Akidata Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Akidata_Book_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 8 of 8
PART1
Page 24_25
Gaba ɗaya ma'aikatan gidan su kayo kan Alhaji Nasir, sedai jikinsa kamar babu rai, 'yan sanda suka ƙaraso cikin gidan aka kwashi Alhaji Nasir a daren zuwa Asibiti.
Widad kam gajiya tayi da zaman motar, saboda tafiya suke bata wasa ba cikin wani irin azababben gudu, jin tafiyar taƙi ƙarewa ne yasa Widad fara mustu mutsu, tun tana mutsu mutsun har bacci ya kwashe ta, a firgice ta farka ta kurma wani uban ihu tana kiran
"wayyo Allah na Yoseef, karka tafi ka barni"
Yusuf yace "Widad ina nan, muna tare har yanzu Allah ze fitarmu insha Allah, ki dena shouting karsu miki wani abun"
Me tuƙa motar yace gara dai kaja mata kunnen.
Memakon tayi shiru ta cigaba da ihu tana "ku ƙyalemu mu tafi, yoseef na gaji da zaman nan hannuna igiyar nan ta dameni, bayana ciwo na gaji bayana ze karye"
Wata hoda su watsawa Widad, wanda hakan yasa ta baccin dole, ba Widad ba har Yusuf gaba É—aya bacci ya kwashe su.
Ana kai Alhaji Nasir Asibiti, aka kwantar da shi aka dinga masa allurai da ƙarin ruwa, ga oxygen ansa masa domin temakawa numfashinsa dake barazanar ɗaukewa.
Likitoci suka duƙufa akansa, suna bashi dukkanin taimakon da zasu iya, ga jininsa ya hau fiye da kima suna ta ƙoƙari jininsa ya sauka.
Yusuf ne ya fara farkawa jin motar ta tsaya, aka buɗe motar suka kwance musu ido, mamakine ya kama Yusuf, tun cikin dare suke tafiyar nan amma da'aka kwance musu ido yaga yanayin garin kamar Azahar ta gota, daji ne sosai ciyayi sun lulluɓe ko ina, gaba ɗaya Yusuf baya gane inane gabas ko yamma ya kasa gane ta ina suka zo nan gurin.
Widad kam sam bata hayyacinta, ta farka amma se tangaÉ—i take haka suka sasu a gaba zuwa wani gini.
Yusuf yayi mamakin yadda aka shigo cikin wannan uban dajin akayi ginin gida, suka buÉ—e gidan suka shiga dasu Yusuf.
Gaba É—aya gurin kango ne, kuma ga dukkanin alamu an samar dashi ne mussman saboda wannan aikin, saboda gurin sabon gini ne harda ragowar kayan aikin ginin.
Wani ɗaki suka kai su Widad suka ajiye, akan tsurar tabarma suka kawo musu ruwan pure water guda biyu suka ajiye musu suka maida ƙofa suka rufesu a ciki.
Yusuf ya ɗau ruwa ɗaya ya fasa ya bawa Widad, aikuwa nan da na ta zuƙeshi da alama tana jin ƙishirwar sosai, ga ko salla ba suyi ba haka ya zuba mata ruwa tayi alwala, ɗan ragowar shima yayi ba tare da sun san inane gabas ba haka suka gabatar da salla.
Shiru Widad tayi, gaba ɗaya jikinta ciwo yake ga wata uwar yunwa da take ji, gashi har yanzu jikinta babu ƙwari saboda hodar da suka watsa mata.
Ta kalli Yusuf da yayi shiru ya sunkuyar da kai, gaba É—aya tausayinsa yakamata duk a dalilin ta wannan masifar ta faÉ—a masa.
Kifewa tayi a gurin, hakan yasa Yusuf É—agowa da sauri yana kiran sunan ta, cikin kasala tace "Yunwa nake ji"
A hankali yace "kiyi haƙuri kinji, Insha Allah zamu bar gurin nan, kuma zaki ci Abinci"
Ba tace komai ba ta maida kanta ta kwanta, wani irin sanyi na ratsa ta, miƙewa Yusuf yayi yana zagaye ɗakin harda ban ɗaki sedai an rufe ko ina babu hanyar tsira.
Zagaye É—akin ya shiga yi yana sake tunanin menene mafita, ya kalli inda Widad ke kwancw ta takure sosai gwanin ban tausayi.
Haka suka wanzu babu me cewa komai tsawon wasu awanni, suka riƙe alwalarsu in sun kintaci lokacin salla se suyi.
Alhaji Bulama ya samu ya koma gida, dan Alhaji Nasir ya farfaɗo ya samu bacci, yana zuwa Matarsa tace "kaikam ina ka tafi haka, na farka na nemeka na rasa na dinga kiran wayarka kaƙi ɗagawa, duk ka ɗaga mana hankali"
"Daula ne babu lafiya" ya bata amsa
Sekuma jikinta yayi sanyi tace "meya same shi?"
"An sace 'yarsa da direbanta, shi kuma ya yanke jiki ya faÉ—i"
Dafe ƙirji Hajiya Sarah tayi tace "Kamar ya an sace su sekace kaji? Yaza' ayi ace 'ya kamar ta Alhaji Nasir an saceta, suwaye suka sace ta?"
"Mutanen da suke bibiyar sa ne, ni nafi kyautata zaton harda haÉ—in bakin direban nata"
Sarah ta girgiza kai tace "Amma Alhaji wannan yaron sam neyi zubin Azzalumai ba"
"ke bari, duniyar nan babu gaskiya shi mugu ai bashi da kama"
"Hakane, Allah ya fidda su lafiya, amma an sanarwa jami'am tsaro?"
Bulama yace "eh na sanar musu an fara bincike ma"
Gaba É—aya Hajiya Sarah ta shiga damuwa, dukda yadda take jin haushin Widad, su Ramadan ma da Iman sin shiga damuwa sosai da jin labarin.
Isa megadi ne ya shigo falon gidan a gigice yana kiran Hajiya.
A fusace Hajiya Halima tace "lafiya kake min wannan kiran kamar wata 'yarka"
"Hajiya babu lafiya fa, muna nan zaune gaho an sace Autar daula da direbanta, shi kuma Alhaji yana kwance a Asibiti"
"to shine me zaka zo kanamin wannan kiran, aita sace tan mana ai hakane ya dace da ita, Allah yasa daga na su kashe ta ma kowa ya huta, fita ka ban guri ka koma kan aikin ka"
Galala Isa ya bita da kallo, "bazaka fita ba sena zo na kwasheka da mari"
Jiki a sanyaye yayi waje yana tunanin, to idan ma bata tausayawa Widad ba saboda tana musu wulaƙanci to Alhajin fa, wanda duk wani gata da jin daɗi a dalilinsa suka same shi.
Yana wannan tunanin yayi karo da Anwar ba tare da ya sani ba.
Anwar yace " lafiya kuwa? Kana tafe baka ganin gabanka"
A firgice Isa ya labarta masa abunda ke faruwa, wata mummunar faÉ—uwar gabace ta kama Anwar yace "garin yaya Isa? Ina Alhajin yake?"
Isa yace "Ance yana Asibiti, amma bam san wane Asibitin bane, sedai a tambayi Alhaji Bulama"
Anwar yace "shikenan nagode"
Ya nufi cikin gida da hanzari, ya tarar mahaifiyarsa da Ramlah suna ta hirarsu.
Anwar hankali a tashe yace "Mummy kin san meke faruwa kuwa, Daddy yana kwance ba lafiya sannan an sace little"
Cike da salo da iya rainin hankali Hajiya Halima ta miƙe tayi gigicewar ƙarya tace "haba dai waye ya gaya maka, bana son wasa fa"
Anwar yace "ba wasa bane Mummy, ki kwantar da hankalinki, zanje gidan su Fahad inji komai, se inzo muje Asibitin".
"shikenan hanzarta Anwar, innalillahi wa inna ialaihi raji'un Allah yasa ba gaske bane"
Anwar yace "Mummy ki kwantar da hankalinki, ina dawowa" yayi waje da sauri ko ganin gabansa ba yayi saboda tashin hankali.
Duhu ya fara yi sosai, ba wanda yasa wani abu a cikinsa tsakanin Widad da Yusuf, can sukaji hayaniyar mutanen da suka sace su sun shigo, Widad tayi zumbur ta tashi zaune, suka saka mukulli suka kwance sarƙar da suka kulle ƙofar da ita da kuma kwaɗon sannan suka shigo.
Manyan torchlight suka kunna suna haske su Yusuf, suka shigo hannunsu É—auke da mugayen makamai, da manyan bindigogi.
Babban ya haske Widad da fitila, ta sunkuyar da kai taƙi ɗagowa yace "shegiya kalleta kamar ta Allah, zamu kawo ƙarshen wannan izzar da gadarar taki uwar taurin kai"
Yai maganar tare da ajiye mata takeaway a gaban ta, wata bushashiyar shinkafa ce a ciki sekace ƙanzo gefen shinkafar duk ƙonanniya.
"ki tashi kici Abinci Malama, sedai ba irin na gidan shashsashan ubanki bane daya sangartaki"
Ƙafarta ta saka tayi Ball da takeaway ɗin shinkafar ta watse a gurin.
Aikuwa ya harzuƙa ya shaƙeta yana faɗin "nan ba gidan ubanki bane da zaki mana gadara, zakiga yadda zamu lallasa ki sekin sauke wannan izzar taki"
A gigice Yusuf yazo ya riƙe hannun sa yace "dan girman Allah kayi haƙuri ka ƙyaleta, a galabaice take zata iya mutuwa inka cigaba da shaƙeta"
Yayi jifa da ita ta faɗi jiki ba ƙwari tana kakari, ya kalli Yusuf yace "banza ɗan shishshigi ga abunda shishshigi yaja maka nan, aka dinga ja maka kunne akanta amma kaƙi ji, ga shi nan koba komai kaima ka shiga wahala"
Yusuf bece komai ba yayi kan Widad yana ɗagota, da ƙyar take numfashi.
Yusuf yace "Uwar É—akina, ki dena musu gardama ko so kike su kashe ki a gurin nan?"
Lumshe ido kawai tayi tana sauke numfashi da ƙyar.
Hadda Saleh aka tafi Asibiti gurin Alhaji Nasir, an samu ya farfaÉ—o har ya zauna sedai yayi shiru baya magana.
Saleh yace "sannu ranka ya daÉ—e"
Daula ya jinjina kai, ya kamo hannun Saleh yana ta haki yace "Saleh 'yata, an sacemin Widad da Yusuf nayi dana sanin saka Yusuf a harkar tafiyar nan, gashi ya shiga matsala a dalilina"
Saleh yayi shiru sannan yace "kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka Alhajin Allah, babu yadda za' ayi akasa gano inda Widad take, a matsayinka na babban mutum a ƙasar nan, Insha Allah zasu kuɓuta"
Daula yace "ai ba wai kuɓutar tasu ba, yadda zasu tsira da rayuwar su bayan sun kuɓutan shi nake tunani"
Saleh yace "karka damu da wannan Yallaɓai, yanzu Addu'ar mu suke buƙata insha insha Allah zasu kuɓuta"
Bulama ne da matarsa suka shigo É—akin shida Anwar da su Ramadan, Bulama yace "sannu ya jikin naka?"
"Alhamdilillah"
"Ubangiji Allah ya ƙara afuwa"
"Ameen" na suka shiga yi masa sannu, Anwar ya ƙarasa kusa dashi yace "Sannu Daddy Allah ya baka lafiya"
Kasa Amsawa yayi sema share ƙwalla da yayi yace "Anwar an sacemin Widad, an sace autar daula, ga yaron dabe ji ba be gani ba shima ta ritsa dashi"
Cikin damuwa Anwar yace "ka kwantar da hankalinka Daddy, Insha Allah zasu kuɓuta, za'a gansu, babansu Fahad yace min an kai report"
Alhaji Nasir yace "Allah yasa su kuɓuta gaba ɗaya yasa karsu cutarmin da su"
Alhaji Bulama yace "ka jika da wani zance, muji da 'yarmu da' aka sace kana wani kar'a cutar dasu"
Alhaji Daula yace "haba Bulama, ai gara su riƙe Widad su saki Yusuf, yana zamansa a dalilina da 'yata ya shiga hatsari, in gaya maka gaskiya tsakanin Widad da Yusuf ba wanda bana so, Allah ya samin ƙaunar yaron a zuciya ta, bazan so ya rasa ransa ba shima, Allah ya bayyana min su duka ba wanda bana so"
Kuka sosai Alhaji Nasir yake kamar ƙaramin yaro, Anwar ne ya rungume shi a jikinsa, yana faɗin "yi haƙuri Daddy, duk zasu kuɓuta cikin ƙoshin lafiya, kar lafiyar ka ta taɓu, kaima muna buƙatarka"
Hajiya Sarah tace "dole Baban Widad yayi kuka kuma gaskiya ya faÉ—a, yaron nan shima abun tausayi ne, beji ba be gani ba tsautsayi ya ritsa dashi abun da tausayi"
Alhaji Bulama yace "dama ku mata wani lokacin ba hankali kuka cika ba, dama Allah yayi haka zata faru dashi, amma mudai mu samu 'yarmu ta kuɓuta"
Hajiya Sarah tace "shi Yusuf ɗin ba uwace ta haife shi ba? Ya zataji idan ta samu labarin ɓatan ɗanta?"
Ramadan ne yai saurin cewa "Mummy kiyi haƙuri kiyi shiru, duk zasu bayyana insha Allah, Allah sarki Yusuf ɗin nan yana da kirki wallahi ga haƙuri da yawan murmushi"
Likita ne ya shigo ze duba Alhaji Nasir, dan haka duk aka basu umarnin su fita daga É—akin domin a duba shi.
Anwar ya maida su Alhaji Nasir gida, ya shiga part ɗin Fahad, sedai ya tarar da shi da mace suna shan shisha, Anwar ya girgiza kai dan ya saba ganin Anwar a wannan halin, mussman da suna ƙasar waje, Anwar yace "Fahad baka san meya faru da Widad bane da direbanta, ina ta kiranka baka ɗaga ba?"
Fahad ya fesar da hayaƙi yace "Nasani mana"
"Amma ko Daddyn namu ai yakamata kaje ka duba"
Fahad ya kalle shi yace "Daddynku ku suwa? Baza'a dubo shi É—in ba, ni burina duk inda ta shiga a nemo min mata ta, dan nasan wannan tsinannen direban ne ya gudu da ita, kuma sena nuna masa iyakarsa"
Karuwar dake tare da Fahad tace "Baby wai maganar wa kuke yi ne?"
Fahad yace "ba ruwan ki uwar shishshigi, jeki shirya inzo in maida ke gida"
Anwar yace "Fahad se yanzu na sake tabattar da Widad a kan gaskiya take na ƙin yadda da mutane, yanzu Fahad kasan nida kai iyayenmu basu da ƙarfin kaimu ƙasashen waje, amma ya ɗauke mu kamar yaransa, ya kaimu ƙasar waje mukayi karatu, dukkaninmu ba wanda be mallakawa motar hawa ba da gidan kansa, muba komai ba silarsa muka zama wani abu, kalli yadda muke fantamawa a cikin rigar arzikinsa, albarkacin sunansa duk inda muka shiga a faɗin ƙasar nan muna da Alfarma, yau shine Iftila'i ze faɗa masa amma ka nuna halin ko in kula, Anya Fahad kana gayawa kanka gaskiya kuwa "
Fahad yace " A'a sedai idan yanzu zaka fara gayamin gaskiyar "
Yai maganar tareda miƙewa ya shige bedroom ɗinsa, jiki a saɓule Anwar ya baro gidan Bulama ya koma Asibiti, ya bawa Alhaji Nasir Abinci ya canza masa kaya, sedai yaita mamakin rashin ganin mahaifiyarsa taje Asibitin gurin mijinta.
Gida ya koma yana tunanin butulci irin na Fahad, a falo ya tarar da Hajiya Halima tana cin Abinci suna kallon zee world, sedai kamar Amal ce a cikin damuwa.
Anwar yayi sallama suka amsa gaba É—aya, Anwar yace "Mummy meyasa ba kije Asibiti ba?"
"bana jin daÉ—ine, bana son inje inga abunda ze sake É—agamin hankali"
"Amma Mummy ai jikin nasa da sauƙi, kuma yakamata ace ko su Ramla sunje duba shi"
A fusace tace "Ubansu ne da lallai se sunje duba shi, fita ka bani guri dalla"
Buɗe baki yayi yana kallon mahaifiyarsa yana ƙoƙarin tabattar da anya daga bakinta wannan maganar ke fitowa?
Duhu ya fara yi, sauro ya shiga ambaliya a gurin nan, Yusuf ya zauna se akin yi mata fifita yake da wani gutsararren kwali, A hankali Yusuf yace "Kidena musu taurin kai kinji, sannan idan an baki Abincin ki karɓa kici, baze yuwu ki zauna da yunwa ba"
"ba zanci ba" ta bashi amsa
"kin fi son su cigaba da azabtar dake?"
Shiru tayi masa ba tace komai ba, can ya kuma cewa
"dan Allah ki basu abunda suke nema, dan su ƙyale ki ko a yanzu kin galabaita"
"wallahi ko zasu kasheni bazan basu ba, shiyasa nace tun farko su sake ka ni su barni anan"
"tayaya zasu sakeni in tafi, alhalin kina gurinsu sedai kome ze faru ya faru muna tare"
Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, tana jin yadda sauro ke shagali akanta, abunda bata saba ba, bata son yin kuka dan yanzu Yusuf ze É—aga hankalinsa
Cikinsu babu wanda ya rintsa, har gari ya waye, taimama sukayi sukayi sallar Asuba.
Fuskar Widad duk ta kumbura saboda sanyi da cizon sauro, kuma har a lokacin jikinta babu ƙwari.
Yusuf yana zaune, yayin da Widad ke kwance akan tabarmar, buɗe ƙofar ɗakin akayi suka sake shigowa su huɗu.
Suka kalli inda Widad ke kwance, É—ayan ya buga mata tsawa yace
"tashi ko in taka ƙafarki in karya banza"
Gyara kwanciya tayi ta juya musu baya, alamar bata da niyyar tashin, yau Yusuf ya ƙara tabbatar da azababben taurin kai da Widad ke dashi.
Da sauri Yusuf yazo inda take ya É—aga ta zaune yace "ya haka ne, so kike yauma su dake ki"
Wani banzan kallo tayiwa shugabn nasu ta É—aunke kai tana hura hanci.
ÆŠayan yace "shegiya se kyau kamar ita tayi kanta, amma zuciyar ta kamar dutse shegiya me kama da sadakar yalla"
Babban su yace "zamuyi maganinta kafin tabar gurin nan, da ganin idonta yunwa take ji, amma saboda taurin kai taƙi cin Abinci, ku ɗakko Abinci ku bata idan taga dama taci"
Shinkafa da wake ce irin garau garau ɗin nan takan 'yan talla, tayi sanyi ƙalau ga ba mai sosai, suka dire mata a gabanta, yunƙurawa tayi zata sake fatali da Abincin Yusuf ya riƙe ta yace "dan Allah ki daure kici, kinga tun shekaranjiya rabonki da Abinci"
Ta kalli idon Yusuf tace "bazan ci ba"
Ɗayan yace "kai dalla ka ƙyaleta mana, kar taci ubanwa tayiwa, Oga ka fara aiki kawai"
Rarrashin duniya Widad tayi mursisi taƙi cin Abinci.
Babban cikinsu ya É—akko wayarsa zeyi kira.
"Nurat ki kaiwa Daddynki tea ɗin nan da baƙinsa, kafin yazo ya ishemu da faɗa"
Nurat ta miƙe ta ɗauki kayan tea ta nufi part ɗin mahaifinta.
Alhaji Munir ya shafa ƙaton cikinsa yace "nifa bakina yaƙi rufuwa ma, nasan dole abun nan yazo hannunmu a yau base gobe ba, nace a tura masa saƙo, kodai ya bayar ko mu cigaba da tsare ta"
Alhaji Musa yace "ba kai kaɗai ba ni kaina ina cikin murna, sun kwana a hannu, Daula yana gadon Asibiti yana ta sharɓar hawaye, mutum se taurin kan tsiya kamar arnen dutse"
Suka kwashe da dariya, Alhaji Haruna yace "dalla ƙyaleshi, gefe guda baze samu Halartar taron shekara na kasuwanci ba, da haka zamu sanar da cewa an samu gagarumar Asara kasuwancin da muke yi, zamu bada fake Account statement, zamu kwashi rabonmu kafin wancan yazo hannunmu, ai daula ya gama yawo wai shi me gaskiya"
Suka sake kwashewa da dariya, wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, ya É—aga ya sa musu a hands free, Alhaji Haruna yace "Ya me ake ciki ne?"
"Yallaɓai tunda nake aikin nan, ko a maza ban taɓa ganin mutum me baƙin taurin kai kamar yarinyar nan ba, kwana biyu kenan taƙi cin Abinci, ruwa kawai take sha, gashi kamar bata da lafiya kullum tana kwance ko magana seta ga dama take yi"
Alhaji Munir yayi tsaki yace "dalla ku rabu da ita, ku karɓo mana abunda muke buƙata, sannan ku turawa ubanta saƙo shima koya bamu ko kuma ku kashe ta"
Daga wayar akace "An gama Oga, yadda kukace"
Nurat da taje kai musu shayi jikinta ya shiga ɓari, dan tsaf taji hirar da mahaifinta suke yi, cikin sanɗa taje ta ajiye farantin kayan shayin, ta ruga da gudu ɗakinta ta saka hijjabi ta ɗau wayarta ta fice daga gidan.
Babban cikin mutanen wanda suke cewa me Adda ne ya É—akko wata kujera ya zauna a gaban Widad ya kalle ta cikin tsawa yace
"ke kalleni nan, ina takaddun nan suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi ko kuma in kasheki in koma in kashe wancan daƙiƙin uban naki"
Sunkuyar da ka tayi tai shiru, Yusuf yace "Yana miki magana ki gaya masa, su ƙyaleki ki huta"
Kallon Yusuf tayi da jajayen idonta sannan tace "takaddun da suke nema, akwai masu shi nayiwa Daddy Alƙawarin miƙasu ga masu shi, kuma na bawa masu shi suna can suna yawon su a gari, me suke so kuma ince musu"
"ƙarya kike, duk binciken da'akayi sun tabattar da suna wajen ki dan haka ki gayamana inda suke"
A harzuƙe tace "bazan faɗa ba, nace bazan faɗa ba kayi abunda zaka yi!"
Kan bindiga É—aya yasa ya buga mata a baki, take jini ya shiga zuba daga bakinta Yusuf ya gigice ze tashi, suka É—ora masa bindiga aka "kana motsawa zamu fasa kanka da harsashi"
Widad ta tattaro dukkan yawun bakinta, me ɗauke da jini ta tofawa shugabannin nasu tace "wallahi ko me zaki sedai kayi, bazan bayar ba ka koma ka gayawa Azsaluman da suka saku aiki cewar bazan bayar ba, kuma matsorata ne tunda suka gaza fitowa gaba da gaba su karɓi abunda suke so, kuma ko sun kasheni na kafa musu tarkon da ko bayan raina se Asirinsu ya tonu, saboda na sansu kuma na tattara duk wata hujja da yakamata a kansu san......
Bata ƙarasa ba ta kuma jin wani marin a fuskarta, a duk lokacin da suka daki Widad Yusuf ji yake kamar ƙirjinsa ya tsage dan baƙin ciki, sedai ba yadda ya iya muddin yayi wani yunƙuri dabe gamshesu ba zasu mata illa, dan ba imani ne dasu ba, ga Widad bakinta yaƙi mutuwa.
Nurat bata tsaya ko ina ba se gidan su Widad, a waje ta tarar da Anwar ya fito da mota ze fita, Anwar ne ya ganta dan sam bata lura dashi ba yace "Nurat"
ÆŠaga kai tai ta kalle shi sannan tace "Yaya Anwar ashe ka dawo, babu Labari"
Anwar yace "Na dawo, ina zaki haka naga kamar bakya hayyacinki"
Nurat tace "gurin Widad nazo"
Anwar yace "baki san na sace ta ba ita da direbanta?"
Hannu ta ɗora a ka, ta durƙusa a gurin ta fashe da kuka, Anwar ya fito daga motar yace "Nurat lafiya kuwa?"
Nurat tace "lafiya ƙalau, dan Allah kasan wani ɗan uwanta wanda suke yawo tare?"
Anwar yace "Ai Widad bata da É—an uwa"
Nurat tacs "Nasani, wannan zaka ga tare suke yawo, ban san sunashi ba ya cemin É—an uwanta me shi, wani dogo kamar bafulatani, me yawan murmushi"
Anwar yace "ko Yusuf kike nufi?"
Nurat tace "ban san sunansa ba"
Anwar yace "indai Yusuf ne tare suke yawo kam, kuma tare aka sace su"
Zare ido waje tayi tace "tare aka sace su, na shiga uku ni Nurat, meyasa aka sace su?"
Anwar yace "shine abunda bamu sani ba, amma 'yan sanda na nan na bincike yanzu haka zanje Asibiti gurin daddynta ne, daga nan mu koma station"
Nurat tace "zan iya binka in duba shi?"
Anwar yace "meze hana? Muje"
Suka shiga motar suka tafi.
Me Adda ya jinjinawa wannan baƙi taurin kai na Widad, yasa bakin bindiga ya daki kanta dashi ta kurma wani uban ihu tace "wallahi ba zan faɗa ba, sedai kayi min duk abunda zakamin"
Ya kuma ɗaga bakin bindiga ze da keta, Yusuf ya miƙe ya riƙe shi gam yace 'Anya akwai imaniba zuciyar ka, kalli yadda take kururuwa amma ba zaka ƙyaleta ba"
Me adda yasa hannu ya hankaɗa Yusuf amma Yusuf ko gezau beba, ya kalli Yusuf ya kuma ƙoƙarin hankaɗeshi amma Yusuf ko gezau balle ya kai ƙasa dukda ya kwana biyu ba Abinci amma hakan besa ya faɗi ba.
HaÉ—uwa sukayi su huÉ—u suka kama dukan Yusuf, da manyan sanduna, suka masa jina jina sannan suka É—aureshi, tun suna dukansa Widad na ihu harta suma a gurin.
Koda Anwar yaje a Asibiti seya tarar da mahaifiyarsa da su Ramlah a gurin, tayi masa ƙaryar wai da'aka gayamata abunda ya faru suma tayi seda aka kaita Asibiti shiyasa bata zoba, shi kuma Daddy ya yarda da abunda ta faɗa.
Anwar tun yana mamakin abubuwan da suke faruwa harya dena.
Nurat ta ƙarasa gaban Gadon Alhaji Nasir tace "Sannu Daddy ya jiki".
Ta faɗa tana sheshesheƙar kuka.
Alhaji Nasir yace "da sauƙi Nurat, ashe kin samu labarin ɓatan ƙawar ki?"
Ta jinjina masa kai alamar eh, yace "to ki cigaba da Addu'a Allah ya bayyana ta, sannan ki koma gida kar babanki yayi miki faÉ—a kinzo nan"
Ya kalli Anwar yace "É—an beauty mayar min da ita gida kaji"
Yai maganar cikin ƙarfin hali cike da zolayar Anwar.
Anwar yayi murmushi, tare da wayancewa ya goge ƙwallar dake idonsa, kallo ɗaya zaka yiwa Alhaji Nasir kasan yana matuƙar jin jiki.
Tunawa yayi da abunda Widad ta gaya masa daren da abun ze faru, take yaji wasu hawayen na bin idonsa, duniya Kenan Abun tsoro.
Saleh ya kasa zama, ya kasa tsaye abun duniya ya dames hi, tabbas Alhaji Nasir mutumin kirki ne ya masa alkhairi daban daban a rayuwar sa, ga Yusuf dabe ji ba be gani ba shima an ritsa dashi, anya hakki ze barshi kuwa, wannan tunanin ne ya cika masa zuciya ko Abinci ya kasa ci.
Widad ta buɗe ido a hankali ta kalli inda Yusuf ke kwance, duk jikinsa jini, se sauke ajiyar zuciya yake, gashi an ɗaure shi tamau da sarƙa.
Ko tashi bata iyayi saboda dukan da take sha, jikin ta ko ina rauni ne, ta janyo jikinta a hankali tazo inda Yusuf ke kwance kawai ta faÉ—a kansa tana kuka.
"Yoseef dan Allah ka tashi, dan Allah kayi magana idan kana jina"
A hankali can ƙasan maƙoshinsa ido a lumshe yace "Insha Allah zamu kuɓuta, ki dena kuka, ina mana Addu'a nasan Daddynki ma yana yi, Ummana ma tana yi mana"
Haka ta cigaba da ƙoƙari ko zata iya kwance Yusuf, amma abu yaci tira.
"Ranka ya daɗe yarinyar nan fa baza tayi magana ba, mun daka mun daka amma kamar jinjirar jaka saboda taurin kai, mun mata jina jina amma taƙi faɗa se rashin kunya take yi, gashi kwana huɗun nan Ruwa kawai suke sha, ita muna bata Abinci amma taƙi ci duk ta galabaita "
Alhaji Haruna yace " A tauna tsakuwa, dan aya taji tsoro kuyi mata azaba wadda zataji a jikinta"
Me adda yace "An gama ranka ya daÉ—e"
Ya buɗe ƙofar ɗakin dasu Widad ke ciki, tana zaune a gaban Yusuf ta zuba masa ido idonta yayi jawur saboda yunwa da wahala, gashin kanta duk ƙasa da abun ciyay, saboda birgimar da take a gurin, ya sauka a kafaɗarta ya baje kamar mara hankali.
Suka ƙaraso suka kwance Yusuf, da shima yake a mugun galabaice, suna kwance shi Widad ta kama ƙasan rigarsa tana goge masa jinin jikinsa, me Adda ya fizgota ya zaunar da ita tana fuskantar sa yace "ke dan uwarki wannan shine karo na ƙarshe da zan tambayeki, dan mun gaji da wannan sintirn a wannan surƙumin dajin, ina takaddun nan suke?"
Cikin tsawa tace "ban sani ba! Kuma karka sake zagin uwata dan uwa bata fi uwa ba"
Yadda gashin kanta baƙi kamar na Larabawa ya baje, gaba ɗaya seta burgeshi danƙo gashin kanta yayi ya miƙar da ita tsaye, tsanani zafi yasa ta fasa ihu, Yusuf ya yunƙura ze miƙe suka sake buga masa sanda a ƙafa ya faɗi ƙasa.
Ya kai bakinsa na Widad da niyyar ya haɗe bakinsu, tayi masa gware da kanta, dukda yaji zafi hakan besa ya cikata ba, ya kuma danƙar gashin kanta ze haɗe bakinsu, ta tattaro ƙarfinta ta daki mararsa da ƙafarta, a gigice yayi jifa da ita, ya ɗakko ƙaramar pistol ya harbe ta a hannu, tare sukayi ƙara da Yusuf ta zube a gurin jini na zuba a dantsenta.
Me adda miƙewa tsaye ma kasawa yayi saboda bala'in azabar da yake ji, 'yan uwansa suka ɗauke shi, suka sake kulle su Widad.
Yusuf ya ƙarasa kan Widad ya ɗagota, a gigice yake magana "Widad sannu, kina ganina?"
Ta jinjina masa kai dukda idonta na ƙoƙarin lumshewa, jikinta se rawa yaje gumi na tsatstsafo mata ta ko' ina.
Yusuf ya É—au É—an siririn mayafint da tazo dashi ya É—aure mata damtsen, ya rungomata jikinsa yana jijjigata yace
"Dan Allah karki tafi ki barni, zamu bar gurin nan insha Allah, zan maida ke gurin Daddy, dan Allah Widad karki tafi ki bar Yusuf"
Sosai hawaye ke zuba daga idon Yusuf, magana takeson tayi amma ta kasa, se rawa da bakinta yake yi kawai, ta ɗaga hannu da nufin ta kaishi fuskar Yusuf amma abu ya gagara hannun ya sauka tun tana ganin Yusuf dishi dishi harta dena ganinsa wuyanta ya langaɓe.
Rungume ta yayi a jikinsa yana ambaton Allah, yana sheshesheƙar kuma, yayin da mayafin da ya ɗaure mata hannu dashi ya jiƙe sharkaf da jini.
In an karanta ayi share please, masu neman recent pages dan Allah ku dinga dubawa a watpad, @ Ayshercool7724.
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
           _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
(GAMAYYAR MARUBUTA NA ELEGANT ONLINE WRITER'S, INA GODIYA DA KARRAMANI DA'AKAYI DA CERTIFICATE NIDA ƘUNGIYATA TA PERFECT WRITERS ASSOCIATION, INA GODIYA DA WANNAN KARAMCI UBANGIJI ALLAH YA ƘARA HAƊA KAN MARUBUTAN MU AMEEN, INAWA KOWA DA KOWA FATAN ALKHAIRI, TARE DA FATAN KOWA YAJE GIDA LAIFIN)
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 26_27
Gaba ɗaya Widad ko motsi ba tayi, Yusuf ya rungumeta sosai a jikinsa kamar wani ze ƙwace masa ita, zuciyar ta na bugawa amma numfashinta baya fita sosai, ga cikinta se ƙara yake saboda yunwa.
Anwar ya kai Nurat gida, suka yi Sallama, ta shige gida jikin ta na rawa ta tafi É—akin mahaifiyar ta.
"ke ina kika fita kikaje ban sani ba?"
"Mummy akwai matsala fa"
Cike da rashin fahimta mahaifiyar ta tace "matsalar me?"
"Widad ta ɓata an sace ta"
Dafe ƙirji tayi tace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, waye ya gaya miki?"
"Mummy can naje fa, Daddynta yana Asibiti ma naje na duba shi ma"
Zaro ido tayi tace "ubanwa yace kije? Sekin jawa kanki faɗa a gurin mahaifinki ko? Tashi maza kije ki cire hijjabin nan ki huta"
Nurat ta kalli mahaifiyar ta tace "Mummy, Daddy ne fa yasa aka sace Widad"
"inji ubanwa? Rufen baki shashasha, in kika sake maganar nan yaji kema zeyi maganin ki"
"Mummy a matsayinki na uwa, ya zakiji idan ni aka sace, yakamata ki cire tsoro a ranki ki gayawa babana gaskiya, ranar da hakki ya tashi bashi kaÉ—ai ze kama ba harmu"
Ta ƙare maganar tare da ficewa daga ɗakin gaba ɗaya
Kwata kwata duk bidirin da'ake Fahad beje yaga jikin Alhaji Nasir ba shima kuma Alhaji Nasir be tambaya ba, yana fama da kansa.
Mussaman Abbas daga inda yake aiki ya kira Umman Yusuf ya sanar da ita ɓatan ɗanta, dama ta kira wayar Yusuf harta gaji bata shiga.
Aikuwa ta kiÉ—ime sosai ta tashi hankalin ta, ta shirya ta tafi gurin aikin Yusuf.
Ma'aikatan su kansu a kiɗime suke tun bayan da suka samu labarin ɓatan Yusuf, Suleman yayi duk yadda zeyi a basu damar bincike akam al'amarin amma daga sama aka hanasu, akace an riga an danƙa case ɗin a hannun wasu jam'ian tsaron.
Sosai Umman Yusuf tasa Abbas a gaba tana zabga kuka
"dan Allah ranka ya daÉ—e ina É—ana yake? Ku kuka sashi aikin nan ina kuka turamin shi shi kaÉ—ai nake kallo inji daÉ—i, Yusuf ne kaÉ—ai dani, dan Allah ku temaka ku nemomin Yusuf É—ina"
Cikin ƙwarin gwiwa Sulaiman yace "ki kwantar da hankalinki Umma, Insha Allah indai Yusuf ne zamuyi duk me yuwuwa muga mun kuɓutar dashi, an baza jami'an tsaro kuma ins me tabbatar miki ba abunda zasuyi masa dan bashi suke hari ba, yarinyar da yakewa aiki suke hari, dan ba suce abasu komai ba, yanzu haka mahaifin yarinyar yana kwance a asibiti, kuma bashi da magana seta Yusuf"
Suleiman ya dinga kwantar mata da hankali, amma abunka da É—a d uwa ta saurari kalaman Suleiman ne kawai, amma bata ga alamar ana neman É—an nata ba.
Umman Yusuf bacci ya ga gareta, balle cin Abinci banda kuka da Addu'a babu abunda take yi wa É—an nata, dan yanzu a duniya idan ta rasa Yusuf ba.
Jikin Alhaji Nasir ƙara rikicewa yake saboda damuwa, Anwar yace wa Mahaifiyarsa "Mummy ya kamata ayi wani abu akan rashin lafiyar daddy, inze yuwu ayi visa a fita da shi, kullum jikinsa ƙara rikicewa yake babu sauƙi"
Hajiya Halima tace "ko bangon duniya za'a kai shi idan Allah yayi niyyar karɓar rayuwarsa ba yadda muka iya, anan ɗinma naga likitocin suna iya ƙoƙarin su, meye kuma se an kwashi jiki an tafi ƙasar waje dan ɓarnar kuɗi"
"Mummy ɓarnar kuɗi kuma? Koma ɓarnar kuɗin ne naga nasane ai, meye amfaninsu in baza'a nema masa lafiya ba"
"kaga Anwar ka kiyaye ni, kafini sanin abunda ya dace ne? Fita ka ban guri kafin in ɓata maka rai, sakarai kawai"
Fitowa yayi gwiwa a saɓule yana tunanin wannan halina Mummynsa.
Gidan Bulama ya tafi, yaje ya tarar yana shirin fita, suka gaisa da Anwar, Anwar yace "Daddy gurinka nazo"
Bulama yace "gashi ina shirin fita ne, Amma meya faru?"
Anwar yace "Daddy dama cewa nayi meze hana a fita da Daddynmu waje a duba shi yadda ya kamata a can, naga kullum ciwon nasa gaba yake ba sauƙi"
Alhaji Bulama yace "Anwar kazo da magana me kyau, amma ka sani ko an fitar da Daula waje in har baze cire damuwa dake ransa ba, babu yadda za'ayi magunguna suyi masa aiki, haka likitoci suke ta faɗa"
"Amma da dai an jarraba, amma jikinsa yana bani tsoro"
Alhaji Bulama yayi shiru sannan yace "shikenan Anwar, zamu yi maganar da mahaifiyarka, zanga abunda ya dace ayi"
Anwar yayi masa godiya sannan ya tafi.
Alhaji Haruna ne zaune akan kujera, fuskar nan tasa babu alamar imani ya kalli wani matashi dake zaune yace
"doctor Sufyan, mun yaba da ƙoƙarin da kuke yi a Asibitinka akan Shahararren Attajirin da'ake ji dashi a faɗin ƙasar nan wato Alhaji Nasir Daula"
Doctor Sufyan yayi murmushi yace "Nagode ranka ya daɗe"
Alhaji Musa yace "Kasan meyasa muka kiraka?"
Sufyan ya girgiza kai alamar aa'
Alhaji Haruna ya gyara zama yace "Abunda muke so da kai shine, bama son Daula ya tashi"
Zare ido Sufyan yayi yace "kamar yaya?"
Alhaji Musa yace "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ba muna nufin ka kasheshi ba, A'a bama so ya tashi ya warke ta hanyar dena bashi magungunan da ya dace, kayi duk abunda zakayi masa wanda ze ƙara kwantar dashi, idan kayi haka akwai lada me tsoka da zamu baka"
Saleh dake gurin gaba ɗaya ya rikice yace "Amma Yallaɓai ba muyi haka daku ba, idan kuma ya rasa ransa fa?"
Alhaji Haruna yace "Saleh ka rufewa mutane baki, karka ɓatamin rai"
Ya maida hankalinsa kan doctor Sufyan yace "Yaya zakayi ko bazaka yi ba?"
Doctor Sufyan yace "Nifa na ɗau Alƙawarin bazan cutar da lafiyar kowa ba kafin in fara aiki, kuma Alhaji Nasir ya yadda dani, na daɗe ina duba shi lokaci ɗaya kuma se in....
" Kai dakata " Alhaji Musa ya dakawa Sufyan tsawa yace " karka kawo mana maganar banza malam, idan baka yi ba zamu nemi wani, kwata kwata aikin wata uku muke so kayi mana, za mu baka Naira miliyan goma, idan yayi maka kaɗan zamu ƙara maka"
Zare ido Sufyan yayi yace "miliyan Goma"
"ƙwarai kuwa, miliyan goma idan kuma kaƙi zamu saka wani amma ka tabattar da kaima ba zamu ƙyaleka ba"
Cikin hanzari Sufyan yace "zanyi ma, na amince zanyi insha Allah karka damu Alhaji"
Shiru Saleh yayi yana tunani, wato akan kuɗi mutanen yanzu duk alkhairinka sesu manta, idan baze manta ba dangin Sufyan ɗaiɗaiku ne Daula be kai aikin Hajji ba, Amma ya amince ze karɓi kuɗi ya cutar da Alhaji Nasir "
Da Sufyan ze tafi dubu É—ari biyar suka bashi wai ya zuba mai a mota.
Saleh yayi shiru abun duniya duk ya dameshi.
Su Alhaji Musa kuwa cigaba da ƙulle ƙullen sharrinsu suka yi.
Wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, suka tsagaita da dariyar da suke Ya É—aga wayar yace
"Yaya me Adda, ya ake ciki ta faÉ—a maka kuwa?"
"Ina fa ta faɗa se wahalar damu take, ga taurin kai da tsiwar tsiya, sannan ta bada saƙo a baku"
Alhaji Musa a gigice yace "Kamar ya ta bada saƙo abamu ta sanmu ne?"
Me adda yace "ina nasan mata, cewa tayi mu cewa wanda suka sa a sace ta, ta tattaar duk wata hujja akan su, ko bayan an kashe ta asirinku ze tonu"
Wani gumine ya shiga tsatsafowa Alhaji Haruna yace "ƙarya take bata sanmu ba, a gidan uban wa ta sanmu balle ta tattara wata hujja a kanmu, yanzu kana ina ne?"
"ina cikin gari mana, naje Asibiti ne wani yarfi yarinyar nan ta min na kasa ko miƙewa tsaye, na ɗauka ma na tashi daga aiki"
Alhaji Musa yace "wani sakarci ne zesa ku baro su acan, maza ka koma ku gana mata Azaba iya Azaba seta faɗi inda takaddun suke, idan ta faɗi inda suke ku kashe su kawai"
Saleh yace "What akan me za'a kashe ta?"
Alhaji Musa be saurari Saleh ba ya cigaba da wayar sa.
Me Adda yace "gaskiya Oga kisan Yarinya kamar wannan ba kamar kashe sauran mutane bane, tsaf wannan cinnakun zasuyi ram damu"
Alhji Haruna yace "ba wanda ze kama ku, zancen nan da muke maka gaba ɗaya mun siye jami'an tsaro ba wani bincike da'ake akan ɓatan nata, dan haka ka gaggauta zuwa jibi idan bata faɗa ba ka tirsasa ta, ta gaya maka wasu hujjoji take dasu sannan ka kashe mana su"
Me Adda yace "angama Oga"
Alhaji Haruna ya sharce gumi yace "bala'i, Musa anya ba dagaske yarinyar nan ta gano mu ba, karfa muje dagaske take"
"Rabu da ita ƙarya take, da dagaske ta sanmu da tuni ta ɗau mataki akanmu, amma kasan bamu gayawa Munir da Bukar hukuncin da muka yanke ba?"
Alhaji Haruna yace "Suma idan mun gaya musu hukuncin da za susa ayi mata kenan a kashe ta kawai, karta ja mana masifa"
Alhaji Musa ya kalli Saleh yace "wai kai meye naka na saka baki dan munce a kashe ta, kabi a sannu fa wallahi kar kasa musa a haɗa da kai, kabi umarnin mu kawai"
Saleh yayi murmushi yace "Tausayin Daula ne ya kamani wallahi, karka damu bazan baku kunya ba insha Allah dani za'a kammala komai nima in samu rabona"
"daka temaki kanka" cewar Alhaji Haruna, yayin da cikkunansu suka É—uri ruwa.
