Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 6 of 6
Page 6
Wata a cikin su mai suna Mina ta ce "Kai ko yanzu zaka tafi da wuri bawan Allah ka bari mu gaisa." Tayi tana fari.
Ya yatsina baki ya ce "No ma gaisa next time,nawa ne kuÉ—in?."
Suka ce "One million."
Ya ce "Ok, ya buɗe mota ya ciro check ya rubuta musu ya miƙa ya ce "Sagir zo muje."
Sai ga Sagir can da wata ya girgiza kai ya shige mota, ya faÉ—a ya yi mishi horn,don yasan Dady zaya iya tafiya yabar shi, shi yasa yayi sauri ya shiga motar.
Dady ya dubeshi "Kaidai sakaraine mata ne ajalin ka,ga mata a gida ka baro ka zo nan kana shirme."
Ya yi dariya ya ce "Tun da kai ka kasa bar mu muyi."
Dady ya ce "dole mata su garaka."
Bayan ya sauke Sagir sai ya nufi gida, shirin ƙwanciya yayi ya ɗauko Hollandia mai sanyi ya zuba a kofi, ya dubi cikin shi,a ranshi ya raya gobe zaya tashi da wuri don ya motsa jiki, tumbin nan nashi yana son ya zauna shi kuma ya tsani tumbi, ya ɗaga kai yana duban zaman yarinyar daya jima yana ƙishirwar gani hoton ta ya bada aka zana ta, tayi murmushi cikin ƙanana kaya ranar birthday ɗin shi akai mata hotunan,da shike me zanen ya ƙware sai ma tafi ƙyau a zanen fitilu yasa ja da blue in wannan ta kawo wannan ta ɗauke yayi addu'a ya shafa sannan ya tsura ma hoton ido ya raya ance tuni an mata aure ƙauyen Katsina yasan yanzu tana da yara tana kuma rayuwa cikin wahala.
Ya lumshe ido wasu Æ´an hawaye suka zubo mishi shi kam daya san inda Pretty take daya taimaki rayuwarta da ya ba mijinta amanar ta daya taimaka mishi cikin waÉ—annan tunanin ya yi bacci.
Bikin Hussain ya kan kama, ƴan mata sai son Dady suke shi kam yaƙi bada fuska,dan ko Zainab taso zuwa bikin ya ce mata "A'a sai ranar dinner."
Zainab Umar ƴar wani minista ce Ƙawar Zina ce matar Sagir, ya shareta, ya shareta amma ta nace ta kuma liƙe,ya yarda zaya aure ta ne saboda dalilai guda biyu, na farko dan idonta yana mishi yanayi dana Pretty, sannan dan ya kare kanshi daga sha'awa tun da shi bai kasance mazinaci ba,in ya ji zaya matsu sai ya yi ta azuminshi shi yasa ya ce zaiyi ta kare sha'awa tunda an dace tana tsananin son shi, sai dai ya ce mata ba ita kaɗai ba ce, yanzu ma yana son su gama da bikin Hussain sannan ya je Kaduna dan kai zancan Zainab.
Sun sha biki taro ya tashi ankai amarya gidan ta dake nan Abuja. Dan su Hussain sun taso bayan ƙarin girman da mahaifinshi ya samu Dady ya je Legos daga can Kaduna ya wuce gurinsu Momy da farko tayi fushi amma yana bata labarin Zainab sai ta hau murna da sanya albarka ita ma Hajja taji daɗin jin labarin Zainab har tana cewa sai asa da wuri indai ana son in ci tuwon Zainabu Abun.
Ya ce "Babu gaggawa Hajja gaggawa daga shaiÉ—an ne.
Ta ce "Allah yasa mu dace, gashi Saude bata nan taje ganin gida da tayi murna sosai."
Ya yi ma Hajja alherin da ya sama, sannan ya fito,yana fitowa nan ma ya shiga yi wa mutanen dake maƙwafta da Hajja alheri, bakin wanda Allah yasa yana wajen kowa ya samu rabon shi haka Dady yake da ƙyauta.
Yana zuwa bus stop É—in daya shiga unguwar su Pretty sai kawai ya tuna da, nan ya samu kanshi da shiga unguwar ya tsaya bakin shagon mutumin nan, bayan sun gaisa ya da mai shagon "Ka kuwa gane ni?."
Mai shagon ya ce "a'a."
