Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 1 of 5
[29/03, 8:04 am] Maman shaheedðŸ˜ðŸ¥°: *RAI DA BURI*
Episode 1
By Maman shaheed
Paid book ne,akan 700₦ mai son karantawa cikin Lumana Akwai a Arewapen sanan zan dinga turawa a paid group ga waɗan da sukayi payment.
Free pages basu da yawa, guda 5 ne....
Ga Account É—in da za'a, biya 👇ðŸ¼
3108794095
Fatima Abubakar
First bank
Sadaidar biya
👇ðŸ¼
08134624555
"OK, kasan bana son asami akasi Ko? duk abin da ya dace kayi, shi ɗin nace maka kamar uba yake a wajena, kuma duk abin da nake musu bani da wata Manu fa face ta Alkhairi da ganin suna buƙatar Taimakon" duk kalaman nan daga wayar Abbas suke fitowa da Ogan shi yake bashi umarni.
"an gama sir duk yadda kace haka za'ayi babu kuskure" Abbas ya firta mai,daga bisani ya kashe wayar.
Yana jinjina ma Ogan da yake ma aiki, aikin da bega ribar shi ba sai zargi in har zargin nashi ya tabbata.
****
"Abdul da gaske kana son yarinyar nan?"
"kai ina son ta mana so in kaji ɗaya kenan son ta da ƙunar ta nake kuma so na Aure" Abdul yaba abokin shi Faisal Amsa.
"wlh Faisal Inaji a jikina yarinyar wani sashi na jiki na ce, Nifa yadda nake ji akanta abun yana ban tsoro matuƙa"
"toh ka sanar mata, ni bana son Yaudara ne ta shigo duk da nasan ba halin ka bane, Amman kana ganin Ammah zata yadda?"
"toh Amma nasan sai ankai Ruwa rana da ita saboda Burin ta na sai head of d house Æ´a Fara Aure Kafin Nabi bayan shi"
Faisal Yace "Kenan Akwai ƙura"
"Bawata ƙura in Sha Allah, kawai zan fara koyama yarinyar sona Kuma alfarma ɗaya zakamin ka nema min gurbi a tahafeez ɗin su tunda kai a ɓangaren Islamiyar kake kai ni sadaƙatul jariya zan koyar Saboda ita da dan ya zama dole na fara zama malamin ta kafin, daga nan kabar min sauran Aikin nasan yadda zanyi da sauran"
"ai wanan mai sauƙi ne, nasan Daktur zai baka gurbi Ai baka da matsala a addinin ka da mu'amalar ka ga sadaƙatul soyayya da zaka yi"
Abdul ya kalle shi yasa dariya "au sunan da ka canja min kenan?"
"a'a wasa nake ma kasan in mun haÉ—u dole sai mun É—ana"
"Ku fa ashe HDH ne bature fa kawai a gidan ku" faisal ya faÉ—a yana dariya.
"shima ai asali ya samo saboda indigen ɗin can da yake da shi ne tun n haihuwa, mu dake Kaga ba ƴan can bane ba a haife mu a ƙasar masu jajayen kunnuwa ba Ai mun dawo ƙasar haihuwar mu, shi ko mun yafe ma turawa shi"
"yanzu da Ammah zan fara har ta bari na fara koyarwan nan Har buri na ya cika na samun soyayyar yarinyar nan"
"toh É—an gaggawa ka bari ka samu gurbin kafin" faisal y tsai da shi.
"eh kuma fa haka ne, toh sai naji daga gareka, kar a É—au lokaci abokina"
Suka sa dariya, sun jima suna hira kafin suka rabu.
****
"nidai duk lokacin da nayi sallah sai na ma yaron nan addu'a ni ban taɓa ganin mai RAI DA BURIN Alkhairi ba irin yaron nan gashi ya ɓoye mana kanshi, ko da yake BURIN Alkhairi ne da shi" wani dattijo ya firta.
"masu yi dan Allah kenan d badan Allah yake yi ba da yanzu ya bayyana kan shi ko BURIN shi akan hakan"
"hakane kuma, Allah ya kare shi ya mai Albarka a duk inda yake"
"Amin malam" Ummi Habiba ta firta.
"salamu alaikum!"
"waalaki salam BINTU" malam da Ummi suka amsa a tare.
Wata yarinya ce matashiya ta shigo, hanun ta riƙe da jaka, jikin ta sanye da uniform na Islamiya da alamu a agajiye ta dawo.
"Ummi, Abu sannun ku da gida"
"yauwa Fateemah, ya karatun?" ummi ta tambaya.
"Alhmd! Ummi yunwa ina abinci na?"
"yana ɗaki har da zoɓon ki mai sanyi, ke in ma indomi kike so jeki dafa, da zafi zafin ta" ummi ta faɗa fuskar ta ɗauke da fara'a.
Da mamaki Fateemah tace "Ummi ina kuka samo indomi?"
