Complete Hausa Novels

Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 4 of 5

PAGE 4

BY

MAMAN SHAHEED

Paid Book...

Ga Account ɗin da za'a biya 👇

3108794095

Fatima Abubakar

First Bank

Shedar biya 👇

08134624555

Akwai book É—in a Arewapen...

Bayan kowa ya zaɓi abin da zeci nihal dai dan ta sake birge yaseen abincin Larabawa ta zaɓa har ya tsokane ta inda ta koyi ci tace a wajen Ammah ta shima irin abin da ta zaɓa ya zaɓa shi dai faisai duk cikin su shine me jin yunwar gaske dan haka da tea ya fara wanda yaji coffee kafin ya ɗora da abinci sai da yaji ya fara ƙoshi ya fara saka musu baki a hirar har suka cinye hira ta biyo baya nihal dai ta kasa cinyewa har sai da faisal ya karɓi nata ya faraci yaji ya ƙoshi ya ajiye yaseen ma bai cinye nashi ba, faisal nata tsokanar su wasu turawa ko Larabawa su dai suka sani, sun ɗanyi hira sosai a wajen kafin yaseen ya biya kuɗin duk abin da sukaci bilƙis taji uban bill batayi mamaki ba dan sun taɓa zuwa so ɗaya wajen aka ƙarar musu da ruwan jiki basu sake zuwa ba na mota ma ranar sai da aka biya mata ta koma gida sai yau na biyu.

Bayan sun gama hirar suka fito, har bakin lecture hall ɗin Su ya mayar da su dan yaseen ne ya tuƙa motar da kanshi.

Yana ajiye su suka tafi da faisal da larabci ma yama nihal Sai anjima, ƙawayen ta kuma da turanci suka mai godiya suka shige suna jinjina kyautar shi da tsari da zubin shi, Amman sun san class ɗin su ba ɗaya ba uwa uba ƙabila.

Ranar koda nihal suka haɗu da mimi tun kafin su koma gida sai da ta bata labarin yaseen da irin bajinta da ya musu da niyar zata koma ta gyara larabcin ta Kodan gudun ɓacin rana irin ta yau da tafi kowa muzanta dama Ammah tayi tayi ko malami a ɗauko musu don gyaran larabcin ita ta bijiri Har mimi ta haƙura yanzu kuwa ta shirya tsaf dan zama wacce zata iya ƙwatan kanta da larabci a ko ina.

Mimi dariya ta dinga mata, har ta nuna mata ta dai dinga nutsuwa ta zama mai kamun kai.

Diver ya jasu Har gida.

Washe gari kusan duk tare zasu shiga school tun dare abdul yace su shirya ze shiga da mota tare zasu tafi dan haka nihal batayi bacci ta saki baki ba ta shirya da wuri, dama Dady yayi tafiyar kwana biyu suka ma Ammah sallama, Abdul da mimi a gaba nihal a baya babu faÉ—a har hira suka dingayi da Abdul yana yabon ta tana ta murna, be ajiye su ko ina ba sai inda su nihal zasuyi lecture Æ´a parka motar Ammah É—alibai aka bisu da kallo É—uuuu, nihal aka fito ana takun isa da jin kai kamar Æ´ar gwamna har ta shiga tana É—agama ya Abdul hannu da mimi har wani kiss aka wurgo ma mimi na Æ´an uwantaka, Abdul ya Harare ta, tunda suka taho sai yanzu ya Harare ta.

Kafin yaja motar dan ajiye mimi, yana ajiye ta

Shima yayi department É—in su Bayan sun haÉ—u da faisal sun gaisa kafin suka rabu.

******

Fateemah ta gama fama da ciwon ta da ta saba har ta gama, ta koma school, suna ta cigaba da karatu da ƙarawta firdausi sadeeq Abu Kamar wasa sun fara shaƙuwa gashi itama tana gane karatu sosai dan haka tafiyar su take neman zuwa ɗaya.

Akazo zaben monitor sakamakon cire ainahin monitor da akayi Daga makarantar, shine akaga fateemah ce tafi dacewa da zama aka bata aka ba firdausi assistant ɗin ta, Aiko class suka dinga bore daga zuwanta dan mugunta Har sai da suka jama kansu duka har class master aka canja musu aka basu wanda ze iya dealing ɗin su Wato teacher zanzaro, sanan suka shiga hankalin su,aka zauna lafiya dan sai da aka mata interview Kafin suka tabbatar da ƙwazon ta.

