Complete Hausa Novels

Akidata Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Akidata_Book_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 8

PART1
Page 12

ÆŠan sandan ya zare ido zeyi magana, Yusuf yayi saurin girgiza masa kai, ya juya ya kalli Widad yaga hankalinta baya kansu.

A hankali ya zura hannu a aljihun sa ya É—akko ID card ya nunawa É—an sandan, washe baki É—an sandan yayi yana niyyar sarawa Yusuf, amma Yusuf ya girgiza masa kai yace

"Dan Allah Yallaɓai ku duba lamarin nan, ni bani da laifi a abunda ya faru, kuma na bashi haƙuri yaƙi haƙura"

Mutumin ya ƙaraso inda su Yusuf suke yace  "kaga Ku tafi da shi ajiyata ne, ku kulle shi har se nazo station ɗin"

ÆŠan sandan Ya kalli Yusuf zeyi magana, sega wasu 'yan sandan sunzo, motar da' yan sandan suka zo ze tabattar maka da manyan wanda mutumin ya kirane, nan na farkon suka shiga sarawa wanda Widad ta kira.

Widad tace  "ina so a duba Accident ɗin nan, idan direba nane yake da laifi, zan biya shi kuɗin motar sa uku, idan kuma shi yayi laifin ze durƙusa ya bamu haƙuri, saboda cin zarafi da ɓata mana lokaci da yayi, in kuma yaƙi a tafi da shi, ajiyata ne a kulle shi se nazo"

Nan fa kallo ya koma sama, nan 'yan sanda suka shiga dube duben su, aka tabattar da mutumin nan shine ya karya doka, nan fa mutanen gurin suka É—au sowa.

Widad taje gaban sa tace " if you are somebody you won't say it yourself, don't ever say you are Somebody when you are nobody, yanzu ka durƙusa ka bawa direba na haƙuri akan cin zarafin da kayi masa"

"Wallahi baki isa ba keɗin banza, in bawa wannan wulaƙantaccen haƙuri, kin san koni waye?"

Ɗaya daga 'yan sandan daya kira ne yaja shi gefe yace  "kai wallahi wannan' yar masu ƙasa ce, idan taso zatasa a ɓatar da kai gaba ɗaya wallahi, kayi abunda tace kota sa a ɗaureka"

"wannan ƙaramar yarinyar 'yar cikina?"

"to karkayi cigaba da taurin kai, wannan' yan sandan data kira muma iyayen gidanmu ne"

Mutumin ya dawo a ƙule ya kalli Yusuf yace  "Yi haƙuri"

"Akan gwiwowinka zaka durƙusa ka bashi haƙuri" cewar Widad

Cikin tsawa wani É—an sanda yace "ba zakayi bane? Semun tafi da kai?"

A hankali yaja da baya ze durƙusa, Yusuf yayi saurin riƙe shi tare da girgiza kai ya kalli Widad yace  "please Madam ina nema masa Alfarma, kiyi haƙuri dan Allah, ni zan durƙusa in baki haƙurin a madadinsa"

Dama Widad tasan Yusuf baze taɓa yadda hakan ta faru ba, tayi ne dan nunawa Mutumin shi ɗin bakomai bane.

"Shikenan tunda ya haƙura, gobe in Allah kaimu, yaje station ɗinka ya karɓi kuɗin motar sa, na ninka maka masa sau uku, Amma ya kiyaye gaba"

Ta juya ta tafi motar su, Izzar Widad da yadda ta tafi da al'amuran cikin isa da izza, da bajinta suka birge mutane, aka dinga sowa, anawa mutumin nan dariya.
Dare yayi musu a gurin nan saboda wannan incident É—in, Yusuf yaja motar cikin nutsuwa suka tafi.

Amma still lokaci lokaci tana goge Hawaye a fuskarta, suka ci gaba da tafiya Yusuf na godewa Allah da Widad bata ga bindigar nan ba, tabbas yasan da Asirinsa ya tonu daya gama kaɗewa, ƙarshen ta seta kulle shi me fitar dashi se Allah.

suna zuwa gida Yusuf yayi horn Isa ya buÉ—e musu gate, Yusuf ya shiga da motar yayi parking, har ya gama abunda zeyi ze buÉ—e motar ya fita, Widad tana zaune ko gezau ba tayi ba, bata da niyyar fita daga motar.
fita yayi ya zagaya ya buɗe mata ƙofar, yace  "Munzo fa" ɗaga kai tayi ta kalle shi, a hankali ta zuro ƙafafunta da take jin kamar ba'a jikinta suke ba waje ta yunƙuro ta fito, sedai tana fitowa ta tafi luuu zata faɗi, cikin zafin nama Yusuf zama shamaki da faruwar hakan, ta hanyar  riƙeta ta faɗa a jikinsa.
Ƙirjinsa ya dinga bugawa da ƙarfi, saboda jin hakan wani irin abu daban, Isa me gadi ne ya zaro ido ganin abunda yake faruwa, Yusuf kamar me raɗa  yace  "Are you ok?"
Jinjina masa kai tayi ta sake ƙoƙarin miƙewa, amma still jiri ke kuma ɗibarta, tafiya take tana tangaɗi kamar wadda tasha wani abu, Yusuf yabi bayanta ya mata rakiya har cikin babban falo, hannunsa riƙe da ƙaramar jakarta da kuma wayar ta.

A babban falon ta zauna tana riƙe kai, hawaye nata zarya a fuskar ta, ƙoƙarin cire takalmin ƙafarta take, amma abu ya gagara, se kokawa take da takalmin.
Yusuf ya taka inda take  ya durƙusa ya kwance igiyar takalmin nata me tsinin tsiya ya cire mata.

Ta gyara kwanciyar ta sosai ta miƙe ƙafafunta akan doguwar kujerar tare da lumshe idonta, don bawa hawayen idon nata damar gangarowa.

Yusuf a ransa yace 'Ikon Allah, wannan wane irin kuka ne?'

"ko za'a kira likita ne?"

"Ni lafiya ta ƙalau" ta bashi amsa idonta a rufe.

"Jikinki yana rawafa, kamar zazzaɓi ze kamaki fa"

"to ina ruwan ka? Jikin ka ne ko nawa? Ni kaimin kayana É—aki ka tafi ka ban guri"

ÆŠan girgiza kai Yusuf yayi yaje ya ajiye mata kayan ta ya fito, tana nan inda ya barta, yasa kai ya fice.

Yana fitowa ƙofar da zata sa dashi da harabar gidan yaji an riƙo rigarsa, waigawa yayi yaga waye wannan.
Amal ce tsaye tana huci,
"Amal lafiya kuwa?"
"dole kace lafiya mana? Yusuf daga ina kake kai da Widad?, saboda tsabar abu harda cire mata takalmi, Yusuf wai kai wani irin mutum ne dan Allah? Me kake aikatawa ne haka Yusuf? me yasa lallai seka yi abunda zaka birgeta, bayan kullum baka da kima a idon ta? Sau nawa nake gaya maka kusanci da ita tamkar kusanci da mutuwarka ne? "

Yusuf yace " look Amal niba wani abu nake nema a gurin Widad ba, kuma ba neman kusanci nake da ita ba, kawai ina tausayinta ne, kuma ina jin daÉ—in yadda mahaifinta ke mutuntani"

"kace tausayi Yusuf? Yusuf daga tausayi so yake shiga, ban taɓa ganin mutumin daya samu damar da ka samu a gurin ta ba, Yusuf a gidan nan ba kowa keda ikon zuwa inda take ba in bada izinin ta ba, kai kuwa kana iya zuwa gurin ta duk lokacin da kake so a matsayin ka na direbanta, Yusuf ina kishin ka, Yusuf sonka nake wallahi bazan zuba ido abubuwa su cigaba da gudana tsakanin ka da Widad a haka ba"

"Amal, Soyayya tsakanina dake ba zata yuwu ba, Mahaifiyarki bata ƙaunar talaka, kuma ni talaka ne inani ina iya Soyayya dake Amal?Hausawa suka ce ƙwarya tabi ƙwarya, idan tabi akushi zata fashe"

"dakata Yusuf" Amal ta katse shi, hawaye tuni ya fara sintiri a idon ta, tace  "bazaka iya Soyayya dani ba, amma zaka iya da Widad ko?"

"Amal ni ba Soyayya nake da Widad ba, inani ina son mace kamar ta, ita a kanta bata yarda da wata soyayya ba, Amal nayi Soyayya a baya, abun da na fuskanta a soyayya bazan ƙara yadda in sake fuskantar sa ba, ke kanki da kin san wayeni bazaki soni ba, ba zaki so kasancewa da mutum kamar ni ba, kiyi hakuri "

"ba abunda ya shafeni, what I know is that ba zan zuba ido ka faɗa soyayya da mahaukaciya mara tarbiyya ba, kuma bari in gaya maka ba zaka taɓa kuɓucemin ba kasa wannan a ranka"

Tana gama faÉ—ar haka ta juya da sauri ciki tana kuka, jikin Yusuf yayi sanyi a haka ya ja jiki ya fito.

