Best / Popular Hausa Novels

Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: KALBIM BOOK2.txt

Chapter 5 of 5

Cigaba da santin ganin yayansu kaman turawa su kawu sukai suna yiwa Allah godiya tareda zaadens din da suka riqesu da amanar gaske.

Modibbo ma sake yiwa Dad godiya yayi sosai akan Hakan kafin suka shiga firar duniya inda su Dad is sake tabbatarda maganar Saleem su Jannah da Fatma dai basu tafi kauye ba yawon shakatawa suka tafi da AZIZ LIMBA Wanda ya cucesu wlh da hakan.

Sai guraren 8 da rabi suka fito dukkaninsu Dan sake zuwa asibiti.

Hadda su modibbo aka fito a motar Muhammad ya daukesu da Fatma sbd su sake samun damar sakewa da yayansu.

Dad da Maheer da saleem da Ammar ma mota daya suka shiga zuwa asibitin.

Suna isa Jannah din ta farka amma Bata iya magna da kowa idanuwan nata ne kawai a bude tana binsu da Kallo ta qare musu Kallo tsaf babu Wanda tayi tinanin tana bude Ido tafara cin karo dashi.

Wasu hawaye masu dumi dumi ne suka gangaro mata ta lumshe idanuwanta tana amsa gaisuwa da sannun da kowa ke mata da Kai cikin sanyi.

Har dare sosai suna asibitin Saleem nata Kiran AZIZ baya samu hakama sayd wayansa Bata shiga Dan haka dole haka suka tafi dukda kusan kowa yasan rashin zuwan waye yake sake taba zuciyar Jannah din amma basuda yanda zasuyi sai fatar yazo din da kansa sbd ta Dan sake ta samu lafiyarta.

Fatma aka bari tareda ita suka koma gabaki dayansu harda Ummah wadda tana isa wanka tayi tai Shirin bacci ta kwanta kawai sbd already taci abinci.

******Sai karfe goma Sha biyun dare LIMBAS suka samu nutsuwarsu ta fara dawowa jikinsu sbd koda suka sauka Lagos jikin Nicky ya rikice sosai Wanda ya sakata har wani fixga takeyi take hankalin kowa ya sake tashi Dan haka kai tsaye daga airport ambulance ce ma ta dauketa zuwa asibiti gabaki dayansu can suka fara sauka suka fara addua da fatan samun lafiyanta sbd babu Wanda tausayinta bai gama sanyaya jikinsa ba a familyn.

Anyi nasarar itama tsayar mata da nata babyn daqyar sedai ita sbd wuyan datasha Bata farfado ba har lokacin.

Sai a lokacin duka familyn suka tafi gida,

Suna isa gida kowa wankan gajiya yayi sunyi sallolinsu already Dan haka abincin ma sama sama kowa yaci ya nufi daki ya kwanta sai baccin gajiya.

Wanka yayi ya shirya ya fito cikin brown sweatsets sbd Dan sanyin da akeyi ya fito sai a lokacin jammy ta kawo Masa milk tea me zafi sosai yasha ahankali tareda sponge cake.

Bai nema wayarsa ba bare ya kunna duk da dare yai babu me kira a lokacin amman bayason damuwa ko kadan Dan haka Sayd ne ya kira saleem Wanda ya turo Masa komai na inda taken Dan haka da kansa ya dauki key shi kadai yaja mota ya fice lokacin kowama yafara nisa a baccin gajiya.

Kai tsaye asibitin ya nufa yana isa Kai tsaye dakin datake din ya wuce yana sanye da hular Burberry data rufe har kunnuwansa kaman wani sabon matashin saurayi.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 73

Yana isowa dakin a natse ya miqa hannunsa zaiyi knocking kaman Fatma ta san ya iso ta bude dakin a natse sbd Saleem daya Kirata ya sanar da ita AZIZ LIMBA na isowa asibitin kowane lokaci.

Cikeda girmamawa Fatma ta gaidasa tana janyewa daga kofar zuwa gefe.

Amsawa yayi a taqaice yana shigowa qamshinsa me sanyi da ratsa zuciya na gauraye dakin da sanyin AC ya gama cikewa da kame koina.

Ficewa fatma tayi daga dakin tana zaunawa a doguwan kujeran dake kofar dakin tana kalle kalle a wayarta Samsung da aka sauya mata tini.

A natse ya tako ahankali cikin yanayi na samun nutsuwansa daya rasa tsawon lokaci tana dawowa Masa a Sannu tana shigarsa ya zuba mata idanuwansa masu haske yana sauke wata sanyayyan ajiyan xuciya data sauka cikin kunnuwanta

cikin baccinta taji kamshin datake tsananin kewa yana shiga hancinta a natse da sanyi,
Motsawa tayi ahankali batareda ta farka ba amma still shigarta kamshin yakeyi Dan haka ta bude idanuwanta ahankali sanyaye.

Akansa idanuwanta suka sauka yana tsaye akanta ya zubawa cikinta daya fito idanuwansa yana Jin wani irin feelings masu karfi na sake shigarsa akan cikin dayake nasa ne,'dansa ko yarsa ne a ciki da zasu fito duniya suyi bearing sunansa,jininsa gudan tsatsonsa.

Kafesa da idanuwanta da sukai laushi sosai tai suna Dan cikowa da hawayen tsananin kewansa da damuwan halinda ya sakata,

Maido da kallansa kan fuskanta yayi sbd Jin idanuwanta akansa ya Kafeta da nasa idanuwan yana mata kallan tsaf na mintina kafin ya janye idanuwansa yana zaunawa a sofa a hankali cikin nutsuwa ya kalleta yace

"Yaya jikin?

Kasa amsawa tayi sbd babu shauqi ko daya a cikin sautin muryansa Dan haka ta zuba Masa ido hawayenta na gangarowa ahankali.

Sake maimaita tambayarsa yayi cikin nutsuwa wadda ta sakata fasa kuka me sauti tana miqewa zaune ahankali tareda ziro kafafunta kasa zata miqe ya tashi tsaye yana riqeta da sauri idanuwansa da suka fara sauyawa sbd kukanta dayake shigarsa suna sauka akanta yace

"Kinsan me kike yi Kuwa?

Kukan ta sake fasawa tana fadawa jikinsa tareda qanqamesa tana cewa

"Kayi hakuri nidai bazan sake ba Dan Allah ka dena fushin haka wlh bazan iya dauka ba xuciyana ciwo takeyi I can't take it anymore please"

Yanda cikinta ya tokalesa ya sakasa kasa cewa komai sbd a Karan farko yaji tudun babynsa a jikinsa Wanda ya kashe duka jikinsa da zuciyarsa datake tsananin kaunarsu Dan haka Shiru yayi batareda yace komaiba yana Jin dumi da tudun cikinta na shigarsa cikeda wata irin kauna mara sirki.

Sake shigewa jikinsa takeyi tana kuka batareda yace komaiba har sai dayaga kukan yayi yawa zai iya sata ciwon Kai ya daga hannuwansa ahankali yana rungumeta cikin nutsuwa ya bude Baki yana cewa

"Ya isa kafin kukan ya saki wani ciwon"

Kamata yayi suna zaunawa ya zaunar da ita kan kafafunsa yana sake kallan cikinta yana mamakinsa ya dago ya kalleta Kanta a qasa ya zuba mata ido yanajin tausayinta duk da yana fushi da ita babu ranar da tausayinta baya cikesa da damunsa sbd Allah ya sani yana mata wani irin so ne Dan baisan Yaya zaiyi dashi ba Dan Kuwa yayi Masa yawan da shine yake fushin amman shine a cikin azabar sbd quncin dayake cikeda kirjinsa na rashinta da rashin jinta.

Lafewa tayi a jininsa sai a lokacin cikin muryan datake cikeda tsananin kauna da shauqinsu yace

"Yaya jikin naki?
Yaya baby limba?
Ya kikeji yanzu?
Akwai inda kike Jin sauran damuwa ne?

Dagowa tayi ahankali cikin sanyi ta kallesa sai Kuma taji tana Jin haushinsa akan fushin da yai da ita Dan haka ta miqe daga jikinsa ahankali tana komawa bakin gadonta ta zauna tana Dan hade fuskanta cikin Jin bacin Rai da gaske.

Karantar yanayinta yayi ya zuba mata ido take ya saki wani malalacin murmushi yana miqewa ya nufi inda take din cikin nutsuwa sedai ko isa beyiba ta miqe tana barin gurin zata nufi toilet ta shige ya riqota yana rungumeta ta baya yana Dora hannunsa akan cikinta ya shafa ahankali yana sauke ajiyan xuciya me sanyi ya bude Baki yace

"Fushin na menene Kuma? I tot mun gama fushi fushin Nan ko?

Zare hannunsa tayi daga kan cikinta tana kokarin sake tafiyarta ya sake riqota yana cewa

"Ok I'm sorry too"

Jin tayi ranta ya sake baci ta fasa Masa kuka tana cewa ya tafi basa sonsa itada baby limba din Kuma babynta baby Zad ne.

Wata murmushin mamaki ya sake yana cewa

"Meye baby Zad Kuma?

Da sauri ta kallesa tana turesa cikin fushi zatai magana yakai lips dinsa ya bawa nata lips din kiss ahankali me sanyi Wanda ya sakata Bata fuska tana turesa tace

"Banaso ka tafiyanka ma kawai"

Ganin da gaske takeyi sai kawai yafara rarrashinta yana kwantar mata da hankali ta gama kukan da fadar bacin ranta da fushinta ta lafe a jikinsa suka shirya abinsu.

Abincin da akai akai taci taqi ci shine ya Bata da kansa taci sosai Tasha ruwa ya zauna hannunsa na cikin nata sarqe da juna a cikin rifarta yana magana a ita cikin kulawa da sanyi harta fara Jin bacci.

Se datai bacci yabar asibitin ya tafi gida.

Washe gari ko data tashi gabaki daya su Dad sunyi mamakin ganin samun sauyinta sbd ta tashi da karfin jikinta da yar sakewa wadda ta saka farin cikinsu dawowa,

Ammar yana shigowa dakin yasan AZIZ LIMBA ya taho sbd kamshinsa da hancinsa ya shakar Masa Dan haka take ya fahimci dalilin warwarewan Jannah din baice komaiba ya kama kansa sbd ba huruminsa bane.

Suma acan LIMBAS washe garin Nicky ta farfado sedai kwata kwata babu kuzari ko wata lafiya me karfi a tattare da ita Dan haka fiddausi ce me kulawa da ita sosai cikin kulawa da tattali sbd kowa yanzu kokarin gyara kuskuren da sukai na shareta ta zama kamar Bata cikinsu yakeyi.

Batada kuzari ko lafiyan doguwan magana dan haka da ido take bin kowannensu da Kallo tana Jin inama ace tanada familyn da zata samu kulawa sosai a gurinsu irin Hakan da yanzu Bata samu Kanta a wannan rayuwan datake ciki ba.

Ciki dai gashinan ya bayyana a idon kowa ansan da tana dauke dashi amma babu Wanda yace mata komai akansa tukuna.

Tin daga AZIZ har Mama da kowa a familyn kulawa yake nuna mata da kauna batareda fara tinanin maganar cikin ba tukuna,

AZIZ bai fadawa Dr Nico halinda ake cikiba tukuna sbd yanason Nicky din tafara dawowa daidanta tukuna,

Kulawan da suke Bata da janta a jiki ya saka lafiyarta take samuwa sosai Dan daman kadaici da rashin kowa ne yake sake lalata lafiyan tata.

Kullum yana zuwa gurin Jannah asibiti itama yana dubata kowane dare acan yake kaiwa Asuba kafin ya fice batareda ya taba haduwa da kowane zaadens ba Saleem kawai yasan yana zuwan Kuma yana gari da familynsa gabaki daya Shima.

An sallami Jannah Takoma gida Dan haka tinda Takoma Bata sake ganinsa ba hankalinsa ya koma ka matsalar Nicky data warware sosai itama.

Ta bangarensu Mama dasu Fi da falaq yanda suke kulawa da ita da nuna son babyn cikinta ya sakata Jin tafara son cikin nata itama musamman idan yana motsawa Jin takeyi kaunar abinta yana ratsata sbd shine kadai familyn datake dashi idan yazo duniya sai yayanta Wanda ta yanke shawarar rashin komawa rayuwansa sbd ta basa damar zaunawa da macen dayake so ya aura tinda tana komawa zata iya sake zama sanadin rabuwarsa da ita.

Babynta shine ahalin datake dashi na jini Dan haka zata so abinta tinda Allah ya riga y kaddara mata Hakan Kuma ta runguma kaddarar tinda dai ta fahimci kowa daya zubar da tashin hankali ya rungumi zaman lafiya gashinan duka sun samu nutsuwa Dan haka itama sbd bawa babynta rayuwa nutsuwa da kwanciyan hankali ta saki komai akansa ta yadda ta shiryu.

********Kwanansu kusan Biyar basu hadu ba sai yau din da aka sallami Nicky itama ta warware tas ankoma gida da ita Kuma har cikin ransa sai yanzu yakejin yana kulawa da amanar da Dr ya basa sbd gashinan ta sake a cikin mutane tana sauyawa ahankali ahankali tana zama macen daya kamata ta zama Dan haka yanzu zaman Jin inda cikin jikinta ya samu ya rage yayi da ita Wanda ya bari ne yau ta huta daga dawowa asibiti zuwa gobe.

Karfe 8 na dare motarsa ta isa Zads Kai tsaye babu shakkar kowa Kai tsaye securities na ganin Lamborghini dinsa suka San Shine suka taso dukkaninsu suna Masa barka da zuwa tareda bude Masa gate din gabaki daya ya shige yana parking.

Saleem ne da Muhammad da suka dawo gidan daidai lokacin suma suka qaraso gurinsa Muhammad na bude Masa mota ya fito yana gaisawa da saleem kwarjinsa na sake cike idanuwansu sbd wani sirrin Kyau daya qara fuskansa fresh kaman koyaushe hutu ne bayyane tako ina.

Kai tsaye Palon gidan Saleem ya nufa dashi suna shiga Dad dasu Maheer dake zaune Palo da qamshinsa suka fara cin karo Yana shiga hancinsu da sauri Dad ya dago cikin ransa yana fatar LIMBA dinne da gaske sbd Jannah ta samu ganinsa ko zata samu farin cikinta data rasa amma a fili Dan kame fuska yayi yana satar kallan gefen Ummah da tsananin farin cikin ganin AZIZ din daya sako Kai ya cikata tana miqewa da sauri ta isa gurinsa ya rungumeta cikin jikinsa yana samun nutsuwan ganinta cikin farin ciki.

Cikin farin ciki ta tambayesa hanya da Kuma su Mama
Kafin ya amsa sakinsa tayi Jin palon tsit kaman ba kowa ta juyo,

Tana kallan Dad ba shiri ya washe Baki baisan ma ya furta

"Wow Masha Allah barka da zuwa"

Murmushi tayi tana kallan AZIZ din wanda yanda Dad din ya washe Baki gabaki daya ba shiri ya sakasa murmushi me nutsuwa yana Dan boye dariyansa ya gaida Dad din Wanda ya amsa dole yana washe Baki sbd ummah dayake neman shiri da ita.

Maheer ma ganin Umman ta kallesa da yanda Dad ma ya washe Shima dole ya Dan sake din suka gaisa yana zaunawa Saleem na yar dariyar mamakinsu su dukan.

Ammar ne kadai ya miqe tsaye da zuciya daya ya miqa AZIZ din hannu yana Masa barka da zuwa Shima a natse ya miqa masa suka gaisa yana cewa "thank you"

Fatma ce ta fito a sake cikin girmamawa ta gaidasa tana Masa barka da zuwa taje da Kanta ta kawo Masa ruwan sanyi da coffee din data San yana Sha.

Dad ne ya fara silalewa yabar palon kafin Maheer ma ya zame aka bar Ummah da Ammar sai Saleem da muhammd suka sake abinsu sukai fira sosai.

Jannah dince ta sauko tana shigowa palon sanye da doguwan riga mara nauyi da hula akanta qamshinta me sanyi yana shiga hancinsa direct Dan haka ya dago fararen idanuwansa ya Kafeta dasu tin Bata qaraso ba tareda mantawa ba shi kadai bane a palon.

Tana isowa ko zama batai ba Ummah tabar musu gurin sbd ganin yanda AZIZ din yake kallanta.

Ammar ma da Muhammad sallama sukai Masa suka bar palon.

Hannu ya miqa mata ta kallesa tana murmushi ta kama zata zauna gefensa ya miqe yana cewa

"Tafiya zamuyi"

Da sauri ta kallesa tana fasa zaunawa kafin ta Kalli Saleem Wanda baice komaiba ta dawo da kallanta kan AZIZ din zatai magana ya Dora hannunsa kan bakinta yana cewa

"Shihhhhhhh zamuga Dr ne"

Ajiyan xuciya ta sauke tana Jin hankalinta na dawowa daidai daga tashin da yai.

Hannunta ya kama suka fice bayan Fatma ta kawo mata mayafi qarami ta yafa suna fita.

Akan idon Maheer motar AZIZ din tafice da Jannah yana Kallo baida abin cewa zuciyarsa na nauyi da tinani kala kala.

Kai tsaye gida suka nufa suna isa ta kallesa da mamaki zatai magana yace

"Welcome home Mrs LIMBA"

Magana zatai idanuwanta suka sauka akan Doctors biyu da suka fito daga motar datake harabar gida suna yin ciki dan haka ta sauke ajiyan xuciya sbd ta dauka ya daukota kenan.

Suna shigowa palon farko na gidan daidai Nicky na fitowa da nata cikin Wanda yafi na Jannah din girma da wani irin shock Jannah ta zubawa cikin Ido Kanta na Sarawa kirjinta na nauyin da numfashinta yafara toshewa ta Kalli Falaq da Mama da suka fito da Nicky din cikeda kulawan data saka take shedan ya saka mata mummunan tinanin daya saka kafafunta kasa daukanta tana kokarin zubewa qasa Nicky data ga halinda take neman shiga da sauri cikin karfin murya tace

"Ba na AZIZ bane na Garba ne......

Da Mama da Falaq da fiddausi da Sayd dashi kansa AZIZ din cikin mummunan firgicin da basu taba shigaba suka juyowa da karfi suna kallanta a rikice Jin sunan Garba.

Jannah Kuwa qarasa kaiwa qasa tayi cikin sabon tashin hankalin daya juye mata Jin sunan Garba.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 74

Mama data rikice Kanta na juyewa batasan lokacinda tace

"Wane garban Kuma?
Garba na zaadens kokuwa Gabriel kike nufi Ayshatu??

AZIZ da kansa yayi wani irin nauyi har zuwa kirjinsa Jin yayi tashin hankali biyu na rufesa na Jin wai cikin Garba ne a jikin Nicky da Kuma Jannah datai tinanin cikinsa ne take neman illata Masa Kanta,

Amma duka kafin wannan Shima kallan Nicky din yayi idanuwansa na yin ja yana dawowa da hankalinsa da Tinaninsa daidai ya bude baki yace

"Waye Garba Kuma?
A ina yake?
A Nigeria ko Greece?"

Shiru tayi kowama Shirun yayi suna sake dauke wutar jikinsu sbd tsananin rikicewa da tashin hankali suna jiran amsarta.

Zufa ne yake gangarowa Nicky din yana jiqata Bata San Yaya ake Jin kunya ba sai yau datake Jin wata irin kunya me tsananin gaske tana rufeta sbd ambatar Garba da zatai a matsayin uban danta Kuma tasan itace ta Kai Kanta Kuma ta jawa Kanta komai,

Tayaya zata bude Baki tace itace ta fara jansa a lamarin Wanda ta tabbatarda kaman itace tai Masa dole duk da basa hayyacinsu amma babu abinda suka manta.

From fiddausi ce jiki a matiqar sanyaye zuciya cikeda firgici har lokacin ta qaraso gurin Jannah datake sake Jin rikicewan tinani ta kamata suka nufi kujera ta zaunar da ita a natse
Falaq ma gurin Jannah din ta qaraso ta zauna gabanta na tsananta faduwa itama da abinda suke kokarin ji me rikitarwa wai garba ne yayiwa Nicky din ciki.

Mama Nicky din ta kama suka qarasa suma suka zauna sbd kowa kafafunsa kokarin kasa riqesa sukeyi Dan haka kowama zaunawa yayi Banda sayd dayake kokarin tina ko yasan wani garban bana zaadens ba.

Shiru AZIZ yayi yana sake juya sunan Garba din a kansa yana kokarin tina Wanda ya sani me sunan bayan Muhammad na zaadens amma babu Dan haka ya sake Dora idanuwansa akanta tayi Shiru idanuwanta a qasa sunyi jajir hawaye cike dasu amma sun kasa saukowa sbd damuwa da quncin datake Jin ya cike kirjinta.

Cikin nutsuwa a kame yace

"Aysha,da naso barin ki huta daga zaman asibitin da kikayo kafin miyi wannan maganar ta waye me cikin jikinki amma Hakan bazata iya samuwa ba yanzu ina son sanin gaskiyan waye ne me shi?
Maana waye babansa sbd ina buqatan ganinsa Kai tsaye batareda batawa Kai lokaciba."