Ana tsaka da haka ƙawar fateemah lubna ta kawo mata gulmar wata a unguwar su da za'ama Auren waybill mijin yana Qatar bata taɓa ganin shi ba ta waya suka haɗu Amman ɗan Najeriya ne har aure yake neman shiga tsakanin su za ayi bikin a tura ta ita kaɗai.

Fateemah dai ta musu fatan Alkhairi dan bata fiye son ire-iren surutan da be shafeta ba lubna kuwa har mamakin yadda take jin abubuwa take.

Haka dai lubna ta gama mata hirar duk ta jita Amman bata tofa Nata ba.

*******

Bayan Dady ya dawo daga tafiyar kwana biyu da yayi shi yama babban yayan su Abdul maganar koyarwan da Abdul ze fara, baban yayan ya nuna be amince ba ya kafa musu hujojin shi masu ƙwari da zasu gamsu da su dan shine baya son duk wani abu da ƙanin nashi ze wahala, suka yadda kuwa, har suka fara nuna ma abdul ɗin ya haƙura, kasa magana yayi a lokacin dan be gamsu ba ya ƙudire a ranshi zeyi magana da yayan nashi da kanshi dan zefi fahimtar shi.

Abdul ya sami mimi suka fara maganar tamai alƙawarin itama Zata taya shi roƙon yayan nasu.

Abdul sosai yama broh H magiya Kamar mai neman wani abu mai mahimmanci a wajen, gashi baya son magiyar shi, sai ga mimi ma ta fara nata roƙon suka haɗar mai biyu gashi yana ji da ƙanen shi su biyun dole ya cika musu muradin su tunda ba saɓo ze aikata ba kawai yana so ne ya hutar tashi shi kuma baya son hutun ƙanin nashi, sai ya barshi ya bashi dama ya gwada a zaton shi da kanshi ze haƙura dan yasan koyarwa akwai wuya Ko wacce iri ce masu yi haƙuri kawai sukeyi.

Lokacin da yayan nasu ya amince har wani side hug Abdul yaba mimi da murnar shi itama ta taya shi murna, ashe nihal na kallon su wanda fitowarta kenan daga kitchen sai taji ta matsu taji murna da farin cikin me sukeyi haka gashi bata isa tama Abdul tambayar kai tsaye ba ya saurare ta, sai da taga ya haura sama wajen su Dady da sauri, sai ta ƙaraso wajen mimi.

"yaya mimi albishir É—in me aka muku keda yah Abdul kuke wanan farin cikin?"

"Haura sama ki tambayo shi in bazaki iya ba kuma na rakaki"mimi n mata wani kallo.

" ke fa matsala ta dake kenan yaya mimi "

" eh kya ce min yaya mana tunda gulma ta motsa yaushe rabon da ki kirani yaya ko anti sai in kinso gulma ko a gaban su Dady ko babban yaya ko a wajen in kinso nuna ni yayar Kice, Amman ai kai tsaye kike kirana"

"toh ba dai ina faɗa ba? Dan Allah ki gaya min ni?" ta turo baki alamun ta ƙosa.

"nace ki bishi ko kije Dadyn Ki ya gaya miki tunda mu duk tsinto mu akayi" mimi ta firta tana mai tashi ta bar mata wajen.

"OK kishi ya motsa aiko ta kwana gidan sauƙi indai Dady ne zan sha labari baze ɓoye min ba ki riƙe ma bana so wanda ze faɗa sai yafi daɗi" nihal ta firta.

"kyaji da shi ciwon Ajali a ɗanyatsa ki dai canja hali gidan wani zaki" mimi ta ƙarasa shiga corridor room ɗin Su ita da mimi.

Abdul ya haura ya sanar ma Ammah da Dady duk yadda sukayi da yayan shi, suma suka sama abu albarka suka nuna amincewar suka mai addu'a, ya musu godiya, suka dab dale zeje Islamiyar a satin, kafin ya sakko.

Yana sakowa nihar ta haura ta fara tambayar Dady murnar me yah Abdul yake na hanun daman nata kuwa ya kwashe komai ya gaya mata, ta dinga mamakin dalilin son wahalar da kanshi da yake son yi haka, ta cika su da surutu har maganar gyara larabcin ta tayi ma Dady tasan shi ze kulata Ammah Ko bazata saurare ta ba ya mata alƙawarin ze nemo musu ƙwararen malami Amman sai yaji ta bakin mimi, ta yadda ta amince, ƙarshe dai sai da Ammah ta koro ta cikasu da magana.