Masallaci ya wuce yai sallolinsa, sannan ya zauna yana karatun Al'qur'ani mai girma, ya daɗe yana addu'a sannan ya miƙe ya nufi titi dan samun abun hawa zuwa gida.

Abunka da unguwar masu kuɗi, tuni unguwar tayi tsit se sanyi bishiyoyi dake kaɗawa, yana ta tafiya a ƙasa yana tunanin abubuwa da dama, ya baro layin su Widad sosai inda security suke, ba tsammani se gani yayi ansha gaban
sa da mota, tsayawa yayi cak yaga ikon Allah.

Wasu ƙarti ne suka fito daga motar suka zagaye shi, ɗayan yace  "kaine direban 'yar gidan Alhaji Nasir?"
Ba tare da tsoro ko shakka ba Yusuf yace  "Eh nine"

"Good labari ya ishemu cewar akwai kusanci tsakanin ka da ita, duk inda zata tare kuke zuwa, an samu mu ɗakkota kwanaki amma ka hana, bari in gaya maka wani abu, zamu ƙyaleka ne saboda zakayi mana amfani, zamu ci gaba da bibiyar ka saboda akwai wani abu da muke so ka karɓo mana a gurin ta" cewar ɗaya daga cikin ƙartin

Yusuf yace "Babu wani kusanci tsakanin mu, aiki nake mata tana biyana, ko meye kuje ku tambaye ta ta baku mana"

ÆŠaya daga cikin sune ya sakarwa Yusuf wani mummunan naushi, da seda jini ya fito daga bakin sa, a zuciye Yusuf ya É—ago yana kallonsu, babban yace

"Wallahi idan baka kawo mana abun nan ba se mun kasheka, akwai wasu mahimman abubuwa da muke so ka karɓo mana a gurinta idan kaƙi semun maka yankan rago"

"Bayan yankan ragon se kuma me?" Yusuf ya faÉ—a babu alamar tsoro

Wani naushin suka ƙara masa a gefen ido,
Maimakon Yusuf ya tsorata, ko ya nuna jin zafin naushin, se yayi murmushi yace

"idan kunmin yankan rago, ku kuma ku zauna a naɗe duniya daku?, babu wani mahaluki daya isa yasa Yusuf yin wani abu dan son zuciya da zalunci, kuje ku gayawa wanda ya aiko ku cewar karya kuskura yayi gangancin cin iyakar gonar da ba tasa ba, idan kuma yaƙi zanwa shukokin feshi in ƙone nawa da nashi, kowa ya rasa, wannan saƙon Yusuf ne ga uban gidanku ko wayeshi"

Wani naushin suka yi niyyar kai masa amma ya riƙe hannun ɗayan.

"Waye kai? Waye ya gaya maka wanine ya turomu?" cewar É—aya daga cikin su

"yadda kuka binciko kuka gano nine direban Widad, haka yakamata ku bincika kusan wayeni, nasani aikoku akayi ku koma ku ƙara tabbatarwa wanda ya aikoku nina ɗauke Widad lokacin da yasa a sace ta, ni aikina tuƙata a mota dan haka ya kiyayi yunƙurin cutar dani"

Hausawa sukace 'sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, sun daki Yusuf sosai, yaso yayi amfani da bindigar sa, amma yin hakan ze rusa masa da yawa daga shirinsa, dan haka ya fasa ɗaukar bindigar, suka daddake shi, wani yana iya ramawa wani kuma baya iyawa.

"zamu cigaba da bibiyarka, harse ka bamu abunda muke nema, zaka gane baka da wayo, Uban taurin kai, Ubangidanmu yafi ƙarfinka"

haka suka barshi a gurin suka tafi.

Da ƙyar Yusuf yaja jikin sa ya hau Napep ya tafi, hancinsa yana ta zubar da jini, jiri ne yake ta ɗibarsa saboda jinin da yake zubarwa da yawa, da ƙyar yaje gida, Allah ya temake shi Umma tayi bacci.

ya cire kayan jikinsa yana goge jinin fuskarsa, Aljihun wandonsa ya taɓa yaji wayar da Widad ta bashi ɗazu.

Hannu yasa ya ɗakko ta yana jujjuya ta  "Ka ɓoye ta kamar yadda zaka ɓoye ranka, wannan wayar tamkar rayuwar ka ce"

Maganar Widad ta dawo masa, kunna wayar yayi, Amma akwai password akai shiru yayi yana nazarin kamar yaya wayar nan tamkar rayuwar sa take? Ajiye wayar yayi ya shiga yayi wanka ya fito, nan ya shiga aikin nasa na tunani dan abubuwa da dama sun faru da suke buƙatar nazari.

"Me Widad taje yi Hotel? Me ta gani ya sata kuka? Waye ya turo mutanen nan? Ko waye akwai sa hannun wani a gidan su Widad? Amma dagaske Tausayin Widad zesa ya fara sonta? Me yasa tasa a durƙusa a bashi haƙuri yau? Tabbas zata iya yuwuwa akwai Alaƙa tsakanin wani a gidansu Widad da mahaifin Nurat"

Ji yayi kansa kamar ze fashe, dan haka ya rintse idon sa yana addu'a da fatan bacci ya ɗauke shi koze ɗan samu nutsuwa, Amal ta faɗo masa a rai itama, wai ita bilhaƙƙi son shi take.
Wani tunani ya shigayi watanni shida da suka gabata, da yanzu yana nan da Auren sa, katsam a dalilin irin tasa ƙaddarar aka fasa wannan Aure, bayan cin zarafi da wulaƙanci daya fuskanta daga iyayen matar daze Aura, bacci dai se ɓarawo ne ya ɗauke shi.

*******************************

Da safe Yusuf ya tashi da matsanancin zazzabi, kansa har sarawa yake sosai saboda dukan da yasha jiya, juyi kawai yake akan gadon gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, ganin har kusan ƙarfe tara be fito ba yasa Umma leƙawa ɗakin sa, ta tarar da shi kwance a kan gadon sa, ƙarasawa tayi ta taɓa jikin sa tace  "Yusuf lafiya kuwa? Naga har ƙarfe tara baka fito ba?"

"Bana jin daÉ—i ne Umma"
"dan baka jin daÉ—i seka zo ka kwanta kana juyi, ka tashi ka watsa ruwa, ka karya seka sha magani"
"to Umma"
Yusuf ya miƙe ya shiga yai wanka, kayan breakfast ɗin ta kawo masa ɗaki, ta kalle shi tace 
"Yusuf kamar kumburi nake gani a gefen idonka da bakin ka"

Yusuf yace  "Mun faɗi akan babur ne jiya da daddare"

"Amma ka kasa gayamin? Meye amfanin hakan, haba Yusuf"
Yusuf yace  "Yi haƙuri Umma, bana son ɗaga miki hankali ne"

"Amma ina fatan ba wani mummunan ciwo daka ji?" tai maganar cike da damuwa

"Eh banji ciwo me yawa ba"

Da kanta ta zauna tana bashi Abinci a baki, ta É—akko masa first aid box É—insa ya É—au magani ya sha, ya koma ya kwanta.

Kwanciyar sa ba daɗewa Abbas ya kira shi, da ƙyar Yusuf ya ɗaga wayar, Abbas yace  "Mutumina kana ina ne? Ina son ganin ka"

"Ina gida bana jin daÉ—i ne"

"Subhanallah, meya sameka?"

"Zazzabi ne" Yusuf ya bashi amsa

"Shikenan gani nan zuwa"
Su kayi sallama

**************************

Hajiya Halima na zaune falon ta tana shan tea, Isa mai gadi yazo yana kwaɗa sallama a ƙofar falon ta, A fusace tace "wai meye hakane? Lafiya kame do kamin wannan sallama kamar kana bina bashi?"

"Hajiya nine, Isa ne"
"to ya a kayi?"
"Hajiya gurin ki nazo"
Ta ɗanyi tsaki sannan tace  "shigo"
Ya shiga falon ya durƙusa yace 
"Ina kwana?"
"Kai bana son doguwar gaisuwar nan meke tafe da kai?"

"to Hajiya kin san shi sha'ani na rayuwa kiwon mutum ake ba dabba ba koba haka ba?"

"kai nifa bana son wannan surutam banzae, ka faÉ—amin kanka tsaye meke tafe da kai"

Isa ya gyara zama yace  "game da sabon direban nan ne Yusuf, gaskiya Hajiya akwai buƙatar kisa ido, jiya yadda na gansu Allah ya nuna min Annabi salallahu alaihi wassalam, kin san dai irin shigar da take yi, bayan kin fita ita dashi suka fita, basu dawo ba se ƙarfe tara na dare, bayan sun dawo a gabana da idanun nan nawa" yai maganar yana gwalo idon nasa ya cigaba da cewa
"da idanu na naga suna rungume juna, Hajiya a saka ido, kina gani idan ba kiranmu akayi ba bamu da damar shigowa kiga yadda take hantarar mu, Amma shi ba yau ba gobe cikin sintiri yake har cikin É—akin kwanan ta, Allah kaÉ—ai yasan me suke yi, gaki da 'yan mata kema kyawawa bekamata yana gardi baligi ya dinga wucewa yana kalle miki su ba, shiyasa nace bari inzo in sanar dake abunda ake ciki "

Dire kofin hannun ta tayi, taja wata nannauyar Ajiyar zuciya tace " Hmm naji maganganun ka, kuma kazo da magana abun dubawa, tashi kaje zan san abunda zanyi "

Isa ya miƙe yana murna yace
"shikenan Hajiya na barki lafiya "

Shiru Hajiya Halima tayi tana zake nazartar kalaman Isa megadi, tabbas Widad bata yadda wani ya Wulaƙanta Yusuf ba, lokacin da ciwon ta ya tashi taƙi yadda da kowa se Yusuf, idan har dagaske wani abu na faruwa a tsakanin su to tabbas akwai yuwuwar ta gayawa Yusuf inda abunda suke nema yake.