"bawan Allah mai ƙudirin Alkhairi"
"Allahu Akbar! Ni ko zanso ganin wanan mai zuciyar kyautatama bayin Allah da, bai da alaƙa da su, ko a mafarki ne namai godiya ta musaman Sai ya ɓace ma ganina"
Dariya suka Mata kafin Abbu yace "banda BINTU a ina zaki ganshi mutumin da yace dan Allah yakeyi, Ai da ze bari mu ganshi da tuni ya bari mun ganshi, Kedai cigaba da mai addu'a, yau ma ya sake tsundumamu cikin farin cikin da ya saba ka kaɓakin arziki can ya sauke mana, unguwa har gulma ake wai wani ɗan nake da shi da yake min aike akai akai niko na barsu d gulmar su Ina ta bin shi da addu'a "
" munafukai ba, saji da shi ta Allah ba tasu ba ai"Fateema ta faɗa taba shirin miƙewa.
"ummi gaskia ƙara'i zanyi indomi zanci yaushe rabon d mu haɗu tunda waccan ta ƙare, mai ruwa ruwa zanyi da yaji" ta faɗa tana shiga ɗaki ta cire uniform ta nufi ƙaramin store ɗin su na masu ƙaramin ƙarfi ɗakine ma aka maida shi store sakamakon itace auta basu da yara sai jikoki in sun zo.
******
"alright! Bro" Abdul ya firta waya kare a Kunen shi.
"ka kula da karatun ka ni kuma ko me kake so zan maka kan ka tsaye ka tambaye ni baka da shamaki Amman ka rage yawan abokanen nan naka bana son su" wata miskilar murya mai cike da kwarjini ta firta ma Abdul.
"yaya dan fa kai baka harka da friends Ne kake ganin aboki bai da wata rana, kuma abokanai na dad da Amma duk sun san su, baka da matsala dani Insha Allah"
"OK, ya lafiyar jikin ka fa babu wata matsala dai ko?"
"eh yaya Jina nake Kamar ban taɓa samu wani heart failure ba zuciyata ma fa yanzu tafi da ƙwari da nagarta"
"ummm baba uban zance indai magana ce ba'a kada kai, kadai kula kawai kamar yadda yace maka" wata hamshaƙiyar datijuwa ta fita ma Abdul da yake waya da yayan shi da yake jin shi kamar mahaifin shi.
"Amman ga baban yaron ki" Abdul ya miƙa ma Amman wayar yana nesa da wayar kar na cikin wayar ya ji shi dan in yaso ya iya wasa da su in beso ba kuma ya iya tsare musu gida kowa sai ya shiga hankalin shi.
"yauwa toh sai anjima, eh suna school sai sun dawo zan gaya musu" Amman ta sanar ma da babban É—an ta da take jin shi kamar tsoka É—ana a miya.
"yauwa Amman na tafi ta kowa, dan Allah ina neman amincewar ki Akan wani abun Alkhairi dan Allah karki ce A'a" Abdul ya kamo hanun ta yana mata magiya da raunaniyar muryar da indai ya mata magana da shi tasan abun ya É—auke shi da mahimmanci.
"ehe go ahead Tun da Naji Kace Amman na ai nasan za'azo wajen inajin ka" ta faɗa mai taɓa bashi listening ear ɗin ta.
"Amman na" yayi narai narai da ido kaman mai shakkan gaya mata.
"na ce fa ina sauraron ka"
"Ammana dama Akwai Darul hadith tahafeez ɗin nan da kike taɓa cewa da nan su Mimi sukayi na iya tahafeez suka ce zasu ɗauke ni don na bada gudummawa da Abin da Allah ya hore min dan ciyar da ilimi gaba and kuma ma Kinga duk wanda kika ga yana koyarwa a makarantar sai wanda aka san yasan me yake ba kowa suke ba Amanar ɗaliban su ba"ya faɗa da ladabi da rauni yadda Amman zata Amince mai.
"ka gama?"
"Amma!"
"nace ka kai aya ko da saura?"
"Amman dan Allah Kar Kice A'a"
"banda BURIN ko niyar hana ka abin Alkhairi, musamman akan Al'ummah ko musulunci baki É—aya, Amman Abdul'ahaad baka tuna situation É—in da kake ne har yanzu fa kana under kulawan Likitoci ne, yes nasan sun sallame ka check up da muke Zuwa ma kulli mukaje Sai ace Komai normal ka samu, Amman kai ajikin ka kana cewa sai kaji kamar da saura Amman kuma kai kanka kasan ka warke, to ya zaka É—auko ma kanka abin da zaka takurama zuciyan ka? "
" Ammah"Abdul ya sake firtawa karo na babu adadi.
"ba ina nufin karatun qur'ani mai girma ze cutar da kai ba a'a ina nufin harkan malunta da ɗalibai dole yau da gobe sai an sami hayaniya sai ka ɗaga murya sai wata rana ɗalibi ya ɓata ma rai kai even Acikin malaman ma yasu yasu suna ɓata ma junan su, na yi fa ko ka manta ne? Nasan ya harkan koyo da koyarwa yake, ga karatun ka baka gama ba da wanne zaka ji? "
" Amman duk zan ji da su kinsan bazan yi abin da ze bani matsala ba, yadda ki first kafin kowa dan Allah"ya marerece Kamar ƙaramin Yaro.