Dady yayi murmushi yana mamakin yanda mutane basa gane shi da sauri. "Yanzu to me ya ƙara ne?"
Ya dubi mutumin ya ce "don Allah ko har yanzu Malam Sani yana gidan shi na nan?"
Mai shagon ya ce "yana nan."
Dady ya koma mota ya rubuto check na dubu É—ari biyu ya ba mai shagon ya ce "Ka bashi ka ce Zakka ce nima an aiko ni ne."
Mai shago ya amsa jiki na rawa duk da bai san ko nawa bane tunda bashi da boko.
Shi ma dubu ashirin Dady ya bashi, ya tafi cike da tausayin Affa kasancewar Allah bai bashi namiji ba bare ya taimaka mishi.
Wannan hutun ma Mom ɗin su Munira ta matsa sai su Ruƙy sun zo mata musamman ma da za'ayi bikin ƙaninta kuma itace Uwar biki, Ruƙy daƙyar Affa ya barta, suna isa suka ci karo da Zayid dama tunda Munira ta ce mishi zasu zo shikenan ya shiga rawar jiki,ko yarinyan da zaya aura yasha bata labarin Ruƙy, tun tana fushi, har ta daina ƙwana ɗaya da zuwan su aka soma biki Munira ta kai su gyaran gashi da lalle, Uncle Jamil ƙanin Mom shine mai auran babban ɗan ƙwangila ne yana da kuɗi sosai ƴar Maiduguri zaya aura.
Sun halarci guraren bikin, har zuwa ranar dinner inda Ruƙayya tayi ƙwanciyar ta tace ta gaji ba zata ba,sukai ta naci taƙi, Mom ta ce "tashi kuje Ruƙy ai daga yau shikenan.
Ado sosai suka yi domin tunda suka zo sabon kaya suke sawa duk Mom tai musu har da jakunkuna da takalma, tare da Bros Zayid suka tafi dan ya ce ba zai je da Jalila ba.
Suna shiga gaban Ruƙayya ya yi wani irin mummunan faɗuwa nan take ta soma jin wata alama da ta jima har ma ta soma manta yanda abun yake,sai yau gurin dinner,tabbas ko shakka batayi matsawar ta ji wannan abin to Dady yana gurin,dan haka sai taji duk jikinta yayi sanyi daƙyar ta shiga, suna zaune a table ɗaya dasu Munira M Bash da Sadiya Armaya'u da kuma Bros,ido kawai Ruƙy take rabawa taga ta inda Dady zaya fito bata gani ba,ta na kai ganin ta ga ango da amarya, sun yi ƙyau sun kuma dace suna zaune,sai kusa da su ga wani table ɗin Ruƙy ta ce "Bros wancan kujerun na wanene?."
Ya ce "na abokinshi ne." Kafin tayi magana sai taga Dady sun shigo da Zainab jerowa suka yi sun sha ado tamkar amarya da ango,nan taji abin magana ya É—auka "Ga babban aminin ango ya iso Yusuf Mansur, Yusuf wanda aka fi sani da Son Guy."
Tsigar jikin Ruƙy ya tashi yar musamman da taji ance tare da amaryar shi Zainab nan da nan kanta ya sara ta soma jin sanyi.
Tana jin su Munira suna cewa kan uba wannan haÉ—aÉ—den Guy É—in fa? Bros Zayid ya ce "Yaro da kuÉ—i kenan, abokin Uncle Jamil ne, amma ya dama Uncle a kuÉ—i, wannan babban yaro ne sai a hankali Guy É—in nan.
Tuni zazzaɓi ya rufe ta haka haƙoranta sai haɗuwa suke yi ta ce cikin makyarkyata,Bros Zi...,Bros Ziyad zo ka kaini gida bani da lafiya shi yasa nace ba zan zo ba."
Ta bayan mutane ta bi dan kada ya ganta, Bros ya kaita gida, shi ma Dady a nashi ɓangaren gaban shi ya faɗi kuma jikinshi ya bashi Pretty tana nan, sai dai shi tunanin shi mai zai kawo ta nan ita da aka ce mishi tana aure ƙauyen Katsina, sai dai fa koma menene tana nan gurin dan har ma ƙamshinta ya shiga ji,dube-dube da ƴan waige-waige har Zainab tana tambayar shi ko lafiya, ya ce mata babu komai.