**************************

Widad kwana tayi da zazzabi da ciwon kai, da ƙyar ta samu tayi bacci.
Jikin ta sam babu ƙwari ta miƙe domin haɗawa magen ta abunda zeci.
Widad na matuƙar son dabbobi, tana tausayin su fiye da yadda take tausayin mutane, akwai shaƙuwa me ƙarfi tsakaninta da dabbobinta, mussman ma wannan magen nata pita, da kuma karen ta dake gidan gona, tana jin daɗin kasancewa da su, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa sukeyi ba.

Ta samu container ta zuba masa madara, ta samo wani ta zuba masa gugguru, ta koma gefe tana kallon magen, maimakon magen yaci seya koma jikin ta ya kwanta, dan ya saba idan lokacin cin Abinci yayi, ta zuba masa nasa yana ci itama tana cin nata

**********************************

Abbas ne yayi Sallama ɗakin Yusuf, da ƙyar Yusuf ya iya amsawa, ya miƙe zaune suka gaisa da Abbas.

"Sannu Yusuf, ko Asibiti za muje in sauke ka"

Yusuf ya girgiza kai yace  "A'a na sha magani kawai, ya kake ya aikin?"

"Alhamdilillah, jiya Oga Suleiman yake neman ka, shine kiran da nayi maka, kuma se kace baka jin daÉ—i, yanzu yau ba zaka gidan su mutuniyar taka ba?"

Yusuf yace  "bazani ba gaskiya, sedai zuwa gobe in Allah ya kaimu idan naji sauƙi"

Abbas yayi ƙasa da murya yace 
"Ya kuÉ—in nan waye ya turo dasu kuwa?"

"itace wai Albashi na ne na watanni uku da bata bani ba, nace mata yayi yawa ta rage taƙi"

"Taɓɗijan kaima Yusuf da wani abu, kamarya ta rage? Malam kawai kaci kuɗi, meye labari kuma?"

Yusuf ya gaya masa Hotel da suka je, da yadda suka dawo tana kuka, Amma be gaya masa zancen wayar nan ba data bashi.
Nan suka cigaba da tattaunawa zuwa wani lokaci Abbas yace ze tafi, Naira dubu É—ari Yusuf yayi masa transfer a cikin kuÉ—in, Abbas yaita murna yana godiya suka yi sallama.

Amma ƙasan zuciyar Abbas kamar ya fasa ihu
'dana san wannan alherin Yusuf zeje ya dinga samu da tun farko nina karɓi aikin nan, ya samu dubu ɗari biyar amma ya bani wata shegiyar dubu ɗari, ga danƙareriyar waya ya samu, na tura shi dan ina gudun wulaƙanci amma yaje yana samo abun Arziki, dole in san yadda zanyi a cire shi daga kan aika ni maye ni"

'Amma hatsari da kasadar dake cikin aikin fa?' wata zuciyar ta tambaye shi, tsaki yayi yana ci gaba da surutai.

*******************************
Shafa jikin magen take a hankali tana lallaɓashi yaci Abinci, wayarta ce ta fara ringing, muzurun nan ya kasa a guje yaje ya ɗakko ta a bakin sa ya kawo mata, shafa kan muzurun tayi tace  "thank you Roux"
Ta amsa wayar tasa a kunnen ta
"Ranki ya daÉ—e Bala fa babu lafiya, an É—auke shi rai a hannun Allah an kai shi Babban Asibitin cikin gari, dan besan waye a kansa ba"

Miƙewa tayi tsaye tace  "what? How comes? Wace irin rashin lafiya ce wannan?"

"Nima ban sani ba gaskiya, Amma an fita da shi daga Asibitin cikin kurkukun gaba É—aya"

Bata kashe wayar ba ta miƙe, da sauri ta shiga bedroom ɗinta ta canza kaya, dukda yanayi na rashin lafiya da take ciki, wayar ta ta koma ta ɗakko ta fara daddanawa sannan tasa a kunnen ta.

Yusuf yana jin wayarsa tana ringing ya ƙi ɗagawa yasa ta a silent, ya ajiye wayar ya cigaba da kwanciyar sa.

Jifa tayi da wayar akan kujera ta fice harabar gidan, gurin su Nura ta nufa, tana zuwa suna gaishe ta amma bata kula suba tace 
"Ku kiramin driver yanzu"
Jiki na rawa suja shiga kiran Yusuf babu ƙaƙƙautawa, Amma be ɗaga ba.

Ta kalli Nura tace "É—akko mota da sauri, zaka fita dani"

Cike da washe baki yaje ya ɗakko mota, ta shiga Nura yaja motar suka fita, gaba ɗaya ji take kamar tayi Amai, dukda a bayan motar ta zauna amma warin hammatar Nura ya cika motar, se tsaki take yi badan ya zama urgent ta fita ba babu yadda za'ayi ta yadda wannan ƙazamin ya jata a mota, suna tafe tana masa tsawa gami da hantararsa, Amma Yusuf ze gane kurensa na ƙin zuwa da yayi yau sannan yaƙi ɗaga waya.

Prison tasa ya kaita, suna zuwa ta fita ta shiga, kai tsaye ofishin Hisham ta wuce.
Yana ganin ta yai murmushi ya sallami kowa daga office ɗin sannan yace  "barka da zuwa lady boss, Ashe kin dawo Nigeria?"

"Ya aka yi Bala ya kamu da rashin lafiya da har ta kai shi ga kwanciya, seda aka fita da shi daga gidan nan?"

"Ranki ya daÉ—e gaskiya dama yana É—anyin rashin lafiyar a tsai tsaye, Kawai se É—an uwansa ya kawo masa ziyara, bayan ya tafi jikin sa ya rikice"

"yanzu kana nufin kace min ÆŠan uwansa ne ya kawo masa abunda yaci, jikin sa ya rikice kenan? Saboda sakaci da rashin sanin aikin ku?"

"A'a ranki ya daÉ—e kin san?...

"Yimin shiru malam, saura sati É—aya tal a koma kotu, kawai se inji wannan banzar maganar mara tushe, shikenan amma kasani idan har rashin lafiyar Bala haÉ—in baki ne, duk wanda yake da hannu a ciki shima abunda ya samu bala ze sameshi. "

Ta miƙe a fusace ta fito, Hashim ya biyo ta da sauri amma ta shiga mota da niyyar ta ta wuce gurin lawyern Daddy, amma ba zata iya jure wannan tsamin da Nura yake ba, dan haka tace ya nsida ita gida, tana mamakin ƙoƙari irin na Daddy da yake iya shaƙe wannan warin hammatar, Yusuf kullum tsaf dashi cikin ƙamshi, amma wannan ƙazamin kamar baya jin yadda yake wari, seda ta bari sun koma gida, sannan tayi wa Nura ta tas akan ƙazanta da warin da yake yi a gaban sauran ma'aikatam.

Gaba ɗaya ranta a ɓace, ga jikin ta ba ƙwari gashi a ƙule take da Yusuf, tana shiga babban falo ta tarar da Hajiya Halima, bata kula ta ba tasa kai zata wuce
"Widad ina son Magana dake"

Widad ta tsaya ta juyo ta kalleta ba tare da tace komai ba.

"Widad bekamata ace kina fita lokacin da kike so ki dawo lokacin da kike so ba a matsayin ki na mace, sannan ki dinga dawowa sanda kika ga dama ba, Alhalin nida nake zaune tare dake ban san idan kike zuwa ba, Sannan wannan yaron da yake sintiri gurin ki har ƙuryar ɗakin ki, Sam be dace ba"

"kinga dakata Malama, zamanki nake a cikin gidan nan? Koke kika ajiyeni? In kun tashi taku yawon gayamin kuke? Kisawa ranki gidan nan tamkar bariki yake, kowa yayi abunda yaga dama muddin be ƙetare abunda masu gidan suke so ba, karki ƙara shiga sabgata, kuma kowa zan kawo cikin gidan nan gidanmu ne, kowa ze je har cikin ɗakina babu ruwanki, kome nake aikatawa karki ƙara shiga, dan ke ba uwa ta bace baki haifeni ba, baki da ikon ki samun ido, kema abar a sawa ido ce, kisa ido akan 'ya' yanki kawai, ba ruwan ki dani....

"Widad!!!" Ramlah ta kira sunan Widad da ƙarfi

"Ramla don't ever try to shout at me, a gidan mu kike ba gidan ku ba, dan haka ki iya bakin ki, tun kan in fusata"

Tana gama maganar ta juya ta tafi part É—in ta.

