Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 5 of 5
PAGE 5
BY
MAMAN SHAHEED
Paid Book...
Last free page... 😔
Ga Account ɗin da za'a biya 👇
3108794095
Fatima Abubakar
First Bank
Shedar biya 👇
08134624555
Ko aje Arewapen...
_Gidan mlm Sadiq Abdu_
Asalin Kakanin Shi ƴan Chadi ne, iyayen sa sun rayu da Kakanin shi ba sosai ba daga baya suka koma wani ƙauye nesa da garin sakamakon wani abu da ya taɓa faruwa a dangin su, har aka samu rabuwar kai kowa yake kusan zaman kanshi.
Malam Sadiq Abdu da wasu suke kira shi da mlm Abdu kawai har sunan ya bishi musamman da ya sami canjin gari.
Daga baya mlm Abdu ya rayu daga shi sai iyayen shi dama su biyu suka haifa shi da ƙanwar shi da ba san inda ta fi ba tun wani mamaya da aka taɓa kawo ma garin babu tabbas tana raye ko bata raye Har iyayen shi suka haƙura suka rungumi ƙaddara.
Shima dama dun acan garin ya fara fuskantar ɓacin rai da kunci da camfe camfe saka makon Yara mata da Allah ya bashi babu namiji ko guda ɗaya
Shi ko da mai É—akin shi ummi habiba sunji sun gani har Kakanin su suna son yara matan ahaka bayan su huÉ—u a duniya babu mai ba yaran kulawa sai tsangwama da kyara da canfi a haka suka taso har suka fara tasawa.
Zaman be musu rashin dadi basai da aka sake samun mace matsayin auta, Kakanin sun rungumi yaran sosai su suke tausan ummi da Abdu Har suka sami nutsuwa.
Ana tsaka da haka wata rana maman Abdu ta rasu sakamakon gajeriya rashin lafiya sun shiga cikin ruɗani sosai lokacin gashi su Khadija da Hindu sun fara tasawa girma ya fara zuwar musu sai ƙanwar su ƙarama.
Ganin irin faɗi tashin da Abdu yake baban shi ya tattara duk wani abu da yake da shi yaba Abdu akan yabar ƙasar yaje ya gina kanshi da iyalin shi, Abdu ya dinga kuka da ummi suka nuna bazasu iya tafiya su barshi ba, shi kuma gani yake in Abdu yaci gaba da zaman wajen baze taɓa samun ƴa'nci ba da yaran shi wata kila ma suƙi auruwa duk da kuwa kyan da Allah ya musu musamman ƙaramar da aka haifa ga Tarbiya iya Tarbiya da nutsuwa da suke da shi Amman banu mai mu'amala da su sai yasu yasu kawai.
Ƙarshe dai sai da baban Abdu wato Abdullahi mai ainahin sunan Abdun ya Sai da gona da gidan da ya malaka ya sake danƙaaa Sadiq kuɗin sanan ya karɓa yana kuka, a karo na ƙarshe ya nemi da Sadiq ɗin ya tattara iyalin shi da su bar gari suyi nesa da garin ko barin ƙasar ma.
Sadiq tun baya so har suka karɓa da ya tuna abubuwa da dama ga son ganin ya inganta rayuwa da Ilimin yaran shi gatan shi da Allah ya bashi.
Amman be bar garin ba sai da mahaifin shi Abdu suka doguwar tafiya ta hanyar abokin shi suka sauka a Jigawa suka fara ganin garin da yanayin komai na garin har ya ɗan taɓa noma a garin ya fara sabawa da mutane, an mai tallan gona da gida duk be siya ba tukunna sai baban shi ya fara tashin lafiya hankalin shi yayi matuƙar tashi, sai da suka kai shi asibiti aka dinga jinya, Amman dake Allah yayi ƙasar shi a Jigawa take anan Allah ya karɓi ran shi, Sadiq da ummi sunyi kuka har su Naja Khadija gani suke kamar gatan su ne ya ƙare yanzu basu da Masoya sai tsirarun yan Jigawa da aminin mahaifin shi da yake jan su yake tausayin su dan yasan komai akan su.
A shekarar Sadiq ya cire amfanin gona sosai har ya siyar ya sami Alkhairi.
Ana haka Allah yasa Sadiq ya fara shiga garin Kano tun yana shiga da kasuwanci har wasu abubuwa suka fara ribatar shi yaji nan ne ya dace yazo ya gina rayuwar shi da Ilimin yaran shi mai tushe bawai dan Jigawar babu Ko bata dace ba kawai dai shi dai yaji kanon ta birge shi ne fiye da har ƙasar haihuwar shi da ya baro.