Yusuf yana nan zaune rungume da Widad, har duhu yayi gari ya waye, sam be bacci ba gani yake da yayi bacci Widad zata mutu, dan bugun zuciyar ta da yake ji shike tabattar masa tana da rai, dan wani lokacin har motsawa take.
A hankali Yusuf ya kwantar da ita, yayi taimama yayi sallar Asuba, shima gaba ɗaya jikinsa a sake yake babu ƙwari saboda azabar wahala, ga yunwa ga duka ga cizon sauro ga azabar sanyi dake gurin, amma gaba ɗaya yafi tausayawa Widad, lokaci lokaci yakan kwance hannun nata, ya goge jinin ya sake ɗaure mata, ga wani irin zazzafan zazzabi da ko sauka bayayi a jikinta.
A hankali Widad ta buÉ—e ido, sedai dishi dishi take gani bata gane komai, tana yi tana lumshe ido haka take kallon Yusuf.
Yusuf ya girgiza ta yace "Alhamdilillah, you are alive"
Bata iya amsa masa ba, sedai idonta ya sake rufewa
Yana rungume da ita, yayi shiru yana ta ambaton Allah, babu zato ba tsammani yaji ana ta sukuwa a saman roofing ɗin ɗakin, Yusuf ya ɗaga kai yana son gane meke faruwa haka? Cigaba da sukuwa akayi a gurin anata ƙoƙarin ɓare kwanon, can kuma se'aka dena, yaji anata ƙoƙarin buɗe ƙofar da suke ciki, waze gani Saleh ne ya shigo cikin ɗakin.
A gigice Yusuf yace "kaine? Da kai aka haɗa baki kenan aka mana haka?"
Saleh yace "baka da lokacin wannan tambayoyin, zuwa nayi na tseratar da ku, ka adana tambayoyinka, idan kun tsira seka yi su"
Hankalinsa ya kai kan hannun Widad dake sume yama zubar da jini, da sauri ya ƙaraso yace "meya sameta haka? Harbinta sukayi?"
Yusuf bece masa komai ba, sedai kallon tuhuma da yake ta binsa dashi.
Saleh yace "zaka iya tafiya kuwa?"
Yusuf ya jinjina masa kai alamar eh, "to taso maza"
Yusuf ya yunƙura ya miƙe, amma ƙafafunsa se rawa suke saboda dukan daya sha, ga uwa uba yunwar da yake ji.
Amma cikin jarumta, da sadaukarwa ya miƙe ya goya Widad a bayansa.
Suka fito daga gidan, Saleh ya maida gidan ya rufe, sannan ya ɓare saman roofing yayi hanya, sannan yayi musu jagora hannunsa ɗauke da compass dake nuna masa direction suka nausa cikin daji.
Yusuf ji yake kamar ze kifa, amma haka ya cigaba da tafiya, Saleh ya kalle shi yace "ko zaka sauketa in ta yaka?"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a karka damu"
Tafiya sukayi bata wasa ba, ƙafar Yusuf ko takalmi babu, ya dinga taka abubuwa danma ta cikin ciyayi suke kutsawa, haka suka dinga tafiyar cikin sauri, suna bi takan ciyayi dan kaucewa barin sawunsu yadda za'a gane hanyar da suka bi, daji ne har daji me sarƙaƙiyar tsiya, da manyan bishiyu.
Sunyi tafiya me nisan gaske sannan suka fito titi, sam Yusuf be san a ina suke bama, Saleh ya nunawa Yusuf mota yace "ya shiga"
Yusuf yayi turus ya kalli Saleh, a wahalce yace "wannan taimakon ma da kayi mana mungode, amma bazan hauba, Insha Allah zamu bar gurin nan".
"Yusuf, wallahi suka kamaku kashe ku zasuyi, da inada niyyar cutar daku da bazan ceceku ba"
Da ƙyar Yusuf ya yadda, ya hau motar, da alama Saleh ya gama shirya komai.
Shima Saleh haka yayi doguwar tafiya dasu a motar, tafiya kamar za'a bar duniya dazuka kawai suke ratsawa, tituna bakowa se su kaÉ—ai, Shiru ne ya wanzu tsakaninsu har suka fara fita gari.
Wani É—an madaidaicin Asibiti suka tarar a hanya, Saleh yayi parking Yasa Yusuf ya É—akko Widad suka shiga Asibitin.
Kuɗi Saleh ya ajiyewa likitan, dan haka ba wani dogon bincike suka karɓi Widad, Amma Yusuf yaƙi zuwa ko'ina, a gabansa aka cirewa Widad bullet, akace se an tafi neman jini za'a ƙara mata.
Yusuf yace a ɗibi nashi, Saleh yace "baze yuwu a ɗebi naka ba, kaima a galabaice kake akwai buƙatar a duba ka"
Yusuf ya dage sedai a gwada jininsa in zeyi a É—iba a sa mata.
Aka duba aka ga Yusuf ze iya bawa Widad jini, saboda rukunin jininsa ake cewa universal donor wato O-, sedai an samu jinin Yusuf da malaria, likitan yaceÂ
"baze yuwu asa mata jinin ba"
Shikuma Yusuf yace be yadda da kowa ba, jininsa za'a saka.
Saleh yace "kaga doctor, koma menene a jinin nasa saka mata, can taƙarke musu dan zamanmu anan akwai hatsari"
Aka bawa Yusuf Abinci, amma ya kasa ci se É—an kaÉ—an saboda hankalinsa na kan Widad, ana É—ibar Jinin Yusuf jiri ya É—ebe shi ya yanke jiki ya faÉ—i, haka aka É—auke shi aka bashi gado.
Akayi treating É—in raunkan jikin Yusuf, aka masa allaurai dan samun relief.
Aka sakawa Widad jinin Yusuf, tare da sauran Allurai, Yusuf na farfaÉ—owa ya fara tambayar ina Widad.
Likitan yace "wai dan Allah meye alaƙarsa da wannan yarinyar haka?"
Saleh yace "ƙanwarsa ce shiyasa ya damu da ita, 'yan fashi ne suka harbeta akan hanyar su ta tafiya, ita kaɗai yake da ita shiyasa"
Yusuf ya koma inda Widad take yasa ta a gaba, ya ƙura mata ido ko ƙyaftawa bayayi, tunda aka cire bullet ɗin nan har yanzu bata farka ba.
A hankali ta buɗe idonta, ta yunƙura zata miƙe Yusuf ya riƙeta yace "bi a hankali fa jikinki babu ƙwari"
Ta kalli Yusuf tace "A ina muke nan?"
"I think we are save now insha Allah, yanzu zamu koma gida" ya bata amsa
Saleh ya shigo ɗakin yace "waye yace maka zaku koma gida ne"?
Widad ta kalli Saleh ta ƙura masa ido, kamar taga baƙuwar halitta.
Yusuf yace "meyasa ba zamu koma gida ba yanzu?"
"saboda idan kuka koma, da kai da ita da mahafinta duk sesun kasheku"
Yusuf yace "meyasa?"
"Zan gaya maka komai, Amma daga nan mafaka zan baku, inda zaku ɓuya ba zasu san inda kuke ba na gama shirya komai daga nan tafiya kawai zamuyi"
Saleh ya miƙowa Yusuf wata babbar jarkar youghurt yace "gashi nan kuci nasan ba wani Abincin kirki a cikinu, sannan ka canza riga ita kuma a sama ta hijjabi"
Yusuf ya karɓi youghurt ɗin ya buɗe ya miƙa mata, amma ta ɗauke kai, Yusuf ya girgiza youghurt ɗin ya ɗaga kai ya sha, sannan ya sake miƙa mata.
Se a lokacin ta karɓa, ta dinga sha saboda azabar yunwar da take ji, sedai tana gama sha ta dinga amai saboda kwanakin da tayi babu Abinci a cikinta.
Saleh yace "Yusuf yakamata mu bar gurin nan da gaggawa in kaiku inda zaku fake, zamanmu anan hatsari ne na gaske"
Yusuf yace "Amma jikinta har yanzu bata da lafiya, ya za'ayi mu tafi a haka?"
Saleh yace "zamu karɓi magungunan da zaku cigaba da Amfani da shi, amma dole mu bar gurin nan"
Haka likitan ya tattara magungunan Yusuf dana Widad ya basu, suka hau mota Saleh ya cigaba da nausawa dasu seda suka sake shafe wata tafiyar, Widad kam magungunan data sha basu saketa ba dan haka duka tafiyar nan bacci take, seda sukazo wata mararraba sannan Saleh yayi parking, wata tsohuwar motace akori kura ('yar ƙurƙura) gaba ɗaya ta sha jiki ta fatattake, hatta fentin jikinta ya koɗe duk ta mole, anyi parking ɗintabakin hanya.
Wani mutum ne ya fito daga a kori kurar, suka gaisa da Saleh, Saleh ya bashi mukullin motar da suka je da ita, suka kwance lambar motar dake jiki da wata.
Saleh Ya kalli Yusuf yace "Yusuf ku fito wannan motar zamu hau mu ƙarasa"
Yusuf yace "nifa Saleh ban gane wannan abubuwan ba, kodai kaima kana da wani ƙudurin ne akanmu"
"Yusuf wallahi ba wani abu da nake shiryawa don in cutar daku, sedai ƙoƙarin ceton rayuwar ku"
Yusuf ya fito hannun sa ɗauke da Widad suka shiga 'yar ƙurƙuran nan, Saleh yaja motar.
(Yau Widad ce a cikin irin wannan motar🙄)
Tashin hankali ba' a samasa rana, duk wannan uwar tafiyar da suka sha Nafila ce akan wadda suke yi yanzu, wata irin ruɓaɓɓiyar hanya suka bi, banda ƙura babu abunda yake tashi wata irin lalatacciyar hanyace, duk kwazazzabai da turɓaya ga uban ramuka, wani ramin in suka shiga da ƙyar suke fita ga ƙurƙuran nan se wani irin ƙugi injinta yake yi, gashi sun matsu a motar, duk yayin da suka shiga rami haka suke bige kafaɗu da ƙarfen motar.
Wannan kwaraf kwaraf É—in ne yasa Widad ta farka, a hankali ta kalli Yusuf tace
"A ina muke?"
Yusuf yace "Sannu ya jikin naki?"
Bata bashi amsa ba ta kuma cewa "A ina muke ne?"
"Mun kuɓuta ne, Saleh ze bamu mafaka"
ÆŠan lumshe ido tayi sannan tace "Na gaji jikina ciwo yake, hannuna zafi kaina ze fashe, Wayyo Allah Daddy na"
Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah komai ze daidaita, zakiji sauƙi mun taho da magunguna"
Shiru tayi ta sake kwantar da jikinta a ƙirjin Yusuf, hawaye na bin gefen idonta.
Tun Yusuf yana sa ran tafiyar ta ƙare har yayi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.
A hankali Yusuf ya fara ganin gidaje tsilla tsilla a gurin, gine gine na tsurar ƙasa haka Gidajen suke, wasuma ko katanga babu a haka suke, yayi mamakin wannan irin ƙasurgumin ƙauye haka da yadda mutane ke rayuwa a cikinsa, suka baro duk bakin hanya suka shigo wannan surƙuƙin guri sukayi ginin Gidaje.
A hankali suna cigaba da tafiya, yaga ƙauyene sosai me ɗauke da gidaje da mutane a ciki, sedai sunyi hannun riga da duk wani abun more rayuwa da jin daɗi, kama daga Makaranta, Asibiti, ko wani abu me kama da borehole tunda suka shiga ƙauyen Yusuf be ganshi ba.
A ƙofar wani babban gidan ƙasa, an shafawa ƙofar gidan farar ƙasa, alama dai mamallakin gidan yana riƙe da wata sarauta ne a ƙauyen.
Saleh yace "Yusuf ina zuwa"
Ya sauka daga motar ya shiga cikin gidan, Yusuf yana ta ƙarewa gurin kallo yana tunanin anya Widad zata iya rayuwa a cikin gurin nan?
A hankali yaji tace "Ka yadda da Saleh, kana da tabbacin shima ba cutar damu zeba?"
"Ko ban yadda dashi ba, Allah baze bashi damae cutar damu ba, nidai fatana inga kinji sauƙi gaba ɗaya"
Ajiyar zuciya tayi, tai shiru ba tace komai ba can Saleh ya fito shida wani dattijon Mutum, kansa É—auke sa rawani.
Suka ƙaraso gaban akori kurar, dattijon yace "sannu dai ɗan samari"
Yusuf yace yawwa Baba, barka da yamma
"Yawwa barka" mutumin ya kalli Saleh yace "sune wannan?"
"Eh sune wanda na gaya maka, ina son su zauna a gidanka na wani lokaci, kafin komai ya lafa su koma"
"Amma kana ganin babu wata matsala Saleh, nifa bana son abunda zezo ya É—agawa Al'ummar garina hankali, kasan ku mutan binni se a hankali"
Saleh yace "Haba dai, wane irin matsala taimako zakayi, baka ga yadda suke a galabaice ba, babu wata matsala insha Allah"
"Shikenan, shigo dasu se a kaisu É—akin daka gyara musun"
Yanzu ma Widad ba zata iya tafiya ba, Yusuf ne ya É—auke ta zuwa cikin gidan.
Duk da rabi tana hayyacin ta rabi bata hayyacin ta, tana mamakin mutane ne ke rayuwa a wannan gidan, roofing gidan kansa na Azarane, ta dinga kallon roofing tana tunanin menene wannan?
Yayin da wasu É—akunan roofing danga ne.
Tunda suka shigo gidan, mutan gidan maza da mata suka fito suka yi cirko cirko kamar zakaru suna binsu Yusuf da kallo kamar sunga baƙin halitta.
Wani ɗakine a can ƙarshen gidan, Saleh yasa mukulli ya buɗe ƙofar katakon dake ɗakin ya shiga yacewa Yusuf "bismillah"
Ba lefi ɗakin yana da girma amma ba sosai ba, yana da taga guda ɗaya wadda akayi ta da katako da kuma langa langa, ɗakin ginin ƙasa ne tsura, sedai anyiwa ƙasan floor, aka shimfiɗa buhu a ƙasa sannan aka kawo tabarma duk aka shimfiɗa.
Akwai matsaikaciyar katifa a shimfiɗe a ƙasa, da bargo guda biyu se fula guda ɗaya duk sababbi.
Gefe ga tulu, da wani ƙaramin kwandon kwanuka da 'yan kwanuka a ciki, gefe ga sababbun bokitai guda biyu, da sabuwar buta.
Akan katifar Yusuf ya kwantar da Widad, da duk inda ya motsa ta ciwo yake mata.
Dattijon yace "wannan bata da lafiya ne haka?"
Saleh yace "Eh bata da lafiya, a hannun masu garkuwa fa na karɓo su, na maka bayanin komai, dan Allah Baba a kula dasu, duk abunda suke buƙata ayi musu"
"Shikenan, indai nine baka da matsala, ko baka kawo kowa ya zauna a gidan nan ba, gidan nan na jama'a ne, Allah ya basu lafiya"
Ya juya ya fita, yana kora yaran da suka yi dandazo a ƙofar ɗakin suna leƙen su Widad.
Idon Yusuf ne ya sauka akan akwatunan Widad data shirya domin tafiyar da zasuyi, da traveling bag É—insa da suka bari a motar da'aka sace su.
Yusuf ya zare ido yace "Nifa Saleh ina buƙatar kamin bayanin abubuwa, ya akayi ka samu jakunkunan mu na tafiya? Ya akayi kasan idan muke kaje ka tseratar damu?"
Saleh yace "Nasan zakayi mamaki, kuma dole ku tambaya, Amma yanzu ina sauri saboda zan koma kano kar su gane wani abu a ƙasa su fara zargina, duk yadda aka shirya sace ku dani akayi shi, Tun bayan sace ku ni kuma na fara shirin yadda zaku tsira, amma ka sani koda wasa karka kuskura kayi gangancin barin ƙauyen nan in bani na fita daku ba, dan wallahi suka ganku sekun kasheku"
Yusuf yace "wai tsaya, wai inane nan ma tukuna?"
"Nan wani ƙauye ne a cikin garin Bauchi, Zan dinga zuwa ina duba ku, a waccan jakar na ajiye muku abubuwan da ba'a rasa ba da zaku buƙata kafin ku saba da irin rayuwar da suke yi, ga kuma kayanku can dana kawo nan, nan gidan ƙanin kakana ne dan haka insha Allah baku da wata matsala, idan ma dawo za kaji komai "
Saleh ya fita tsakar gida ya kalli wata dattijuwa yace "Gwaggo dan Allah Amana nan, a kula da baƙin nan dan manyane duk abunda suke buƙata ayi musu"
Gwaggo tace "Lallai kam, baƙin suna da girma a gurinka, tunda sanadinsu gashi kana leƙo mu"
Wata mata a tsakar gidan tace "Eh aimu da yake cinyesu zamuyi shiyasa ba'a bamu amanar baƙin ba se ita"
Saleh yace "Aifa kedai halinki yana nan bazaki canza ba" yayi gaba abunsa, ya tafi gurin me gari suka sake tattaunawa sannan ya tafi.
Haka Saleh ya tafi ya bar su Yusuf a cikin wannan ƙasurgumin ƙauye.
A hankali Widad tayi juyi, ta ƙarewa ɗakin da take ciki kallo, wai anan zata zauna ita da suka zo sam bata zaci wai nan mutane ne ke rayuwa a cikin gurin ba se yanzu.
Yusuf yaje yayo Alwala, yazo ya tada salla sedai duk inda yayi se mutanen gidan su bishi da kallo.
Widad ta cire hijjabin jikinta, jikinta se faman ƙaiƙayi yake mata, Yusuf ya idar da salla zeyi magana ta riga shi ta hanyar cewa "zanyi wanka"
ÆŠan zare ido yayi yace "to shikenan, bari inwa mutan gidan magana"
Ya fito tsakar gidan, yaga wadda Saleh ya kira da Gwaggo ɗazu tana ta aiki a tsakar gida, yace mata "dan Allah Mama ko zamu samu ruwan ɗumi, mara lafiyar zata yi wanka, nikuma ko na sanyi ne na samu se inyi Amfani da shi"
Tayi murmushi tace "bakomai, na zuba ruwan tuwon dare dama, bari in ɗibar maka"
Yusuf yace "to nagode"
Ya tafi ɗakin su, ya ɗakko sabon bokiti, aka zuba ruwa aka sirka Yusuf ya koma ɗakin yace "An haɗa ruwan"
Ta tashi zaune ta fara kiciniyar cire rigar jikinta, sedai hannunta na hagu shine wanda aka harbeta, na dama kuma yana ciwo saboda duka da wahalar mota.
Yusuf ya juya mata baya da nufin ta kintsa ya kaita banÉ—akin.
"Zoka tayani cire wannan rigar na kasa cirewa....
(Akwa ƙura fa🚶 🚶 🚶 🚶 🚶)
Share, share and share please ðŸ™
Domin, gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
   _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 28_29
Gaba ɗaya dirircewa Yusuf yayi, se yayi kamar beji me tace ba, ganin yaƙi magana yasa itama tai shiru ta nemi guri ta kashingiɗa.
Yusuf ya waigo yace "Kin gama kintsawar ne?"
Kawai ya ganta a zaune.
"Ya haka kuma? Se ruwan ya huce?"
"Ban sani ba, ai kana jina ina magana kayi min shiru, nace kazo ka tayani in cire rigar nan, amma kayi kamar baka jiba"
Ikon Allah bata da lafiyar ma, an tsira da ƙyar bakinta be mutu ba, gashi da ƙyar take maganar.
Yusuf yace "bari inyiwa mutanen gidan magana, se suzo su cire miki"
"Wallahi babu matar da zata taɓani" tai maganar tana kuka
Seda Yusuf yayi shiru, sannan ya tako a hankali kan katifar da take, ya zagaya bayanta hannunsa rawa yake ya zuge zip ɗin doguwar rigar tata ƙasa.
Farar fatarta ta bayyana cikin wata baƙar vest, shiru yayi yana kallonta, ta janyo hijjabi ta mayar ta yunƙura zata miƙe tsaye amma jiri ya kwashe ta.
Yusuf yace "ki dena gaggawa, a halin da kike ciki ɗin nan, idan kika faɗi zaki ji ciwo fa"
Ya duba ya ɗakko soson wankanta dake cikin Akwatinta, sedai babu sabulu haka ya riƙota suka fito, Gwaggo na ganin haka ta taho da sauri da nufin ta taya Yusuf, Amma Widad ta maƙale hannunta, ta manne a jikin Yusuf tabi gwaggo da ido, gwaggo ta tsaya sororo tana kallonsu.
Yusuf yace "Mama karki damu, kiyi haƙuri haka halinta yake bata da yadda ne"
Matar dake gaban murhu ta juyo ta kallesu tace "yau nake ganin ikon Allah, wannan gwandamemiyar matar ce take ƙyuya se kace me shan Nono, taɓ amma lamari ya ɓaci, koda yake wannan kamar ma ba irin tamuce ta nan ƙasar ba"
Widad tabi matar gaban murhun da kallo, haƙoranta yellow shar ga haƙorannata wasu sunyi goyon kura, gata baƙa sosai ga fuskarta duk tsagu, gashi se ƙara baje hanci take.
Gwaggo tace "Haba Hari, ina ruwanki da ita irinku ne ke sawa adinga cewa Hausawa basu da kirki, yanzu da taji abunda kike faÉ—a ba"
Zatonsu duk Widad bata jin hausa, gwaggo ta kalli Yusuf tace "ga banÉ—akin can seka kaita"
Suna zuwa ƙofar banɗakin Widad tayi tiris taƙi gaba taƙi baya.
Yusuf yace "muje mana seki shiga kiyi wankan"
Girgiza masa kai tayi tace "Ni wallahi tsoro nake ji bazan iya shiga ba" sam Widad gurin be mata kama da banɗaki ba, kamar wani gidan horo haka taga gurin.
"meye abun tsoron, zan jiraki anan gurin kiyi ki fito"
Riƙe shi tayi tsam tana girgiza kai tace "Ni na fasa wankan, bazan shiga nan ba"
Gwaggo tace "ɗan nan ya naga bata shiga ba, lafiya kuwa?"
Yusuf yace "wai tsoro take ji ba zata iya shiga ba"
Gwaggo tace "Allah sarki, ƙasashenku babu irin wannan banɗakin ko? Abun duk se haƙuri ai, akwai wani ɗaki da babu komai a ciki ta shiga tayi a ciki kawai"
Yusuf yace "mungode Mama"
"A'a bakomai"
Ta nuna musu ɗakin, duk yadda Yusuf ya tsani roƙo, haka ya karya billensa ya tambayi sabulun wanka, sedai Sabulun da suke wanka da shi irin sabulun nan ne kore na wanki me ƙarnin tsiya, Yusuf ya miƙawa Widad, tasa hannu ta karɓi sabulun ta kalli Yusuf kawai yaga Hawaye a idonta.
Tausayinta ya kama shi, amma ya basar kamar bega hawayen idonta ba, haka ta shiga ɗakin da siminti a ƙasan ɗakin, tayi wankan nan tsigar jikinta na tashi saboda yadda ruwan in ya zuba a ƙasa yake taɓata, ga tashin zuciya saboda ƙarnin sabulun, ba shiri ta ajiye sabulun tayi wankan a haja, sedai taji daɗin ruwan zafin sosai "
Ta fito tana kama bango, Yusuf ya riƙeta ya maida ita ɗaki, ya duba Akwatinta ya ɗakko kaya ya bata, ta saka itama tayi salla.
Saleh beje gida ba se bayan sha biyu na dare, yayi tunanin ko yaje yayi magana da doctor Safwan amma wata zuciyar ta hana shi, saboda yadda Safwan ya dinga rawar jiki da yaji batun kuÉ—i tsaf zeje ya gaya musu, yaje ya sameshi.
Gaba ɗaya tunaninsa ya koma kan yaze ƙwaci Alhaji Nasir a gurin wannan Azzaluman mutanen? Dan ba ƙaramin shiri suke dashi ba.
Me Adda suka koma inda suka ajiye su Widad, da niyyar ayita ta ƙare, suna zuwa suka buɗe gidan, suka shiga suka saka mukulli suka buɗe ɗakin suka ga wayam ba kowa a ciki, a kiɗime ɗayan yace "Me Adda bafa kowa a ɗakin nan"
Ƙarasawa yayi da sauri ya shiga ɗakin shima amma ba kowa a ciki, nan da nan suka gigice suka shiga lalauben su Widad.
Me Adda yace "Mutanen da ko iya takawa basayi, ta yaya zasu gudu? Duk matakan tsaron dake gurin nan ina sukabi suka fita?"
Cam ɗaya daga cikinsu ya ɗaga kai ya kalli Roofing ɗakin yace "me Adda kalli ta nan suka fice" yai maganar yana nuna musu saman roofing ɗakin
Me Adda a gigice yace "ya zama dole mu bazama neman su, amma ta yaya suka samu abu sukayi hanya har suka fita?"
ÆŠaya daga cikinsu yace "Allah ne ya san yadda suka gudu"
Me Adda yace "bamu da lokacin ɓatawa, maza maza mubi sahun su yadda suke a galabaice ba lallai su iya tafiya me nisa ba"
Haka kuwa akayi suka rarraba kansu a cikin daji.
Saleh yaje duba Alhaji Nasir a Asibiti, ya tarar da Anwar a gurinsa, suka gaisa yayi masa ya me jiki, ya É—an dubi Anwar yace
"Amma meyasa baza'a fita da Alhaji waje a nema masa magani ba?"
Anwar yace "Nayi duk me yuwuwa inga an fita da shi, amma Mummy da Alhaji Bulama sunce nan ma ana kula da shi"
Saleh yace "Abunda za'ayi yanzu shi ne, ka É—auke shi ka canza masa Asibiti ba tare da ka sanar dasu ba, ko ba'a fita dashi waje ba a camza masa Asibiti, sedai kawai suga ka canza maaa Asibiti"
Anwar yace "Amma zasuji babu daɗi idan nayi hakan, suna ganin nanma ana ƙoƙari akansa amma inyi haka kamar ban kyauta ba"
"Anwar zamanku a Asibitin nan yaci ace jikinsa yana karɓar treatment yadda yakamata, amma har yanzu babu wani cigaba, mu canza masa wani Asibitin kawai"
Anwar yace "Kana ganin babu matsala idan muka yi hakan?"
"eh babu matsala, Amma karkace ni nace ka canza masa Asibiti"
Anwae yace "shikenan, ka kawo shawara me kyau insha Allah gobe in Allah ya kaimu da Safe, sedai suzo su tarar na canza masa Asibiti ni kaina rashin samun sauƙin nan nasa yana bani mamaki"
Doctor Sufyan ne yake ta zagaye acikin Office É—insa, yana tunanin me yakamata yayi akan batun su Alhaji Haruna, yana tuno irin halacci da kirkin Alhaji Daula, idan aka haÉ—a kai dashi aka cutar dashi to tabbas mesa Adalci ba, Amma wani mataki Alhaji Musa zasu É—auka akansa idan har be abunda sukace ba?.
Fitowa yayi da sauri daga office É—in nasa ya nufi É—akin da Alhaji Nasir yake, yana zuwa shiga suka haÉ—u da Saleh, suka yi kallon kallo babu wanda ya cewa kowa komai suka wuce.
Ya shiga É—akin da Sallama, Anwar ya amsa masa, doctor Sufyan yace "Anwar yame jikin kuwa?"
"Jiki sedai muce Alhamdilillah, amma doctor na fara karaya da yanayin jikin sa, babu wani cigaba fa gashi nayiwa su Mummy magana a fita dashi amma sunƙi amincewa, na rasa dalili"
Sufyan yace "ka kwantar da hankalinka Anwar, treatments ɗin dai da muke masa anan, shi za suyi masa a can, komai ze tafi dai dai ze warke in Allah ya yarda"
Anwar yace "Shikenan Allah yasa"
Haka Widad ta kwanta akan katifar, Yusuf ya ɗau bargo ɗaya ya koma bakin ƙofa ya shimfiɗa ya kwanta, shiru Widad ta kasa bacci, tana tunanin wai itace zata kwana a gurin nan, ga sauro se kururuwa yake mata a kunne, ga zafi ga jikinta da yake ciwo, ga rashin lafiya tana fama.
Æangaren Yusuf ma shiru Yayi yana saÆ™e saÆ™e, yana tunanin wani hali Ummansa take ciki, yasan duk inda take hankalin ta a tashe yake, dan tun tasowarsa be taÉ“a nesa da ita ba, wani É“angare na zuciyar sa yana tunanin Alhaji Nasir yasan tabbas shima yana cikin damuwa, ko wani haki yake ciki Allah masani, ga zamansa da Widad a É—aki É—aya baze yuwu ba, tunda ba muharramarsa bace, gashi ba ta yadda da kowa se shi, ga wasu abubuwan se anyi mata saboda bata da lafiya, dole idan Saleh yazo yayi masa magana asama masa wani É—akin, dan gudun afkawa tarkon sheÉ—an.
Yana nan kwancw sauro yana cizonsa, yana masa hada hada aka, ga cinnaka da yake ta gasa masa cizo a gurin nan, tunani yake Allah yasa kae cinnakan ya ciji Widad.
Katsam ya jiyo sheshsheƙar Widad tana kuka, da yayi kamar ya basar amma ya dinga jin kukan nata a zuciyar sa, tabbas yakamata a tausaya mata.
Ɗakin baƙiƙirin da duhu, ko tafin hannu ba'a iya gani saboda duhu, haka yaja jikinsa cikin lalube yaje gefen katifar ta yace "uwa ɗakina kukan me kike?"
Maimakon tayi magana seta sake fashewa da kuka, Yusuf yace "Am sorry, i feel your pain kiyi haƙuri ki karɓi hakan a matsayin ƙaddarar mu, yakamata ki gode Allah da yasa muka tsira daga hannun mutanen nan, kuma insha Allah zamu koma gida ki dena kuka, kiyi bacci zaki ji daɗin jikin ki"
"I can't sleep, sauro ya dameni zafi nake ji, kuma ina tunanin Daddy na"
Tai maganar tana sake fashewa da kuka.
"kiyi hakuri, Insha Allah Daddy yana nan lafiya, komai ze wuce kamar be faru ba, ki dena kuka kinga baki da lafiya"
Ajiyar zuciya kawai tayi, ta lumshe idinta tana jin yadda zuciyarta ke raÉ—aÉ—i.
Da Asuba yayi Alwala yazo ya tada Salla, bacci take dan sam bata samu bacci ba da daddare, seda ya idar sannan ya tashe ta ya kaita tayi alwala tazo ta tada salla.
Da gari ya fara haske me gari da kansa yayi sallama a ƙofar ɗakin su Yusuf, Yusuf ya fita ya durƙusa ya gaishe shi.
Ya amsa cikin mutuntawa yace "Ya me jikin kuwa?"
Yusuf yace "Jikinta da sauƙi Alhamdilillah"
"Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa ya bata lafiya, karkaji komai ku saki jikinku duk abunda kuke buƙata kuyi magana insha Allah baze gagara ba"
Yusuf yace "Masha Allah, mungode sosai da wannan karamcin naku"
"Karka damu, ai shi É—a na kowa ne"
Wajejen ƙarfe tara na Safe aka aiko yaro ya kawowa Su Yusuf Koko me zafi da ɗumamen tuwo, Yusuf ya karɓa yace sun gode.
Ya kalli Widad dake zaune tayi shiru, gwanin ban tausayi yace "ga Abinci an kawo, ki daure kici se Kisha magani"
Kallon kwanon tuwon tayi, sannan ta kalli kwanon da'aka zubo kokon, har ɗan gara kwanon kokon, amma na tuwon dai se a hankali ga warin daddawar nan ji tayi kamar tayi amai, miyar nan baƙa wuluk ga uban tuwo a ido in ka kalli Tuwon nan kasan ze azabar tauri.
Ta kalli kokon tana tunanin ta ina zata sha abun sha a cikin kwano, ta kalli Yusuf tace "janye min wannan baƙin Abincin kar inyi amai"
Kallonta yayi da mamaki, tuwon ne bata sani ba ko kuma tsabar rainin hankali ne? Ta miƙa hannu ta ɗau kwanon kokon, ta dinga juya kwanon sannan ta kai bakin ta, karɓa ɗaya tayi ta dire kwanon ta yamutsa fuska kamar zata yi kuka.
Yusuf yace "ya dai?"
"Ba daÉ—i" ta bashi amsa
"to ai badan daÉ—i zaki sha ba, kinga nan ba kamar gida bane da zakici abunda kike so, ki daure kisha"
Banza tayi masa taƙi kallonsa, ya ɗau kwanon ya zuƙi kokon, kokon dawane kuma gasarar tayi tsami dan ta ɗan fara wari ma, gashi babu ko ɗigon sugar a ciki.
Yusuf yace "kinga babu wani Abincin da zan baki, idan baki sha ba babu wani Abincin da zaki samu kici, ki daure ki É—auke numfashi kawai kisha"
Da ƙyar ya lallaɓata ta sha kokon nan shima kaɗan ta sha tace ita ta ƙoshi, sannan ya bata magungunanta.
Yusuf yace "Inaga yakamata inyi musu magana, idan da hali a bani ɗakin da zan dinga kwana, kinga be dace mudinga kwana a ɗaki ɗaya nida ke ba, sannan dole kiyi haƙuri su ɗan dinga temaka miki ko gurin wankan ne da canza kaya, nida nake miki be dace ba, tunda ba muharrama tace keba"
Da sauri ta kalle shi tace "NikaÉ—ai zan dinga kwana a É—akin nan? Ni gaskiya bazan iya ba"
"to se a samu a yaran gidan wasu su dinga ta yaki kwana"
Ai tuni ta fara kuka tace "Ni wallahi ba wanda nasani a gurin nan ba zaka tafi ka barni a ɗakin nan ba, kuma wallahi niba zasu dinga taɓani ba, wannan matar me haƙora tsoro take bani, in ba haka ba kawai ka maida ni gida"
Yusuf ya ƙara kwantar da murya yace "Widad mufa musulmi ne, mun san illar zaman mu a guri ɗaya, bekamata yadda nake kula dake ba bayan ga 'yan uwanki mata a gidan nan ba"
"to ni ka maida ni gida mana, kkme ze faru ya faru amma wallahi ba inda zaka tafi ka barni".
"so kike mu koma gida wani abu
ya sameki?
" Idan ba zamu koma gida ba, to bazaka bar É—akin nan ba, in ba haka ba ni zan tafi gidan nikaÉ—ai "
"Amma kin san zamana dake a ɗaki ɗaya ya saɓawa shari'ar musulunci?"
Shiru tayi bata ce komai ba, Yusuf yace "kiyi haƙuri, mutan gidan nan suna da kirki kuma duk mutane ne, babu wanda ze cutar dake, kiyi haƙuri zanje in samu me garin muyi magana"
Riƙo rigar Yusuf tayi ta fashe da kuka tace "Wallahi bazan dinga zama a ɗakin nan nikaɗai ba, sedai duk inda zaka in bika"
Shiru yayi yana Kallonta, kuka take sosai har cikin ranta, tabbas yasan halinta da ƙyanƙyami da rashin yadda, ba zata yadda ta zauna da kowa a ɗaki ɗaya ba in bashi ba, kuma gashi hakan ya haramta.
Jiki a sanyaye yace "shikenan is ok kidena kuka, idan har kina son mu cigaba da zama tare a ɗakin nan inyi jinyarki bisa shari'a mafita ɗaya ce, kuma mafitar nasan me tsaurin gaske ce a gurinki ba lallai ki yadda ba"
Widad ta É—ago idonta tace "Meye mafitar?"
Yusuf yace " Sedai ki amince muyi Aure zuwa lokacin da zaki warke, mu koma gida semu rabu"
Gaban Widad ne ya faÉ—i ta tsaya tana masa wani irin kallo
Duk yadda me Adda yake tunanin lamarin ya wuce tunaninsa, dan babu wata alama ko sheda da zata nuna maka inda su Yusuf sukabi, suka yi sintiri da neman duniya a dajin nan basu sami su Yusuf ba, me Adda yace "gaskiya ina mamakin guduwar mutanen nan, tabbas akwai munafiki a cikinmu, wanda ya kuɓutar dasu banda haka yaza'ayi mutanen da ko tashi basa iyawa ace sun gudu?"
"Oga nima dai nayi wannan tunanin, dan tabbas maganar ka haka take, da saka hannun wani a kuɓutar tasu"
Me Adda yace "Ni yanzu tunanina yadda zanwa wannan mutanen bayanin sun ɓata, dan wallahi babu lallai su ƙyalemu"
"To Oga ko muma sanfewa za muyi muyi ta kanmu"
Me Adda yace "ƙwarai kuwa, Amma zamu fara kiransu mu gaya musu su san meya dace suyi, sannan muma muyi ta kanmu da ba mutunci mutanen nan suka cika ba"
Suleiman shike zuwa ya rarrashi Maman Yusuf, dan ko Abinci bata iya ci, sedai wataran inzeje yayi mata Nasiha ya sai wani abun ya kai mata.
Yauma bayan Azahar da ya taso daga gurin aiki gidan su Yusuf yaje, yatarar da Umman Yusuf akan dadduma taci kuka ta ƙoshi, idanunta duk sunyi jawur.
Suka gaisa Suleiman yace "Umma har yanzu baki dena kukan ba? Ki sani wannan carbin da kike ja kina masa Addu'a yafi wannan kukan da kike yi, dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar wani ciwon ya shige ki"
Umman Yusuf tace "To Suleiman dangana ta zama dole, yau da gawar Yusuf na gani seta fiyemin kwanciyar hankali akan ɓatansa, ban san a ina yake ba, yaci Abinci? Yayi wanka? Me yake ciki? Yana samun Abincin da yake so duk ban sani ba, Allah ne kawai ya barwa kansa sani, dole in shiga damuwa inyi kuka"
Suleiman yace "hakane Umma, amma ki kwantar da hankalinki, muna nan muna bincike akan mu gano inda Yusuf yake, very soon zakiji labari me daɗi, kuma kisawa zuciyarki addu'ar nan da kike tana isa ga Yusuf insha Allah muna sa ran jin labari me daɗi akan Yusuf"
Umman Yusuf tace "Nagode Suleiman, Allah ya saka da alkhairi tunda abun nan ya faru kai kaÉ—ai kake zuwa inda nake ka rarrashenin, Nagode Allah yayi Albarka"
Suleiman yace "Ameen Umma, kin san mahaifin yarinyar ma yana can a gadon Asibiti, sedai fatan Allah ya bayyanasu"
Umma ta amsa da Ameen.
Nurat ta kuma satar jiki, mahaifiyarta bata sani ba ta tafi Asibiti duba jikin Baban Widad, koda taje Anwar kawai ta gani a gurinsa, sedai abun mamaki har yana zaune yana cin Abinci da kansa.
Nurat tace "Alhamdilillah lafiya ta fara samuwa, ya ƙarfin jiki kuwa Daddy?"
Daula yayi murmushi yace "Alhamdilillah, yau gani a zaune ina cin Abinci ma"
Nurat tace "Alhamdilillah"
Ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar ina kwana"
Anwar yace "lafiya ƙalau, ya mutan gidan?"
"duk suna lafiya Alhamdilillah, Amma ina su Anty Ramlah ne?"
Ɗan kame kame Anwar ya fara yace "kin san da yake tunda Daddy ya kwanta itama taƙi lafiya, tana can tana jinya su Amal ke kula da ita"
Nurat tace "Allah sarki, Allah ya sawwake naje in duba ta"
Saleh ne yayi sallama ya shigo, yana ganin Daula a zaune yace "Alhamdilillah Alhajin Allah, kaine a zaune haka kake cin Abinci?"
Daula yayi murmushi yace "Alhamdilillah, tambayi Anwar da kaina na tashi na zauna, sedai bana jin daÉ—in Abincin sam tunanin 'ya' yana nake, ban san a halinda suke ciki ba"
Saleh yace "Insha Allah suna lafiya, kuma da yardar Allah za'a gansu"
Nurat tayi shiru zuciyarta gaba É—aya ta tsinke, tausayin Daddyn Widad ya kamata, ji take tamkar ta gaya masa abunda ke faruwa, Amma idan ta faÉ—a da wani suna za'a kirata, kuma meye hujjarta na cewa da hannun mahaifinta a sace Widad tunda ita kaÉ—ai taji abunda suka faÉ—a, Mahaifinta yana zaune da nasa iyalin cikin kwanciyar hankali, amma ya jefa rayuwar wannan iyalan cikin fargaba da damuwa.
Tana cikin tunanin Daddy yace "Nurat, ki koma gida kinji ko, nagode sosai Allah yayi miki Albarka"
Nurat tace "Ameen Daddy"
Ta miƙe tsaye ta fita, Anwar yabi bayanta suka fita, suna fita harabar ta tsaya ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar wai meyasa baza'a fita da Daddy waje ba, tunda yana da kuɗin nan ba babu ba? Kana kallon da yadda yake numfashi fa"
Anwar yace "Wallahi Nurat, nayi iya yina amma su Mummy sunƙi Amincewa, wai anan ma ana kula dashi, Jiya Saleh ya bani shawarar ko Asibiti in canza masa basu sani ba, sedai kawai suga an canza amma ina tunanin abunda ze biyo ba idan nayi hakan"
Nurat tayi ajiyar zuciya tace "ya batun taron kasuwanci da'ake yi duk ƙarshen shekara da ma'aikata da 'yan kasuwa kuwa?"
Anwar yace "Ana nan za' ayi jibi insha Allah"
Nurat tace "babu wanda ze wakilci Daddyn Widad kenan?"
"Nurat ana ta lafiyarsa wake ta wani taron kasuwanci"
"Amma idan da kara, tunda shike jagorantar taron ayi wani abu akai, tunda yana kwance ba lafiya"
"Ayi wani abu kamar me kenan?"
Nurat tace "A É—aga taron zuwa wani lokacin"
Anwar yace "kina ganin su saura mahalarta taron zasu yarda da haka?"
"Yaya Anwar, ƙaddara bata wuce kan kowa ba, dan haka babu laifi idan munyi wani abu akai"
Anwar ya gyara tsaiwa yace "to gurin wa zamuje ayi mana wannan Alfarmar?"
Nurat tace "karka damu ina da hanya, duk yadda ake ciki zan kiraka amma wannan maganar da gani se kai, karka gayawa kowa"
"insha Allah babu wanda zan gayawa, Allah ya saka da alkhairi da wannan taimako da zakiyi"
"Babu komai yaya, yiwa kaine inda kara ai bekamata ayi taron nan Daddy na kwance ba"
A ranta kuwa cewa tayi "daka san Abunda ake shirya yi a gurin taron nan, da kaima ka nemawa Alhaji Daula mafita '
Saleh ya kalli Alhaji Daula yace
" Yanzu idan nace maka na san inda Widad take zaka yadda? "
Daula yayi murmushi yace " daka san inda Widad take da baka ƙyaleni ina fama haka ba"
Saleh yace "Hakane, jikina yana bani Su Widad sun kuɓuta, sedai kasan su dawo cikin garin nan hatsari ne?"
Daula yayi shiru yace "Tabbas, dan mutanen nan basu da imani, Allah kaÉ—ai yasan halin da suke ciki, ina cikin damuwa sosai Saleh"
Saleh yace "Insha Allah nan ba da daÉ—ewa ba zanzo maka da Labari me daÉ—i a kansu"
"kamar yaya kenan?"
"Kai dai ka kwantar da hankinka Alhajin Allah, kasan retired solder neni, nasan techniques na abubuwa da dama, dan haka ina daf da gano su"
Riƙo hannun Saleh yayi yace "Dan Allah Saleh dagaske kake? Gaba ɗay....
Farinciki yasa Daula kasa cigaba da magana, sema tari daya sarƙeshi.