"Tirƙashi Mummy dan Allah ki bani dama ko sau ɗaya, inci mutuncin yarinyar nan in koya mata hankali ko zanji sanyi a zuciyata"

Mummy ta girgiza kai tace  "Kina yin haka Ramla kin ɓata komai, rabu da ita lokaci ne, yana nan zuwa da zata girbi abunda ta shuka"

**********************************

Se wajen la'asar sannan Yusuf ya ɗanji sauƙi ya tashi, ya shirya yaje Asibiti, aka duba shi aka bashi magunguna.
ya dawo gida ya wuce ɗakinsa, wayarsa ya ɗakko ya duba, yaga missed calls rututu, ko ba'a  gaya masa ba yasan Widad ce take neman sa, bebi ta kansu ba ya ajiye wayar ya cigaba da harkokinsa.

Dayaji ya ɗanji ƙwarin jikin sa, seya shirya tsaf ya tafi hotel ɗin da suka je da Widad, Manager yaje nema amma be sameshi ba, ya cewa ma'aikatan su bashi lambar wayar sa, da farko suka ƙi, seda ya nuna musu id card ɗin sa sannan suka bashi, seda ya zagaya lungu da saƙo na Hotel ɗin, yana sake monitoring mutanen dake shiga da fice a hotel ɗin sannan ya koma gida.

Washegari da safe dukda ya tashi jikin sa babu daÉ—i, Amma haka ya shirya ya tafi gidan su Widad.

Tunda yaje Isa yake masa wani irin kallon banza, yanata habaice habaice
Shi dai Yusuf be kula shi ba, Nura yace

"Wallahi Yusuf yau kana ruwa, bama kusa da kada ba, cikin bakin kada, jiya ta fusata sosai, dan zata fita seni na kaita saboda baka zo ba"

Murtalah ya kwashe da dariya yace  "bayan kun dawo kuma tai maka tatas a gabanmu ba, saboda ƙazanta kai Nura jiya kaga tijara a tsakar rana, ai idan nine kai ko maganar ba zan ɗakko yau ba" yai maganar yana dariya

Nura ya haÉ—e rai yace
"Bana son rashin mutunci da Iskanci"

Ganin suna nema suyi faÉ—a yasa Yusuf yin gaba abunsa ya barsu a gurin, tafiya kawai yake yi amma jikin sa babu daÉ—i.

Yana shiga falon ya tarar da Ramadan É—an gidan Alhaji Bulama da Amal suna hira.

Yusuf yace  "barkanku da Safiya"

Bata amsa masa ba se Ramadan ne yace  "Yawwa barka dai, bodyguard ɗin gimbiya" Yusuf ya ɗanyi murmushi ya nufi hanyar Widad.

Bayansa Amal tabi da kallo, taji wasu hawaye na ƙoƙarin zubo mata, ta tsani kusancin Widad da Yusuf gani take komai ze iya faruwa, wani sashin na zuciyar ta ma yana gaya mata akwai wata alƙar a tsakaninsu saboda kusancinsu yayi yawa.

Ramadan ya kalleta yace "lafiya kuwa my?"

Girgiza masa kai kawai tayi tace  "lafiya ƙalau"

Yusuf ya shiga ya tsaya a bakin ƙofar bedroom ɗin ta sannan yayi sallama kamar yadda ya saba.

Yayi Sallama kusan uku amma bata amsa ba, haka ya cigaba da tsayuwa a gurin, seda aka kwashi wani lokaci sannan ta fito, kallon sa tayi daga sama zuwa ƙasa sannan tace 
"Sannu ishashshe kaga damar zuwa kenan?"
Shiru Yayi ya sunkuyar da kai, É—akin ta shige yabi bayanta da sallama

"Meya hanaka zuwa jiya? Kuma kaƙi ɗaga waya?"

"Bani da lafiya ne shiyasa"

"ƙarya kake" ta faɗi kai tsaye ba tare da duba ratar shekarun da Yusuf ɗin ya bata ba, shiru ya sake yi bece komai ba, ta tako tazo daf dashi tace 
"for the second time meya hanaka zuwa jiya?"

"bani da lafiya ne" ya sake bata amsa

"wai me yasa baka kunyar yin ƙarya ne, meyasa? Ban gaya maka bana son ƙarya ba?" tai maganar tana ƙoƙarin sa idon ta a cikin nasa

Babu zato ya janyota gaba ɗaya tana facing ɗinsa, ya kafe ta da idon sa, nata cikin nashi ya ƙura mata ido

Ayi sharing please 🙏🙏🙏

Ayshercool
07063065680
                    
                    _*AƘIDATA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

      

                   

     PART1
                              Page 13

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Ba ƙaramin firgita tayi ba da abunda Yusuf ɗin yayi, sedai riƙon da yayi mata tana iya jin huci me zafin da jikin sa ke fitarwa, masifa take son yi amma gaba ɗaya Yusuf yayi mata wani irin kwarjini ta kasa cewa komai se binsa da tayi da manyan idanunta.

Cike da jarumta Yusuf yace "Meyasa koda yaushe idan nayi abu seki ƙarya tani? A koda yaushe ina ƙoƙarin gaya miki iya gaskiya ta amma seki ce ƙarya nake, kin san yadda mutum keji kuwa idan aka ƙarya tashi, it's really hurts, duk abunda nake yi ba inayi ne dan in samu kusanci dake ba, nasan AƘIDARKI nasan abunda bakya so, ina ƙoƙarin kiyaye dokokin da kika kafamin ne, dokokin dana sawa hannu amma koda yaushe burinki kici zarafina"

"Malam cikani ko"  ta faɗa tana masa wani irin kallo

Cikata yayi ya koma gefe ya tsaya.

Seda tayi ajiyar zuciya sannan tace

"hmm tunda nake babu wanda ya taɓa Yimin abunda kayi min a yanzu, ina ɗaga maka ƙafa ne saboda wasu dalilai biyu zuwa uku, dalilai biyu bakomai ne a gurina ba, dan ba zasu hanani yanke hukuncin dana ga dama akan ka ba, dalili ɗaya ne me ƙarfin da yazo da ƙaddarar da ni ban isa in canza shi ba koda hakan bemin ba, ba yadda zanyi da kai dukda har yanzu ina doubting akan wannan dalilin, Anyway zamu fita yanzu zamu je gidan gona"

"A wace motar?" ya tambayeta a taƙaice

"kowacce ta bashi amsa"

Har ya juya ze fita yaji tace 
"meya sameka a fuskarka?"

Ya juyo ya kalleta

"kar kayi min ƙarya" ta faɗa kafin ya bata amsa

"Duka ne" ya bata amsa

"Kamar ya ya duka? Suwaye suka dakeka?"

"Nima ban sansu ba"

Ɗan tsayawa tayi tana nazarinsa, yayin da ya ɗauke kai yaƙi kallonta

"Shikenan, muje"

Suka fito falo, yana gaba tana bayan sa, Amal ta bisu da wata uwar harara.

Ramadan yace 

"Allah ya temaki 'yar masu gida, Gimbiyar gida a biki a zauna lafiya, a ɓata miki mutum yai kwanan baƙinciki,' yar gaban goshi sha lelen masu arziki, tun ɗazu nake zaman jiranki anan, Megida ne ya aiko ni, yace yana son ganinki"

Ta yamutsa fuska tace  "Ina da abunyi, da  haka ba zani ba"

Ramadan yace "haka zanje in gaya masa"

"Eh haka za kaje ka gaya masa, bazan zo ba, bazan ƙara zuwa inda yake ba"

"shikenan, kunfi kusa keda shi"

Ta juya suka fice ita da Yusuf.

Amal tace  "Ramadan, dan Allah yanzu baka jin haushin irin abunda takewa mahaifinku?"

Ramadan yace  "to me zance Amal? Ni meye nawa a ciki? Da mahaifina da mahaifinta tashi nayi na gansu tare, kuma haka muka tashi muka ga an sangartata se abunda take so sukeyi, sun ɗauki son duniya sun ɗora mata, ba'a kwaɓarta komai tayi dai dai ne, meyasa zanji haushi, tunda ba yau ta fara ba, kuma idan tayi baya jin haushi, a gabana a gaban sa idan bata ga dama ba  Bulama take cemasa kanta tsaye, an riga an barta ta tashi akan wannan AƘIDAR"

"gaskiya ni abun yana damuna, mu kanmu a cikin gidan nan bamu tsira daga wulaƙancin ta ba, bamu ba har mahaifiyar mu fa"

"kin san wani abu? Ni yanzu babbar damuwa ta itace, Daddy yace  Fahad zasu aurawa ita, Fahad kuma mutum me faɗa baya son raini ni ban san ta yaya za'ayi wannan zaman auren ba"

Amal tace  "ai duk wanda ya kwashi wannan ya kwashi masifa, gata mahaukaciya ga ba tarbiyya, gaskiya ina tausayin Fahad"

***********************************

Yusuf yayi parking ɗin motar a gidan gona, Widad na fitowa kamar kullum haka ma'aikatan suka yo caa suna gaishe ta, ɗaga musu hannu tayi ta kalli Wani daga cikin ma'aikatan, wanda ya tsare Yusuf da tambayoyi wancan karon tace 
"Ya aiki ya kuma dabbobi na?"

