Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 1 of 6
*FIN ƘARFI BOOK 2*
*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
Page 1
Sulaiman sun yi iya nasu ƙoƙarin dan ganin uban amarya ya sauka amma abin ya ci tura domin har ya kai da faɗin wallahi baza a ɗaura auran ba,in dai shine ya haifi Ruƙayya ba zata auri Yusuf ba.
Gefen Dad shima ya ce "ban da ɗan yau da ƙaƙule-ƙaƙule ɗan shi yafi ƙarfin ƴar talaka. Kuma in ƴan mata huɗu yake so yau ɗin nan zaya aura masa don haka ya jiƙa ƴar tashi yasha.
Jami'an tsaro sun so damƙar Affa amma sai Dad ya hana su ya ce "ku bar shi yaji da hasarar da yajawa ƴar tasa tunda yai mata baƙin cikin hutawa da cin tuwon dawa."
Gurin ya kaure gami da ya mutsewa jama'a sai surutu suke yi wasu na ƙorafin an ɓata musu lokaci ya yin da dangin amarya suka rasa dalili da yasa Affa ya aikata haka,su ko dangin ango nasu ganin su aka wulaƙanta don haka sun shaƙa matuƙa.
Dad tsaye jikin motarshi yana waya Momy yake mawa inda yake ce mata "In son be fito ba Hajiya kada ki barshi ya fito."
Gaban Momy ya faÉ—i ta ce "saboda me?"
Ya ce "Akwai matsala ne shi yasa dan auran ma an fasa É—aurawa."
Ta ce cikin faÉ—uwar gaba "akan me?"
Ya ce wulaƙanci mana mahaifin yarinyar ba dattijo bane ki tare son kada ya fito fa."
Jikin Momy yayi sanyi ta ce "ai tuni sun fita shi da abokinsa sai dai gyaran Allah."
Cikin shadda galila ƴar gaske blue takalmi da hula duk sun amshi angon yayi ƙyau, har ya gaji suna ta ratsa jama'a cikin motocin su da suka jero shi da abokinshi guda goma kowacce cike take da ɗan adam.
Yayan Dad shi ne ya tsaida su tare da faÉ—in su fito, ya dubi Dady ya ce "To Dady sai ka daina rawar kai tunda an fasa É—aura auran." Jin maganar Dady ya yi kamar saukar aradu ya dubi wan mahaifin shi, ya ce "In dai da gaske kake yi kodai kana tsokana ta ne?"
Ya ce "Kai abokin wasa na ne da zan tsokane ka? Don haka ku juya gamu nan zuwa," ido Dady ya tsurawa Uncle ɗin nashi tamkar yau ya soma ganin shi tun yana ganin shi tar-tar har ya soma ganin wasu taurari suna zagaya kan Uncle ɗin,kai har ya zamana duhu ya mamaye baya ganin komai da kowa. Su Sadiƙ da suma suna cikin ruɗani suka juya domin su lallashi Dady ya zo su wuce,sai ganin shi suka yi ya kusan kaiwa ƙasa,da sauri suka kama shi suka saka shi a mota, Dad cikin ruɗewa shi ma isa da gudu ya shiga mota, girgiza shi yake yana faɗin My son! My son!! Kai innalillahi,wai wama ya sanar da shi wannan abin.
Ita ma Ruƙayya lokacin da labarin ya iso mata nan take ta faɗi sai dai ita hankalin ta be gushe ba,ta dai shiga ruɗu mara misaltuwa,kuka har muryar ta ta dushe. Yaya Murja da Yaya Fati su ne suka sa ta tsakiya suna lallashinta gami da nuna mata kada ta damu in har Dady mijinta ne babu makawa sai ta aure shi sai dai in ba mijinta ba ne.
Cikin kuka Ruƙayya ta ce "nasan zaya yi wuya in auri Dady kuna fa jin yanda me nan gidan ya ce, cewa fa yayi Affa ya cewa mahaifin Dady,ko Dady ne autan maza ba zaya bashi ni ba ya fasa,kun fi kowa sanin halin Affa mutum ne shi wanda baya magana biyu.
Yaya Murja ta ce "haka ne to amma abin mamaki menene dalilin Affa na ƙin amincewa da auran, alhalin da farko ya yarda? Bugu da ƙari sai da ya bari mutane sun taru, wannan abin sam be min daɗi ba don za'a zage shi a gari.
Fati ta gyara zama sannan ta dubi Murja ta ce "amma fa ina ganin aƙwai dalili mai ƙarfi."