Saleh yace" ka kwantar da hankalinka, Amma wannan maganar iyani da kaine, ban yadda wani yaji ba, ko Bulama karka sake ka gayawa "
" Insha Allah bazan gayawa kowa ba, Nagode Saleh "
Yusuf ya cigaba da kallon Widad da take masa wani irin kallo, zame hannun ta yayi daga jikin rigarsa yace
" Shikenan tunda baki amince ba, na manta baki da babban maƙiyi kamar Aure, kuma Aure ma kamar Auren maƙasƙancin mutum irin direbanki, bani da wani zaɓi na zama dake inba Aure mukayi ba, kuma niba abunda ze haɗa ni dake har mu gama zamanmu anan mu koma gida, tunda baki amince ba shikenan "
Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya nufi hanyar fita, jiki a sanyaye Widad tace
"Na Amince!"
Share, share and Share please ðŸ™ðŸ™ðŸ™
Domin gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
          _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 30_31
Yusuf ya tsaya cak ya waigo ya kalle ta yace "are you serious kin amince?"
Shiru tayi, taƙi ce masa komai, har yanzu izzar tana nan, abune mawuyaci ta maimaita magana sau biyu, Yusuf yace "Shikenan, idan Saleh yazo zanyi masa magana, kokuma in samu maigari in masa bayanin komai"
Gyara kwanciyarta tayi tace "kuma ranar da zamu koma gida zaka sakeni,gara kasa wannan a ranka"
Yusuf yayi murmushi yace "karki damu, nidai fatana ki samu lafiya komai ya lafa mu koma gida"
Nurat ta koma gida, ta lallaɓa zata silale ta shiga ɓangarenta, "daga ina kike?"
Taji muryar mahaifinta, tsayawa tayi amma takasa cewa komai, cikin tsawa yace "Nace gidan ubanwa kikaje?"
"Amm.. Ammmm. Dama... Damanaje gidansu ƙawata ne shine....
" shine ubanki, yaushe kika fara fita ke kaÉ—ai babu direba? Daga gidan ubanwa kike? Zaki gayamin ko sena kwantar dake na yankaki a gurin nan"
Nurat ta faɗa a Shagwaɓe "Nifa ba inda naje"
"Ubanwa ya kaiki duba Daula a Asibiti ubanki ne?"
A razane ta É—ago ta kalleshi, ta shiga rarraba ido.
"ba magana nake miki ba?"
"Daddy waye ya gaya maka naje duba shi?"
"Ubanki ne ya gayamin" Alhaji Musa ya bata amsa
"Kin san a duniya mutumin nan maƙiyinane, shine kika kwashi jiki kika tafi?"
Nurat tace "Daddy, 'yarsa ƙawatace kuma dukda abunda ke tsakaninku tazo gidan nan birthday na ta bani kyautar mota, yanzu kuma a sace ta mahaifinta a gadon Asibiti in kasa duba shi"
Kafin ta ƙarasa ya ɗauketa da mari, wanda seda ta dena gani na wani ɗan lokaci.
Da sauri Mahaifiyar Nurat ta fito tana cewa "lafiya kuwa? Me tayi maka ne?"
"dole ki tambayi me tayimin mana, munafuka daga ke har ita, wato da saninki ta fita taje Asibiti duba Daula, babban maƙiyina ko?"
Mahaifiyar Nurat tace "haba Alhaji kai waye ya gaya maka can taje"
Alhaji musa yace "Rufemin baki kafin in haɗa dake in muku duka, na wuce duk yadda kuke tunani, duk wani motsinku a waje ina da masu kawomin rahoto, kuma daga yau na saka doka, kada ki kuskura Nuratu ta sake fita daga cikin gidan nan, ban yadda ta sake zuwa ko'ina ba, idan kuwa ta sake sena saɓa muku daga ke har ita"
Maman Nurat taji zafin marin da yayiwa 'yarta, dan ba taga laifin da tayi wanda harta cancanci wannan marin ba.
Taja hannun Nurat zuwa ɗakinta, ta kalleta tace "kema Allah ya ƙara, gobe ma ki sake, gashi nan ya mareki a banza, kin fiye rawar kai Nurat"
Nurat ta share hawayenta tace "Ni ban san wani tantirin munafikin ne ya gaya masa naje ba, Amma idan harna cika 'ya ta halak inason mahaifina ya dace da rahamar Ubangiji, dole in shiga rusa duk wani mummunan ƙudirinsa, ta haka ne kawai zan huce wannan marin da yayi min"
"kinga karki jawa kanki wani tashin hankalin, ki É—akko mana magana kin san halinsa sarai"
"Mummy, wallahi zubawa Mahaifina ido yana abunda yaga dama, alhalin nida ke munsan ba dai dai yake ba bamu kyauta ba, babu ruwanki a ciki nikaÉ—ai zanyi komai.
" Na sani, amma Nurat ina jiye miki matakin daze É—auka akanki, idan ya gane abunda kikeyi "
Nurat tace "ba abunda ze gane, sedai inke zaki gaya masa"
Ta É—au jakarta ta bar É—akin, ta nufi nata É—akin.
Amal ta zama kamar wata me jinya, ta rame sosai dan ko Abinci bata iya ci Sam, sedai abunda ba'a rasa ba, yanzu ma Mummy ce da Ramlah suke cin Abinci suna hirarsu, yayin da Amal juya cokali kawai take, ba ta kai ko loma É—aya bakin ta ba.
Ramlah tace "wai Abincin ne bakyaci, kokuwa? naga se juya spoon kike"
Hajiya Halima tace "na lura da yarinyar nan, kwanakin nan sam bata walwala ta takure kanta da yawa"
Amal tace "Nifa wallahi ɓatan Yusuf ne ke ɗaga min hankali, wallahi na damu sosai beji ba be gani ba am sace shi, Allah kaɗai yasan wahalar da yake sha"
Ramlah tace "Ai kece 'yar wahalar, dama abunda yasa kike wannan damuwar kenan?"
Hajiya Halima tace " waini Yusuf ɗin nan ko tare mukayi Naƙudarki ne muka haifeki ban sani ba? Ubanki ne shi? Ko haifarki yayi idan baki kiyayeni da maganarsa ba sena fasa miki baki, kije ki kashe kanki saboda wani ɗan iska, Allah yasa su haɗa dashi su kashe"
Zare ido Amal tayi tace "Mummy a kasheshi kuma?"
"Eh a kashe shi, munafikin yaro na tsani yaron nan wallahi ba ƙaramin daɗi naji ba da aka sace dashi"
Ramlah tace "wallahi nima naji daɗin hakan, munafuki yaita sunkuyar da kai kamar na Allah, saboda shi ba irin wulaƙancin da wannan makirar ba tayi mana ba, yanzu da suka ƙara gaba se hutawarmu muke"
Amal ta dire cokalin ta miƙe ta bar musu dining ɗin.
Mummy tace "Allah ya kawo lokacin da burinmu ze cika, ita kuma tana wani shirme daban"
Ramlah tace "kedai bari Mummy, nifa harna fara tunanin irin bushshar da zanyi, da yadda zan fantama in kece raini a cikin manyan yara, wayyo Allah daɗi"
Mummy tace "kedai bari yarinya, ai komai yana tafiya daidai"
Suka kwashe da wata uwar dariya, hakan yayi daidai da shigowar Anwar, hakan yasa suka ja baki sukayi tsit.
Ganin yadda sam halin da Daula ke ciki baya gaban mahaifiyarsa da 'yan uwansa yasa ya girgiza kai, tunda Daula ya kwanta a Asibiti bata taɓa kwana a gurinsa ba, se tafi kwana uku ma bata je ba.
Hajiya Halima tace "Allah sarki yaron kirki, Anwar duk ka rame fa, anya baza' a nemi me kula da Alhaji a dinga biyansa ba, ba haƙƙinka bane yin jinyarsa, duk kayi wani iri jinya ba sauƙi fa"
Ya kalli mahaifiyarsa yace "Ciyar damu ɗaukae ɗawainiyar karatunmu da sauran buƙatunmu da yake haƙƙinsa ne? Me yasa lokacin da yakw ɗawainiyar damu baki ce masa ba haƙƙinsa bane, babanmu yayi mana ba tunda yana raye?"
Ya ajiye kayan hannunsa yayi waje zuciyar sa na ƙuna, da irin wannan hali na mahaifiyarsa.
Ramlah taja wani ɗan gajeren tsaki tace " Mummy ya kamata anemo wanda zasu ɓalle ƙofar ɗakin yarinyar nan, mu ɗibi abunda zamu ɗiba, kuma mu shiga ɗakin ubanta mu kwashi abunda muka samu kafin wancan manyan suzo"
Hajiya Halima tace "hakane, amma dole muyi komai a hankali naga Anwar yana neman ya gane halin da'ake ciki nikuma bazan so hakan ba"
Ramlah tace "Ai Mummy ki rabu da Yaya Anwar É—in nan kawai"
Saleh ne a hukumar 'yan Sanda na farin kaya, ya nemi ganawa da Sulaiman, ai kuwa be sha wata wahala ba saboda Kasancewar shima ma'aikacin tsarone.
Ya shiga Office ɗin Suleiman suka gaisa, Saleh ya gabatarwa Suleiman kansa sannan yace "kamar yadda nima jami' in tsaro ne nazo maka da wata mahimmiyar maganane akan jami'inku da'aka sace tare da 'yar gidan Daula"
Suleiman yace "ya akayi kasan jami' inmu ne? Ba kowa yasan Yusuf ɗan sanda bane"
Saleh yace "ba abun mamaki bane dan na san hakan, Amma yanzu ba wannan ne mafi a'ala ba, ka tsaya ka saurareni da kyau, na kuɓuttar da Jami'inku tare da 'yar gidan Daula"
Wani irin kallo Suleiman yayi masa yace "ya akayi kasan inda suke harka kuɓuttar dasu? Kenan dasa hannunka akan sacesun da' akayi"
Saleh yace "ka dena wannan muzuran, ka tsaya in maka bayani dan baka da ikon da zaka kamani ko gayawa duniya abunda ya faru, idan kayi haka kayi abakin ranka"
Nan Saleh ya warwarewa Suleiman komai sedai be faɗa masa ƙauyen daya bawa su Widad mafaka ba, Suleiman yayi matuƙar girgiza da jin labarin da Saleh ya gaya masa, Saleh yace "a yanzu haka babu wani bincike da akeyi akan ɓatansu, saboda sun siye jam'ian tsaro gaba ɗaya kuma suna harin rayuwar Daula duk saboda dukiyarsa, na fuskanci idan nayi wani kyakkyawan yunƙuri a gurin ceton Daula tabbas Asirina ze tonu, kuma zasu kasheni, kaima na gaya maka dan ka sani, ka samu iyayen Yusuf ka musu bayani, dan hankalinsu ya kwanta, sannan ka gargaɗesu akan suyi shiru da bakin su "
Suleiman ya jinjina kai yace ai abunda za'ayi yanzu shine, zan É—aukeka muje gaban mahaifiyar Yusuf kayi mata bayani da bakinka dan ta samu nutsuwa"
Saleh yace  "kana ganin babu matsala?, bafa nason a ganeni"
Suleiman yace "babu wata matsala insha Allah, hankalin mahaifiyarsa ne yaƙi kwanciya, ta damu sosai"
Saleh yace "shikenan muje"
Suleiman yayi musu jagora har gidansu Yusuf, ba ƙaramin farinciki tayi ba da jin an kuɓuttar mata da Yusuf ɗinta, sedai jin an ɓoye shi a ƙauye, ga kuma bata san ranar dawowarsa ba yasa tace "Allah sarki Yusufa na, koze iya rayuwar ƙauye? Be saba ba nace ko zaku kaini in ganshi?"
Saleh yace "A'a hakan bame yuwuwa bane, akwai hatsari a cikin hakan, sedai zanyi recoding É—in muryarki in kai masa, amma baze yuwu in kaiki inda yake ba"
Umma tace "ynzu dai dan Allah dagaske kake ya tsira baya hannun Azzaluman da suka sace shi?"
Saleh yace "tabbas basa nan, ya kuɓuta"
Umma tace "Allah kaine abun godiya, ubangiji Allah ya ƙara tsare su"
Widad kuwa wunin ranar nan ji take kamar ba ita ba, wai ita da bakinta ta Amince da Auren Yusuf, abun da tafi tsana a rayuwar ta yau da bakinta ta amince.
Amma da:ace wannan me korayen haƙoran me kama dana horo tazo ta dinga kwana da ita, ko wannan yaran nasu masu kallon jaraba, gara tayi maleji ta Auri Yusuf ɗin su dinga kwana guri ɗaya, tunda duk abu dai shi ta sani.
Widad sam bata iya cin Abincin da ake kawo musu, saboda gaba É—aya kwanon da'ake kawo Abincin kansa idan ta kalla be mata ba ba zata ci ba, se taji kamar tayi amai, Yusuf yayi ta fama da ita ga larura tana fama, ga rashin cin Abinci.
Haka a daddafe suka kwana uku, kullum tana kan katifa, Yusuf yana bakin ƙofa a ƙasa, idan ta fito tsakar gidan nan to tare da Yusuf ne ze rakata banɗaki, shima bata shiga banɗakinsu, wannan ɗakin da ba kowa a ciki take wankanta, shima idan tayi abunda zata yi tun safe bata sake yadda ko fitsari ta sake yi.
Ko sannu bata taɓa haɗata da mutan gidan ba, shiyasa suke zaton ko bata jin hausa ma, haka suke wuni a ɗaki bata yadda Yusuf ya fita ya barta, tsakaninsa da ita sedai kallon kallo.
Babban abunda yake ƙara bata haushi be wuce yadda data fito, gaba ɗaya sesu koma kallonta ba, sekace sunga wasu halittu daban, ita tarasa meye abunda suke kallo.
Yanzu tana ɗan iyayiwa kanta wasu abubuwan, dukda bata gama warkewa ba, bata cin Abinci sosai, dukda a da ɗinma ba wani ci take ba, Yanzu kam cimar ƙauyen nan ta sha banban da irin wadda ta saba gani, gaba ɗaya kalar Abincinsu yasha banban da wanda ta saba gani ko ta saba ci.
Yusuf yana son yayiwa megari bayani, amma yana tsoron irin kallon daze masa kuma gashi besan me Saleh yace masa ba game dasu
A haka suka kwana uku, ranar kwana na ukun da yamma ba tsammani suka ji salamar Saleh, ba ƙaramin farinciki Yusuf yayi da zuwan Saleh ba, yayo musu siyayya cikin ledoji.
Saleh suka gaisa da Yusuf, yace "Yusuf ya zaman haƙuri ya me jiki kuma?"
Yusuf yace "Alhamdilillah, me jiki tana samun sauƙi"
Saleh yace "fatan dai komai lafiya, kuna lafiya kuda mutan gidan?"
Yusuf yace "Alhamdilillah komai lafiya ƙalau"
Saleh ya kalli Widad yace "Autar Daula ya jikin naki?"
Banza tayi masa ba tace komai ba, Saleh yace "hmm aike in dan halinki ne ko kashe ki za'ayi mutum baze ceceki ba, sedai amiki dan Allah dan karamcin mahaifinki, mace se tsabar girman kai da izzar tsiya, yanzu dai dole ki sauke su ki rungumi ƙaddarar da tayi kutse cikin rayuwar ki ba tare da kin shirya mata ba, ki sani abunda kika gayawa wanda sukayi garkuwa da ku, sun Sanarwa da wanda suka sa a sace ku, dan haka idanma dagaske kin san wanda suka sa a saceku inama baki sani ba kikace kin sani, sun bada umarnin a kasheku, zuwa yanzu basu san kun kuɓuta ba, da zarar sun farga kun gudu zasu saka ɗambar nemanku, dan haka idan kin gadama ki haƙura ki zauna anan na wani ɗan lokaci domin ki tserar da rayuwar ki, in baki ga dama ba kuma kiyi yadda kike so "
Yadda Widad take a kashingiÉ—e ko motsi ba tayi ba, balle Saleh yasa ran jin wani abu daga gareta.
Yusuf ne yace " Ayi dai haƙuri, Insha Allah zata zauna ma, kuma mungode sosai da taimakon da kayi mana Allah ya saka da alkhairi, ya Yallaɓai kuwa? "
Saleh yace "Yana nan ƙalau, dan ina daf da sanar dashi cewar kun tsira, kasan komai nima se nayi lissafi nake yinshi, domin ɓadda sahu, jiya munje gidanku na gana da mahaifiyarka ma"
Da sauri Yusuf ya É—ago ya kalle shi zeyi magana, Amma Saleh ya girgiza masa kai.
Yusuf yace "Amma ya akayi kasan wanda suka sacemu, harka kuɓutar damu?"
Saleh yace "labarin dogone Malam Yusuf, uwa ɗakinka tasa an kama ɗan uwana an tsare shi tsawon shekaru goma, akan zargin dasa hannunsa akan kisan mahaifiyarta, na haɗa kai da maƙiyanta domin in rama abunda tayi min, sedai suma maƙiyan nata kansu kawai suka sani basu da adalci, gefe guda dukda zargin da yake kan ɗan uwana mahaifinta be fasa kyautatamin ba, yana matuƙar girmamani yana kyautatamin ga kuma kai Yusuf da babu ruwan ka, shiyasa na ceceku ba dan halinta ba Wallahi "
"I don't judge based on Assumptions, what happens ten years back is still dancing in my memory, abunda ya faru a wancan lokacin ina jinsa a raina kuma ina ganinsa a idona tamkar a yanzu yake faruwa, da sa hannun Bala akan abunda ya faru, kuma ko ka ceceni ko kar ka ceceni hakan baze taɓa canza ƙaddarata ba, nasan wanda suke bibiyar abun nan tsawon shekaru suna da Alaƙa da wanda suka kashe mahaifiyata, kallona kawai kuke but am beyond your expectations, idan kaje ka ƙara tabattar musu ko bayan raina se sun Wulaƙanta se Asirinsu ya tonu wulaƙanta mafi muni a duniya "
Tuni Hawaye ya wanke fuskarta, yadda take maganar zaka san abun yana taɓa mata zuciya sosai, Yusuf yace
"Amm inaga ku bar wannan maganar, it's hurt her feelings kuma kaga bata da lafiya, dama ina son muyi wata magana da kai ne"
Saleh yace "Ina jinka"
Yusuf yace "kaga zaman da muke da ita a ɗaki ɗaya be halarta ba, tunda ba muharrama ta bace, kuma kasan ba zata yadda matan gidan nan su kula da ita ba, ga yanayi na jinya tana ciki, da nace mu raba ɗaki taƙi yadda, amma munyi shawarar zamuyi Aure, yadda zan iya jinyarta lokacin da Allah ya ƙaddara zamu bar garin nan semu rabu, da naso in yiwa megari bayani, amma ban san yadda kuka yi da shi ba"
Saleh yace "eh to ni namanta kam banyi tunanin raba muku ɗaki ba, taɓ amma wannan zaka aura? Allah ya baka haƙuri da juriya, tashi muje gurin me garin, dama Jibi in Allah ya kaimu Juma'a se'a ɗaura"
Widad dai bata tanka musu ba, suka tashi suka tafi turakar mai gari.
Mai gari na ganinsu tare yace "Masha Allah, Saleh fatan dai ba wata matsala ba suce, mun musu wani laifin bako?"
Saleh yace "Lafiya ƙalau babu wata matsala, munzo da wata 'yar magana ne"
Maigari yace "Masha Allah"
Saleh yace "Ina son in Allah ya kaimu jibi da rai da lafiya, ka ɗaurawa baƙinka Aure"
BuÉ—e baki Maigari yayi yace "dama ba matarsa bace?"
"Eh ba matarsa bace, ƙanwarsa ce hatsarin ya ritsa dasu tare kamar yadda nayi maka bayani, 'yar uwarsa ce amma da Aure a tsakanin su"
Maigari yace "Shikenan babu laifi, amma hakan baze kawo matsala ba idan suka koma gida?"
Saleh yace "kaikam Baffa ba dai tsoro ba,' yan uwane fa kuma ba lallai su koma gida nan kusa, se rigimar da'ake a garinsu ta lafa"
Maigari yace "Shikenan Allah ya kaimu, idan anyi sallar Juma'ar se' a É—aura"
Saleh yace "yawwa Baffa godiya muke, nima ina nan bazan tafi ba se Allah ya kaimu juma'ar idan an É—aura Auren"
Maigari yace "to madalla babu laifi"
Suka fito shida Yusuf, Yusuf yace "nikam me ka cewa Maigari ne a kanmu?"
Saleh yace "kasan mutumin ƙauye, kawai kifeshi nayi, nace masa faɗan ƙabilanci ake a garinku, kun samu kun tsira da ƙyara akan hanyarku ta guduwa kuma akayi garkuwa daku, har yanzu garinku babu lafiya"
Yusuf yayi murmushi yace "Allah sarki, yana da kirki da karamci kam,
Amma nifa bani da sadakin da zan bayar"
Saleh yace "karka damu zan bayar, Allah yasa Auren ka yayi silar shiryuwarta daga wannan baƙin taurin kan da izzar, shegiya me kama da Aljanu"
Yusuf yace "dan Allah kadena zagin ta, bana jin daÉ—i idan ka zageta, É—azuma ka sata kuka"
Saleh ya yamutsa fuska yace "Yusuf ina zaton kana son yarinyar nan ne, in bahaka ba tun a baya su Nura dama sunce baka ganin laifinta, da'an mata abu sekaji haushi"
Yusuf yayi murmushi yace "Saleh, duk ɗan adam tara yake be cika goma ba, duk rashin kirkinta akwai halayenta masu kyau, su kansu su Nuran yanzu zasu gane Amfaninta"
Saleh yace "eh amma rashin kirkinta yafi kirkinta yawa ai"
Yusuf yayi murmushi yace "koma dai yane ni nasan tana da kirki ai, amma dagaske kaje gidanmu? Ya akayi kasan gidanmu?"
Saleh yayi murmushi yace" Yusuf kenan, har gurin aikinka nasani kai jami'in tsarone na farin kaya"
Gaban Yusuf ne ya faÉ—i "ya akayi kasan hakan?"
"saboda ina tare da maƙiyan Daula, binciken da'aka saka ma duk cikin shirinsu ne, ni naje na shirya komai, ba lallai kasan komai yanzu ba, amma anaso ka gama ka tattara bayanai akan binciken se akai sama, su kuma su karɓa su basu, duk cikin ƙoƙarin su na goge duk wata sheda da zesa asan sunawa Daula da 'yarsa zagon ƙasa, sedai basu san cewar kai aka saka kayi binciken ba, sudai kawai zaman jiran sakamakon bincikenka suke, basu san kaike binciken ba shi kanaa me gidanka Suleiman be san hakan ba, sedai akwai wani abokin aikinka da nayi connecting dashi, da zimmar idan ka gama binciken ya dinga bani wasu bayanai daga abunda kake binciken, sedai bazan gaya maka waye ba"
Shiru Yusuf yayi gaba É—aya kansa ya gama kullewa, kenan dama duk wannan wahalar da yake sha shirine, jiki a sanyaye yace "Widas tasan koni waye?"
Saleh yace "Yadda take shiri haka maƙiyanta sukeyi, sannan da ta san kai waye, wallahi da yanzu kana prison saboda bata yafewa wanda yayi mata ƙarya koya yaudare ta, kayi fatan Allah yasa ta fara sonka kafin lokacin da zata san ko waye, wataƙila ta sassauta maka"
Gaba É—aya Yusuf yayi shiru ya rasa abunda yake masa daÉ—i.
Saleh yace "zomu je mu ɗan zazzaga, kaga yanayin yadda ƙauyen yake"
Haka akayi Yusuf yabi Saleh, garin yana da kyau sedai ƙauyen ƙayau ne, babu ababen more rayuwa sam.
Ramlah tasha kwalliya cikin wasu ƙananan kaya, tayi kyau sosai, tana zaune a falo tana kaɗa ƙafa, aka kirata a waya, tana ganin me kiran ta miƙe tsaye, ta ɗau ƙaramin gyalenta ta yafa tace "Mummy yazo bari inje"
Hajiya Halima tace "shikenan sekin dawo"
Amal tace "wallahi Ramlah baki da aji, daga zuwansa harkin miƙe kina rawar ƙafa zaki fita da nice da yanzu kina nan kinamin surutu, wani banza dashi gwalagwaji se shegiyar ƙarya da iyayi"
Ramlah a fusace "Mummy kinga kiyiwa Amal magana ba ruwanta dani"
Mummy tace "Amal kar in ƙara jin bakinki a gurin nan"
Amal ta kwaɓe fuska tace "eh ai tuni na gane, kin fi son Ramlah akaina, damuwar ta ce kawai damuwa ni kuma baki damu dani ba, shikenan"
Ta miƙe fuuuu ta bar falon, Ramlah tayi waje abunta, a harabar gidan taga Fahad sanye da ƙananan kaya da tabarau yana tsaye a jikin motarsa, ta ƙarasa gurinsa tana wani yauƙi, tana ƙarasawa inda yake ya rungume ta, ba kunya ba tsoron Allah suka fara kissing ɗin juna a gaban ma'aikatan dake gurin, Fahad ya zame bakinsa a hankali yace
"you look so cute Baby"
Ramlah tace "Really, you look good too baka ga yadda kayi kyau ba"
Ya riƙo ƙugunta yace "mu tafi ko"
"Ke Ramlah!" muryar Anwar ce cikin fushi yace "meye haka? Baki da hankali ne? Malama wuce ki koma gida"
Fahad yace "kamar ya ta koma gida, meyasa kake hakane Anwar"
A tsawace Anwar yace "zaki koma ko sena ɓaɓallaki a gurin nan, ballagaza kawai"
Da sauri Ramlah ta jiya da gudu cikin gida.
Anwar ya kalli Fahad yace "Fahad kayi Asara wallahi, ita waccan da kake iƙrarin zaka aura baka samu ba, shine ka dawo zaka lallaɓa ka lalata ƙanwata, meyasa baka da imani Fahad, kana da 'yar uwa mace fa, baka tsoron ayimata abunda kake wa' ya'yan wasu, ya zakaji idan wani yayiwa Iman abunda kake yi "
Be rufe baki ba ya jiyo muryar Hajiya Halima tana masifa
" Anwar meye haka, yaushe ka zama haka? Ya zasu fita da yarinya zaka ce ba zata ba, tunda wannan shashashar ta ɓata ai ita ze Aura, me zesa ka kore ta haka akeyi? "
Anwar kamar zeyi kuka yace
" Mummy ke uwace, kamata yayi kisa ido sosai akan Yaran nan, yanzu ya dace Ramlah tabi saurayi da yammacin nan, kalli suturar dake jikinta fa"
"rufemin baki ko in gaggaura maka mari, ke wuce ku tafi"
Anwar yana kallo Ramlah ta shige motar Fahad, yayin da Fahad ke masa wani irin kallo na ya kaga lamarin.
Anwar dama Asibiti zashi gurin Alhaji Nasir, dan haka be sake cewa komai ba ya juya ya tafi.
Nura yace "Bala'i ana shegiya a gidan Nasir Daula, duk iskanci shigar banza da izzar Gimbiyar Daula ban taɓa ganin ta aikata makamancin abunda wannan kwazgwamar tayi a gaban mu ba"
Isa me gadi yace "kaidai bari Nura, ai iskanci guri yake samu, kai da Yarinyar nan tana nan waya isa ya shigo gidan nan ya aikata wannan baÉ—alar, kuma wallahi kayan basu yiwa wannan shegiyar Ramlan kyau ba, wanka ai se Gimbiyar gidan nan, kaga kaya cas a jikinta kamar ita tayi kanta"
Nura yace "kai dai bari Malam Isa, ni se yanzu nake ganin Amfaninta a gidan nan, duk wulaƙancinta idan tana nan se an bamu Abinci sau uku a rana munci mun ƙoshi a gidan nan, amma kalli yanzu sau ɗaya ma ba'a bamu"
Isa yace "kai ba wannan ba, nifa ban gane kan wannan matar ba, kofa Asibiti basa zuwa, Anwar ɗin nan ne kawai yake zuwa yana kula dashi su kuwa ko a jikinsu"
Nufa yace "Hmm kai dai bar kowane munafuki inda ka ganshi, kallon mutan gidan nan kawai nake yi"
A kayan da Saleh ya kawowa su Yusuf, hadda kayan sawa ya kawowa Yusuf, dan Widad Akwatinan ta akawai kayan sawa, ya kawo musu man shafawa da sabulun wanka, dasu Omo, ya siyo musu sabon risho, da fitila sekuma kwalin batir, saboda garin ba Wuta.
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, Ranar Juma'a bayan an idar da sallar juma'a aka ɗaura Auren Yusuf da Widad akan sadaki naira dubu goma sha biyar, shi kansa inda masallacin juma'ar nasu yake se anyi wata uwar tafiya daga nan inda su Yusuf suke kafin aje, ga shi duk ya lalace ya fatattake.
Nurat ce zaune a É—akinta da system akan cinyarta, a hankali ta zare earpiece É—in kunnenta tace "Alhamdilillah, done with this chapter"
Ta É—akko wayarta ta kira Anwar, tayi sa'a ya É—aga, ko gaisawa ba suyi ba tace "Alhamdilillah Yaya Anwar, na turo maka lamabar wani Bature, abokin cinikayyar baban Widad ne sosai, tare dashi za'ayi zaman taron kasuwancin, dan sune kusan wanda suke shirya taron kasuwancin, na san shi lokacin da nayi makaranta a England, muna zuwa gidansa tare da Widad, nayi masa bayani, Amma dukda haka nace zan bashi lambarka kuyi magana "
Jiki a sanyaye, tunda acikin damuwa yake yace " Madalla, Allah yasaka miki da Alkhairi Nurat, abokan kasuwancinsa da yakamata suyi wannan ƙoƙarin babu wanda yayi tunanin yin hakan, kowa harkar gabansa kawai yake, kamar ba wanda ya damu da halin da yake ciki"
Nurat tace "Hakane dama Yaya Anwar, kasan wani ya gayawa mahaifina naje duba Baban Widad, yanzu ya hanani fita kwata2"
Anwar yace "haba dai? Waye ya gaya masa?"
"Nima ban sani ba, amma insha Allah karka damu, zamu cigaba da communicating ta waya, ya jikin nasa kuwa?"
Anwar yace "to Alhamdilillah za'ace, yau dai naga jikin nasa ya tashi, dan se NG tube aka samasa tanan na bashi Abinci yau"
Nurat tace "Allah yasaka maka da alheri Yaya Anwar"
Anwar yace "Nurat kome nayiwa Alhaji Nasir Daula ai kaina nayiwa, karki damu Allah yayi mana jagora"
Ta amsa da Ameen.
Sukayi sallama tace "Alhamdilillah, saura kuma kuɓutar da Yusuf, Allah ka bani ikon kuɓutar dashi" tunani ta shigayi, ta yaya zata san inda su Yusuf suke balle ta kuɓutar dasu?
Yusuf, da Saleh se megari da samarin 'ya' yansa suka shigo gidan, hannunsu É—auke da goro dabino da alawa, uwargidan megari wadda suke cewa gwaggo tace
"Malam ya dai na ganku da kayan É—aurin Aure haka? Bikinwa akeyi?"
Megari yace "baƙin 'ya' yanmu aka ɗaurawa Aure yau, ga naku kayan Ɗaurin Auren nan ayi musu addu'a"
Harira wadda itace matarsa ta tsakiya tace "Taɓɗijan kwaɗo, auda ba matarsa bace suke kwana ɗaki ɗaya? Aikin gama ya gama ai, me kuma za'a ɗaurawa Aure?"
Megari yace "ina ruwanki? Meye naki a ciki? Ke bakinki baya taɓa faɗar alkhairi"
Saleh yace "ke Hari ki iya bakinki akan mutanen nan, bana son rigima fa kin san halina, uwar gulma kawai"
Dama sun saba faÉ—a basa jituwa da Saleh sam
Gwaggo tace "daka gayamana da wuri, aida mun ɗanyi girki mun gayawa maƙwabta"
Saleh yace "gwaggona 'yar Aljanna, karki damu hakanma mungode, Allah yasaka miki da alkhairinsa"
Daga nan Yusuf da Saleh suka wuce ɗakin Widad, tana sanye da hijjabi da alama salla ta idar, tana zaune a gefen katifa suka shigo ɗakin, Yusuf ya ƙaraso gabanta ya ajiye mata goro da alawar ɗaurin Auren, ya miƙa mata sadakinta yace "uwaɗakina ga Sadakinki nan, an ɗaura Auren"
Ta ɗaga kai ta ɗan tsurawa Yusuf ido, sekuma ta sunkuyar da kai tana zubda hawaye, Yusuf yace "me kuma ya faru?"
Girgiza masa kai tayi alamar bakomai, yace "ga sadakinki nan, ki karɓa na kine"
"ka barsu a gurinka ni ba'abunda zanyi dashi"
"Ai haƙƙinki ne, mallakin kine"
"Nikuma nace ka riƙe" tai maganar a ɗan hasale
"Ai hakan baze yuwu bane, amma ki dena kuka kinji, bana son yawan kukan da kike, nidai tunda na sanki kusan kullum cikin kuka kike, dan Allah kiyi hakuri ki sassautawa zuciyarki, wallahi ba ƙaramin damuwa nake shiga ba idan naga kina kukan nan"
Saleh yace "dalla in bazata karɓa ba, ka sai mata ɗan Akuya da kuɗin, idan na tafi ka zauna kayi ta rarrashin nata, kazo muje zanyi magana dakai, ina son in tafi kafin mutanen nan su farga"
Alhaji Musa ne a tsaye, hannunsa É—auke da waya yace "wai kaji abunda naji kuwa, wai an É—aga taron kasuwanci na kamfanunnukan Daula saboda bashi da lafiya"
Wanda yake wayar dashi yace "Naji, ƙarewa ma ni message aka turomin"
Alhaji Musa yace "to wani matsiyacin ne ya shirya hakan? Waye da wannan aikin, ya'akayi ma turawan nan suka san da bashi da lafiya?"
"Nima ban sani ba, nayi iya bincike na ban gane wanda ya gaya musu ba, amma dole muyi wani abu akai, idan wannan damar ta wuce mu, kuma bamu samu abun hannun 'yarsa ba to tabbas zamu tafka gagarumar asara"
Alhaji Musa yace "Shikenan, dole muyi meeting yau ƙarfe biyu na dare, zan sanar dasu Alhaji Haruna"
Ya kashe wayar yana cigaba da masifa, wayar ta sace ta sake fara ringing, a fusace ya É—aga yace "meye waye?"
"Me Adda ne"
"Yawwa me ake cikine me Adda? Ta faÉ—a É—in ko kuwa? Kaga idan bata faÉ—a ba, kusa flier ku dinga cire mata yatsu É—aya bayan É—aya har seta faÉ—a"
Me Adda yace "ka tsaya ka saurareni da kyau, yau kwana biyar kenan sun gudu da inda muka ajiye su, mun zaga ko'ina a dajin nam bamu samesu ba shine ma yanke shawarar in sanar da kai"
"what!!!"
(Mutanen Zamfara masu an yanke mana Network, da masu Anty cool daga farko, dan Allah idan kuna da manhajar Wattpad, idan kukayi searching ɗin littafin AƘIDATA kokuma Ayshercool7724 zaku sameshi tun daga farko har inda na tsaya, kuna bani aiki yaseen 🙄🙄🙄 duba ga yadda ake ta yaɗa cewar what's app ze dena aiki dukda bani da tabbas, ga link ɗin group ɗina na telegram nan meso se yayi joining
https://t.me/joinchat/SYIfEaoQo_JlNDM0 ina godiya da Æ™aunar ku masoya ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜)
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
  _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 32_33
Alhaji Musa yace "Me Adda, ina irin wannan wasan da kaine? Wace irin maganar banza kake faÉ—a haka?"
Me Adda yace "ba maganar banza bace, roofing kwano suka buÉ—e suka gudu"
"Roofing kwanon ne ba kuyi da kyauba kokuwa?"
"wallahi munyi komai yadda yakamata, ni babban abunda ya bani mamaki be wuce yadda ko iya miƙewa tsaye ba sayi saboda wahala, amma suka iya tserewa, ni yanz....
Alhaji Musa ya katse shi ta hanyar cewa " kaga dalla rufemin baki, na yadda da ƙarewarka a wannan fannin shiyasa na baka aikin nan, amma ka kunyatani, shekara nawa kayi kana aikata irin wannan Aikin? Miyagun ayyuka mawa ka aikata kana Nasara, amma se yanzu wannan ɗan ƙaramin aikin ka bari har suka gudu saboda hauka, wallahi tun wuri ka nemo su na gaya maka"
Ya ajiye wayar tare da yin jifa da ita yana dafe kai, jinjina kai yayi yace "Akwai babbar matsala"
Ramlah ce kwance akan gadon Hotel, se bacci take yi kamar matacciya, ta lulluɓe jikinta da blanket, Fahad na gefenta yana ta busa shisha.
Seda yasha me isarsa sannan ya duba agogon hannunsa, ya miƙe zaune dagashi se gajeren wando, yaye blanket ɗin da Ramlah ke ciki yayi ya ɗagota zaune, ko sutura babu a jikinta, busa mata hayaƙi yayi a fuska, a hankali ta motsa ta fara tari, buɗe idanunta tayi wanda sukayi mata matuƙar nauyi ta kalle shi.
Fahad yayi wani murmushi irin na 'yan bariki yace "baccin ya isa haka, yakamata mu koma gida, kafin yaynki ya fara masifa"
Miƙa tayi ta sake kwanciya a jikinsa tace "ƙarfe nawa ne?"
"Ƙarfe takwas na safe" ya bata amsa, ba shiri ta watsakke tare da zaro ido tace
"takwas na safe, na shiga uku Fahad, wacw irin ƙwaya ka bani haka? Me zan cewa Mummy?"
Murmushi yayi yace "matsoraciya kawai, ashe iskancin naki na ƙarya ne, karki damu baby zance mata a gidanmu kika kwana kawai"
Tayi ajiyar zuciya tace "kuma kasan Mummy tana yarda da maganar ka sosai, har naji daɗi wallahi I love you Fahad"
"Love you too baby"
"Fahad tunda Widad ta ɓata zaka Aureni?"
Ya sake rungumeta yace "idan ban Aureki ba wa zan aura? Itama na yadda da Aurenta ne dan in Aureta in Wulaƙanta ta, Allah ya temake ta wannan abu ya faru, amma a duniya in bake ba wace macece ta dace da Fahad?"
Murmushi tayi tama jin daÉ—in kalamansa ma yaudara suna ratsa ta.
Saleh ya kamo hannun Yusuf suka fito waje, Saleh yace
" Samun mutum managarci me Amana kamarka abune me matuƙar wahala Yusuf, ka cika mutum nagari abun a jinjina masa, iyakar sadaukarwa kayi ta, ina fatan wannan Auren anyi shi kenan har gaban Abada, duk macen da ta auri namiji irinka yakamata ta gode Allah, nasan kayi haƙuri a baya dan haka ina fatan ka ƙara haƙuri, Widad yarinya ce me tsiwa da girman kai amma zakaji daɗin zama da ita, saboda tana sa sauƙin kai ga wanda ya gane kanta, dan wani lokacin gane kanta se a hankali, nasan zata baka wahala kafin ta saba da zaman garin nan, amma kayi haƙuri a hankali zata saba, babu wanda ta sani a yanzu daga Allah se kai, ka riƙe Amana Yusuf babu tabbacin ku koma gida Widad ta tarar da mahaifinta a raye! "
Wata irin mummunar faÉ—uwar gaba Yusuf yaji, yace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, me kake Nufi? "
"tunda kuka ɓata Daula yake gadon Asibiti, kullum zancensa 'ya' yana wani hali suke ciki? An ɗaga taron da suke burin ayi suyi amfani da sunan Daula su damfari biliyoyin kuɗi, yanzu idan suka farga kun gudu akwai gagarumar matsala, maganar da nake maka matarsa ba ita take jinyarsa ba, tana can tana shagalinta, babban ɗanta Anwar shike ta sintirin jinyarsa, sannan an bawa likitansa maƙudan kuɗi sunce yayi duk me yuwuwa kar Daula ya warke, Nayi duk ƙoƙarin da zanyi a rabashi da Asibitin amma ba hali, muddin nayi wani babban yunƙuri komai ze lalace "
Yusuf ya dafe kai ya shiga jera salati,
"Rananar da'aka ɗaukeku ni naje na janye Motar da kuke ciki daga titi na maida ita, aka cire lamabr motar, shiyasa na samu wayoyinku da kuma wannan Akwatunan naku, amma bazan baku wayoyin ba, dan nasan tabbas za'a iya tracking ɗin inda kuke, zan kawo maka ƙaramar waya da sim wadda zamu dinga communicating da kai, mahaifiyarka na gaisheka tana ta samaka Albarka "
Yusuf kasa magana yayi se zuciyarsa daketa faman tafasa, suka nufi turakar megari Saleh yace " Baffa zan koma yau, na bawa ila kuɗi da kayan aiki, zezo yayi musu banɗaki, wallahi nan da kwana uku idan beyi ba, yasan halina, na bashi isassun kuɗi wallahi na dawo beyi ba koya cinye kuɗin sena karya shi, kaja masa kunne"
Megari yace
"Subhanallah zeyima Insha Allah, É—akin nan da bakomai shi za'a gyara ba wani abu, ai kaine ka sashi zeyi insha Allah"
Saleh yayiwa Megari sallama, Yusuf ya É—anyiwa Saleh rakiya sannan ya koma.
Gaba É—aya kamar an zarewa Yusuf laka jin maganganun da Saleh ya gaya masa, ji yake tamkar mahaifinsa ne a wannan haÉ—arin, wani irin tausayin Widad ya kama shi.
Ya shiga gidan yana takawa da ƙyar, gwaggo ce tace "Malam Yusufa Allah ya Sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya, yasa anyi kenan kasan lamarin Aure se anyi haƙuri Allah ya baku zaman lafiya"
Yusuf ya ƙaƙaro murmushi yace "Ameen ya Allah nagode sosai"
Gwaggo tace "sedai akwai ɗan bikin Al'ada da mukeyi anan in akayi Aure, yakamata mu gayyaci mutane mu ɗanyi mu tayaku murna"
Yusuf yace "Allah sarki Mama, base kin wahal da kanki ba, kinga ita Amaryar ma bata cikakkiyar lafiya kuma har yanzu a tsorace take, baki ga ko magana bata sonyi ba, Addu'ar ku da kulawar da kuke bamuma mungode sosai"
Gwaggo tace "shikenan Allah ya bata lafiya"
Yusuf yace "Ameen"
Jiki babu ƙwari ya ƙarasa ɗakin nasu, kayan ɗaurin Auren suna nan a inda suke, da kuɗin sadakin nata, tana zaune ta haɗe kai da gwiwa se rusar uban kuka take.
Dole Widad tayi kuka, rayuwar ta cike take da ƙaddara daban daban, a hankali ya ƙaraso bakin katifar ya zauna, sam bataji zuwansa ba seji tayi ya taɓa ta, a ɗan razane ta ɗago ta kalleshi, ganin Yusuf ne yasa ta maida kanta kan gwiwarta ta cigaba da kukanta.
Yusuf yasa hannu ya É—agota yana kallon yadda farar fatarta ta koma ja saboda kuka da wahala.
Girgiza mata kai yayi amma yakasa ce mata komai, dan bema san ta'ina ze fara ba, Widad ta cancanci tayi kuka.
A hankali tasa hannu ta ture nasa hannun ta kwanta, tare da É—ora hannunta akan fuskarta tana ci gaba da kukan, A hankali take furta
"Ya Allah, aslihli sha'ani kullahu, wala takilni ila Nafsi, É—arfatu ainun"
(wuya koda magani ba daɗi, ashe Widad ta iya Addu'a haka 🙄)
Yusuf ya zauna ya zuba mata ido wai a hakama bata san halin da mahaifinta ke cikiba kenan, inaga inta sani.
Yarone yayi Sallama É—akinsu Yusuf, Yusuf ya amsa, yaron yace "Wai gashi inji gwaggo"
Yusuf ya karɓi ƙwaryar da'aka rufeya da faifai, yace "Masha Allah, kace mata mungode"
Yaron yace to ya fita, Yusuf ya ajiye Ƙwaryar yayi shiru yana kallon Widad da jikinta har rawa yake saboda tsabar kuka.
