Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KALBIM BOOK 1.txt
Chapter 2 of 7
Cigaba da aikin abinci da maman keyi tayi tana cewa
"Eh nace mu tafin amma tace basai antafi ba
A bari zuwa anjiman idan bata dena jin yanayin ba sai mu tafin kawai"
Wayar Sayyid dince tafara ringing da sauri ya daga ganin Hamman ne yake kira.
Yana dauka kai cikeda girmamawa ya gaidasa yana cewa Ummitan ce batajin dadi.
Shiru ABDULAZIZ yayi batareda yace komaiba sbd yanda yaji a zuciyarsa a duk lokacinda akace Ummitah batajin dadi wani irin nauyi da daci yakeji ya cike zuciyarsa sbd ganin kaman ya gaza ne har akai mata auren wuri daya sakata a halinda take ciki wanda bata isaba yake gani kwata kwata hakama an sauya masa tsari da burinsa gaba daya akanta dan kuwa duk gwagwarmayarsa da nemansa akanta ne sbd ita ne,
Komai dayake son ya zama a rayuwarsa sbd Ummitah ne,
Sbd ya inganta rayuwarta ya hanata shiga quncin daya taso a cikinsa,
Sbd ya bata farin ciki da gatan da kowanne da zai samu amma a lokaci daya an sauya masa komai an lalata masa rayuwarta ta hanyarda baida zabi bayan karban hakan hannu bibbiyu dan hakan nema ya karbi Sayyid tareda alqawarin inganta rayuwarsa shima kamar qanin dasuka fito ciki daya.
Numfashi me sanyi ya sauke tareda bude baki a natse yace
"Ku shirya gaba dayanku yau komai dare zaa taho a tafi daku,
Karku bari Ummitah tayi komai hakama basai kun tafi asibitin ba,
Zanyi magana da Ummitah"
Da sauri Sayyid din ya bawa Ummitah waya ta amsa ahankali tareda dorawa a kunnanta ta ambaci sunansa ahankali cikeda kewarsa datake tsananin ji da buqatansa a kusa da ita.
Jin sautin muryanta cikin sanyi daya sauka a kunnensa ya sanyasa miqewa ahankali daga inda yake zaune ya nufi bakin window din dakin ya tsaya yana sauke numfashi mara sauti zuciyarsa na sake daukan wani irin nauyi da dacin rashin kasancewansa a kusa da ita a daidai yanzu datake tsananin buqatansa.
"Ummitah" ya ambaci sunata ahankali cikeda nutsuwa da sautinda ita kadai yakewa magana ahakan sbd matsayinta rayuwarsa gaba daya daban yake da komai.
Hawayene masu dumi suka gangaro mata ta rintse idanuwanta kuka mara sauti na zuwar mata a karo na farko tace masa
"Hammah inason ka dawo dan Allah,
Hammah inason na haihu a hannunka kaman yanda aka haifeni a hannunka,
Hammah ka.......
Kasa qarasawa tayi sbd hawayen da suka tsananta mata gudu haka kawai buqatansa take a kusa da ita sbd ita kadai tasan yanda take jin cikin jikinta.
Mama da sayyid shiru sukai jikinsu na sanyi batareda kowannensu ya iya cewa komaiba saima tsinkewa da mama tayi tana ajiye aikin datakeyi batareda ta juya ta kallesu ba.
Acan bangaren shiru yayi tareda kasa cewa komai dan duk abinda zai samu a aikin daya kawosa ko shine zai qarasa sauya rayuwarsa to tabbas saiya bar qasar ya koma gida a goben nan.
Kasa cewa komai yayi ya kashe wayar bayan yace mata ok kawai dan babu me basa umarni yace ok ko yes kawai sai buqatan Ummitah kadai kaf rayuwarsa kuwa a yanzu.
Yana kashe wayar kai tsaye ticket ya kira aka siya masa ya shirya komawa gida.
Yana gamawa wayar Alh saad ya kira ya sanar dashi a samar masa driver yaje ayau din koman dare ya dauko su Ummitah shima gobe insha Allah zai dawo.
Ummitah kuwa tana miqawa Sayyid wayarsa kasa dagowa tayi ta kalli kowannensu sbd sosai takejin jikinta ba dadi.
Sayyid da maman ma jin sukai hankalinma yafi karkata ga tafiyar sbd jikin Ummitan dan haka ba wani bata lokaci suka fara bankwana da mutane shima sayyid din gida ya koma gurin iyayensa tareda Ummitah duk da batajin dadi amma hakan ya lallaba suka tafi sukai bankwana sosai kowa na tausayawa Ummitan sbd duk ta sauya ta fara kumbura sosai irin na masu cikin daya fara tsufa.
Duka kayansu Mama kyauta tayi dasu tin daga kayan sakawa har kayan amfani da komai,
Sayyid ma kusan komai nasa kyautarwa yayi sutaransa kawai ya bari suma basu fi kala biyu ba ya bari.
Ummitah kwata kwata bata cikin walwala sbd yanayinta dan haka sayyid da mama suka matsu driver ya iso su tafi sbd akai Ummitan asibiti.
Karfe uku na yamma driver ya iso da lafiyayyar motar ABDULAZIZ din aka daukesu daga garin gaba daya bayan sun rabu da yan uwa da abokan arziki ana kukan rabuwa na tafiyar da baa san ranar haduwa ba.
Sayyid Mahaifinsa har cikin ransa yakejin sanyin jikin rabuwa dansa namiji daya tal sedai kaman yanda ABDULAZIZ yayi masa alkawarin Sayyid zai zama abin alfaharinsa kuma har abada ya riga ya zama yaya kuma dan uwan Sayyid din ya saka yakejin damuwarsa bin iska.
Mama ma tayi kukan rabuwa da yan uwanta duk da batada uwa da uba a garin amma tanajin radadin rabuwa dasu.
Ummitah kuwa nauyi kirjinta yayi mata bata iya ko kukan ba sai jajir da idanuwanta sukai mata tanajin ita kam kamar har abada bazata taba dawowa ba ta tafi kenan,
Wani nauyin ta sake jin ya danne kirjinta ta dafe kirjinta ahankali tana zubawa mutanen dake musu bankwana a tsaye ido tana rasa tinanin yi.
