Complete Hausa Novels

Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 4 of 6

Page 4

Mata ta da yarana, lokacin su waɗannan ya nuna su (Ruƙayya)suna ƙanana haka ƴan'uwa da Abokaina suka dinga samun manyan mutane don su sa baki, amma kowa ya ji da (Former I.G)ne Alhaji Mansur,sai suce gaskiya sai dai kayi haƙuri ba zamu iya tunkarar shi ba, don ubanmu ne, to Hajiya ƙarewa ma ƙwamishinan ƴan sanda na jihar Katsina a wancan zamanin shi ne da kanshi ya zo ya tafi damu, kuma don tsohon wulaƙanci.

Bayan mun saida sauran kadarorinmu mun haɗa miliyan biyun su mun basu sai da muka ƙara ƙwana uku sannan suka sake mu,bugu da ƙari sun sa ƙwamishina ya amsa mana takardar gurin. Kinga sun amshe mana guri ga ɗauri ga kuma asarar sauran kadarorinmu, baƙin cikin wannan abun shi ne yasa ni nabar Katsina na dawo nan Kaduna da zama, kayan koli nike saidawa kuma ba laifi dashi ne na samu na sai wannan tsohon gidan nawa kuma nike biyawa yara kuɗin makaranta nake ci dasu.

Sannan yanzu duk mutumin da ya yi min wannan aikin na ɗan shi ƴata,ai ko ƴan sanda ka kira min ka gama da ni bare har kasa a tsare ni saboda haka kayi haƙuri ba zan iya bada ƴata gare ka ba, kayi haƙuri.

Gwiwa biyu Dady ya durƙusa a gaban Affa ya ce "don Allah Affa ka taimake ni kada kaimin haka."

"Ni ban maka komai ba." Yusufa ba ƙaramin ɓakin cikin rashin wannan auran nayi ba,don har ga Allah zuciyata tana tsananin son ka har yanzu,sai dai in har na baka ƴata Yusufa ban ma san abin da nake yi ba kenan."

Momy ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Tabbas nasan sanda abin nan ya faru domin kusan mata uku a wancan lokacin sun zo dan neman nayi ma Alhaji magana, koda nai masa sai ya ce min maganar ta mutu."

Affa ya ce "To kin ji ma kinsan lokacin."

Ta ce "To don Allah Affan Ruƙayya kada ka biyewa halin shi, kayi haƙuri don Allah."

Ya ce "Hajiya na gama magana, hawaye Dady yake sosai amma Affa ya ce "ina."

Itama Ruƙayya sai ta samu da jin zafin abinda Dad ya yi wa Affan ta.

Amma duk da haka sai ya zamo bata ga laifin Dady ba, tunda shi ba shine ya yi ma Affa ba, ta dubi Dady ya ruÉ—e ya fita haiyacin shi.

Ta dube shi ta ce"Kayi haƙuri Allah zai baka wadda ta fini."

Cikin ruɗewa ya ce "Kina nufin kin haƙura dani? Kada kiyi min haka Pretty ni mai sonki ne har abada."

Kuka sosai Ruƙayya ta saki cikin kukan ta ce "Bayan da zan yi ne."

Fati da Murja suka dube ta cikin ƙulewa,dan sukam sun matuƙar jin zafin abinda Dad ya yi ma Affa dan haka sai suka ce "ke kima mutane shiru, tashi mu je tunda ke baki kishin ubanki."

Ruƙayya ta ce "Ku tausaya min rabani da Dady ba ƙaramin abu bane." Suka yi tsaki suka fita.

Momy ta kasa magana dan tasan lallai an ma Affa FIN ƘARFI, yanzu tana jin nauyin ta matsa mishi,miƙewa tayi ta kama hannun Dady ta ce "To zo muje mu bar komai a hannun Allah."

Affa ya ce "Ga kuÉ—in ku nan bari a fita da jakunkunan kayan."

Momy ta ce "Kar kayi haka Affan Ruƙayya,ai Ruƙayya ƴata ce,dan haka daga kayan har kuɗin na bar mata."