"lafiya ƙalau ranki ya daɗe, ko za'a ɗakko dokin ne?"

"A'a sedai ina so kayi min rakiya in zaga su"

"to shikenan ranki ya daÉ—e" haka suka shiga suna zagawa, sosai Widad take jin nishaÉ—i idan tana kallon dabbobi, gaba É—aya mantawa take da damuwar da take ciki, suna cikin tafiya tace

"Sale naji wata magana, ban sani ba ko kai ka jita, takanas nace bari inzo domin mu tattauna ta"

Saleh yace  "Allah yasa ba wani abun akace nayi ba ranki ya daɗe?"

"idan ka yadda da kanka ba kayi lefi ba meye na tsarguwa? Labari ya isheni cewar É—an uwanka bala bashi ds lafiya, naje har prison dan in duba shi, amma akace min an fita da shi zuwa babban Asibiti dan be san wake kansa ba, ban kai ga zuwa duba shi ba har sena je naga lawyer na tukuna "

A gigice Sale ya kalle ta yace " ya za'ayi ace yana rashin lafiya, harta kai ga baya gane mutane? Shekaranjiya fa naje duba shi, na sameshii lafiya ƙalau, taya haka zata faru? "

"Nima abunda na gaza ganewa kenan, ace beyi rashin lafiya ba se daya rage 'yan kwanaki a cigaba da shari'a, Babban Albishir É—in dana zo maka da shi shine, muddin na tabbatar da sa hannun ka, zaka maye gurbinsa ne"

Saleh ya kalleta da sauri, bata bari yace komai ba, ta juya ta tafi. Turus Saleh yayi yana nazarin maganganun Widad.
Tunda Yusuf ya fara aiki da Widad, a kullum se yaga abun mamakin daze kulle masa kai.

Ya kunna motar suna shirin tafiya wayar ta ta ɗau ruri, tana kallon screen ɗin wayar ta ɗan ɓata rai ta tura baki, ɗaga wayar tayi tasa a hansfree  "Hello Daddy"

"lovely fushi kike dani ko?"

"A'a"

"Fushi kike mana, Daddynki yace ya aiko a kira masa ke kince ace bazakiyi zo ba, Baby Why meyasa kike haka?" shiru tayi taƙi cewa komai.

"Yanzu haka munyi waya, ina so kije kiji meze ce miki"

"Daddy nifa yanzu wani gurin zani, Na gaya maka ina cikin damuwa kunƙi saurara ta, sema kawomin wasu abubuwa da bana buƙata yake, na gaya maka akwai matsala amma kunƙi saurara ta"

"Ba shawara nake baki ba, Umarni ne kije gurin Bulama yana son ganin ki"

Tura baki tayi ta ajiye wayar tana haɗe rai, Yusuf be nemi shawarar ta ba ya kaita gidan Bulama, Ranta a ɓace ta buɗe motar ta fita tana tura baki, har tayi gaba ta tsaya ta juya taga Yusuf yana rufe mota
"Malam ni ka hanzarta ba zaman jiranka zan tsaya yiba"

Yusuf ya biyo bayanta, suna shiga katafaren falon suka tarar da Iman, ƙanwar Ramadan, Iman tai murmushi tace  "Ohhh beb, ashe zaki zo yanzu Ramadan ya dawo"

Hannu kawai ta É—agawa Iman ta nufi matattakalr bene.
Iman tace "Widad, Nurat ta kirani tace min tun ranar da kika bar gurin birthday ɗinta baki ƙara ɗaga wayarta ba, i hope ba saɓani kuka samu ba, dukda nasan halinki dai"

Shiru Widad tayi ta tsaya, saboda yadda abubuwa suka yi mata yawa, sam bata cigaba da bibiyar meyasa meta a gurin birthday ɗin Nurat ba, dan tafi tunanin ko ciwonta ne ya tashi a gurin, shiyasa ta kasa tuna komai, juyawa tayi tana kallon inda Yusuf yake, ya ɗauke kai yaƙi kallon ta.

Still ba tace komai ba ta cigaba da tafiya Yusuf na binta.

A babban falon dake saman benen wanda ya kasance na Bulama anan suka tarar da Bulama shida matarsa.

Yusuf ya gaishe su suka amsa, Widad kam kyam ta tsaya tana ƙare musu kallo, sannan ta nemi guri ta zauna abunta tana hura hanci, wata uwar harara matar Bulama take wa Widad.

Bulama yace "lovely ba gaisuwa?"

Tura baki gaba ta sake yi tana ƙunƙuni, Bulama yayi murmushi yace

"Ikon Allah, ƙiri2 'ya na fushi da babanta, har in tura a kiraki kiƙi zuwa ko? Duk dan nace a miki Aure kike wannan fushin dani haka?"

Cike da tsiwa tace "Eh dan kace ayimin Aure ne, nace maka bana so, bana so, Amma kaƙi ban sani ba ko kaima da wata manufar a ranka, nace a min Visa in koma inda na fito shima kace A'a, ba dole inyi fushi ba"

"Widad meyasa baki da kunya ne? Sam baki da ta ido" cewar matar Bulama.

"Ba dake nake magana ba, ina magana da mijin ki ne karki sake shiga harka ta" Widad tai maganar a fusace

Bulama yayi murmushi yace 
"Ummu Ramadan excuse us please"

A fusace Matar Bulama ta tashi ta bar ɗakin tana mita, Bulama ya kalli Yusuf yace 
"Young man can you excuse us please?"
Yusuf yace  "ok sir" ya juya ze fita

"ba inda zeje, ko mene faÉ—i a gaban sa"

"wow daughter kin yarda dashi haka yaji abubuwan da suka shafi rayuwar ki? Lallai sauƙi yana samuwa"

"ba wani sauƙi daya samu, ina nan a mahaukaciya ta kamar yadda kuka saba faɗa"

"waya isa yace miki mahaukaciya, ba mahaukaciya bace ke Daughter"

"Eh amma kuke kaini gurin likitocin mahaukata"

Alhaji Bulama yace  "Daughter a bar wannan maganar, magana ce Maman ki tazo min da ita"

"ni uwata ta mutu, an kasheta bani da wata uwa, ta haifi dai wanda ta haifa"

Bulama ya girgiza kai yace  "What ever dai, ta kawomin ƙorafi akan ki, kina fita lokacin da bata sani ba, ki koma bata sani ba, kuma kinsan babu tsaro haka kike yawo ga rayuwar ki a hatsari, kuma tayi koke akan wannan direban naki, bata jin daɗin yadda direban ki yake sintiri a sashenki, gaki budurwa ga ta da manyan yara mata, bekamata ya dinga sintiri kuna keɓewa dashi ba, daughter meyasa ba kya ɗaukarta kamar mahaifiya ne? "

Shiru Widad tayi tana jinjina kai, Yusuf kam gaba ɗaya ji yayi kamar ƙasa ta tsage ya nutse, dan shi kansa baya jin daɗin yadda yake shiga inda Widad take, yana ganin rashin dacewar hakan.

Bulama yace " Daughter baki ce komai ba"

"so nake ka gama tukuna"

"Na gama feedback É—inki nake jira"

Widad ta gyara zama tace "Ka gaya mata wanda ze iya zama a gidanmu a ƙarƙashin mulkina shikenan, wanda baze iya ba ƙofa a buɗe take ya ƙara gaba, tunda basu da zuciya dole su zauna su cigaba da zama, yadda ba ruwana dasu to sudena samun ido, idan zargin da takemin kenan, to ka gaya mata idan maza nake son kawowa bata isa ta hanani ba, tunda gidan mu ne, sannan ni bani da uwa, Uwata ta bar duniya an kasheta, bazan ƙara yadda da wani ba, ban yadda da kowa ba kuma bazan yarda da wani ba, i start loosing trust on you Bulama, bani da uwa an kashe uwata! Karta ƙara kiran kanta uwata, ni bani da uwa! Bana son kowa ya raɓeni, ban yadda da kowa ba wannan AƘIDATA ce"

Jikin ta ne ya fara rawa, wasu irin hawaye na zuba daga idon ta, da sauri Yusuf ya tashi suna rige rige da Bulama zuwa ga Widad, Numfashi take da ƙyar tana kuka, Yusuf yazo kanta da sauri yace
"Are you ok?" jinjina masa kai tayi
Bulama jiki a sanyaye yace 
"daughter, ban faɗi wannan maganar dan in ɓata miki rai ba, Nayi ne dan in tunasar dake mahimmancin haƙuri, kuma koba komai matar mahaifinki ce sannan.. Ɗagawa Bulama hannu tayi ta miƙe ta nufi waje da sauri.

