Akidata Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Akidata_Book_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 4 of 8
Cigaba da cakalar Abincin ta tayi ba tare da ta kula shi ba.
Ko ɗaya bisa ukun Abincin bata ci ba, ko naman kai bata taɓa ba, ta ture Abincin ta ɗau tissue tana goge bakin ta, 'Iko se Allah, Abincin naira dubu huɗu akayi wa wannan cakalar aka barshi, wani yana nan yana fama da Yunwa'
"wai Harkin ƙoshi?"
"wai ina ruwanka dani ne? Ta yaya zan iya cinye wannan Abincin duka?"
"Amma kin san bazaki iya cinyewa ba kika sa aka kawo miki? Akwai dubban marasa ƙarfi da Abincin naira ɗari ma gagarar su yake a rana, kalli uban Abincin da kika bari, wataƙila yanzu wannan da kika rage sedai a zubar, ba kyau Wulaƙanta Abinci, wataran kema ze iya Wulaƙanta ki"
Ko kallonsa ba tayi ba, ta É—auke kanta tana kallon wani gurin, amma tayi shiru tana saurarensa, gefe guda kuma ta shiga tunanin maganar sa, dagaske akwai wanda suke rasa Abincin naira É—ari ya gagare su? To wani irin Abinci ma mutum zeci da naira É—ari, se a samu mutum yace bashi da naira É—ari?.
Yusuf Yaja plate É—in Abincin gabansa ya É—au spoon ya fara cin Abincin da Widad ta rage.
Kallon Yusuf take, sosai mamaki yake bata shi sam be É—au komai da zafi ba, Abincin data rage yake ci, ko dan dai shi talaka ne oho.
Yusuf ba ƙaramin mamaki yake ba yadda take ɗaga masa ƙafa, dan shi kansa yasan wasu lokutan yana wuce gona da iri, tana ƙyaleshi ne kawai
"ya naga kina kallona ko nayi wani abun ne na rashin yadda?"
ÆŠauke idonta tayi daga kallonsa zuwa wani gurin daban.
Yusuf ya ciko spoon yace
"Kinga yadda ake cin Abinci a ciko cokali da Abinci, se mutum ya ƙoshi ba yadda kike yi ba, kamar kina wasan yara, koda yake yarinyar ce ai"
Ɗago ido tayi ta kalle shi, amma ya cigaba da cin Abincin yaƙi kallonta, lallai Yusuf ya samu dama a kanta ya fara rainata, tunda harya samu damar gaya mata maganganun da yaga dama, ita kanta Widad tana mamakin yadda take ƙyale Yusuf, ba yadda za tayi dashi wata ƙaddara me ƙarfi ta shigo dashi cikin rayuwarta, wanda ko dan albarkacin hakan yaci ta dinga ɗaga masa.
Seda ya kammala sannan ta ajiye masa ATM ɗinta, ta miƙe ta nufi hanyar fita, Yusuf kuma ya nufi gurin biyan kuɗin, kafin Widad ta kai ga ƙofar fita wani mutum da tunda suka shigo yake kallonta yabi bayanta.
Yusuf yace "ashe akwai mini Drama yau"
Ya biya kuÉ—in ya fito, sedai yana fitowa ya tarar tana zazzagawa Mutumin masifa.
"Kalle ka ni zaka biyo kace in baka lambata? Bazan bayar ba shashsasha an gaya maka kowa sakaraine irin ka?"
"Ni kike cewa sakarai?"
"Na gaya maka ko akwai abunda zaka iya ne?"
Yusuf ya ƙaraso da sauri gurin yace "haba bawan Allah, ya zaka biyo matar Aure kace kana so?"
Mutumin ya kalli Yusuf yace "Matar Aure kuma? Da wannan shigar tata?"
"koma wace irin shiga ce tayi ina ruwan ka? Haka muka tsara rayuwar Aurenmu, haka muka ga damar yi, idan har kasan shigar da tayi bata dace ba meye na biyo ta? Kana gurin nan muka zo tare mu kaci Abinci, danme zaka biyo ta kace kana so?"
Mutumin yace "Amma indai wannan matarka ce gaskiya kayi dacen Auren kyakykyawar mace, sedai bata da É—a'a kuma bata san darajar Auren ta ba"
"bakomai a haka nake son a bata, sannan karka kuma gangancin kiran ta da wasu miyagun kalamai, ka gode Allah da ban É—au mummunan mataki akanka ba"
Ya juya ya kalli Widad da mamaki ya hana ta magana, A fusace ta juya ta tafi mota ba tare da tace komai ba
Yusuf ya juya ya koma motar shima yana shiga ya zauna, ya kunna motar suka fara tafiya, ba tace komai ba se tafasa da zuciyar ta take yi
Ba zato ba tsammani, Widad ta Ƙanƙance ido tace
"i thinks you drunk something abusive today, kasan me ka faÉ—a kuwa? Which type of Weed did you take today? Wane irin rashin hankali ka aikata? Meye hakan kake ne dan me zaka dinga danganta kanka dani a matsayin mijina, kai ko Auren zanyi zan auri talakan mutum kamar Kane?"
Dukda yadda kalaman Widad suka daki zuciyar Sa haka ya daure, yayi parking ɗin motarsa, ya matsa Kusa da ita ya matsa yace "Abunda kika ci dai shi naci, dukda baki san meye So ba, ƙarewa ma kince baki yadda dashi ba, amma the magic behind Love is that, ba ruwan sa da talaka kome kuɗi, sannan wannan abunda nayi shine kaɗai mafita daze hana kowane kare da biri binki, da kuma ƙarewa surar jikin ki kallo, please Dress decently to avoid such type of people, dukda ina matsayin me miki aiki, aikin ma na direba, I have to tell you something, you have an attractive beauty Widad, stop exposing it anyhow yana taɓa zuciyata a duk lokacin da kika fito da wannan shigar naga wasu na ƙarewa wannan kyakykyawar halittar kallo, your beauty suppose to be only for your husband, duk wata mace me tsadace jikinta ma me tsada ne meyasa zaki dinga bari ana ganin naki?"
Ɗaga ido tayi tana kallon sa, gaba ɗaya Yusuf ya rufe mata baki, ya kulle mata kai, gaba ɗaya ta nemi izzar da jin kan da zata masa wulaƙanci ta rasa, yau wani irin kwarjini yayi mata data kasa cewa komai, shi kuma ya samu damar hakan yake ta abunda yaga dama, a baya zata iya rantsewa baze aikata haka ba, ganin yadda ko magana baya son yi.
Haka suka cigaba da tafiya kamar kurame, kowa da abunda yake saƙawa a zuciyar sa, gaba ɗaya tunanin rashin mutuncin da zata yi wa Yusuf take.
Har suka ƙarasa airport bata iya cewa komai ba, parking yayi amma bata buɗe murfin motar ta fita ba, shima zaman sa yayi yaƙi fita, ya sauke glasan suka cigaba da zama, lokaci2 ta dinga duba agogon hannun ta.
Buɗe ƙofar tayi ta fita, shima ya buɗe ya fito, Alhaji Nasir ne yake tahowa da brief case ɗinsa a hannun sa.
Yusuf ya ƙarasa da sauri yana gaida Alhaji Nasir tareda karɓar brief case ɗin hannun sa.
Alhaji Nasir yace "Yayana na kaina, fatan na sameku lafiya ya amana ta?"
Yusuf yay murmushi yace "Alhamdilillah"
Ya kalli Widad yace "my Lovely har yanzu kina fushi da Dad ko?" yai maganar yana rungume Widad, kamar anmata dole tace "Welcome Daddy"
Alhaji Nasir ya É—an shafa bayan ta yace"thank you sweetheart" suka É—unguma zuwa mota gaba É—aya, suna tafiya Alhaji Nasir da Yusuf ne kawai ke hira, Amma Widad tunanin ta ta yaya zata hukunta Yusuf.
Har Yusuf ya gama aikin sa na ranar ya tafi Widad bata samu mafita ba.
***********************************
"Jama'a bafa a bori da sanyin jiki, wannan ce damar da yakamata muyi amfani da ita, tunda Allah yasa yarinyar nan tana ƙasar nan musan abunda za muyi" cewar Alhaji Munir
Alhaji Musa yace "Ni idan an samu abun nan falillahil hamd, amma babban burina be wuce in Wulaƙanta Alhaji Nasir a idon duniya shida ahalinsa ba kamar yadda ya Wulaƙanta ni ya ɓata min suna"
Alhaji Haruna yace "gaba ɗayanmu buƙatar mu ɗaya ce, kuma kunsan Alhaji Bukar shike bamu umarnin abunda zamuyi, karmu yadda muyi abunda ze waegaza shirin mu, yanzu yarinyar taje gidan yari tayi wa Hashim barazana akan indai da hannun sa akan wannan lamari daya samu Bala to tabbas zata ɗau mataki akansa "
Alhaji Musa yace " Umarnin Alhaji Bukar kawai nake jira, amma akwai yuwuwar shima a kauda shi, dan komai ze iya faruwa barinsa a doron ƙasa"
Alhaji Haruna ya zame akan kujera yana shafa tumbinsa yace
"Ni dai kam da zan samu yarinyar nan, So nake gaskiya, dan akwai ta da ƙira daidai gwargwado".
Tsaki Alhaji Munir yayi yace "kai ka fiye shirme, ana ta kai wake ta kaya, in in hutawa kake so, ka fita ƙasashen waje ga mata nan farare yadda kake so, amma yanzu ka bari idan muka karɓi abunda muke so, muka aika Nasir Daula kiyama, se kayi yadda kaso"
Wata uwar dariya suka saki hadda shewa.
**********************************
"Bulama tafiya tayi Alhamdilillah, na samu approval na fara business É—ina da China"
"Masha Allah, naji daÉ—in hakan, Allah yayi jagora"
Baban Widad yace "Ameen ya Allah, sedai ko kun samu saɓani da 'yar taka ne? Tunda na dawo naga bata walwala ko akwai matsala ne?"
Alhaji Bulama yai murmushi yace "hmm Widad' yata ta kaina, tabbas munyi faɗa, kasan tunda nace ayi mata Aure take jin haushi na, tazo ta sameni akan wai sena mata Visa ta koma naƙi, shine take fushi"
Alhaji Nasir ya girgiza kai yace "Nima wancan satin ta kirani tana kuka, akan lallai sena kiraka nasa an mata visa ta koma, ni kuma gaskiya bazan bari ta koma ba, idanma zatavkoma se bayan Auren ta da Fahad sa tafi tare"
"hakane, daga lokacin da ta fara tara iyali dole ta dena wannan halayen nata, sannan mamanta ta kawomin ƙararta akan yadda suke da direban nan, na kirata nayi mata faɗa, nanma ta sake yin fushi dani"
Alhaji Nasir yai murmushi yace "ina tunanin akwai wani ɓoyayyen al'amari a tattare da yaron nan, ba ƙaramin daɗi naji ba ganin shine mutum na farko bayan nida kai da Widad take sakewa dashi"
"Amma karfa muyi sake yazo suyi shaƙuwar da zamu yi da nasani"
"Insha Allah ba zamuyi ba, dan yaron yana da tarbiyya sosai"
"Amma idan soyayya ta shiga tsakanin su fa?"
