Trending Hausa Novels

Kwarata Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Kwarata Complete.txt

Chapter 3 of 7

Ci gaba nayi da tafiya har yanzu yana tsaye a wurin dana barshi , motoci masu komawa katsina nayi ta É—agawa hannu har Allah yasa na samu masu ragemin hanya shiga nayi na nufo katsina yayin da Dikko ya shiga suka kama hanyar abuja ,

Budurwar Dikko kuma ga wayarta a hannuna , domin dana koma mota dama ba jaka na koma É—aukowa ba waya na É—auko abinda yasa na fito da jaka dan karsu zargi ni na sace kuma nasan idan sukayi gaba zasuyi tunanin wurin fitowa ta yada ita , Baba da Mama da kowa nata yana cikin waya...

Tunda Dikko suka tafi yake kukan zuci daren jiya da An mata tasan irin matsalar daya fuskanta akanta da bata baɗa mishi ƙura ba , abinda ya faru tsakaninsu sirri ne babu wanda ya sani sai shi sai ita sai Allah , yana bata mutuntukar mutuncinta daya ɗauka amma yarinta ta hanata kusantowa gareshi !

Abinda ya faru jiya , bayan Dikko ya faÉ—awa An mata yana santa tafiyarta kawai tayi ta barshi palo zaune kamar wani sakarai , bata daÉ—e da shiga É—aki ba Dady yace yana nemanshi duk abinda yakeyi ya barshi yazo , shine ya tashi ya fita babban palo ya É—auki makullin mota ya fita kuma a gaban idon Sultana yabar gidan...

Bayan yaje gida a palon Dady ya samu Al ' Ameen gurfane a gaban Dady , kallo É—aya yayi mishi ya É—auke kanshi tare da samun wuri shima ya zauna can nesa da Dady , bayan ya zauna ya gaishe da Dady ya ansa shima Al ' Ameen ya gaishe da Dikko , Dikko bai ansa gaisuwar ba , kallon Al ' Ameen Dady yace ya kira mishi Ummar ,

Miƙewa Al ' Ameen yayi kafin ma ya fita daga palon Umar ya shigo saboda dama tuni an kirashi bai samu isowa da wuri bane , bayan kowa ya zauna Dady ya kalli Al ' Ameen yace ga Babana nan ka sake faɗar abinda ka faɗa , shiru Al ' Ameen yayi , Dady kuma ya kalli Umar bayan Al ' Ameen yaƙi magana yace Umar wace yarinya ce take zaune da Baba ?

Da sauri Umar ya kalli Dikko amma shi basu yake kallo ba yana kallon wani wuri daban , cike da fargaba Umar yace wallahi Dady nidai ban sani ba , Dady yace tou aini Al ' Ameen yace min ya ajiye mace gidanshi na goroba road bayan ni nasan Babana baya huÉ—É—a mata shi yasa hankalina ya tashi , Umar sake kallon Dikko yayi amma har yanzu Dikko fuskar nan tashi dai kamar yadda take kullum kuma har yanzu baya kallonsu kawai dai yana saurarensu.

Dady yace ƙarya zakamin ne ? Ya tambayi Umar , Umar yayi shiru , Dady yace ma Al ' Ameen yanzu ina yarinyar take ? Tana gidan har yanzu ? Al ' Ameen yayi shiru , gyara zama Dikko yayi yace tana gidan Dady , amma lokacin dana fito na barta tayi bacci , nayi kuskuren rashin sanar dakai amma da Allah kayi haƙuri nayi amfani da maganar ka ne da kace na zama mai kyautatawa duk wanda naga rayuwarshi tana buƙatar taimako ,

Yarinya ce ƙarama shekarunta bazai wuce 18 ba kuma na baka labarinta kwanakin baya itace yarinyar da mukeyin faɗa tou yanzu mun daina faɗan ne , a tsawace Dady yace ɗiyar ɗan caca ? Karuwar Babana ? Cikin ladabi Dikko ya sauke kanshi ƙasa tare da rufe idanuwanshi , Dady yaci gaba da cewa duk ƙoƙarin kare martabar ka da nake maka ni zaka ɓatawa siyasa ka ɓatamin suna har cikin jahata ? Ni zaka zubarwa da mutunci ? Ka ɗauko karuwa ka ajiye a gidanka ka bar matarka kaje ka kwana da "yar iska mara tarbiya wacce tafi ƙarfin iyayenta itace wacce kake ganin kaine zaka gyara mata rayuwa ?

Masifar da tasa iyayenta suka yada ita ba ƙarama bace kai shine kaje ka ɗauko ka dawo da ita rayuwarka kai sarkin imani da tsoron Allah ? Kana siyasa zaka ɓatawa kanka suna , ka zubar da mutuncinka a idon duniya ina amfanin mu'amula da karuwa ? Ko zaka dafa Al ' Qur'ani kayi rantsuwa kace baka neman yarinyar nan babu wanda zai yadda , da yarintar ka baka bi mata ba sai yanzu da shekaru suka fara hawanka ? Tou idan dan rashin lafiyar matar ka ne Momynka ta nemo maka auren ɗiyar yayarta shikenan na kashe maganar...

Murmushi Dikko yayi tare da cewa gaskiya Dady ban tsara zama da mace 3 ba a rayuwata itama Sadiyar haƙuri nayi kawai na ansa amma ni gaskiya mata 3 sunmin yawa wannan karon bazan ansa ba kuyi haƙuri , ciki ɓacin rai Dady yace wallahi idan dai ina lumfashi a duniyar nan baza ka auri karuwa ba sakaran banza da baka san macen da ya kamata ka aura ba , shi aure daka ganshi yana buƙatar cancanta mutuntaka asali da nasabar mace , banda kake sakarai ka rasa wacce zaka so sai karuwa ? Karuwar kake tunanin zata zama uwar "ya "yan ka ? Ni wallahi ko jirgi zan siya bana buƙatar na hannu sai sabo shi yasa bazan iya auren zawara ba amma kai dan baka kishin kanka har kake tunanin auren karuwa , wallahi da kasan kanka ko mace baka nema ,na tsani wani yayi amfani da abu nayi amfani dashi saboda tsanar da nayi ma abun yasa bana sauka hotel , duk jahar daka gani babu inda banda gida babu ƙasar da ban mallaki gida ba dan na tsani wani ya shiga a wuri na shiga sakarai wawa dakai idan baka fita harkar yarinyar nan ba zaka haɗu da fushi na ,

Dady kayi haƙuri kasan.... Tsawa Dady yayi masa yace nasan me ? Ko zaka mutu banajin komai Babana , Dikko zai sake magana Dady yace fita bana san ganinka , jiki a sanyaye Dikko ya miƙe ya fita , ɗakin mom inshi ya nufa itama faɗa ta mishi sosai domin Allah kaɗai yasan abinda Al ' Ameen ya faɗa akan Sultana ,

Itama wata yayarshi da isowarta kenan nigeria tazo ganin Sadiya ta sako bakinta tayi ta ma Dikko faɗa tare da cewa kadaiji kunya wallahi kuma kayi asara ka rasa wacce zaka so sai ɗiyar ɗan caca , abun kunya duk nasabarka da mutunci gidanku kaje ka auro mana ɗiyar marasa asali , jiƙar matsafi ɗiyar ɗan caca karuwa tou ka faɗamin ita me zata haifa ? Kalli yadda tazo ji yadda take tata rayuwa wace irin tarbiya zata ba "ya "yanta ? Gaskiya Dikko ka bani kunya da ina alfahari dakai amma , Dikko ya tareta da cewa amma yanzu kin daina ko ? Tou kije kiyi ta daina warki kuma ki fitar da bakinki idan ba haka ba kuma duk abinda nayi miki ke kika jawa kanki ,

Momy tace rufemin baki mara kunya ko itama halin karuwanci zaka nuna mata ? Dikko yace tou ta ƙara aibata ta kiga yanda zanyi da ita ! Wallahi saina zane mata jiki tas idan kuma tana ganin zaki hana na daketa ta fito waje wallahi saina bi ta kanta da mota na wuce , wani irin mari Momy taimishi dan tasan halin Dikko da kafiya idan dai yace zaiyi sai yayi idan kuma ya rantse akan abu ko za,a mutu baya kaffara saiya aikata wallahi ,

Kallon Yayarshi yayi yace akanki aka mareni ko ? Jinjina kanshi yayi tare da miƙewa yace zan haɗu dake , tace ni ba'a kaina aka mareka ba akan karuwa dai , cikin ɓacin rai Dikko ya nufi wurinta Momy tace idan ka taɓata ban yafe maka ba shanyayye , dariya yayar tashi tayi tare da cewa aikin san karuwa koba asiri akwai bariki mai wahalar goguwa a zuciya , wallahi Dikko ka daiji kunya ɗiyar daka isa ka haifa ai ko baka haihu ba ka kalli ɗan abokinka , fita Dikko yayi daga ɗakin dan idan ya tsaya komai zai iya faruwa ,

Wurin motarshi ya samu Umar , kuma Umar shine ya faɗawa Dikko cewa Al ' Ameen yazo ya faɗawa Dady komai kuma ya ɗora da cewa idanma aure mai gida zaiyi ga ɗiyar yayarshi , shine ya kawota gidansu Dikko kuma tayi sati tunda tazo Dikko bai taɓa ganinta ba sai yau , kuma Dady shine ta tursasa Dikko yaje asibiti ya ɗauketa ya tafi da ita ya ajiyeta kaduna , tunda tazo itace take kula da Sadiya , tana kyautatawa kowa na gidan ,

Ita kuma Momy ta riga data yanke shawara kawai Dikko zai auri autar ɗiyar yayarta , kuma duk zagin da yarinyar nan tayiwa Sultana wallahi Dikko baiji ba , baisan sunayi ba dan hankalin shi baya wurinsu yana can ya tafi duniyar tunani , bige²nsu kawai yaji , amma wallahi baiji zage²nsu ba , Al ' Ameen shi yasan komai akan Sultana kuma shine ya bawa ɗiyar labari yace ta faɗawa Sultana tace Dikko ne ya bata labari , amma tayama Dikko zai fara wannan sakin layi ? Bayan bai haɗa Sultana da kowa ba ,

A gajiye na iso anguwarmu tafiyata babu jimawa anguwar ta samu ci gaba sosai , tun daga farkon layin hannun da Dikko ya sissiye har zuwa gidan dawankashi an bugeshi anyi wani irin zuƙeƙen gini babu wani maƙoci daya raɓeshi baya tare da kowa sai gidajen dake kallon gidanshi , waje kawai aka gyara aka ciccina mishi fulawowi ciki kuma aka watsa dawakuna da wasu irin lafiyayun karnukan turawa masu kama da kuraye , an ƙawata gidan da wasu irin fitulu wanda idan dare yayi aka kunnasu haskensu zai gauraye ko ina da ko ina ,

Gidanmu na shiga da sallama , Nana tana gani na ta tashi da gudu ta shige É—aki , Babana na gani kwance saman tabarma yanajin magana na ya karkato da kanshi dakel ya kalleni ,

Kowa ya tsaya yana kallona babu wanda ya ansa min sallamar da nayi , wurin Babana na nufa na durƙusa na kamo hannayenshi nace meke damunka ? Kallona yayi cike da tsantsar ƙauna sannan ya buɗe baki dakel idonshi ya cika da hawa yace shine kika tafi kika barni....? 😭

Murmushi nayi tare da goge mishi hawayen nace ai gani na dawo ? Kana tunanin zan tafi na barka ne ? Bayan bana iya rayuwa saida kai ! Dare da rana safe da yamma yanayin farin ciki da damuwa halin yunwa ko ƙoshi babu kowa a zuciyata sai kai , farin ciki ya dawo rayuwar kunci da damuwa zata kama gabanta ,

Har yanzu babu wanda yayi mana magana ga gida cike da jama'a yayin mutane suka fara janye "ya "yansu , matar Baba ƙarami ta kira "yarta gefe tace ki wuce ki tafi gida annoba ta dawo ,

Wane yaro ne ya shigo gidan cikin farin ciki yana barka da dawo uwar É—akinmu , ban kalleshi ba kuma ban saurareshi ba ina kallon yadda jama'a suke tsame "ya "yansu saboda zuwana , jinjina kai na nayi tare da cewa wane yaro a kawomin abinci da Allah , saida ya saramin caucau Allah dai ya kare miki sharri yayi maganar cikin muryar dabanci , nace Amin shi kuma ya fice...

Fitar wane yaro nabi duk wanda ke gidan da kallo , sannan nace duk sannun ku ? Na dawo ya mai jiki ? Babu wanda ya bani ansa , murmushi nayi na zauna gefen Babana , ban gama zama ba Amisty ta shigo , fitowar Nana daga É—aki shigowar wane yaro da kwanon abinci , Hafsa A ' i Saude Zalifa Karima sai kuma wata daban wacce nake tunanin itace suke zuwa gidanta wato Asma'u ,

Murmushi nayi tare da miƙewa tsaye nace dama nasan ranar nan tana zuwa shi yasa na taho gida na dawo kuma a tafe nake da sabon salo na baya ba komai bane ba , ga Sultana ga Amisty ga kuma Hafsa ku kaɗai nake da damuwa daku sauran kuma banma sansu ba , ....

26/09/2019

*JAMILA MUSA....*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 42

*_AHUMAGGAH yadda kika fara lafiya ubangiji yasa ki kammala lafiya , ku nemi naku karku bari ya wuceku daga alƙamin SURAYYAHMS haziƙar marubuciya mai tafiya dai² da zamani yana nan yazo..._*

Kallon wane yaro nayi nace kai muje ƙofar gida kaji , na faɗi maganar ina nufar hanyar fita , riƙoni Amisty tay ta baya tana cewa babu wani wajen da zakije anan zamu ci uwarki , ban kalleta ba na kalli inda ta riƙeni nace sakemin hijabi , Hafsa tace baza'a saki ba kina nufin mu zaki ɗauka wasu ƙolaye mu barki kuma , murmushi nayi na kalli Hafsa nace sakarar banza ba ƙolaye ake cewa ba kuzo muje ƙofar gida , saboda bana so ayi wulaƙancin a gaban Babana da kuma sauran jama'ar dake gidan gani na ma kawai yasa sun kora "ya "yansu ina kuma ga anyi wannan maganar a gabansu , duk a zuciyata nayi wannan nazarin ....

Babana ya karkato cikin yanayin jin jiki yace Uwar masu gida me ya faru ne ? Nace ba komai Babana , a kadarance Amisty ta kalleshi tace ai kasani , a wahalce ya kalleta yace me na sani ne Amina ? Nace Baba da Allah ya isa haka kayi bacci abun ka kada a ruwa ai sarki ne kaja bakinka kawai kayi shiru domin ni wutar kara ce ba'a kwana dani ba saidai idan ba bacci ake ba !

Mamana..... Ya faɗa tare da lumshe idanuwan shi yace mene ne ? Kallonshi nayi cikin ɓacin rai nace wutar da aka daɗe da kashewa ni kuma nake so yanzu ta ruru , cikin hayaga ga , nace ɗaukar fansa da ramuwar gayya a cikin jininka yake Babana , baka gada ba ni kuma na gada ɗan koyo da ɗan gado dukansu idan suka tashi sai sun zarta ,

Na rantse da ubangiji da ya bani aron lumfashi da rayuwa dawowa ta sai ta zame ma kowa tashin hankali saina firgita kowa saina jinyata duk wanda ya shigo rayuwata , wallahi ׳ Amisty da Hafsa kun sake toƙalowa kanku masifa idan baku kiyayeni ba uwar kowa a cikinkun nan , na nuna su da ɗan yatsa na jinjinashi nace kuma nayi rantsuwa...

Da sauri Hafsa ta kalli Amisty suka kalli juna cikin firgici , komawa nayi na zauna tare da cewa har kun firgita kenan ko ? Jinjina kaina nayi tare da cewa baku ga komai ba furtawa kaɗai nayi kuma ban faɗa muku abinda zan aikata ba amma tabbas wani abu zai faru , kallon wane yaro nayi nace kai bani abinci kaji , gabana ya ajiye abinci nace muci shi tare , babu ɓata lokaci yasa hannu mukaci gaba dacin abinci ,

Kallo Babana ya bini dashi na wani lokaci sannan ya kalli Amisty yace mi ya haÉ—aku da Uwar masu gida ? Amisty tayi shiru tou maganar dai bata faÉ—uwa da kunya tace tsiraicin Babanta na É—auko , tayi shiru ta kasa magana , lashe hannuna nayi tare da cewa bara kaji abinda ya haÉ—amu Babana ,

Kafin in ɗago su Amisty sunyi layar ɓata domin dai bansan ta inda sukabi suka fice ba , murmushi Babana yayi mai nuni da yana alfahari dani , kallon wane yaro nayi nace jeka idan Allah ya kaimu jibi ka dawo ina neman ka , godiya yayi ya fice daga gidan , ni kuma ɗakina na nufa ina zuwa na cire kayana , alwallah nayo nazo nayi sallah azahar har saida nayi la'asar sannan na tashi ,

Komai na ɗakina yana nan yanda yake babu abinda aka taɓa har kuɗin dana sata a jakar Amisty duk suna nan , wanka nayi na saka kaya na fice daga gidan , a napep naje gidan su Mamy wacce muka haɗu da ita a wurin saloon , ban sameta gida ba , saidai nabar saƙo idan ta dawo ace mata Sultana tazo mu haɗu gidanmu jibi idan Allah ya kaimu ,

Kasuwa na shiga nayi "yan hidimomi na har katifa na siyowa Babana da sabbin zannuwan gado 3 sabuwar ledar tsakar ɗaki sai ƙaton bargo saboda yanayin sanyi ² dake shigowa da labulaye masu kyau , bayan na gama da kasuwa naje na siya sabon sim card na wuto gida...

ÆŠakin kusa da É—akina na share na shinfiÉ—a leda na saka katifar na rataya labululluka na shinfiÉ—a zanin gado mai kyau a saman katifa , É—akina na koma na É—auko fulaluwa nazo na saka musu rigarsu irin na zanin dake saman katifar , ruwan zafi na dafa na kaiwa Babana bayi yaje yayi wanka ,

Kafin ya fito na ɗauko mishi kayan da zai saka dan naga kayan a gefen katifar ɗakina , ɗakinshi nakai mishi da turare shima a kusa da kayanshi na gani turare mai shegen tsada da ƙamshi , yana fitowa ya saka kayanshi ya shafa turare sannan yayi alwallah dan magrib ta gabato , abin sallah na shinfiɗa mishi ya hau sama , nima na fito nayi alwallah na wuce ɗakina...

Duƙe yake saman bayan kujera ya ƙurawa waya ido yana kallon hotunan Sultana , murmushi yayi a bayyane yace da wannan kyakkyawar zan kere sa'a na kasace na daban abina , amma dai ya kamata na bata shawara ta daina ciki baki akan cewa baza ta taɓa so na ...

Zagayawa yayi ya zauna saman kujera yana cewa dani dake yau zanga waye tunani zai hana bacci , kwanciya yayi saman kujera ni na kwanta kuma bacci zanyi ya ƙarasa maganar yana murmushi , saida ya lumshe idanuwanshi yace ki kasance cikin farin ciki na barki lafiya....

Saida na gama duk abinda nakeyi na kwanta saman katifa a gajiye , a hankali naja bargo na lulluɓe tare da ƙurawa wayar dana ɗauko ido kira sai shigowa yakeyi babu ƙaƙƙautawa , uhum murmushi nayi tare da kashe wayar gaba ɗaya na rufe idonuwana danyin bacci....

_Ƙarya kike..._

Wannan kalmar itace ta fara zomin a cikin kwalwar kaina , É—an jujjuya kaina nayi a hankali na gyara kwanciya ta ,

_Zuciyata ta faɗamin cewa ko kin tafi sai kin dawo , bata taɓa faɗamin ƙarya akanki ba duk abinda ta faɗamin gaske ne_

Murmushi nayi har yanzu idanuwana a rufe nace tou ya akayi ban dawo ba ?

_Zaki zo zuwa gareni kina roƙon na baki soyayya ta , tabbas ranar zata zo , murmushin shi yazo ya tsayamin a rai kalmar ƙarya ta sake dawomin a zuciyata..._

Da sauri na tashi zaune nace wallahi ƙarya kakeyi na tsaneka....

Murmushi yayi ya gyara kwanciya , nasan baki tsaneni ba ɓacin rai yasa kike faɗar wannan kalmar , idonshi a rufe yayi magana ...

Wallahi a daren ranar banyi bacci ba , tun daga ranar dana fara ganin Dikko har zuwa yau da muka rabu ko ta ina Dikko ya zargemin zuciya , nayi juye² wallahi bai fita ba , ganin dai baccin bazai zo ba yasa na haƙura na fita nayo alwallah naci gaba da sallah !

***

Yau laraba kuma itace jibin da nake jiran zuwanta , bayan hantsi ya ɗaga na dafa ruwan wanka wa Babana , kafin ya fito na gyara mishi ɗakinshi na share na goge fess na zuba mishi turaren wuta , bayan ya fito wanka ya shirya cikin shiga ta kamala ya baɗa ƙamshi ,

Sama ² ya yagi abin kalacin dana kawo mishi , bayan ya gama ya umurceni dana fitar dashi ƙofar gida saman dakali , ɗakina na koma na ɗauko kafet na naje na shinfiɗa mishi sannan na dawo na kamashi dan har yanzu yanayin abu irin na wanda yasha jiya harya gaji ,

A hankali muka fito dani da Babana muna lallaɓawa , saman dakalin na samu Amisty zaune ita da Hafsa , ko inda suke ban kallaba na taimakawa Baba ya zauna , a dai² lokacin da Umar yake tsugunniya a gaban Baba yana gaishe shi cikin girmamawa tare dayi masa sannu da jiki ,

Naji daɗi sosai dan haka nima na gaishe shi , ya ansa cikin kulawa tare da cewa wurina yazo ya faɗi maganar yana miƙewa , bayanshi nabi mukayi nisa da Baba , bayan mun samu madakata yace mai gida ya aikoni wurinki , kallonshi nayi banyi magana ba , wayarshi ya ciro daga aljihu ya kira Dikko bayan ya ɗauka yace mai gida gata , ya faɗi maganar tare da miƙomin wayar ,

Cikin jin daɗi na ansa na kara a kunne na tare dayin sallama , ansawa yayi cewa ya kike ? Lafiya qalau kaima kana lafiya ? Alhamdulillah , tun shekaran jiya nake so nai miki ya hanya Umar yace yazo ² bakyanan ina kike zuwa ne ? Banje ko ina ba , tou da kyau , na sake cewa banje ko ina ba , yace ai shine nace hakan yayi kyau sai anjima , shiru nayi dan bana so wayar ta tsaya hakanan , shi kuma kashe wayar yayi abunshi...

Miƙa mishi wayarshi nayi , shi kuma yace min yana zuwa , mota ya koma ya ɗaukomin wata "yar ƙarama leda mai tambarin waya a jiki yace gashi yace a kawo miki kuma akwai layi a ciki anyi mata caji ,

Uhum ni da zanma Dikko cikon kuɗi saina ɓige da ansar waya , cikin farin ciki mukayi sallama da Umar , ban koma wurin Babana ba nayi cikin gida ina zuwa na shige ɗakina na zazzage ledar na ciro "yar kyakkyawar wayata na dudduba bansan sunan wayar ba anma an rubuta a jikin wayar , ban damu da sanin sunanta ba nidai tamin kyau kuma ta burgeni sosai , ajiyewa nayi na koma ƙofar gida wurin Babana dasu Amisty dana baro waje ,

Ina fitowa a daidai lokacin da Mamy ta faka da tsadajjiyar motar ta , tasha wani irin dakeken gilashi wanda ya cinye kaf rabin fuskata , karuwa ce data ansa sunanta karuwa , ba karuwar muje mu dawo ba , ba karuwar wahala ba , ba karuwar ya zanyi ba ? Kana ganin zubin iskancinta kasan karuwanci takeyi mai aji kuma mai matsayi ba iskanci cini inci tuwo ba ,

Tana fitowa ta fara bi bi biyyy 👍🏻 cikin yanayi mai nuni da "yar hannun ce , murmushi Babana yayi cikin jattako da gogewa , wata alama yayi mata da ido irin tasu ta "yan bariki , dariya tayi tare da cire gilashinta tace *BINNA* 👍🏻 , Binna kaci dubu ka binne dubu , binna zaki binna kura binnan ƙarshen ƙarni binna ka taushe ..... Sai kuma ta fasa ƙarasawa !

Dariyar "yan duniya Babana yayi tare da É—an kauda kanshi gefe cikin jin kunyata , Mamy ta sake cewa Binna wuta , wuta na wurina.... Ba tare daya kalleta ba yace ga Mamana nan da nake baki labari ku gaisa , gaba É—aya tabi mu da kallo dani da Amisty da Hafsa a wani irin yanayi tace wace ce Uwar masu gida ?

Kakkaɓe idanuwa na nayi nace nice , ƙwalalo idanuwa tayi tana kallona sannan ta sake kallon Babana tace Binna Sultana ɗiyarka ce ? Jinjina kai Babana yayi alamar Eh , ƙara kallona tayi sannan ta sake kallon Baba ta juyo ta tsareni da ido....

Kusa da ita na matsa na duƙa ƙasa² nace matsayin kura daban amfanin labule sirri , huɗɗakir da Babana daban nima tawa dake daban ,

Murmushi tayi tare da kallon Amisty tace Amina kuma tsaf ta kira sunan Hafsa , tace ke kuma Sultana ? Nace sosai suma mu'amular ki dasu daban nima har yanzu nawa daban da nasu.....

Kallon Babana tayi shi kuma yayi murmushi tare da cewa mijinki ya dawo ne ? Miji kuma ? 😳 wane irin miji na tambaya a bayyane , kallona Mamy tayi tare da cewa ya dawo ya koma ta ƙarasa maganar tana murmushi , Babana yace sai kuma yaushe zai dawo ? Har yanzu ni take kallo tace harsai na kirashi.... !

Dama kina da aure ne ? Na tambayeta tace Eh amma auren jeka nayi ka kawai idan yazo miji idan baizo ba sauka lafiya , ƙara duƙawa nayi nace ina kika san Amisty da Hafsa ? Wurin Babanki na sansu , Babana kuma kamar ya ....?

Dariya tayi tare da cewa amfanin labule sirri yanzun nan kika faÉ—a Sultana , saboda haka a sake labulen muje ciki inji neman da kike min ,

Amisty tace Aunty Mamy amana don Allah , cikin rashin fahimta na kalli Amisty nace amanar uwarki .... Dariya Mamy tay tare da cewa ai kinsan ba haka nake ba , kowa da wurinshi ,

Murmushi nayi na nuna mata da "yan yatsuna biyu manuni da mai bi mishi 🤞🏻 kamar ina datsa abu nace kema ...? { lesbian } Tace ina yaran wata ƙawata ne , nace baƙar magana kika faɗamin kenan kikace wurin Babana kika sansu ko ? Tace wallahi tare da Babanki nake ganensu kullum rana ,

Kallon idonta nayi tare da cewa kuma fa da gaske kike ba ƙarya kika faɗa ba , tou amma idan na gano akwai wani abu tsakaninsu da Babana tabbas zaune da tsaye bata ƙare ba , murmushi Mamy tayi tare da cewa ki kiyayi Binna duk macen da kika ga tana manneshi ki mata uziri idan ya gaji da kanshi zai wulaƙansu wallahi babu asiri ba komai idan dai kika faɗa tarkonshi fitarki sai Allah , matan yanzu da kansu suke bibiyarshi , kuma duk mutanen da kika sa nayi musu vidio kwanaki kinsan ko su wayen Babanki ne ?

Nace sai kin faɗa , jinjina kanta tayi tare da cewa gaba zaki sani amma Allah yasa dai wani abu bai shiga tsakaninki da Baban Hafsa ba , ni babu abinda ya taɓa haɗani dashi saidai munayi waya ana maganganu dai irin na gyaran kasuwa , so ɗaya kawai ya taɓa rungumeni ya bani cake a bakin partyn birthday ina , Mamy tace gaskiya an samu matsala shi kanshi Binna da yasan waye Hafsa a wurinshi daya haɗe zuciya ya mutu , itama bata san wayenta ba , shima Baban Hafsa baisan ke wacecen shi ba , kowa iskanci ² gaba ɗayan ahali sun zama *KWARATA...*

Cikin rashin fahimta nace su waye ahali ɗayan ? Murmushi tayi tare da cewa wai dani da mijina shima neman matan bariki yakeyi , murmushi nayi nima dan ban taɓa daukar akwai wani abu ba , saidai tacemin da Baban Amisty da Baban Hafsa na fita hanyarsu tsohuwar motace su koda mai sai an tura , na gane karatunta kalami ne na matan bariki ,

Kallon inda su Amisty suke suna fira da Babana cikin tsantsar soyayya akwai soyayyar Babana mai zafi a cikin kwayar idon ko waccensu , sun tsareshi da ido daga gani sunajin daɗin kallonshi dan Babana yana kyau sosai gaskiya kuma ɗan gayu ne ƙirƙirar farko yana da aji kuma yanayin komai nasa cikin tsari da burgewa , tabbas saboda Babana su Amisty suka ƙyaleni amma da ba haka ba idan duk katsina dangina ne babu wanda ya isa ya kwaceni a hannun su Amisty...

Cikin gida muka nufa da Mamy amma zuciyata tana tamin tariya akan maganar Mamy ,

_Gaskiya an samu matsala shi kanshi Binna da yasan waye Hafsa a wurinshi daya haɗe zuciya ya mutu , itama bata san wayenta ba , shima Baban Hafsa baisan ke wacecen shi ba , kowa iskanci ² gaba ɗayan ahali sun zama *KWARATA...*_

Juyawa naji kaina nayi kwalwata na zakuÉ—awa wasu abubuwa sunamin yawo a cikin kai da sauri na rufe idanuwana jikina ya fara kyarma lokaci guda zufa ta ketomin kaina da tunanin da nake dashi da wani sauran sani ya juye kwalwata ta sake toshewa , na sake tashi wata kidahuma ta karfi da yaji.....

Gaba ɗaya saina manta maganar da nayi da Mamy nayi ² na tuno amma sai zuciyata tacemin bamuyi wata magana ba , duk yanda naso na tuno wallahi gaba ɗaya komai ya goce daga cikin kaina , amma ban manta na fitar da Babana waje ba kuma na riƙe nabar su Amisty kuma na tuna nayi waya da Dikko amma sauran maganganun sun ɓacemin ,

Ina ƙofar ɗaki tsaye Mamy ta miƙomin waya cewa ana kiranki , da sauri na ansa na ɗauka , An mata Dikko ya kirani a cikin wata irin murya yace meke damunki ne ? Ba komai na bashi ansa , yace karki min ƙarya meke damunki ne ? Tunani na fara yi , sassauta murya yayi yace me kikeyi yanzu ? Ba komai , kina yanayin tsayuwa ko zama ? Nace tsaye nake , An mata zaki iya faɗamin ko wane iri ne Dikko ? Shiru nayi ina tunani , yace tuna ² An matana , har yanzu kaina juyawa yakeyi , yace kin tuno ko wane iri ne Dikko ko ?

Wallahi Dikkon ma ya ɓacemin , An mata tsaya kiji kin tuna nine mukayi fada dake har kika mareni , kin tuna ? Eh na ganeka , amma me yasa kamin wannan bayanin ne ? Murmushi yayi tare da cewa kawai mafarki nayi wai kin manta dani shine nayi sauri na tashi a baccin na kiraki dan Allah kimin adalici karki manta dani kinji An mata , nace tou yawwa An matana..... Muah yai sumbata , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya na kashe wayar....

ÆŠaki na shiga na É—auko wayar budurwar Dikko ina zama kusa da Mamy nace ciro layin ciki ki saka a wayar nan.....

27/09/2019

*JAMILA MUSA....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 43

*_Ina miƙo saƙon ta'aziyya gareki HALIMATU SADIYYA MUHAMMAD { Leema } Allah ya bada haƙuri ya jiƙanta yasa ta huta mu kuma ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo..._*

*_Don Allah dan Annabin rahma kuyi haƙuri yadda labarin yazo min kenan haka nake rubuta shi_*

Me za'ayi da layin idan an ciroshi ne ? Shine tambayar da Mamy tayimin , kallo nabi Mamy dashi yayin da nima nake tambayarta wane irin layi kuma...? Mamy tace kina miƙomin waya ne kince na cire layin ciki na saka a wannan wayar shine nace meye ?

A ni ban wani faɗa ba ko dai kin fara ƙarya ne Mamy ? Nifa bana san ƙarya da kika ganni ƙatuwa dake bakyajin kunyar Allah bare kunya na kike nema kijamin sharri ko ? Tou tashi fitar min ɗaki , kamar sakara haka Mamy ta tsaya tana kallona , a hayagagance nace fita....... Da Allah malama , na faɗi maganar ina nuna mata hanyar fita , kallona Mamy tayi sosai tace ke Sultana anya kina da lissafi kuwa ?

A , a banda shi sai ke kika iya malamar lissafi , kila ma kece makarantar boko gaba ɗaga ko ? Murmushi Mamy tayi tabi Sultana da kallo cikin yanayin tausayawa , shi yasa ramuwa ga ramuwar abinda akayi maka babu kyau ka rama sharri ga sharri , Binna kuma idan har na faɗa mishi komai tabbas rayuwar yarinyar nan zata ƙare a gariri ne kawai , tun farko da bai anshi buduricin matar Bello a daren farko ba duk da haka bata faru da tilon "yar shi da ya ɗauki soyayyar duniya da ƙauna ya ɗora mata , dogon tunani Mamy ta tafi , tunanin abinda ya wuce shekaru da yawa shine wani sashe na daban yazo mata a kanta...

_Cikin farin ciki Binna ya shigo gidansu , dan dashi da Bello kowa baya ma kowa iyaka da shiga gidan kowa , kowa kai tsaye yake shiga..._

_Bello yana zaune tsakar gida Binna ya rungume shi cikin farin ciki da in ina yace kai banzan abokina an haifomin balarabiya yanzu na aihu a duniya duk na gaba hoton banza ne , kaga yarinyar kuwa ? Kyakkyawa da ita gata fara , burina akan ta zai sauka , itace Uwar masu gida dama nace sai an haifomin mai kyau zansa sunan mahaifiyata , zan gina mata rayuwa mai kyau dan ina so inyi alfahari da ita..._

_Murmushin yaƙe Bello yayi tare da cewa wane irin farin ciki kake ji a yau ɗin nan ? Binna yace baya musultuwa , Bello yace yanzu alal misali yarinyar nan sai kawai ayi mata fyaɗ...... Ai bai gama faɗa ba Binna yakai mishi wani irin duka harsai da Bello ya suma , duka ɗayan da Binna yayi masa yasashi tafiya duniyar suma , da gudu Mamy ta ɗauko ruwa ta yayyafawa Bello ya dawo , kallon Binna yayi tare da cewa alal misali fa kawai nace ! 👌🏻 Binna baiyi magana ba sai huci yakeyi kamar ɗan matashin zaki , jinjina kai Bello yayi tare da cewe hakan ya nunamin irin soyayyar da kake yi wa yarinyar nan , tsoki Binna yayi ya fice daga gidan..._

_Fitar Binna Bello yayi dariya tare da kallon Mamy yace wallahi tabon da Binna yamin yana nan bazai taɓa gogewa ba , shi a tunaninshi yaci banza , ya amshe min budurci mata a daren farko kuma yake tunanin zai gujeni , kyaleshi nayi kawai ni da kaina naje na bashi haƙuri duk da ni yayi ma laifi , na lallashe shi muka dawo muka koma ɗaya , tun kafin Binna yai aure yake bada labari akan zuwan Uwar masu gida , yau tazo kuma ta faɗo a dai² lokacin da Bello ke jiranta , ɗaukar fansa ba'a kan "ya "yanshi yake ba akan zuciyarshi yake wato Uwar masu gida mu tafi wasan daga yanzu Binna dani dakai wanda ya fasa shi ba ɗan iyayenshi bane ba..._

_Mamy tace haba dan Allah wai harsai yaushe zaku daina wannan ɗauke ²n fansar naku ne ? Ya kamata abu ya riƙa wucewa a wurinku don Allah , kayi haƙuri don Allah karka cutar da yarinyar ku daina jefe² da tsafe²n nan Bello , Bello yace na rantse da ubangiji daya aiko annabi da gaskiya sai yarinyar nan tayi karuwanci , shine abinda ya tsana tayi , kuma sai tayishi wallahi , namiji ɗaya ne zai buɗe mata ƙofa daga nan zata firgice ,kuma yaci buri akan sai ta zama malamar asibiti wallahi har a busa ƙaho ita da ilimin zamani , zan cuɗanya "yan uwa su halaka zan ɓata zumuncin su ,.... !_

Murmushi Mamy tayi tare da kallon Sultana tace tou zan wuce , kallonta nayi nace kai tun yanzu ? Haba dan Allah karki tafi ki zauna muyi magana , Mamy tace ba komai zan dawo zuwa asabar in Allah ya yadda , ansar wayata tayi ta sakamin numberta , tace kinga number na nan , idan kika tuna abinda zaki faɗamin to ki kirani kinji ko ? Jinjina kaina nayi alamar gasuwa , zan wuce ta sake faɗa , miƙewa nayi dan in mata rakiya...

Har ƙofar gida tayi sallama da Baba tahau motar ta tayi tafiyarta , wurin Baba naje na zauna dan Amisty bata nan kila tana gidan Asma'u , kallon Hafsa nayi dake muguwar matsoraciya ce kamar ni , nace da Allah ba mutane wuri zasuyi magana da Babansu , babu gaddama ta miƙe itama ta wuce gidan Asma'u...

Kusa da Babana na matsa sosai ina kallonshi nace Babana , yace Mamana ya akayi ne ? Runtse idanuwana nayi kwalwata tanamin wani irin zafi kamar zata fita daga cikin ƙoƙon kaina , hawaye ya cikamin idona cikin kuka na sake cewa Baba , riƙeni yayi tare da cewa wai miye ne Mamana ?

Buɗe idona nayi tare da cewa zaka iya misulta irin soyayyar da kakemin ? Murmushi yayi tare da kafeni da idanuwanshi , faɗamin Baba , hannunwashi ya buɗe kamar zai rumgumi wani abu , kallon yanda ya buɗe hannuwan nayi nace ɗan haka Babana ? Ƙara buɗewa yayi na sake cewa wannan kaɗai ? Murmushi ya sakeyi tare da buɗe ko wane hannu saida ya taɓa bango iyakar buɗewa sannan yace ina miki soyayyar da bata da farko bata da ƙarshe ,

Murmushi nayi tare da kamo hannayenshi na riƙe nace nima ina sanka , ina kuma tausawa rayuwata ranar da za'a waye gari babu ɗaya a cikin wa'annan masoya , idan na rasa ka zanyi kuka Babana harsai na haukace , idan kuma na rigaka mutuwa nasan kaima zaka zare kamar dai yadda zanyi idan baka duniyar nan ....

Murmushi yayi tare da cewa haba Mamana idan har na mutu karki sake kimin kuka kimin addu'a itace kawai zata tabbatarmin da irin soyayyar da kikemin , tou mudaina maganar mutuwar nan Babana...

Yace tou an daina , nace to wai Babana ina kasan Mamy ? Yace tsohuwar matar Bello ce , murmushi nayi tare da kallonshi nace kaima ka zagaya zawarci ba .... ? Na ƙarasa maganar ina nunashi ina dariya , dariya yayi shima cewa ita dai tayi zawarci na , tou mi yasa baka aureta ba ? Ba tsari na bace ba , ya bani amsa , murmushi nayi nace to wai kuma da gaske tana da aure ? Eh mana tana da aure hada yaranta amma bata aihu da Bello ba , tou Baba amma kuma naga kamar karuwa ce ! Yace Eh me yasa kika ce haka ? Shiru nayi dan dai babu dama na bashi labarin abinda ya faru tsakani na da ita akan iyayensu Amisty ,

Share maganar nayi da son nayi mishi maganar su Amisty amma sai kawai zufa taci gaba da kwararomin , kaina ya ci gaba da tafasa zuciyata tanamin wani irin zafi , lokaci guda kuma É—imuwar tunani ta sake zuwa min , kallona Baba yai yace ya akayi kuma kinyi shiru ? Saboda hijabi ne jikina da yaga irin zufar da nakeyi...

Miƙewa nayi kawai na koma cikin gida , ina shiga Nana ta nufoni tana magana ko saurarenta banyi ba bare insan abinda take cewa , ina zuwa ɗaki na faɗa saman katifa na dafe kaina wai meke faruwa dani ne......?

Gaskiya Bello baka da mutunci kuma kaci amanar amintaka Allah bazai barka ba , Mamy ke faÉ—awa Bello magana dan daga gidansu Sultana wurinshi ta nufa kai tsaye , dariya Bello yayi yace umm dama nasan sai kin hallara ai mayya , wai me yasa kike san Binna da yawa haka ne ?

Murmushi Mamy tayi tace duk abinda yasa ma nake maitar tashi ka sani kuma maitarshi yanzu na fara , dariya yayi yace iska na wahar da mai kayan kara kuma wallahi kika sake dawomin da hannun agogo baya saina shafe babinki a saman doron ƙasa ... Dariya Mamy tayi sannan tace ina jiranka , tana faɗin haka taja motar ta tayi gaba...

Ranar juma'a da daddare bayan na gama sallar isha'e na fito da makullin mota ina sauri dan jirana Baba yakeyi sai kira yake kwalamin , ina fitowa Nana tace Alaji yazo nemanki bansan kina nan ba aka ce masa bakya nan , ko inda take ban kalla ba , muka fita daga gidan dani da Baba majalisarsu zan ajiye shi yacemin yanajin sauƙi naje na kaishi yaga abinda ake ciki ,

Ina ajiyeshi na dawo gida ban biya ko ina ba , ko parking ban gama gyarawa ba na hango wata mota a gabana kamar ana kokowa a ciki sakamakon haskasu da nayi da fitilar mota ta , da sauri na fita daga cikin mota ta na tun karesu ina zuwa na buÉ—e motar wai in rabasu , me zan gani.... Haka ?

Ƙanwata na gani ana iskanci da ita a cikin motar watanni biyar na bata da aihuwa , kallon saurayin nayi sannan na kalleta nace me kukeyi haka ne ? Babu damuwa ko fargaba a tare da ita sukaci gaba da abinda sukeyi , jiki a sanyaye na rufe musu ƙofar na koma motata na zauna ina jiran su gama ,

Hawaye naji ya cikamin ido nasan duk yadda akayi kila ta nemi wani abu ta rasa kuma ta tambayi Baba kawai zaice taje saurayinta ya bata , kwantar da kaina nayi saman sitiyarin mota ina goge hawaye , zata fito zan mata faɗa nace duk abinda take so ta faɗamin zan riƙa bata ,

Ai ban gama tunanin ba kaina ya juye , zuciyata tace karki wani yi mata nasiha kinga kin samu ƙarin fasinja daga nan zaki samu tayo miki yaƙi da "ya "yan gidan Baba ƙarami kawai kuci gaba da sha'aninku tunda kun rabu dasu Amisty , murmushi nayi tare da cewa tabbas haka za'ayi...

Dama ranar dana dawo naga kowa sai janye ɗanshi yakeyi karna gurɓatashi , zuciyata tacemin Eh kiyi ƙoƙari ki yaƙi duk wanda ya kyamaceki kinga idan kowa ya zama ɗan iska abun zai miki sauƙi wurin gori ,

Haka ne fa , ina ƙoƙarin fita a mota shima yayi parking in tashi daga bayana ya riƙa wasa da fitilar motarshi , ta kashe ta kunna , rufe mota ta nayi na nufi saman dakali inda zan jira fitowar "yar uwata ,

Ina zuwa dai² motar zan wuce ya buɗe murfin motar ƙamshin shi da sanyi a c suka lulluɓemin kaf ilahir ɓargon jikina , a kasalance na tsaya tare cewa ashe kaine ? Ey mana nine nazo gaishe shi , murmushi nayi na kunna fitilar wayata dan idanuwana sun ƙagara suga fuskar Dikko , haskashi nayi yaɗan shanye idanushi saboda hasken fitilar...

Sai ya ɗan rufesu ya buɗe su yayi haka yakai sau biyar sannan yace kinasan ki ganni ne ko ? Bara na kunna miki fitila ki ganni sosai , da sauri na kashe fitilar wayata na taɓe baki nace wa ni ? Tirr Allah ya sawaƙemin me zan kalla fuskarka , a dai² lokacin daya kunna fitilar motarshi yana cewa kinfi kowa sanin abinda kike kallo....

Murmushi yayi tare dayimin wani irin kallo yace ya kika gannin ne ? Ya ƙarasa maganar yana kashemin ido ɗaya , juya mishi baya nayi ina murmushi cikin jin kunya , gyara zamanshi yayi yana cewa bari in tafi zuwana kenan nace saina fara ganinki yakai hannunshi ya kashe fitilar daya kunna ,

Harararshi nayi tare da cewa kuma bakai kyau ba , dama banda abinki meya haɗa namiji da kyau ? Kece dai mai kyau kuma daga yanzu idan na kiraki saima na riƙa cewa ya kyau ? Zan tafi yayi maganar yana rufe motar , shiru nayi banyi magana ba dan bana san ya tafi kuma shima ya gane haka ,

Sauke gilashin motar yayi ya kwatar da kanshi saman murfin motar yana kallona ta sama yace ko kar in tafi ne ? A , a , a , a kawai kaje abunka , cikin sigar zaula yace kedai....... In tsaya ki ƙara gani na ko ? Matsawa nayi ina cewa wuce , murmushi yayi tare da cewa to na wuce sai Allah ya kaimu , nace amin , ɗage gilashin motarshi yayi ya fice da rubos tun daga ƙofar gidanmu har bakin titi , yana fita yaci taya ya ɓace abunshi , murmushi nayi komai na Dikko burgeni yakeyi ,

Cike da soyayyarshi na isa bakin dakali na zauna , ban daÉ—e da zama ba ta fito zata shige gida nace yaki Hamida , zuwa tayi tace gani , cikin tausayawa na kalleta dan itama babu uwarta a gidan , nace Hamida kin tambayi Baba wani abu bai baki ba ko ?

Shiru tayi tana kallon ƙasa , nace kimin magana kinyi shiru , yanayin ta ya nuna bata san ta faɗamin abinda ya faru dan sunsan bana san laifi Babana , tou tun yaushe kika fara wannan harkar ne ? Tace an daɗe gaskiya , nace yanzu har kinsan daɗin namiji kenan ko ? Daga gefenmu naji maganar Fa'iza na cewa wai na cikin masai ke cewa na waje ya taka kashi , nawa kike Sultana ? Kema kinsan daɗin namiji bare ita ko an faɗa miki ita dutse ce ba mutum ba ? Duk yadda kikeji itama irin abun takeji , ko nufin ki kiyi mata nasiha ? Keji Sultana da buƙulu zatama yarinya baƙin ciki ,

Ba tare dana kalleta ba nace ke kuma ina ruwanki da firarmu ? Da ruwana mana idan bata samo kuɗinta ba kece zaki riƙa cida ita ne ? Fita sabgar Fa'iza nayi nace nawa ya baki ne ? 150 zaro idanuwa nayi nace 150 sai kaci yaci yaɗi ? Fa'iza tace waike Sultana ina ruwanki da rayuwarta ne ? Ko ke wani ya shiga taki sabgar ne ? Banma Fa'iza magana ba naci gaba da cewa aiko kina karuwanci wahala gaskiya , janyeta Fa'iza tayi tana cewa kyaleta idan kika biye mata sai yinwa ta kamaki a gidan nan , tunda Allah ya baki kin samu na kalacin safe...

Suna gaf da shiga gida nace Hamida idan zaki iya huɗɗa dani kizo zan kaiki inda zaki samu kuɗi karki kuskura ki bari a koya miki toya awara a ƙofar gida hayaƙi ya kashe miki ido , kizo in haɗa da wani Alhaji ki biya buƙatarki kuma ga tulin kuɗi , Fa'iza tace naje na toya awarar dan uwarki , dama habaici ne nake mata kuma taji haushi tunda ta tanka , Fa'iza taci gaba da cewa kuma ita bata bin manyan Alhazawa ta bar miki kije kija , nace kece shedar inaja tunda kinga motar da nake hawa , danni ba sakara bace bana barin namiji ya hauni ya a banza ya sauka ni kuma in tashi a 150 ko doki namiji zai hau sai bada kuɗi da yawa bare kuma mace mai daraja....

Idan dai ka murza tou tabbas nima saina murje aljihunka fess , janta tayi sukayi shige gida , dariya nayi nima nabi bayansu , ina cewa 100k idan kin shirya ki sameni É—akina...

29/09/2019

*JAMILA MUSA....*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 44

Ina ƙoƙarin shiga ɗaki Nana ta taho wurina a firgice jikinta yana kyarma tace Uwar room zo kiji wani abun tashin hankali , a firgice na kalleta nace kai miye haka har kin bani tsoro wallahi , magana ƙasa² tace zo muje ƙofar gida tayi maganar tana jan hannuna har muka fito waje...

Muna fita ta fara waige² irin yanda magulmata keyi idan zasuyi kilbibi , bayan ta tabbatar babu kowa tace da Amisty da Hafsa suna asibiti , a nutse nace meya samesu ne ? Ƙara matsowa kusa dani Nana tayi kamar zata koma cikin cikina tace gidan matar da suke zuwa...

Meya faru a gidan ? Nana tace mijinta yazo ya samesu suna maɗigo , { Lesbian } Asma'un tana ganinshi ta fara kuka ashe sun manta basu rufe ƙofa ba ya rutsasu duk sun haye mishi mata , Asma'u tace ya rufa mata asiri tana cewa ita wallahi ba halinta bane cutarta kawai akayi tana bashi haƙuri ,

Bai mata magana ba ya koma ya kulle ƙofa , bayan ya kullo ya dawo yace kiyi haƙuri my wife ba wani abu da zai faru sukadai yi miki haka ko ? Tace Eh yace tou koma gefe yanzun nan zan rama miki abinda sukayi miki , wayarshi ya ciro daga aljihu ya fara kiran abokanshi yana cewa suzo gidanshi yanzu akwai babban aiki kuma kowa ya shawo ta dubo ya taho dan yau a gidanshi za'ayi kwana ana wasan *DANBE...* shagon mada da shagon gwaggo zasu buga babbar lamba...

Bayan ya gama waya ya hunce tare da jawo ƙarfar Hafsa yace kece kika sha mata nan ko ? Ya ƙarasa maganar tare da taɓa inda yaga tana ma matarshi , cikin kuka Hafsa tace dan Allah kayi haƙuri tsautsayi ne , mijin Asma'u yace ai nima tsautsauyin zan nuna miki , Hafsa zata sake magana ya haɗe bakinshi da nata , wata irin ƙara Asma'u tayi ba tare daya kalleta ba yace Swry madam rama miki zanyi....

Cikin kuka Asma'u tace dan Allah kar kayi , har yanzu bai kalleta ba yace tou ni banza ne inzo in samu wasu na ƙwaƙulemin mata in barsu su tafi a haka ai wallahi ko waccensu saina bata tukwuici , kowa a cikinsu sai taji nauhi na , ihu Asma'u takeyi tana ba mijinta haƙuri baya ji kuma baya gani , kusa dashi ta matsa ta riƙoshi wani irin mari yayi mata wanda yasa tayi zaman dirshen dole a katsa ,

Haka ya farke Hafsa tas kuma bashi ne farko ba shima akan hanyar wani yabi ya wuce , bayan ya gama ya jawo Amisty itama ya kaita , yana gamawa da Amisty ya sake jawo Hafsa saidai ya zagaya ko waccen su so 3 sannan abokanshi suka shigo suma sukaji yanda kowa keji , bayan sun gama yace itama Asma'u suyi mata , ke a gidan dai haka aka kwana bala'e ana zagaye ² har gari ya waye , da safe kuma ya bawa Asma'u saki 3 gaba ɗaya , kai naga cikakkin *KWARATA...*

Wato a gabanki akayi komai kenan ko ? Na tambayi Nana , tace a , a ina ni ayi a gabana ? Ita Amisty tamin waya na taro musu mai napep , dani dasu Zalifa mukaje dan har muka isa asibiti Hafsa bata farko ba , itama Asma'u taji jiki sosai dake Amisty jar wuya ce ita bata wani damu ba ,

Shiru nayi ina kallon Nana zuwa wani lokaci nace mata miye wasan *DANBE... ?* Nana tace wani sabon iskanci ne maza ke zuwa su saka kuɗi a jera musu layin mata , ko wane namiji zaibi mace goma wanda yakai ba tare daya gajiya ba kuma ya gamsar da ko wace a cikinsu tou dama kuɗi ake zubawa , idan ko wace ta samu biyan buƙata kuma namiji bai huta ba tou wannan miliyoyin kuɗin nashi ne shi zai lashe su , tou ai irin *DANBEN...* mijin Asma'u yakeyi, shine sana'arshi...

Haka nan naji raina ya ɓaci wato Dikko kallo yake zuwa shima shi yasa naji yana cewa Saminu a wurin wasan danbe ya haɗu da wata ya bita baisan matar aure bace ba ,

Cike da ɓacin rai na koma cikin gida , ina shiga ɗakina na ɗauki wayata na fara kiran lambar Dikko , na kirashi yafi sau a irga amma bai ɗauka ba , zuciyata tacemin yana can kallon Danbe , raina ɓace na koma ƙofar gida na ɗauki mota ta na ibi hanyar goruba road , dan nasan irin wannan lokacin suna can suna kallon kwallo , 10:29pm na isa , inayin horn aka buɗemin get na shige...