Affa ya ce "a'a sam." Momy ta ce,in har kace haka to tabbas akwai wani abu a ranka,ba mahaifin Dady ya baka ba,ni ce nan kuma ko É—aya ban ga laifin ka ba sai na mahaifinshi, domin ko ni akai ma haka, tsakani da Allah ba zan bayar da Æ´ata ba."

Ganin zasu fita Affa ya ce "To shikenan."

Ruƙayya ta duƙar da kai tana kuka mai tsuma rai, sauraron ta Affa yake tayi, tayi har muryar ta ta dushe, ya ce"ki yi haƙuri Ruƙayya ban maku FIN ƘARFI ba,bana son mahaifinshi ya raina min wayo,ko ba komai zai san cewa shima talaka yana da rana da kuma baiwa, wacce zayayi iko da ita, ina son ki nutsu ki bar zancen aure, karatun ki shi zaki sa gaba,ki manta da Yusufa dan ki samu zaman lafiya a cikin gidan nan, tunda matsawar kika bijiremin ko ƴan'uwanki ba zaki samu ƙwanciyar hankali da su ba."

Ta ce "To."

Ya ce "Maza tashi kije kiyi sallah."

Ta miƙe ta fita. Koda ta shiga ɗakinsu su Murja suna sallah, bayan sun idar itama ta idar ta tashi taje ta kawo musu abinci, ta koma kan katifa ta ƙwanta saboda tsabar ciwon kai,da yake damun ta suka bita da kallo, basu ce ƙala ba suka cigaba da cin abincin su suna hira,taji tausayin kanta wato ma fushi suke yi da ita,tasan da dane taƙi cin abinci zasu yi ta lallashin ta ne har sai taci. Isha'i ma sai a zaune tayi ta ƙwanta cikin tunanin Dady. Shikenan yanzu soyayyarsu ta zama tarihi, tsarin da Dady ya yi musu na zaman aure yasha ruwa,ta tuna wata rana da suke hira da Dady game da bikin su,ya ce "Pretty." Ta dube shi ya ce in mukayi aure nifa kinsan ina son haihuwa da wuri, ina son yarinya ta mace ƙyaƙƙyawa, Ruƙayya tayi dariya ta ce, Ni bana son na haihu da wuri, ya ce "Saboda me?" Ta ce "don na tsufa kai ka auro wata ya yi dariya ya ce "Ai Pretty duniya da lahira ke kaɗai ce mata ta kuma uwar ƴaƴana kullum in ta tattalin ku ina shagwaɓa ku, komai ni zan miki kamar bawa zan koma miki abinci a baki,in miki wanka,in miki wanki,in ki ka ce be miki ba sai na sake miki wani,in zamu fita ni ne mai ɗaukar miki jaka, hannu tasa a bakin ta tana dariya tana faɗin kada kasa ace na mallake ka, ya ce na nawa aini yanzu sai yanda kika ce,kin san Momy zata so mu taso yaranmu.

Ruƙayya ta ƙara fara sabon kuka, Fati ta dubi Murja ta ce , Murja ki ji min ikon Allah zata cika mana kunne.

Murja ta je ta jawo ta ta zauna,bazaki mana shiru ba ko?

Cikin sarƙewar murya da shashshekar kuka ta ce "Yanzu ba zaku tausayawa halin da na shiga ba."

Fati ta ce "Ba fa zancen tausayi a cikin sa kai dan wannan sa kaine, kuma ki mana shiru ko ki ci duka."

Tasan tsaf zasu dake ta,dan haka sai tayi shiru tare da yin kukan zuci.

Shi kam Dady ai akan shi aka ƙwana asubar fari sai asibiti,ƙwananshi sha ɗaya abu ba sauƙi sai na Allah. Dad da kanshi ya yi ma wanshi waya yana neman shi, bayan ya zo suka yi shawara Dad ya so suje su roƙi Affa ya yi haƙuri ya ba Dady Ruƙayya, amma sai ɗan'uwanshi ya ce, a'a ba haka za ayi ba, abin da zaya fi shi ne haɗa Dady da Yusra, tunda ai Ruƙayya ba fin Yusran zatayi ba, bayan haka ma tunda Yusra tafi Ruƙayya girma zata mantar dashi Ruƙayya tare da tattalinshi,ka ga tunda an gama komai game da wannan Company shi sai a haɗa da bikin buɗe Company dana auransu.