Koda ya nemi shawarar aminin shi be Mai baƙin ciki ba ya bashi goyon baya har dashi aka wuce mai gaba suka shiga kanon har aka sami madaidaicin gida suka shiya Sai aka sami wani shago shima da haya suka nema sai aka nuna musu sai dai su siya dan siyar da shi za ayi suka siya kuwa.
Aka ɗan gyara gidan ranar da aka gama gyaran gidan su Sadiq Abdul da Malan Musa a gidan suka kwana suka sake shiga kasuwa suka ɗan sisiyo abun buƙata na gidan suka sai katifu guda biyu suka saka a ɗakuna biyu da sauran kayan amfanin gida daidai ƙarfin su, dan basu Da komai sai abun da suka samu a Jigawa dan Jigawa sun musu karamci bazasu taɓa mantawa da su ba inda aka fara nuna musu so, tatali, kulawa da ja ajiki musamman mlm Musa da iyalan shi biyu da dangin shi dole ce kawai tasa zasu bar garin.
Da iyalan malam Musa aka taho rako su har da wasu tsirarun yan garin dan an saba, har Kano suka rako su ana ta koke koke masu kuka, wasu daga iyalan malam kala kamar amaryar shi mmn nusaiba da su Rafi'at duk sai da suka kwana a kanon an zama kamar Æ´an uwa sai washe gari suka tafi da niyar duk ai basu rabu ba, asu dinga ziyartan junan su.
Malam Sadiq Abdu da Taimakon malam Musa suka zuba kawayan hatsi a Shagon da ya shiya, ya fara gwada sana'ar awo.
Ahankali ya ƙara wasu abubuwa a gidan, ganin ana samun wuta sai ya samu ya sai musu kayan kallo da wasu kujeru na hannu mai L shape suka saka a baban falon gidan, su Nana Khadija da Hindu ya samu ya fara ciku cukun mayar da su makaranta, nan da nan kuwa aka karɓe su suka fara daga sss one dan duk tare suke tafiya.
Ya sami Islamiya ma ya sasu mai kyau sai yaji hankalin shi ya kwanta ya fara mu'amala da ƴan unguwar suma sun riƙe shi da amana.
Ana haka su Nana Khadija da babu mai zuwa wajen su sai ranar tayi mafarkin Wai anzo Ana kamar gasar aure maza kala kala a ƙofar gidan su har sai sun zaɓa ita da Hindu sai suka ji kamar wani ƙulli ne ya kunce wanda da ya musu dabaibayi, tana farkawa ta gane mafarki ne tayi addu'a ta fara sanar ma ƴar uwar ta, aiko itama ta sanar ma ummi, ummi abin ya bata mamaki har Abdu Amman suka barma Allah komai ummi tayi sadaka da kyakyawan niya akan koma meye Allah ya nisanta su daga sharrin dukkan abin halitta.
A ranar ba a kwana ba sai da saurayi ya biyo nana Khadija har gida abun ka da bata saba ba ko kare be taɓa shinshinata ba sai abun ya mata wani iri taƙi kula shi ma kamar ma tsoro yake bata dan yadda yake mata kamar yaga wata sarauniya kamar ya sace ta yake ji, da ƙyar ta mai ƙaryar an mata miji suka rabu badan ya haƙura ba.
Bayan sunyi jarabawa ss two suna da ƙawayen su daidai gwargwado, ganin yadda ƙawayen suke da samarin su sai yasa suka fara gogewa akan tsayuwa da saurayi mai mutunci da kula su, shima sai da ummi tayi da gaske da Taimakon nasiha da shawarar ta Hindu d yaya Khadija suka fara tsayuwa da samari.
Lokacin ƙanwar su fateemah tana primary, gashi suna son ta kamar su haɗiye ta itama ta saba dasu sosai ita tasa ma Sadiq sunan Abdu ma har ya bishi itace ta juya sunan tun tana yarinya akan shi har yayun suke dariya suke faɗa har ya zauna a bakin su.
Ana tsaka da haka biki ya taso a Jigawa bikin aure babar yarinyar malam Musa, har anko malam Abdu ya ma su Hindu suka tafi har shi Jigawan da tsarabar su ta kular abinci da wasu kofuna da plate duk na amarya, iyalan malam Musa kuwa sunji daÉ—in zuwan su, nan da nan aka basu É—aki guda masauki, Æ´an gari ma suna ta murnar ganin su sunyi kyau sun zama cikakun Æ´an mata.
Akayi biki da duk wasu al'adu na bikin lafiya suka koma cike da tsaraba, har suna jin cewa ko yan Jigawa sun ishe su zama dangin su, ayanzu basu da wata damuwa.