Motoci sunfi goma a harabar gidan , dama nabar wasu a waje ma , cike da ɓacin rai na sauko ko ganin gabana banayi na tun kari palon , ashe ina fitowa mota ya ganni dan haka ya taso da sauri dan ya tareni , a bakin ƙofa ya tsaya ya raba hannunwa shi ya tare ni , kwantar da kanshi saman kafaɗarshi ta dama yace An mata lafiya ?

Cikin ɓacin rai nace ashe kai ɗan iska ne , da sauri ya buɗe bakinshi cikin yanayi mamaki yace me kuma yayi zafi haka ? Nace ban sani ba , ɗan buɗe idanuwanshi yayi sosai yace tou ai kin bani dunƙule bansan abinda nayi miki ba , kince ni ɗan iska ne nace me akayi kuma kince baki sani ba ,

Rufe idanuwana nayi hawaye na zubowa nace ashe danben ranar nan da kake magana iskanci ne , dariya Dikko yayi tare da sauko hannayen shi daga inda ya ɗorasu , jan hannu na yayi muka koma cikin mota ta , bayan mun zauna yace waye ya faɗa miki ? Banyi munafinci ba na kwashe kaf na zayyanawa Dikko labarin da Nana ta bani , dariya yayi sosai yace tou ni bana zuwa kallon danbe ban taɓa zuwa ba , ina da labari dai kuma abinda yasa kikaji nayi maganar danben a waccan rana shi Saminun abokina ne , kuma shine ya kirani yake faɗamin abinda ya faru dashi , kuma nace kizo muje kikace baza ki ba , da wannan abun yasa kika taho ? Da Allah baisa na ganki na tareki ba da haka zaki zo ki ɓara maganar gaban mutane ?

Tou ni ban taɓa kallon danbe kowa ba sai nawa da naki , kuma ina addu'a ubangiji ya tabbatar min dake a matsayin mata ta naci gaba da miki kina alfahari dani , yanzu kin yadda kinajin soyayya ta ko ? Ya ƙarasa maganar yana leƙo fuskata , kauda kaina nayi saboda kunya , Dikko yace kinga kinyi kuka dan kina tunani DK n ki yana zuwa kallon danbe , ki kwantar da hankalinki Dikko naki ne ke ɗaya da izinin ubangiji , ni bana zarginki har abadan duniya anma dan Allah karki sake ki bari zuciya da sharrin shaiɗan yasa aimin wasan danbe dake , ni ɗaya tak na isheki bana gajiya kuma bazan taɓa gajiya dake ba har ƙarshen numfashi na ,

Kwantar da fuska ta nayi saman sitiyari nace to me yasa gwamnati baza ta hana wannan saɓon ba ? Dikko yace tou waye yasan sunayi ? Bayan sun ɓoye babu wanda yasan inda suke sai su kaɗai , muna tare dasu muna cuɗanya bamu sansu ba tunda ba rubutawa akeyi a jikin mutum ba , yanzu dani dake da muka ɓoye mukayi waye ya sani ? Babu wanda ya sani daga ni sai ke sai Allahn daya haliccemu kuma kullum ina neman ya gafarta min kuma ai kin yafemin An mata ko ?

Shiru nayi banyi magana ba , kallon agogon hannunshi yayi yace kizo ki tafi gida dare yayi ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin fita daga motar , nidai bana so ya tafi banƙi mun kwana muna magana ba , dan wallahi maganar Dikko daɗi gareta ga sa natsuwa wani irin harshe yake amfani dashi wurin magana nidai tunda nake ban taɓajin irin yanayin maganarshi ba , amma shi na lura baya san yana daɗewa tare dani , ƙara maido maganar baya nayi cewa ,

Tou baka san Saminu ba , yace An mata ƙungiya ce fa , kuma daga jin irin kuɗaɗen da ake zubawa ai kinsan ba talakawa bane ba , can matsalarsu suyi rayuwarsu muyi namu rayuwar manta da sha'anin wasan danbe kin fara so na yanzu ko ? Shiru nayi , yace tou nidai ina sanki kuma kullum saina faɗa ,

Maganar abokinshi naji yana cewa DK wace "yar yarinya ce ka ƙurmusa a mota ? Fita yayi yana cewa An mata ce zo ku gaisa da ita , a tadai zo ta gaisheni baka faɗa mata ni yayanka bane ? Ya ƙarasa maganar yana zama saman bayan mota , ba tare daya bashi ansa ba ya maidai fuskarshi kamar yadda take wato ya ɗaure tare da rufe murfin motana yana cewa Allah ya tsare hanya ,

Kunna mota ta nayi zan fita , gaba ɗaya mazan dake palon suka fito suna cewa mai gadi karka buɗe yau sai munga "yar matan da yake ɓoyewa , cikin ɓacin rai Dikko yace kai buɗe mata hanya ta wuce , da sauri ya fara ƙoƙarin buɗewa su kuma suna cewa idan ka bari ta fita bamu ganta ba wallahi ubanka zamuci , Dikko yace wai da Allah mi yasa kukeyin abu wani iri ? Koma ce mana kayi mahaukata wallahi sai mun ganta ,

Dikko yace ashe kuwa zakuyi kaffara , kallon mai gadin yayi cikin tsananin fushi yace na rantse da girman Allah ka buɗe get in nan idan kuma baka buɗe ba na rantse da wanda rayuwata ke hannunshi saina taka ka da mota in take ka mutu kamar ɓera kuma babu abinda za'ayi na kashe banza , sanin hali yafi sanin kama , da sauri ya buɗe get in duk zagin da ake mishi ni kuma na fice da da gudu...

Sultana tana fita sukayi kanshi suna zagi dan ubanka ba cewa mukayi karka buɗe mata ba ? Mu da bama bi takanka da mota ko ? Faffala mishi mari kowa yayi sannan suka bi bayan Dikko daya koma palo ya kira Sultana yace karta sake zuwa idan tana san ganinshi zaizo ya sameta ko tana ina , tace insha Allah , bayan ya gama wayar yace hmm An mata ta rainani , bata ganin girmana ko kaɗan , tacemin ɗan iska munafiki hada mari , idanma ban auri yarinyar nan ba ai ta gama dani duk lokacin data ganni tana min kallon sakarai na nasha dakai , duk borinki na waje ne bari dai in lallaɓaki kizo hannu zaki gane ruwa ba sa'ar kwando bane...

Saida na biya ta majalissa akacemin Babana sun tafi wasan caca , raina ya ɓaci naji banji daɗi ba ace daga fara fitowarshi harya fara zuwa caca , ƙaraurawar kaina ta buga dan haka na manta da ɓacin rai nayi gida abina...

Washe gari ranar asabar tunda safe Mamy tazo gidanmu , kuma har yanzu Babana bai dawo ba , da murna na tareta muka shige É—aki abunmu , bayan mun gaisa ta tambayeni na tuno abinda zan faÉ—a mata ranar laraba data zo ? Nace mata Eh , wayar na É—auko na bata nayi mata dukkan bayani amma ban faÉ—a mata Dikko bane ba ,

Layin kawai ta cire daga cikin wayar ta bani wayar ta saka layin a jaka , nace da Allah Mamy wai da gaske kina da aure ? Tace ina da aure Sultana , nace keko me yaja miki bin mazan waje ? Bayan ga naki a gida ? Naga wasu ma basu samun ƙoshi ɗaya a bayan wasu shekaru { wanda basu da mazaje , basu da masu kwantar musu ko sauke musu sha'awarsu } kuma sunayin haƙuri keko naga kamar kin girtse da yawa...

Kici abincin gidanku kuma kici na gidan wasu , murmushi Mamy tayi tare da cewa aike yarinya ce bakya gane inda aka dosa gashi kuma kwalwarki tana tafiyar ɗimuwar rabin sa'a , murmushi nayi tare da cewa gaskiya ne inajin ƙaraurawar hauka tana bugamin duk bayan wasu "yan mintuka , Mamy tace da yanda idanuwanki da zuciyarki suke ganewa haka kanki ke ja da anyi alfahari dake , kauda kaina nayi gefe nace kwantar da hankalinki ina da ayyuka ne a gabana amma nasan komai zai warware ,

Mamy tace Allah yasa , zatayi magana kiran Hafsa ya shigo wayarta , ɗauka tayi tare da cewa Hafsa ya jiki cikin murna Hafsa tace Aunty ai jiki ya warke matar Dikko ta mutu , shegiya an gaji da ƙwaƙwar duniya an tafi anya mayyar matar nan baza tayowa mutane fatalwa ba ,

Mamy tace innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , ke waye ya faÉ—a miki ne ? Tace Mom ina taje ganinta safiyar nan tana can ma ta rasu amma tace Dikko yaji mutuwar saboda yana zaune kusa da ita tana bashi labarin abinda ya faru da ita bata gama bashi labarin ba ta zuge gilashi ta kama gabanta ,

Tou Allah ya jiƙanta ubangiji yasa mu cika da imani ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo amin , Hafsa tace yanzu tashin hankalina kuma ɗaya kinaji saura sati ɗaya a daura mishi aure , Mamy tace Hafsa bari anjima zamuyi magana , tana faɗin haka ta kashe wayarta ,

Wayoyin mutane ta fara kira tana tambayar da gaske ne matar Dikko ta rasu ? Abunka da masu jaha magana ta karaɗe kaf gari , kowa Mamy ta tambaya sai yace mata Eh ta rasu , kallona Mamy tayi tace kodai maganar mutane ta tabbata ? Nace me mutanen suke cewa ne ? Ƙasa² da murya tace kinsan kuɗin gwamna suna firgita al'ummar , ɗanshi kuma ya taso da ƙarfin dukiyar da ubanshi kanshi abun tsoro yake bashi ,

Anyi itifaƙi kaf gwamnonin nigeria babu mai kuɗinshi , danshi tunin duniya dama yayi kuɗinshi ba'a siyasa ya samesu ba , siyasa daya shiga kawai neman suna yasa ya shigeta amma badai kuɗi ba , to shi kanshi daya haifi Dikkon yana tsoron dukiyar shi , mutane cewa akayi wai ɗan nashi matsafi ne , dama tunda matarshi ta fara rashin lafiya akace ya tsafeta mutuwa zatayi ,

Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji , yayin da zuciyata tace ki rufe idonki ko sau ɗaya ne kiyiwa Dikko adalci Sultana , rufe idona nayi gaba ɗaya a halin Dikko babu ɗaya na zaɓe , Mamy tace da zan baki labari amma gaskiya tashi zanyi na sake dawowa , nace tou , har ƙofar gida nayi mata rakiya saida ta tafi na dawo gida ,

Tunda Mamy ta tafi nake saƙawa nake warware , me yasa Dikko ya zaɓi tsafi ? Me zaiyi da kuɗi dattin duniya da za'a koma ga Allah a barsu a duniya ? Tsikar jikina sai tashi takeyi ,

Har akayi kwana bakwai da mutuwar Sadiya ban daina tunanin maganar nan ba , Dikko kuwa ya kirani har bansan adadin kiran ba amma naƙi ɗaukar waya , daga ƙarshe ma kashe wayar nayi gaba ɗaya ,

Marecen yau kuwa ina ƙofar gida duk abin duniya ya dameni na rasa ina zan saka rayuwata naji sanyi , tunani ya dameni na babu gaira babu dalili , tsayuwar mota a gabana tasa na ɗago kaina da sauri dan a tunani na Baba ne , Dikko ne dan haka na tashi da sauri a daidai lokacin daya sauko daga saman mota , yana fitowa na taga ƙafa ina ƙoƙarin rugawa , a zuciyata nace an cuci sunna gaskiya ga gemu ga tambarin sallah wallahi ka ɓata kyanka ,

Ya kusa isowa inda nake na ruga da gudu ina wayyo Allahna......

29/09/2019

*JAMILA MUSA....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 45

Tsaye yayi yana kallona , ni kuma da gudu nayi cikin gida har na kusa faÉ—uwa , a mamakince Dikko yabi Sultana da kallo a ranshi yana cewa ko lafiya ?

Mota ya koma ya gyara parking , yayi zamanshi ciki bai fito ba ranshi ɗauke da tunani daban ² , ga zafin mutuwar matarshi ga ciwon auren da za'a ɗaura mishi wanda rasuwar Sadiya yasa aka ɗageshi , ga iyayenshi sam² sun rufe idanuwansu akan aurenshi da Sultana...

Ya É—an rame har yayi duhu saboda damuwa da tunani , a gajiye ya fito daga cikin motar ya nufi gidanshi , kafin ya ida shiga Baban Sultana ya faka tashi motar daga can gefe dan kar yayiwa Dikko laifi...

Dikko yana ganinshi ya dawo suka gaisa , bayan gaisuwa yace am dama ina san ganin wannan yarinyar ne , cikin damuwa Baba yace ta sake janka ne ? Fuska dai a murtuke babu fara'a yace a , a zanyi magana da ita ne kawai !

Baba yace tou Allah dai yasa lafiya , a É—an rashin jin daÉ—i Dikko yace ba komai fa , shi baya so yayi ta nanata magana kuma anajinsa amma a kasa fahimta ,

Cikin gida Baba ya nufo zuciyarshi cike da damuwa , tunda ya shigo gida yake kwalamin kira kamar ranshi zai fita daga jin yanayin maganarshi babu daÉ—i a zuciyarshi ,

Da gudu na fito ina tambayar Baba lafiya , cikin faɗa yace me ya sake haɗaki shiga sabgar yaron can mara mutunci kuma ? Ɗan iskan yaro da baya ganin kowa da mutunci , ya raina arziƙin duk wani mai farin gashi dake doron ƙasar nan , fitinanne yaro dako bakin duniya baya tsoro ga rashin mutunci da masifa kamar kishiyar ɓarauniya...

A ruɗe nace ni babu komai , dakamin tsawa Baba yayi yana cewa babu komai inji waye ? Gashi can ya kafe mota ƙofar gida yana ɓacin rai duk abinda nace bana so sai kinyi Mamana kina so dai ki samin ɓacin rai idan na mutu kin huta ,

Hannuwa na duka biyu na ɗaga alamar bada haƙuri nace a , a Babana kayi haƙuri don Allah , dan bana so naga Baba yana fushi akan komai bare kuma ni daya ɗauki soyayyar duniya ya ɗoramin ,

Sassauta murya yayi cikin tausayi yace tou kije ki bashi haƙuri nidai bana so kina jawoshi faɗa uwar masu gida , nace tou Baba , a tsorace na fita ƙofar gida gabana sai faɗuwa yakeyi ,

Dikko yana tsaye ya jingina da mota , da gudu na isa inda yake na riƙe hannayen shi , na irin gani karka kasheni , kallona yayi cikin sigar so da ƙauna yace tou kin kama min hannaye ai gara ki riƙeni gaba ɗayana tunda abin har yakai ga riƙe hannu ,

Sakin hannuwan nashi nayi na É—aga kaina na kallo cikin kwayar idonshi , wani irin kallo yayi min kwayar idonshi tana motsawa a hankali wanda idan baka iya saka ido ba baka gane motsi takeyi ,

Hmmm me yasa kika gudu da kika ganni ? Ko na zama dodo ? Bansan abinda yasa bana iya ma Dikko ƙarya ba amma da nauhi wannan kalma mai muni ta fito daga bakina ,

Tou tunda baki da abun faɗa ni zan faɗa nawa , shiru nayi ina saurarenshi , yace zanyi tafiya kuma bana tunanin idan na tafi zan dawo yanzu , bana so na shiga haƙƙinki da yawa dan ina baƙin ciki kiyi damuwa a rayuwa , ina so miki farin ciki bana so kiyi kuka haka kuma bana so ki kasance cikin damuwa ko ƙunci ,

Na baki daga yau zuwa jibi kwana biyu kenan ko ? Ya tambayeni , ina kallonshi banyi magana ba , yace tou kije ki natsu kiyi sharawa da zuciyarki shin kina so na ko bakya so na ?

Cikin yarinta nace ni bama sai nayi shawara ba gaskiya bana sanka , kallona yayi sosai yace karkiyi ƙarya An mata zakiyi nadamar hakan wata rana , nace wai ni ? Na ƙarasa maganar ina masa kallon rainin wayau nace Allah ya sawaƙemin ai baka cikin tsarin mazan da nake so , cikin damuwa yace .

Kina da matsaloli fa daban ² An mata , saurara samar da farin ciki a domin ɓatawa wani ba dai² bane , haka zafin murmushi a yayin da wani yake baƙin ciki da takaici hmm baya da amfani , karki damu kawai cewa zakiyi ina sanka , shi kenan fa babu wani wahala , uhum kana ba kanka wahala kaji , ince ina sanka ? Allah ya sawaƙemin ,

Murmushi Dikko yayi maicin rai yace tou ni kuma na san a cikin kwanaki biyu da wannan taurarin idanuwan naki zaki zamo masoyiyata babu jayayya , zaki zo ki rumgumeni , numfashinki zai shiga kwalwata, zaki kalli idanuwana , ina sanka , idan har baki faÉ—a kina so na ba , shiru yayi yana kallon fuskata , zuwa wani lokaci yace sai kin faÉ—a , yana faÉ—in haka yayi tafiyarshi ya barni a wurin...

Cike da damuwa na koma gida yayin da zuciyata ke shawarta ta ince ina san Dikko wata zuciyar tace karki sake ki faɗa ko zaki mutu ki barshi kawai kuje a haka , kina mace kice kina san namiji haba ai kinci ƙasa ,

Lokacin da kwana biyu ya cika zuciyata ta gama tabbatarmin da bata san Dikko , dan haka kuma na yanke shawarar sanar dashi bana sansa yayi haƙuri ,

Da daddare bayan yazo ya aiko aka kirani dan har yanzu ban kunna wayar ba tunda na kashe ta ban sake buÉ—ewa ba , bayan na fita muka gaisa dashi , bayan gaisuwa yace ina saurarenki , nace gaskiya ansar dana baka tun farko itace har yanzu ,

Shiru Dikko yayi , bayan wani lokaci yace , wannan rana ta kasance min ranar juyayi ne , bana fatan wannan ranar ta sake zomin , ranar ƙarshe kenan banda wani ƙwarin guiwa , An mata ce kaɗai abin alfaharina , umm abinda bana so ya kasance duk lokacin dana runtse idanuwana nakan iya ganin kyakkyawar fuskarki , bansan mace ba sai a kanki idan har na taɓa san wata mace a rayuwata to kece An mata ,

Zan tafi idan har naci gaba da ganinki to zan ɓata miki , kiyi haƙuri bazan sake kiranki ba , haka ma zuwa ba zaki sake ganina ba An mata , kin daɗe kina ƙonani inajin kamar na rasa wani abu , me zanyi ? Bazan iya koda dariyar ƙarya ba , jawoni yayi ya rumgumeni duƙowa yayi ya kwantar da kanshi saman kafaɗa ta , cikin wata irin murya mai tsayawa a zuciya yace sai wata rana , ki yafemin don Allah karki riƙeni zan fita daga rayuwarki dan ina so kiyi farin ciki , zan tafi ki huta koda kuwa ni zan shiga halin damuwa ,

Bayan wani lokaci ya ɗago ya kalleni , cikin kallonshi mai ɗaukar hankali yaɗan ɗauki lokaci yana kallona sannan yazo dai² bakina lumfashin shi yana fitowa saman fuskata , gashin gemunshi yana shafar dai² saitin bakina , lokaci guda jikina ya canja tsikar jikina ta tashi ban taɓa jin irin wannan yanayi ba , bafa haɗa bakinmu yayi ba , daga waje ya sunbace ni wani abu naji ya shiga jikina da gudu saida ya gama zagayawa ya dawo zuciyata ya shiga da ƙarfi , ajiyar zuciya na sauke yanajin nayi ajiyar zuciya ya sakeni da sauri daga jikinshi yaɗan turani baya yace ki tsaya da kyau karki faɗi , zan bada saƙo Umar ya kawo miki kafin in wuce ,

Kasa magana nayi nabi shi da kallo da sauri ya shiga mota ya bar ƙofar gidanmu da gudu , har ya fita daga anguwarmu ina tsaye a wurin daya barni , yana ɓacewa na kyalkyale da dariya , na zabgaga wani irin ihu , daga cikin gidanmu Zainab ta fito da gudu tana tambayata lafiya ?

Sai dire² nakeyi kamar anyi ma doki allura ƙarfi , Zainab tace wai miye yake faruwa haka ? Goge hawaye nayi nace har yanzu na kasa yadda da wannan , Zainab tace miye ne kika kasa yadda dashi ? Nace masoyina ya faɗamin dukkan na kasunsa , shi da yace zan rungumesa sannan na faɗa masa cewa ina sanka DK ,

Zainab tace waye DK murmushi nayi nace baki sansa ba , Zainab tace tou ki faɗa masa kina sansa mana , nace ke jinan ya nunamin yatsansa yayin da yake ƙalubalanta ta cewa a cikin wasu kwanaki zance ina sansa , murmushi nayi tare da rufe idona , nace kamar dai yadda yace naji ina sansa , ƙara ɗaga murya nayi ina sanka mutumi na , ina sanka , Zainab tace to me yasa baki faɗa a gabansa ba ? A , a , a , a , idan na faɗa masa tou zaiyi ta jamin ƙafane har abada , Zainab tace zakiyi duk abinda kike so amma kuma idan kika makara a soyayyarshi fa ? Nace sam ² ki rabu dashi kawai yayi kuka na wannan daren nasan bazaiyi zuciya ba da safe zai sake zuwa , ni kuma yana zuwa zance barka dai DK idan ba tare dakai ba ina ne zanje .....?

Cike da farin ciki na shiga gida , Zainab ta rufomin baya , alwallah nayi na shige cikin É—akina ina farin ciki ,

Dikko kuwa yana isa gidanshi wanka yayi , bayan ya shirya ya ɗan faffaka abu mai mahimmanci ba kaya ya ɗauka ba , wasu takaddu ne kawai ya tattara , layinshi ya cire ya ajiye , dube² yayi na irin banyi mantuwa ba kuwa ? Sannan ya fita daga cikin ɗakin ,

Wajen da aka tanada dan ajiye motoci ya samu Umar kamar yadda yace su haɗu , Ashiru a gefe sai Al ' Ameen , duk gaisheshi sukayi cikin girmamawa , bai ansa ba , makullin mota ya miƙewa Umar tare da nuna mishi mota yace ka kaima yarinyar nan akwai kuɗi a but in tasha mai , Umar yace mai gida wace yarinya ? Yarinya nawa kasan ina tare da ita ? Haƙuri ya bashi tare da cewa tou ai naji bakace An mata ba , murmushin baƙin ciki Dikko yayi a zuciyarshi yace tace bata so na , kuma fa ba'a soyayya dole Allah ma yasa bansha wahalar shawo kan kowa ba dasai nasha wahala na shawo kan iyayena tace bata aurena , gara kawai na haƙura nayi nesa da rayuwarta na barta ta huta , Umar kallon motar yayi Al ' Ameen ma ƙwalalo idanuwa yayi cikin tashin hanki yace mai gida wannan motar zaka bata ?

Cikin ɓacin rai yace Ey ita zan bata , cike da hassada yace ko ka manta nawa ka siyota ne ? Dikko yace kila babanka ya nemomin kuɗin shi yasa na manta , dan wani irin haushin Dikko yakeji kuma Dady yace idan yayi masa wani abu bai yafe masa ba , Al ' Ameen ya kalli motar ya ƙiyasta kuɗinta tou ai wallahi kaf garin katsina wannan motar ita ɗaya ce tak , bazai manta ba lokacin da Dikko ya siyo motar wallahi ganinta ake zuwa yi ana mata hoto ko wata motar batayi ba kuma Dikko bai taɓa hawanta ba , shine zai ɗauka ya bawa karuwa ? Kai amma yarinyar nan ta shanye mai gida da yawa , motar miliyoyin kuɗi haka ?

Kaf ma'aikatan gidan nan suka haÉ—u suna ma Dikko addu'a Allah ya tsare , wallahi game da kyauta dai Dikko baisan darajar kuÉ—i ba , yana kyauta maisa mutum ya kasa gane bacci yake ko idonshi biyu ? Bayan ya gama sallamarsu ya shiga mota Ashiru yaja suka bar gidan ,

Al ' Ameen kuwa sai ƙara kallon motar yake hada kukan baƙin ciki ina ma ɗiyar "yar uwarshi ta samu wannan mota ? Mai gida baisan abunshi haka nan yake neman kuɗin baisan darajarsu ba wallahi , yo wannan mota ai daya sani siyar da ita yayi ya sayi gidaje masu kyau kawai ya ɗauki mota ya ba shegiyar yarinyar da Z bata tantancewa , lallai zaima Yayarshi waya idan har Mai gida ya dawo nigeria Haneefa taje Abuja wurinshi...

Daga gidanshi gidansu ya wuce kai tsaye , danyi musu sallama , momy tace idan an É—aura aure matarka zata isko ka , cike da biyayya yace tou , bedroom ta koma ta É—auko maganinshi tace gashi nan saura idan ka tafi ka yadda shi , ansa yayi ya saka a aljihun wandoshi , addu'a tayi mishi tare da mishi fatan alkairi harya fita , Dady kuma baya nan ,

Cike da soyayya tabi bayanshi da kallo , haka nan taji dai bari ta mishi rakiya , bayanshi tabi har inda ya ajiye motarshi , saida zai shiga mota yaga Momy ta biyoshi , kallonta yayi yace inzo ? Murmushi tayi tace a , a , kusa dashi ta matsa tace karka zo rakiya nayi maka , taci gaba da mishi addu'a Allah ya tsare tana É—aga mishi harya shiga mota suka tafi ,

Tun a mota ya goge hotunan Sultana , bayan yayi musu kallon ƙarshe dayi mata addu'a Allah ya bata miji na gari , ya kuma sa ta yafe masa karta riƙeshi a zuciyarta , shi kuma Allah ya bashi haƙuri da dangana akan ta...

Bayan ya gama goge ²nshi da addu'a shi ya anshi tuƙin motar dan gani yakeyi Ashiru ma baya sauri , tuƙin ganganci da wauta Dikko na fama da iskanci cike da kwalwarshi , ga raini ga rashin ganin mutuncin mutane amma yana da tausayi da taimakon wanda baya dashi ,

10:09pm suka isa kano , anan aka canja abokan tafiya , saida jirginsu Dikko ya tashi Ashiru ya juyo katsina bai kwana ba , sauka lafiya mai gida Dikko Allah ya tsare....

Cikin farin ciki na wayi gari kuma nayi alƙawari yau zan faɗawa Dikko nima ina sansa , duk wanda ya ganni yasan inajin daɗin wannan rana , saida hantsi ya ɗaga na sheƙaƙa wanka na , naci gayuna dan nasan yau Dikko yayi kwanan haƙuri nasan ya ƙagara gari ya waye zai fara zarya ganin dokuna ,

Cike da farin ciki nayo ƙofar gida na zauna ina jiran isowar jarumina , har lokacin zuwanshi yazo ya wuce babu Dikko babu labarinshi , gida na koma na ɗauko wayata na kunna , bayan ta gama kunnuwa na fara neman layinshi , amma dai inajin maganar ɗaya ce kodai wayar tana kashe ko kuma babu kuɗi a wayata ,

Gida na koma nasa aka dubamin ko banda kati , kowa sai yacemin akwai idan nace nawa ne sai su kasa lissafomin , Babana na bashi ya dubamin yace akwai kuɗi , nace nawa ne Baba ? Yace dubu ɗari biyu ne , nace tou kiramin wannan lambar na ƙarasa maganar kamar zan faɗa masa ,

Duba sunan da akayi saving in number yayi yai murmushi tare da cewa iye Mamana ta fara soyayya ya ƙarasa maganar yana kallona kuma cikin zaulaya yayi maganar , cikin jin kunya na zauna kusa dashi ina dafa kafaɗarshi nace aini bana soyayya , yace ai ba wani ne ya bani labari ba nine na gani da idona , tou me yasa kace haka ? A dai² lokacin da yacemin wayar a kashe take ,

Cikin rashin jin daɗi na anshi wayar kaina ya fara min ciwo haka nan naji ɓacin rai ya lulluɓemin zuciya , cike da damuwa na fito tsakar gida , amma sai naga gidan kamar yana juyawa , Baba kuma yana min magana daga bayana wallahi kwata² banajin abinda yake faɗa ,

Wai ance ana kiran Sultana , da sauri na fara kakkaɓa idona daya cika da hawaye inayin dariya cikin farin ciki , nayi ƙofar gida da gudu Babana ya fito da sauri ya biyo bayana yana lafiya ? Turus na tsaya ganin Umar , nayi tunanin zanga Dikko babu shi , sake cika da hawaye idona yayi nace ina yake ? Miƙomin makullun mota yayi a dai² lokacin da Baba ya fito yace gashi yace a kawo miki kuma akwai kuɗi a but wai kisha mai , sai ki bani tukuwici in wuce , nace tou ina shi Dikko yake ya aiko ka ? Umar yace yayi tafiya ,

Kallona Baba yayi yace waye ya kawo wannan motar ? Hawayen da suka taru a idanuwa na suka samu damar gangarowa daga saman kumatu na , da sauri na juya na rumgume Babana ina kuka , É—agoni yayi daga jikinshi yace wai miye ? Waye ya baki wannan motar ?

Cikin kuka nace Dikko ne , kallon motar Babana yayi sannan ya kalli Umar yace wai wane Dikko ne ? Da hannunshi yayi mishi nuni da doki , kallona Baba ya sakeyi yace meke tsakaninki dashi ? Goge hawaye nayi na anshi makullin na buɗe but in motar , bandir in "yan dubu² ne guda goma , guda biyar na ba Umar nayi godiya , shima godiya yayi ya wuce abunshi...

Umar yana tafiya Babana yace wai Mamana ke ya akayi ya baki wannan motar ne ? Nace shi yaga dama ya bani ita ba roƙarshi nayi ba , kallon motar Babana ya sakeyi yace aiko wannan motar bata hawuwa wurinki garin nan saidai a siyar da ita kuma duk ma garin nan bana tunanin akwai mai siyenta shima ƙuruciya tasa ya siyeta , { ba rashin kuɗi baba yake magana ba da yace baya tunanin akwai mai siyenta } babu dai wanda zai ware wannnan kuɗaɗen ya siyi wannan motar kawai dan dai ya hau , murmushi nayi kaɗan nace baza'a siyar da ita ba gaskiya ,

Baba yace ki hauta ace miki wa Mamana ? Nace idan na hauta kaji yadda za'a kirani , tou ina zaki ajiye wannan mota ? Nace gidan dokunanshi zata riƙa kwana ... Allah ya tsare Babana ya faɗa , na ansa da Amin ,

Da kaina nakai ma masu gadin gidan ajiyar mota , suma kansu mamaki ya kamasu ya akayi motar mai gidansu tazo wurina ? Saboda kowa ya sani tashi ce shi É—aya yake da ita duk kaf cikar faÉ—in garin katsina , dan anyi surutun motar sosai a lokacin daya siyota kuma har yanzu ba'a gama ba , wannan ansa basu da mai basu ita....

Na shiga cikin ɗimuwar rayuwa nayi kukan rashin Dikko nayi harna gode Allah , na rasa ina zan saka kaina naji daɗi , "yar jakar daya bani a lokacin da muka kama shago dasu Amisty na ɗauko na zazzage , cingom in daya bani nashi na ɗauka nayi ta ci ina haɗiyewa , saida naji zan mutu na haƙura na tattara sauran na mayar ,

Na faÉ—awa iska ina san Dikko bansan adadin kalamai nawa suka fita daga sautin bakina ba , baida wani amfani dan Dikko dai baya nan kuma bazaiji ba , nayi kukan rashin Dikko har tsawon sati É—aya ina zubar da hawaye duk nabi na rame na susuce , na kira wayarshi kullum dai maganar É—aya a kashe , duk lokacin dana kira wayarshi naji kashe sai nayi kuka kuma bazan daina kukan rashin ka ba Dikko har abadan duniya....

Bayan wata É—aya ,

Abubuwa da dama sun faru , Babana ya warke tas kamar bai taɓa wani rashin lafiya ba , su Amisty kuma an ƙaro iskanci domin dai suma a anguwarmu suka sayi gida ,

Ta siyi motar hawa ta baro iyayenta tana zaman kanta , Nana ma ta tashi daga gidanmu ta koma nasu Amisty , Saude A ` i Zalifa Karima ma duk sun tare a can , Hafsa ma nan take yini amma bata kwana , itama Asma'u anyi mata register kuma suna faɗa cewa yanzu zanga yanda ake shugabar duk wani ɗan iska daya kwana a katsina suna da masaukinshi , idan inajin nima wata ƙwaro ce na kafa manya ²n karuwai kamar nasu...

Lokacin da naji saƙon su Amisty dariya nayi , bana san komawa ruwa dan naji kwata bana sha'awar karuwanci dan zuciyata bata da lokacin sauraren kowa saboda Dikko yabi ya mamayeta da soyayyarshi , kafin inyi wani nazari na yanke hukunci naji gam × ³ a cikin kaina , kamar wacce aljannu yake shiga jikinta haka jikina ya fara fizge² idanuwana sunamin zafi sosai , kaina ya juye , nace tabbas zasu san nawa ba kalar nasu bane mu zuba mu gani dani dasu.

A wannan halin Mamy ta sameni , bayan mun gaisa ta fara rattafomin bayani akan Baban budurwar Dikko , wacce mukayi faÉ—a da ita a mota.....

30/9/09/2019

*JAMILA MUSA....*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 46

Tsare Mamy nayi da ido na kasa magana duk saida ta gama buɗemin komai ta ƙare da cewa harma ta gayyato shi zaizo katsina jibi , har ta gama kallonta nakeyi saida takai nunfashinta ƙarshe nayi murmushi amma har yanzu idona akanta yake , kuma banyi magana ba ,

Mamy taci gaba da cewa tou ya kike ganin za'ayi idan yazo ? Zance gaki ko kuwa ? Shiru nayi na É—ora wayata a saman goshina na rufe idona na dama ina nazari ,

_Kije abunki amma duk abinda zaki kiyi na hankali da tunani ,_

_Ni bana zarginki har abadan duniya anma dan Allah karki sake ki bari zuciya da sharrin shaiɗan yasa aimin wasan danbe dake , ni ɗaya tak na isheki bana gajiya kuma bazan taɓa gajiya dake ba har ƙarshen numfashi na,_

_Jarumi ɗaya tak akeyi a ƙarni nine jarumin wannan lokaci , Dikko jarumin maza ne kuma ke da kanki zaki faɗa kije ki dawo ina nan ina jiranki....!_

Hawaye ya gangaromin daga cikin ido nace a ina kake jirana inzo ....? Murmushi Mamy tayi tare da cewa soyayya ? Shiru nayi ina hawaye , dariya tayi sosai tace har kin bani tausayi Sultana uban waye ya shiga zuciyarki har kike kuka ?

Saida nayi shashshekar kuka sannan na kalli Mamy da ido ɗaya nace ni kike tausayi ? Tace Eh ai soyayya babu abinda ke cikinta sai wahala da dana sanin da bashi da amfani , murmushi nayi mai ƙuna nace gara ki tausayimin dan a halin yanzu banma san a babin da nake ba ,

Yana so na har yanzu ko ya goge ni daga zuciyarshi banma sani ba , dama yace idan bana sansa zai tafi kuma bazai sake dawowa ba , yazo a lokacin da bansan waye shi ba , kuma ya tafi ya barni a dai² lokacin daya koyawa zuciyata soyayyarshi , bazan gaji ba , ba kuma zan daina faɗa ba har kalma na ƙarshe a duniya , ina sanka ׳ Na ƙarasa maganar ina goge hawaye ,

Tsoki Mamy tayi tare da cewa yanzu kinji abinda na faɗa miki , sai magana na gaba , akwai wani mijin ƙawata yaga wata anan anguwar yana so ya ɓata dare ɗaya tak da ita , tou na biyota bayan nayi bincike sai akacemin matar aure ce , dana faɗa mishi sai yace min dama matar auren yake nema shin zaki iya kawo mishi ita ? Akan wane farashi ? Na tambayi Mamy , tacemin 50k nace kai haba zunubin fa akwai girma , yadai ƙara wani abu...

Mamy tace Sultana haka zai baki , kallonta nayi ido cikin ido nace gaskiya ƙarya kikeyi ke kika rage kuɗin da za'a bani , Sultana ni nake ƙarya ? Nace yo wace ce ke da baki ƙarya ? Mamy tace dama naga kin raina ni ko girma na baki bani ? Murmushi nayi da gefen baki na , nace babu wanda ya kawoni bariki ni na shiga da kaina , bana ƙarƙashin kowa ina bisa ƙarƙashin ikon zuciyata ne , banda uwar ɗaki haka kuma banda ubangida , bana nema wurin kowa dan kowa baida abin bani , wannan harkar ra'ayina ne yasa na shiga badan ra'ayin kowa ba , abuna yana jikina naki yana jikinki , tayuwu ke ki bada naki a baki 1k wannan ra'ayinki ne kuma kinji kina iyawa ne , niko babu dalili na buɗewa namijin banza ƙafata ya hauni ya sauka ya bani kuɗin da bazasu kashemin kwarnafi ba ,

Ban kawo ki bariki ba baki kawoni ba ,baki koyamin ba haka nima ban koya miki ba , a rana tsaka muka haɗu kin gama gogewarki nima idona biyu kika ganni ba bacci nake ba , tuni na bushe fitilar idona , banda Aunty banda Yaya banda Mama haka kuma banda uwar ɗaki a bariki wallahi , ta yuwu ma kila namiji ɗaya ya nemu a tare yana gamawa dake ya jawo ƙafata , wane girma gareki a wurina ? Sana'ar fa iri ɗaya ce , uwar data haifeni ma data ga bata iyawa kayanta ta tattara ta kama gabanta tou bare fa ke banzar bazara kashi a masai , na faɗa kuma zan sake maimaitawa idan bakiji ba kiji , idan kuma kin manta ki sake fahimta ,

Matar aure bana kawota a dubu 50k wallahi idan dai yana so tou dubu ɗari biyar zai bani nayi miki alƙawari kuma ki mishi albishir a cikin sati ɗaya tak zan kawota babu asiri babu bori , idan haka yayi miki to idan bai miki ba a daina cinikin dan bana san rainin hankali da yawa....

Shiru Mamy tayi tana kallona ni kuma naci gaba da gwada layin Dikko , can kuma tace tou za'a baki rabin kuɗin idan an gama sai a cika miki , ba tare dana kalleta ba nace ni bana da sasshen jikin mutum , Mamy tace kamar ya kuma ? Nace tou kamar yadda zaki bani rabin kuɗi ! Me zan ciro na fara kawo mishi ? Mamy tace Sultana zan baki rabin kuɗi idan aka gama na cika miki , tsoki nayi nace kinga da Allah ki tashi kina ɓatamin magana a banza , kije idan kun shirya ansar mace kuzo da dubu ɗari biyar na gama magana....

Jakarta ta buɗe ta ɗauko dubu ɗari biyu tace gashi zan cika miki anjima , ai banma da lokacinta bare kuma tayi tunanin naji abinda tace , can kuma tace kin cika kafiya gasu bara na ranta cikin kuɗin ƙawata idan naje banki na cire ita saina bata , da gefen idona na kalli kuɗin , miƙomin tayi na ansa na tusasu fes sun cika , hoton matar ta turamin a wayata tace gata nan kuma bama so sai tazo tayi ta wani noƙe ² nace inki so kije abunki ,

Har zata fita nace , maganar mai zuwa katsina kuma jibi akwai Hamida akwai yaran gidan Baba ƙarami ki taimakamin suma su shigo sahunmu tafiyar zatamin dai² , Mamy tace baki da damuwa , godiya nayi mata ta wuce abunta , ni kuma naci gaba da nazari akan hanyar da zan fiddo matar aure a kaita wurin mijin da ba nata ba kuma banma taɓa magana da ita ba ina dai ganinta tana wucewa !

*America...*

Mai gida Dikko ne kwance a gefen gado , ya ƙurawa waya ido ko kiftawa bayayi , daga can ƙarshen gado kuma amaryace sanye cikin wata irin tsadajjiyar alkebba , mutum biyar suka kawota kuma kwanansu biyu yau suka juya bayan sun ƙara gyarewa ango amarya suka shiryata cikin shiga ta alfarma da ɗaukar hankali , bayan tafiyar "yan rakiyarta ta dawo ɗakin da take tunanin nan ne ɗakin mijinta ta tsareshi da kallo kamar kwarton namiji yaga wawan zama..

Tafi minti 15 zaune bataji yayi magana ba , dan haka ta tashi tsaye ta zare alkabbar ta ajiye a gefen gado , cikin gogewa da buÉ—ewar ido ta fara tafiya cikin natsuwa ta zagaya inda Dikko yake kwance.

Kafin ta iso Dikko ya tashi da niyar shiga toilet , da sauri tasha gabanshi tace haba ina ne kuma zakaje ne bayan kayi wanka , kallonta yayi sannan yace zan tsaya kiyi ta kallona ne kamar banda aikin yi ne ? Haba Yayana aiko kaine kake da aikin yi a gabanka , nuna kanta tayi daga sama har ƙasa tace mai wannan zundumemiyar mace inashi ina bacci a daren nan ? Ga kallo kuma ga aiki , kasan yanzu ba'a sake da miji mai mummuna ma ta tattala abinta ina gani mai tsadajjiyar fuska da ƙira mai ɗaukar hankali kamar ka ? Ai banga ta zama ba aiki ya sameni harsai na goge tambarin ɗiyan ɗan caca a zuciyarka...

Wace ce É—iyan É—an caca ? Dikko ya tambayeta yana mata kallo mai nuni da zaici ubanta ! Haba Yaya DK kana tunanin bansan komai ba ? Kaf labarinta a hannuna yake , me zakayi da wannan yarinyar ? Yarinya mara tarbiya , marar asali jahila da bata gane komai sai karuwanci..

Murmushi Dikko yayi maicin rai dan duk duniya ya tsani a famo mishi ciwon tunanin An mata , haka kuma ya tsani a soketa , cikin ƙunar rai yace ni na sanki tun baki san kanki ba , haka kuma nasan waye ahalin babanki ciki da waje , idan har zan duba girma da tsatson ahali da tarbiyar iyaye ke ko matsayin mai aikin gida na baki ba , da cancanta aka bimin wurin auren da aka yomin ke kinsan baki kai cikin layin matan da zanbi hanya ɗaya dasu ba , An mata bata sanki ba kuma baki gabanta dan bata san da zuwanki ba , tana can tana rayuwarta bake ba ko ni bata da lokacina bana san munanan kalamai yana fitowa daga bakin ki akanta , ba ƙoƙarin gogeta zakiyi ba domin bata gogowa har abadan duniya a zuciyata , idan dai zaki iya kiyi ƙoƙari ki kafa soyayyarki a zuciyata shine abinda zakiy farko kenan ,

Sassauta muryarshi yayi sannan yaci gaba da cewa , tana da tarbiyya , nine zan bada wannan shedar , asalinta kuma yana tare da asalina , tabbas bata gane komai sai karuwanci , nine na yanka mata tikitin karuwanci nace ta koyo dan tamin riƙo da bazan taɓa tunani wata mace a duniya ba sai ita , ta shafe kaf illahirin zuciyata , tabi cikin kwalwata da jinin jikina , yarinya ƙarama mai tafiya dai² da irin rayuwar da nake so , zan bata labarin ki , kuma ince kina mata gori itama ta goranta miki tunda dai uba baifi uba , sa'arki ɗaya ma da mamanki ta haɗo da momy ai da ina ganinki sai nayi amai...

Goge maganar tayi dai tare da nunawa Dikko ya bata haƙƙinta , shareta yayi ya shige toilet, bai daɗe ba ya fito da alama alwallah yayo , itama shiga tayi tayo alwallah ya gabatar da komai kamar yadda yayi a daren farkonsu da Sadiya cikin natsuwa , bayan sun gama suka koma gado anan Dikko ya farke sabuwar amaryarshi kuma ya sameta a cikakkiyar budurwarta ,

Yayi farin ciki dan a tunaninshi yadda take ta nuna haÉ—ama tana zalama baiyi tunanin zai sameta a cikakkiyar mace ba , komai yaji gaskiya amma Dikko yace gishiri yayi yawwa , { tasha kayan mata sosai } dan shi Allah ya bashi ilimin gane tsurun mace idan ta haÉ—a da "yan dubaru ya sani , amma wallahi An mata itadai ta dabance...

Sai kukan kissa matar Dikko keyi , cikin nuna tasha wahala , Dikko kuwa ɗan jirgiwa yayi ya kifar da kanshi saman katifa tunanin yadda darenshi ya kasance da Sultana yakeyi , wallahi ya cuci budurcin An mata daya karɓa ta ƙarfi da yaji , ƙaramar yarinya da ƙananan shekaru ya saki ƙarfinshi ya haɗa da magunguna yaje mata a gigice , bata taɓa gani ba kuma bata taɓa ji ba sai a gareshi , me yasa ....?

Me yasa? Me yasa haka ta faru ? Dole kice bakyasan Dikko saboda Dikko ya zama mugu a wurinki , An mata da kinyi haƙuri kin bani dama a karo na biyu da kinyi alfahari dani , da bazan barki kiyi kuka ba , bazan barki kiyi baƙin ciki ba , shi kenan kin fita a hannuna zaki tafi wurin mai rabo ya ɗaukeki ya dasa wasan sa daga inda na tsaya...

A hankali ya lumshe kyawawan idonuwanshi a bayyane yace Allah ya sanyaya miki zuciyarki , a tunaninta da ita ake tace amin mijina , har yanzu idonshi a rufe yace kin yafemin kenan ? Ummm ai bakamin komai ba ma , kenan babu zafi ? Umm umm , to me yasa ki key kuka ? Ba komai , sai yanzu ya gane bada Sultana yake maganar ba , buÉ—e idonshi yayi da sauri ya ganshi kwance akan sabuwar amaryar shi , kuma "yar uwa a gareshi...

Ko tsakar dare dana farka haka naci gaba da gwada wayar Dikko wanda ya zamarmin kamar hauka dan ƙaranci ban kira wayarshi ba a rana na kirashi sau 200 da wani abu ,

Ina zaune tsakar daren nan ina ta aikin neman wayar naji maganar Baba ƙasa² daga bayan ɗakina dake daga tagar ɗakin sai a fice zaure a fita ƙofar gida , bana iya jiyo abinda Baba yake cewa saidai naji maganar Amisty cikin shagaba tana cewa nidai Dady don Allah... Ta ƙarasa maganar kamar tana kuka !

Da sauri na haska fitila na duba agogo naga 3:45am cikin sauri na miƙe na sake matsawa da kunnena jikin window naji shin da gaske Amisty ce ko kuwa dai wata ce daban ! Wallahi Amisty ce dan duk duniya babu mai irin wannan muryar sai ita , me suke cewa ? Me ya haɗa Amisty da Babana a wannan salasunan daren ? Me ke tsakanin Amisty da Baba ? Duk wannan tambayar banda ansoshinsu nayi yunƙurin yin wani abu tunani na ya tsaya cak domin kaina ya riga da ya juya...

Buga kaina nayi da ƙarfin bala'e a jikin bango na kurma wani irin ihu duk wanda ke cikin gidan saida yayo waje saboda ƙarfin ihun da amonshi ni kuma na fito da gudu nayo hanyar fita , babu Amisty domin tuni ta fice , ina ƙoƙarin fita Baba ya riƙeni da ƙarfi yana lafiya ? Fizge ² na farayi na kwace nayi waje , da gudu ya bini ya riƙoni nafi ƙarfin riƙonshi domin na sake zuƙewa daga riƙon da yayimin , cikin tashin hankali zugar gidanmu suka yo kaina dakel suka kaini ƙasa suka daddanne ni na birkice gaba ɗayansu na watse su , na yanki santa , yayuna maza suka taimaka aka kamani aka mayar dani cikin gida ,

Kowa tambayar abinda ya sameni yakeyi ? Murmushi nayi mai ciwo na kalli Baba nace ina ka ɓoyeta ne ? Cikin rashin fahimta yace wa ? Kafi kowa saninta me takeyi a gidan nan a wannan lokacin me tazo yi me take nema...? Baba yace wai wace ce ? Ga sunan Amisty a zuciyata amma ƙiri² ya gagara na faɗa a baki na , nace ita mana ita wace ce ? Kai ji nan na nunashi da ɗan yatsa nace tana ina karfa ka ɗaukeni mahaukaci nasan abinda nake ina ka ɓoyeta ne ?

Amma Baba sai ya fara tofa min addu'a yana cewa aljannu sun kama uwar masu gida , a taimakamin da addu'a , inaji ina gani Baba yasa aka mayar dani mahaukaciyar ƙarfi da yaji , kowa yayi ta tofamin yawu , banda yanda zanyi dole nayi shiru amma wannan abun bai gogemin daga zuciya ba kuma saina bi salsala na gano abinda ke tsakanin Baba da Amisty , maganar Mamy ta dawo min a kaina kamar yanzu take faɗamin maganar...

_Gaskiya an samu matsala shi kanshi Binna da yasan waye Hafsa a wurinshi daya haɗe zuciya ya mutu , itama bata san wayenta ba , shima Baban Hafsa baisan ke wacecen shi ba , kowa iskanci ² gaba ɗayan ahali sun zaman *KWARATA...*_

Lallai akwai alamar tambaya a wurin nan amma waye zai fiddo maganar daga cikin zuciyata ? Waye ? Waye zai taimakeni ne ? Wai wace ce ni ? Anya kuwa ni mutunce ? Mutane kuwa suna gani na ? Wai meke damun rayuwata ? Me ke damun kwalwata ? Wannan wane irin masifa ne ? Wace irin rayuwa nakeyi ? Ina mahaifiyata wai me Baba ya ɗaukeni ? Me nene ׳ na ƙarasa maganar ina ɗaga muryata wanda ina tunanin duk mutumin dake anguwar nan yaji irin hayagagar da nakeyi...

Fashewa nayi da wani irin kuka nace tabbas ko wace ce ni da sanin wace irin rayuwa nakeyi amsar tana wurinki , kuɗin da Mamy ta bani na ɗauko na irga suna nan yadda ta bani su , maidasu nayi na aje , amma a zuciyata nayi alƙawari zan bautata mata tiƙuru kuma zan bata girmanta kamar yadda take so zan nemo matar nan kuma zan kaita zan bawa Mamy kuɗinta kuma zanci gaba da farauto mata duk wanda take so adalci ɗaya zatamin ta warwaremin sirrin rayuwata wannan shine kawai mafita....

Gari na waye nayi wanka yau ko inda Babana yake ban kalla ba kuma ban gaishe shi ba , makulin mota ta na buƙata ya bani amma sai yacemin wai anci motar a caca , kallonshi nayi nace ni bansan caca ba mota ta kawai na sani kuma sai ka biyata ,

Mamana ni kike cewa saina biyaki mota ? Kaine ka siyata ne ? Ai ko ban siya ba naci albarkacin haihuwarki da nayi , ka maidani ciki idan kaji munin maganar amma sai ka biya wannan motar babu gudu babu ja da baya kuma ba abinda ya dameni na baka daga yanzun nan zuwa bayan sallah isha'e ... Ina faÉ—in haka nayi waje abuna na barshi ta tagumi...

Ina fita na shiga maƙota na nuna hoton matar da Mamy ta turomin a wayata nace da Allah ina neman gidanta , matar tacemin lafiya dai ko ? Nace lafiya qalau gwamnati tace a taimakawa masu ƙaramin ƙarfi wanda suke shan wahala a gidan aurensu , an ɗauko jaddawalin sunan ko wace macen aure da ƙaramin katin hotonta , sai naga ita kamar tafi kowa shan wahala shine nake so ita a taimaka mata da yawa , mata da kuɗi sai Allah kuma nayi haka dan in rubzata rami itama , ta haka zanji wane irin hali matar take nasan komai nata kafin na isa gidanta , !

Murmushi matar tayi tare da ɗaukomin kujera na zauna tace amma Sultana kunsan kuna da hanyar taimako shine mu ba'a saka sunanmu ba ? Jakata na zuge na fiddo damen "yan dubu² nace kin gansu nan kowa da sunanshi ai bansan kuna buƙata ba , itama banda tabbacin da zataje ko bazata ba ,

Tace zuwa kai , muje na rakaki gidan ta amma don Allah nima kisa a rubuta suna na don Allah , nace baki da matsala , saman ƙyaure ta ɗauko hijabinta tana ba yaranta umarni karsuyi mata ɓarna idan Babansu ya shigo ta shiga maƙota baza ta jima ba ,

Ta gaban gidan Amisty muka wuce gaba ɗayansu suna ƙofar gida hada Asma'u an saka kujeru na roba Amisty kuma tana ta tofi da hayaƙin sigari , yayin da wata tantiriyar "yar iska ke shan shisha tana murza hayaƙin cikin ƙwarewa da gogewa a cikin harkar ,

Har mun wuce naji bana iya haƙuri na dawo da baya , dai² Amisty na tsaya na ciro sigarin daga cikin bakinta na kasheta a saman goshinta , wata irin ƙara tayi saboda zafi ta riƙo hannuna na , da hannun damata na riƙe hannunta saboda dana haggun na kashe mata tabar sannan nace na rantse da Allah duk ranar da hasashena ya zamo gaskiya yadda na murje wannan sigarin a goshinki haka zan murje miki rayuwa..