Yusuf yayi shiru, abubuwa suka cinkushe masa kai, nan da nan kansa ya fara sarawa, ya jingina da jikin bango ya rasa abunda yake masa daÉ—i.
A hankali Widad ta buÉ—e idonta, ta kalli inda Yusuf ke zaune yayi shiru, jijiyoyin kansa duk sun tashi, ga idonsa yayi ja kallo É—aya zaka masa kasan a cikin damuwa yake.
Ta miƙe zaune a hankali, yai saurin juyowa yana kallonta, ta goge hawayenta tace
"me'aka kawo? Yunwa nakeji"
Yusuf yace "ban san me'aka kawo ba bari im duba"
Ya ɗakko ƙwaryar ya duba, fura da Nono ne aka dama, tace "bani cokali a can gurin"
Ya duba ya É—akko mata, ya bata. Sosai take jin yunwa ta É—iba ta kai bakinta, ajiye cokalin tayi a gefe ta kafa kai ta dinga sha, tasha ya kai rabi sannan ta ajiye, ta koma gefe ta zauna tana lumshe ido.
Yusuf yace "kin ƙoshi ne?" ta jinjina masa kai ba tare da ta buɗe idonta ba, yasa hannu ya ɗau wadda ta rage ya fara sha, an zuba zuma a cikin furar shiyasa tasha da yawa.
Gaba ɗaya Yusuf tausayi yake bata, beji ba be gani ba ƙaddara ta haɗasj se wahala suke sha tare, duk abunda za'a kawo na Abinci indai zata iya ci, se taci ta rage sannan zeci, kuma seya tabattar ta ƙoshi sannan ko yaya ta rage shima yaci.
Kallonsa take yadda ya duƙa yana shan furar, wadda ba isarsa za tayi ba, ta lura shidai a rayuwarsa be ɗau komai da zafi ba, irin mutanen nan ne da duk yadda rayuwa tazo zasu karɓeta a haka.
Yusuf ji yayi kamar tana kallonsa, ya É—ago kai ba tayi zato ba suka haÉ—a ido, tao saurin É—auke nata idon.
Jiki a sanyaye yace "har yanzu dai kukan baki dena ba? Yakamata ace zuwa yanzu kin sawa zuciyarki haƙuri, kukan nan bashi da amfani, kina ƙaramin damuwa akan wadda nake ciki ne"
"Ni nace ka damu dani ne? Don't try to comfort me when ever am crying, kaji da damuwarka kaima"
Yusuf yace "tun daga lokacin da kika fara kuka saboda damuwa zuwa yanzu, maganin me kuka yayi miki? Kuka baya maganin damuwa wasu lokutan sema dai ya ƙara maka ƙuncin zuciya, ina tare da ke a guri ɗaya ta yaya zan zuba miki ido kiyi ta kuka, kina wahalar da kanki da yawa "
" kowa yaji da kansa malam ka dena damun kanka akaina"
Yusuf yace "Ai bazan iya bane, in dai kina kuka nikuma zuciyata rauni take"
Tsaki tayi tace "Se kai tayi ai"
Yusuf murmushi yayi bece komai ba.
Can tace "yanzu kaga death contract É—in da nake gaya maka muddin zakayi aiki dani ko? Meyasa baka yi tunani akai ba kasa hannu, dukda na gaya maka haka? "
Yusuf yace "saboda shi bawa baya taɓa tsallake ƙaddararsa, Allah ya ƙaddara se haka ta faru"
Shiru tayi ta shiga duniyar tunani, tana cikin tunanin ne bacci ya kwasheta daga nan inda take zaune, ta lanƙwashe wuyanta.
Yusuf ya miƙe yaje da nufin ya gyara mata kwanciya saboda wuyanta, ashe baccin nata ba nisa yayi ba, ta buɗe idonta ta kalle shi, haɗe rai tayi tace "meye haka?"
"yi haƙuri, gani nai kin lanƙwasa wuyanki, kar yayi miki ciwo kuma bana son in tasheki"
"to ina ruwanka inma yayi min ciwon? Dalla cikani kuma karka ƙara taɓani na gaya maka"
(Nikam nace Mamaki 😂 jimin mara kunya, sekace yau aka fara)
Murmushi yayi yace "shikenan Allah ya huci zuciyarki"
Ta kwanta tareda juya masa baya, Yusuf ya ƙura mata ido tare da yin murmushi a ransa yace 'insha Allah sena maye gurbin wannan damuwar taki da farinciki'
Yusuf ji yake kamar bashi ba, wai shine ya Auri Widad, yasan badan ƙaddara ta Ubangiji ba, kamar shi a yadda yake ya Auri mace irin Widad kyakkyawa 'yar me kuɗi haka, sedai wani iko na ubangiji.
Haka nan yake fatan Allah yasa su kasance tare har Abada, Allah yasa idan ta gano waye shi karta guje shi.
Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, Nurat taji motsi a harabar gidansu, ta leƙa ta taga ta hango mahaifinta ya fita shida direbansa, tunani ta shiga yi ina mahaifinta zeje a wannan daren haka? Tashi tayi ta tafi ɗakinsa, ta murɗa ƙofar a hankali ta shiga, ƙarƙashin gadonsa taje ta ɗakko wayarta da ta ajiye ta kunna recording.
Tayi saving ta fito daga ɗakin ta koma nata ɗakin, anan taji wayar da yayi da batun kuɓutar su Widad, da sauri ta miƙe tsaye tana Alhamdilillah, ta dinga kunna recording ɗin tana sake saurara, hankalinta ya koma son sanin me zasu tattauna a meeting ɗin da zasuyi a wannan tsakiyar dare kamar wasu matsafa.
Babban falon Hotel ne suke zaune, sunyi jugum jugum kamar masu jiran tsammani kallo É—aya zaka musu kasan suna cikin damuwa.
Alhaji Haruna yace "jama'a ayi magana, abubuwa da sun taho kamar abun arziki, amma yanzu komai taɓarɓarwa yake, ta yaya za'ace sun gudu se kace a film, ko wata tatsuniya.
Alhaji Munir yace "nima abun ya ɗauremin kai, ga kuma wannan samu da rashi da muka gani, muna shirya abu amma wai an fasa taron, wannan shegun turawan ne suka ce a ɗaga, na rasa wani baƙin munafukin ne ya gaya musu ba, nifa kaina gaba ɗaya ya kulle"
Alhaji Musa yace "babu yadda za'ayi ace su kasa jim rashin lafiyarsa ko kun manta shahararsa ne? Dole zasuji ai"
Wayar hannun Alhaji Musace ta fara ringing, ya fito da ita ya É—aga .
"ban samu halartar zaman da kuke a daren yauba, hakanma duk yana cikin shirina ne, yakamata ku maida hankali gurin gane cewar wani yana muku zagon ƙasa, akwai na jikinku wanda yasan siriinku shine yake ta dagula muku lissafi, ku maida hankali gurin gano waye, sannan kusam duk yadda zakuyi ku kama wanda sukayi garkuwa da 'yar gidan Daula ku kashe su, in bahaka ba akwai gagarumar matsala, sannan ko a mace ko a raye ku tabattar an kama yaran nan an kashesu" yana gama maganar ya kashe wayarsa.
Nan fa suka sake shiga wani ruɗanin, tabbas inba wanda yake cikinsu ba babu ta yadda za' ayi Su Widad su iya tsira daga inda aka ɓoyesu.
Alhaji Haruna yace "to kun daiji abunda Alhaji Bukar yace, yanzu abunda za'ayi shine, kusa a binciko mana wanda aka bawa bincike hukumar jam'ian tsaro, ayi karɓo mana sakamakon binciken, hakan ze ƙara haska mana wani abun"
Alhaji Munir yace "wannan kuma aikin Saleh ne, shi'aka É—orawa wannan ragamar"
Alhaji Musa yace "Na kira shi sam labarsa bata shiga, inaga zan tura É—an aike a kiramin shi da safe"
Haka suka gama tattaunawa suka tashi ba tare da cimma wata ƙwaƙwarar matsaya ba.
Da safe Hajiya Halima nata safa da marwa, layin Ramlah sam baya shiga, ƙarfe goma na safe sega Ramlah ta dawo, Hajiya Halima tace "daga ina kike?"
Kafin tayi magana Fahad ya shigo, Yace 'Mummy barka da safiya, mun miki laifi ko? Wallahi bayan mun dawo daga cinema ne naga kwana biyu ba taje gidanmu ba, kawai muka zarce can, daga nan kuma mumsy tace seta kwana tunda bata zumunci "
Hajiya Halima tace " Aida ta kira ta gayamin, hankalina ya tashi ince kaddai kuma an sace mana ku"
Ramlah tace "haba Mummy wani irin sacewa kuma, ai an san wanda ake sata, ina tare da Fahad waye yavisa ya saceni"
Sukayi dariya gaba É—aya, Fahad ya kashe mata ido, sukayi Sallama ya tafi.
Ramlah na zuwa ɗakinta ta jefar da jakarta ta kife akan gado ta cigaba da bacci, saboda har yanzu ƙwayar da ta sha bata saketa ba, kuma ga rashin sabo dama, dan bata taɓa shan kayan maye ba.
Yusuf bayan ya dawo daga sallar Asuba, har ya kwanta ya tashi, ya duba shimfiɗar Widad yaga bata nan, zumbur ya miƙe zaune a gigice yana waige waige, miƙewa yayi ya fito tsakar gidan bakowa, saboda yanayin garin da sanyi kuma gari be gama waye ba, leƙe leƙe ya shiga yi yana nemanta, can ya hangota daga wani ɗan lungu tana tsaye tana leƙa wata taga se murmushi take, hannunta riƙe da brush da toothpaste, kan nan ko ɗan kwali babu, gashinta ko taza babu ta naɗeshi da ribbon ya kwanta a bayanta.
A hankali ya ƙarasa inda take cike da son sanin me takewa wannan murmushi haka?
Jin mutum tayi a tsaye a bayanta, ta juyo a É—an razane, Yusuf ta gani a tsaye a daf da ita.
"meye haka?"
Yusuf yace "gani nayi kina tsaye kina murmushi, shiyasa nace bari inga abunda ya saki nishaɗi haka? Sannan gari akwai sanyi fa, kalli kanki babu ɗan kwali kar mura ta kamaki, sannan kayan jikinki maza na shiga na fita a gidan nan, kar gari yayi haske suzo su sameki a haka, su kansu matan gidan zasu ga hakan wani iri saboda ya saɓawa Al'adunsu"
"Wai kai meyasa ka fiye shishshigi da takura ne?"
"ba shishshigi da takura bane, kinga yanzu kina da Aure fa"
"kaga wannan Auren fa dashi da babu duk ɗaya, karka ƙara sawa ranka wani Aure mukayi"
Yusuf ya ɗanyi murmushi, cike da basar da zancen yace  "kin tsorata nifa, harna kwanta na duba ban ganki ba, shiru shiru kuma naga baki shigo ɗaki ba"
"hmm kayi zaton zan gudune? In gudu inje ina? Ko kana zaton zan gudu da wannan Auren naka a kaina? Idan kaga na gudu ko na bar ƙauyen nan to tabbas ka sakeni ne"
Yusuf yace "idan kuma ban sake kin bafa?"
Juyowa tayi ta saka idonta a nasa tace "me kace?"
Girgiza mata kai yayi alamar bakomai, ta harareshi tace "ban guri in wuce"
Seda ta tafi ya Leƙa me take kallo, ɗakin zomaye ne, an kunna musu aci balbal an rataye ta, se guje guje suke suna haƙa ƙasa, da wasanninsu shine abunda yasa ta nishaɗi ta tsaya take kallonsu.
Yusuf ya koma ya kwanta bacci ya É—auke shi, ita kuwa Widad data gama brush É—in komawa tayi ta cigaba da kallon zomaye, seda ta gaji sannan ta koma É—aki.
Yusuf yayi juyi ya buɗe idonsa a hankali, ya sauke su akan Widad, ta gyara shimfiɗarta sa kanta, ta sauke Akwatunanta tana ta gyara kayan ciki, ta ware masu datti ta tattare Akwatunan ta canza musu guri, duk Yusuf yana kallonta, Widas sam bata son ƙazanta, tana da matuƙar son tsafta a rayuwarta.
Yusuf ya tashi ya kwashe kayan shimfiÉ—arasa ya ninke, bata kula shi ba sabgoginta kawai take, Yusuf yayi mamakin danganar da Widad tayi, dukda har yanzu bata saba da abubuwa da yawa ba.
"wai babu inda za'a samu inji wanki ne? Ina son a wanke min wannan kayan ne"
Yusuf yace "Ai baki da wani injin wankin daya wuceni, in kin haÉ—a se in É—iba inje in wanko su"
Widad tace "kaine zaka wankemin kayan?"
Yusuf yace "eh mana, ko kinga alamar injin wanki a garin nan, tunda muka zo kin taɓa ganin wuta?"
"to gasu nan na haÉ—a, kaje kace a bani ruwan wanka"
Yusuf ya girgiza kai yace "to"
Ya miƙe ya ɗau bokiti ya fita, Widad ta buɗe Akwatinta ta ɗakko towel ta ɗaura, ta saka hijjabi ta biyo bayansa yadda ana haɗa ruwan se ta shiga tayi wanka.
Mutan gidan sunata hada Hadar yadda za'a haÉ—a karin kumallo, ga dukkan alamu yau mutuniyar Widas ce da girki, wato Harira.
Yusuf ya durƙusa ya gaishesu, cikin jin nauyi kafin yayi magana Gwaggo tace "Yusufa na ganka da bokiti, ruwan wankan za'a zuba mata?"
Yusuf yace "eh Mama"
Tace "kawo in zuba maka anan, ya jikin nata kuwa"
Yusuf yace "jiki Alhamdilillah"
Tace "Madalla, nikam ya sunan nata ne? Bamu san sunanta ba"
Yusuf yayi murmushi yace "Sunanta Widad"
Hari dake gaban murhu ta juyo da sauri taceÂ
"Bala'i, wannan wane irin sunane? Hudas ko wudas sekace kayan citta da masoro wane irin sunane wannan"
Tsakin Widad ne yasa Yusuf juyawa, yadda ta tamke fuskane ya tabattar maaa sa taji abunda Hari tace, Yusuf kamar yayi dariya Amma ya basar kar suyi faÉ—a a gaban mutane.
Gwaggo tace "kaga 'yar halak, ana zancenta se gata, sedai ni wannan sunan nata na Larabawa bazan iya faÉ—a ba, Amarya ya jikin naki?"
Widad a ranta tace "wai Amarya Taɓɗijan"
Yusuf yace "Ana miki ya jiki?"
"Naji sauƙi"
Galala Hari ta bita da kallo tace "Ashe bahaushiya ce, wallahi ganinta nake kamar bata jin hausa, yo aini harna fara tunanin ko kurma ce, ashe tana magana sannu Amarya wudas, ashe kina magana Allah sarki, ya jiki?"
Sake yamutsa fuska Widad tayi, 'ita dai wannan matar bata gajiya da magana, kodai bata san yadda haƙoranta suke bane take buɗesu tana surutu haka, bar wani kore kore ne a jikinsu, ga maganar tsiya da take dashi"
Widad bata kulata ba, aka haÉ—a mata ruwanta, Yusuf ya kaimata inda take wanka.
Aka haÉ—a Yusuf da yaro ya rakashi rafin da matasan garin suke haÉ—uwa suyi wanki.
Amlace ta shiga ɗakin Ramlah, ta dinga bubbuga mata filo, da ƙyar Ramlah ta tashi a fusace tace "Meye haka Amal?"
Amal tace "Anya lafiyar ki kuwa? Ƙarfe biyi fa, amma har yanzu bacci kike, yakamata ki tashi haka ai"
Miƙewa tayi zaune tana miƙa tare da duba agogo, dagaske biyu na rana, haka ta miƙe ta tafi banɗaki tayi wanka sannan ta ɗanji ƙarfin jikinta.
Koda Saleh ya dawo kano, be biya ko'ima ba Asibiti ya fara zuwa duba jikin Alhaji Nasir, amma yanayin jikin nasa se godiyar Allah, Nurses suka gaya masa Anwar yaje masallaci.
Saleh ya zauna a kusa da Alhaji Nasir, wanda idanunsa ke lumshe yake numfashi da temakon Na'urar dakw bashi iskar Oxygen, ya riƙo hannunsa da suka yi sanyi ƙalau, cike da tausayawa ya kai bakinsa daidai kunnensa yace
"Allah ya baka lafiya Yallaɓai, 'ya' yanka sun kuɓuta daga hannun miyagun nan, yanzu haka suna wasu ƙauye na basu mafaka, saboda tseratar da Rayuwarsu, Yusuf yayi ƙoƙari matuƙa ya kula da Amanarka, yana kula da gimbiyarka sosai, Amma munyi maka wani laifi da ban san ya zaka ɗauki abunba, Na wuce gaba Yusuf ya Auri 'yarka, dan kasan bata yadda da kowa seshi, kuma baze yuwu ya cigaba da kula da ita ba, tunda ba muharramarsa bace"
Dukda Alhaji Nasir ba iya magana zeba, da alama yana jin abunda Saleh yake faɗa, ƙara riƙe hannun Saleh yayi gam sannan yayi masa murmushi.
Saleh yace "Amma karka kuskura ka gayawa kowa, kayi shiru da bakinka"
Anwar ne ya shigo bakinsa É—auke da Sallama, yana ganin Saleh yayi murmushi yace "Saleh sannu da zuwa, naje Sallane"
Saleh yace "bakomai Anwar, ya me jiki?"
Shiru Anwar yayi, Æ™walla na taruwa a idonsa yaceÂ
"Saleh na rasa wane irin abokai Allah ya bawa bawan Allah nan, sam hankalinsu baya kansa, amma lokacin da yake da lafiya sune kan gaba gurin nuna masa ƙauna, Amma dubi yanzu, look at how he's suffering alone, ba wanda ya bani mamaki kamar mahaifiyata"
Anwar ya ƙarasa maganar, jijiyoyin kansa na tashi idonsa yayi ja, Alhaji Nasir ne yayiwa Anwar Alamar yaje da hannunsa.
Anwar ya ƙarasa gaban gadon Alhaji Nasir ya zauna.
Alhaji Nasir ya kamo hannun Anwar, sannan ya miƙa hannunsa ɗaya yana shafa kan Anwar tareda yi masa murmushi a hankali yace "Nagode, Nagode"
Kawai Anwar ya rungume Daula ya fashe da kuka, shima Daula hawayene suka fara bin gefen idonsa, da ba ƙaramin mamaki ya shiga ba, ganin yadda gaba ɗaya mutanensa da suke tare dashi suka watse suka barshi, ciki harda matarsa da take morarsa.
Yusuf yaje ya tarar da matasa da magidanta a gurin wankin nan, wasu na wanki wasu na wanka a ruwan, in an koro dabbobi suma suzo su sha ruwan, amma a haka yaga wasu na É—iba na tafiya dashi abun ya bashi mamaki, dama a gurin salla megari ya gabatar dashi, dan haka wasu daga cikinsu sun sanshi.
Duk rashin son mutane irin na Yusuf ya É—an sake dasu, suka dinga hira suma bashi labari akan yanayin garin nasu.
Abun ya dinga bawa Yusuf mamaki, suna rayuwa cike da son juna mutanen ƙauyen, sedai abun mamaki ɗan majaillisar dake wakiltar yankin kakannisa 'yan garinne, amma abun mamaki sukace lokacin da yake campaign har falafalan wuta aka samu su, ya gina musu borehole guda ɗaya can wajen gidan kakaninsa shima se anyi tafiya me nisan gaske borehole ɗin yake, yace idan suka zaɓe shi yaci ze janyo musu wutar lantarki, tundaga wannan campaign da yazo tsawon shekara uku basu sake ganinsa ba, ko gidan kakannin nasa baya zuwa ziyara gaba ɗaya ya koma Abuja.
Haka Yusuf suka cigaba da hira shikuma yana wankinsa, seda ya gama suka bushe ya ninko kayan tsaf, sannan suka taho sa wani maƙocin gidan megari zuwa gida.
Yana zuwa gida ya tarar da Widad a ƙofar ɗakinsu a zaune, zaman dirshen a ƙasa fuskarta tayi jawur saboda kuka, Yusuf ya razana ko ciwonta ne ya tashi.
Gwaggo na ganinsa tace "yawwa Yusufa, wallahi muna tsakar gida muna aiki muka jiyo ihunta, ta fito da gudu mukaje kanta, juyin duniya taƙi magana tayi zamanta a nan gurin, munce ta bar ranar ta shiga ko ɗakina ta zauna taƙi.
Yusuf ya ƙarasa inda take ya ajiye bokitin hannunsa me ɗauke da ninkakkun kayansu yace "lafiya kuwa? Meyasameki haka?"
Cikin harshen turanci tace masa, "wasu ƙwarine suka yi ta cizona, sekuma naga spider manya guda biyu a ɗakin, dana fito nan ma ƙwarin suka cigaba da cizona"
Girgiza kai yayi yace "shikenan tunda na dawo tashi mu shiga É—aki, kalli a yadda kike kin zauna a tsakar gida kowa yana kallonki a haka, kuma kinga kin tayarwa da mutanen gidan hankali"
"wallahi bazan shiga ba se an cire wannan spider ni bana sonshi, bana son ganinsa it's irritating me, looks at my body"
Se yanzu ya lura da yadda kafofin gashinta suka buÉ—e, jikinta yayi wani irin burÉ—in_ burÉ—in, fuskarta ma tayi ja saboda cizon sauro.
Hari tace "Allah dai yasa ba wani abun mukayi mata ba, dan naga alamar makirace, tun ɗazu muke fama taƙi magana, Amma tana ganin mijinta ta fara magana hadda karairaya"
Widad ta ɗaga kai ta ƙurawa Hari ido, yayin da gwaggo taji haushin abunda Harin tayi.
Yusuf kam ba ƙaramin dariya Hari ke bashi ba idan ta kunna Widad, yasan Widad tana mata kawaici ne kafin ta ɗan sake.
Yace "ba wani abun kukayi mata ba, wai wani abune ya cijeta amma, bakomai yanzu zan shiga in duba"
Yusuf ya shiga ya duba bega gizo2 ba, sedai cinnaku dake yawo a É—akin, da alama su suka cijeta.
Yasa tsintsiya ya shashsharesu tsaf, sannan yace ta dawo É—akin.
Yusuf "Yace meye ya cijekin?"
Guri ta zauna ta janye rigar jikinta, ta nuna masa cinyarta, fara tas fiye da fuskarta, sedai tayi ja saboda cizon cinnaka, banda wanda ya gasa mata a hannu.
Yusuf yace "Sannu bari in tambayi gwaggo inda zaitun ta bani ki shafa"
Zumɓura baki tayi tace "ni banyi wanka ba"
Haka ya karɓo ruwa tayi wanka, sannan ta dawo ɗakin, ya bata guri ta sa kaya, ya ɗakko zaitun ta zauna ya shafa mata a na hannun, ya fara shafa mata a ƙafarta ne a hankali, haka kurum taji jikinta wani iri, kawai seji yayi ta doke hannunsa tace
"meye haka?"
"Me kuma nayi miki?"
"ban sani ba" ta bashi amsa tare da miƙewa, ɗan sunkuyar da kai yayi yana murmushi.
Daga Asibitin gurin Alhaji Musa Saleh ya wuce, yaje ya sames hi a office É—insa.
Saleh yace "Ranka ya daɗe kwana biyu bani da lafiya, ko ƙofar ɗaki bana iya fitowa, shiyasa kwana biyu bana zuwa"
Alhaji Haruna yace "Akwai damuwa fa, ko Kasan me Adda ya cemin yarinyar nan sun gudu"
A razane Saleh yace "wace irin maganar banzace wannan? Kamarya sun gudu?"
"Nima dai abunda na gani kenan, gaba É—aya sun mayar mana da aiki baya, yanzu Bukar yace ko a raye ko'a mace anemosu a kashesu kar Asirinmu ya tonu, sannan kaje ka bincika mana wa'aka bawa aikin binciken nan a cikin jam'ian tsaro?"
Saleh yace "Amma fa wani hanzari ba gudu ba, ina kyautata zaton me Adda yana sane ya sake su, wataƙila tace zata bashi kuɗine koma ta ninka masa abunda kuka bashi, shine ya sake su, in bahaka ba ta yaya zasu iya tserewa? Kokuma a cikinku ne wani ya zagaya ya haɗa baki dashi, idan an karɓo abun a gaya masa shikaɗai ba"
Shiru Alhaji Haruna yayi yace "Biri yayi kama da mutum, kuma fa Saleh kayi magana, tabbas dan nasan zata iya, kuma babu Abunda me Adda baze iya akan kuÉ—i ba"
Jinjina mara adadi ga ɗumbin masoya littafin AƘIDATA, niba abunda zance muku se godiya Allah ya bar ƙauna, ga dogon page nan, nima inga dogon sharhi, ga link ɗin telegram nan a ƙasa
https://t.me/joinchat/SYIfEaoQo_JlNDM0
Share, share and share please 🙠🙠ðŸ™
Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680
            _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 34_35
Saleh ya cigaba da ziga Alhaji Haruna, akan lallai yayi bincike, dan zata iya yuwuwa abokan harƙallaesa ne wani yasa a karɓo masa abun hannun Widad, shiyasa me Adda yace masa sun gudu.
Alhaji Haruna yace "Nagode sosai Saleh, Insha Allah zanyi tunani akai"
Saleh yace "bakomai yallaɓai, bari in ɗanje gida in huta, kasan bana jin daɗin jikin nan nawa"
Alhaji Haruna yace "shikenan Allah ya sawwake"
Saleh ya tashi ya tafi
Sakina ce fuskarta É—auke sa damuwa ta shiga ofishin Suleiman, Suleiman yace "Sakina lafiya kuwa?"
Sakina tace "Yallaɓai akwai damuwa, yau sati biyu sa sace Yusuf amma har yanzu babu wani kyakkyawan rahoto, da yake nuna ana bincike akan lamarin nan, anya anyi adalci kuwa duba da yadda Yusuf yake bada gudunmuwa akan harkar tsaro, amma ace shi wannan iftila'in ya faɗa masa amma babu wani yunƙuri da'ake gurin ceto shi, idan ya rasa ransa fa? " ta ƙarasa maganar kamar zata yi kuka.
Suleiman yace "look Sakina, kiyi wani tunani kodan Albarkacin 'yar babban attajirin da' aka sace su tare, yaci ace an maida hankali akan nemansu, amma har yanzu shiru, shikansa Daulan yana gadon Asibiti a kwance, na kai ƙorafi akan abari muma mu gudanar da namu binciken, amma daga sama aka bani umarnin cewar ba'a samu ba, ana gudanar da bincike akan al'amarin, babu wani abu da zamu iya banda muyi musu Addu'a "
Sakina tace " shikenan Yallaɓai, ubangiji Allah ya kuɓutar dasu lafiya, bari in koma kan aikina"
"Shikenan Sakina, Allah ya taimaka"
Sakina na tafiya, telephone ɗin gaban Suleiman ta fara ringing, ya sa hannu ya ɗaga, jin muryar wanda ya kira shin yasa shi miƙewa tsaye cikin girmamawa yana amsa wayar.
"A cikin ma'aikatanka wa'aka saka akan binciken masu bibiyar Alhaji Nasir Daula?"
Suleiman yace "Yallaɓai Yusuf ne, wanda aka ƙarawa matsayi kwanan nan"
"A gaggauta kammala binciken nan, a miƙo bayanan binciken nan headquarter"
Suleiman yace "Ok Sir"
Yusuf ya kalli Widad da tayi kicin kicin da fuska yace "ga kayan nan na wankesu, sun bushe ma gaba É—aya"
Tasa hannu ta ciro kayan daga bokiti, taga kayan a haÉ—e dana Yusuf, kwashe nata tayi ta zube masa nasa a gurin, Yusuf yasa hannu ya kwashe ya zuba a jakarsa.
Ya kalleta yace "kinci Abinci kuwa?"
"ni banci wani Abinci ba, kaga fa abunda aka kawo"
Kwano ta miƙa masa, yasa hannu ya buɗe dafaffiyar masarace a ciki da ɓawonta da komai, Yusuf yace "to me yasa baki ciba?"
"ta ina zanci ? Kawai se in kama cin masara, ni ban taɓa ganin anci masara ba, nidai kawai nasan Abinci akeyi da ita, amma ba'aci"
Yusuf yace "ikon Allah, wannan wace irin hausa ce? Waye ya gaya miki ba'a cin masara"
Ya zauna ya ɓare masarar tsaf, ya ɗaurayeta, yace "nasan kece baki taɓa ciba, amma ana cin masara dafaffiya ko gasashiya, ci kiji"
Ɗauke kai tayi taƙi karɓa, Yusuf kuwa yasa masara a gaba ya fara ci, zuba masa ido tayi tana kallon ikon Allah, yana nufin itama haka zata ɗau masarar ta dinga wannan kokawar haka sekace wata saniya.
Plate ya ɗakko ya shiga ɓanɓarowa yana tara mata a plate yace "gashi na ciro miki ɗauki kici"
Ba kunya tasa hannu ta fara tsinta tana kaiwa bakinta, dan bilhaƙƙi ita bata taɓa ganin ana cin masara a haka ba, amma kuma tabbas da daɗi, ya dinga cirowa yana tara mata tana tsinta tana ci, kamar wata 'yar yaye, cikin ikon Allah a haka kuma ta ƙoshi.
Shiru tayi ta tuna lokacin da sukaje restaurant cin Abinci, Yusuf yake gayamata Naira ɗarin cin Abinci tana gagarar wasu, take ganin kamar ƙarya yake, se gashi yanzu ta gani da idonta, da wanine ya bata labarin ana dafa masara aci a matsayin Abinci zata ce ƙaryane dan bata taɓa gani ba.
Can Yusuf yace "inda ƙwaron ya cijeki ya dena zafin?"
Ta gyaÉ—a masa kai alamar eh, yace "hannun da'aka harbe ki fa?"
"yayi sauƙi, ina iya motsa hannun sosai, sedai idan ma bige ne nake jin zafin"
Yusuf yace "masha Allah, Allah ya ƙara miki ingantacciyar lafiya"
Shiru tayi kamar ba taji ba, Yusuf yace "Addu'ar ma bakya so?"
Shiru tayi masa tana sake ƙarewa roofing ɗin ɗakin kallo, tana son gane dame akayi shi.
Yusuf yace "me kike kallone?"
Widad tace "kai subhanallah, wallahi ka dameni da surutu haba, sekace waccan matar me haƙora"
Yusuf yace "to shikenan na dena gimbiyata"
Ɗagowa tayi ta masa wani irin kallo, ba shiri ya miƙe yayi waje ya bar mata ɗakin yana murmushi.
Wasa2 Ramlah ta ganewa shaye2, bata salla se wajen ƙarfe takwas na safe, da ta idar zata ɗakko Coca-Cola tasha, seta kai ƙarfe biyun rana tana bacci.
Yanzuma Amal ce ta shiga É—akin Ramlah, ta tarar da ita tana girgiza jarkar Coca-Cola.
Amal tace "Ramlah, wai me yake damunki ne haka? Wane irin coc ne kike sha ba yau ba gobe ga shegen bacci kamae kin haɗiyi kasa"
Ramlah ta kalleta tace "kina da matsala da hakanne?"
"ba wai batun ina da matsala da hakan bane, sedai cewa kina ganganci da rayuwar ki, baccin da kike ya wuce ƙa'ida, kuma wannan coc da kike sha yayi yawa sosai, nifa na fara zargin wani abu kike sha a cikin coc ɗin nan"
"Ke Amal! Ki kiyayeni, dalla wuce ki barmin É—aki, ina ruwanki dani idanma wani abun nake sha?"
Amal tace "shawara ce nake baki, amma
" wallahi Amal in baki barmin ɗaki ba sena miki rashin mutunci, Dalla ƙara gaba kije kiji da kanki"
Amal tace "shikenan Kije ki ƙarata" ta fito daga ɗakin.
Yanzu kusan kullum se Ramlah ta fita, ko tare da Fahad ko ita kaɗai, kuma Hajiya Halima bata taɓa yi mata magana akan hakan ba.
Anwar kam ya tattara yasa musu ido, ya maida hankali akan kula da Alhaji Nasir, kwata kwata ya dena shiga sabgarsu ma.
Abubuwa suka fara cakuɗewa su Alhaji Musa, suka kuma hayar wasu 'yan ta' addan domin a nemo musu su Me Adda, yayin da Alhaji Haruna ya keta tunani akan maganar da Saleh ya gaya masa game da tserewar Su Yusuf.
Meeting suke akai akai akan yadda zasu ɓullowa al'amarin,
Alhaji Munir yace "tabbas idan har yaran nan suka kuɓuta suka dawo Asirinmu ze iya tonuwa"
Alhaji Musa yace "yakamata ku kwantar da hankalinku, babu yadda za'ayi Asirinmu ya tonu, yanzu naga Likitan nan yana aikin da muka sashi, dan yanzu baya gane waye akansa sam"
Alhaji Haruna yace "hakane Daula ya zama abun tausayi, talakawan da yake fafutuka akansu, an hana kowa zuwa inda yake, manyan ƙasar nan ma kowa yayi watsi da lamarinsa, yanzu haka nasa Jam'ian tsaro su hana kowa shiga inda yake, se ɗan matar nan tasa, shi kuma wannan soko ne, ba abunda yake ganewa, shekaranjiya wasu baƙin turawa sunzo duba shi, amma an hana su ganinsa ance yana ƙarƙashin kulawar likita baza'a ganshi ba"
Alhaji Musa yace "Good hakanma yayi, a hana kowa zuwa inda yake muyi yadda muke so, Amma Nifa har yanzu ina mamaki akan guduwar yaran nan, kuma da suka kuɓuta aida zasu dawo a gari a gansu, amma har yanzu babu wanda yaji ɗuriyarsu"
Alhaji Munir yace "ni kaina abunda yake ɗauremin kai kenan, zuwa yanzu ai yaci ace anji labarin sun dawo, amma babu wanda yaji hakan"
Alhaji Musa yace "shiyasa nake tunanin akwai wata a ƙasa ruwa baya tsami banza, akwai munafiki a cikin mu"
Alhaji Haruna yace "kamarya? Kana nufin a tsakaninmu munafikin yake kokuwa?"
Alhaji Munir yace "kunga ya isa haka, nima nayi zargin haka amma babu lallai da munafuki a tsakaninmu, sedai a wanda suke mana aiki tabbas, kokuma akwai wani a gefe daya ke farautar abunda muke nema"
Alhj Haruna yace "ba abunda baze iya faruwa ba, Amma kar mu ɗora komai akan zargi semun tabattar"
Kamar yadda Saleh ya bada umarni, aka ginawa Widad nata banɗakin, akwai wata ƙatuwar rijiya a gidan ruwan sam bashi da kyau, haka nan ake amfani dashi a gidan, ko kuma mutum yayi tafiyayyiya yaje rafi ya Ɗebo.
Yusuf kuwa tafiya yake me nisa, yaje ya É—ebo ruwa a wannan borehole guda É—aya tal ta garin, yazo gida ya tafasa idan ya huce seya zuba a randarsu suke amfani da shi a matsayin na sha.
Har yanzu Widad bata saba da kowa a gidan ba, ba ruwanta dasu sedai in sun haɗu a tsakar gida suka mata sannu ta amsa, amma bata shiga sabgar Hari sam, saboda Hari baƙar magana take gaya mata.
Yanzu ma tana tsugune tana brush da yamma, yaran Hari suka kewaye Widad suna kallonta, mussman dogon gashinta dake É—aukar ido, gata ba ma'abociyar saka kallabi ba, abun haushi hadda 'yan matan gidan da suka tasa, se kallonta suke ita ta rasa se yaushe zasu saba da ganinta su dena mata wannan kallon haka?.
Widad tace "kai me kuke kallone, haba bana son kallon nan da kuke min, did i look like a beast?"
Hari tace "yo sunga abunda basu saba gani ba, kin fito tiɓitiɓi da wasu irin kaya ai dole su kalleki ni wallahi da ban zaci ma musulma ce ke kina jin hausa ba"
Widad tace "eh ba musulma bace ni, gunki nake bautawa yana É—aki idan kina so ki ganshi"
Sam hari bata zaci Widad tana da baki hadda baƙar magana ba.
Gwaggo tace "Amarya ƙyaleta kiyi haƙuri"
Sannan ta kalli Hari tace "haba Hari, kin fiye magana wallahi duk haƙurin yarinyar nan kinsa ta fara tanka miki"
Hari tace "yo Yaya yara sunga abunda basu saba gani ba ba dole su kalla ba"
Yusuf yana ta tunanin wace sana'ar ze ɗan fara, saboda ya saukewa mutan gidan ɗawainiyar da'ake dasu, ga Widad bakomai take ciba duk ta rame, ya dawo daga sallar Azahar ya tarar an kawowa Widad gujjiya, tanaci hadda ɓawon, Yusuf yace "mekike ci ne?"
Ta ɗan taɓe baki tace "na manta sunanshi, amma inaga wake ne wannan maman ce ta bani"
Yusuf ya kwashe da dariya, ta haɗe rai tana kallonsa, yace "haba Madam, wannan ne waken? Kuma da ɓawo kike ci bari kiga"
Ya zauna yana ɓarewa yana bata, ita tunda take bata san wata gujjiya ba, da taci a baki se taji kamar wake, ta zata ma wake ne yazo a haka.
Tun Yusuf yana mamakin bata san abubuwa da yawa ba, har ya dena mussman duba da yanayin rayuwarta, ita ba sakewa take da mutane ba, kuma mafi yawa a waje tayi rayuwarta, dan haka yake mata uzuri a wasu abubuwan.
Yusuf yace "Ina son in fara zuwa kasuwar garin nan, inga me zan fara siyarwa saboda mu ragewa mutanen gidan nan É—awainiyar da suke damu"
"dama akwai kasuwa a dajin nan?"
"daji kuma?"
"Eh mana" ta bashi amsa
Yusuf yace "eh akwai kasuwa amma se anyi tafiya me nisa sosai, nayi magana da megari ya haÉ—ani da yaronsa tare zamuje kasuwar gobe in Allah ya kaimu inga yanayin abubuwan"
Tace "Shikenan" tana ci gaba da cin gujjiyarta, seda ta gama ta kalle shi tace "Wanka"
Yusuf yace "to"Â ya haÉ—a mata ruwa sannan ya fita sallar la'asar
A gurin salla Yusuf yaga abun mamaki, akwai ƙaramin gurin da suke jam'in salla, akwai ƙarancin ilimi ga mutan ƙauyen, liman ya makara wani yaja salla a raka'ar ƙarshe liman yazo, raka'ar ƙarshe kawai ya samu, itama an ɗago daga ruku'u, da'aka idar Yusuf yana jira yaga liman ya tashi ya kawo wadda be samu ba amma yaga liman yayi ƙyam yaja gefe yana laziminsa.
Yusuf ya dinga kallonsa ko ze tashi ya canza sallane, amma yaga aka jima liman ya shafa addu'a ya miƙe ya gaisa da mutane ya ƙara gaba.
Yusuf yayi shiru a ransa yace "wannan mutumin dabe san hukuncin salla ba, shine kuma yake jan salla? Tabbas akwai matsala babba, mutanen garin nan suna buƙatar ilimin Addini, ya barwa ransa cewa zeyi wa megari magana, yaga ta inda ze iya basu gudunmuwa.
Ya shiga cikin gida ya shiga ɗakinsu da sallama, Widad ta fito daga wankan tana shafa mai, ba tare da ta kalle shi ba ta amsa ƙasa ƙasa, ta cigaba da abunda take.
Kusa da ita yaje ya zauna yana kallonta, duk cikin salon son yasa ta kula shi, dan idan har bashi yayi mata magana ba in zasu kwana idan ba wani abu take buƙata ba, ba zata kula shi ba.
Tana jin yadda ya zauna daf da ita ya ƙureta da ido, kamar tasan maganar yake so tayi, taƙi magana.
Cike da fargaba dan yasan ze sha masifa, amma ya maze ya kai hannunsa gashin kanta yace
"wannan gashin yaushe rabonsa da a taje shi? Insha Allah idan na fara zuwa kasuwa indai naga comb zan siyo, in taje shi da kaina"
Bige hannunsa tayi tace "wai kai meye haka? Me yasa kake son taɓani ne? Na gaya maka bana son karka ƙara taɓani na gaya maka, in ba haka ba duk abunda nayi maka kai ka siya, haba sekace baka da zuciya, ko baka gane magana"
Shiru yayi kawai yana kallonta yadda take ta masa masifa, shi yaga tana magana ma se yaji daÉ—i a ransa, dan yaga ta rage yawan kukan da take yi.
Ga mamakinta murmushi yayi maimakon taga yaji haushi.
"kawo man in tayaki shafawa" yai maganar yana ɗaukar robar man, ƙwacewa tayi tace
"bana so na gama"
Yusuf yace"Shikenan bari in baki guri kisa kaya"
"inma baka bani gurin ba baze hanani sa kayana ba"
Yayi murmushi ya miƙe cike da jin daɗin yasa ta magana, bayansa tabi kallo yana fita ta ajiye abunda ke hannunta ta shiga goge hawayen da ita kaɗai tasan dalilinsu.
Doctor Sufyan yana Office É—insa, yana jiran lokaci yayi ze shiga tiyata, wayarsa yaji ta fara ringin, ya tsaya ya É—aga tareda yin sallama.
"Sufyan ne?"
"Eh nine"
"ina son ka kasa kunne ka saurareni dakyau, dukda nasan baka san dawa kake magana ba, hakan ya faru ne sakamakon sanin wanda kake maganar dashi a gurinka bashi da amfani, ina son ka saurareni da kyau kaji abunda zan gaya maka, kana jina ko?"
Sufyan yace "ina jinka"
"kamar yadda aka baka kwangilar sake kwantar da Daula, aka baka miliyoyin kuÉ—i akan karya warke, kuma kayi dan tuni wani percentage ya shiga hannunka, to nima aiki nake son kayi min, niba kwantar da Daula nake so kayi ba, kawar da Daula nake son kayi!!!"
Miƙewa doctor Sufyan yayi tsaye ya shiga waige waige karya je wani yaji abunda ake faɗa masa a waya, cikin rawar murya yace "amm.. Ban gane me kake fada ba fa"
"ƙarya ka keyi ka gane, kuma kaji me nace tunda ka iya karɓar kuɗi kake bashi wrong treatment, to zaka iya karɓar kuɗi ka kasheshi, likita ne kai babu me zarginka, tunda kowa yasan condition ɗinsa yayi worse, bazance ga abunda zan bi yaka ba, sedai da kanka nakeso ka yanke abunda zan bi yaka "
Wani wahallalen gumine ya dinga ratsowa Sufyan, gumi yake ji har tsakanin cinyoyinsa, yace " Amma kisan Alhaji Daula hatsari ne, dole se anyi bincike akan gawar sa, don a tabattar da abunda ya kashe shi, idan aka ganoni fa, ina da iyali da ƙananan yara nasan kasheni za'ayi, Daula babban Attajiri ne"
"meye marabar abunda kake masa yanzu da wanda nace kayi masa, sanin kanka ne wrong treatment ɗinma ze iya kasheshi, baka da damar cewa ba zakayi ba, saboda na maka tarko ta ko'ina, ina da duk yadda akayi ka karɓi kuɗi kake bashi wrong treatment, duk wata hujja daza'a kamaka ina dashi, idan kuma naga dama zan saka ɗauke ɗaya daga
'ya' yan naka ko kayi ko kuma ransa ya salwanta, zaɓi ya rage naka, sannan idan kaga dama ka gayawa wani"
Ƙit aka katse kiran, gaba ɗaya doctor Sufyan yaji kamar an zare masa laka, jikinsa se rawa yake ya duba wayarsa yaga anyi hiding ɗin lambar, dan ko unknown number be fito ba, duk sanyin Ac dake office ɗin shi gumi yake, kamar wanda ya tuƙa tuwon gidan biki a tsakae rana.