Kuka sosai Ruƙy ta yi cikin dare har zuwa wayewar gari, shikenan Dady ya ci amana ya karya alƙawari ya yi aure ya manta da ita, ashe Dady zaya daina sonta? Lallai namiji a gaida maza basu da tabbas haka ta ƙwana da safe dole Mom ɗin su Munira ta yi ma Doctor ya zo ya duba Ruƙayya bayan tasha allurai ta samu bacci.
Shi ma Dady a daddafe ya bari aka gama dan dai yana matsayin babban abokin ango shiyasa ya haƙura ya na sauke Zainab bai saurari sallamar da zatai mishi ba, ya yi gaba,bin motar tayi da ido har ya ƙule ta ce "kai mutumin nan halin shi daban ne."
Washegari Ruƙy ta ce gida zata je amma sai Mom ta hanata ta ce sai gobe haka suka kuma ƙwana duk sun kasa gane kanta sai kuka take yi, koda ta koma gida ma Umma ta kasa gane kanta, sai dai cewa tayi kin san Umma ƙarshen wata shi yasa jikina ya soma mutuwa, Umma ta ce "To ai sai azo a siyo maganin da ki ke sha."
Ruƙayya ta yi tsaki ta ce "Magungunan nan masu shegen tsada haushi suke bani."
Umma ta ce "Aiko kina jin daÉ—i tun da baya yi miki mugun ciwon nan."
Ta ce "Sai dai kuma haka."
Umma ta ce "Au na manta na gaya miki ranan nan wani ya bada check a ba Affanku,wai zakka har dubu É—ari biyu ne,ko nawa ne, kuma ba'a gane ko wanene ba,dan Mai shago ya ba shi kuma mai shago ya ce bai gane ko wanene ba,dan shima ya bashi dubu ashirin."
Ruƙayya ta ce "To ko wanene Allah ya bashi lada haka dama ake son zakka.
Karatu babu kama hannun yaro su Ruƙayya Allah ya kawo su shekarar ƙarshe, sai dai inda da hali suna gamawa su je law school wata tara sai dai taji Munira ta ce mata da tsada amma ai komai yana gurin Ubangiji tunda da farko ma bata zaci zata gama karatun ba.
A ƙwana a tashi babu gurin a wajen Allah sun cikin sa'a wata biyu bayan nan aka soma shirye-shiryen bikin Munira su Ruƙayya manyan ƙawaye an soma yawo ba zama, ango Mustapha ya yi murna da ganin Ruƙayya,daya ke yana jin labarin ta gurin Munira, sun gama da abokan ango sun yi maganar komai bikin zaya kasance ne ranar sati saboda aiki, don haka tun Monday zasu soma bikinsu.
Ranar Lahadi kayan da zasu sa na musamman ne,dubu ashirin Affa ya ba Ruƙayya ta sai ma Munira gudunmawa suka haɗa da Sadiya Armaya'u suka buga zannuwa,Bros Zayid ma ya bata kuɗi duka ta haɗa.
Suna saloon ranar Monday sai ga wata yarinya ta shigo, Ruƙy tana ta satar kallon yarinyar domin tana ganin kamar ta santa, ta ce sannunku suka amsa.
Ta zauna ita ma gyaran kai tazo, haka komai yasa sai Ruƙayya taji bata son yarinyar, can sai yarinyar ta dubi kan Ruƙayya ta ce "Kai amma gaskiya kina da gashi,ga cika ga tsawo."
Ruƙy ta ce "To nagode,kema ai ba laifi."
Ta cire ɗanƙwalin ta, "kin ganshi dai.
Nata gashin tsawo ne dashi babu cika. Ruƙayya ta ce "Ga naki kina son na wani "
Suna cikin hira sai wayar yarinyar ta soma ringing,ta ciro ta ce "wanene zaya dameni?"
Tana dubawa taga sunan, cikin sauri ta ce "Oh My husband ya ya ne?."
Ko me yace? Sun dai ji tace "Ok, yau? Sai kuma suka ji ta ce "bikin ya zo ne? "Oh wannan satin lallai biki ya zo,to sai iso." Ta kashe waya.
Da yake mayyar surutu ce, sai ta dubi Ruƙayya ta ce "wanda zan aura ne ya je Holand shi ne yake gaya min zaya dawo don bai gama abin da ya kaishi ba, kuma ga bikin friend ɗin shi "
Sadiya ta ce "karatu ya je ne ko?"