Gaba dayan su sukayo kaina suna kee.... Nace heeee ku saurara na kaso daku sannan ku É—auka domin yanzu babu sauran muradin É—aukar fansa a zuciyata ina neman rayuwata ne amma idan kuka bari na É—auki zafi anbaliyar wuta zan fara hattaranku domin ni fetir ce kuma sai cikin wuta nake amaina !

Kallon Amisty nayi nace ki fara addu'ar kuɓuta daga sharrina domin na yanzu ba irin na baya bane , na yanzu maciji zansa ya cinye kwansa { uba ne zai kwanta da "yar sa } ki kiyayi haɗuwa ta da ke domin abin bazai miki kyau ba ,

Sakinta nayi na kalli matar nace mata muje... Wuce su mukayi muka tunkari gidan matan , da sallama muka shiga , ta amsa mana cikin sakin fuska tare da shinfiÉ—a tabarma tace ku zauna sannunku da zuwa ,

Zama mukayi , baiwar Allah ta dama ɗan kokonta da ɗumamen tuwo suna ci ita da yaranta tana ma Allah godiya , amma dole tayi haƙuri domin Sultana ta shigo mata rayuwa , mijinta ya fito daga cikin ɗaki muka gaisa dashi ita kuma tabi bayanshi danyi mishi rakiya , wayyo bawan Allah kayi haƙuri Sultana tazo yanzu zan firgita maka iyalinka ka kasa gane gabanta bare bayanta...

01/10/2019

*JAMILA MUSA....*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 47

Cikin sakin fuska ta shigo cikin gidan bayan ta dawo daga rakiyar mijinta , a mutunce ta zauna kusa damu saman tabarmar da muke aka gaisa a mutunce suka ɗan taɓa fira a tsakanin su da matar da muka zo tare mai nuni da akwai sanayya mai girma tsakaninsu ,

Bayan sun gama gaisawa da Maman Sadiq itace wacce muka zo da ita , ita kuma mai gidan naji Maman Sadiq in tana kiranta da Ummu Affan , Maman Sadiq tace tou Sultana wannan itace kike nema ko ? Murmushi nayi cikin jin kunya nace itace , kallona matar tayi tace lafiya dai ko ? Nace lafiya lau , Ummu Affan tace ya akayi ne ?

Nace dama ƙungiyace gwamnati ta buɗe domin taimakawa matan aure marasa ƙarfi , an ɗauki sunayen wasu matan da kuma yawan "ya "yansu , mai girma gwamna ya bada izini dan gyara siyasar shi , shin kina da wata sana'a da kikeyi ko bakya da ?

Ummu Affan tace gaskiya bana sana'ar komai , tou mi kike buƙata wannan gwamnati mai adalci ta taimaka miki dashi wanda zaki taimaki kanki da kuma iyalinki a cikin gida ba tare da kinsha wahala ba ? Tace Eh tou gaskiya idan dai san samu da gaske za'a taimakamin a siyamin injin markaɗe da kuma injin taliya domin shine abinda yayi ƙaranci a wannan anguwa tamu , tou amma bashi za'a raba kayan ko kyauta ?

Nace haba wane kuma da gaske Ummu Affan ? Kinga ai ban taɓa zuwa gidanki ba sai yau , kuma duk mutumin daka gani a gidan ka ai da dalili , gwamnati tsaye take a kan ƙafafuwanta dan ganin ta taimaki talakanta , idan zaki amince ma ai sai a naɗaki shugabar ƙungiya ki tattaro mana matan aure waɗanda suke san taimako kinga ke sai ki zama shugabarsu idan yaso sai a baki kuɗin da kuma kayayyanki da gwamnati zata bayar ke kuma saiki riƙa raba musu ya kika gani ?

Maman Sadiq tace to ni me za'a bani ne ? Nace ke kuma sai a naɗaki matemakiyar Ummu Affan amma ban sani ba ko mazajenku zasu riƙa barinku kuje wurin taro ? Dan naga duk lokacin da ake taro dubu goma ² ake bawa duk wacce ta halacci taron , Maman Sadiq ta zaro ido tare da cewa dubu goma ? Nace sosai ma idan ma gwamna yazo wurin taron dubu ishirin ake rabawa ga duk mace ɗaya ga lemu ga ruwan roba hada naman kaji ga abinci mai kyau kici ki ɗaurowa yaranki a leda...

Ummu Affan tace dubu ishirin ? Nace sosai ma , tace idan dai taron bana dare bane wallahi sai muje ko ƙawata ? Suka kashe da Maman Sadiq , Maman Sadiq tace aini ko na daren ne wallahi ina iya zuwa uwar me ake baka auren ƙaddara auren ya zanyi ? Auren cida kai ? Kana gida zaune kullum kamar mai takaba babu wani ci gaban rayuwa sai tsofewa kakeyi kai baka mori rayuwarka ba kazo a wahala ka rayu a ƙunci ka koma a alakoro , nidai gaskiya ina zuwa ,

Nace tou ki bari muji ta bakin shugabar ƙungiya mana ? Na ƙarasa maganar a dai² lokacin dana zage jakata na fiddo irin kuɗin dana fiddo a gidan Maman Sadiq dubu biyar² naba ko wace a cikinsu nace idan kunyi shawara ku neme ni , gaba ɗayansu dubu biyar² ta ruɗasu dan yanayin fuskarsu ya nuna haka , ina basu nayi sallama dasu na wuce gida abuna...

Fitar Sultana daga gidan sukaci gaba da tattaunawa yayin da Ummu Affan tace ni zan faɗawa Abbu Affan idan ya yadda , Maman Sadiq tace ki rabu dashi kinsan mazanmu baƙin ciki garesu su kaɗai suke so su ƙaru da sunga hanyar da zaka samu sai su nemi bulo da suminti su yaɓeta , kiyi shirunki kici gaba da sabgar gabanki gaki shugabar ƙungiya kinga idan aka baki kayan ki raba kina iya danne abunki kice ance za,a kawo amma har yanzu bai iso ba , idan kuma kina ganin zai hana taron sai a riƙayi a gidana , ni nafi ƙarfin mijina dan bai tsaremin ci 3 a rana ba bare ya juyani wallahi.

Ummu Affan tace tou idan kuma akace an ganni a wurin taron fa ? Tsoki tayi tare da cewa banda kike banza ai niƙaf zaki saka waye ya isa ya ganoki ? Ey fa haka ne , tou Allah yasa karta juya tunaninta akanmu ta samu wasu daban , Maman Sadiq tace ai gobe idan Allah ya kaimu sai muje gidansu muce munzo gaisheta sai mu sake tuna mata muce karda ta manta damu , Ummu Affan tace haka ne zanzo , bara na bada a siyomin cefane yau a gidan nan miyar ja kowa zai sha... Dariya sukayi tare da cewa sai sun haɗu goben ta fita a gidan...

A ƙofar gida na samu Babana yana zaune ya zagba tagumi ga dukkan alamu akwai abinda yake damunshi , gaskiya ina san Baba kuma wallahi yana bani tausayi bawan Allah , daga nesa dashi na tsaya nace mike damunka kake tunani kamar macen data rasa miji ? Ba tare daya kalleni ba yace ba kince saina biyaki motarki ba , nace idan nace sai ka biyani mota kuma sai ka zauna ? Ka tashi kaje ka nemomin kayata , nifa saidai kawai in siya miki wata tunda ba ɓacewa tayi ba nace miki a caca aka cita ,

Kiyi haƙuri Mamana , nace idan na ƙyaleka baka biya motar nan ba gobe gidan zaka saka shima a cinyeshi sai mu koma kuma muna raɓe² tunda cacar ta daina yinka basai kayi haƙuri ba ? Baba yace insha Allah nama daina cacar daga yau idan dai hakan zai miki daɗi , zanyi magana naji ƙaraurawar kaina ta buga da ƙarfi , addu'o'i naci gaba dayi dan na fara fahimta sheɗanci na yana cikin kaina ,

Ƙarfin hali nayi cewa daka hutama kanka ina faɗin haka nayi cikin gida , ina tunanin anya kuwa kaina ɗaya ? Koma dai miye Allah yana tare dani ,

Al ' Ameen durƙushe a gaban mai girma gwamna yana gulma , Allah ya taimake ka har yanzu mai gida bai rabu da yarinyar nan ba , kai kace in saka ido sosai kuma duk abinda yake faruwa a tsakaninsu in faɗa maka , tou wallahi wannan motar daya siya kayi mishi faɗan siyenta ita yama ɗauka gaba ɗaya ya bata ita , kuma hada kuɗi yace tasha mai amma kuɗin bansan ko nawa bane ,

Dady yace tou ai ya kyauta ni bansan yadda zanyi dashi ba , mai ɗaki shi yasan inda ruwa ke zubar mishi sai yaje yayi ta tarayyar da ita , ƙara duƙar da kai Al ' Ameen yayi yace Allah ya taimake ka a gani na bai kamata a zuba ido abarshi da ita ba ya kamata a sake dakatar dashi kafin abun ya wuce misali , Dady yace idanma gidansu zai koma da zama yaje ya koma tunda ba yaro bane shi ai yasan abinda yakeyi ,

Al ' Ameen yace ranka ya daɗe ai bazaka so a kaishi a baroshi ba , gara a tari abun tun wuri basai yayi nisa ba a kasa taroshi ba , Dady yace wai ba Dikko bane ba ? Yace Eh , yace tou ka ƙaleshi tasu ta haɗosu kasanshi baida gwani ka basu wasu kwanaki zakasha mamaki , ba haka Al ' Ameen yaso ba amma baida yadda zaiyi dole ya haƙura amma zai faɗawa Momy ita kaɗai zatayi maganin Sultana , daga nan shi kuma ya samu ɗiyar yayarshi ta shigo babu ɓata lokaci ,

Da daddare bayan na gama abinda nakeyi Alaji na kira { Abbu Afsar } ya kaini gidan Mamy tunda banda mota , motar da Dikko ya bani kuma ba yanzu zan fara hawanta ba akwai tanadin da nayi mata nasan duk ranar dasu Amisty suka ganni da ita sai sunyi hawan jini ,

Da sallama na shiga gidan , daga cikin ɗaki ta ansa min sallamar tare da cewa shigo Sultana har ta ɗauki miryata , nace tou ɗakin na shiga da sallama na samu wuri saman daka²n kujerunta na zauna , bayan na zauna na gaisheta cike da biyayya sannan na gaishe da wani mutum dake zaune yanacin abinci , kallonshi Mamy tayi cewa tou ɗauki abinci ka koma waje zamu tattauna da baƙuwa , yace tou Hajiya ya ɗauki abincin ya fita daga ɗakin...

Bayan fitarshi nace Aunty kiyi haƙuri da Allah akan abinda ya faru dani dake jiya , nayi miki rashin kunya wanda haka bai kamata ba kuma ba tarbiya bane ɓatawa na gaba da kai ba , kiyi haƙuri kuma insha Allah bazan sake ba , jakata na buɗe na fiddo kuɗin data bani nace kuma gama kuɗinki na dawo miki dasu , maganar matar kuma zan kawota kiyi haƙuri bazan sake ba ,

Murmishi Mamy tayi tace ba komai Sultana ni dama banji komai ba , Allah ya haÉ—ani dake kuma yasamin soyayyarki a zuciyata kuma nayi É—amarar taimakonki in Allah ya yadda ,

Godiya nayi tare da matsawa gabanta zan ajiye kuɗin , tace ki barsu ki riƙesu , nace a , a Aunty ki barsu wallahi , tace bani nace ki barsu ba ? Bana so muna jayayya dake ki maida kawai a jaka , nace tou , jakata na buɗe na saka kuɗin , daga nan muka ɗan taɓa fira har take cemin kece kike mamakin ina da aure ko ? Murmushi nayi amma banyi magana ba , mutumin data fitar yanacin abinci shine ta kira , bayan yazo tace tou kinga mijina nan ,

Kallonshi tayi tana cewa wai mamaki take ina da aure , cike da biyayya yace Allah sarki , Mamy tace tou jeka tunda ta ganka , kamar sakarai kuma ya juya ya fita , a kunyace nace tou Aunty ya maganar baƙonmu na gobe ne ? Tace zaizo yanzu ma muka gama waya dashi , nace tou ya maganar yaran gidan Baba ƙarami ? Mamy tacemin komai ya tafi dai² karki damu amma ina ganin tunda ita Hamida tahau layi kawai mu fita safgarta , nace da ina so ta samu kuɗi , Mamy tace manta da "yan gidanku domin dama su tuni suna cikin sahun *kwarata...* tuni sun daɗe a harkar bariki tunda sune suke kula da kansu ki rabu dasu kowa yayi sabgar gabanshi , nace tou ,

Mamy tace yawwa akwai wani Uncle Al ' Ameen lokacin dana saka layin da kika bani yana ta kira babu ƙaƙƙautawa , gajiya nayi da nacinsa na ɗauka waya , bayan mun gaisa yacemin da Allah wannan wayar ta doughter inshi ce aka yadar da ita , ko ina zai sameni ya ansa ? Sai nace masa ni ba waya na samu ba layi na tsinta ,

Gaskiya da nayi niyar mu haÉ—u na bashi layin dan naji shima yacemin a katsina yake , abinda yasa na fasa yamin burga da cewa zaisa a kamani , nace masa shi É—an uban waye a garin katsina shine yacemin daga gidan gwamnati , nace gwamnan ya tsaya maka ko waye ? Shine sai yacemin layin wayar matar É—an gwamna ne , cika bakinsa yasa na saka number a wayata na duba ta whatsapp hoton Dikko ne na gani a d pn inshi , abinda na fahimta wato shi yaron Dikko ne , amma idan na tuna da labarinki kuma idan na fahimta Dikko shine kukayi faÉ—a a motarshi ! Me ya haÉ—aki dashi kuma miye tsakaninku ?

Ajiyar zuciya na sauke tare da gyara zamana nace tou kila sato wayar tayi amma ita wannan ai bata taɓa aure ba , shi kuma mai maganar yace miki layin wayar matar Dikko ne , ko kin manta matar Dikko ta mutu ne ? Tace min haka ne kuma fa , nace gaskiya shiri ne abun , naci gaba da cewa yanzu wayau ɗaya zamuyi mishi shine kice masa ya turo miki lambar wayar da za'a iya samunta , domin akwai wasu tambayoyin da zamuyi ma mai layin idan ta bada ansa za'a bata wayarta da layinta wannan shine mafita , nayi haka ne dan na samu ta hanyar da zan turawa yarinyar nan vidion da zamu ɗauki ubanta , naƙi yadda kuma na faɗa mata nasan Dikko saboda gudun bita da ƙulli , bayan kuma Sadiya ta rasu babu wanda yasan Dikko yayi auren ...

Miƙa hannuna nayi tare da cewa Mamy inga hoton , miƙomin wayarta tayi bayan ta kamomin hoton Dikko a wayarta tana cemin yanzu lambar wayar yarinya zansa shi Al ' Ameen in ya turo mana kenan ko ? Banajin ta domin hankalina da duk natsuwa ta ya tafi wurin kallon kyakkyawar fuskar mutumina ,

Wallahi bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar Dikko , yayi min kyau sosai a hoton kuma yayi hoton a cikin yanayin fushi ya ɗan soɓaro leɓonshi na ƙasa , yayi kyau sosai kuma shima Al ' Ameen in yasan hoton ya haɗu shi yasa ya sakashi a whatsapp inshi , idona ya cika da kwalla a zuciyata nace shine dai kayi fushi dani ko ?

Kiran waya ya shigo a wayar dan haka na miƙawa Mamy wayar na miƙe ina cewa sai mun haɗu goben idan Allah ya kaimu , tace tou Allah ya kaimu ki gaida gida , banyi magana ba na fice buzum² zuciyata namin babu daɗi ,

A gajiye na isa gida , koda Alaji ya ajiyeni kawai ce masa nayi saida safe dan banajin daɗi kwata² kuma yaso na tsaya muyi fira na nuna masa bana buƙatar hakan ,

Ina shiga gida ɗakina na shige , saida na kwanta sannan naci gaba da tunanin Dikko , inayi ina hawayen baƙin ciki naci gaba kuma da kiran layinshi , har na gaji nayi bacci....

Washe garin ranar kuwa tunda safe Maman Sadiq da Ummu Affan a gidanmu suka bayyana , lokacin ko baccin safe ban tashi ba , dan tunda nayi sallah asuba na koma bacci , zuwansu ya tasheni , saida na fita na wanko fuskata da bakina sannan nazo muka gaisa dasu , bayan gaisuwa Maman Sadiq ta fara cewa dama cewa nayi bari muzo muji yaushe ne taron ?

Shiru nayi tare da tsaresu da idanuwa dukansu , bayan na gama fahimtar wani abu daga garesu nace gaskiya shugaban ƙungiyar munyi magana dashi yacemin in ƙyaleku danshi baya san azo a samu matsala dan basaso a ɓatawa siyasar su suna , matan aure basa iya basu gudumawa yadda ya kamata akwai matsalar mijina yace karna fita , ko kuma ina zan bar yarana ? Ko kuma ni bana zuwa hotel ko kuma inane za'ayi taron ?

Saboda jiya bayan na rabu daku naje wurinshi nayi masa bayani yadda mukayi daku bayan na nemi alfarma dan yaɗan ƙara muku wani abu saboda na lura iyali sunyi muku yawa gashi babu wata sahihiyar sana'a kuma yaran naku duk basu kawo ƙarfi ba , na samu dai yayi muku ƙarin budu goma tunda kune shuwagabannin ƙungiya ,

Sai yace na kawo mishi shugabar ƙungiyar ya gani shine nace ai matar aure ce , kinji faɗa ? Yace mi yasa kika naɗamin shugabar ƙungiya matar aure ? Bayan kinsan meeting na gaggawa zai iya tashi na kirata tacemin bata shirya ba ? Nidai ki mayar min da budurwa ko zawara , dakel dai na bashi haƙuri yace min ai matsalar matar aure wai kina iya zuwa kice aike bakya zama wuri ɗaya da mijin da ba naki ba , bayan dole zaku riƙa ɗan warewa ku tattauna abinda ya shafi ƙungiya ,

Ummu Affan taji zance kuÉ—i dan haka tace anyi ma aikin kishiya bare na uwar miji ? Daga magana sai mi kuma ? Nace kinsan wayayin maza basa so ayi ta wani dunkumewa a hijabi kinsan "yan boko basa san suga ana sha''ani da hijabi ,

Tacemin ai bansan wurin taron ko za'a nuna a talabijin ba , nace a , a ba'a sakawa a TV , Maman Sadiq tace tou Sultana ai sai mu tafi tare kice nice matemakiyar Ummu Affan , nace kibi sannu duk za'aje da kowa , tace a , a abari ya huce fa shine ke kawo rabon wani , nace aiko bai hucen ba idan rabon wani ya shiga tun yana kan wutar wani zaizo , kinga kuwa ai dole zakuci tare ko ? Tace haka fa , nace tou kudaije ku sake tunani shin zaku iya huÉ—É—a da maza ? Dan duk zama É—aya ko wace zata tashi da dubu ishirin idan kuma gwamna yazo ko wace tana da dubu talatin idan kuma kin iya gogayya da maza zama É—aya ma da hamsin zaki tashi ,

Zasu sake magana wayar Mamy ta shigo , nace tou anyi ma sa'a ga shugaban nan yana kirana ku jira muji me zaice ne ? Ɗaukar wayar nayi bayan mun gaisa da Mamy tacemin in shirya gata nan zata taho , nace tou , sai nace yawwa Alhaji maganar matan auren nan ina dai ƙara baka haƙuri yanzu haka ma muna tare dasu kuma sunyi alƙawari babu wata matsala , shiru nayi bayan wani lokaci nace dubu ɗari da keken ɗinki ? Allah ya ƙara arziƙi wallahi godiya suke , kallon juna sukayi suka ƙyarawa junansu ido , ni kuma na sake shiru bayan wani lokaci kuma nace kai Alhaji dani da ita zamuje har a gaban mai girma gwamna ? Tou muna godiya sai munzo goben , nagode ׳ , yawwa sai anjima na kashe wayata , Mamy kuwa cewa tayi kai wannan yarinya batajin magana ,

Ummu Affan har sauri take wurin cewa wai waye za'a ba keken ɗinkin da dubu ɗari ? Nace shugabar ƙungiya wai cewa yayi idan Allah ya kaimu gobe duk shuwagabanni zamuyi zama da mai girma gwamna shin zaki samu damar zuwa ko kuwa yadai ?

Tace zuwa ma kai zanje , nace tou kidaiyi shiga mai kyau dan kinsan shiga gidan gwamnati bana yara bane , kiyi wanka ki ɗauro kallabi ƙarshen layi kizo muje amma kuyi shiru da bakinku karku sake ku bari wani yaji idan ba haka ba "yan zidaƙuiy zasu zo su anshe ma ɗan tama doki , Ummu Affan tace haba wallahi bama faɗa , nace tou yayi kuje sai mun haɗu goben , Maman Sadiq tace ai wallahi baku bari na wannan ai baƙin ciki ne taya ni na rakaki gidanta kuma a gabana aka haɗa komai sai ku tafi gidan gwamnati ku barni dan baƙin ciki ? Nace kema hada ke za'aje , tace tou yanzu naji magana , murmushi nayi tare da cewa kuje zan shiga wanka ,

Maman Sadiq ce ta fara fita ɗakin dan haka na riƙo hijabin Ummu Affan nace karki faɗa mata ƙarfe biyu na rana zamu tafi , idan ba haka ba keken ɗinkin nan da dubu ɗari tare zaku rabasu , tace bazan faɗa nace tou ku gaida gida ,

Kwando na ɗauka naje nayi wanka , bayan na fito na fara shiri ina saka kaya Mamy ta iso , bayan mun gaisa nake bata labarin yadda mukayi da matan aure , na ƙara da cewa kinga goben idan mukaje sai muyi ta zama ace gwamna yana meeting , ni kuma ina ci gaba da gyara hanya cikin sauran kwana shiddar daya rage har an kaita an baro ta ,

Mamy tace gaskiya ne , nace tou shi mutumin saiki faÉ—a masa idan munje muka tashi tafiya ya bata dubu hamsin kinsan ita mace da kuÉ—i ake tafiya da imaninta , Mamy tace haka ne karki samu damuwa nace dama banda ita ,

Bayan na gama shiri na ɗauki jakata da abinda nake shafawa mutane su tafi bacci , saida muka fita ƙofar gida nake tambayar Mamy ko Al ' Ameen ya turo lambar yarinyar ? Tace yace babu waya a hannunta sai dai ta Mamanta take amfani dashi kuma ya turo nace shikenan magana ya ƙare mata tacewa mijinta shege..........

02/10/2019

*JAMILA MUSA....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 48

Ni naja motar muka tafi Mamy kuma tana gefe na tana waya , dama ta shigo tanayin abunta kuma har yanzu bata gama ba , hanya na iba ɗoɗar saboda ta nunamin hanyar da zanbi da hannunta ta kuma nunamin kawai in tafi miƙe kar in kwanta ,

Munyi tafiya mai nisan gaske sannan Mamy ta gama waya , sawa tayi nayi parking ta anshi tuƙin motar mukaci gaba da tafiya har muka iso inda muka zo Mamy bata sake magana ba ,

Get in gidan buÉ—e yake dan haka muma muka samu damar antayawa daga ciki , tun kafin Mamy tayi parking Allah ya nunamin Al ' Ameen , haka nan naji gabana ya yanke ya faÉ—i gaba É—aya sai guyawuna sukayi sanyi nama kasa fitowa daga cikin motar , ni kaÉ—ai nasan Al 'Ameen Mamy bata sanshi ba , sannan kuma numbershi da ta saka a whatsapp inshi ba shine ba Dikko ne ,

Dogon nazari na shiga to me ya kawo Al ' Ameen wurin nan kuma ?Tunani nayi sosai firata da Mamy ta daren jiya ta dawo min , to duk yadda akayi yarinyar da mukayi faɗa da ita kenan tana da alaƙa da Al ' Ameen ? Na shiga tunani sosai amma na kasa fahimtar ya abun yake ,

Mamy kuma fita tayi daga motar tabar harabar gidan ta koma ƙofar gida , bayan wani lokaci kuma ta dawo ita da wata matashiyar yarinya shekarunta da kamanunta duk bana iya ganewa saboda ta saka niƙaf ta lulluɓe fuskata , ciki suka wuce ta barni zaune a mota kamar mage na dakon tsuntsu ,

Shiru² babu Mamy ba labarinta , ni kuwa sai sassada kai nake ƙasa dan bana so Al ' Ameen ya ganni , gashi ina so na fita nima na shiga amma dole banda yadda zanyi saboda Al ' Ameen zaune yake kuma baida alamar tashi ,

Har su Mamy suka gaji da daɗewarsu suka fito , yarinya bata shigo motarmu ba ficewa tayi Mamy kuma ta shigo mota taja muka tafi , saida mukayi nisa nace mata wai mutumin dake zaune a wurin nan shi kuma waye ? Ko gadi aka sashi ne ? Mamy tace ƙanin matar Baban yarinyar ne , jinjina kaina nayi sannan nace tou wace ce da niƙaf kuma ? Tace "yar uwarki ce da kika ce na farauto ,

Nace Hamida ? Tace ɗiyar ƙanin Babanki ce , dariya nayi sosai nace tsakaninki da Allah tace wallahi kuwa , tou ya akayi kika farauto ta da wuri haka ?

Mamy tace wallahi ina zaune gidana Allah ya kawo minsu ita da ƙanwata , ashe ita ɗiyar ƙanin baban naki aure zatayi ? Mamy ta tambayeni nace mata Eh Safiyya ce zatayi aure , Mamy tace to ai kinsan "yan matan zamani sun saka kansu ƙarya basa haƙuri da abinda iyayensu sukayi musu , basa da gashin wance sai suce dole zasuyi kitso irin nata ,

Ƙanwata tacemin tana naima wa ƙawarta aiki a ƙarƙashi na , na taimaka wannan ƙawarta ce zatayi aure iyayenta basuyi mata wani abun kirki ba na kayan ɗaki , shine ta kawota wurina ko zan taimaka na ɗauketa aiki ita kawai talabinjin in bango da kayan sautin ta take so ta siya sai labulaye masu tsada ta gyara palon ta dan bata so ƙawayenta su raina mata gidan aurenta ,

Saina tambaye su bikin kwana nawa ya rage ? Shine tacemin wata 3 nace tou yarinya banda abinki wata3 taya zaki samu kuÉ—in da zaki sayi talabinjin in bango da kayan sautinta ? Kona É—aukeki aiki na baki kuÉ—i da yawa a wata baifi na baki albashin 3k ba , kinga 3k sau wata3 ya kama 9k ba talabinjin ba ko labule bazai siya miki ba ,

Tacemin haka ne , tou bayan nayi bincike naji daga inda ta fito kuma naga kina nemansu da karuwanci ruwa ajallo yasa nayi mata tayin karuwanci bayan munyi ciniki dashi baban ƙawar faɗan taki akan zai bayar da dubu hamsin , nayi ² ya ƙara wani abu akai umm lusarin a haka ya tsaya , bayan mun gama ciniki dashi ya kafe kai da fata haka zai bayar ,

Kodai yane tunda na samu an farketa shikenan kinga ta tsaya zaman jiran talabinjin dan ubanta saidai kawai taji a salansa tamin hauka akan na bata kuɗi ga vidio na ɗauko ta ƙarasa maganar tana dariya , nima dariyar nayi tare da cewa yaro inya iya ruwa ai bai iya laka ba , dariya Mamy tayi sosai tare da tambayata meye ruwan kuma miye lakar ? Nace zancen sai wanda ya kwana a bakin gabi.... Mamy tace ina ne gabi kuma ? Nace wata matattara ce ta karuwai dake can wajen gari !

Haka dai mukayi ta taɓa fira har muka iso ƙofar gidanmu , bayan Mamy tayi parking ta fara kiran wayar Maman budurwar Dikko da mukayi faɗa da ita wacce bayan an ɗauki wayar naji Mamy tana cewa da Allah Momy ko Mardiyya tana kusa ne ? Eh tana nan Mardiyya kizo anyi miki waya ,

Tazo ta anshi wayar , bayan gaisuwa Mamy tace mata kin gane ɗiyar ɗan caca wacce kukayi faɗa da ita a motar saurayinki akan haryar ku ta zuwa Abuja ? Wacce bayan kunyi faɗan tayi zuciya ta barku a hanya ta samu mota ta dawo katsina kin tuna har kikace mata jahila daƙiƙiya kidahuma jaka kin tunota ? Tace Eh na ganeta ya akayi ne ? Mamy tace yawwa dama cewa tayi ki riƙe wayar Mamanki a hannu ki duba ta whatsapp zata turo miki saƙon ta tashi daga jahila ta koma ma... Da sauri na anshi wayar daga hannun Mamy nace.

Mai ilimi barka da tsakiyar rana , barka dai ta amsa a daƙile , nace suna na *SULTANA ALIYU MUHAMMAD BINNA...* ina miki albishir da mummunan gani , salona ne yin albishir da mummuna ga abokin gaba sai kuma nayi albishiri da kyakkyawa ga masoyina , idan baki manta ba a waccan ranar nace mutuwa kaɗai zaki ki huta da ganin baƙin cikina , tou yanzu muka fara ki fara yininki da wannan anjima ma zan turo miki na kwanciya bacci kisha kallo lafiya...... Gashi nan zuwa , ki gani ke ɗaya idan uwarki ta buƙaci gani itama ki bata ta gani muna da maganin ciwon zuciya na hausa idan kina buƙata kallon Mamy nayi tare dayin dariya nace masu magani kasuwa ta buɗe ....

Ina faÉ—in haka na kashe wayar , Mamy kuma ta ansa ta tura vidion data É—auko kuma hada Safiyya a cikin hoton tana ta kwarara ihu saboda azaba yayin da Baban Mardiyya ke kwarara wani irin gurnani kamar kura tayo kamu , na raka vidion da voice note cewa mi yasa ya faÉ—a ruwa bai iya iyo ba ?

Dariya mukayi dukanmu , saida muka tabbatar an buɗe saƙon kuma ya ɗauki lokacin da ya isa Mardiyya ta gama gani sannan naba Mamy Umarni data goge shi daga wayar mamanta , wato ta saka delete 4 everyone , bayan an goge duka hada voice note in da nayi nasa Mamy ta rubuta cewa ta kawo kuɗi masu yawa sai mu goge idan kuma ba haka ba ta tara a tashar yanar giza gizo.

Bayan mun gama nayi sallama da Mamy na wuce gida akan sai mun haÉ—u gobe idan Allah ya kaimu , tace Allah ya kaimu lafiya , a gajiye na shiga gida dan haka ruwa na watsa kawai nayi sallar la'asar na kwanta ina hutawa.

A ɓangaren Ummu Affan da Maman Sadiq kuwa fitarsu suka yanke shawara cewa idan na kaisu so ɗaya bazasu sake tafiya dani ba dan abinda suka fahimta zan riƙa ci musu aljihu , ma'ana idan aka basu zan riƙa ragewa ni inci da yawa su abasu kaɗai , ummm kuji ɗan adam butulu ,

Yayin da Maman Sadiq ke bayar da shawara cewa suyi wayau muna zuwa su lallaɓa su anshi lambar shugaban ƙungiyar sai suce masa idan ana taro ko yana nemansu karya kira Sultana ya nemesu kai tsaye , Ummu Affan tace gaskiya haka ne , dan kinga idan aka bamu dubu ɗari zata saka rai a cikin kuɗin ta, ga, tunda itace ta haɗani dashi zata jira na bata wani abu a cikin kuɗin , Maman Sadiq tace haka ne , ai tana nuna mana hanya mun gama da banzar , haka dai suka yanke shawarar su ,

Bayan sun rabu kuma kowa ya yanke shawarar saiya koro abokin tafiyarshi dan kowa yaci shi É—aya , yayin da Maman Sadiq take tunani idan gwamnati ta bada mai da sabulu da magi da rigunan siyasa da ake rabawa zatayi samayya fiye da tunanin mai tunani ,

Itama a ɓangaren Ummu Affan haka ne dan har ta kasafa dubu ɗari yadda zata kaya mata tun kafin akai inda za'aje har sun yada Sultana a gefe , Ummu Affan ma tana tunanin yadda zata yada Maman Sadiq yayin da itama Maman Sadiq in take tunanin yadda zata kora Ummu Affan taci ita ɗaya ba tare data samu mai tayata ba.

Washe gari kuwa tun 7:22am Ummu Affan ta bayyana a gidanmu , tasha wanka ta ɗauko jagira irin ta zamani sai baɗa ƙamshi takeyi anci jaka da takalmi masu kyau ta ida rufe wankan da wani irin tsadajjen gyale tayi kyau fa abunta ,

Tana zuwa ta ganni ban shirya ba , tacemin da Allah muje kafin wacce mayyar tazo , nace tun yanzu ? Tace Eh na samu na ajiye yaran a maƙota muje mu dawo , nace tou ki bari itama Maman Sadiq in tazo basai mu tafi tare ba ? Tace nidai karmu jirata da Allah ki tashi mu tafi , nace tou yanzu gwamna ma kanshi ai bai tashi bacci ba , tace haba ai da a jiraka gara kai ka jira , dan Allah ki tashi mu tafi , nace kai gaskiya ni ko shara banyi ba , kuma ban wanka ba , tace jeki kiyi wankan ni kuma sai in tattara miki ɗakin kafin ki fito , nace to amma mi yasa bakya so aje da Maman Sadiq , na tambayeta ? Danni dama bana so aje da ita ,

Ummu Affan tace kinsan mutanenmu da baƙin ciki sai kaja mutum inuwa ƙarshe kuma yakai ka rana , nace tou ba aminiyarki bace ba ? Tace wa ni ? Ta nuna kanta sannan taci gaba da cewa ba aminiyata bace ba kawai dai muna gaisawa cikin anguwa , nace tou ina kika cewa mijinki zakije da wannan safiyar ?

Saida tayi murmushi tace tambaya kamar "yar jarida , ce masa nayi ƙawata bata lafiya za'a tafi da ita asibitin zariya zanje na dubata kafin su tafi , nace to misali idan mukaje bamu samu ganin gwamna ba fa sai akace gwamna abubuwa sun mishi yawa mu dawo gobe tou sai muka dawo idan zaki fita goben sai mijinki yace baza ki fita ba tou ya zakayi ?

Tace ina ai dabara ma bazata ƙare ba , idan yace bazan je ba nasan hanyar da zan biyo masa , nace Allah ya taimaka ina faɗin haka nayi waje dan inje inyi wanka , kafin in fito wankan ta share ɗakin tas ta goge shi ta shinfiɗamin zani a katifa , ina fito na shirya a gaggauce ko kalaci banyi ba muka bar gidan kafin Maman Sadiq tazo.

A napep muka je gidan Mamy , a ƙofar gida muka same ta cikin motar wani namiji ga kuma wanda ta nunamin da sunan mijinta yana zaune saman dakali yana kallon ikon Allah , gaisawa mukayi dashi na umarci Ummu Affan da ta shiga ciki na nuna mata gidan tare da cewa shiga muna zuwa ,

Tana shiga ni kuma nayi wurin Mamy muka gaisa na gaishe da baƙon nata , bayan mun gama gaisawa Mamy tacemin in shigo mana , baya na buɗe na shiga bayan na zauna muka ƙara gaisawa ,

Shiru na wani lokaci sannan Mamy tace Sultana ga mutumin ki yaga mutuniyarshi kalli iskanci da yakeyi leƙo ta nan ki gani , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya nace ni basai na gani ba , tace dan girman Allah leƙo kiga yadda bironshi ki rubutu babu takarda , dariya nayi sosai nace nidai bana san gani , Mamy tace haba so ɗaya fa zaki gani kawai , nace ba komai idan ya rubuta a takardar zan gani danni bana gane rubutu bisa iska ,

Dariya akayi gaba ɗaya , bayan wani lokaci kuma mukaci gaba da maganganu dai na sakin layi , bayan an gama mutumin ya tambayeni yadda mukayi da sabuwar sheƙar tashi , na goga mishi bayani duk yadda mukayi da su Ummu Affan hada Maman Sadiq duk ban ɓoye masa ba !

Yace babu damuwa ba hamsin za'a bata ba dubu É—ari zan bata yanzu sai ince mata gwamna yaje Abuja sai jibi zai dawo , kinga tana dawowa jibin ke Mamy sai ki bamu aron É—aki mintuna 30 sun ishemu sau É—aya kaÉ—ai zan sa mata hannu kuma in bata kuÉ—i daga nan da kanta zataci gaba da zuwa ana mata singing ,

Shiru nayi sukaci gaba da firansu da Mamy , bayan wani lokaci kuma ya juyo yace Sultana kirata na sallameta tafiya zanyi na ansa da to tare da fita daga motar na nufi cikin gidan babu jimawa muka dawo tare da Ummu Affan bayan sun gaisa yace mata gwamna yaje Abuja wurin shugaban ƙasa amma zai dawo jibi idan Allah yasa muna da rayuwa , tace tou Allah ya dawo mana dashi lafiya...

Ya ansa da amin tare da karkacewa ya fiddo bandir in "yan ɗari biyar² masu zafi ya bawa Ummu Affan da kwalin sabuwar waya yace kuma da akwai layi a ciki , ruɗewa tayi ta duƙe har ƙasa tana zabgaga mishi godiya tare da cewa Alhaji kasa min lambar ka a ciki ? Yace zan kiraki zuwa gobe yadda mukayi da gwamna zan faɗa miki , godiya tayi sosai kamar zata faɗa mishi sai ƙara godewa take godiya irin ta maroƙa ,

Wani irin kallo ya bita dashi yana lashe loɓonshi na ƙasa mai nuni da zan kashe wuta dake , Mamy kuwa fitowa tayi daga mota mukayi mishi sallama bayan muma yayi mana wanka da ruwan naira ya tafi ya barmu da ɗaurewa da ruwan godiya ,

Ai Ummu Affan kuwa cewa tayi bazata koma cikin gida ba lokacin da Mamy tace mu shiga ciki , juyin duniya nayi mu koma ciki tacemin tabar yaranta suna jiranta gida zata tafi , babu ko tayin kuɗin bare ta jira taji munce ko mun ƙoshi , haka ta saɓe abunta tabarmu da kuɗinta da wayarta tai tafiyarta , mu kuma muka koma gidan Mamy , gaba ɗayanmu a palo muka zauna inda Mamy take cemin Al ' Ameen ya kirata ya zageta fess dan Mardiyya ta kirashi ta faɗa mishi babu daɗi yace duk sai yaci uwarmu dagani har ke kuma ya faɗawa mai gida abinda mukayi ma matarshi kuma shi mai gidan yace duk sai an tattaremu an ɗauremu , ni kuma jin haka yasa na kira wannan mutumin na faɗa mishi tunda naga yana cikin gwamnati shima.

Nace to yanzu ya ake ciki ? Mamy tace sai munemi mafita , nace shi Alhajin ya yace miki ? Mamy tace yace mu jira idan anyi ƙararmu zai ɗaukar mana lauya , idanuwa na zaro nace wane irin lauya kuma na shiga 14 nidai gaskiya bana san huɗɗa da koto ƙarshe akai mutum gidan yari ni banda wanda ya tsayamin , kawai saina fashe da kuka , Mamy tace haba Sultana tou miye abun kuka muna fa da bakinmu ki barshi ya yanko sammacin kiga yadda alƙalin zaiyi idan yaga lafiyayun katifu ,

Cikin kuka nace shikenan kullum mai makon katifa tahau saman gado sai gado yai ta hawan katifa nidai na shiga 3 , Mamy tacemin da Allah ke banza ce ki kwantar da hankali babu abinda zai faru domin na sake kiran yarinyar nayi mata baraza na da zan saki vidion a social media idan Al ' Ameen ya sake magana kuma ta kama kanta sosai ,

Dakel dai Mamy ta lallashe ni ta kwantarmin da hankalina ta sake bani ƙwarin guiwa , a gidanta na yini saida nayi sallah isha'e ta kawo ni gida ,

Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya , yanzu tsawon watanni 3 kenan da kafa su Ummu Affan da Maman Sadiq a ƙungiya kuma tun daga ranar dana kaita bata sake bi takaina ba , yanzu tama ƙwace sosai wuta kawai takeyi abunta a cikin anguwa ,

Mijinta kuma tuni ta wanke ta bashi dan tunda ya taso ya fara hayagaga ta kwantar da banza da asiri , Maman Sadiq itama tuni an mata register amma bata ƙarƙashin ƙungiyata tana ƙarƙashin ƙungiyar su Amisty ne ,

Safiyya kuwa ɗiyar Baba ƙarami ciki gareta , gashi biki yazo Mamy ta hana talabijin bare labulaye , fitina sukayi ta rashin lissafi akan rashin talabijin da labulaye , ga rashin lafiya ya taso ta gaba tun Safiyya tana boyewa har abu ya fara damunta dan haka ta faɗawa Mamy cewa bata lafiya wata 3 bata ga jinin al'ada ba , kai tsaye Mamy tace ciki gareki sai kawai kije ki zago bedi ki saɓa kisha ,

Safiyya kuwa ta gaji da ɓoye ²ta rasa ina zata soka rayuwarta gashi Mamy bata , bata sahihiyar mafita ba , dan haka kawai ta haƙura ta faɗawa mahaifiyarta komai bata ɓoye mata ba , da Mamy da mahaifiyar Safiya akaci gaba da musayar harshe tsakanin Mamy da Uwar Safiyya , tashin hankali naƙin ƙari , ni ko kada Mamy ta faɗamin cewa nayi ai ba danneta akayi ta ƙarfi aka ƙwata ba lokacin da Alhaji yake bata tana ta tanɗewa tare da wa suka tanɗene ? Taje can taji da abunta sakaran banza tunda bata iya shan gishiri ba ,

Ƙarshen film in dai mahaifiyar Safiyya zama akayi aka sasanta suka fuskanci juna ita da Mamy daga ƙarshe dai a asibiti aka wanke cikin tass , ta tashi babu talabijin ba labulaye babu budurci kuma babu albashin kuɗin aikin da alhaji yayi , bayan wanke ciki da sati biyu aka ɗaurawa Safiyya aure , kwanata biyu a gidan miji ya korota tare dayi mata shegen duka rashin samunta da baiyi ba a matsayin budurwa , itama daga nan ta yanki nata tikitin na shiga sahun jerin *Kwarata...* kuma buƙata na ya biya.

Rayuwa mukeyi dai tsakanin ni dasu Amisty kowa naji haushin kowa , har yanzu ban sake ganinta da Babana ba , ta sake faɗaɗa ƙungiyarta da manyan mata masuji da duniya kuma duk matan aure sunfi yawa a cikinta domin yanzu kasuwar sutafi ja ba'a neman "yan mata kuma bata zawarawa akeyi ba matan auren dai ,

Ƙungiyar Amisty ta samu karɓuwa fiye da tunanin mai tunani ta samu kuɗi ta goge ta zama lafiyayyar hajiya , nima kuma inata bakin ƙoƙarina wurin ganin na kafa tawa ƙungiyar amma wallahi taƙiya daga ni sai Mamy a ƙungiyarmu , itama Ummu Affan ta kafa tata tana bada hayar matan aure ko a hanya ta ganni batamin magana saboda tana ganin tafi ƙarfina , al'amirin duniya ya fara bani mamaki dan haka na fara sanyi da rayuwata.

Mazan kuma nabi su² amma da an fara ciniki dai kalmar ɗaya ce 1k gani ni kuma haɗama gareni bana iya iba kaɗan sai in kantamo dubu ɗaruruwa , zuwa wannan lokaci kuma al'amura sunjamin baya sosai tun ba'ayi nisa ba duniyar ta ajiyeni bani ake yayi ba lokacin ba nawa bane na wasu ne , kenan tun kafin na ajiye bariki tana neman ta ajiyeni , dan har alaji su Amisty sunyi gaba dashi !

Ina cikin wannan tararrabi Allah ya kawomin wani zazzafan matashi maiji da kanshi ga kuÉ—i ga gayu amma matsala É—aya wallahi mummuna ne ,

Naji daɗin zuwanshi kuma mun antaya soyayya shi ya wankoni daga talauci yayi ta yayyafin ya cidar hadarin naira da anyi tsawa saidai kiga yana ɓarin naira , cikin ƙanƙanin lokaci nima na farfaɗo na fara dawowa hajiyata ,

Naci gaba yanzu har hotel nake kwana amma matsalar ɗaya abunda na fuskata bayada alƙamin rubutu , kullum haka zanje in kwanta salaf in taso babu wani ɗan shafe² ko ɗan lashe ² ko ɗan tsotse² idan kuma na tashi tafiya haka zai bani kuɗi masu sa mutum ya kasa gano hanyar gidansu , abun a dameni dan haka na tambayeshi nace shin wai kai bakajin kanajin sha'awata ? Saidai yayi dariya yace yana da sha'awa in kwantar da hankali ranar hawa na zuwa ,

Ina kwance ina bacci a saman gadon hotel nayi guda² ina sararawa abuna idanuwana a rufe amma ba bacci nake ba , a tunaninshi nayi bacci dan haka ya tashi saf² ya fita daga bedroom in , wallahi haka nan naji tsikar jikina ta tashi jarr hankalina ta tashi ƙararrawa ta doka hayani ta riƙa tashi cikin kaina , da sauri na sauko daga saman gadon nayi bakin ƙofa ,

Da sanɗo na shiga palon ya bada baya yana waya cikin harshen turanci , hakanan na tsargu dan haka zuciyata tace kiyi masa vidio ko recording kamar yadda kika saba wannan da ganinshi baida gaskiya , da sauri na latso recording na fara ɗauka saida ya gama wayar tas sannan ya juyo da wata irin siffa mai ban tsoro dasa firgici tunda nake duniya ba taɓa ganin irin siffar ba , dakewa nayi banji tsoro ba kuma ban firgita ba naci gaba da addu'a nima na tsareshi da ido ,

A hankali siffarshi ta dawo siffarshi da nasanshi da ita , murmushi yayi yace ke matar aure ce ? Na girgiza kai da a , a , yace tou ki wuce daga yau karki sake dawomin matan aure muke nema , murmushi nayi tare da cewa ngode kuma na barka lafiya , ina faÉ—in haka nayi gaba abuna ko ciki ban koma ba bare na É—auko gyalena , saida na fita daga É—akin na ruÉ—e na firgice na kwarara wani irin ihu mai tada hankali ,

Hmmm

_Ƙalu bake gareku matan aure......_

04/10/2019

*JAMILA MUSA....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 49

Gaba ɗaya na firgice na fita hayyacina kururuwar da nakeyi ta karaɗe kaf girman hotel in , hayagagata ya jawo hankalin mutane akayo wurina ana lafiya ? Duk wanda na gani sai inga fuskar mutumin nan gareshi wayyo Allahna na shiga 3 🙆🏻 na lalace shikenan mutuwa zanyi na bani ׳ na ƙarasa maganar tare da faɗuwa ƙasa ina burgima.

Baiwar Allah lafiya ? Meke damunki ? Shine tambayar da mutanen da suka zagaye ni sukemin amma maimakon naji maganarsu sai naji muryar mutumin cikin muryar tsoratarwa da firgitarwa yana cemin da hantarki da ƙodarki ko zuciyarki wanne kika bamu....

Da sauri na dafe cikina na tallabo saitin zuciyata amma har yanzu wayata na riƙe ram a hannuna , cikin kuka nace wallahi bazan bayar ba , nawa ne ni ɗaya , cikina ne da zuciyata hantana da ƙoda Allahna ya bani ba wani ba , kuma ubangiji bazai baku damar rabani da ko ɗaya ba , wata irin gigitacciyar dariya akayi tare da cewa kina nufin kinci kuɗinmu a banza ? Tou wannan kuɗin ki sani jinin wasu ne da wasu sassa na jikin ɗan adam dole ki bayar da naki kema domin a bawa dodo ya bamu kuɗi zuciyarki zata shiga kwarya , bankwana da duniya sai wata rana....

Gaggaɓewa akaci gaba dayi da dariya data gigitani a karo na biyu , addu'o'e naci gaba dayi da ƙarfi idan ina addu'a bana gama wata saina saketa na kamo wata , dai najin sautin muryar dariyar nayi sai sautin kuka har zuwa wannan lokacin ban daina addu'a ba , bayan wani lokaci kuma na dainajin sautin kukan gaba ɗaya...

Da sauri na miƙe ko jikina ban tsaya kakkaɓewa ba nayi gaba , mutane suka bini da kallo yayin da wasu ke tunanin ko ina da taɓin kwalwa ne , da gudu na fita daga hotel in , ina na fita na samu napep sai gidan Mamy amma har yanzu hankali na baya jikina gaba ɗaya a ruɗe nake , napep na tsayawa na fita da gudu nayi cikin gidan Mamy , bata nan sai yara na samu nace musu ina Mamarsu ? Sukacemin yanzun nan ta fita tace idan kinzo ki kirata ,

Jikina yana ƙyarma na fara laluben wayar Mamy babu ɓata lokaci ta ɗauka , gaisawa mukayi nace mata kina ta ina haka ne ? Sunan hotel in dana baro ta faɗamin tare da cewa wani sabon sauna ne na samu ki jirani na wankoshi cikin mintuna kaɗan zan dawo , kaina ya juya a gigice nace karki je , ki dawo hotel in nan akwai wani gahurtaccen matsafi daya bayyana karki shiga ɗaki ki dawo , Mamy tace wane ɗaki ? Nace ɗakin dana shiga wallahi matsafi ne karki shiga ki dawo akwai zama na musamman , Mamy tace tou lamba nawa ne ɗakin ,

Da sauri na dafe kaina duniyar ta riƙa juyamin kamar nahau shillo mai wanawa , gafa lambar ɗakin ina gani a idona bana iya faɗa dan na iya lissafin lambobi tunda dasu nake sarving numbobin mutane a cikin wayata , ganin na kasa faɗa kawai nace ....

Ki dawo........... Na faɗi ki dawo cikin wata irin murya hawaye suka gangaro daga cikin idona ina cewa nidai kawai ki dawo matan aure yake nema ko wane ɗaki bana so ki shiga ki dawo Auntyna bana san na rasa ki adaidai wannan lokacin ki dawo dan Allah na ƙarasa maganar ina durƙushewa ƙasa naci gaba da kuka , amma duk wannan maganar da nayi sam Mamy bata jini ta riƙa hello , hello idan kina jina kawai ki jirani , tana faɗin haka ta kashe wayarta ,

Da gudu na fita daga cikin gidan , mai napep in daya kawoni shi nace ya maidani inda ya É—aukoni dan dama ban sallameshi ba , nace kayi gudun bala'e ka kaimin motar nan maleji karka tsaya kuma karka kauce ina so kawai na buÉ—e idona na ganni a hotel in nan kamar kyaftawar ido ,

Gudu mai napep yakeyi amma ce masa nake ya ƙara ina kiran wayar Mamy amma ba'a ɗauka , saidai na daki napep in nace wuta mai mota nace karka tsaya kaucewa ababen hawa muje kayi tuƙin nan kamar babu koma bisa titin nan saimu , gudu yake balbalawa na tashin hankali amma gani nake kamar baya tafiya , wayar Mamy kuwa saidai ta ƙari ringing inta ta tsinke amma ba'a ɗauka har muka isa hotel in ban daina kiran wayar Mamy ba kuma bata daina shiga ba haka kuma babu wanda ya ɗauka...

A harabar hotel in naga dandazon mutane , da gudu na tunkari inda suke kamar wata mahaukaciya na riƙa ture mutane , hasahsena ya zama gaskiya domin Mamy ce yashe a ƙasa mutane sun zagayeta ga "yan sanda har sun rigani hallara a wurin , jini ne kawai ke ɗiga daga cikin idon Mamy kamar babu ƙwayar idonta dan baka gani hasken idon ko sai jini dake ɗiga ɗis ² ,

A wurin mutane ke cewa yanzu wata ta fita itama tana ihu ita Allah yasa tana da sauran shan ruwa a gaba , goge hawaye nayi a zuciyata nace ba ni suke so ba matan aure , mutane sukaci gaba da cewe lallai akwai abinda yake faruwa , jiki a sanyaye na na isa gaban Mamy nace Aunty na ƙarasa maganar ina mai kamo hannuwanta , bata iya magana ma kwata² dan haka na rungumeta naci gaba da kuka , bayan "yan sanda sun gama bincikensu kuma basu samu wata sahihiyar sheda ba haka aka ɗauki Mamy da wayarta akayi asibiti da ita... Nima napep na koma nace masa mubi bayansu.