Yau da wuri Yusuf ya shirya, dan zebi É—an megari kasuwa, É—an megarin shima matashi ne be kai Yusuf ba, a bayan gidan megari nasa gidan yake, da matarsa da 'ya' yansa shida.
Har Yusuf ya gama shirinsa, aka kawo musu Abincin safe Widad bacci take, a hankali ya ƙarasa gaban katifarta ya janye bargon jikinta, bacci take hankalinta kwance, se yarintarta ta sake fitowa ta ƙara kyau a idon Yusuf, yayi shiru yana kallonta.
A hankali ya ɗan daki pillow ɗin da take kai, amma bata motsa ba, ya sake taɓa pillow amma still bata motsa ba, hannu yasa ya ɗan daddaki nata hannun, kamar me tashin ƙaramin yaro, juyi tayi amma taƙi buɗe ido.
"Widad" karo na farko a rayuwarta data ji ya kira sunanta, taji zuciyar ta ta buga da ƙarfi, ta buɗe ido ta kalle shi
Yace "ga breakfast an kawo karya huce, kuma inason zan fita ni"
"shine zaka wani durƙuso kaina haka? Kamar zaka shige cikina"
"ke komai nayi miki lefi ne? To sorry tashi karya huce kinji gimbiyar..
Kallonsa take taji meze ƙarasa, maimakon ya ƙarasa se yayi murmushi yace "tashi kije kiyi brush, muci Abinci "
Ta miƙe ta ɗau brush tayi waje, Yusuf ya gyara mata shimfiɗa, ya gyara ɗakin.
Widad ta fita tsakar gida, gwaggo tace "Amarya ina kwana"
Widad tace "lafiya ƙalau"
Gwaggo tace "Alhamdilillah ya ƙarfin jiki?"
"Naji sauƙi"
Gwaggo tace "to madalla"
Hari ta Æ™urowa Widad ido tana so tayi magana, Widad taceÂ
"idan baki dena kallona ba, sena saka butar hannuna na ɓallo miki wannan haƙorin da yake leƙowa idan kina magana"
Hari tace "ke hudas kike ko wudas, yau dai ban kulaki ba balle ace na shiga harkarki"
Widad ta Harareta ta wuce banÉ—akinta.
Data fito ta manta da batun Yusuf dake jiranta, ta tsaya gurin da take leƙen zomaye.
Seda tayi me isarta, sannan ta koma É—aki.
seda taga Yusuf sannan ta tuna ashe ita yake jira suci Abinci, yace "naga kin daɗe?"
Kai tsaye tace "kallon zomaye nayi" , ta ajiye kayan brush ɗinta, tazo ta zauna ta buɗe kwanon farko, dakakken ƙuli ƙuli ne a ciki, ta rufe ta buɗe ɗayan dafaffen dankalin hausa ne a ciki da ɓawonsa da komai manya guda uku.
Ta kalli Yusuf tace "meye wannan?"
"Dankali" ya bata amsa
"kuma a haka? Ta yaya za'aci"
Yusuf yace "ga mahaɗin nan ƙuliƙuli a wannan kwanon"
Widad tace "ta yaya za'aci wannan abun ba tea?"
Yusuf yace "seki kora da ruwa" yai maganar tare da fara ɓare dankalin.
ta zuba masa ido, ya ɓare tsaf ya yayyanka shi a kwano, ya ɗebo ruwa ya ajiye mata yace "bismillah"
Tsayawa tayi tana kallonsa kamar wata sokuwa, ya ɗakko ɗaya ya dangwala da ƙuli ƙuli ya kai bakinta, ɗauke kanta tayi tasa hannu ta karɓa tasa a bakinta.
Ba zata ce babu daɗi ba, sedai gurin haɗiyewa ne daƙyar take yi, dan kasa haɗiyewa tayi seda ta haɗa da ruwa.
Dan haka shima ba taci dayawa ba tace ita bazata iya cin wannan abun ba, shaƙe mata wuya yake.
Yusuf ne yaci sauran, sannan yayi mata sallama ya tafi.
Sufyan abun duniya ya dameshi, ya rasa inda ze saka ransa, ba ƙaramin hatsari bane kashe shahararren mutum kamar Daula, amma kowa se saka rayuwarsa yake a hatsari saboda suna taƙamar suna da kuɗi, shiba abun ya kaisu gurin 'yan sanda ba, shi ze kwana a ciki.
Gaba ɗaya daren nan yakasa bacci, sedai juyi dafa da Asuba aka kuma sake kiransa, bashi da zaɓin daya wuce ya amsa wayar.
"baka da isasheshen lokacin ɓatawa gurin aiwatar sa wannan aikin, kana da yau zuwa gobe in Allah ya kaimu ne kawai, idan baka yi ba ni zan aikata maka abunda nace"
Aka katse layin, Doctor Sufyan yayi jifa da wayar ya dafe kai, matarsa ta lura da yana cikin damuwa ta tambaye shi ko lafiya, yace mata babu komai.
Widad bata taɓa shiga damuwa ba, tsawon lokacin data ɗauka tana rayuwar kaɗaici a rayuwarta se wannan karon, tunda Yusuf ya fita be dawo ba taji gaba ɗaya duniyar ta mata faɗi, gashi ita bata saba da kowa ba se shi, seta ji ta wani iri kamar ita kaɗaice a duniyar, koba komai ganin motsinsa yana rage mata damuwa.
Yau wuni guda tana É—aki, ba wanda yake shigowa inda take, saboda bata da fuskar daza'ayi mata hakan, bayan tayi sallar la'asar yunwa ta isheta ta fito tsakar gida.
Gwaggo tace "Amarya lafiya dai ko?"
Widad tace "Naga har yanzu Yusuf be dawo ba kuma ni yunwa nakeji"
Gwaggo tace "Allah sarki, yau Harice da girki bata aiko miki da Abinci ba kenan"
Widad tace "kota aiko ba zanci ba, dan ƙazama ce"
Hari dake salla a tsakar gida ko sallamewa ba tayi ba tace "jar'uba kekam anyi mara albarka, nice ƙazamar?"
"Eh kece ƙazama, kalli zanin jikinki kalli faratanki, hijjabin jikinki ma me datti ne, sekiyi abu ki bani inci, an gaya miki komai nake ci?"
Wato Widad sam ta dena ragawa Hari, gwaggo tayi murmushi tace "Yanzu to me zakici?
Widad tayi shiru ba tace komai ba, gwaggo tace "Akwai Furar megari dana dama, bari in ɗebar miki"
Widad tace "Nagode"
Hari tace "Furar malam É—in zaki É—iba ki bata? Lallai Yaya akwaiki da neman gindin zama"
Widad tace "Eh ita za'a ban, ba zanci Abincinki ba"
Gwaggo dai ba tace komai ba, ta É—ebowa Widad fura a kofin silba ta bata, ta samu guri ta zauna tana sha.
Furar tayi zaƙi zau da zumar da'aka zuba a ciki, tana cikin shan furar can seta miƙe tsaye, gwaggo tace "kin ƙoshi ne?"
Widad tace "A'a Yusuf na ragewa"
Hari tace "Ohh ni jikar Hama, ji wata fitsara take cewa ta ragewa mijinta abu"
Wasu matane suka shigo su Uku, É—aya 'yar babba biyu kuma 'yan mata da sallama suka shigo, Hari tace
"Ahh marabanku da dawowa, wai an sha suna"
Ɗayace ta kalli Widad tace "Hari wace wannan?"
Hari tace "wasu baƙine mukayi"
Ɗayar tace "kalleta kamar balarabiya"
Widad bata tanka musu ba ta koma É—akinta.
Sukam bajewa sukayi a tsakar gida, ɗayar itama matar megari ce hansai, se 'yan matan Hindu da Hanne, suma' ya'yansa ne sunje wani ƙauyene, inda 'yar megari take Aure ta haihu.
Se bayan la'asar Yusuf ya dawo gida, kallo É—aya zakayi masa kasan a gajiye yake, ya gaisa da mutanen gidan ya shiga É—akinsu.
Ba sannu da zuwa bakomai Widad tace "Shine kaƙi dawowa se yanzu?"
Yusuf yace yanzun ma tun É—azu na taho, akwai nisane sosai.
Ya ajiye kayan hannunsa, yaje yayi wanka, a É—aki yayi salla saboda gajiya ya nemi guri ya kwanta yayi shiru.
Widad tace "to ni dai gaskiya ka dinga dawowa da wuri, kawai seka tafi ka barni nikaɗai, gaba ɗaya nagaji"
Yusuf ya kalleta yace "Aikin me kikayi kika gaji?"
"Aikin zama ba abunda nake, ba kowa a É—akin nan seni kaÉ—ai"
"Amma ai da mutane a gidan, seki fita kuyi hira"
"Ni gaskiya dana fita wannan me haƙoran take min rashin mutunci, nikuma ramawa nake"
Yusuf yace "Kidinga ƙyaleta, kinga babbace ba sa'arki bace ta girmeki"
"da alama ka manta Widad Nasir Daula ce ko?"
Yusuf yace "ya za'ayi na manta nina isa? Yau ba'a kawo komai bane yunwa nake ji"
Widad ta taɓe baki tace "wannan ƙazamarce tayi girki, ni kuma nace ba zamu ciba, shine Mama ta bani furar mijinta"
Buɗe baki Yusuf yayi yace "ba dai ce mata kikayi ƙazama a gabanta ba?"
"idan na gaya mata zata cinye nine?"
Yusuf ya dafe kai, ita Widad a rayuwar ta bata san kara ko alkunya ba sam.
Ta ɗakko kofin furar nan tace "gashi nasha na rage maka"
Yusuf yace "dagaske ragemin kikayi?"
"is there anything special, dan na rage maka?"
Yusuf yace a"a a ransa kuma yace "lallai kin damu dani"
Yusuf yace "Naje kasuwa, naga abubuwa ana saye da siyarwa ba laifi, ɗan megari ze aran kuɗi, inga me zan fara siyarwa, ranar daba kasuwa kuma naje wani gurin inga me zanyi"
"to duk meye na wannan wahalar?, naga dai barin gurin nan zamuyi"
"A'a yakamata in koma ciyar dake da kaina, da duk buƙatunki be kamata mucigaba da ɗora musu ɗawainiya ba, nauyinki a kaina yake yanzu"
Kallonsa tayi tace "don't bother yourself, wannan fa ba Aure neba"
"meye inba Aure ba?"
Tace "Shiri mana"
Yace "Ba ruwan Allah da shiri, kuma koda shirin ne aini yakamata in kula da Gimbiya ta"
"karka ƙara cemin gimbiyarka"
Yusuf yayi murmushi yace "Lokacin da muna gida gimbiyar Daddy ce, yanzu kuma da muke nan ba wanda kika sani seni, dan haka gimbiyata ce"
Tsaki tayi ta miƙe daga inda take zaune, Yusuf yace "Komai naki me kyau ne Widad"
Ko Kallonsa ba tayi ba tayi masa shiru, yace "ga Alƙawarin da nayi miki, na samo comb da ƙyar a kasuwa, yaushe zamu gyara gashin namu?"
Ficewa tayi daga É—akin ta barshi, shi kuma ya dinga murmushi ganin takaici ya hana ta magana, Yusuf yace da haka da haka gimbiya"
Sufyan fa hankalinsa gaba É—aya ya gama tashi, ya hanga yaga bashi da wata mafita data rage masa banda ya aikata abunda akace, ya haÉ—a allurai a cikin syringe ya zauna ya zuba musu ido, gabansa nata dukan biyar biyar, kiransa akayi a waya, hannun narawa ya É—auka
"Ka shirya aiwatar da aikinne ko kuwa?"
Cikin jan numfashi Sufyan yace "Eh na shirya"
"shikenan, ina jiran sakamako a yau, ka duba wayarka zakaga Alert É—in kuÉ—i"
Sufyan bece komai ba ya ajiye wayar yana yakice gumi.
Zuwa yanzu Widad ta fara dangana, ta É—an fara sabawa da halin data tsinci kanta a ciki, Cikin dare Widad tana bacci tayi juyi, hasken farin wata ya hasake É—akin, ta hangi Yusuf a zaune akan shimfiÉ—arsa yayi tagumi,
Da alama tunani yake.
A ranta tace 'Ashe shima yana damuwa, amma ya dinga basarwa yace nize hanani kuka'
"wai tunanin mekake?"
Firgigit ya dawo hayyacinsa, yace "idonki biyune?"
"A'a mafarki nake na maka magana"
Yusuf yace "hmm ba tunani nake bafa, cinnaka ne ya cijeni na kasa bacci"
"yaushe ka fara ƙarya?"
"dagaske nake" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje, Alwala yaje ya ɗauro yazo ya tada salla, Widad kam baccinta ta koma.
Yusuf yana cikin sallar ne yaji A gigice Widad tace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wayyo Allah Daddyna"
Ta miƙe da gudu tayi hanyar waje
(Up Up masoya littafin AƘIDATA, Comments É—inku na matukar Æ™ayatar dani, shike bani Æ™warin gwiwa nayin posting, Allah ya bar Æ™auna 😠😠ðŸ˜)
Share, share and share please 🙠🙠ðŸ™
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
     _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 36_37
Riƙeta gam Yusuf yayi, yayin da ta cigaba da fizge fizge tana kuka, a hankali Yusuf ya zame ya zauna da ita a jikinsa, ya toshe mata baki, saboda dare ne nan da nan sautinta ze iya cika ko'ina.
Yusuf yace "Widad, ki nutsu mana darene yanzu karkisa hankalin mutane ya dawo kanmu, mafarki kikayi fa"
Girgiza masa kai ta shiga yi, cikin kuka tace "is not just a dream, wani abu na shirin faruwa da Daddyna, ka ƙyaleni inje in ganshi, wani abu ze sameshi"
"yanzu idan kika tafi ina zaki? Daddy Addu'ar mu yake buƙata, tun ɗazu nan salla nake ina mana addu'a muda iyayen mu, Insha Allah babu wanda ze iya cutar dasu, kuma Saleh ya cemin ya gaya masa muna nan tare, kidena kuka"
Girgiza kai take tana kuka tace "Daddy na, shikaɗai ya ragemin bani da kowa, bana son in rasa Daddyna, idan na rasa Daddy babu sauran me ƙaunata sedai dukiyar daze bari, wayyo Allah Daddyna, ya Allah secure my Dad, Allah yasa in koma in tarad da kai a raye"
Gaban Yusuf ne ya faÉ—i, ya tuna abunda Saleh ya gaya masa game da mahaifin Widad.
Kuka take sosai jikinta har rawa yake, ga wani irin gumi daya rufe ta, ɗora hannunsa yayi a saman ƙirjinta, se bugawa zuciyarta take da ƙarfin gaske.
Yusuf ya shiga karanta mata dukkan Addu'ar da tazo bakinsa, a hankali zuciyarta ta rage bugawa da sauri da sauri, can kuma bacci ya É—auketa, ta shiga sauke Ajiyar zuciya.
Yusuf ya miƙe a hankali da ita, ya kaita kan katifarta ya rufe ta da bargo, ya koma ya sake alwala ya cigaba da sallar sa.
Alhaji Musane keta sintiri a cikin É—akinsa, se safa da marwa yake ya kai gwauro ya kai mari, ya rasa abunda yake masa daÉ—i, sosai maganganun Saleh sunyi tasiri a zuciyarsa, sosai zargi ya É—arsu a ransa cewar a cikinsu akwai wanda ya zame yake shirin cin amanarsu, kamar yadda ya zame a baya yaso ya haÉ—a kai shida Alhaji Bukar.
A fili ya furta dole "inyi wani abu akai"
Juyowa yayi yaga Nurat a tsaye a ƙofar ɗakinsa da tray ɗauke da kayan marmari a ciki, a fusace yace "dan uwarki laɓe kika koma Yimin ko?"
Cikin dakewa tace "meyasa zan maka laɓe kuma Daddy, tun ɗazu nake sallama amma baka amsa ba"
"Kuma shine seki tsaya ki laɓe?"
"Daddy bafa laɓewa nayi ba"
"zoki ajiye kayan nan ki fita ki ban guri"
Nurat taje ta ajiye masa tray ɗin ta fita, gaba ɗaya Nurat ta lura mahaifinta a kamar a ruɗe yake, akwai abunda yake damunsa, zata so sanin abunda yake damunsa, dan wataƙila yana da alaƙa da harƙallar da suke ƙullawa akan Alhaji Nasir da iyalansa.
Bayan sallar Asuba yau a masallaci, Yusuf ne ya tsaya ya ɗanyi wa mutanen ƙauyen Nasiha akan neman ilimin Addini, ta hanyar janyo musu ayoyi da hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam, be fito yace musu basu da ilimi ba, amma a cikin bayanin da yake musu ya kawo musu misalin yadda mutum ze kawo raka'oin daya rasa idan yazo bin jam'i, nan suka dinga gano irin tafka tafka da kwaɓar da suke yi.
Wani mutum yace "gaskiya Malam Yusufa munji daɗin wannan bayanin naka, danni harga Allah na ƙaru da abubuwa da dama, danni wallahi na zata idan mutum yayi alwala in yayi tusa indai ba tayi ƙara ba to bata karye ba"
Na kusa dashi yace "Nikuma wallahi na zata ko sujjada ka samu in ana salla shikenan ka samu salla, dan Allah yakamata ka cigaba da yi mana wannan bayanin idan anyi sallar Asuba ko kuma da daddare mudinga taruwa anan kana ƙara fahimtar damu abubuwa"
Megari yace "hakane kam, Yusufa idan bamu takura maka ba, muna buƙatar hakan"
Yusuf yace "Ai babu batun takura ranka ya daÉ—e, mafi alkairin mutane shine wanda yasan ilimi kuma ya sanar dashi"
Seda gari yayi haske tukuna suka watse, suna mamakin kurakuran da suke aikatawa a sha'anin addininsu.
Yana shiga gidan yayi karo da wata budurwa tana koro dabbobi daga turke zasu fita kiwo, tana ganin Yusuf tayi turus tana kallonsa, har Yusuf ze wuce tace masa "Ina kwana"
Yusuf yace "Yawwa lafiya ƙalau sannunki"
Yai gaba abunsa, ƙura masa ido tayi harya wuce ya shige ɗakinsu, anan ta tabattar da cewa shine mijin wannan farar matar me gashi.
Da sauri ta koma É—akinsu, tana kiran "Hindu, Hindu"
Hindu dake sharar ɗaki tace "lafiya kikemin wannan kiran?"
Hanne tace "kinga mijin wannan farar matar nan ta jiya kuwa?"
"me yayi?" hindu ta tambaya
"innalillahi, wallahi ban taɓa ganin namiji me kyau kamarsa ba"
Hindu tace "har LamiÉ—on rigarsu gwaggo?"
Hanne tace "wallahi harshi, taɓ bakiga kyau ba masha Allah, ban taɓa ganin namiji me kyansa ba"
Hindu tace "bakiga matarsa bama, fara me kyau"
Hanne tace "dalla wannan da gani bata da mutunci, kinga kallon da tayi mana jiya kamar taga kashi, da gani bata da mutunci"
Hindu tace "ke Hanne karkice haka, aikinga bata sanmu ba"
Hanne tace "ke dallacan Allah yasa in kuma ganinsa"
Yusuf ya shiga ɗaki ya tarar da Widad a zaune, ya kalleta yace "ina kwana?"
Kallonsa tayi kawai ba tace komai ba, Yusuf yace "Munyi magana da ɗan megari na bashi kuɗi, zeje cikin gari ze siyo miki kayan tea da sauran abun buƙata"
Ita dai ba tace komai ba, sema lumshe idanunta da tayi.
"wai meke damunki ne kuma?"
"Bakomai"
"zakiyi wanka ne? Ina son zan fita"
Tace "kaje kawai, zanyi komai da kaina"
Yusuf yace "Aini tsoron fitarma nakeji, jiya da daddare ki tsoratani sosai, kar in fitane kema kice zaki tafi"
Shiru tayi masa ta ƙara rufe idonta, "Widad" ya kira sunanta, a ɗan hasale tace "meye ne?"
"Inaga bari in haƙura da fitar nan, bari inje inyiwa abokin tafiyar tawa magana se in dawo"
"Nifa ban hanaka tafiya ba, ba inda zani jiyanma na tsorata ne mafarkin da nayi"
Yusuf yace "dagaske idan na fita bazaki tafi ki barni ba"?
ÆŠagowa tayi tana kallon cikin Æ™wayar idonsa, ta jinjina masa kai alamar eh, yayi murmushi yaceÂ
"to bari inje in wanke mana kwanuka, in wanke miki banÉ—aki se in tafi, sena dawo, in a kawo abun karyawa kiyi breakfast É—inki kawai, base kin ragemin ba"
Yai maganar tare da miƙewa ya fice, ya kwashi kwanukan ya zuba ruwa, Hanne ce ta hango Yusuf da kwanuka, ta taho da sauri tace
"kawo in wanke maka"
Yusuf yace "A'a bakomai nagode, yanzu zan wanke in gama"
"dan Allah ka kawo, ai be kamata kayi wanke wanke da kanka ba, idan Baffa ya gani ma ze iyayi mana faÉ—a"
Yusuf yace "kema 'yarsa ce ne?"
Hanne tace "eh nima' yarsa ce nida Hindu, muje wani ƙauyene suna, se jiya muka dawo"
Yusuf yace "Allah sarki, Allah yayiwa rayuwar ku Albarka"
Cike da jin daɗi Hanne tace "Ameen" ta karɓi kwanukan, yace "in kin gama, seki kai mata ɗakin"
Hanne tace "to" tana mamakin ace yana da mata amma shize wanke wanke, Yusuf ya janyo ruwa a rijiya ya wanke banɗakinsu, yayi wanka ya fice.
Hanne ta gama wanke wanke, ta tafi ƙofar ɗakinsu Widad, ta tsaya tana sallama, ƙasa ƙasa Hanne ta shiga ɗakin ta cewa Widad "ga kwanuka inji mijinki"
"Ajiye anan"
Hanne ta ajiye, ta juya ta fita tana mamakin wannan irin nuna isa na Widad.
Anwar ya gayarawa Daula jikinsa, ya canza masa kaya ya bashi Abinci da sirinji, ta cikin robar dake hancin Daula, ya gyara É—akin ya tattara kayansa marasa kyau ya fita ze bayar akai gida su Nura su wanke.
Sufyan ne ya tinkari ɗakin da Alhaji Nasir yake, gaban sa se faɗuwa yake, ji yake kamar kowa kallonsa yake a baranda ya haɗu da Anwar, suka gaisa da Anwar, doctor Sufyan yace "ina zaka haka Anwar? Kasan bama san ana barinsa shi kaɗai"
Anwar yace "yanzu zan koma, kayan nan na fito dashi zan kaiwa direba ya kai gida a wanke"
Sufyan yace "to masha Allah, ga wasu magunguna na rubuta, idan ka kai kayan wankin seka biya pharmacy ka siyo"
Suna nan tsaye aka fito da wani mutum ya mutu an turo shi a gado za'a fita dashi.
Anwar yace "doctor, dan Allah nasan lafiyar Alhaji ba a hannunka take ba tana hannun Allah, dan Allah ka ƙara ƙoƙari, bawan Allah nan kullum jikinsa ƙara rikicewa yake"
Sufyan ya dafa kafaɗar Anwar yace "karka damu Anwar, kamar yadda ka faɗa sauƙi na Allah ne, Amma muna fatan Allah ya bawa Daula lafiya"
Anwar yace "shikenan nagode, bari inje"
Anwar yayi gaba, Sufyan ya tsaya a gurin yayi shiru, sannan yayi gaba jikinsa gaba ɗaya babu ƙwari, a haka ya taka har yaje ƙofar ɗakin da Daula yake, yasa hannu ya murɗa ƙofar ya shiga, sedai me yana shiga yaga wayam ba kowa akan gadon, ya ƙarasa gaban gadon da sauri ya yaye bargon kai, ba Daula babu alamarsa, ya buɗe banɗaki ya duba nan ma kowa, ya duba bayan ƙofa zuwa ƙarƙashin gado, amma be ganshi ba ƙarewa har fridge ya buɗe amma bega alamar Daula ba.
Cire gilashin dake idonsa yayi yana zazzare ido, yana waige waige kamar Æarawo
Fitowa yayi da sauri daga É—akin, aikuwa yayi karo da Anwar, Anwar yace "doctor Sufyan ya dai? Naganka a haka? Na kawo maganin"
Doctor Sufyan yace "Amm... Mmm.. Nace ina Mara lafiyar ne?"
Anwar yace "kamarya? Yana ciki mana"
Sufyan yace "Baya nan na duba ko ina ban ganshi ba"
Anwar yace "kamar yaya? Ya za'ayi in fita barshi, daga zuwa siyo magani kace baka gasnhi ba? Sekace wata eiga, mutumin da komai sena masa ta yaya ze iya fita?"
Sufyan yace  "Nima abunda ya bani mamaki kenan, na duba ko'ina ban ganshi ba, har banɗaki na duba baya nan"
Kallon tuhuma Anwar yayiwa Sufyan yace "Amma gaskiya ni ina tantama, babu wanda ya shiga É—akin bayan fita ta sekai"
Sufyan yace "Wallahi ban tarar dashi a É—akin nan ba kaji na rantse"
Anwar ya É—aga waya ya kira 'yan sanda, ya kira ya sanar da Bulama abunda ake ciki.
Widad ta gaji da zaman ɗaki, ta fito tsakar gida ƙarƙashin bishiya ta zauna, yaron gurin hansai ne da baze wuce shekaru uku ba, yake ta kallon Widad yana leƙa gashin kanta, murmushi Widad tayi tace "Naga kana son gashin nan, zo in baka ka taɓa"
Tsayawa yaron yayi yana murmushi, a hankali ya ƙaraso inda Widad take, ta riƙe hannunsa ta ɗora akan gashinta, nan yaron ya shiga wasa da gashin nata yana dariya.
Hansai data fito taga abunda yake faruwa, tunda suka dawo suka tarar dasu Widad, ko sannu bata taɓa haɗasu ba, ko murmurewa bata taɓa ganin tayi ba, Hausawa sukace me ɗa wawa se taji daɗin yadda Widad take wasa da ɗan nata.
Hindu data fito tsakar gidanma, tana ganin haka ta ƙaraso tace "kai Sani sakar mata gashi mana, ya takura miki ko?"
Widad tace "A'a nibe takura min ba, naga yana son kamawa ne shiyasa nace yazo ya taɓa"
Hindu tace "Abunka daba'a saba ganiba shiyasa yazo ya saki gaba"
Widad tayi murmushi har haƙoranta suka fito tace "gashin ne ba'a saba gani ba, bayan duk kanku ba'a aske yake ba"
Hindu tace "to ai ganin gashi me yawan naki dai basu saba gani ba, kuma dan Allah ke 'yar ƙasar nan ce?"
Hansai dake ƙoƙarin haɗa wuta tace "wallahi nima abunda ke bani mamaki kenan, dan Allah' yar ƙasar nan ce ke?"
Widad tace "taɓ 'yar ƙasar nan ceni mana, banyi kama da Hausawa bane"
Hindu tace "gaskiya ko bahaushiya ce ke, to sedai ko ruwa biyu"
Widad tace "ruwa biyu kamar yaya?"
Hansai tace "kamar ace mamanki bahaushiya mahaifinki wani yaren, ko mahaifinki bahaushe mamanki wata yaren"
Widad ta É—anyi jim sannan ta murmusa tace "dukkansu Hausawa ne, mazauna Kano"
Hindu tace "kano, dan Allah a kano kike?"
Widad tace "kin taɓa zuwa ne?"
"Ni waze kaini kano? Muna dai jin labarin kano, ance garin yana da kyau sosai, kuma mutanen kano suna da kirki"
Widad tace "Insha Allah wataran zaki kano, ba laifi kam kano tana da kyau, nikam ya sunanki ne"
Hindu tace "sunana Hindu"
Widad tace "Masha Allah, Hindatu"
Gwaggo ce ta fito hannunta ɗauke da ƙwarya da rariya tace "Amarya yau hira ake haka? Badan da kaina naga kina surutu ba, da zance bake bace"
Widad tace "Wallahi gwaggo bani da surutu, amma ina magana sosai ai"
Hanne kuwa dake bakin rijiya tana wanke wanke ko kulasu ba tayi ba.
Itakuwa Hari fitowa tayi da gero, ta zuba a turmi ta fara daka tana habaice habaicenta, basu kulata ba suka cigaba da hira.
Gwaggo tace "Ai Amarya mutum rahama ne, ko yaya idan kina É—an fitowa ana hira zaki rage kaÉ—aici, amma ace ke mijinki kawai kika sani"
Widad tace "Mama kenan, to ai shikaÉ—ai É—in kawai na sani, kawo in tayaki tankaÉ—awa"
Gwaggo tace "A'a kar in takura miki"
Widad tace "ni baki takuramin ba"
Ta ɗaga kai ta kalli Hari tace "dan Allah malama kiyi ɗaya, ko dakan kokuma waƙe waƙen haba dan Allah, da wanne za muji ƙarar daka ko kuma na wannan hayaniyar da kike yi"
Hari tace "Allah ya haɗani da Baƙar Jaraba ni Hari jikar Hama, na kulaki ne ko tsabar jan bala'i ne? Wallahi ki fita a sabgata, tun kafin in miki wulaƙanci"
Widad ta sunkuyar da kai tana dariya, dama abunda take so kenan, ta zungurota taita masifa, dan ita yanzu ta maida Hari comedy.
Widad ta karɓi tankaɗe kamar abun Arziki, ta riƙe rariyar da hannu ɗaya, ta ɗaga hannun sama tana girgiza rariyar, garin kuwa se kama gabansa yake, dan haka iska ta dinga kwashe shi, gwaggo kuma takasa yi mata magana saboda kawaici.
Yusuf ne yayi sallama hannunsa ɗauke da ledar viva, hango Widad yayi tayi buɗu buɗu a cikin gari, gashi a ƙarƙashin bishiya take tankaɗen, iska duk ta kwashe garin.
Hanne na ganinsa ta wani fara mutsu mutsu da gyare2, tace "sannu da zuwa" Yusuf be kula da ita ba
Da sauri ya ƙarasa inda Widad take yace 'Subhanallah Widad waye ya saki wannan aikin "
Gwaggo tace "seda nace base tayi ba, tace in bata tayi"
Yusuf yace "wa yace ki bata, Mama bata iya bafa, kalli yadda tayi miki Asarar gari"
Murmushi gwaggo tayi, ta É—auke kai daga kallonsu.
Widad tace "Na iya, ba gashi inayi ba, kai komai nayi seka gwalemin"
Yusuf yace "Ni na isa kiyi abu in gwale, amma kalli yadda kika ɓata gurin"
"Ni dai ka ƙyaleni in cigaba da aikina"
Yace "Naji, amma kawo in nuna miki yadda akeyi"
"A'a ni naga yadda akeyi ai, shine nima nake gwadawa"
Gwaggo kam gaba ɗaya kunya suka bata, dan haka ta miƙe ta bar musu gurin gaba ɗaya.
Yusuf yayi ƙasa da murya yace "dan Allah kiyi haƙuri ki kawo, wallahi baki iya ba kawaici kawai tayi miki, amma wannan aika aika kike mata"
Sakar masa rariyar tayi, ya shiga gwada mata yadda ake yi, kawai ta kwashe da dariya, ya kalle ta yace "lafiya kuwa?"
"A'a gani nayi ka iya sosai"
Ba ƙaramin kyau tayi ba dariyar da tayi, karon farko da tayi fara'a haka sosai ya gani.
Kawai ya shagala da kallonta, ya É—anyi murmushi ya cigaba da nuna mata yadda akeyi.
Hanne kuwa ji tayi ta tsani Widad gaba ɗaya, ko ganinta bata son yi ganin Yadda Yusuf ke wani ƙure Widad da ido se taji kamar tayi kuka.
Megari ne yayi sallama ya shigo, yace "Malam Yusuf ka dawo kenan?"
Yusuf yace "eh Baba na dawo" Megari yana jin daÉ—in yadda Yusuf yake girmamashi
Yace "ya kasuwar kuwa?"
Yusuf yace "Alhamdilillah, naje harna dawo"
Megari yace "to masha Allah"
Widad kam ko kallon Megari ba tayi ba, balle tace masa wani abu, Megari ya ƙaraso inda take yace "wannan 'ya tawa akwai miskilanci, tunda ba zata kula baban nata ba, toga tsaraba na kawo mata, Allah ya ƙara ƙarfin jiki"
Ya ajiye mata dabino rabin kwano a gabanta, Yusuf yace "Mungode sosai Baba, Allah yasaka da alkhairi"
Megari yace "A' a bakomai Yusufa, Allah ne ya haÉ—a mu zama tare, kuma naji harga Allah kun kwantamin, Allah yayi muku Albarka"
Yusuf yace "Ameen"
Yusuf ya É—au ledae daya shigo da ita, da wadda Megari ya bawa Widad, ya shige gaba Widad na binsa a baya, gwaggo tace
"Amarya karɓi kayan hannun nasa mana"
Widad tace "Ai ze iya É—auka, ni yamin nauyi"
Gwaggo ta jinjinawa gaɓunta irinta Widad, akwai buƙatar a zaunar da ita ayi mata takara akan zama da miji.
Suna shiga É—aki Yusuf yace "yanzu uwaÉ—akina abaki abu amma ki kasa cewa kin gode, baze ji daÉ—i ba fa"
Maimakon tayi magana, sema sosa kai data hauyi tana wasa da gashin kanta ta wuce inda katifarta take, Yusuf ya bita da ido, wato se yanzu yake ganin tsabar yarintar Widad, wato a da ɗinma tsabar izzarta da jin kaine yake sa ka ganta kamar wata babba amma kwanan nan wautar da Widad keyi wasu lokutan, suke ƙara fito da yarintar ta, sedai har yanzu wannan izzar da jin kan basu barta ba.
Yusuf yace yakamata kidinga gaida Megari, kinga yana mana ƙoƙari shima kinji gimbiyata.
Aikuwa nan da nan ta haÉ—a rai , Yusuf yace "meye kuma na haÉ—e ran?"
"Ai kafini sanin abunda ka faÉ—a, kuma kasan bana so"
Hindu ce tayi sallama a ɗakin nasu Yusuf ya amsa, ta shigo da kwano ta durƙusa ta gaida Yusuf, Yusuf ya amsa mata, tace "Amarya gashi inji Gwaggo"
Widad tace "to Nagode"
Hindu ta juya ta fita, Widad ta buÉ—e kaanon tace "yau kuma meye wannan?"
Yusuf ya karɓa ya duba yace "kwaɗon rama ne"
Ta kalle shi tace "meke nan?"
Yusuf yace "kici kiji mana"
Tashi tayi taje ta wanke hannu tazo ta zauna, ta ɗiba takai bakinta, yatsine fuska tayi tana taunawa da ƙyar, kamar tayi kuka tace
"Wai su mutanen nan basa girka abunda akeci ne?"
Yusuf kamar ya tintsire da dariya yace "wannan me ake dashi in ba ciba"
"to naji tsami, ga gishiri da kamar sugar"
Yusuf yace "kyaji dashi, nidai bari inje inyi salla" ya miƙe ya fita.
Abu kamar wasa, sa 'yan sanda suka tashi suka kama Anwar da Doctor Sufyan, wai za' ayi bincike a kansu akan ɓatan Alhaji Nasir Daula, aka kama wasu daga ma'aikatan Asibitin sannan aka rufe Asibitin. Tun ana ɓoye ɓoye har abu ya fara bayyana cewar wai Alhaji Nasir Daula ya ɓata a Asibiti.
Hankalin Hajiya Halima ya tashi, jin an kama mata É—a an kai shi police station, gidan Bulama ta shirya ta tafi bagazan bagazan ta É—au mota ta fice.
Tana fita Isa yace "Matsiyaciyar mata, da yake É—anta aka kama kalli yadda ta fita afujajan, amma mijinta na kwance a Asibiti ko a jikinta, ni É—anne ma yake bani tausayi da nace Allah yasa baza'a sake shi ba"
Murtalah yace "ai Matsiyaciya É—aya kenan, kalli yadda ta saida fiye da rabin motocin gidan nan, kalli Yadda tabi ta rage mana albashi dan Azzaluma ce, Allah sarki Yusuf da uwaÉ—akinsa, ko a wane hali suke oho?"
Nura yace "Ai wallahi se yanzu nake ganin ranar yarinyar nan, duk wulaƙancinta haƙƙinmu baya ciwo koda megida baya nan, ubangiji Allah ya bayyana Alhaji Daula"
Isa yace "Ameen dai abubuwa se faruwa suke kamar almara wai anemi mutum a gadon Asibiti a rasa, Allah ya kyauta"
Suka haɗa baki sukace "Ameen"
Yusuf ya dawo daga salla, yaga kwanon rama a rufe, yace "kaddai baki ci ba"?
Dabinonta take ci tace "ni bazan iya cin wannan Abunba"
Yana duba kwanon yaga ta tattare ƙuli ƙulin, da tumatir da Albasar da gurjin dake kai ta cinye abunta, ta bar gayan ramar duk ta lashe ƙulin jiki.
Murmushi yayi bece komai ba, ya ci ramar nan a haka, se jikinta yayi sanyi taga bata kyauta ba.
"Gimbiyata, ga wake nan na siyo mana a kasuwa yau da yamma za'a kawo kayan tea harda bredi"
Da sauri ta kalle shi tace "dan Allah dagaske hadda bredi?"
"ya zan miki ƙarya, inje ki hukunta ni, dagaske nake"
"Yau zanci bredi"
Yusuf yace "hadda shayi makuwa, bari inje in watsa ruwa na gaji sosai"
Widad tace "to, ba zaka ci dabinon ba?"
"bari in wanka tukuna"
Ya tashi ya ɗau bokiti ya fita, seda taga ta kassara dabinon nan, ta masa cin ƙoshi sannan ta ajiyewa Yusuf sauran.
Ta miƙe ta tattare ƙwallyen ta tafi taje ta zubar, gwaggo na ganin Widad tace "Amarya zo kinji yarinyar kirki"
Widad ta ƙarasa inda take, gwaggo tace "Amarya, daga yanzu idan mijinki ya dawo in yazo da kaya duk abunda kike ki tashi ki karɓi kayan hannunsa kinji?"
Widad a ranta tace 'wai nan duk zatonsu wani Auren kirki mukayi?'
A fili tace "To Mama zan dinga yi, amma gaskiya banda kaya me nauyi"
Gwaggo tayi murmushi tace "dama bance dame nauyi ba, amma ki dinga kula dashi sosai, ko so kike yayi miki amarya?"
Widad dariya kawai tayi tace "Mama kenan, to in yayi meye a ciki, nidai fatana mu koma gida"
Gwaggo tace "hakane amma yakamata kidinga nuna kishi akansa, zeji daɗi ko Auren dolene kukayi?"
Ganin kamar Widad bata son zancen ne, yasa Widad tace "jeki abunki É—iyata"
Widad ta juya ta tafi É—aki, tana zuwa ta tarar Yusuf ya fito daga wankan, yana tsaye da gajeren wando a jikinsa yana goge ruwan wankan jikinsa, wasu irin dogayen gashi ne a jikin Yusuf, taga yayi mata wani irin girma da kwarjini.
A É—an gigice tace "Yoseef meye haka?"
Da sauri ya waigo ya kalleta yace "meyafaru?"
"meyasa zaka shigomin É—aki a haka? Kalleka fa tsirara"
Yusuf ya kalli kansa yace "Niba tsirara nake ba"
"to meye haka, naga a can banÉ—akin kake sa kayanka"
Yusuf yace "Ramawa nakeyi, Allah ya bani haƙuri in dai a haka tsirara nake, toke ban san a ya kike yawo ba"
Tsaki tayi ta shige can lungun É—aki, ta juya masa baya ya juyo ya kalleta, yayi murmushi ya gama tsane jikinsa, ya zura riga, ya É—akko man shafawa yazo kusa da ita yace
"dan Allah ki tayani shafawa a bayana mana"
"Allah ya kiyaye, ni ka tashi daga kusa dani" ƙememe taƙi kallonsa.
Yusuf yace "kalli kiga"
Rintse ido ta sake yi tace "ni bazan Kalleka ba, seka sa kaya wallahi ko inyi ihu da ƙarfi"
"Aina saka kayan"
A hankali ta buÉ—e idonta tana kallonsa, Wani irin kallo yake mata, wanda ta kasa gane ma'anar kallon da yake mata.
Zamewa yayi ya kwanta akan cinyarta, yace "Wash na gaji bayana ciwo yake kamar zan ɓalle"
Itadai kamar Yusuf ya É—aureta yau, ta kasa magana sam balle ta motsa, hannunta ya kama yana ta murzawa a hankali, har bacci ya É—aukeshi.
Har yanzu hannunsa yana cikin nata, Ƙura masa ido Widad tayi, gaba ɗaya Yusuf tausayi yake bata mussman idan ta tuna beji ba be gani ba tsautsayi ya ritsa dashi, se wahala yake faman sha, kuma be taɓa nuna mata ya gaza ba.
Riƙe hannunsa ta sake yi, ta toshe bakinta tana kuka, hawayen tausayinsu ya kamata.
Yusuf da bacci ya ɗauke shi, ya buɗe idonsa jin saukar hawayenta a fuskarsa, a gigice ya miƙe zaune yace "subhanallah meyafaru? Nine me nayi miki"?
Bata iya bashi amsa ba se kuka data cigaba dayi, Yusuf yace
"yi haƙuri na ɗagaki, tunda bakyaso bazan sake kwanciya a jikinki ba, yi haƙuri"
Ta lura baya son yaga tana kuka, dan haka ta basar dan karya gane acikin damuwa take yasa tace "Kuma idan muka koma gida sena gayawa Daddy taɓani ka dingayi"
Yusuf yace "Yi haƙuri bazan sake ba, goge hawayenki bazan sake ba insha Allah, bari in sauka ma daga kan katifar"
"A'a ka kwanta anan, amma idan ka sake taɓani se nayi kuka, kuma Daddy zan gayawa idan muka koma gida"
"To shikenan naji"
Ya kwanta ya juya mata baya, murmushi ta dingayi ta miƙe ta tsallake shi tayi waje.
Alhaji Munir yace "Impossible, ta yaya Alhaji Nasir ze ɓata a gadon Asibiti, sekace ɓatan rigar sawa"
Alhaji Haruna yace "Abun da mamaki, a yadda yake dai be isa ya gudu da ƙafafunsa ba akwai wata a ƙasa"
Alhaji Munir yace "tabbas akwai lauje cikin naɗi, inma dai akwai wanda yake gefe yake mana manaƙisa, amma kowaye idan muka tono shi abun baze masa da daɗi ba"
Babu ko sallama Hajiya Halima ta shiga Falon Hajiya Sarah, a fusace ta kalli Sarah tace "ina megidan nan yake?"
Hajiya Sarah tace "lafiya kuwa, maman Anwar?"
"bani da lokacin baki wannan amsar, kije ki gaya masa ina son ganinsa"
Bulama yace "Ai gani nan ina kusa"
Hajiya Halima ta kalleshi tace "da sanin ka aka kama min É—ana?"
Bulama yace "haka labari yazomin an kama shi"
"to ba labari bane ba, an kama min É—ana, to wallahi baze yuwu ba, daga abun Arziki seya koma na tsiya, daga yayi jinyarsa an sace shi a Asibiti se'a kamamin yaro akanme?"
Bulama yace "yanzu sace mijin naki be dameki ba?"
"Dalla karka gayamin maganar banza ko ka rainamin hankali mana, kai sace shin damunka yayi?"
"Yaya za'a sacemin Aminina É—an uwana, sannan kizo kina tayarmin da hankali akan an kama É—anki? Ki bar doka tayi aikinta, in sunga bashi da laifi zasu sake shi"
"dokar banza dokar wofi, ni zaka gayawa doka, doka nawa kayi amfani da kuɗi kayi fatali da ita a ƙasar nan? Ina son kayi Amfani da wannan damar taka da ikon kayi fatali da wannan dokar kasa a sakarmin ɗana, in bahaka ba you know what am capable of doing"
Godiya me tarin yawa Fans ina godiya 😠😠😠😠😠ðŸ˜
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
            _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 38_39
Shi kansa Saleh abun ya É—aure masa kai, ta yaya za'a je har Asibiti a sace mara lafiya, kuma bayan da jam'ian tsaro a cikin Asibitin da suke tsaron lafiyarsa, koda yake ba abun mamaki bane a haÉ—a baki dasu a sace shin, saboda da yawa mutanen yanzu suna iya yin komai saboda kuÉ—i.