Shiru ta sake yi Saida Mama dake zufa ta tabata tana cewa

"Kaddarar samunsa ta riga tafaru a yanzu mafita ake nema ta yanda zaa fuskanci lamarin Dan haka kiyi magana,
Kin ambaci sunan Garba ne ko Gabriel bamu fahimta ba ki bude Baki kiyi bayani dallah dallah asan matakin dauka akansa idan ma wani abin ya Miki"

Ahankali hawayenta suka gangaro ta sauke numfashi me dumi da ciwo ta dago tana kasa kallan kowa ta bude Baki cikin sanyi da tsananin Dana sani sosai a muryanta tace

"Garban Zaadens ne Daddyn cikin......"

Wani salati me karfi Mama ta sake tana kallan bakin Nicky din tinaninta na kasa daukan zancen.

Fiddausi Kuwa cikin sanyi da mutuwan jiki taja Falaq suka bar gurin sbd zancen yayi nauyi da mamakin da kan Falaq ma ganin take bazai dauka.

Sayd guri ya nema ya zauna a natse sbd dai garban Zaadens din take nufi kenan ba wani garban ba.

Jannah Kafe Nicky tayi da idanuwanta da sukai jajir tana kokarin karantar idan ba sharri zataiwa garban ba sbd Kanta da zuciyarta bazasu taba dauka wai Muhammad dinsu ne zai zama uban cikin Nicky wanda kwata kwata ma basu San juna ba a ganinta bare Kuma tayaya ma wani abin me kama da wannan zai shiga tsakaninsu,

A ina? Ta Yaya?

AZIZ ma kasa kwantar da zancen yayi cikin kansa ya sake Kallanta ganin tana kuka cikin tausayi da kokarin dawo mata da hankalinta jikinta ya ambaci sunanta tareda nuna mata kusa dashi yace ta dawo Nan ta zauna.

Miqewa tayi jiki a sanyaye idanuwanta jajir ta dawo gefen nasa ta zauna ya juyo ya fuskanceta da Kyau yana sake daidaita nutsuwarsa akanta ya bude Baki yace

"Aysha kikace Garba ne??

Gyada kai tayi hawaye masu dumi na gangaro mata.

"Garban Zaadens???

Sake gyada Masa Kai tayi tana kallansa da idanuwanta masu ja da hawaye.

Handkerchief dinsa ya ciro me tsananin kamshinsa ya miqa mata cikin kulawa kafin ya sauke numfashi me zafi yana kokarin controlling tsananin fushinsa da bacin ran dake tafaso Masa sbd kada ya firgita Nicky din da babyn cikinta ya Dan dauke idanuwansa daga Kanta yana sake danne kansa kafin ya sake Kallanta yana bude Baki yace

"Raping naki yayi k.....

Cikin tsananin quncin dake tafasa a kirjinta Jannah dake kallan yanda yakewa Nicky din ta katsesa da cewa

"AZIZZ"

Bai juyoba yayi Shiru yana qara hadiye nasa bacin ran shima

Nicky data bude Baki zatai magana Jannah ta miqe tana kallanta tace

"Karki batawa Garba suna pls Nicky ki fada gaskiyan waye me cikin nan sbd garba bazai taba aikata wannan abin da kike kokarin maqala Masa ba"

Dawo da kallanta kan AZIZ din tayi Wanda yake kallanta da mamaki tace

"Tayaya zaka kira Kalman raping ga Garba??

Nicky cikin wani irin kuka Mai tsima xuciya tace

"Wallahi tallahi na Garba ne,
Cikinsa ne na rantse da Allah Shima aka tambayesa zai fada"

AZIZ da maganar take sake caza kwakwalwansa kallan Mama yayi yace

"Mama a shiga da ita dakinta ta huta gobe zanga garban dama duk Wanda ya tsaya Masa"

Yana fadar Hakan ko juyowa baiyiba ya kama hannun Jannah wadda ta fizge da karfi tana kallansa masifa na cinta zuciyarsa na mata radadi.

Wucewa tayi tabar gurin kirjinta na sake daukan zafi Kai tsaye Palonsa ta nufa tana isa ta tsaya kirjinta kaman zai tsaga da tsananin bacin ran kalamansa da abinda yayi din tana Jin shigowansa ya juyo a fusace zata fara magana ya rungumeta jikinsa gabaki dayanta yana neman nutsuwa da kwantar da nasa bacin ran dayake tafasa a kirjinsa Dan ita kadai ce zata basa wannan sassaucin.

Turesa ta fara yi da karfi tana dukan kirjinsa tana hawaye cikin fushi tana cewa

"I hate you for real AZIZ LIMBA,I hate you......

Sake qanqameta yayi jikinsa kalamanta na ratsashi suna tsananta radadin dayake zuciyarsa ya rufe idanuwansa yana sake rungumeta tsamtsam a kirjinsa yana nemo kansa dayake neman gushewa.

Kuka ta fasa Masa tana ci gaba da turesa tana jin gidansu kawai take son komawa gurin familynta taci gaba da turesa tana kuka tana cewa

"I hate you AZIZ LIMBA"

Cika kunnuwansa maganganun nata sukai suna yanka xuciyansa Dan haka ya saketa a hankali take ta nufi kofa da gudu zata fice tabar gida gabaki daya sai Kuma ya kasa barin Hakan Dan haka ya sake riqeta yana rungumeta ta baya a jikin kofar daya kasa barinta budewa ya saka kansa wuyanta yana rufe idanuwansa yana sake Jin kukanta na ratsasa.

Karewa karfinta ya fara yi sbd yanda take turesa da kukan duk sun fara cinye karfinta da kuzarinta ta fara sanyi tana cewa

"Ya barta tafiyarta zatayi ita ta dena sonsa gaba daya"

Juyo da ita yayi yana zubawa fuskanta data lalace da hawaye sosai har lokacin kuka takeyi na wani irin kishin dayake neman kasheta da Kuma kalamansa akan garba.

Lura da Hakan tareda karantar Hakan sosai ne ya sakasa sauke numfashi me dumi yana gano fushinta cikin wani irin sanyi ya ambaci sunanta zaiyi magana ta sake kokarin turesa Wanda Hakan ya sakasa dafeta jikin kofar yana Kai fuskansa Kai tsaye ya hade bakinsa da nata yana hanata fadan maganganun datake fada Masa masu soya zuciyarsa.

Turesa take kokarin yi daga bakinta amma yanda ya mata kyakkyawan riqo da jikinsa a jikin kofar ya saka ta kasa kwacewa sai hawaye masu dumi dake gangaro mata tana sake Jin zuciyarta Bata dena zafi ba.

Kissing dinta yakeyi sbd samar musu sassaucin zuciyoyinsu dake wani halin ya dauketa cak yana barin kofar da ita ya isa bedroom dinsa da ita yana wucewa bathroom Kai tsaye yana shiga bai tsaya koinaba sai a cikin bathtub dayake cike da ruwan sanyi masu qamshin Sweetest desire bathperf.

Wata ajiyan xuciya me karfi ta sake sbd yanda sanyin ruwan ya ratsata har cikin Kanta ta bude idanuwanta da suka fara kumbura ta kallesa tana son sake dukansa amma sanyin na ratsata yana kashe jikinta Dan haka zuba Masa idanuwa tayi hawaye na gudu akan fuskar.

Kamo fuskan yayi Shima sanyin na shigarsa ahankali yana ratsasa yana Jin yana samun nutsuwa ya janyota jikinsa ya dorata a sama yana daga qasa suna cikin ruwan ya bude Baki cikin sanyi da rashin iya hayaniya yace

"Bazan taba iya hating naki ba ko a Baki Jannah Zad.......

Wani sabon kuka ta fasa mara sauti sosai Jin abinda ya fada ta tana kokarin barin jikinsa ya sake dawo da ita yana sake hade bakinsu ahankali yana fara kissing nata cikin wata Sonta data gama Masa illa.

A jikinsa ya shigar da ita yana sake samun daman kissing nata cikin ruwan sanyi Wanda ya saka ta fara rage Jin sanyin ruwan tana sake gangaro hawayenta a fuskansu dake hade Dana juna.

Sbd cikinta da bayason sanyi ya kama ya sakasa fitowa dasu ruwan yana zare mata kayan jikinta ya dumamata da ruwa zafi tukuna suka fito da kansa ya saka mata kayan bacci masu kauri suka kwanta babu me magana har lokacin.

Bacci gagarar kowannensu yayi Dan haka ya dago fuskanta ya zuba mata idanuwa yana Dora hannunsa daya akan cikinta.

Irin kallan dayake mata ne ya sakata sauke fuskanta qasa tana dauke idanuwanta daga kansa tareda bude Baki cikin tsananin sanyi da muryanta data Dan toshe sbd rigimar datai Masa a sanyaye tace

"AZIZZ" alaman ya dena mata kallan.

Tana rufe bakinta ya daga yanda take ambatar sunansa koyaushe da wani irin sauti dayake tada gashin jikinsa ya Dora bakinsa akan nata yana zira harshensa ya tsotso cikin bakinta da yai missing taste nasa yana lumshe idanuwansa ya Dorota saman jikinsa gabaki daya yana kwance ya sake hade bakinsu suna kissing juna ahankali yana Jin cikakkiyar nutsuwarsa na dawowa jikinsa.

Zaune ya tashi da ita a jikin nasa yana zare rigar jikinta ahankali yana bin fatar wuyanta da kirjinta da wasu kisses masu sanyi hannuwansa na yawo a kan cikinta zuwa cinyiyinta da suke zagaye dashi ya saka harshensa ya lashi kirjinta da Saida tsigar jikinta ta miqe gabaki daya tayi baya ya tarota yana sake hade bakinsu a zafafe da tsananin shauqin junansu suna fidda numfashi me sanyi da kewan juna.

Sbd cikinta ya saka ya ringa binta ahankali yana rikitata har Saida suka gama lalacewa a gadon tas sun watsar da komai nasu kafin yaiwa kafafunta wata kyakkyawar warewa akansa yana sake hade bakinsu yana kissing nata sosai cikin wata irin salon da Bata saniba kawai tajisa yana bi da ita Kuma har lokacin bakinsa na hade Dan haka idanuwanta suka rife wani numfashi me karfi suke sakewa yana Jin motsi tako ina a kansa.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 75

Baccin nutsuwa sukai sbd tsawon lokacinda suka dauka ba tareba ba qaramin kewan juna sukai ba dan haka washe gari late suka tashi bayan sunyi Asuba kenan sun koma.

Sai karfe 10 na safe ya tashi daga baccin datakeyi me nutsuwa a cikin jikinsa Wanda shi ya jima da tashi amma bai sauka ba sbd a cikin jikinsa take da haka wayarsa kawai yake Dan dubawa yana Dan kallan fuskanta akai Akai har Saida ta farka Dan Kanta.

Tana bude idanuwanta akan fuskansa ta saukesu tana zuba Masa su tana kallansa tanajin hannunsa daya yana shafa cikinta ahankali.

Hannunta daya ta Dora akan nasa dayake kan cikin ta lumshe ido ta bude Baki a sanyaye tace

"Good morning"

Idanuwanta ya kalla cikin kasala kafin ya Kalli bakinta dayayi maganar ya kai bakinsa yayi kissing hancinta tukuna yace

"Barka da tashi Mrs LIMBA,ohh na manta kaman jiya kince kin dena auren kin sakeni ko??

Turesa tayi tana Bata fuska tareda tashi daga jikinsa tana Harararsa ta sauka gadon tana nufar bathroom.

Saukowa yayi ya bita yana murmushi daga shi sai short din bvlgari daya manne Masa a jiki.

Ko daya shiga tana kokarin fara brush Dan haka qarasowa yayi ta bayanta yana saka kafarsa cikin towel dinta ta qasa yana ziro kansa wuyanta ya dauki bush yana farawa sunayi tare yana sake shafa cinyoyinta ahankali da kafansa.

Sun Bata lokaci kafin suka gama shiriritan sukai wanka suka fito.

Itace ta fara fitowa ta shirya cikin doguwan riga sbd sune kayanta yanzu.

Shima shiryawa yayi cikin milk kaftan da hula tareda gold Rolex watche qamshinsa na tashi kaman koyaushe yana gauraye hanyar dayake bi.

Fitowa sukai Kai tsaye Jannah na zare hannunta daga nasa ta nufi hanyar dakin mama.

A hanya suka hade da Falaq Dan haka tare suka qarasa Falaq na maqale gefenta tana Jin farin cikin dawowan Jannah cikinsu da baby limba dinsu.

Suna isa dakin Mama na zaune tana waya da Ummah tana sanar da ita masifar da suka kwana suka wayi gari a cikinta.

Ummah Mummunan tashin hankali ta shiga tana kasa ta inda ma zata fara fadar wannan masifar a zaadens da haka zatai Shiru sai AZIZ din yazo kaman yanda suka San sai ya iso din sbd fuskantar yanayin.

Kashe wayar mama tayi tana kallansu fuskanta a Dan sake da suma cikin nutsawa da girnamwa Jannah ta qaraso tana gaidata.

Amsawa Maman tayi tana sake Dan rarrashinta akan kada tayi fushi da AZIZ akan abinda yanzu dukkaninsu sukeji daga Nicky din Kuma idan har tace garba ne shi dinne idanma ba shi bane ai bazaa yanke hukunci ba sai anji daga garesa Shima garban koda nasa ne ma yace ba nasa bane ai babu abinda zasu Masa sbd Nicky da babynta sai sun riga sun zama amanarsu duka Dan haka zasu kula da ita su taru su Rena abinda zata haifa.

Shiru Jannah tayi kafin ta sauke ajiyan xuciya tana cewa Allah ya kawo mafita a lamarin to.

Shigowan AZIZ dinne ya saka Mama kallansa tana sake fuskanta sosai da kulawa
Falaq ma tashi tayi tana isa gurinsa ta Dan kama hannunta daya tana tsayuwa gefensa tace

"Ina kwana besty"

Amsawa yay yana qarasowa ya zauna yana gaida Mama wadda itama take amsawa tana cewa Falaq Sam ta kasa sanin ta girma a gurinsa.

Jannah miqewa tayi ta fice daga dakin tana neman fiddausi wadda sai a lokacin itama ta fito sanye da riga da wandon Rissap palazzo da qaramar hula a Kanta tana kamshi me sanyi.

Kitchen suka nufa sbd yunwar gaske Jannah din takeji.

A kitchen din ta hada tea da biscuit Tasha suka fito lokacin kowa ya fito breakfast suka zauna aka fara cin abincin hadda Nicky dake zaune gefen Mama tana rarrashinta akan taci abincin sbd damuwan data sakawa Kanta.

Suna gama breakfast Jannah ta matsu yace ta tashi su tafi amma Shiru babu zancen komai haka ya fice gidan ya barta ta ringa Kiransa a waya bata samu har se yamma ya  dawo yashige.

Tana sane da dawowansa taqi baro dakin fiddausi har magrib tukuna ta koma gurinsa.

Ana gama magrib dukkaninsu suka fito a Shirye zuwa zaadens Banda Falaq da fiddausi daga shi sai Mama sai Nicky da Jannah din wadda ita take ganin komawa gidane zatai.

Sayd na parking harabar ZADs jikin Nicky ya sake sanyi idanuwanta dake kumbure sosai tin jiya sbd kuka ta dago ta Kalli inda suka Taho din tana sake Jin hawaye masu tsananin zafi na gangaro mata.

Jannah ma hankalin nata duk a tashe yake da yanda Dad zai karbeta ko Maheer Dan haka jikinta yayi mugun sanyi ga tashin hankalin abinda ya kawo LIMBAS din zaadens musamman ganin AZIZ daya sauya take ya dauke dukkanin rahamar fuskansa ya kame sosai sbd fuskantar lamarin da Kyau batareda tsayawa duba matsayin kowa ba zai bawa lamarin gaskiyansa.

Ganin yanayin AZIZ din ya saka kowa sake shiga taitayinsa suka nutsu ga Nicky ma sai kukan takeyi sosai sbd kunya da baqin cikin abinda zasu fada a gaban kowa da Kuma fargaban kada garban yayi denying din cikin a gaban kowa sbd Bata buqatan komai bayan koma yayane uban danta ya Yadda da nasa ne Dan tanason babynta ya tashi da sanin yanada uba bawai a rasa ma wa zaa Kira da sunan mahaifinsa ba,
Garba ya yadda da shine Daddyn babynta ya isheta komai zuciyarta ta gama samun nutsuwa ta karshe akan babynta da zata Haifa abinta.

Saleem ne ya fito da kansa harabar gidan ya tarbesu cikeda kulawa da sakewa kaman family sai Kuma Ammar dayake motarsa yana waya sbd dawowansa kenan bai shiga ciki ba.

Fitowa motar yayi yana kallansu d mamakin ganin familyn su duka ya miqawa AZIZ din hannu yana Masa sallama da barka da zuwa Shima AZIZ din miqa masa yayi suna gaisawa yana tambayansa Ummah sbd sanin shine danta a yanzu.

Kokarin nufar ciki sukeyi gabaki dayansu Ammar din ya Kalli Nicky wadda take cikin doguwar hijab Kanta a qasa baice komaiba mama ya gaida kafin Jannah ta gaidasa suna gaisawa aka barsu a baya suka biyo bayansu yana magana da Jannah din wadda ke tambayansa su Dad duka suna ciki.

Dariya yayi me nutsuwa yana cewa

"Zaune Kuwa a palo dukansu harda su modibbo gashi tin jiya kawu isiya akai Akai saiyace wai ina Jannah ne?"

Kallansa tayi zuciyarta na sake tsinkewa jikinta na sake mutuwa da kunyar da batasan ina zata saka Kanta ba sbd damuwa.

Saleem na shigo kamshin AZIZ LIMBA ya sako Kai palon take Dad ya dago yana kallan kofar hakama Maheer da Ummah dake kokarin zama tin safe a sanyaye take da Mummunan labarin da mama ta sanar Mata.

Modibbo dasu kawu duka suna palon ana Zaune gabaki daya fira sukeyi table din tsakiyan palon cikeda chops kala kala dasu snacks masu dadi da Ummah da fatma sukai sai fruits da sukai sanyi sosai da aka yanka a babban tray aka ajiye da fork da bowls.

Sanyin AC da qamshin shegun designer turarukan kowa ne suka bada wani combo suke tashi Dan haka hankali kwance da annashuwa kowa ke fira su kawu sai cika Baki akeyi dasu apples da chops ana bada zance.

Shigowan LIMBAs ya saka kowa kallansu ana musu barka da zuwa da mamakin ganinsu su dukan a Daren.

Su modibbo AZIZ ya gaida bayan ya gaida Dad da Ummah tukuna ya bawa Maheer hannu suka gaisa Maheer din na baasa gurin zama.

Jannah a bayan Ammar ta Dan boye tana kasa fitowa gabaki daya ta gaidasu muryanta na rawa
Dad da kwanan zaune yayi sbd sanin Bata gidan kallanta yayi yana son yin magana amma Jin idanuwa Ummah Kafe akansa ya sakasa hadiye maganarsa yana kasa juyowa ya Kalli Umman.

Gurin fatma Jannah ta koma suka silale daga palon zuwa sama suka bar palon sunason magana kala kala a tsakaninsu.

Masu aiki ne suka sake kawo Karin chops da fruits suna yiwa AZIZ LIMBA barka da zuwa suka fice.

Rashin sabo da jituwan dake tsakanin ahalin biyu ya saka kusan zaman kowa wani iri yake jinsa Saida Saleem ya gabatarwa AZIZ su modibbo a matsayin iyayen Muhammad da Fatma.

Sake gaisawa sukai suma suna sake masa barka da zuwa,

A natse AZIZ din ya Kalli Dad Wanda yake satar kallan Ummah data hanasa tashi ya tafi da idanuwanta sbd yanda sukai dashi ta sanar Masa daga ranar da Jannah ta baro AZIZ to ita zata koma ta kula da 'danta itama.

Tinda ta fada Hakan ya kasa cewa komai akan dauke Jannah da AZIZ din yayi da anyi maganar Jannah sedai ya sauke ajiyan xuciya ya kasa maganar komai Dan haka ko yanzu din tinda suka shigo yake sauke ajiyan xuciya ta hadiye magana akai akai.

Cikin nutsuwa Kai tsaye AZIZ din ya bude Baki yana kallan Dad yace

"Magana ce me mahimmanci ta kawo mu wadda naji dadin daya kasance ma iyayen Muhammad din suna gari"

Kawu isiya na Jin Hakan ya hadiye apple din bakinsa dayake cike yana kallan AZIZ LIMBA din farin ciki na mamaye zuciyarsa sbd Jin maganar Garba ce me mahimmanci zaayi.

Su modibbo ma da suka kasa sabawa da sunan dakatawa sukai dukansu suna Maida hankali akan AZIZ din.

Shima Dad Shiru yayi yana sauraron AZIZ din sbd ganin yanda yayi maganar a kame da bawa maganar mahimmanci sosai.

Tsit palon yayi daidai nan Muhammad din ya fito daga hanyar dakinsa ya gamo Wani class da Ammar ya sakasa a online na koyan karatu Wanda yau suka jima basu gama ba.

Sanye yake da Gucci wears black da sukai Masa Kyau da black agogo a hannunsa.

Kallansa AZIZ yayi da idanuwansa da suke a tsananin kame Wanda Hakan ya saka kowa zubawa Muhammad din ido hadda Nicky din data dago jajayen idanuwanta tana kallansa sbd Sam ita ko kamanninsa bazata fada sosai ba tinda bama abinda yake hadasu kowa hanyarsa daban sbd matsayinsu daba daya ba.

