A Rubuce Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Rubuce_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 101
Page 11
Iska mai zafi ya furzar daga bakinsa yana miqewa tsaye,kafin yakai ga aiwatar da komai mimi ta kama cikinta
"Abba......yunwa nakeji,tun dazu mommy tace zata dafa mana indomie......bata gama bane har yanzu?" Idanunsa ya zubawa yarinyar,a nutse yace
"Bakuci abinci bane yau?" Kai ta gyada masa
"Eh,momy tace tana jin bacci,kada mu dameta,musha tea,idan ta tashi zata dafa mana,har nawwara ma ta zuba ruwan tea din a qafarta,tayita kuka" lumshe idanunsa yayi,wani abu ya taba ransa,sai ya duqa a hankali tana laluben qafan yarinyar yana son ganin wajen,dai dai sanda yaji an murda qofar an kuma budeta,sanin waye ya sanyashi qin waiwayo yaci gaba da duba qafar nawwaran.
Matashiyar macace,wadda a qalla zata doshi shekara ashirin da takwas ko kuma da tara,wankan tarwada ce wadda kalar fatarta ta kusa juyewa ta baqaqe,banda hutu da jin dadin data samu,mai matsakaicin tsaho ce,tana da 'yar qiba kadan da tudun hanci,idanuwanta basu fiya girma ba,saidai tana da 'yar cikar gira da kuma fararen haqora da suka sake bayyana duhun fatarta.
Sanye take da kayan bacci a jikinta,kanta saye cikin wata hular zaren lilo da qabilu sukafi amfani da ita,zaka tsammaci qarfe bakwai ne na safiya a lokacin,saboda yadda fuskarta ke nuna alamu na bacci,uwa uba kuma sleeping dress din da take sanye dashi.
Tsaye tayi daga bakin qofar tana qare masa kallo,fushi takeyi dashi sanda ya tafi,ta kuma ci alwashin sai yaga fushin nata,saidai tun bai jima da tafiyar ba kewarsa ta dameta,idanuwanta kuma suka damu da son ganinsa,ta ajeshi qololuwar matsayi a rayuwa da kuma zuciyarta,shi din na musamman ne,tunda har yana da qarfin ikon juyata da sauya mata ra'ayinta zuwa wadanda yakeso,abu mafi girma kenan dake haddasa sabaninsu,kowa da alqiblar da yake kalla tsakanin shi da ita,hakanan kowa yana ganin akan dai dai yake.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.