A Rubuce Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Rubuce_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 101
Page 06
"Gaskiya ne,kema kinzo da naki hanzarin,sannan a zahiri cikin musulunci babu auren dole,duk da shi mahmudu yana ganin kamar gata ne zaiyi mata,kuma hakan shine dai dai,to amma kuma duk da haka tana da damar da za'a bata zabi,iyaka idan aka duba ya zamana akwai kuskure ko rashin dacewa a ciki sai a soke lamarin",tana tausayin widad,tasan akwai maqiya da magauta fal cikin rayuwarta,shi ya sanya take a tsaye ga duk wani abu da zaya cutata mata.
Bangaren widad kuwa haka ta yini ta kwana,ummu nata dakon zuwan mahaifinta suyi magana da alhajin,bai shigo gidan ba sai a washegarin da azahar,akayi sa'a alhajin shima yana nan amma yana shirin fita.
Shuru abban yayi sanda alhaji ke masa maganar gami da bashi umarnin janye wancan qudurin nasa
"Alhaji,naso ace an hada abun nan saboda a qarfafa zumunci,sannan yanzun bansan da wanne ido zan kalli isma'il ba(mahaifin mahfood)" murmusawa alhaji yayi
"Akwai dangi da yawa,ba lallai sai mahfood ba tunda jininsu baizo daya ba,kada azo ayi abinda za'a zo daga baya ana dana sanin aikata shi,isma'ila kuwa shi da mahfood din kabar komai a hannuna zan magana dasu" kansa a qasa amma ransa a matuqar bace ya amsawa da alhaji,gami da yi masa godiya da fatan samun qarin shekaru masu albarka da lafiya me dorewa.
Ummu da kanta ta shiga dakin inda widad keta fama kwanciya don yi mata albishir,a kwancen ta sameta,ta janye rufarta tana cewa
"Tashi......ruwa sarkin kwanciya" sake curewa tayi waje daya tana turo baki gaba,don har ta gaji ma da kukan
"Nace ki tashi hakanan, kwanciyar ta isa,maganar aure ce an janyeta an fasa" da sauri ta waiwayo tana kallon ummun gami da jin fitar maganar daga bakinta kamar almara,ko kuma tayi hakanne don ta tashi ta sake?,babanta fa?,wanda baya fadin abu ya canja,wanda baya magana ya sabata,tsayayyen akan duk abinda ya sakawa ransa zai aikatashi,to amma kuma......ummu bata qarya sam sam tasan halinta,fadi da cikawa ce,sannan yadda take qaunarta ta tabbatar ita da alhaji ne suka aikata hakan,sai kawai ta bugo wani tsalle ummu bata ankara ba sai jinta tayi a jikinta ta dane mata wuya cikin madaukakin farinciki.
Murmushi ummu keyi tana jin farinciki cikin ranta itama,tasa hannunta tana banbanreta a jikinta tana cewa
"Zaki qarasani 'yar nema,ashe duka iskanci ne,mitsitsiyarki dake wai kinsan meye auren dole,maza saiki sauka ki shiga bandaki ki wanka ki shirya ki shiga cikin 'yan uwanki" ummu kuwa bata kai qarshen zancan ba ta dire sai bandaki,tayi wankanta sarai,akwai kayan dama da taketa cin burin sakasu,yau kuwa zata gwangwaje kwalliyarta,latifa ta zuba mata abinci taci da kyau,sannan ta tsala kwalliyarta cikin wani lace mai azabar kyau da tsada da ummu ta dinka mata ita kadai,ta zauna ta tsara kwalliyarta dai dai da shekarunta da kuma iyawarta,sai gata ta fito dagwas dagwas gwanin kyau.
A falo ta samu ummu tare da baqin da suka fara zuwa mata yawon sallah,wanda duka 'yan uwa ne da surukai,batulu ce matar baban widad din,haka suke rabawa duk sallah,wata zata fara zuwa gaida ummu dayar ta zauna a gida,washegari ko wata washegarin sai dayar tazo.
Jakarta ummu ta kaba ta zuba mata sababbin kudi 'yan biyar biyar,duk da tasan halin kayarta,qila sai a gama yawon sallar a ci a cinye bata kashesu ba,daga qarshe dasu da wadanda ta samu duka dawo mata dasu zatayi
"Ga barka da sallah ta nan" rungume ummu tayi tana dariya cikin farinciki
"Na gode ummu" sai a sannan ta waiwaya ta rusuna kadan tana gaida batulu.
Can qasan zuciyarta maqare fal da baqinciki da takaicin yarinyar,amma a saman fuskarta kadaran kadaham,tayi qoqarin gyara mood nata ko don ummu dake wajen ta amsa mata
"Yammatan ummu,lafiya lau sai ina?"
"Wajen anty madina zani" ta amsa mata tana yin gaba,duk da qarancin shekarunta,amma kwanyarta na iya tuna wasu abubuwan da suke gudana tsakaninta da matan baban nata,suke kuma kan gudana din,shi yasa dai dai da wuni guda bata marmarin zuwa gidan nasu bare ayi batun kwana,ummu ma ba zata bari ba,koda kuwa babanta yana da muradin hakan.