Ganin ana kallansa ya sakasa qarasowa ahankali yana sauke idanuwansa akan Nicky wadda sai a lokacin ya lura da ita Kuma rabonsa dashi da ita su hadu face to face haka tin bayan faruwan mummunan kaddarar tsakaninsu Dan haka ya zuba mata idanuwansa yana kallanta cikeda damuwa da Jin wani irin ciwon laifin da suka taru suka aikatawa ubangiji.
#MAMUH
07019691719

Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍

‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

Gyaran gashi da kitson zamani

Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido

Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai

Kayan gyaran fata na gaske

Lalle mai kyau da salo na zamani

Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi

Shirin amare da na musamman

Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391

Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge

KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 76

Takardu sayd ya qaraso ya ajiyewa Dad gabansa cikin girmamawa yana komawa inda yake zaune kusa da Saleem kowa na sake nutsuwa da shiga tinani da shakka,

Su modibbo Kuwa ganin takardu aka ajiye Kuma ance Muhammad take zuciyoyinsu suka sake cikewa da tsananin farin ciki da zaquwa suna kallan juna qasa qasa da maganar Ido a tsakaninsu bakinsu na kasa dena motsin Dan danne farin cikinsu.

Daukan takardun Dad yayi yana kokarin budewa AZIZ Kai tsaye ya katse Shirun da cewa

"Aysha Nicky na dauke da cikin wata biyar Wanda Kuma tace Muhammd ne Ubansa Wanda shine ya.......

Wani mugun yunqurin tasowan apple din da ba gama isa qasan cikinsa bane ya tasowa Kawu isiya yana dafe kirjinsa da karfi yana Maida abinda yake ji shine ya katse zancen AZIZ din Wanda ya Maida kallansa Kai tsaye kan Garba yana qarasawa da yanke zancen da cewa

"Ciki ne a jikinta Wanda nakeson jin shin kasan da Hakan?

Tsit palon ya dauka babu Wanda ya motsa kaman babu me rai a cikinsa Saida Mama ta ringa kallansu daya bayan daya tana ganin yanda kowannensu ya dauke wuta.

Kuka me cin Rai Nicky tafasa ahankali Jin kowa yayi Shiru damuwanta na sake tsananta da quncinta,

Mama ce ta dafata tana rarrashinta AZIZ Kuwa baya buqatan sake maimaitawa su gama shock dinsu su fito sai kowa ya maimaitawa kansa zancen.

Garba da yayi mummunan mutuwan tsaye yana kasa dauke idanuwansa daka kan Nicky wadda kukanta ke sake ratsa kowa palon Jin yayi jiri ya debesa ahankali ya zaunar qasa da karfi jajir idanuwansa sukai kirjinsa na cikewa da tsananin sabuwar baqin ciki da ciwon wannan mummunan kaddarar daya dauka sirrin rayuwansu ne da har abada basa fatan maimaitawa ko kansu ne bare wani yaji bai dena tubarwa Allah ba haryanzu sai Kuma kwatsam Allah ya ninka musu wannan jarabawan kaddara,
Cikinsa aka dauka Bata hanyar aureba ta hanya mafi muni da baqin ciki,
Me zasu fadawa yaron ko yarinyar idan ta girma?
Da wane idon zai iya kallan abinda zaa Haifa?
Wasu hawayen tsananin baqin ciki da sabuwar danasani ne suka gangaro idanuwansa dake rintsewa ahankali yana yin qasa da kansa cikeda kunya da baqin ciki mara misali.

Dad na ganin yanayin Muhammad din shock dinsa ya sakesa ya bude takardun hannunsa da sauri yana karantawa illai Kuwa takardun asibitin ayshan ne Dan watannin cikin tareda cikakkiyar lafiyansa.

Rawa hannunsa ya fara ya dago da sauri ya sake Kallan garban Wanda zuwa lokacin hawayen baqin cikinsa sun tsananta kansa na qasa yana kasa dagowa.

Maheer ne ya dauka takardun ya duba Shima yana bawa Ammar muryansa na rawa yace

"Duba mana likita da sauri"

Ammar da Shima mugun mamaki da tashin hankalin yake ciki karba yayi yana budewa yafara karantawa yana koro musu bayanin komai a bayyane.

Take kowa ya Maida kallansa kan Garba Wanda jikinsa ke rawa sosai yana Jin tsanar kansa gabaki daya.

Numfashi modibbo ya sauke lokacinda Dad da kowa suka dawo da kallansu kan su modibbon dake Kallan kowa da kalar tausayi sbd Sam basuma kawowa kansu Garba dai nasu ake magana akansa ba Dan haka kallan da aka juyo hankali tashe ana musu ne ya saka modibbon sauke numfashi yana kallan Dad da idanuwansa sukai jajir da tausayawa yace

"Allah sarki waye wannan ake magana ne akansa?
Akwai aure ne tsakaninsu Hakan ta faru?

AZIZ da baida lokacin batawa akan lamarin Kai tsaye ya kalli modibbon da mamaki kafin ya Kalli su Dad da suka kasa cewa komai kirjin kowannensu cikeda radadi da nauyi ya Maida kallansa kan modibbon ya bude Baki yace

"Garba dai gashinan a gefe shi ake magana yayiwa kanwata ciki batareda aure ba sedai bansaniba ko auren sukai ba sanin kowa gashinan nima amsa nake nema daga bakinsa"

Modibbo kallan Garba yayi ya dawo da kallansa kan AZIZ yace

"Wannan Garba din kake magana dai?

AZIZ din bai iya bada amsaba sbd zuciyarsa dayake iya kokarinsa gurin dannewa sbd girmamasu sedai mama ce takarbi zancen da cewa

"Gashinan ai tambayansa zakuyi duka yai mana bayani mu fita a duhu sbd ita dai yarinyar ta fada Wanda yayi cikin shikuma yanzu nasa bayanin muke jira asan abin yi tinda dai wanna mummunan kaddarar ta riga ta faru haihuwa ake magana yanzu datake matsowa........

"A ina haihuwan zata matso?" Modibbo ya katse Maman Shima ransa na fara baci da wannan mugun alkabain da ake kokarin binsu dashi wai haihuwan shege a gidansu.

Kawu jibo da duk zufa ta gama jiqasa kansa na neman kuncewa gyara zama yayi yana kallan Nicky yace

"Itace wannan me cikin?

"Itace" ummah ta bada amsa jiki a mace cikeda tausayin Nicky da garban Wanda har lokacin ya kasa motsawa hawaye yakeyi sosai.

"Qare mata Kallo kawu jibo ya hau yi haka Shima kawo isiya tinda akai maganar ya Kafe Nicky da idanuwansa ba ko kyaftawa Saida kawu jibo yace

"Jamaa wannan fa baturiya ce nake gani a gabana,
Itace tayiwa Garba cikin kokuwa shine yayi mata sbd nasan dai wlh wannan Garba bazai tinkareta ba sbd tafi karfinsa ko a ido matsayinsu bama dayaba,

Kawu isiya daya rasa abin fada kawai kuka sukaji ya fasa yana kasa cewa komai sai girgiza Kai yakeyi yana nuna Nicky yana nuna Garba saiya sake fasa kuka yana girgiza Kai hannuwansa na rawa.

Kalaman kawu jibo suka Sanya Nicky fasa sabon kuka ahankali tana Jin tsanar Kanta da Jin inama ta tafiyarta tin kafin kowa yasan da cikin taje wani gurin ta haife abinta ta renesa.

AZIZ ma kalaman sun sosa ransa ya dago idanuwansa jajir zaiyi magana Mai zafin gaske Mama ta hanasa ta hanyar dafa hannunsa tana kallan Dad Wanda su shine Wanda zasu iya fuskanta kansa a qasa idanuwansa jajir Shima tace

"Dzad kaine Wanda muka xo gurinsa Kuma muke fatar samun kyakkyawan fahimtar fuskantar wannan matsalar wadda badan darajar ku dinba da babu abinda zai hanamu daukan mataki sbd mune da mace mune aka Fi cutatarwa Dan haka muna neman Jin magana me karfi daga gareka kafin komai"

Dad da kirjinsa ma yaji yana ciwo sbd baqin cikin dayake neman kashesa na Yara daga wannan se wannan,

Ya gama fitowa shock din cikin Jannah yanzu Kuma a kawo Masa wani cikin shikenan jikokin zaadens dinma sirki zaa samu.

Cikin fushi da tsananin bacin Rai da baqin ciki Dad din ya Kalli garba yace

"Muhammad zakai magana ne kokuwa baqin cikin kake jira yayi ajalin daya a cikin ni dasu modibbo?
Meye muke ji yanzu da kunnuwanmu?
Meye tsakaninka da Ayshan?
Akwai muamalan data saka ake ambatarka da uban cikinta kokuwa ba haka bane kayi gaggawan bude Baki kayi magana"

Shiru kowa ya sake yi cikin zaquwa ana jiran amsarsa wadda yana bude Baki kawu isiya ya dakata da kukansa yana jiran amsar da zata fito daga bakin garban Wanda muryansa cikeda baqin ciki mai tsanani da kunyar Allah yace

"Muamala ta shiga tsakanina da ita bisaga kaddara Dan haka Bazan iya musa cewan ba Nine uban cikin ba,
Amma wlh tallahi kaddara ce da haryanxu ina neman tuba da gafara a gurin ubangiji.......

Wani salati me karfin gaske modibbo ya sake yana kallan Garba jikinsa na rawa hakama muryansa yace

"Garba soyayya kukeyi ne ko dole tayi Maka?kokuwa kudi ta baka??

Wasu hawaye masu tsananin ciwo ne suka sake gangarowa Nicky sbd tasan zai fada itace tai Masa dole Wanda Hakan zai qarasa zubar da martabarta ta har abada a idon kowa harma da abinda zata haifa sbd zaa goranta Masa wata ran uwarsa tayiwa ubansa Dole koma ace ta nemesa ko Masa fyade ma.

Shi kansa Garba maganar ta ratsesa sbd fadar koma Yaya almarin yake baida amfani tinda kaddarar dai ta afku Kuma kowa yanzu yasani Dan haka dago idanuwansa da sukai jajir yayi ya sauke numfashi me zafi ya bude Baki yace

"Babu Wanda yayiwa wani dole a cikinmu akan raayin mu ne da Kuma zuwan kaddara"

Hakan daya fada ya saka gabaki daya kowa ya sake shiga bacin Rai da fushi take modibbo ya fara zufa yana neman iska,

Kawu isiya Kuwa kuka ya sake fasawa yana dafe kirjinsa yana cewa

"Innalillahi ina zan Kai garba da abinda Garba zai haifa?
Garba jika bature ba aure Wayyoni Allah na me nakeji nake gani"

Kawu isiya ma rikicewa yayi Nan take yace

"Inace maganar cikin Jannah aka fara ita Allah ya yayyafawa kaddararta rufin asiri da aurensu itada mijin
Yanzu Kuma Garba da haihuwa ba aure,ita binnin haka akeyi kowa haihuwa kota Yaya?
Ina Fatma wlh tazo gida zamu koma bazan barta ba auren shehun da batason wlh shi zaa mata asiri rufe Shima garban wlh auren zamu Masa tin kafin kowama yaji maganar daya debo mana"

Modibbo da jikinsa ke tsananin rawa cewa yayi

"Da gaske dai garba cikin haihuwan Dan mutum ne a jikin yarinyar Nan Kuma Kaine uban?
Garba zuwa kayi ka fara Raba mana zuria ba aure?
Garba wlh tallahi aure duka zamu muku kaida fatma Dan zamanku anan ya qare tinda kuka fara haife haife"

Fatma da suke can gefe da Jannah kuka ta fasa jikinta na rawa Muhammad dinma kuka yakeyi sosai shi da Nicky wadda yanda ya rufa asirin ta ya Kuma yadda da cikinsa take tausayinsa Dana Kanta ya sake sakata kuka Mai sanyi tana jiran duka hukuncin da AZIZ zai yanke ko zabar mata.

AZIZ kuwa rasa ma abin fada yayi sai dayaga su modibbo sun miqe hankalinsu duka a tashe da tsananin no ciki da dacin Rai suna cewa ayau din zasu koma da garban da fatma take Shima ya miqe yana cewa ai babu maganar tafiya da Garba sbd shine yayi barnar Kuma shine zai runguma Nicky da babynta Dan haka maganar aurensa da kowama Bata taso ba sedai Nicky wadda tanajin Hakan ta sake fasa Kuka tana rufe Kanta cikin kafafunta.

Dad ma cikin damuwa da tashin hankali yace maganar AZIZ din itace daidai babu maganar komai data wuce a hada Nicky da garban aure tinda since da yardarsu suka muamalaci juna,

Maheer Kuwa da Ammar fatma dake kuka suka miqe suna tare su kawun dake daka mata tsawar tayi gaggawar hado kayanta ta fito su tafi ayau yau dinnan.

Rikicewa gurin yayi Jannah ma gurin Dad taxo tana rokonsa Dan Allah su modibbo suyi hakuri kada a tafi da fatma.

Cikin tsananin fushi modibbo ya Kalli zaadens din daya bayan daya kafin ya tsaida idanuwansa akan Dad dake sake magiyar suyi hakuri Dan Allah kada a lalata rayuwan Fatman a bari tayi karatun da ake kokarin farawanta.

Cikin fushi da wani irin baqin ciki da bacin Rai modibbo yace

"Wallahi fatma aure zamu daura mata ida kuma kana ganin zaka iya cetan rayuwan tata Da kake ganin zamu lalata to ai kanada Yaya Maza daura mata aure da daya a cikinsu musan a matsayin da zamu barta anan din"

Juyowa Dad yayi ya Kalli Maheer kafin ya Kalli Ammar da Saleem yanajin baida baqin ciki ko kadan Dan wani a cikinsu ya auri Fatma Dan haka ya tsayar da idanuwansa akan saleem Wanda Hakan ya saka Saleem saurin miqewa tsaye yana girgiza Kai tsaye ya bude Baki yana kallan AZIZ LIMBA yace

"Banda ni sbd inada mata ta already"

Gabaki dayansu suka juyo suna kallansa Banda AZIZ daya matsu a gama wannan tashin hankalin ya fadi nasa tsayayyen raayin akan Muhammad da zai auri Nicky.

Maheer Dad ya kalla sbd yasan Ammar bai gama Shirin sake bawa wata macen dama ba a rayuwansa yace

"Zan daurewa Maheer fatma inshallah"

"A gobe muke son Hakan Dan tabbatarwa kafin mu wuce mu shaida"
#MAMUH
07019691719

*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 77
Alhamdulillah

It’s Official! MG’s Beauty Lounge Opens Monday, 2nd June 2025 – Just in Time for Sallah!

Ladies of Kaduna, are you ready to shine this Sallah?
Your new beauty destination MG’s Beauty Lounge is opening with elegance, class, and all the pampering you deserve!

Here’s what awaits you at MG’s Beauty Lounge:

Beautiful Hair Styling & Braiding

Glamorous Makeup for Sallah

Relaxing Pedicure & Foot Spa

Natural Skincare Products & Full Kits

Fresh Henna Designs

Fragrance Oils, Humra, Incense & More

Bridal & Special Occasion Packages

We don’t just offer services — we offer an experience of royalty.
Come wash your feet, get styled, henna your hands, and glow with elegance—all under one beautiful roof.

Address: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, Behind Indomie House, near Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Bookings & Enquiries:
WhatsApp: 08062991549
Call: 09016108092 / 08064532391

Come See the Difference. Come Feel the Magic. Come Be a Queen.
Follow us on IG & TikTok: @MGsBeautyLounge

Maheer da sauri ya kalli Dad da modibbo a lokaci daya yana rasa wa zai tsayar da idanuwansa akansa cikin su biyun itama fatma silalewa tayi a jikin bango tana kaiwa qasa kukanta na tsananta sbd ba auren takeso ba kwata kwata hakama Maheer din ba saar aurenta bane bayan tsananin taxarar shekaru yafita komai bama zai taba karbanta a matsayin matarsa ba sedai matar cinne.

Numfashi me zafi Saleem ya sauke a sanyaye yana kallan Maheer Wanda ya zame ya zauna kan kujera idanuwansa na sauyawa zuwa Ja sbd auren macen daya girma sosai nesa sosai baya cikin tsarinsa yafison macen data qosa shekarunta suka tafi kusan daidai na nasa hakama kallan Jannah yakewa Fatma.

Saleem tausayin Maheer din yaji amma Kuma dukkaninsu a gurinsu babu baqin ciki ko asara ko abin damuwa Dan wani a cikinsu ya auri Fatma sbd takai macen da kowane namiji zaiso bayan rashin ilimin boko Wanda a yanda ta wanke din yanxu sai anfada ma ake sani sosai,

Shi a nasa bangaren babu maganar auren kowace mace a duniyarsa sai wadda zuciyarsa keyi tsananin so me karfi,zurfi da tsafta danma Allah yasa Bata gurin da kallansa da kawai akai a lissafin zabawa fatma Miji daya Sha rigimar da zata hanasa sukunin Watan gabaki dayansa.

Ammar Kuwa zubawa su modibbo idanuwansa yayi yana Jin mamakin tayaya bayan ance zaayi auren suce sai anyi yanzu bayan auren taruwa a rufawa juna asiri ne ba abin gaggawa ba Dan haka Matsowa yayi gaban su modibbon zaiyi magana Dad ya riqe hannunsa yana juyowa ya kallesa da idanuwansa da suke ja na duka wannan tashin hankalin da masifun dasuke neman warwarewa ya Maida kallansa kan kawu ya fara kallansa kafin ya Maida kallansa kan modibbon ya bude Baki yace

"Ba damuwa zaku sheda Hakan, gobe jumaa ce a daura auren bayan sallar jumaa a yanke masa sadakin Fatman"

Shiru sukai dukkaninsu kawu jibo na Jin zuciyarsa na tsallen farin cikin samawa Fatma tata mafitar har abada din me Kyau yana Kuma Jin shakkar yanda Maheer zai karbeta ko ya qi daukanta matsayin mata,
A dayan bangaren Kuma idan ya duba halinda Garba yake ciki sai yanajin gwara su tattara yaransu su tafi dasu amma Kuma a yanda yake satar kallan AZIZ LIMBA dake zaune yasan ko su da suka Haifa garban babu inda zai bari su tafi dashi sbd cikin dake jikin kanwarsa Sam ba fuskan da zai dauka abarta da babyn ita kadai.

Modibbo ma kusan tinanin da jibon keyi shi yakeyi amma Kuma yasani a ransa a bayyane zaadens bazasu taba cutatar da yayansu ba Tinda gashinan sun kula musu dasu tamkar nasu Wanda Hakan ne ma yanzu ya saka suke kokarin auren Fatman Dan Hana a tafi da ita a mata auren kauye da Wanda bataso.

Kawu isiya Kuwa ko magana da tinanin komai baya iyayi sai kallan Nicky da Garba yana sake tsiyayo hawayen ina zai saka ransa da jika bature, Garba ya gama da rayuwansa.

Kai tsaye modibbo ya Kuwa yanke sadakin yana kallan Maheer Wanda Dad ya kalla Dan haka ya taso a hankali ya Kalli modibbon ya bude Baki yayi godiya ya Kalli su kawun suma yayi musu godiya yana koma gefe kansa na sarawa.

Ammar gurin Maheer din ya koma Shima kansa na sarawa sbd yana Jin damuwan da Dan uwansa yake ciki.

Kaman daga sama suka tsinci muryan AZIZ data sakasu duka sake dawo da kallansu da hankalinsa gabaki daya akansa ba shakka ko kwana bare lankwasa kowane zance yace

"Zan karbi muhammd a yanda yake sbd inganta rayuwarsa dan tsayuwa da kansa ya kula da 'dansa Idan an Haifa da matarsa wadda tana haihuwa zaa daura musu aure,

Muhammd zaiyi karatu ya Gina kansa da kansa ban yadda kowa tsaya Masa ba sbd dole yasan nauyin daya dorawa kansa daga shi har itama dole zata auri Muhammad din Tinda ta iya Daukan cikinsa zata iya zaman aure dashi Dan haka Muhammad zai dawo karkashin Sayd.......

Da sauri dukkaninsu suka kallesa kawu isiya a rikice yace

"Bayan wannan barnar Kuma da girmanka Garba zaa karbeka riqo??

Modibbo ma cewa yayi

"Kai baka bamu macen ba munyi renan cikin zaaka ce a baka zabgegen namiji yaje ranan cikin??
To wlh akan wannan muna Nan sai an haife cikin"

Dad ma da Dan mamaki da kame fuska yace

"Inganta rayuwar Muhammad ko da babu wannan nauyin daya hau kansa ko da akwai duka akan zaadens ya rataya sbd shi namu ne Kuma sunan zaadens yake amfani dashi a yanzu Dan haka babu buqatan zamowa karkashin wani zamu dauki nauyinta Dana babyn tin daga yanzu har lokacin da zata haihu"

AZIZ da daman Hakan yakeson ji daga bakinsu Kuma yasan yana Sanya zasu banzatar da Nicky ne Dan haka sbd ya sake sakasu a zancen sosai yace

"Bayan ta haihu zan dauki nauyin komai na aurensu tin daga gidan da zasu zauna a duk kasar da sukeson har.......

Maheer ne dayake cikin nasa juyayin ya katse AZIZ din da hanasa qarasawa yace

"Wannan ma duka nauyin mu ne zamu dauka tin daga yanzu har daurin auren da duk abinda Aysha da babyn zasu buqata zamu dauki nauyin inganta rayuwarsu gabaki daya sbd babynta Zaaden ne"

Ajiyan xuciya AZIZ LIMBA ya sauke yana miqewa tsaye fuskansa a sake yana sake tsananin kamewansa ya Kalli Dad da Maheer dasu modibbo dake zare idanuwa jajir suna jiran ta baci Dan suma a Shirye suke da zuwa kauye su kawo dukkanin dukiyar shanunsu Dan tsira da martabar iyalinsu zasu bada komai da dukiya me yawa a basu Nicky su reneta da cikinta akan su bada Garba ya tafi LIMBAs renan ciki sbd kawai AZIZ LIMBA din yafi zaadens arziki da power.