Alhaji Nasir yace " Yarinyar da bata yadda da soyayya ba, ta ina zasu fara soyayya? Gaba ɗaya Widad ɗina a birkice take bata da alƙibla"
Bulama yace "Kasan bata da alƙibla ai kuwa ba abun mamaki bane ta fara soyayya da direban ta, tunda shi so baya sallama".
"to nidai duk abunda ze saka ta farinciki shi nake so, idan ta kawo shi tace tana so bakomai se in Aura nata shi"
Bulama yace "Allah ya kiyaye mu aura mata direba haba Daula"
"to masu 'ya, ai seka biye mata kuyi tayi"
Sukayi dariya suka shiga hirara duniya.
***********************************
Sintiri take a ɗakin ta, tana son gazgata abunda take ji a zuciyar ta game da Abokin ta. Dagaske na kamu da Son wanda yake daga ɓangaren maƙiyin mahaifi na, amma ban san alaƙarshi da Widad ba, amma tunda na gansu tare suna da alaƙa.
Shiru tayi tana tuna yadda ya zauna a kusa da ita yana mata magana, cikin rarrashi danta saki jiki dashi.
Kamar light da yake kiran ta dashi yafi komai yi mata daÉ—i, Amma dagaske yana da Aure? Ta tambayi kanta, anya za'a yarda a auramin me mata? Gashi kuma É—an uwan Widad.
Dafe kai tayi tace "Subhanallah"
"ke lafiya kuwa? Sintirin me kike tayi haka kamar kinwa sarki ƙarya?"
Juyawa tayi ta kalli inda Maman ta ke tsaye tace "bakomai fa"
"bakomai, a hakan? Gaba É—aya alamu sun nuna baki da gaskiya sam"
Ta É—an tura baki tace "wallahi ina da gaskiya"
"shikenan, idan tayi wari maji"
Nurat ta koma kan gadonta ta zauna ta É—akko wayarta ta shiga kiran layin Yusuf amma shiru baya shiga, tayi2 harta gaji ta ajiye, tana mamakin ya akayi hakan ta faru?
Shikuwa Yusuf tun ranar data kira shi agaban Widad, yana komawa gida ya cire layin ya ajiye gaba É—aya.
**********************************
Oga Suleiman ne zaune akan kujera yana gwadawa Sakina wasu ayyuka a computer, sun maida hankali sosai kan aikin.
Abbas ne yayi sallama, suka ɗago gaba ɗaya suka dube shi tare da amsa sallamarsa, Sakina ta gaida Abbas, yayin da Abbas ya ƙamewa Suleman cikin girmamawa.
Suleiman ya bashi damar zama, sannan ya miƙa masa hannu suka gaisa, Suleiman yace "Abbas kwana biyu banga Yusuf ba fa, ya kamata ace yazo ya gabatar min da sakamakon binciken da yayi"
Abbas yace "ranka ya daÉ—e, nima kaina na kasa gane inda yasa gaba, gaba É—aya kamar ba aikin yake ba, yaje ya shantake se abun Arziki yake samu a gidan, alherin da suke masa yasa gaba É—aya hankalin sa baya kan aikin, da dai da hali a canza shi da wani kawai"
Suleiman yace "Amma kaika cemin ze iya aikin, da kai nace zan bawa ka nunamin ya fika haƙuri da juriya"
"Ai Oga sam ban san haka ze faru ba, ban taɓa sanin Yusuf yana da son abun duniya ba seda ya karɓi aikin nan, ba abunda yake se neman gindin zama a gidan da yake"
Sakina kam sakin baki tayi tana sauraren yadda Abbas ke ɓata Yusuf a gurin ogansu, wanda hakan ze iya jawowa Yusuf babbar matsala a gurin aikin nasu, Yusuf ya yadda da Abbas sosai, dan yana masa kallon ɗan uwa bama abokin aiki ba.
Oga Suleiman yace "shikenan, zan duba idan da dama zan kira shi a waya ma, inaga karɓar aikin zanyi daga hannun sa in bawa wani"
***********************************
Gidan shiru babu kowa, Yusuf yana inda ya saba zama idan yaje gidan su Widad, Murtalah ne yazo inda Yusuf yake yace "Malam Yusuf kana nan kana hutawa ashe?"
"wallahi kuwa Murtala ya aikin?"
"Alhamdilillah, ai kana fama Yusuf, kullum se kazo ko zakayi aiki ko ba zaka yi ba"
Yusuf yayi murmushi yace "to ya za'ayi tunda na yadda zanyi aikin, ai dole in cika ƙa'idar aikin"
Murtalah yace "hakane" suna cikin hirar Amal ta fito, ta ƙaraso inda Yusuf ke zaune, ranta a ɓace tace "kazo ana son ganin ka"
Ba musu ya miƙe yabi bayan ta, suna shiga babban falo har Yusuf zeyi hanyar ɓangaren Widad, dan yasan be wuce ace ita take kiransa ba, tunda Alhaji Nasir baya nan.
Amal tace "A'a, ba a nan ake neman ka ba"
Ta nuna masa hanyar ɗaya part ɗin dabe taɓa taka gurin ba, seda ya ɗanyi jimmm ya kalle ta sannan yace "shikenan muje"
Suka rankaya ɓangaren data nuna masa, tana tafe yana binta a baya
Wata ƙofa ta buɗe suka shiga, matsakaicin bedroom ne, me ɗauke da kayan more rayuwa sedai be kai haɗuwar na gimbiyar gidan ba.
Amal ta juyo ta kalle shi tace "Yusuf Meka ke nufi dani ne?"
Cike da rashin fahimta yace "kamar yaya? Kince ana kirana kuma kin kawo ni nan"
"Yusuf nina nake nemanka ba wani ba, na gaya maka abunda ke raina amma ka maidani kamar wata banza, Haba Yusuf me yasa baka da tausayi ne? Soyayyar ka nata wahalar dani amma hankalin ka yana kan waccan banzar mahaukaciyar, har dama ka samu a kanta wanda zaka rama irin wulaƙancin da take maka, ATM ɗinta kwanansa nawa a gurin ka? kamata yayi kayi amfani da wannan damar ka azurta kanka, tausayin mara tausayi asara, asara ne gagaruma ko dai dan Widad tana da kuɗi shiyasa kake Wulaƙanta ni?"
Yusuf be taɓa jin son Amal a ransa ba, ta yaya suna muzanta wadda suke cin Arzikin gidan su, ina gashi da yake bare? Kuma suna ta jadadda masa yayi wannan gagarumar sata haka?
"Amal ki fuskance ni, niba na WulaÆ™anta mutane, sannan bani na tara musu dukiya ba, ta yaya zan musu wannan mummunan aiki? Ni ba Æarawo bane, dukiyar Widad bata gabana mutunci da girmamawa ya fiye min wata dukiya komai yawan ta, indai ban rasa ci da sha ba Alhamdilillah a yadda Allah ya ajiye ni, Widad batamin laifin komai ba, babu wani abu da tayi min wanda zesa in cutar da ita ko mahaifinta, tsakanina da su in musu aiki ne su biyani bisa ga yarjejeniyar da na sakawa hannu, Amma Amal tsakani na dake babu batun Soyayya duba da banbanci da kuma tazarar dake tsakanin mu, ke 'yar masu kuÉ—i ce, ni kuma talaka ne matsiyaci kamar yadda mutan gidan ku suke faÉ—a"
"Yanzu kana nufin ba zaka karɓi Soyayya ta ba Yusuf, ka zaɓi cigaba da wahalar da zuciya ta, mace me kima kamata ince ina sonka amma ka watsamin ƙasa a ido? To wallahi baka isa ba, zaɓi biyu ke gareka kodai ka karɓi Soyayya ta, ko kuma in shirya maka gadar zaren da idan ta rufta da kai har Abada ba zaka sake wani Amfani ba"
'Kiyi duk abunda ki kiga dama, tabbas da soyayyar gaskiya kike min da baki faɗi haka ba, tabbas na taɓa Soyayya nasan zafin ta, Amma ba' a dole a soyayya "
Yana gama maganar ya juya ya fice daga ɗakin, biyo bayan sa tayi tana ƙwala masa kira, Amma yaƙi tsayawa yana buɗe ƙofar part ɗin ze fita yayi tozali da gimbiya 'yar masu gida, Widad ce a tsaye a bakin ƙofar dake facing ɗin wadda ya fito, se muzurai take idanunta sunyi Ja, tana masa wani irin kallo me wuyar fassara.
Me kuke tunanin ze faru?
(Masha Allah, am speechless wlh, Addu'arku tayi tasiri a gareni ina miÆ™a muku godiya, masu tambayar jikin Daddy Alhamdilillah ya warke ras💃💃💃 almost done with the exams only some part remains, saura fatan Nasara, farinciki yasa nace bari inyi surprising É—inku da posting, ina jiran jin comments me fasa waya, idan anyi Comment yadda nake so gobema akwai posting insha Allah ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ ina godiya masoya)
Domin sharhi, gyara, ko shawara feel free to contact me
Ayshercool
07063065680          _*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
             PART1
                Page 15
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Turus Yusuf yayi ya rasa me yakamata yayi? Me zeyi wanda zesa Widad ta yadda da shi, Amal ma da ta ƙaraso domin cimma Yusuf, tana ganin Widad itama tayi Turus ta shiga rarraba ido kamar an sacewa karya 'ya' ya.
Widad tayi wa Yusuf alama da hannu ya biyo ta, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige, haka ya bi bayan Widad zuwa part ɗin ta, gaba ɗaya ya saddaƙar yana jiran jin ruwan masifa daga bakin Widad.
Ta kalle shi tace "nayi list na abubuwa da nake buƙata ne, za kaje ka siyomin, ka lura da duka abunda na rubuta bana buƙatar product ɗin basu nace ba"
Jiki ba ƙwari ya jinjina mata kai, ta ɗakko paper ta miƙa masa tare da ATM card, a sanyaye yasa hannu ya ksrɓa, amma harya juya zefita beji tace masa komai akan ganinsa ya fito daga sashin su Amal ba.
Har ze fita ya tsaya ya juyo ko zata yi magana, amma yaga tana danna wayarta, tana É—aga ido suka yi ido huÉ—u dashi ta kalle shi tace
"Lafiya? Ka tafi mana"
Ya kalle ta yace "bakomai"
Ya juya ya fita yana sake waiwayen Widad ko zata yi magana.