Rufe musu kofar mota akai ta zubawa kofar gidansu idanuwanta da suke sake yin ja...
Ahankali aka tada motar aka tafiya ahankali sai alokacin taji wasu irin hawayen da batasan dasuva suna gangarowa akan fuskanta ta rintse idanuwanta ahankali tana dora hannunta akan cikinta dake motsawa da karfi.
Shiru sukai babu motsin komai a motar sai sanyin ac dayake ratsasu babu wansa zuciyarsa batai nauyiba sbd Allah ne kadai yasan rayuwar datake gaba tana jiransu.
Tafiya sukeyi sosai da gudu akan titi da lafiyayyar motar da basa jin iskar komai bare kuka karfe ko jijjigar karfe sbd lafiyar motar da tsadarta.
Qarfe 11 dare suka isa Abuja kai tsaye gidan ABDULAZIZ din aka nufa dasu wanda yake a tsare kaman bana ABDULAZIZ dinsu da suka saniba,
Dayake dukkaninsu suna cikin sanyin jiki da damuwar rabuwa da gida basu tsaya kalle kalle sosai ba Matar Alhaji Saad Anty Maryam taxo ta kawo musu mai aikin da aka tanadar musu tareda abincin da zasu ci lafiyayye sai dakunan dasuke na kowannensu da aka nuna musu.
Dakin Ummitah shine a can daban palonsa kusa da nasa Master bedroom din
Sai dakin Mama dayake dayan palon shima babba lafiyayye dana mai aiki a kusa da nata sai Dakin Sayyid lafiyayye babba da shima yake palon tareda lafiyayyen toilet aciki.
A cikin gidan babu wanda dakinsa baa zuba masa komai na jin dadi da tsarin masu kudi ba.
Sallolin dayake kansu suka fara yi kafin sukaci abinci ba bata lokaci bacci ya dauke kowannensu har Ummitah dake fama da jikinta gajiya ta sakata baccin dole ciwon na tafiyarsa.
Washe gari me aikin gidan ce Fiddausi ta tayardasu sallah dukkaninsu sbd gajiya da sanyin ac ya sakasu wani irin nannauyan bacci.
Suna gama sallah babu wanda ya fito duk da Ummitah tana dakin mama a tare suka kwana sbd sabo.
Karfe 9 na safe Fiddausi ta gama komai na breakfast da gyaran gidan taje ta sanar musu suka fito cin abinci.
Fiddausi ta kaisu har dining ta nuna musu su zauna suka zauna suna kallan gurin dayake kaman wani shagon saida gilasai da qwan lantarki sbd haske da katon madubin console dayake kallansu a gurin.
Ba wani abincin da bazasu iya ci bane doya ce da egg sauce sai Pepper meat da kunun gyada dayaji madara.
Ummitah ce kuzarinsu da yanayinsu dan haka ganin ta samu warwarewa tana cin abincin ya sakasu sakewa suma sukaci abincin cikin jin dadi da mamakin arzikin da ABDULAZIZ din yake rayuwa a cikinsa duk da bai ragesu da komaiba shiyasa basa cikin yunwa sa kwadayi ko kadan daman can.
Suna gamawa Anty maryam na isowa gidan daukesa kayan sakawarsu da aka tanada tin kafin zuwansu.
Sayyid ne kadai babu kayansa se ta saka haydar danta ya daukesa ya fita dashi dan siyyyar nasa kayan.
Ummitah ta kalla cikeda kulawa da tattalinta sbd sanin wacece Ummitah a rayuwar ABDULAZIZ yasa duk wanda yake kaunarsa to tabbas saiya kaunaci Ummitah ma sosai.
Sannu tai mata tareda wuni a gidan tana nuna musu komai tareda debe musu kewa tinda bayanan ABDULAZIZ din.
Ko aranar ABDULAZIZ bai samu isowaba dan haka dole anty maryam ta taho gidan da yaranta duka suka sake yiwa su Ummitan wuni suna debe musu kewa tareda kokarin ganin sun sake batareda nuna qyamar ganinsu yan kauye ba.
Cikin jikin Ummitah ya saka Anty maryam ringa nuna mata wata irin kauna sosai da kulawa dan hakan ne ma mama taji tana samun nutsuwa da sakewa dasu.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_Arewabooks@Mamuhgee_*
20/21
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
*************
A cikin qananin lokaci suka ji suna samun nutsuwa da iyalan Alh saad wanda shima ya shigo sun gaisa har so biyu ya kuma cewa anty maryam da kanta takai Ummitah asibitin taga doctor kafin dawowan ABDULAZIZ.
Da safe suke shirin Anty maryam din tazo suje asibiti dan haka a ranar a dakin mijinta ta kwana sbd Shine zai tasheta tinda asuba sufara shiri bare kuma daman Ummitan da kanta ta tafiyarta gurinsa itama mama bata hanaba tinda kila idan ABDULAZIZ din ya dawo bazai barsu guri daya ba sai Ummitah ta haihu ta koma masa yanda yake ganin ya kamata ta koman.
Irin tsananin Asalin son da Sayyid kewa Ummitah kusan a duniyarta ABDULAZIZ ne kadai nasa ya fi nasa sbd So me tsaftar dayake mata daga Allah ne shi ya halitta masa shi a zuciyarsa,
Kwana yayi a zaune yana kulawa da ita tareda tarairayanta yana jin kaman ya rabata da cikin jikinta taji sauki hakama shi kansa ya shirya bazata sake haihuwa yanzu ba tinda ciwo da wahala cikin yake sata hakama yana tsoron wani abin ya sameta koda agurin haihuwa ne bare ya sani ko Hammanta ABDULAZIZ bazai bari ta sake haihuwa anan kusa ba idanma bai rabasu ba akan sai sun gama karatun dayace zasuyi.
Karfe tara suka fito a shirye tsaf suka nufi dakin mama wadda tinda tai asuba bata koma ba tana zaune tana jiran lokacin zuwan nasu asibitin yayi.
Dining suka nufa wanda suka ga ancika sa sosai ayau din fiyeda kullum hakama abincin dayake kai a yau an samu sauyinsa.