Bayan mun isa asibiti "yan sanda suka danƙamu a hannun likitoci babu ɓata lokaci aka shiga duba Mamy , tashin farko dai likitocin sun tabbatar da babu idon Mamy kuma har yanzu jini bai gama fita ba , ni kuma hankalina yafi karkata akan wayarta dan haka naje wurin ɗan sanda nace ranka ya daɗe wayar zaka bani na kira Babanmu ,

Kallona yayi sama da ƙasa sannan yace wace ce ke ? Nace ɗiyar mara lafiyarce ni , dan bana nan na dawo gida "yan uwana sukace Mama tace ta fita amma idan na dawo na kirata , bayan na dawo suka faɗamin na kirata mun fara magana da ita a waya daga baya kuma saita nunamin batajina , ka duba jerin kira kuma zaka gani dan daga baya nayi ta kiranta bata ɗauka ba ,

Miƙomin wayar yayi domin wayar Mamy ba'a buɗeta sai an zana pattern yace buɗeta tou tunda kince ta Mamanki ce , lafiya lau na zana na buɗe wayar domin kullum a gabana take zanawa kuma baida wahala , bayan na buɗe ya duba yaga kiran da nayi mata kamar dai yadda nayi masa bayani , yana cikin dubawa kira ya shigo dan haka ya ɗauka , bayan gaisuwa naji yace muna genaral , yana faɗin haka ya kashe ya miƙomin wayar ,

Babu wani daÉ—ewa mijin Mamy ya iso asibitin , yasha kuka kamar ranshi zai fita duk iskancin da Mamy ke zubawa baya gani yana san matarshi , jikin gadon Mamy ya matsa cikin kuka yace Mamy Allah ya tsinemawa wanda yayi miki haka , Allah ya baki lafiya mata ta ubangiji yasa ki warke ,

A wahalce Mamy tayi murmushi ta lalabo hannun mijinta tace kayi haƙuri mutuwa zanyi amma ina roƙonka daka yafemin , cikin kuka ya rungume Mamy yace Hajiya baza ki mutu ba wallahi baki mutuwa , Mamy tace naji amma kawai kace ka yafemin , cikin in'inna yace na , na na ya.... Ya fe miki , godiya tayi masa tare da cewa naji muryar Sultana tana ina ? Yace gata nan hajiya ya kamo hannuna ya haɗa da nata ,

Umarni ta bashi cewa da Allah ya fita zatayi magana dani , cike da ladabi ya fice daga ɗakin , Sultana ta kira suna na , nace na'am tace dubamin babu kowa a kusa dani ? Babu Aunty na faɗa cikin girmamawa magana ta farayi bayan na tabbatar mata da babu kowa a wurin :•

Sultana ta kira suna na , nace na'am Aunty , tace tou ki saurareni dakyau , nace inajinki Aunty , Mamy tace kinga whatsapp in nan da kike ganinta ? Wallahi ba ƙaramin haukata mata takeyi ba , shiru nayi ban sake magana ba naci gaba da sauraren Mamy .

Aurena biyu a duniya , ina da shekara 39 akamin auren farko bayan nasha gwagwar mayar rayuwa , iyayena ba masu kuɗi bane suna dai da rufin asiri na ci da sha da sutura , mahaifina ba ɗan kasuwa bane kuma ba wani shahararen ɗan boko bane ba , yana aiki a ƙarƙashin kamfani wani attajiri ,

Matan Babana biyu daga mahaifiyata sai abiyar zamanta , muna da yawa sosai mu "ya "yan babanmu , cikin hukuncin Allah matan gidanmu suna auren mazaje masu rufin asiri , duka matan gidanmu saida aka aurar dasu kaf har ƙanne na ni ban samu mijin aure ba ,

Na tayar da hankalina sosai domin auren nake so ido rufe amma ban samu mai aurena ba , abin ya dameni sosai saina ma daina fita kwata ² kullum ina gida ko a familynmu daina shiga nayi domin na ganɗame sosai saina farajin kunyar shiga mutane ko baƙi akayi gidanmu sai in ɓoye ,

Ina wannan ɓoye ²n ne Allah ya kawomin Bello a rayuwata , Bello abokin Yayana ne duk duniya baida aminin daya wuce Bello shima Bello baida aminin daya wuce Yayana , kowa yana san kowa kuma kowa baya ɓoyewa kowa sirrin junansu , sun yadda da juna fiye da tunaninki domin dai Bello zai iya tarawa da matar Yayana shima Yayana zai iya tarawa da matan Bello ,

Tunda Allah yasa ya ƙyalla idonshi ya ganni ya liƙemin , nasan baƙin halin Bello sosai nasan illarshi kuma nasan miyagun halayyarshi dan haka koda ya furtamin kalmar so ban ansa ba nace bana sansa , shine ya faɗawa Yayana yana so na amma nace bana sansa , shine Yayan nawa yazo ya sameni yayi min kaca ² , nace ni bashi ne bana so ba halinshi ne bana so , kuma kaji tsoron Allah kai kanka baza ka iya bashi auren "yar uwarka da kuke ciki ɗaya , Yaya yace tou ko kinso ko kinƙi sai kin auri Bello idan baki aureshi don Allah ba zaki aureshi dan dole , saikin nemo Bello da kanki , yana faɗin haka yayi gaba abunshi ,

Tun daga wannan ranar sukayi ta kusatsamin asiri na firgice na fita hayyaci na da kaina nake nemo Bello , idan na fita ban ganshi ba ko zankai gobe ban dawo gida ba saina ganshi hankalina zai kwanta ,

A taƙaice dai Bello na aura aurena na farko , ranar da aka kawoni gidan Bello bayan mutane sun watse shima Bello ya shigo da abokanshi da suka rako ango ɗakin amarya kamar dai yadda akeyi ,

Kowa fatan alkairi yaimin da addu'ar zaman lafiya , bayan an gama Bello ya bayyanar min da abokanshi kowa ya faɗamin sunanshi , saida yazo kan *BINNA...* ya dafashi cike da soyayya yace kinga wannan nace Eh yace Binna kenan Bello baya rayuwa saida Binna kamar yadda mutum bai rayuwa saida lumfashi , ina san Binna fiye da yadda nake san kowa a duniya , Binna nawa ne nima nashi ne , murmushi Binna yayi cike da izza amma baiyi magana ba , gaskiya Binna ya shiga zuciyata kuma duk duniya ban taɓa ganin wanda nake so a daidai wannan lokacin ba kamar Binna ,

Sun É—an daÉ—e dai suna fira amma har akayi firar aka tashi Binna bai saka baki ba har suka gama suka tafi , bayan Bello ya dawo daga rakiyar su yacemin na tsani Binna na nuna miki shi domin ki ganshi , hawaye ya cika a idon Bello yace tsinan Allah kawai ranar da zan zama ango Binna ya É—auke budurci ya gudu , saboda kawai nayi ma yarinyar gidan da suka É—aukoshi a bakin titi suna taimaka mishi ,

Nayi alƙawari saina ƙafa babban tarihi a zuciyar Binna saina tagayyara mishi rayuwa saina zama silar rushewar kaf ahalinsa wanda suka gabata da wanda basu zo ba , saina jefa ƙiyayya mara gogewa tsakaninshi da "yan uwanshi da suke uba ɗaya , nayi alƙawari kuma babu gudu babu ja da baya ko duniya zatashi saina cika muradina ,

Wani irin nishin wahala Mamy tayi har yanzu jinin bai daina É—iga ba , a wahalce taci gaba da cewa....

Bayan Bello ya gama alkaba'inshi ya hawo gado babu wata sallar godiya ga Allah babu wani abunda ya shigo min dashi irin wanda ango yake zuwa ma amarya dashi a daren farkonsu , haka ya hayeni yaita sassaƙa kamar mai faskare ya samu babban bedi , haka kuma babu wata addu'ar tarawa da iyali ,

Sam banajin daɗin zaman aure da Bello dan na fahimta mugun atsabibi ne , babu sallah bare salati haka kuma bai yadda da ƙaddara ba komai dai malamin tsibbu , ina haƙuri dai ina zama amma sam bana sansa dauriya ce kawai ,

Tun daga ranar da aka kawoni ina amarya ban sake ganin Binna ba saida yazo faÉ—ama Bello an haifeki ,

Duk ƙudirin da Bello yayi akan Sultana da burin mahaifinta akanshi ta faɗawa Sultana , tace wannan shine silar abinda ya rabani da Bello domin na nuna ban yadda ba ya aiwatar da ƙudirinshi akan Binna ba domin gaskiya ina sansa kuma bazan bari a cutar masa da rayuwa ba ,abun yayi ma Bello ciwo dan shine ya sakeni ,

Bayan mun rabu nayi ² Binna ya aureni yaƙiya ina sansa kuma ina sha'awarshi dan haka nayi masa tayin kaina kuma Allah ya taimakeni ya ansa , da sauri na runtse idanuwana , Mamy bata gani na dan haka taci gaba da cewa kullum ni nake isko Binna ko ya nunamin baida buƙata sai nayi yadda za'ayi ya kwanta dani danni kaɗai nasan yadda nakeji idan ina kwance dashi ,

Har na shekara 2 ina zawarci Binna fa ya kame akan bazai aureni ba , dole na haƙura na samu miji nayi aure , tunda nayi aure na daina zuwa wurin Binna , ina zaune da mijina lafiya babu abinda na nema na rasa , saidai zaman kaɗaici yana damuna , wannan dalili yasa na saya babbar waya na fara chating..

Banda friends sosai a whatsapp dan haka dana duba naga wanda ke online saina dameshi da surutu , idan nayi magana sai mutum ya ɗauki tsawon lokaci bai bani ansa ba , na gaji dai nacema wata ƙawata wai sai inyi magana kuyi kamar baku gani ba , dariya tayi sannan tacemin haba hajiyata yaushe rabon duniya da ayyaraye , ni bana cht da mutum prvt ina can group inmu na mata masu duniya , wayayyin mata masu aji masu faɗa a gidan aurensu aji ina ƙaruwa ina zan tsaya saurarenki.

Koda na tambayeta me ake koyawa a group in sai tacemin bara tayi adding ina gani ya kori ji , nace tou , bayan tayi adding ina ta gabatar dani tare da tura hotona , kowa dai yaimin fatan alkairi , a hankali dai nake rayuwa da "yan group in ina fuskantar su ,

Basu da aiki sai turo style na ɗinki , idan sabuwar atamfa ta fito sai an turota , wasu takalman yayi masu zafi suma a turo jukkuna gyaluluwa "yan kunne tsarƙa , bawai na siyarwa bane ba , a , a sune dai na zamani su matan idan suka gani zasuje kasuwa su siya ,

Mace kuwa idan tayi lafiyayen girki saita gama tsara abunta kaf a tebirin cin abinci sai ta ɗauko hoto ta turo a group , idan wanka kikayi kika kai ƙarshen adaka zakiyi hoto ki turo matan group in suna zugaki ,

Shin da Allah mace ta dafa lafiyayyen abinci komai yaji banda bala'e kina kallon yadda naman kaji ke wali ga lemuna masu kyau da tsada an jera ki faɗamin ke kinyi ɗan wake da miyar ƙuli ko kinyi zazafen tuwo kin ɗauka ki tura ?

Mace ta share ƙaton fili ga filawowi ta ɗauko hoto tasha kafirarriyar shadda ko wani ƙaton leshi ko super ke kuma mijinki baida halin ɗinka miki super atamfa rober yake da halin ɗinka miki kuma ita gareki shin kin ɗauka hoto ki tura a group in mata masu duniya ?

Banda ko sisi amma ina da style na É—inkuna a wayata yafi dubu , duk wata jikkar da ake yayi ko atamfa sabuwar fitowa tana cikin wayata , banda sisi mijina baya dashi na manta da hatta yatsun hannuna ba É—aya suke ba , duk lokacin da wata ta É—auko hoton palonta ta turo sai ince ya zanyi na maida nawa haka ?

Kafin wani lokaci na fara tadawa mijina hankali cewa duk mazan duniya suna kishin matansu suna musu sutura sun wadatasu da komai amma duk lokacin da nayi maka magana sai kacemin kai babu ,

Idan yayimin nasiha ya bani haƙuri sai kuma in haƙura , kullum dai abu ci gaba yakeyi dan haka na fita daga group in , amma kash ina fita admin in ta biyoni prvt tacemin taga nayi left lafiya ? Ban ɓoye mata komai ba nace gaskiya ina ganin kayane hankalina yana tashi zuciyata tana min wasi² kuma mijina baida kuɗi shi yasa na fita , dan na lura idan aka turo kayan yayi duk wacce ta sawo idan ta ɗinka hoto takeyi ta turo kowa ya gani ,

Tacemin bara in kiraki nace tou , babu ɓata lokaci ta kirani bayan mun gaisa tacemin duk wanda na gani a group in nan matan aure ne , kuma yadda nake tunanin mijina ma baida hali yafi na wasu a cikin group in , kinsan yanzu ana zamanin rayuwar "yanci kina da aurenki amma kina da abokinki a waje , wanda zai ɗauke miki duk wata hidima taki ,

"Yanci shine babban mutunci da zaran kin rasashi taki ta ƙare , cikin mintuna biyar kacal abokinki zaiyi ya miki abinda mijinki da kike aure bazai miki irinshi ba , yanzu an daina duhun kawai rayuwar ƙyaunci ta gushe , ki riƙe babbar waya kici mai kyau kisha mai kyau ki ɗaura mai kyau ki gyara muhallinki babu wanda yaji kuma babu wanda ya gani ,

Nace tou idan kuma mijina yace ina na samu kuɗin da nake wannan hidimar fa ? Tace dama ai kafin ki shiga zaki rufe banza a tulun ƙasa zaki riƙa juya rayuwarshi kamar remote sai yadda kikace dashi babu shi babu magana kuma idan "yan uwanshi sukayi mishi magana tou fa ko uwarshi ce zai iya rabuwa da ita akanki , nace tou abokinki me ake bashi yake bada kuɗi haka kuma a ina zan samu abokin , tace abinda zaki bashi yana nan jikinki samun shi kuma nine zan haɗaki dashi , nace tou zanyi shawara ,

Sati ɗaya ina neman mafita kuma kullum saita kirani ta ƙara bani shawara , ƙarshe dai na haƙura nima na antaya a duniyar kwaratanci , social media tana da amfani tana gyara amma illolin sunfi gyaratanta yawa kusan irin mutanen da kuke huɗɗa dasu , tari tayi sosai cikin yanayin wahaltuwa tace ki riƙe wayata a hannunki akwai wata ƙawata dana haɗa da Bello akwai wasu maganganu da nayi da ita akanki kuma na haɗasu domin ina so duk wani shiri nasa ya lalace ƙarshenshi tazo , naso na kafa rayuwa mai inganci a gareki amma lokaci ya ƙuremin , cikin kakari tace kuma Baban Hafsa da Baban Amisty da Binna ...... Daga nan lumfashin Mamy ɗauke ,

Shikenan Mamy tata , ta ƙare ina da tulin tambayoyi da zan mata amma ta tafi inda bazan sake ganinta har abadan duniya , me mutumin yayi mata ? Ya akayi aka ƙwaƙwale idonta ? Ina ƙawarta data haɗu da ita a sanadin whatsapp ? Ya akayi Babana bai aureta ba ? Cikin abokan Bello waye Yayan Mamy a ciki ? Ina iyayenta suke ? Wayyoni Allahna na shiga 3na , tou wai meye take san faɗamin data kira sunan Babana dasu iyayensu Amisty ? Wai ya rayuwata take tafiya a taltala ? Wani irin juyi kaina yayi na saki wani irin gahurtaccen ihu tare da faɗuwa ƙasa somammiya ,

Ihun Sultana yasa mijin Mamy ya shigo da gudu , da taimakon likitoci aka samu aka farfaÉ—o da Sultana daga duniyar sumar data tafi , a lokacin dana farko har an fita da gawar Mamy waje an sakata a mota ,

Mijin Mamy ya bani wayoyi duka domin duk firar da mukayi da Mamy yaji komai , yace min kije gida sai Allah ya kaimu gobe za'ayi jana'izar Hajiya , mai napep in da kika zo dashi na sallameshi kije kar a nemeni ,

Yana faɗin haka yayi gaba , kamar wata doluwa haka na riƙa tafiya irinta sakarkari har na fito waje , napep na samu na faɗa masa inda zai kaini , har na iso gida kuka nakeyi haka na sauka daga napep in nayi cikin gida abuna , shima Babana ya sallameshi ya tafi ,

Wanka na farayi har na fito kuka nakeyi , zuwa wannan lokacin kuma labarin mutuwar Mamy ya fara zagawa a cikin gari , har su Amisty sunji labari kowa so yake yaji dalilin da yasa aka ƙwaƙwalewa Mamy idanuwa , bayan na fito wanka ina zaune a gefen katifa na kunno recording in da nayo bana gane komai amma fa ga murya nan lafiya zaw kanajin komai , aje wayar nayi na fita nayo alwalla ina dawowa na saka kayana ban shafa mai ba , hijabi na saka nayi sallah la'asar da ban samu yi ba ina gamawa na maida magrib bayan na sallame na ɗauki alkur'ani naci gaba da karantawa dan har yanzu bana cikin natsuwata ga tsoron da naji daga farko ga kuma mutuwar Mamy da aka zare ranta a gaban idona ....

Tsaye yake gaban madubi yasha ƙananan kaya cikakken namiji kenan tsawonshi ma kanshi abun burgewa ne , sanye yake cikin farar riga da bakin wando rufaffen takalmi baƙi yasha stocking da bakin belt ƙamshin turare mai daɗi da dasa farinci mai jefa mutum yanayi marar gogewa a rayuwa sai tashi yake , murmushi yayi yayin daya fara sharce gemunshi yana cewa , sa'a da kanta take kwankwasa mana ƙofa ga duk nasarar namiji mace ce jigonshi , cingom yasaka a bakinshi saida ya ɗan tattauna yace gani nan zuwa gareki An matana......

05/10/2019

*JAMILA MUSA....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 50

Cike da farin ciki ya juyo , amma me ? Sai yaga *Jiddah* tsaye ta zarge hannuwan ta , wayoyinshi ya ɗauka sannan ya tunkaro ta dan ta hanyar da zaibi ya wuce ta tsaya , cike da kissa tace haba Yaya daga dawowa kuma ina zakaje haka da daren nan ? Inda raina yake so zanje , haba Yaya gaskiya haka an shiga haƙƙina , kallon raini wayau yayi mata tare da cewa a haba ? Umm gaskiya ina so mu kwanta mu huta duk gajiyar jirgi tana damuna , ta ƙarasa maganar tare da san kwanciya a jikinshi , zamewa yayi da sauri ya karkata ya fice daga ɗakin.

Ni kuma bayan nayi sallah isha'e tunanin duniya yazo ya tokaremin zuciya , ikon Allah wato ita rayuwa haka take , Mamy bata taɓa tunanin mutuwa ba kwata ² a "yan wa'annen lokuta , hawaye ya gangaromin daga cikin idona nace shikenan anyi zamaninta an gama , duk saɓawa ubangiji da tayi saboda samun duniya kuma Allahn ya yaddar mata ta samu kuma ta tara , amma ta tafi ta barshi domin ansa kiran mahaliccin ta ,

Me ake ma haÉ—ama a duniyar ? Bayan babu wanda yazo dashi kuma babu wanda zai tafi da komai , anan aka samu kuma anan za'a tafi a barshi , haba mata meke ruÉ—armu a cikin duniya ?

"Yar uwa ko kunyi yar jejeniya da mala'ikan mutuwa ga lokacin da zaizo miki ? To kisani mutuwa bata sallama bata jira sai kin gama sharholiyarki wallahi zata iya riskarki a duk yanayin da kike ciki , ba ruwanta da kina aikata alheri ko akasin haka , ya ubangiji ka karɓi rayuwarmu muna masu aikata alkhairi ka sada mu da aljannar ka dan darajar fiyayyen halitta S. A. W , am3n.

Gadai Mamy nan an tafi neman duniyar amma an haɗu da mala'ekan mutuwa a hanya , kai ubangiji kasa muyi kyakkyawan ƙarshe , ko waye ma ya haɗa Mamy da wannan ibilishin ?

Ƙarar wayata naji a gefena a firgice na juya inda take na miƙa hannuna na ɗauko , lambar Dikko naga ta bayyana a saman screen in wayata , ajiyar zuciya na sauke da sauri na ɗauki wayar tare da miƙewa tsaye na karata a kunnena ,

Sai sauke wani irin wahaltaccen numfashi nakeyi mai nuni da nasha wahala , cikin muryarshi maisa natsuwa yace har kin fara bacci ne ? Kukana ya ƙara kwacewa ban bashi ansar tambayar shi ba nace shine ka tafi ka barni.... ?

Murmushi yayi mai sauti cikin murya mai kashe jiki yace in dawo ne ? Da sauri nace Eh , dariyar mugunta yayi yace An mata taji a jikinta tou fito gani nan ƙofar gida , da gaske ? Na tambayeshi sai kin fito zaki tabbatar da haka , da sauri ya ajiye wayata nayi waje da gudu ,

Dikko yana tsaye ya jingina da mota ya rungume hannayenshi a guje na isa inda yake tsaye da niyar in rungumeshi , a wayance ya matsa daga saitina ni kuma na É—an sassauta gudu na saboda na iso ina ganin ya kauce nima na basar na rumgumi mota ,

Kauda kanshi yayi gefe tare da cewa ya kike ? Nima juya mishi baya nayi ina wasa da ƙasa da babban ɗan yatsana na ƙafa nace aini dana san kaine ma da ban fito ba , buɗe mota yayi ya shiga yana cewa ai dan nasan dama idan nine baza ki fito ba shi yasa nace miki ga Dikkonki ya dawo , ya ƙarasa maganar a daidai lokacin da yake zama a mota ,

Juyowa nayi dan a tunani na tafiya zaiyi , murmushi yayi yace ba tafiya zanyi ba banajin daÉ—in tsayuwar ne shigo mu tafi , da sauri na zagaya na buÉ—e mota na kame a gaba , ina rufe murfin motar ya taka motar muka shiga gidan dawakan shi ,

Kusa da motar daya bani yayi parking , ajiyar zuciya ya sauke tare da riƙe sitiyarin da duka hannayen shi biyu yayi miƙa cikin yanayin gajiya tare dayin hamma yace An mata na gaji wallahi yayi maganar cikin murya mai ladaftar da zuciya ,

Murmushi nayi amma banyi magana ba , dan idan inajin muryar Dikko sai inji tawa wata iri shi yasa ban cika magana a gabanshi ba , wayarshi ke ringing dan haka ya É—auketa daga gefenshi daya ajiye yana cewa tou fa , karkace kaina nayi ina kallon fuskar shi yayin da hasken wayar ya haskaka fuskarshi dan duba mai kiranshi waya ,

Ɗan kallo yayi mai kyau yayin da idanuwan shi ke duba daga saman wayar zuwa ƙasa , zai ɗauka yace nifa bana san kallo da yawa , ki daina kallona haka nan tunda bakya so na , a dai² lokacin daya ɗauki wayar yana cewa inajin ka ,

Tou haka yace kuma ? A , a gaskiya bana kusa kawai kuje idan na dawo Ashiru zai tattaro minsu , ba komai fa kawai kaje abunka , to yayi kyau , ya kashe wayarshi ,

Bayan ya gama wayar ya juyo ya fuskance ni sosai yace An mata mi yasa kika bar mota tayi datti bakya hawanta ? Nace haka nan , hmm tunda bakyasan Dikko motar da ya baki ma bata burgeki ko ? Nace tana burgeni mana kuma ai nahau ta ma , Dikko yace haba An mata ai da kin hau wannan motar da naji a jikina , zansa a wanketa a daren nan ko baki so na ki hau motar nan don Allah inji daÉ—i kuma ko bakida inda zakije gobe kiÉ—an hau ta ,

Nace tou , yace yawwa ngode sosai , bayan wani lokaci kuma ya sake kallona yace An mata wai dan Allah mi yasa kike da kunne ƙashi ? Mi yasa bakyajin magana ? Nace me kuma nayi yanzu ? Bama kisan abinda kikayi ba ko ? Nace Eh , jinjina kanshi yayi yace yanzu ina amfanin irin rayuwar da kika koyama kanki don Allah ? Kullum baki da aiki sai ɗaukar tsiraicin mutane ,

Idan an taroki nan sai ki koma nan kina rayuwa kamar baki da kwalwa a kanki , shiru nayi banyi magana ba , cikin ɓacin rai yace ki kiyayeni ranar da nima zan miki tsirara in miki irin abinda kike ma mutane , bana san ɓacin raina akan ki saboda fushi na baida kyau idan har nace zanyi miki hukunci dai² da irin abinda kike aikatawa lafiyayen duka ɗaya zan miki ki mutu , cike da ɓacin rai nace tou ni yanzu waye kuma nayi ma vidio ,

Ƙanƙance idanuwa yayi yace Baban Mardiyya dama shine baƙin cikin da kike cewa zaki dasa mata a zuciya ? Ki bari bana so , nace tou , sake maimaitawa yayi cewa bana so ׳ idan kuma kuma kika sake zakiji babu daɗi , nace tou ,

Hararata yayi cikin salon so , yace to me kuma akayi miki kikayi kuka naga fuskarki duk sai a hankali , ban bashi ansa ba na canja maganar da tambayarshi wanda ya faɗa mishi nayi ma Baban Mardiyya vidio ? Cikin lallausar murya yace babu ruwanki da wanda ya faɗamin idan nace bana san abu kawai ki bari idan baki so mu ɓata , a ɗan zuciye nace tunda baza ka faɗamin ba bari in tafiyata , hannuna ya riƙo yace yi haƙuri An mata , tou faɗamin , yace ni bana san ɓacin ranki Al 'Ameen ne ya faɗamin , gaskiya An mata Al ' Ameen bai jitu dake ba kullum burinshi ya nemo aibunki ya faɗa a gidanmu duk da kince bakya so na ina so ki zama mai mutunci a idon "yan uwana da kuma iyayena kinga idan aka tashi bada labari cewa za'ayi ƙawar Dikko bata da hali mai kyau ni kuma kinga ai bazanji daɗi ba ko ? A kunyace nace Eh , yace tou da Allah ki baryin abu mara kyau duk ki barbaɗawa "yan baƙin ciki yaji a ido ya ƙarasa maganar yana kashe min ido ɗaya na dama , nace tou ,

Tada motar yayi yana cewa bari in ajiyeki haka nan kar ace kin ɓace , a dai² lokacin daya fara tafiya a hankali , yau da natsuwa yakeyin tuƙi yana ƙara jamin kunne na daina shiga sabgar kowa nayi rayuwata ni ɗaya idan banji bari ba kuma zanji hoho a jikina , a ƙofar gida ya ajiyeni yana cemin idan Allah ya kaimu gobe zai dawo , nace tou Allah ya kaimu ya kuma hutar da gajiya , ya ansa da amin ni kuma nayi cikin gida da gudu , murmushi yayi ya wuce cikin farin ciki ,

Yau zuciyarshi ta ƙara tabbatar mishi da akwai soyayyar shi a zuciyar An mata tunda har tasan idan ya daɗe bai zo ba idan yazo zata zo da gudu ta rumgume shi , kuma yace ko tana so ya dawo tace Eh , babu abinda ya kawo haka idan ba soyayya ba , yau kam yana cikin farin ciki.

Washe gari sai 9:30am na fita daga gida domin zuwa wurin jana'izar Aunty Mamy dan naji ance 10:00am za'ayi mata sallah domin kaita gidanta na gaskiya , doguwar hijabi nasa mai hannu ta saukar min har ƙasa mai ruwan jinin kare , dake ina da haske sosai sai hijabin ta matuƙar martabamin fuskata , babu abinda na shafa domin yau ranar ta jimami ce , makullin mota na ɗauka nayi gaba abuna ,

Ina fita naga su Amisty suma sunsha nasu hijaben cikin mota suna tahowa , ganin zan shiga gidan dokuna yasa Amisty tayi parking dan ganin abinda zanyi , a natse na shiga da jakata a hannuna saboda riƙon wayoyin zaimin yawa a hannu ,

A gidan na iske Dikko da kayan training jikinshi ya cire takalma rufaffi ya jiye a gefenshi ya naɗe kafafuwan wandonshi , silifas ne a ƙafarshi ɗorowo { Yellow } masha Allah shine abinda na furta lokacin da na kalli ƙafarshi , hutu dajin daɗi ya tabbata a gareta har wani hurhurun haske takeyi tsabar tasha madara ta ƙoshi "yar gayun ƙafa da ko mai ba'a shafa mata sabar hutawa , ga wani gargasa ya sauko saman ƙwaurinshi "yan yatsunshi masu kyau dan dani keda ƙafafuwan shi babu abinda zaijamin saka wasu takalmi idan ba irin silifas in daya saka a ƙafarshi ba domin yafa burge ,

Yana gani na ya tashi tsaye ya tare da ɗauko takalman daya ajiye a gefenshi ya tun karo inda nake yana cewa ina zaki tunda asuba haka ? Nace rasuwa akayi , Allahu Akbar Allah Allah ya sawaƙe , nace ba rashin lafiya ba mutuwa , yace Ey ai na sani ina nema ma ahalin gawar sauƙi ne , Allah ya kiyaye hanya nace amin , biyoni yayi bai sake magana ba shima ya nufi wurin motarshi ya buɗe but in mota ya watsa takalman ya rufe ya shiga motarshi nima na shiga wacce ya bani wanda yau itace ranar farko da zan fita da ita ,

Tasha wanki tayi kalar ɗaukar hankali , saida na shiga harna sauko daga inda na ajiyeta shima ya sauko yana cewa mintuna 15 na baki ki dawo , tsayawa nayi nace ya kuma minti 15 sai kace kai ka aikeni ? Ban aikeki ba amma wallahi kika wuce lokacin da nace saina ɓata miki rai za'a faɗamin lokacin da kika dawo ai , haba wai mi yasa kake yin haka ne ? Ki wuce lokacin da nace miki sai kiga dalili , cikin hayani nace aure na kakeyi da zaka tsaramin yadda zanyi rayuwata ne ?

Murmushi yayi ba tare daya kalleni ba yace ai da ina aurenki babu abinda zaisa na barki kije gaisuwar wacce aka kwakwale ma ido tirr ya ɓata baki tare da ficewa ya barni cikin mota kamar sakarai.

Da sauri na kalli agogo naga 10:19am , kenan zan dawo gida 10:34 ? Gashi kuma har naci minti 1 , ina da sauran minti 14 yaushe naje har nayi musu ta'aziyya na dawo ? Tsoki nayi kamar kar naje wata zuciyar tace kije kawai kina ɓata lokaci ,

Da gudu na fito daga gidan kamar zan tashi sama , su Amisty suka rufowa motar baya dan a tunaninsu Dikko ne a ciki , lokacin da suka fito bakin titi tuni na ɓace musu ko ƙurata basa gani , hanyar da motar tabi ta wuce suka gaza gano ta ina motar tabi ta wuce ,

Da nasan haka hawan motar nan zai jawomin tashin hankali wallahi da ban hauta ba , ni kuma na hauta ne kawai dan Dikko yayi farin ciki saboda tayi wata huɗu da "yan kwanaki da bani ita amma ban taɓa hawanta na fita sai yau ,

Ina isa ƙofar soro har an dawo daga kai Mamy dandazon mutane kamar ƙasa gaskiya Mamy tayi jama'a a hankali na shiga mutane suka riƙa darewa suna bani hanya duk wanda ya kauce saiya bi motar da kallo kowa ya ƙagara yaga Dikko ya fito dan nace muku lokacin daya siyo motar anyi ihunta a gari duk garin katsina wannan motar Dikko kaɗai keda ita ,

Daga Qerau zuwa ƙofar soro minti biyu kacal ya kaini shima dan nabi a hankali dan motar tana da tafiya sosai , nabar gida 10:20 , na iso ƙofar soro 10:22 harda parking da nayi , manyan mutane suka fara yayyaɓe motar dan cikawa Dikko sheda ba'a iya gane waye a motar saboda gilashin motar duhu gareshi , wa za'a gani ta fito daga motar ? Ɗiyar ɗan caca ,

Tunda na fito kallo ya koma sama a dai² lokacin dasu Amisty suka iso , banbi takan kowa ba na ɗauki jakata na wuce jama'a suka bini da kallo yayin da surutu ya fara tashi ƙasa² danni taron mutane baya hanani tafiya kuma bai ruɗani bai firgitani haka kuma yawansu basa gigitani kuma banayin tafiya inji kamar zan harɗe na faɗi ,saida nakai gaf da zan shiga gidan Mamy naga Bello , kallona yayi ƙasa da sama yace wai Sultana ce haka bakya ko gane mutane ? Murmushi nayi tare da cewa ya za'ayi lafiya ta kasa gane mai bata damuwa ? Magana ce na faɗa masa ina faɗin haka na shige abuna na barshi da dogon nazari ,

Gidan mutuwar sai koke ² akeyi yayin da tabarmin zamar gaisuwar suka rarraba kashi ² , dangin Mamy da tasu , sai dangin mijinta makota sai kuma wasu lafiyayun karuwai suma sunyi nasu mazauni , ahalinta na farawa ta'aziyya sannan "ya "yanta , sai dangin mijinta , ko inda karuwan suke ban kalla na miƙe zan fita wata mata tacemin nan zaki zauna ke ?

A dai² lokacin dasu Amisty suka shigo gidan , miƙewa nayi banyi mata magana ba , tace ke Sultana take ko wa ? Ta tambaya , aka ce mata Sultana , tace nan ne mazaunin mu , juyawa nayi da niyar feƙe mata uwa saidai banda isashshen lokaci dan ina so nayiwa mijin Mamy ta'aziyya , ina ƙoƙarin fita matar ta biyoni ta cakumoni ta baya tana cewa akace ina zakije ? Baki ga inda karuwai suke zaman gaisuwar su ba ? Ban mata magana ba na fiddo wayata daga cikin jakata nace ki duba zaki ga an rubuta Sultana itace lambar wayata ,

Kallona tayi sosai kuma kome tayi tunani Oho sai ta sakarmin hijabi ba tare data anshi wayar ba , ɗan gajeren murmushi nayi da gefen bakina na juya na fito ba tare dana sake mata magana ba , a ƙofar gida nayi ma mijin Mamy ta'aziyya da "ya "yanta maza Bello kuma sai kallona yake , murmushi nayi mishi na miƙe shima ban mishi magana ba ,

Tunda na fito daga barandar ƙofar gidan Mamy ake nunani nice nazo a motar Dikko , wasu kuma na cewa ni karuwa ce amma meya haɗashi dani bayan baya harkar mata , wasu kuma na cewa ɗiyar ɗan cacar nan ne shege mashayin giya ya haifo wannan kyakkyawar , wani yace ai yarinyar shegiya ce tana burgeni domin tanayin karuwancin cikin tako ne , kowa dai da abinda yake faɗa akaina abundai babu daɗin saurare ,

Murmushi mai ciwo nayi yayin dana tunkari mota ta , wato shi karuwanci babban tambari ne da baya gogewa har "ya "ya da jikoki kayi ƙoƙari ka zama na gari domin gori akan karuwanci ciwo gareshi yau mutane da sun san zasu taɓani su kwana lafiya inajin dasai sunci ubana kafin na fito , mota na shiga na karce duk wanda bai ga zuwa na saida yaga fita ta ,

Wuta ² na iso anguwarmu , a ƙofar gida naga motar shi , lokacin 10:33am kai tsaye inda na ɗauko motar na maida ta , lokacin dana fito ban sameshi ba kenan yazo da kanshi yaga lokacin da zan dawo ? Da sauri na wuce cikin gida dan inada abinda zanyi ,

Wuri ɗaya naje da mota amma yau gari magana ta kawai akeyi wata karuwa take tare da ɗan gwamna ta gama dashi ta tsafeshi har ya bata motar daya siyo ta miliyoyin kuɗi , duk inda ka saƙa a gari Sultana ɗiyar ɗan caca kafin wani lokaci kuma hotuna na sun fara yawo a social media da motar dana hau ɗiyar ɗan cacan da yafi ko wane ɗan caca sa'ar rayuwa ,

Al ' Ameen kuwa tuni yaje ya samu mahaifiyar Dikko ya faɗa mata halin da ake ciki dan yaga Dady yayi sanyi , Momy kuwa tayi zafi har ta wuce tafasashshen ruwa , matar Dikko data zo gaisheta itama ta cika ta kawo wuya , tace ma Al ' Ameen ya bari Dikko ya tafi a kamo Sultana zata ƙagi azabar da zata bata , Al ' Ameen yace ai ko yanzu ina iya kawota , Momy tace kudai bari yabar katsina dan koni baya so kamar yadda yake san mayyar yarinyar nan ,

Wane dalili yasa Dikko ya matsamin nahau motar daya bani yau ? Tabbas dan yasan za'ayi magana ne kuma haka yake so dama kowa yasan ina tare dashi shima yana tare dani dan idan babu wata alaƙa dani dashi mai girma me zai haɗani da motar shi.... ?

Yau kuma idan akwai wanda yafi *Jiddah* baƙin ciki bai wuce Momy ba kuma sun tanadin shaglin partyn wulaƙanta ni , Jiddah bata ƙara jin takaici ba saidai Dikko ya tura Ashiru ya maida ita gida , tace bata komawa , koda Ashiru ya faɗawa Dikko tace bata komawa cewa yayi ya barta idan ta gaji ta koma da kanta ,

Tunda naje gidan rasuwa ban sake komawa Dikko ya hanani , sai yau sadakar 3 yace inje amma yau mintuna 10 ya bani , Umar ya aiko ya kawomin kuÉ—i in bada sadaka idan naje , kuma har yanzu yana gari bai tafi ba saboda kullum rana muna tare ,

Ina ta shiri zan fita saiga Ummu Affan wai tazo min gaisuwa , bayan ta gama ta'aziyyar tacemin ashe kuma sai kikayi mota ? Murmushi nayi ban bata ansa ba naci gaba huÉ—É—ar gabana kenan ba gaisuwar ta kawota ba dan kawai taji labarin mota , saida na gama shirina kaf nace tou zan rufe É—akin , tace tou bari in tafi idan kika dawo na dawo , fita tayi nima na fita na rufe É—akin .

Ina fita naga Baba zaune a tsakar gida duk yayi wani kalar ban tausayi , nace Baba baka lafiya ne ? Kallona yayi yace wallahi Mamana gabana keta faɗuwa , nace miya faru ne ? Yace nidai nayi miki alƙawari nabar caca har abadan duniya nace Eh Baba , yace tun daga ranar da mukayi maganar dake da na saka motarki a caca wallahi ban sake zuwa koda wurin caca ba haka duk abokai na bana tare dasu tun ranar ban sake shan giya ba haka kuma ban sake neman mata ba ,

Nace to yanzu meya faru ne ? Yace abun ya dameni ne tun ranar da nayi wannan maganar idan na kwanta bacci sai inga wani mutum tsaye a gabana yana cewa idan baka koma caca ba ajalinka ne zaici gaba da fuskantar ka , ka koma caca kaci gaba da neman mata kasha giya idan ba haka ba zamuyi maka kisan wulaƙanci domin zaka lalatamin duk wani tsari na ,

Shine nace bazan koma ba , jiya itace rana ta ƙarshe daya bani kuma yace yau idan banje gidan caca ba wallahi kasheni zaiyi , murmushi nayi nace Baba kenan wannan ai duk shirmen bacci ne , yace Mamana ba shirme bane da gaske ne dan har sunanki naji an kira a mafarkin yace shine ya toshe miki rayuwa wai ya rufe ƙwalwarki a bakin mataccen kwaɗo , dariya nayi sosai nace ji wani magana Babana ni na tafi saina dawo ,

Saida na fita daga anguwarmu zuciyata ta fara tabbatarmin da ba shirme bane , maganar Baba abin dubawa ce da tunani iri ² na isa gidan rayuwa , ban jima ba na fito bayan na basu kuɗin da Dikko ya bani duka ban rage komai ba ,

Jiki a sanyaye na dawo gida ban samu Baba ba , dan haka na shiga É—akina kaina sai juyawa yakeyi , wayata na É—auka na kira Dikko kaf na rattafa mishi abinda Babana ya faÉ—amin , yace baya nan yaje kano amma idan yayi magrib zai taho in Allah ya yadda , nace tou don Allah daka dawo kazo wurina , yace insha Allah An mata ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru sai alkairi , nace tom saida ya kwantarmin da hankalina sannan ya kashe wayar ,

Ina gama waya da Dikko wayar Mamy ta fara kuka , da sauri na ɗauki wayar ba tare dana san mai kirana ba , ina ɗauka nace Hello , mai magana a waya tace Mamy na samu duk bayanan da kike buƙata , kila bata san Aunty Mamy ta rasu ba , akwai wani kwaɗɗo da aka rufe gawarshi a kwalbar lemu kuma gawar kwaɗon saida aka zuba kwata a cikinta , akwai bokan dake gyara aikin kullum amma yace abu ya warware komai zai iya faruwa tunda har Binna ya fita a caca ,

Anyi ƙoƙarin juya al'ƙamin tsafi ya sauka akan yarinyar da kike magana bokan yace sai ta tsallake sallar isha'e da asuba idan har batayi su ba tana dai cikin tsarki ba jinin al'ada ba itace zata maye gurbin ubanta , yarinyar tana da addu'a gaskiya kuma bata wasa da sallah , kiyi sauri yanzun nan suka kira Binna zasu kashe shi.... Kwalbar da akayi asiri gata a hannuna , amma kiyi gaggawar zuwa gidan........ Ihun matar naji ina ta hello ׳ amma cikin wahaltacciyar murya tace kiyi gaggawa zuwa bayan gidan caca acan za'a kashe Binna ni kuma zanci da sauran....

A firgice na fara kiran wayar Dikko amma sai akacemin a kashe take , wayar Babana na fara kira sai ringing take amma ba 'a ɗauka , wayyoni Allahna na sake faɗawa wata rayuwar , me yasa Dikko ya kashe wayarshi ? Su waye suka kirashi ya fita ? Me akayi ma wacce nake magana da ita a waya ? Wayyo Allahna rayuwa me yasa zakiyimin haka ne .....⁉ 😭

06/10/2019

*JAMILA MUSA...* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 51

*_Godiya ta mussaman gareku ma'abota mutunci da mutunwa , ngode ׳ ina godiya sosai wanda idan nace zanyi ta rubuta ngode ² sai cajin wayana ya ƙare ban gama rubuta godiyar ba ,_*

*_Hassan 80k_*
*_Hassana Masko_*
*_Hafsat Sa'idu Galadima_*
*_Muhammad Musa Muhammad { Na Allah... }_*
*_Halimatu Musa { Uwa }_*

*_Gaba ɗayan shafin nan na yau sadaukar wane ga masoyana a duk inda kuke a faɗin duniyar nan ina sanku ina ƙaunarku kuma ina alfahari daku , fatan alkairi a gareku_*

*_Kuma na gaishe ku..._*

*_Abdulrahman & Ja'afar , Allah ya tabbatar da farin ciki da kwanciyar hankali a gareku ubangiji ya jiƙanku yasa ku gama da duniya lafiya , Am3n_*

Juyawa ɗakin yakeyi dani kamar anayin hajijiya dani , wayyo Allahna ina zan dosa ? Mi zanyi ? Ya Allah ka kawomin mafita ka tausayawa rayuwata kuma ka tabbatarmin da alkairin ka , banda zaɓi sai naka banda wurin gudu ko tsira sai yadda kayi dani ya ubangiji al'arshi taimakon ka nake nema bana san taimakon kowa sai naka , duk abinda ya faru da Babana dani haka yazo a rubuce kuma babu wanda ya isa ya goge,

Da gudu na fito daga cikin ɗaki ina cewa yaku taron "yan uwana kuzo kowa ya biyoni domin dai yau wata baƙuwar rayuwa tana tunkaro mu , ciwon ba nawa bane ni ɗaya , babu babba ba yaro ba matar Baba ba mace ba namiji yau tashin hankalin gaba ɗayan gidan ya tunkaro ku taho Baba yana buƙatar taimako !

Ina faɗin haka nayi gaba da gudu , namiji ɗaya ya biyoni shine babban yayanmu yana ke Sultana ina zaki ? Banda lokacin bashi ansa gudu nakeyi kamar taɓaɓɓiya shima da gudu ya biyoni ina fitowa bakin titi na samu napep nace muje , Yaya yana fitowa tuni mun tafi , shima dafe kai yayi tare da riƙe ƙugu , ganin hakan ba mafita bane yasa ya tari mai machine yace yabi mishi bayan napep inmu.

Muna isa tun kafin napep inmu ta tsaya na dire na tun kari inda nake hango mutanen da basu wuce su biyu ba , sunyi rami sun saka hannun takobi cikin ƙasa tsinin kuma yana sama , bayan sunyi wa Babana wani irin duka a kai ya tafi duniyar ɗimuwa jini sai bin jikinshi yakeyi , bana iya gane fuskar kowa a cikinsu saboda rufe take idanuwansu kaɗai ake gani ,

Mai napep yana ganin haka ya gudu babu shiri dan tsira da rayuwarshi yayin da ni kuma na tunkari wurin haiƙan ina cewa kai na rantse da Allah idan wani abu ya sameshi gaba ɗayanku sai tsinuwar Allah ta tabbata kanku , ku barshi me yayi muku ne ? Me rayuwar shi ta tsone muku ko kune kuka bashi aron lumfashi ne ? Ubangijin al'arshi shine ya bawa Babana aron numfashi kuma shine ya bashi lafiya ku ɗin nan banzaye da ku baku isa ku fitar da ransa ba sai Allah yaso ,

Dariya sukayi sosai tare da cewa tou Allahn ne yaso shi yasa ma ya kirashi kuma yanzu zai tafi domin ansa wannan kiran idan kina iyawa ki kamo ran ki dawo dashi cikin jikinshi , suka ƙarasa maganar tare da ɗauko Babana suka birkitashi saitin zuciyarshi suka ɗagashi sama suka dakoshi saman takobin da ƙarfi , sai kuma suka ɗagoshi suka juyashi yana kallon sama suka sake sokeshi...

Da gudu na isa wurin Babana na durƙusa saman guyawu na , nace Babana karka sake ka rufe idanuwanka babu abinda zai sameka kallarni gani nan nazo Mamanka Uwar masu gida jikina yana ƙyarma na fara ƙoƙarin ɗago Baba amma na ƙasa idan kuma nace zan juyoshi ina tunanin inda bai yanku ba ma zai yanku ,

Babu abinda ke ɗiga daga cikin idanuwan shi sai hawaye yana lunshe ido nace kar kayi bacci ka rufamin asiri karka rufe ido idan ka rufe ido tawa ta ƙare , waye ? Waye wai waye mutumin da kake gani a baccin ka ? Waye ya kiraka wurin nan ? Karfa ka rufe ido yi murmushi yimin murmushi Babana , dakel ya ɗago idonshi ya kalleni cike da soyayya sannan yayi murmushi da gefen bakinshi la'elaha illallah muhammadur rasulillah ya ƙarasa tare da rufe idanuwanshi , nice na ida da S. A. W ,

Kai........ Na shiga 3 na bani na lalace wayyoni Allahna wayyo rayuwa ina zan sa kaina , nace kar kayi bacci shine kayi bacci me yasa ? Me yasa kayimin haka haba Babana , shine zaka tafi ka barni ? Bayan kamin alƙawari baza ka tafi ka barni ba , shine ka tafi ka barni ? Ya ubangiji ka farkar dani wannan mafarki ka tausayamin badan halina ba dan darajar manzan tsira kasa bacci nakeyi ,

Isowar Yayana shima da gudu ya iso wurin cikin tashin hankali yaga Babanmu soke a saman takobi dan suna soke Baba suka gudu , shima wani irin ihu ya kurma hakan ya jawo hankalin jama'a , kafin kace me ? Wuri ya cika sai kuka nakeyi ina ƙarawa tare da cewa wai Allahna , wai Allahna , Allahu Akbar ,

Sauko Baba akayi daga saman takobin har yanzu murmushin da yayimin yana nan akan fuskarshi bai goge ba , kamar kace taso ya taso sai kayi tunanini bacci yakeyi , duk wanda yazo saiya haskashi saboda duhu yayi sosai , ganin ana ta kallemin Babana yasa na cire hijabina na lulluɓeshi a lokacin har Yayana yayi waya an kawo mota ,

Allah mai girma da ƙafafuwan shi yazo wurin nan amma gashi yanzu baya iya tafiya sai an ɗaukeshi , bayan an saka Baba a mota Yayana ya kamoni nima ya shigar dani duk muna zaune a baya yayin dana kwanta saman gawar Baba inaci gaba da kuka ,

Zuwan Mamy gidanmu na tuna ranar data zo ta samu Baba zaune a saman dakali tana bi bi biyyyy , murmushin da Baba yayi mata na tuno da alamar da yayi mata da ido , yau gashi daga Baba har Mamy duk basa cikin wannan duniyar , kai.... Wani irin ihu na sake kurmawa daga nan ban sake sanin abinda ya faru dani ba saidai na farko na ganni a ɗakina Dikko durƙushe a gabana idanuwan shi sunyi jajir Ashiru da Umar suna tsaye a bayanshi .

Tashi nayi cikin kuka na rungume Dikko nace me yasa ka kashe wayarka ? Kiyi haƙuri har yanzu wayar a kashe take banda caji , kauda maganar nayi da cewa kaga Babana ko ? Ranar da nayi faɗa dakai na dawo gida shine Baba yayi kuka yace Mamana shine kika tafi kika barni ? Ni na goge mishi hawaye da wannan hannun nawa na nunama Dikko hannun naci ga da cewa nace masa ai na dawo ,

Nace Baba kana tunanin zan tafi na barka ne ? Bayan bana iya rayuwa saida kai ! Dare da rana safe da yamma yanayin farin ciki ko damuwa halin yunwa ko ƙoshi babu kowa a zuciyata sai kai , farin ciki ya dawo rayuwar ƙunci da damuwa zata kama gabanta , cikin kuka nace shine ya tafi ya barni , ni in rayuwar ƙunci da ɓakin ciki wayyo Allahna , wai Allahna.....?

Inajina kamar inayin rayuwar da bana cikin sahun mutane yayin da farin ciki yake tunkaro rayuwata sai mutuwa tazo ta shafe wannan farin ciki , duk wanda yazo da niyar ya taimakeni sai a shafe labarinshi a duniya , bana so ka rasa rayuwarka ka tafi daga rayuwata kada kaima su kashe ka....

Juyawa Dikko yayi yace ma Ashiru ku jirani waje , fita sukayi , Dikko ya ɓanɓareni daga jikinshi ya zauna kusa dani yace ina Mamanki ne ? Cikin kuka nace ta gudu tabar rayuwata banma san ita ko "yar gidan wane ahalin suka haifota ba , ni ɗaya nake rayuwata a wannan ɗakin babu ruwan kowa dani nima banda ruwa da kowa babu mai so na sai Allah banda wanda zai nunamin kyakkyawa ko mummuna duk rayuwar dana ɗauko ita nakeyin abuna gani yau na zama marainiya.....

Kallona Dikko yayi yace ke ba marainiya bace Allah yana tare dake kuma Dikko yana tare da rayuwarki , duk wanda kika ga ya mutu kwananshi ne ya ƙare ki daina mishi kuka kiyi mishi addu'a , nace to , Dikko yana gidanmu shi ya tayani zama a ɗakina yana min nasiha sai 1:39am yabar gidanmu ,

Bayan tafiyarshi ma na tuna banyi magib ba bare isha'e , fita nayi nai alwallah nazo nayi sallah nayi karatun al'qur ani mai girma tare da roƙawa Babana rahma a wurin ubangiji , har gari ya waye banyi bacci ba kuma banje ɗakin da aka kwantar da gawar Babana ba ,

Tunda safe gidanmu ya fara É—aukar mutane su Amisty da suka zo É—akina suka sauka , suna shigowa ni kuma na tattara wayoyina da tawa data Mamy na fita , É—akin da aka kwantar da gawar Baba na nufa , har anyi masa wanka an shiryashi yana kwance a mankara , ina tsuguniya abinda ya tunomin shine ,

Ranar da muna zaune dashi a ƙofar gida nace Babana ina sanka ina kuma tausayawa rayuwata ranar da za'a wayi gari babu ɗaya a cikinmu , murmushi yazo ya tsayamin a rai da maganarshi da yace min ai bazai tafi ya barni ba , a bayyane nayi magana cikin kuka nace shine ka tafi ka barni...

Naci gaba da kuka mai tada hankali , ina Allah ya jiƙanka ubangiji yasa ka huta , Allah yasa can yafiye maka nan Allah ya sadaka da mala'ekun rahma ubangiji ya kauda kai akan duk laifukan da kayi masa ya yafe ma ya gafarta maka ya baka aljanna dan arziƙin annabi muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wasallam....

Zainab ce ta riƙeni duk gidanmu Zainab tafi kowa tausayi na tana so na , tace Sultana kiyi shiru don Allah , cikin kuka na rungumeta nace don girman Allah ki tasheni daga baccin nan haka nan wallahi zuciyata ta kusa ɓarewa ,

Haƙuri kawai take bani , ina nan zaune a ƙasa kusa mankarar Baba sai kuka nakeyi , bayan wani lokaci kuma maganar Baba ta faɗomin a rai da yace idan har na mutu karki sake kimin kuka addu'a zakimin shine kaɗai zai tabbatarmin da soyayyar da kike min , shiru nayi naci gaba da gumji ina addu'a wa Babana ,

Misalin 08:50am gidanmu ya gama cika duk ta inda baka tunani , 09:00am aka ɗauki mankarar da Babana yake sama kwance za'a fita dashi domin salla tar gawarshi shi , shikenan Baba zai tafi inda bazan sake ganinshi ba bazan sake jin muryarshi ba har abadan abada duk soyayyar da yakemin ya tafi da gaske ya barni.... Sake ɗaukewa nayi na ƙara somewa !