Maman Nurat ce ta shigo ɗakinta, ta tarar da Nurat tana kan system tana danne danne, ta ɗago ta kalli Mahaifiyarta tace "Mummy lafiya kuwa?"
Mummy tace "Mhmm, wani labari naji"
Nurat tace "labarin me?"
"wai an nemi Alhaji Daula an rasa a Asibiti, yanzu haka an kama Shugaban Asibitin doctor Sufyan da kuma Anwar"
Zare farin glashin idonta Nurat tayi tace "What are serious Mum?"
"did I ever lie to you?"
Cikin kaɗuwa Nurat ta girgiza kai tace "Na shiga uku da wannan masifa, daga wannan se wannan ana ƙoƙarin a kashe wannan amma se waccan ta faru, an sace masa 'ya har yanzu ba wanda yasan inda suke, yana kwance yana fama da jinya an bishi gadon Asibiti an sace shi, innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Mummy me Anwar yayi aka kama shi to? "
Mummy tace " ina zan sani, ance dai har dashi a cikin suspect "
Nurat tace" idan harda sa hannun Yaya Anwar a ɓatan baban Widad, to tabbas beyi hakan dan cutar dashi ba, akwai dalili yakamata in ganshi "
Zare ido Mummy tayi tace " kiga wa? Ba dani ba Wallahi idan kika sake kika fita duk abunda yayi miki ke kika siya, na gaya miki babu ruwanki ki koma gefe ki taya su da Addu'a yafi "
Shiru Nurat tayi bata kuma cewa komai ba, Mummy ta gama mitarta ta tashi ta fita, ita kuwa Nurat ta shiga tunanin yadda zata yi ta fita.
Yanzu duk lokacin da aka idar da sallar Asuba, se Yusuf ya tsaya sunyi karatu a masallaci, aikuwa gasu da son karatun babu girman kai a lamarin su, dan haka yake jin daÉ—in koyar dasu, kuma ya basu damar yi masa tambayoyi, wasu tambayoyin idan kajisu sam bazaka ce musulmi ne ba, saboda tsagwaron Jahilci, Yusuf baya kyararsu ko hantararsu, haka yake amsa musu.
Akwai wanda yake tambayar Yusuf bayan an watse daga gurin karatun, wai shi ya zata in mutum ya kwanta da iyalinsa ba'a wanka se ranar Juma'a, Yusuf yayi masa bayani dalla dalla, kuma ya ƙudurce babu batun kunya, shine maudu'in daze musu gobe in Allah ya kai rai a gurin karatu "
Ya koma gida ya tarar da hakimar tanata kwasar baccinta, ya nemi guri shima ya ɗan kwanta, nannauyan bacci ne ya ɗauke shi, can cikin baccin nasa ya jiyo ihun Widad a tsakar gida, aikuwa a gigice ya tashi ya fita, wata kazar harice Widad tazo wucewa ta zata 'ya' yanta zata taɓa mata, dan haka ta fara bin Widad tana kai baki zata cije ta, shine take ta wannan ihun tana zagaye, ita kuma kazar na cigaba da binta.
 Hari na kallonta, ta dinga tintsira dariya, a gigice Yusuf ya fito, yazo da sauri ya kori kazar ya kalli Widad yace "haba my queen, gaskiya kin ban kunya kaza ce fa kawai "
Widad tace "to ba cizona take son tayi ba, kuma wlh idan ta sake bina sena kamata na tura ta a cikin wutar can ta ƙone kowa ya huta"
Hari tace "kan bala'i, kazar tawa zaki saka a murhu? Aikuwa dana miki rashin mutunci kuma wallahi da sekin biyani"
Yusuf yace "yi haƙuri bama iyawa zata yi ba, tana faɗane kawai yanzun ma tanawa kazar ihu, ta ina zata iya kamawa balle tasa a murhu?"
Widad tai farat tace "to sena buga mata wannan icen ta mutu, ko in Takata da ƙafata harta mutu, garama kija mata kunne"
"Kazar zan jawa kunne ko kuma wa?"
"Eh ita kazar"
"ta yaya zanjawa kaza kunne? Ko nima kazarce?"
Widad tace "to waya sani"
Gwaggo dake banÉ—aki kam dariyarta ta sha, dan yanzu sun saba kusan kullum da rigimar Widad da Hari suke karyawa.
Yusuf da wanine yace masa Widad ta iya neman magana cewa ze ƙaryane, amma yanzu yake ganin zahiri da ikon Allah, haka yaita bawa Hari haƙuri sannan yasa Widad a gaba zuwa ɗaki.
Ya ƙura mata ido sannan yace "da wanine ya cemin kin iya rikici haka cewa zanyi an miki ƙarya, amma gashi da idona ina ganin ikon Allah, kullum sekin nemi magana"
"da da bana yi ancemin mahaukaciya bana son mutane, yanzu kuma kace na fiye rigima"
Yusuf yace "yi haƙuri, amma adinga ragewa kinji queen, waini ya'akayi kika sake da mutan gidan nan, abun ya bani mamaki fa"
"Basu san ni wace ba, dan haka bana tunanin zasu cutar dani, dukda suma bawai yarda dasu nayi ba, amma inajin daÉ—in yadda suke kyautata min ne"
Yusuf yace "to nifa, an yarda dani?"
Kallon up and down Tayi masa tace "tukuna dai"
"shikenan ni na yadda dake ai, zoki zauna kusa dani muyi hira"
"Baza'ayi hirar ba, idan nazo kusa da kai taɓani zakayi"
Dariya Yusuf yayi, yace "taɓakinne bakya so inyi?"
"Eh bana so, kai kuma sekace dole seka taɓani"
"ba laifina bane, laifin zuciyata ne Gimbiyata"
"kai ka sani kai da zuciyar taka"
Tai maganar tare da kwanciya ta koma bacci, a hankali Yusuf ya dawo kusa da ita ya kwanta, tana yunƙurin juyi akan katifarta taji mutum, ta leƙo kanta daga bargo taga Yusuf.
"wai dan Allah meyasa kake min hakane, tasarmin daga kan katifa"
"Niba taɓaki zanyi ba, ina son inyi bacci ne zuwa ƙarfe goma in fita, Amma cinnaku se cizona suke wuyana ciwo yake saboda kwanciyar ƙasa, haba uwa ɗakina, atemaka a tausayamin mana"
Tura baki tayi tace "to matsa ni in fita tsakar gida in baka guri seka kwanta"
Zaro ido yayi yace "haka kawai inje ki fita ki jawomin magana, ki fita neman rigima, a'a yi zamanki anan"
"toni gaskiya bazan kwanta a kusa da kai ba"
Banza yayi mata ya gyara kwanciyarsa, tare da lumshe ido, yunƙurawa tayi zata fice ya fizgota ya zaunar da ita yace "yi haƙuri, bari in tashi in bar miki katifar, base kin fita kin janyomin magana ba, har mamaki nake yadda kika koyo rigima"
"nifa ba magana zan É—akko ba, ni kawai zomaye zan kalla"
"Idan kika tsokani Baba Hari, ba zan baki bredin ba"
"aikuwa kuka zanyi in ka hanani" ta miƙe tayi waje abunta.
Hankalin Hajiya Halima ya kasa kwanciya sam, saboda rufe mata É—a da'akayi, Amal ma duk abun ya dametta, suna ta zaryar station amma abu ya gagara, Yanzu ma Amal ce ta tafi É—akin Ramlah, ta tarar da ita a zaune tana waya, da Fahad.
Amal ta samu guri ta zauna, ta jira ta kammala sannan ta kalli Amal tace "lafiya kuwa? Kin shigomin É—aki kin sani a gaba kina ta kallona"
Amal tace "Ramlah waike baki damu bane dan Allah, kwanan Yayanmu Uku a hannun 'yan sanda, Mummy se zarya take anƙi sakinsa, amma kin shigo ɗaki wayarki kawai kike"
"to Amal haukacewa kike so kiga nayi ko yaya? Shima Allah ya ƙara masa waishi ga me mutunci ya zauna yana jiyyar uban da ya tsinta a rana, kinga hakan ze zamo masa darasi gobe baya ƙara taimakao ba"
Amal tace "bekamata ki faÉ—i haka ba Ramlah? Ta wani fannin in aka duba abunda Yaya yayi beyi laifi ba, ko so kike duniya ta farga da halin da'ake ciki? Ace bashi da lafiya amma babu wanda ya damu a cikinmu? Ni wallahi abun ya fara damuna koba komai Yaya Anwar É—an uwanmu ne"
Ramlah tayi ajiyar zuciya tace "kuma fa hakane, ni kaina ta wani fannin inajin ba daɗi rufe shin da'akayi, amma me zan iya akai wanda Mummy ta kasa"?
Amal tace "Fahad zakiyiwa magana, dan Mummy taje har gidansu ta gayawa mahaifinsa amma yaƙi ɗaukar abun da mahimmanci, ke tunda kuna ɗasawa dashi kisa yayiwa mahaifinsa magana yasa baki a saki Yayanmu"
Ramlah tace "Anya kuwa? Fahad fa akwai lafiyar kafiya mussman yanzu da suke takun saƙa da yaya"
Amal ta taɓe baki tace "ashema ba son naki yake ba tsakani da Allah tunda ze iya barinki cikin damuwa, Allah wadaran wannan soyayyar"
"Amal ni kike cewa Allah wadaran?"
"Na faɗa Allah ya wadaranta, dama wannan banzan Fahad ɗin me fuskar jakai kansa kawai ya sani, in ba soyayyar ƙarya ba, yayiwa mahaifinsa magana yasa baki a saki ɗan uwanmu mana, naga shima dai ɗan uwansa ne"
Ramlah tace "Aikuwa Amal i will prove you wrong, zan nuna miki soyayyar mu ta gaskiya ce"
Amal tace "in gani ƙas, ancewa kare ana biki a gidansu, ƙaryar banza burodi a lefe, ina amfanin soyayyar da baka da alfarma a gun wanda kake so"
Ta tashi ta bar mata É—akin, tana ci gaba da mita da tsaki.
Nurat ta shirya cikin doguwar riga, tayi rolling ta ɗau wayarta da jakarta ta fito, ta leƙa ɗakin mamanta taga tana bacci, ta taho cikim sanɗa ta fito harabar gidan, da sauri sauri ta tafi bakin gate tace "zoka buɗemin ƙofa zan fita"
Me gadi ya kalleta yace  "ina zaki?"
"ka aikeni ne? Ka buÉ—emin zan fita"
Ya É—an sosa kai yace "Madam, me gidan nan yace kar in kuskura in sake bari ki fita, muddin bashi ya bada umarnin hakan ba"
A É—an hasale tace "ka buÉ—emin ba nisa zanyi ba, yanzu zan dawo"
Girgiza mata kai yayi yace "dan Allah kiyi haƙuri, wallahi zan fuskanci fushinsa muddin na bari kika fita"
Juya tayi cikin gida, jiki ba ƙwari tana tunanin meye mafita, can wani abu ya faɗo mata, ta miƙe ta fito tace masa "kazo Mummy na kiranka"
Ya miƙe ya biyo bayan Nurat, yana gaba tana binsa a baya, yana shiga falonsu cikin sanɗa ta dawo baya a hankali, tayi waje tana zuwa tasa mukulli ta buɗe gate ɗin tayi waje abunta.
Gidansu Widad ta tafi, tana zuwa tayi sa'a ta tarar da Amal a babban falo tana karyawa, Amal na ganinta ta buÉ—e baki tace "Nurat yau kece a gidanmu haka? Abun mamaki"
Nurat tayi murmushi tace "meye na mamakin kuma?"
Amal tace "ni dai nasan koda zaki zo gidan nan saboda Widad zaki zo, kuma duk garin nan ba wanda be san anyi kidnapping É—insu ba, kuma dai amma baban ku besan kinzo ba"
Nurat tayi murmushi tace "tabbas nasan an sace Widad da É—an uwanta, sedai...
Amal tace " É—an uwanta kuma? Direbanta dai"
Nurat tace "direba kuma kamar yaya direba?"
Amal tace "kamar yadda na gaya miki, ita da Yusuf ne aka É—auke su, Yusuf kuma direbanta ne"
Nurat tayi shiru, sannan tace "Amma meye alaƙar dake tsakaninta da Yusuf?"
Amal tace "Allah kaɗai yasani, Wallahi Nurat ina cikin matuƙar damuwa ɓatn nan nasu, mussman Yusuf idan nace zan nuna damuwar da nake ciki ma babu me saurarata a gidan nan, Amma duk rashin yardar Widad ta yadda da Yusuf fiye da tunaninki"
"Amma Amal mezesa matashi kamar Yusuf ya ɓige da aikin direba a gidan masu kuɗi?"
Amal tace "bake ba ni kaina ina wannan tambayar, amma kin san da wani aikin gwamnatin gara aiki a gida kamar wannan, dan ba Widad ba hatta me gidan nan ya yadda dashi sosai, Amma a yadda Yusuf ya haɗu kam, bekamata ace aikin direba yake ba, nayi masa zancen ya nemi wani aikin, amma yaƙi yarda, yafi ƙaunar kasancewa a ƙarƙashin wannan uwar izzar, tana hantararsa tana komai amma baya ganin laifinta"
Shiru Nurat tayi kamar ba zata ce komai ba, can tayi ajiyar zuciya tace "Amal ya batun Yaya Anwar kuwa?"
Amal tace "hamm, yana can Mummy tana ta fama anƙi sakinsa, wai har yanzu bincike ake akai"
Nurat tace "wani station É—inne?"
"Suna state CID shida Likitan"
Nurat tace "Allah ya fidda shi lafiya, Insha Allah zanje in ganshi"
Amal tace "kai amma kuwa mungode sosai Nurat"
Nurat tace "bakomai Amal, se anjima"
Yusuf yayi baccinsa ya tashi, ya buÉ—e jakarsa ya É—akko kayan tea daya bada sautu aka kawo masa, ya É—ora tea Widad tana tsakar gida suna hira da Hindu, da hansai.
Yayinda Hanne se wani gyatsine fuska take yi, bata kallon ko inda Widad take, Widad data fita bata taɓa nuna tasan da halittar Hanne ba, abun da Hanne bata sani ba shine, mutanen da suka damu da itama ba kowa take iya shiga sabgarsa ba, balle wanda ya nuna be damu da ita ba.
Yusuf ne ya fito tsakar gida, yaje ɗakin megari suka sake gaisawa ya zauna suka shiga hira.
Widad na zaune kusa da gwaggo, tana dama koko tana kallon yadda take yi, Widad tace "Mama haÉ—a kokon nan ma ashe ba wahala, na iya haÉ—a custard shima zan iya wannan"
Hansai tace "meye kuma kostan?"
Widad tace "wani abune shima sha ake, kamar haka ake dama shi amma suna da É—an banbanci da wannan, Ai zaki ban watarna nima inyi ko?"
"taɓ za'a sha kwaɓa kuwa, yadda kike a sangarcen nan ba uwar da kika iya, mijinki na fama wallahi, ba uwar da kika iya se zance"
Widad ta ɗaga ido ta kalli Hari tace "Mijinki ne yake fama da ƙazantarki ba nawa ba, kuma karki ƙara cemin sangartacciya"
Gwaggo tace "yi haƙuri Amarya, ƙyaleta"
Gwaggo ta fara rabon koko, ana zuba na kofin megari Widad tasa hannu ta É—auka tace "wannan nake so, wannan kofin yafi kyau"
Gwaggo ta É—anyi shiru, Hansai tace "Amarya kofin megari nefa"
Widad ta tura baki tace "toni ina son kofin, wannan nake so"
Gwaggo tace "Hindu, jeki ki duba ƙasan gadona a cikin kwanukan Hanne ki ɗakkon sabon kofi irina Malam"
Hanne tace "kai gwaggo kofin Auren nawa za'a É—akko?"
Gwaggo tace "eh kema ba Allah ne ya baki ba, a sai miki wani"
Haka aka ɗakko sabon kofin silva, se ƙyalli yake da murfinsa aka zubawa Widad koko a ciki, Hanne ta dinga mita tana kumbura baki, ai Widad bata nuna tasan da zaman Hanne a gurin ba.
Hanne na tsaka da masifar ne sega Yusuf ya fito daga É—akin megari, ai nan da nan Hanne ta nutsu ta fara murmushi, Yusuf ya harari Widad dan yaji duk abunda ya faru, ita kuwa tayi kamar bata ganshi ba.
Hanne ta durƙusa ta gaida Yusuf, Yusuf ya ɗan saki fuska ya amsa mata, yazo ya durƙusa ya gaida su gwaggo, duk faɗan da Hari keyi da Widad, tana matuƙar girmama Yusuf, dan suna ɗasawa dashi.
Hanne tace "yau ba wanke wanke ne ka kawo ayi?"
Yusuf ya kalli inda Widad take, yaga ko a jikin ta, jujjuya kofin kokonta kawai take.
Yusuf yace "A'a babu na wanke tun Asuba.
Gwaggo tace "kaine kake wanke wanken? "
Yusuf yayi murmushi yace "A'a Mama, wani lokacin ina rage mata aikine kawai"
Gwaggo ta kalli Widad tace "Anya ÆŠiyata?"
Widad tace "Mena yi? Shine yake cewa zeyi fa, kuma idan nace zanyi se yace ban iya ba"
Hanne tace "ka dinga barinsu, da safe se in haÉ—a in wanke, tunda bata iya ba"
Hansai tace "ikon Allah, toke Hanne dole ne sekin wanke musu kwanukan?"
Widad tace "Yoseef kaga sabon kofinmu, Mama ta bamu"
Yusuf yace "Ahh mama mungode sosai Allah yasaka da alkhairi"
Ya kalli Widad yace "let's go and have a breakfast"
Ta miƙe tayi gaba, suna zuwa ɗaki yace "sannu kinji"
Cikin rashin fahimta tace "aikin me nayi kakemin sannu?"
"yanzu memakon kice in sai miki kofin kina so, kawai seki sa rigima ke se'an baki?"
"ko zaka Ƙwace ka mayar ne?"
Yusuf yace "A'a ni bance ba, na dafa shayi ne kuma gashi kin karɓo koko"
Da sauri tace "dan Allah dagaske?"
Bece mata komai ba, ya wuce ya sauke tukunyar tea É—in, ya buÉ—e jakarsa ya É—akko kayan tea É—in ya haÉ—a mata shayi yasa mata madara, tana zaune tana kallonsa, ya É—auka ya kai ya É—anÉ—ana yaji in beyi zafi da yawa ba sannan ya bata.
Ta kalle shi tace "meye kuma seka sha zaka bani?"
"Na duba ne inji in beyi zafi da yawa ba karki ƙone baki"
"to shine zaka sa baki a jikin kofin, toni gaskiya da cokali zan sha tunda kasa baki, ko in canza kofi"
Tsayawa yayi yana kallonta, taje ta É—akko wani kofin ta juye a ciki, ta É—au bredin ta gutsura ta koma gefe.
Karon farko da taga fuskar Yusuf ta canza saboda abunda tayi, ta nuna ƙarara tana ƙyamarsa kenan.
Tana kallon yadda ya ɗan ɓata fuska, ya kasa sakin jiki yaci Abincin ma, amma ta basar ta cigaba da cin bredinta, da a gidane ba yadda za'ayi taci bredi babu mahaɗi, amma yanzu se tura shi take kuma tana jin daɗinsa a haka.
Ƙarshe Yusuf miƙewa yayi yaje yayo wanka, yazo ya fara shirin fita sedai yaƙi cewa uffan, be sake kula ta ba shirinsa kawai yake.
Widad ta matsa inda yake tace "wai naga ka wani yi shiru, lafiya dai?"
Girgiza mata kai yayi, ya cigaba da shirinsa "Amma naji kayi shiru haka? Nasan baka saba zama haka kayi tsit ba"
Still shiru ya kuma yi mata, yana gyara kayansa dake cikin jakar matafiya.
ÆŠagowar da zeyi taga idonsa yayi jawur, gaba É—aya se jikin ta yayi sanyi.
"dan Allah meye ya same ka?"
Raɓata yayi ze wuce ta sha gabansa tana kallonsa.
Ze kuma kaucewa ta kuma shan gabansa, ba tayi tsammani ba Yusuf ya janyota ya haÉ—e bakinsa da nata.
Mutsu Mutsu ta dingayi tana ƙoƙarin ƙwacewa, amma ta kasa ko ƙwaƙwaran motsi, saboda yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba.
A hankali ya cika ta, tayi baya da sauri tana rarraba ido, tare da sauke numfashi.
Tofar da yawun bakin ta ta dingayi, tana goge bakinta tana kuka.
Yusuf ya ƙaraso inda take, amma ta shiga ja da baya, riƙota yayi ya ƙura mata ido, take yayi mata wani irin kwarjini.
Cikin sanyin jiki Yusuf yace "Widad da zuciya zatamin adalci to da ban iya jure duk wulaƙancin da kikemin a baya ba, saboda Yusuf baya Jura wulaƙanci dan shima mutum ne kamar kowa, sedai kash zuciya ta ta fara son abunda tasan yayi mata nisa har abada, wanda be dace da ita ba, zuciyata ta saɓa Alƙawarin da mukayi da ita nayin ban kwana da soyayya har Abada, hakan shine kawai mafita ga irin rayuwar da Yusuf ya tsinci kansa a ciki, Amma ko warkewa banba daga cikin zugi da raɗaɗin da zuciyata ke ciki ba, ƙaddara ta haɗani dake, kuma zuciyata ta shiga begen ki, Auren nan da mukayi har cikin zuciyata nake som Auren nan, sedai nasan dole wataran zamu rabu saboda bamu gina Auren akan tirbar soyayya ba, dan Allah Widad ni bance sekin soni ba, saboda nasan hakan baya cikin tsarin rayuwar ki, kuma tamkar ƙasƙancine a gareki Auren mutumin dabe kaiki a komai ba, nasan yanzu ma kutsen ƙaddara ne ya haɗamu zama inuwa ɗaya dake, ko baki soni ba dan Allah kidena nunamin ƙyama kinji Gimbiya, yi haƙuri na saki kuka" yai maganar yana ƙoƙarin goge mata hawaye
Fizgewa tayi tace "Dalla ni cikani in wuce, the must useless word i hate in my life Love, kaima ka shiga sahun imagination da shirme kenan, ban guri ni zan wuce"
Ta ture shi tayi gaba abunta, ta É—akko brush da toothpaste ta tafi sake wanke baki, duk dan Yusuf yayi kissing É—inta.
Jiki a sanyaye ya ƙarasa shiryawa, ya fito ze fita ko kallon inda yake ba tayi ba, ganin ba kowa a tsakar gidan se Hanne yasa yazo gabanta yace "Zan tafi"
"Jirani inzo in zama mota seka hau ka tafi"
Ya girgiza kai yace "nasan kina jin haushina, kiyi haƙuri"
Banza tayi masa ta cigaba da abunda take, Hanne tace "Adawo lafiya Allah ya tsare"
Yusuf yayi murmushi yace "Allah yasa nagode"
Har yayi gaba ya waigo ya kalle ta, suka haÉ—a ido ya É—an lumshe ido yace "I love you My queen"
Wata uwar harara tayi masa ta miƙe ta bar tsakar gidan.
Nurat tana zaune a reception, da ƙyar aka bari taga Anwar, fuskarsa duk ta ɗaga yayi wani iri, a gigice tace "Yaya Anwar me kayi aka kama ka haka?"
Anwar yace "wallahi Nurat ban saniba, wai ana tuhumata da haɗin bakina akan sace Daddy, kuma wallahi ban san komai ba, na gyara masa jiki na bashi abinci, likita yace inje in karɓo wani magani, ina komawa se cemin yayi wai ya shiga ɗakin amma be ganshi ba"
Nurat tace "kamar yaya, ta yaya za'a sace mutum a Asibiti mutumin dako motsin kirki baya iyayi"
Anwar yace "wallahi bam sani ba Nurat, ni yanzu ba kamanin da'akayine damuwa ta ba, sanin inda Alhaji Nasir yake shine babbar damuwa ta, ba shi da lafiya waye ya sace shi? Waze kula dashi? Waze bashi magani na rasa wacce irin masifa ce tasa ake bibiyarsa haka"
Shiru Nurat tayi tana zancen zuci 'Anya kuwa babu sa hannun mahaifina a sace Alhaji Nasir?'
Ta É—ago ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar baka yi laifi ba dan baka banga dalilin da zesa a kama ka ba, dan haka ka kwantar da hankalinka, akwai wani cousin brother É—ina, barrister Abdallah zan masa magana ya shiga cikin case É—in"
Anwar yace "bakya ganin akwai matsala? Kar a sashi a matsala fa, sunce in suka gama bincike za'a sakeni"
"babu wata matsala insha Allah, ka kwantar da hankalinka, Insha Allah zak bar gurin nan"
Anwar yace "Nagode sosai Ƙanwata, Allah yasaka miki da alkhairi"
Nurat tace "you deserve it dear" ta ɗau jakarta tayi waje.
Ramlah ce zaune a motar Fahad, ta murtuke fuska yana ta surutu amma tayi shiru, kallonta yayi yace "beb, ya inata magana amma kinyi shiru, lafiya kuwa?"
"Fahad yanzu ace brother na yana É—aure, amma koka jajantamin talk less of kace zaka kai masa ziyara"
Fahad yace "ni inje state CID no i can't tarnish my image"
"Amma fa kaima É—an uwanka nae"
"Yeah really, you are right dear but zuwa gurin nan se masu manyan crimes da manyan terrors, kuma kinga daddy na sanannen mutum ne, ace anga mutum kamar ni a irin wannan gurin is not fair at all, it will tarnish our family image"
Ramlah tace 'but your dad can bale him out, so you don't care about my feelings, É—an uwana yana rufe kaikuma abunda ya dameka daban ko? "
"Ai na miki bayani, ban san me kike so ayi ba kuma"
"ina son ka saka baki, Daddynka yayi magana a sake shi"
"Amma Ramlah kin san ba abune me sauƙi yin hakan ba ko, yaynki an haɗa baki dashi an sace Daula, me zesa Daddy yasa baki"
A fusace Ramlah tace "shut up Fahad, ta yaya Anwar ze hakan, tare kukayi school room ɗinku ɗaya, you know what he can do and what he cannot do, dan haka ina jiran kaje kayi magana da mahaifinka a fito da shi, that's the only way you can prove to me that you loves me"
Tana gama maganar tayi waje ta bar motar, ɗan taɓe baki yayi ya kunna motarsa yayi tafiyarsa.
Yau da Yusuf ya dawo a É—aki ya tarar da widad, kamar tana cikin damuwa ya kalle ta yace "Na dawo"
Jinjina masa kai kawai tayi, amma ta kasa magana, se ya zata tun abunda ya faru da safe ne yasa take jin haushinsa.
"Meke damun kine? Ko har yanzu fushin kike dani?"
A kasale tace "Bakomai fa"
Haka ya fita yaje yayi wanka ya dawo ya sameta a inda ya barta, yau dambun tsaki Hansai ta girka ta aiko musu, amma taƙi sakin jiki taci, ya kaɗa ya raya amma tace lafiyarta ƙalau, sedai ya lura buni buni seta tafi toilet ta dawo.
"Gimbiya ko cikin kine ya ɓaci?"
Girgiza masa kai tayi tare da kwanciya, haka taita yi har washegari gaba ɗaya kamar bata da sukuni, kuma taƙi gaya masa abunda yake damun ta, haka ya fita ya barta ya ɗauka dai fushi kawai take, Da Azahar ya dawo sedai ya tarar da tun Abincin safe bata kuma cin komai ba.
Yaje gabanta ya durƙusa yana ƙare mata kallo yace "dan Allah idan fushi kike dani kiyi haƙuri, kin sani a damuwa fa"
"Nifa ba fushi nake ba, ka ƙyaleni kawai"
"baki da lafiya ne?"
"lafiya ta ƙalau"
"but you look so much restless"
Shiru tayi bata ce uffan ba, ya miƙe yana duba kwanuka yaga abunda aka kawao, se yaga tana ta dube duben abun shimfiɗar dake kan katifarta.
Yana zuwa ya ɗagata cak daga kan katifar, meze gani jini ne a jikin ta, ya ɓata mata jiki da katifar.
A gigice yace "Subhanallah, Widad meya same ki haka?"
Take ta fashe da kuka tace "Period yazo min tun jiya bani da pad"
Cike da damuwa yace "shikenan is ok, kwantar da hankalinki"
Yasa hannu ya naÉ—e bedsheets É—in, ya É—ora ruwa yayi É—umi ya haÉ—a mata ruwa, ya rakata banÉ—aki, ya dawo ya haÉ—a abun shimfiÉ—ar da kayan data cire ya zubasu a bokiti.
Tayi wankan ta fito ta dawo É—akin, har yanzu bata dena kuka ba, Yusuf yace "jeki zauna bari inje gurin Mama inga inda wani taimako da zata bamu"
"Idan na zauna ɓata gurin zanyi"
Yusuf yace "bakomai zauna, idan ya ɓaci zan gyara"
Ya zaunar da ita ya fita da sauri.
Yana fita tsakar gida Hanne ta kalle shi tayi murmushi tace  "kana buƙatar wani abune?"
Yusuf yace "gwaggo zaki kira min dan Allah"
Tace "to"
Ta tashi ta shiga É—akin gwaggo, gwaggo ta fito ta kalli Yusuf tace "lafiya dai malam Yusuf?"
Cike da kunya, Yusuf yayi mata bayani, Gwaggo tace "to mudai yaranmu da tsimmane suke amfani, ban sani ba ko zata iya amfani da shi"
Yusuf yace "bakomai Gwaggo, zata iya insha Allah"
Gwaggo ta shiga ɗaki ta ɗakko sabon turmin Atamfa, da sabuwar reza, da ƙyar Gwaggo ta iya shiga ɗakin nasu saboda kunya.
Widad na zaune da towel se vest a jikinta, Gwaggo tace "Sannu Amarya ya jiki?"
Widad tace "lafiya ƙalau"
Tasa reza ta yanka Sabuwar Atamfa ta gwadawa Widad yadda zata yi.
Widad tayi shiru taƙi cewa uffan, Yusuf yace "Mama nagode sosai da taimakonki, Allah ya saka da alkhairi"
Gwaggo tace "bakomai Malam Yusufa"
Gwaggo ta fita, tana fita Hari tace "Yaya wai Wudas É—ince bata da lafiya?"
Gwaggo tace "Eh"
"meya same ta?"
Gwaggo bata amsa mata ba, Hanne tace "waini Gwaggo meye na yanka sabuwar Atamfarki, wallahi kin fiye zaƙewa akan wannan fitsararriyar"
Gwaggo a fusace tace "wallahi kika kuma magana sena kwaɗa miki mari, ina kallon ki duk abunda kike yi, ɗa na kowa ne, meye dan na yanka Atamfa? Abum duniya fararre ƙararre"
Haushi Hanne taji, dan da wuya kaga Gwaggo tana faɗa se an ɓata mata rai sosai, Amma yau akan wannan koɗaɗɗiyar tana ta mata masifa.
Yusuf ya kalli Widad yace "gimbiyata nasan baki saba amfani da irin wannan ba, amma kiyi haƙuri gidanmu babu mata nikaɗai ne shiyasa nima ban san kan wannan abubuwan ba, da tuntuni nasa an nemo miki abunda zaki yi amfani dashi"
Da ƙyar Yusuf ya lallaɓata ta saka ƙyallen nan, sam she's not comfortable with this thing, gaba ɗaya ta takure kanta, Yusuf yana kallonta ta kwanta ta zauna gaba ɗaya ta kasa zama.
Ya kwashi kayan data ɓata yaje ya wanke su tsaf, taga ya dawo ɗaki yana goge hannu ta kalleshi tace "wai me kayi?"
"kayanki na wanke"
"Kayan jinin?"
"Eh mana, nasan idan na bar miki ba zaki iya wankewa ba"
Shiru tayi ta bishi da kallo, tuno abunda ya faru da safe tayi, yadda tay masa wulaƙanci amma har ya manta yana tarairayarta, yasa hannu a kayanta na jini ya wanke.
Ganin da yayi ta kasa zaune ta kasa tsaye yace "Gimbiyata meya ke damunki yanzu?"
"ƙafafuna ne kamar ba nawa ba, babu daɗi marata ma ciwo takemin"
Yazo ya zauna a kusa da ita, ya kamo ƙafafunta ya ɗora akan cinyarsa yana matsa mata a hankali, lumshe ido ta dinga yi.
Ta ɗauke ƙafafunta daga kan cinyarsa, ta ɗora kanta sannan ta miƙa masa hannunta, tana masa nuni daya ja mata yatsun, haka Yusuf ya riƙe yatsun ta yana matsawa a hankali, babu daɗewa kuwa bacci yayi gaba da ita.
Seda Nurat ta tinkaro komawa gida sannan gabanta ya shiga faɗuwa, dan se yanzu ma ta tuna taɓargazar da tayi.
Kanta tsaye tana ta Addu'a ta fara buga gate É—in, me gadi yazo ya buÉ—e mata bece mata uffan ba, ta shiga cikin gidan, sedai me a harabar gidan idonta ya sauka a cikin na mahaifinta yana zaune yana kallonta.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
(Ina ma'abota karatun littafin AƘIDATA, a fari nace zan bada littafin kyauta ba tare da ko sisi ba, amin Afuwa wani dalili zesa zan saida book2 and 3,dukda nima ba hakan naso ba, gaba ɗaya kyauta nayi niyya bada littafina, Amma dalilin me ƙarfi zesa in saida ƙarashen in na gama book1 ina fatan zaku fahimceni)
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
         _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 40_41
Gaban Nurat ne ya shiga bugawa da sauri da sauri, ta shiga zazzare ido be kula ta ba bece mata komai ba, tazo ta tsaya tana kallon sa, taga harta wuce bece mata uffan ba.
Ta shiga ɗaki ta nemi guri ta zauna, tayi shiru tana tunanin yadda zata samu Anwar ya kuɓuta, babu zato taji an murɗa ƙofar ɗakin nata.
Mahaifinta ne ya shigo yana rarraba ido, gadan gadan yayo kanta yana faÉ—in "gidan ubanwa kika je?"
Miƙewa tayi a gigice ta shiga ja da baya tana faɗin "babu inda naje Daddy"
"ƙarya kike munafuka, harni zan saka doka ki sa ƙafa kiyi fatali da ita? Uwarki ta ɗaure miki gindin kiyi rashin mutunci ko? Ni da Daula waye ya haifeki?"
"Daddy niba gurinsa na je ba, Ai an É—auke shi daga Asibiti"
Sekuma yayi sak, "Ubanwa waye ya gaya miki?"
"wallahi Daddy a gari naji"
"to gidan ubanwa kikaje? Zaki gayamin ko sena yanka ki a gidan nan?"
Girgiza kai take, takasa magana ya cakumo wuyanta yana zazzare ido, kakari ta dinga yi tana kuka tace "Wallahi Daddy ba inda naje, kawai gajiya nayi da zaman gidan na fita, dan Allah kayi haƙuri"
"se naci ubanki yadda idan na sake saka doka ba zaki takamin ba"
Cikin kuka Nurat tace "Wayyo Allah Mummy, ki temakeni karya kasheni"
Maimakon ya saketa sake shaƙeta yayi, yana kuma zaro mata ido kamar tsohon maye.
Kakarin Nurat ne yasa mahaifiyar ta, ta sallame salar da take, a guje ta rugo É—akin Nurat, ta tarar ya shaÆ™e Nurat kamar ya kama sa'ansa ko kuma wani shahararren Æarawo.
"Kayi haukane, ka cikamin 'yata ita kaɗai ce dani, kana gani duk yaranmu mutuwa suke, ita kaɗai Allah ya barmin ka ƙyalemin' yata"
Juyowa yayi a fusace ya mangare mahaifiyar Nurat yace "itama ɗin gara in aikata inda waɗancn suka tafi, muddin zata dinga takemin doka, tasan a duniya bani da maƙiyi sama da Daula, danme zata dinga zuwa inda yake, akan me?"
Yai maganar tare da wurgi da Nurat, wadda tuni ta fara fita a hayyacinta, dan daya jefar da ita ko motsi ba tayi, se kokawa take da numfashi.
Da sauri Maman Nurat ta nufi kan Nurat, yayin da Alhaji Musa ya cigaba da banbami, ta É—ago Nurat sedai bata numfashi.
Cikin kuka tace "wallahi idan ka kashe min 'ya se nayi shari'a da kai, Kai kanka kawai ka sani, buƙata in ba ta kaba baka damu da kowa ba"
A fusace yace "Maza karki fasa yin shari'a dani, idan na kashe ta na kashe banza, duk son da nakewa mutum muddin ze bujiremin to zega ba dai dai ba tabbas"
Banza tayi masa, Taje ta buɗe fridge ta ɗakko ruwa me sanyi ta shiga shafawa Nurat, a hankali ta dinga sauke Numfashi, tana buɗe ido ta fashe da kuka tace "Mummy anya Daddy ne ya haife ni? Kalli yadda yayi yunƙurin kasheni me nayi masa haka?"
"kema da halinki Nurat, kin fiye taurin kai, na hana ki wannan abun da kike amma kin kasa ganewa, gashi ze kashe ki a banza"
Shiru Nurat tayi, tabbas tunda mahaifinta yake yunƙurin kashe ta akan taje inda Daula yake, to tabbas wani mummunan abu yake aikatawa, kuma na abunda baze iya aikatawa akan kowa ba.
Lumshe idon ta tayi tana jin yadda ƙirjinta yayi nauyi, wani irin baƙinciki ya mamaye zuciyarta.
Shikuwa Alhaji Musa yana komawa É—aki ya shiga sintiri, kamar yadda ya zame masa jiki a 'yan kwanakin nan, ba shi da nutsuwa sam, musamman da' aka ce su Widad sun gudu daga inda aka sace su, gashi sunsa a nemo su a ko'ina suke amma abu ya gagara.
Gashi yanzu wata maganar rainin hankali da ta taso, wai an sace Daula akan gadon Asibiti, 'Anya ba wani rainin hankalim su Alhaji Haruna suke shiryawa ba?'
A hankali Widad ta buɗe ido daga baccin da yayi awon gaba da ita, taga Yusuf ya jingina da jikin bango ya lumshe idanunsa, hannunsa ɗaya yana wasa da gashin kanta, a hankali tayi miƙa tare da hamma, da sauri ya buɗe ido yana jera mata sannu.
Ba tace komai ba se jinjina masa kai da take.
Miƙewa tayi zaune, se kuma yaga ta yamutsa fuska.
Kallon ta yayi da sauri yace "lafiya dai?"
ÆŠan tura baki tayi tace "am not confortable at all, ji nake kaman am stain"
Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah, zan san yadda zanyi a samo miki wancan da kike amfani da shi"
Widad tace "baza a samu wanda nake amfani da shi ba, sedai a siyomin kowanne ne, bana son wannan abun da nake using dashi yanzu, is so much irritating"
Yusuf yace "Shikenan, Insha Allah zan san abunyi"
"Sannan kuma..." se kuma tayi shiru
"sannan kuma me?" Yusuf ya tambaya
"Nasan baza'a samu shaving cream ko powder ba, a siyomin shaver please"
Cike da son ya kunnata Yusuf yace "shaver kuma, me zakiyi da shaver?"
"Abunda kake yi da ita" ta bashi amsa cike da tsiwa
Yayi murmushi yace "Aini gemuna nake askewa da ita"
Ta kalle shi ta É—an tsuke baki tace "Nima nawa gemun zan aske"
Aikuwa Yusuf ya kwashe da dariya, sosai yadda tayi magana da abunda ta faÉ—a É—in ya bashi dariya, kallonsa take yi yadda dariyar tayi masa kyau.
"wallahi idan ka ƙware ba ruwana"
Tai maganar tana shirin Miƙewa, ya kalleta yace "Ina zaki?"
"tsakar gida nake son fita"
"Amma kin manta halin da kike ciki ne?"
"To zama zan tayi ina kallonka, ni na gaji da kwanciyar ma, zan kula sosai"
Yusuf yace "Aini bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar nan taki, muyi zamanmu a É—aki nima na iya hirar se in miki, kuma baki ci Abinci ba, ko kin manta?"
'ƙyale Abincin nan, ni idan ina period bana son Abinci sosai "
Yusuf yace " dama can haka kike, ina lura dake tarkace kawai kike ci ba Abinci ba, so nake ki ƙara Ƙiba ki daure kici ko kaɗan ne mana"
"Ni gaskiya, ba irin wannan nake so ba"
"wanne kike so" ya faÉ—a cike da kulawa.
ÆŠan tsura masa ido tayi, sannan tace
"Bari dai inci kaÉ—an"
Ya É—akko kwanon dambun ya ajiye mata, tasa cokali ta fara ci, dambun tsaki ne amma yaji gyaÉ—a da zogale yayi daÉ—i Sosai.
Widad tace "tunda nazo ƙauyen nan, ban taɓa cin Abinci me daɗin wannan ba"
Yusuf yayi murmushi yace "harda bredin jiya?"
Widad tace "hmm dan dai kar kaji haushi ne, amma gaskiya bredin nan ya daÉ—e a ajiye, se marmashewa yake ba daÉ—i"
Yusuf yace "dagaske ba kya son inji haushi?"
ÆŠan kallonsa tayi tace "No i mean banyi niyyar magana ba lokacin shine kawai, ka É—akko spoon muci Abinci mana"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a kici kawai, idan kin rage se inci"
Widad tace "meyasa? Ai ze ishemu"
Yusuf yace "bana son in samiki yawuna a jiki, naga bakya son hakan"
Ɗan tura baki tayi, cikin ƙunƙuni tace "na nawa kuma, ƙarewa ma ai Yawun naka ka samun a bakina jiya"
Yusuf yace "ai bazan manta wannan moment É—inba, nayi kissing É—in gimbiyata the most memorable moment in my life"
Widad tace "tabbas kam, ka kafa tarihi, kayi abunda wani mahaluki be taɓa gangancin gwadawa ba, kayi min abunda ban taɓa zaton wani zemin in ƙyaleshi ba, hmm ban san meyasa kake min abubuwa son ranka ba, ƙyaleka kawai nake"
"Are you sure babu wanda ya taɓa kissing ɗinki seni?"
Watsa dambu tayi a bakinta, ta ja wasu seconds sannan tace "Idan an taɓayi kana tunanin zanji tsoron ka ne? Ban taɓa shan yawun Ƙato ba se a kanka, kuma bashi ka ɗauka, tunda kasa na haɗiye yawunka"
Murmushi Yusuf yayi yace "Yaushe ne ranar biyan bashin?"
Banza tayi masa taƙi ko kallon inda yake, can Yusuf yace "Amma meyasa kike zuwa Clubs da kuma Hotel?"
Jin tambayar tayi a bazata, take taji tana kokawa da dambun dake bakinta, gaba É—aya Mood É—inta ya canza a hankali tace
"ai tun a lokacin na gaya maka me nake zuwa yi, na gaya maka ni karuwa ce kamar yadda matan gurin suke"
Haɗe rai Yusuf yayi yace "Kamar yadda bakya son ƙarya, na tabbata kema bakya aikata ta se bisa kuskure, meyasa zaki gayamin haka? Ko kina son zuciya ta ta buga ne?".
"Tunda baka yarda ba shikenan, amma kasan dai bazan zauna ina rantse maka dan ka yarda dani bako?"
Ta ajiye spoon É—in Abincin ta je ta sha ruwa, tayi waje abunta ta bar Yusuf a gurin a zaune.
Roƙon Allah ya shiga yi akan Allah yasa abunda Widad ta faɗa ƙaryane, dan ba ƙaramin kishi yaji ba, kuma yasan halin ta ko meye zata yi ƙoƙarin gaya maka gaskiya, ko ta maka daɗi ko akasin hakan'
Tana fitowa Gwaggo tace "Amarya kin ware kenan?"
