata, wanda hakan ya rikita ta, tamkar ba ta taɓa saninsa ba.
Bai ce mata komai ba, ya miƙe ya yi gaba. Asal ta bi shi cikin fushi tana tambayarsa "Wai me ta ce maka?"
Ya numfasa ya ce "Da tana son ki ji, ba za ta zaɓi ta gaya mini ba".
"Imam ban gane ba, mene ne abin da ba za ta faÉ—a kowa ya ji ba?"
"Ai kin san duk wanda yake ƙarƙashina, ina ba shi lokacina na saurare shi. Kar ki manta mutumin da yake da Asal doka ba ta ba shi dama a kan wata wadda ba ƙabilarsa ba, mussaman baƙar fata, kin fi kowa sani na, ki daina saka wani abu a ranki dan Allah"
Ya yi maganar daidai lokacin da suka ƙarasa gurin. Daga nesa Nana take hango an ba shi shayi a kofi, ya karɓa ya shanye, an sake zuba masa ya karɓa ya sha.
Aka cika gurin da kaɗe-kaɗe, juyi suka din ga yi tare da sauran 'yan uwansa Imam, su na wasa da takubbansu, gwanin burgewa. Duk da tashin hankalin da Nana take ciki, sai da abin ya ƙayatar da ita.
Aka jero raƙuman nan, suka din ga kama su su na hawa.
Nana gabanta ya tsananta faɗuwa, cike da ƙwarewa ya kama raƙumin nan ya haye.
Idonsa suka sauka a cikin na Nana, fuskarta ɗauke da damuwa, ya lumshe idanunsa ya saita akalar raƙumin nasa, ya wuce gaba sauran suka bi bayansa.
Mutane suka rufa musu baya, suka kama hanyar barin gidan.
Jiki a sanyaye Nana ta koma.
A tsaye ta jingina a gurin girki, tana tunanin abin da ka iya biyo bayan hawan Raƙumar nan da ya yi.
But Asal ta faÉ—o cikin huci, Nana ko motsawa ba ta yi ba sai bin ta da kallo kawai da ta yi.
Har gabanta Asal ta zo tana huci "Uban me ki ka gaya wa Imam, kuma saboda me za ki din ga kiransa da Sayyid? Ban yi miki gargaÉ—i a kan sa ba?"
Nana ta kalle ta, ta ga kar ta yi wani abun da zai sanya ta kore ta a yanzu, dan haka ta sassauta murya ta ce "Haba ya shugabata, Sayyid da Imam duk abu ɗaya ne ai, yana nufin shugaba, mu a Nigeria Sayyid muke cewa, kema idan ki na so sai na kira ki Sayyada. Kuma me Sayyid zai yi da baƙar mace 'yar Nigeria, ai ramin kura sai 'ya'yanta. Kawai ne nemi afuwarsa ne a kan rashin samun gudanar da aikina da na yi, a kwanaki da suka gabata, saboda shi ne ƙa'idar gidan sarauta.
Ki yi haƙuri iya matsayina da aikina nake tsayawa."
Asal ta numfasa tana huci, duk da hankalinta ya É—an kwanta.
"Shikenan na ji, daga yanzu za ki bar É—akin da ki ke, za ki koma É—akin hadimai da ke tsakanin sashen Imam da nawa.
Sannan akwai gurin girki a gurin girki a gurin, yadda za a din ga sauƙaƙa miki, sai dai babu ke babu fitowa a duk lokacin da yake nan, muddin ba abinci ki ka kawo masa ba, kuma ba gyaran sashen za ki yi ba. An dawo da ke sashen nan ne, domin ƙara tabattar da tsaron abincin da Imam zai ci"
Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, na gode sosai da sosai"
"Ki hanzarta, ki kwaso kayanki ki mayar can, a yau ba sai gobe ba, ku yi magana da Balaraba ta kai ki"
Nana ta risuna ta yi wa Asal godiya, haka aka yi, a ranar ta kwashe kayanta ta mayar can ɓangaren, barorin gidan na ta ƙara mamakin, yadda a ke ɗaga likkafar Nana baƙuwar haure sama da su.
Nana kuwa murna ta din ga yi, ganin tana ƙara samun kusanci da Imam, ta san addu'a da take yi ce Allah yake taimakonta, kuma tana fatan Allah zai yanke mata wannan wahalar nan kusa.
Fita ta yi da nufin ta kwaso kayan wancan É—akin girkin ta dawo da su nan, ta ga mutane na kaiwa da komowa a sashen.