Ruƙayya ta ɗaga ido ta dubi Yaya Fati "shin wane dalili yasa Affa yayi min ƙwalele haka."
Yaya Fati ta ƙwantar da ita a jikinta,ta ce "Auta kiyi haƙuri, Affa shi ne ƙaɗai yake da amsar wannan tambayar,ki jure wata rana sai labari."
Lamo tayi tana sauraron Yaya Fati,tasan dole ne ma ta jure amma yanzun tana tunanin da wane ido zata dubi Dady?
Shin yanzun wane hali ma yake ciki? Duk da yake ma yanzu tasan baya tare da hankalinsa tafi kowa sanin irin son da Dady yake mata.
Sabon kuka ta saki tana cewa "nasan Dady yana cikin wani hali."
Su kansu sun rasa yanda zasuyi, basu kuma yi mata magana ba har tayi ta gaji, kafin wani lokaci tuni zazzaɓi ya rufe ta.
Ƴan biki jin anfasa tuni kowa ya kama gaban shi, sai dangi na jiki suma da gari ya waye gaban su zasu kama. Hafsi kam ji tayi tamkar sallah dan Yusra har da rawa tana jin daɗi.
Har zuwa wayewar gari Dady be farfaɗo ba, tashin hankali na ƙarshe iyayen shi sun shiga, don haka duk ilahirin likitocin dake asibitin, sun taru akan Dady, Momy kam kuka take da addu'o'in Allah yasa kada ɗan tilon ɗan nata kada ya tafi ya barta, shi kam Dad cewa yake in har yaron shi ya mutu bazaya yarda ba, to ko wanene zaya biya shi? Oho.
Kusan sha biyu saura na rana Dady ya farka, ruwan da ake ƙara masa ya bi da kallo shiru yayi yana tuna komai dalla-dalla, kanshi ya soma tambaya shin menene yasa Affa ya fasa bashi Pretty? Yasan yanda yake tsananin son ta kuwa,? Bama zai yiwu bane ace bazai auri Pretty ba,shin yanzu Pretty ɗin ma cikin wane hali take?
Tuni su Dad sun san cewa ya farfaɗo,sai dai likitan ya hana su suyi mashi magana, cewar likitan wai su barshi ya tuno abin da ya faru cikin sauƙi Dady ya juya ya dubi Dad ido ya zuba mishi kamar ya warke makanta, sannan ya mai da duban shi ga Momy,a ƙarshe ya koma ga likitan dukkan su suma shi suke kallo,a hankali likitan ya taka ya isa bakin gadon, yasa hannu ya shafa gefen fuskar Dady ya ce.
"Yusuf Son ya jikin? Kuma ina ne yake damun ka yanzun?
Shiru Dady ya yi tamkar kada ya tanka dan shi yanzu haushin kowa ma yake ji, amma daya tuna yana son yaje yaga Pretty ɗin sa sai ya tattara ɗan sauran ƙarfin halin ya yunƙura za ya tashi zaune likitanne ya taimaka masa, da sauri Dad da Momy suma suka iso bakin gadon ya dubi likitan ya ce "Doctor ni fa ina son a sallame ni dan ba inda yake min ciwo."
Dad ya riga likitan magana, My son kayi haƙuri kaɗan ƙara jin sauƙi mana, cikin sigar lallashi Dad ke magana, likitan ya ɗora kan batun Dad, "ko nan da ƙwana uku, sannan ka zama normal."
Dady ya ce gaskiya fa ko awa uku bana jin zan ƙara a nan,dan ina son naga Pretty na kuma san halin da take ciki.
Idon Momy ya cika da hawaye dole ne ma tasan abin yi game da wannan lamarin, Dad ya soma mishi faÉ—a.
"Ka kashe kanka saboda wata ƴar matsiyata duk da irin wulaƙancin da ubanta ya yi mana,da zagin da yayi min cikin bainar jama'a,na tara mutane manyan ƙasa da Sarakuna ya bani kunya gabansu,ai dole ne ma na nunama mutumin nan kuskuren sa."
Dady ya ji zuciyarshi ta na mishi ƙuna saboda irin zagin da Dad ke ma Affa,yana da tabbacin cewa aƙwai wani babban dalilin da yasa Affa ya aikata wannan abun, kuma yana zargin cewa Dad ko ɗan'uwanshi ne sila,wato Uncle.