Bata tsaya ba seda taje mota, gaba É—aya rayuwar Widad abun tausayi ce, tunda Yusuf yasan ta bata cikakken sati bata zubar da hawaye ba, Amma ina dangin mahaifinta kona mahaifiyar ta? "

A haka ya kaita gida, yana tuƙi kamar baya so, saboda yadda yake jin kukan ta me ban tausayi, kamar yadda ta saba indai sukaje guri suka dawo, kame tazo dashi a motar zata barshi, se Yusuf ya kawo mata.
Dan haka yana parking ta buÉ—e ta fice, ya É—akko jakar da Wayar ta ya bita.
Sedai yana shiga Falon ya jiyo sautin kukan Widad cikin gurɓatcciyar hausar ta take faɗa
"danme zaki dinga zuwa kina kai ƙarata, bafa ki haifeni ba, keba uwata ce ba, kin sani meyasa kike shisshigi a al'amura na, idan baki dena min haka ba zan ɗau mataki mafi muni akanki, ki ƙyaleni inji da abunda nake ji, ki ƙyaleni inji da ƙunci da baƙin cikin dana ke ciki tsawon shekaru mana, danme zaki dinga min haka?"

Masifa take sosai kamar zata shaƙe Hajiya Halima, Abun na Widad ya fara wuce gona da iri.

Yusuf yace  "kina hayyacinki kuwa? Meyasa kike haka?, a haife ta haife ki, bekamata kidinga gaya mata wannan maganganun ba"

Ta juyo kan Yusuf cikin faɗa tace "Bana hayyacina, ni mahaukaciya ce, idan baka sani ba yau in gaya maka, bani da hankali har ƙasar waje ake kaini ganin likitan mahaukata, Amma baka san me nakeji a zuciya ta ba, An kashe mamana ban san kowa ba se ita, aka kashe ta ba wanda ya damu dani se Babana da Bulama, kowa kansa ya sani babu wanda ya damu da abunda Widad take ciki, kasan me nake ji a raina idan na tuna lokacin da aka kashe mahaifiyata? Wannan tabin baze bar zuciyata ba, a ƙyaleni inyi rayuwar da naga dama mana, "

Yusuf yayi ƙasa da murya yace
" is alright I feel your pain "

" you don't feel my pain, your mum is still alive but me... Kasa ƙarasawa tayi se sake fashewa da tayi da kuka, ta tafi part ɗinta da sauri, Yusuf kam kasa bin bayan ta yayi wannan karon,  Hajiya Halima kam ƙamewa tayi ta zubawa sarautar Allah ido.

Yusuf ya juya ze fice Hajiya Halima tace  "Ina zaka tsohon munafuki, zuwan ka gidan nan shiya hargitsa komai, da yarinyar nan duk rashin mutuncinta bata fiye magana ba, seda kazo kana hure mata kunne, to idan ma wani ne ya turoka to tabbas zanyi maganin ka, dan da zarar Alhaji ya dawo zansa ya sallameka, matsiyaci banza dana wofi kawai "

" Niba matsiyaci bane, Amma talaka ne me wadatar zuci, sannan kafin kisa a koreni da kaina nayi deciding yin resigning, zan bar aikin nan dan nima abunda yake faruwa ba daÉ—i yake min ba ko dan tsira da mutuncina, dole in bar aikin nan tunda bana shiga aljanna bane"

Fitowar Amal yai daidai da maganganun Yusuf da yace ze bar aikin, sakin ƙaramin plate ɗin hannun ta tayi, tabi bayan sa da sauri tana kiran sunan sa.

" Idan kika bar ƙofar falon nan da sunan bin bayan sa, zan sallamawa duniya ke in bar masa ke, tunda haka kike so"

Juyowa tayi tana kallon Mummy, ta juya da sauri part É—inta tana kuka.

************************************

Abbas se juyi yake akan kujera yayi shiru, gaba ɗaya abun alherin da Yusuf ke samu a hannun Widad ya tsaya masa a zuciya, yaji meyasa yasa aka tura Yusuf aikin shi beje ba? Yayi gudun kar yaje a dinga masa wulaƙanci yasa aka tura Yusuf, yanzu gashi kuɗin data bashi Yayi Albashinsa uku, ga gefe ana biyan sa Albashinsa, Sallamar Sakina ce ta dawo da shi hayyacin sa, ya amsa mata sallamar ta kalle shi tace 
"lafiya kuwa Yallaɓai?"
"lafiya ya bata amsa"

Ta ɗan taɓe baki tace 

"dama zuwa nayi in tambaye ka, dan Allah meyasa Yusuf baya zama a office yanzu? Wane irin aiki ne aka bashi haka?"

Abbas dama a ƙule yake yana neman wanda ze gayawa matsalar sa, dan haka ya zayyane mata komai, ciki harda Aibata Yusuf, ba ƙaramin mamaki ne ya kamata ba, ganin duk headquarter nan babu wanda Yusuf yake sakin jiki dashi kamar Abbas, Amma ace Abbas ne da bakin sa yake faɗar wannan mahanga akan Yusuf, lallai ɗan Adam ba abun yarda bane.
A zahiri ta maze tace
"gaskiya kai yakamata ace kana samun wannan sha tara ta Arziki ba shi ba, yanzu kayi duk yadda zakai kasa a maye gurbin sa da kai, a karɓe aikin daga hannun sa, idan kana buƙatar taimakona ma zan maka, kasan mu mata akwai iya makirci"

Abbas ya washe baki yace 
"ƙwarai kuwa, amma fa nagode sosai Sakina"

************************************

Har Yusuf ya kama hanyar gida, kawai ya É—akko wayarsa ya kira Manager Hotel É—in nan, ai kuwa wayar ta shiga, Yusuf ya tambaye shi idan yana son ganin sa ya zasu haÉ—u? Ya gayawa Yusuf inda zasu haÉ—u a gidan sa, beyi wata wata ba yaje har gidan nasa.

Da ganin manager Hotel ɗinma kaga ɗan duniya, suka gaisa da Yusuf, Yusuf yace  "dama wata buƙata ce ke tafe dani, ina son ka nunamin mutanen da suka kama ɗaki a hotel ɗinku, tun daga farkon wannan watan"

Manager yace  "Kai Malam, ni na zata ma wata harkar cigaba ka kawo, wannan abun da kake tambaya sirri ne bama fitar dashi, manyan mutane ke zuwa Hotel ɗinmu, ba zamuyi exposing ɗinsu ba dan duniya babu yarda"

"ze kasance sirri ne tsakanina da kai, kasa a bani babu wanda ze sani"

"Malam bazan iyaba, ka tashi ka tafi kawai"

"zan baka dubu É—ari biyar, zaka bani akan wannan farashin?"

(Abunda yasa Yusuf baya son nuna shi waye, ma'aikaci ne na sirri, no need asan shi waye)

Murmushi mutumin yayi yace "yanzu naji batu, Amma tsakani da Allah turoka akayi, kokuma ma'aikaci ne kai?"

Girgiza kai Yusuf yayi yace 

"Dani ma'aikaci ne ko sisi bazan baka ba, sedai inyi amfani da ƙarfin aiki na, Matata nake zargi ina so in kamata red handed, kuma kona kamata bazan taɓa sako sunan ku a lamarin ba"

"Shikenan, Amma dan Allah ya zama sirri tsakaninmu"

"in Allah ya yarda babu meji, da gani se kai"

"shikenan muje se a baka"

Yusuf yace  "No bana son yawan zuwa gurin bana son a ganni a gurin, ta Email ɗina nake so ka turamin, zan baka ɗaya bisa huɗu na kuɗin seka turomin zan baka sauran, bana saɓa Alƙawari dan haka kaima karka saɓa"

Haka ya amince da wannan yarjejeniyar.

*********************************

Saleh ne yake kaiwa yana komowa, Alhaji Bukar ya fito ya sa meshi, ya kalle shi ya yatsuna fuska yace  "lafiya?"

A fusace Saleh yace  "dole ka tambaye ni lafiya, me kasa akayiwa ɗan uwana? Ta yaya zanje in ganshi lafiya ƙalau kawai labari ya isheni wai bashi da lafiya"

Alhaji Bukar yace  "dakata! Da ina son ganin bayan ɗan wanka da tun a shekarun baya gudun karya tona min Asiri da tuni ya bar duniya, zaman kotu daza'a koma bani da fargaba sam, inada ƙwararrun lawyoyi da na biya su wanda zasu tsayamin, dan haka ba abunda zesa in yiwa ɗanuwanka wani abu"

"Au haka ma zakece? Wato kai a wanke ka shikuma ya cigaba da zama a prison ko? Ga wannan mahaukaciyar Yarinyar taje ta sameni, tace muddin wani abu ya samu Bala ni zan maye gurbin sa, me kake tunani ne wai? Yarinyar nan tana da kuÉ—i zata iya aikata duk abunda taso"

Alhaji Bukar ya ɗan daki kafaɗar Saleh yace 

"shiyasa nace kazo mu haÉ—a kai mu raba ta da dukiyar, mu mallaki gundurin dukiyar da muke ta farauta muga ta tsiya"

Saleh ya make hannun Bukar yace  "Niba dukiyar tace a gabana ba, babu irin kyautatawar da mahaifinta be minba, ni dukiyar sa bata gabana, ni burina a wanke ɗan uwana a fito da shi daga kurkuku tunda bashi da laifi"

Wata uwar dariya Alhaji Bukar ya saki yace  "ubanwa yace maka bashi da laifi? Lallai har yanzu kanka a kwano yake, ka ƙyaleshi ya girbi abunda ya shuka, kazo a haɗa kai a nemi Arziki".