Fahad ne keta shirya kayansa a trolley, Anwar ya kalleshi yace "Fahad ji nake kamar in bika mu koma Nigeria tare, amma ba yadda zanyi, munzo tare ka rigani kammaluwa"
Fahad yace "Ai kai ba komawa Nigeria ce ta dame ka ba, zuwa kaga wannan yarinyar ne ya dame ka"
"ƙwarai kuwa faɗi ka ƙara Fahad, ni kaɗai nasan abunda nake ji game da ita, nima ina nan dawowa ai Insha Allah, inga farincikin zuciya ta"
"Allah yayi maka magani, dan kaibnaga abun naka ka afka da yawa"
 "kadai bari kawai, dan Allah Fahad kayi ƙoƙari ka samo min lambar ta idan kaje Nigeria"
Yatsuna fuska Fahad yayi yace "gaskiya ban maka Alƙawari ba, dan tamin rashin mutunci marinta zanyi"
Anwar yayi dariya yaceÂ
"da kuwa ka ƙare rayuwar ka a prison"
"kaini ka isheni da zancen yarinyar nan haba"
Ƙarshe Fahad ya fice ya barwa Anwar ɗakin, dan ba ƙaramin haushi yake bashi ba idan yana zancen Widad.
***********************************
"Ana ƙoƙarin a hallaka min ɗan uwana, sannan kuna min barazana da rayuwa ta, gefe guda ga yarinyar nan itama ta sakoni gaba, anya Alhaji Haruna kunmin adalci kenan?"
Alhaji Haruna yace "Adalci ɗaya za muyi maka Sale, kayi aiki nan na ƙarshe da muke so, in ba haka ba da kai da ɗanuwanka haka zaku ƙare kuyi biyu babu, tabbas muka samu abunda muke so zamu fidda ɗan uwanka, sannan baku ba na kusa da kuma seya azurta"
Saleh ya fesar da iska yace "kamar yaya? Yanzu dai ta tabbata kune kuja bawa ɗan uwana abunda yasa rashin lafiya ta kama shi, don ku kasheshi karya tona muku asiri"
Alhaji Haruna yayi murmushi yace "zata iya kasan mune, kuma zata iya kasancewa bamu bane ba, ka sani ko ɗan uwanka ya tona mana Asiri bashi da wata cikakkiyar hujja a kanmu, kuma muna da ƙarfin da zamu siye Alƙalai da lawyoyi, shari'ar ta tafi a banza, shi kuma a cigaba da tsaron sa, abu ɗaya ya rage maka, shine ka haɗa kai damu mu gudanar da wannan aikin tare "
Maimakon Saleh yayi magana, sema tsaki da yayi yai waje yana wani irin huci kamar kumurci.
***********************************
Kafin Yusuf yaje aiken da Widad tayi masa seya wuce gida ya É—akko system É—insa ya wuce office.
Yana shigowa harabar station ɗin ya tsaya yana gaisawa da mutane, Sakinace ta hango shi, ta yunƙuro ta fito da sauri ta tare shi, ta kalle shi tace
"Sannu da zuwa yau ka leƙo mu kenan?"
"Yawwa sannu" kawai yasa kai ya wuce, ya nufi office É—in Abbas, gaba É—aya dirircewa tayi ta shiga tunanin ya zata yi ta fahimtar ds Yusuf, irin illar Kasancewar sa da Abbas.
Yusuf yana zuwa ya miƙawa Abbas hannu suka gaisa, Abbas yace "mutumina gidan daula sun ɓoye mana kai gaba ɗaya fa"
Yusuf yace "bari kawai Abbas, kullum a cikin zullumi nake, the more nake binciken the more nake sake gano Wata sarƙaƙiyar, in taƙaice maka ma an fara bina wallahi"
"Kamar ya an fara binka?"
"Wai wani abu ake so in karɓo a hannun Widad, gashi yau na shiga wata cakwakiya a gidan nan, ina ta jira ta sauken kwandon bala'i amma taƙi kulani, ƙarewa ma aikena tayi, shine nace tunda na samu chance bari inzo inga oga Suleiman"
Abbas yace "ka gan shi kayi masa me?"
"In fara presenting abunda bincike na ya nuna min mana, akwai buƙatar tsananta bincike a wasu guraren, amma kaga ai yakamata in gaya masa"
Abbas yace "garajen Meka ke hakane Yusuf? Ka bari ka kammala binciken nan, idan ka kammala base ka kawo masa ba, Yallaɓan mafa baya nan ana nemansa a headquarter za suyi meeting, kasan koka bashi cewa zeyi kabi komai a hankali"
"So kake inzo inyi laifi kenan? Ni nafi ganewa in fara presenting É—in aikin"
Abbas yace "A'a karka damu, kabi komai a hankali"
Yusuf yace "shikenan bari in tashi in tafi, dama nan aikena aka yi"
Abbas yace "Amma Yusuf akwai cigaba a cikin binciken kuwa?"
Yusuf yace "Sosai makuwa, an samu ci gaba, the more nake binciken the more nake sake cin karo da wasu matsalolin, Amma idan bincikena ya tabbatar da abunda nake zargi, mutane da yawa a ƙasar nan za suji kunya"
Abbas yace "wai tukuna ma inga abunda kayi kake son ka nuna masan, suwaye za suji kunyar?"
Yusuf yace "kabari sena kuma dawowa se mu cigaba da zancen yanzu ina sauri tunda baya nan tafiya zanyi"
Yusuf yaja System ɗinshi yai waje, bayansa Abbas yabi da kallo yana ƙwafa, 'Sena sa an Ƙwace aikin daga hannun ka tukuna za kayi bayani'
Sakina tana so ta yiwa Yusuf magana, amma sam yaƙi bata fuska, tana ji tana gani ya fice daga gurin, tunani ta shiga yi, yadda Yusuf ya yadda da Abbas babu lallai kota gaya masa ya yadda da abunda tace.
Yusuf yaje yayiwa Widad siyayyar data aike shi, ya wuce gida ya gama abunda yake yi sannan ya koma gidan su Widad.
Har yanzu gabansa faÉ—uwa yake, ya É—au kayan ya shiga ya kai mata, sedai da yaje bata part É—in nata se maganta akan gado.
Ya ajiye mata kayayyakin, ya ɗaga ƙasan pillow ɗinta ya sa mata ATM Card ɗinta ya fito.
A falo ya ci karo da maman su Amal, ta masa wani irin mugun kallo tace "kai daga yau, bana son sake ganin ka shigomin falo ba tare da ka nemi izini ba, na gaji da wannan sintirin da kakemin, baligi kana ratsawa kana wuce ɗakin ta, baze yuwu ba"
"kiyi haƙuri Hajiya, nima ba da san raina ba, sedai ita Madam bata jiran izinin kowa kafin ta yanke hukunci, dan haka wannan maganar a tsakanin ku ya kamata ku tattauna ta"
Har Hajiya Halima ta buÉ—e baki zata yi magana se kuma tayi shiru, waiwaya wa yayi yaga Shigowar Widad ce tasa ta yin shiru, bata kula su ba tayi part É—inta, shima Yusuf ya silale ya bar falon.
*******************************
"Maman Yara ina cikin farinciki Ɗana ze dawo, yakamata ayi dukkanin wasu shirye shirye da suka dace domin tarbarsa, yasuhe rabon sa da ƙasar nan? Sannan ya dawo ya tarar da kyakkyawan Albishir"
Haɗe rai Hajiya Sarah tayi tace "nikuma takaici ne fal raina wallahi"
"Saboda me takaici fal ranki, kamar ba É—anki me ze dawo ba?"
"Eh É—ana ne, amma abunda kake shirin yi kaima kasan be kamata ba, ta yaya yarona lafiyayye zaka haÉ—a shi Aure da mahaukaciyar da bata san girman kowa ba, ga bata da tarbiyya"
Alhaji Bulama yace "Easy Madam, Sarah shifa ɗa na kowane, bekamata ki cigaba da aibata Widad ba, itama kamsr 'ya take a gurin mu duba da yadda mahaifinta yayi mana halacci a rayuwa, muna ƙoƙarin yin abunda zesa ta dawo hayyacin ta ne, kuma kinga mu munsan larurarta, Fahad ze iya haƙuri ya zauna da ita, saɓanin a bawa wani a waje Auren ta"
"to kai kaÉ—ai ne yakamata kayi tamakon? Ina sauran mutanen gari? Nidai gaskiya aka haÉ—a Auren É—ana da wannan tantiriyar mara mutuncin an cucemu, kai kanka da kake matsayin uba a gurin ta cin zarafin ka take, inaga É—anka kuma?"
"Sarah, bazan zaɓawa yarona abunda ze cutar da shi ba, Aure yana gyara mutum, wuyarta su zauna a guri ɗaya ze iya canza ta"
"A'a canza halin wannan yarinyar banga ta inda ze yuwu ba Sam, kawai ka canza shawara da tunani"
Tai maganar tare da miƙewa ta bar masa ɗakin
************************************
Yallaɓai Suleiman na dawowa, Abbas ya miƙe ya tafi Office ɗinsa, ya shiga ya gaida Sulaiman cikin girmamawa irin ta masu ɗamara, se da yayi masa izini sannan ya zauna, suka sake gaisawa.
Abbas yace "Yallaɓai, lokaci fa na ƙurewa, game da aikin nan daka bawa Yusuf, bana tunanin abunda aka sashi yake yi, ɗazu yazo gurin nan, na ɗanyi masa tambayoyi akan aikin, Amma Amsoshin daya bani sam basu gamsheni ba, da alama dukiyar dake gidan da alherin da suke masa yasa ya bar aikin da 'aka sashi "
" Amma a iya sanina Yusuf mutum ne me hazaƙa, nasan shi da ƙwazo da himma akan aiki, ba shida kwaɗayi sam"
"Yallaɓai mutum na iya canzawa a kowane lokaci, Yusuf abokina ne, amma ba yadda zanyi, bana son inci amanar aiki ko' a samu matsala akan harkar aikin mu kimar mu ta zube a idon duniya, Amma ya kamata kayi wani abu yallaɓai"
Suleiman ya ɗanyi shiru sannan yace "idan kuwa hakane, to tabbas Yusuf ya bani mama, sedai zan kira shi muyi magana, zan bibiye shi idan har na gano maganar da kake gayamin gaskiya ne, zan ɗau mataki na musamman akansa"
Abbas yace "Yallaɓai idan har ka kira shi kuyi magana ai zaka ɓata komai, zeyi duk me yuwuwa ya kare kansa koda kuwa ƙarya ze maka danka yarda da shi, tunda shima jami'in tsaro ne yasan duk hanyar da zebi ya kare kansa"
Suleman yace "Abbas base ka nunamin aikina ba, Nagode da wannan bayani naka zan bincika, ka ciji jami'i nagari tunda har kishin aikin ka be hanaka ɓoye laifin Abokin ka ba"
Abbas ya miƙe ya sarawa Suleiman sannan ya fice.