Ɗaya hannun shi yasa ya zare allurar da aka sa mishi cikin hannu,dama shi ne ƙarin ruwan, ya miƙe tsaye da sauri.
Ganin haka likita ya riƙe shi "Ina zaka Yusuf?" Da sauri itama Momy miƙe ta riƙe shi tana faɗin.
"Dady ina zaka ne?"
Ya ce yana haki "Bar ni na tafi koma ina ne kina jin irin faÉ—an da Dad yake yi bana son ji, zuciyata na min zafi, kamar ta faso ta fito waje."
Momy ta ce "to kaji,in ɓacin ran da yake ciki be kashe shi ba, to kuwa kai faɗan ka ya kashe shi,kabar shi mana yaji daɗi."
Tsaki yayi sannan ya ce "Na rasa menene Son ya gani gurin yarinyar nan ga mata ma nan ƙyawawa ƴaƴan manyan mutane, amma ya ƙi ya tsaya gurin wannan ƴar matsiyatan."
Da sauri likitan ya ja Dad ɗin Office ɗin shi bayan sun zauna Doctor ya dubi Dad da ke ta cika yana batsewa, ya ce "Alhaji ba abin da ya dace kayi kenan ba,ya kamata ka kula da yaron nan dan kuwa yana cikin wani hali,so ba ƙarya bane,ko kasan jinin ɗan ka ya hau?"
Da sauri Dad ya miƙe cikin tashin hankali,ya ɗaga murya ya ce "Doctor ka ce jinin Son ɗina ya hau?"
Doctor ya ce "Of Course,bayan haka ma zuciyarshi zata iya bugawa a kowane lokaci matsawar zaya dinga shi ga irin wannan halin da yake yanzu,ko kuma a dinga sanyashi cikin tashin hankali.
Matuƙar tashin hankali Dad ya shiga ya dubi likita "to yanzu menene mafita?"
Doctor ya ce "Yauwa,da farko sai ayi ƙoƙarin ƙwantar mishi da hankali ta hanyar nuna mishi za'a san yadda za'ayi a mallaka mishi yarinyar."
Dad ya ce"zaya yi wuya ya samu yarinyar nan saboda wani ƙwaƙwƙwaran dalili mahaifinta ba zai yarda ba, shi yasa nike so Son ya haƙura da yarinyar dan tun farko ma bata dace da shi ba, ƙaramar yarinya ce sosai fa,ban san me yake ganin gurin yarinyar nan ba."
Murmushi likitan ya yi sannan ya ce "Alhaji ka taɓa jin ciwon so kuwa? Koda yake ƙila baka taɓa ɗanɗana raɗaɗin so ba haƙiƙa saboda duk wanda ya taɓa ɗanɗana raɗaɗin so dole zai tausayawa yaronka so ba ruwan shi da talaka ko mai kuɗi,so ba ruwan shi da yarinta ko tsufa,ƙyau ko muni, duk mai yin so ba waɗannan bane damuwar shi,damuwar shi ya samu abin da yake so,don haka yaron ka damuwar shi ya samu yarinyar da yake so, yanzu a ƙwantar mishi da hankali mu samu jininshi ya sauka in yaso kai kuma sai ka je kayi shawara ka sama mishi mafita, don Allah kada kai mishi FIN ƘARFI."
Sai da suka koma ɗakin Dady yana zaune Momy ta na kusa da shi duk suna bakin gadone, kanshi na kan ƙafar Momy baki take bashi da cewa "Dady ka zama musulmi na ƙwarai mai yarda da ƙaddara mai ƙyau ko mara ƙyau a duk sanda ta same ka, komai zaya zo maka da sauƙi nasan kana son Ruƙayya amma in Allah bai yi matarka ba ce babu yanda zaka yi."
Wata ajiyar zuciya yayi sannan ya ce "Momy ni ban halicci kaina ba,bare na hana kaina son Pretty,ban san yanda akayi na faÉ—a son ta ba, haka nan jikina yana bani zan auri Pretty,ki tausaya mini ki taimaka mini Momy,I love Pretty to much,I need her,zan iya mutuwa domin ta ko kin musu?"
Ta tsura mishi ido kalaman sa suna matuƙar bata tsoro ta san shi tasan wanene shi,tasan halinshi, Dad da suka jima a tsaye suna sauraron ya ƙara shiga cikin tashin hankali ya dubi Doctor "Kana jin shi ko?".
Doctor ya ce "Come down Alhaji kar ka damu."