Har akayi ma Baba sallah aka kaishi gidanshi na gaskiya Sultana bata san inda kanta yake ba , zata dawo² shiru har la'asar babu Sultana babu labarinta , duk wani taimako daya kamata ayi mata anyi amma har 5 na yamma bata dawo ba ,

Dan haka yasa Dikko yace a fito da ita a kaita asibiti , Zainab ce akan Sultana sai firfita take mata dama itace ta kula da ita a asibiti lokacin da Dikko ya farke mata mutuntakarta , da taimakon wasu matan aka fitar da Sultana aka sakata a mota da Zainab kaɗai aka tafi sai Ashiru dake tuƙi saishi Dikkon.

Asibiti mai kyau aka kai Sultana likitoci suka rufa akanta dan ceto rayuwata , amma duk yadda akayi saida Sultana ta kwana huɗu bata cikin hayyacinta , ga dai ido tana kallon kowa amma ƙiri² bata iya magana , bata ci bata sha sai kuka , hankalin Dikko idan yayi dubu ya tashi ya lallashi Sultana har ƙarfinshi ya ƙare amma Sultana taƙi tayi magana da kowa , da tsiya² Dikko ke bawa Sultana ruwan tea shima idan tasha saita amayar dashi ,

Zainab itace ta bawa Dikko shawara ko a riƙa ba Sultana fura duk tsiya dai ko tayi amai wata zata tsaya , Dikko yasa Ashiru ya samo fura ake ba Sultana amma ko tasha sai ta dawo da ita ,

Dikko yace haba An mata wai me yasa kikeyin haka ? Gaskiya banajin daɗin abinda kike yi ko nima so kikeyi in mutu shikenan sai ki huta ? Kiji tsoron Allah ki tausayawa rayuwata haka nan mana , ke shikenan abu baya wucewa wurinki ? Kina nufin ke Allah bazai jarabce ki ba ? Ko akanki ne aka fara rashin iyaye ? Ba'a fara a kanki ba , ba kuma za'a gama akanki ba , mutuwa tana nan tana zagayawa tsakanin rayuwar kowa kuma babu bararre a duniya duk wanda yazo sai ya koma , ina ilimin naki da kike alfahari kina dashi ? Wannan shine sakamakon da zaki sakawa rayuwa dashi ? Shi kukan mutuwa da kika ganshi ba'a gamashi kuma baya ƙarewa har sai ranar da rai ya ƙare kiyi haƙuri don Allah .

Murmushi Sultana tayi mai ciwo dan gani takeyi Dikko baima da hankali , ya za'ayi ta daina kukan rashin Babanta ? Ubanda ya ɗauki soyayya duniya ya ɗora mata , cikin "ya "ya sattin da wani abu itace kaɗai ya ɗauki duk soyayyarshi ya bata , taya ma zata manta Baba ? Taya zata daina kukan rashin shi ? Duk ma wanda yace tayi haƙuri ta daina kukan rashin shi wallahi mahaukaci ta ɗaukeshi ,

Banyi magana ba na sauko daga saman gadon na fice daga É—akin , Dikko ya biyo bayana yana ina kuma zaki ? Banza nayi dashi ban juya ba kuma bansan abinda ya sameni ba bana iya magana sai hawaye , da sauri ya iskoni yasha gabana ina zaki nace ? Kaucewa nayi daga inda ya tsaya na tun kari hanyar fita asibitin ,

Zainab ma tambayata takeyi ina zanje duk banza nayi dasu nayi wurin mota na tsaya dan gida nake so inje , murmushi Dikko yayi mai nuni da baya san abinda nakeyi amma bai sake magana ba ya buɗemin mota na shiga na zauna ya rufe itama Zainab shiga tayi Ashiru ma haka amma yanzu Dikko yaja motar rashin a matuƙar ɓace ,

Har muka iso ƙofar gida babu wanda yayi magana , bayan yayi parking Zainab ta fita nima na fita Dikko kuma bai mana magana ba yaja motarshi yabar anguwarmu ranshi a ɓace , jiki a mace na shiga gida Zainab tana bina baya har ɗakina dan "yan gidanmu sai sharholiya sukeyi yadda kukasan ba mutuwa akayi ba , wayoyina Zainab ta kawomin tare damin bankwana tace Allah ya ƙaddara saduwarmu ,

Taci gaba da cewa yau kwanan Baba 5 da rasuwa ke kuma kina asibiti tunda aka É—aga mankarar shi baki sake sanin abinda kikeyi ba , wannan gida naki ne babu maishi duk duniya saike tou a cikin kwanaki biyar da rasuwar Baba har sun siyar da gidan sun raba kuÉ—insu an bani nidai gaskiya ban ansa ba , kuma wanda ya sayi gidan yaba kowa daga yau zuwa gobe ya tashi .

Murmushi nayi tare da jinjinawa Zainab kai , ansar wayoyi na nayi ta fice ɗakin , tashi nayi na dudduba , kayana masu kyau da tsada duk an sacemin su kaf har kuɗaɗene gaba ɗaya an dauke su , tsoki nayi na fita nayi wanka na wanko bakina nazo nayi sallah magrib na gamesu da isha'e , ƙarfe 10 na dare kuma Dikko baiyi zuciya ba yazo ,

A saman dakali muka zauna , ya ƙaramin gaisuwa tare damin nasiha yacemin kuma idan Allah ya kaimu zaije Abuja kwana biyu zaiyi ya dawo idan ya dawo zai tafi dani , cikin kuka nace to kuma kayi haƙuri ɗazu da nayi maka shiru , jawoni yayi jikinshi cikin sigar rarrashi yace ba komai An mata ai kinsan bana iya zuciya dake ,

Murmushin ƙarfin hali nayi cikin shashshekar kuka nace Allah yasa kaima kar a kashe ka , yace shima da suka kashe shi sai kuma ya kauda maganar da cewa tunda har An mata tayi rashin lafiya nima banajin daɗi ,

Bai dai wani daɗe ba mukayi sallama dashi har mota na rakashi ya bani kuɗi masu yawa yace in ajiye mishi nace ni sata akemin yanzu , yace idan an sace ba komai idan baki da kuɗi na arami ki , nace nidai bana ajiyewa haba yi haƙuri ki ajiyemin , nace kuɗin sunyi yawa bazan iya ajiyewa ba , kallona yayi yace tou ibi wanda zaki iya ajiyemin , nidai ko ɗaya bana iya ajiyewa ,

Tou É—auka na baki duka , zaro ido nayi banma yi mishi magana ba na wuce da sauri gida , An mata zo , da Allah kizo kiji , ban dawo ba , murmushi Dikko yayi yaja motarshi ya tafi...

Jiya Dikko ya koma Abuja kuma munata waya dashi yana gayamin ya ƙagara gobe tayi ya dawo kuma yacemin yanzu idan zan koma makaranta Abuja zai tafi dani bazan sake makarantar kwana ba , yace shine zai riƙa kaini yana ɗaukoni wai sai muzo katsina juma'a da daddare mu riƙa komawa lahadi da daddare , bawan Allah shi kaɗai ke lissafin shi , haka dai ya ƙari surutunshi yamin saidai safe.

Muna gama waya da Dikko aka aiko kirana , dan haka na ajiye wayar na fita , Al ' Ameen na gani ƙofar gidanmu bayan mun gaisa yacemin mai gida yace nazo na ɗaukeki ki gano wani gida idan yayi miki yana so acan zaki koma da zama , murmushi nayi nace aiko yanzu muka gama waya dashi bai faɗamin zaka zo ba ,

Al ' Ameen yace nidai shine ya aiko ni , ni kuma nace tou bazanje ba na juya da niyar komawa gida , matan dake bayan mota suka fito kaca² muka fara kokowa har sukayi nasarar dannani a mota Al ' Ameen aja muka bar ƙofar gidanmu...

07/10/2019

*JAMILA MUSA....*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 52

Ina zamu je yanzu ? Al ' Ameen ya tambaya ? Muje gidana Momy tana can tana jiranmu , juya kan sitiyarin yayi muka kama hanyar gidan Dikko , babu wacce nayi ma magana a cikin su kuma banyi ta wani fizge² ba kawai na tsaya ne naga iya gudun ruwansu nasan dai bana kasuwa a wurinsu saidai su dakeni , murmushi nayi mai sauti tare da binsu dukansu da kallon rainin hankali ,

Jiddah harararki takeyi , wacce aka kira da Jiddah ta juyo tare da yankamin wani irin lafiyayen mari harsai da gefen bakina ya fashe , murmushi nayi cikin takaici nace wallahi kinyi sa'a rayuwa taimani duka amma da yanzu²n nan na kifar da motar nan kowa ya mutu , me nayi muku kuka shigo rayuwata a dai² lokacin da nake kukan mutuwar mahaifina ?

Ɗayar tace munafika ji tana nuna kamar bata san komai ba , idan kin manta bara a tuna miki , ai kinsan Dikko ko ? Wannan matarsa ce ta nuna Jiddah ke ɗin banza ɗiyar mashayin giya jikar matsafi ki haɗa ƙirji da mijin ɗiyar masu wankakken asali , da sauri na rufe idona amma kafin ta rufe bakinta tuni nakai mata kaina da ƙarfi hancinta ya fashe jini yaci gaba da kwarara , cikin tsananin ɓacin rai nace ita jakar da kike magana itace baƙuwar Dikko ,

Da tun farko kun faÉ—amin ko suwaye ku da ba'asha wahala ba , domin ido na a buÉ—e yake inga macen da zata kalli mai girma Dikko in tsiyaye mata kwayar idanuwa ke dan ganganci ma aurenshi kikayi ko ? Hmm hawan doki ba linzami muguwar kasada ne domin in baka faÉ—o ba kasha wahala , idan kin isa ki kira Dikko a waya na kirashi dani dake a ga wayar waye zai riga É—auka , matar sadaka dake ,

Gaba ɗayansu suka rufeni da duka a dai² lokacin da muka iso cikin harabar gidan , dukana suke tun daga cikin mota har waje suka jawoni , matar Dikko ta bugamin kai a jikin mota sai dukana sukeyi babu ji babu gani kamar an kama musulmin ɓarowa a chochie , murmushi nayi cikin wahaltuwa nace kinji haushi ko ? Nace miki matar sadaka !

Kiyi haƙuri mace ɗaya ce a zuciyar gwarzon namiji idan har akwaita to ba kowa bace nice , haka yake faɗamin kullum rana , kuma yacemin babu wata mace a duniya saini domin zuciyarshi da idanuwan basa ganin kowa saini , kunnen sa bayajin maganar kowa sai tawa ,

A dai² lokacin da Umar ya iso wurin yana ranki ya daɗe lafiya ya tambayi matar Dikko , sai kuma ya kalleni yace Sultana ya akayi kika zo nan ke kuma ? Goge hawayen baƙin ciki nayi sannan nacewa Umar Al ' Ameen ne yaje har gida ya ɗaukoni da ƙarfin tsiya , a gigice Umar ya kalli Al ' Ameen tare da zaro idanuwa yace da kanka ?

Wayarshi ya ciro daga aljihu yana wallahi saina faɗa mishi , ka kamo An mata da tsiya² ka rungumar mishi An matar shi ? Hmmm lallai akwai matsala dan nasan idan har naga mala'enka mutuwa tabbas nasan tafiya tazo wallahi yau babu abinda zai hana mai gida dawo katsina cikin daren nan ,

Jiddah tace ka kirashi ka faɗa mishi ni banajin tsoronshi , Umar yace yau zaki fara ji ki jirayi zuwanshi a dai² lokacin daya fara cewa ranka ya daɗe Al ' Ameen yaje har gida ya ɗauko Sultana kuma da ƙarfin tsiya ya jawota gata nan sai dukanta sukeyi kamar agola yaci zarafin ɗan masu gida !

Banji yadda Umar da Dikko suka ƙare ba suka jani mukayi ciki , a gaban mahaifiyar Dikko suka gurfanar dani tare da cewa Momy gata nan , kallona tayi sosai irin yanayin kallon da Dikko yakeyi irin kallon takeyi , itama dai kyakkyawa ce kamar buzuwa hutu ya tabbata ga kyakkyawar matar nan ,

Ɗan zamowa tayi daga cikin kujera tace yarinya ya sunan ki ? Ɗan kauda idona nayi dan bata girmanta nace suna na Sultana , meye tsakaninki da ɗa na ? Cikin ladabi nace babu , miye dalilin da yasa ya ɗauki mota ya baki ? Shiru nayi dan banda ansar bata , dake nake , nayi shiru , tace tou saurara kiji da farko zaki bada makullin motar nan aka kawomin shi , na biyu kuma ki fita daga harkar Dikko idan ma yana miki ƙarya yana sanki tou ƙarya yake miki baya sanki , ya faɗamin bakina da nashi yace halakar dake zaiyi da soyayyar shi ya kaiki ya baro ki , kuma tun yanzu ya kaiki ya dawo domin kin tafi kuma Dikko ya dawo , dama in banda baki da lissafi ya za'ayi a haɗa doki da jaki ? Siga ko a faɗar sunan ba iri ɗaya ne ba , ina ke ina zinari ? Matsayin Dikko ya wuce naki ki tuna idan kin manta , gidajen da kuke haya gaba ɗaya ya tattara ya siye ya mayar dasu gidan kiwon dokunan shi ,

"Yar talaka waye ya kaiki kiwon doki ? Jidda tace kuma ita ba jinin sarauta ba , Momy tace duk dinari sunanshi dinari akwai na talaka akwai na masu kuÉ—i wallahi Dikko babban zinari ne koda kuÉ—inka saida rabonka kuma ba'a saka irin kaÉ—É—ararshi a caca tsaftatacce ne shi baida sirki ba'a haÉ—ashi da komai ba ko goro baya ci bare yasha sigari ke ko naki uban kwalbewa yakeyi kuma saiya raba titi biyu tirrr da sanin zuri'ar da ubansu baya ciyar dasu ,

Tadai wulaƙanta ni sosai ta faɗi duk wasu sirrika na gidanmu abun dai babu daɗin ji , ta tozartamin Babana bawan Allah da yana can lahira duk a gaban Jiddah tayi min wannan wulaƙancin sannan ta rufe da cewa in tattara inbar garin katsina saboda jahar mijinta ne idan taji labarina kusa ² wallahi zata ɓatar dani , Al ' Ameen maida banza ka taho da makullin motar ɗana ,

Jiki a sanyaye na miƙe na kalli Al ' Ameen dake gefena nace mu haɗu gidanmu in baka , Momy tace ku haɗu a ina ? Ki bishi ku tafi tare , ko inda take ban kalla ba nayi gaba abuna yau banda inajin mutuwar Babana tana yagarmin zuciyata da babu abinda zai hanani na faɗawa matar nan miyagun kalamai masu zafi .

Da sauri na fita daga gidan zuciyata tana tafarfasa kamar zata zubo ƙasa saboda azabar zafi , nayi tafiya mai nisan gaske sannan na samu abin hawa , gashi banda ko sisi kuɗina an sace su duka , a ƙofar gidanmu na samu Al ' Ameen nacewa mai napep in ya jirani ina zuwa yace to ,

Gida na shiga na É—auko mukulin mota na bawa Al ' Ameen ya tafi , shi kuma mai napep nace masa kana san katifa ? Dan gidan babu kowa duk kowa ya kama gabanshi , mai napep yacemin hajiya siyarwa zakiyi ne ? Nace Eh idan na samu masu siya dan siyar idan ban samu ba sai na bayar kyauta tashi zamuyi ....

Dame ² zaki siyar ne ? Nace katifa labulaye sai gas sai tukunya ɗaya bokitin wanka da dai sauran tarkacenmu na mata idan kuma kana da kuɗi kawai ka bani dubu 3 ka kwashe duka , da sauri ya warwaro 3k ya bani , muka koma dashi gida har ledar tsakar ɗakin saida ya cire ganin katifar mai mutunci ce yace hajiya bara na ƙara miki ɗari biyar nace ngode ,

Yana cikin kwashe kayan wayar Mamy ta fara ringing da sauri na ɗauka cikin wahalalliyar murya tace Mamy mu haɗu dake general yanzu ² tafiya za'ayi dani gida a daren nan , wane ɗaki kike ne ? Emargency da kinzo ki kirani amma karki daɗe nace tou , a wurin nabar mai napep na fice daga anguwarmu ina mai cike da kewarta.

Napep nahau babu ɓata lokaci muka isa general a lokacin har an fiddo matar za'a sakata a mota ina kiranta ta ɗauka na faɗa mata na iso , tace ta ganni itace aka kamo in matso inda suke , da sauri na matsa wurin duk na gaishe su suka ansa tacemin ina Mamyn take ? Cike da damuwa nace mata Aunty ta rigamu gidan gaskiya , ni nice Sultana , salati matar tayi tare dayin kabbara tace tou Sultana shiga mota muje , nace tou babu wani wasi² ko kokonto na shiga mota ahalinta suka shiga muka fice daga asibitin bansan garin da zamu ba....

01:30am ihun Al ' Ameen ya karaɗe kaf ilahirin girman gidan gwamnati , a ɗakinshi ya farayi mishi wata irin azzalimar shaƙara bayan an ƙwaƙwale Al ' Ameen daga hannunshi dakel , shine Al ' Ameen in ya fito da gudu ya nufi inda zai haɗo da Dady dan yasan duk girman gidan nan babu wanda ya isa ya hana Dikko yayi mishi wani abu saishi , kuma duk Umar ne ya ƙara zuga Dikko yadda ya kamata kuma duk zagi dacin zarafin da akayiwa Sultana saida ya laɓe yaji kuma ya faɗawa Dikko , tsakanin Abuja da katsina ji yayi tayi mishi nisa yaci titi yadda ya kamata Allah dai kawai ya kawoshi katsina dan Ashiru ma baiyi tunanin zaizo katsina da rayuwa....

Ihu Al ' Ameen yakeyi a taimakeni zai kasheni yayin da Dikko ya koma mota cikin ɓacin rai yabi Al ' Ameen da gudu , na bani na lalace gefe² ya riƙe hayewa inda mota bata hawa amma hankalin Dikko ya fita daga jikinshi duk mai lumfashin dake gidan nan babba da yaro babu wanda bai fito , cikin tashin hankali Dady ya tunkari motar yana Babana meye haka kakeyi wai ?

Da gudu Al ' Ameen ya ɓoye a bayan Dady cikin tsananin ɓacin rai Dady yace meya haɗaka dashi ne ? Al ' Ameen yace babu abinda nayi mishi kawai ina ɗaki kwance yaje yaita dukana da ya gaji kuma shine ya shaƙeni ,

Dikko da aka fito daga mota dakel yace babu abinda kamin ko ? Dady yace Babana wai meke damunka ne ? Cikin tsananin ɓacin rai yace saifa na kasheshi matsalata kafin na gano kanamun munafinci ne amma da zaran na gano ka tou babu sauran amfaninka a duniya da ƙarfin bala'e zan shaƙeka saina kashe ka hankalina zai kwanta ,

Momy data iso yanzu tace ka kashe tunda kai mahaukaci ne , kamar jira yake tayi magana ya fizgo Al ' Ameen yayi mishi kyakkyawar shaƙa yana zaka sake shiga sabgata ? Ina makullin mota ta dan ubanka ? Dady yace sakarshi Babana ! Dikko yaci gaba da cewa tunda kake kaga ina shiga sabgar wani a gidan nan ne ? Ubanka ne ya bata motar ko ni ? Har kaine ka isa ka taɓa An mata ,

Saida Al ' Ameen yayi fitsari a wando saboda azaba kuma anyi a cire Dikko daga riƙon da yayi mishi an kasa , saida Dady yasa hannu aka ciroshi dakel bayan Al 'Ameen ya suma , wani irin ihu Dikko yayi mai tada hankali yayi wata irin jijjiga ya sake tattaka Al ' Ameen zaiyi magana lumfashin ya tsaya ,

Su Ashiru suka É—aukeshi aka shiga dashi ciki kamar yadda Dady ya bada umarni , cikin bedroom aka kai Dikko saman gado aka kwantar dashi , koda Momy ta shigo Dady cewa yayi ta fita baisan ganinta kuma wallahi idan bata fita harkar Baban shi da yarinyar nan da yake magana wani abu ya sameshi wannan Jiddah da kika matsa kika auro mishi wallahi saina sashi ya saketa , Dady yaci gaba da cewa ai nima ina da "yan uwa kuma suma suna da"ya "ya sai yaje ya auro yarinya mai É—a'a da tarbiyar.

Kullum kina gidan yarinya ke ko kunya bakyaji kin hana yarinya ta zauna É—akin mijinta kullum tana gidan surukai , tou kayi mata gori tazo ta kwana kuma ko Dikko baya aurenta nan gidan uwarta ne saita kwana kaje ka koreta tana can ta kwanta , tsoki Dady yayi mai nuni da bata da hankali ,

Nan yabar Momy tsaye ya ɗauko maganin Dikko ya zuba mishi a baki , da sauri ya buɗe idonshi maganar Umar taci gaba da dawo mishi wai Jiddah ta bugawa An mata kai a mota , ta daketa har ta fasa mata baki , kuma ka faɗawa Dikko saboda ni banajin tsoronshi , murmushi yayi ciwon mugunta ya tashi da sauri ya diro daga saman gadon ya fita Momy tabi bayanshi da sauri , kafin ta fito harya ɓace mata ya nufi part inta ,

Kwance ya samu Jiddah saman gado tayi ɗai² tana shan iskan A C bata da wata damuwa hankalinta kwance , ƙafarta ya riƙo ya jawota ƙiyyy a firgice ta buɗe idonta wayyo Allahna Yaya me nayi maka ? Dake da waye kuka je gidansu An mata ? A tsorace ta nuna mishi ƙanwarshi dake kwance gefenta tana bacci , kallon ƙanwar tashi yayi sannan ya sake kallon Jiddah yace bana dukanki amma ki tattara ki kama gabanki ki tafi gidan babanki babu wanda yaji babu wanda ya gani har sai na gano An mata ,

Idan baki tafi ba na rantse da Allah sakinki zanyi kuma saki na wulaƙaci da tozarci amma in kika haɗa ya nayi ² sai ki ɓace abinki babu wanda yaji babu wanda ya gani , idan wani ya kirani ya bani haƙuri zan sakeki ne , idan kika sake dawowa gidan nan ba tare da An mata ta dawo ba saki ne , idan har kika bari Momy taji ta zageni ko tamin faɗa saina sakeki ya ƙarasa maganar yana fizgo ƙanwarshi itama da sauri ta buɗe idonta wayyo Allahna na shiga 3 tasan haukan Dikko Yaya wallahi Momy ta aikeni itace tace naje , wani irin mari yayi mata saida ya bata kashin bala'e yace idan ta aikeki gobe sai kije ,

Kuma a gidan nan An mata zata dawo da zama idan akwai wanda ya isa saiya hanata zama na gani , wasu kwashe ² ma sunzo bare kuma matar ishashsshe , wallahi idan dai na ganta a daren nan saita kwana gidan kallon banza ko harara wani yayi mata saina makantashi har abadan duniya , Momy data shigo yanzu tace da Allah rufemin baki sakaran banza ka kawota gidan nan kaga yadda zanci mutuncinta a gaban idonka , baiba Momy ansa ba yace ma Jiddah kuma ki anso mata makullin motar ta kafin kiji babu daɗi ,

Momy tace makullin mota yana hannuna Jiddah zata riƙa hawa motar , taɓe baki Dikko yayi yace ba komai An mata dai ta hau ta bata kwance yana faɗin haka ya fita yaci gaba da kiran wayar An mata...

Dikko na fita Jiddah tace Momy idan Allah ya kaimu gobe zanje gida , Momy tace lafiya ? Jiddah tace tunda muka dawo daga america nake cewa zanje ² Allah bai bani ikon zuwa ba , Momy tace sai kuma cikin dare zaki faɗamin zaki ? Jiddah tace kiyi haƙuri Momy ai kwana biyu zanyi in dawo , Momy tace tou Allah ya kaimu , sun dai daɗe suna ɗan firarsu sannan kowa ya kwanta yayin da Jiddah tayi ƙudirin warware soyayyar Sultana daga zuciyar Dikko ,

Wurin Dady ya koma har yanzu yana kiran An mata amma taƙi ɗaukar waya ita ai dole tayi fushi , shi kuma bai daina kiranta ba , a gaban idona kiranshi yake shigowa kuma a gaban idona yake tsinkewa dukan kiraye ²n da yayi min ina ganin su,

Dan sai 10:58pm muka iso garin Daura , kuma tun muna hanya Dikko yake kiran wayata har yanzu kusan biyu da rabi yaƙi daina kirana , ni ɗaya ce kwance a ɗakin da aka bani gidan "yan gayu komai dai yaji bakin gwargwado matar da ta taho dani tace na kwanta da safe zamuyi magana ,

Hawaye ya cikamin ido tausayin Dikko ya kamani sosai dan abinda na lura idan za'a kwana a haka bazai daina kirana ba haƙura nayi na ɗauki wayar cikin kuka nace ka daina kirana mayaudari mai yaudararin kalamai , Dikko yace An mata wai mi yasa ke birkitaccen tunani gareki ne ? Kaine mai birkitaccen tunani ashe da kake cewa ka ƙagara gari ya waye kazo gareni duk yaudara ce , ka shirya munafircinka shine kasa aka wulaƙantani aka tozartani aka zage Babana da baisan irin rayuwar da nakeyi ba a halin yanzu , to na bar katsina sai ka zuba ruwa ƙasa kasha kuma daga nan gaba naci kada Allah yasa na sake ganinka ko a mafarki na , a haka dama kake tunanin zance ina tsanka ? Tou bana sanka na tsanake ׳ ,

Cikin hayani Dikko yace kada Allah yasa ki soni An mata idan baki so ni ba zan mutu ne ? Sai lallaɓaki nakeyi kin ɗaukeni kamar wani sakarai sai gagari nake tsakanin rayuwata da taki , baki saurarawa kiji abinda zan faɗa miki kije kiyi duk abinda kika ga dama idan kin tashi ma kibar Nigeria ƙarewar katsina nima kada Allah yasa na sake ganinki a barci na sai me , ƙaramar yarinya dake , sassauta murya yayi yace kiji tsoron Allah An mata domin ubangiji yana iya jarabtarki da irin soyayya da ya jarabeni da ita taki , me nayi miki haka kika tsaneni don Allah ? Haba An matana nasan kina san Dikkonki kuma kina tausayina kiyi haƙuri yanzu kina ina inzo ?

Fashewa nayi da kuka idan har nace bana san Dikko nayi ƙarya ina sanshi ׳ amma nasan babu yadda za'ayi gidansu su bari ya aureni saidai kawai mu dawwama muna soyayya , duk soyayyar da babu aure a cikinta ta zama shirme ni haka rayuwata zata ƙare tsanin sama da ƙasa ? Saina hau sai na sauko ? Me yasa zuciyata ta cuceni ta koyi soyayyar wanda tasan yafi ƙarfinta ,

A gajiye Dikko ya kwanta saman kujera 2siater yace inajinki kina ina ne ? Ina ina sai kuma nayi shiru , kina ina Nidai kayi haƙuri bazan faɗa ba , cikin sigar lallashi yace ai nasan zaki faɗa irin ɗan jan ajin nan ne na mata kuma duk a rasa wanda za'aja ma aji saini An mata ni ko bana iya ja miki aji wallahi saboda baida wani anfani inja miki aji ince na jawa wa aji ? Da kinsan yadda na ɗaukeki wallahi da baki fara tafiya kika barni ba , amma nasan kema wasa kike kina katsina ,

Ina katsina amma bana cikin katsina , yace ai na sani saboda wallahi inajinki kusa dani amma zaki ɓatamin rai a daren kuma dole sai kinyi saboda yarinta , baza ka sake samuna a waya ba , kuma baza ka sake gani na har abadan duniya ba , murmushi yayi tare da cewa ƙarya kikeyi , zaka gani shima yace kema zaki gani , yana faɗin haka na kashe wayata gaba ɗaya ,

Koda Dikko ya sake kiran wayar Sultana yaji ta kashe cikin ihu yace Dady ta kasheni , dan dama a gabanshi yake wayar , wallahi idan bata buÉ—e layin nan nima zan rufe rayuwata kowa ya huta ,

Cikin tashin hankali Dady ya dafe zuciyarshi yace Babana idan dai ka kasheni ka huta , shima Dikkon yace nima idan na mutu kowa ya huta wallahi idan bata buɗe wayar nan ba zan zama shafaffen a cikin "yan kwanakin nan , cike da iskanci ya sauko daga saman kujerar yana layi kamar yasha giya ya ƙoshi wurin firij ya nufa yana Allah kasa inyi kyakkyawan ƙarshe ashe iyakar ibar da nayo kenan ,

Da sauri Dady ya tashi ya nufi wurinshi a lokacin harya ɗauko ruwan sanyi ya fara sha hawaye na fita daga idonshi Dady ya riƙeshi yana cewa Babana wai miye kakeyi haka ne ? Ɗora rober ruwan yayi saman firij yace kaima ka fara jiyo ƙanshi mutuwar ne Dady ? Ka riƙe wannan daren domin zai riƙa ebe maka kewa idan bana raye , riƙeshi Dady yayi yana cewa baka dai so ka bar in zauna lafiya ko ? Dikko yace gangar jiki kaɗai ake tattali ba ruhin ba , idan akwai wani wanda ba'a so ya zauna lafiya to ba kowa bane nine ,

Wai me An mata tayi muku ne kuka tsane ta haka da yawa ? Naga shege ma mara uba ana aurenshi bare ita ba shegiya bace ba , kuma nasan namiji yana zuwa gidan karuwai ya auro mata ita a gidan wane karuwan take zaune ? Caca ² kowa saboda Babanta yayi caca sai ace bana aurenta ? Tou nima zan zama ɗan caca kuma na fara neman matan na sha giya shikenan sai ta zama matar mashayi , sassauta murya yayi cikin kuka yace na wahalar da An mata na bata azabar da duk lokacin dana tuna abinnan sai naji kunyar kaina....

Cike da damuwa Dady yace a , a Babana da hannu Dikko ya dakatar dashi bai sake magana ba ya É—auki robar ruwan daya fara sha ya matsa wurin kujera ya É—auki makullin motarshi ya fice , a lokacin har 3 na dare yayi , shida Ashiru suka fita daga gidan suka koma g r a gidan Dikko ,

Fitar Dikko Dady ya zauna ya zabga tagumi yana tunanin da bashida da gaira bare dalili ,

Ni kuma bayan na kashe waya na fashe da kuka nima wanda bansan dalilin yinshi ba , ji nake kamar in taho katsina in haɗu da Dikko zuciyata ta tabbatarmin cewa Dikko bazai taɓa wulaƙantani ba har abadan duniya , kwana nayi ina kuka kafin gari ya waye fuskata tayi jajir saboda kuka , idanuwana sun kumbara saboda rashin bacci , ko kalaci kasa cin komai nayi ina ta tunanin Dikko ,

Kwance yake yayi ruf da ciki ya kifa kanshi a katifa shi kaÉ—ai yasan masifar da yakeji , bayan wani lokaci kuma ya juyo shima dai yaji masifar so yayi kuka har ya gode Allah , shi mamakin da yakeyi duk girmanshi a shekarunshi wai yake ma mace kuka , macen ma "yar ficiciyar yarinya wahalallen murmushi yayi mai ciwo a bayyane yace An mata baki da adalci kanki kaÉ—ai kika sani , kema Allah sai kamaki bazai barki ki huta ba tunda kika hana marawuta zaman lafiya ,

A hankali ya lumshe idanuwan shi ya fara tunanin tun farkon haɗuwar shi da An mata , da abinda yayi mata da gishirin daya zuba mata ya korashi da ruwa , wayyo Allahna me yasa nayi haka ? A lokacin ina hankalina ya tafi ? Ina tunani na ? Dama baya zata dawo dana gyara wannan kuskuren wayyo Allahna , me yasa ² ? Wai me yasa sai nine aka zaɓa ? Wai wane hauka ya kani ? Kai An mata me ya sa kin cika taurin kai haka da yawa insha Allah ubangiji bazai barki kimin wasa da rayuwa ba wallahi sai kin nemo Dikko ina nan ina jiranki bazan sake zuwa ko ina ba sai kin dawo kuma sai kin kirani nima bazan sake ɗaukar wayarki ba sai kinzo kin bani haƙuri , yafa san baya hanani kuma baya ɗaga murya shine yakeyi ,

Ashiru yace mai gida dan girman Allah kayi haƙuri , Dikko yace kai baka da hankali na cuci yarinyar nan babu wanda yasan abinda ke tsakani na da An mata daga ni sai ita sai Allah , murmushi yayi yace An mata manya duk duniya inba ita ba waya isa ya mari Dikko ya kwana lafiya sai ita ta ɗaga hannunta mai daraja ta zabgagamin mari kuma nace ina santa tace na tsanake Dikko inba Ubangiji ba waya isa yayi wannan tsarin ? Saishi ubangijin samman da ƙassai , a hayaniyance yace sai kin dawo wallahi........ Tari yayi yaci gaba da cewa kema Allah ya zargeki tunda na dawo daga america na gani sama lumfashin ya farayi , a wahalce yace kuma wallahi bazanyi shiru ba saina faɗa , riƙeshi Ashiru yayi cikin damuwa yace mai gida don Allah , idon Dikko cike da hawaye yace shitttttt🤫 ya karasa yana fiddo kyawawan idanuwanshi , Ashiru yace don Allah , cikin hayani yace kaimin shir bai ƙarasa faɗa ba lumfashin shi ya ɗage.

Ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe Al ' Ameen ya ɗauki Jiddah suka fara laluben hanyar kaduna ranta a ɓace amma babu yadda za'ayi ta faɗawa wani ayi ma Dikko magana kuma tasan wallahi kamar yadda yace zai saketa zai saketa addu'ar ta Allah yasa aga Sultana da wuri , kuma ko ta ƙarƙashin ƙasa saita shiga ta fita ta raba wannan tarayya...... Murmushi

Zaune nake a gaban matar da tazo dani , kwalbar data faɗin a waya ajiye a gefenta babu abinda ke cikinta sai tsutsotsi da wasu irin mahautan layu mataccen ƙwaɗon da Babana ya faɗa gashi ina kallo , gyara zama tayi tare da cewa jira Yayata tazo tacemin ta kusa isowa , cike da ladabi nace to Aunty , ji nake dama Dikko yana tare dani shima yaga abinda nake gani yana tayarmin da tsikar jiki........

08/10/2019

*JAMILA MUSA....*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 53

*_ƊAN MACE...! Sabon abinci yafi ɗumame daɗi 😋 na zaune makahon duniya , wasan kokowa bana gurgu bane hanzarta ki nemi naki karki sake ki bari a baki labari , tsohon hannu ce tuni ta shahara wannan marubiciya kuwa itace HAWWA MUH'D USMAN {{ real smasher }} ina tayaki murnar fara sabon littafinki ubangiji yasa yadda kika fara lafiya ki gama lafiya , Am3n..._*

Cikin tashin hankali Ashiru ya fara kiran wayar Momy dan ya sanar da ita halin da mai gidanshi yake ciki , koda ya faÉ—a mata cewa tayi ko nazo ba abinda zan mishi dan maganinshi yana hannunshi ka nema ka zuba mishi a bakinshi ,

Kallon Dikko yayi yace Hajiya wannan ba irin waccan ciwon bane ba , tsoki tayi tare da kashe wayarta tana masifa cewa ni mutuwarshi bata wani hanani nayi rayuwata dan wanda ya mutu shi jin daɗi ya ƙare mawa danni a halin yanzu banda wani abinda ya isa ya tashi hankali na , mijina kawai zai kwanta ya mutu in tashi hankali ba Dikko ba ,

Ƙanwar shi daya zane jiya tace Momy miye ? Cike da masifa tace Dikko ne kinsan shi idan bai ɓatawa mutane rai ba hankalinshi baya kwanciya ni yanzu bazai sake tayarmin da hankali ba saidai ya tada ma ubanshi danni na gaji da iskanci shi , tunda na haifi Dikko duniya ya hanani in zauna lafiya dan yaga bana so ya shiga damuwa shi yasa duk hanyar da yasan zaibi ya tadamin hankali yasanta ,

Meya sameshi yanzu kuma Momy ? Ta tambayi mahaifiyarta cikin damuwa , tashi Momy tayi daga palon tana cewa koma miya sameshi cansu ta dama ba abinda ya dameni , É—an uwa da É—an uwa sai Allah duk dukan da Dikko yayi mata jiya ta manta dashi ta É—auki wayarta ta fara kiranshi , Ashiru ya É—auka tace ina Yaya ? Ashiru yace baida lafiya ,

Bashi waya mana , cikin damuwa yace ai baya iya magana , kamar ya baya iya magana ne ? Tayi maganar cikin tsawa , shiru Ashiru yayi tare da kashe wayar , wayyo Yaya...... Momy Yaya fa baya magana kuma an faÉ—a miki zakice ba ruwanki ? Daga ciki Momy tace ba ruwan nawa ke mai ruwa sai kije kiyi.

Cike da tausayin ɗan uwanta ta fara kiran wayar Dady amma bai ɗauka ba ta kirashi yakai ×3 baya ɗauka kawai ta tura mishi text Yaya bashi lafiya !

Ashiru kuwa ya ɗako magani ya zuba² amma kamar ana zubashi a ƙasa Dikko ya ɗauke gaba ɗaya sai hawaye dake gangarowa daga gefen idonshi , cike da tausayi Ashiru yabi mai gidanshi da kallo yana tunanin tou wane irin sirrin ne yakeyi da Sultana da yace Allah kaɗai yasan tsakaninsu yace babu wanda yasan abinda ke tsakaninsu daga shi sai ita sai Allah , wannan wane irin sirri ne mai ƙarfi haka......?

A wannan hali Dady yazo ya samu Dikko , fuskarshi ɗauke da damuwa yace ma Ashiru ya koma palo , fita Ashirun yayi Dady yabi Dikko da kallo bayan wani lokaci ya saka hannunshi a aljihu ya ɗauko wani garin magani ya shaƙa mishi a hanci tari Dikko yai tayi yana atishawa , saida ya ɗauki wani lokaci yana tari da atishawa sannan ya dawo dai².

Cikin natsuwa Dady ya kalleshi yace Babana kana neman dai ka kasheni ko ? Ka hanani in zauna lafiya kullum jini na a saman akaifa ko wadataccen bacci bana samu kullum zuciyata a takure take banda walwala bare kwanciyar hankali wannan fitinar daka tsiro da ita ba kanka kake wahalarwa da ba , ni kake ba wahala duk duniya baka da jigon daya wuceni idan har ka bari wani abu ya sameni ko na mutu taka ta ƙare ,

Cike da ladabi yace kayi haƙuri na bari , Dady yace kai zan ba haƙuri , Dikko yace insha Allah bazan sake ba , Dady yace da ka taimaki rayuwata , saida ya tabbatar Dikko ya dawo hayyacin shi sosai ya tafi tare da jaddada mishi ya daina fushi da tunani tunda yasan baida cikakiyar lafiya , kuma yaje gida da daddare yana nemanshi , da kanshi yayi ma Dady rakiya har wurin mota saida ya tafi sannan ya dawo palo wurin Ashiru ya kwanta.

Ni kuma ɗaki na koma na cire wayata daga jirgi na fara kiran wayar Dikko , duk kiran da nake mishi yana gani yaƙi ɗauka dan yayi alƙawari cewa sai nazo da ƙafafuwana na sameshi idan dai ya furta zaiyi ko zai mutu saiya yayi , tun ina kiranshi yana basarwa ƙarshe sai ya riƙa rejecting , nima na daskare naci gaba da kiranshi bayan wani lokaci ma kashe wayarshi yayi gaba ɗaya ,

Murmushi nayi maicin rai a bayyane nace ni zaka wulaƙanta ina kiranka ka kashe min waya nima har abadan duniya bazan sake kiranka ba na ƙarasa maganar tare da maida wayata a jirgi.

Ranshi a ɓace ya kalli Ashiru yace zanyi tafiya zakaje ? Dariyar jin daɗi yayi tare da cewa mai gida zanje mana amma kace baza ka sake zuwa ko ina ba sai Sultana tazo , hmmm manta da An mata Dikko ya bashi ansa...

Saida na ƙara yin kuka sosai sannan na sake cire wayata daga jirgi na ƙara kiran Dikko , har yanzu wayar a kashe take ci gaba nayi da kira har matar da ake jiran zuwanta ta iso amma Yaya DK bai buɗa waya ba , yayi fushi dani yayi tafiyarshi London ya manta dani ,

Sultana ....! Aka kira suna na daga palo da sauri na tashi na fita ba tare dana ansa kiran ba , gaishe da matar nayi bayan na samu wuri na zauna , ansawa tayi cikin sakin fuska tace sannu baiwar Allah , murmushi nayi mai ciwo dan yanzu duk duniya banda damuwar da tafi rashin Dikko a tare dani...

Auntyn da tazo dani tace Yaya kinga kwalbar nan kallo É—aya tama kwalbar ta kauda idonta tare da neman tsari daga azaluman mutane a wurin ubangiji , abin babu kyan gani gwanin tashin zuciya da tashin hankali , Auntyn da tazo dani tace tare da ita za'a tafi ne ? Yayar ta tace a , a cewa yayi kawai na anso kwalbar na kai mishi , Aunty tace gata nan , kwalbar matar ta É—auka tare da cewa saina dawo zuwa jibin insha Allah , godiya Aunty tayi sosai wa "yar uwar ta , ita kuma ta tafi tana mai addu'a ubangiji ya yanke wahala.

A daddafe nayi kwana ukku , ga ciwon mutuwar mahaifina dake nuƙurƙusar min zuciya , ga maraicin Dikko dake damuna gashi banda abokin fira kuma gidan ba'a fita gashi ni ban saba da Auntyn da tazo dani ba , abubuwa dai duk sun dameni na rasa inda zan saka raina naji sanyi , duk alƙawarin da nayi bazan sake kiran Dikko ba na kasa kullum saina kirashi kuma har yanzu wayarshi ya rufeta.

Al' Ameen da yakai Jiddah ƙin dawowa yayi wai sai ranar da zata dawo zasu taho tare , haɗuwa sukayi sukaci gaba da gulmar Sultana yayin da Al ' Ameen ke cewa ai Sultana asiri tayi ma mai gida ta gama dashi danshi tunda yake duniya ma bai taɓa ganin mai gida yana shiga sabgar mace ba sai akan yarinyar nan , tayi mishi asiri na gani kasheni , idan dai kina san zaman lafiya ki miƙe tsaye ki fitsare ƙafafuwanki.

Jiddah tace aini bansan ta ina zan fara ba , Al ' Ameen yace ina da malami a zaria zan kaiki amma karki fara neman mai gida dan ɓannar kuɗinki zakiyi saboda yana da addu'a sosai , banda toshewar basira irin na Jiddah yanzun nan Al ' Ameen ya gaya mata cewa Sultana ta nemi Dikko da asiri fa , amma ita yace mata kar ta nemi Dikko da asiri wai ɓannar kuɗinta zatayi , yaci gaba da cewa saidai ita yarinyar a firgitata a saka mata shakkun mai gida a zuciyarta , idan ta ganshi tayi kamar taga cici , Jiddah tace tou haka yayi yaushe zamu je ?

Al ' Ameen yace bara inyi waya dashi saiya fitar mana lokaci da kanshi , Jiddah tace ngode Al ' Ameen da Allah ya haÉ—ani dakai da na shiga gararin rayuwa , tayi godiya sosai shima ya gode tare da fitowa daga palonta ,

Bayan ya fito yayi dariya yace sakarar banza zan kaiki malam yayi ta ɗirka miki asirin da ke da kanki zakice mai gida ya sakeki , ina ansar taimako ina kaiwa Mardiyya insha Allahu sai mai gidana ya auri Mardiyya zuri'armur zasu fita daban yarinyar "yar uwata ta samu sa'ar rayuwa , ita kuma Sultana zamu goge labarin mai gida daga zuciyarta , shi kuma mai gida soyayyar da yake ma Sultana sai a juya sunan Mardiyya a kan soyayyar da yake ma Sultana , sai ya koma san Mardiyya wannan shine mafita , Yeeee wannan shawara tayi , yayi "yar rawa tare da taɓawa cikin farin ciki.

*_London_*
Dakel ya juya kwanciyar shi cikin yanayin gajiya idanuwan shi a rufe , miƙa yayi sosai yace An mata , saida ya gyara kwanciya yace duk ki gama yarintarki da duk abinda kika ga dama insha Allahu duk duniya baki da miji saini , buɗe idonshi yayi a hankali yaci gaba da cewa ni wallahi tausayi kike bani dana tuno na tattara fushi na da ƙarfina na sauke a kanki sai tausayinki ya kamani , tsoki yayi tare da saukowa daga saman gado yana cewa banso ranar tazo a haka ba , amma ya na iya yadda ubangiji ya tsara kenan.

Toilet ya shiga bai wani daɗe ba ya wanko bakinshi da fuskarshi ya fito , Ashiru ne ya shigo cikin bedroom in ya miƙawa mai gidanshi waya wai Jiddah tana kira , ansa Dikko yayi ya kara wayar a kunnenshi tare da cewa inajinki ,

Cikin soyayya da gogewar kalamai tace haƙuri na kira in bada ranka ya daɗe , sai yanzu na gane nayi kuskure kishinka ne ya rufemin ido har na aikata abinda bakaji daɗi ba , amma ka gafarceni insha Allah haka bazai sake faruwa ba kayi haƙuri don Allah , waye ya faɗa miki bana nan ne ? Cike da ladabi tace Momy ta kira Hajiya tace kayi rashin lafiya , sai tace zata zo ta ganka shine Momy tace baka nan amma zata turo mata number ka ni kuma data turo saina ɗauka in bada haƙuri.

Ajiyar zuciya Dikko ya sauke shima cikin kulawa yace ba komai ya wuce , tou Yaya zan koma dan Allah , a , a , haba Yaya ka rufamin asiri don girman Allah ka barni na koma , Dikko yace keyy..... Jiddah tace Allah baka lafiya yasa kaffara ne , yayi kyau ya ƙarasa tare da kashe wayarshi.

Kallon Ashiru yayi bayan ya gama wayar ya nuna mishi hanyar fita da hannunshi , da sauri Ashiru ya fita shi kuma yaci gaba da tunanin An mata......

Kwance nake saman gado na ƙurawa wayata ido dan yanzu na cireta a jirgi kwata² ina tsammanin kiran Dikko ko wane lokaci , Yayar Aunty ce ta shigo dan sun daɗe suna kirana banji ba hankali ya tafi tunanin Dikko , dan na kalli hotonshi dake cikin wayar Aunty Mamy wanda Al ' Ameen yasa a d p inshi Aunty kuma ta ajiye hoton a ma'ajiyar hotunan cikin wayarta , nasha kuka har na gode Allah dan idan zan kalli hoton shi so goma sai nayi kuka sau adadin kallon da nake ma hoton.

Dafani tayi na dawo a firgice tare da goge hawayen idona ina sauke ajiyar zuciya , murmushi tayi mai haÉ—e da cewa sannu , nima murmushin nayi na sauko daga saman gadon na gaisheta , ansawa tayi cikin sakin fuska tace muje tayi gaba nabi bayanta ,

A palo , Auntyn da tazo dani ce a saman keken guragun ta , sai Yayar Aunty sai wani babban mutum yasha rawani zubinshi dai irin na malam zaure ne , duƙusawa nayi na gaishe su cikin ladabi , cike da kulawa ya ansa tare da cewa sannu baiwar Allah , nace yawwa,

Shi kuma yaci gaba da cewa cikin hukuncin ubangiji abinda ya faru shekaru da dama da suka wuce Allah ya bada iko cikin hukuncin sa da yaddarsa ya warwareshi , bamu yi ƙoƙarin bincike ba saidai nayi amfani da bayanin da Hajiya Suwaiba tayimin ya nuna Auntyn da tazo dani yaci gaba da cewa.

Hajiya Mamy kafin ta rasu tace duk musabbabin abinda ya janyo wannan rikici da tashin hankali da jefe² duk sanadin ɗaukar budurcin matar Bello ne wanda shi Binna yayi a matsayin ɗaukar fansar abinda akayi ma yarinyar da ya zauna gidansu ,

Wannan dalili yasa shi Bello ya ƙwallafi marigayi Binna a zuciyarshi wannan itace ƙiyayyar dake tsakaninsu , kafin haka kuwa abinda ya shigo da Bello a rayuwar Binna shi ɗan uwan Binna wanda suke Baba ɗaya shine ya turo Bello a rayuwar Binna bayan mahaifiyarshi ta haɗa tuggun da mahaifinshi ya korashi daga gida ,

Taga ya tafi bai lalace ba shine ta tashi hankali su kuma "ya "yanta suka taimaka mata wurin ganin sun cika mata muradin ta na ganin Binna ya lalace dashi da ɗan uwanshi kuma babu abinda sukayi mata haka kuma mahaifiyarsu Binna batayi mata komai ba , da sukaji labari su Binna sun samu gidan aiki da ake kula dasu , shine suka nemi hanyar lalatashi wannan dalilin yasa suka tura Bello ya shigo rayuwarshi ya shanmace shi da sihiri ya samu damar afkashi a wasan caca kuma suka fidda ma Binna tunanin waiwayar gida , ana cikin haka ne kuma Bello ya lalatawa yarinyar gidan dashi Binna yake zaune rayuwa sai aka korasu , Bello kuma yajasu suka zama suna ƙarƙashin ikonshi har Allah yasa shi Bello yayi aure Binna ya ɗauki budurcin matarshi a daren ranar da ango zai shiga ɗaki.

Daga nan sukayi faɗa na tashin hankali suka rabu , bayan rabuwarsu ne "yan uwan Binna suka tura Bello akan kar ya sake ya yadda ya nemi Binna ya bashi haƙuri idan ya dawo rayuwarshi shima ya ɗauki fansa akan kaff ahalinshi ,

Haka yabi kaf ahalin Binna yaci gaba da jifarsu , amma saiya lura hankalin Binna baya kansu bai kuma damu da lalacewarsu ba , yaci gaba dai bai daina ba har Allah ya kawoki kuma mahaifinki ya ci buri akanki kuma yaso kiyi ilimi mai zurfi ganin Binna dai ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗora miki yasa Bello ya juya akalar tsafinsa akanki shine yaje yayi wannan tsibbacin nasa wanda kuma ubangiji ya kawo ƙarshenshi da izininshi da yaddarshi kuma an warwareshi , ga magunguna nan Hajiya zata faɗa miki yadda zakiyi amfani dasu.

Gyara zama nayi na kalli Hajiya Suwaiba nace Aunty da kika kirani kince an tafi a kashe Babana su waye suka tafi kashe shi ? Kuma ke me kikeyi a wurin lokacin da kikemin waya me yasa kikayi ihu bayan ke kuma na ganki baki da ƙafafuwa ya akayi kika je wurin..........?

Cike da damuwa tace bani bace kikayi waya dani , yadda kika ga wannan kwalba da wannan waya da na kiraki da ita ina kwance a saman gadon asibiti Allah ya kawo min matar da kikayi waya da ita batamin bayanin komai ba tadai bani wayarta tacemin amana ce aka bata kuma itama ta bani amana , tabbas tamin maganar Mamy idan baki manta ba da kika zo asibiti ai kinji nace miki ina Mamyn take ? Bansan Mamy ba amma matar ta nunamin hoton Mamy a cikin wayarta ,

Wannan bawan Allah kuma da kike gani itace tace in duba cikin wayar ta zanga lamba an rubuta malam ɗayyu inyi ƙoƙari na nemeshi shine zai kawo karshen matsalarki domin tamishi bayanin komai , ni banda ƙafafuwa shi yasa na kira "yar uwata bayan ni nayi waya dashi malam ɗayyu ya faɗa mana mazauninshi shine na tura Yayata takai mishi kwalbar ,

Idona cike da hawaye nace shin ina ita matar data baki wayarta da kwalbar nan take ? Aunty Suwaiba tace bansan inda take ba domin tana saƙamin a cikin bargon da nake lulluɓe dashi naga wasu mutane sun shigo suna nemanta ita kuma tabi ta wata hanya ta fice , ba'a sallameni ba gudun bi baya yasa nima na baro asibitin dan bana san rayuwata ta sake komawa cikin matsala.

Kai ׳ innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , Allah ngode maka ubangiji ya bayyani min duk masumin wannan bita da ƙulli , an kashe Aunty Mamy , an kashe Babana ita kuma wannan tana raye ko tana mace oho ? Ya zamar min dole nabar gidan baiwar Allah nan da bata san sake mayar da rayuwata a damuwa ita kuma meya faru da nata rayuwar ?

Kallon malam ɗayyu nayi tare da cewa shin ko kasan inda gidansu Babana yake ne ? Yace yasan gidan a katsina yake ƙofar marusa , nace kai a wane gari kake ne ? Yace katsina yake , miƙewa nayi tsaye tare dayi ma Aunty Suwaiba godiya na koma ciki na tattaro wayoyina ina dawowa palo nace ma malam ɗayyu muje katsina.

Miƙewa yayi tare da tattara magungunan daya zo min dasu yayi gaba , ni kuma na duƙa a gaban keken guragun ta nace Aunty ngode sosai zan tafi amma zan dawo domin ina sha'awar jin wace irin rayuwa ce kikayi ta baya wacce har baki so ki sake komawa cikinta , miƙewa nayi tare dayi ma Yayarta sallama na fice daga palon ina kewar mutanen kirki irinsu Aunty Suwaiba amma tabbas akwai dawowa bayan kowa ya ajiyewa kowa lambarshi a cikin wayarshi......