Kallan Nicky da idanuwanta sukai jajir suka kumbura har fuskanta yayi Mama ta tayar da ita ya tsayar da ita gefensa yana kallanta cikeda kulawa yace

"Babynki ya samu identity dinsa tin kafin yazo duniya,
Kina dauke da baby Zad ne Dan haka kuka ya qare tubarwa Allah zakiyi ta yi yanzu kina neman gafarar laifin da kuka aikata har Allah ya saukeki lfy"

Ajiyan xuciya ta sauke tana dagowa ta kallesa sosai da idanuwanta kafin ta bude Baki cikin tsananin sanyi tace

"Thank you LIMBA"

Murmushi me Kyau ya sakar mata yana sake kwantar mata da hankali da idanuwansa batareda yace komaiba.

Har a ranta batasan tayaya zata auri Garba ba amma sbd tanason bawa bin umarnin na gaba da ita dama ko zataga sauyi da amfanin Hakan ga rayuwanta ya sakata kasa cewa komai akan maganar auren sbd ta jira haihuwanta ta gani ko zata iya idan Kuma taga bazata iyaba zata sanar da kowa ta bawa kowa hakuri ta tafiyanta da babynta tinda dai ubansa ya yadda dashi hakama iyayensa da familynsa sun yadda da babyn Dan haka ko a Hakan ita alhmdllh Allah ya mata rahama.

Sai a lokacin bayan komai ya natsa Ummah ta samu daman saka baki tana sake bawa kowa hakuri a lamarin tareda nusar da kowa ba abin damuwa bane tinda Allah ya kawo lamarin cikin bazata da tashin hankali Kuma gashi an nema mafita a cikin sauki da rufin asiri batareda kowa ya sani ba.

Mama Kuwa ganin yanda hankalin su modibbo ya tashi akan fatma da irin abinda suke gudu ya sake biyowa baya a cikin zuria ya saka itama nata hankalin taji ya Dan tashi sosai ya Kuma karkata akan nata ahalin da Bata fata amma kaddarar Bata wuce ta fada wa wani ba a gidan gashi yanzu tana ji tana gani AZIZ ya riga ya gama karban Nicky kwata kwata a matsayin kanwarsa Dan haka dole dai itama itace uwar Nicky din kenan gashi zata fara da tarbon jika na biyu bayan Falaq da babu aure sbd cikin Nicky yana gaban na Jannah.

Kai tsaya taji hankalinta yasake tashi Dan haka ta matsu su isa gida ta yanke nata hukuncin a nata Yayan.

Babu sauran gurin sake zama ko wata firar sbd babu Wanda ransa yake a cikin dadi kowa da nauyin kirji yake numfasawa Dan haka sallama LIMBAs sukaiwa Zaadens din suka fara kokarin tafiya.

Mama ce Kai tsaye ta Kalli Jannah tace

"Jannah mu tafi ai gobe zaki dawo daurin auren tinda auren aminiyarki ne da Kuma yayanki"

Kallan Mama Jannah dake rungume da Fatma tana tayata hawaye tayi tanajin gabanta na faduwa.

Sake magana Maman tayi Wanda ya saka Jannah kallan Dad Wanda ya hade fuska sosai ya saci kallan Ummah Shima wadda tama qi kallansa sbd kada ma wani ya gano ita yake Satan kalla.

Cikin sanyi Jannah ta bude Baki tace

"Mama Dan Allah a barni anan din"

Kallanta Mama tayi AZIZ dake gap da isa kofa a cikin kunnuwansa zancen ya sauka ya Dan lumshe idanuwansa tareda juyowa ya Kalli Mama a natsensa ba damuwan komai yace

"Mama mu tafi"

Mama kallan Ummah tayi tace

"Kinji yarki tace gidansu take so bari mu barta kafin a kwana biyu a gama hidimar bikin"

Murmushin karfin hali ummah ta sake tana cewa

"Aikuwa mun gode da Hakan ana gama hidimar inshallah kawota ma zaayi har gida"

Murmushi Mama tayi tana juyawa tabi baya AZIZ Wanda ya fice tini.

Suna ficewa Jannah taji jikinta yayi sanyi tana Jin kaman ta samesa ta duba idan ba fushi zai sake yi ba.

Ummah juyawa tayi tabar palon tana yiwa kowa Saida safe ta tafi da fatma da rarrashinta akan auren da gobe zai hau Kanta.

Kowama watsewa yayi ya nufi dakinsa Banda Garba Wanda sai da kowa yabarsa a palon kansa na qasa har lokacin idanuwansa sunyi jajir sbd Kukan da yayi Kuma har lokacin ma Jin radadin komai yakeyi yana tubarwa Allah jiki a mace.

Ammar ne ya dawo ya kamasa zuwa dakinsa suka zauna ya fara basa qwarin gwiwa yana sake Masa nasihar kaddara ce da jarabawan Allah ya bayyana laifin da sukai a boye sbd ya zama izina ga wainda suke tareda su da Kuma Allah ya riga ya qaddari akwai Rabon haihuwan a tsakaninsu Dan haka rungumar nauyin daya hau kansa da zuciya daya da Kuma kauna tinda dai jininsa Kuma Ayshan ma ta saduda shine mafita da abinda ya kamacesa.

Maganganun Ammar sun sanyaya zuciyar Muhammad din sun Kuma sake bude idanuwansa akan babu abinda yanda ya iya bayan rungumar Ayshan da babynsa tinda dai har Allah ya sake taimakonsa iyayensa na nan akai Komai baida fargaban yanda zai fuskancesu a gaban da Dan gaban fatiha tindai da su akai Komai Dan haka yaji nauyin kirjinsa da damuwansa suna ragewa yana Jin kaman anzare Masa ciwon dayake kirjinsa na tin ranar da sukai abin shi da Ayshan yanzu tubarwa Allah kawai zasuci gaba da nema.
#MAMUH
07019691719

*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 78

Ummah har daki takai Fatma ta zaunar da ita ta fara rarrashinta tana nuna mata ba abin kuka bane sbd Maheer dai mijin da kowace mace zataso aurensa ne sbd yanada abubuwan so hakama rayuwarta zata inganta zatai karatu ta samu kwanciyan hankali da nutsuwa auren gida batareda taje koina ba a ciki wainda ta saba rayuwa a cikinsu tasan halaye da kyakkyawan maamalan datake tsakanin ahalin Dan haka ta dena kuka ta sakawa ranta Maheer shine mafi alkhairin da aketa jira ana fatan samu.

Jannah datake a sanyaye kasa cewa komai tayi sai sauraron Umman takeyi rabin hankalinta Kuma yana kan AZIZ dinta da batasan Wane halin suke cikiba ita dashi.

Ummah ma Bata nuna damuwan komaiba ta sake hadasu su biyun tai musu nasiha tana gamawa ta miqe ta fice tana komawa dakinta ta shige ta rufe.

Jannah ma sbd rashin dadin zuciya da son sake cirewa fatma fargaban auren da damuwa a dakin ta kwana tareda Fatma wadda Sam babu bacci a idanuwanta sallar ishai sukai suka kwanta Shiru ba me dogon motsi.

***LIMBAs Kuwa suna isa gida AZIZ ya sake maimaita maganar auren Aysha da Muhammad tareda kulawa da babynta batareda tina ta hanyar da aka samesa ba ya Kuma sake kwantar wa da Nicky hankali sbd ta sake da wannan ya gama magana kowa ya shige Nicky na Jin inama tin farko a matsayin Yayan ta dauki AZIZ LIMBA da yanzu Bata zo wannan matsayin na kaddarar datake ciki ba.

Mama Kuwa tana shigewa dakin bayan ta gama komai ta zauna bakin gado wayarta ta dauka ta bugawa baba Al'hassan waya sukai magana sosai ta sanar dashi duka abinda yake faruwa Dan haka take Shima yaji hankalinsa ya Dan tashi da lamarin Dan haka yace Shima yana Nan tafe su toshe hanyar faruwan ire Iren wainnan kaddarorin.

Wayan dashi ya saka zuciyar Maman samun sukuni Dan haka ta samu nutsuwa harma tayi bacci me nutsuwan tana fatar itama azo ayi me yiyuwa a tsakanin Sayd da Fiddausi kowama ya fidda abokin rayuwa suyi auren zaman ya isa hakanan ba aure.

Washe gari na wayewa Zaadens suka tashi da hidimar daurin auren da suke dashi a yau din Dan haka tin asuba Ammar da Saleem suke wayoyin hidimar sai Kuma gayyatar mutanensu na kusa masu mahimmanci wainda zasu samu daman halarta,

Muhammad duk da yana cikin wani halin Shima hakanan ya daure yashiga hidimar sbd auren kanwarsa ne da Dan uwansa Dan haka shine ma ya fita zuwa karbo kayan da Maheer din zaiyi amfani dasu wainda tin cikin dare Ammar ya zabesu.

Su modibbo sun kasa fitowa daga damuwansu kwata kwata Saida Dad ya sake zaunawa dasu shi da Ammar suka kwantar musu d hankali tareda rufe zancen maganar cikin Aysha da Garba akan babu me ji har acan kauye kada kowa yaji a bari ta haihu a daura musu auren kawai batareda kowa yasan ya sukai suka samu 'yayansu ba Dan haka suyi hkr su dauki kaddara tinda Allah ya kawo lamarin da sauri yaran zasu auri juna Kuma basa inda ake rayuwan saka Ido ko wani abin makamancin Hakan itama Fatma gashinan zaa yi Mata auren cikin amincin Allah da yardarsa.

Da wannan su modibbon suka samu sake zuciyoyinsu sbd daurin auren hakama Garba sun sauko Masa daga wutar da suka dauke Masa Dan ko gaisuwansa babu Wanda ya amsa a cikinsu

Maheer baida zabin daya wuce karban komai duk da Sam fatma dashi din baiga ta inda zasu fara bama amma kasancewan ko bai karba aurenbama baida lokaci ko ranar sake wani auren Dan haka ya barwa Allah zabi akan auren.

Ummah tinda ta tashi itama take wayoyi da mutanen da Mama ta hadata dasu da zasu Taho su gyara mata Fatman Dan haka itama busy take
Jannah Kuwa dole ta ajiye damuwanta gefe ta fara nuna farin cikinta da murnan auren Dan haka Bata gurin Fatma Bata gurin Maheer din Wanda nasa lamarin yasa yama manta Dana Jannah din da Bata kwana gida ba yanzu ta kansa yakeyi ta inda zai fara.

Kamar wasa sai gashi qaramar hidimar da basu shiryawa ba ta zama babba sbd yanda kowa yaketa hidimar auren daya kama ba shiri.

Koda aka tafi sallan jumaa su Mama dasu fiddausi da Falaq sun iso gidan harma dasu anty Maryam din alh saad duka sun iso sbd mama data gayyacesu daman suna son zuwa gaida Umman AZIZ LIMBA Dan haka sai gashi gidan ya Tara baqi masu aiki Kuwa aikin lafiyayyan abinci suketa yi na baqin gidan.

Gabaki daya mazan Zaadens din haka suka fara fitowa a Shirye daya bayan daya suna Jan lafiyayyun motocinsu suna ficewa zuwa daurin auren sai Maheer dinne ya fito karshe ya fice tareda Muhammad da shine zai tafi tareda shi cikin wata lafiyayyar farar Mercedes Benz S550 Muhammad ne ke Jan motar suka fice daman su Modibbo tini suka fice tareda Dad a motar Dad din driver ya jasu.

Lafiyayyan ready made lace Mai shegiyar tsada Ummah ta siya mata a acikin kudi masu yawan da aka ware na Shirin Fatman dama matan ZADs din gaba dayansu dan haka ko masu gyaran Kai da fata da fuska duka gida suka taho sukai mata komai Dan haka itama koda baqi suka iso angama shirinta tai Kyau simple ba hayaniya sai Dan glowing takeyi na gyaran da akai mata.

Jannah ma da Ummah duka dasu akai gyaran fuskan da skin din Dan haka kowannensu yayi kyansa yanda daukan ido musamman Jannah da cikin jikinta yake qarawa skin dinta Kyau.

Mama da Ummah suna dakin Ummah din suna maganarsu Maman na sanar da Ummah abinda suka tattauna da Baba Al'hassan itama ummah Naam tayi da shawarar tasu sbd gwara duka yaran a tattara ayi musu aure a huta da fargaban me zaije ya dawo Dan ita data tatace ma da har Falaq sai amata auren tinda uwarta ma ance iyakacinta Sha Biyar akai mata auren.

Mama data San zancen bama me isa gaban AZIZ bane dariya tayi tana cewa

"Ai idan kika anyi auren Falaq a yanzu ai bayan idon AZIZ ne zamuyi sa dan har gobe shiyasa baya Tina ko sunan dangin Mahaifinsa sbd auren da suka tilasta Akaiwa Ummitah da wannan shekarun.

*******Ana gama sallar jumaa aka daura auren MAHEER ZAD da FATMA JIBO ZAD Wanda mutane da yawa suka shaida anata taya murna da barin kudi wa maroqa kawai manyan mutane da manyan motoci ne keta ratsowa wasu na kokarin fita wasu na Pake anata gaggaisawa ai take su modibbo dasu kawun sukaji baqin cikinsu na yayewa suka hau farin cikin gaske anata sake gaisuwa da manyan mutane sosai.

AZIZ LIMBA ma ya halarci daurin auren Wanda ya saka tin ana yan media da maroqa suka ringa Kiransa a matsayin sirikin zaadens Wanda dole Dad ya ringa washe Baki yana farin ciki sbd yawancin manyan mutanen gasken da suka halarta mutanen LIMBAn ne dan haka a idanuwan mutane LIMBAs da Zaadens kusan ahali daya ne sbd sun zama dayan.

Ana gama daurin aure sai kusan yamma suka dawo gida sbd lafiyayyan reception da akai na masu abin duniya securities tako ina daga can AZIZ Kai tsaye gida ya koma shi Kuwa Sayd airport ya wuce yana ajiye AZIZ din gida yaje daukan Baba Al'hassan daya iso ayau din.

Tinda aka dawo daurin auren anata Dan sake taya juna murna su mama sunwa su Dad da modibbo Allah ya Sanya alkhair hakama Modibbo ya kira Fatma sun mata nasiha sosai suka Dora da maganar Garba Shima sukai fadan daya saka jikinsa sake sanyi kafin suka hakura tareda rungumar komai suka Barwa Allah.

Fatma sama ta koma Bata bari sun hadu da Maheer din ba sbd tasan dai Yana gidan tinda kowa ya dawo.

Sai magrib su Mama suka tafi gida gabaki dayansu Banda Falaq data maqalewa Jannah dole suka barta.

Da daddare kowa a gajiye yake Dan haka abincin Daren ma kusan kowa daban yaci sbd wasu a daki aka Kai musu wasu Kuma sun fito dining din koda 9 zuwa 10 na dare tayi kowa ya shige sbd neman hutawa.

Sai washe gari dukkanin suka hade a dining kowa gajiyansa ta sakesa.

Fatman ce dai kaman yanda ta saba sedai wannan Karan tana Jin nauyi yana hawa Kanta yana mata yawa ita ta saka aka shirya dining din yanda ya kamata ta qarasa gyara komai ta koma tayo wanka ta sauko a Shirye ciki riga da skirt na lace me laushi na hayaniya ta sake komawa kitchen ta hado Turkish tea da kusan kowa yana Sha ta nufo dining din lokacin kowa ya iso suna zaune.

Jin tayi jikinta na neman sanyi amma dai a daure ta qaraso tana ajiyewa ta gaida Dad cikeda nutsuwa da girmamawa kaman yanda suka saba.

Amsawa yayi cikeda kulawa yana sake jinta ta zama cikakkiyar yarsa yanzu data zama tasu har abada tinda ta riga ta zama matar Maheer dinsa.

Maheer din dake zaune sanyeda milk tsadaddiyar yadi me laushi daya Masa Kyau ta kalla cikin sanyi da mutuwan jiki tace

"Ina kwana Yaya Maheer"

Dagowa yayi daga wayarsa dayake kokarin ajiyewa ya zuba mata idanuwansa yana kallanta ita Kuma ta sauke kai ahankali tana Dan wasa da farcenta dayasha gyara jiyan yayi fes yana Dan shining.

Bude Baki yayi ya amsa a natse yana dan rage kallansa akanta,

Ammar ta gaida kafin Muhammad tukuna Saleem Wanda ya dago Dan amsawa fararen idanuwansa suka sauka akan Falaq dake tafe tareda Jannah sanye da riga da wandon Bvlgari da babu inda suka kama jikinta sunmata Kyau sosai sbd yarintarta ta fito sosai qaramar silk Louis Vuitton scarf ne a Kanta itama shi ta kalla ganin yanda yake kallanta ta juyar da idanuwanta tana bude Baki ba sauti tace

"Falaq Aziz ta fasa"

Wani mayen murmushi ya sauke yana Dan sauke kansa sbd kada kowa yaga halinda yake ciki ya Dan dago ya sake Kallanta ta sake juyar Masa da ido tana lafewa gefen Jannah.

Kansa yaji yana neman zarewa sbd Jin kaman ya janyota gabansa yayita kallan cute eyes dinta da bakinta me fadan ta fasa din.

Ganin murmushinsa dake sanyaya zuciyarta tin ba yanzu ba ya sakata sake boyayyar murmushi tana zaunawa gefen Jannah bayan ta gaida kowa cikin sanyi da yar shagwaban data taso a cikinta.

Breakfast din suka fara idanuwansa duk motsinta suna Kanta harma ta gaji cikin narkewa tace

"Saleem pls ka dena mana"

Da sauri kowa ya Kalli Saleem din Wanda ya Dan ware idanuwansa akanta yana kasa kallan kowa dake masa kallan mamaki.

Itama da maganar ta fita bakinta ba shiri saurin kallan kowa tayi tana cewa

"Sorry"

Jannah ce ta kalleta qasa qasa tace

"Me ya Miki?

Ruwa ta dauka tanasha fries din bakinta ya wuce tace

"Ze cinye wa daddy ni da ido ne"

Saleem daya ji abinda ta fada rintse idanuwansa yayi yana sake tausayawa kana da yarinyar Falaq da koyaushe yake fama da ita.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 79

Suna gama breakfast din kowa ya bar dining Fatma Kuma ta koma kitchen Dan rage wani aikin,

Jannah gurin Dad dinta ta tafi tareda brothers dinta suka shige Palonsa suna tattaunawa sbd tafiyan da Maheer zaiyi wani business deal kwanakin gwara ya tafi da fatma kawai wadda tana dawowa zata fara karatunta.

Ummah Kuwa tana dakinta itada Falaq suna fira tana Dan hada kayanta ta dauki waya ta kira sayd Kai tsaye tace yazo ya dauketa zata zo Nan gida.

Acan LIMBAs Kuwa koda Umman ta kira suna tattaunawa ne akan maganar aure da baba Al'hassan ya Tarasu yayi musu gabaki dayansu hadda AZIZ daya kamata ace zuwa yanzu yana guri daya da iyalinsa bai kamata aceba sunada aure amma tana gidan iyayenta a zaune.

Jin Ummah na tafe ya saka baba Al'hassan din taqaitawa sbd idan taxo a sake zaman na ita sbd hankalinsa ya tashi kawai da wannan lamura tinda koshi AZIZ din me auren kwatsam kowa haka yaji cikin babu wani tarewa babu wani zance babuma Wanda yasan da sauran ran aurensa Dan haka Shima ai duk abin mamaki da fargaban ne Dan haka ya kame ya bada umarninsa me karfi na karshe akan kowa ya gabatarda abokin rayuwa ayi musu aure.

Sayd daya rasa ta inda zai fara bayani Shiru yayi har aka gama tukuna ya fice zuwa dauko Umman,

Itama fiddausi Shirun tayi tana kasa dagowa ta kalli baban Dan batada abin fada bare iya fadan waye suke tare dashi hakama itama tinda cikin Nicky ya bayyana na Muhammad ne take cikin tsoro da tsananin kame Kanta daga zuwa dakin Sayd tin suna Greece sbd Bata daukesa komaiba kaman yanda Shima be dauka komai dinba sbd turai data ratsasu daidai gwargwado.

Yanzu Sam bata zuwa ta dena zuwa sbd kaucewa kaddarar shedan Dan kila su Kam AZIZ Batama San hukuncin dazai musu ba.

Sayd na fita fiddausin ma ta miqe ta fita ta koma dakinta tana tinanin kada ace auren hadi zaa musu daban daban da wasu idan basu fada halinda suke ciki ba.

Ko da Sayd ya iso Falaq na hangosa ta window din saman ta sauko da sauri suka hade palon qasa daidai yana shigowa da sauri ta kama hannunsa tana cewa

"P badai daukana kazo ba?
Ni tareda Jan zan koma fa,
I love staying here..." ta qarasa fada tana kallan Saleem daya qaraso fuskanta da sanyayyan murmushi tana sake lafewa gefen papan nata.

Wani mayen Kallo Saleem din yayi mata yana jin tako ina yarinyar tai Masa illar da baya iya control na idanuwansa da xuciyansa idan tana guri.