Koda ya bar Office É—in Suleiman Office É—insa ya koma yana tunani, tunani yake akanme zeyi wanda zesa gaba É—aya aikin da Yusuf yayi ya lalace kowa ma ya huta?
************************************
Gaba ɗaya Nurat ta rasa abunda yake mata daɗi, ta shiga damuwa rashin samun wayar mutumin da ko sunansa bata sani ba, dama Widad ta dena ɗaga wayarta gaba ɗaya, tun ranar da tazo birthday ɗin ta, abun nan ya faru, ta fara shawarar ko gidan su Widad zata je don ta tambaye ta wannan wanda suka zo taren.
Sedai kuma tayi wani tunani, aiki ne me matuƙar sauƙi a gurin Widad ta sa aka mata a ɗaure, bata da tabbacin Abokinta ya gayawa Widad abunda ya faru kokuma A'a, gaba ɗaya ta rasa abunda yake mata daɗi, komai ya dena mata daɗi se tunanin wannan bawan Allah, me matuƙar kirki, a farko tayi zaton shima mugu ne lokacin da ya ritsata har yayi mata barazana, amma yanzu ta gane ba haka abun yake ba, ranar da yazo gidan yanayin yadda ya mu'analance ta da kyakkyawar ma'amala.
************************************.
Fahad ne da Anwar tsaye a tashar jirgin Sama, Anwar yace "Fahad ina taya ka murnar kammala karatun ka, Allah ubangiji ya kaika gida lafiya, sena taho nima in next couple of weeks Insha Allah"
Fahad yayi murmushi yace "to baban Soyayya, kaima ina taya ka murna, tsiran namu befi sati biyu, ina maka fatan Nasara ɗan uwana seka taho".
Suka rungume juna suna murmushi, sannan Fahad yaja trolley É—insa yayi gaba.
"Amal kin san wani abu kuwa? Munyi waya da Yaya Anwar yace min Fahad yau ze dawo Nigeria, baki ji daÉ—in da nake ji ba, dan Allah me ya kamata inyi wanda zan sake kama zuciyar sa, yaji in ba niba se rijiya"
Wani banzan kallo Amal tayi wa Ramlah tace "Ban sani ba, kije kiyi abunda kika ga ya dace"
Cike da mamaki Ramlah tace "lafiyar ki kuwa? Me yayi zafi daga neman shawara zaki hayayyaƙomin?"
"dole kice haka mana, da yake matsalarki itace damuwa kawai, ni ina lokacin da nake cikin tawa damuwar ziga Mummy kikeyi, kuka haɗemin kai kuka dinga hantara ta, har dena kulani kukayi saboda kawai nace ina son Yusuf, Ashe ke kaɗai kika san So, ni ban sanshi ba ko? Can ta mulmule miki gara tun wuri kema ki cire shi daga ranki, dan in kin manta bari in tuna miki, 'yar masu gida akace ze aura kuma kinsan baki isa kice kina da matsala da hakan ba, danke ba mutum bace a kanta, kuma kinsan baki isa kiyi takara da ita ba, akan haka ba' aƙi a baki red card daga gidan nan ba, you better go back to your senses "
Tana gama faɗin haka ta miƙe ta fice daga ɗakin, wani zazzafan gumi ne ya shiga karyowa Ramla, dan gaba ɗaya ta manta ds batun ance za'a haɗa Auren Widad da Fahad.
Gaba É—aya kanta ys kulle dan bata san wama yakamata ta tunkara ba, Mummy ba abunda zata iyayi, shiru tayi tana tunanin meye mafita? "
************************************
Widad ta dudduba Aiken da Yusuf ya kawo mata, ya siyo komai kamar yadda tace, harda receipt ya kawo mata, tana duddubawa taci karo da wata leda, ɗakko ledar tayi ta buɗe me zata gani, wasu tsala tsalan Abaya ne kala biyar, kowacce da kalar ta sunsha stones se ƙyalli sukeyi, ta ɗauka ɗaya bayan ɗaya tana jujjuya su.
'me wannan gayen yake nufi?' ta tambayi kanta
'harni ze saiwa kaya ya bani? Meya maida ni ko nayi masa kalar saka wannan kayan?'
Tattare kayan tayi ta fito falo a fusace, da watsasu akan kujera, part É—in su Amal ta nufa tana huci, babu ko sallama ta banka É—akin su Amal, gaba É—aya seda suka razana, mussman Amal dan a tsorace take tun ranar da Widad ta gansu tare da Yusuf.
Ta kalli Amal tace "Kije bakin gate, ki kiramin wancan sakaran direban yanzun nan" tana gama maganar ta juya ta fice
Ramalh na ganin a yadda Widad ta shigo tayi magana, tasan akwai matsala dan haka ta miƙe ta fita dan ganin me ze faru,
Jikin Amal na rawa ta miƙe tayi waje kiran Yusuf.
Koda saƙon Kiran Widad ya riski Yusuf yasan a rina, yasan ze fuskanci wulaƙanci, Amma ya dake ya shiga cikin gidan.
A falo ya tarar da ita a tsaye, tana wani irin huci, haɗi da sauke numfashi, Tabbas Widad Yarinya ce ƙarama Amma Allah yayi mata kwarjini na musamman.
Yaje daf da ita ya tsaya ya sunkuyar da kai ba tare da yace komai ba.
"Kalleni nan"
A hankali ya ɗaga idonsa yasa a nata, dukda bugawar da ƙirjin Widad yayi be hanata cewa
"Nayi maka kama da matsiyaciya ko me neman temako?"
Kallon ta yayi bece komai ba
Cikin tsawa tace "magana nake maka"
"temako ana yinsa ga kowa, duba da rayuwar gaba É—aya taimakon juna mukeyi, dan haka ba fuska ake gane...
" Shut up!!! "
Tai maganar tare da É—aga masa hannu
"waye kai? Me kake da shi? Me kake taƙama dashi wanda har yasa kake ganin kana da abunda zaka ɗauka ka bani? Me kake da shi? Ni zaka bawa wannan banzayen Abubuwan na maka kama da wadda zata saka wannan tarkacen, shara? Ka taɓa ganin na saka irin wannan kayan? Ko na ce maka ina da buƙatar su? "
Te Ɗebo kayan dake kan kujera ta watsa masa a fuskar sa tace " don't you ever try to make this mistake again, ka nemi mabuƙata ka basu Widad tafi ƙarfin saka wannan tsumman"
Idon Yusuf jawur ya ɗago ya kafe ta da ido, ko ƙyaftawa baya yi, dukda hucin da take hakan be hana ta tsayawa tana kallon sa ba itama.
Ba zato ba tsammani suka ga Daddy ya ƙaraso cikin falon, ya durƙusa ya tsince rigunan, yazo gaban Yusuf ya kamo hannun Yusuf yasa nasa yace
"Yusuf wannan kyautar ni kayi wa, ba Widad ba, lokacin da zanyi tafiya ka kawo alheri ka bani kace in ƙara a guzuri, kuma ka nemi da kar in gayawa kowa, yanzu ma ka ɗakko kyauta ka bawa 'yata ɗiya tilo da nafiso, Tunda Allah yayi min Arziki babu wanda ya taɓa ɗaukar alherin naira biyar ya bani, saboda kowa gani yake ni me wadata ne bana buƙata, sedai ma kullum a nema a gurina, idan kuwa kaga anmin kyauta to wani abu ake nema a gurina, Mutum na farko da yayi min kyauta har sau biyu kuma saboda Allah, nagode sosai Yusuf, nasan kana haƙuri Amma ka ƙara zaka ga ribar sa, Widad ta gode da wannan kyautar"
Tabbas ba dan Alhaji Nasir ba, ko duniya yake samu a gidan nan baze sake zuwa ba, da babu abunda ze hana ya miƙa file ɗin aikin a ɗora wani dan ya gaji.
Yusuf bece komai ba, ya jinjinawa Alhaji Nasir kai ya fice, zuciyar sa na ƙuna dan gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun miƙe saboda ɓacin rai.
Alhaji Nasir yayi wa Widad wani irin kallo, ya wuce part É—insa da kayan a hannun sa.
Se a lokacin ta sha jinin jikin ta, bin bayan Daddy tayi da sauri zuwa part É—insa.
Ramla tace "Allah ya ƙara, maganin me shishshigi kenan, da haka da haka wataran zata sallameshi kowa ya huta"
Amal tace "kema kiji da abunda ke damunki mana, aikin banza kawai"
A É—aki Widad ta riski Mahaifinta, tace "Daddy are you angry?"
Shiru yayi mata yana ƙoƙarin ninke rigunan.
"Daddy am talking to you, why will you be angry? Am I wrong?"
Shiru ya kuma yi bece mata komai ba.
"Daddy magana fa nake maka"
"Me kike so ince miki Widad? Yaron nan yana matuƙar ƙoƙari da haƙurin zama dake, Amma kalli yadda kike treating ɗinsa, yana miki biyayya yadda ya kamata amma bakya gani, can you remember when last someone offer you a gift, for the sake of God? Meye laifin sa dan ya baki wannan kayan, irin wannan rigunan Amminki take sakawa, sunfi mutunci akan wanda ke kike sakawa, bana son takuramiki saboda yanayin halin da kike ciki, Amma ba kya tausayin kanki, meye aibu da wanda yake ƙasan ka ya baka kyauta, dukda muzguna masa da kike da wulaƙanci amma ya miki alheri, meyasa zaki Wulaƙanta shi, Widad ko baki yadda da abunda na gaya miki kwanaki ba? "
Shiri tayi tana nazarin maganganun Mahaifinta.
"baki ga yadda ya fita ransa a ɓace ba? Baki kyauta ba sam"
"to yanzu ni me kake so inyi?"
"ki karɓi wannan kayan kiyi amfani da su"
"Over my death body, gaskiya Daddy bazan iya saka wannan kayan ba"
Daddy ya jinjina kai yace "As you wish, zanje ganin likita gobe in Allah ya kaimu, sannan baƙonki yana nan zuwa da weekends ɗin nan"
"Waye baƙona kuma?"
"Fahad, mijin da zaki aura!!!"
Widad ji tayi tamkar Daddy ya watsa mata wuta me matuƙar zafi.
(MASHA ALLAH NA KAMMALA JARRABAWA ALHAMDILILLAH, INA GODIYA DA ADDU'OINKU NAJI DAÆŠI NAGODE SOSAI NA GAMA JARRABAWA YAU ALHAMDILILLAH)
Domin gyara sharhi ko shawara feel free to contact me
Ayshercool
07063065680
           _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
               Page 16_17
(Ayimin afuwa jiya nayi mistake É—in pages)
Ko kallon inda Daddy yake bata kuma yiba ta fice ta bar masa É—akin.
Komawa ɗakinta tayi, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu kamar zata fasa ƙirjinta ta fito 'kenan har yanzu Daddy be janye maganar nan ba? Daddy why?'
