Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 3 of 5
PAGE 3
BY
MAMAN SHAHEED
Paid Book...
Ga Account ɗin da za'a biya 👇
3108794095
Fatima Abubakar
First Bank
Shedar biya 👇
08134624555
Ko Arewapen karatu mai fakasiti (capacity) ðŸ˜
Gidan su fateemah gidane madaidaici na masu ƙaramin ƙarfi, suna zaune lpy da Maƙotan su, makaratun da fateemah take zuwa duk ba wasu masu tsada bane Nadai ɗan talaka ne mai kwazo da son koyo.
Yau ya kama Lahadi da wuri fateemah ta shirya dan tafiya tahafeez, kafin ta fita ma ƙawarta lubna ta biyo mata suka tafi bayan tayi shara da wanke-wanke dan bata so ta barma ummi aiki.
Bayan sun bada hadda aka musu ƙari, har lokacin break yayi sukaje sukayi suka dawo lokacin ana ta shirye-shiryen sauka da ƴan sauka fateemah na ciki da ƙawayenta.
Bayan ta dawo gida taci abinci ta koma dake wuni suke acan.
Ummi taso ta dinga kaimata Abincin ta hanata dan bata so mahaifiyarta ta wahala akanta na É—awainiyar Kai mata abinci.
Tana gab da komawa ne bayan tazo cin abincin ciwon mara ya turniƙe ta wanda tama manta shaf da lamarin shi ashe tana gab da baƙon watanta ne, komawa makarantar da bata yi ba kenan dan in ya tashi mata baya mata da sauƙi dan ma ba duk wata takeyi ba wani lokacin har kusan wata uku takeyi kafin tayi wani lokacin kuma wata biyu in yazo dai ta kan sha wahala har suma take kafin ta farfaɗo ko ta kusa fita a hayyacin ta, yauma har suman tayi Sai abin Yama ummi daɗi da ya sameta a gida, ta sake ƙudirar aniyar sake mayar da ita asibiti dan ganin likita karo na uku..
Sai da ta sami bacci na wasu awwani kafin ta samu sassauci sai a lokacin ta tuna da makaranta ma, bayan ta yi wanka ta gyara ta rasa yadda zatayi dan akwai karatun da bata so ya wuce ta tasan ummi bazata barta ta koma ba dole ta haƙura.
Har lokacin tashi yayi, lubna tazo gidan su da sauran litattafan ta da ta bari a makaranta.
"ya naganki haka? Ko abun ne?" lubna ta tambayi fateemah.
"hmm bakijini shiru ba, shine y kusa halakani" ta bata amsa.
"wani irin halakawa kuma in da sabo ai kin saba duk da ba'a ba a sabo da wuya, duk da ke É—in jaruma ce ji nake da nice da yanzu sai gawata"
"Hmmm haka dai kika ce da kece ma wataƙil ki fini dauriya"
"ina fa nafi ki, Kedai Allah ya rabaki da ciwon nan lafiya duk da wasu sunce wai sai Aure, to uwar me zesa Sai a auren ze dena ya Dena yanzu mana, nima fa ɗan guntun ciwon da nake fadeela tace min ina Aure zan neme shi na rasa, na tambaye ta dalili munafukar taƙi faɗa"
"ke hawar wani tambaya kike ni banma taɓa ji ba sai a bakin ki kuma in jikina duka kunne ne ban yadda ba"
Lubna ta miƙa ma fateemah sauran litattafan ta "yauwa ustaz Aliyu ya mana karin Arba'una da gulubul maram duk in kin sami lafiya na biya miki iya inda na fahimta in da ban fahimta ba ya biya miki ko kya tsinta a muraja'a ɗan nasan baki da matsala"
"toh shikenan nagode"
"yauwa barin tafi kafin mama ta fara turo min su shema'u "
"yauwa to nagode sosai"
Lubna tama fateemah sallama ta wuce gida.
