Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 2 of 5
PAGE 2
BY
Maman shaheed
Free pages basu d yawa, guda 5 ne..
Ga Account ɗin d za'a biya👇
3108794095
Fatima Abubakar
First Bank
Shedar biya...
👇
08134624555
Fitar Abdul keda wuya, nihal ta fito falon ta samu Ammee, sai a lokacin taje gareta.
"Amme sannu da hutawa"
"yauwa, an dawo?" kawai Ammee ta bata amsa dan in da sabo ta saba da halin nihal dan ma tana tsaye akanta.
"eh Ammee, yaya Abdul fa?"
"baki da number shi ne na baki?" Ammee ta bata amsa.
Sai taga kamar baƙar magana, Ammee ta gaya mata,gashi babu wasa a fuskar ta.
"a'a Ammee, naga bangan shi bane kawai"
"uumm, sai ki tafi neman shi" Ammee ta sake bata amsa ba tare d ta ko kalle ta ba.
Ganin dai Ammee kamar a fusace take da ita sai ta lalaɓa tabar wajen, musamman da taga fitowar, mimi tasan in suka haɗu Sai ta gane tayi ba daidai ba.
Kitchen ta nufa dan neman abin ƙwalama da zata ɗan sa abakin ta, tama su baba A'ee sannu, da Laraba, dan aikin girki suketayi na gidan gaba ɗaya.
Abdul be jima ba ya dawo da wata babbar Leda guda ɗaya, da saƙon Ammee, ya ƙarasa har gabanta ya bata, tana ta mai sannu sa da dawowa, sai da Ammee ta duba komai taga dadai ne saƙon Nata kafin ta ware na kitchen tasa aka Haura mata da sauran saman Dady.
Bayan magrib kowa na falo suna zaune gaba É—ayan su, sukaji motar Dady da alamu ya dawo ne, Nihal ce ta zabura zata tashi taje dan yimai oyoyo, wani mugun kallo da Abdul ya mata shi ya tsaida ita dan inda sabo ta saba da Dadyn ta musamman da yake nuna mata itace auta shiyisa take duk wasu abubuwa dama babban wansu ne dodon ta da ya dawo gidan komai nata yake setuwa.
Abdul ne yaje ya taro Dadyn ya riƙo mai jakar shi har suna ɗan taɓa hira a hanyar, sai da suka shigo, nihal ta tafi da sauri.
"sannu da zuwa Dady, an dawo lafiya"
"yauwa, lafiya lau ya naga kina behaving Kamar mara gaskia?"
Da sauri kowa y kalleta, tayi mitsi-mitsi da idanduna kafin ta bashi amsa "Dady babu komai kawai na gaji ne da muka dawo daga Islamiya"
"OK, sannun ku toh, Allah yayi albarka"
"Ameen" ta amsa.
"Dady sannu da zuwa, an dawo lafiya?" mimi ta firta.
"mimi lafiya ya gida ya karatu?"
"Alhamdulillahi Dady" mimi ta bashi amsa.
"my love an dawo? Ya hanyar?" Ammee ta jefo Mai nata tambayar d ta bari kowa y gama nasa.
"My Dear lafiya lau, ya kuka wuni, Koma lafiya dai ko?" Dady y tambaya.
"lafiya lau, sannu da hanya, muje ka yi wanka kafin sallah sai kasa wani abu acikin ka ko?"
"OK Dear, Yauwa Abdul jeka mota a sit É—in baya akwai Leda guda biyu ka kwaso su ka hauro min da su"
"OK Dady" Abdul ya amsa ya tafi.
Bayan Dady d Ammee sun haura, sai nihal ta fara raraba ido tasan tsaraban su ne Dady ya kawo maybe Har ta matsu taga meye.
"meye haka kikeyi kamar wata me jiran wani abu ko wacce ta bada ajiya? Ke dai naga ranar da shekarun girma da na hankali d nutsuwa zasu zo miki ke kam" mimi ta zunguri kan nihal.