Tayi maganar da ƙarfi, tana sauke numfashi a hankali ta zube a ƙasan carfet, gaba ɗaya kanta ya kulle ta rasa abunyi, tabbas wannan karon Daddy dagaske yake, idan kuwa har Daddy ya dage a wannan ƙudurin nasa to tabbas zata bijre, koma hakan yayi sanadiyyar ya rasa ta gaba ɗaya, kuma seta shata babban layi tsakanin ta da Bulama.
Ramla tunani take me zata yi wanda zesa a janye maganar Widad da Fahad, ya za'ayi mutumin data daÉ—e tana tararirayar soyayyar sa lokaci É—aya a wargaza mata komai, sam hakan bame yuwuwa bane, dole tasan abunyi dan yiwa wannan tufkar hanci.
************************************
Kallo ɗaya zakayi wa iyalan kasan suna cikin farin ciki, gaba ɗaya sun hallara a katafaren falon gabansu shaƙe da nau'ikan Abinci kala kala, kowanne fuskarsa ɗauke da farinciki.
Ramadan yace "Wallahi broz Fahad gaba É—aya kaima ka zama kamar Bature, kaga yadda skin É—inka tayi fresh kamar wani jariri"
Alhaji Bulama yace "Wannan Ƙaton ne fatarsa kamar jariri, kai dai Ramadan ka fiye shiririta"
Hajiya Sarah tace "Haba Daddy, ka kalli yadda ya wani murje yayi ƙalau dashi"
Iman tace "Nikam banga abunda ya canza ba sedai yayi haske ya ƙaro iyayi, ko hausarma bata fita sosai se kace Widad"
Ɗan ɓata fuska Hajiya Sarah tayi jin an ambaci Widad.
Alhaji Bulama yace "se suje can su cigaba da gwarancinsu"
Sam Fahad be fahimci abunda mahaifinsa yake nufi ba, haka suka ci gaba da ciye ciyensu suna hira cike da ƙaunar juna.
Yusuf kuwa tunda ya baro falon nan ransa a ɓace kai tsaye gida ya wuce, zuciyar sa nata faman tafasa, tabbas ƙarshen wulaƙanci yau Widad tayi masa, banda dalilin aikin sa da kuma mutuncin mahaifinta da baze sake komawa gidan ba.
Nurat bata da aiki se tunanin Yusuf, ko bacci ta kwanta mafarkinsa take, gaba É—aya zuciyar ta ta kasa samun nutsuwa, ta kira lambar Yusuf harta gaji, ta koma kiran ta Widad, amma itama bata tafiya, abun duniya duk ya ishe ta.
Tana zaune tana wannan zaman tunanin mahaifinta ya shigo ɗakin ta, da sauri ta miƙe daga kwanciyar da take.
Ya kalle ta yace "ke meya ke damun ki ne?"
Girgiza masa kai tayi tace "bakomai Daddy"
"to naga Maman ki bata nan, gobe in Allah ya kaimu zamuyi baƙi ki gaya mata, za'ayi mana girki bana son na masu aiki fa"
"To zan gaya mata insha Allah"
"shikenan sena dawo"
"Adawo lafiya Daddy"
"Allah yasa"
Gaba ɗaya ɓacin rai ya hana Yusuf bacci, kamar shi dukda yasan ba wata uwace da shi ba amma Widad ta dinga gaya masa wannan baƙaƙen maganganun gaskiya idan ya ƙyaleta tabbas taci bulus.
Tunani ya shiga yi me ze mata wanda ze nuna mata mahimmancin É—an Adam.
Da ƙyar bacci ya ɗauke shi cike da ɓacin rai.
Da gari ya waye so yayi yaje gurin aiki amma ya fasa, yayi zamansa a gida se bayan azahar sannan yaje gidan.
Nura da Isa se wani kallon banza suke masa, Yusuf bashi da lokacin su dan haka bebi ta kansu ba.
Be daɗe da zuwa ba Alhaji Nasir ya fito, yana ganinsa kamar babu abunda ya faru Yusuf ya miƙe ya nufi inda yake.
Cike da girmamawa kamar kullum suka gaisa, Alhaji Nasir yace "Yusuf kaga yau ma tafiya ta kamani, kar a gaji dani dai ga Amanar tilon 'yata nan, Fahad zezo gurin ta a satin nan Insha Allah, dan Allah a samin ido akan ta, sannan ka cigaba da haƙuri"
Yusuf yace "Insha Allah, Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya"
"Ameen Yusuf"
Ya shiga mota, Nura yaja suka fita.
Larai me aiki ce ta fito ta samu Yusuf tace "kaje inji 'yar masu gida"
Yusuf yace "Ina zuwa"
Yai zaman sa kamar bashi akace ana kira ba, Isa yace "da alama Yusuf ka raina Yarinyar nan, badan kaine ba akwai wanda ya isa yayi mata haka ta ƙyaleshi, turowa fa tayi tana kiran ka, amma ka basar kana shagalinka"
Ko gezau Yusuf beyi ba, balle Ya nuna yasan me Isa yake faÉ—a.
Isa yace "da kai fa nake magana"
Still be tanka masa ba, Isa yace "eh da alama kaima ta koya maka baƙin halin, kadai bi a hankali tunda kaima ɗan uwa talaka ne, inka ɗau wannan rayuwar ba inda zata kaika"
Yusuf be kula shi ba ya miƙe ya bar gurin.
Yusuf na tafiya sega Abbas yazo, Isa na ganin shi ya washe baki yace "Sani dama kana nan? Kwata kwata wayarka ta dena shiga"
"ina nan wallahi, na koma ƙauye ne, ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah, ya ka baro mutan gidan?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ina Yusuf kuwa?"
Isa ya taɓa baki yace "Yana nan yanzun nan ya shiga cikin gida, gimbiyar masu gida tana kiransa"
"Allah sarki, ina fatan yana aikin sa babu matsala?"
"Eh to yana yi, se shishshigi da zaƙewa, yaga ya samu gurin zama a gurin masu gidan, shine yake ta Wulaƙanta mu gamu gashi amma se yaga dama ze kula mu"
"Hmm ni kaina wannan baƙin halin nasa yana ƙular dani, dama haka yake se kunyi a hankali wasu lokutan bashi da kirki sam wallahi".
Yusuf seda ya É—an tsorata, ganin Widad ta rame daga jiya zuwa yau, idanunta a kumbure da alama kuka tayi sosai, gaba É—aya se yaji tausayin ta ya kama shi.
"Gurin Bulama zaka kaini yanzun nan"
Jinjina mata kai yayi, ta miƙa masa jakarta ya karɓa sannan suka fito.
Tunda suka fito Abbas ya ƙura musu ido, se kace mata da miji, tabbas Yusuf ya samu gindin zama yadda yakamata a gidan nan.
Yusuf na ganin Abbas tun daga nesa ya fara murmushi, suna isowa inda su Abbas suke kafin Yusuf yayi magana, Widad ta ƙurawa Abbas ido, shikansa Abbas seda yasha jinin jikin sa.
"Waye wannan?" Widad ta tambayi Isa megadi"
Cikin inda inda Isa yace "Amm... Am. Dama abokina ne, kuma shine wanda ya kawo Yusuf aiki a gidan nan, ina tunanin ma É—an uwansa ne"
"Kar in ƙara ganin sa a gidan nan, ko a harabar area nan na sake ganinsa zan ɗau matakin da ya dace"
Binta sukayi da kallo, inda sabo Yusuf ya saba da wannan halin nata, dan haja yayiwa Abbas Alama da zasu yi waya.
Abbas ya miƙe cikin mamaki ya bar gidan.
Yusuf dama beyi zaton zata gaya masa dalilin ta na korar Abbas ba, amma abun ya bashi mamaki, seya barshi a matsayin kawai duk cikin hakinta ne na rashin yarda da mutane.
Koda suka iso gidan Bulama, kafin su shiga megadi ya sanar dasu cewar Bulama da shi da iyalansa basa nan sun fita.
Haka Yusuf ya juya akalar motar suka koma gida.
Abbas ba ƙaramin mamaki yayi ba, yaga dai farkon zuwansa gidan daya kawo Yusuf tare suka je, amma yau ta nuna bata sanshi ba wai kar ya ƙara, zuwa gidan.
Kai tsaye Abbas ya É—akko wayarsa ya kira layin Saleh.
"Hello Saleh kana ina ne?"
"ina gidan gona bakin aiki, meyafaru?"
"ina son ganinka ne"
"ka bari zanzo in same ka a gidanka, karka zo nan babu security"
"shikenan sekazo"
Yusuf Alla Alla yake ya kai Widad gida ya tafi gurin Abbas.
Seda suka je gida yay parking, Widad ta kalle shi tace "Karka bar gidan nan se bayan sallar isha'i"
"Saboda me?" ya tambaye ta
Bata bashi Amsa ba ta fice daga motar ta barshi a gurin, ba ƙaramin haushi yaji ba, yasan dai duk abu ba wani gurin ze kuma kaita ba, Amma tace baze tafi ba, da niyyarsa yayi tafiyar sa amma se ya fasa, haka ya cigaba da zama har se lokacin da tace ya tafi.
Saleh ne zaune shida Abbas a wani É—an madaidaicin falo, Saleh yace
"Neman me kake min ne haka?"
Abbas yace "dole in neme ka ai, Yusuf se alheri yake samu a wannan aikin da yake, ta sakarmasa kuÉ—i kawai take sakarmasa, seda nayi dana sanin rashin yin aikin nan da kaina"
Saleh yai murmushi yace "tabbas Widad akwai kyauta ta ban mamaki, Sedai kasan aikin da yake a rayuwar sa a hatsari take ko?"
"Nasani amma babban abunda ya ɗauremin kai shine yau naje gidan gurin sa, Amma tana ganina tace kar in ƙara zuwa ko area gidan"
"zata aikata saboda bata da yadda sam, dan haka bata son baƙuwar fuska, gani take kowa ma cutar da ita zeyi, yanzu ya ake ciki game da binciken da yake yi, naga alamar yaron yasan aikin sa, duk yadda kaso ka daki cikin sa ba ze gaya maka komai ba, na jarraba shi rannan da suka zo tare, Amma naga yana da wayo "
Abbas yace " Hmmm, aiki kam yasan kan aikin sa sosai, dan ina tabbatar maka da yana aikin yadda ya kamata yana tattara abubuwa masu mahimmanci sedai har yanzu ban san meye sakamakon binciken nasa ba"
Saleh ya numfasa yace "yanzu abunda nake so da kai shine, ka kawomin rahoton duk binciken da yayi, ka kawomin file ɗin zan miƙa shi ga wannan mutanen dan su sakarmin ɗan uwana dan ina zargin su suka yi poisoning ɗinsa yake kwance ba lafiya"
Abbas yace "yana na'aikaci ina ma'aikaci tayaya kake tunanin ze yadda ya bani kundin binciken sa?"