Dad ya amince amma Momy ta ƙi yarda, ta ce "Sam a bar mata yaronta ya samu lafiya kafin ayi mishi shawara in ya yarda,fa ni'im in bai amince ba sai a fasa."

Shi ma likitan ya ba Dad shawara, suka bari yaji sauƙi kuma kada ai mishi dole, wannan ne dalilin da yasa Dad duk ya fita daga haiyacin sa,koda ya tuntuɓi amininshi mahaifin Hafsi sai ya ce mishi "baya goyon baya mutum kamar shi ya je yana roƙo ga talaka, don haka ya barshi kawai."

Kan Dad ya yi zafi yama rasa yadda zayayi, Momy ce ta zaunar da shi ta ce "Ya ƙwantar da kai ya je ya samu su Alhaji Sabitu su dafa mishi baya ya je ya ba Affan Ruƙayya haƙuri.

Hakan ce kuwa ta kasance amma Affa ya ce "Sam."

Zuwan su Dad uku saboda kowa yaga Dady sai ya tausaya mishi in dai kana da zuciyar imani. Shima Affa duk da baiga Dady ba ya tausaya mishi,sai dai yana son Alhaji Mansur yaji yanda ya ji shima san da aka tsare shi akai ta zuwa ana roƙon shi amma yaƙi.

Ita ma Ruƙayya duk da tana ƙoƙarin nuna cewa ta haƙura babu daran da bazatayi kuka ba, kuma su Murja sun san tana yi, suna nuna mata basu sani bane, kuma suna tausayin ta sai dai basu so su nuna mata ne dan kada ta samu ƙofar kawo musu zancen Dady duk ta rame karatun tama ya yi rauni tun daga boko har islamiyya.

Germany su Dad suka yanke shawarar kai Dady dukansu suka tafi har ma da ƴan rakiya. Su Ruƙayya suna tsaka da zana jarabawa ciwon cikin ta ya motsa, kasancewar wancan watan batayi ba sai yazo mata da muguwar matsala tasha wahala sosai, ita ason ranta ma Allah ya ɗauki ƙwananta ta huta saura paper ɗin ta uku batayi ba,dan ma tayi masu muhimmanci.

Haka lokaci ya cigaba da tafiya sai ki ga da gari ya waye har yamma tayi sai ki ga dare ya shigo gari ya ƙara waye wa,ba wuya ace juma'a ta zago gashi har Dady ya samu wata uku a can Germany ya warke sarai sai dai zuciyarshi ce bata warke ba har yanzu son Pretty ɗin shi yana nan daram ƙauna zalla daga Allah, ya yi ƙyau ga wani haske da idonshi ya ƙara sai dai bai gama maida jikinshi ba. A wannan lokacin Ruƙayya tuni ta soma karatun ta a makarantar ƙwana dake Bakori a jihar Katsina. Affa ya yi hakane dan ya nisanta ta daga gida, duk da labari ya sameshi an fita da Dady (Germany)ta soma (S.S.1) ɗin ta ne cikin haƙuri da juriya.

Suna makaranta aka yi bikin su Fati,taso ace tana nan amma ina,taji haushi sosai ƙawayanta Safiya Umar da Walida da Amira sune suka yi ta bata baki. Safiya ƴar Katsina ce a Tudun Wada ita ko Walida ƴar Funtuwa ce ya yin da Amira ta zama ƴar Zariya.

Su huɗun nan koda yaushe suna tare. Suna mata labarin samarin su,Amira auran zumunci zasuyi ita da Mansur, ɗan kawun ta, ita ko Walida yaron Ogan Babanta zata aura na gurin aiki, Safiya kuwa ɗan layin su ne Usman, dukkansu Ruƙayya ta san su saboda sun zo lokacin ziyara.

In sun ce tana da saurayi,sai ta ce a'a, wata rana suna ƙwanarsu suna ta hira sai Walida ta ce "Ruƙayya don Allah zan tambaye ki wani abu zaki bani?."