"toh ke wai ina ruwanki dani ne? Ke kike ganin banda nutsuwa naga ai nutsuwar yaseen Abdallah ya gani yake kirana ƙanwar shi"
"ina rabaki da wanan jan kunnen ki tsaya matsayin ki, ki kama kanki, in kinƙiji kuma toh"
"to Wai sis me nakeyi da baya dadai, kawai dai kinfi so Kowa ya zama kamar ke, baki da wani say, sai kara d kawaici da rashin son nuna kedin kinsan kanki nikam Bazan iya rayuwar ki ba, in abu yamin yamin kawai in bemun ba kawai bemin ba shine gaskia zance" nihal ta faɗa tana mai miƙewa dan taro yah Abdul da ya shigo da Leda, wani mugun kallo ya mata ta tura baki ta fasa karɓan Ledan ta ja da baya.
Mimi ta bushe Mata da dariya, ta na mai miƙewa ta nufi kitchen, yah Abdul yayi saman Dady.
"kyaji da shi, Ai ba dukana yayi ba ko zagina"
"oho dai" mimi ta sake firta mata tana gab d shiga kitchen É—in kafin ta shige.
Yah Abdul da kanshi bayan Ammee da Dady sun nuna mai yadda zeyi yaba kowa tsaraban shi, ya sakko ya ba su nihal da miki har masu aikin gidan kowa godiya yayi yana sa Albarka, nihal ko gani tayi kamar nata yayi kaɗan tasan d tana wajen nata sai yafi haka yawa, Amman Abdul na falon da tayi yunƙurin haurawa sama tasan me ze buyo baya dole ta karɓa da haƙuri, daga baya da taga su mimi da yah Abdul suna hira har ta ɗan sa musu baki, yana ba mimi labarin ze fara koyarwa a darul hadith, ganin Nihal tasa baki ya kama kunnen ta yana mata gargaɗi inyaji maganar Sai ta sani, shine ta toshe bakin ta har Ammee ta sauko bata sake sa musu baki ba a hirar su.
"yauwa Dota mimi jeki haɗa ma Dadyn ku komai na buƙata da zeyi amfani da shi a kitchen ɗin sama na girka, mai abin d zeci iya bakin shi, bari uwar rigima ta biyo ki da lemun shi"
"Ammee... Uwar rigima kuma? Yaushe rabon da ki kirani da wanan sunan da Dady ya hana?" mimi ta faɗa tana taɓara.
"na kira sunan asamin gas ko ki kai ƙarata gun Dadyn, ba sunan ki bane? Tashi ki haɗo ki kaimai sama ni kafin Inzo in sameki a wajen saura in kin kai ki tsare shi da surutu ya gaji kar ki barshi ya huta"
Sum sum Nihal ta miƙe, mimi kuwa ta jima da haurawa saman.
"yauwa Son ya zakayi ne da karatun ka da wanan rigimar da kake neman ƙarama kanka?" Ammee ta tambayi Abdul.
"kai Ammee duk zan iya karatun da nakusa gamawa koma na gama za'ace, final exam Kawai Fa ya rage min kimin addu'a kawaiAmmee dan Allah"
"toh Banace a'a ba Amman karka sa rai, sai Dadyn ka ya nutsu zan mai maganar duk da kasan ba lalai ya yadda ba, in be yadda ba sai kayi haƙuri"
"toh Ammee, Amman ze yadda da yaddaki Ma in sha Allah"
***
"BINTU kizo kiyi maza karki makara" Ummi ta firta ma Fateemah.
"toh Ummi Safa Kawai zansa, yanzu zan fito"
Babu jimawa matashiyar budurwar ta fito "toh Ummi sai na dawo, Ina Abdu na?"
