Gidan Aunty Book 1 Complete Hausa Novel By Mrs Lee
Reading file: GIDAN AUNTY BOOK 1.txt
Chapter 18 of 28
Page 57
Tana idar da sallar isha’i tasaka rigimar bazata kara kwana a dakin ba sai dai ya mayar da ita wajan ammey,yasan abunda take cewa ba mai yuwa bane dan bazai taba yadda ba shima , a hankali ya kama hannunta da take kokarin kwacewa fuskarta a hade ta ki yadda ta kallesa,”am sorry please,ki canzamun wani punishment din amma banda wannan please, I can’t “,kuka ta fashe masa dashi”ai daman ka fadamun bakasona shiyasa kayi kokarin kashe nii, ni dai Allah ka mayar dani”,kwantaccen gashin kansa ya dan shafa kansa har ya fara yi masa ciwo, shi kadan yasan yanda kukanta ke cakarsa har cikin zuciyarsa, har yanzu zazzabinsa be tafiva shima,”look at me”, ya furta a hankali,kin kallansa tayi sai ma kara kawar da kan da tayi, gyada kansa yayi kafun ya taba button din rigarsa “ok shikenan kamar Kari kikeso bari muyi round two”,ba karasa zancan saba tayi saurin rike hannunsa da yake kokarin cire rigar jikinsa,hawaye har sun fara cika mata ido,yanda tayin ne ya so bashi dariya amma ya danne gudun karya kara janyowa kansa wani saban rigimar,a fili kuwa dan tabile bakin sa yayi kadan yana d’auke idanuwansa shima ,marairaice masa fuska tayi ashagwabe ta furta “kace mun fa bazaka kara ba”,be kalletaba ya cigaba da kokarin cirewa “toh yanxu na fasa tunta bakyajin magana “, da sauri ta girgiza masa kai” Allah inajin magana , tsoro nakeji “, yanda ta karasa dinne ya bashi tausayi, kara rike hannunta yayi kafun ya goge mata hawayenta “idan wannan hawayen suka kara sauka toh zanshanye kayana”,da sauri ta goge hawayen nata,”ya ciwonki fa”, kawar da kanta tayi kafun tace masa “Ni lapiya ta kalau”, Tohm shikenan zamu iyayin wani kenan” cewar king ,ynxu ma kanta ta girgiza masa “Allah ban warke ba wajan da zafi,kuma kace mun ka dena fa”, rungumota yayi a jikinsa “ am really sorry zawj, nayi leafi Amin afuwa, kinji, am so sorry “a hankali ta gyada masa kai”banaso ka dena mun kaji”, murmushi ne ya subuce masa a fuska Ba tare da ya amsa mata ba sai dan shafa mata bayanta da yake.”zaki iya tafiya”, kanta ta daga masa alamar eh, mikewa yayi shi yana miko mata hannu “let’s eat something kar ki wanta haka”, a shagwabe ta turo masa bakinta “uhm uhm bana jin yunwa “, lumshe idanuwansa yayi kafun ya kalli bakin nata “ you’re making me to ad more “, ai be kai karshen zancen nasaba ta rufe bakinta ruf,dariya ta so bashi amma ya Waske, taku ta somayi a hankali duk da zafin ya ragu makamar dazu ba, duk yana kallan yanda take tafiyar , da te makonsa suka karasa falon, da kanshi ya ja mata kujera kafun ya soma serving dinta, kadan taci tace ta koshi, be kyaletaba saida ya tabbatar ta koshi sosai kafun su koma ya bata magani.
wajan wanciyama sai da yasha rigimar bazata kwana a dakin ba, saida yace mata ba abunda zai mata sannan ta yadda ya kwanta a gefenta amma taki yarda ya tabata, shima din be tabata har saida yaga tayi bacci kafun ya rungumeta a jikinsa yana kashe gabaki d’aya dum light din.