Tana sauka tayi É—akin su "anti mimi dan Allah ki nuna ma Dady Dani da ke muka yanke shawarar gyaran larabcin mu please sis" ta É—an rungumo ta alamun rarashin yaudara.

Hararar ta mimi tayi kafin tace "al munafuk, watan yaudarar ne ya kama?"

"kai yaya mimi a'a, Nifa roƙon ki nake kome kikace nayi zanyi Kinji Kawai ki cema Dady tare mukayi shawarar shine kawai roƙona da ke"

"ko me nace kiyi ko?" mimi ta sake tambayar ta.

"eh anti mimi Ai nasan bazakice na faÉ—a wuta ba"

"zaki sani ne, kodai meye kuma ko ba yanzu ba?" mimi ta sake jadada mata.

"yes! Yes!! Na amince kuma ni na faÉ—a" nihal ta nuna kanta.

"Tom shi kenan inhar ya tambaya zan sanar mai"

Da sauri nihal ta rungume mimi "yauwa yayata Tafi ta Kowa" suka sa dariya.

Washe gari ma kusan tare suka shiga school da ya Abdul.

Wasa-wasa kusan sati biyu nihal bata ga yaseen ba tana son tambayar Faisal ta kasa, ranar katsaham ya shigo school da wata sabuwar motar mai ɗaukar ido, a kusa da su ya Parker ta ashe ya hango ta ita ko bata san waye a motar ba tana zaune tana jiran ƙawayen ta, taji tsayuwar motar Sai bata ko ɗago ba bare ta kalli motar, saboda kar ta zubarma da kanta aji akan kallon wata mota.

Matan wajen da samarin wajen kuwa kallon motar kawai suke Sina jiran ganin mamalakiyar motar, sai ganin yaseen sukayi wani balarabe da sai da wasu matan suka tsure hasken shi da kwantacen gashi shi ya yaudare su, sai kallo ya koma kanshi da inda ya nufa yana murmushi da wayoyin shi manya guda biyu a hannu da makulin mota.

"hy nihaal" ya firta mata yana shirin zama gefen ta, yayin da tuni ƙamshin turaren ta ya bata labarin waye ya ziyarce ta kasa ɗagowa kawai tayi.

"hy Akhee yaseen" ta firta da sai da yayi mamaki ya akayi ta gane shi ne kamar mai tunanin shi alhalin bega ta kalle Shi ko so É—aya ba.

Sai suka fara gaisawa da larabci, ya tambaye ta karatun ta da mutan gida duk ta bashi amsa ranta fal farin ciki.

Sai daga baya ya fara mata gwarancin Hausar sa, ya fara kiran wayar Faisal Yana gayama nihaal ya kira shi kusan so uku be É—aga ba, sai ko nihaal tace "Ai suna lecture Fa Kamar naganshi É—azu"

Sai ya nemi tamai rakiya zuwa hall ɗin da suke, ta miƙe dama kamar jira take, suna cikin tafiya sun wuce ta department ɗin su mimi Kenan sai ga mimi, tama nihaal wani kallon tuhumah.

"ukty mimi" nihaal ta kira ta da salon iya yi ita ga mai Æ´ar uwa za'a larabce ta, ta mata magana da larabci mimi ko baya kayan iyayi duk da Hausa ta bata amsa har yaseen ya dinga mamakin to ya akayi take ji Amman bata iya mayarwa?

Nihal ce ta gabatar ma da yaseen, wace mimi a wajen ta, sanan suka ƙara gaisawa, Nihal ta sanar ma mimi wajen yaa Faisal Zata rakashi tazo suje, dan Kar ta mata gulma awajen yah Abdul, mimi ma kuma dan ta ƙure ƙaryar ta badan taso ba suka jera, Yaseen Nata janta da magana da turanci mimi na bashi amsa a gajiye alamun kamar har ya dame ta, can ya jefo mata larabci ta mayar mai sai yaji ashe tama fi nihal ƙwarewa da gogewar harce Sai ya zubar da mamaki da yake ɗazu, har suka isa hall ɗin su Faisal larabci Kawai suke zubawa da mimi da ta gaji da surutun yaseen har ta fara tsoron kar ya kurema larabcin ta gudu, nihal ko daɗi Abin ya mata, mimi sun fara sabawa da yaseen.

Suna zuwa suka ga lokacin ake fitowa malamin ya gama musu karatun, sai ga Faisal, yaseen ya Harare shi, Faisal ya Mai wani kallo ya basar.