Samari fa har Abdu ya fara gajiya da zuruntun su a ƙofar gidan shi dan Abun har mamaki yake bashi badan yasan shi da matar shi basu da irin shige-shigen nan ba da sai yace "ko maganin farin jini suka ba yaran nasu?" ganin abun ya fara yawa ya fara hana su fita.
Daga baya yayi shawara da ummi da mlm Musa da wani abokin shi anan kusa da shi da suka saba akan zece su fidda mji Kawai yayi musu aure dan tsayar da duk wani saurayi.
Suna gab da shiga aji uku na babbar sakandiri, yace "Acikin ku inaso kowacce ta zaɓi wanda taga zata iya rayuwar aure da shi sai yayi magana in ya shirya sure Sauran Kuma dukku salame su"
Suka ce "toh Abdu in Sha Allah" suka zaɓi wanda suke so kuwa basubi dukiya ba duba da har da masu motoci da attajirai a masoyan nasu suka zaɓi samari masu hankali da ilimin addini da na zamani akayi bincike akan su aka ga basu da aibu, aka umarci da su turo suka turo akasa biki suna candy da zarar sun gama makaranta sai aure sai abokin mlm Abdu da kanshi ya salami Sauran samarin ahankali suka Dena zuwa sai wanda zasu aura kawai.
Fateemah ma an fara girma an kusa gama primary anata murna.
Tun da akasa ranar bikin su Khadija mlm Abdu ya É—an shiga damuwa ummi ce ma mai tausan shi akan Ai abin da Allah ya hore mai shi zeyi kuma Allah zai basu mafita ya dena damun kanshi har ya samu ya sami nutsuwa ba sosai ba.
Dama kudin auren su adanawa yayi, a kasuwa inda yake ma duk an sanshi ko bashi ya nema ana bashi dan baida wasa har limanci yana jansu a kasuwar dan yana da ilimin shi.
Lokaci nayi na biki ya samu da abin da aka bashi gudummawa na ƴan kasuwa da na mutan Jigawa masu kara ya samu ya ɗan karɓi bashi kaɗan yayi musu kayan ɗaki dashi da ummi da yaran sukaje kowacce ta zaɓi daidai ƙarfin shi, ya siya suka taho da su mota biyu aka zubasu a wani ɗaki da babu komai aka kulle.
Duk abu na talaka dai sun siya wasu kuma an basu gudummawa dan ummi ma ta fara zuwa Islamiya har tayi tsirarun ƙawayen Har sun Bata gudummawa.
Baƙin Jigawa suka zo ɗaki biyu aka ware musu a gidan maza aka basu ɗakin zaure suka sauka Gashi sun taho da kayan abinci babu abin da aka nema haka akayi bikin lafiya taro ya watse amare sunga ƙara da gata na al'ummar gari haɗuwar mutunci aka kaisu Gidajen su Sunata kuka ummi Har taya su tayi fateemah auta kuwa da taɓara wai itama a gidan su zata zauna duk da ta fara girma itama.
Bayan biki ahankali mlm Abdu ya fara biyan bashi d yaci har ya gama biya har wani kyau yayi sai ya fara gina fateemah duk abin da ya gani sai ya siyo ma fateemah indai kuɗin shi zai kai ko ya namu na masu ƙaramin ƙarfi dan ita kaɗai ta rage mai.
Khadija da Hindu suna zaune a gidan su lafiya da mazajen su wata iriyar soyayya suke nunama junan abin Har ya kusa ba mutum tsoro gashi sai Allah yasa dangin mijin duk suna son su dan yaran mlm Abdu suna da shiga rai kamar wanda ake koyama rayuwar zama da kowa lafiya shi yisa basu da matsala da kowa ko abokin faɗa basu da shi tun barin su Chadi basu sake sanin wani abu wai baƙin ciki ba sai farin ciki da samun ci gaba.
A shekarar su ta farko suka haihu Khadija ta sami ɗa namiji akasa sunan Abdu suke kiran shi musaddiq Hindu ma Namiji ta haifa Sunan uban mijin ake kiran shi Areef, akayi taron suna lafiya, daga baya kowacce ta koma koma gidan ta dan tsirar su sati biyu ne da haihuwar fateemah tasha renon yaran, masu jegon sun sami kulawa daga dangin miji da mazajen nasu ga abun arziki daidai ƙarfin su.
Tun da aka sami yaran nan kusan duk bayan sati biyu sai fateemah BINTU taje gidajen yayun Nata É—an tayadu raino.