"yana wanka ki tafi nace kina mai sallama, yi sauri"
"toh ummi saina dawo ace mai na tafi"
"toh Allah ya tsare da nawa da nashi Allah ya bada ilimi mai Amfani"
"Ameen Ummi" BINTU ta amsa mata.
"yauwa sai ki lalaɓa kuɗin ze osheki ai ko?"
"eh ummi In sha Allah
,sai na dawo na tafi" ta fice ba tare da ta ji me Ummi ta firta ba.
Hankalin ta a ɗan tashe ganin ta kusa makara take tafiya, da takunta na sauri-sauri gudu-gudu babu abin da take buƙata illa ta ganta cikin school ɗinsu.
Tana cikin tafiya ta ga wata mota tasha gabanta, sai tayi zaton parking motar zatayi sai ta kauce ma motar tayi kamar tazati gefe tayi tafiyar Ta sai, taji an kira sunan ta "Fateemah kin kusa makara fa kizo akaiki dan ki Isa da wuri"
dumm! Taji ƙirjin ta ya bayar sai ta fara tunanin in da yasanta har ma da sunan ta, bata fita daga tunanin ba, ya ƙara mata da wani tunanin "indai bakya son dukan makara kizo in ajiye Ki, in kuma kinfi son dukan toh Allah ya kiyaye Amman teacher zanzaro Yana Nan Har ya fara dukan yan makara kuma zakice na gaya miki"
Bata san lokacin da ta ɗago ba ta kalle mai maganar daga cikin motar da bama ta yadda da motar ba da mai motar gaba ɗaya sai gashi ya sake shayar da ita ruwan mamaki ya akayi yasan teacher zanzaro? Ta so zargin ko ya santa Amman zuciyar ta taƙi bata daman yadda da hakan, sai ta ma mamalakin motar kallon ƙarshe, fuskar shi rufe da nose marks da glass duk yadda taso gane ko waye ko ta san shi bata ita ba, sai kawai ta tsinci kanta da firta mai.
"malam nagode, Amman babu inda zan shiga yadda na saba tafiya haka zan tafi" bata jira me zece ba ta wuce shi tayi tafiyar ta.
Yaso bin ta sai kuma ya fasa ya É—aga waya, yayi magana ta tsawo minti 30 kafin ya kashe wayar ya bar unguwar.
Fateemah na isa taga ana dukan makarar kuwa da gaske taji ranta ya ɓaci bata son abin da ze taɓa lafiyar ta yanzu jini ze taru ahanun ta ita tama manta yaushe rabon ataɓa lafiyar ta, cikin ayari ta shige jerin wanda suka jiran dukan yazo kansu, ana zuwa kan balaraba Sadiq ana zamɓaɗa Mata ɗaya tasa ihu ta kwasa da gudu zata gudu cikin harabar makaranta ya bita yasha gaban ta ya dawo da ita tana kuka sai da ya mata guda biyar masu zafi, hasana Usman kuwa da aka zo kanta gocewa ta dingayi Har yace sai ya mata goma, ana haka malam Malam Ali yazo ya nuna fateemah "sorry Sir Fateemah zo nan kiyi wani aiki pc ne yace na nemo yar class din ku mai hankali da nutsuwa ba irin masu ihun bulala ba" wanan maganar malam Ali ita tace ci fateemah ya kaita office tana ta ajiyar zuciyar ta tsira daga duka dan yau kamar da gayya yake dukan ma.
"yauwa Fateemah Sadeeq ga sabuwar É—aliba tafi da ita ajin ku yau ta fara zuwa sai ki nuna mata abin da akayi da bata nan"
"OK sir" fateemah ta amsa.
"firdausi Usman abin dabaki gane ba ki tambaye ta baki da matsala sai ki dage"
"Tom malam" firdausi ta amsa mai, suka tafi har class tare da jagoranci fateemah suka sami mazauni suka zauna.