Widad tace "eh Alhamdilillah"
"Masha Allah, haka nake son ji"
Hari tace "Wai meya same ki ne?"
Widad tace "Kaji Baba Harin nan, sekace kin damu dani, bayan ko gani kika yi zan mutu murna zaki yi, to ciwon yara nake bana tsofaffi ba dan haka base kinji ba"
Aikuwa a fusace Hari tace "karki ƙara cemin tsohuwa, ta ina nayi miki kama da tsohuwa? Da ƙuruciyata dudu shekarun nawa ba zasu gaza Ashirin da shida ba, amma kike kiramin tsufa"
Ai gaba ɗaya wanda ke tsakar gidan ba wanda be dariya ba, Widad tace "A'a kin manta a zanin goyo kike ma ƙarewar yarinta, harfa jikokine dake amma kice shekarar ki Ashirin da shida, shekarar ki biyar akamiki Aure kenan"
Hari tace "koma yane dai, niba tsohuwa bace ba ehee, dan jina nake garas kamar 'yar shekara goma sha shida"
Widad tayi dariya tace "dama zaki dinga gayune, za kiga yadda zaki koma yarinya sharaf, amma indai baki dena ƙazanta ba, to tabbas wataran za' a kalle ki ace shekararki sittin da 'yan kai"
Hari tayi kicin kicin da Fuska, dan Widad ta fara kaita bango, idan ta cigaba da biye mata to tabbas za suyi ba daÉ—i, dan haka tayiwa Widad banza.
Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsinke zogale ta zauna tace "Hindatu, ya ki keyi? bari in tayaki"
Hindu Ta gwadawa Widad yadda ake tsintar zogale, ta zauna suna yi tare.
Can Widad tace "Hindu, wai kuma idan kuna period bakwa amfani da pad ne? Se tsimma"
Hindu tace "meye kuma firiyios?"
Widad tace "A'a ba kije makaranta bane? Me yasa Common things idan na faÉ—a, seki ce baki sani ba?"
Hindu tace "bari Amarya wallahi muna son karatun nan, amma ba yadda muka iya ne, kinga inda muke zuwa makarantar furamarai can wani ƙauye ne, kusan ƙauyuka biyar duk ita muke zuwa, to guri ba kusa ba nisa kafin kaje duk anyi wani abu baka nan, lokacin damuna kuwa bama samun zuwa, sannan akayi ruwan Sama me ƙarfi ya kwashe kwanon da'aka rufa azuzuwa, ai kuwa akace mu dena zuwa se an gyara, dan haka tun aji huɗu furamarai nidai na dena zuwa har yanzu "
Widad tayi shiru, ita ko a tatsuniya bata taɓa jin wannan al'amarin ba, ace a Nigeria akwai 'yan ƙasa wanda basa samun ilimi, ina wakilansu? Meye amfanin shugabannin da suka zaɓa suka wakilta dan suyi musu aiki? Ace ƙauyuka huɗu su dogara da primary ɗaya, kuma shima se sun sha baƙar wahala kafin suje, dole abun ya fita daga ransu'
Widad tace "gaskiya banji daɗi ba Hindu, ai Ilimi shine mutum, tabbas da'a bakin wani naji cewa zanyi ƙarya ne labarine kawai"
Hindu tace "aikuwa gashi a zahiri kinji, shiyasa duk muka haƙura wasu suka kama talla har zuwa lokacin da mace zata samu miji tayi Aure, dama idan kana karatun wasu kallon ɗan iska suke maka, muka koma zuwa ta Allo ta Allonma gata nan dai nidai na samu nayi izu biyar na haddace itama munyi yawa, babu wata kulawa yadda yakamata, dan anan wajejenmu makarantar Allo ɗaya ce"
Widad ta jinjina kai tace" to sauran litattaafai fa, kamar Ahlari, fiqhu hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam, suma ana koya muku? "
Hindu tace" Taɓɗijan, Al'qur'ani kawai ake koya mana a makarantar Allo, kuma shima mun dena zuwa, se Baffanmu ne dai da yana koya mana Alhadisin Auwwalu, shima yace mana Babansa ne ya koya masa, kuma ma yanzu duk mun manta tunda shekarun da yawa "
Widad kawai tayi tagumi tana sauraren Hindu, tana jin kwamacalar da ko a Film bata taɓa ganin irinta ba, yanzu dama da irin wannan mutanen suna rayuwa a haka, amma ake samun mutanen da suke wawashe dukiyar al'umma, a 'ya' yan sanatoci akwai wanda tasan ana biya musu ku&in makaranta na secondary naira milyan uku, duk term miliyan ɗaya, iya 'yan tsirarin' ya'yansa, amma ga dubunnai zaune a gida babu arabi babu boko, irin wannan ne idan suka faɗa harkar ta'addanci basa imani sam.
Hindu ta kalli Widad tace "ya naga kinyi shiru ne?"
Widad tace "Mhmm bakomai"
Hindu tace "Yawwa, dan Allah meye Firiyas É—in da kika ce?"
Widad tace "Period nace, ina nufin jinin Al'ada"
Hindu tace "Auho ai ban gane ba, seki cemin baƙon wata, ai mu da tsumma mukeyi, mu yayyanka tsumma semu dinga amfani dashi, duk wanda muka cire se mu wanke mu ninke"
Widad ta kalleta da sauri tace "ku wanke me?"
"tsimmar mana, idan É—an kamfan mutum É—aya ma haka ze haÉ—a duk ya wanke, ya É—an jira ya bushe seya sake mayarwa"
Dafe kai Widad tayi, tayi shiru ta shiga duniyar tunani, ta tuna yadda take fantamawa a cikin kuÉ—i, babu abunda ta nema ta rasa a rayuwar ta, Kama daga Abinci, sutura abun hawa gurin kwana, har wasu kuÉ—i ne da ita na musamman wanda take kula da dabbobinta kawai, tayi kyautar mota, tayi kyautar gida ta bada kuÉ—i kamar aikin banza, ashe akwai bayin Allahn da sun fidda rai da samun wani jin daÉ—i.
Hindu tace "Amarya, Allah yasa ba wani abun na miki ba, naga kin ɓata rai?"
Widad tace "bakomai Hindu, mu cigaba da aikin kawai"
Widad bata iya tsinkar zogalen ba, dan haka wani yanayi wani kuma harda kararen jiki take zubawa, Hindu bata damu idan Widad ta zuba a haka se tabi tana gyarawa.
Hanne ce ta taho a fusace tasa hannu ta ɗauke robar da suke tara zogalen tace "Aikin banza, ke Hindu kin san ba abunda ta iya kawai kin ɗauki abu kin bata kinsa se ɓatawa mutane take, tana mayar mana da aiki baya kin zauna se surutan shirme ki keyi, da yanzu an wanke an ɗora amma duk ta ɓata mana"
Hindu tace "Haba Hanne, to ba a hankali zata iya ba, kuma ai tayani take tana yi ina gyarawa, meye a ciki dan munyi tare"
Tsaki Hanne Tayi, tai gaba da robar zogalen, Widad ko É—aga kai ba tayi ba balle ta kalli Hanne, tayi shiru ba tace komai ba.
Cikin damuwa Hindu tace "dan Allah Amarya kiyi haƙuri, ni ban san meyasa take wannan abubuwan ba"
Widad tayi murmushi tace "Ni banyi fushi ba ai, bakomai"
Saleh ya É—au waya ya kira Abbas, sedai har tayi ringing ta katse be É—aga ba, tana katsewar ne Abbas ya biyo kiran, Saleh ya É—aga tare da yin Sallama Abbas ya amsa, Saleh yace
"Malam Abbas, kayi gaba ko waiwaye baka yi, kana da labarin an sace amininka kuwa tare da 'yar gidan Daula?"
Abbas yace "ƙwarai kuwa na sani, dan nine ma na gayawa mahaifiyarsa"
Saleh yace "Wani tunani kayi akai kuwa?"
"wani tunani zanyi kuwa, maganinsa kenan ai, shegen shishshiginsa da rawar kai yaja masa, ni Allah ne ya dube ni, dani naso in maye gurbinsa da dani za'a ɗauke, Amma kuwa an karɓi files ɗin daga hannunsa?"
Shiru Saleh yayi sannan yace "basu karɓa ba tukuna, ni suke jira, har yanzu basu san cewar Yusuf ne jami'in tsaron ba, zancen da nake maka yanzu haka Yusuf sun tsere daga inda aka ɓoye su"
Abbas yace "haba dai, garin yaya akayi suka tsere? Kai Yusuf fa ba ƙaramin hatsabibi bane ba"
Saleh yace "babu wanda ya sani, kuma har suka gudu ba'a samu karɓar abun nan daga hannun yarinyar ba, yanzu maganar da nake maka, shi kansa Daulan an ɗauke shi a gadon Asibiti, babu wanda yasan inda yake"
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, garin yaya, yanzu shikenan munyi biyu babu, nifa ba wanda yake tuntuɓata yanzu tunda akamin transfer"
Saleh yace "karka damu, ina son ka saurareni da kyau, duk abunda ake ciki zan dinga sanar da kai, karka kusakura wani daga cikin su yayi yunƙurin haɗa kai da kai, dan yanzu gaba ɗaya kawunansu a rarrabe yake, duk wanda ya tuntuɓeka koya tambayeka wani abu game da wanda aka bawa binciken nan kace baka sani ba"
Abbas yace "to aini basu sanni ba, kai suka sani me zesa su nemeni?"
"Abbas mutane ne masu wayo matuƙa, yanzu haka a manyanka na gurin aiki wani ze iya bugun cikinka ya tambayeka wani abu, karka kuskura ka gaya wani, wani abu akan harkar nan, na gaya maka kansu ya rarrabu, wasu zasu iya zamewa suyi harkar nan babu mu, bayan wahalar da mukayi "
Abbas yace " bakomai na fahimce ka, Insha Allah babu wanda zeji wata magana daga bakina, dama kai ka jawoni cikin harkar "
Saleh yace " Good nagode "
Sukayi Sallama, Saleh ya jinjina kai yanzu ya sake jinjinawa Widad, lallai bata da laifi naƙin yadda da mutane, ƙir ƙiri Abbas na jikin Yusuf ne, amma saboda kuɗi yake masa zagon ƙasa, tabbas mutum abun tsoro ne, kuma da alama Abbas Soko ne, dan haka yi masa wayo ba wani abu bane me wahala.
Saleh yana son sake komawa gurinsu Widad, dan haka yana ta É—anyi musu siyayya.
Alhaji Musa ne ya kira shi a waya yace 'lallai yana son ganinsa a guest house É—insa'
Haka Saleh ya bar abunda yake yi ya tafi gidan Alhaji Musa.
Yaje ya tarar dashi a lambun dake gidan, suka gaisa Alhaji Musa yace "Saleh ina cikin damuwa fa"
"wace irin damuwa kuma ranka ya daÉ—e?"
"Na fuskanci Nurat tana ƙoƙarin fara yin shisshigi ga al'amuran Daula, gashi yanzu ina ɗari ɗari da su Haruna, ina tsoron Ayi Amfani da ita a cutar da ita koni, yanzu babban abunda ya sake bani mamaki be wuce yadda Daula yayi ɓatan dabo ba, ko kusa ko alama an rasa inda yake, zargina yana ƙara tabatta akan ana min maƙarƙashiya, kodai su Alhaji Haruna suke cuta ta suke al'amuran su suka ɗai, kokuma akwai wani a gefe daya ke harin abunda muke hari, ko kuma yasan siriinmu yake son temakawa Daula"
Saleh yayi ajiyar zuciya yace "banƙi ta taka ba, Amma ko waye wannan tabbas na jikin ku ne, amma abun da mamaki ace an nemi Daula ko sama ko ƙasa an rasa sekace wata takadda"
"Shine abunda ya É—auremin kai ai, ni yanzu gefe zan koma in nemawa kaina mafita, idan abun nan ya samu shikenan, in be samu ba shikenan, suma har yanzu da suka gudu babu wanda ya sake jin É—uriyarsu, dan haka ni inaga tunda babu wanda yasan inda Daula yake, zan fito takarar Senate ne kawai "
Da sauri Saleh ya kalle shi yace " Amma ta yaya kake tunanin mutane zasu yarda su zaɓeka? Bayan Daula ya riga ya ɓata siyasarka a idon duniya? "
Alhaji Musa yace " shiyasa nima na ƙuduri aniyar kota wane hali, sena Wulaƙanta Daula a idon duniya, sannan malamai zan shiga a rufemin bakin jama'a, akwai yarana da suke aiki a wasu daga kamfanunukan Daula, zamu haɗa kai dasu mu karkatar da wasu kuɗaɗe inyi amfani da su, niba kuɗin Daula ne sjka dameni ba, yadda zan Wulaƙanta shi in ɗaiɗaita shine ya dameni, amma ko yanzu na rage raɗaɗin dake zuciyata, kuma zan cigaba da bibiyarsa se naga babu inda ya rage wanda ze jingina yaji daɗi, sannan in dawo kan su Alhaji Munir"
Yadda Alhaji Musa ke maganar babu alamun tausayi ko imani a tare da shi, har zuciyarsa yake faÉ—ar wannan maganganun.
Saleh ya ɓoye duk mamakinsa, ya dinga ziga Alhaji Musa, Alhaji Musa ya kawo kuɗi ya bawa Saleh, Saleh a ransa yace "ka bada kuɗin da zanyiwa maƙiyan ka siyayya, kuma nima zancigaba da bibiyarku, ɗaya bayan ɗaya sena ɗau fansar cin amanata da kuka yi, da saɓa Yarjejeniyar da muka yi daku"
Widad gaba É—aya hirar da suka yi da Hindu ta tsaye mata a zuciya, ta tuna yadda haka siddan se É—an kasuwa yayiwa É—an siyasa kyauta motar miliyoyi, ko biliyoyin nairori, Amma al'ummar su suna tagayyara, da yunwa da rashin kyakkyawan mahalli.
Yusuf yaga gaba ɗaya Widad tayi wani iri, seta zauna tayi shiru tana tunani, dukda shima zuciyarsa ba daɗi, Amma sam baya son ganinta a damuwa dan haka yace "Ran gimbiyata ya daɗe meke damunki ne?"
Jiki a sanyaye tace "Abubuwa da yawa"
Yusuf yace "Kamar me? Ko har yanzu fushin kike dani"?
Jiki a matukar sanyaye ta bashi labarin hirar da suka yi da Hindu, daga ƙarshe tace "tabbas ƙaddarar data sameni na zuwa ƙauyen nan, ishara ce Allah ya nunamin, na rayu cikin gata wanda nake ganin babu wani abu da zan iya nema in rasa a rayuwata, ranar da kace min akwai mutanen da Naira ɗari take gagararsu, gani nake kawai ka faɗane dan ka rainamin hankali saboda a lokacin, abun da ke cikin asusun bankina ya ninka ɗari sau ɗari, bani da wata damuwa ko matsala, Amma ace a rayuwa akwai tarin 'ya' ya mata da suke zaune ba ilimi? Akwai tarin mutanen da suke rayuwa da gurɓataccen ruwan sha? Akwai tarin yara manyan gobe da rayuwarsu ta lalace saboda rashin gurin samun ilimi, Yoseef yaran masu kuɗi na Almubazzaranci da dukiya, da yawanmu bamu san yadda aka tara kuɗin ba... Kasa ƙarasawa tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, wani irin ɓacin rai ke taso mata, yadda ake ɓarnar kuɗi gurin bukukuwan birthday dana Aure, da makamantan su.
Yusuf ya taso daga inda yake, yazo ya samu guri ya zauna kusa da ita yace "Widad baki ga komai ba, a yanzu haka a cikin ni'ima muke, a gidan megari muke a zaune, kuma gidansa da rufin Asiri, ya kike tunanin gidajen sauran talakawa da suke garin nan? Wanima abunda zasu cin ma babu, Widad talauci gaskiya ne, shiyasa Wulaƙanta mutane bashi da kyau "
Widad tace" tabbas wulaƙanta mutane bashi da kyau, nasan mutane dayawa sunamin kallon mace me izza da Wulaƙanta mutane, sedai...
Se kuma tayi shiru, Yusuf yace "sedai me?"
"Bakomai" ta bashi amsa tare da basar da zancen.
Da Asuba bayan Yusuf ya dawo daga sallar Asuba yazo ya tattara kwanuka zeje ya wanke, Widad tace "ka bari zan wanke"
Yusuf yace "No ki huta kawai, bari in wanke ai ba yawa kwanukan"
Widad tace "ce maka akayi ban iya wanke wanken bane?"
"Ni na isa ince gimbiya bata iya wanke wanke ba?"
Widad tace "gashi nan kuwa ka faÉ—a"
"A'a ni ban faÉ—a ba, taso muje muyi tare"
Widad ta tashi tabi Yusuf suka je suka wanke kwanukan tare, ta tattare duk kwanukan wanke wanken da'akayi fatali dasu na Abincin dare a tsakar gidan, ta haÉ—esu a guri É—aya, Yusuf yasa tsintsiya duk girman tsakar gidan yana sharewa, Widad ta dinga kallon ikon Allah, yadda Yusuf yake sarrafa tsintsiya kamar mace.
Widad tace "dan Allah dagaske kai ka É—aine a gidanku?"
Yusuf yace "Eh nikaÉ—ai ne Mamana ta haifa, ni nake mata aikin gida, shara, wanke_wanke hadda girki duk ta koyamin ni nake yi, idan ta tafi unguwa kafin ta dawo nayi komai"
Widad tace "shiyasa ka iya aiki sosai, nima nasan da tare na girma da Ammi na da duk na iya aiki, da baza'a dinga kallon ban iya komaiba"
Yusuf yazo kusa da ita ya tsaya, ya kalleta yace "karki damu gimbiyata, Insha Allah muna tare zaki iya komai kafin mu koma gida"
Widad ta kalle shi tace "dagaske har girki zaka koyamin? Nafa iya girki amma ba sosai ba"
Hannu yasa ya ɗago haɓarta yace "zaki iya komai insha Allah, duk zan koya miki, amma bana son taurin kai, dan nasan halinki"
"Nice me taurin kai?"
Yusuf yace "eh kina dashi amma kaÉ—an"
Murmushi Widad tayi tace "Ni dai in zaka koyamin zanyi duk abunda kake so"
Yusuf yace "dagaske?"
Widad ta jinjina masa kai, ya matso daf da ita yace "to shikenan, Yimin kiss a goshina ma ba'a baki ba, se in koya miki kunna risho yau"
Tureshi tayi tace "Baza'ai wannan É—inba"
Matseta yayi a jikin bishiyar ya riƙota, cikin sigar magiya yace "please Gimbiyata, ko sau ɗaya ki nuna kin damu dani please"
Cikin tsiwa tace "to Jaririne kai? Ko goya ka zanyi?"
Kwantar da kansa yayi a kafaÉ—arta yace "to goyanin mana, ko daga nan zuwa É—akine"
"Eh ba shakka, ba kunya wai in goya ka, sakeni ko in cijeka yanzun nan"
Hanne ce ta fito daga É—akinsu, tana fitowa idonta ya sauka akan Yusuf da Widad dake tsaye a jikin bishiyar ceÉ—iya dake tsakar gidan, kamar zasu shige jikin juna.
Da ƙyar ta haɗiye wani irin mugun yawu a wuyan ta, ta koma cikin ɗakinsu tana fesar da numfashin baƙin ciki.
Hindu ce ta Kalle ta tace "Hanne lafiya kuwa?"
Hanne tace "wallahi Hindu na tsani matar Yusuf, ji nake kamar in shaƙeta"
Cike da mamaki Hindu ta kalle ta tace "kamar yaya kin tsane ta?"
Hanne tace "Hindu dan Allah kina ganin Yusuf ze iya Aurena?"
Wani mugun kallo Hindu tayi mata tace "Anya kina kallon kanki a mudubi kuwa? Kina ganin mace jawur, kalle ki kice kina son mijinta, matar nan fa tana miki kawaici akan Mijinta, kiyi ta mata wulaƙanci amma tana ƙyale ki, karki kuskura Gwaggo taji wannan maganar da kike"
Hanne tace "ba zaki gane ba Hindu, wallahi Yusuf ɗin nan yana da kirki sosai, ita ba abunda ta iya se rashin kunya, gata bata da tarbiyya sam gata a wani taɓare, ga tsbar iskanci da rainin hankali, komai se tace bata sani ba"
Hindu tace "A'a wallahi tana da kirki, niba abunda tamin da zan zageta, kije kiyi ke kaÉ—ai, Allah ya yaye miki wahala, dan tabbas yana da wannan matar babu abunda ze dake"
Yau kam Widad ta É—an rage yiwa Widad rashin kunya, dan tare suka ci Abinci saboda tana son ya dinga koya mata aikin gida, dan tana jin zafin gorin da'ake mata, wai bata iya komai ba.
Bayan sallar la'asar Widad ta fito daga É—akinsu, dama gyara É—akin baya mata wahala da gyara gado duk wannan ta iya.
Hari ta hanga a inuwar bishiya tana saƙa mafici, Widad ta ɗakko kujera ta zauna a kusa da ita tace "Uwata ta kaina"
Hari ta harareta tace "Allah ya kiyaye in haifi 'ya irin ki, na haifi fitinanniya kamarki ai se ince ko sa kamun hannu akayi"
Murmushi Widad tayi tace "ba wannan ba, É—an koyamin wannan abun da kike yi mana, idan na iya se in dinga ta yaki"
"Lallai nasan ba iyawa zakiyi ba"
Widad tace "Allah zan iya"
Hari tace "Keɗin ce zaki iya, taɓ"
Widad tace "ni zaki wulaƙanta dan zaki koyamin abu? Shikenan"
Hansai tace "Amarya ba wahala, nima na iya zan koya miki"
Widad tace "Yawwa ummu Sani, thank you very much, May Allah subhanahu wata'ala bless and unite your Family"
Hari tace "kekam wudas akwaiki da tsirfa, meye hakan kuma kika faÉ—a? Ke ba zaki iya magana ba sekinyi yaren Yahudawa, kiyi ta zagin mutane"
Widad tace "aini kona rasa abun zagi, bazan zageki ba"
Hindu tace "Nidai dan Allah amarya ki koyamin turanci, ina son inga na iya"
Widad tace "Shikenan, zan koya miki insha Allah, amma nima zaki dinga koyamin abunda ban iya ba"
Hindu tace "duk abunda kika ce zan koya miki"
Gwaggo na gefe tana jinsu, tana murmushi, sam Widad bata da girman kai idan bata iya abuba, zata yi ta magiya a koya mata.
Da Yamma aka kawo manyan Ayaba daga gonar megari, aka raba aka bawa kowa, Widad se murna take dan tana son Ayaba, ajiyewa taje tayi a É—aki tace, se Yusuf yazo zasu raba.
Yau Yusuf se gefin magariba ya dawo gidan, ya gaji sosai.
Tunda ya samu ya watsa ruwa ya dawo É—aki ya kwanta, salla ma a gida yayi.
Widad tace "Yoseef ga Banana, an bamu daga gonar megari aka cirota, nace in ka dawo semu raba dan idan na fara ci, bazan iya rage maka ba"
Murmushi yayi yace "bani guda É—aya kawai ta isa, kici Abunki"
Ta ɗan ɓata fuska tace "saboda me bakaci? In ajiye maka abu kace ba zaka ci ba"
"i don't have appetite, that's why"
Ta kalle shi tace "kamar yaya?"
Rungume ta yayi a jikinsa, ya kwantar da kansa a kafaÉ—arta yayi shiru.
Widad ta kalle shi da sauri tace "Subhanallah, ai baka da lafiya jikinka yayi zafi sosai fa"
Yusuf yace "karki damu zan warke insha Allah"
Yana nan rungume da ita, yana ta juya kansa a jikin ta, tana jin yadda jikinsa yake tsuma jikinsa na ƙara ɗaukar zafi.
Widad cike da damuwa tace "Yoseef jikinka zafi yake sake É—auka fa"
Kasa magana yayi, sosai jikinsa yake rawa, da sauri ta miƙe ta ɗakko bargo ta rufa masa.
Haƙoransa se karkarwa sukeyi, ta ɗebo ruwa ta duba kayan ta, ta ɗakko wata vest ɗinta, ta shiga shafa masa ruwa a jikinsa, amma kamar tana ƙara rura masa wuta, jifa tayi da abunda take jiƙa masa jikin ta rungume shi ta fashe da kuka.
Share, share and share please 🙠ðŸ™
(insha Allah ranar 20th ga wata zan fara posting ɗin book 2&3, befi saura page biyu ba in kammala book 1, nagode ga wanda suka fahimceni, wanda suka zageni ma nagode, wanda suka shirya siya zasu iya tuntuɓata ta wannan lambar 07063065680 nagode ƙwarai dagaske, a nunamin ƙauna ta hanyar siyan littafin akan farashi me rahusa, Akwai garaɓasa ga mutum biyar ɗin farko da suka fara siya, cakwakiya da warwara suna book 2&3 don't missed it guys sena jiku"
Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680
            _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITEDÂ (BANYI EDITING BA)
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 42_43
Sosai Widad ke rusa kuka, Yusuf kasa magana yayi sedai ya ƙanƙameta a jikimsa, yana dukan bayanta da sigar rarrashi.
Can ta miƙe cikin hanzari ta fito waje, tana ta goge Hawaye ta samu Gwaggo tace "Mama Yoseef bashi da lafiya"
A gigice Gwaggo tace "Subhanallah, meya sameshi?"
Maimakon Widad tayi magana seta fashe da kuka, Hanne da take wanke wanke take ta dire kwanukan ta miƙe tsaye.
Gwaggo tace "Yi shiru, muje muga jikin nasa"
Hansai ma da Hari gaba É—aya jikinsu yayi sanyi, É—aki gwaggo tabi Widad ta tarar da Yusuf yana ta karkarwa a cikin bargo.
Gwaggo tace "Subhanallah, sannu Yusufa Allah ya baka lafiya"
Be iya magana ba se jinjina mata kai da yayi, Hari tace "Yaya meya abunyi yanzu, ga Malam baya nan yaje taronsu na masu sarauta"
Hansai tace "ina sauran saiwoyin nan, a jiƙa a bashi mana, kan malam yazo asan abunda yakamata ayi"
Widad ta koma kusa da Yusuf, tana ci gaba da share Hawaye, Hansai tace "Kidena kuka in Allah ya yadda ze samu lafiya"
Hanne ce ta shigo ɗakin itama, ta leƙa taga yadda Yusuf ke rawar jiki, gaba ɗaya se taji jikin ta yayi sanyi, a ranta tace 'dama wannan kinibabbiyar zazzaɓim ya kama'
Suka dinga rarrashin Widad, yayin da Yusuf ko iya ɗaga kansa ba yayi, Hansai ce ta kawo wasu jiƙe jiƙe wai a bawa Yusuf, Widad ta kalli kwanon ta girgiza kai, cikin kuka tace "A'a wannan abubuwan suna da hatsari ga lafiya, nidai a kai shi Asibiti kawai"
Hari tace "Asibiti, ai kuwa ya mutu ba'a jeba, dan daga nan kafin aje Asibiti har mutum ya mutu akai gawarsa ba'a isa ba"
Sake rushewa Widad tayi da kuka tace "In Allah ya yadda baze mutu ba, semun koma gida tare, dan Allah Yoseef kaji sauƙi"
Gwaggo tace "Hari kina da matsala wallahi, wace irin magana ce haka ba tsari, kalli yadda kika sake tayar mata da hankali fa"
Hari tace "Wallahi Yaya ni bada wani abu na faɗa ba, misali dai na bata, amma Wudas kiyi haƙuri, Insha Allah ze warke amma Asibiti kam kafin aje shi sedai idan amalanke za'a samo a ɗorashi, a fita can wajen gari sannan...
Hansai tace" haba Hari, ana rarrashin ta kina ƙara Sakata kuka, Amarya karki damu insha Allah za'a kai shi Asibiti bari Malam yazo "
Widad ta riƙe hannun Yusuf tana ci gaba da kuka, Hanne tace " Sannu Allah ya baka lafiya "
Har magariba sannan megari ya dawo, ya tarar da zancen rashin lafiyar Yusuf, megari yace " me aka bashi na magani? "
Hansai tace " Na jiƙo tazargade nace a bashi, matarsa tace baza'a bashi ba sedai akai shi Asibiti"
Megari yace "Kin san mutan birni, basu fiye amfani da irin wannan magunguna namu ba, Amma yadda za'a kai Yusuf Asibiti nake ji, kafin Aje ya ƙara galabaita, dan miƙaƙiyar tafiya ce ta gaske"
Widad tace "Yanzu duk garin nan babu Asibiti, ko chemist babu?"
Hindu tace "kamis É—ayane a garin nan, shima a cikin kasuwar yamma da gari yaje, ba'a buÉ—eshi se ranar kasuwa"
Dafe kai Widad tayi tana faÉ—in "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wane irin abune haka, gari kamar wannan me É—auke da al'umma suna rayuwa a ciki, ace babu gurin shan magani, Yasalam sannu Yoseef Allah ya baka lafiya"
Bece komai ba, se riƙe hannayenta da yayi, da hannu yayi mata nuni da zeyi alwala, Gwaggo ta bada ruwan ɗumi, Widad ta sirka masa, se a ɗaki yayi alwalar dan ko tsakar gida baya iya fita, saboda azabar sanyin da yake ji.
A zaune Yusuf yayi salla, Widad idanunta har sunyi jawur saboda kukan da tayi, ta kalle shi tace "me zaka ci? Kaga tun safe baka ci Abinci ba"
Girgiza mata kai yayi, alamar baya son komai "
Ya nemi guri ze sake kwanciya, Widad tace " kwanciyar nan zata ƙara kashe maka jikine, ka bari gobe in Allah ya kaimu duk yadda za'ayi za'a san yadda za'a kaika Asibiti kaji, sannu Allah ya baka lafiya "
Ta ƙarasa maganar idonta fal hawaye.
Murmushi Yusuf yayi, ya kai hannunsa dake rawa fuskarta ya goge mata hawaye tare da girgiza mata kai, alamar ta dena kuka.
Haka Widad ta raba dare ba tare da tayi bacci ba, data motsa sedai tayi ta shafa masa ruwa, amma jikinsa kamar wuta.
Tun tana yi da ƙarfinta, har bacci ya mamaye idonta ta kife a gurin tana bacci, a haka ya janyo ta jikinsa, yana kaɗe mata sauro yayin da ya kasa bacci saboda azabar ciwon gaɓoɓi da zafin zazzabi.
Da Asuba Widad ta farka, tana buÉ—e ido tace "Yoseef"
Da Mm ya amsa mata.
"baka yi bacci bane?"
"Nayi ya faÉ—a a hankali"
"ya jikin naka?"
"Naji sauƙi, samomin ruwan Alwala"
Ta miƙe ta fita waje, ta kawo masa ruwa yayi alwala yayi sallar Asuba.
Gwaggo tayo kunu ta aikowa da Yusuf, kasa sha yayi saboda yana jin jiki, amma saboda kukan da Widad take, ya karɓa ya sha kaɗan, haka nan ya amayar da shi gaba ɗaya, nan fa abun duniya ya ishi Widad, ta kasa cin Abinci se kuka.
Megari ya tashi É—ansa, yace "yaje can gaban su, ya aro babur azo a tafi da Yusuf Asibiti"
Har wajen ƙarfe sha ɗaya Widad tana tare da Yusuf, ko tsakar gidan ta kasa fita, ta kama yatsunsa tana ja masa a hankali kamar yadda yake mata, sam taƙi cin komai.
Wajen sha biyu na rana Saleh yazo gidan, zuwan Saleh ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, Megari yace "Alhamdilillah, kazo a dai dai, dama Yusuf yana kwance babu lafiya na aika azo ds babur a kai shi Asibiti, tun jiya ko magana baya iyayi"
A gigice Saleh ya tafi ɗakin su Widad, Hindu da Hanne dasu Gwaggo suka bishi dan a yanke shawarar ƙarshe game da rashin lafiyar nasa, Saleh yayi Sallama Widad ta amsa, ya shiga ɗakin ya tarar da Yusuf ya ɗora kansa akan cinyar Widad, idanunta sunyi ja har sun fara kumbura.
Seda Saleh ya É—anyi turus dan tabattar da abunda yake gani, wanda ko a wasan kwaikwayo akace Widad zata yi hakan baze yadda ba.
Ya ƙarasa cikin ɗakin, ya kalli Widad yace "meyasa me shi haka?"
Tsuke Fuska tayi sannan tace "zazzabi yake"
Ya kalli Yusuf yace "Sannu Yusuf, bari inje wannan sedai ko mota a samu, ba zaka iya hawan babur ba, se inzo akaika Asibiti"
Yusuf be iya cewa komai ba, se jinjina masa kai da yayi, tun a hannun wanda suka sace su Widad ta jinjinawa jarumta irin ta Yusuf, tunda harta kai ga baya magana to tabbas ta tabbatar yana jin jiki ƙwarai.
Saleh yace "Ranki ya daÉ—e bari inje a duba motar ko, se a zo a tafi dashi"
Cikin isa da take nunawa ma'aikatanta tace "ina fatan kaga halin da yake ciki, dan haka bana buƙatar ɓata lokaci, duk inda abun hawa yake a nemo azo a kai shi Asibiti, kar ya sake galabaita"
Mamaki ne ya kama su, Yadda Widad take wa Saleh magana cikin isa da gadara, dukda irin taimakon da yayi musu, ga kuma tarin tazarar shekaru da ya bata, amma take masa wannan isar haka, se suka ga ta canza kamar ba Widad É—in dake magana sanyi sanyi ba.
Saleh ya ɗago ya ɗan ƙurawa Widad ido na wani ɗan lokaci.
Cikin tsawa tace "Kamar na gaya maka bana son ɓata lokaci, ka tsaya kana kallona, he's condition is getting worse, ko nawa za'a kashe ayi a nema masa lafiya" tai maganar tana wani sauke wahalallen numfashi.
Cikin harshen turanci Saleh yace "You are under my care now, why are you still shouting at me like this, so you are still rude up to now"
"My name remains Widad Nasir, Nothing will make me change, No matter what you did to help me, my policies remains constant, nothing has change"
Cikin rawar sanyi Yusuf ya shiga girgizawa Widad kai alamar tayi shiru.
Sudai mutan gida se binsu su kayi da ido.
Hanne ce taja wani uban tsaki tace "Aikin banza, ace mutum baya ganin girman kowa, se tsabar wulaƙanci da rashin ta ido"
Da sauri Saleh yace "Ke dawa kike? Idan kika kuma gangancin yin wannan mummunan furicin akanta duk abunda ya biyo baya ke kika siya, ko dan kin ganta zaune a gidanku, kin sam wace ita?"
Gwaggo tace "ayi haƙuri dai, naji tsayuwar Babur a waje, ina ga Ila ne ya dawo, maza jeka ku samo akori kura a kai shi Asibiti"
Haka akayi, Saleh yaje suka hau babur suka tafi nemo akori kura.
Sosai Fahad ya fara missing ɗin Ramlah, dan ba ƙaramin hutawa yake da ita ba, itama a ɓangarenta tana missing ɗinsa, amma tana so ta tabattar da idan dagaske yana sonta, kamar yadda Amal ta goranta mata.
Fahad ya É—au waya ya kira Ramlah, tana ganin kiransa babu ko jan aji ta É—auka da rawar jiki
"Hello Baby, shine kika watsar dani ko?"
"ba watsar da kai nayi ba, kaine ka watsar dani ka kasa Yimin abunda na tambayeka"
"Ramlah ki gane, baƙi nayi ba fa, kin san halin Daddy, ko zancen baya so na ɗakko masa, yaƙi saurarata sam gashi bani da lafiya se tunaninki nake, kuma nasan damuwa ce tamin yawa"
"dan Allah dagaske baka da lafiya? Ai ban sani ba, ohhh Sorry please i understand you, nasan kana son za kayi iya ƙoƙarin ka, bakomai hakanma nagode sosai my love"
Yayi ajiyar zuciya yace "Never mind baby, yanzu ya za'ayi ne? Inzo mu É—an fitane yau É—in?"
"Ni gaskiya a'a"
Ya ƙara marairaicewa yace "please na, ko so kike ace kizo ga gawata?"
"No bazata kaimu ga haka ba, kazo anjima mu fita, kasan bana son dsmuwarka my one"
"wow that's my only Ramlah, na ɗauka nikaɗai nake sonki na damu dake ai, shikenan dan Allah ki ƙure a daka, kiyi kwalliyar nan wadda ke narkamin zuciya"
"shikenan karka damu, sekazo"
Sukayi Sallama Fahad yace "akanme zanso a sako wani Anwar, yazo ya hanani rawar gaban hantsi, ai gara ayi ta tsare shi a can kowa ma ya huta.
Wasa2 labari ya karaÉ—e gari, an nemi Daula an rasa, abu kamar wasa kusan sati biyu amma babu ko wanda yaji É—uriyarsa, Alhaji Munir ne da Alhaji Haruna zaune a office, sunyi jugum jugum.
Alhaji Munir yace "Nifa gaba ɗaya abubuwan nan suna nema su kwaɓe, wai kamar almara har yanzu babu ɗuriyar Daula, babu ta wannan shegiyar 'yar tasa me baƙin taurin kai kamar ubanta, kuma gashi an ɗaga taron kasuwanci komai ya watse, nifa gaba ɗaya na fara karaya"
Alhaji Haruna yace "wace irin karaya kuma? Ai ba gudu ba ja da baya a wannan harkar, mun ɓata shekaru da dama akan wannan sabgar, kawai kuma semu sare yanzu, a'a baze yuwu ba, ni yanzu na fara tunanin anya ba wanine yake mana maƙarƙashiya ba?"
"Hmm bari kawai, ni kaina nayi tunanin hakan, an tuhumi doctor Sufyan har yanzu yace be san komai akan ɓatan Daula ba, ga ɗan gidan Hajiya Halima shima da yake kula da Daula, an tsare shi amma yace besan komai ba, wannan wane irin lamarine haka?"
Alhaji Haruna yace " Wani abun haushin ma, Halima se shiga take tana fita a sakar mata É—anta, tana neman ta tona mana Asiri "
Alhaji Munir yace " Ai duk wata sabga daza'a saka mata a ciki, to tabbas za'a sha takaici, tun farko nace kar a saka matar nan amma aka ƙi bin shawarata, gashi nan komai se kwaɓewa yake"
"Haba Munir, kai badan da temakonta ba ai da wata nasarar bamu sameta ba, ta bamu gudunmuwa sosai, sedai yanzu tana neman ta ɓata rawarta da tsalle"
Alhaji Munir yace "Kai ba wannan bama, kasan se siyar da manyan motocin Daula, tana ta holansuba ɓoye tana siyarwa, da wasu ƙananan kadarorinsa a ɓoye"
Zaro ido Alhaji Haruna yayi yace "bangane ba, kai waye ya gaya maka?"
"Al'amarin duniya baya ɓuya fa, nima labari naji kuma kana ganin mun fita wayo ne, kar take kallonmu matar nan mugun wayo ne da ita fa, tsohuwar 'yar duniya ce"
Shiru Alhaji Haruna yayi yace "Amma wannan ta cika muguwa, rabu da ita in tasan wata ai bata san wata ba, zamuyi magana da Musa, su tattauna da Bukar, muga yadda zamuyi maganinta"
Se wajen la' asar sannan Saleh suka zo da Mota, sedai akori kuran ta ɗanfi wadda aka kawo su ƙauyen a ciki, da ƙyar Yusuf ya miƙe Saleh ya riƙe shi, yana takawa a hankali.
Widad ta zuro Hijjabi tace binsu zata yi, Aikuwa Seleh yace "A'a base kinje ba, nida Ila da Megari za muje mu kai shi"
Ai nan da nan tasha gabansu ta tsaya ta kalli Seleh tace "wai kai a tunaninka har nayi yaddar da zaka É—auke shi ka tafi da shi, bayan ban san inda zaka kai shi ba, baze yuwu ba duk inda za'aje sedai aje dani"
Saleh yace "look, idan ina da nufin cutar daku, to da yanzu ba wannan zancen ake ba, ni bani da niyyar cutar ku, Asibiti zamu kai shi"
Megari yace "ki kwantar da hankalinki, Insha Allah babu abunda ze sameshi"
Kunyar Megari da Gwaggo ne yasa Widad fasa binsu, ta kalli Yusuf tace "Allah ya baka lafiya Yoseef, Allah ya kula da kai kamar yadda kake kula dani"
ÆŠagowa Yusuf yayi ya kalle ta, ya sakar mata murmushi suka yi waje.
Wajen ƙarfe Biyar na yamma, Anwar yazo gidansu Ramlah, ya kirata a waya ta fifo, har tazo falo suka haɗu da Amal, Amal ta kalli Ramlah tace "se ina?"
"zan fita ne" Ramlah ta bata amsa.
Amal ta jinjina kai tace "A dai dinga kula Ramlah, a dinga abunda ƙuda zebi, wannan gabtalin da kike ba yau ba gobe, ze ɓata miki suna ne"
"Ke dalla sauraramin, bana son shisshigi na gaya miki, ina ruwanki dsni ne? Kinfa fara isata na gaya miki"
Ta sa kai ta fice daga falon cike ɓacin rai.
Kai tsaye taje ta shige motar Fahad suka fita, Nura yace "Allah wadaran wannan shegiyar Ramlah me kama da balbela"
Isa yace "bari, iskancin da take mana a gidan nan ko Gimbiyar Daula ba tayi shiba, kullum suna titi ita da wannan me kai kamar tumatir É—in"
Murtalah yace "Ai har gara ma Amal da Anwar, Amma da matar gidan nan da Ramlah Allah ya tsine musu Albarka"
Isa yace "Ameen ya Allah, kalli duk manyan motocin dake gidan nan tabi ta siyar, kamar dasu tazo se facaka suke da kuÉ—i, Kai ta wani fannin yanzu bana ganin laifin 'yar masu gida da take musu rashin mutunci"
Murtalah yace "dama Hausawa sunce,' kada Allah ya kawo ranar yabo' duk rashin mutuncin da take Yusuf se yayi ta kare ta, se yanzu nake ganin gaskiyar zancensa da yace bata yiwa mutum wulaƙanci seya yi mata laifi"
Nura yace "Mhmm Ai kawai Allah yasaka mana, amma gidan nan ana abubuwa sedai fatan Allah ya kyauta"
Duk inda Hajiya Sarah tasan zata buga ta buga, amma anƙi sakin Anwar, gaba ɗaya ta rasa inda zata tsoma ranta, Anbi an toshe duk wata hanya da zata saka a samu belin Anwar.
Yanzu ma haka ta dawo fakan fakan kamar korarriya, a mugun guje ta shigo da mota gidan.
Tana shiga ta fara kiran "Ramlah! Ramlah! Ke Amal kuna inane?"
Amal ta fito tace "Mummy Ramlah fa bata nan"
"gidan ubanwa taje?"
Amal tace "sun fita ita da Fahad"
"zanci ubanta ita da Fahad ɗin kuwa, ai tunda ubansa ya watsa min ƙasa a ido, to tabbas zan masa rashin mutunci, zan nuna masa wacece Halima idan ya manta"
Amal tace "Mummy É—an uwan naki?"
"Eh shi É—in, tunda bani da kima a idon sa, nima zan nuna masa bashi da ita a nawa idon"
Amal tace "Mummy a bi dai komai a hankali, kar azo ayi aika aika"
Hajiya Halima tace "dalla rabu dani, ze gane ni ya taɓa, ai ɗa befi ɗa ba, yasani yaron nan besan inda aka kaai mutumin nan ba, amma se cemin yake wai in ƙyale doka tayi aikinta, na zagi dokar shi doka nawa yayi fatali da a rayuwar sa, zega tsiya"
Tai part É—inta tana cigaba da banbami, kamar wadda ke shirin Zarewa.
Saleh da Yusuf da É—an megari suka tafi kai Yusuf Asibiti, aka bar Widad da mutan gida tana ta faman yi musu kuka.