"A'a harkokin kasuwanci shi ne ya kaishi sati biyu za yayi da,yau ƙwanan shi taƙwas kenan."
Ruƙy ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya."
Sun gama sun barta nan, Munira ta ce,"Kai wannan ta cika surutu tamkar an tambaye ta."
Ruƙayya ta ce "Ni fa haka nan batai min ba."
Sun iso gida suka samu sauran ƙawayen amarya na nan cikin garin Abuja sun iso, don haka sai suka haɗu suna labarin yanda kowanne program zaya kasance.
Sadiya Armaya'u ita ce tafi sauran damuwa ta ce "Gaskiya Munira abokan angon nan sun cika ƙwauro, gaskiya su ƙaro kuɗi ba zamu yi yanda muke buƙata ba.
Munira ta ce "nima naga haka shiyasa na ce ma Al-Mustapha sun mana ƙwauro,ɗari da hamsin ya yi kaɗan." Sauran suka ce gaskiya.
Munira ta ce "Ya ce in kuɗin be isa ba zaya ƙara mana yace dan ɗayan abokin baya nan ne shi yana da kirki yafi sauran,yana da zumunci."
Ruƙy ta ce "Kada dai mu nuna musu maitarmu a fili fa."
Ruƙy tana wanka ta ji ana "ga ɗayan abokin da ake labari ya zo, sai kawai ta ji gabanta ya yi mugun faɗuwa ta soma jin alamar Dady yana gurin, jikinta yayi sanyi Sadiya ta zo tace, "Ruƙy kiyi sauri ki zo ga wannan Guy ɗin da ake labari Allah ya kawo mana shi."
Ruƙy ta ce "Ku je kawai Armaya'u yanzu ma na soma wankan." Ta ce don Allah kiyi sauri ganin ki zai sa ya bamu ko nawa muka buƙata tunda waɗancan masu maƙon ma ganin kine suka ƙara."
Ta ce "To jeki zan zo." Guri ta samu cikin toilet ɗin tayi zamanta, hawaye suka ƙwace mata,ta tabbata ko kaffara ba zata yi ba, Dady ne ya zo,su shida suka fita duk da amarya, abokan kuwa su biyar ne banda ango Dady tun shigowar su unguwar nan jikinshi ya bashi Pretty tana nan. Suna tsayawa ƙofar gidan ya soma tunanin ko dai ita ma tazo bikin,to dalilin wa? shi ne bai sani ba.
Bayan sun gaisa sam fuskarshi babu walwala, Master É—aya daga cikin abokan shine ya ce "Gafa É—ayan abokin mu ya iso kema amarya nasan baki san shi ba ko?.
Munira ta ce "Kaman dai na taɓa ganin shi, ina wuni?."
Ya ce "Lafiya,ya gida?"
Ta ce "lafiya."
Master ya ce "Ai ku ma ƙawayen amarya sai a gaisa ko?." Suka gaisa da Dady Sadiya ma ta gane shi.
Ya dubi Master ya ce "Kun gama komai ko?"
Master ya ce "Ƙwarai."
Ummi cikin ƙawayen ta ce "A'a suna son ƙarin kuɗi.
Master ya ce "Kun cika rainuwa mune fa zamu kama hull mu kawo drinks.
Sauran ƙawayen suka haɗa baki "Gaskiya ɗari da hamsin yayi mana kaɗan."
Sadiya ta ce "Ok Ruky M ko to tana wanka gaskiya ba zamu kira ta ba, komai Ruky sai ta ce kada mu matsa muku shiyasa ku kafi son magana da ita."
Dady yana jin su kuma duk da yasan ba Pretty É—in shi ba ce sai ya samu kanshi da son ganin Ruky M ya dubi amarya, to Ruky É—in tazo muji ta bakinta.
Wasu daga cikin ƴan matan sun ji haushi yana ta share mutane daga jin ance Ruƙy ya yi tsagal ya ce a kira ta.
Munira da kanta ta je ƙofar toilet ta ce "To sai ki fito ya ce dake zaya yi magana.
Ta ƙoƙarta ta ce "Bazan fito ba ku ce dashi kome ya ƙara ko nawa ne shikenan."
Yanda Munira ta ji muryar Ruky sai bata matsa mata ba ta juya. Ya na jiran ganin Ruky ta ɓullo sai ya ji Munira tana cewa har yanzu bata fito ba,dama fa ita in tashi ga wanka sai Allah.