Bayan an fita break wasu daga cikin ɗalibai suka fara tsegumi Fatima da bata kula mutane sosai tayi ƙawa ashe girman kai ne yasa bata kula su sosai ita ba ƴar kowa ba, ita kuma firdausi tun da aka haɗa su take gani babu da wanda ta saba sai fateemah shi yisa taƙi matsawa daga kusa da ita, Fateema kuwa dama ba kowa take kulawa ba karatun da ya kaita shi kawai takeyi dan tana ss two ne yanzu daga sss one ta fara makarantar bata biye ma duk shirmen ƙawaye balaraba sadeeq Kawai take kulawa sai tsirarun ɗalibai masu nutsuwa Itama balaraban dan sunan baban su yazo ɗaya ne amma tafita rawarkai.
Har sai da aka tashi suka fito tare sanan suka rabu a hanya kowa yayi hanyar gidan su, fateemah ta samu suka rabu da firdausi.
Koda ta isa gida a ajiye dan tataki tayi kuma makarantar da tazara tsakanin ta da unguwar su, tana shiga cire kayan makaranta ta nufi bayi ta watsa ruwa Ummi nata mata sannu da dawowa.
Tana fitowa ta samu ummi ta rabza uban tagumi ta Lula dogon wani nazari da alama wani tunani take da yake son zame mata jiki, har fateemah ta fito ta tsaya na daƙiƙu bata san tana kallon ta ba sai da ta tsinkayo muryar ta.
"Ummi! Ummi!!" firgigit ta juyo takalle fateemah.
"ummi yaushe zaki rage ma kanki wanan tunanin ummi? Kefa kike ƙarfafar mu da Abdu tunda muka dangana muka yadda da ƙaddara mai kyau da mara kyau daga Allah take, sai ke kuma kika maye gurbin mu da tunani ko da yaushe in abin ya faɗo miki ko kika tuno, natabbata tunanin su..."bata ƙarasa ba, ummi ta datse ta.
" hmmmm BINTU iya juyama tunani baya inayi Amman sai yashaa gaba na in abun ya motso har yanzu gani nake kamar mafarki nake, kamar akwai ranar da zan farka daga mumunan mafarkin da na jima da imanin kamar babu ranar farkawa"
Fateemah ƙarasawa tayi kusa da ita ta dafata da kulawa da rarashi da tuna mata ƙarfin tawakkali da hukuncin ubangiji "Ummi duk munajin haka har masoyan mu da masoyan su, yadda na kasance ayanzu a gaban ki kaɗai ya isa mu godema gwanin hikima Mu Jinjina Mai mu cigaba da rungumar ƙaddara har iya rai da mutuwa"
"hakane kullin inna tuna hakan ko na kalle ki Ko na ga su Arfat Sai na sake gode ma Allah da wanan ni'imar, babu yadda zanyi ne na goge wanan ƙaddarar da Sanadin da tuni na goge Kodan samun nutsuwa ta da ku iyalaina a yanzu, Amman zan sake ƙoƙartawa, Kinji? Tashi kije ki sanya kaya, nagode da kulawa"
"hakane ummi, ke ɗin dole ta ce kuma gata ta duk abin da na miki ban bi yaki ba"fateemah na gama faɗa ta miƙe zuwa ɗakin ta da yake ko yaushe a gyare tsaf.
Bayan ta gama shafa mai babu jimawa aka kira sallah ta É—auro alwala ta gabatar da sallah ta.
Bayan Abdu ya dawo ya kawo musu ýar tsarabar yalo da su Karas suka karɓa suna ta murna suna mai sannu da kasuwar da yake ɗan zuwa yake taya wani mai Shagon kayan masarufi jiran Shagon da tayashi awo,
"Ummi yau aka kawo sabuwar É—aliba, duk sai naji na takura duk inda naje tana tare dani, dake pc da malam Ali ne suka haÉ—ani da ita muka tafi class"
"ke dai kawai rashin son mutanen ki, Ina laifi an haɗa ki da ƙawa in halin ku yazo daidai ba shikenan ba sai ku taimaki junan ku, tunda kince duk ýan ajin ku da daman su sai ahankali" Ummi ta bata amsa Abdu nata lomar Tuwon Shi yana musu murmushi baya son Magana sai ya gama.