"toh Naji Amman ban ce maka nayi na Amin ce ba sai my love ya dawo in munyi shawara sanan yayan ka at last in ya amince shikenan"
"Amman ur love Ai..."
Wani mugun kallo da ta mai sai ya ankare da suɓutar bakin da yayi, ya gyara "oh sorry Dady ze Amince da Amincewar ki"
"ni ma da tashi zan amince na gama magana, tashi kaje ka ci Abincin da kasa aka girka ma" ta kama Kunen shi da wasa, ya riƙe hanun "Auch Amman ze tsinke fa"
Kafin ta sake mai bata dire shi ko ina ba sai kan dining," A'ee" Amma ta kira mai aikin kula da Abincin Abdul.
"na'am ranki ya daÉ—e"
"kawo mai kunun Ayan Nan Kar Asa Mai ƙanƙara tunda yana freeza nasan yayi sanyi daidai sha"
"toh ranki ya daÉ—e, baban mutum za'aci abincin ne"
"eh in sha Allah" ya bata amsa ta tafi kawo mai.
Ammah kuma ta haura sama, dan É—auko Atm É—in ta.
"Assalamu alaikum" wasu kyawawan Æ´an mata suka firta su biyu, da alamu daga makaranta suka dawo ta Islamiya dake yau Asabar.
"yaya barka da gida" mimi ta faÉ—a ma Abdul.
Nihal kuma sai da ta kusa gota shi ya kira sunan ta, ta san me yake nufi ba tare da ya kalle ta ba da sauri tace "yaya sannu!" kamar an mata dole.
Ƙwafa ya mata ta wuce bedroom ɗin su da sauri ta ajiye jakar ta ta faɗa bathroom.
Mimi kuwa tsayawa tayi tambayar Abdul ina Ammah, yace tana sama tasan Dady baya nan ta haura sai da ta mata barka da gida kafin ta sauko, ta wuce É—akin su.
"kede mai hali baya fasa halin shi kullin magana É—aya, laifi uku cikin É—aya ko Ince a mintunan da basu wuce shabiyar ba"
Nihal a fusace da tsiwa tace "me nayi kuma sai ki lisafo min su Naji"
"mara kunya gurje miki baki zanyi ni, kin dawo kin samu yaya a falo baki iya mai sannu ba sanan bakiga Amma ba ko ajikin ki, nan mun dawo É—aki kamar ba mace ba jaka a gado Takalmi a capet, hijab a bedside Kamar ba mace ba ki canja hali gidan wani zaki"
"duk ni kaÉ—ai, wlh badan nasan uwa da uba É—aya bane suka haife mu da nace kin tsaneni"
"yanzun ma kin faÉ—a ai, halin ki ne abun tsana, ki gyara"
"anƙi ɗin"
"ke kika sani" mimi ta É—age kafaÉ—a, kafin ta kwashe komai da Nihal ta zubar ta adana a inda ya dace ta adana nata ma, ta shige bathroom.
Abdul na kamalawa, Ammah na sakowa Daga Sama.
"yauwa Abdul kazo ka karɓo min saƙon a Shagon ƙaraye na samu na ware wanda zanyi amfani da shi dan kar nazo gobe na manta jibi kana makaranta"
"toh Ammah uwa ta gari yanzu kuwa" ya taso yana goge baki da tissue.
"Amma wai Nihal kullin magana É—aya meyeke damun ta ne?"
"me tayi maka kuma dan Allah bana so kana sa damuwar Nihal ko wani abu bare har ya dame ka ka mata addu'a ai da sauƙi ma yanzu, me tayi?"
"hmm shikenan dama kawai naga sun dawo mimi sai da ta ganki hankalin ta ya kwanta tasan kina lafiya, Itako ko oho, nima fa kamar bata ganni ba sai da na kira sunan ta kafin ta min magana, Wai ni? mimi?" ya nuna kanshi d mamaki.
"kayi haƙuri koni haƙuri nake da ita bawai dan banda yadda zanyi da ita ba sai dan kawai na rabu da ita da halin ta, haka Allah ya yota ya tsindumo ta cikin mu dole mu karɓe ta a yadda take duk da haka muna yima tufkar hanci Ai Kaga da wani gidan ta samu da yanzu wata maganar ake ba wanan ba, tsangwama, kyara, zagi, duka, rashin ja ajiki baya gyara yaro, ku tayani da mata addu'a ku dena biye mata tunda mun fahimci bata da Aljanun komai sai banbancin Ɗabi'a kuma kai fa nata ne tafi ji da kai akan yayan ku"
"ai munafuka ce haka dai take cewa tafi rainani ai, Abayan ido na ta nuna ni wanta ne a gaban Idona dani da banza duk É—aya a wajenta"
"assha! Bana son irin furucin nan dan Allah, a dena kar na ƙaraji"
"toh Amman in sha Allah" ya faɗa da girmamawa ta miƙa mai makullin motar ta da Atm, ya karɓa, ta mai a dawo lafiya ya fice.
Maman shaheed ceðŸ˜ðŸ’ƒðŸ¼
[29/03, 8:04 am] Maman shaheedðŸ˜ðŸ¥°: *RAI DA BURI*