➰➰➰➰➰➰➰
Zaune su amrah suke a falon Ammeey gabaki d’aya yan matan su ke su 5, ihsan, sumayya, firdausi,amrah da basma , kowa yana sabgar gabansa, su ihsan suna zaune kan carfet din Ammeey lokacin ta tafi part din data, suna shan fruit jifa jifa suna hira, amrah na kwance kan 3 sitter , basma kuma na zaune kan 1 sitter kafa daya kan daya yayinda take latsa babbar wayarta sai faman ya tsine take, cikin da rigar da sumayya take dannewa ta dan kallesu kafun ta kashewa su firdausi ido d’aya da dan karfi ta soma magana “ Nifa yau banga sis tahee ba, ko da mukaje part din ta kinga yaya king yace mana bacci take ,Anya kuwa su yaya bari dai nayi shiru,” kyalkyalewa da dariya sukayi jin iskancin da sumayya take wa su amrah dan sunsan halinta , itama firdausi dariyar take dannewa” uhm ke dai bari , a yan kwanakin nan da muke zuwa part din ai kinga baya hade mana rai kamar da yanxu fa har gaisuwar mu yake amsawa amma da dane ai bamu isaba,” wata dariyar suka kuma saki , ihsan sai satar kallansu basma take da suka cika fam , daga karshema basma mikewa tayi tare da barin part din ba tare da ta tanka musu ba, amrah kuwa harara ta dunga sakar musu, tayi alkawari kuwa sai ta haddasa musu wutar da bazasu iya kashewa ba,tunanin abunda zata musu take kafun ta dan saki murmushin mugunta tana barin wajan ba tare da tace musu uffan ba suma . Suna ganin ta bar wajan suka tafa gabaki dayan su , ihsance ta soma magana “wallahi bamu da mutumci, kun iya tsiya, ku kalli yanda fuskar su tayi kamar wanda aka fadawa mummunan abu”, itama firdausi dora tayi “ rabu da yan iska wai su soyayya , in banda ma iskanci irin nasu su kalli kamar yaya king suce wai sai sun aureshi ko da bala’I ai suma sun kwasowa dala da ganmu”, dan murmushi sumayya ta saki” Aah feedy, so sone fa, Kema kinsani duk Wanda ya kalli zubin yaya king ,ko baya sansa sai yaji wani abu aransa ,musamman idan aka samu marasa tsoran Allah, ko ni kunsani naso yaya king kamar raina tun bansan Menene so ba, har zuwan amrah muka fara samun sabani akan shi, amma yanxu na hakura dashi har abada Sabida yayi mana nisa nesa ba kusa ba , ku duba ku gani fa wa ya taba kawowa zai auri sister , duk da irin abunda mukayi mata bata kullacemuba lokacin da mukaje mata, gaskiya masu irin halin sister kadan ne”, jinjina kai sukayi gabaki d’ayansu kufun ihsan ta furta “ Allah sarki AKHII Allah ya jikanka da rahma, har na tuna lokacin da idan yaya king zai hukunta mu zai hana sa , ko uktiii ta hanashi, ban taba sani yana jin maganar su ba sai lokacin da mukai masa lefi akhiii moha ya bashi hakuri shi da ukhti, sai gashi kuwa beyi mana komai ba , da Yaya kabeer ne ko yaya haroon ina tunanin rugu rugu za suyi mana , duk da suma suna tsoran yaya king sosai kamar sunga mala’ika “,gabaki dayan su saida suka shiga jimamin mutuwar akhiiii kafun kuma su fara bada labarin laifikan da suke yake tema kar su da Wanda king yake Zanesu ukhti ke cecensa.” Ku naji fa Ance sun kusa dawowa suma duk da sun makale a turai sunki dawowa gida ,amma naji ance boss yace su dawo nan da one week kafun ransu ya baci” dariya suka sani kin yanda feedy ta kira king da boss, “itama ukhti fa taji anacewa zatazo tunda batazo bikin yaya king ba , ni har na matsu tazo dan nasan dole ko yayane sai anyi mana dinner indai taso kuma yaya king nasan zai amince ko sabo da ita ne”, gabaki dayan su kuwa jin hakan sai suka fara tsara yanda abun zai kasance duk da basu da tabbacin hakan, sunayi suna dariyar kansu musamman in suka tuno yanda king zai ci ubansu.
➰➰➰➰➰
➰➰➰➰➰➰➰
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.