Mama ce ta zauna Sayyid kuwa Ummitah yake kokarin taimakawa ta zauna
Ahankali wani irin qamshi me sanyi ya fara shiga hancinsu mai nutsuwa,
Ahankali Ummitah ta dakata daga zaunawan da zatai tana dago fararen idanuwanta dasuke sak da nasa ta waiwayo cikin sanyi hancinta da gurin suna sake gauraya da qamshinsa.
Sayyid ma qamshin ya sanyasa sakin hannun Ummitan Ahankali yana juyowa sbd Tin ranar farkon haduwarsa da Hamman ya riqe qamshinsa sbd Kaunarsa da Allah ya dasa masa arai shima sbd Ummitah.
Inda suke kalla Mama ta juya ta kalla taga mene sbd ita hankalinta da hancinta basu wani bata tinanin qamshinba.
Daidai lokacin ya sako kai a natse cikin wani irin kwarjinin daya saka Sayyid sauke kansa cikeda girmamawa yana kasa qure kallansa akansa sbd ba kwarjininsa kadaiba hatta hasken fatarsa datake wani irin shining na hutu da kwanciyar hankali tareda daula datake samu ya saka kyansa yin yawa.
Ummitah ce ta qure kallanta akansa tana jin dukkanin jikinta na mutuwa wani sanyi yana sauka zuciyarta yana mamayewa,
Batada abinda yafi mata dadin kallo a rayuwarta sama da kallansa a gabanta,
Kyansa da asalin kammminsu dasuke iri daya amma shi ya sauya gaba daya komai nasa daban yake da nata sbd rayuwar da inda suke rayuwar ba dayaba,
Hasken idanuwansa zuwa dogon hancinsa ta kalla tana rokon Allah ya basa tsari da kariya daga dukkan sharrin kowace mace a duniya.
Shima ita yake kallan cikeda wata irin kewanta dake cinsa kaman cikin kansa zai kunce dan haka yana isowa hannunsa duka biyu ya bude ya rungumeta yana karanta mata adduoin tsari da kariya itada abinda yake cikinta kafin ya saketa ya saki wani Kyakkyawan murmushin daya saka sayyid kasa dena kallansa da tattausan sauti yace
"Sorry Ummitah ABDULAZIZ,
Yaya,ya jikinki?
Kafin ta amsa gurin mama ya juyo cikin kulawa da sakewa da girmamawa yace
"Barka da safiya Mama,
Yaya fama da sauyin guri?
Na sameku lfy??
Murmushin farin cikin ganinsa tayi tana cewa
"Duk lafiya kalau
Sauyin guri kuma ai munata kokarin sabawa,
Tafiyar dare kayi kenan?
Zaunawa yayi Ahankali yana cewa
"A cikin dare na iso sai ban tasheku ba tinda kun riga kuna hutawa"
Sayyid ma zaunawa yayi yana cewa
"Barka da dawowa"
Kallansa yayi cikin kulawa da sakar masa fuska sbd ya sake yace
"Thank you,yaya kaima kanata fama da kadaici right?
Gyada kai Sayyid yayi yana kokarin sakewa da hamman.
Ummitah na gefensa fuskanta cikeda da murmushi me kyau da nutsuwar data kwana biyu bata iyawa sbd yanayinta.
Breakfast suka fara cikin kokarin sakewa dasu dukkaninsu sbd sayyid ya sake dashi tinda tsakaninsa da mama da Ummitah babu wani kamewa ko rashin sakewa.
Bazai taba tina yaushe Zuciyarsa ta samu asalin farin ciki irin wanda yake cikinsa a yanzuba sbd kasancewarsa dawowa rayuwa a guri daya da Ummitah wadda babu ranarda zasu sake rabuwar gurin rayuwa daban daban har abada sedai rabuwar kwanaki na tafiya dayake yawan yi sun hadu kenan sai mutuwa insha Allah,
Kallan Sayyid dake cin abinci yayi a natse yana kallan Ummitah yaji zuciyarsa na sake karban Sayyid din cikeda Kauna sbd Aurensa dayake kan Ummitah bazai rabasa da ita ba tinda shi kansa mahaifinsa a hannunsa ya basa amanarsa kuma ya karba har Abada insha Allah.
Yanzu ne yakejin Nutsuwa da godewa Allah da hakan dan Sayyid dinne kadai Ummitah zata aura suci gaba da zama a taredashi,
Ahankali ya bude bakinsa cikin sauti me nutsuwa da rashin sauti yace
"Thank you Sayyid"
Kallansa sukai dukkaninsu dukda ba sauti yayi maganar cikin turancinsa dayake kashe Sayyid.
Mama ce kadai da batasan wani thank you ba bata kallesa ba.
Bai wani ci abincin ba hankalinsa na kan Ummitah wadda ita kuma idan yana tareda ita take cin abincin dama bata saba cin ba sbd jin take komai nata ya bude.
Mama tasan daman indai yana tareda Ummitah ba wani abincin kirki yake ci ba dan haka bayan Ummitan ta gama sai ta kallesa cikin kulawa tace shima yaci abincin.
Tea da chips mara maiqo yaci yana gamawa gaba dayansu suka miqe suka bar dining din.
A shirye yake sbd yasan da kai Ummitah asibitin dan haka ma ya fito da wuri da sai yakai guraren 11 bai fitoba.
Key din mota da wayarsa ya fito dasu a hannunsa sai tsadaddiyar Hular fcap ta fendi daya sako ya fito.
Daga shi sai Ummitah din suka fita sai sayyid mama a gida suka barta yace ta koma bacci ta huta.
Shine yake driving a hankali Sayyid na zaune a gaba sai Ummitah din dake baya tana kallan garin cikeda shaawa da burgewa.
Sayyid dayake yana fitowa sosai suna tafiya gurare daman can sai baya wani kalle kalle sosai sbd ya saba ganin ire iren hakan.
Wani babban private clinic me tsada sosai yakaita suna isa babu wani jira ko bata time a asibitin sbd kyanta akai mata registern Prenatal visit da zata ringa zuwa.
Wani Dr Ken ne ya dubata dakyau cikeda kulawa ganin Yanda ABDULAZIZ sam tsananin kaunarsa akanta bata boyuwa duk da bai saniba ko shine mijinta ko yayanta koma waye a gunta kaunarsa a bayyane take.