Wani ta gani a cikin mutanen fuskarsa rufe da rawani, amma ta ga kamar ta san shi ta taɓa ganinsa, kamar ta bi bayan mutumin, sai ta ji ana faɗin Imam ne ya faɗo daga kan Taguwarsa.!
AREWABOOKS
Nana ta rasa wa za ta nufa ta samu cikakken bayanin abin da ya faru. Ta san za a rina, tun da ta ga abin nan kuma ta din ga ji a jikinta, ta san wani abun sai ya faru.
A can É—aki kuma, sannu Asal ta din ga jera masa, ya jinjina mata kai kawai.
Ya lumshe idanunsa yana tuna yadda Nana ta roƙe shi kar ya hau Taguwar.
"Wace ce ke?" Ya furta a hankali.
Asal ta ce "Magana ka ke yi ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
Tun da ya hau kan Taguwar nan yake jiri, duk yadda ya ƙwarara jikinsa, da ƙoƙarin sarrafata ya kasa, dan daina gani ya yi gaba ɗaya sai jin sa ya yi ya zamo ƙasa.
Ya yi ajiyar zuciya yana sauke numfashi.
"Imam na saka ta dawo ɗakin Hadaimai kamar yadda ka buƙata, ko za ka ci wani abun a kawo maka?"
Ya girgiza mata kai alamar a'a.
"Ina ne yake yi maka ciwo to?"
Ya yinƙura ya tashi ya ce "Babu ko ina salla zan yi"
Yana tangaÉ—i haka ya shiga ya yi salla, ya sake kwanciya.
Nana na ta kai komo falon babu kowa, tana son ta san halin da yake ciki amma babu wanda za ta tambaya.
Wata tawaga ta ga sun shigo sashen, kallo É—aya ta yi masa ta gane Sultan, tana son fita tana jin tsoron kar ta yi laifi, haka ta tsaya tana hangen abin da yake faruwa.
Asal ta fito cikin hijjabi suka gaisa, ta yi wa Sultan jagora zuwa cikin É—akin.
Da hanzari ya nufe shi yana faÉ—in "Hammad, tashi maza a tafi Asibiti"
Ya buÉ—e idonsa ya kalle shi ya ce "Babu abin da yake damuna Sultan, ba sai na je Asibiti ba"
Cikin damuwa ya ce "Me yasa ka yi hawan bayan ka san ba cikakkiyar Lafiya ce da kai ba? Kuma da ka ji ba za ka iya ba ai sai ka haƙura"
"Lokacin da na yi ba na jin komai a jikina, amma tuba nake ba zan sake ba"
Sultan ya ce "Ka tabattar ba ka jin komai a jikinka ba sai mun je Asibiti ba?"
"Ba na jin komai Abie, ka kwantar da hankalinka"
Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, Allah ya tsare gaba ka kwanta ka huta sosai"
Ya jinjina masa kai, suka yi sallama ya tafi.
Duk yadda Nana ta so sanin halin da yake ciki, haka ta haƙura, sai dai bacci mai daɗi ya gagara ɗaukan ta.
Da sassafe ta fita ta hau gyaran sashen, tana jira ko za ta ji motsin Asal, duk yadda za a yi ta tambaye ta, ya jikinsa sai dai ta ji shiru, haka ta ajiye Abincin kari ta koma É—akin da aka ba ta.
Sai wajen sha daya da rabi, ta ji motsi a falon, ta fito ta leƙa.
Shiru ta yi tana kallon mutumin da ya zo, kamar shi ta taɓa gani a gidan cin abincin su Al Hussain. Yana tare da Imam Asad.
Sayyid yana zaune a ƙasan Carfet, shi kuma yana saman kujera.
Allah ya taimaki Nana da Hausa suke magana, ba yarensu ba.
"Kai ya aka yi ka faÉ—o daga kan taguwa, ko ka fara shan wani abu ne ba mu sani ba?"
Asal ta ce "A'a Imam ba ya shan komai, dama ba shi da cikakkiyar lafiya ai"
"Ina magana kina sanya baki?" Asal ta ja bakinta ta tsuke.
Ya mayar da idanunsa kan Hammad ya ci gaba da cewa "Allah ya sauwwaƙe ya kuma kiyaye gaba. Amma ka din ga kulawa dai"
Bai ko É—aga kansa ba, balle ya tanka masa, sai dai jikin Asal ya yi sanyi. Ba ta ji daÉ—in yadda Tafawa ya zarge shi da shaye-shaye ba.
Wuni aka yi zuwa duba Imam Hammad, sai dai ds Yamma Nana na tsaka da gyaran falon ta ga wannan takardar, mai ƙwarangwal ɗin nan yana ci da wuta.