"wannan ya rage naka kuma Abbas, ni na gama magana kuma ka saka ido ka cigaba da bibiyar sa dan jin yanayin kusancinsa da ita"
"Shikenan zanyi iya abunda zan iya, Insha Allah zan kawo maka abunda ka buƙata.
Ba ƙaramin haushi Yusuf yaji ba da Widad ta hana shi tafiya da wuri, dan haka se bayan isha'i sannan ya tafi gida, bayan yaje gida yaci Abinci yana shirin kwanciya message ya shigo wayarsa
"HAR YANZU MUNA SANE DA KAI, KUMA ZAMU CIGABA DA BIBIYAR KA HAR SEKA BAMU ABUNDA MUKE SO A HANNUN WIDAD"
Tsaki Yusuf yayai ya ɗanyi shiru yana tunanin wai wani abubne wannan haka da'ake son karɓa a gurin Widad, da har ake masa barazana haka?
Ganin bashi da amsa yasa yai kwanciyarsa.
************************************
"Fahad kasan meyasa na kiraka muyi magana a daidai wannan lokacin?"
Fahad ya girgiza kai yace "a'a Daddy"
Bulama yace "Yawwa, na yanke wani hukunci ne kafin ka dawo, shine nake so ka baani aron hankalin ka da kunnuwan ka da kyau ka saurareni"
"To Daddy ina jinka"
"Kasan Widad ai ko? 'yar gidan Alhaji Nasir daula"?
"Eh Daddy nasani"
"Kasan alaƙar dake tsakanina da mahaifinta ko?"
"Nasani Daddy" Fahad ya bashi amsa
"Masha Allah, Kasancewar ka yaro me biyayya shiyasa na yanke wani hukunci wanda nasan ba zaka bijiremin ba Insha Allah"
"Ina jinka Daddy".
"Kamar yadda kasani, yarinyar nan ta gamu da larurar Ƙwaƙwalwa, ta ɗau wata AƘIDA da wata irin rayuwa ta nayi, ta zaɓi rayuwar kaɗaici wanda hakan ke barazana ga lafiyar ƙwaƙwalrwata, shine muka yabke hukuncin yi mata Aure nida mahaifinta, koda Allah zesa a dace a samo kan hankalin ta"
Fahad yace "to ai Daddy ni banga meye nawa a ciki ba"
"Fahad kai muka yanke shawarar zaka auri Widad"
A razane Fahad ya kalli Mahaifinsa yace "Kamar ya ni Daddy, kawai se in auri mahaukaciya kaifa kace bata da hankali ta yaya zan Aure ta?"
"ta yadda na gaya maka mana, aiba hauka take tuburan ba se lokaci lokaci yake tashi, dan haka umarni nake baka ba shawara ba, idan bamu haÉ—u an temaki yarinyar nan ba waze aure ta da wannan larurar?"
"Amma Daddy a rasa wanda za'a bawa seni? Ina da wadda nake so meyasa za'amin haka? Ta yaya za'a yanke min hukuncin yarinyar da zan aura ba tare da izinina ba"
Cikin tsawa Bulama yace "rufemin baki, na gaya maka wannan umarnina ne, kuma dole kabi gobe in Allah ya kaimu zakaje ku gaisa da ita, kuma wallahi naji wani abu daga gareka wanda be gamshe ni ba, kasan halina sakarai kawai"
A hasale Fahad ya tashi ya bar falon mahaifinsa, É—akin mahaifiyarsa ya tafi yana kumbura fuska.
"lafiya ka shigomin ɗaki ba ko sallama kana ta haɗe rai kamar tsohon raƙumi?"
"Mumsy kina gidan nan, kina raye za'ayi min Auren dole? Kamarni ta yaya za'a auramin mahaukaciya?"
Ajiyar zuciya tayi tace "Fahad this is out of my control, I did my best to destroy this matter but is beyond my control, ba yadda banyi da mahaifinka ba amma fafur yaƙi, ya zanyi sedai kayi haƙuri"
"Au Hakama zaki ce? Wallahi se yarinyar nan tayi dana sanin Aure na, sena mata wulaƙancin daba'a taɓa yi mata ba se naci mutuncin ta, zata gane kuskurenta"
"Kai Fahad ka shiga hankalin ka, 'yar gidan Daula ce fa, ita zaka ciwa mutuncin? Amma kasan me ci mata mutunci ke nufi ko?"
"ko' yar gidan bushashace ba Daula ba ba ruwana wallahi"
"shikenan kaje kayi abunda ka ga dama kaida ubanka ba me É—agamin hankali wallahi"
Fuuuu Fahad ya fice ya bar É—akin yana tsaki
Da safe Yusuf yanata shiri, dan yau gurin aiki yake son zuwa dole yana son ganin Yallaɓai Suleiman, Amma message ya shigo wayar sa.
"ka tabattar ƙarfe takwas tayi maka a gidanmu, zakamin aiki yau"
Yana ganin message É—in yasan daga Widad ne, haushi ne ya kama shi gaba É—aya bashi da lokacin kansa sena wannan fitsararriyar yarinyar.
Haka ya shirya a gaggauce ya tafi gidansu Widad, mutan gidan ko tashi daga bacci basu yi ba, tsabar takura irin ta Widad da son nuna isarra yasa take masa wannan ikon.
Wani ɗan ƙaramin lambu dake gidan Yusuf ya tafi yai zaman sa, yana kallon shuke shuke da tsuntsayen dake gurin.
Jin tsayuwar mutum yayi a bayan sa dan haka da sauri ya juyo.
Amal ce tsaye a bakin lambun tana ƙare masa kallo "barka da Safiya Yusuf"
"Yawwa barka" ya faɗa a taƙaice
"Yusuf wai ya naga kana wani baya baya dani? Dan Allah kayi haƙuri da abunda ya faru, wallahi ina matuƙar kishin ka ne"
"Amal dan Allah kiyi haƙuri, ni bana son abunda zesa ki jamin matsala, ki ƙyaleni dan Allah"
"Idan kaga na ƙyaleka to tabbas ɗayan mu ruhinsa ya rabu da gangar jikinsa, ni matsala duk girmanta duk ƙanƙantar ta bana gudun ta, indai akan biyan buƙata tane, kalleni Yusuf me na rasa? Wace tawaye Allah yayimin da ban kai ka kalleni ka karɓi soyayya ta ba, kana ganin irin mazan da suke sintiri a gidan nan da sunan suna sona, Amma na ajiye class ɗina na ajesu a gefe nace kai nake so, me zesa kace baka sona"
"Saboda bana Soyayya, bata gabana babu ita a tsarina, dan Allah ki ƙyaleni"
"ƙarya kake Yusuf kana Soyayya, koma baka yi zaka fara a kaina bazan taɓa ƙyaleka ba, zan cigaba da bibiyar ka sena hanaka jin daɗi muddin baka amince da soyayya ta ba "
"Masoyiyar gaskiya ba zata taɓa faɗar haka ba, ke ba abun yadda bace dan haka bazan taɓa yadda da wannan shirmen ba"
"Yusuf ko nawa kake so zan mallaka maka, in har zaka yadda ka karɓi soyayya ta"
"Shi son gaskiya tsada ne dashi, kuɗi komai yawan su basa siyansa, dan haka Allah be baki arziƙin da zaki siyi soyayya a gurin Yusuf ba"
Yana gama maganar ya juya ya fice daga lambun yana mamakin wannan naci irin na Amal.
************************************
Ramla ce kwance hannunta riƙe da waya tana magana a hankali cikin iyayi
"Abun ƙauna ta, yau kwananka huɗu da dawowa Nigeria, yakamata ace kazo na ganka fa, Allah badan inajin nauyi ba da tuni ni zanzo inda kake in ganka"
Daga can ɓangaren Fahad yace "Am Sorry beb, ina cikin damuwa ne gidan naku ne gaba ɗaya bana son zuwa, Ramla wai Daddy ze haɗani Aure da wata mahaukaciya a gidan ku, Ramlah kamarni za'ayiwa Auren dole? Auren ma da mahaukaciya, kuma Daddy se masifa yake wai se nazo mun gaisa da ita"
"Fahad nasan maganar nan tun kafin ka dawo, ban gaya maka ba saboda bana son ɓacin ranka, Amma ina cikin damuwa Fahad you know I love you" tai maganar cikin damuwa
"easy baby, ki kwantar da hankalinki, idan nazo se nayiwa yarinyar nan rashin mutunci, ni bazan aure ta ba dan ba sonta nake ba, bazan taɓa yadda da Auren nan ba, naga Daddy ya fara fushi, in anjima zan shigo gidan naku in ganta, Amma ni ke zanzo gani Beb"
Murmushi tayi tace "Ohh my God, amma naji daÉ—i Fahad seka zo".
Ta kashe wayar tare da yin wani tsallen murna.
************************************
Se ƙarfe sha ɗaya na safe tayi miƙa, ta farka daga nannauyan baccin da take, ta sakko daga kan gadonta magen ta yana biye da ita.
Corridor ɗin ɗakin ta tabi wanda ze sada ta da barandar benen, miƙa ta sake yi tana ambaton sunan Allah tare da shaƙar sassanyar isakar dake kaɗawa, haka nan take jin wai irin nishaɗi da bata san dalilin jinsa ba, tsyawa tayi tana kallon komai dake harabar gidan.
Yusuf ji yayi kamar ana kallon sa dan haka ya ɗaga kansa sama, ai kuwa karaf idanunsa suka sauka a cikin nata, alama tayi masa da hannu ya zo, dan haka ya miƙe ya tafi.
Dukda yana jin haushin abunda tayi masa akan kayan daya bata, amma yau yaga fuskarta ba yabo ba fallasa haka nan yaji hakan yayi masa daÉ—i.
A ɗakinta ya sameta, tana tsaye a gaban madubi ta janyo drower mudubin tana ƙoƙarin ɗakko wani abu.
Idan kunnuwan ta ba ƙarya suke gaya mata ba tabbas Yusuf cewa yayi "Good morning daughter" kamar yadda Daddyn ta yakan faɗa, shiru tayi ta cigaba da duba abunda take nema tsawon wasu daƙiƙu, sannan ta ɗago ta kalle shi tace "Roux taƙi cin komai tun jiya, na rasa meke damunta na bata Madara taƙi sha, ka siyo mata ko cabin ne, in gani in zata ci ban san me yake damunta ba" (wato magenta)
Haushi ne ya kama Yusuf, saboda tsabar wulaƙanci mage ze fita siyowa Abinci.
Bece komai ba ya juya ya fita yana ƙoƙarin ɓoye jin haushin sa.
Yana tafiya ya tuna da Message É—in da'aka turomasa da daddare dan haka ya samu guri ya kira Oga Suleiman.