"kuma Ummi in Allah ya yadda bazan sake makara ba badan Taimakon rakata aji da zanyi bafa da na casu yau kamar dawa Ko casuwar shinkafa, tama fa taimake ni kawai zuwanta yau shi ya ƙwace ni a hanun teacher zanzaro"
"toh kingani ashe ma ta miki rana, sai ki riƙeta da kyau in kin yadda da ɗabi'u da halin ta, uwa Uma ilimi da mai da hankalin ta a karatu"
"toh gamu nan dai yau aka fara babu abin da zan fahimta tukunna, nadai Ara Mata wasu note books ɗina zata kwafi aiki, in tafiyar mu tazo ɗaya to Kodan na ƙarya ta ýan aji nayi ƙawance da ita in bata zo ɗaya ba sun jima basuyi tsegumin ba suje suyi tayi sunfi so kowa ya zama daƙiƙi kamar su"
"Kedai ki dage babu ruwan ki da kowa kiyi abun da ya kai ki" ummi ta sake jadada mata.
"in sha Allah, ummi na"
Lokacin Abdu ya kuskure baki ya zubar yana murmushi ya firta ma fateemah "Kinji dai Abin da ummi ki tace in wani abu suka miki akwai nagaba da ku babu ke babu É—aukar doka a hanun ki, kuma maganar makara ki dinga shiryawa da wuri koni in narigaki ko ummin Ki tashi zan dinga É—ora miki ruwan wanka karaya kuma ko batare damu ba ki karya kiyi tafiyar ki"
"toh Abdu na Insha, Allah ya ja min da kwanan ku badan nafi kowa ba ya Allah" ta ɗaga hannu alamun roƙon ubangiji.
Ummi da Abdu suka mata murmushi suka amsa mata a zuciyar su suna jin wani abu agame da Æ´ar tasu tilo a yanzu, wanda Ada sun mallaki yara mata har uku lafiyayu har Suka girma suka Aurar da su har sun haihu a gidajen auren su dukan su biyun sai Autar su fateemah kawai yanzu.
Ranar Juma'a ma su fateemah da suka koma school duk saurin ta a makaranta ta sami firdausi, haka suka sake zama tare har aka tashi suka tafi gidajen su.
Ranar Asabar da sassafe fateemah ta shirya ma makarantar tahafeez É—in su su a
Hanya suka haɗu da lubna Ahmad ƙawarta suka ƙarasa, suna zuwa suka bada hadda aka ƙara musu suka biya su hadisai kafin aka tafi break.
Ana shirin komawa break ne taji wani mugun abu ya mata dabaibayi mai kama da idanun kura a jeji da idan tasa maka arwa ko motsi bazaka iya ba ta ƙafar da kai a wajen kenan, itama kasa ɗogowa fateemah tayi ta fahimci wani mugun ido mai cike da tasiri ne ya mata ɗaurin huhun goro, Gashi ta kasa ɗagowa bare ta tabbatar, sai da lubna ta kamo hanun ta, ta samu kuzarin bin ta suka wuce ba tare da ta san me ya faru ba.
Har aka tashi suka tafi gida su huɗu da ƙannen Lubna, bilkisu da shema''u suna ta hira a hanya, dake unguwar su ɗaya sai ƙannen sukayi gaba ma suka barsu, lubna ta tsaya ma fateemah labarin wani saurayi da tayi Abban ta ya hanata, Ance yace ba yanzu ba fateemah nata bata shawarar bin umarnin iyaye dan ganin daidai a rayuwa.
08134624555
[29/03, 6:49 pm] Maman shaheedðŸ˜ðŸ¥°: *RAI DA BURI*