******
"wanan shine tashi na uku da zan miki daga shi babu ƙari sai dai Ko yaa Abdul yazo ya tashe ki Ko Ammah"
Nihal Najin Mimi ta ambaci sunan Abdul ta buɗe ido da ƙyar ta fara turo baki "Alhudahuda sarkin karatu, kina shiga hakki na wallahi shiyisa jami'a tafi daɗi karatun ƴanci ka shiga lokacin da Kaga dama, ai dan haka na dage sai da aka Mana jumping na 2yrs ɗinan da yanzu bamu shiga jami'ar ba ma da yanzu banyi kyan ganin nan ba ma inajin"
"ke dai kika sani kiyi saɓo ko firta abin da ze iya fitar dake daga musulunci naga hankalin ki na nisa dake wani lokacin, ba dani zakiyi ba sai dai kiyi da bangon ɗakin nan" mimi na gama faɗa ta fara shirin barin ɗakin.
"wai kafirtani kike son yi ne? Mena faÉ—a da, aki kafirta ni? Ba gaskia na faÉ—a ba kinfi kowa takura min a gidanan" nihal ta Mike ta shige bathroom.
Mimi kuwa ta fice ta barta da mitar ta.
"Good morning yah Abdul" mimi ta firta ma Abdul d suka haÉ—u a baban falon su.
"morning sis meemee, kin tashi lpy?" ya mayar mata da kulawa.ya tambaye ta
"lafiya lau"
"ina yarinyar nan bata tashi ba ko?" Abdul ya tambaya yana kanne ido.
"eh toh yanzu dai ta miƙe zata shirya" mimi ta bashi amsa.
"Hmmm, in bata fito ba nan da 20mints ki wuce makarantar ki kuma sai na hukunta ta a gidanan"
"Ok yaya" kawai mimi tace.
Suka zauna a dining zasu fara break Kenan, sai ga Ammah da Dady sun sauko.
Da sauri mimi ta fara gaishe da Dady da girmamawa da shaƙuwa irin ta ƴa da uban ta, kafin ta juya ta gaishe da Ammah ta amsa da walwala atare da ita har tana shafa kan mimi tana sa mata albarka kafin suka, zauna dan Dady yau a falon ƙasa yake son yin break da iyalan shi.
Dady har ya buɗe baki ze tambayi nihal, kawai ya hango ta tana tahowa, Abdul ne yayi wata muguwar ƙwafar da sai da kowa ya kalle shi, Ammah ta mai wani kallon kafin ta firta "akwai wani Abu ne son?"
"a'a" kawai ya bata amsa ya fara haÉ—a tea.
Shiru tayi badan ta yadda ba, har nihal tazo Ammah ta fara gaisarwa ta rungume ta Kafin ta koma kan Dady ta mai side hug "morning Dady"
"morning daughter, Sai Yanzu aka tashi?" Dady y tambaye ta.
"eh Dady baccin ma bai ishe ni ba" sai muryar Abdul taji yana firta mata.
"ko zaki koma? Akwai wanda ya miki dolen tashin ne?"
Shiru tayi sai sum sum da tayi ta fara neman wajen zama ba tare da ta amsa mai ba, shi ko ya tsare ta da idonduna.
Tana son gaishe shi mata kasa sai da ƙyar ta iya firta "yaa Abdul Ina kwana?" tana turo baki tana kallon Ammah da ta haɗe rai.
"da ban kwana ba zaki ganni" da sauri ta fara haÉ—a tea, Dady yana ta kallon su yana murmushi, Ammah na haÉ—a mai abin da ze karya da shi.
"son yi mata ahankali ko dan health É—inka kaji? Ka dena sa damuwa kowa a ranka"
Shiru Abdul yayi sai amsawa da yayi da kai kawai dan haushi nihal É—in ta bashi.
A haka har suka gama Dady ya fita tare da rakiyar Ammah da Abdul sai su mimi da suka wuce bayan Dady ya tafi, gidan ya rage daga masu Aiki sai Ammah d Abdul É—inta.
"Ammah Na kunyi maganar da Dady?"
Ammah taba Abdul Amsa da "son yace abar maganar sai ya dawo sai muyi, yace kuma dole yayan ka ya sani shima muji amincewarshi Ko rashin Amincewar"
"Ammah!"
"Abdool!" itama ta kira shi kafin ta É—ora da "ka bari zamuyi maganar anjima kaji?"
"toh Ammanh" ya amsa da bin umarnin ta.
Kafin suka shiga wata hirar.
Abdul nata chart a wayar shi da yayan sa "haba yaya munyi missing É—in ka fa sosai"
Broh H
"me ka rasa da bana kusa da kai?"