Bayan sun gaisa Yusuf yace "Yallaɓai na so in shigo yau in nuna maka report ɗina amma abu ya gagara, Wannan rigimammiyar ta kasa ta tsare ban samu na shigo ba"
Suleiman yace "Aikam dan har na fara ƙorafin, yanzu me ake ciki?"
"Yallaɓai akwai abubuwa na ban mamaki a binciken nan, zan turomaka report ɗin ta Email ɗinka ka duba, Yallaɓai case ɗin akwai sa hannun mutanen dan ban zata ba, sannan karo na biyu ana min barazana wanda ya ƙara tabattar da tabbas ana bibiyar yarinyar nan ana son karɓar wani abu a hannunta wanda ni kaina ban san menene ba"
"Masha Allah, har kayi aiki haka Yusuf? Ka turo zan duba in Allah ya yadda inda yuwuwa zan miƙa report ɗin naka gaba, nasan zaka iya dama bazan can zaka daga kan aikin ba"
"Yallaɓai da karɓar aikin za kayi?"
"karka damu da wannan, ka turomin zan duba dan daga sama ana tambaya ta ina muka tsaya a binciken?"
Yusuf yace "Amma Yallaɓai wai wa yasa ayi wannan aikin ne? Waye yace ayi binciken?"
"Yusuf nima ban saniba, daga sama aka bada order ayi wannan aikin"
"Yallaɓai ya kamata kasan gawa zaka bada aikin, dan abun akwai sarƙaƙiya"
"Karka damu Yusuf, komai ze tafi daidai insha Allah, kamar yadda kace ana maka barazana, duk lokacin da ka buƙaci temako kayi magana, sannan ka kasance cikin shiri ka dinga yawo da makaminka"
"Ina lura sosai Yallaɓai, Allah yayi mana jagora gaba ɗaya"
"Ameen Yusuf Allah ya tsare"
Yusuf seda ya tsaya ya turawa Suleiman aikin sannan ya tafi.
Koda Yusuf ya dawo daga aiken yiwa mage siyayya, ya tarar da uwar É—akinsa ta fito daga wanka, pink É—in rigar wanka ce a jikin ta, ta naÉ—e gashin kanta da towel shima pink.
Zare towel ɗin dake kanta tayi, gashin ta ya zuba a kan kafaɗunta, Satar kallon ta Yusuf yake, tabbas Allah yayi mata halitta mekyau, tana da kyau sosai ga dogon gashi, Yarinya ce sedai izza da gadara, tana kallon Ya dawo amma taƙi kula shi.
Wani ƙaramin plate ta ɗakko ta miƙawa Yusuf tace "ka sa mata cabin ɗin anan, ga madara ka haɗa mata dashi"
Yusuf yai shiru yana sauraren ikon Allah, yanaji yana gani aka sashi haÉ—awa mage Abinci.
Still dai magen bataci ba se kwanciya da take.
Cike da damuwa Widad ta kalli Yusuf tace "taƙi cin wannan ma, inaga bata da lafiya idan akwai wani private veterinary se mu kaita" ta faɗa cike da damuwa tana sake shafa magen, hakan ya ƙara fito da tsantsar yarintar ta.
"waye ze buɗewa wani private veterinary? Babu wani private veterinary dana sani nidai, yunwa take ji kawai bata ƙoshi ne"
"kamarya? Ina bata Abinci sosai fa"
"Ai kema ba Abinci kike ciba balle magen, kullum abu É—aya ai dole ta gaji ta dena ci"
Cikin damuwa tace "to me zan dinga bata?"
"Abinci me nauyi na hausawa, amma kullum daga popcorn se madara ai dole ta mutu"
Da sauri ta kalli Yusuf tana girgiza kai tace
"A'a ni bana so ta mutu ina sonta fa"
Gaba ɗaya yau Yusuf cike yake da mamakin yadda take masa magana cikin nutsuwa ba izza, yasan kuma saboda magen ne, dan ya lura tana tausayin dabbobi fiye da yadda take tausayin ɗan Adam, tana matuƙar ƙaunar dabbobi Yusuf a ransa yace "ta wani fannin rayuwar turai ba tayi ba"
"to muke rasa 'yan uwanmu mutane ma balle dabba, idan ta mutu seki É—akko wata"
"Ni nafison wannan gaskiya, tun ire iren magunan Ammi ne, idan ta mutu zan shiga damuwa"
Shiru yayi yana kallon Widad data sunkuyar da kanta tana shafa jikin magen, magen tayi lamo a jikinta, gashin kanta har rufe mata fuska yake, Yusuf yana mamakin wannan dogon gashin na kan Widad dan har yanzu yana tantama idan nata ne.
A hankali ya matso daf da ita ya shafa jikin magen dake hannun ta yace "Allah ya bata lafiya, don't worry Madam zata warke Insha Allah"
Widad ta jinjina kai, tare da jin ƙaruwar bugun zuciyar ta kasancewar yadda suke daf da juna, ta ɗago idonta ta kalle shi tace "da ina so mu fita zanje Saloon, Amma zan zauna inga yadda jikin nata ze kasance ko zuwa yamma ne semu tafi"
Yusuf ya ɗan ƙura mata ido sannan a hankali yace "As you wish your majesty" ji tayi tsigar jikin ta tashi, wanda ta rasa dalilin jin hakan, haɗe rai tayi tace
"karka sake ka fita kaje ko'ina idan ba nina baka izini ba, ka zauna zuwa la'asar insha Allah zamu fita"
Murmushi yayi mata tare da ɗan duƙawa cikin girmamawa yace "Considered it done Gimbiyar Daddy"
Ya yunƙura ze miƙe Amal ta shigo hannun ta ɗauke da waya, turus tayi tana binsu da kallo, yayin da taji wani abu tundaga ƙafarta zuwa ƙirjinta ya to kare mata wuya.
Da ƙyar ta miƙawa Widad waya tace "gashi Daddy zeyi magana dake"
Widad bata kalle ta ba, bata bata amsa ba ta kalli Yusuf tace "bani wayata akan mirror"
Amal bata kuma cewa komai ba ta juya ta tafi a hasale.
Widad ta karɓi wayar ta kira lambar Daddy, ya ɗaga suka gaisa yace "Lovely meyasa wayarki bata shiga?"
"Jinyar Roux nake, bata da lafiya"
"To Allah ya bata lafiya, dama munyi waya da Daddynki yau baƙonki zezo"
"waye baƙona?"
"Fahad mana, zezo ya ganki ku gaisa dan Allah Lovely banda wulaƙanci ko makamancin haka, shima ɗanuwankine Yayan Ramadan ne, yana nan tafe Anjima Insha Allah"
Nan da nan dukkan annurin fuskarta ya É—auke ta dire wayar tace
"Ina nan ina jiran zuwan sa, yazo ya sami Widad Nasir Daula, yazo yaga mahaukaciyar da'ake shirin ƙaƙaba masa"
Ayshercool
07063065680
            _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 18
Binta da Kallo Yusuf yayi, ganin yadda ta canza lokaci É—aya annurin fuskarta ya É—auke, tabbas akwai drama yau.
"Jeka anjima zamu fita" ta faÉ—a ba tare da ta kalli Yusuf ba
Miƙewa yayi ya fito daga ɗakin ya nufi hanyar fita, ba zato Amal tasha gabansa wanda ya tilasta masa tsayawa.
"Yusuf ka fara ƙoƙarin tsallake iyaka, Yusuf meyasa baka tsoron Allah ka dinga nuna kai na Allah ne amma baka kyautawa rayuwarka, Yusuf kai mugune mara tausayi baka da tausayi baka tausayina, ko kaɗan soyayyata bata da daraja a idonka, na rasa meye a tsakaninka da Widad, wallahi akan Son da nake maka banƙi komai ze faru ya faru ba, wallahi akanka koni ko Widad "
Girgiza kai Yusuf yayi yace " keya dace a nemawa maganin mahaukata ai, nayi iya ƙoƙarina in ganar dake amma kin kasa ganewa, bana Soyayya bani da ra'ayinki, ba abunda ya kawoni nan kenan ba, ki ƙyale rayuwar Yusuf ta huta, tun kafin in nuna miki ainihin kalata na gaya miki"
"Haka kace?"
"Eh haka nace, ko baki da kunne ne?"
"bayan ƙalubalen dake gabanka saboda Kasancewar ka da wannan mahaukaciyar, ka shirya ƙalubalen da zaka fuskanta daga gareni"
"duk wanda ya dogara da Allah, to ya isar masa"
Yusuf ya bata amsa yasa kai ya fice, ya barta tana mamakin wannan taurin kai irin na Yusuf.
Bayan Suleiman ya gama nazarin abunda Yusuf ya tura masa, yayi mamakin jajircewa da kuma ƙoƙarin da yayi, tabbas Yusuf jajirtacce ne me kuma hikima da iya aiki, amma meye dalilin da yasa Abbas yakeson lallai a ƙwace aiki a bashi? Lallai akwai wata a ƙasa Abbas yana da fuska biyu.
Yusuf yana nan zaune yana ganin yadda aketa aiken su Murtalah, anata shirye shirye da alama akwai baƙon da gidan zasu tara yau, shi dai yana guri ɗaya nasa ido.
Ƙarfe biyu na rana Yusuf ya dawo daga masallaci sallar Azahar, wata dalleliyar mota ta shigo gidan, wani matashi ne ya fito daga motar, jikinsa sanye da ƙananan kaya kallo ɗaya zaka masa kasan ɗan hutune, ya ɗaga kai ya ƙarewa gidan kallo tsaf, su Isa mai gadi suna gaisheshi yana ɗaga musu hannu ba tare da ya amsa ba.
Shidai Yusuf be kula shi ba, sema É—auke kai da yayi kamar bega Matashin ba, ba zato suka jiyo muryar Ramla ta taho da gudu tana faÉ—in "Oyoyo my heart beat"
Ba kunya suka rungume juna a gurin.
Fahad yace "I miss you so much Baby"
"I miss you too mine" Fahad yayi kissing É—inta a forehead yaceÂ
"kin ƙara kyau my Ramlat"
"Kyau ai kaine ka ƙara kyau, mutanen Amurka muje daga ciki ko"
Suka shige hannunsu saƙale da juna.
Nura direba yayi tsaki yace "ƙaryar banza burodi a lefe, waisu a dole turawa ba kunya taje ta rungume ƙasurgumin gaddi tana ce masa Baby tir da wannan hali"
Shidai Yusuf bece musu komai ba suka ci gaba da gulmarsu.
A babban falon dake ɓangaren Hajiya Halima aka sauki Fahad, suka dinga hira yana basu labarin Anwar shima ya kusa dawowa.