Ta ce dai wai kuyi mana ƙari, ya ce "Check zan baku ko cash."
Suka ce "Cash don kasuwa zamu shiga."
Ya ce "To sai naji gida,dan ban fito da kuÉ—i ba,zan ba Master ya kawo."
Suka haÉ—a baki "A'a mudai gaskiya kada ka bashi."
Ya ce "To wa zan ba?"
Suka ce "Mudai kowa zaka ba ka ba amma ban da Master."
Master ya yi dariya ya ce "Kun min muguwar shaida ko?"
Suka sa dariya suka ce "Mun san zaka iya ragewa." Nan dai suka yi sallama.
Yaron shi Sunday ya yi ma ƙwatance ya kawo kuɗin, bayan an gama musu zanan dayis da suka yi gidan Aunty Farida sai suka wuce kasuwa.
Washegari Mom tayi mother day an cashe sai ranar Laraba suka yi Sister Day nan ma ba maza sannan sai Launching, Dady bai samu zuwa launching ba don yana Kaduna duk da zuciyarshi tana matuƙar son taga Ruƙayya ɗin nan, gashi ba zaya dawo ba sai ranar ɗaurin aure, kuma zasu halarci dinner yana jin shi da Zainab.
Yau ne ɗaurin auren Munira M Bash bayan gama ɗaurin aure an gabatar da walima anan cikin gidan su inda Malama Rukiya ta yi musu wa'azi mai shiga jiki tayi tsokaci kan zaman aure da kuma ƴan mata waɗanda basa son aure,ba dan sun rasa masu son su ba sai don wani dalili nasu na daban, gaba ɗaya Ruky sai tama ji tamkar dan ita akayi wa'azin,tayi tunanin wanda take wannan kanshi ya ma yi auren shi ya manta da ita don haka ita ma zata san abin yi don tunda ya karya mata alƙawari ta haƙura dashi garama da matsalar ta fito ta gurinshi, hawaye ya zubo mata,sam bazata iya zama da kishiya gidan Dady ba garama in wani ne amma ban da Dady,shi ɗin na daban ne a zuciyarta.
An kai Munira gidan ta dake Maitama, za'a je dinner ita kam ta yanke shawarar bazata je ba saboda ta san zaya yi wuya Dady bai je gurin ba kuma ita bata son su haÉ—u, tafi son koda zasu haÉ—un itama tayi aure ko kuma ta kama mijin auren a hannu.
Dan haka duk ƙawayen sun zube akan gadon amarya suna ta labari yawanci batsa tafi yawa a cikin hirar tasu. Ruƙayya wadda tayi shiru tana dubansu ta dubi Sadiya Armaya'u da ke ta faman zuba labarin yanda daren farkon ta zai kasance in anyi auren su da Shitun ta tace "Ke Armaya'u baki fa kida mutunci dan na kula da ace Hajiya zata ƙyale ki tsaf zaki kai kanki gidan shitun.
Sadiya ta ce "Ba dai ke kin tsaya yanga ba,dubi haɗaɗɗun Guys a B.U.K yadda suka mutu a kanki amma ki kai ta wulaƙanci."
Munira ta ce "Har kin tuna min da Faruk yaron nan ya mutu kan Ruky."
Sadiya tana dariya ta ce "Kai munci kuɗin Guy ɗin nan,sai muce zamu shawo masa kanta,kin ga yanda yake mana ƙyauta da a alƙawaruruka in mun shawo masa kanta zaya bamu."
Ruƙy ta ce "Ai ku dama ƴan iska ne."
Kafin wata ta ce wani abu phone É—in Munira ta soma ringing Ango Al-Mustapha ne yake sanar da ita su shirya ga motoci nan zuwa,wai zo kiga shiri gurin amare ko ince Æ´an matan amarya.
Ruƙy kam tana ƙwance lakadan tana duban su ɗaiɗai, Munira ta ɗaɗa mata duka "Ki tashi ki shirya Malama kin wani min ɗai ɗai a gado."
Armaya'u ta ce "Kin san ta gurin ƙwaliya ba dama, kallon mu kawai take yi,a ranta tana cewa kuyi ku gama zan baku assignment."
Su Ummi suka ce "Gaskiya Ruky aƙwai ta da tsara gay,in tana guri sai kiga duk ƙwalliyar ka ta zama dusu-dusu."
Na tashi zaune ina faÉ—in "Dukkanku nagode da zagi ke M Bash har da gorin gado ko? Ni ma ki jira nawa gadon very soon."