Fateemah har an shiga jss one an fara zama manyar yara tana ta karatun ta duk ranar da yayun ta suka zo gida sai ummi tayi da gaske take tafiya makaranta boko da Islamiya.
Yaran su nada shekara guda mijin hindu ya ɗauke su sukayi tafiya sakamakon kasuwa da ta tsaya mai sai abokin shi ya ja shi zuwa kudancin ƙasar nan, har sai da suka shekara biyu.
Duk sai Hindu da Æ´an uwa da suka ji babu daÉ—i sai waya da sukeyi kawai, lokacin fateemah an shiga jss 3.
A shekarar su Hindu suka dawo gari akan yaci gaba da kasuwancin shi a gida kamar yadda iyayen shi suka nema.
Har sunje biki Jigawa gaba É—aya gidan akwai wani da za a sake na nusaiba akan su ummi bazasu sami zuwa ba sai dai su Hindu da Khadija da fateemah sunce su zasu koma, basu koma ba ma aka daga bikin sai wata shekarar.
Rayuwar gidan mlm Abdu cike da jin daɗin yaran shi na zaune lafiya sai autar shi kawai, sai Hindu da ta sake samun ciki wata yara ta haifi yarta macce nimrah, lokacin kuma Khadija ta sami ciki mai laulayi har sai da fateemah taje ta ɗan zauna mata anan ƙanin mijin ta yaga fateemah ya fara nuna alamun so Khadija ta dakatar da shi ta nuna mai karatu zatayi kar ya fara ma ta dai mai bayani dake yana da fahimta ya haɗiye mugun yawun shi.
Yaron Hindu ya fara wayo, cikin Khadija kuma yana wata shida tafiya biki Jigawa yazo suka dinga zumuɗin zuwa bikin nan har anko Khadija ta musu da su Abdu sukace su zasu tsaya a bikin Maƙotan su na abokin malam Abdu, fateemah ma suna da karatun musaɓaka a Islamiya tafiyar tata a ƙila waƙala take su kuma yayun sunfi son su tafi da ita.
Mijin Khadija har ya hana ta tafiya bikin da yaga dai tana son zuwa sai ya barta, ranar suna zaune sai tace "Abban musaddiq da gaske fa in baka son naje zan iya haƙura, naga kamar bana hankalin ka be kwanta da tafiyar nan ba, sai na haƙura ai baka taɓa hanani ba kana da hujja in kace ba sai naje ba"
Ya mata wani kallon so da tatali ya rungumo ta yana shafa bayanta zuwa gadon bayan ta "toh in kin tafi wace dinga miki tausa a gadon bayan ki? Kinga cikin nan da ciwon baya yazo miki in bani ba wa kije da shi da ze dinga taushe miki bayan har ki samu ki É—an ji daÉ—i acan"
Ƙara shige wa tayi jikin shi "kuma haka ne fa my Dee, hannun ka kawai Naji ajikina nutsuwa yake sani, umm nama fasa tafiya
Kasan kwanakin nan sai na dinga jin banaso nayi nesa da kai kamar wata zata ƙwace min kai, in mun samu kaɗai ci har ji nake kamar kar mu rabu, kuma fa abun kullin a ƴan kwanakin nan gaba yake ƙara yi fa my Dee "
wani hot kiss ya Bata Kafin Yace" wai kina jin yadda nake ji ashe, baki lura bana son nisa dake ba? "
" na lura mana, sai nayi zaton ko buƙata ce take hana ka nesa da ni"wani cakulkuli ya mata kafin yace "da baƙatar ma Amman begen Ki ne kan gaba da wata wutar son ki da kishin ki da yake sake ruruwa a ruhi na na kasa gane ko na meye"
"kace duk abu guda muke ji, to mu haÉ—iye junan mu kawai mu hutu"
"toh muyi hakan in ze yiwu"
Dariya suka sa gaba ɗaya, ranar wani irin faranta ma juna suka shagala da yi hatta girki ranar basu sami damar yi ba fita kuwa be samu yi ya fita ba,tafiyar ma sun kusa haƙura da ita, Amman a ranshi yana ganin in ya hanata be Mata adalci ba, sai ya amince taje kawai, sai da ta tabbatar har ranshi ya amince kafin ta yadda zatayi.
A washegarin ranar Ma ya ɗauke ta a babir ɗin Shi ya dinga zaga dangin shi da ita suna zuwa gidan gwagwo mahaifiyar shi ta karɓe musaddiq, suka sami damar yawon ziyarar su dan taga ga ciki ga yaro sau ta tausaya mata, har inda be taɓa kaita ba ya kaita basu suka goma gida basai sha ɗayan dare musaddiq ma a gidan su ya kwana