Ruƙayya ta ce "Faɗa ko menene."

Ta ce "wannan zoben nake so."

Ruƙayya ta ce "Kash,aikuwa Walida sai dai ki amshi ɗayan nan amma ban da wannan don mutuwa ce kaɗai zata raba ni da zobannan."

Amira ta ce "Zoban alƙawari ne."

Ruƙayya ta yi murmushi ta ce "Ko masu bincike makarantar nan sun bar ni da zobannan, Zoban Dady Allah sarki Dady mai sona da gaskiya." Sai hawaye kuka sosai tayi da ƙyar su Amira suka lallasheta suka kaita har gadonta suka zauna.

Safiya ta ce "Ruƙayya Dadyn ya rasu ne?"

Murmushin ɓacin rai tayi ta ce "Dady yana nan sai dai yanzu ban san inda yake ba." Nan ta basu labarin Dady har ta nuna musu wayar ta daya bata sun sha mamaki, tare da tausaya musu sannan suka ɗauki alwashin sa ta a cikin addu'arsu kullum suka yi sallah biyar.

Walida ta ce "Ba zaki kirashi a wayar ba ne?"

Ruƙayya ta ce "bazaya yiwu ba tunda bazan same shi ba,gara nayi ƙoƙarin nesanta kaina dashi."

Su kam su Walida sun so ace wayar da chaji su ga yanda ake amfani da waya kasancewar wayar a wancan lokacin sai wane da wane ko a masu kuɗin. Suna cikin haka har lokacin hutu ya zo sun yi murna da ɗoki sosai na zuwa gida, Umma ta ce "Auta har yanzu kina nan kina ƙulafucin Dady ko?."

Ruƙayya ta yi yaƙe sannan ta ce "Haba dai Umma ai ni nama mance da wani Dady me kika gani?.

Ta ce "har yanzu baki maida jikinki ba, gashi kin samu É—an wake sai Allah."

Ruƙayya ta ce "munyi ciye-ciye ne a mota (ta sako wata maganar) Umma lokacin dana samu labarin auran su Yaya Fati sai da nayi kuka nace shin Affa yasa lokaci kusa dan kada naga bikin ko?"

Umma tana dariya ta ce "Ke da Affan naki in yazo sai ku ƙarata."

Ruƙayya ta ce "ina aka kaisu?"

Ta ce "Fati tana Kakuri, ita kuma Murja N.N.P.C ƙwatas."

Na ce "Eh,anan Yaya Ahmad yake aiki."

Umma ta ce "Eh, suna ta labari har Affa ya shigo duk da ya kula har yanzu Ruƙayya bata maida jikinta ba,ya ji daɗin ganinta tana ƴar walwala suna aiki tare da Ummanta.

Ruƙayya ta durƙusa ta gaishe shi cikin fara'a,ya amsa mata tare da nuna mata murnar shi na ganinta. Cikin hirar da suke yi da daddare take ƙorafin anyi biki bata, Affa lokacin da aka aiko min da wasiƙar nan sai da nayi kuka."

Ya yi dariya ya ce "Neman ilimin kenan,kema gashi makarantar Islamiyyarku da kuka yi sauka anyi walima ba ƙyanan,sai dai ke an aiko miki da ƙyautukan ki

Ta ƙara turo baki "kai gaskiya ni dai ban so haka ba."

Affa ya ce "To ai shikenan ya wuce ai ko?."

Ta je gidan Fati ta wuni washegari ta je gidan Murja,sun ji daɗin ganinta sai dai dukkansu sun mata ƙorafin rashin maida jikinta, cewa ta yi karatu ne, tayi sha'awar yanda mahaifin nasu yayi matuƙar ƙoƙari ya tsarawa ƴan'uwanta ɗaki ta je gidan su Yaya Amina Yaya Suwaiba da Sadiya, duk sun yi murnar ganin Auta ta ƙwantar da hankalinta.

Bayan sun koma makaranta sun haɗu da ƙawayenta suka ci gaba da karatu.