Scanning akai mata bayan angama diban jininta da sauran samples na aune aune da zaa mata.
Cikin kulawa da sake fuska sosai yana tayasu murna ya kalli ABDULAZIZ daya dawo dakin bayan angama Scanning din yace
"Congratulations Sir its a baby girl"
Kallan Tvn yayi Ahankali kafin ya dawo da kallansa kan Ummitan da itama shi ta kalla suka kalli Sayyid a tare wanda farin cikinsa shima yake a fili sedai a duk lokacinda ABDULAZIZ yake kusa baya zaqewa akan Ummitah dama cikinsa dayake jikinta sbd kawaici da nauyin ABDULAZIZ din.
"Thank you dr" Yafada yana karban result din suka fito yana rasa yanayin dayake ji a zuciyarsa duk da abu daya ya sani shine kome Ummitah zata haifa ya fito a cikinta,jininta zai kaunacesa kaman yanda yake tsananin kaunarta.
Sun dade a asibitin sbd formalities din da daukan time da kuma aune aunen,
Suna baro asibitin kai tsaye shopping mall ya biya dasu aka siya fruits masu yawan gaske suka wuto gida sbd bayason yayi yawo da Ummitan dan yanayinta.
Suna isowa gida barwa Sayyid ita yayi ya wuce bangarensa dan Amsa waya da kuma fitowa sallah dan time yayi na laasar sunyi azahar already acan.
Dakin Mama suka nufa sayyid da Ummitan.
Zaunawa tayi gefen mama tana dan kwantawa jikin maman tana cewa
"Mama harna dan gaji"
Murmushi mama tayi tana shafa fuskanta da kulawa tace
"Ummitan Mama Allah dai ya nunamun kin haihu lafiya dan ki samu hutawa kema"
Murmushi tayi tana dafa cikin sbd motsawa da yayi tana cewa
"Amin Mamana"
Sayyid zainawa yayi yana fadawa maman duk abinda akai dama abinda dr yace cewan mace ce
"Kai jamaa har yasan abinda zaa haifa kenan shi likitan"
Dariya sayyid yayi yana cewa
"Ba gashi mun saniba kuma nasan Shima hamman daya sani yasan 'ya zai samu irin Ummitah ba namiji ba dan bansan tayaya zai sake dashi ba amma macen ita ya saba yasan yanda zai tarairayeta kamar mamanta da haryanzu taqi sanin ta girma"
Harararsa Ummitah tayi tana sake kwantawa jikin maman tace
"Maman Ummitah kina jinsa dai ko?
Yanzu ina cewa zan fadawa hamma zai fara kama kansa amma ita mama ka renata kana fada mata hakan"
Dariya yayi yana daukan ruwan sanyin da Fiddausi ta kawo ta ajiye musu ya bude yasha yana cewa
"Mama kinji zata lauye zance na ko??
Dariya maman tayi tana cewa
"Ai ku duka indai hakan ne kun renani sam bakwa jin kunyata ko kadan"
"Mama shine dai bayaji tinda shine sirikinki nikuma ai bazanji kunyan mamana ba"
Katseta yayi da cewa
"Nima ai Maman tawa ce shiyasa banajin kunyarta"
Dariya maman take musu tana cewa
"To ya isa naji ni na hakura tinda babu wanda yakejin kunyar tawa a cikinku
Nima kuma banason aji kunyar tawa tinda maman taku ce kaman yanda kuka fad"
Bata fuska Ummitah tayi tana sake hararsa tana cewa
"Gaskia Ni mama saiyaji kunyar mamana tinda a gidansu inajin kunya sosai fa"
Dariya yake mata datake qarawa Kyakkyawan fuskansa shima kyan ganin yace
"Bafa zaki sakani jin kunyar mamana ba tinda dai nima na zama dan gaban goshinta nama kusa kamoki"
Tashi tayi daga jikin maman tana kallanta zatai magana maman ta katseta da cewa
"Kyalesa fada yake dan kiyita fitinar rashin dalili,
Banda kamarki a rayuwata kinji Ummitan mama"
Murmushin jin dadi tai tana harararsa shima dariyar yake mata.
Miqewa yayi yana ficewa sbd sallah da ake kira.
Bedroom dinsa ya nufa ya shiga toilet yayi alwala ya fito daidai ABDULAZIZ ya fito cikin wasu kayan daban ba wanda suka dawo dashi ba a jikinsa suka nufi masallacin tare yana tambayarsa yayiwa mama bayanin yanda Ummitah zata ring shan maganinta koda baya nan.
Eh ya fada masa suna isa masallacin dayake estate din nasu.
Suna dawowa daga masallaci abinci sukaci tareda shi da Ummitah da sayyid sedai Fiddausi ta kawo fruits da aka gyara wanda shi sune best abin shansa dan haka Ummitah ma su ya sakata sha sosai bayan taci abinci.
Suna gamawa palonsa ta bisa acan suka zauna shida ita yana wayoyinsa da fira da ita da biyewa zantukanta.
Sai magrib suka suka fito ya tafi masallaci ita kuma taje daki tayi sallah
Sayyid baya nan sai da akai sallan ishai suka dawo gidan shida Hamman.
A palo suka zauna su dukansu suna fira da mama wadda taketa biyewa Ummitah sa sayyid yake sakowa gaba da tsokana amma yana dan kaucewa sbd Hamman dayake gurin.
Hamman yana lure dasu da yanda sayyid ke tsokanarta sai ya dan dauke kai yana fira da mama sbd kada ya takurasu.
Sunci abincin dare banda shi sbd baya buqatan cin wani abincin tinda da yamma sukaci lunch energy drink kawai yasha yayi wanka yayi shirin bacci ya kwanta.
Ummitah sayyid ne ya bata Maganinta bayan tayi shirin bacci tukuna suka kwanta a dakinsa.
#MAMUH
#HOTLOVE
#ROMANCE
#CRAZYLOVE
#THE GREAT AZIZ AY LIMBA
#JANNAH DZAD ZAADEN
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
21
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
***********
Washe gari breakfast kawai suka gama su anty maryam suka iso gidan da yara gaba daya nan mama da Ummitah sukai murnan zuwansu.
Sai guraren 11 ya fito suka gaisa da anty maryam da yaran tukuna ya fice gidan tareda sayyid.