Abdul.
"kai yaya ganin ka ne kawai, irin innayi tsokanababu mai tare min" sai yasa tura mai sticker dariya.
Broh H.
"kayi tsokanar ka mai lasisi kai da kake da Fahaad har wani ni kake nema?"
Sai da Abdul yayi dariya sosai kafin ya bashi amsa "hakane fa kuma fa yaya"
Broh H
"ya nihal fa tana ta halin koh da sauƙi nade ce ka Dena biye mata duk abin da tayi ka sanar min komai ƙanƙantar sa, mimi bani da case da ita, karatu dai sunayi sosai yadda ya kamata ko?"
Abdul.
"eh kasan ba'a rasa ta da cases Mu Ai itace ciwon kanmu a gidanan, mimi ko normal baiwar Allah"
Broh H
"me da me tayi ko ta sake gigin kawo wani mai tsautsayin ne gida?"
Abdul.
"a'a kawai dai ka share yaya ba wani big case bane sai nasu makara ko yau mimi ta rigaya shirin Islamiya, ga raina mutane in taso wulaƙancin"
Broh H.
"OK banni da ita zanyi magana da ita in sun dawo, inaso ka karɓi wayar ta kamin investigation akai in and out dan kanta Yana rawa a university Nan bawai dan Ina zargin ta ko tunanin zata aikata wani abu ba sai dan karta tara banzayen contacts a wayar ta Ko chart da kowa, Har da ce min wai na sai musu mota fa last week, yarinyar Nan Ko guda ɗaya ce ita da mimi, Nace to ta bari sai ta zama Ammah wacce ta kawo ni duniya ba dan naga kamar umarni taso bani, shine bata sake maganar ba har yau.
Dariya kawai Abdul yayi da, kafin ya amsa mai da "Hmmm ai kanta yana hayaƙi yarinyar fa kaine maganin ta Nifa ma fa saboda su Dady da Ammah nake rabuwa da ita da na motsa saboda issue ɗin ka, ni wani lokacin bani jin daɗi ma sai naga kamar mai wata muguwar lalura ake kallo na, Alhalin lafiya na qalau ta kowanne fanni yanzu dai kam"
BrohH
"kai dai ka dena biye mata, kuma ba kallon mara lafiya ake ma ba, ai koni kama fini lafiya ƙanina tunawa suke da baya da abin yaƙi ɓace musu Amman lafiyayen mutum ne kai Ai ƙanina"
"yauwa yayah Kaine Kawai kake kallo na a haka shiyisa raina fansa ne a kanka, luv u so much my nakusa da ran, Bayan Dady fa sai kai wallahi Allah" sosai kalaman yaman Yama broh nashi daɗi kuma dama dan yayi farin ciki ya firta mai, dan suna ji da junan su jini ɗaya ba wasa ba yana kyautata ma ƴan uwanshi gaba ɗayan su,baya Shayin musu komai duk abin da suke so ze musu ko nawa ne ze iya kashe musu duk shi yake ɗaukan nauyin su Dady kawai ƙara musu yake.
Bayan sun gama chart ɗin sukayi sallama saboda brother nashi ze shiga office,a ƙasar da yake.
Murmushi ya dingayi bayan yaba Ammah labarin yadda sukayi da Yayan nashi tana ta musu addu'a da É—orewar zumuncin su da yadda suke kula da junan su har iya rai da mutuwa, kafin ta koma kan mimi da nihal.
Da yammah da suka dawo nihal ce ta fara shigowa babu ko sallama ta buÉ—e falo waya a kare a kunnen ta da alama waya take.
Bata yi aune ko saurare ba taji Ance "fita ki koma lokacin da kika koyo sallama sai ki shigo, fita nace!" ya firta mata da tsawa.
Da sauri ta katse wayar dan kashewa ma tayi gaba É—aya jiki na rawa dan batayi zaton yana falon ba, Ammah na jin su da kallon su.
Komawa tayi bata da zaɓi har mimi ta shigo bakinta ɗauke da sallama suka amsa mata da sakin fuska ta nufe su ta musu sannu da gida kafin ta leƙa su baba A'ee a kitchen ta musu sannu, har lokacin nihal bata shigo ba.