Kamar ko yaushe chamber ta hadu a sassan anty madina,shigarta wajen kallo ya koma kanta,masu tankwa da yabawa nayi,masu baqinciki suna nasu aikin,ko meye saman fuskarka kusan ta saba dashi,uwa uba ga quruciya da bata sanyata daukan abubuwansu da muhimmanci,fatanta da burinta kawai ta shiga cikin 'yan uwanta ayi mu'amala da ita kamar kowa.
Wunin ranar gaba daya cikin walwala ta yita,sai takejin kamar wadda aka daddaure ayau ta samu 'yanci,sai dare ta dawo sassan umnu,tana gefanta tana bata labarai na abinda suka faru,kowa cikin jikoki na zaune saman carfet suna cin abinci amma ita na nanuqe da ummunta,tare suka ci abinci kafin dare ya miqa su wuce dakin kwanciya.
Sai bayan isha'i a ranar alhj mahmud ya koma gida,har lokacin akwai sauran damuwa da bacin rai a tattare dashi,yayi wanka ya canza kaya,umma dake da girki ya gabatar masa da abinci,sannan ta zauna a gefansa tana sake karantarsa,bakinta cike fal da tambayoyi da kuma son jin qwaqwafi,don tunda ya shigo ta karanci akwai wani abu daya faru.
Ganin shuru yana ta cin abincin baice komai da ita ba,sai ta danyi gyaran murya tana gyara zama
"Amma abbansu fuskarka kamar akwai damuwa,Allah yasa lafiya?" Tsaki yaja yana ajjiye cokalin hannunsa,ya kalleta
"Bari kawai hauwa'u,yarinyar nan ce ta watsamin qasa a idanu,takeson ta kunyatani a dangi"
"Wa fa?" Ta tambaya tana yamutsa fuska,duk da zuciyarta ta gama gaya mata wacece
"Widad mana,qiri qiri yarinyar nan ta fandare taqi mahfood,har sai da alhaji yasa baki a maganar ya dakatar da abun" baki hauwa ta riqe tana sakin salati cikin sake kambama abun,lallai yarinyar shafaffa da mai ce,tana cewa su din akwai yaransu da aka yiwa haka?,kuma suna zaune lafiya lau a gidajensu har kwanan gobe sai tashin zancen
"Yanzu abbansu,lamarin da aka faro zancansa tun yarinyar nan bata cika mutum ba,amma yanzu saboda idanunta sun fara wayewa zata ce bataso?,kuma alhaji shima ya biye mata?,wannan wacce irin tabara ce?,ah to lallai abu ya girmama,billahillazi idan ba'a yi wasa ba gaba sai abinda tace za'a yi mata,idan ba haka ba ran kowa ya baci harda mu iyayenta" fushin abba ne ya motsu sosai akan widad din,kuma dama abinda hauwan keso kenan
"Haba ita din banza?,wallahi bata isa ba,ita ta haifemu ma ashe kenan"
"To tana ganin haka tana faruwa tun yanzu gaba basai abinda taga dama ba?,aure kuma dama ai uba ya isa da diyarsa budurwa ya zaba mata miji,bare wannan da ko minzalin budurwa bata kai ba" shuru yayi yana juya zancan,abun ma sai yanzun yake sake bata masa rai,tabbas bazai barta haka ba,duk da ya sani rayuka zasu iya baci,don ummu ba zata lamunci takura ga widad din ba.
A wannan daren da taimakon zugar hauwa ya kwana cikin tunani,washegari.batulu da hauwan ta bincina mata abinda ke faruwa itama ta dora da tata zugar,sai ya sake hawa sosai
"Banason wannan maganar,ku qyaleni haka" yace dasu daga bisani,ya riga ya gama yanke matakin da zai dauka akan maganar.
Widad kuwa walwalarta takeyi sosai abinta hankali kwancw,tunda ta samu akwa kwance ta daga daurin talala na auren mahfood,bikin sallarta take abunta gaba gadi,koda abbanta yazo gidan bayan kwanki biyu bata kawo komai a ranta ba,batasan cewa yazo da sabon alqawarin bada ita ga ma'aruf,ma'aruf dai,ma'aruf din da kalmar zo na kasheki bata taba shiga tsakaninsu ba,ma'aruf din da tsakaninta dashi saidai ido,saidai bata da labarin wannan alqawarin,domin ummu ta rufe zancan don kada a katseta daga walwalar data samu cikin bikin sallar,ta sakaya zancan bayan ta cewa abba
"Mahmudu ni bazan dakatar dakai ba daga baiwa yarinyarka duk wanda kakeso ba,amma muddin babu haduwar jini ko taji bata sonsa bazan lamunci a kaita inda zafa quntata ba,don ina kallonta ne kamar amana a hannuna,idan tasu tazo daya da ma'aruf zanyi farinciki da hakan,don atika(mahaifiyar ma'aruf,jika ne shi cikin gidan,d'an mace ne)tamkar 'ya take a waje na".
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.