Yana gama maganar ya wuce ya bar Saleh a gurin.

************************************

Yusuf yaita safa da Marwa yana duba wayar sa, ba zato Sega abunda ya nema an turo masa ta Email É—insa, message É—in na shigowa Manager ya kira Yusuf, Yusuf yayi masa godiya sannan ya tura masa sauran kuÉ—in, wanda kuÉ—aÉ—en da Widad take bashi ne, dan wani lokacin idan ta bushi iska se yaga alert.

Yusuf ya tura message ɗin cikin System ɗinsa da sauran wayyoyinsa, nan Yafara aiki akan bayanan da aka turo masa, ba ƙaramin mamaki ne ya kamashi ba ganin mutanen da suka ka kama ɗakuna a wannan watan zuwa ranar da suka je Hotel ɗin tare da Widad, wanda ya kama ɗaki ranar da sukaje shida Widad yafi bashi mamaki, Abun tambayar anan shine 'ya akayi Widad tasan da zuwan mutumin gurin? Me Widad taje yi? Gurinwa taje?' me ta gani ya sata kuka? '
Yusuf zuciyarsa ɗaya baya jin Widad zata aikata wani mummunan aiki na alfasha, amma akwai wani ɓoyayyen abu da yakamata ace ya sani.

Kamar wanda aka mintsina ya miƙe ya shirya, ya duba agogonsa ƙarfe takwas na dare, haka ya fita ya tari abun hawa ya tafi unguwar su Nurat.

Unguwar tasu shiru, amma haske ko ina da yake rukunin Gidajen masu kuɗi ne, har ƙofar gidan aka kaishi aka sauke.
Ya sauka ya nufin gidan su Nurat, ya tsaya suka gaisa da megadin, Yusuf yace  "Dan Allah gurin Nurat nazo"

Maigadin ya kalle shi yace "tasan da zuwanka ne?"

"A'a, bata sani ba, Amma ka gaya mata tayi baƙo"

Mai gadi ya kira Nurat a waya yasa a hansfreee ya gayamata tayi baƙo.

"Babu wanda zan haÉ—u dashi yau, dan haka ba zanga kowa ba"

Yusuf yace "kace mata Widad ce ta aiko ni"

Aida jin Widad ce tayo aiken Nurat ta rikice, tace "Kaishi guest room, ina zuwa"

Maigadin yayiwa Yusuf jagora, har wani katafaren Falo, Yusuf ya zauna yana jiran fitowarta.
Ko mintuna goma ba'ayi ba se gata ta fito, ta ƙaraso cikin falon da hanzari, sedai tana arba da Yusuf ta rikice ta buɗe baki zata yi ihu ta gudu, Cikin zafin nama Yusuf ya riƙeta tare da toshe mata baki.

"Meye haka kamar kinga wani aljani ko mugu? Kinga fa mutum ne ni"

Fizgewa tayi, ta shiga Ja da baya ta kwaɓe fuska zata yi kuka tace
"Nifa wallahi tun ranar da kuka bar nan, Widad bata ƙara zuwa gidan mu ba"

Gaba É—aya Nurat ba tafi sa'ar Widad ba, sedai Widad tafi Nurat jiki sannan Izzarta da jin kanta yake sa ka ganta kamar Babba.

Yusuf yace  "Haba Nur, nifa ba wani abu zanyi miki ba kawai tambayoyi zan miki in tafi"

Girgiza kai ta shiga yi tana kiran sunan Daddy a hankali.

"Daddyn yana nan ne?" ya tambaye ta

Ta girgiza masa kai alamar A'a

"to ki nutsu ki zauna, hira za muyi in tafi"

A hankali ta zauna, tana rarraba ido dan a tsorace take da Yusuf, dan ba zata manta randa Yusuf ya shaƙeta ba, har yayi barazanar sace taba.

Yusuf yace "Calm down dear, hira zamuyi kawai in tafi"

Ganin taƙi sakin jikin ta yasa Yusuf ya miƙe ya zaro komai na Aljihunsa, dan ya tabattar mata da babu wani makami a tare dashi.

Ya kalleta yana ɗan nazarin ta sannan yace 
"ko ki tambaye ni ina Widad ko? Tun ranar da ta bar nan baki sake neman ta ba"

"Na kirata bata É—aga wayata ne, nasan bazata sake yarda dani ba"

"Waye yace miki ba zata sake yarda dake ba? She's very simple and kind, but why do you attempt to kidnapped her?"

Kamar Nurat zatayi kuka tace  "bafa laifi na bane, Daddy ne"

Yusuf ya ɗan ƙara matsowa yace  "Amma me tayi wa Daddy haka da zesa a saceta?" yai maganar yana kallon idon Nurat, Yarinya ce dan haka yake binta a sannu cikin hikima

ÆŠan shiru tayi sannan tace "Nifa ban sani ba"

"Haba me sunan manya, Haske maganin duhu, baki kama da maƙaryata ba, ni ya akayi ma kika san Widad har kuke hulɗa bayan bata son mutane?"

"Nifa ba wani hulɗa mukeyi sosai ba, da tun ina ƙarama, gidan su na U. K yana kusa da namu daga baya suka dawo Nigeria shine... Sekuma tayi shiru tana satar kallon Yusuf.

"Shine me? "

"Dad É—ina sunyi faÉ—a da Daddynta akan Siyasa, shikenan abunda nasani, Amma dan Allah karka gayamata Daddy nane yasa ayi kidnapping É—inta idan ta sani, zata sa a kai Daddy na prison ne"

"bazan gaya mata ba, ai kin gayamin gaskiya, amma naga Daddynta É—an kasuwa ne ba Siyasa ba me zesa suyi faÉ—a da Daddynki akan siyasa"

"to ainima bakomai na sani ba, muna yara lokacin Amma tabbas sunyi faÉ—a ne shine yake son ya rama akan Widad, amma ni ban san me yake so yayi mata ba"

Yusuf yace "shikenan nagane, gaskiya you are so kind dear, Insha Allah bazan bari taji ba, Amma dan Allah karki bari a cutar da ita, kinga marainiya ce ita abun tausayi, ke kina da Mum da Dad É—inki ita kuma she's orphan"

Jinjina masa kai kawai tayi.

Yusuf yace "Bani wayarki in sami ki lambata, se mudinga gaisawa ni daga yau nayi ƙawa, ni zan maye miki gurbin ƙawancen ki da Widad"

Kallon sa tayi ta ɗanyi murmushi yadda yake magana ya burgeta, bashi da hayaniya, ya iya tsara magana daki daki, se yanzu ta gane ranar da yayi mata wannan barazanar ne ya koma kamar wani mugu amma ba haka yake ba, ta miƙa masa wayar sannan tace 
"Amma ni ban sanka a Family É—insu ba, waye kai a gurin ta?"

Yusuf yayi murmushi yace
"i don't belong to her family, but a very important person attached to her destiny"

Kallon sa tayi cike da rashin fahimta za tayi magana ya kashe mata ido É—aya, gaba É—aya seta sunkuyar da kai ta kasa maganar, ya daÉ—e yana daddana wayarta, ita kuma ta kasa cewa komai.
Seda ya gama abunda yake sannan ya miƙo mata wayar yace 

"Nagode sosai ƙawata, Allah ya bar zumunci, ni zan koma naji daɗin kasancewa dake da wannan hirar da mukayi"

Murmushi tayi tareda sunkuyar da kai tace  "baka gayamin sunan ka bafa"

"Sunana Abokin Nurat, Just call me Aboki or any name you like, good night Nur"

Ya ƙarasa maganar tare da nufar hanyar fita yana addu'a Allah ya  shiga lamarin sa akan wannan aiki me hatsarin gaske da yake yi, yasa hanyar da ya ɗakko ta zama mafita ga al'amuran.
Yayinda Nurat ta rakashi da ido har ya fice

Nurat tana komawa cikin gida Maman ta tace
"Ke lafiya kuwa? Waye wannan yazo kika daÉ—e haka?"
"Abokina ne yazo muka gaisa" tai maganar cike da basarwa ta shige É—akin ta tana tunanin Yusuf

(Masha Allah, daga wannan posting bana tunanin zan kuma wani posting se Allah ya kaimu ranar Asabar insha Allah, gobe in Allah ya yadda zan fara jarrabawar ƙarshe ta makaranta, ku sani a addu'oinku please 🙏 🙏 🙏
Dana kammala exams insha Allah zanyi ƙoƙari ku dinga samun update akan lokaci, comments ɗinku zesa kudinga samun update kullum, idan kun shirya yanzu aka fara wasan, ba'a fara komai ba thank you for being with me 😍 😍 😍)

Domin gyara sharhi ko shawara, feel free to contact me
Ayshercool
07063065680                   

                     _*AƘIDA TA*_
   

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

                              PART1
                                  
                                  Page 14

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Sosai Yusuf yake ƙara samun haske akan lamarin binciken da yake yi, Sam babu specific lokacin da Widad take bawa Yusuf albashi, duk lokacin da ta bushi Iska sedai yaga alert ɗin kuɗi, kuma kuɗi masu yawa, sannan be isa yayi magana ba.