Suka isa gurin shi Dad cikin fara'a ya ce "Come on My Son dole ne ma ka auri Pretty ɗin ka kaifa ɗan gata ne gaba da baya, ya kamo hannun shi ka taɓa neman wani abu ka rasa? Dady ya girgiza kai.
"To ka ƙaddara ka auri Pretty ɗinka ina nufin koma ta halin yaya ɗin nan da nace ka gane?"
Ido Dady ya tsurama mahaifin nashi,yasan tunda ya furta haka da gaske hakan nan ne zaya aikata, Dad zaya iya nuna ƙarfin kuɗi kona mulki dan ganin ya cika masa burinsa, amma kash shi kam baya buƙatar samun ta ta wannan hanyar dan haka sai ya dubi mahaifin nashi ya ce "Dad duk da tsananin son da nake ma Pretty ba zan so in mallake ta ta hanyar FIN ƘARFI ba zan fi son in sameta cikin yarda da amincewar mahaifinta.
Kafin Dad ya yi magana likitan ya riga shi da cewa "Oh lover boy dama ai sai da yardar mahaifinta za'ayi ba dole za'a yi mishi ba, yanzu me kaÉ—an sa a cikin ka ne don ina son mu baka magani tare da maka wasu Æ´an gwaje-gwaje.
Dady ya ce "Momy ni fa a sallame ni dan nasamu sauƙi sosai ina son in je in ga halin da Pretty take ciki."
Dad ya ce "haba my son ka bari mana ka kara samun sauƙi."
Momy ta ƙara da cewa "zan je na kawo maka ita in dai kayi ƙoƙarin ƙwantar da hankalinka."
A hankali ya sulale ya ƙwanta akan gadon yana faɗin "Momy don Allah je ki kawo min ita yanzu."
Doctor ya ce "to zata je" yana magana yana É—aura mishi abin gwada jini."
Ita kam Ruƙayya daidai wannan lokacin tana ƙwance rigib cikin zazzaɓi lokacin tuni ana sallama da baƙinsu ƴan biki wasu abokan wasan ta suna ta mata tsiya,yarinya taga samu taga rashi kiyi haƙuri sai kuma Allah ya kawo sabon ƙwastoma in ji Jummai.
Yaya Murja ce ta amshe da cewa "Bakomai ai dai ba shine ya ce ya fasa ba mune muka ce."
Binta ta amshe "to ita amaryar menene na zazzaɓi ki tashi mun dai gane dama ganin tsoro ya yi miki,sai ranar ɗaurin auren ya ganki ashe ƙarama ki ke ga muni."
Yaya Fati ta ce "don Allah mu dai ku tattara ku nufi ƙauyenku har kina cewa Ruƙayya ƙarama ke san da muka je bikin ki kinfi shekara tara ne?" Duk ƴan biki suka ƙwashe da dariya.
Ƙanwar Babansu ta ce "amma Fatsima banga abokin ƙaryar ki ba,san da aka yi bikin Binta ai ko haihuwar ki ba'a yi ba.
Ruƙayya kam tana sauraren su ta ƙosa su tafi dan bata son wasan da suke mata bayan sun tafi ne Murja ta fita dan samo mata magani ita dai a son ta da ciwon zaya taimaka mata ya ɗauki ranta da taso,dubi ƴan'uwanta suna mata dariya saurayin ta ya gudu ina ga mutanen gari dama kuma ba son ta da Dady suke yi ba,kai zama ta iya ratsa layinsu? Domin wasu ma daga cikin ƙawayenta har cewa suke yi tana musu yanga dan zata auri ɗan masu dashi gaba da gaba wata Zina a layinsu tayi mata wannan batun. Hawaye suka zubo mata masu zafi yanzu ya ya zatayi da ƴan makarantar su da mutanen gari? Shin in wani ya yarda mahaifinta ne ya fasa bada ita wasu zasu yarda?
Kai ita da yaya ma zatayi ne? Gaskiya inda tasan inda zata je da ta tafi yau ƙwana uku da faruwar abun amma Affa baice da Umma ga matsalar da tasa ya aikata hakan ba, ita ma bata tambayeshi ba dan tasan tsarin shi, shi mutum ne da sam baya son raini ko wasa da mutuncinshi ta tabbata yana da wata hujja mai ƙwari kuma tasan da zaran hankalinshi ya dawo jikinshi sosai zaya mata bayani, ita dai fatan ta Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.