Fahad ya ɗan ɓata fuska yace "Hajiya wai ina Yarinyar take ne? Ance inzo in ganta karta ƙullamin wani sharrin a gurin father ta jamin magana, danni sam ba'a kyautamin ba da'akace zan Aureta"
Æata rai Ramla tayi ta miÆ™e ta bar falon, Hajiya Halima tace "Aikuwa dai an gama da kai, dan yarinya ce ba tarbiyya ga kuma uwa uba hauka"
"wallahi Hajiya na rasa wani irin tunani Daddy yayi haka, da yasa yake son illata rayuwa ta, nazo ne dai kar'ace banzoba amma sena tabattar da na mata rashin mutunci yadda ko ganina tayi ba zata nuna ta sanni ba"
Amal ta kalleshi a yatsine, sam Fahad haushi yake bata yana ta wani iyayi shi lallai ya dawo daga Turai, indai Widad ce ze gane kurensa ne.
Ba kunya Fahad ya miƙe yace "Hajiya bari inje gurin Ramla, naga tayi fushi"
"Shikenan kunfi kusa ai"
A ɗakinta ya sameta tayi kicin kicin da rai, ta haɗe fuska, ya zauna kusa da ita ya janyota jikinsa yace "haba Baby, meye abun damuwa nifa danke nazo gidan nan, ba dan wata banza ba meye na ɓata rai, ki tsaya kiga matakin da zan ɗauka yau akanta"
"Fahad inajin tsaro fa, su Daddy suna san Auren nan naku, zasu iya tursasa maka fa"
"waye ya gaya miki? Kamarni aina wuce ajin amin auren dole, calm down Baby" ya faÉ—a yana jan hancinta
Murmushi Tayi tace "bari in shirya maka Abinci a dining, na maka girki"
Kafin yayi magana wayarsa ta fara ringing yace "excuse me Daddy ne"
Ya ɗaga wayar yasa a kunnensa yace "hello Daddy"
"Fahad kaje gurin nata kuwa?"
"Amm.. Eh ina gidan amma ban ganta ba"
"to ka tsaya ku gaisa, sannan yarinyar nan ka bita a hankali bata da cikakkiyar lafiya, kabi a sannu ka kwantar mata da hankali"
Tura baki Fahada yayi yace "Haba Daddy sekace uwata, yarinyar ma ashe mahaukaciya ce"
"ba zakayi ba kenan?
" Naji zanyi "
" idan naji wani abu na rashin kyautawa daga ɓangarenka sena saɓa maka, shashasha wanda be san halacci ba, aiko wani kaga ze Wulaƙanta 'yar Nasir Daula kai me tare matane"
Bulama yayiwa Fahad tatas sannan ya kashe wayar
Fahad yace "kar wannan abun ya ɗaga miki hankali kinji babyna, ina tare dake, nasan matakin da zan ɗauka"
Ta jinjina masa kai suka fito babban falo, Fahad yace "kiramin ita".
Ramla ta nufi part ɗin Widad, a falonta ta tarar da ita tana kwance a ƙasa ta ɗora ƙafafunta akan kujera, mageneta na kan cikinta a kwance, itakuma tana danna waya.
Ramlah tace "Fahad yazo, yana falo yana jiranki"
Ai kamar da kujerun gurin Ramla ke magana ba da Widad ba, dan ko motsi ba tayi ba.
"Magana fa nake miki"
"And then? Ko bayan hauka kuma inada larurar kurmanta ne? Kinyi magan na jiki kin cigaba da tsayawa a kaina, ki matsa daga kaina"
"Amma se ki bani amsa ai, tunda keba kurma bace"
Miƙewa Zaune Widad tayi tace barmin falo.
"Amma...
" ki fice nace, ko Bulama ne yazo da kansa be isa ya tursasani in saurare shiba, kije ki gaya masa ya cigaba da jira idan ze iya daga nan zuwa lokacin da zan fito, idan baze iyaba ze iya komawa ya tambayi Bulama tsarukana, idan ya shirya É—auka ya sake dawowa, fita ki barmin É—akina"
Buɗe baki Ramla tayi tabi Widad da kallo, wato ita kullum rashin mutuncinta ƙara ta'azzara yake, ina ita ina zuwa ta Sanarwa da Fahad wannan baƙin saƙo, mussman shi dabe san kan Gimbiyar ba.
Ramla ta juya ta fice ta koma main falo tace "Baby naje yanzu ta tashi daga bacci zata shirya ta fito"
Ramla ta zauna a kusa da Fahad suka shiga hirarsu, tun Fahad yana tsammanin fitowar Widad harya fara ƙulewa.
"Ramlah wai yarinyar nan ba zata fito bane?"
"Fahad baka ga komai ba, indai akan wannan Yarinyar ne, idan ka kuskura ka aureta taka ta ƙare wallahi"
"zan saita mata zama kuwa, dan nafi ƙarfin wata banza ta Wulaƙanta ni, bari inje akwai wani friend ɗina a quarters ɗin nan, inaso mu gaisa ina dawowa"
"to ka fara cin Abincin mana"
"karki damu yanzu zanje in dawo"
Ramlah ta rakashi har gaban motarsa, kallo ɗaya Yusuf yayi musu ya ɗauke kai, Fahad yace "Baby wai waye wannan ne?"
Yai maganar yana nuna Yusuf, yamutsa fuska tayi tace "Direban wannan sakaryar ce"
"yanzu wannan ne direba?"
"direba ne, sedai ya samu gindin zama fiye da duk wani me aiki a gidan nan, shiyasa har wani jin kansa yake"
"ku kuka ƙyaleshi baku saita masa zama ba"
"ni yanzu ba shine a gabana ba, kaje kayi sauri ka dawo kaci Abinci"
Suka yi sallama Fahad ya tafi, se bayan ƙarfe huɗu Yusuf yaga message ɗin Widad, ya miƙe ya shiga part ɗinta.
Yau dogon skirt ne a jikinta baƙi, da wata riga me dogon hannu ta ɗora ɗan ƙaramin veil akanta, tayi kyau sosai kayan sun zauna cif a jikinta sedai ana ganin duk wani shape na jikinta.
Tunda Yusuf ya shigo ba tayi magana ba, se sabgar gabanta take yi.
"Ya jikin magenki?" ya tambaye ta
Abunda Yusuf ya faɗa ne yasa ta ɗagowa da sauri tace "i think she got better now, she's able to play"
"Allah ya bata lafiya, na É—auka mutuwa zata yi ashe da sauran kwananta a gaba"
Harar Yusuf tayi ta ɗau jakarta tayi waje, binta yake a hankali baya sauri yana tafiya kamsr kazar da ƙwai ya fashewa a ciki , ta juyo ta kalle shi tace "wannan wace irin tafiya ce kuma?"
"Nifa gaskiya Yunwa nake ji, tun safe ban kuma cin komai ba, kuma kince kar inje ko ina ban samu na fita naci Abinci ba"
Hararasa tayi tai gaba abunta, suna fitowa falo taga an shaƙe kan dining da Kulolin Abinci, wani murmushi tayi ta kalli Yusuf tace "jirani anan"
Ta juya ta koma part É—inta, fitowa tayi hannunta É—auke da magenta ta nufi dining.
Alama ta yiwa Yusuf da hannu yaje, ya nufi kan haɗaɗɗen dining ɗin da'aka shaƙe da kayan Abinci.
Tai masa alama da ya zauna, yaja kujera ya zauna tace "buɗe duk abunda kake so a gurin nan kaci"
Kallonta yay yace "Amma ranki ya daɗe, naga kamar baƙo aka shiryawa teburin
" bana son musu ko jayayya, umarni na baka ba shawararka nake nema ba" ta faÉ—a cikin faÉ—a da bada umarni.
Yusuf ya shiga buÉ—e Kulolin, Abinci ne kala kala kamar ba'asan zafin nema ba, yasan duk tsiya wanda aka shiryawa Abincin baze iya cinyewa ba.
Widad ta zuba kifi akan plate ta miƙawa magenta, Taja plate itama ta ɗiba ta zuba, dama Yusuf yunwa yake ji ga Abinci yayi daɗi nan ya dinga zurawa
(samun guri direba a dining 🤣🤣🤣)
Ramla ce ta fito itada Amal suna magana, me zasu gani Widad da mage ga direbanta suna cin Abincin da'aka shirya karɓar baƙon Ramla sannan baƙon Widad, Amal tayi saroro tana kallon Ramla.
A fusace Ramla ta ƙarasa dining ɗin kamarta fashe da kuka tace "Widad wane irin wulaƙanci ne wannan, ta yaya za'ayiwa baƙo girki ki zauna kina ci naga dai idan munyi Abinci ba ci kike ba, dan kawai ki muzgunamin kika yi haka? Saboda wulaƙanci kuma ace harda direbanki saboda tsabar tozarci"
Shidai Yusuf bece komai ba, Widad cikin ko in kula tace "Ramla me direban nan nawa yayi miki ne haka? Naga kuna takun saƙa sosai dashi, kina yawan manta wani abu Ramla, duk wanda yake aiki a ƙarƙashina matsayinsa ɗaya da duk wanda yake zaune a gidan nan ƙarƙashin kulawa ta, dan haka babu laifi dan na bashi Abinci ko?"
Cike da ɓacin rai Ramlah tace "Amma fa baƙo nayiwa, ta yaya zaki min haka? Ina laifin kice inda saura in zuba masa"
Widad tace "waini wannan baƙon gurina yazo ko gurinki?"
Ras gaban Ramla ya faÉ—i jin tambayar da Widad tayi mata,
"naga alamar gurinmu yazo nida ke, nasan kina tunanin me zakice masa ne, idan baki da abunda zaki gaya masa kice kinyi masa girki, 'yar masu gida tayi yadda take so dashi"
Hajiya Halima da ta fito ta riski rigimar tace "Amma Widad baki kyauta ba, ya za' ayi kidinga nuna direba yafi 'yan gida"
"Ni bana abu dan in kyauta dama, bana abu dan in birge kowa, muddin zan cigaba da saka doka ana watsi da ita nikuma zan cigaba da ɗaukar matakin daya dace, if i can recall a falon nan nayi kashedi akan a dinga bawa direbana Abinci, akayi fatali da dokar aka barshi da yunwa tun safe, nayi abunda ya dace ne, ga ragowa nan mun bari idan baƙon naki yana buƙata seya ci dan naga ƙirarsa ta mayuntace dama kamar baya ƙoshi"
Tai maganar tana kallon Ramla, tare da goge hannunta da tissue.
Da gudu Ramla ta bar falon tana kuka, ita kanta Amal ba taji daÉ—in abunda Widad tayi ba taji haushin hakan.
Yayi parking É—in motarsa a harabar gidan ya fito daga motar, yana rufe motar tare da amsa waya, kamar an ce ya É—aga kai ya hangota tana fitowa, fara ce sosai fari me É—aukar ido, tana da matsakaicin tsayi sannan tana da shape me kyau.
Tabbas idan ba gizo idonsa ke masa ba wannan itace Yarinyar da Anwar yake kallo a hoto yana nuna masa, kenan itace Widad É—in daza'a haÉ—a shi Aure da ita? '