Hannu ya miqawa sayd suna gaisawa cikeda sakewan datake tsakaninsu Dan wani irin shakuwa da sabo suna qarasawa ciki har lokacin tana maqale gefen Sayd din tana murmushinta.

Shakuwa ce da kulawan daya ringa bata a lokacin jinyarta da Kuma sacrifice dayayi akanta na Bata zuciyarsa wadda baa karba ba Kuma ya dage ya nace ya haukace Saida ya samo mata wadda take kirjinta ya saka soyayya shiga tsakaninsu wadda da farko dukkaninsu sun dauka shaquwa ce kawai da kulawan dayake mata me tsanani kafin daga baya daya fara zama busy suka fahimci suna cikin zuciyar juna,

Yayi kokari sosai gurin danne duk abinda yake ji a Kanta sbd taxarar shekarunsu me yawa da Kuma ganin tayi qanqanta amma Kuma shagwabanta da rashin wayonta ya saka zuciyarsa ta qarasa macewa akanta a hankali ahankali dole suka yadda da soyayyar da sukewa juna sedai ya sani zaman jiranta ne zaiyi har lokacinda zata gama duka karatunta.

A nata bangaren batasan komaiba bayan cewa Saleem Zad nata ne ita kadai,baida iKon kula kowace mace me shakaru da mara shekarun ita kadai take dashi Wanda Hakan ya saka sam Baya iya muamala da mata ko a gurin aikinsa irin sosai sbd kaucewa fitinarta da rigimarta wadda idan ta tashi Bata tina lokacinta baiyiba na irin wannan rigima take Masa sosai,

Daddynta da Sayd sunsan akwai shakuwa da kauna tsakaninsu sosai amma basusan da soyayyar data gigita musu yarinya ba bare kudirinta na batason dogon karatu saita fara auren Saleem Zad ya zama nata kafin ta qarasa karatun daga baya.

Suna qarasowa tsakiyan palon suna zaunawa Ammar ma yana fitowa a Shirye zai fita wani gurin Dan haka hannu ya fara bawa sayd suka gaisa a Mutunce haryana tambayar Yaya jikin Aysha tukuna ya fice daga Palon yana daga wayarsa da ake kira.

Ammar na ficewa fatma da Jannah suka sauko suna gaisawa da Sayd din suna kokarin zama masu aiki suka sauko da akwatinan Ummah suna ficewa dasu harabar gidan.

Gabaki dayansu miqewa sukai suna kallan kayan kafin Ummah dake saukowa hankalinta kwance fuskanta a sake tana cewa

"Aa Falaq Baki shirya bane?
Bafa zama Sayd din zaiyiba tashi ki dauko kayanki muje"

Falaq cikeda mamaki tana kasa cewa komai ta miqe tana nufar sama.

Jannah Umman ta kalla itada Fatma da Saleem da sauri tace

"Ummah tafiya zakiyi ne?
Ina zaki bansan zakiyi tafiya ba"

Saleem ma kallanta yayi yace

"Ummah lafiya dai ko?

Fatma cikowa kawai idanuwanta sukai batason ummah tayi tafiya a yanzu datake buqatanta.

Murmushi umman tayi tana kallansu tace

"Tafiya zanyi amma bama nisa zanyi daku ba gida kawai zan koma"

Tana fadar Hakan ta Kalli Sayd dayake kallanta da mamaki tace

"Muje na shirya"

Miqewa yai yana yin gaba tabi bayansa.

Dad ne ya fito daidai lokacin yaga Umman na ficewa ya kallesu ya bi bayan Umman.

A kofa ya cimmata yana saurin riqo hannunta yana dawo da ita baya kadan.

Ganin hakan kowa yabar palon
Jannah data fahimci kaman tafiyarta ne Umman zatai take hawaye suka ciko idanuwanta tafara gangarowa dasu tana son magana bama tasan me zata fada ba.

Dad dayaji zufa na kokarin keto Masa kallan Umman yayi yana sake riqe hannunta cikin nasa yace

"Fatima ina zaki tafi da kaya haka?
Meya faru Kuma?
Ba duka na dena shiga lamarin yaran ba na barsu,
Gashi ma yanzu komai lafiya"

Numfashi Umman ta sauke ahankali tana dagowa ta kallesa cikin nutsuwa tace

"Haryanzu akwai damuwan auren Jannah da AZIZ dayake damunka,
Kai fa mahaifi ne,tayaya kana kallo yarinya da aurenta tana zaune gida ta zabi zaman gida akan gidan mijinta sbd kawai tasan abinda yake ranka,

Aure tsakanin LIMBAs da Zaadens dai bazai taba yiyuwaba Dan haka kowane auren ma a hakura dashi kawai idan zaka zo karban takardar 'yarka saika kawo Masa takardar uwarsa daga nan.."

Tana gama fadar Hakan ta juya zata wuce Dad ya share wani mugun zufan dayake tsiyayo Masa yana kallanta duk yama rikice cikin qasa qasa da murya kada Yara su jisu yace

"Fatima wane takarda ana Zaune kalau da girmanmu?
Dena fada ma kada Yara suji
Ni yaushe nace zanje karban takardar Jannah?wallahi tallahi bance ba Kuma bazance bama,
Yi hkr yanzu ki koma ciki sai miyi magana anjima kinji?"

Numfashi ta sake saukewa tana zare hannunta ta wuce gaba tana cewa

"Kowa ya riqe nasa ai haka kakeso ko?

Mota ta isa daman sayd ya bude mata tana isowa ta shige a rufe Dad na qarasowa ya tsaya yana Kallo Falaq ma ta iso ta shige sayd yaja motar suka bar gidan.

Suna barin harabar gidan Jannah dake sama tana Kallo ta silale qasa tana kuka.

Fatma ma tashi hankalinta yayi jikinta na sanyi ta zauna tana rafka tagumi.

Dad jiki a tsananin mace ya dawo ciki ya shige Palonsa yana Jin gidan na Masa wani irin empty yakuma San duka yaransa babu Wanda bazai shiga tsananin damuwan rashin Fatiman ba musamman Ammar Wanda itace kamar garkuwansa a yanzu.

Sayd da Falaq baby Wanda ya iya cewa komai a motan har suka isa gida aka shiga ciki da kayan Umman Wanda ya saka Mama mamaki amman batace komaiba sbd ganin kowa na nan,

A lafiyayyan bedroom din dake Palo daya da Mama aka Kai kayan Umman,

Koda AZIZ ya taho gaida Umman yana ganin kayan datazo dasu baice komaiba Shiru yayi kaman bai luraba sbd ya dena shiga tsakanin Umman da Zaadens.

Har dare babu Wanda ya cewa ummah komai gameda dawowan nata itama batace komaiba haka suka sakewansu cikin walwala da farin cikin kasancewanta cikinsu.

Ammar na komawa gida a daren ya Samu Ummah Bata gida Dan haka kai tsaye LIMBAs din ya taho gurinta.

Yana zuwa har ciki aka shiga dashi bayan sun gaisa dasu AZIZ harma da baba Al'hassan Falaq ce takaisa har dakin Umman datake zaune tana waya da Jannah daketa rokonta ta dawo tana shashantar da ita.

Tana ganin Ammar din tai sallama da Jannah ta kashe wayar tana ajiyewa gefe tareda kallansa cikeda kauna da kulawa tana nuna Masa gurin zama.

Acan Zaadens tinda Ammar ya tafi suke fatan yadawo da Umman tinda sunsan tana ji dashi zata iya biyosa ta dawo Dan haka duka suke zaune a palo suna jiran dawowansu.

Sai dare sosai Ammar ya rabu da ummansa bayan sun tattauna sosai ya dawo gida,

Da mamakin rashin ganin Ummah suke kallansa Shima da mamakin ya kallesu yana basarwa yaci abincinsa ya shigewansa daki.

Haka kowa ya kwana jiki a mace washe gari kafin Maheer ya wuce office LIMBAs ya fara biyawa gurin Umman Shima yayi nasa rarrashi ya Dade sosai Shima kafin ya wuce office.

Kafin Kace me zaadens suka fara zarya a LIMBAs takai har dasu ake cin abinci wasu lokutan musamman Ammar Wanda babu ranar da baya zuwa gidan yakai dare sosai,
Maheer ma kullum saiya biyo kafin ya wuce office kokuma bayan ya dawo,

Saleem dayake kaman da gida shikam koyaushe ma zuwa yakeyi,
Muhammad ma tin yana Jin nauyin zuwa harya fara zuwa duba Aysha da cikinta da Kuma Umman.

Jannah da fatma ne kawai basu samu daman zuwa ba sbd Jannah na kunyar yanda zata zo gidan ta koma hakama shi kansa AZIZ din ya kawo idanuwansa ya saka mata bai nemeta ba bare ce mata Komai,
Itakuma fatma batasan yanda zata je gurin Maheer ta rokesa son zuwan bane shiyasa duk damuwa da kadaicin rashin Umman ya musu yawa suka koma abin tausayi a cikin gidan gashi su modibbo sun koma.

Dad ma da kwata kwata ummah Bata daukan wayarsa a cikin sati biyun take ciwon zuciya da damuwa suke neman Kaisa kwance Dan haka yau yana tashi Tara yaran yayi gabaki dayansu yayi zaman nasiha dasu yana Jin Sam bazai iya rayuwan ba Dan kadaici zai Masa illa da yaran duk da ba Yara bane amma zaman Umman yana sake bawa familyn farin ciki da jinsu a cike.

Da daddare kusan karfe goma Jannah harta fara Shirin bacci jiki a mace saiga Kiran Dad din a wayarta.

Hijab ta sako akan kayan baccinta ta sauko ta nufi Palonsa.

A tsaye yake ko data shiga Dan haka a Sanyaye ta qaraso tana gaidasa.

Amsawa yayi yana kasa kallanta yace

"Je ki hado kayanki yanzu ku fito muje"

Kallansa tayi da Dan sauri ya kalleta Kai tsaye yana cewa

"Kije"

Juyawa tayi ta fice cikeda mamaki me girma amma ba fuskan tambaya a gurinsa.

Dakinta taje ta kasa ma hada kayan sedai fatma da jikinta yake tsananin mace ne ta hada mata tana Jin kadaici tin yanzu yana mamayeta ba Ummah ba Jannah.

Saukowa sukai gidan tsit kowa na dakinsa Dad ya kama hannunta fatma Kuma takai mata kayanta har motan da Dad ya kira Muhammad ya Kaisa.

Fatma suna shigewa mota hawaye suka fara gangaro mata ta juya da Sauri tana komawa ciki sukuma suna ficewa Jannah ma hawayen takeyi.

Fitan motarsu Dad din ya saka Maheer fitowa sanyeda kayan baccin Frnsess masu santsi black da suka qarawa haskensa haske ya nufi kofar palon yana kallan time.

Fatma data shigo tana kuka mara sauti tana Jin gidan itama duk ya isheta Bata lura dashiba sbd hannuwanta dake fuskanta sai Jin tayi tai karo dashi da sauri ta janye hannuwanta hawayenta na gangarowa ta kallesa cikin sanyi da kuka tace yayi hakuri.

Kallan bakinta da yayi maganar da hawayenta dake gangarowa yai yana Jin tausayinta kafin ya bude Baki yace

"Waye ya fita?

"Dad ne da Jannah ya tafi kaita"

Shiru yayi yana kokarin juyawa ta bude Baki tace

"Yaya Maheer nima dan Allah zan bisu saimu dawo tare da Ummah"

Dakatawa yayi sbd Jin zancen wani iri da Kuma muryan datai amfani da ita gurin zancen.

Juyowa yayi ya kureta da kallo me sanyi kafin ya miqa hannunsa ahankali ya kama nata ya janyota gabansa sosai har kirjinsu na haduwa yace

"Ita Jannah gidan aurenta ta tafi,
Ita ummah mijinta ne yakai mata sirikarta ya daukota ita Kuma ke Kuma me zaace kinje yi?

Kin manta kinada aure ne yanzu?

Gyada kai tayi cikin wauta da Kuma fadan gaskiyanta tace eh ta manta.

Da mamaki ya sake Kafeta da ido yana auna shekarunta Dana Jannah wadda ya kusa haihuwa.

Ajiyan xuciya ya sauke yana Dan rankwafowa ya dauketa cak gabaki dayanta yana nufar dakinsa da ita sbd Bata matsayin da zai hanata manta auren dayake Kanta daga yau din.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 80

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa da ita yana shiga da kafarsa ya tura kofar dakin yana rufewa tareda saka key.

Tsakiyar dakin ya ajiyeta yana Dora idanuwansa akanta tayi Dan baya ahankali tana kasa dagowa ta kallesa kirjinta na Dan bugawa da karfi ta bude Baki Jin Shiru a sanyaye tace

"Ba nufina na manta ba,ina nufin zanje ne....

Shiru tayi tana kasa qarawa sbd yanda ya matsota sosai ahankali qamshinta na shigar hancinsa direct hakama tana Jin saukan numfashinsa me dumi a fuskanta.

Sake ja baya tayi kadan tana Dan dagowa ahankali ta kallesa da idanuwanta da suke cikeda hawayen datake tin a wajen.

Idanuwansa akanta suke bai dauke ba yana qare mata wani nutsatsen kallo sbd bai taba tsayawa ya Kafeta da ido ya Kare Mata Kallo ba sai yau din.

Kayan baccin dake jikinta ya kalla riga da wando masu tsantsi har qasa sai qaramar hula dake Kanta wadda bata rife gashinta dayake a tsaf gyare duka ba.

Wuyanta dayake bayyane yafara Kai hannunsa ya shafa ahankali tareda yanjota ta fado jikinsa ya sake shaqar qamshinta daya fara kashe Masa jiki yace

"Fatmah" cikin wata murya Mai cikeda kasala sbd rabonsa da koma a mafarki shaawansa ta mace ta motsa tin bayan rabuwansa da Anny Dan haka ya sauke ajiyan xuciya data fidda numfashi Mai dumi a fuskanta again take ta rintse idanuwanta tana Dan qanqame jikinta tana kokarin janyewa baya ya mannota jikinsa gabaki daya yana hadesu kirjinta yayi kyakkyawan sauka a kirjinsa yana Jin wani irin taushinsu da tudunsu a lokaci daya suna tada tsikar jikinsa gabaki daya.

Fargaba taji tafara shigarta hannuwanta suka Dan fara rawa ta kasa dagowa ta kallesa ta bude Baki tace

"Kayi hakuri to Yaya Maheer bazan sake ba nafasa zuwan zan zauna gida"

Tana fadar Hakan tana Dan kokarin zame jikinta amma ba damar Hakan sbd harga Allah gabaki daya haduwan jikinsu ya gama tada Masa komai musamman Kamshin datake fitarwa me tsananin dadi a hancinsa da kwakwalwansa.

Cikin wata murya me sautin daya sakata kallansa ahankali tana sake shiga fargaba yakai fuskansa ya hade da tata yana shaqar qamshi da numfashinta dakyau yace

"No nasan zaki sake ne gwara kema ki zama cikakkiyar matan auren saiki koyi zaman gidanki tinda kafarki yawo takeso"

Girgiza Kai tayi tana kasa magana sbd hannuwansa dake yawo jikinta suna sake manneta jikinsa yana rungumeta tsam tsam da Kyau.

Daqyar cikin wani sauti ta bude Baki tace

"Yaya Maheer dan Allah fa"

Shima kasa Bata amsa yayi yana kama fuskanta ahankali sbd hakurinsa da control dinsa dasuke qarewa ya Dan dago fuskan nata yayi mata wani irin mayen Kallo kafin yakai bakinsa ahankali kan nata yana hadewa cikeda wani irin yanayi ya lumshe ido yana jinsa kaman yau zai fara sanin mace.

Kissing nata yakeyi yana Jin wata lafiyayyar shaawansa na sake motsawa tareda abubuwan dayake samu a tattare da jikinta Mai laushi da kamshi Dan haka ya fara Jin zai zare gashi ita gabaki daya tsoro takeji rawa kawai jikinta yakeyi sbd ta kasa sakewa da Yaya Maheer dinne ajikinta saduwan aure Kuma zaiyi da ita gashi Bata iya ko saba wannan kisses dinba Dan haka ta rasa me zatai sai hawayen fargaba.

Daqyar ya iya sakinta sbd yanason wannan Karan aurensa da zuria idan Allah zai basa su kasance masu albarka Dan haka janta yayi sukai alwala suka fito da kansa yakaita har dakinta ta sako hijab ya sake dawowa da ita suka shige.

Sallah sukai tareda addua me yawa kafin suka shafa ya sake janyota jikinsa suna daga zaunen basu tashi ba ya dorata kan kafafunsa yana kallanta cikeda mamakin kunya da fargaban datake ciki.

Hijabinta ya zare mata ahankali yana sauke idanuwansa akan kirjinta dake sama yana qasa sbd harbawa da fargaban datake ciki sosai.

Murmushi me sanyi yayi yana rungumeta jikinsa ahankali yana shafa bayanta Dan samar Mata da nutsuwa tukuna yana ambatar sunanta cikin sanyi yana sake fada mata mahimmancin aure dayake Kanta yanzu.

Shiru tai a jikin nasa tana sauraronsa fargabanta Da tsoronta ya tafi sosai sbd yanda yake mata da Kuma tinanin ya fasa komai.

Ahankali taji hannunsa me laushi da sanyi yana shiga cikin rigarta ya shafi bayanta zuwa wuyanta kafin ya fara gangarowa cikinta dayake a shafe ya shafa ahankali take ta qanqamesa tana Jin wani irin numfashi na kufce mata ta tashi daga kwancen datake jikinsa tana dagowa zata kallesa ya Dora bakinsa kan nata yana mata wata fitinanniyan tsotsa yana bude botiran gaban rigarta gabaki daya lokaci daya batareda ya tsaya daya bayan daya ba kawai rigar ya bude suka ringa zubewa ya zare rigar daga jikinta yana jefarwa.

Non padded bra din dake jikinta nude kala ya zubawa ido yana kallan fararen Kirjinta da suke ciki ya lumshe ido yana Kai hannuwansa ta bayanta ya balle hook na bra din ya zare ahankali ya jefar tayi saurin daga hannuwanta zata rife kirjinta ya riqe hannuwan yana saka kansa a maimakonsu take ta fasa wani irin malalacin kuka tana Jin jikinta na Dan tsananta rawa Dan Bata taba sanin da wannan rikitacciyar wasan ba Mai zare Kai.

Rigar jikinsa ya jefar Shima yana sake hadesu yana mata mayyar tsotsa tako ina kafin ya miqe da ita a jikinsa ya nufi babban lafiyayyan gadonsa yana kwantar da ita tareda mata rumfa yana zare wandon baccinta da kafarsa sbd hannuwansa are busy da wani zazzafan aikin a kirjinsa da bakinta daya kissing kaman zai cinye.

Fatma Jin abinda yafi karfin rayuwanta gaba daya kuka ta ringa Masa Wanda yake sake zare nutsuwan kansa yana sake Jin dadi da shauqi me karfi sbd Anny Bata taba Masa kuka ba ko a Daren farkonsu.

Lafiyayyan nutsuwa da gamsuwa ya samu da fatman wadda taji jiki ba laifi Dan Kuwa gajiyan gaske ya sauke mata ta shekarun daya debo ba samun cikakkiyar gamsuwan aure da samun mace me sauran yarinta.

Rungumeta yayi jikinsa yana lumshe idanuwansa yana Jin duniyarsa ta gama cika cif cif a yanzu dayake mace kaman Fatman Dan haka baisan lokacinda ya ringa sakawa su modibbo da duk Wanda yaje daurin aurensu ba albarka harma da Garba da Nicky da sukai sanadin rikicewan komai akai musu auren.

Fatma Kam bacci da Dan zazzabin gurzuwa ne suka sakata lafewa a jikinsa sai gap da Asuba suka tashi.

Wanka sukai tareda sallah kafin ya sake maidata bacci a jikinsa bayan ya sake samun wata gamsuwan a tareda ita wadda ta sakasa baccin me nauyi Shima yanajin kaman bai taba samun kwanciyan hankali da nutsuwaba kaman yau din.

******Dad a lokacin da yabar zaadens din cikin Daren da Jannah Kai tsaye LIMBAs suka nufa yana Jin zuciyarsa na hakura da dukkanin abinda ummah bataso,

Abu daya gani ya Kuma fahimta ya Kuma saka kansa a gurin shine idan har yana so da kaunar umman kaman yanda yake ji to dole zai sakawa ransa kaunar danta idan har bazai iya kaunarsa ba sbd tsananin son da Jannah ke Masa dakuma kasancewansa uban jikansa dayake so tin baizo duniya ba,

Ummah tana tsananin kaunar nasa Yayan da har ta zabi barin nata ta zauna dasu Wanda yasan shi bazai taba iya barin yayansa ba sbd tsananin son dayake musu Dan haka yasan dole tayi sadaukarwan da har abada bazai iya dena Sonta ba Dan haka ya zabi son dayake mata ya kaunaci 'danta akan abinda zuciya take saqa Masa.

Suna isowa dayake securities sunsan Muhammad da motarsa take aka bude Masa ya shige suna Masa barka da zuwa.

Parking yayi tareda Dan juyowa ya Kalli Dad din Wanda ya sauke ajiyan xuciya yana sake cirewa ransa Komai ya fidda wayarsa ya karbi numbern AZIZ LIMBA a gurin Muhammad din ya saka Kiransa Kai tsaye.

A wannan lokacin AZIZ na tareda Sayd suna wata tattaunawa so lokacin daukan wayarsa ya wuce hakama baquwan number ce Dan Haka Kai tsaye kashe kiran yayi tareda kashe wayar gabaki daya yana ci gaba da abinda yakeyi.