Sai da ta gama tura baki da mita kafin ta shigo bakin ta É—auke da sallama, zata wuce É—aki Abdul ya sake ce mata "ke zo nan!"
Zuwa tayi tabi umarnin dole,hannu ya miƙa mata, ganin bata gane me yake nufi ba, ya firta mata "bani wayar ki keda kuke waya da har kike mantawa da sallama kamar ba ƴar musulmai ba haihuwar musulunci?"
Da sauri ta fara "laa yaya nayi fa kawai aciki nayi, kuma wallahi..." be bari ta ƙarasa ba ya miƙe yana sake miƙa mata hannu, da sauri ta ɗora mai wayar.
Ya karɓa yaga akwai security akai ƴa miƙa Mata buɗe min, da face lock ta buɗe ta miƙa mai, ya koma ya zauna ya fara duba kiran da ta gama, tasan tana da gaskia a wayar ta dan sun kurɓi ruwan da madarar Tarbiya Amman sai taji ƙirjinta na dukan tara-tara bama uku-uku ba dan ba abin mamaki bane ta taka ruwa ya Abdul yace ta tada ƙura, haka take kallon shi.
Yana dubawa da mintunan da ta ɗauka tana wayar yaga da ƙawar ta suke wayar yabi contacts ɗin ta tsaf babu wani abu da ya gani na rashin gaskia tun tana jiran shi har ta tafi ta barmai wayar, sosai ya lalube wayar har chart ɗin ta be kamata da laifin komai ba, kafin ya ajiye wayar a kusa da shi, suka fara hira da Ammah tana tambayar shi ko yaga tayi wani abu ne? Ya bata amsa da.
"a'a kawai dai daughter taki ce Ammah sai ana sa mata ido lamarin nihal in kin koma ummarah ki fara jefata a addu'a first kafin mu biyo baya" ya firta da gaskia yar shi har ranshi.
Dariya Ammah tayi kafin tace"toh Ai tare zamu har su Kaga kenan kaima, aka tayani itama sai tama kanta, dan ina tunanin Dadyn a nmai Alƙawarin kujera uku Sai yace ze cika biyu mu tafi tare, har yayan ku yaji yace shi ze biya har shi ma zamu haɗu acan, Kaga ko wanan maganar ita kaɗai ce bata sani ba dan da ta sani da ta ishe mu da surutu ƙawayen ta kuwa da sun fara mana suntirin tayata murna da zuwa tsegumi, mimi Ko Shiru kakeji Har masu aikin gidanan na sanar musu shiru nasan babu mai yayatawa itako na Barta a duhu"
"good Idea, Ai nihal ɗin ce dafa yanzu har maƙota sun shigo tunda ita kowa naka ne ga alfahari da arziki da nihal takeyi kamar ba ƴar gado ba kin taso a Abunan Amman kamar sabon shi ga, ni ai dan kince in Dena ce mata nafison mimi ne da na tattara ta nasa sata a kwandon shara, toh jini ɗaya ma baze barni ba da inada yadda zanyi da na maida ita kamar mimi to bani da wanan ikon, nima ai baki gayamin ba Ammah Sai Yanzu? "
Dariya Ammah ta mai" toh ba gashi ka sani ba, kuma ai nasan zaku yi maganar da dadyn ka Ko yayan ka ne shiyisa "
" haka ne to ya manta ko maganar ce bata zo ba kuma addu'a kam zata shashi kamar dan ita zamu tsabar addu'a, tafiyar fa zatayi ma'ana Ammah musamman da Naji da yayah"Abdul ya firta.
"sosai ma kuwa In sha Allah, ya karatun ka kuwa kun gama presentation É—in?" Ammah ta tambaya.
"mun kusa dai Sai week É—in nan in Sha Allah, ga project akwai fa aiki" Abdul y nuna alamar kamar ya gaji yana yamutsa fuska.