Yana ta tattara bayananan daze gabatar a gurin aiki na sakamakon binciken da yake yi.

Tunda Yusuf ya tafi Nurat take tunanin, ko ta gayawa Mahaifiyarta yadda suka yi da Yusuf, wata zuciyar ta gargaÉ—e ta akan hakan.

********************************

Gaba É—aya Widad ta takura kanta, sam ko Babban falo bata fitowa, tana iya sashin ta daga ita se magenta, duk da haka Yusuf kullum se yaje koda baze ganta ba kuwa.

Lambar wani abokinsa likita ya dubo a wayarsa ya kirashi, se da ta kusa katsewa sannan ya É—auka.

"Yusuf kana da kirki kuwa? Ace ka ɓata ko neman mutane baka yi?"

Yusuf yace "Amma ka tsaya mu fara gaisawa, sarkin ƙorafi"

Nan suka gaisa suka taɓa hirar yaushe rabo, sannan Yusuf yace "dama doctor Hamza ina da wata 'yar tambaya ne, dukda nasan tambayar da zan maka ba a fannin daka karanta kenan ba, amma na sanka da shige shige"

Hamza yace "shikenan ina jinka, Allah yasa nasan amsar tambayar taka, in babu amsar ma  se'a nemo"

'Masha Allah, dan Allah Hamza wace irin larurar ƙwaƙwalwa ce take sa mutum ya dinga gudun mutane? "

Doctor Hamza yace
"Anthropophobia kenan, is a mental disorder, masu irin wannan larurar suna jin tsoron taron mutane, idan abun ya tsananta ma ko ahalinsu basa son su raɓe su, sedai wasu tsirari daga mutane, basu fiye son taron jama'a ba, ko shiga cikin mutane basa so"

Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "to me yake haddasa ciwon"

Hamza yace "eh to, abun da yake haddassa wannan larurar ga wasu, idan an taɓa cin amanarsu, mussaman wanda suka yadda da shi, ko kuma wani abu da ya taɓa faruwa dasu mara daɗi a rayuwarsu, wasu kuma hormones ne suke haddasa musu excessive fear ya danganta dai, zakaga wataran suna lafiya ƙalau ga wanda ciwon be tsananta a gare su ba, amma idan ya tashi zaka ga basa son haɗa ido da mutane, basa son suga ana kallonsu, kosu kasa bacci, ko yawan ciwon kai, bugun zuciyar su ya canza, wasu numfashinsu har ɗaukewa yake, ko su dinga karkarwa in sunga baƙo, ko wanda basu yadda dashi ba, ko kuma su dinga wrong perception akan abubuwa, ko su dinga ganin duk wanda ya raɓesu ze cutar da sune"

"Ok magana, nagode sosai Hamza amma meye maganin ciwon?"

"gaskiya babu wani sahihin maganin ciwon gaskiya, rehabilitation ne a dinga kwantar musu da hankali tare da ƙoƙarin canza musu tunani daga mummuna zuwa kyakkyawa, dan wasu in damuwar tayi musu yawa suna fara shaye2, ko dinga wasu tunani wanda ya saɓa da abunda yake a zahiri, ayi ƙoƙarin samar da wani abu daze dinga ɗebe musu kewa, koya ɗauke musu hankali daga damuwarsu, in kaga an basu magani mafi akasari sedai a basu magani akan sauran matsala, kamar bugun zuciyar, ko daidaituwar hormones ɗin ko makamancin hakan...

Shiru Yusuf yayi yana tunani, meye alaƙar ƙwayar daya gani a ƙasan kofin shayin da za'a bawa Widad da ciwon nata, Doctor Hamza Yana cikin yiwa Yusuf bayanin ne ya hango Widad ta fito, tana nufo inda yake zaune, gaba ɗaya fuskarta a haɗe kamar kullum, yauma shigar tata da ta saba ita tayi, jikin nan a tsuke a cikin ƙananan kaya.

Da sauri Yusuf yace "shikenan nagode sosai doctor, nagane Allah ya saka da alkhairi" ya katse wayar

Ya shiga wani tunanin, "to wace irin Allura akewa Widad haka? Amal tace masa ana mata wata Allura, ga kuma abunda likita yace"

Ta ƙaraso ta kalle shi a yamutse tace
"É—akko mota, zamu airport ne yanzu"

Ya kalle ta yace
"me zamuje yi a Airport?"

"ban sani ba" ta bashi amsa

Ƙasa yai da idonsa yayi mata wani irin kallo sannan ya miƙe yai gaba, gaba ɗaya kasa gane kalar kallon tayi meya ke nufi da haka?

Ya É—akko mota ya kunna suka fara tafiya, suna tafiya yana satar kallonta yana tunanin, me zeyi wa Widad wanda ze temaka gurin canza tunanin ta mara kyau zuwa me kyau, kamar yadda doctor Hamza ya gaya masa.

Yana cikin tunanin wayarsa ta fara ringing, sedai lambar ba suna, kuma yana tsoron ya ɗaga yaje a cikin abokan aikinsa ne, wani yayi masa kwaɓa, sekuma ya tuna halinta, yanzu yana ƙin ɗaga wayar zata masa wata fassarar, haka ya basar ya ɗaga wayar yasa a kunnen sa tare da yin sallama.

Siririyar muryar mace ce ta amsa tace
"Aboki ya kake?" se yanzu ya gane muryar Nurat, murmushi yayi yace "lafiya ƙalau, light ya kike?"
Wani murmushi ne ya suɓuce mata tace "lafiya ƙalau friend, dama cewa nayi bari in kiraka mu gaisa"

"Amma gaskiya kin kyauta Light, ina fatan kina lafiya ba kya cikin kowace irin damuwa? Kin san damuwa da yawan haɗe rai yana sa mutum ɓacin rai da saurin tsufa, kuma duk kyansa ya koma kamar wani abun tsoro"

Da sauri Widad ta juyo ta kalle shi, amma ya basar ya cigaba da wayar, yayin da Nurat tayi murmushi tace "Ni lafiya ƙalau nake, bani da wata damuwa ko matsala ina Widad?"

"tana gidansu, ko ince kina gaishe ta ne?"

Kamar Yusuf yana ganinta ta girgiza kai tace "Kamanta kace kar in gaya mata muna abota? Na tambayane kawai dan inji ko tana lafiya"

"Eh kuma fa hakane? Amma yaushe zakizo ki ganta?"

"Ai ban san wane irin kallo za tayi min ba idan nazo gidansu, inajin tsoror"

Tsaki Widad tayi ba tare da ta kalli Yusuf ba tace

"Malam ka isheni, ka cikamin kunne"
Murmushi Yusuf yayi yace
"light, se anjima Madam tace na cika mata kunne"

Jiki a sanyaye Nurat tace "Madam kuma? Dama kana da Aurene?"

Yusuf yace "Babba dani kice bani da Aure, ina da Aure mana muna tare da ita ma, munɗan fita ne, se anjima kar in sake ɓata mata rai"

Wani irin wulaƙantaccen kallo Widad tayi masa, dama yasan a rina
"ni kake cewa matarka? Baka da hankaline, ni ka kalleni ka cemin matarka"

"waye cemiki dake nake ne? Am just kidding idan ba haka nayi mata ba zata ga kamar na mata wulaƙanci ne, kuma babu daɗi ka Wulaƙanta mutum it hurts a lot, Yusuf baya Wulaƙanta mutane"

Wani tsakin ta kuma ja ta ɗauke kanta, yayin da shi kuma yayi murmushi, a ransa yace 'Insha Allah, sena canza miki dukkanin wannan gurɓatattun tunanin naki kafin in kammala bincike na"

Gurin wani restaurant sukabi, tace masa ya tsaya ai kuwa yayi parking, tana yi tana duba agogon hannunta, ta buÉ—e motar ta fita, shima ya fito yabi bayanta.

Cikin restaurant É—in ta shiga ta samu guri ta zauna, Yusuf be jira unarninta ba shima yaja kujera ya zauna.

Aka kawo musu menu
(jadawalin Abincin da suke available)
Ta karɓa tana jujjuya menu ɗin, ɗan ɓata fuska tayi ta zaɓi Abunda take so,
Aka bawa Yusuf ma, ya kalli Menu É—in ya girgiza kai yace
"Ni ban iya cin irin wannan Abincin ba gaskiya, Umma ta cika min ciki da É—umamen tuwo dan haka ni ba abunda zanci"

Kallonsa tayi ta ɗauke kanta, yayin da waiter ɗin tayi murmushi ta karɓi menu ɗin ta tafi.

Karon Farko da Yusuf yaga Widad tana cin normal Abinci, sam bata damu da Abinci ba, sedai yaga tana 'yan ciye ciye, ta yaya mutum zeyi lafiya ba tare da cin cikakken Abincin da ze gina masa jiki ba, ko duk cikin rashin yardar ne oho mata.

Yanzun ma ba wani cin Abincin take ba, ɗan cakala take a jikin spoon, kamar wata ƙaramar Yarinya kamar me wasa da Abincin tana kaiwa bakin ta .

Yusuf ya ɗan ƙura mata ido yace "Madam are you really Hungry?"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.