Ƙarfe 7:43pm acikin garin katsina tayi mana wanda malam ɗayyu shine ya jawo motar tun daga daura har zuwa cikin birnin garin katsina , kai tsaye ƙofar gidan su Babana muka tsaya , ina ƙoƙarin fita daga motar naga Baban Hafsa ya fito , kallonshi nayi sosai yayin da Bello ke biye bayanshi , kallon malam ɗayyu nayi nace lallai² nan gidansu Babana ? Yace shakka babu wannan shine .

Dogon nazari na tafi anya Baban Hafsa yasan ni ɗiyar ɗan uwanshi ce kuwa ? Da babu Bello dana sauka nayi masa magana na gani ko zai ganeni ? Kenan wannan shine dalilin da yasa Mamy tace da Binna yasan wace ce Hafsa a wurinshi da ya haɗiye zuciya ya mutu , a bayyane nace ummm tare da taɓe bakina naci gaba da cewa ƙaddara da ajali ba'a kauce musu tou amma kuma meke tsakanin Hafsa Amisty da Babana ? Wannan ansa banda mai bani ita itama.

Daga gidan su Baba gidan Baba Ƙarami muka nufa na nuna masa zan zauna ne zuwa wani lokaci amma saboda tsabar shi butule ne ya manta da irin karamci wanda mahaifina yayi mishi ya shafawa idonshi kwallin rashin mutunci yayi min wulaƙanci na ƙarshe tare damin gori karuwar banza karuwar wofi wacce ubanki ya mutu a gidan caca.

Kallon Baba Ƙarami nayi ƙasa da sama nace aiko caca ta gama maka komai tunda harya ciyo gida ya baka kake zaune dan na tabbata da "yan uwana sunsan wannan magana wallahi da sai sun ƙwace gidan nan sunce na magada ne , kuma da kake cewa ya mutu a wasan caca kai kaga yadda taka ƙarshen tazo maka ne ? Kuma da kacemin karuwa inda na gode Allah tambarin ba a kaina kaɗai yake ba kaima kana da taka karuwar zaune a gida.

Cikin hayani yace ni ban haifi karuwa ba kuma bazan haifeta ba har abadan duniya idanma nasan ina da karuwa a gidana saina kashe ta ko an faɗa miki ni lusarin ubana ne ? Nace shima uban nawa ba lusaranci ya janyo mishi haka ba ƙaddara ce kuma babu wanda ya isa ya goge ƙaddara , haka kuma shiriya ba iyawar kowa bace ba daga Allah ne kuma na rantse da Allah idan baka barni na zauna gidan nan ba saina nemo "yan gidanmu sun anshi gidan ubansu tunda ba takadda ya rubuta ya baka shi daga duniya har lahira ba ,

Matanshi suka sako baki wallahi bazan zauna musu gida ba na lalata musu tarbiyar "ya "ya inji maman safiya , kallonta nayi nace aike taki ta daɗe da lalacewa ko kina tunanin bansan komai ba ? Naci gaba da cewa ƙofar soro , asibitin da akayi komai ke hatta gidan da aka samo tukuicin da niƙaf taje , da sauri Safiya ta tashi tayi cikin ɗaki , uwarta ko ta kama bakinta bata sake magana ba gudun kar in tona mata asiri a gaban kishiyoyi ,

Tunda abokan zama sukaji haka kowa ta fara ɗakinta zan zauna sarai na gane dan suji labarin abinda Safiya tayi amma sam nace ɗakinsu Safiya zan zauna , uwar Safiya kuwa bata sake magana ba shima Baba Ƙarami ɗaureren azumin magana ya ɗauka , waje na koma wurin malam ɗayyu na anso magunguna na bayan yamin bayani duk yadda zanyi amfani dasu , godiya nayi masa na anshi lambar wayarshi tare da cewa saina shigo.

Satina biyu a gidan Baba Ƙarami na kammala kaf magungunan da Malam Ɗayyi ya bani , natsuwa ta shigo cikin kaina tsoron Allah da gudun duniya ya dawo amma kaf iskancin da kuka sani yana nan ɗibge akaina saidai idan ba'a latsomin wurin ba ,

Ranar dana cika sati biyu cif ranar na ɗagawa Baba ƙarami hankali saiya maidani makaranta , yace min baida kuɗi nace aiko ni ba'a gayamin babu duk inda zai samo kuɗi saiya samosu ya maidani makaranta , yacemin wallahi baida inda zai samosu , dole na haƙura amma na yanke zan kira Alaji in jaraba sa'a na gani ko an dace amma kafin nan zan koma islamiya in fara hadda.

Da daddare na tambayi Baba Ƙarami ƙarfe nawa yake rufe gida ? Yace min ƙarfe 10 idan har goma ta wuce koda minti ɗaya ne saidai mutum ya kwana waje , nace tou babu damuwa , saida nayi alwallah sallar isha'e na kira Alaji nayi masa kwatancen gidan Baba ƙarami nace mu haɗu dashi yanzu da Allah ina san ganinshi yace yana zuwa.

Ban daÉ—e da gama sallah ba yazo , bayan na fita ko gaisawa bamuyi ba nayi masa kwatancen wurin da Baban su Hafsa yake zama nace masa can zaka kaini , ya tada mota muka tun kari wurin kai tsaye....

12/0/10/2019

*JAMILA MUSA...*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 54

Har muka isa daga ni har Alaji babu wanda yayi ma wani magana a cikinmu , kuma munyi sa'ar samun Baban Hafsa kamar dai yadda nayi tunanin dama zamu sameshi , gabansu nasa Alaji yayi parking ban fito daga cikin motar ba na sauke gilashin gefe na tare da cewa Assalamu Alaikum....

Cikin farin ciki ya É—ago daga latsa wayar da yakeyi jin muryana , ba tare daya ansa sallamar ba yace Hajiyata da kina duniyar nan ? Kin kama waya kin rufe ruff , saboda kunsan layina na farko Dikko ne ya karya shi , nace Ey wallahi , tasowa yayi daga cikin mutane yana kaucewa inda babu jama'a cewa fito kiji mana.

Fita nayi daga cikin motar nabi bayanshi bayan wata container dukanmu muka tsaya , kusa dani ya matso sosai ya riƙemin ƙuguna magana ƙasa² yayi cewa haba ina kika ɓoye haka kika barni ina ta garari a garin nan na rasa ina zan samu labarinki ? Shiru nayi ban bashi ansa ba kuma ban cire hannunshi daga riƙo da yayi min ba ,

Yace ya na ganki duk rai a haɗe ko anyi miki wani abu ne ? Ajiyar zuciya na sauke tare da cewa Binna , me Binna yayi miki ne ? Neman sa nake saina ga bayanshi , kashe shi zakiyi kenan ? Nace tabbas kuma ba gudu babu ja da baya , amma me yayi miki haka da ciwo wanda kikayi ƙudirin ɗaukar fansa rayuwarshi haka babu sassauci.....?

Cikin ƙunar rai nace shin ko kasansa ne ? "Yar dariya yayi ta duniyanci sannan yace ai wani ya rigaki shafe labarinshi a duniyar nan , ɗago kaina nayi na kalleshi nace wane mai zarra ne haka wanda yafi mace zafin nama ? Baban Hafsa yace abin duhu ne amma ke wane irin duhun ya baki na rayuwa haka ?

Sauke hannunsa nayi daga riƙon da yayi ma ƙuguna nace , shin wai da kake tambayana duhun da Binna ya bani kama san waye Binnar tukunna ? Ni kuwa nasan Binna domin Babanmu ɗaya dashi , kamar walƙiya haka naji duniya ta juya , cikin dakiya nace amma kasan ɗan uwanka ne ka barni nake furta kalmar kisan sa daga bakina ? Sake rungumoni yayi ya rumgumeni sosai , kunsan akwai runguma akwai rungumewa tou rumgumewa yayi ya kwantar da fuskarshi a saman ƙafaɗata , hawaye ya cikamin ido wato wannan shi Yayan Babana ne ?

Goge hawaye na nayi tare da saita muryata nace me yasa bakwa zuminchie da Binna ne ? Har yanzu yana kwance a saman jikina , cikin disashshiyar murya yace aishi kanshi Binna bai isa yasan ni wayen shi ba bare kuma "ya "yanshi , banma san gidan da yake zama ba amma kaf rayuwarshi da duk wani motsinshi a tafin hannuna yake ,

Amma me yasa ka sakawa rayuwarshi ido bayan kuma ya fita daga rayuwarku ? Ai bashi ya fita daga rayuwarmu mune muka fitar dashi , akan wane dalili ? Ɗago kanshi yayi tare da sunbata ta yace labarin yana da tsayi ni kuma na yanke miki wahala tunda an sheƙar miki da Binna zuwa duniyar mutuwa...

Murmushi nayi mai nuni ina farin ciki amma a baɗinance ina cikin tashin hankali , ƙarfin hali nayi tare da cewa labarin yana da tsayin gaske amma duk meye musabbabin fitinar taku ne.... ? Murmushi yayi tare da shafa gefen fuskata yace keko kuɗi ne silar komai , yanzu dai zamu ɗan rage dare ne ko yadai.... ?

Share maganar nayi da cewa wai kasan "ya "yan Binna kuwa ? Taɓe baki yayi cewa shi kanshi Binnar dakel na sansa bare wasu "ya "yanshi can na wahala , dariya nayi nace tou ina da sharaɗi ɗaya tak zanyi tarayya dakai amma duk wata so ɗaya ka yadda ? Yace Eh na yadda , nace yau nawa ga wata ne ? Ya faɗamin , nace tou ni bana zini a farkon wata da tsakiyar wata sai ƙarshen wata kuma shima ƙarshen wata sai daren da wata zai fita haka yayi maka ne ? Eh na yadda nace tou idan Allah ya kaimu gobe dani dakai mu haɗu a *Erudite comprehensive sch*.

Me zamuyi a makaranta kuma ? Zubin adashe zaka fara dan zan koma makaranta ne kuma itace makarantar da nake so , sabon machine uniform littafai da duk abinda makaranta ta buƙata zaka biya ne sai ka biyamin kuɗin makaranta tun daga aji 1 zuwa aji 3 idan haka yayi maka mu ƙulla tarayya dakai bana san surutu ka kame bakinka kayi shiru abinka kamar yaro ya kama nonon uwarshi....

Zai sake magana nace yi haƙuri 9:44pm zan tafi gida ana rufe mana ƙofa 10:00 , mu haɗu makarantar idan Allah ya kaimu gobe misalin 12:30pm kuma karka zo da aboki ko ɗan rakiya , ina faɗin haka na wuce da sauri na koma cikin mota Alaji yaja muka tafi...

Tunda na shiga motar wasi² nakeyi kenan Hafsat "yar uwata ce da Baban Hafsa da Babana babansu ɗaya ? Tou wane irin sirri ne kuma Aunty Mamy ta ɓoyemin wanda tace da Binna yasan matsayin Hafsa a wurinshi daya haɗiye zuciya ya mutu ? Tunani nayi mai zurfi zuciyata ta faɗamin cewa ko shima Baba kwarto ne ? Da sauri nace astagafurillah , ita kuma Amisty ya muke da ita ne ? Hmm Allah ka iya mana ,

9:57pm a ƙofar gidan Baba Ƙarami tayi mani nacewa Alaji yayi haƙuri yaje zamuyi waya idan na shiga ciki yace tou , kuɗi ya bani har 10k ina san Alaji ko ba komai akwai kyauta , godiya nayi na shige ciki , ina shiga Baba Ƙarami ya fara banbamin bala'e daga gidan uwar wa kike a tsohon daren nan ? Balbaɗaɗɗa irin iskanci da kika saba a gidanku idan kikace zakimin shi nan saidai ki tattara ki kama gabanki "yar iska karuw...... Kuɗin hannuna na miƙa mishi duka sai yaci gaba da cewa Allah yayi miki albarka ubangiji ya ƙara koro kasuwa yasa kifi haka matsayi.

Ban mishi magana ba nayi cikin ɗaki , maman safiya kuma tace sai ki kwashe duka ki bashi ai ya kamata ma ki riƙa biyan kuɗin hayar ɗakin nan , ko inda take ban kalla ba na kwanta tare da saka airpiace a kunne na ina sauraron firata da Baban Hafsa , bayan na gama ji tass nayi murmushi tare da kiran wayar mutumina amma a kashe take har yanzu , saida na kalli hotonshi sannan nayi bacci.

Jiddah da Al ' Ameen zaune a gaban bokansu ya kwarara ihu tare da ɗirkaka uwar ashariya bayan duk sun kora mishi bayani , roƙo na farko abinda aljannu suka buƙata shine a basu jinin jariri sabuwar aihuwa , matakin farko kenan , mataki na biyu kuma idan ba'ayi wannan ba ita Jidda zata kawo jinin al'adarta , mataki na ukku shine za'a kawo maniyin Dikko , wane kuka zaɓa ne ? Boka ya tambaye su ,

Cikin rawar jiki Jiddah tace haba a ina za'a samu wani jinin jariri ne ? A daina maganar jariri gaskiya , wata irin dariya bokan yayi mai firgitarwa , yace arne zaisha jini ne shine zai shiga zuciyar ita yarinyar ya sanya mata wasi² , idan kuma kika bayar da jinin al ' adarki duk duniya yadda Dikko zaiji maganarki ko ta uwarsa bazaiji haka ba , idan kuwa aka kawo maniyinsa labarin yarinyar ya goge a zuciyarshi kwata² har abadan abada zaima manta daya taɓa sani wata yarinya wai ita Sultana , bazai sake san wata mace ba sai ke , ke ɗaya ke ya sani kuma ke zaiyi ta ƙauna har a mutu , Hahahahaha.....

Jiddah tace boka aini yanzu bana tare dashi ya koroni gida yace sai yaga ita Sultanar zan koma kuma babu wanda yasan ma inda take zaune a halin yanzu dan ita mahaifiyar Dikko tace tabar katsina kwata² , dariya bokan yayi sosai sannan ya ɗaga hannunshi daga gefen shi yace tana katsina gata nan , lafiya lau aka nuno hoton Sultana kwance , Jiddah tace Eh wallahi itace , itace boka , dariya yayi tare da ɗaukar kaza ya wurga sama cikin seconds ta dawo ƙasa har an tsotse mata jini , Jiddah ta firgice sosai boka yace idan har kika faɗa masa tana katsina sai ya dawo , idan ya dawo daga nan komai zai tafi mana a sauƙaƙe ,

Al ' Ameen yace haka za'ayi ranki ya daɗe kinga idan kika samu kika samo sai ki bani ni kuma sai nazo na kawo ko ? Jiddah tace Eh , tadai daɗe tana faɗawa boka yadda take san aikin ya tafiyar mata yadda take buƙata , da suka tashi tafiya ta yayyafawa boka ruwan kuɗi shi kuma ya watsa kuɗin sukayi sama.....

Koda suka koma gida Al ' Ameen sai ƙara jaddadawa Jiddah yake tayi ƙoƙarin samo sperm in mai gida idan aka goge ko wace mace a zuciyarshi aka sakata ai taci lafiya , Jiddah tace ai yanzu wanka zanyi na kirashi , Al ' Ameen yace ki bada himma dai karki tsaya sanya , tace insha Allah , sallama yayi mata ya fice daga palon ,

Yana fita ya kira Mardiyya , bayan ta ɗauka yace doughter nasara tana ƙara tunkaro ahalinmu , lallai ke mai nasara ce kuma kece tauraruwarmu gaba ɗaya , fitila mai haskawa amarya a gidan mai gidana , dariya Mardiyya tayi tare da cewa Uncle ya ake ciki yanzu ? Al ' Ameen yace boka yasa a samo masa sperm in mai gida kuma na faɗawa boka yadda zaiyi kinga ina kai masa za'a goge Jiddah a goge banzar Sultana , filin zuciyar mai gidana naki ne ke ɗaya my doughter , Mardiyya tace godiya nake Uncle Allah ya taimake ka ya bada sa'a , Al ' Ameen yace am3n. Sukayi sallama !

Koda Jiddah ta faɗawa Dikko Sultana ta dawo katsina cewa yayi da kyau , ta tambayeshi ranar da zai dawo yace shi daga nan ma gaba yaci , tace haba Yaya nidai tunda an ganta ya kamata kayi haƙuri ka dawo , Dikko yace kiyi wata maganar bana san wannan , Jiddah tace dawowa na ne baka so ko kuwa zancen Sultanar ne yanzu baka so ? Tsoki yayi ba tare daya bata ansa ba ya katse kiran ,

Yana katse kiran Jiddah ya fara kiran mai gadinsa na goruba gidan daya ajiye Sultana , bayan sun gaisa Dikko ya tambayeshi ko An mata tazo nemansa ne ? Yace A , a , gaskiya bata zo ba , katse kiran yayi ya kira Umar yace masa An mata ka ganta ne a katsina ? Umar yace gaskiya bata dawo ba , shima katse kiran yayi tare da cewa "yar ranin hankali ashe kinga dama kin dawo , hmmm kedai kika sani mara aikinyi kuma aradu bazan kiraki ba.

Washe gari bayan na gama duk abinda nakeyi na kira Aunty Suwaiba muka gaisa , nayi mata sannu da jiki ta ansa cikin farin ciki da faɗamin tayi kewata , nace mata insha Allah ai zanzo , tace Allah ya yadda , nace ko Aunty ta kira waya ne ? Aunty Suwaiba tace har yanzu dai shiru gaskiya bata kira ba saidai wata number ake ta kiran wayar da ita , nace kin ɗauka ne ? Tace tunda naji namiji ne ban sake ɗauka ba , ki turomin number , Aunty Suwaiba tace a , a gaskiya Sultana kiyi sabgar gabanki ki fita daga rayuwar wani zaƙule² , Aunty turomin number da Allah , Aunty Suwaiba tace gaskiya bazan turo ba , juyin duniya nayi amma taƙi haka nan na gaji na haƙura mukayi sallama.

Dani da Baban Hafsa dukanmu 12:30pm a cikin makarantar tayi mana , a napep nazo bayan na iso na anshi kuɗi a wurinshi na sallami mai abin hawa , daga nan kuma muka ɗunguma zuwa Ofishin shugabar makaranta , bayan gaisuwa Baban Hafsa da kanshi yayi bayani tare da nema min gurbin karatu a makarantar , duk dai abinda ya kamata shine yayi , duk wani rubuce² shine ya cike komai da hannunshi da sunan MARYAM ALIYU ,

Bayan ya gama ya tambayi shugabar makaranta shin ko zai iya biyan kuɗin makaranta na daga aji 1 har zuwa 2 tace anayi zai iya kuma ta ƙara masa da cewa ana shiga aji dan koyon karatu na musamman bayan ɗalibai sun tashi , extra lesson , tambayana yayi ko ina ra'ayi nace masa ina so , gaba ɗaya akayi lissafi yayi mata transfer kuɗin zuwa cikin asusun makaranta ,

Ranar da zan fara zuwa makaranta aka faÉ—amin fita nayi daga ofishin na basu wuri domin su ida abinda suke san kammalawa , bayan sun gama ya fito dani dashi duka wurin motarshi muka nufa , bayan munje muka buÉ—e kowa yayi ma kansa mazauni.

Bayan mun zauna yace min Hajiyana gaskiya baza ki hau machine ba wurin zuwa makaranta , motar makaranta zata na zuwa tana É—aukarki , sch bus , nace kuÉ—i ne baka da ko a ina matsalar take ne ? Yace ina da kuÉ—i kawai dai girmanki ya wuce ki hau machine , faÉ—uwa gabana yayi kardai yaga hotona a lokacin da akayi ta yamiÉ—iÉ—i dani a social media lokacin da Dikko ya bani motarshi ?

Dakewa nayi nace shin wane irin girma ne kake gani ina dashi wanda har kake tunanin nafi karfin hawa machine ? Jawoni yayi jikinshi yana cewa aike babbar ƙaddara ce samunki sai namiji mai babban rabo , tarayya dake kuma sai jarumin namiji irina , matsayinki da darajarki saima kin ɗora mutum a linzaminki zai tabbatar da haka nine zan tabbatar idan har muka keɓe na samu nasarar taka ruwan cikinki , murmushi nayi tare dayi mishi kallon ɓatacce.

Lalube jikina ya farayi , kallon sakarai nayi masa tare da ƙara ƙureshi da ido sosai yanzu na tabbar da ɗan uwan Babana ne dan naga kamarshi da Baba harta ɓaci wallahi kuma sai yanzu na fahimci maganarsu iri ɗaya sukeyi yanayin kallonsu da komai dai iri ɗaya saidai shi Babana yafi shi haske sosai kuma yafishi hanci da ƙaramin baki amma gadai jinin nan yana yawo a jikinshi.

Hannunshi ya tura cikin rigata tare da ƙoƙarin haɗa bakina da nashi na riƙe hannunshi na kauda fuskata gefe ɗaya idona ya cika da hawaye dan wallahi kallonshi nakeyi kamar Babana , cijewa nayi cikin jarumta nace kar ka manta da nace maka bana ci sai ƙarshen wata , ƙara riƙoni yayi yana cewa tou ai ba cewa nayi zanyi ba koma zanyi kina tunanin zanyi a mota ne ? Kuma a motar ma tsakar gari da tsakiyar rana ? Murmushi nayi tare da cewa ai ba matsala bane ba ra'ayinka ne cin duk abinda kake buƙata yayin da yunwa ta taso maka dan ba'a tarar abinda za'aci a dai² irin lokaci buƙata ɗaya kawai aji ciki yayi nauhi ,

Kin san da haka tou kike ta wahalar da rayuwata ? Kika ɓace min ɓat kuma da kika dawo sai kika zo da wani tsarin banza , jifa yanzu ko hidimar da nayi miki ai ya isa ki bani tukwuici mana , tou kayi min gori ka biyamin kuɗin makaranta , a , a ba gori nayi miki ba ina so dai kisan yadda akeyin halakkaci da sakayyar farin ciki yayin da akayi maki karamci ya ƙarasa maganar tare da haɗe bakina da nashi wuri ɗaya zuyzuy ya riƙa lashewa yana tsotsewa wani irin ihu nayi tare da cewa nace bana so wai kai maye ne iye ?

Dariya yayi irin dariyar Babana yace maye ne ni mana , kin taɓa ganin namiji ba mayen mace ba ? Duk uztazancin namiji duk imanishi duk haukarshi ko hankalinshi duk talaucinshi ko arziƙinshi duk wani matsayi da yake taƙama dashi mace ce remote control inshi , ke yaufa duk masifarki saina sha wannan dadɗan bakin naki wallahi , matsowa yayi daga saman kujerar da yake zaune yayi sosai dan sai zuƙewa nakeyi inayin baya amma maye ɗan mayyar saida ya jawoni ya ƙara lasar bakina , cikin kuka nace haba Bab..... Kimace Baban ai na isa in haifeki tunda yarinyata ta huɗu ma nasan zata girmeki amma dady suke cewa. Kema sai kice Dady daga yau....

Cikin kuka nace dan Allah ka daina irin wannan abun mana ! Ai yanzu na fara miki irin wannan abun dan ni daɗi nakeji idan inayi miki , haka zamuyi dake ƙarshen watan iye ? Haka zaki ta ihu kina kiran Dady har maƙota suji kukanki ? Fuskata kaca² da hawaye nace tou ka bari sai ƙarshen watan yayi mana ka bari ƙarshen wata yazo idan bakayi abinda kake so ba sai kacemin marowaciya ce ni mana , Allah ya taimakeni yace Allah ya kaimu yayi maganar tare da gyara rigarshi ya gyara fuskarshi dana daƙune hawaye ,

Ajiyar zuciya nayi a lokacin daya fara tafiya da motar yana cewa ina zan ajiyeki ne ? Ajiye ni kasuwa , me zakiyi kasuwa ? Yayi tambayar yana kallona nace hijabi zan siya , sai me kuma ? Nace shikenan , yace tou a siyo hada niƙaf dan banasan ayi ta kallemin wannan kyakkyawar fuskar mai ɗaukar hankali ya karasa maganar tare da shafo fuskata nace tou ,

Har muka zo kasuwa daga haka babu wanda ya sake magana sai shashshekar kukana dake tashi kaɗan² , bayan ya ajiyeni kasuwa ya bani 30k yana cewa sun isheki ? Da sauri na buɗe mota nayi gaba ko ansa ban bashi ba , murmushi yayi tare da bin Sultana da kallon mai tattare da tsantsar so , saida ya daina hangota ya wuce yana mai addu'ar Allah ya bashi sa'ar "yar yarinyar can ya more abunshi.....

Ta bayan kasuwa nabi na fice daga kasuwar ina ta kuka tare da goge bakina wai Yayan Babana shine yake haÉ—a bakina da nashi har yake addu'a Allah ya bashi sa'ar hawa saman ruwan cikina ? Wayyo Allahna wai meya haÉ—a wannan bala'e wanda yasa "yan uwa suke cuÉ—anya da "yan uwansu babu wanda yasan matsayin kowa , wayyo Allahna Aunty Mamy me yasa tun farko baki faÉ—amin abinda ke tsakanin Babana dasu Amisty ba ? Juyawa naji garin yanamin , Malam ÆŠayyu ya faÉ—omin a rai dan haka na fara kiran wayarshi !

Bayan ya ɗauka muka gaisa nace Malam kamin bayanin abinda ka sani akan abinda ke tsakanin Babana da Bello tou ko kasan dalilin da yasa matar Babansu Babana ta kori su Baba daga gidansu ? Malam Ɗayyu yace a , a , nace Aunty Mamy ta faɗa maka tsakanin Amisty Hafsa da Babana ? Karka ɓoyemin komai ka faɗamin abinda ya riga ya wuce ya wuce ka faɗamin meye tsakanin Babana dasu don Allah........?

Malam yace Eh gaskiya abinda mariganya ta cemin shine , tace shi Bello yace yana san ya jefe ƙiyayya mai girma a tsakanin ahali ɗaya duk akan fansar budurcin matarsa da Binna ya ɗauka a ranar da yake tunanin itace ranar sa ta farko a angwanci , shine yayo dillacin ita Hafsa da Amisty wadda ita Amistyn da Baban shi Binna da Kakan Amisty suke Baba ɗaya , da sauri nace tirrr da wannan ahali , malam bana san sanin zuminchie su sauran bincike da sanin dalilin da yasa aka kashe min Babana da wanda suka kashe shi bana kowa bane nawa ne , miye tsakanin Babana dasu Hafsa ?

Malam yace muradi ne , nace wayyo Allahna wane irin muradi Malam ? Malam yace muradi wanda baya buƙatar kawaici kunya ko kara , tirrrr Allah ka tsinewa Bello albarka tsinannen Allah ubangiji ma bazai barka ba kuma nima bazan barka ba da zaran na gama haɗa abinda nake buƙata ƙaryarka ya ƙare aihuwar asara ban yafe maka ba kuma kada Allah yaba uwarka ladar aihuwarka , kashe wayata nayi tare da dafe goshina da hannun damata kaina naji yanamin ciwo kamar zai faɗo ƙasa , Aunty Mamy tayi gaskiya da tace gaba ɗaya ahali sun zama *KWARATA...*.

Baba ya nemi Amisty kuma ya nemi Hafsa , ɗiyar Yayanka , da ɗiyar shi ta zumincin Allah , kowa mayunwanci ne duk wanda aka bashi saiya ansa yaci babu mai haƙuri inama anfanin irin wannan muradi , yanzu nima gashi Baban Hafsa yana muradina a hayaniyance nace ni kuma ba muradikanka nakeyi ba dukiyar da tasa mahaifiyarka ta lalata zuminchie itace muradina kuma saina ga bayanta kaf saina mayar daku faƙiran ƙarfi da yaji , tunda har tayi sanadin lalacewar zuminchie ta fasa kan "yan uwa saina tarwatsa komai har gobe dai zata rayu da taƙaicin *BINNA* kuma saikin mutu da nadamar sanin *BINNA* , kun kashe maciji amma baku sare kanshi ba , kun kashe *BINNA* amma baku sani ba *BINNA* yana nan a saman doron ƙasa na ƙarasa maganar tare da buga ƙafata ƙasa , sai kun mutu dukanku da baƙin cikin *BINNA* domin Binna ya dawo daga duniyar mutuwa.........

A sassauce nace koma miye yasa kuka korashi daga duniya kuma sai kun tafi baku ci koma miye ba kuma haka zaku tafi ku barshi kunaji kuna gani...

A gajiye na koma gida zuciyata cike da masifu iri² , a ƙofar gida na samu Baba ƙarami zai fara magana na bashi kuɗina kaff amma bai ansa ba yace ki tattara naki ya naki ki kama gabanki domin zamanki a tare dani babban haɗari ne da kuma barazana a rayuwata , cike da ladabi nace yanzu kuma laifin me nayi maka ne ? Idonshi cike da hawaye yace babu abinda kikamin amma yau duk mutumin dake anguwar nan babu wanda bai shiga tashin hankali ba da ɗimuwar rayuwa ba sanadinki ,

Ƙara tausasa muryata nayi cikin kuka nace sanadina kuma Baba ? Nida bana nan me kuma ya faru ? Baba yace wasu mutane ne suka zo ni banma taɓa ganin irinsu ba sai yau suka shigo anguwar nan sai hauka sukeyi sukayi ta harbe² suna nemanki duk gidajen anguwar nan babu gidan da basu binke ba suna nemanki , nace su waye su ? Hukuma ce ko kuwa "yan gani na iya ne ? Baba yace koma "yan waye ki tafi daga anguwar nan dan zasu iya dawowa ko wane lokaci , murmushin ƙarfin hali nayi tare dayi ma Baba godiya na wuce......

Ina tafiya ina nazari , babu yadda za'ayi Bello ya fito fili yasa a nemo mishi ni saboda ta ƙarƙashin ƙasa yakeyin cutarsa kuma idan ma banda wata sahihir sheda babu yadda za'ayi nayi shara'a da Bello , tou wane sabon abokin gabar ne ya ɓullo haka a lokacin da abubuwa sukayi ma kaina yawa ? Wata zuciyar tacemin Mardiyya ce , kaina na girgiza tare da cewa a , a , Ummu Affan ce ? Ba ita bace , su Amisty ne ? Um ummm basu bane ,Momy ce , tabbas itace tunda dama tace idan aka sake gani a garin katsina aka faɗa mata zatamin tire² tabbas itace ba kowa ba , wallahi itace ma , dariya nayi tare da cewa nayi gidan ɗanki kije can ki kamoni , na karasa maganar a dai² lokacin dana tsaida napep nace mishi kaini goruba road.

Tafiye muke a napep ina kiran wayar Dikko a kashe dai take har yanzu , amma ina mamaki ya akayi Momy tasan nazo katsina ? Murmushi nayi koma dai miye na tafi wurin Dikko naga yadda za'ayi dani dan na lashi takobin zama katsina ko za'a kasheni , tunani dai iri² a zuciyata muka isa goruba road 1k naba mai napep saboda babu canji , yana wucewa nima na shige gidan ,

Gidan a buÉ—e yake , gaisawa nayi da mai gadin na wuce ciki , palon kuma abokan Dikko ne cike wasu nacin abinci wasu kuma hankalisu yana kan tv suna kallon boll duk yadda akayi Dikko yana nan ko kuma zaizo dan ba'a irin wannan zaman sai idan yana nan ko kuma idan zai dawo daga tafiya ,

Banma kowa magana ba na wuce ciki kuma suma babu wanda yayi min magana dan ko sallama banyi ba , ɗakin da nake zama na wuce na shiga da sallama , yana nan dai yadda nasanshi tun farkon farko , kayana a gefen katifa lulluɓe kamar dai yadda aka saba lulluɓesu , zama nayi gefen katifa na rufe wayata na ɓoyeta dan idan har Dikko yazo nasan zaiyi bincike , kuma bana buƙatar yasan matsalar data shafi ahalina da rayuwata saboda wata rana dan bansan inda abun zai tsaya ba , kuma babu wanda yasan abinda gobe zatayi sai Allah ,

Rufe ɗakin nayi na wuce bayi nayi wanka bayan na fito na canja kaya , kwanciya nayi naci gaba da tunanin rayuwa irin tawa , sai kuma su Amisty suka faɗomin a rai ko sun daina karuwanci yanzu ? Allah sarki Hafsa har tasan Babana ya gogeta taso ita da Amisty su gurjeni suma , hmmm ko ina labarin Ummu Affan ? Ina san sanin rayuwar Aunty Suwaiba duk yadda akayi cire mata ƙafafuwa akayi tou fa , naji dai da rayuwata naga wannan irin rayuwa.

Dariya nayi tare da cewa kema uwar Dikko har yanzu baki gano inda nake ba ? Tou zo kiji in faÉ—a miki ina nan gidan É—an rainin wayan É—akin a É—akinshi kwance saman katifa an tada man gen ina shan iskkan A C babu abinda ya dameni da zafin gari , kuma yazo ya bani abinci mai kyau inci ga masu gadi suna gadina duk É—iyar É—an caca da kika raina É—anki kuma yasan darajata tou nice na samu wannan matsayin , ummm turo bakina nayi tare da gyara kwanciyata nace bacci mai daÉ—i.........

13/10/2019

*JAMILA MUSA....*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 55

Tunda na samu na kwanta bacci har gari ya waye ko fitsarin dare ban farka ba , wadataccen baccin dana samu shine ya bani damar tashi asubahin farko , kuma tunda na tashi nayi sallah asuba ban koma bacci ba , wayata na ɗauka saidai na kunno maganar mutumin nan da nake tunanin shine ya kwakwalewa Aunty Mamy ido ta mutu , Allah ɗaya gari ban² shi nan magana yake , da , da yare na yakeyin magana zanji abinda yake cewa to banaji saidai na saurara amma ba damar na fihimta , hmmm ya zamar min dole na miƙe da zuciyata da kwalwata nima nayi ilimi kodan ceton rayuwata daga duhun jahilci....

Bayan na gama saurare na kashe wayar na saƙata a gefen katifa na koma nayi kwanciyata ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni , na ɗauki lokaci mai tsayi ina bacci hankalina kwance banda wata damuwa data wuce yunwa , sai ɗaya saura na farka ,

Koda na farka wanka nayi nayo alwalla kaya na canja ni "yar gayu dan ina cire kaya na ajiye a palo za'a É—auka a wanke a gogemin shi yasa ni kuma kullum saina canja kaya sau biyu , idan nayi wankan safe na saka idan nayi na marece ma na sake !

Bayan na gama sallah azahar na ɗauki kuɗi na fito da zumar in ba mai gadi ya siyomin abinci , amma ina shigowa palo naga ɗika²n kulolin abinci da filets da cokula kamar dai yadda aka saba ajiyewa a kullum idan Dikko yana gari idan har yana nan haka ake ajiye wannan abinci da rana da daddare shi yasa ko wane lokaci gidan baya rabuwa da mutane kalacin safe ne dai bana tunani ana kawowa gaskiya dan bana gani saidai iya wanda zan karya dashi.

Saida na zuba abinci dai² wanda zai isheni nakai ɗaki na ajiye sannan na dawo nace ma mai gadi wai Dikko baya nan ne ? Yace min yana nan mana , nace tou ai ban ganshi ba , yace min yana nan ciki tun ɗazu ya shiga kila bacci yakeyi , nace yayi mishi kyau , na juyo na dawo a raina ina cewa miya faru bai nemeni ba ? Wurin mai gadin na sake komawa nace yasan nazo kuwa ? Yace Eh na faɗa masa , ya yace maka ? Baice komai ba , daya zo yace ina ne ? A , a bai tambayeki ba , tou ya yanayin fuskarshi ? Yayi farin ciki ko yayi yanayin damuwa ne ? Yace ni bansan ya yayi ba.

Ban sake magana ba na koma na É—auki abinci na naci gaba da ci , bayan na gama nazo na ajiye filet in a inda na zuba abincin , ban daÉ—e da komawa É—aki ba gidan ya fara É—aukar taron mutane kamar yadda ya saba a ko wace rana , wannan zama haka zasuyi tayinshi har sai dare yayi sannan kowa zai kama gabanshi.

Hayaniyar sai ƙara ƙaruwa takeyi palon sai ƙara cika yakeyi harabar gidan kuwa an cika ta da motoci , aikin gardamar suka fara kenan basu da aiki sai maganar "yan kwallo , ƙaramin palon na fito na zauna inga ta ina Dikko zai fito amma har akayi la'asar naje nayi sallah na dawo banji Dikko ya fito ba , gajiya nayi na koma ɗakina naci gaba zaman jiran tsammani.

Yau ko abincin dare banci ba inayin sallah isha'e nayi kwanciyata jiya banga Dikko ba yauma ban ganshi ba haka nan na haƙura na kwanta , amma ba haka naso ba naso mu haɗu ko so ɗaya , tou ko baiso nazo masa gida bane shi yasa yake ta ɓoyewa kila yayi haka ne idan na gaji da zama in kama gabana ,

Bandai yi bacci ba ina kwance ina ta tunanin duniya har 11:05pm a hankali gidan ya fara ragewa har yanzu banyi bacci ba , wurin misalin 11:49pm gidan yayi shiru gaba É—aya , yau gaskiya sun tashi da wuri dan wani lokaci suna kai har 1:30am suna fira !

Duk masu fita gidan akan idona suke fita amma har yanzu babu Dikko a cikinsu kuma har akayi zaman nan aka tashi banji an kira sunashi ko so ɗaya ba , kuma banji maganarshi ba , saida gidan ya zama babu kowa na haƙura nayi bacci.

Wasa² har nayi kwana 3 gidan banga Dikko ba kuma mai gadi ya tabbatarmin yana nan ya dawo , na duba ɗakinshi ban ganshi ba , kuma idan na kira wayarshi yanzu tana shiga amma baya ɗauka , haka nan naji duk na takura gaba ɗaya na kama kaina saima na daina cin abincinsu kwata² saidai in tura a siyomin abincin da nake so naci lashe ² da duk wani abun kwaɗayi da zuciyata take sha'awar ci ko sha da kuɗin da Baban Hafsa ya bani,

Ranki ya daɗe yau kwananki 2 da dawowa amma har yanzu shiru nakeji , gyara zama Jiddah tayi tare da cewa waini tayama zan fara samoshi ne ? Kwantar da murya Al ' Ameen yayi cewa haba ranki ya daɗe duk wayewarki da gogewarki kice baki san yadda zakiyi ki samo ba ? Tou taya akayi kika kwanta da shi ? Jiddah tace kwanciya daban maganar samun abinda boka yake magana daban ya bani "yar ƙaramar kwalba yace a ciki zan matso taya zan fara tara kwalbar nan na matso bayan kuma yana kallona.

Al ' Ameen yace ranki ya daɗe idan ya kwanta dake bayan kun gama abinda kukeyi sai kiyi kamar irin kina masa wasa naku na ma'aurata saiki lallaɓa kiyi dabara ko a hannunki ki samu , dama kin ajiye "yar kwalbarki a toilet kina matsowa sai ki tafi toilet kamar zaki wanke hannunki kina shiga sai ki zuba a kwalbar , ki maida hankali kinga abun kullum gaba yakeyi , kuma anje kamo yarinyar nan ta gudu yanzu babu wanda yasan inda take ma ,

Jiddah tace gaskiya wannan shawara haka tayi , tou insha Allah zanyi , Al ' Ameen yace dadai kin taimaki rayuwarki , haka yaita É—ora Jiddah yana kaita yana baro.

Da marece bayan na gama abinda nakeyi na fice daga gida , kasuwa na fara zuwa na siya niƙaf kamar yadda Baban Hafsa yace , banyi hijabi ko ɗaya ba saboda ina da hijabai sunkai goma a gidan Dikko , ina sayen nikaf in na lulluɓe fuskata na haye napep , ban sharce ko ina ba sai majalissar su Baban Hafsa , mai napep na sallama ya tafi ni kuma na isa wurin tare da sallama.

Gaba É—aya suka ansa sallamar yayin da Baban Hafsa ya taso fuskarshi É—auke da yanayin kishi yana cewa sai ki kama kizo nan kuma bazaki faÉ—amin ba ? Wurin motarshi ya nufa ya É—auko leda yana cewa da Allah kada ki sake zuwa nan kinji ko ? Nace tou , yawwa ga kayan makarantarki nan da littafanki komai akwai a ciki , nace ngode Dady shi kuma yacemin idan Allah ya kaimu goben zanzo makarantar taku nace Allah ya kaimu lafiya , ya ansa da am3n da kanshi ya tsaida min napep ya biya kuÉ—in , saida na samo abinda zanci da daddare da wanda zanyi kalaci da safe idan Allah ya kaimu sannan na wuce gida.

Yauma gidan ɗinke yake da mutane babu masaka tsinke ko dana tunkari palon dole tasa na dawo saboda babu ta hanyar da zanbi in wuce , gaba ɗaya palon ya gauraye da ƙamshin turare iri² har baka iya gane na wani , kowa dai ɗan gaye ne babu sakarai kuma babu ƙazami dan duk "ya "yan attajirai ne , kowa dai yanaji da kanshi dan babu wanda yake so a fishi ,

Bayan gida na zagaya wurin masallacin dake cikin gidan , a ƙofar masallacin na samu wuri na zauna sannan na fara duba kayan da nazo dasu , hada waya a ciki da layin waya kila Dady yana tunanin banda waya shi yasa ya haɗomin da ita , ƙaramar waya ce nokia ko kwali bata da sai caja , murmushi nayi tare da maida wayar na fiddo abinci naci gaba da ci saboda yunwa nakeji ,

Ban daɗe da gama cin abinci ba suka fara fitowa danyin sallah magrib dan haka na tashi na zagaya ta ɗayar hanyar dan gaba ɗaya a wurin ƙofar masallacin suke alwallah , lokacin dana zagayo gaba ɗaya babu kowa a wurin sai Dikko kaɗai dake alwalla a ƙofar palon , gaishe shi nayi tare da mishi sannu da zuwa kallona yayi amma baiyi magana ba ,

Sake gaishe shi nayi ya ƙara basarwa , raɓashi nayi zan wuce ciki a dai² lokacin daya gama alwalla ya ciko bakinshi da ruwa kamar da yayi niyar watsamin su sai kuma ya zubar a gefe yana warware hannun rigarshi daya naɗe yace ina kikaje tun ɗazu ? A daburce nace ina ina ta can na nuna mishi baya da hannuna , kina ta can ko ? Yayi maganar tare da jinjina kanshi yace yayi kyau,

Daga haka bai sake magana ba ya wuce nima na shige ciki , ina shiga ɗaki na ajiye kayan dana zo dasu nayo alwallah nayi sallah , ina gama sallah na fara haɗa littafaina a cikin jikkar makaranta wani irin farin ciki nakeji naga Dikko kuma naji daɗi dana ganshi kullum nidai ƙara burgeni yakeyi addu'a ta ɗaya Allah yasa idan ya gama sallah yazo , ni kuma ince masa me yasa baka ɗaukar wayata idan na kiraka......?

Zuciyata tace karki sake ki tambayeshi raina ki zaiyi , a bayyane nace ko yane gaskiya ya kamata nasan miye dalilin da yasa baya ɗaukar wayata , zuciyata ta sake gargaɗina a karo na biyu cewa ki kama kanki shi namiji ma ya riƙe ajinshi sai ke banza zaki damu dashi , murmushi nayi a bayyane nace ina wani maganar aji kuma bayan ina zaune a gidanshi , anya akwai wanda ya taɓa shiga rayuwa irin tawa ? Nidai ko a labari ko littafi ban taɓajin wanda yayi bahaguwar rayuwa mai tattare da ƙalu bale ba kamar tawa ,

Babana ya rasu , gidana kuma dana siya "yan uwana sun siyar dashi , ƙanin Babana kuma yace min zamana a tare dashi babban riskine , Yayun Babana kuma basu ma sanmu ba , Mamana ta gujeni ta tafi ta barni ina ta gararin rayuwa me nayi ma duniya ta juya min baya haka da ƙuruciyata ? Dole in cire wani girman kai inbi Dikko in zauna lafiya idan ba haka ba shima ya juyamin baya bansan ya rayuwata zata koma ba , ga mahaifiyarshi ta ɗanawa rayuwata tarko idan kuwa har nayi kuskuren bari ta kamani kashina ya bushe ,

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Allah ngode maka ubangiji ka yafemin ka yaye min ƙunci da damuwa dan alfarmar sayyadis sadati , ka tausayamin ka karkato da hankalin mahaifiyata gareni kaji ƙaina badan halina ba , Inna kina wace duniya haka kika manta dani ? Niko duk halin dana shiga bana mantawa dake har abadan duniya kuma ina sanki Allah ya dafa miki ya jiƙanki a duk inda kike a faɗin duniyar nan kuma ya huci zuciyarki , Allah kaji ƙan Babana kasa ya huta....

7:19am a cikin makaranta tayimin , ina cikin ayarin É—alibai har a wurin taron assembly ko a wurin taron komai da turanci ake faÉ—a kuma abinda na fahimta kowa idan zaiyi magana da É—an uwanshi bayayi da yaren hausa saidai da harshen bature ,

Bayan an gama ko wane É—alibi yayi ajinshi nima nayi nawa ajin JSS 1B shine ajina , duk "yan ajin nafi su girma kuma sai dariya sukemin suna kallona , wuri na samu na zauna ina tunanin idan har yaran nan nabar suka shiga gabana a karatu raini zasumin bana wasa ba , idan har na bar wani É—alibi yayi na 1 a ajin nan bani ba naji kunya , dan haka na tattaro hankalina da natsuwata na fara É—aukar karatu yadda ya kamata domin malamai sun fara shigowa.

Babu laifi ina fahimta dan ina da ilimin addini sosai shi yasa nake ganin karatun boko bazai wani bani wahala ba , lokacin da aka fita break banje ko ina ba ina cikin aji ina ta naci , bayan an dawo malamai suka ci gaba da shigowa har aka tashi daga makaranta , bayan an tashi saida nayi azahar tare da addu'a ubangiji ya dafamin sannan na shiga ajin koyon darasi na musamman ,

Saida la'asar muka tashi muna tashi saida nayi la'asar nabar makaranta kuma Dady bai zo ba , daga makarantar boko tsohuwar islamiyarmu na nufa na siya form na shiga ajin harda kuma ni na cika abuna da kaina da larabci , daga islamiya na wuce kasuwa na É—inka hijabi da wando na islamiya sai gab magrib na isa gida.

Yau duk taron su bai hanani wucewa ba , tunda na shiga kowa yabi ni da kallo har na shige , ina shiga wanka nayi tare da ɗauro alwallah na saka kayana ko mai ban shafa ba nayi sallar magrib dan an kira sallah , ina gama sallah wayar da Dady ya bani ta fara tsuwa tashi nayi na ɗauko ta a inda na ajiyeta , bayan na ɗauka muka gaisa yacemin kiyi haƙuri don Allah yau baƙi nayi a Office amma ina san ganinki yanzu ina zan sameki ne ? Nace saidai kai ka faɗamin a inda zan sameka , inda zan sameshi ya faɗamin nace tou gani nan zuwa yace sai kinzo ,

Daga saman abin sallah dana miƙe wayata kawai na ɗauka wanda zanyo recording idan an taɓo labarin daya shafi Babana , haka na sake ratsowa na fito ina fitowa Dikko yace ina kuma zaki ? Nace yanzu zan dawo ina faɗin haka nayi gaba , yace ke karki sake fita daga gidan nan sai kuma gobe idan Allah ya kaimu , banma saurareshi ba na fice abuna.

Ina fitowa daga palon na samu wuri na ɓoye dan nasan dole saiya biyo bayana , ina ɓoyewa kuwa ya fito yana kirana amma abun mamaki ya fita waje ko sahuna bai gani ba na ɓace kamar walƙiya , mai gadi ya tambaya ta wace hanya "Yar mata tabi ? Yace mai gida banga fitarta ba , Dikko yace baka ga fitarta ba ? Yace Eh , tabi ta gabanka ta wuce kace baka ga fitarta ba dan ka ɗaukeni sakarai ? Cikin girmamawa yace wallahi mai gida ban ganta ba , kallonshi Dikko yayi yace amma ai duk wanda zai shiga ko fita a gabanka idonka , kusa dashi ya matsa yace ta wace hanya tabi ? Mai gadi yace mai gida wallahi bata fita ba ,

Dikko yace to rufe ƙofar karka sake kabar wani ya sake shigowa kuma karka sake ka bar kowa ya sake fita yace tou , daga ƙofar palon ya koma ya tsaya bayan wani lokaci kuma ya taho da sauri ya tunkari hanyar fita daga gida bayan yaje ya sake komawa ƙofar palon ya tsaya , magana yayi ma mai gadi cewa lokacin dana fito ƙofa a buɗe take ko a rufe ?

Mai gadi yace a buɗe , Dikko yace buɗemin ƙofar , buɗewa yayi Dikko ya sake tahowa saida yazo fita yace tabbas bata fita ba tana cikin gidan nan dan ko da gudu ta fita fitowa ta ya isa na hangota ko yane , zanga ta inda zaki bi ki fita yarinya , yana faɗin haka ya koma motarshi ya zauna , dariya nayi a raina tare da cewa mu zuba wallahi babu wanda ya isa ya hanani fita a daren nan saina fita.

Har aka kira sallah isha'e ina tsugunne cikin filawowi Dikko yana cikin mota , gaba É—aya suka fito suka zagaya hanyar masallaci Dikko yace ma mai gadi karka sake ka bar wani ya shigo kuma kar wanda ya fita bari muyi sallah , dariya nayi nace aiko na fita na gama kuma tunda har ka bar motarka buÉ—e da ita zanje ,

Yana zagayawa na fito na shige motarshi tunanin mai gadi Dikko ne ya buɗemin get na fice da gudu sakarai ya manta Dikko yace mishi zaiyi sallah , ina fita na kira Dady nace har yanzu kana wurin ne ? Yace min yabar wurin daya ji shiru kuma ya kira wayata a kashe , nace tou yanzu kana ina ne ? Yace ina nan asibiti , nace lafiya a asibiti ? Yace Hajiyarmu ce batajin daɗi , nace wace asibiti haka ? Yace min fmc nace wane ɗaki yacemin zuwa zakiyi ne ? Na gane wayanshi idan zanzo bazai faɗamin ba , dan haka nace aini tsoron asibiti ma nakeyi Allah ya bata lafiya dama ko nazo sauƙi zan nema mata daga nan ma nayi mata addu'a Allah ya bata lafiya , yace amin , cikin nuna damuwa da tausayin matar nace amma dan Allah da kun sake mata asibiti , yace ai anan likitan ta yake , nace tou Dady ai kuma da ɗakin sarakai kuka kaita tunda Allah yasa kana da iko , yace ai nan take nace tou Allah ya sawaƙa yace amin , sallama mukayi dashi na dawo gida ,

Ina dawowa nayi horn ya leƙo yaga Dikko ya buɗe na shige a inda ya ajiye motar na ajiye na shige ciki da sauri , ina shiga nace fmc ɗakin sarakuna , gani nan zuwa gareki muguwar tsohuwa , hayaniyar Dikko najiyo yana cewa waye ya fita kuma waye ya shigo ? Ina alwallah naji ka buɗe ƙofa yanzun nan ina fitowa naji ka sake buɗewa , mai gadi yace mai gida ai kaine ka fita , Dikko yace na fita naje gidan wa ? Mai gadi yace na rantse da Allah kaine ka fita , Dikko yace idan ka sake cewa nine na fita saina mareka wallahi , mahaukaci ka ɗaukeni ko kuwa me ? Shiru yayi yana nunawa da hannunshi wallahi Allah kaine ,

Dikko yace aiko ubanka zanci , abokanshi suka bashi haƙuri tare da cewa ya canja mai gadi kawai , mai gadi yanajin za'a canja shi ya fara wallahi ײ Dikko yace idan bakaimin shiru ba saina harbar maka baki da ƙafata , duk inajin hayaniyarsu na koma nayi kwanciyata na ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya ina ɗigawa bakina fura ina lashewa ,

Motarshi ya koma yayi "yan dube² sannan ya rufeta bai ciro makullin ba yayo ɗakina , kwance ya sameni ina ta ɗiga fura a bakina hankalina kwance kuma ko inda yake ban kalla ba na ƙaddara ma babu shi kawai a wurin , An mata ina kikaje ? Ban kalleshi ba nace naje saman katifata ne kuma gaka ka ganni kwance ina shan fura ko zaka sha ne ? Bana san sakarci ina kikaje ? Tashi nayi zaune nace to ko nima mai gadin zaka maidai ni ne ?

Rufe idonshi yayi yace ina kikaje nace ? Shiru nayi na koma na kwanta naci gaba da shan furata , har yanzu idonshi a rufe yake ya maimaita ina kikaje ? Ni nace maka babu inda naje sai tambayata kakeyi ina naje idan naje wani wuri zaka sameni ina kwance wai ?