"toh ya za'ayi sai addu'a ai, Allah ze dafa Nadai gayama ga uncle D Nan duk wani taimako da kake buƙata shima ya gaya ma ga abokanen yayan ka kai ɗan gata ne ta ko ina baka da case nafi son ƙoƙarin Kane Ma dan Dama Kai mai ƙoƙarin ne da kana kwance za'ama komai toh nafison kaci gumin ka, ƙwazon ka ya baka komai sai Allah yasama abun Albarka Amman babu hanyar da bamu da shi"
"hakane Ammah shi yisa Nima bana kallon wanan nake abuna wani lokacin na samu mafita ta da kaina ba tare da su ɗin ba, Amman in wani abu ya gagara dole zan taɓo su musamman a final year ɗinan"
"hakane Allah ya taimaka, Ina Alfahari da ku ai, ko zaman mu a America kunyi gogaya da turawa baku zama marasa hazaƙa ba duk da kuna yara ne bare yanzu, Komai baze gagare ku ba Insha Allah"
Sun jima suna hira kafin suka tafi gabatar da sallah magrib, akaci abinci dare har lokacin wayar nihal na gurin Abdul kira kuwa ƙawayen ta sun kira kusan mutum biyar sai namiji guɗa ɗaya da yaga ansa Hafiz grp dsc Sai ya fassara abin a (group discussion) Kawai dan Har ɗagawa yayi sai yaji ya fara mata maganar group Assignment da aka basu yayi shiru kafin ya katse kiran.
A ranar be bata wayar ba gashi tana son amfani da kayan ta dole ta zuba ido sai mita da take tayi, mimi na ce mata "ai ba anan zakiyi ba kije ki same shine"
Taƙi kulata ta nemi mimi ta bata Aron wayar ta, mimin ta hanata Wai bata son gayyar ƙawayen nan nata masu katin samari su dameta awaya dan in suka fara waya basajin Kati dake basu suke saka katin ba har su dami mimi.
Washe gari da zasu school shine ta mai gaisuwar mutunci ya jaja Mata kunne da gargaÉ—i mai yaji ya bata wayar har da mai godiya dan ta zata baze bata a ranar ba sai taga ya bata.
Tasha tsokana kuwa wajen mimi Har tana ce mata "mai ladabin kura" nihal ta murguda Mata baki, zata mata rashin kunya ta murÉ—e bakin.
A shool Kowa department É—in Shi da ban sbd course É—in Kowa daban Kawai time É—in lecture É—in Su ne yake zuwa kusan É—aya ko wani ya jira wani Amman da karatu ya fara zafi wata ran dole su tafi daban daban.
Nihal ta gama lecture ɗinta na 11:30am sun fito da bilkis da su dinner suna magana kan karatun su sai Faisal Abokin Abdul ɗin Su yazo wucewa ya gansu sai ko ya Tako har inda suke gefen wani hall"ƙanwata ya lecture? "
" yah Faisal Ina wuni Kwana biyu, Alhmd, mun fito sai 1 kuma zamu shiga"
Sai ƙawayen ta suka fara gaishe shi, duk yabi ya amsa, suna tsaye a haka sai wayar Faisal ta fara ringing alamun kira ya shigo ya ɗaga "Hello yaseen Abdallah ya Ne?"
Tun da nihal taji sunan da Faisal ya kira ta bada attention É—inta a wayar da suke kamar da ita ake.
"OK, Ina kusa da hall É—inan Inda ka sameni shekaranjiya"
Wani blushing nihal ta fara ganin kar a gano ta sai ta seta nutsuwar ta, har Faisal suka gama waya tana jin su, haka kawai yaseen Abdallah yake birgeta Kawai abun da yayi katanga a tsakanin su shi balaraben Libiya ne aiki ne ya kawo su Nigeria uncle ɗin Shi ya buɗe kamfanini yaseen ɗin yake kular mai da wasu inya gaji ya tafi yawo gashi ya gama karatun shi tun a Tripoli bare yace karatun Nigeria ne yake birge shi har masters Ne da shi yayi karatun shi kashi kashi yama girmi Faisal ɗin Kawai abota sukeyi Mai tsafta Saboda Faisal ɗin ƙwaro Ne kwanyar sa tana ja yana final ya ɗin shine Yanzu na masters to Abdul ya bashi alhakin kula da su mimi ne kafi ya gama shima ya dinga taya shi dan duk makarantar su ɗaya, karatun kowa ne daban.