Duk me buqatan ganinsa ko magana dashi sayd yake nema Dan haka Dad bai sake Kiransa ba sai kawai ya kira sayd Kai tsaye Wanda yana ganin Kiran ya Kalli AZIZ din Wanda bai dago ya kallesaba hankalinsa na kan abinda yake karantawa.

Daukan wayar sayd yayi Wanda take ya gane me magana cikeda yar girmamawa ya gaidasa yana miqewa yafice zuwa harabar gidan Dan tarbonsa sbd sanar dashi yayi Kai tsaye yana LIMBAs.

Da girmamawa sayd ya tarbesu tareda bude Masa motar ya fito hakama Jannah wadda hannunta yake cikin na Dad dinta tana kallansa cikeda tausayawa sbd tasan ya ajiye komai ne ya hakura sbd soyayyar dayake mata dakuma wadda yakewa Umman AZIZ din.

Babban palon gidan Kai tsaye sayd ya isa dashi yaje ya sanar dasu Mama harda Umman sai gashi duk sun fito cikeda girmamawa aka gaisa fiddausi ta gaidasa taje da Kanta takawo Masa ruwa batareda ma saka masu aiki ba sbd basa girmamawa a matsayin mahaifin Jannah da Kuma mijin Ummah.

Ummah Bata fito ba mama dasu fiddausi ne kawai suka fito sai ga AZIZ Wanda sayd yaje ya sanarwa da zuwan Dzad din.

Sanye yake da jallabiya fara qal me tsananin laushi da santsi tana Daukan ido ta zauna jikinsa daidai size nasa data fidda tsawonsa da kakkarfan jikinsa sai kamshinsa me sanyi dayake tashi hankalinsa kwance da kwarjininsa da sai ayau yake cike idanuwan Dad din Wanda ya qare Masa Kallo tin daga nesa yana hango kyawawan kamannin Fatimansa a gurin AZIZ din.

Yana qarasowa gaida Dad din yayi yana kawar da mamakinsa cikeda girmamawa kafin ya zauna yana kallan Jannah wadda tayi Masa kallan tsaf kafin ya iso tana dauke Kanta sbd ganin nutsuwa da kwanciyan hankalin dayake ciki abinsa ita Kuwa duk tabi ta zama abinda ta zama sbd Tinaninsa da tinanin halinda yake ciki na damuwa.

Dauke idanuwansa yayi daga Kanta yana Dan basar da murmushin ganin yanda tayi wani irin ya dawo da hankalinsa kan Muhammad suka gaisa Nan fiddausi da Falaq suka fice daga Palon suna barin manya,

Sayd ma ficewa yayi hakama Muhammad fiddausi ce tayi Masa jagoran zuwa duba Aysha da jikin sai ahankali daidai lokacin Ummah ta fito sanyeda hijab har qasa hankalinta a kwance ta kallesa tana musu barka da zuwa Harshi har Jannah din Wanda Hakan ya sakasa rudewa ma daga abinda yake kokarin son fada ya fara kame kame.

Dan boyayyar murmushi AZIZ ya sake yana tayasa Nemo zancen Daya manta yace

"Duka komai ya wuce Dad"

Karban zancen Dad yayi da cewa

"Komai ya wuce ga Jannah Nan ta dawo hannunka,matarka ce iyalinka ce ina fatan har abada zaka zamo gata da majingininta itada Yayan da zata Haifa maka,
A matsayin na mahaifinta ni nakawo Maka ita da kaina sbd na baka amanar yarinyata da kaina ina fatan soyayyar da kake mata zata dore har abada,
Allah ya sake kawar mana da shedan yayiwa aurenku albarka tareda zuriarku"

Amin" kowa yace kafin yaci gaba da nasiha tareda neman afuwa ga duka ahalin LIMBAs bisaga abinda ya faru shekaru wanda bai taba bude Baki ya nema yafiyar ba.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 81

Muhammad da bai taba isa dakin Aysha ba duk zuwan dayake yi ganinsu yawanci a Palo yake tsayawa a cikin mutane yake Dan iya ganinta ya gama ya tafi wani lokacin ma ko ganinta baya samun damar yi sedai yabar tarin kayan fruits dayake kawowa kaman hauka ya tafi sbd daga shi har ita sun rasa ta Yaya zasu fara fuskantar juna Dan hakanne suke da avoiding haduwansu su kadai.

Ko a yanzu ma ya dauka fiddausi zata tsaya tareda su ne Dan haka ya isa dakin a natse fiddausi tayi knocking ta bude bakin tareda sallama ta duba taga Nicky din bata dakin tana toilet Dan haka tace ya shigo.

Shigowa dakin yayi yana zaunawa a sofa cikin nutsuwa yana shaqar qamshin turarenta da bazai taba Manta kamshinba har abada sbd a wancan lokacin da kaddarar ta afku tsakaninsu ya dauki lokaci qamshinta na jikin kayan dasuke jikinsa lokacinda ya hadu da ita,

Qamshin yayi yayi yaqi fita kayansa sbd tsadan turaren da karfinsa Wanda daga karshe kona kayan yayi sbd koyaushe suna Tina Masa yanayin nasu da bayason tinawa.

Fiddausi juyawa tayi ta fice dakin tana jan kofar dakin.

Shiru yayi yana Dan duba wayarsa a natse.

Babu daukan time sosai sai gata ta bude kofar bathroom din tafito batareda tasan dashi ba Sai data fito sosai ta fara takowa tsakar dakin me girman dayake dauke da babban lafiyayyan gadon Turkish set da sofas masu laushi da ctable da sauran luxury decos.

Kaman daga sama taga mutum a zaune kawai da sauri ta dakata tana kallansa da idanuwanta da sukai laushi sosai sbd Amai ne ta gamo tai brush.

Ajiye wayarsa yayi Shima a natse yana dagowa ya zuba mata idanuwansa masu kyau da hakuri yana kallanta.

Kasa daukan kallansa tayi tana Kuma rasa abin fada ta tako ahankali tana isowa bakin gado ta zauna shi Kuma ya gangaro da idanuwansa akan cikinta dayake bayyane sosai sbd sanye take da rigar bacci doguwa har qasa Mai Dan kauri babu ko hula akanta gashinta da bai taba samun kitso ba yana daure tsakiyan Kanta baa tanke ba sbd kada Kanta yayi ciwo.

Tana zama qaramin mayafin dake kan gadon ta dauka tana rufe Kanta tana kasa dagowa ta kallesa ta fara kokarin hada maganar da zata fada ya katseta ya hanyar saukaka mata shi yayi maganar sbd tausayinta daya cikeda haka kawai sbd ganin yanda cikin yake mata kaman nauyi.

"Yaya jikin?

Ba karamin taimaka mata yayi ba daya karbi maganar Dan haka ajiyan xuciya ta sauke a boye tana Dan dagowa ta kallesa Shima ita yake kallan ta zubawa fuskansa me haske Ido tana mamakin kasancewansa fari sosai duk da a kauye ya rayu hakama nutsuwa da sanyinsa suna Nan babu sauyi duk da zai sameta a matsayin matarsa bai taba nuna wani rawar kai ko nuna girman Kai akan hakanba duk da yasan bai cancanci mace kamarta ba Amma duka yayi Shiru ya runguma sbd darajar abinda yake cikinta Wanda koma tayaya aka samesa dai jininsa ne.

Hawaye ne suka ciko idanuwanta taji tana kasa iya yadda da zuciyarta akan cutatar dashi da aurenta Dan haka Bata iya amsa tambayarsa ba ta bude bakinta muryanta cikeda danasani da kunyar abinda taja musu tace

"Ina rokon yafiyanka sbd nice sila Kuma sanadin halinda kake Ciki ayau na bacin suna da auren dayake kaman na dole a gareka"

Ahankali cikin kunya da baqin ciki ta sanar dashi abinda ya faru Wanda tayi datasani da nadama harma da baqin ciki da tsanar Nicky din baya ta Kuma fara kuka tana rokon gafararsa.

Shiru yayi yana kasa cewa komai sbd baisan mema zai fada din ba Dan haka ya kasa ma kallanta sbd zuciyarsa datai duhu sosai yana mamakin macen da zata iya bawa namiji abinda zai sadu da ita kenan a wancan lokacin da AZIZ dinne yasha haka zata basa Kanta ya sadu da ita ko me?
Hakama da Ammar ne yasha haka zai haqewa Jannah da auren wani akanta sai rayuka da dama su lalace kenan duk sbd zuciyarta data Kitsa mata wannan mummunan tinanin da qazanta.

Miqewa yai ya fice dakin kawai yana Jin tsanar kansa gabaki daya kasance yaji wannan mummunan zancen daga bakin macen da zata zamo matarsa Kuma uwar 'yayansa.

Miqewa tayi tana kuka tabi bayansa da sauri tana Kiran sunansa muryanta na rawa sedai bazai iya tsayawa ba Dan bayason ya tsaneta yana buqatan tafiya kafin Tinaninsa ya dawo daidai zuwa wani lokaci.

Palon ya ratso inda su Dad suke zaune suna magana har lokacin idanuwansa ko gani basayi itama nata idon ya rife ta biyosa da sauri tana sake Kiransa.

Ganin yanda take tafiya Bata duba gabanta ne tana neman faduwa ya saka Mama tashi ta tareta tana cewa

"Aysha lafiya Kuwa?

Kuka ta fasa tana kasa boye komai ta fara fadan komai akan yanda ta samu cikin kunya da baqin cikin kalaman nata na sake kasheta tana kuka sosai tana ce su roki Muhammad din ya yafe mata.

Kowa Shiru yayi sai a lokacin AZIZ ya Tina da lokacinda Jannah ta shiga halinda Ayshan ke fada Wanda shi kadai ne yasan da Hakan take yaji wani mummunan zufa na rufesa sbd kenan a wancan lokacin da Ammar Jannah tafara haduwa dashi komai zai iya faruwa ko me???

Saurin ajiye tinanin yayi sbd wani mugun nauyi da zafi daya rufe kirjinsa da idanuwansa take ya miqe baya ko gani sosai yabar palon.

Dad ma da zufa ya gama jikasa miqewa yayi jikinsa na yar rawa yabar palon Shima yana nufar kofa sbd kenan da Mummunan balain da suke ciki yanzu ya kere komai da duka plans din Nicky din sunyi aiki da cikin Ammar da auren wani akanta ne yake kan Jannah din hakama da Shima AZIZ din cikinsa ne a jikin Nicky din,Jin Dad yayi kaman ma zaiyi amai Dan haka ya isa mota batareda angama meeting dinba kowa ya watse babu Wanda ya iya cewa komai sai Ummah datakai Ayshan dakinta ta wuce nata itama.

Jannah ma da rawa jikinta yakeyi sosai miqewa tayi tana rasa gurin zuwa Dan haka tayi dakin fiddausi Kai tsaye tana neman guri ta zauna har lokacin rawa jikinta yakeyi ta dafe cikinta tana ta jerowa Allah godiyan da cikinta ayau ya kasance na mijinta AZIZ dinta bana Mummunan kaddarar da zata kashe Kanta ba akan baqin ciki.

AZIZ ma yana isa Palonsa Jin yayi jiri ya debesa ya zaunar kujera da karfi,

Abinda yakeji a kirjinsa Jin yayi yana Masa yawan da kaman ciwonsa Daya fara mantawa yana neman tashi sbd kishin Jannah kadai dayake neman kashesa na iya wannan maganar da abinda ya tashi faruwa kenan a baya.

Jin yayi numfashinsa na toshewa babu abinda yake tsananin buqata face Jannah din gabaki dayanta Dan ita kadaice zata yaye Masa abinda yakeji ya ganta a gabansa ya Kalli cikinsa dayake jikinta ya sake tabbatarda ita tasace sai mutuwa Dan haka kai tsaye ya miqe baya ko gani sosai ya fito.

Yasan tana dakin fiddausi Dan haka kai tsaye can ya nufa yana isa kofar dakin kafin yayi knocking aka bude fiddausin ce zata je ta kawowa Jannah da har lokacin jikinta ke rawa ruwa.

Ganinsa tsaye idanuwansa jajir ya saka fiddausi janyewa daga kofar batace komaiba Shima baice komaiba ya saka hannu ya janyo Jannah din suka fice Bata tinaninta sosai itama sbd tsoron dayake sake jijjigata na kaddarar data tsallake.

Suna ficewa fiddausi ta koma dakin tareda rufewa tana hayewa gadonta.

Ganin tafiyanta kafafunta na hardewa ya sakasa juyowa ya dauketa cak yana barin bangaren da ita kwata kwata ya nufi Masa Wanda yake underground suna shige ya rufe kofar tareda ajiyeta bakin kofar ya zuba mata idanuwansa yana Jin duk ranar da wani yayiwa matarsa ko kallan shaawa ne zai iya zama makashinsa bare abinda aka fada din ya faru....

Ita Kanta zuba Masa idanuwa tayi hawaye masu zafi na tsiyayo mata batasan lokacinda ta fara godewa Allah daya saka aurenta da AZIZ din yana Nan ba hakama ayau taji Bata danasanin daya maidata cikakkiyar macensa da har ta dauki cikinsa ba.

Shi Kuwa dayaji jikinsa na tsananta rawan ciwonsa take ya manneta jikin kofar palon yana hade bakinsa da nata yana Bata wata fitinanniyar mahaukacin kiss yana yaga hijabinta ya jefar yana sake manneta jikin kofar.

Kuka takeson yi sbd halinda zuciyarta take ciki Amma ganin yanayinsa da lura da ciwonsa yana tashi ne ya sakata barinsa samun nutsuwar da ita.

Kwance suke tayi Shiru a jikinsa har lokacin Bata iya cewa komaiba.

Shima jikinsa a mace yake da kasalar dogon love din dayayi making da ita kafin ya bude Baki a sanyaye cikin nutsuwa yafara Bata hakurin kawo Nicky cikin rayuwansu da hakurin duka abinda ya faru tukuna ya bige da rarrashinta sbd kukan datake yi Masa ahankali na samun nutsuwa da sukuni a tareda mijinta a gidanta yanzu Kam.

Washe gari lafiya kalau suka tashi Kuma kowa ya cire tinani Da damuwan komai sbd su Ummah ma sun sake zama da Ayshan sun mata fada da nasiha ta iyaye mata tareda sake dorata a hanyar data kamata.

Har palon AZIZ Mama takai Ayshan ta basa hakuri sosai tareda nuna tubanta itama Mama ta sake basa hakuri akan nata kuskuren Jannah ma Aysha ta Bata hakuri ta Kuma hakura sbd ummanta data shige daki da ita itama ta sake mata fadan zaman aure da nasiha tareda Bata hakurin abinda Ayshan tayi suka watsar da komai aka ajiye.

Nicky Bata sake sanin kyan hali nada dadi ba Saida taga a cikin wunin kowa ya yafe mata suka ajiye komai kaman bai faru ba sbd Ummah dataiwa kowa nasihar yafiya na Mantawa tareda tinatar dasu Allah bai bari sun samu kansu a mummunan kaddarar ba ko Dan haka su gode Masa su manta komai Tinda Ayshan da Kanta tayi nadama.

Yanda kowa ya yafe mata aka ci gaba da Bata kulawanta da lafiyarta ya sakasa rasa Baki da idon da zatai musu godiya ga Kuma identity data samu a LIMBAs da batada shi a baya sbd a baya batada identity din daya wuce yayanta Wanda bama sa zaune qasa daya.

Dad kuwa a Daren suna komawa kasa nutsuwa yayi sbd tausayin Garba Da nasa Dana yayansa da dayanxu sun qarasa zama abin kwantance.

Muhammad Kuwa kwana yayi yana kukan baqin cikin da baisan Kuma wa zai fadawa ba sbd tamkar tonawa uwar 'yayansa asiri ne tinda koma menene shine yayi muamalar da ita bawai itace tayi dashi ba dan haka shima Mai lefin ne amma rayuwarsa ta cutatu matiqa.

Alwala yayi ya kwana yana fadawa Allah kukansa tareda neman zabi da mafita mafi alkhairi a cikin lamarin nasa da Aysha.

Dad ma daya kwana yana sallah washe gari bai fadawa kowa ba bayan modibbo dasu kawu daya kira a waya ya fada musu komai sbd su cire baqin cikin abinda suke tinanin garban yayi Susan ba laifinsa bane kaddara ce duka ta hau kanshi da ita Kanta Ayshan.

Hakan Kuwa da yayi ya saka zuciyar kawu isiya samun sukuni da saukar nauyin dayake danne da ita tin ranar da cikin ya bayyana sbd yanajin kaman tarbiyansa ce ta gaza amma yanzu ya yadda da kaddara ce bawai halin garban ba Dan haka yaji ya yafe Masa Kuma ya fara rokon idan aurensa da Ayshan alkhairi ne Allah ya tabbatar ya Kuma inganta Masa rayuwan garban da zuriarsa.

Shi kansa Muhammad din ko da gari ya waye Jin yayi damuwansa duka ta yaye bayajin komai face nutsuwa da sake aminta da hukuncin Allah Dan haka har cikin ransa yaji ya yafewa Ayshan tinda har ta iya fadan laifinta to tubanta tsaftatacciya ce.

Fatma da Maheer sai rana sosai suka tashi tana fitowa sama ta wuce ta sauya kaya sbd tayi wanka acan tana saka kaya ta sauko taje ta gaida Dad Wanda ta tadda Maheer din acan Dan haka a kunyace ta gama tafito.

Already an shirya dining Dan haka babu aikin datai kowa ya fito sukai breakfast masu fita suka fice ita Kuma ta koma sama ta kwanta a sbd batada kuzari ko kadan.
#MAMUH
07019691719

BOOKS BY MAMUHGEE
Buri daya 500
Kaunarmu 500
Min walk 500
Ubayd Maleek 500
Deen marshall 500
Noor Albi 500
Inayah 500
Idon Nera 500
Zafin Kai 500
Amatulmaleek 500
Ameenatou 500
Kalbim 500
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 82

A kwance fatma ta wuni sallah kawai take tada ita har yamma sai bayan magrib Maheer ya Kirata a waya akan ta shirya zasu fita.

Simple shiga tayi ta doguwan rigar abaya me tsada ba kwalliya a jikinta ta ziro takarmin original Versace ta sauko Shima ya fito suka fice ba kowa ma a gidan lokacin sai Dad Kuma yana Palonsa.

A LIMBAs ma Jannah fitan dare tayi da nata mijin Wanda basu dawoba sai dare sosai babu Wanda yasan dawowansu ma suka shige wanka kawai sukai suka kwanta bacci yana shigewa jikinta sosai kaman zai shiga cikinta tareda babynsa.

A kwanakin kowa dena zama yayi sun zama busy sbd Shirin tafiyan datake gaban kowa,

AZIZ LIMBA Greece zai tafi tareda matarsa wani aiki hakama zasu tafi da Nicky wadda Dr Nico ya roki akai Masa ita ta haihu acan.

Ammar ma Shirin tafiyarsa da Ummah yakeyi Umrah daga can zasu wuce India inda zaiga wani qwararen likita acan na tsawon wata biyu Wanda dashi kadai ne zai tafi Amma yanzu tareda Umman zasu tafi sbd tanason daga can zata turasa sauka port Harcourt ko yayane shi yaje yaga mahaifinsa Wanda bai taba nemansa ba sbd bai daukesa 'dansa ba.

Dad tinda yaji maganar tafiyar yaso joining nasu amma sbd yanason bawa ummah da Ammar din dama sbd alamu sun nuna Warakarsa taxo da yaddar Allah Dan haka sai ya kyalesu suyi tafiyar idan yaso daga India sai Ammar din ya wuce shikuma ya samu Umman acan su dawo.

Maheer ma tafiyarsa da tasa matar zuwa Poland ta gama shiryuwa Dan haka lokacin kawai suke jira.

Muhammad classes Dinsa na online sun karu sosai sbd yanda ya dage da Kuma yanda yake kokarin fuskantar Yayan Aysha Dr Nico idan yaje can ya saka ya sake zama busy Shima.

Ummah Bata dawo zaadens ba tana LIMBAs haryanzu sai ta dawo zata koma tukuna ga Kuma bikin fiddausi da Sayd da zaayi Wanda Fiddausinma ta koma garinsu tini sai an daura aure a daukota tukuna Dan haka kusan tafiyan kowa sai bayan daurin auren ne Wanda aketa hidimar biki.

Irin tarin dukiya da kudin da aka kashe a gurin lefen da akai na mutum hudu ya saka aka iringa yawo da dukiyar a media,

Lefe uku ne Wanda duka AZIZ LIMBA ne ya ware dukiyan gaske aka hada,

Na Jannah da Nicky Wanda yake tamkar na haihuwa sai na fiddausi da fatma Wanda yake na aurensu duk da itama Fatman da alama bugu daya ce Dan Kuwa tinda Maheer ya zare koyaushe yana manne da ita tin Bata saba ba harta saba koyaushe cikin zuba lafiyayyan soyayya da hot hot suke dan haka kafin Kace me ta debo ruwan dafa Kanta itama Dan haka koda aka fara bikin Fi su Ummah tini suka gano cikine a tattare da ita itama sabo.

Ba kunya Dad ya bugawa su modibbo ya sanar dasu albarkan da aka samu sbd farin cikinsa shikam jikokin da sai yanzu zai fara samu

Shima kawu jibo ba kunya ya ringa godewa Allah da akaiwa Fatman auren da yanzu Shima wannan cikin haka yanaji yana gani zasu qara rungumar 'dan gaban fatiha tinda dai yaran duk sun zare sai cikin haihuwa sukeyi kaman baa gaban iyayensu suke ba.