Gaban Nana ya faÉ—i, ta yi shiru tana kallon takardar.
Jikinta ya ba ta kowaye yake yi masa wannan aika-aika yana cikin waÉ—anda suka zo dubiya yau.
Nana tana aiki a kitchen, Asal ta same ta, ta miƙa mata wani ƙulli ta ce "Ga shi nan, ki dafa wa Imam a shayi, maganinsa ne"
Nana ta karɓa ta amsa da to. Ba ta yi tunanin komai ba, ta dafa shayin ta je ta ajiye a falo.
Asal tana zaune tana jiranta a falo.
Ta tashi ta karɓa, Nana ta ce "A yi wa shugaba sannu, ina fatan Allah ya ba shi lafiya ya kiyaye gaba"
Asal ta amsa da Amin a ciki, ta nufi É—akin baccinsu.
Yau Nana kamar ta fasa ihu, ta cika wata guda a gidan Asal, yau gaba É—aya hankalinta yana kan É—an jaririnta.
Ga shi tun da ta zo ba su yi waya ba ko sau É—aya ba.
Haka kwanaki suka ci gaba da shuÉ—ewa, kwana uku Asal na ba wa Nana maganin Sayyid tana dafa masa.
Sai a na ukun yake fitowa ya zauna a falon, amma ba ya fita.
A kai Abincin safiyar kwana na uku, Nana ta haÉ—u da shi.
Cikin girmamawa ta ce "Barka da safiya Sayyid, ashe tsautsayin da ya faru kenan, Ubangiji Allah ya kiyaye gaba."
"Ba ki yi mini sannu ba sai yanzu?"
Ta É—aga kai ta kalle shi, duk ta ji abin wani banbarakwai, amma har cikin ranta ta ji dadin maganar da ya yi mata.
Ta ɗan juya idanunta ta risunar da kanta ta ce "Tuba nake Shugabana, ban samu damar ganinka ba ne, duk da na yi ƙoƙarin hakan, ba na son uwar gijiyata ta ce na zaƙe ne, amma tuba nake Ubangiji Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani "
"Amin na gode sosai. Ina ganin ƙoƙarin da ki ke ta yi, ina yabawa, ki yi haƙuri da Asal kar ki tsane ta, duk da na san tana takura miki wasu lokutan"
"Babu takura a ciki, matuƙar hidima taka ce shugabana"
Ya ce "Madalla na gode sosai"
Ta tashi ta bar falon, a ranta tana cewa ina Asal ta ga kirki, shi da yake hangenta daga nesa ma, ya san tana ƙoƙari, ita kuwa ban da jaraba da uwar hantara da nuna mata ƙyama babu abin da take yi.
Asal ta shirya ta fita tun safe, dan haka Imam ne kawai a sashen.
Da Nana ta tashi kai masa abincin rana, ta sha kwalliya cikin doguwar rigar Atamfa.
Duk yadda yake jin jikinsa babu daÉ—i, yana motsa shi da kyar, amma bai hana shi satar kallon Nana ba.
Ba ƙaramin kyau ta yi ba, ga ƙamshin turaren sa da yake tashi a jikinta.
Ta kalli idanunsa da suka yi jawur, tamkar jini zai zubo daga cikin su.
"Sayyid lafiya kuwa?" Kai kawai ya jinjina ya mayar da idonsa ya lumshe, yana jin wannan ƙarar mara daɗin ji a kunnensa.
Haka Nana ta tashi ta bar shi a gurin, saboda tsoron abin da ka iya biyo baya.
Sai dare Asal ta dawo, kuma itakaÉ—ai Nana ta ga ta ci Abincin dare.
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, Nana ta gabatar da sallolinta na dare. Ta zauna tana karanta Alqur'ani, a hankali sai ta daina ganewa.
Ziiiiiiiiii ta fara jin ƙarar guguwar iskar sahara tana tasowa. Ta rufe Alqur'anin a hankali ta ajiye, sannu a hankali sanyi ya fara ratsa ta.
Ji ta yi tamkar an buga wani abu da ƙarfi, ta zabura ta miƙe tsaye.
Cikin hanzari ta buɗe ƙofar ɗakin da take ciki ta fito corridor da ɗakinta yake ta tsaya.
"Imam mene ne haka? Meye haka ka ke yi wai?"
Sautin kakarinsa ya daki kunnuwan Nana. Gaba É—aya ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Asal ta gani ta fito da gudu daga ɗakin, ta yi waje ta fice daga falon, ta ja ƙofar falon da karfi ta rufe.