A gidan su anty maryam suka wuni har dare tukuna suka tafi sai alokacin ya samu ganin Ummitan da kyau tana palonsa har bacci ya fara daukanta kafin suka rabu.
Washe gari ma fita yayi da Sayyid wansa yake kokarin sakawa a jikinsa sa huldodinsa duk da karatun zaiyi amma yana buqatan ya sakasa a business dinsa tinda shekarun Sayyid din sun wuce a ce sai yanzu ne zai fara university.
Mama da Ummitah kwata kwata basu samu kansu a cikin wani kadaici ko damuwa da kewan gida ba sbd ABDULAZIZ shine farin ciki da abinda suke buqata a rayuwarsu to tinda suna tareda shi babu wani abu dasuke buqata ko kewa sbd ya maye gurbin duk wani abu da rayuwarsu take buqata,
Inda yake shine inda suke buqatar kasancewa kuma a dik inda yake acan farin cikinsu yake so babu komai a yanzu rayuwarsu bayan kwanciyar hankali da farin ciki tareda nutsuwa.
Sayyid ma yanda ABDULAZIZ LIMBA yake jansa a jikinsa cikin Rashin damuwa da rashin saninsa akan wasu abubuwan yana kokarin sauya masa rayuwa a lokaci mara tsayi ya sakasa yake sake jin matsayinsa yana wuce sirikinsa yana jinsa tamkar dan uwansa na jini tamkar yayan da suka fito jini daya dan haka ya bude kansa sosai dan fahimtar komai ya zama wanda ABDULAZIZ LIMBA zaiyi alfahari dashi.
******Rayuwa ta sauyawa su Ummitah,umma da sayyid harma dashi ABDULAZIZ din dayake tareda familynsa yanzu,
Rayuwa tayi dadi ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa sbd suna tareda junansa a cikin arzikin da Allah yake sake bude masa tareda matsayinsa dake qara yin sama hakama ya zama abokin manya dan abokan huldansa na nan din duk manyan mutane ne,
Jin dadi da daula babu abinda bai wadata fmlynsa dasu ba,
Babu abinda suka nema suka rasa,
Rayuwa suke ta tsari da farin ciki,
Tsananin kaunar dake tsakaninsa da hasken idaniyarsa ya qaru baya boyewan da Familyn Alh Saad suke mamakin irin wannan kaunar da shaquwar da basu taba gani ba sbd basu taba ganin abinda ABDULAZIZ LIMBA baya wasa ko kadan dashi ba yake bawa mahimmanci fiyeda kansa da rayuwarsa kamar Ummitah da abinda yake cikinta,
Bayan Ummitah a rayuwarsa mama itace mutum ta biyu da bai hada da komaiba amma ita kanta maman tasan Ummitah itace rayuwarsa da har take tausayinsu duk ranar da Allah ya dauki daya a cikinsu yabar dayan.
Duk ta tino akwai ranar hakan ko bayan sun tsufa sai taji hawaye na cika mata ido tsoro na kamata dan kuwa koda bata duniyar ita alokacin tasan Allah ne kadai zai hana wanda aka bari zarewa.
Fatanta Allah ya saukakawa kowannensu kaddarar da Allah ya rubuto musu ya zama gata ya basu kariya daga sharrin duk sharrin dayake duniyar.
A rayuwarta bata da adduar tin daga ranar da suka dawo hannunta sai tasu,
Uwa da ubanta kadai takewa addua sai ABDULAZIZ da Ummitah sbd mantawa takeyi ma da ba itace ta haifesu ba sbd kaunarta akansu ta gaskia da tsafta ce.
Cikin Ummitah yanata sake kusantar watannin haihuwarsa cikin Aminci da lafiya dan ta dena yawan ciwukan datake ta fama dasu wanda yawancinsu damuwace dake cin zuciyarta akan rashin 'dan uwanta.
ABDULAZIZ LIMBA duk tarin ayyuka da schedules dake gabansa basa hanasa bawa Ummitah kulawan datake buqata daga garesa dan kuwa bai taba hada hidimarta da komaiba,
Kowanne dare tana tareda shi sai lokacin baccinta yayi ta tafi dakin mijinta tayi kwanciyarta,
Kulawan dayake bata daban take da kowa a gida,
Su mama ma basa hanasa sosai aka basa damar kulawa da yar uwarsa yanda ya kamata,
Duk ranar zuwa awonta shine da kansa yake ture ayyukan gabansa yakaita da kansa a dubata y dawo da ita.
Siyayyar haihuwarta aka fara wadda yake yinta kamar ba baby daya zata haifa ba,
Duk baqin ciki da quncin dayake a zuciyarsa na rashin da suke ciki a alokacin da aka haifi Ummitah da yanda suka ringa yawo da ita batada suturar sakawa a kan cikin Ummitah ya rage radadinsa dan kuwa bazai taba mantawa da hakanba har abada,
Bayan irin wadda yakeyi haka ya saka Anty maryam daukansu Mama da Ummitan sika ringa fita siyayyar haihuwan.
Kaman yanda mama batada adduar daya wuce nemawa rayuwar ABDULAZIZ din albarka itama Ummitah batasan uwarta batasan ubanta sai ABDULAZIZ wanda yake uwa da ubanta dan haka adduarta koyaushe akansa ne sai mama da sayyid wanda shima tasa kaddarar tazo a cikinsu dan shima kauna me karfi da tsafta yake musu.
Sun fara sabawa sosai da abujan sbd famlyn gidan Alh Saad da suka zama tamkar family daya dasu kuma koyaushe suna tare da anata hayaniyar datake saka ABDULAZIZ sakewa Anty maryam da yaranta kudi sosai sbd suna saka familynsa farin ciki da walwalwa babu wani ji da kai,
Shi kuwa duk wanda zai saka Ummitah da mama dariya da farin ciki babu abinda bazai iya masa ba dan haka itama anty maryam dataga hanyar cin arzikinta tazo sai bata tsaya cutar da kanta da girman kai ba ta zage tana nuna musu kauna da kulawa harma da yawo datake daukansu suna fita harsai da ABDULAZIZ din ya dan taqaita musu sbd Ummitah bayason tana yawaita yawon sbd yanayin.