******An daura auren Sayd da fiddausi Wanda ya saka AZIZ LIMBA da mahaifiyarsa ziyartar gidan mahaifinsa da aka jima da mayarwa babban masallacin jumaar kauyen dama kauyukan zagayen Dan masallaci ne da aka Gina me girman gaske da solar datake haske kusan duka kauyen hakama tsarinsa kaman baa kauye ba Dan haka kaf nahiyar anan ake sallar idi da daurin auren kauyukan kusa duka kaf.

Anan aka daura auren Sayd da fiddausi sbd garin su fiddausin da Shima yake wannan bangaren.

Daurin auren yatara mutane sosai musamman zuwan manyan mutane kaman AZIZ LIMBA da jamaarsa sai zaadens da suma dukkaninsu suka halarta cikeda farin cikin kasancewansu ahali daya a yanzu.

Dangin mahaifin AZIZ LIMBA gabaki dayansu qwansu da kwarkwatansu haka suka Taho ganinsa sbd sunfi shekara nawa a garare suna nemansa da inda zasu gansa.

Basu samu ganinsa ba sbd ana gama daurin auren suka Kai ziyara kabarin Ummitah shi da Sayd da Zaadens wainda kowa jikinsa yayi sanyi suka bar kauyen.

Su Ummah aka bari dasu Mama sbd su taho da amarya Dan haka dangin baban nasa ummah kawai suka samu gani wadda ta musu alkhairin Daya ringa sakasu kuka suna rasa abin fada,

Tsohon Mijin Mama ma yazo dayaji ana rabon arziki Shi Kuma Jannah ce tayi Masa alkhairi sosai hakama ta qarawa dangin mahaifin AZIZ din.

Securities sosai aka bari a kauyen har lokacin tafiya da amaryan yayi suka baro kauyen a lafiyayyun motoci har cikin Capital inda suka hau jirgin Lagos suka wuce.

Ko da suka sauka 8 na dare Dan haka kowa a gajiye ya sauka.

Bangaren sayd da aka sauya komai zuwa sabo Mai dauke da babban lafiyayyan Palo da 2 bedrooms a ciki sai babban dining room dayake hade da kitchen duk da bawai girki zatai a cikinsa ba tinda akai main kitchen aka Kai amarya fiddausi.

Ummah jirginsu na sauka ita da fatma  drivern Zaadens ne yazo daukansu Dan haka tin daga airport suka rabu.

Jannah dake Jin kaman zata haihu sbd gajiya sallah kawai tayi ta kwanta bacci ya dauketa sai tsakiyar dare ta samu daman tashi cin abinci ta tada AZIZ din Wanda ya sauko gadon sanye da rigar bacci da bvlgari short qarami Daya manne jikinsa.

Basu fita ba kitchen din Palonsa suka tsaya ya hada mata iced coffee da shortbread cookies taci ta Koshi ya daukota suka dawo dakin suka kwanta tana lafewa jikinsa.

Washe gari haka suka tashi hankali kwance ba wani shirin duk da a Daren ranar jirginsu zai tashi subar qasar.

Bayan sallan magrib bada jimawa sosai ba motar Muhammad ta shigo harabar gidan yayi parking ya fito sanye da fararen Gucci wears fuskansa fresh ya sake samun kwanciyan hankali da nutsuwa ya nufo ciki.

Su Jammy ne suka tarbesa suna Masa barka da zuwa.

Mama ce tafito suka gaisa tana sake Masa gajiyan biki Shima yayi mata suka Dan tattauna sama sama kafin tace ya qarasa dakin Ayshan tana ciki.

Miqewa yayi ya qarasa yana sake Jin nutsuwan fuskantarta Dan haka yana isa kaitsaye yai sallama yaa bude dakin ya shiga.

Tana tsaye gaban mirro ta gama rufe handbag dinta data saka wayarta a ciki ne taji sallamarsa ta juyo ahankali jikinta na mutuwa ta kallesa tana Jin sanyin ganinsa kafin wucewata.

Zuba mata ido yayi kafin ya sauke ajiyan xuciya yana sake mata kyakkyawan murmushi me sanyi yana zaunawa yace

"Yaya jikinki?
Harkin gama Shirin tafiyan ne?

Zaunawa tayi tana kasa dauke idanuwanta daga murmushin dayake kan fuskansa kafin ta iya bude Baki tace

"Eh na gama shiryawa"

Numbernsa datake rubuce jikin card na zaadens Daya rubuta ya miqa mata yana cewa

"Idan Kun sauka kin nutsu kin huta pls ki kirani"

Karba tayi a Sanyaye tana cewa

"Kayi hakur.....

Girgiza mata kai yayi yana sake qayata fuskansa da murmushi me Kyau yace

"Ya wuce ki dena tada zancen Allah ya yafe mana gabaki daya,
Ki kula da kanki sosai idan kinje,
Kar kiyi tinanin komai sbd babyn"

Wani sanyin maganarsa taji ta dago tana kallansa har lokacin ta gyada kai tana kasa dena kallansa sbd tinanin babynta zai iya dauko sanyin halinsa da hakurinsa tareda Kyan fuskansa bayan kyan halinsa.

Shiru sukai kowannensu yana rasa abin fada shine ma yake Dan daurewa yana kokarin tambayarta yanda take jin babyn tana basa amsa a kunyace.

Anan yayi ishai har sai da time na tafiyansu airport yayi shine ya riqo handbag dinta bayan su Jammy sun gama fita da kayanta suka fito harabar gidan.

Saida kowa ya fito aka gama shirya komai har motocin an tayar kafin AZIZ LIMBA ya fito hannunsa riqe dana matarsa a gefensa dukkaninsu suna sanye da Ash Balenciaga wears da sneakers ita tayi rolling mayafi Mai laushi da handbag dinta qarama ta original LV bag shi Kuma p-cap ce a kansa haskensa na daukan ido.

Yana fitowa Kai gurin Mama sukaje sukai mata bankwana tayi musu addua kafin yayi bankwana da babynsa data maqale Masa kaman zata koma baby qarama suka fito suka shige mota.

Fi ma kaman kada ta rabu da Falaq Amma hakanan sukai bankwana suka shige mota take aka fice daga gidan dasu.

Aysha a lafiyayyar motarsa Muhammad ya dauketa daban suka jera zuwa airport.

Koda suka isa cikin saa Kuwa suka hade da Maheer da fatma Wanda Suma a Daren jirginsu zai tashi su Ummah da Ammar Kuma sai washe gari.

Su Jannah ne suka fara dagawa kafin su Maheer daga baya Dan haka kowa sabon babin rayuwa ta fara bude Masa daga nan.

*******Sun sauka washe gari Dan haka tin daga airport Dr Nico ne ya tarbesu Kuma yayi farin cikin ganin kanwarsa sosai da babynta dayake cikin koshin lafiya Dan haka tin daga nan suka rabu ya tafi da ita.

Su Kuwa Kai tsaye masaukinsu suka nufa sbd Sam baa gida zasu sauka ba sbd gidan yana buqatan a sauya komai Tinda matan gidan zasu tare ne yanzu a matsayin amare.

Wani luxurious Tower hotel suka sauka Wanda dakin AZIZ din yake karshe na Sayd na Fi Kuma yana kusa dashi Dan haka babu tazara a tsakaninsu sbd yanason Sayd yaji dadin rayuwan aurensa da sabuwar macensa.

*****Baccin gajiya sosai sukai babu abinda yake tashinsu sai sallah wadda sunayi suke komawa bacci har sai yamma lis gajiya kowa ya sakesa tukuna sukai wanka suka fito balcony din dakinsu inda wata ni'imtacciyar iska take kada musu me sanyi da nutsuwa.

Abinci ya aka kawo musu Wanda sukai order aka Jeresa cike da table din dayake balcony din gaban qaramar swimming pool din dake daukan ido sbd tsaftar ruwan.

Wayoyi dukkaninsu sukeyi a natse hankali kwance har sai da sukai magrib tukuna suka zauna cin abincin tana kan qafafunsa daga ita sai wata fingilalliyar rigar da kusan duk cinyiyinta a fili Dan kadan ma da a sauka daga cikinta.

Shima short ne kawai a jikinsa Dan haka akan kafafunsa ta fara cin abincin bayan ta kashe wayarta gabaki daya.

Abincin yaci Shima yana gamawa sallar ishai sukai suka dawo ya zauna sai a lokacin ya zuba hot coffee dinsa me zafi sosai zai Sha.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 83
SECOND TO THE LAST.......

Qarasowa tayi itama ta zauna kan kafafunsa tana Daukan cup din coffee dinsa takai bakinta Kai tsaye Tasha batareda sanin yanada zafi sosai ba take ta saki qara tana ajiye cup din da sauri tana miqewa bakinta na mata wata irin azaba sbd Da yawa tasha.

Kamota yayi cikeda kulawa yana janyota jikinsa yafara hura mata bakin yana shafawa ahankali yana cewa

"Sorry,sorry Mrs LIMBA"

Hawaye idanuwanta suka ciko dashi tana cewa

"Meyasa baka fadamun yanada zafi sosai ba ni wlh na kone ma"

Sake shafa bakin yayi yana hura mata iskan bakinsa ahankali yana cewa

"Bansan zakisha bane Sorry baby"

Mita ta sake bude baki tanayi tanajin masifa na cinta wadda duk kwanakin haka kawai komai masifa take Masa.

Ganin tanata mita yana rarrashinta amma ta kasa denawa ya sakasa kama fuskanta ahankali yana Dora bakinsa kan nata ta fiddo harshensa yafara lashe lips dinta yana hurawa ahankali yana cewa ya dena??

Girgiza Kai tayi ya kama lips din ya fara tsotsa ahankali yana lumshe idanuwansa ya kalleta yace yanzu fa??

Girgiza Kai tayi tana kallansa.

Cikin bakinta ya saka harshensa ahankali yana laso kowane saqo na cikin bakin kafin ya fara tsotsa ahankali yana dauketa sama ahankali ya zauna da ita akan inda suka tashi tana Kan jikinsa yana ci gaba da tsotsanta tsawon mintina kafin ya zare bakinsa ya Kalli fuskanta itama shi ta bude idanuwan tana kalla ya bude Baki da wani mayen sautin rikita mata tinani yace

"Ya ya??

Da Kanta ta kama fuskansa ahankali tana Kai bakinta lips dinsu suka gogi juna ta sakar Masa numfashi me dumin Daya saka idanuwansa lumshewa suna sauyawa ta bude Baki da sautin daya jisa har cikin jijiyan kansa tace

"Idan nace da saura fa??

Hannunsa ya ziro ta qasan rigarta datake kama da babu ya shafi cinyarta kafin ya shafi cibiyarta data sakata lumshe ido yayi sama da hannunsa yana zare rigar ta fice gabaki daya daga jikinta ya jefar gefe yana kallan kirjinta da suke cikin Transparent underwired bra din da babu abinda baya gani a cikinsu..

Lips dinsa ya fidda harshe ahankali yayiwa wata lasa yana shafar saman bra din kafin ya saka hannunsa bayanta ya balleta ahankali yana jifa da ita gefe yakai bakinsa ya lashi gefen fuskanta yana fidda numfashi me sauti ya cika hannuwansa duka biyun da abinda yake sake kashesa a kirjinta yafara kissing bakinta passionately yana sake rikita jikinta da hannuwansa.

Kissing dinsa takeyi itama tana sake rikita lissafinsa daya gama lalacewa tana shafa kirjinsa zuwa cikinsa da mararsa take ya ringa fidda numfashi masu karfi suna rikita gurin da zazafafan numfashi da Nishin da jinsa kawai zai tada tsikar jikin mutum.

Sbd yanayi na cikinta daya fara tsufa ya saka salonsu sauyawa da dama Dan haka a inda suke din tana zaune kan kafafunsa ya gyara mata zama yana ware kafafunta dakyau akansa ya fara Bata rayuwan data kusan saka naquda kamata cikin wani irin lafiyayyar soyayya da iya binta ahankali harsuka samu nutsuwansu suka kwanta a gurin tana jikinsa suna Jin gabaki daya rayuwarsu na gama daidaita a yanzu.

A daidai wannan lokacin Says da Fi suna nasu dakin wadda Saida suka gama komai cin abinci sukai sallan ishai da nafila tukuna sukai Shirin bacci tana kokarin barin gaban mirror sanye da kayan baccinta riga da wando masu kyau tana fidda kamshi me sanyi ya kasa dauke idanuwansa daga Kanta yanajin hakurinsa ma gabaki daya ya gama qarawa sbd ko hannunta bai kama ba tin ranar da aka kawo Masa ita sbd zazzabin datake Dan kwana dashi kullum na gajiya da abubuwan da aka ringa bata a gida tana sha da ci shiyasa ya barta ta warke.

Tasowa yayi yana qarasowa bayanta ahankali ya rungumota ta bayan yana sauke ajiyan xuciya me sanyi da tsafta sbd son dayake mata a xuciyansa kaman bazai iya riqe kansa ba ayau din kwata kwata Dan haka ya sake qanqameta ahankali yana zira kansa wuyanta yana Jan kamshinta da duk ta sauya Masa.

Shiru tayi gabanta na Dan faduwa ta Dan kama hannunsa zata zame jikinta ya sake qanqameta yana girgiza mata kai sbd shi kwata kwata ma jin yake yana neman fita hayyacinsa tin baiyi mata komaiba.

Juyo da ita yayi suna fuskantar juna ya Kafeta da Kallo yana yiwa Allah godiyan Daya nuna Masa ya mallaketa dan gap yake da rasa kansa akanta Shima.

Jin kallan dayake mata ya sakata dagowa ta kallesa zatai magana ya girgiza mata kai yana cewa

"Don't say a word pls...ya Dora bakinsa akan nata yana fara kissing nata ahankali ahankali kafin yaji komai na loosing take yafara mata zazzafan kiss yana hadeta da madubi yana lumshe idanuwansa hannuwansa na shafa wuyanta dayake son gangarawa ga kirjinta dasuke a cike Kuma a kyam.

Kasancewan tanada wayewanta ya saka batai kokarin hanasa kantaba sedai fargaban datake cinta da ganin irin karfinsa dayake bayyana Dan daukanta yaji cak ya kwantar a gadonsu yana zare rigar jikinta ya jefar Shima yana karewa bridal bra din dake kirjinta Kallo yana hadiye wasu shegun yawun da Saida maqoshinsa yayi kukan wucewansu take ya juyata baya ya zare rigar ya shafi curve dinta tukuna yajefar yana kama na zahirin yana Jin kaman zai zuba ihun abinda yakeji.

Tsananta tsoron fiddausi yayi Jin yanda yake zafafa a cikin yanayinsa Wanda yake zuba mata zafafan romance din da jikinta take yayi dumi tafara rawar jikin Jinsa da girmansa kafin tayi wani yunqurin roko ko zamewa tini ya gyarata yana kama hanyar maidata macensa batasan lokacinda ta sake rikicewa ba da tsoro da zafin datakeji shikuma take fara hidimarsa cikin zaucewa yana fidda numfashi da Nishi masu karfi yana ambatar sunanta kama zai zare sbd abinda yake ji na yawo a kansa da kunnuwansa.

Sbd Jin kansa cikin sabuwar rayuwan daya manta dadinta zarewa yayi ya kasa tausaya Mata so biyu yana aikace ta Wanda dole da safe Saida aka Dan Nemo dr ta dubata sbd zazzabi me karfin data tashi dashi na rashin sabon abinda ya sameta.

Ita Kanta Jannah da suka kwana suna shiriritansu da kasala ta tashi Dan haka daga su harsu Sayd din Saida suka kwana biyu basuga juna ba duk da suna guri daya.

Sai da sukai sati biyu cif basu fita koina ba babu abinda kowannensu yakeyi sai hutawa da iyalinsa hakama acan Maheer Shima hutawa yakeyi da tasa matar kafin ya fara fita abinda ya kawosa.

AZIZ ma ranar da suka fara fita asibiti sukaje aka Duba Masa babynsa da matarsa kafin suka wuce wani gurin daban dagashi sai ita.

Fiddausi jinya takeyi kwana biyu sbd wutar da Sayd ya bude hutawansa kawai yakeyi Saida Tasha wuyan kwana biyu tukun ta saba itama tafara gogewa tana basa hadin Kai yanda ya kamata ai Kuwa Hakan ya qarasa kashesa akanta.

Sati uku kafin suka hadu da Fi suna fita nasu yawon shan iskan harma da Aysha da suke zuwa dauka sbd ta sake sakewa Dan ita tana kusan gap da haihuwa sbd cikin ya tsufa sosai ga Muhammad dinta Shima ya dage sosai yake kiranta yana Jin lafiyanta Dana babyn Wanda ganin hakan da yanda mazajen su Jannah din ke kulawa dasu suna soyewansu hankali kwance ya sakata fara shaawan nata auren da Muhammad din Wanda baya Nigeria Shima yana Malaysia gurin karatunsa daya fara karfi da yaji wanda Ammar ya gama samar Masa da komai Dan da gaske yakeso rayuwan Muhammad din ta inganta.

*******Watansu biyu a qasar nakuda ta tasowa Nicky Wanda ta saka hankalin Jannah tashi ganin halinda Ayshan ta shiga Dan haka duk da shiga damuwa da fargaba Saida AZIZ din ya rungumeta jikinsa yana kwantar mata da hankali suna jiran haihuwan duka suna asibiti.

Acan India ma su Ummah da Ammar sun shiga adduar Allah ya saukar da Ayshan lafiya.

Su Dad ma adduar sukeyi hakama su modibbo da aka sanarwa,

Maheer da fatma ma daketa laulayinta basu dawo ba Dan haka daga can ana haihuwa Greece din suka wuto.

Aysha Nicky ta haifi baby girl dinta Mai Kyau da lafiya sbd kamannin mahaifinta data dauko hasken Kuma da kusan na Nicky dinne duk da Shima Muhammad din fari ne amma kasancewan Nicky tafisa hasken kana gani kasan na Mamanta ne.

Farin ciki da murna aka ringa yi musamman Muhammad din wanda baida daman tahowa duk yanda yaso sbd karatun dayake riqe dashi babu dama ko kadan.

Anturo Masa 'yarsa ya gani yayi farin ciki yayi sujjada ya godewa Allah ya kuma ji har cikin ransa yana tsananin kaunarta da Mamanta.

Nicky tayi video call dashi yagansu itada babyn ya Kuma nuna musu kulawansa da tsananin son kasancewa tareda su sedai ba dama.

Cikin kulawa Nicky din tace Karya damu suna jiransa har lokacin da zai samu dama.

Gabaki daya duka families din mantawa sukai da yanda aka samu babyn Dan haka farin ciki da kaunarta sukeyi abinsu Wanda Ammar daya iso bayan isowansu Maheer Muhammad ya basa daman sakawa babyn suna.

KHADIJATUL KUBRA Ammar ya sakawa babyn wato sunan MIMI Kuma da sunan MIMIn zasu Kirata,

Aikuwa takwarar da akaiwa Mimi ya saka kaunar yarinyar sake shigar familyn zaadens din illai Kuwa ana sati biyu cif da haihuwa aka daura auren AYSHAN da MUHAMMAD GARBA Wanda daga amaryar har angon basa guri daya Zaune.

Jannah tsananin kaunar datakewa babyn kaman kada su rabu sbd Nigeria da Ayshan zata koma gurin Mama ta qarasa jegonta acan sbd suna yin 3 month zasu wuce Malaysia gurin Daddyn Mimin Wanda zasu zauna acan kafin gama karatunsa tukuna su dawo Nigeria kwata kwata.

Watan Mimi Daya cif da haihuwa suka dawo Nigeria wannan Karan hadda Dr Nico Daya kawo kanwarsa da kansa kafin zai koma daga baya.

Ummah sbd haihuwan Jannah da edd yayi zamanta tai anan shi Kuma Ammar ya wuce gurin mahaifinsa da yayiwa Ummah alkwarin zuwa Kuma abin farin ciki Dad ne da kansa ya isa port Harcourt din suka hade yakai Ammar din da hannunsa Wanda a ranar d suka tafi farin ciki da Dana sani tareda nadamar abinda baban yayiwa Ammar yana kwance yana jinya tsawon shekaru hudu yayi nemansa harya gaji babu labarin zaadens.

Ammar ya yafe Masa duk da babu wani kusanci ko kauna me karfi dayake ji akan baban sbd ya tashi da baqin cikin abinda yayiwa mahaifiyarsa a Daren gap da Asuba Allah ya karbi ran baban Wanda Kuma baida da namiji ko daya bayan Ammar din Dan haka washe gari dasu akai janazah.

Fasa tafiya Dad yayi Saleem ma ya iso zaman gaisuwan harma dasu modibbo duka sun taho da baba Al'hassan sunxo har port Harcourt din gaisuwa.

Zaadens din basu tafi ba Saida akai sati biyu cif da rasuwar suka tattara suka tafi.

Gadon dukiyar da aka bawa Ammar din gabaki dayanta sadaka yayi da ita tareda bude masallatai sbd ladan tajewa iyayen nasa sauran kudin Kuma ya dauko kaso me tsoka ya bawa muhammd yace a juyawa Mimi dukiyar sbd idan ya mutu a musulunce batada gadonsa Dan haka a juya mata.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 84
Last chapter

*******Rasuwan baban Ammar da sati uku Jannah ta haifi lafiyayyan baby boy dinta da babu inda ya daukota sak Daddynsa Dan haka ya tabbata baby limba din da AZIZ din da yarsa Falaq suke fada.