Gaba ɗaya sai kan Nana ya kulle ta rasa abin yi, ta bi bayan Asal, amma ta ji ƙofar a rufe gam.
Ta juya a hankali ta kalli hanyar bedroom É—in da sautin kakarinsa yake ta fitowa.
A hankali ta fara takawa tana tunkarar hanyar ɗakin, duk da ba ta taɓa zuwa ko daf da gurin ba.
Zuciyarta na bugawa cike da tsoro ta buɗe ƙofar ɗakin.
Wani irin sanyin na'urar sanyaya ɗaki ta dake ta, hakan ya ƙara ninka sanyin da take ji. Wani ni'imtaccen ƙamshi ya ziyarci hancinta.
Girman É—akin baccin har tsoro ya ba wa Nana, ita dai tana mamakin yadda suke abubuwan su kamar babu lissafi, É—akin kwana kawai an yi shi gari guda.
Idanunta ya sauka a kan Sayyid da yake shirin faɗowa daga kan gadon yana jijjiga. Ta ƙarasa da sauri daidai lokacin ya faɗo ƙasa.
Ta ɗaukko pillow za ta saka masa, kawai ta ga wannan hoton a ƙasan fulonsa. Cikin mamaki take kallon hoton, tare da mamakin yaya aka yi ya zo kan shimfiɗarsa.
Ta durƙusa a kansa, ta kalli jikinsa duk wata jijiya da take jikinsa ta miƙe ta kumbura.
Ƙwayar idonsa ta koma fara ƙal, gashin kansa ya hargitse, gaba ɗaya ya koma abin tsoro tamkar wani dodo.
Ta yi Bismillah ta zauna, tare da jin sai dai komai zai faru ya faru, ko a mutu ko a yi rai, ko da za a zo a kama ta gara balli ya tashi ko za su ƙaryatata gara duk abin da zai faru ya faru, da bar shi a wannan yanayin da bayan shi kansa babu wanda ya kai ta sanin mawuyacin halin da yake shiga.
Tamkar mayen ƙarfe haka ya riƙe ta gam, bakinsa yana karkarwa yana furta "Wuta! Zafi!"
Ya danneta a ƙasa ya ƙanƙameta, bakinsa na fitar za kumfa.
A hankali ta fara karanto suratul Saffat, ta sanya hannunta a cikin gashin kansa tana shafawa a hankali.
Sannu a hankali ya daina wannan gurnanin da yake yi ya yi shiru, sanyin jikinta ya fara É—ibarsa. Ya yin da ita kuma take jin tamkar ana gasa ta a tukuba saboda zafin Jikinsa.
Sosai Nana ta ƙanƙame shi ita ma, cike da matsananciyar kewarsa, wasu hawaye da ita kanta ba ta san na mene ne ba, suka din ga sintiri a kan fuskarta.
"Sai ki tashi ki tafi tun da ya samu bacci, tun da ke dai a rayuwarki ba kya tsoron matsala, tarar aradu kawai ki ke yi da ka. Maimakon ki bari mutumin nan ya gane ki, a yi duk wadda za a yi, amma sai ƙoƙarin kunno wa kan ki matsala ki ke yi" Ƙaisar ya yi maganar cike da takaici yana harar ta.
Nana ta ce "Wasu lokutan nasara ns buƙatar sadsukarwa, da kuma tarar aradu da ka. Mu da ku ba irin zubin halittarmu ɗaya ba, ba zan iya jure ganinsa a wannan mawuyacin halin ba. Ina tausaya masa a yanzu fiye da a lokacin da na san shi bai kan sa ba, yake ce mini yana ji a jikinsa rayuwar da yake da ni ya fi wadda ya manta aminci da kwanciyar hankali, ga shi kuma yanzu ina gani. Sai na ƙyale shi a haka?"
Ƙaisar ya yi tsaki ya ce "Allah ya sa shi zai iya yin abin da ki ke yi a kan sa"
Nana ta numfasa ta ce "Dama ba dan ya rama mini nake yi ba"
Sai gefen asuba jikinsa ya saki, ya ci gaba da nannauyan bacci. Ta saka masa filo ta tashi, sai dai jikinta tamkar ana karyata haka take ji, saboda azabar riƙon da ya yi mata.
Bayan ta idar da sallar asuba, ta yi adduo'inta ta shiga kitchen.
Kafin ƙarfe tara har ta kammala komai, ciki har da gyaran katafaren falon Imam Hammad. Tana son sanin halin da yake ciki, ya farfaɗo ko kuwa bai farfaɗo ba.