Dr ken ta nasa bangaren ya dage da kulawa da Ummitah wadda results dinta ya sakasa yin wasu test akanta da sunan checkup sbd bincikensu akanta daya nuna komai nata lafiya kalau da kuma bgroup nata da sauransu.
Shekarunta dasuke kusan daidai dana wanda ake nema yake sake sakasa jin son tsananta bincikensa akan lafiyarta duk da a dayan bangaren tsoro ne me tsananin gaske yake cikasa akan hakanan sbd ABDULAZIZ da har yanzu baisan alaqarsa da ita ba kuma alamu suna nuna shima kila zai iya kisan akanta kaman yanda ake neman rayukan akan wadda akeson bawa new life suma.
Numfashi ya sauke a lokacinda dukkanin sakamakon full binciken da yayiwa lafiyar Ummitah wadda kusan 99% sun samu abinda ake buqata,
Baima taba samun matching kamar hakan ba wanda komai yayi fiyeda ma abinda ake buqata.
Numfashi me zafin gaske ya sake saukewa a karo na babu adadi yana jin zuciyarsa na shiga tsoron aikata abinda yake son aikatawan sedai kuma Alkhairan da burikansa da zaa cike masa harma fiyeda yanda yake burin na son barin qasar zuwa uk dan fadada karatunsa tareda iyalansa cikin wadata ya sakasa jin kuma zai iya aikatawa.
Dafe goshinsa yayi yana sauke ajiyar zuciya me karfi,
Hada takardun yayi tareda sakasu a folder qarama ya saka a envelope yayi sealing tareda tattara wayoyinsa da laptop dinsa ya miqe ya nufi kofa ya fita office dinsa ya rufe ya nufi parking lot inda motarsa take ya bude ya shiga ya tada yaja yabar asibitin yana fidda wayarsa dan kiran wanda zai miqawa takardun dan baisan Asalin su waye suke buqatan heart transplant dinba dan kuwa duk wainda aka saka aikin barnar basusan asalin su waye masu aikin ba kawai dai sun san zasu bar qasar bare ma a gane career dinsu ya lalace.
Washe gari Ummitah tazo ganin likita tareda ABDULAZIZ wanda zaiyi tafiya me mahimmanci a kwanakin hakan ya saka kawai gabaki daya Ummitah ta sauya jin tsoron tafiyar tasa data samu kanta a ciki mai tsananin dayake yawan fadar mata da gaba dan haka ahankali zazzabi yake yawan shigarta.
Dr ken kuwa ganin yanayin Ummitan ya sakasa jin wani irin farin ciki sbd akwai alluran dayake buqatan yi mata.
Babu wani bata lokaci cikin nuna kulawa da tattali yana rarrashinta yayi mata alluran suka dawo gida.
#MAMUH
#BESTLOVE
#ROMANCE
#JANNAH ZAD
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
22
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
**************
ABDULAZIZ tafiyar ta zamar masa dole ne dayake buqatan yi wanda zaiyi ne ya dawo a qanqanin lokaci kafin ta shiga watan haihuwanta da baifi wata daya ba dan haka yayi mata alkawarin kafin lokacin zai dawo insha.
Shiru tayi ahankali a lokacinda ya gama fada mata hakan yana kallanta da fararen idanuwansa da suka sauya sbd yanayinta,
"Fatima" ya ambaci sunanta cikin nutsuwa da sauti mara karfi cikeda sanyi.
Kasa dagowa tayi sai wasu irin hawaye masu dumi suka gangaro ahankali kan fuskanta tanaji bugun zuciyarta na bugawa sosai.
Handkerchief ya ciro daga aljihunsa ash yana qamshi ya dago fuskanta da hannunsa daya yana goge mata batateda ya iya cewa komaiba.
Jin tayi wani irin abu yana taso mata mai radadin data rasa sanin menene ta fasa wani irin kuka mara sauti da ciwo tana qanqame hannunsa dayake riqe da fuskanta.
Ja Idanuwansa sukai take zuciyarsa na cikewa da wani irin dacin da shima baisan daga ina yake sauko masa ba,
Kukanta ne yake ratsasa yana rusa duk wani sanyi da kuzarin dayake rayuwarsa gaba dayanta,
Ahankali daqyar ya iya furta sunanta na asali wato Fatima a karo na biyu sedai ya kasa cewa komai kukanta ne kawai ke ratsa kunnuwansa yana rusa kuzarinsa.
Wani irin nauyi da radadi takeji a zuciyarta na rabuwa dashi wanda bata taba jinsaba a rayuwarta amma bazata iya fada masa hakan ba sbd tana fada komai alkhairi da cigaban da zai samu a tafiyar zai iya fasawa akan hakan dan haka ta dago idanuwanta da sukai jajir ta kallesa tana taqaita kukanta dan ganin yanayinsa kuma ta san ba komai zai iya cewaba.
Ajiyar zuciya me sanyi ta sauke tana kallan idanuwansa da sukai jajir ya zuba mata su baice komaiba,
Ahankali ta sake murmushin karfin hali daya bayyanarda kamarsu sosai kaman an tsaga kara ta bude baki tace
"Hamman Ummitah Allah ya tsareka idan ka tafi ya baku dukkanin Alkhairin dayake cikin wannan duniyar da tafiyar"
Numfashi ya sauke mara sauti kalamanta na dukan zuciyarsa ya dan rintse idanuwansa ahankali ya bude ya bude baki da nannauyan sauti mara hayaniya yace
"Bakyason na tafi saikin haihu right??
Zuba masa idanuwanta tayi tana kallon Asalin kyau da haibar da Allah yayi masa wanda tasan duk macen da Allah yayi itace matarsa tayi dacen namijin da duk wannan kyan halittar tas zuciyarsa tafi kyau da tsafta.
Girgiza kai tayi ahankali tana riqe hannunsa cikin nata dakyau ta sanyin murya me nutsuwa tace
"Aa,ka tafi ina jiran dawowanka insha Allah kafin na haihu...
Numfashi ta sauke me sanyin daya sakasa kallanta ta dago da sanyi muryanta na fitowa a tausashe tace
"Hammah ka dawo da wuri sbd inason na haihu kana nan,
Inason kafara daukan abinda zan haifa kaman yanda kaine kafara daukana dana taho duniya..