"ya Faisal Ina wuni Y lectures?" mimi ta gaishe shi.

"sis mimi lpy y naku karatun? An fito ko baku da shi yanzu?"

"eh yaya sai nan da 30mns" ta bashi amsa.

"OK Allah y taimaka, Komai normal dai ko?"

"eh yaya Alhmd, Amin"

"nihal d autares" faisal ya firta mata.

Tayi dariya "ya faisal ina gajiya"

"gajiya akwai ta mimi" faisal ya amsa mata.

"guy yane? Ka kirani ina class nasan maybe kana cikin school shiyisa na bari na gama kafin" faisal ya kali yaseen ƴa miƙa Mai hannu suka gaisa yana mai dariya.

"toh sarkin lecturers, badai ka gama ba?" yaseen ya tambaye shi.

"eh saura ta anjima da zamu shiga, wai kai gayen nan sai Uncle Haroon ya fara maka hukunci kana fita kana bar mai company a duk time É—in da kaso ko?"

"toh ina nake zuwa? Nan ne fa kawai sai outing da nake zuwa shima sai time to time nafi fita da kai ma, zan mutu a company ne?" yaseen ya tambayi faisal da yake ta mai kallon rainin hankali.

"a'a bazaka mutu ba Amman dai in ya gane ka kasan akwai case kuma count me out Daga case É—in naku kai da shi"

"wallahi in dai ba out ba, kaima Kayi ka ƙare karatun nan ka fara managing da company Abu ya gagara"

"au ni zan gama karatun da kaina ba time bane ze kaini? Yanzun ma ai ina shiga ina abun da zanyi" faisal ya FaÉ—a kafin yaji muryar mimi da ta gaji da jin conversation É—in su tace "yah faisal zan wuce inaso zamu É—anyi karatu da group members É—in mu"

"OK sis mimi, Hakan nada kyau, Allah ya taimaka"

Nihal Ko hirar tasu daÉ—i take mata haushi taji ma da mimi zata tafi tasan dole ta kaÉ—a ta.

Wani kallo da mimi tama nihal tasan me take nufi kuma bata son nuna mata bata isa da ita ba sai kawai ta turo baki ta ma su yaseen sallama ya mata wani kallo da mimi da nihal suka rasa gane ma'anar kallon, sai suka wuce.

"wallahi nihal Ina rabaki wanan mayunwacin Jan zakin ki kula sosai, ki dawo hayyacin ki muna da banbancin jinshi, yare da sauran abubuwa ki tsaya a matsayin ki, tom" mimi ta mata gargaÉ—i.

"toh yaya mimi me kika ga nayi? Da duk kike wanan maganar?"

"au sai ma kinyi? take taken dai na gani nake shawartan ki matsayin ki na Æ´ar uwata"

Sai da suka je masallaci suka É—an huta sanan kowa ya tafi karatun shi dan yau nihal sai ta jira mimi ma na kusan awa É—aya da rabi.

"Ammah barka da gida ya ƙoƙari?" Abdul da ya shigo falo ya sami Ammah ita kaɗai.

"lafiya lau son, ya karatu , yaushe zaka kasuwar naga kwana biyu kana sha ruwan tsuntsaye ko gata ne Yama yawa?" Ammah ta tambaye Abdul.

"a'a Ammah gata kuma, akwai abin da nake jira ne order da mukayi a Gallary ɗin ne bezo ba kuma Kinga da dani za a fita order sai aka tafi da hamza ni sai next time zan dinga Shiga Sosai da kaya sunzo jibi In sha Allah Ai akwai harka kuma Kinga akwai aminta tsakanin oga da dady Kodan Dady Ai dole na cigaba da zaman Gallary kuma Kinga kuɗin da yake biyana yafi na sauran yaran wajen dan ko Aure nayi yanzu zan iya riƙe mata da albashina" ya firta yana dariya dan yaji ta bakin Ammah.

"Au me? Aure dai Naji kamar kace? To in ma ka faÉ—a ne dan jin daÉ—in bakin ka to kaji, ni kuma ka É—auka ma bana wajen ka faÉ—a" ta cigaba da latsa wayar ta da alamu furucin nashi be samu gurbi a zuciyar ta ba.