Shigowa yayi cikin ɗakin ya shaƙoni ya ɗagani tsaye yace zaki faɗamin inda kikaje ko saina buga miki kai da bango ? A tsorace nace babu inda naje ina nan tunda kace karki in fita na dawo na faɗa mishi duk yadda sukayi da mai gadi da lokacin da zai tafi sallah nace idan bana nan taya na san haka ? Naji kina nan amma dana tafi sallah ke kuma sai kika fita da mota ta , nace wai na fita naje ina ? Murmushi yayi tare da sakarmin wuya daga shaƙar da yayi mini yace Allah ya sawaƙe miki ganin ɓacin raina , wallahi dan ina tausayinki amma yau dasai kinsan kinmin gardama ,

Fita yayi daga ɗakin yana magana ƙasa² , ajiyar zuciya na sauke daga tsaye na ida shanye furata na wuce nayi alwallah nayi sallah isha'e , ina gamawa nayi kwanciyata dan yanzu bana daɗewa banyi bacci saboda makaranta dan banda lokacin baccin safe kona rana !

Yau da kanshi ya kaini makaranta kuma bai tambayeni wanda ya sani makarantar ba haka kuma bai tambayeni dalilin da yasa na koma makaranta ba , kawai dai tunda safe yazo dana fito zan tafi yace muje in saukeki , kuma daya saukeni yacemin zai dawo ya É—aukeni , nace masa idan na gama zan kiraka saboda munayin lesson banza yayi yai tafiyarshi bai cemin komai ba ,

Caf lallai ni zaka sakawa rayuwata ido ? Hmm idan kasan wata baka san wata ba malam Dikko , wallahi sainaje asibiti naga kishiyar kakata , yauma "yan ajinmu dariya sukemin hada wanda bama aji ɗaya dasu an gayyatosu suzo suka ƙatuwa a JS 1 , nima dariya abun ya bani dan haka basu bani haushi ba ,

Ana tashi makaranta na fice saida naje fmc nayi waya da Dady nace masa yamai jiki ? Yace da sauƙi , nace kana asibitin ko kana office ? Yace idan ina asibitin miye ? Nace wai da ka haɗani da ita in mata sannu da jiki jiya da tunaninta na kwana ko da nayi sallah dare saida nayi mata addu'a Dady , murmushi yayi tare da godiya sannan yacemin yana Office ! Nace Allah ya sawaƙe ya bata lafiya yace am3n ya gode , mukayi sallama dashi ,

Bayan mun gama waya da Dady nace ma mai napep muje , tada motar yayi muka isa ɗakin , da tambaya na gano ɗakin da take a nuste na shiga da sallama , suka amsa min cikin sakin fuska tare damin sannu da zuwa , wuri na samu na tsugunna na gaishesu cike da ladabi tare da tambayarsu ya mai jiki ? Sukacemin da sauƙi nace Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne , suka amsa da am3n , wurin tsohuwar na matsa nayi mata sannu ta ansa da yawwa nace ni ƙawar Hafsa ce , tace Allah sarki aiko yanzu ta tafi ita da ƙawayenta nace Allah sarki , 5k na bata cikin kuɗin da ɗanta ya bani nace ayi haƙuri daga makaranta nake , godiya sukayi tayi tare da tambayata idan Hafsa tazo wa za'ace mata , nace ace mata uwar ɗakinsu ce , sukace da ance haka shikenan nace Eh kuma ai zan sake dawowa sukace Allah ya yadda , godiya sukayi sosai ni kuma na fito abuna.

Kai tsaye makaranta na koma saidai nayi sallah na shiga aji kuma malam yamin faÉ—a kar na sake na sake makara nace insha Allah .

A asibiti kuwa abinda yasa nace musu su faÉ—awa Hafsa uwar É—akinsu ce dan kada a faÉ—a Dady yana nan idan yaji Sultana kila hankalinshi zaikai kaina , tou dukansu babu wanda yasan nasan kowa a cikinsu , Dady nasanshi ya sanni , Hafsa ta sanni na santa amma gaba É—ayansu babu wanda yasan ina tare da wani a cikinsu , Hafsa tasan ni É—iyar Binna ce amma bata san ina da zuminchie da ita ba , Dady kuma bai sanni ba kuma baisan daga ina na fito ba yasan Binna amma baisan ni É—iyarshi bace ba , su kuma asibiti basu san ko wace ce ni ba ni kaÉ—ai nasan ko suÉ—in su waye.

Yauma sai gab magrif na koma gida saboda naje islamiya , kuma Dikko yayi masifa sosai yace har makaranta bokon bazan sake zuwa ba duk abinda nake idan ban sani ba motsina ɗaya a waje wallahi saman tafin hannunshi yake kuma ya faɗamun naje asibiti saboda kin ɗauke ni bansan abinda nakeyi ba ni zaki gayamin idan kin gama zaki kirani , wallahi kallonki kawai nakeyi amma ki sani koda gira kikayi magana nasan ƙafar dake miki ɗingishi ,

Na fiki hankali na fiki wayau nafi sanin rayuwa shekaruna da naki ba É—aya ba gogewa ta da taki ba iri É—aya ba duk wani wayau da kike tunanin kina dashi ni a wurina Xeyro , mu zuba dani dake tunda kin rainani zanyi miki maganin rashin kunya.

Nace yi haƙuri don Allah kuma dama ai kasan zan faɗa maka kuma saida na faɗawa mai gadi nace nabi ƙawata zan gano kakarta ko Yayana yazo , ki rufemin baki ke ɗaya kika shiga napep sannan kuma kika fito daga cikin makaranta kina waige² yaushe kikayi magana da mai gadi ?

Ba mai gadi ba malam na faɗa mawa , tou malam kika faɗa mawa koma dai waye na soke makaranta daga yanzu , dan girman Allah kayi haƙuri wallahi bazan sake ba , na gama magana yana faɗin haka ya wuce ɗakinshi , binshi nayi naci gaba da magiya ina bashi haƙuri , banza yayi dani ya wuce toilet yana alwallah , saida ya fito nace dan Allah kayi haƙuri Yaya Dikko , murmushi yayi yana maida agogonshi yace da kince Yaya cuta na zakiyi ya ƙarasa maganar yana kallona , nima murmushi nayi ina kallonshi cike da soyayya , shima cike tsantsar ƙauna yake kallona kowa ya kasa daina kallon kowa.

Dafa kujera yayi yace An mata wai a haka baki so na ko ? Ɗan turo baki nayi banyi magana ba , yace Hmm irin wannan kallo haka idan kuma kika fara so na wane iri zakimin kenan ? Kunya naji dan haka na juya na fice da sauri daga ɗakin murmushi yayi tare da cewa Allah ka kamamin zuciyar yarinyar nan kasa mata tsantsar sona da tausayin rayuwata , ubangiji ka ƙaramin haƙuri akan duk abinda zatamin ka wadatani da tausayinta ka bani ikon riƙeta da gaskiya ka kauda sharrin shaiɗan tsakani na da ita dama duk ko wane namiji dake zuwa gidan nan har ta gama zaman ta a gidan nan , ya ubangiji ka ɗauke idon duk wani namiji akanta , ka janye mata tunanin ko wane irin namiji saini ,

Ina shiga ɗaki saman katifa na faɗa tare da rufe idanuwana na kwantar da fuskata a saman bargo daɗi kawai nakeji Dikko yayimin murmushi kuma nasan wasa yake bazai hanani zuwa makaranta ba dan yaɗan latsani ne , wallahi Dikko ɗan gayene mai kyau na burgewa yanayin magana cikin salo mai ɗaukar hankali , ihu nayi tare da murginawa nace ina sanka mutumina , ina sanka ׳ , juyowa nayi na kwanta rigingine fuskata tana kallon sama na rungume hannaye na a ƙirji na lumshe idanuwana cikin yanayin jin daɗi nace kuma wallahi bazan sake tafiya na barka ba dan ina shan wahala idan bana tare dakai ,

Jiddah tsaye a gaban Al ' Ameen duk ta fita hayyacin tace ni wallahi na kasa , Al ' Ameen yace haba ranki ya daɗe kamar dai ba wayayya ba ? Saboda rashin wayau aiko ƙawarka mace bakya faɗa mata yadda kike kwanciya miji ba bare yaron mijinki , Jiddah tace ai idan ya kwanta dani baya sauka daga jikina sai bayan mintuna 15 , Al ' Ameen yace basai ki saukeshi da dabara ba ? Jiddah tace wallahi baya sauka , tsoki Al ' Ameen yayi yace haba Aunty Jiddah karki bari kiyi wasa da wannan damar ki sake jarabawa a ƙaro na ƙarshe mu gani , Jiddah tace to saidai idan ya dawo ya tafi Abuja Al ' Ameen yace Allah yasa ya dawo lafiya ta ansa da am3n ,

Haba Jiddah waye ya faÉ—a miki Dikko na Abuja.......?

14/10/2019

Taku a kullum mai san farin cikinku 👇🏻

*JAMILA MUSA...*💅🏻

⚜*BRILLIANT WRITERS ASSO🖊~{{-pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}