Farin cikin LIMBAs da Zaadens Kam a yanzu ya wuce na koyaushe duk da Tasha wahala sosai a gurin haihuwan danma AZIZ din yana tareda ita yana Bata wata irin kulawa kaman zai soke career din likitocin yakeji sbd sun kasa rage mata azabar haka dai ya ringa tayata wahalan har Allah yasa ta haihu suma Doctors din suka huta.

Kulawa da Ummah da Fi dashi kansa uban gayyar suke Bata itada babyn ya saka zaadens daurewa suka qi zuwa duk da kaman su zo su qwace Jannah din sukeji.

ABDULAZIZ AZIZ LIMBA shine sunan da AZIZ LIMBA din ya sakawa 'dansa Kai tsaye sbd Yana son 'dansa ya zama AZIZ LIMBA ubansa.

Watansu Daya suma suka tattaro suka dawo lokacin fiddausi ma anata fama da laulayi.

Suna dawowa gida Ummah ta wuce da ita bayan mama ta rarrashesa yabarsu tayi zaman haihuwanta a gidansu kenan.

********Tinda suka dawo ayyuka sukai Masa yawa Dan haka shi da Sayd suka sake tafiya sbd ma ya basu Daman zaman haihuwan gida hankali kwance Dan idan yana Nan bazai iyaba koyaushe yana zaadens.

Dad da dukkanin zaadens Jin AZIZ LIMBA junior sukeyi kaman Rai sbd duka soyayyar Jannah ta koma kansa sai gasu AZIZ LIMBA junior a bakinsu kaman salati tinda babu yanda suka iya ga Ummah a gidan rayuwansu Takoma kaman baya ahalin ya rayu a cikin sabuwar rayuwa me dadi da nutsuwa.

Ummah data San abinda take gani a gurin Falaq bayan tafiyan da akai aka barsu Saleem kusan koyaushe yana gidan yarinyar ta gama gigitasa ya gama mutuwa akanta dole ummah ta fara neman yanda zatai a tinkari AZIZ da zancen aurensu tinda exams take rubutawa yanzu ta gama secondary gwara ayi mata aure.

Baba Al'hassan tafara sanarwa Shima take yayi Naam da Hakan ta sanar d ummah saiga zancen har gaban Dad da kowa Nan kowa ya rasa ta inda zata fara tinkarar AZIZ LIMBA da zancen auren Falaq Dan Sanin kowa AZIZ LIMBA din bazai taba yadda ba yanzu.

Saleem Kuwa ganin anriga ansani ya kasa hakura ya daga hankalin Dad da ummah akan a taimaki rayuwansa awa AZIZ din magana ko ba yanzu zai mata aure ba shi a daura auren zai jira harta gama karatunta.

Da wannan su Dad da baba Al'hassan da alh saad harma da tsohon aminin mahaifinsa aka kira alh Aliyu duk aka Tara wainda zasu iya tinkararsa tukuna aka tinkaresa da zancen yana dawowa.

Shiru yayi yana dagowa ya kallesu gabaki dayansu yana Jin wani irin dumm sbd anzo Masa da maganar da bazata taba yiyuwa bane Dan shi baimasan Falaq din tasan menene soyayya ba sbd haryanzu kallan yar babynsa yake Mata.

Girman mutanen dake gabansa ne da duk aka Tara Masa ya sakasa kasa cewa komai sbd bazai iya amincewa ba hakama bazai iya cewa bazai musu abinda suka taru suka rokesaba.

Falaq din ya kira yana mata kallan mamakin Daya kasa sakinsa wai soyayya takeyi da saleem Daya tsananin girmanta.

A natse ya kalleta ya tambayeta ta kasa musawa tace eh.

Sake tambayanta yayi ta yadda a daura mata auren da Saleem still tace aa ita yanda yace haka zatayi.

Murmushin karfin hali yayi yace ta tafi kawai.

Sbd zuciyarsa data gama sakewa da kasa iya hanata abinda takeso da Kuma duba girman su baba Al'hassan din da matsayin ubanta da aka basa bayan ga ubanta Daya haifeta a zaune dashi ake tausarsa yasakasa amincewa.

Dad na ganin ya amince ya fidda sadakin dasuka zo dashi akai Komai cikin Sunnah take aka daura aurensu Amma da sharadin da AZIZ din ya bayar karatu zatai sai tagama zaayi biki ta tare.

Hakan kowa ya yadda dashi take akai karkar arziki cikin farin ciki.

Saleem a ranar Jin yayi kaman zai taka kan jariri sbd murna da farin cikin cikar Burinsa.

AZIZ daya shirya daukan matakin yanke haduwan Saleem din da Falaq din sbd da gaske yake bayason kowace sabuwar rayuwan aure ga 'yarsa saita gama karatu Dan haka take yasa sayd ya fara Shirin tafiyarta da Aysha Nicky tayi karatunta acan a gidansu Muhammad din batareda ya sanar da kowa kasar da zata karatun ba musamman Saleem din.

*******Saida Mimi tayi wata biyar cikin na shida tukuna suka bar qasar zuwa Malaysia tareda Falaq wadda tinda aka daura mata aure Bata sake haduwa da Saleem Zad ba a zahiran.

Jannah ma suna barin kasar ta koma gidanta tareda AZIZ LIMBA junior cikeda lafiyayyan gyaran data samu daga ummanta hakama tareda dukiyan aure me yawan gaske.

Jannah na komawa fatma ma Takoma gida haihuwa bayan Maheer ya yadda dakyar bayan su modibbo sun roka sosai Dan haka yace idan zata haihu zaa aika mata nurses.

Mama Jannah na dawowa tafiya tayi itama zuwa kauye ganin gida sbd AZIZ din daya koma mata sabon mutum gabaki daya ya zare a cikin gidan kaman bashine Mai kamewa ba idan ya fita ba fuska.

******Jirginsu Aysha Nicky na sauka Malaysia,Mimi's Dad kaman yanda Nicky ke fada shine yazo da kansa airport ya tarbesu cikeda tsananin kauna da soyayyar data ginu a xukatansu batareda sun saniba sbd 'yarsu.

Ya sauya sosai ya zama Wani sabon mutum daban Wanda kana kallansa kasan Allah ya masa halittar Kyau da nutsuwa.

Ita Kanta Nicky ta sauya sosai tayi jikinta me Kyau haskenta ya qaru sbd ta koma yar gayunta ta baya tayi fresh ga babynta me Kyau kana gani kasan yar turawa ce ga hutu da daulan d suke ciki.

Kallo Daya muhammd din yayiwa Ayshan yaji sanyi da nutsuwa na cike zuciyarsa data matsu da zuwansu.

Itama kallansa tayi ta sauke ajiyan xuciya tana Jin daga karshe dai sun iso hannun Wanda zasuyi rayuwan farin ciki kaman kowa itada Mimi.

Karban yarsa yayi ya rungumeta jikinsa tsam yana kissing fuskanta data daukosa sak yana mata addua.

Falaq ya kalla da kulawa ya mata barka da sauka kafin ya tsayar da idanuwansa akan Aysha data dauke Kai qasa a natse da kulawa ya miqa mata hannunsa daya yana cewa

"Barka da sauka Mimi's Mum"

Murmushi me sanyi ta sake tana kama hannunsa ahankali da nata hannun suka sauke ajiyan xuciya a tare yana nufa mota dasu hannunsa riqe dana matarsa daya matsu ta iso garesa sbd yanda yake jinta a zuciyarsa yanzu da Kuma gama kunce Masa lissafi datai gabaki daya a videocalls da sukeyi da bayyanarda nonuwanta gurin baya Mimi.

Mota suka shiga suka isa gidansa Mai Kyau da tsari nanny din da Dr Nico yariga ya samarwa Mimi a ranar itama ta iso tana gidan tana jiran su Dan haka Falaq aka Kai babban lafiyayyan bedroom dinta dayake palon farko sai bedroom din Ayshan da nasa Master bedroom din dayake Dan kurya kadan da qaramar Palo me Kyau,

Komai na gidan me Kyau da tsari da wayewa ne sbd Dr Nico da kansa yazo suka kama gidan sbd yasan tsarin kanwarsa Muhammad ya bada kudinsa sosai akai Komai sbd bayason Dr Nico ya taimaka Masa sosai yanason ya riqe matarsa da yarsa da kansa.

Dr Nico yayi mugun yabawa da Muhammad din sbd halayensa masu kyau da nutsuwa Dan haka yaga inda kanwarsa zatai rayuwa da Kuma mijin da zatai rayuwan dashi Shima ya bawa muhammd dukiya me yawa yace a hada duka a juyawa Mimi yabar Malaysia ya koma.

Tsarin gidan ya saka zuciyar Aysha sake yin fes sbd zasu rayu a cikin inda zasu ji dadin rayuwansu da soyayya.

Hutawa sukai sai dare suka fito da wankansu ya fita dasu cin abincin sikaci suka dawo suna sallan ishai kowa ya shige sai baccin gajiya.

Washe gari da kansa shi kadai yaje shopping na abubuwan buqatan Mimi da sauran abubuwan komai da zaa buqata a gidan yana dawowa Shima ya karbi Mimi ya shige dakinsa da ita sukai baccinsu sai yamma sosai suka fito ta tashi lokacin.

Sake mata wanka da kaya akai Shima Wonkan yayi ya fito a dining sukaci abinci gabaki dayansu Wanda nanny ce tayi girkin.

Suna gamawa fita yayi sai dare after 9 ya dawo lokacin Falaq ta shige tini hakama nanny babu kowa.

Rufe koina yayi ya kashe komai yana isa dakinsa yayi wanka haryayi Shirin bacci yaji kukan Mimi ya fito y isa dakin Ayshan ya bude Yana shiga idanuwansa akansu.

Sunyi Shirin bacci Mimi tafara rigima.

Karbanta yayi yana mata yar wasa ba Bata lokaci Kuwa bacci ya sake dauketa.

Tafiya yayi da ita dakinsa yana cewa Ayshan ta Kai Masa gadonta can.

Biyosa tai da gadon tana shiga dakin sanyin AC da kamshinsa me sanyi kaman shi suka shiga hancinta ta qaraso tana gyara gadon shikuma ya kwantar da mimin yana mata addua.

Yana gamawa ya juyo yana kallanta tana tsaye itama tana kallansa cikeda Burgewa sbd yanda yake kaunar yarsa.

Kayan baccin dayake jikinta ya kalla wata yar qaramar riga ce wadda ba transparent ba Amma batada tsayi.

Cikin sanyi tace

"Goodnight" tana juyawa zata fice ya kamo hannunta yana Dan takowa ahankali ya iso bayanta gap ya Dan shaki kamshin wata fitinanniyar khumrah datakeyi wadda take cikin kayan Mama data siya mata na gyaran jiki.

Sake shakar kamshin yayi yana Dan sake hade bayanta da kirjinsa ya zagayeta da hannuwansa ya sauke numfashi me sanyi ya sake saukewa yana sake shigar da ita jikinsa yace

"Ina zaki tafi ki barni da Mimi bayan zata iya tashi neman Mum dinta"

Kasa juyowa tayi ta bude Baki tanajin yanda yake sauke mata numfashi me dumi a fatar wuyanta tace

"Idan ta tashi ai bana nesa"

Fatar wuyanta da tsikar gurin ta tashi sbd numfashinsa dayake sauka yakai bakinsa ahankali yayi kissing wuyan yana cewa

"If baki yiwa Mimi nisa ba Mimi's Dad fa??

Sai a Lokacin ta Dan juyo Kanta kadan ta kallesa tana kokarin janyewa daga kisses din dayake sauke mata wuya sbd zazzabin dasuke neman sakar mata.

Matseta yayi jikinsa yana birkitota suka fuskanci juna yana sake Jin kamshinta har cikin kwanyarsa.

Idanuwansa suka fara nuna mata halinda yake ciki take taji Dan tsoronsa sbd Tina karfinsa.

Zamewa take kokarin yi ba zato sbd bai iya kwana kwana ba ya bude baki yana mata kallan abinda yakeji yace

"I love you Nana Aysha,
I love you Mimi's Mum"

Cak ta tsaya tana kasa janyewa daga garesa Kuma sbd gabaki daya zuciyarta dataji tayi mata wani irin fayau da fresh.

Kallan cikin idanuwansa yayi ya sake maimaita mata zancen Wanda ya sakata fasa janyewa ta shige jikinsa ahankali tana rumgumesa.

Shima rungumeta yayi yana jero mata gaskiyan abinda yake ransa gameda ita Dan yarsa.

Gabaki daya kashe mata jiki yayi da kalamansa da gaskiyansa Dan haka ta bude Baki ta fara Masa godiya da nuna kaunarsu garesa itada yarta.

Janta yayi sukai alwala suka fito sukai sallah yayi musu addua da Kuma duk abinda zasu Haifa kafin ya zare mata doguwan rigar sallar yana daukanta cak ya nufi lafiyayyan gadonsa da ita yana Jin tsananin buqatan kasancewa da ita.

Laushi da qamshin dayake tashi a fatar yake sake ruda Tinaninsa Dan haka rigarta kawai fara zarewa ya yar yana zubawa plunge bra dinta idanuwa sbd cikakkun kirjinta da suke ciki suna daukan idanuwansa.

Rasa ta inda zai fara yayi sbd shauqinta da yai mugun Masa yawa Dan haka itace ta kamo fuskansa ahankali tana Dora bakinta akan nasa tafara kissing nasa cikin sanyi Wanda take ya karba kissing din yana mata mayen tsotsa yana mannota kirjinsa idanuwansa na wani rufewa.

Kissing din da sukewa juna yana mata wata irin shafa ya dagota jikinsa gabaki daya yana sake manne bakinsu kaman zai hadiyeta gabaki dayanta.

Bra dinta ya dago yana yiwa Wata mayyar Kallo ya rasa t inda zai zareta daga jikinta Dan haka ya balleta gabaki daya ta gaba yana Rabata biyu ya jefar yana qarasa kwantar da ita flat akan gadon bayan ya jefar da nasa kayan baccin kasa yana fara kokarin kasancewa da ita kaman a Karan farko yakeji sbd ya goge wancan kaddarar tasu a ransa.

A yanda suka kasance da juna cikin Daren ya tabbatar mata da Muhammad din da gaske yake Sonta Dan haka ta fara sake jikinta sosai dashi a cikin kwana biyu suka mannewa juna amarci kawai sukeci ba sauki,soyayya, kwanciyan hankali da nutsuwa dajuna na sake wanzuwa a tsakaninsu.

**********Watansu uku da zuwa Falaq ta fara zuwa makaranta Shima Muhammad karatunsa yakeyi sosai basuda matsala sai farin ciki da kwanciyan hankali.

Fatma da fiddausi duka sun haihu sedai fatma ta riga haihuwa harma ta dawo ta haifi Dzad junior Wanda Shima suke tsananin ji dashi,

Fi Kuwa UMMITAH ta haifa da haka a LIMBAs an sake samun Hamma ABDULAZIZ da UMMITAH wadda AZIZ LIMBA ke ji Da ita itama sbd kasancewanta takwarar ummitansa.

Jannah wadda hankalinta yake Dan tashe a yau din yar damuwa ta shiga har dare Bata wani walwala,

Wanka tai tayi Shirin bacci cikin wata qaramar riga tana kokarin isa gado ya fito daure da towel daga wanka yana isowa gurinta ya rungumeta yana shafa mata ruwan wankan jikinsa yace

"Meya samu Matan AZIZ LIMBA ne??

Jin tayi haushin komai yana rufeta ta turesa kadan tana cewa

"Duk Kaine ka sake Jamun zaace na ake ciki bayan AZIZ junior bai gama girma ba.......

"Wat" ya fada yana kallanta da wani irin mara misalin farin ciki yana dauketa sama gabaki daya kafin ya sauketa ya zira bakinsa kawai cikin nata yana Bata wata irin crazy tsotsa yana saka hannunta daya ya zare towel dinsa dashi ya yar a gurin yana sama da ita bakinsa na yaga rigar baccinta ya wurgar yana sake bude bakinsa gaba daya yana hadesu da nata yana mata kissing din dabai taba yi Mata ba na asalin maita.

A daidai wannan lokacin Falaq data fita tin safe school Bata dawo da wuri ba sai yamma ko data dawo Yaya Muhammad da antynta basa gidan sun fita shaqatawansu da suka saba suma koyaushe yake free.

Bacci tai ta huta sosai sai magrib ta tashi tayi wanka tayi Sallah ta saka doguwan riga mara hannu har qasa ba komai akanta ta fito taje kitchen tana fira da Nanny Anna tanashan cornflakes tana gamawa Tasha fruit tana sake fira da Anna din.

Door bell dinsu ne yayi Kara dan haka Anna ce taje dubawa.

Munti Daya ta dawo ta Kalli Falaq din tace

"Kinada baqo"

Da mamaki Falaq ta kalleta kafin ta fito tana kokarin isa dakinta ta dauko abin rufe jikinta kafin ta isa kofar tana fitowa palon taji muryansa me shegen dadi da Bada nutsuwa a kunnuwanta yace

"Hi Mrs Saleem"

Cak ta tsaya tareda juyowa da karfi zuciyarta na wani irin harbawa ta kallesa ta Kuma kallansa taga shi dinne da wani irin gudu da farin cikin gaske ta iso gurinsa tana isowa ya dauketa sama yana qanqameta jikinsa yana Jin yau rayuwarsa data firgice tana haduwa guri daya sbd daga karshe dai ya samu ganin abincin ruhinsa matarsa Falaq AZIZ wadda mahaifinta baisan ya samu sanin inda take ba haryaxo.

Kuka ta fasa Masa kawai ita tana sake shigewa jikinsa yana sake kankameta kafin ya dago ya Kalli fuskanta ya sake qanqameta ya sake dago fuskanta sai kawai ya hade bakinsa da nata ahankali for the first time a rayuwansu su duka suna fara kiss.

Kissing dinta yakeyi cikin sanyi kaman zai hadiyeta tsawon mintina kafin ya saketa yana sauketa qasa ahankali.

Hawayenta y fara share mata yana cewa

"I love you Falaq Aziz"

Hawayen ta sake gangaro Masa tana rasa abin fada sbd ba qaramin kewansa tai ba tsawon watannin masu yawa.

Jacket din jikinsa ya zare yana barin shirt din ciki ya saka mata ahankali tareda hulan dayake kansa kaman qaramin yaro saka mata ya kama hannunta zai fice da ita tayi saurin tsayawa tana kallansa tace

"Ina zamu?

Kallanta yayi Sonta na neman Masa illa ya janyota jikinsa ahankali yayi kissing hancinta ya kalleta yace

"Karki manta ke matan saleem Zad ce ayanzu??

Sai a lokacin ta sake kyakkyawan murmushi tana zare hannunsa dayake shafa fuskanta tace

"Idan Daddyna yasan kazo inda nake harma ka tabani ko tafiya Dani wani gurin zai rataye ka"

Wani mayen murmushi ne ya kubce Masa ya janyota jikinsa da dan karfi suka manne sosai ya Kalli idanuwanta masu kyau dake sake kashesa a kasalance yace

"Idanma ban tafi dake ba mutuwan zanyi so gwara na tafi daken daga bayan ya rataye ni shekana at least bazan mutu ban bar little me ba"... Ya qarasa zancen yana sake hade bakinsa da nata tareda daukanta cak ya fice da ita zuwa motarsa ya sakata ya zagaya ya shige yabar gidan gabaki daya da ita yana sarqe hannunsa cikin nata sbd sedai Daddyn nata ya ratayesa dagaba baya Amma zuciyarsa ta kasa hakura da matarsa.
#MAMUH
07019691719
ALHMDLLH ALHMDLLH ALHMDLLH

BANDA ABIN FADA BAYAN ALLAH YA SAKAWA MABIYA LABARIN KALBIM DA MAFIFICIN ALKHAIRINSA SBD NUNA KAUNARSU GARENI DA KUMA LABARAINA,

AKWAI KURA KURAI NA SANI,
AKWAI ABUBUWAN DA AKA MANTA BAA SAKABA NA SANI,
HAKAMA AKWAI WAINDA ZASUGA ANYI BA DAIDAIBA,
AKWAI WAINDA ZASUGA GAZAWATA

TO DUKA INA BAWA KOWA HAKURI AKAN DUK ADINDA YAKE BA DAIDAIBA,

ALLAH KA YAFE KUSKURE DA BA DAIDAIBA DAYAKE CIKI
ALLAH KUMA YA BAMU IKON GYARA INDA BA DAIDAI DINBA,

DAN ALLAH KADA KUCE KOMAI BAYAN KHAIRAN SBD ANRIGA DAI ANGAMA KUMA NA ROKI AFUWAN INDA AKAI BA DAIDAIBA DAN HAKA KUYI FATAN ALLAH YA HADAMU A NEXT BOOK WANDA INSHALLAH ZAI ZO MUKU BADA JIMAWA BA.

NAGODE ALLAH YA BIYA KOWA

MASU NEMAN SABUWAN NUMBER NA NA RASA WANCAN LAYIN NE SBD WAYAR DATA FADI NA KASA WELCOME BACK SBD MATSALAR REGISTER AMMA INSHALLAH ZANYI KOKARIN NAGA NA DAWO DA LAYIN SO KAFIN NAN INA AMFANI DA AIRTEL DINA SHINE LAYINA A YANXU.
07019691719
MAMUHGEE

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.