Ƙwanci tashi gurin Allah ba wuya sai gashi sun shiga S.S.2, ciwon cikin ta kam yana nan tana shan wuya,malaman su har sun gane ta, saboda duk wata sai tayi wani sa'in kuma tana yin wata biyu ko uku,in ta dawo hutu samari kamar me amma bata fita ko Umma ta ce tashi ki je tunda ai ba danki zamuyi dake ba kina gamawa aure zakiyi,sai ta tura baki tana fita zata korashi,in ko a hanya ne sai ta ce tana da miji.

A haka dai har suka shiga S.S.3 ance aski in yazo gaban goshi tafi zafi to haka suma karatun nasu yafi zafi yanzu,dan haka suna ƙoƙari kuma har zuwa wannan lokacin Ruƙayya tana kukan Dady da yawa tana ganin shi cikin mafarkin ta,yana faɗi mata kar ta karya alƙawari.

Sun samu hutun zango na biyu a shekarar su ta ƙarshe bakin titi suka tsaya suna ta banƙwana Ruƙayya da Amira hanyarsu guda dan haka tare suka taho a Zaria Amira ta sauka ita kuma ta nufo Kaduna.

Girma da cika Ruƙayya tayi ga ƙyanta ya bayyana fatar ta tamkar Black America wasu kuma su ce kamar ƴan matan Ethiopia duk saurayin da ya ganta sai ya sake dubanta.

Cikin shadda pink kayan ya yi matuƙar amsar ta gidan Yaya Murja zata. Bayan ta miƙa ɗinkinta gurin Nasir,a hankali cikin natsuwa take tafiya ƙwarai tana birge mutane, shagon Nasir ta tsaya ƙyaƙƙyawan saurayi mai son neman na kansa ya yi matuƙar iya ɗinki da aikin surfani na mata,dan haka ma shine ke ma mata manya da ƴan mata masu son a birgewa,yana ganinta ya ce "manya Ruƙayya saukar yaushe?"

Tayi murmushi ta ce "shekaran jiya na dawo ya aiki?."

Ya ce "Alhamdulillah,"ta zube mishi zannuwan ta "kin san kuÉ—in zannuwan nan kuwa."

Ta ce "Nasir kenan, nima ban sani ba."

Ya ce "ai naga alama daga yanayin riƙon da kikai musu. Dariya ta saki tana cewa "lallai Nasir to wane irin riƙo nayi musu?."

Ya ce "Oga ne ya siya miki ko?"

Ta ce "wane Oga aini banida wani Oga."

Ya gyara tsayuwa dan ya daÉ—e yana son ta sai dai yana shakka dan yasan dole tana da samari "Ban yarda ba, domin ke son kowane." Ta É—an rage fara'a.

Ta ce "To nagode, yanzu kana da style a ƙasa."

Ya ce "Ko babu dole na nemo shi."

Ta ce "ayimin landin full a riguna,sun fi zama."

Ya ce "An gama."

Ta ce "Bill É—in kuÉ—ina naji."

Ya ce "Ki je sai angama."

Gidan Yaya Murja ta wuce ta sameta tana dafa abinci a kitchen,kicin ɗin suka shiga tare,alalanwake da hanta da ƙwai take yi Ruƙayya ta ce "ina mama ne?"

Murja ta ce "tana bacci yanzun nan ta ƙwanta bayan ta gama rigima zata bi babanta."

Ruƙayya ta ce "Ai dama mama ƴar dan ja ce aƙwai rigima, Muhsin ɗin Yaya Fati yafi ta haƙuri."

Murja ta ce "Jiya ko can gidan su muka wuni,sai faman labarin auren ki muke yi sai kace bikin ya zo."

Ruƙayya ta taɓe baki ta ce "Ni fa shiyasa bana son muyi hutu saboda zancen auren nan."

Murja ta na dariya ta ce "Ka ji yarinya ba dole ai miki zancen aure ba tunda kin isa."

Ruƙayya ta ce "To ai banida saurayi."

Murja ta ce "Aƙwai wani faruk ƙanin Baban Mama yasha min zancen ki,yana da kirki, gashi yana da aikin shi."

🖊️🖊️🖊️
[7/28, 18:44] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 2*

*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.