Dare ya tsala misalin ƙarfe biyu da rabi,shiru garin bakajin ƙarar komai Ruƙayya tana zaune kan katifa kanta yana bisa guiyoyinta,a ranta tana faɗin anya ko gaske ne da hausawa suke cewa dare mahutar bawa? A da kam ta yarda amma yanzu tana da ja,dan duk ƙwanakin nan da abin ya faru sam bata ko da gyangyaɗi,duk yarda ake labarin iya satar bacci baya iya satar ta, tsabar tunani ne kawai yake ɗawainiya da ita, kullum tunaninta yanda rayuwar ta zata kaya ba tare da Dady ba,bata ƙara tsinkewa da al'amarin ba sai da ta tuna yau da yamma Affa ya turo su Umma da su Yaya Fati suka shiga ɗakin su inda Ruƙayya ta ke ƙwance cikin zazzaɓi.
Ya ce ki sani Ruƙayya ada ni ne na yarda miki auran Yusufa, amma a yau na janye,a bisa abin da mahaifinsa ya yi min, Allah ya sani da tun farko nasan, Alhaji Mansur shi ne mahaifin Yusufa da bazan taɓa amincewa da zancen aurenku ba, ga ƴar'uwarki ga mahaifiyar ki na kira sune zasu zama shaida bani son ƙara jin labarin Yusufa anyi shi a gidan nan ballantana har ma yazo gurin ki,ki sani nayi rantsuwa wallahi koda Yusufa ne kaɗai ya rage ɗa namiji a doran duniya na raba ki dashi,sai dai ki mutu gwauruwa ma,kar ki yarda na samu labarin ko a hanya kin saurare shi, lokacin da Affa yake wannan bayanin ɗakin shiru dan kowa kasa gane menene ainihin dalilin da yasa Affa haka tamkar ya karancesu sai ya ce inna samu zama zaku san dalili ya nuna Umma sannan ya ce ke Maimuna kin manta Alhaji Mansur Yusuf da Yaran shi Alhaji Aminu jega? Faɗin Jega yasa Umma tayi saurin duban Affa.
"Me kake nufi Yusuf É—an su Jega ne?"
Ya ce"ƙwarai kuwa tunda ɗan uban gidan Jega ne."
Umma ta ce "TabÉ—i,an so tabka kuskure gwara da Allah yasa aka farga.
Affa ya miƙe in mun samu lokaci kun san wanene Alhaji Mansur da kuma Aminu jega."
Umma ta fita ta hau aiyukanta tana cewa "aiko da an ɗaura a ƙwance Allah ya tsare mu da azzalumai."
Shi ko Affa waje yayi suka bar yaran cikin tunanin shin wanene Jega?
Ta kuma duban su Fati sai faman bacci suke yi ita kam tananan tana ƙoƙarin lallashin zuciyarta dan ta yarda ta rabu da Dady, kuka sosai take yi da ta gano ba zaya yiwu ta cire son Dady a ranta ba da tasan auran nasu ba me yiwuwa bane ta kuma rushewa da sabon kuka.
Kamar a mafarki Murja ta ji kuka dan haka sai tayi ƙoƙarin juyawa dan ta gyara ƙwanciya,sai ta gane ba mafarki take yi ba, gaske ne, ta tashi zaune ta ce "Ruƙayya me ya faru? Kiyi shiru kin san a yanzu dare ne,nasan kina cikin wani hali ki yi haƙuri ki daure komai me wucewa ne,Yaya Fati ta farka nan suka haɗu sunata lallashin ta. Ta dai yi shiru ta ƙwanta tasan dai badan bacci sai dai dan kada ƴan'uwanta su ga taƙi ji,tana ji har aka kira sallah.
Tamkar Dady da shima aka yi mishi allurar bacci,tun misalin takwas na dare likitan ya ma su Momy zai yi bacci sosai dan sai zuwa shida na safe zaya farka dan yana buƙatar hutu, amma abin al'ajabi daƙyar ya samu awa huɗu yana bacci misalin sha ɗaya da ran ya farko,lamo kawai yayi dan yana jin sanda abokan Dad suka zo duba shi, Momy ta ce ai da sauƙi allurar bacci akai mai dan likitan ya ce yana buƙatar hutu,jin haka yasa yayi lamo.
Saƙe-saƙe kawai yake yi yana ƙwance ma, tunanin shi a wane hali Pretty ɗin shi take shin ta wane hali ne ma Dad zaya aura mishi Pretty?.
🖊ï¸Â🖊ï¸Â🖊ï¸Â
[7/25, 21:01] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 2*
*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*