Shiru yayi yana tino rayuwar azaba da gararin dasukai shida mahaifiyarsa a lokacin renon cikin Ummitah....
Wani irin nauyi da daci kirjinsa ya cikeda dashi jikinsa na mutuwa yana kasa kallan Ummitan data zuba masa ido tana karanto dacin dayake cike zuciyarsa idanuwanta suka ciko da hawayen da suka gangaro gefen idonta.
Ranar haihuwarta ya tina irin ukuba da qangin da mahaifiyarsa ta shiga tareda juyewan hankalinta tareda gararin datai cikin rashin hankali har bacewanta...
Hawayenda tin lokacin batar mahaifiyarsa bai sake sanin ya ake zubdasu ba sbd taurin zuciyar dayake dashi ne suka ciko Kyawawan idanuwansa ya rintse idanuwan yana hadiyesu dan radadin Rashin mahaifiyarsa shine radadi mafi munin dayake yanka zuciyarsa.
Ahankali Ummitah ta kwantar da kanta kafadarsa tana kasa cewa komai sai hawayen da suke gangaro mata tana son ta tambayesa kamannin Mahaifiyarsu da mahaifinsu da bata taba saniba sedai tanajin radadin dayake ji na tinano ranakun quncinsu na baya da suka wuce dan haka bata iya cewa komaiba shiru kawai sukai babu wanda yace komai har kusan dare sosai ta tashi yakaita har dakinta ya kamo hannunta ya saka mata wani tsohon hoton daya tsufa sbd har ruwan sama yasha sosai sbd wahala ya juya ahankali ya wuce bedroom dinsa.
Zaunawa tayi a sanyaye bakin gadon dakinta tareda dago hannunta da yayi mata sanyi ta bude hoton ta zuba masa idanuwanta da suka sauya sbd kukan datai sosai.
Hoton Mahaifinsu ne tareda Hamman yana qarami sanye da uniform din makaranta a ranar daya fara kaisa makaranta a ranar sukai hoton a makarantar me hoto yayi musu shi
Murmushi baban yakeyi fuskansa a sake sosai yan riqe da hannun ABDULAZIZ din shima Murmushin yakeyi na farin cikin zuwansa makaranta.
Wani irin abu takejin yana tasowa a kirjinta me nauyin gaske tsananin son Mahaifinsu na mamaye zuciyarta
kuka mara sauti ya taso mata ta silale a gurin tanayi tana jin tausayin Hammanta wanda ya rasa uwa da uba dan ita kam shine uwa da ubanta.
Sayyid ne ya shigo dakin gabaki daya gidan a sanyaye kowa yake ba walwala sbd Ummitah gaba daya ta sauy kwana biyun bata cikin walwala musamman da tafiyar Hamman gobe ce sai gaba daya yau ta rikice bata jin dadin komai hakama suma duk sun shiga damuwa.
Ko kadan a daren Ummitah bata rintsa ba hakama ABDULAZIZ din kwana yayi yana mata adduar Allah ya saukar da ita lafiya.
Da asuba koda ya dawo sallah wanka kawai yayi ya shirya ya fito dan 7 jirginsa zai tashi,
Sanye da Black UGG knit top da Straight jeans ya fito sai fcap ta balenciaga yana qamshi me sanyi ya fito Sayyid tini yakai kayansa mota ya dawo.
Fuskansa tayi wani irin fresh yayi fayau sbd rashin rintsawar da baiyiba da damuwar datake cin ransa dayake ganin tafiyar da zaiyi ne yabar Ummitah a wannan halin.
Cikin dauriya da danne damuwar ta harma da ciwon datakeji ta fito itama fuskanta tayi fayau ta qarasa har gabansa ta miqa masa hannu tana sakin murmushi me kyau dan kwantar masa da hankali.
Ajiyar zuciya a fili ya sake ahankali yana mata kallan tsafta ya miqa hannu ya kama hannunta data basa sukai musabaha ta sauke ajiyar zuciya tana sake qanqame hannunsa cikin nata tace
"ALLAH ya baka nasara akan abinda zakaje ya baka nasara a duk abinda zaka nema a duniya ya kuma dafa maka ya hanaka damuwa kowace iri ce...
Shiru ta dan yi kafin tace
"Allah kuma ya dawo da kai lafiya Hammah"
"Amin ya furta ahankali yana kallan cikin idanuwanta da ita shi take kalla tana murmushi me kyau da nutsuwa.
Mama ya kalla da sayyid yace
"Idan akwai abinda ya taso a kula sosai a tafi asibiti akirani,a kula"
Addua mama tai masa itama tana masa fatan dawowa lfy.
Hoton daya bata jiyan Ummitah ta fidda a cikin dayan hannunta ta saka masa shima a hannunsa tana cewa
"Nagode Hammah"
Murmushin karfin hali shima yayi mata yana shafa fuskanta ya matso kaman yanda ya saba ya karanta mata adduar dayake mata tin tana yarinya ta neman tsarin ubangijin a kunnenta ya share mata hawayen da suka gangaro mata tana murmushi ya juya ya shige mota yana daga musu hannu.
Sayyid ne ya shiga motar sbd tareda shi zasu Airport din da drivern gidan Alh Saad.
Motarsu na barin gidan gidan ta sauke ajiyan zuciya me karfi tana jin wani abu kamar yabar jikinta dan haka mama ta jata suka koma cikin gida.
Koda Sayyid ya dawo daga Airport bai dameta ba kyaleta kowa yayi sbd ta samu ta warware da kanta sedai hakan bai yiyiba dan kuwa zazzabi me qarfine ya kamata wanda ya sakasu damuwa.
Haka suka wuni da ita har dare batajin dadi sedai tace ba buqatan zuwa asibitin dan haka sai baa takurataba.
Washe gari ma haka ta wuni cikin yanayi na rashin lafiyar datake cinta a hankali,
Fama su mama suka fara da ita sbd gabaki daya lafiyar tana neman gagaranta sbd wani irin silent ciwo take fama dashi wanda ta rasa menene yake damunta itama hakama da kanta ta hana a sanar da Hamman sbd kada ya shiga damuwa tace zata iya daurewa har lokacin haihuwanta ya qara yi tinda ta kusa.