Armaya'u ta ce "Um kamar da gaske mu dai kawai ki shirya Malama."
Ta koma ta sake ƙwanciya tare da jawo filo "Ni fa ba zan je ba,Gara ma kun daina damuna da wani batun shiri."
Munira ta ce "Kina ƙarya ne." Ta soma ja mata hannu.
Ta ce Allah da gaske nake yi, babu inda zan je.
Suna ga kamar wasa ne amma sai Ruky tayi ƙiri-ƙiri ta ce bata zuwa.
Ran Armaya'u ya ɓaci ta ce "Haba Ruƙy M yama zaki ce wai ke bazaki je dinner ba, Ruky ta ce "To ai sai kiyi, tunda na ce baza ni ba,ba sai ku barni ba,ko dole ne? Ta ci gaba da ƙwanciyar ta ƙafa ɗaya kan ɗaya tana taunar cingam.
Munira ta ce "Shikenan nima na fasa zuwa tunda haka ne."
Sauran ƙawayen da wasu ƴan'uwanta suka ce don bazata ba,sai ki fasa lallai ma Munira.
Munira ta cire rigar da ta soma sakawa tare da nunkewa tana faÉ—in "Wallahi matsawar baza ta je ba,nima na fasa."
Mamakin ta ne ya cika sauran ƙawayen yayin da Ruky abin ya bata dariya, ta ce "M Bash kina hauka ne zaku tara mutane kice ba zaki je ba? Ashe kuma zaki bawa angon ki kunya kenan ko?"
Tsaki Munira ta ja, sannan kuma ta haye kan gadon itama, Armaya'u ta zauna bakin gadon tana cewa "Bani phone É—in ki."
M Bash ta ce "To ba ga ta nan kusa dake ba."
Armaya'u ta É—auka kai tsaye number angon ta nema.
Ga zaton shi amarya ce har ya ce "Sweet Darling kun gama shiryawa ne."
Armaya'u ta ce "a'a ba ita bace ni ce Sadiya Armaya'u dama zan sanar da kai ne cewa,wai Ruky da Munira sun fasa zuwa gurin dinner É—in don haka sun ce ka sallami jama'an daka tara."
Ya ce "What,Me ya faru ne? Munira ta me? Sadiya ta ce "ban san me ya faru ba kuma ga Muniran nan."
Ya ce "Bata phone É—in Please."
Sadiya tana dariya ta miƙa ma M Bash wayar. Cikin shagwaɓa ta ce "Hello Babyna." Ya ce "Sweet Darling me yake faruwa ne, ance kin fasa zuwa dinner ɗin.?"
Cikin shagwaɓa tamkar zata rushe da kuka ta ce "Ba Ruky M bace tace wai ta fasa zuwa nima shi ne kawai na fasa Please ka zo da kanka in kana son na je sai mu lallashe ta ko?"
Ya ce "four mint gani nan."
Shi da Master suka zo har cikin bedroom ɗin suka shigo yanda suka ƙwanta tuni suka tashi suka sake, Munira tana ta ɗan danne-danne a waya kanta na saman cikin Ruky, Al-Mustapha dariya suka bashi ya ce "Haba Ruƙy ke kuma da zaki gyara wasa sai kuma ki ɓata."
Ta tashi tana dariya ta ce "Ban ɓata ba Al-Mustapha na ce bazan samu zuwa bane shi ne wannan shagwaɓaɓɓiyar amaryar taka tace ta fasa sai ka ce kaine kace ba zaka je ba."
Ya ce "To ke me yasa bazaki bane?"
Ta ce "Wani dalili ne kawai."
Master yasa baki "Haba baby a gurin nan na boby kin gane?"
Al-Mustapha ya ce "Kai kuma malam kai mana shiru."
Ruƙy ta harari Master, ya ce "Allah ya huci zuciyarki Baby gani nayi kin fi sauran aji ko baki san aji ba?"
Al-Mustapha ya dube ta "don Allah Ruky saboda menene?"
Ta ce "Gaskiyar magana aƙwai wanda bana son mu haɗu da shi.
Ya ce "Kada ki damu ba zaku haɗu ba."Nan dai ta yarda zata daƙyar........
Ku ɗan ƙaramin haƙuri zuwa na uku dan jin yadda zata kaya..
Taku Halima Abdullahi K/Mashi