Suna nan babu jimawa yaseen yazo ya parka Wata Benz É—in motar da ta tafi da imanin su nihal gaba É—aya dan kowa sai da yayi addu'ar (Allahuma arzukuni sayyara) Yana fitowa kallo ya koma kanshi maza da matan da suke wajen gashi yadda ya fito a wani haÉ—aÉ—en balarabe mai kwarjini da haiba ga kyau na
Asalin Larabawan Libiya,Amman in anso ganin munin shi za a fahimci yana da ɗan gatso a haƙoran shi.
Ganin ya nufi wajen su nihal sai kallo ya koma kan nihal a gulmar student Wajen nihal yazo, kowa da abin da yake tofawa, nihal kuwa class É—inta ta tsaya tatarowa Har ta É—auke ido daga kanshi dan kar raunin kallon shi ya shagaltar da ita.
Yana ƙarasowa yaba Faisal hannu suka gaisa da larabci dan Faisal ɗin ƙwaro Ne kusan yare uku ko huɗu yake ji kuma ƙwarare ne dan ƙwaramcewar shi ne yasa suke abota da Abdul dan shima yana jin duk yaruka ukun nan da shi da yayan shi na America, sunajin larabci, turanci da French ga Hausa yaren su na gado, saɓanin su nihal da suka ƙi dagewa a jin larabci da yi sosai har su goge da French gara mimi ma sukanyi French da Dady larabci Kuma da Ammah dan tasan addini sosai fiye da boko,duk da hakan ma suna iya magana da larabci sosai kawai basu goge bane musamman nihal.
Faisal suna gama gaisawa da yaseen ya fara cema yaseen shifa cafeteria zeje dan Ko break beyi ba, sai ko yaseen ya kalli su nihal ya fara musu magana da larabci alhalin yana ɗan jin Hausa Faisal Ne Kuma ya koya mai har waƙar Hausa yake bi ya ɗora a social media musamman TikTok.
Kaf cikin su babu wacce tasan me ya faɗa bare su mayar mai da amsa sai ido suke Rabawa kamar shege a rabon gado, nihal ce tayi ta maza ta bashi amsa cikin kwainane da tace muryar ta da ƙalƙala irin na larabawan asali duk dan ta birge shi sai abun yazo a daidai taji me yace har ta iya mayar mai.
Hakan ba ƙaramin birge yaseen da Faisal yayi ba Har ƙawayen in suka cire hassada, ganin haka har yaseen ya ƙara janta da hira da larabcin duk suna jin su kafin suka juya turanci cikin salo da iya sarrafa harshe ta dinga mayar mai, dama yasanta Sanadin Faisal Amman tsakanin su gaisawa, ƙarshe dai dole yaseen ya gaya ce su zuwa rakasu cin abinci a cafeteria su bilkis Kamar Kar suje Sai suka ga su zasu daki gurbi, nihal Ko Sai da akaja aji Faisal ya Mata magana Kafin ta yadda suka tafi, da suka tafi zasu shiga motar ma students Sai kallon su ya koma kansu kamar suyi me, yaseen daga nesa ya cilla ma Faisal Makulin motar ya Cafe a wani style Kamar yadda ƙwararen gola yake tare ball, har sai da abun ya birge wasu suka murmusa, yessen da kanshi ya buɗe ma su nihal bilkis ce ta fara shiga sai diner Sai nihal a ƙarshe kafin yaseen ya rufe marfin motar ya shiga wajen me zaman banza, faisal ya ja mota a skwane ya shana su be tsaya ko ina ba sai cafeteria mai capacity, suka buɗe suka fito.
Faisal ne ya zaɓa musu inda zasu shiga dan yasan yaseen da tsagina gini koshi ya bashi abu ba komai yake ci ba.
Da Taimakon yaseen ɗin suka shiga suka kama tebir ganin ɗazu kamar su bilkis sun muzanta shi kuma bada manufa ya musu ba sai ya musu magana da turanci da Hausar sa ta gwarawan Larabawa da suka ari Hausa,yana tambayar su abin da zasuci kowa ya zaɓa.
Kowa da ƙarfin gwiwa ya zaɓa sun san ba ƙarya bare babu a tare da yaseen sosai suka zage dan yagar rabon su maybe ma ba sake ganin shi zasuyi ba
[01/04, 8:38 am] Maman shaheedðŸ˜ðŸ¥°: *RAI DA BURI*