Tana can tana tunani, shi kuwa tuni ya fito ras da shi, ya hau buɗe-buɗen kwanuka. Har wani murmushi ya yi ganin ƙosai a cikin kayan karyawarsa.
Shiru ya yi yana kallon kofin madarar raƙumin da ke gabansa, bayan da ya buɗe ya ga 'ya'yan habbatussauda a kan madarar.
Ya ciro wayarsa ya daddana, ya kara a kunnensa.
"Al Hussain"
"Allah ya taimaki Imam Hammad adalin shugaba abin koyi"
"Barka da wannan lokaci ya aiki?"
"Alhamdillah, ina nan tafe cikin Agadez a wannan satin, tun da an ce mini yanzu ana ganin ka"
Imam ya ce "Eh, ammm tambayarka nake son yi"
"Ok Imam, Allah ya sanya ba wani abun aka ce na yi ba"
"Akwai yarinya da Asal ta zo da ita, ta ce a nan gurin cin abinci na MaraÉ—i ta É—aukko ta, wata 'yar Nigeria"
Al Hussain ya ce "Haka ne, sai dai ba na nan suka tursasata Gimbiya Asal ta tafi da ita, na ɗauka ma nan gidan cin abinci na Agadez za ta dawo da ita"
"A ina ku ka samo ta?"
Al Hussain ya ji gabansa ya faÉ—i cike da tsoron, ko wani abin ne ya faru.
"Wani kamfani ne suka kawo ta, da muke neman ma'aikata masu ƙwarewa a fannin girki"
"A nemo kamfanin, da shugaban kamfanin"
"To in sha Allah, amma ina fatan ba wani abin ne ya faru ba?"
Imam ya ce "Sarkin ruÉ—ewa, babu abin da ya faru, ina sauraren ka" Daga haka ya ajiye wayar daidai lokacin da Asal ta shigo.
Ya É—aga kai ya kalle ta ya ce "Ke ina ki ka tafi ne? Na yi zaton ma ko ki na sashenki ne?"
Ba ta ba shi amsa ba, Sultan ya shigo a rikice. Da mamaki yake kallon su.
Sultan ya ƙaraso cikin hanzari ya ce "Hammad ka na lafiya ya jikin naka?"
Imam ya ce "Ai ni lafiyata ƙalau, tun ranar da na faɗo fa babu abin da ya same ni"
Sultan ya kalli Asal, a rikice ta ce "Wallahi Sultan ba shi da lafiya, ba ka ga riƙon da ya yi mini jiya ba, wasu abubuwa ya din ga yi masu ban tsoro".
Imam ya ɗaga kai ya yi mata wani irin kallo, da sai da hantar cikinta ta kaɗa. Ya gyaɗa kai ya ce "Ni ban san me take magana a kai ba, lafiya ƙalau na kwanta kawai dai ba na jin daɗi kaina yana yi mini ciwo, ban sani ba ko ciwon haukan ne ya motsa mini ba"
Sultan ya ce "A'a ba ka da wani ciwon hauka, kawai dai rashin fahimta ne, ka san ba ka da cikakkiyar lafiya"
Hammad ya miƙe riƙe da kofin madararsa, yana sha a hankali ya ce "Abie zan je na shirya, zan ɗan fita ne"
Ya nufi É—akin sa.
Asal ta kalli Sultan ta ce "Wallahi Sultan ba ƙarya nake yi ba"
"Na sani, na san ba ƙarya ki ke yi ba, ki yi haƙuri. Dan Allah ki yi shiru da bakinki kar ki gaya wa kowa. Zan san abin da zan yi a kai"
Nana kuwa burgima ta din ga yi a É—aki, saboda azabar ciwon da jikinta yake yi mata, kamar ta saka ihu haka take ji.
Tun da ta jiyo muryar sa sama-sama a falo, hankalinta ya kwanta ta san jikinsa da sauƙi.
Sai dai wunin yau ma ba su haÉ—u ba, Asal ta ce mata ta ajiye masa Abincin, za a É—auka a kai masa inda yake.
Ruwan zafi Nana ta dafa, ta shiga ta ya wanka da shi, ko za ta samu afuwa, ta gyara jikinta ta fita. Gidan ya yi shiru saboda dare ne, kowa ya kwanta. Ta shiga kitchen ɗin ta tabbatar komai lafiya ƙalau, sannan ta koma ɗakinta.
Tana shiga ɗakin ta ga duhu an kashe fitila, ta nufi gurin kunna fitilar ta ji an mayar da ƙofar ɗakin an rufe.
Ayshercool
08081012143
1K NE VIA 0069685771
Aisha Adam stanbic bank
💃💃💃