Abdul wani iri yaji wanda har ranshi sai yaji beji daɗin rashin karɓan abin da Ammah tayi ba,Abun ze zamar mai ga match ya taro babu ƴan wasa bugawa kenan? dan shi da gaske yake ya kuma shirya tsaf koyarwan da zeje yayi Ma gini mai ƙwari da ƙarko yake son yi dan yana jin yarinyar kamar wata tsoka Ko tsagi ce ta cikin jikin shi ko wata ahali daga ahalin gidan su yama rasa gane yadda lokaci guda abun Yamai zuwan bazata shi da ko cikakiyar budurwa bashi da ita sai wanan da bata wuce ko bata kai sa'ar su nihal ba ma a kallon da yake mata.

Dan ya samu daidaito da Ammah sai ya bar zancen sai ya shigo mata da maganar tafiyar su ummarah ya Fara sanar mata sun fara maganar da yaya, shine har ta bashi haÉ—in kai sukayi hirar sosai.

Har yaje makarantar sun gama komai da malaman akwai wanda yasan Dady su ma har yake ganin Abdul É—in ze iya kuwa ya ganshi É—an ajebota dashi, Abdul É—in ya bashi tabbacin In sha allah ze iya, abin da yafi burgesu da ya nuna kamar sadaukarwa zeyi, kamar addini zema hidima kyauta yace zeyi ba tare da neman a biya shi ko sisi ba, sun gama komai har ya shigo yau Asabar ze fara koyarwa.

Fateemah yau ita kaɗai ta shiga makaranta da wuri ta Fara muraja'a ta sami waje ta zauna kusan su uku ne kawai a ajin ta zauna kusa da window tana ta karatu da muryar ta mai zaƙi ba ɗaga sauti take ba Amman in kana kusa da window zakajiyo ta, Abdul kuwa dama tun shigowar ta a idon shi ta shigo, dan haka yana zagaye yajiyo muryar ta kamar an ƙamar dashi a wajen ya tsaya kamar mai amsa kira a waya Amman a zahiri ita yake saurare.

Yana tsayen Har É—alibai suka Fara taruwa suna ta shiga aji, shi kuma be bar wajen ba sai da wani malami Yamai sallama suka gaisa ya shiga ajin su Fateemah dan gabatar da darasi, kafin ya bar wajen.

Suka haɗu da Faisal na Islamiya dan Ranar Asabar d Lahadi baya shiga Islamiyar Amman yau ya shigo saboda abokin shi Abdul yaka yadda abin yake tafiyar mai,har suka shiga aji aji dan ya gabatar ma da ɗalibai sabon malamin su wanda ze ɗauke su Qur'ani da tajweedi, ko da aka zo ajin su fateemah har aka shigo da shi aka gama gabatar da shi bata ɗago ba bare ta ganshi tana ta gyara hadda ta da malami ze shigo ya karɓa dan har Wani runtse ido take irin kar wani abu ya ɗauke mata hankali tana ta motsa baki, Abdul ko yana ta satar kallon ta,har suka fita bata dago ba dan b jimawa sukayi ba.

Bayan an yi break an dawo, Abdul ya shigar musu sai anan fateemah ta ganshi ganin farko shima ji tayi kamar ana kallon ta shine ta ɗago idanun ta masu kama da madara dan tabbatarwa, tayi tozali da shi, daga shi har ita kowa ɗauke idon shi yayi daga kallon ɗan uwanshi, yaci gaba da musu bayani kafin ya musu ƙarin Qur'ani, kowa ba ƙaramin jin zaƙin muryar Shi yayi ba aajin wasu ko ma shi suke bi da kallo ba karatun ba sun shagala sosai karatun mai daɗin sauraro kamar ba daga bakin shi yake fitowa ba.

Ganin wasu kamar ba karatun suke ba ya fara tashin wasu daga ɗaliban suna biyawa wanda ya kula basu bada hankali da nutsuwar su ba, duk ciki babu wanda ya iya biya mai sai da ya tashi fateemah taji duk kamar an ɗaureta dole ta aro nutsuwa ta biya mai da ƙira'arta mai daɗi da Abdul ya sake yabawa, kafin yace ta zauna aka mata kabbara ya mata jinjina, kafin yace sauran ma su zauna ya sake maimaita musu.

Har aka tashi fateemah taji bata son su sake haɗuwa da sabon malami, shi ko yanzu ji yake dama iya ajin su yace ze ɗauka dan so yake ya karance ta sosai ya bata ruwa daga ruwan Ilimin da yake da shi dan ya fahimci mai ƙwazo ce.

[06/04, 9:17 am] Maman shaheed😍🥰: *RAI DA BURI*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.