Gwaggo da Hindu ne suka iya zaman rarrashin Widad.
Hari tace wai ke Wudas daga miji na zazzaɓi seki zauna kita mana kuka, memakon ki masa Addu'a "
Ko kallon Hari ba tayi ba, ta miƙe ta tafi ɗakinsu tayi kwanciyarta tana cigaba da kuka.
Nurat suka dinga communicatinga da cousin É—inta akan yadda za'ayi belin Anwar.
Yanzu ma tana kwance akan gadonta hannunta É—auke da waya, tace" Brother ya ake ciki ne? Yakamata a gaggauta fitar da Anwar bashi da laifin komai fa"
"Nurat, kince bakyason asan muna ƙoƙarin belinsa, dan haka nake taka tsantsan, sedai abunda na gano shine tsare Anwar da akayi da manufa akayi shi, idan muka matsa tabbas za'a gano ke kikasa ayi belinamsa, tunda an san alaƙar dake tsakanin mu"
Cikin karaya Nurat tace "yanzu Brother babu abunda zaka iyayimin, Anwar be cancanci ya zauna a gurin nan ba"
Yace "Nurat, lawyan mahaifiyarsa ma yana ta ƙoƙari, amma har yanzu sun hana belinshi bansan meye abunyi ba, amma meyasa kika damu ya fita bayan kin san munin Alaƙar dake tsakanin mahaifinki da Daula?"
"Brother, idan akazo batun gaskiya da adalci ba'a kawo maganar alaƙa, an cutar da Anwar fiye da yadda kake zato, shikaɗai ne akan lamarin rashin lafiyar Alhaji Nasir, amma kalli abunda ya biyo baya, kodai an masa hakane dan a tozarta shi, ko kuma wanda ya sace shine yake son wanke kansa ta hanyar sawa a kama Anwar "
Barrister yace "Amma abun da mamaki ta yaya za'a iya sace mutum Attajiri kamar wannan a gadon Asibiti, kuma babu wani ƙwaƙwaran bayani, abun da mamaki fa"
Nurat tace "Brother, dan Allah idan kana da dama ina son kazo in ganka, ina son mu tattauna wani zance da kai dan Allah"
Barrister yace "Fara gayamin mana"
"A'a Brother, nidai so nake ina ganka, akwai magana ne a bakina"
"shikenan karki damu, Insha Allah idan ma samu lokaci zanzo insha Allah"
"Yawwa brother nagode sosai"
Ta kashe wayarta ta ajiye, shiru tayi abubuwa da dama suna damun zuciyarta, har yanzu bata ji alamar labarin inda su Yusuf suke ba, har yanzu bata sake jin wani magana game dasu ba, ta shiga tuna hirar da suka yi da Amal akan alaƙar Widad da Yusuf, ji tayi tana gumi dukda sanyin AC dake ɗakin nata, amma ta shiga haɗa gumi, miƙewa tayi ta tafi toilet da niyyar ta watsa ruwa ta rage damuwa.
Har bayan magariba babu labarin dawowar su Yusuf, nan fa Widad ta sake gigicewa, ta shiga sintir a gidan nan tana  "Allah ka duba Yoseef ka bashi lafiya, Allah ka bashi lafiya ba danni ba"
Gaba ɗaya tausayin ta ya hana Gwaggo nutsuwa, se aikin rarrashin Widad take, ita kuwa Hari harta ƙule saboda ganin abun na Widad take kama harda shagwaɓa dan taga ana lallaɓata, kawai dan mutum yana zazzaɓi ta cikawa mutane gida da ihu.
Dukda Hanne itama tana cikin damuwar rashin lafiyar Yusuf, amma ji take kamar ta make Widad, gaba É—aya ta hana mutane sukuni, se wani kuka take se kace wadda akace ya mutu.
Gwaggo ta zauna tasa Widad a gaba taci Abinci, amma ta gagara ci, Gwaggo tace "Amarya kiyi haƙuri, kici Abinci kinji, ki cigaba dayi masa Addu'a"
Cikin kuka Widad tace "Mama idan wani abu ya samu Yoseef sanadina ne, ba danni ba ba dan yasanni ba da duk baze shiga wannan halin ba"
Gwaggo tace "A'a kiyi haƙuri, Allah ne ya ɗora masa, kuma ze yaye masa"
Har dare basu dawo ba, ba Saleh ba dalilinsa, hankalin Widad ya sake tashi, yanzu take sake ganin Amfanin Yusuf a tare da ita, dare yayi tace bazata iya zama a ɗakin ita kaɗai ba, Gwaggo tace taje ɗakinta ta kwana, amma Widad fafur taƙi, ƙarshe Hindu ce tabi Widad ɗakinsu ta tayata kwana.
Har yanzu hankalin Umman Yusuf yaƙi kwanciya, rashin Yusuf a tare da ita ba ƙaramin abu bane a gurinta, sam rayuwa kawai take ba dan tana jin daɗin rayuwar ba, Yusuf shine ɗanta ɗaya tilo, yau a sanadin aikinsa yayi nesa da ita, bata san inda yake ba, gashi a hukumance babu wanda yace mata komai, se Suleiman da yake sintirin zuwa ganinta yana kwantar mata da hankali.
Wataran a ɗakin Yusuf ɗin take kwana, taita kuka gwanin ban tausayi, tana matuƙar ɗan nata rabuwarta da shi ji take kamar ta rasa komai na rayuwarta.
Bacci kam Widad ba tayi shi ba, Hindu tun tana rarrashin ta harta gaji tayi bacci, Widad kam kwana tayi tana Addu'a, Allah ya bawa Yusuf lafiya.
Se washegari sannan Ila da suka tafi kai Yusuf Asibiti tare yazo gidan, Widad na ganin shi a gigice tace "Ina Yoseef É—in? Yana ina?"
Ila yace "ki kwantar da hankalinki, kwantar dashi akai, can cikin garin Bauchi muka kai shi, ya ɗan samu sauƙi Amma yaji jiki fa, kafin muje har Suma ya dinga yi a mota, amma ya farfaɗo, baza'a sallameshi yau ba"
Hanne dake gefe tace "Alhamdilillah"
Gaba É—aya suka juya suna kallonta, banda Widad da tace "dan Allah dagaske kake ya tashi?"
Ila yace "kwarankwatsa dagaske nake, dan yace in gaidaki, Saleh na baro a gurinsa"
Se a lokacin Widad ta É—anji hankalin ta ya É—an kwanta, harta samu tayi wanka, megari ma yayi ta mata Nasiha akan wannan kukan data dingayi.
Ramla kam a kusan buge ta dawo gidan nan, Hajiya Halima bata ga dawowarta ba, Amal ce taga wucewarta kamar tana tangaÉ—i, binta tayi da sauri É—akinta, ta tarar tayi cilli da jakarta da takalmanta ta zube akan carfet tana bacci, Amal tace
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Ramla me zan gani haka, meya same ki?"
Ramla kasa magana tayi se É—aga hannu da take, cikin maye tace "ke.. Keee.. Nace ina ruwank.... Ki dani neeeee.. Ki fita nace"
"Ramla, shaye2 kika fara ne?"
Shiru Ramla tayi mata, ta cigaba da baccinta.
Gaba ɗaya hantar cikin Amal ya kaɗa, tabbas Ramla shaye2 take, dan maye take yi, ta tuna yadda take bacci ba ƙaƙƙautawa, da tayi kamar taje ta gayawa mahaifiyarsu, se kuma ta tuna dama a ƙule take da Fahad da mahaifinsa, muddin ta gayamata za'ayi ɓatacciya ne.
Kwanan Yusuf uku a Asibiti, gaba ɗaya Widad ta rame, idanunta duk sun kumbura, jama'ar ƙauyen duk sun san rashin lafiyar Yusuf, dan shike jansu Sallar Asuba da magariba zuwa isha'iyanzu, kuma ga karatu da yake koya musu suna jin daɗinsa.
Widad ta zuba ido, taga ta ina Za'a dawo mata da Yusuf, dan Ila ya gaya musu ranar za'a sallameshi.
Gwaggo tasa akayi Abinci, aka dama Fura saboda Yusuf.
Ila ya shigo gidan da Sallama yace "ku kintsa, mun dawo maƙota sun baibaye mota zasu shigo da shi"
Da ƙyar Gwaggo ta janye Widad zuwa ɗakinta, saboda maza zasu shigo, dukda damuwar da Widad ke ciki be hana Widad kallon Ɗakin Gwaggo ba, yasha jeren samiru da fanteku, ga gadonta na ƙarfe me rumfa da mudubi, ginin tsurar ƙasane ɗakin amma yayiwa Widad kyau nesa ba kusa ba, ga ƙwarya da'akayi wa itama nata jeren, ƙwaryar ta sha zane mekyau, ga wasu a cikin ragaya, Widad bata taɓa ganin irinsu ba"
Idan ba gizo kunnuwanta suka yi mata ba, to tabbas a cikin muryar mazan da suka yi Sallama hadda Yusuf.
Zumbur ta miƙe tsaye, Gwaggo tace "aikuwa ga muryar ɗana nan, Alhamdilillah lafiya ta samu"
Kasa jurewa Widad tayi, kawai se gani Gwaggo tayi Widad tayi waje, kai tsaye ta nufi ɗakinsu, ga mutane maza a ciki, wasu na ƙoƙarin fitowa, haka ta kutsa ta shiga, ta hango Yusuf yana zaune yana murmushi, sedai yayi rama sosai, yayi haske.
Da gudu ta ƙarasa ta rungume shi, ta kasa magana kawai ta fashe da kuka.
Ɗaya bayan ɗaya suka zame suka bar ɗakin, yau suka ga taɓara, ba kunya bakomai ba kara tazo ta rungume Yusuf a gabansu.
Suna fita Yusuf ya ha&a hannayensa ya rungumeta shima yace "Queen kin rame, duk kinyi wani iri"
Maimakon ta bashi amsa se sake kwanciya da tayi a jikinsa tace "Ya jiki ka warke?"
" Na warke amma ina ganin yadda kika rame naji zata dawo"
Hanne ce tayi sallama da kayan Abinci a hannunta, sedai me taga Yusuf da Widad rungume da juna, take taji jikinta ya hau rawa, bata taɓa ganin hakan a zahiri ba, sannan ga wani kishi daya taso mata, take ta saki kwanon dake hannunta.
(Gobe insha Allah, zan kammala book 1,Ashirin ga wata insha Allah zan fara book 2&3, tuni an fara biyan kuɗin, kuma zaku iya hanzarta biya ta wannan hanyar dake ƙasa "
Normal group duka littafi biyun ₦300
Idan kuma ɗaya zaki siya ₦200
VIP ₦ 500
Inkuma sena gama zaki sai complete document ₦700
Account Number
Aisha Adam
0009450228
Ja'iz Bank
Ko katin MTN banda VTU please
A turo evidence of payment ta 07063065680
Duk Wanda ya biya yayi min magana ta what's app number É—ina inyi adding É—insa a group É—in Nagode
Domin gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
 _*AƘIDATA*_
   Â
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠: Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITEDÂ (BANYI EDITING BA)
ELEGANT ONLINE WRITER'S
             PART1
                Page 44_45
Yusuf ne yayi saurin ɗagowa ya kalli Hanne, Yusuf yace "Subhanallah, garin yaya kika ɓarar da Abinci?"
Widad kam ko motsawa ba tayi ba balle ta tashi daga jikin Yusuf.
 Cikin rawar jiki Hanne tace "Tuntuɓe nayi shine ya zube, bari in samo in kwashe"
Ta juya ta fita da sauri, tana fita tsakar gida Gwaggo ta kalleta tace "ke meye haka, ba dai Abincin da nace ki kaiwa mara lafiyan kika zubar ba?"
Cikin inda inda tace "Amm.. Mm... Tuntuɓe nayi shine ya zube"
A fusace Gwaggo tace "kekam kamar mara hankali wani lokacin, kije ki kai Abinci kawai seki zubar dan shirme"
Hanne ba tace komai ba ta tafi ta ɗau tsintsiya da abun kwashe shara ta tafi gyara inda ta ɓata musu, cike da zullumin me zata je ta sake tararwa.
Gwaggo tace "Hindu tashi ki duba sauran kunu a É—akina ki kai musu ba'a bar mara lafiya da Yunwa ba"
Sukam Maƙota da suka rako Yusuf ne suka dinga jinjina rashin ta ido irin na Widad, a gabansu ba kunya taje ta rungume mijinta.
Wani da'ake kira da Lado me Jakai yace "to ai kunsan su ba namu ne na nan ba, jama'ar birni ne baku ga matar tasa bama kamar balarabiya, su sun saba irin wannan bakomai ne ba"
ÆŠayan da'ake cewa Liti yace "Aradu amma ai kunya wani abuce, tunda nasan duk abu Hausawa ne"
Lado yace "ku kuga haka, su a gurinsu ba wani abun bane ba"
Liti yace "Sumi sumi dashi haka, Amma ta rungume shi ya wani basar abunsa, memakon ma ya É—anyi mata tsawa ya hanata"
Wani me shekaru a cikin su yace "Kai waye ya gaya maka suna hantarar matansu, lallaɓasu suke yi, ni wallahi birgeni ma suka yi"
Kwashewa sukayi da Dariya gaba ɗayansu, harda ƙyaƙyacewa.
Hindu tayi Sallama, da kofin kunu tace "gashi inji Gwaggo, tace dan Allah kuyi haƙuri Hanne ta zubar da Abincin"
Yusuf yace "bakomai Hindatu hakanma mungode"
Hindu tace "Amarya yau za'a ci Abinci, tunda me gidan ya dawo"
Yusuf yace "Ai naga alama bata cin Abinci ta rame sosai"
Hindu tace "bata ci, Gwaggo taita fama da ita sedai tayi ta kuka, ko bacci bata iyayi"
Widad ta yatsine baki tace "Akanme zanƙi bacci, in kasa cin Abinci toni ƙiba ma nayi, ci nake in ƙoshi"
Hindu tayi dariya tace "bari a kirawo Gwaggo a tambaye ta"
Sukayi dariya, Hindu tayi waje, Yusuf ya kalli Widad yace "bani kunun insha dan inajin Yunwa"
Widad ta miƙe ta ɗakko kofin kunu, tazo ta zauna tana bawa Yusuf, Saleh ne yayi Sallama ya shigo ɗakinsu.
Kallon Widad yayi yai murmushi yace "Allah me iko, Allah ba yadda be iyaba, wai Gimbiyar Daula ce ke bawa direbanta Abinci a baki, abun da mamaki"
Banza tayi masa ta cigaba da bawa Yusuf kunu, Yusuf yace "Saleh ƙaraso ka zauna mana"
Saleh yace "to bari in ƙaraso, ina fatan hankalinki ya kwanta ban gudu dashi ba, gashi na dawo miki da shi, kuma Alhamdilillah jikinsa yayi kyau"
Shiru ta kuma yi bata ce komai ba, Yusuf yace "Ana magana fa"
Widad tace "me zance?"
Saleh yace "base kince komai ba kam, Malaria me ƙarfi da typhoid ne suka kama Yusuf, sannan ulcer na damunsa, ga rashin sabo da wasu abubuwa da yake yi, wanda be saba ba, dan haka shine damuwa gajiya da pressure ga kuma zazzaɓi gaba ɗaya suka dameshi, amma Alhamdilillah mun samu an ceto miki shi, yasamu sauƙi Alhamdilillah, na samo Net guda ɗaya, yace min ba guri ɗaya muke kwana ba, dan haka ga guda biyu nan ke ɗaya shi ɗaya, likita yace 'ya dena zama da yunwa, ya dena barin sauro yana cizonsa, sannan a kula ya shanye magungunansa"
Widad tace "Aishi zaka gayawa bani ba, tunda ze iya kula da kansa ko"
Mamkine ya kama Saleh, ya tuna yadda ta dinga kuka ranar da zasu tafi da Yusuf, amma yanzu tana faÉ—ar wata magana daban, shi kansa Yusuf beji daÉ—in hakan ba, amma ya basar.
Saleh yace "koma dai menene, Zan zauna zuwa jibi in Allah ya kaimu zan koma, nayi muku siyayya wajen gobe in Allah ya kaimu za'a kawo muku"
Yusuf yace "Mungode sosai da É—awainiyar da kake mana, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya ka"
Saleh yace "Ameen"
Ita kuwa madigar, miƙewa tayi tai waje abunta, ba tare da ta sake tanka musu ba.
Amal na kwance akan gadonta tayi shiru sosai take tunani, tayi zurfi sosai a tunani, Mummy ta shigo É—aki Amal ta tarar a kwance tayi shiru tana ta tunani"
Mummy tace "ke meye haka? Tunanin me kike yi? "
Amal ta ɗan tura baki tace "lafiya ƙalau Mummy"
"Amma kika zauna kika yi shiru haka? Kina ƙarama dake kike tunani haka"
"Mummy ina É—an zancen zuci ne kawai"
"to idan waccan uwar baccin ta tashi ki gaya mata zan fita, ni na rasa gane kan wannan baccin banzan dat take yi sekace wata kasa"
Ita dai Amal bata gayawa Mummy abunda Ramlan keyi ba.
Bayan fitar Mummy kwanciya Amal ta sake yi tana cigaba da tunani, kuma ba tunanin kowa take ba face Yusuf, tun tana dannewa yanzu abu yavfara gagara, bata iya ɓoyewa sam, Bata iya cin Abinci ba tayi zaton ƙaunar Yusuf haka tayi mat wannan mugun kamun ba, gaba ɗaya yanzu haushin samarin ta take ji, gani take duk cikinsu Yusuf yafi su komai dukda Kasancewarsa talaka, amma ya haɗu gashi nutsatse babu Hayaniya a tare da shi, ji tagi inama a sako Yusuf a riƙe Widad, dama itake hana ta rawar gaban hantsi, dan ta rasa wace irin Alaƙace ke tsakanin su, Widad bata da yadda kamar me, bata yadda kowa ya raɓe ta ba, amma ta yadda da Yusuf ya shiga jikinta sosai da sosai, Yusuf yasan abubuwan dasu da suke zaune da ita basu sani ba.
"Ke Amal! Tun É—azu nake miki magana amma se kace wata kurma, kinmin shiru"
Firgigit Amal ta kalli Ramlah, tayi ajiyar zuciya tace "Meye nayi min ihu kuma?"
"na dole inyi miki ihu ba, tun É—azu nake kanki ina magana amma kinyi shiru"
Amal ta miƙe zaune ta kalli Ramlah tace  "ban san kin shigo abane, dana san kin shigo ai zanyi responding"
"Wai nikam wane irin tunani haka kike yi?"
"Ramlah tunanin komai ma inayi, Abubuwa da yawa sun dameni, Amma Ramlah jiya fa maye kike kika dawo"
"Maye kuma?"
"Eh mana, wallahi jiya a buge kika dawo gidan nan, Mummy kuma a ƙule take dake, fitar da kikayi da Fahad"
Ramlah ta ɗan ɓata rai tace "ba wani maye da nake, na gaji ne kawai, sannan me Fahad ɗin kuma yayi?"
Amal tace "Eh to, kin san sunyi faÉ—a da É—an uwanta akan belin Yaya Anwar, shiyasa"
"to kuma shine seya shafi Fahad, laifin meyayi? Kuma shima bakiga yadda yake ƙoƙari akan lamarin ba, amma kin san halin babansu da kafiya"
Amal tace "wani tabacci kike da shi na yana ƙoƙarin nan, nifa kallon Fahad ɗin nan kawai nake, bakin maƙaryata ne dashi"
Ramlah tace "zaki fara ko? Karki kusakura kici masa mutunci"
Amal tace "ke niba wannan ba, nifa naji tana cewa za'ayi uwar watsi idan ba'a fito mata da Yaya Anwar ba, karta yi wani abu daza'a zo ana da nasani daga baya"
Ramlah tace "kuma fa hakane, kin san bata iya fushi ba, bari inje É—akinta in sameta"
Amal tace "to ai ta fita"
"ta tafi ina?"
"Nima ban sani ba, ni dai tacemin zata fita"
Ramlah tace "Shikenan, bari inje kitchen in samu ɗan abunda zanci, da yamma zanje gurin wani birthday na 'yar gidan IG na ƙasa, na tura a ɗakkomin wata sabuwar motar megidan nan daga kamfani, da ita zanje, kin san gurine na manyan yara fa"
Amal tace "Mhmm yakamata kam"
"waini meke damunki ne Amal, bakya walwala fa"
"Ramlah wace walwala zanyi? Yaya Anwar a rufe, hankalin Mummy yaƙi kwanciya, ga uwa uba wallahi Ramlah Ji nake kamar inyi me saboda rashin Yusuf, na shiga damuwa wallahi ko bacci na kwanta yanzu mafarkinsa nake yi, na rasa inda zan saka raina, tun ina iya dannewa yanzu na kasa "
Wani uban dogon tsaki Ramlah taja tace " Aikin banza, shine zaki kashe kanki saboda wannan jakin"
"Karki sake kiransa da Jaki, Inda wanda za'a kira Jaki to tabbas Fahad ne, dan kunnuwansa ma irin na jakaine ga ƙaryar tsiya".
Haka abun nasa ya koma faɗa, ƙarshe sukayi baran Baran.
Widad ta fita tsakar gida, ta ƙarasa inda Gwaggo take tana murmushi, Hari tace "ohh ni Harira, se wangale baki kike miji ya dawo, kin ware"
Widad tace "Toke ya kika gani? A garin nan banda Allah se shi na sani, idan lafiyarsa ta taɓu akwai damuwa sosai"
Gwaggo tace "ƙyaleta Amarya, zolayarki take"
Widad tace "Mama, dan Allah abun nan na É—akinki sunmin kyau sosai"
Gwaggo tace "me fa?"
Widad tace "kwanukan nan da kika shirya a É—akinki, sunyi kyau sosai fa"
Gwaggo tayi murmushi tace "Widad kenan, kayan Su Samira da fanteka kenan, mu dasu mukeyin adon É—aki"
Widad tace "Masha Allah, gaskiya sunmin kyau sosai Mama"
Can ta hango bulugari, a gefen Gwaggo zata kaÉ—a miya.
Widad tace "ya sunan wannan Mama? Wanda kike juya miya dashi"
Gwaggo tace "Bulugari kenan, dashi muke kaÉ—a miya"
"Mama wannan tunkunyar naganta baƙa sosai"
Gwaggo tayi murmushi tace "wannan itace Talle Amarya, tukunya ce ta ƙasa, muna girki a cikinta, miya tafi zaƙi da daɗi Sosai"
Widad tayi murmushi tace "taɓ Mama duk ban san wannan abubuwan ba, ban taɓa ganinsu ba"
Gwaggo tace "hakane dama, tunda ba kuyi rayuwar karkara ba ba lallai ki sansu ba, bari inje É—aki in É—akko abun kaÉ—i"
Gwaggo ta tashi ta tafi, tana tafiya
Hanne tayi tsaki tace "Aikin banza mutum ya zauna yaita ƙarya, mtseww aikin banza dana wofi, wai bata san bulugari da fanteka ba"
Widad ko waigawa ba tayi ba, tai shiru abunta, Hari tace "wato Wudas kinfi jin tsoron Hanne, ta gayamiki duk abunda data ga dama, kiyi ƙus amma da nice da tuni kim hayayyaƙomin"
Wani irin kallo Widad tayi wa Hari, nan take cikin Hari ya kaÉ—a, ganin wani irin kallo da Widad tayi mata, se taga kamar ta canza gaba É—aya daga kamaninta, ba shiri Hari taja bakinta ta tsuke.
Saleh ya kalli Yusuf yace "Sannu Yusuf, gaskiya kana fama, yanzu haka kuke zaune? Tana maka wannan gadarar da jin kan, bayan taimakonta kake"
Yusuf yayi murmushi yace "lafiya ƙalau muke zaune da ita, duk wannan abubuwan bata Yimin, ƙalau muke zaune Alhamdilillah"
Saleh yace "kaga nifa bana son wannan kawaicin naka, kalli yadda take wani bintsire bintsire, tana cin magani, na zata tuni ta dena wannan halin nata?"
Yusuf yace "Kai da ita ta baka amsar wannan tambayar, Amma nan ma shigo ka tarar tana bani Abinci ai"
Saleh yace "kuma fa hakane, lallai kai ɗan baiwa ne kuma na musamman Yusuf, wannan yarinyar me Azabar taurin kai, amma take kula da kai haka, ta yadda ka shiga jikimta gaskiya abun da mamaki, kayi namijin ƙoƙari fa"
Yusuf yayi murmushi yace "Haka lamarin ubangiji yake, yanzu ya jikin mahaifinta?"
Saleh yayi shiru da alama jikinsa yayi sanyi yace "labari mara daɗi Yusuf, yanzu ma badan ka tambaya ba bazan gaya maka ba"
A rikice Yusuf yace "Subhanallah, meyafaru kuma?"
Saleh ya gyara zama ya waiga yaji babu motsin kowa sannan ya waigo ya kalli Yusuf yace "An sace Daula akan gadon Asibiti"
Dafe ƙirji Yusuf yayi yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, kamar yaya?"
Saleh yace "kaima dai ka tambaya, abun kamar almara, Kasan tunda yake rashin lafiya Anwar ne kawai yake sintirin jinyarsa, matarsa da sauran yaran ba ruwansu dashi, daga ya É—an fito daga É—akin, ya koma aka nemi Daula aka rasa, yanzu haka an kama Anwar da me Asibitin ana tuhumarsu, yau sati uku kenan sun tsare "
Dafe kai Yusuf yayi ya shiga murza goshi, wannan wane irin bala'i ne? Duk yadda yake zaton lamarin ya wuce tunaninsa, wane irin tashin hankali ne haka?
Saleh yace " ka kwantar da hankslinka fa, ban gaya maka dan ka É—aga hankalinka ba, sedai ka tayata da Addu'a, sannan karka bari ta sani"
Yusuf yace "kuma ana bincike akan lamarin, ba'a gano inda yake ba?"
Saleh yace "kai dai ayi sha'ani, har yanzu babu Labari"
"Amma naji kamar kace kasan suwaye ke wannan abubuwan"
Saleh yayi murmushi yace "kaifa jami'in tsarone, kuma kai aka bawa wannan aikin na binciken, zuwa yanzu ai nasan ka samu haske akan binciken da kayi"
Yusuf yace "kamar yaya kenan?"
"Kana nufin baka gane me nake nufi ba? Ai shikenan mu bar zancen, kar tazo ta same mu muna maganar"
Yusuf yace "Ya Ummana kuwa Saleh?"
"tana nan lafiya, Suleiman yana kula maka da ita"
"Amma Saleh, Akwai wani abokin aikina Abbas, babban Abokina nane, yana Ibadan akan aiki, ko Suleiman yayi maka maganrsa, nasan idan yasan ina nan Abbas ze shiga damuwa ina da tabbacim se yazo nan"
Ƙura masa ido Saleh yayi, ya ɗanyi shiru sannan yace "gaskiya ba muyi maganar wani da shi ba, kai dai kunci gaba da haƙuri, komai ze wuce kamar ba'ayi ba Insha Allah"
Yusuf yace "Allah yasa"
Saleh yace "bari in ɗan fita waje, in zaga gari"
Yusuf yace "bari in bika bana son zaman gidan ne, gara in fita in É—an tattaka"
Saleh yace "kar kasa matarka tamin tijara fa"
Yusuf yai murmushi yace "bakomai"
Suka fito shida Yusuf, Can Saleh ya hango Widad a kusa da Gwaggo suna hira, Widad ta maida hankalinta sosai akan Abunda Gwaggon take yi.
Saleh yace "iko se Allah, da a mafarki aka haskomin wannan abun ze faru, zance sharrin mafarki ne"
Widad ta É—aga ido ta hango Yusuf, ya fito da alama fita za suyi, Widad tace "ya dai, naga ka fito, ina zaka haka?"
"You leave alone in the room, am so boring, Saleh is going out, so i feel like to follow him"
Widad tace "gaskiya ban yadda ba, ka koma ka huta in kuma ka faÉ—i fa?".
"Bazan faÉ—i ba insha Allah, ina son in ga gari ne kawai"
Widad tace "Shikenan, kar kayi nisa dai"
"As you wish your majesty"
Saleh jinjina kai kawai yayi, yayin da Yusuf yake jin wani irin matsanancin tausayinta, ko ya zataji idan taji labarin mahaifinta ya ɓata shima?.
Haka yabi Saleh suka fice.
A harabar gidan su Nurat kuwa, Nurat ce zaune a É—aya daga fararen kujerun dake harabar gidan, ita da Barrister Khalil cousin É—inta, teburin gabansu É—auke da lemu ka da kuma kofunan glass.
Barrister Khalil yace "kince kina son ganina, gashi nazo amma kin kasa cemin komai"
"Brother, aini sam ban san ta ina zan fara maka bama, na rasa me ya kamata ince maka"
"Ki nutsu, ki gayamin komai a hankali, an fahimceki Insha Allah"
Ta ɗanyi ajiyar zuciya sannan tace "brother, game da maganar da mukayi da kaine na belin Anwar" Se kuma tayi shiru.
Khalil yace "Mhmm ina jinki, gayamin ke nake sauraro"
"Barrister, kai ɗan uwana ne, kona ɓoyewa kowa wani abun, kai bazan ɓoye maka ba, amma ina son maganar ta tsaya iya nida kai, ko Kasan akwai hannun mahaifina a cikin abubuwan da suke faruwa da Alhaji Daula?"
A hankali Khalil ya zare glashin fuskarsa, ya kalle ta yace " kamar yaya? Ban gane me kike nufi ba"
'Nasan abun ze baka mamaki, amma kasan Alhaji Daula me silar ɓacin siyasar Mahaifina? "
"Eh na sani, nasan da wannan"
"Mahaifina yayi alwashin ko ze mutu se ya rama abunda Alhaji Daula yayi masa, ya haɗa kai da wasu manyan abokan kasuwancin Alhaji Daula, suna ƙoƙarin ganin bayansa, zancen da nake maka, da saninsa aka sace 'yar gidan Daula da direbanta"
Hankici ya É—akko a aljihunsa ya share gumin fuskarsa yace "wani tabbaci kike dashi, akan wannan maganar da kike yi"
"Brother, nikaɗai ce sheda, se Mummy amma kasan halin Mummy da tsoro, ba zata taɓa bamu goyon baya ba, yanzun kaima ma gaya maka ne, saboda yadda abun ke cin zuciyata, na rasa wa zan gayawa inji daɗi a raina"
Khalil yayi shiru sannan yace "am sorry to say, Nurat mahaifinki gaba É—ayansa zuciyarsa babu Allah a cikinta, yanzu muddin ya gano mum sam me yake yi to tabbas ze É—au mataki a kanmj, nasan shi ba tun yanzu ba"
"Nasani brother, nikaina tunda naje na duba Daula a Asibiti ya samun takunkumi, ya hanani fita, rannan dana fita baka ga yadda ya shaƙeni ba kamar ze kasheni"
Khalil ya jinjina kai yace "yanzu Addu'a zamu ci gaba dayi, mahaifinki yana da goyon bayan manya sosai, dan haka babu wanda ze tsaya ya É—au mataki, sedai muyi ta addu'a"
Nurat tace "hakane Brother, but am so much disturbed wallahi"
"Kakri damu, ki kwantar da hankalinki, Dukda haka zan duba inga me zan iyayi akai"
"Shikenan nagode sosai brother, Allah ya ƙara ɗaukaka"
"Ameen ya Allah karki damu kinji, ki kwantar da hankalinki, komai zezo da sauƙi"
Haka sukka cigaba da tattaunawa.
"Alhaji Musa wai yanzu duk kuna kallo haka É—ana ze cigaba da zama a prison? Ba zakuyi komai akai ba? Na gaji da yawon da kukemin da hankali fa"
Alhaji Musa yace "Ni yanzu me kike son inyine? Nifa bani na sa aka kama É—anki ba, me kike so inyi?"
"Idan ba ku kuka sa aka kamashi ba, amma kuna da ƙarfin da zaku sa a sakarmin shi aiko? Wane irin abune haka, se zarya nake a tsakanin ku, amma kowa da kalar rainin hankalin daze mun"
"Kinga saurara, ni babu abunda zan iyayi akan wannan al'amarin, wannan babban case ne da yake buƙatar bincike, idan bashi da laifi zasu sake shi fa"
Hajiya Halima tace "Shikenan nagode sosai da abunda kukayi min, wato na gama yi muku amfani, zaku watsamin ƙasa a ido, zaku ga abunda zanyi"
Ta juya fuuu tayi waje kamar zata tashi sama, tana tafe tana banbami, ofishin Bulama ta tafi, ta tarar yana shirin fita, ya kalle ta yace "Halima lafiya kuwa?"
"karka ƙara tambaya ta ko lafiya, lafiyar kenan kana nan hankalinka kwance, ni kuma nawa a tashe ko baccin kirki bana samu, na zama kamar mahaukaciya, ɗana yana can a tsare, kun nunamin halin ko in kula, kun nuna baku damu da halin da nake ciki ba"
Bulama yace "Nikam Halima kina bani mamaki, ɗanki fa ɗana ne, nima nawa hankalin ba'a kwance yake ba, muna iya ƙoƙarin mu, amma abunda ake gayamana shine, ana zargin da sa hannun Anwar a wannan abu daya faru, kuma duniya ta kasa kunne taji wani mataki za'a ɗauka, me kike tsammani idan aka ji da sa hannuna aka saki Anwar? "
" Kaga sauraramin dan Allah, bana son maganar banza data wofi, na sani ka sani Anwar baze iya aikata laifin da ake tuhumarsa ba"
"A'a karki shedeshi, ba'a shedar ɗa a zamanin nan"
"Bulama, na gama magana da kai, zanje inyi abunda ya dace kawai"
Bulama yace "abunda ya dace kamar yaya?"
"Ka zuba ido zaka gani, bar ganin kai É—an uwanane zan iya yin komai akan É—ana, na gaya maka"
Bulama yace "hmm kibi a sannu dai, kin san ido ya fara dawowa kanki yadda kike wadaƙa da wasu daga cikin kadarorin mijinki? Mutane sun san me kike aikatawa, ki sani tsalle ɗaya ke kai mutum rijiya, amma se yayi dubu be fito ba"
Tsaki tayi, ta É—au mukullin motarta tace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, nasan abunda nakeyi"
Tai waje abunta, tana fita Bulama ya ɗau waya, ya danna yasa a kunnensa yayi shiru, can kuma yace "Yawwa kana jina da kyau, ina son ku ƙara tsananta tsaro da sa ido akan yaron nan Anwar, under no circumstances zaku bada belinsa, ku matsa se ya faɗi inda Daula yake, dan uwarsa ba abunda ba zata iya ba"
Daga cam ɓangaren yace "Ok sir an gama Insha Allah"
Bayan barin Hajiya Halima Office É—in Alhaji Musa, su Alhaji Haruna suka dira, dukda haushinsu da Musa yake ji, amma ya maze ya sakar musu fuska yace "kun san yanzun nan wannan mahaukaciyar ta bar gurin nan"
Alhaji Haruna yace "wa kenan?"
"Hajiya Halima mana, tazo nan tana ta banbami, wai munƙi saka baki a sakar mata ɗa"
Alhaji Munir yace "ƙyale wannan mahaukaciyar, ni wata shawara nazo mana da ita"
Suka tattara masa hankalinsu, suna saurarensa "Abunda nake gani shine, mu samu lauyoyin Daula, mu siye su, su saka hannu su fitar mana da wasu daga kadororinsa, a sasu a kasuwa a karya su, sannan ayi takaddun ƙarya, muce muna binsa zunzurtun bashi"
Alhaji Haruna yace "kayi magana mekyau, sedai abunda ka manta shine, lawayoyinsa basu san kan dukiyarsa kamar yadda wannan koÉ—aÉ—iyar 'yar ta sani ba, ta san komai tasan inda komai yake"
Alhaji Munir yace "to tunda yanzu ba ita babu ubanta aise muyi yadda zamuyi mu kwashi rabonmu, ko so kuke se wannan mahaukaciyar matar tasa ta ƙarar da komai ita da' ya'yanta? A ɓoye fa se saida kadarorinsa sukeyi, haka zamu zauna mu zuba ido."
Alhaji Musa ya nisa yace "duk naji ta bakin ku, kuma kowa yazo da magana me kyau, zamu jarraba lawyoyin suma, danni yanzu kuÉ—in tsayawa takara nake nema"
Kallonsa sukayi gaba É—aya sukace "kamar ya tsayawa takara?"
"kamar yadda na gaya muku, bazan zauna bani ga tsuntsu bani da tarko ba"
Alhaji Haruna yace "hala ka manta da baƙin fentin da kake da shi, a dalilin Daula?"
"ina fa na manta, sedai a ƙasar nan indai kana da kuɗi ba abunda baze yuwu ba"
"Amma baka ganin hakan, ya saɓa da Yarjejeniyar mu, idan kayi haka kamar ka zame daga cikinmu ne, kuma me zaka cewa Bukar?"
"Bukar ubanane, ko haifata yayi? Ba gudu ba ja da baya, ina tare da ku amma tabbas zanyi takara"
Gaba ɗaya Yusuf ya fara jin kunyar mutanen da yake ja salla, musamman idan ya tuna abunda Widad tayi a gaban su, tunda su hakan kamar baƙon al'amarine a gare su, haka nan ya ɗan dinga basarwa, sukayi sallar magariba da isha'i suna ta sake duba shi.
Widad jin shiru Yusuf be shigo ba, yasa ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan gidan Hansai tace masa "kaga ɗan jeka waje ka cewa Yoseef in jini nace, baze dawo ba se sauron ya sake cizonsa yazo ya kwantamin?"
Gwaggo dake alwala tace "A'a kul kaje ka faɗi haka, kace tace 'dan Allah ya shigo gida, kar sauro ya kuma cizonsa'"
Widad tace "to ai kusan abunda na faÉ—a kika maimaita"
Gwaggo tace "A'a ke naki umarni da kashedi kika yi, aishi miji abun lallaɓawane da tattalawa, ki kalli yadda kika damu da bashi da lafiya, ki dinga masa magana da girmamawa kinji Amarya, yana da kirki mijinki, kema ki dinga tausasa harshen ki a kansa"
Widad tace "To Hajiya Mama"
Gwaggo tace "ni a Hajiya, to me rai baya fidda rai da rahama, amma abun da wuya"
"Insha Allah indai da rai da rabo, zaki je saudi Arabia in dai Allah be ɗau rayuwar wani daga cikin mu ba, idan muka koma gida lafiya zaki je ƙasa me tsarki"
Tsaki Hanne tayi tace "san a sani, ji wata ƙarya kuma da son nuna iyawa, karma kisa rai ana gayamiki gaibu"
"Ke! Ki kiyayeni, dake muke taÉ—in, ina ruwan ki Hanne ki kiyayeni fa"
Widad ta juya kawai ta koma ɗaki, ta ɗakko ƙaramar fitilarsu ta kunna, batirin ma ya fara sanyi.
Ta zauna tayi shiru tana tunani, sallamar Yusuf ce tasa ta É—ago ta amsa masa, yaje kusa da ita ya zauna, daya kalleta se tausayinta ya kama shi yace "gani naji ance kina nemana"
"shine tun la'asar kaƙi dawowa, se sauro ya kuma cizonka ko?"
"Ai na warke, Alhamdilillah"
"dan ka warke shine se kaje, ka kuma kwaso wani zazzaɓin, kazo ka ɗagamin hankali"
"Insha Allah na warware ai, ance jinina ma yayi ƙasa, dole in dinga cin ganyayyaki"
"Sannu kaji jiki ai"
"Gaskiya muje ki dawomin da jinina dana baki"
"wai jininsa, jinin naka ma duk malaria ya ƙara samun zazzaɓi, zan biya ka jinin ka harda riba ma"
Dariya Yusuf yayi yace "ni iya nawa nake so, bana son naki danni bana son jinin me taurin kai"
"kai kai, nice me taurin kai? Zaka ga taurin kai'
Kwanciya yayi a kafaÉ—arta yace " dan Allah a sake rungumeni mana, i need your body warm "
Ture shi tayi tace 'kaje kaji É—umin bargo mana"
Cikin kwantar da kai yace "A' a ni gaskiya naki nake so, ai naga yau ke kika rungumeni, idan muka koma gida sena gayawa Ummana, nima ince kina rungumeni"
Widad tace "ai kai ka fara bani ba, ka koyamin abunda ban iya ba"
Dariya Yusuf yayi yace "nayi mamakin yadda kika damu da rashin lafiya ta My queen"
"A cikin AƘIDATA babu butulci, bana manta alkhairi, bazan taɓa manta wahalar daka sha saboda rayuwa ta ba, idan na nuna halin ko in kula ga kafiyarka to tabbas banwa kaina adalci ba, dukda ana faɗin bani da kirki, banj da mutunci amma bana manta alkhairi"
Yusuf yace "waye yace miki baki da kirki, kina da kirki uwaÉ—akina"
"Hmm yoseef kenan, ka dena kareni danka burgeni, amma nasan bani da kirki kamar yadda da yawa mutane ke faÉ—a"
"ba kareki nake dan na burgeki ba, ina faÉ—a miki gaskiya ne kawai, amma kince bakya manta alkhairi, amma meyasa bakwa jituwa da Saleh, dukda irin taimakonmi da yayi?"
"saboda bana yafiya ga mutane ma'abota fuska biyu, da fari mahaifina ya yarda da shi da ɗam uwansa, amma ya koma ɓangaren maƙiyanmu, yanzu ya kuma dawowa ɓangaren mu, wani tabbaci muke dashi na muma baze sake juya mana baya ba? Duk yardar da nayiwa mutum, duk girman Alkhairin da yayumin, muddin yaci amanata koya min ƙarya to tabbas ze shafe dukkan alkhairansa a idona, bana yafewa mayaudari da maƙaryaci ko me fuska biyu, wannan itace AƘIDATA!!!
TOFA! Alhamdilillah nan na kawo ƙarshen kashi na ɗaya a littafin AƘIDATA,
ÆŠanÉ—ano daga Littafi na biyu
(idanunta sunyi jawur, kamar wadda aka zubawa barkono saboda kuka, ta sunkuyaf da kanta ta shafi ciknta, cikin zubda hawaye tace "wace amsa zan bawa abunda yake cikina, idan har ya girma ya samu labarin mahaifiyarsa taje kotu ta bada sheda akan mahaifinsa an kai shi prison, kaicona haɗuwa ta da Yusuf ta zame masa babbar ƙaddara a rayuwarsa, ya sadaukar da rayuwarsa don in ganta tawa, amma maƙiyana sun na ƙoƙarin cin galaba akanmu, abun da basu sani ba shine...............)
Karku bari a baku labari, saƙar labarin mukayi a na farko, tufaka da warwarar gami da cakwakiyar suna littafi na biyu dana uku, anan gwaramar take
SHINE MEYE LABARIN YUSUF?
MEYE LABARIN WIDAD?
WAYE MAMALLAKIN ABUNDA AKE NEMA A HANNUN WIDAD?
MEYE ABUNDA AKE NEMAN?
WAYE YA SACE DAULA?
SHIN ZASU BARO ƘAUYEN NAN?
ZASU KOMA GIDA DA WANNAN AUREN?
YA ZATA KAYA TSAKANIN WANNAN MANYAN ALHAZAI?
YA WIDAD ZATA YI IDAN TA GANE YUSUF JAMI'IN TSARO NE YA MATA ƘARYA?
Akwai cakwakiya me tarin yawa karku bari a baku labari, ga masu buƙatar siya
Normal group duka littafi biyun ₦300
Idan kuma ɗaya zaki siya ₦200
VIP ₦ 500
Inkuma sena gama zaki sai complete document ₦700
Account Number
Aisha Adam
0009450228
Ja'iz Bank
Ko katin MTN banda VTU please
A turo evidence of payment ta 07063065680
Zan fara posting É—in littafi na biyu dana uku, ranar 20 ga watan October
Masu neman complete zasu sameshi ranar biyar ga watan November insha Allah
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool. 07063065680
Nagode da ƙaunar da kuka nunamin