******ciwon kwana daya kwana biyu zai qara gaba yakeyi cikin tsananin azabar da bata taba saniba take a yanzu hakama batasan me zatace yana damunta ba ga damuwar datake damun zuciyarta da kwata kwata bata mata dadi,
Wata irin rama me muni ta fara da wani irin haske dayake bawa mama da sayyid tsoro sosai hankalinsu ya tashi sosai kuma har lokacin sun kasa fadawa ABDULAZIZ din.
Zuwansu asibiti biyu dr yana dubat yana ce musu lafiyarta kalau kawai yanayi ne na haihuwan daya matso.
Dawowa sukai gida suna cigaba da kulawa da ita sedai tashin hankalinsu da tsoronsu tsananta yakeyi sbd qarewa takeyi kamar wadda mayu suka kama takai komai tafara gaza yiwa kanta jinya takeyi sosai wanda ya fara taba lafiyar cikinta.
Dole suka tattara suka sake komawa asibiti gashi anty maryam bata nan su kadai suketa Fama sai drivern da aka samar musu sbd fitarsu.
********Dzad ne a zaune a lafiyayyar office dinsa dayake cikim mansion dinsu ya zare farin glass dinsa yana kallan Ammar wanda Maheer ma shi yake kalla.
Numfashi Ammar din ya sauke cikin samun nutsuwar biyan buqatan shekara da shekaru yace
"Komai na matar da aka samu zuciyarta ya kammala magani ya gama aiki akanta wanda kowane time a wannan stage din datake shine daidai lokacin da zataiwa Jannah donor,
Anyi bincike akanta ba kowa bace daga kauye suka taho suna zama gidan wani relative dinsu ne wanda baima cika zamaba so bandai tsaya nasan sunansa ba kokuma buqatan hotonsa sbd ba buqatan hakan,
Abu daya ne shine lokaci yayi zuwa jibi zaayi aikin wanda muke fatan wannan shine na karshe sbd baa taba samun matching din da ake tinanin yayi 99% ba kuma gashi cikin ya riga yazo lokacin haihuwa so the right and perfect time has come"
Maheer jin yayi wani nauyi da sanyi na cike zuciyarsa lokaci daya
Dad ma jin yayi bayajin komai baya buqatan komai kawai ayi aikin su samu abinda suke so shine burinsu.
Nutsuwa da nauyin daya danne musu zuciya shekara da shekaru ne sukaji dukkaninsu yana fada musu.
Washe gari ranar da zaayi aikin Anny ce ta bawa Jannah maganin data yanke jiki aka kwasheta zuwa asibitin sbd suna buqatan ta kasance a asibitin koda zaa shigo da Fatima Abdulaziz Ayoub din
Wannan shine sunan dayake jikin katinta.
Ummitah kuwa a daren ranar gabaki daya jikinta ya rikice jini ne yake mata zuba ba kakkautawan daya saka a cikin daren mama da sayyid suka kwasheta zuwa asibiti hankali tashe.
Dr ken yana asibitin daman yana jiran zuwansu sbd yasan hakan zata faru,
Dayake ansan shine dr dinta kiransa akai da gaggawa
A rikice cikeda kulawa da tashin hankali yayi kanta yana kiran nurses.
Naquda ce ya tayar mata tareda mata allurar da zata hanata iya haihuwa da kanta dan haka hankalin nurses ya tashi gashi bleeding takeyi sosai gashi tayi wani irin ciwon data jima acikinsa ya bayyana sosai a jikinta.
A cikin daren ganin an kasa shawo kan matsalar take yayi mata transfer zuwa ZADEEN HEALTH CEN.
Su mama da sayyid tinda suka gwada kiran Hamman baa samesa ba sai suka maida hankali kan Jikin Ummitan da aka tabbatar musu ba sauki gashi private hospital ce babu mutane sosai sbd tsadarta da tsarinta.
Dr ken kallansu yayi cikin nuna damuwa da kokarinsa yace
"Haihuwace tazo mata gadan gadan gashi lokacin bai qarasa yiba sbd bata bude ba gashi kuma babyn ruwan dayake rayuwa a cikinsa cikin cikinnata ya tsiyaye dole Aiki zaa mata a cire babyn idan ba hakanba komai zai iya faruwa da ita har babyn dan haka aikin Gaggawa zaa shiga da ita a acikin daren nan anan likitocinmu duka basa nan Nayi muku transfer zuwa qwararriyar asibitin da muke da ita Kusa yanzu can zaa tafi da ita.
Babu abinda mama da sayyid ke nanatawa bayan sunan Allah cikin matsanancin tashin hankali dan haka basuda zabin daya wuce aminta da hakan.
Cikin ambulance da gaggawa akai Asibitin da ita koda suka isa tafara nisa dan haka Hannu kawai sayyid ya saka a takardun komai aka shige tiyata da ita suna kallonta kowannensu idanuwansa na cikowa da hawayen dake zana radadi a zukatansu har aka shige da ita aka rufo kofar wadda ta saka kirjin mama bugawa da wani irin ciwon daya sakata dafa bango tana silalewa qasa ta zauna har lokacin kirjinta na qara ciwo.
Sayyid kuwa sunkuyar da kansa yayi yanajin kaman kunnuwansa da kansa iska na musu yawa.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
23
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
*************
Wayar hannun sayyid da yayiwa wani irin riqon dayake gap da saka screen din lalacewa batareda ya saniba sbd damketa yayi zuciyarsa najin kamar zata baro kirjinsa sbd abinda yakeji,
Ummitah bayan mahaifinsa a duniya itace abinda yakeso fiyeda komai da kansa sbd baida mahaifiya shima ta rasu,
Ummitah itace wadda baya kaunar gani ko yanayinta kadai ya sauya dako ciwon kai bare damuwa ko wani babban abin,
Ayau gata a gabansu anshiga aiki da ita yankata zaayi a ciro abinda yake cikin amma basuda abin yi sbd Allah yin Allah ne da ikonsa.
Hawaye ne sika cika idanuwansa da sukai jajir amma sun kasa saukowa,
Wayarsa ya kurawa ido yana sake saka kiran Hamman a karo na babu adadi ayau din amma har lokacin bata shiga.