*KWARATA*
{{kalu bale gareku matan aure}}

*JAMILA MUSA* {Meelat musa}

sadaukar wa gareku,👇🏻

*ASMA'U ZAYYANA{{Asmeenat}}

&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿-----56

```kuyi hakuri yau baxaku samuba saboda matsalar charge da banda amma insha Allah gobe zakujini```

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 56

*_MAIMOUNATH O . G {{ Mahnoor }} ni bansan da irin kalaman da zanyi amfani dasu wurin miƙa saƙon godiya ta a gareki ba , idan zanyi ta rubuta ngode² sai cajin wayana ya ƙare ban gama cewa ngode ba , duk da haka dai ngode sosai Allah ya saka da alkairi ubangiji ya ƙara arziƙi ya ƙara zaman lafiya tsakaninki da naki master ya kawo zuri'a masu albarka..._*

*_Ummu Farhana ta sake zagayo muku da wani sabon salon labari nata mai taken FANNAH {{ marainiya }} hanzarta ki samu naki karki sake ki bari a baki labari , ina miki barka da fara sabon littafinki Allah ya taimaka yasa yadda kika fara lafiya ki kammala lafiya...!_*

Saida Al ' Ameen ya tafi sannan Jiddah ta koma ɗakinta cikin tashin hankali , ta zagaya ƙaton palon ta bata san adadi ba , mafita ta farko da zuciyarta ta yanke mata shine duk yadda za'ayi kawai a fara kamo mata Sultana , shawarata ta biyu kuma sai gata ga Dikko...

Wayarta ta É—auka ta fara kiran Momy bayan ta É—auka suka gaisa tun kafin a gama gaisuwar Jiddah tace Momy har yanzu dai kin kasa wani abu akan yarinyar nan , Momy tace waye yace miki na kasa.....?

Jiddah tace to ai naji shiru har yanzu babu wani ci gaba , murmushi Momy tayi tare da cewa kwantar da hankalin ki an gano komai nata tana shiga makaranta kullum da ƙarfe 7 da wani abu na safe ,

Tana fita daga makaranta kullum karfe 4 , daga nan tana wucewa islamiyya , tana zuwa a napep idan aka tashi kuma ta shiga motar makaranta ta sauka islamiya , yau ba'a napep taje ba ance wani yakaita kuma basu san ko waye ba ,

Momy tou mi yasa basu kamata ba ? Kinsan komai yana san bin diddiƙi kuma har yanzu sun kasa gano gidan da take zaune , saboda sunce daga Islamiya kullum take ɓace musu saboda tana amfani da abun rufe fuska { niƙaf } mafiya yawan ɗalibai dashi suke amfani , Momy basai an gano gidan da take zama ba nidai burina kawai a kamota idan ba haka ba zata iya sake sulɓewa , Momy tace babu damuwa ,

Sun dai daɗe suna saƙawa yadda zasu ci mutuncin Sultana idan aka kamota daga baya sukayi sallama , Jiddah kuwa taci alwashi idan har aka kamo Sultana tunda dai har take tarayya da mijinta tou tayi alƙawari sai tayi mata tsarki da ruwan tsidagu bayan ta jajjaga attaruhu ta zuba abonaki a cikin ruwa zafi zata zaunar da ita a ciki , sai taci ƙaniyarta yadda gobe ko ance tayi iskanci da Dikko sai tace ta tuba....

Kamar yadda na saba fita daga gida yauma haka na fito sanye cikin kayan makaranta na , a palo na samu Dikko zaune saman abin sallah ya jingina da kujera ya miƙe kafafuwanshi ɗaya saman ɗaya yana karantun al'qur'ani mai girma ,

Kallona yayi amma baiyi min magana ba , hannu na ɗaga mishi alamar saina dawo nayi gaba , gab da zan fita daga palon yace An mata nace karki je makarantar nan ko , cikin muryar lallashi nace haba Yayana na ƙarasa maganar ina kwantar da kaina nayi kalar ban tausayi , rufe al'qur'anin yayi yace nidai banajin daɗi , jikina yana min wani iri inajin kamar wani abu zai faru dake wallahi , nidai dan Allah kiyi haƙuri da makarantar nan !

Nidai zanje a haka , a kasalance ya lumshe idanuwan shi yace a , a , nace dan Allah , kallona yayi tare da cewa kiyi shiru zanyi fushi , zama nayi saman hannun kujera ina magana ƙasa² cewa kayi fushin mana ko an faɗa maka nima banda zuciyar ne ? Na ƙarasa maganar ina hararar bango ,

ÆŠan kintsa bakinsa yayi ya kallo inda nake yace banji abinda kika ce ba , ai dama bana so kaji , saboda kinajin tsorona ko ? Sallamar Ashiru ya hana na bawa Dikko ansa , gaishe shi nayi bayan na ansa sallamar da ina kwana , maidomin gaisuwar yayi da ina kwana ranki ya daÉ—e , kunya naji dan haka na kwantar da kaina jikin kujera banyi magana ba ,

Daga inda yake tsaya ya haɗa hannayen shi ta baya tare da rusunawa cikin girmamawa yace mai gida barka da safiya , yawwa Dikko ya faɗa a taƙaice ,

Matsawa yayi ya duƙa kusa da Dikko yana magana , ya daɗe sosai kuma banajin abinda suke faɗa amma duk yadda akayi gulma sukeyi , bayan ya gama maganar ya fita , shima Dikkon tashi yayi ya maida al'qur'an inda yake ajiyewa ya fita , nima na tashi nabi bayanshi...

A ƙofar fita mukaci karo , shi yana ƙoƙarin dawowa ni kuma ina ƙoƙarin fita , cikin faɗa yace ina zaki je ne wai ? Komawa nayi na zauna banyi magana ba , ciki ya koma bai wani daɗe ba ya fito , yana fita yace jeka kawai zanzo bayan la'asar in Allah ya kaimu ,

Saida Ashiru ya tafi Dikko ya dawo , ba tare daya tsaya ba ko ya kallo inda nake yace fita zanyi idan kina zuwa ki cire uniform in sai in tafi dake , kaje bazan je ba , sai kinje ya faɗa a dai² lokacin daya shige ciki....

Tunda naga ya daÉ—e bai fito ba raina ya bani wanka yakeyi zaman toilet sai kace mai jego , tashi nayi na É—auki jikkar makaranta ina na koma É—aki ,

Wayoyina na ɗauko na fara dubawa , tarin miss calls a wayar da Dady ya bani ya kira sau adadin da bazan iya ɓata lokacina wurin faɗar su ba , Alaji ya kira Aunty Suwaiba , Malam Ɗayyu da baƙin numbers wanda banda su a cikin wayana !

Cikin baƙin numbobin na fara kira , ana ɗauka naji ya fara babbaka min ashariya tare da cewa duk inda kike a faɗin duniyar nan idan na kamoki kwanakin rayuwarki ya ƙare , Lahaula wala kquwwata illa billahil aliyyul azeem , waye kai ...? Tsoro , tsoro ne , ni tsoro ne mai ban tsoro kuma na duƙufa akan cewa saina ɗan ɗana miki ɗanɗano tsoro sannan na kasheki ,

Na ganki nasan inda kike ƙoƙarinki ya ƙare kuma na tiso rayuwarki gaba saina ga kin shaƙe kinbi iska hankalina zai kwanta wuƙa zan caccaka miki a zuciya a wurin zaki mutu ko harbawa bazakiyi ba yau zan kashe ki....... Yanzu ne ? Ko anjima koma dai yaushe ne kici abincin bankwana gani nan tahowa.....

A firgice na juyo zufa ta tsatsanfomin dan ya faÉ—i kalaman nashi da kaushi , a wahalce nake fitar da lumfashi dan wanda baya cikin É—akin yana iya jin sautin fitar numfashi na , zufar goshina na goge da sauri na juyo Dikko na gani tsaye yace me ya sameki ne ?

Mutuwa zanyi..... Na bashi ansa kai tsaye , cikin rashin fahimta yace wace irin mutuwa kuma ? Cikin kuka nace nima zasu kasheni kamar yadda suka kashe Babana kuma suka kashe Aunty Mamy suka kashe wata Auntyn wacce ma bata samu damar isowa wurina ba suka shafe labarinta ,

Tsoki Dikko yayi ya juya yana aike kanki rawa yakeyi kullum baki gajiya da sakin layi kamar zararriya , yadda yayi min sai abun ya tunomin ranar da za'a kashe Babana daya faÉ—amin nace masa shirmen mafarki ne ni kuma yau gashi na faÉ—a amma ni an danganta ni da mai rawar kai.

A tsorace na sake lalubo wata baƙuwar lambar na sake kira , itama wata murya ce daban ta tabbatar min da mutuwa ta yau babu gudu babu ja da baya , kashewa nayi na kira wayar Dady bayan ya ɗauka muka gaisa na tambayeshi mai jiki yace da sauƙi , ya akayi baki je makaranta ba yau ? Ya tambayeni ,

Cikin faÉ—uwar gaba da dakiya nace naje mana , abinda naje makarantar ban sameki ba , nace da wane lokaci kaje ne ? Tunda safe ina bakin get in makarantar ban ganki ba , jinjina kaina nayi tare da cewa amma me yasa kaje kai tsaye bayan baka saba zuwa ba saika faÉ—amin zaka zo , yau shawara na sake shi yasa naso yi miki bazata kawai , yanzu kina ina ne ?

Kai kana ina haka ? Har yanzu ina bakin get in makarantar ku ? Ka jirani gani nan zuwa , ina faɗin haka na kashe waya , lambar Alaji na kira bayan na gama waya da Dady , tana shiga ya ɗauka ko gaisawa bamuyi ba yace Sultana kina ina ne ? Ina Lokoja na bashi ansa kai tsaye , wace irin Lokoja kuma ? Nace lokoja nawa ka sani ? Tou ke meya kaiki lokoja ? Idan aka ga kuɗi katsina aka gansu a lokoja abin mamaki ne ? Ai kuɗi yawo sukeyi babu inda basa iya zuwa a cikin ƙanƙa lokaci , nace to karkayi mamaki domin karuwa da kuɗi duk ɗaya suke yanzu nan zaka ganni anan zuwa anjima kuma in ɓace , nabar katsina ina lokoja , zai sake magana na katse kiranshi na kira Aunty Suwaiba , bayan ta ɗauka muka gaisa nayi mata sannu da jiki ta ansa cikin kulawa tare da cewa Sultana kina ina ne ? Aunty ina kaduna , yaushe kika tafi ne ? Tunda muka rabu da malam ɗayyu a katsina ranar nabar katsina da daddare !

Amma me yasa baki faɗamin ba , murmushi nayi sannan nace kiyi haƙuri Aunty , tsoki tayi tare da kashe wayar bata sake magana ba , tana kashewa na kira malam ɗayyu shima mun gaisa muka ɗan taɓa fira sannan yace min kina katsina kuwa ? Nace masa kana san gani ne ? Yace Eh nace ina Abuja , yaushe kika tafi ? Nace jiya da daddare , yaushe zaki dawo ? Sai bayan wata ɗaya ina faɗin haka na katse kiran malam ɗayyu.

Lallai kawai abinda zai faru , tabbas akwai masu farautar ruhi na , mutum ya bashi da tabbas kuma yakan iya canjawa a cikin ƙanƙanin lokaci , kuɗi sunkan canja mutum tsoro yana canja mutum , nacewa Alaji ina Lokoja , Aunty Suwaiba nace mata ina Kaduna , na faɗawa Malam Ɗayyu ina Abuja , Dady kuwa na faɗa masa ina Katsina....... Murmushi nayi tare da ajiye wayoyi na a gefen katifa dani daku mu zuba lumfashina yana hannun ubangiji idan mutuwa ta yazo wayau ko tsimi da dubara bazai hanani ansa kiran mahalicci ba , fatana Allah yasa inyi kyakkyawan ƙarshe.

Amisty da Bello zaune a mota , bayan ya kora mata wani birkitaccen sharhi ya ɗora mata da cewa yayi tarayya da Sultana ne ta ɗauki hoton videon abinda mukayi tana ta bazashi a social media gashi yanzu ta durƙusar dashi a harkar wasan caca idan Amisty zata iya tou da Allah ta kawo mishi Sultana ko ta faɗa mishi wurin da Sultana ke zama idan kuma bata sani ba ta binkico mishi inda Sultana take a cikin sa'o'e 24 zan bata naira dubu ɗari ,

Su Amisty anji zancen kuɗi dan haka tace ai sanin inda take ba abu bane mai wahala dan nima haƙe nake da ita saboda ta ɗauki tsiraicin mahaifina ta turomin , naso na ɗauki na ubanta nima na tura mata dan kai kanka kasan nidai Binna Allah kaɗai yasan iyakar abinda ke tsakaninmu , ina san Binna tunda nake ban taɓa huɗɗa da wani namiji ba sai akan Binna , shine ya koyamin ya gogar dani tun ban iya ba har na ƙware dan Binna aharkar mata yai zarra , na jaraba bin wasu mazan amma banji daɗinsu ba nayi niyar ɗaukar videon tsiraicin shi sai nayi tunani idan har ya sani nice nayi masa zai rabu dani ni kuma idan ya barni bansa ya zanyi rayuwata ba , kwatsam kuma sai ga mutuwarshi dan da na lashi takobin auren Binna dan in dasawa Sultana baƙin dafi mai wahalar amayarwa amma sam Binna yace bazai aureni ba.

Murmushi Amisty tayi mai cin rai tare da cewa Hmmm Allah ya jiƙan "yan maza a ƙiyama , Binna namijin duniya jajirtaccen namiji mai kafawa mace soyayyar shi a zuciyarta mai wahalar goguwa ya tafi ya barni da maraicinsa , na tsine kuma bazan daina tsinewa wanda yayi sanadiyar mutuwar Binna ba , amma a tsaye nake saman ƙafafuwana saina wulaƙanta rayuwar Sultana idan dai har ina numfashi a duniya...

Ta ƙarasa maganar tare da fara kiran wayar Sultana , ni kuma lokacin da kiran wayar Amisty ya shigo cikin wayata a lokacin muna gidan abokin Dikko su suna saman tebirin cin abinci sunayin kalaci dan tunda Ashiru ya kawo abin kalaci Dikko bai fito dashi daga mota ba yace idan yazo nan zamuyi kalacin tunda jiranshi akeyi wai wasu dokuna ne aka kawo mishi zai gansu , shi kuma abokin nashi ya uzira mishi wai zai tafi ɗauko matarshi ,

Ko ina zai ɗaukota Oho mishi , ɗaukar wayar nayi muka gaisa , bayan gaisuwa Amisty tace uwar room gaba ɗaya kin manta damu , miye duniya dake abu baya wucewa wurinki ? Da Allah kiyi haƙuri idan dai akan abinda ya faru baya ne muyi haƙuri abinda ya wuce ya zama labari muyi haƙuri dukanmu mu fuskanci sabuwar rayuwa ,

Labarin Babana ne ya dawo min a kaina da yace bayan nayi fushi da Bello saida yayi yadda ya yaudareni ya sake dawowa dani cikin rayuwarshi ya jagwalgwalamin rayuwa , murmushi nayi cewa ba komai Amisty ya wuce , to kina ina ne yanzu dan ina so inzo har gabanki in durƙusa a saman guyawuna in baki haƙuri , ina kano aiko yanzu ma sa'a kikayi kika sameni gab nake da kashe waya kiranki ya shigo ,

Amisty tace me kikaje yi kano uwar ɗaki ? Zanje Lagos ne kuma a jirgi zan tafi , tou yaushe zaki dawo ? Ƙarshen wata ina faɗin haka na kashe wayata murus ,

Shiru Bello yayi bayan ya gama jin wayar Sultana da Amisty , bayan wani lokaci yace ma Amisty jeki kawai zan dawo anjima , fita Amisty tayi daga cikin motar tana mishi addu'a Allah ya dawo dashi lafiya ta wuce ,

Fitar Amisty Bello ya dunƙula uwar ashariya yace lallai yarinyar nan ta ɗauki mutane "yan iska , dan duk wanda sukayi waya da Sultana banda Dady a gaban Bello akayi ta , saboda Bello yaje gidan Baba Ƙarami ya tambayeshi inda Sultana take a matsayinshi na aminin mahaifinta , Baba Ƙarami yace baisan inda Sultana take ba tunda shi Baba baisan baƙin halin Bello ,

Bello yace masa ko kasan mutanen da take huɗɗa dasu ? Kai tsaye Baba ya faɗi Alaji da malam ɗayyu , kuma duka mutanen nan babu wanda yasan Bello sunansa kawai sukeji , kuma babu wanda yasan akwai tsama tsakanin Bello da Baba , koda yaje wurin malam ɗayyu cewa yayi shi aminin Baban Sultana ne kuma yana nemanta dan ta tattaro mishi kan "yan gidansu ya taimake su , kuma ya kira wayar Sultana bata ɗauka kila bata ɗaukar baƙuwar number , shine yace malam ɗayyu ya kira Sultana suji ko tana ina ? Tunda shi tana da number shi ,

Da malam É—ayyu ya kira bata É—auka ba shine ya kira Aunty Suwaiba , kuma duk da suka samu damar yin waya da Sultana ta rarraba musu , tacewa Alaji tana lokoja , ta cewa Aunty Suwaiba tana Kaduna , ta kuma faÉ—awa malam É—ayyu tana Abuja da sukayi waya da Amisty kuma tace tana filin jirgin kano a cikin jirgi zasu tashi yanzu zuwa Lagos ,

Itama Momy da aka faÉ—a mata cewa Sultana bataje makaranta ba cewa tayi karsu sake su dawo sai sunganta ,

Shi kuma Bello bokanshi yace dole sai an kashe Sultana idan ba haka ba masifa da balbalin bala'e tsutsar magana zata cizar mishi harshe zai tonawa kanshi asiri duk abinda yayi zai faÉ—a da bakinshi makarin wannan masifa shine kisan Sultana....

Dikko kuwa bayan sun gama kalacinsu da kanshi ya tattara komai ya bani yace in mayar a mota , ansa nayi naje nakai mota na dawo na samesu a inda suke ta tattaumawa , maganar dokunan kawai akeyi a hankali abokansu suka fara cika gidan sai an zakuÉ—a doki yayi sama yana haniniya sai ayi mishi hoto , hanayi kawai ke tashi ganin inda muke tsaye mutane sun fara yawa Dikko yace in koma mota in jirashi yana jiran Umar yazo ne , dan abinda na lura shima gidan babu mata a ciki,

Wurin mota nazo na tsaya ina neman sa'a inyi waje , ina tsaye ina neman sa'a nake ganin rashin aikinyi na maza ko kuwa rashin sanin darajar kuɗi ne , dan naji wai duk doki ɗaya ana maganar miliyoyi gaskiya Dikko baisan darajar kuɗi ba , wato rayuwarshi zata ƙare a mota ne da dokuna sai yawon tsiya kamar kuɗi , na daɗe a wurin sannan Umar yazo.

Umar na shigowa na samu nasarar fecewa daga cikin gidan , da gudu na fita ina gudu ina ɗaura niƙaf ina ,gidan baya da nisa da titi saidai kawai ace anguwar gayu ba'a samun abin hawa tunda mafiyan su kowa da mota yake amfani ,

Wayar da Dady ya bani na ciro na kirashi yafi a irga amma bai ɗauka ba , na kirashi har na gaji yaƙi ɗauka , ganin bai ɗauka ba kawai nahau napep na nufi makaranta dan a tunanina yayi fushi na ɓata mishi lokaci ,

Ina fitowa napep da Al ' Ameen na fara cin karo ina ganinshi na nufi napep da gudu da zumar komawa , dan tunda Dikko yacemin Al ' Ameen baya so na yana biye da rayuwata dan ya ɓatamin suna yasa ina ganinshi na nufi hanyar komawa dan karya bawa Dikko labari ya ganni tare da wani , yawwa gata can ku kamota , inajin ance a kamoni ai banma yi gigin komawa napep ba na ibi santa nabi ta lunguna na yanki fili naci gaba da gudu , ai kamar kura taga kare haka suka biyoni da gudu , ganin da gaske ni suke bi yasa na sake tattarewa naci gaba da gudu kamar raina zai fita.

Dikko kuwa bayan Umar yazo ya dawo mota bai samu Sultana ba , idan hankalinshi yayi dubu ya tashi da guda² cikin palon ya koma dan a tunaninshi ko ta gaji da tsayuwa ta koma ciki , ya duba bai ganta ba ya dawo ya duba iya inda yasan mutum zai iya lafewa a gidan babu Sultana babu ma mai irin siffar mata a gidan kawata² ,

Wayarshi ya ciro daga cikin aljihu ya fara kiran wayarta amma a kashe , dan tunda ta gama waya da Amisty ta kashe wayar , cikin tashin hankali Dikko ya shiga mota ya fita daga gidan da gudu wallahi kai tsaye makarantar su Sultana ya nufa dan a iya fahimtar da yayi mata tana da taurin kai da kafiya abinda tasa kanta shi zatayi bata jin bari kuma bata san yi haƙuri ba , tunda tasawa ranta zuwa makaranta yasan sai taje can wallahi.

Shi kuma yau yayi alƙawari idan harya kamata sai taji babu daɗi saiya jagula mata rai yadda ko baya nan idan yace mata kar tayi abu zataji tsoron fushinshi ,

Ta wata ƙatuwar santa na ɓullo ina ta raba idanuwa kamar nayi ma sarki ƙarya , ina ta murna na samu wurin ɓoyo , duƙawa nayi tare da cire niƙaf ɗina ina fita da hijabina dan nasha gudu zafi ya tasomin , ɗan lumfashe idona nayi ina maida numfashi bayan na sarara buɗe idon da nakeyi mukayi ido huɗu da Bello , kamar a mafarki da sauri na ƙara buɗe idanuwana wata irin harara ya zabgagamin bara'uban nan wani irin tsalle nayi na haura wata katanga na tsula da gudu Bello ya biyoni , tashin hankali abinda na ambata kenan yayin dana juya naga rundunar da suka biyo bayana , ga masifar yunwa da nakeji duk yau babu abinda naci gashi juwa ta fara ibana , har bana ganin gabana sosai saboda wahala......

Dikko kuwa bayan yaje makaranta yayi bincike ce masa akayi Sultana bata zo ba , jinjina kai yayi cikin tsananin ɓacin rai wallahi idan har An mata ta bari ya kamata yana cikin fushin nan kashin ta ya bushe ,

Bello kuwa cewa ya farayi wayyo jama'a ku tare ku taremin ɗiyata ku agazamin don Allah , dariyar mugunta nayi tare da addu'ar Allah yasa masu bin bayana su riƙe Bello suce tunda shine ubana su bashi azaba mai tsanani.........

13/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 57

Follow me on wattpad meelatmusa

Muryar Al ' Ameen naji yana cewa daga duniyar mutuwa ka dawo bayan ka mutu kuma kowa ya sani , Bello yace wallahi nine ubanta ni na haifi abuna ku baku lura da kamin mu ba shi wancan ai uban riƙonta ne , cikin shashsheka ta wanda yasha gudu harya gode Allah ya ɗaga murya cewa ki tsaya mu tafi gidan Sultana , muryar wani daban naji shima cikin haki yace kai kuma neman me kake mata ?

Allah ya kama bakin Bello yace wasu ke harinta kuma kasheta zasuyi shi yasa zan tafi da ita in ɓoyeta , shi a tunanin shi wannan wayau ne , domin gani yake idan ya kamani ko wani abu ya sameni baza'a zargeshi ba , a gajiye na kurɗo ta wani siririn lungu na sake bullowa bakin get in makaranta mu , kai tsaye na hawo titi yayin da Al ' Ameen ya ɗauki wani irin lafiyayen dutsi ya saitani ya jefoni da ƙarfi , na tafi tangal² zan faɗi kafin in gama saita kaina ya sake dan ƙaromin wata jifar ,

Jama'a suka fara kai ׳ lafiya ? Al ' Ameen baya saurarar kowa gaba ɗaya sukaci gaba da jifata kamar muslmin da yayi ridda yayin dana raba tsakiyar titi biyu na kasa gaba na kasa baya , tsayuwar da nayi ne na kasa tafiya saboda jifar dasu Al ' Ameen sukayi min suka samu nasarar riƙeni sukaci gaba da dukana wai na basu wahala yayin da suka kasu gida biyu wasu suka riƙe Bello suna kai ɗan iska kaine ka ɗaure mata ƙugu take abinda taga dama ko ?

Kai tsaye yace Eh , saida suka bashi kashin bala'e ko motsi baya iyayi sannan suka ɗaureshi suka jefa banza mota kamar kare , lokacin da aka kai Bello mota aka dawo neman Al ' Ameen aka farayi amma tuni yayi layar ɓata babu wanda yaga ta inda yabi ya wuce.

Gaba ɗaya hankalin kowa ya koma wurin Dikko dake zaune cikin mota yana kallonmu , a tunanina ni bai ganni ba , dan haka ina ganin sun juya hankalin su ya tafi wurinshi nima na samu sa'ar ɓacewa daga wurin , cikin ƙanƙanin lokaci na isa gida jikina sai ciwo yakemin ina zuwa wanka nayi da ruwa masu ɗumi , bayan na fito na canja kaya naje na zuba abinci naci nayi kwanciyata ,

Gaba É—ayansu wurin Dikko suka nufa cikin farin ciki dan ba saboda Dikko suka saki Sultana ba sundai tafi maularsu ne kawai , kuma shi kullum ranshi a haÉ—e yake shi yasa baka iya gane a wane irin yanayi yake farin ciki ko damuwa ,

Sudai umarni kawai aka basu su kamo Sultana saboda haka basu san komai game da ita ba , sundai ga Dikko kawai sunzo su gaishi dan sun san zasu samu kuɗi ne a wurinshi shi yasa suka saki reshe suka kama ganye , suna isowa suka fara kirarashi irin dai yadda "yan maula sukeyi , kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke kanshi yana so yaga ta ina Al ' Ameen zai ɓullo ,

Shi kuma Al ' Ameen bayan wasu mintuna a tunaninshi Dikko ya tafi dan haka ya fito daga maɓoyar shi , fitowar da zaiyi yaga Dikko dan haka baiyi gigin komawa wani wuri ba ya nufi mota da gudu ya shiga yaja ya tafi a haukace , da gudu Dikko yabi bayanshi dan yayi alƙawari yau da Al ' Ameen da An mata babu abinda zai hana ya tabbatar da baƙin ciki a zukatansu ba ,

Abinda yasa zai ci mutunci Al ' Ameen saboda yadda yaga yana jifar An mata ya wulaƙanta mishi "Yar matanshi kuma shima sai ya wulaƙanshi ko da kuwa haka zaiyi sanadiyar gogewa farin ciki daga rayuwarshi har ƙarshen numfanshin shi , in banda ƙasƙanci "Yar mata ma zai jefa ? Kuma saman titi kowa yana wuce yana gani sai kace ta aikata wani babban zunubi....?

Ita kuma yau zai nuna mata shi cikakken mai zuciya ne in bata san haukarshi ba yau zata sani kuma zatayi baƙin gani da dana sanin saninshi tunda yana tausaya mata bata sani ba , ya ɓarar da farin cikinshi da komai ya zauna tare da ita dan dai ya sama mata farin ciki da natsuwa , yabar matarshi ya taho wurinta shi zata maidai baisan abinda yakeyi ba , zuciyarshi kuma sai ƙara tunzurashi takeyi tana hasko mishi irin balbalin azabar da zai horar da ita da ita.

Ai jima yayi bazai iya bin Al ' Ameen ba saiya fara da An mata , wani irin mahaukacin burki ya taka ya fara ƙoƙarinyin kwana saman tsakiyar titi yayin da mutane suka fara kaucewa dan kar ya gogar musu abin hawa , aiji yayi ma bazai iya tsayawa ɓata lokacin yin kwana ba , da ribos ya fita daga titin yana kai ƙarshe ya juya sitiyarin motarshi ya yanki hanyar goruba , yanda yake tuƙin ne yasa hankalin jama'a ya tafi wurinshi , yayin da wasu ke cewa ko lafiya wancan wasu kuma na cewa ai shi dama haka yake wannan iskanci babu abinda ya dameshi da rayuwar da wani zai shiga shi kanshi kawai ya sani dan Allah ya basu damar duniya shi yasa basu san darajar kowa ba , a , a gaskiya sun san darajar mutane shi dai kaɗai keda wannan halin , waye wai ...? Wani ya tambaya.

Dikko ne ai shi kaɗai keda wannan baƙin halin mahaifi shi ba haka yake ba , wasu kuma cewa sukeyi ai ɗan iska ne , yayin da wasu kuma suke cewa aini burgeni yakeyi ko nine matashin da na samu irin damarshi saina fishi iskanci kasan su kuɗi jigo ne masu nuna isashshen iko ku barshi yayi Allah ya bashi gara yaji da ƙuruciyarshi wata rana ko ance yayi shekaru sunfi karfinshi baya iyawa , wani yace gaskiya izzar kuɗi da ƙarfi take muma Allah ka bamu masu amfani dan idan kana da kuɗi ji kakeyi kai kafi karfin kowa ka taka wanda kake so ka murje wanda ya shiga gabanka , magana dai ce ta kuɗi su zasuyi bayani kuma da kansu kuɗin zasu baka hakuri kuma ka haƙura , niko dai nace hmm ita dai rayuwa duk abinda mutunci baiyi ba rashin mutunci bazai yi ba , idan an ciza dai a busa dan ita duniya bata da tabbas yanzu takeyin ka anjima ta barka , idan ka raga sai ta raga maka dan duk abinda kake tunani kafi karfinshi sai a wayi gari ya gagareka Allah dai yasa mu dace ,

Bansan ta inda ya biyo ba kuma banji shigowar shi ba ina kwance dan har na fara bacci saboda gajiya , bansan yadda akayi ba kawai dai na farfaɗo naga ana ta riƙe Dikko yana wata irin zabura yana magana da turanci saidai inji yace An mata sai yace Momy yace Dady ,

Jini na gani a jikina bansan ta ina ya biyo ba , duk inda na shafa fuskata jini ne bansan da ina da ina ya fasamin ba , tunda nake ban taɓa ganin irin masifa ta Dikko ba ɗan bala'e ne na ƙarshe duk taron abokanshi sunfi su nawa amma wallahi girgiza ɗaya yakeyi ya zuddasu sai su sake riƙoshi so kawai yake ya iso wurina amma sun san idan ya sake riƙeni tawa ta ƙare ,

Ciƙin ɓacin rai yaci gaba da magana da hausar shi irin kamar bata riƙe mishi baki sosai ba wata irin magana yakeyi , kuma ba irin ta yare ba wata irin murya dai gareshi cikin sanyi yakeyin magana ko yana fushi maganarshi bata canjawa yarinyar can saboda ta ɗaukeni ɗan iska har marina tayi , yana nuna inda na mareshi yaci gaba da cewa idan aka buɗe min fili da irinki dubu duk wanda nayi ma duka ɗaya ya tafi bazai sake dawowa ba har abadan abada ko kina ganin tsoronki nakeji ? So hauka ne ? To ki sani bani na ɗora ma kaina ba Allah ya jarabceni kuma kema idan ya juya alƙamin sa akanki naki ya ƙare ƙaramar yarinya dake babu abinda ke cikin kanki sai wawanci da ƙuruciya , ke banda ƙaddara da hukunci Allah har kin isa kisha inuwa ɗaya dani ina ɗaga miki bakya gani tou yau ƙaryarki ya ƙare saina raba gangar jikinki da ruhinki , badai ina cewa kada Allah yasa kiga fushina ba ko ? Yau yazo kuma bazai tafi ba kin bani ׳ ya ƙarasa maganar yana nunani da ɗan yatsa , kwacewa yayi daga riƙon da sukayi mishi ya fita ,

Wani abokinshi da naji yana cema Yazeed yace ke An mata kike baki kyautawa abinda kikeyi ba'a rayuwa haka yana ƙoƙarin kare miki mutuncinki da martabarki bakya gani , tunda yace karki je dole sai kinje , yace miki bayajin daɗi yaji wani abu zai faru dake ai sai ki tausaya mishi kamar yadda yace miki jarabta ne daga Allah kiji tsoron jarabta ya dawo kanki , ke da kinsan halin DK da kuɗi idan yace kar kiyi wani yace kiyi zakiji tsoron fushin shi , Allah ma ya rufa miki asiri da mutane a gidan yau da kin gwamce ma aya zaƙinta ,

A tsiwace nace dan naje kawai sai ya dakeni ko ni baiwa ce ne ? Da mamaki Yazeed ya kalleni yace tou ai da yake yanzu zai dawo sai ki tambayeshi abinda yasa ya dakekin yama iya saka suna da yace miki An mata... "Yar ƙaramar yarinya dake sai tsattsaga masifa Dikkon ne ma dai² dake.

Dama nace kaine dai² ni ? Dariya yayi yace ai riƙon mahaukaci sai sarki , nice mahaukaciyar ? Yace ah ah karin magana ne ni na isa ince miki mahaukaciya ai ke da ss kikayi kama sarkin bincike , dariya sukayi tare da tafawa suka koma palo sukaci gaba da kallon boll insu.

Wallahi Allah yau sai an faɗamin abinda yasa ba'asan An mata a gidan nan , laifin me tayi muku ne wai ? Momy tace na tsani yarinyar nan Dikko idan zakayi rai kayi rai idan zaka mutu ka mutu dan ubanka bansan yarinyar nan kuma har abadan duniya bazan taɓa santa ba , kuma har gobe har jibi ina nan zaune akan bakana sai an kamo min ita kuma saina wulaƙanta mata rayuwa kamar yadda nayi alƙawari bazan fasa ba ,

Haba Momy wai me tayi miki haka da ciwo don Allah ? Me tayi min ma kake tambaya ko ? Tou ubanka tayi min kaji ko ? Momy bana so ayi abinda za'azo aji babu kyau ki sauƙaƙa zafin ƙiyayyarki akan ta kafin aji wani iri wata rana , ko wata ranar tazo banajin komai kuma babu abinda zai faru idan wanda ya mutu zai dawo naga yadda zakayi ka auri karuwa ina numfashi ,

Wai waye yace karuwa ce ? Abinda kowa ya sani duniya da mutane sunyi mata tofin Allah barbaÉ—e , murmushi Dikko yayi mai ciwo yace duk bakin daya tofawa An mata Allah tsine insha Allah saiya tofa mata albarka babu daÉ—ewa ,

Momy tace mahaukacin banza ka taɓa ganin albarka ta sauka akan tsinuwa ? Ko ka taɓa ganin iccen da tsawa ta faɗa ma ya sake tofowa ? Ai tsawa so ɗaya take faɗawa icce ya mutu shikenan ya gama rayuwa a duniya dai , juyawa Dikko yayi bai sake magana yana tafiya cikin yanayin mai wahalar fassaruwa ,

Yace gaskiya ne nine tsawar da na sauka akan An mata , kuma Allah zai taimakeni ita bazata mutu ba zata rayu cikin farin ciki kuma zatayi ganye tayi rassai zata zama alfahari a wurinki Momy idan har na auri An mata zaki sameta mai biyayya , ajiyar zuciya ya sauke dakel tare da lumshe idanuwanshi a bayyane yace Allah dai ka taimakeni a gano min inda mahaifiyarta take da wuri in miƙata cikin aminci da salama.

Harya taho bai samu nasarar ganin Al ' Ameen ba amma ya ja mishi layi zasu haɗu komai daɗewa kuma wallahi yadda ya jefi "Yar matanshi sai yayi mishi wulaƙanci na kafa tarihi marar gogewa a rayuwa.

Da tunanin Sultana ya isa gidanshi baiji daÉ—in abinda yayi mata ba amma ya zama dole ya koya mata tsoronshi dan idan harya aureta da wannan taurin kan nata matsala za'a samu , dole ta yadda shine a samanta kuma dole ta koyi bashi girma idan dan tana ganin murmushin shi zaisa ta rainashi zai tsare girmanshi bazai ma sake mata wasa ba tunda ita bata da wayau ,

Cike da tsantsar sha'awar kasancewa da Jiddah ya shiga gidanshi , shi baisan abinda yasa idan harya haɗa jiki da An mata yakanji yawan buƙatar kasancewa tare mace ba , dakel yayi wanka yana fitowa ya samu Jidda zaune a gefen gadonshi tasha wanka na ɗaukar hankali sai zabgaga ƙamshi takeyi mai tada hankali duk mai wata "yar guntuwar sha'awa ,

Cikin bariki ta fara mishi sannu da zuwa dakel ya ansa dan rabi da kwata hankalinshi baya nan ya tafi wata duniyar , yau tafiyar safe kayi my excellency ? Kallonta yayi tare da tambayarta ina naje ? Murmushi tayi mai ɗaukar hankali tace Abuja mana , waye yace miki ina Abuja ? Ai naga kwana biyu baka nan nasan kuma idan kana gari ina zaka je bayan gani ta ƙarasa maganar tare da "yar karairaya dai ta matan da suka san hannunsu wurin iya tattalin miji ,

Wani irin kallo yayi mata mai tayar da tsikar jiki cikin salon tafiya da hankalin mace yayi magana cewa Ey to miye ? Yayi maganar tare da miƙa mata hannunshi , tasowa tayi bayan ta bashi hannun nata saida ya sumbaci bayan hannun sannan ya buɗe tafin hannun yayi tsini da harshenshi yayi mata wata irin lasa a tsakiyar tafin hannun nata ya ƙare da sumbatar inda ya lasa ciki tako mai nuni da yayi rashinta , lumshe idanuwanta tayi tare da sauke ajiyar zuciya cikin yanayi mai nuni da saƙonshi yazo.

Jiddah fa ba'a baya ba shima Dikko jajirtacce cike da kulawa da junansu suka shiga masayar soyayyar ta hanyar ƙoƙarin dasawa junansu farin ciki irin na ma'aurata daga baya aka koma saman gado domin doguwar tafiya dole saida guziri , suma dai sunyi ma kansu guzirin gado , a sama aka caskale yadda ya kamata saida Dikko ya tabbatar ya kore duk wata tsohuwar ƙishirwar dake tattare da ita sannan shima ya samu natsuwa , amma wani abu da Jiddah tazo dashi shine ,

Kai tsaye ta nunawa Dikko kwalbar da bokansu ya bata cike da rashin wayau tace Yaya da Allah ka ɗan taimakamin , idonshi a rufe yana samanta bai sauka ba yace wane irin taimako ? Wani magani ne zan haɗa kuma da sinadirin namiji ake amfani dashi dan Allah ɗan kaɗan zaka zubamin anan ta miƙa mishi kwalbar , jin kwalba a hannunshi yasa ya buɗe idanuwanshi yace wane irin magani ne ake haɗawa da najasa dan tsabar ƙazanta ,

Nidai don Allah , tou ke me zai hana baza kiyi da naki ba tunda kece kike ra'ayi , ai na namiji akace , um umm aini ba namiji bane ba , nidai haka nan don Allah murmushi Dikko yayi a rashin shi yace kila wani fahami aka bata ta jiƙamin a soɓo mata ni sharrinku ai sai in rubuta littafi tunda cikinku nayi rayuwa , kallon agogo yayi ya jinjina kanshi yace da 15 yanzu zan koma 20 duk masifarki lokacin ya tafi bazai dawo ba , wato harma na namiji ,

Jiddah taci gaba da dan Allah dan Annabi , banza Dikko yayi bai mata magana ba , saida lokacin daya iba ya cika ya sauka daga saman gadon ya nufi toilet , bayan mintuna 30 ya fito , ƙananan kaya ya saka bayan ya feshe jikinshi da turare ko inda Jiddah take bai kalla ba ya ɗauki wayoyinshi ya fice.

Yana fita ta ɗauki wayarta ta kira Al ' Ameen ta rattafa mishi yadda sukayi da Dikko , faɗa yayi mata cewa haba ranki ya daɗe ya akayi kikayi wannan kwaɓar kinja ma kanki nayi imani da girman Allah mai gida ya taso ki gaba da bin bincike kinja mana kuma ki rubuta ki ajiye wallahi ko ruwan gidanki bazai sake sha ba , ke kina wasa da mai gida ? Wai kin kuwa san yadda yakeji da rayuwarshi ? Kai gaskiya kin ɓata wallahi mi yasa kikayi haka ???

Jiddah tace no ka gane Al ' Ameen wannan ba damuwa bane ba idan haggu taƙi kawai mu dawo dama , ka bari saura sati ɗaya na fara period sai in zuba kawai ka kai mishi , tunda malam yace idan akayi amfani da jinan al'adata sai yadda nayi da Yaya , sperm in nashi ne yace idan anyi amfani dashi za'a goge mishi ko wace mace daga zuciyarshi saini ɗaya...

Ba haka Al ' Ameen yaso ba kawai dai yace to , bayan sun gama waya da Jiddah ya kira Mardiyya tana ɗauka yace Doughter zan shigo kaduna zuwa cikin sati na gaba yaushe kike fara al'adarki ? Uncle meya faru ? Boka yace a kawo sperm in mai gida tou naso ace an samu amma matar tashi wata aljihun gefe ce ta kasa , wai dan wawanci irin na sakakkin "ya "ya kawai taba mai gida kwalbar wai ya zuba mata maniyinshi kiji hauka da ɓacewar hanya , dariya Mardiyya tayi tare da cewa Uncle ni zanzo in kawwo ƙarshen film in nan haka nan ,

Al ' Ameen yace karki zo dan in faÉ—a miki yauma nemana yake saboda tsigaggiyar yarinyar nan , yanzu dai yaushe kike fara naki jinin ? Mardiyya tace jiya na fara , Al ' Ameen yace tou zan shigo kadunar gobe in ansa in kaiwa boka , dan dama nama boka bayani akan ki zai haÉ—a maganin kinga idan akayi sai a kawo ma Jiddah sai mu samu tayi mana amfani dashi wurin ba mai gida , tana jiran taji soyayya sai kawai tajita a out... Cikin jin daÉ—i Mardiyya tace na gode Uncle Allah ya kawo ka lafiya yace amin my doughter ki gaishe da Yaya saina zo , zataji sukayi sallama.

Wallahi ni ba Babanta bane ba , wani irin mari aka wanka mishi harsai da haƙorinshi na ƙurya ya fita , cikin kuka yace wallahi ranka ya daɗe ɗiyar abokina ce , wani ne yakai mishi duka a ciki tare da cewa idan tafi ƙarfinka batafi karfin hukuma ba , Bello cewa yakeyi wallahi ranka ya daɗe ba "yata ce ba , saida sukayi ma Bello lullusar fitar hayyaci sannan suka wurgashi a cell suna cewa idan ka kawota sai mu fitar dakai.

Nayi ² na tuna abinda ya faru dani ban sani , na kasa sanin ta yadda akayi Dikko yayi min wannan dukan har yajimin ciwo ba tare dana sani ba , ko dami ya dakeni ? Duk yajimin ciwo fuskata kuma duk sahun mari ne lallai duk yadda akayi bugun bala'e yayi min tou meya ɓata mishi rai haka .... ?

Dakel nayi sallah isha'e kafin in tashi daga inda nayi sallah masarar ta lulluɓeni kasa komawa nayi saman katifa duk jikina ciwo yakemin na kasa wani ƙwaƙƙwarar motsi gaskiya nasha azaba ta ban mamaki a ranar nan !

Tunda na kwanta ban iya wani isashshen motsi ba har gari ya waye , haka na tashi jikina yayi tsami dakel na iya yin wanka nayo alwallah dan yau na makara tunda na kwanta sai 8:39am na farka ,

Bayan nayi sallah ko mai ban shafa ba na saka kayana na fita palo , kamar jiya yauma yana zaune a inda ya zauna jiya ko inda nake bai kalla ba ya ƙaddara ma baisan Allah ya ajiyeni ba , daga nesa dashi na tsaya nace ina kwana ,

Bai ansa ba , kuma bai kalleni ba hankalin shi nakan wani littafi yana dubawa , wuri na samu na zauna kamar an sani na zame gefen hijabin nace duk wanda jamin ciwo anan ban yafe mishi ba , kuma tafiyata zanyi tunda bansan abinda nayi maka ka dakeni ba , na ƙarasa maganar ina kuka ,

Ba tare daya kalleni ba yace An mata zo nan , tashi nayi na tafi kusa dashi ina kuka , wuri ya nunamin na zauna , cikin tausayi ya kalleni yace nine baki yafe mawa ba ? Ni badai nake ba , to dawa kike bayan dagani saike a palon , aini ba kai nake jama Allah ya isa ba , to kin yafemin ni ? Kaina na ɗaga alamar Eh , yace kiyi haƙuri ni bana iya sarrafa fushi bansan abinda yake damuna ba idan nayi fushi saina sauke ki daina ɓatamin rai kinga dai ina sanki bana so kina shiga rayuwa mara kyau , kowa dariya yakemin wai An matar ma da nake taƙama da ita abida batajin magana kuma bata so na , kinsan me nake cewa ?

A , a , na bashi ansa , kyakkyawan murmushin shi yayi tare da tsareni da idanuwanshi masu ɗaukar hankali yace ai nasan zaki faɗa ya ƙarasa maganar yana min hararar so , murmushi nayi cikin jin daɗi na gyara zamana ina kallon kyakkyawar fuskarshi gaba ɗaya sai naji masassarar da nake ji babu , yace ko nayi ƙarya ? Girgiza kaina nayi alamar a , a ,

Shi kuma yaci gaba da cewa ni ko nace zanyi fushi dake wallahi ƙarya nake bazan iya ba , da kinsan yadda kike da mutunci da daraja a wurina da kin daina wahalar da zuciyata da taki , kina ta fama da wahalar dakon so bayan nasan yanzu idan har zamu rabu sai kinyi kuka , tafiya zata iya riskata a ko wane lokaci zan tafi na barki da tunanina babu dare ba rana , zaki kasa bacci dare zai miki nisa wurin kwanciya zai miki girma zaki ga rana ta daɗe bata faɗi ba yayin da kika tuna Dikko baya tare dake , kawai ki daina wani ɓoyewa ki faɗi abinda ke cikin zuciyarki nidai tuni na faɗi nawa , ya ƙarasa maganar tare da miƙomin ɗan yatsan shi mu shirya , dan kinsan jiya na ɓata dake....

Miƙa mishi ɗan yatsana nayi ya lanƙwashi shi da nashi yace faɗamin me yasa bakya so na ? Shiru nayi yace amma ai kina so na mi yasa kike ɓoyewa ? Rufe idanuwana na nayi yace yi haƙuri An mata faɗamin matsayaina a wurinki me yasa kike min wasa da zuciya ,

Cikin kuka nace a wata rana kayi magana akan idanuwa na , to wannan ranar tayimin naji kamar in rungumeka a wannan ranar sannan nace ina sanka ,

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke da sauri tare da dafe dai² zuciyarshi da duka hannunshi biyu ya kwantar da kanshi saman kujera tare da lunshe idanuwanshi yace me yasa baki faɗa ba a wancan lokacin An mata ?

Shashshekar kuka nayi tare da cewa saboda ina tsoron kada na rasa ajina , sauko kanshi yayi ya kalleni yace wallahi Allah babu ranar da ajinki ko wani mutuncinki da zai rage a idona ko a zuciyata , ki taka yadda kike so ina tare dake tsakanin rayuwa da mutuwa , waccan ranar kinji kamar zakice kina so na , yau fa ? Yauma kinajin kamar kina so na............?

Su Yazeed ne suka shigo palon , cikin zaulaya yace An mata an shirya kenan a dai² lokacin daya iso yaba Dikko hannu suka tafa , bayan sun tafa Dikko yace aimu bama faɗa ko An matana ? Jiya ma sheyɗan ne yazo kuma mun koreshi bazai sake dawowa ba ko ? Shiru nayi zan tashi ya riƙoni tare da turani saman kujera shima ya dawo kusa dani ya zauna su Yazeed suka samu wuri suka zauna ,

Yazeed yace zakaje ko ka fasa ne ? Ya tambayi Dikko , ɗan gyara bakinshi yayi ya riƙe leɓonshi na ƙasa dana sama yace gaskiya banajin zanje , a , a kar kayi haka kayi haƙuri ko daga ƙarshe ne muje ai yafi bamu je ba , kallona Yazeed yayi yace ai kema zakije ko "Yar mata , dogon kallo Dikko yayi mishi sosai sannan ya kalleni tare da nunamin inda makullin mota yake yace jeki ki ɗauko abinci a mota , saura idan kinje ki ƙara gaba......

ÆŠaukar makullin nayi na fita........

17/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA...*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 58

Follow me on wattpad meelatmusa

Ina zuwa jikin motar na buɗe na kame a mazauni driver na tada mota na gyara parking kawai dan neman magana , Yazeed yace ga mutuniyar ka can zata fita , murmushi Dikko yayi tare da cewa wai dan in fita inta hayani so take ta maidani lusarin namiji , fitowa nayi na buɗe but in motar na fara fiddo ƙattin food flakes ina ajiyewa ƙasa.

Ban gama fiddowa ba Dikko da Yazeed suka fito a dai² lokacin da aka buɗe get Umar ya shigo saman doki wasu motoci biyu kuma suka biyo bayanshi , ɗaukar ta miya nayi na nufi hanyar shiga palon ina zuwa na tsaya kusa da Dikko nace ka ɗauka fita zanyi ko ? Kallona yayi bainin magana ba , murmushi nayi tare da cewa dama dan inji yadda zaka ce , yadda zance ai a jikinki zakiji idan kin fita zaki dawo ki sameni ni kuma zan ɗora miki a inda na tsaya bazan gaji ba , yana faɗin haka ya gangare yana ba Umar umarni ya ida shigar da abincin ciki.

Ina ajiye miyar É—aki na koma na kwanta , shi kuma Dikko mota ya koma yana cema Umar ka taho da allurar ne ? Innalillahi bara in koma in É—auko ya faÉ—i maganar yana mai lalabu aljihunshi ya fita da sauri daga gidan.

Umar yana fita Yazeed yace DK yarinyar ka fa ta koma , gaba ɗaya hankalinshi yana cikin mota yana dube² yace ai zata fito yanzu , Yazeed ya fara ƙwala min kira An mata Dikko yace me zata maka ne ? Dariya yayi tare da cewa da Allah barta ta fito insha dariya , tsoki Dikko yayi yana fitowa daga cikin mota yace to ita abokiyar wasanka ce ?

Yazeed yace dan Allah barta ta fito , Dikko yace to ai bani ne na hana ta fitowa ba ita idan tanajin yunwa ragguwa take zama ya ƙarasa maganar yana leƙowa ta window ɗakina yace me ye ? Ba komai na bashi ansa ba tare dana kalli inda yake ba , taso ki zo ina kiranki , ba tare da nace tou ba na tashi na fito wurinsu.

Yazeed yace ke "yar yarinya sai kiyi ta zama a ɗaki sai kace mai jego ? Ki fito kisha iska sai fama kike da hijabi kamar matar mamaci , murmushi Dikko yayi yana kallona yaɗan shafo gemunshi da bayan hannunshi ta ƙasa yana cewa kai wallahi wannan matar ustaz ce ko An matana ? Ya ƙarasa maganar yana ɗagamin gira , murmushi nayi tare da matsawa kusa da Dikko hannu na yaja ya maidani mota yana cewa wani wuri zamuje kina zuwa in tafi dake ?

A , a , ni banajin daÉ—i , tou meya sameki ko kema in miki allura ne ? Wace irin allura ? Allura nawa kika sani ne ? Idan mutum baya lafiya akeyi , Dikko yace to aikema kince bakyajin daÉ—i idan nayi ma doki kema sai in miki amma bazan miki da zafi ba , ni doki ce ? Nayi maganar ina harararshi , murmushi yayi yace An mata kenan kanki baya É—auka dana faÉ—a miki wata magana idan ma dokince ke da kanki zaki faÉ—amin ,

Ɓata raina nayi nace kaina baya ja ? Dikko yace ba haka nake nufi ba ina nufin kinyi "yar ƙarama ni babba dani in zauna in ta sakin layi , idan na faɗa miki baza ki bani ansa yadda zanji daɗi ba ina iya faɗa ki dangana abun da wani shirme daban ki bani ansar da zata ɓatamin rai shi yasa kikaji nace haka......!

Tou amma sai kace kaina baya ɗauka , Dikko yace a , a karfa muyi haka dake wai me yasa kikemin bahagguwar fahimta ne ? Kanki yana ɗauka mana abinda nake nufi maganganuna ni idan nayi miki sun girmi kwalwarki da lissafinki , fashewa nayi da kuka nace nice banda kwalwa banda lissafi , ɗaure fuska Dikko yayi cikin ɓacin rai yace An mata naje nace kiyi yadda zakiyi dani idan zaki iya mtsww ya fita daga motar yana sabbatu , Yazeed dake sauraren firarmu yayi dariya , tsoki Dikko ya sakeyi tare da ansar allura a hannun Umar ya nufi palo.

Bai daɗe ba ya fito da wata "yar madaidaiciyar kwalba a hannunshi ya soka sirinji ciki yana tsotsowa , hararar inda nake yayi cikin yanayin jin haushi , fitowa nayi daga cikin mota nima cikin ɓacin rai na tsaya ina kallonshi yana ma doki allura.

Bayan ya gama yake ma Umar bayani yadda zaiyi amfani da allurar yana ci gaba da cewa mantawa yayi da ya taho da ita kai kuma cewa nayi kawai kazo ka ansa ka kama ka taho doki ni bana san kuna hawan dokin nan tunda baida lafiya , wata takadda ya ciro a aljihunshi ya bashi yana cewa yayi sauri ya anso mishi , Yazeed kuma palo ya koma zaici abinci , wanda suka zo a mota suma fita sukayi tare da Umar , filin wuri ya rage daga ni sai Dikko.

Ciki na koma na sako dogon wando tunda har naga ya ɓata rai akan rashin san hawan dokin saina hau na ɓata mishi rai nima , ban daɗe ba na fito Dikko yana cikin mota yana waya , motar Yazeed na taka saboda dokin a kusa da ita yake , cikin fargaba Dikko yace An mata ki bari karki faɗo kiji ciwo wai me yasa kikeyin haka ne ? Idan an taroki ta nan sai ki koma tanan wai meke damun kanki da Allah......?

Banza nayi na ƙyaleshi na tattara hijabina na haye saman dokin , murmushin mugunta yayi ya koma palo makullin motar Yazeed ya ɗauko tare da rufe palon da makulli ta waje ya rufe gidan , ɗauke motar yayi daga inda take ya matsa da ita kusa da tashi , bayan ya kaita ya dawo kusa dani ya dafa dokin yace kinyi kyau bari in miki hoto ko kuma ba yanzu ba bari sai anjima , bakin dokin ya buɗe ya tura mishi wani abu bansan ko miye ya bashi ba , lokaci guda dokin ya firgice ya riƙa wata irin zabura yana jijjiga sai wata irin samarya yakeyi yana haniniya gaba ɗaya kukanshi ya cika kaf gidan...

Kallona Dikko yayi yace ai dan ki ɓatamin rai ko ? Kema naki zai ɓaci sai naga mai sakoki duk sai jikinki yayi ciwo , idan kuma kin bari kika faɗo wallahi ta samanki zaiyi wannan haukan kuma ko sannu bazan miki ba , Allah ya taimaka a sauko lafiya , yana faɗin haka ya koma mota ya kunnata ya ɗage glasses yaci gaba da wayarshi cikin kwanciyar hankali ya barni saman dokin daya haukata....

Kallon nisan ƙasa da saman da nake nayi lallai idan na kuskura na faɗo wuyana karyewa zaiyi in mutu , gaskiya Dikko mugune , riƙe dokin nayi sosai gashi yaƙi tafiya wuri ɗaya ya tsaya yana hauka ,

Riƙe wuyan dokin nayi sosai ina kuka , saboda abinda na fahimta duk bayan wasu seconds ƙara haukacewa yakeyi , saiya jirgoni na rabo daga samanshi sai inyi sauri na ƙara riƙewa , tun ina dauriya har ƙafafuwana da cinyoyina suka fara ciwo , dani da doki haka kowa yaita kuka ,

Yazeed kuwa da yaji ihun doki ya taho dan ya fito yaji ƙofa rufe , ta window ya leƙa yaga Sultana ta haɗa zufa da hawaye waya ya buga ma Dikko bayan ya ɗauka yace haba DK karfa yarinyar mutane ta faɗo taji ciwo , Dikko yace yarinya tace bata kowa ba duk faɗin duniyar nan nine nake da ita , inajin daɗine kawai tana wahaltuwa a sauƙaƙe ita kangara ni kuma cuta , idan ma ta faɗo taji ciwo nine zanyi jinyarta ba wani ba , dan Allah zo ka buɗe tafiya zanyi , idan na gama abinda nakeyi ai kasan dole zan buɗe yana faɗin haka ya kashe wayar.

Kwanciya nayi saman dokin na riƙe wuyanshi sosai naci gaba da kuka dan kawai na haƙura idan ma na faɗo duk abinda ya faru haka yazo a rubuce , tausayi na bashi ya fito yaje ya buɗe ƙofar ya saukoni da kuka na wuce da gudu na tafi ɗaki.

Cikin kuka nayi wanka ina fitowa na saka kaya ko abinci ban samu naci ba na kwanta sai bacci ,

Saboda azabar duka da fitar da haƙorinshi yayi har fuskarshi ta kunbura , fito dashi akayi dan ya anshi na safe , wato duka , bayan an fiddoshi akace ina take ne ? Cikin kuka yace wallahi ranka ya daɗe bansan inda take ba , saida suka sake mishi lullusar fitar hayyaci sannan suka sake tambayarshi ka tuno inda take ne ? Cikin kyarmar jiki yace Allah ya taimake ka wallahi bansan inda take ba , cire mishi rigar jikinshi sukayi suka bashi azaba saida sukayi ma jikinshi kaca² suka rufe sahun dukan da gishiri , wata irin ƙara Bello yayi kamar ana cire ran kafiri yace oficer bansan inda take ba ,

Saida aka sake tattaka Bello wanda ya takashi yace lallai soyayyarta mai girma ce a zuciyarka , wannan ɗiya kanaji da ita sosai ya ƙarasa maganar tare da halbashi ya tafi suuu ya shige cikin magarƙama ya kullu yana cewa ka tuno inda ka ɓoyeta kafin nan da wayoyi biyar.....

Cikin farin ciki Al ' Ameen ya ɗauki hanyar Kaduna , bayan ya gama zabgagawa Jiddah ƙarya ya anshi dubu ɗari biyar a hannunta kuma yasa tayi mishi full tank da motar da aka kwace daga hannun Sultana yace boka yayi kira na gaggawa za'a anso mata saƙo kafin zuwan jininta...

Yana isa Kaduna ko hutawa baiyi ba ya ɗauki Mardiyya suka dawo zaria wurin mushiriki , bayan ya baje kayan tsafinsa yaci gaba da koro musu jawabi maganar dai ɗaya akan Sultana kuma ya tabbatarsu da rabuwar Dikko da Sultana babu jimawa ya ƙara da cewa kuma sai Dikko ya ɗiga ma Sultana ruwan rashin mutunci bayan yayi mata wulaƙanci da gori na rashin arziƙi zai korata...

Bayan ya gama bayani ya anshi jinin hailar Mardiyya ya wurga kwalbar sama cikin ƙanƙanin lokaci ta dawo babu jinin a ciki sai garin magani yace Mardiyya ita da kanta zata zubawa Dikko a abunci ko abunsha idan dai tayi wannan tou magana ya ƙare , saboda Dikko zai zama nata ita ɗaya idan ta ajiye masa ƙara tace karya tsallaka bazai wuce ba saboda gudun ɓacin ranta , amma da sharaɗi a kiyaye kar wanda ya sake ta taɓa kwalbar nan saike idan kuwa wani ya taɓa bake ba tou kashinki ya bushe ya ƙarasa maganar yana nuna Mardiyya da ɗan yatsa !

Ansa tayi tare dayin godiya Al ' Ameen ya bashi dubu É—ari da hamsin tare da cewa dubu É—ari na aikin Mardiyya dubu hamsin kuma ayi mishi aiki akan mai gida ya maidashi bakin aiki dan gaskiya yana fama da talauci kuma gashi Dikko zaiyi tafiya yana so yaje dashi waccan tafiyar da Ashiru aka tafi , tafiya da mai gida kuÉ—i mutum yakeyi akafin a dawo....

Boka yace ya dawo sati na gaba ya anshi saƙo , godiya sukayi suka tafi har suka bar wurin boka basuyi maganar Jiddah ba , bayan ya maida Mardiyya gida ya bata cikon dubu ɗari 3 ya riƙe dubu hamsin yace ki sayi kaya masu kyau da turaruka wani satin idan na dawo sai in tafi dake wurin Momy ince kinzo gaisheta ta , ke kuma daga nan sai kici gaba da gyara aikinki har mu samu nasara , godiya Mardiyya tayi ma Uncle sannan sukayi sallama ya kamo hanyar katsina....

Sai bayan la'asar sakaliya na tashi daga bacci , shima bani na tashi da kaina ba Dikko ne ya tasheni wai in tashi haka nan inci abinci kada yunwa ta kama mashi ni , koda na buɗe idona na ganshi ɓata rai nayi na juya da niyar ci gaba da bacci , ke ki tashi haka nan nace fita zamuyi , basar wa nayi na rufe idona dan gajiya nakeji sosai tsakanin jiya da yau duk banji daɗi ba...

Hawowa yayi saman katifar ko takalminshi bai cire ba tsabar wulaƙanci yana janye abinda na lulluɓe , kallonshi nayi sannan na kalli ƙafarshi , shima kallon ƙafar yayi yace palo mota kawai naje babu wani datti a jikin takalmina ,

Tashi nayi na sauka daga saman katifar nace na tsanaka , wannan ai ba baƙuwar kalma bace wurina , kin tsaneni bakya so na duk nasansu , Dikkon banza Dikkon wofi shima wannan ai na sani sai me kuma ?

Baka burgeni , to aini kina burgeni ba lallai saini na burgeki ba , tunda ni ina sanki kuma kina burgeni kinmin a haka , fushinki da duk wani kunburinki bai damuna dan banma san kinayi ba ko aure mukayi kika ɓatamin rai sai nayi miki hukunci dai² da abinda kikayi kuma ko yanzu na zaneki miki jiki tass bazai hana in miki magana ba ko inƙi ansar haƙƙina a wurinki idan na biya buƙata ta kije can kita kunburinki , gara ki iya ki kuma koyi kauda fushinki ki koyi haƙuri dani ko kuma ki kiyaye ɓatamin domin da zaran nayi fushi bani ne ba gara ki koyi kaucewa fushina kawai sai ki zauna lafiya , wuce kiyi wanka kuma karki ɓatamin lokaci jiranki nakeyi.

Wanka na shiga ina tunanin rashin kunya ta Dikko wato shi É—an iska ma har tunani yakeyi zai dakeni kuma yayi tunanin kwanciyar aure dani , to wai waye ma yace yana san sa bare yasa ran zan iya aurenshi zuciya akamar ahalin kutare.....

Koda na fito wanka a É—akin na sameshi sai tattara duk wani abu daya shafeni yakeyi yana jibgawa a cikin trolley bag , jikina a sanyaye nace Yaya me yasa kake zubasu anan ko baka so ina ajiyewa a gefen katifa ne ? Shiru yayi baiyi magana ba yaci gaba da tattarawa amma yanayin fuskarshi babu daÉ—i ,

Cike da damuwa na matsa kusa dashi na duƙa nace D-kow wai miye ya faru ? A dai² lokacin daya zage ziff in jakar ya ɗago yace An mata dole rabuwa zamuyi , cikin damuwa nace mi yasa ko nayi maka wani abu bakaji daɗi ba ? Ba abinda kikamin kuma bana tunani har mutuwa ta zanji babu daɗi daga gareki , tou me nayi maka zaka rabani da kanka a dai² lokacin dana ke farin ciki kasancewa dakai , me yasa ka koyamin sanka kuma zaka rabu dani yanzu ina zaka kaini......?

Me yasa kakemin irin wannan wasan nidai bana so dan Allah , na ƙarasa maganar tare da duƙawa na buɗe jakar na zazzage kayana ina cewa babu inda zanje , ina ne kake tunanin zanje bayan kasan kaine hatimin sa'ata sai kawai lokaci ɗaya ka rusa min sa'ar rayuwa tou wa kake so ya zauna dakai idan bani ba.....?

Sake tattara kayan yayi ya maida cikin jakar ya rufe , cikin kuka nace wai me yasa kake min bana so bara na sake fiddo kayan idan ka mayar dasu nima zanyi fushi , riƙeni yayi yace gida zaki tafi , cikin hayagaga nace wane irin gida ? Dama inda zakuje dani kenan kaida Yazeed munafikai ne ku tou bazanje ba ɗin sai inga mai fitar dani haba da Allah ,

An mata , kafin yayi magana nace An mato Allah babu inda zanje sauƙaƙa kuka na nayi na rungume Dikko nace a gaban idonka jiya mutuwa tayi wasa da rayuwata , kuma kaga yadda tayi wasan kura da Babana , kowa baya so na Baba ƙarami ya koreni Aunty Mamy ta rasu , wata Aunty ta mutu ban ganta ba , shashshekar kuka nayi tare da sakin Dikko nace ita kuma Aunty Suwaiba cewa tayi in tafi dan bata san damuwa ta sake zuwa a rayuwarta , nazo wurinka shine zaka korani shikenan ka daina so na , goge hawaye nayi tare da ɗaukar kayan daya ajiyemin na saka ina kuka....

Cewa shikenan ba komai zan tafi amma ka bar kayanka bana so , dama ai badasu nazo ba , kusa dani ya matso zai riƙeni cikin hayani nace karka taɓani bana sanka , Allah ya gogemin kai a zuciyata na tsaneka , riƙe ƙugu yayi yana kallona cikin yanayin mamaki yace wai baza ki tsaya nayi miki bayani ba ko kuwa ke kaɗai kika iya fushi wai ? Ki bari bana so muyi rabuwar fushi dani dake ki tsaya ki natsu , bana san ayi rabuwar arziƙi ta bala'e nake so ayi , tsoki Dikko yayi tare da kiran Ashiru , babu ɓata lokaci yazo yace ɗauka jakar ina zuwa , ɗauka Ashiru yayi ya fita yana fita Dikko ya sake matsawo nace karka taɓani bana sanka...

Zuƙewa nakeyi amma da ƙarfi Dikko ya riƙeni tare da rungumewa a jikinshi ya sauke wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya mai saukar da kasala , tunda ya haɗani da jikinshi nayi shiru na kasa wani wadataccen motsi na kwantar da kaina saman ƙirjinshi na rufe idanuwana , shima rufe nashi idanuwan yayi tare da cewa An mata kiyi haƙuri kinsan ina sanki kuma ba wani abu kikamin ba , zan rabu dake ne dan sadaki da farin ciki na gaba tun ranar rasuwa Baba dana tambayeki Mamanki kikacemin bata nan ta tafi ta barki , tun daga wannan lokacin na duƙufa wurin nemota , bayan wanda nasa sun mun samota dakel suka mata bayanin ki cewa tayi ta yafe ki wa Babanku ,

Da suke nemi ba'asi , shiru Dikko yayi ya kasa ƙarasawa , abinda Inna tace shine taji baƙin cikin lalatamin rayuwa tayi kuka kamar ranta zai fita tun lokacin da abokan zama sukaji Baba ya sakani a wasan caca suka farayi mata gori da habaici suna cikin farin ciki , bayan sun samu labarin abinda akamin aka yadani a ƙofar gida shine kunya tasa ta gudu dan bata iya haɗa ido da kishiyoyi , bayan ta tafi shine Baba ya aika mata da saki har saki 3 yace shi mace bata mishi yaji kuma ba'a kome a gidanshi....

Shine ta nemi ya bata ni amma yace ai bai gagara riƙe Uwar masu gida ba , ko dan tana ganin suna da kuɗi a gidansu take tunanin zai bata "yarshi shi jininshi baya zuwa kwaraka dan su basu gaji kwakwa ba ,

Ko baki faɗa ba nasan kina so na An mata , ina sanki bazan iya zuwa rakaki ba nima cikin daren nan zan bar katsina bansan zamu rabu a dai² irin wannan lokacin ba , karkiyi rashin ji banda yawo kinji ko ? Duk wani bincike ² ki daina kibarma Dikko komai tsaye nake babu dare ba rana akanki An mata ko bacci nake kece a saman idona , kece mafarkina komai na kece rayuwarki kaf a raina take ki natsu dan Allah dan annabi , idan kuma kikayi taurin kai zanzo kuma kinsan abinda zai faru ,

Kwanaki na ce bana zarginki , kinsan abinda yasa nace miki haka ? Shiru nayi banyi magana ba , yace kinga ya nunamin tafin hannunshi yace duk motsinki yana nan ciki kuma na yafe miki abinda kikayi a baya nasan ɓacin rai ne da ƙaddara karki ƙara kinji ya ƙarasa maganar yana ɗagoni daga jikinshi ƙara komawa nayi na kwanta murmushi yayi mai sauti har cikin zuciyata ya soka , yace insha Allah zamuyi aure babu jimawa An mata zan dasa farin ciki a rayuwarki nima ki haifomin wata "yar matan , amma bamai taurin kai irin naki ba ya ƙarasa maganar cikin zaulaya.....

Dakel ya ɓanɓareni daga jikinshi ina kuka ya kamo hannuna muka fito , muna shigowa palon gaba ɗaya abokanshi suka taso suna Allah sarki An mata tafiya zakiyi ? Yazeed ne yake cewa sai munzo zance , ko zaki hau dokin bankwana , dariya sukayi dukansu Dikko yace kadaiji kunya , Yazeed yace kaine kaji kunya daka ɗora An mata a doki har tayi kuka , murmushi Dikko yayi tare da cewa Allah yasa ma banji abinda kace ba !

Har wurin mota suka rakani , Yazeed yace yana zuwa , gaskiya sunmin halakci suna cewa basu san zan tafi ba , yawansu da daloli suka sallameni Yazeed ne ya bani kyautar zoɓen zinari mai kyau amma Dikko ya ƙwace shi ya ƙaryashi tare da cewa suma dan karsuce wani abu na barta ta ansa kuɗinsu sai kai ɗan haɗama zaka bata zobe ? Tou har yaushe ma ka siya ka ajiyeshi ? Wato kana jira idan bana nan ka saka mata ko ? Ko ni na taɓa ba matarka kyautar zobe ne ? Cikin yanayin rashin jin daɗi Yazeed yace aikai ba matarka bace ba kuma dan na bata zobe miye duk su da suka bata kuɗi baka ansa ka zubar ba saini ? Dikko yace kaima ka bata kuɗin kaga idan ban barta ta ansa ba , ai ni ban fito da kuɗi ba , sai zobe ka fito dashi ? Allah dai yasa ta tafiya zatayi ɗan iska ƙaton banza kadaiji kunya wallahi , ashe da anci amanata.....

Dariya sukayi gaba ɗayansu hada Yazeed banda Dikko amma maganar dai cikin sigar zaulaya yayi ta dan dai bai cika dariya ba kawai ke baiyi ba , Yazeed yace ba komai An mata zanzo jibi , Dikko yace Allah ya kaimu , kallona yayi yace An mata Yazeed zaizo jibi idan muna da rayuwa amma idan yazo ya baki zo be a , a , kinji nace tou , to ku tafi muyi bankwana yace , wani ne daban yace to ku tafi tare kawai mana , murmushi Dikko yayi tare da fita daga cikin motar yace sai munyi waya ya ƙarasa maganar yana rufe motar... !

Ashru yaja muka tafi daga gidan suna ta ɗagamin hannu , kukana ƙara yawa yayi ina cike da kewar Dikko , tunda muka hau titi na duƙar da kaina naci gaba da kuka ina maraicin Dikko da duka zuciyata.....

Da malami da karuwa ba abin yadda bane ba dan basu da amana , Al ' Ameen kuwa saida yazo malumfashi ya tsaya wurin wani gahurtaccen malamin tsubbu ya anshi asiri , abinda yasa bai anso wurin boka ba saboda Jiddah taga wurinshi taje tayi mishi ɓarin kuɗi ya kwashe komai ya faɗa mata , asirin farko Jiddah karta riƙa jin maganar kowa sai nashi , na biyu kuma Dikko akayi ma ya maidashi aiki na ukku kuma , Sultana rabuwa ita da Dikko , na huɗu kar Jiddah ta aihu dan so yakeyi duk wannan tulun dukiyar ta Dikko su lasheta idan Mardiyya ta aihu sai su kashe shi su cinye komai nashi....

Bayan yazo katsina ya bawa Jiddah yace inji boka kuma duk ya faÉ—a mata yadda zatayi amfani dasu hada wanda zata zubawa Dikko a abinci godiya tayi sosai ta bashi dubu É—ari 3 tace yasha maganin gajiya , godiya yayi sannan ya fita...

Dikko kuwa tafiyar Sultana bayan kowa ya tattara abinda yake buƙata government house suka nufa bayan ya shirya ma abokanshi abinda ya shirya dan ya kuɓutar da Sultana daga tarkon Momy ta shafawa An mata lafiya tayi rayuwarta free.

Tare ya shiga da zugar abokanshi da sukayi amfani da motoci huɗu , bayan ya fara bincika Al ' Ameen bai samu ba , daga inda yake tunanin zai samu Al ' Ameen babu kai tsaye ƙofar palon Momy suka nufa bayan sunyi parking ya zame ya rufe idonshi , gaba ɗaya suka fito daga cikin motoci suka fara ƙoƙarin fito da Dikko daga cikin mota , jin tsayuwar mota yasan ƙannenshi mata suka fito dan sun san shi kaɗai ne ke zuwa da irin wannan tuƙin kuma sunji an ɗauki lokaci bai shigo ba suka fito , su dai Allah yasa musu san ɗan uwansu kodan shi ɗaya ne namiji ? Da mamaki sukaga ana fito da Dikko daga mota sai kakkafawa yakeyi , wayyo me ya samu Baban Dady sukayi wurin suna kuka dasu aka fiddo da dikko daga mota aka shiga ciki !

Momy na zaune a cikin ƙaton palon gidan gwamnati tanajin daɗin ta bata da wata damuwa ko tashin hankali na duniya tana shan iska yadda ya kamata taga an shigo da Dikko sai kakkafewa yakeyi , ciwon da bata taɓa ganinshi da irinshi ba gaba ɗaya ta ruɗe cikin tashin hankali tace meya sameshi ne ? Wanda Dikko ya ɗaura a matsayin lawyer n shi yace wai kasashi akayi ne ? Gyara zaman kallabin kanta tayi tace miye kasawa ? Wata yarinya yakeso shine akayi mata aure , cikin hargowa Momy tace wace yarinya ? Yazeed yace muma bamu santa ba kawai dai muna zaune ya faɗi yana cewa An mata , dariya Momy tayi tare da cewa shikenan Allah ya raba faɗa , yaushe akeyin bikin ? Yau aka kaita gidanta , Momy tace babanta yaci uwashi shi yasa yayi sauri yasa akayi mata aure ,

Bedroom ta nufa ta ɗauko magani tazo ta zuba mishi amma saiya watsoshi maimakon ya miƙe , ƙara zuba mishi tayi ya ƙara fesewo , cikin ruɗewa ta koma ciki "ya "yanta suka bita suna kuka , tana shiga Dikko yayi murmushi tare da ɗagawa su Yazeed gira ya kashe ido ɗaya ya koma yanayin da yake kamar baya , a firgice ta sake dawowa da wani maganin tana ni maganinshi kamar yana wurinshi , a ruɗe ta fita dan wannan ciwon ya tadawa Momy hankali da gudu ƙannenshi sukabi bayanta dan sunga mahaifiyarsu tana cikin tashin hankali , tana fita Dikko yace ko idan ta sake zubamin maganin ince bazan tashi ba sai an kawo An mata , wani yace a kawo ta daga gidan ubanwa bayan kace muce an mata aure , zaro ido Dikko yayi cewa innalillahi na rantse da Allah da nasan hankalin Momy zai tashi haka da ba wannan dabarar akayi ba , wayyo Allahna gani gareka , shigowar Momy wata irin zabura yayi tare dayin harbe² danma karta ga kamar yana magana shi yasa ya birkice su Yazeed suka fara ƙoƙarin juyoshi amma duk yawansu suka kasa firgito Dikko , Yazeed yace karfa ƙaramar magana ya zama babba.....

Duk wani shaƙe² Momy tayi amma Dikko yaƙi tashi gashi Dady baya nan , ciki ta koma ta kira Dady ta sanar mishi abinda ke faruwa , inda zata samu maganin da yayi mishi amfani dashi a gidanshi ya faɗa ajiye wayar tayi ta fita da sauri ta daɗe sosai sannan ta dawo ana shaƙa mishi ya miƙe yana tari da atishawa Yazeed yace ashe da gaske....?

Momy tace da gaske mana ai dan ubanshi yasan baida cikkar lafiya yake so kashe kanshi , dan anyi mata aure miye ? Ba rabokan bace shi yasa baka sameta ba , nasiha Momy tayi ma Dikko daga ƙarshe tace ai An mata hadari ce kuma tazo ta tafi kawai ya manta da ita ,

Tashi yayi baiyi magana ba ya fita suma abokanshi suka bi bayanshi , suna fita suka fara kai daga wasa sai kawai kayi mana haka ? Ai ka sake ganin mai rakoka kayi ƙarya , bai basu ansa ba suka ga ya shiga mota da gudu , ashe Al ' Ameen ya hango ,

Momy data fito dan taga yanayin jikinshi ko ya warware tana ganin Dikko a mota ta hango Al ' Ameen cikin tashin ta nufi wurinshi ta ciro makullin dakel yayin da Dikko yayi tsalle ya tsallake motar dake gefenshi , tace su Yazeed su riƙeshi suna riƙeshi yayi wani irin ihu yace saina kashe shi , ya watse su gaba ɗayansu suka faɗi ƙasa , cikin ruɗewa Momy tace ku rufamin asiri ku riƙoshi , da gudu suka tashi suka bi Dikko yana wata irin zabura ,

Momy kuwa fashewa tayi da kuka tare da cewa ya Allah kayimin sakayya tsakanina da duk wanda keda sa hannu acikin lalurar Dikko , an maidamin ɗa mahaukacin ƙarfi da yaji , wani irin ihu Dikko keyi yana wani irin gurnani mai tada hankali dasu Yazeed sun riƙeshi saidai ya ɓaresu yana wata jijjiga , yayin da Al ' Ameen ya haye saman wani ƙaton tanki yana fitsarin tsoro , dakel aka kai Dikko ƙasa da taimakon duk wani maiji da ƙarfi dake gidan , cikin kuka Dikko ya ɗaga ido dakel ya kalli Al ' Ameen a hankali idanuwanshi suka rufe Momy tasa aka dawo dashi ɗaki....

Sai 1:30am su Yazeed suka tafi amma har yanzu Dikko bai dawo ba , momy tasha kuka kamar ranta zai fita wasu matan basu da adalci ita ba ita taba kanta Dikko ba Allah ya bata shi dan kawai an nemi namiji a gida ba'a samu ba ita ta aifa sai kawai a hana yaro ya zauna lafiya , tou wallahi bata yafe ba kuma bazata yafe ba duk wanda yayi ma Dikko wannan abun ubangiji ya saka mishi Allah kuma ya bashi lafiya duk da dai tasan yana da baƙar zuciya da rashin ɗaukar iskanci abun yayi yawa , shikenan da rai ya ɓaci sai kawai mutum ya riƙa ɗaukewa kamar wutar nepa , ai kowa yanajin fushi kuma kowa yanayin zuciya su duk masuyi me yasa basa suma sai Dikko so kawai akeyi ɗanta ya mutu kuma insha Allah Dikko bazai mutu yanzu ba...

Bayan ta gama kokenta ta kira mutanen da suka kama Bello tace suyi mishi dukan leƙa lahira ya dawo kuma su faɗa mishi idan ya fita ya nemi dafa'in zaman aure ɗiyarshi ta zauna karta fito daga miji idan kuwa ba haka ba to wallahi aka sake mamoshi na gobe saiya fishi jin daɗi...

19/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA...*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 59

Uhum wai ashe duk abin nan inna tana cikin garin katsina ita da iyayenta "yan gayu dasu sun wani shige cikin ƙaton gidansu sunayin farin ciki basu da wata damuwa abun su a cikin ɓarkeken gidansu dake cikin anguwar layout , yanzu Inna suna da wannan gidan wace ƙaddara taja mata auren Babana taja mukaje mukayi ta rayuwar cin ƙanzo da garin kwaki , wannan irin ƙaton gida an ƙawatashi da ciyayi ga ma'aikata an baza ta ko ina , amma dan mugunta suka bar Inna tayi rayuwa a gidan haya ina ma amfanin arziƙin da baka samma wanin ka.....

Ashiru da kanshi ya shigar min da kayana har cikin ƙaton palon gidan da aka ƙayatashi da wasu irin azababbin kujeru masu kyau da tsada tayils in palon yasha guga duk dare ne sai ɗaukar ido yakeyi tvn bango da sifiku umm amma yanayin palon ya nuna tsohuwa ce ke rayuwa a gidan , wuri Ashiru ya samu ya ajiyemin jakata ya zauna gefen jakar...!

Nima rakuɓewa nayi ina tunanin Dikko Allah yasa karya tafi yabar katsina tsakanin layout da goruba road ai ba wani tashin hankali bane kawai sai in riƙa zuwa ina yini wurinshi in dawo nan in kwana ! Murmushi nayi cikin yanayin jin kunya na rufe idanuwana tare da kwantar da kaina gefe ina tunanin yadda na kasance a jikin Dikko ,

Hannunshi mai laushi baya da wata wahala a cikinshi kamar ba'a amfani dashi , ƙara sinsina jikina nayi turaren Dikko a jikina kamar nice na shafashi , murmushi na sakeyi ina ƙara tunano yadda ya kamani dakel a jikinshi ya rungumeni , ajiyar zuciyarshi dana tuno itace tasa naji tsikar jikina ta mimmiƙe gaskiya Dikko yayi ya gama haɗuwa tako ina , ga aji ga natsuwa ga kyau ga wayewa ga gayu sai maganarshi mai sa mutum cikin halin tunani babu dare ba rana...

Maganar Ashiru ta dawo dani daga duniyar tunanin dana lula , buɗe idona nayi naga wata dattijuwa mai cikar kyawu da asali kame a saman kujera tasha lulluɓi da gyale mai kyau kanta babu kallabi ta ɗora gyalen a saman kanta ta fiddo kunnuwata waje kodan ta nunawa mutane tasa "yan kunne zinari oho , kila kuma nata ra'ayin ne haka...

Gaisheta nayi yayin da nakeji dama ahalin Babana ne dan duk cikar arziƙi ko asali na uwa tou wallahi na uba ne a sama dan uba dashi ake tunƙaho shine ado ga kowa ɗa , duk cikar arziƙi irin na mutum da duk wani mulki ko sarauta da yake taƙama dashi da bazar uba yake taƙama , da zaran ka rasa ahalin Baba na gari tou ka zama sai a hankali , cikin sakin fuska ta ansa gaisuwa daga nan na kama bakina nayi shiru sukaci gaba da fira da Ashiru , a cikin firarsu ne naji tana cewa wai inna ta tana Dubai kunji fa.....

Sun daÉ—e suna fira da Ashiru kuma har sukayi suka gama ban saka musu baki ba , da Ashiru ya tashi tafiya saida na rakashi har mota ina cewa ya gaishemin da Dikko sosai kuma yace masa idan na kirashi waya ya É—auka zanyi magana dashi yace insha Allah , saida ya tafi sannan na dawo ciki ,

Lokacin dana dawo har an shigar da kayana ciki , tsohuwar da nake tunanin itace kakata tayi min jagora zuwa É—akin da zan zauna tana ta jana da fira cikin soyayya amma ni wallahi banajin maganar kowa saita Dikko domin duk ilahirin hankalina da tunani na yana wurin tunanin shi , abinda yafi tsayamin a rai kawai rungumar da yayi min da kuma fitar sautin ajiyar zuciyarshi...

Gajiya tayi da surutu ta fita dan dai Sultana bata ita take ba , tana fita na shiga toilet nayi alwallah nazo nayi sallah bayan na gama kawomin abinci akayi naci ina gama cin abinci na soke saman gado na fara kiran wayar mai gida Dikko......!

Na kirashi bansan so adadi ba amma bai ɗauka ba , tun inayi daga kwance har na tashi zaune haka kira zai shiga yaje ya dawo Dikko baya ɗauka , faɗuwa gabana yayi shikenan ƙarshe kawai zai kashe wayarshi ne daga nan sai ya manta dani , bansan yadda akayi ba kawai naji hawaye na gangaromin daga cikin idanuwana saida nasha kuka har na gode Allah bansan sadda bacci ya ɗaukeni ba na kwanta da tunanin Dikko a zuciyata ,

Yauma horon safe akayi ma Bello yaci ubanshi cikin farashi mai tsada , yayi kuka harya gode Allah , bayan an mishi kashedi akan karya kuskura ya bari auren Sultana ya mutu saida suka haÉ—a mishi jini da majina sannan suka sallameshi , yana fitowa ya faÉ—i a wurin da taimakon wasu tsirarun mutane suka É—auki banza suka wuce dashi asibiti suna zuwa gado aka bashi dan lalubo mishi sauran rayuwa.

Dikko kuwa sai asuba ya farko kuma da ihun saiya kashe Al ' Ameen ya dawo , dakel Momy ta rarrashi Dikko akan ya fita hanyar Al ' Ameen cikin gamsuwa yace mata ya barshi bazai mishi komai ba , Momy ta ƙara da cewa dan Allah uban masu gida kar na sake jin wani maganar kisa ya fita daga bakinka kar kuma ka sake ka dakeshi , jinjina kanshi yayi alamar bazaiyi ba ya ƙare ajiye kan da murmushi ,

Momy da kanta ta rakashi É—akinshi , acan yayi wanka ya canja kaya ya fita masallaci , daga masallaci gidanshi ya wuce ko Jiddah bata san ya shigo ba kai tsaye É—akinshi ya wuce dan har yanzu gajiya ke murzar mishi jiki .

Tunda nayi sallah asuba naci gaba da kiran wayar Dikko amma sam bai ɗauka ba , ganin baya ɗauka na haƙura na kwanta bacci tunda na kwanta kamar jaka ko motsowa banyi ba sai bayan azahar , dan nima ina tattare da nau'en gajiya , akwai gajiyan gudu da jifar dasu Al ' Ameen suka min , dukan da Dikko yayi min sai gajiyan hawa doki...

Ina tashi da wayata na fara na duba ko Dikko ya kira babu miss call inshi , saida na sake kiranshi bai ɗauka ba ni kuma nayi alƙawari daga nan har a busa ƙaho idan ba shine ya kira ba bazan sake kiranshi ba.

Yinin ranar yau dai har dare Dikko bai kirani ba kuma nima na basar da lamarinshi , da daddare kuma kaka ta haÉ—ani da gyatima mukayi waya wai nace Inna ni zata dake ma kashedi kar na sake ce mata Inna , nace gwaggo zance miki ko me ? Dariya tayi tare da canja maganar da wata fira ta daban , mun daÉ—e sosai muna waya da ita cikin farin ciki daga baya mukayi sallama na maida ma kaka wayarta danni dama ban wani san wannan kakar ba gaskiya sai a hoto nake ganinta dan Babana baya bari ina zuwa ko ina kuma duk inda zanje tare muke tafiya dan abinda na fahimta a can baya akwai "yar tsama data faru tsakanin Inna da iyayenta da kuma Babana É—an uwan Inna É—aya kawai na sani shima saboda yana mana hidima ne lokacin muna tare da Inna a gidan Baba !

Bayan nayi sallah isha'e ina shirin kwanciya mai aikin Kaka ta shigo wai nayi baƙo a waje , cikin farin ciki na tashi na ƙara gyarawa na fesa turare gyale na ɗauka da sauri na fita ,

Ina fitowa motar Yazeed na gani parke a wurin da aka tanada dan ajiye motoci , cikin farin ciki na isa wurin dan a tunani na shida Dikko ne kuma jiya da zan taho Yazeed yace min zaizo jibi , kenan sai gobe ne ranar da zaizo , cike da farin ciki na isa jikin motar ina zuwa Yazeed ya buɗe motar ya fiddo ƙafarshi ɗaya waje yana kallona cikin yanayin farin ciki ,

Gaishe shi nayi ina leƙa cikin motar ko zanga Dikko , murmushi yayi irin na wayayyin maza yace An mata ni bada DK nazo , me yasa baku zo tare ba ne ? Nima bansan zanzo ba kawai hanya ya kawoni nace bara in biyo miki da mamaki kafin zanzo gobe , a yatsine nace kazo yau gobe ka dawo ? Yace Eyy mana jibi ma zanzo kullum zanyi ta zuwa har sai bana nan ne kaɗai bazan zo ba.....!

Kallon rainin hankali nayi mishi nace to meye nasabar hakan ? Kula mana , meye halaƙar ka ta san kula dani ? Neman kusanci ! Ta wane dalili kusanci zai ƙullu tsakanin namiji da mace ? Abokanta ka , ai babu abota tsakanin mace da namiji , murmushi yayi tare kauda maganar ta hanyar cewa tou ya kike ya gajiyar kuka da hawan doki ? Ya ƙarasa maganar yanamin kallon ƙarƙashin ido....

Lafiya qalau na faɗa a ƙagare , fitowa yayi daga cikin motar ya jera dani , ja baya nayi sannan na juya mishi baya , murmushi yayi tare da cewa haba An mata miye kikeyi haka ? Babu kyau kinsan yana daga cikin ɗabi'u masu kyau martaba baƙo irin wannan tarbar zakimin haba An mata yadda ya ƙarasa faɗar An matar sai naji kamar maganar Dikko , ba tare dana juyo ba nace yi haƙuri bacci nakeji ne ,

Iyya yi haƙuri na tuna kinayin bacci da wuri to zan tafi zanzo goben fa , Allah ya kaimu ina faɗin haka nayi gaba abuna , da gudu na isa ɗakina cikin ɓacin rai ina shiga wayata na duba dan ganin ko Dikko ya kirani , ya kuwa kira amma miss call ɗaya ne , shine duk kiran da nayi masa bai ɗauka ba ni zaima wannan miss call ɗin ɗaya dan ya maidani bansan abinda nakeyi ba ? Tsoki nayi tare da kiran wayarshi dan da bai kirani ba nayi alƙawari bazan sake nemanshi har abadan abada.

Saida kiran ya kusa ƙarewa ya ɗauka , cikin disashshiyar murya kamar wanda mura ya kama yace An matana ya kike ? Ban ansa ba nace me ya sameka muryarka wata iri , gyaran murya yayi irin dandai maganar ta tafi dai² yace babu daɗi ko ? Murmushi nayi tare da kwanciya saman gado nace da daɗi mana , yace wallahi muryar shaƙewa tayi bansan abinda yasa ba kinga kuma ni bana huɗɗa da abu mai sanyi da sai ince mura ya kamani , sannu nace masa yace yawwa yaci gaba da cewa wallahi wayar a mota na barshi sai yanzu dana fita naga tulin miss calls kuma ke na fara kira An mata... Yayi maganar a sakace,

Murmushi nayi cikin yanayin jin daÉ—in yadda yayi maganar nace tou amma yanzu ka fasa tafiya ko ? Yace zanyi tafi amma sai wani satin banajin daÉ—i ne duk jikina ciwo yakemin , ni kuma nace ciwon tunani nakeyi , murmushi Dikko yayi tare da cewa Allah ya baki lafiya saida safe... Yana faÉ—in haka ya tsinke kiran,

Cikin jin haushi na sake kiranshi amma yaƙi ɗauka , ni bansan abinda yasa yakemin irin wannan abun ba , ko wurina yazo baya so ya daɗe , idan inayin waya dashi a ƙagare yake ya barni anya Dikko zai soni kamar yadda nake sansa ......?

Murmushi yayi bayan ya tsinke kiran yace An mata kenan itafa nan a wayan ta so take ta ganni amma bazata iya faɗa inzo ba sai ta fake wai tana ciwon tunani tou ai sai kisha magani ko kin samu sauƙi.....

Daga G R A kai tsaye tsohuwar anguwar su Sultana ya taho inda gidan da yake kiwon dawakai yake , tunda ya shigo anguwar ya ganta cike da taron jama'a maza da mata kuma duk wadda ka gani kasan cikakken É—an iska ne maza "yan daudu mata karuwai duk wacce ta ansa sunanta tanaji ita wata shegiya ce a cikin iskanci ta hallara a wurin gaba É—aya anguwar ta karaÉ—e da kiÉ—a ko wane É—an iska da iyayenshi suka ce jeka ka gani su Amisty sun hallarar dashi a wurin ,

Da gudun bala'e ya shiga cikin santar saboda tsabar gudu motarshi har wani tsalle takeyi , kamar fari haka mutane suka riƙa tashi da gudu dan keɓe rayuwarsu daga faɗawa mummunar rayuwa , a ƙofar gida yayi parking ya fita ya shiga ciki rai a haɗe , shigarshi hayani ta fara tashi kowa dai da abinda yake faɗa akanshi ,

Bayan ya gama abinda yakeyi zai fito Umar ya biyo bayanshi yake cewa mai gida yau kaga anguwar namu cike ? Banza Dikko yayi dashi bai bashi ansa ba shi kuma yaci gaba da cewa wata karuwa ce take ajo na cika shekaru biyu da fara barikinta sai kuma shagalin samun "yan cin kai na zaman kanta watanni bakwai , Dikko dai baiyi magana ba yana fitowa ya shiga motarshi ya fice da ribos har ƙarshen santar yana kaiwa titi ya juya sitiyarin motar shi ya wuce inda suke majalisarsu , Hafsa kuma tabi bayanshi ,

Umar kuma mamaki yakeyi ko akwai abinda yake damun Dikko duk dai haka yake amma kamar wani abu ya taɓashi , ko wani abu ya ɓata mishi rai idan an gaishe shi zaice yawwa , ko lfy ko da kyau ko yayi amma yau duk wanda ya gaishe a gidan nan bai ansa gaisuwar kowa ba kuma baiyi magana da kowa ba har ya shigo ya fita...

Har yanzu ban daina kiran wayar Dikko ba , duk kiran daya shigo wayarshi na Sultana yana kallo saida yazo goruba gidanshi sannan ya ɗauki wayar cikin tsananin ɓacin rai da hayani yace wai me ye ne............? Ni bana san maita sai kirana kikeyi kin dameni bansan masifa da kwakwa da Allah mayya kawai , cikin tashin hankali na tashi zaune tare da sake kallon lambar wani abu naji yazo ya tokare min a zuciya nace Dikko nice mayya....? Eyyy kece nace mayya ko ba mayyar bace , nima kamar an sakani cikin ɓacin rai nace kaine maye marar tunani wanda baka san ina duniya ya nufa ba , kamar ƙaramin yaro haka Dikko ya biyemin mukai ta zage² duk abinda yace min saina rama ,

Daga ƙarshe ya zageni tass da turanci , cikin kuka nace Dikko An mata ce fa , tsoki yayi ya kashe wayarshi , wayyo Allahna meke faruwa haka ? Yanzu na gama waya da Dikko lafiya qalau sai kuma in sake kiranshi ya zageni me yayi zafi haka don Allah ? Wayyo Allahna , da sauri na kalli agogo 9:24pm zuciyata kamar zata tsage saboda tashin hankali idona kuwa banda aman hawaye babu abinda yakeyi , da gudu na fito har bakin get , wanda nake tunanin shine driver naje gabanshi a rikice na fara magana cikin rawar baki nace da Allah ka kaini goruba road taimakeni don girman Allah na ƙarasa maganar ina jan hannunshi....

Lafiya ya tambaye ni ? Babu lafiya muje don Allah zan baka kuɗi idan muka dawo yanzu zamu je mu dawo yi sauri don Allah na ƙarasa maganar ina goge hawaye idona , muje ya faɗa yayi gaba nabi bayanshi ,

Ko a mota a gaba na kasance ina ce masa yayi sauri , sauri ׳ malam driver , gudu yakeyi sosai amma kayi sauri kawai nake cewa har muka isa goruba road , a harabar gidan na haɗu da Hafsa Dikko ya bata kashin bala'e ana ta riƙonshi ya haukace gaba ɗaya , cikin tausawa na kalli "yar uwata dake duƙe tana kuka Dikko sai ruwan rashin mutunci yakeyi ana bashi haƙuri kamar ana ƙara tunzurashi yana sai ya tattaka ta ,

Wurin Hafsa naje na kamata na miƙar da ita ina bata haƙuri tare da tambayarta meya faru ? Kallona tayi amma bata ce wani abu ba sai kuka takeyi , sakinta nayi zanyi wurin Dikko aka tareni cike da iskanci yake cewa kizo ku barta tazo yayi maganar yana kirawoni da kanshi , turesu nayi na tunkari Dikko kai tsaye ina isa ya yankamin wani irin mari saida na wurwura kamar ranfa na dawo gaban Hafsa ko gabana bana gani sai duhu , kafin in dawo hayyacina na sake komawa inda nakejin sautin muryar Dikko dan kawai ji nake gara in mutu da masifar da zan fuskanta a gaba dan rabuwa ta da Dikko a halin yanzu na dangana abun kawai da mutuwa ta ,

Riƙeni akayi cikin ihu nace ku sakeni saiya kasheni , ka kasheni Dikko kasheni bana so ka barni da raina gani na matsa gabanshi ina kuka , da ƙafarshi yayi min wani irin halbi saida aka ɗagani sama sannan na faɗo ƙasa ruf da ciki , da sauri na sake tashi cikin kuka na sake tafiya wurin Dikko wani irin tsalle yayi ya ɗaga hannunshi sama rigarshi ta ɗage har kana gani cibiyarshi yace idan taurin kaine ɗabi'arki nine kangara zai kaimin duka saman kai Yazeed ya riƙeshi birkicewa Dikko yayi yana saina kasheta , andaiyi tashin hankali sosai munyi zage² da Dikko abun dai babu daɗi dakel Yazeed ya sani mota muka dawo gida can na baro Hafsa kuma bansan abinda ya haɗata da Dikko ba kuma babu wanda yasan abinda ya jawoma Dikko wannan haukar ba,

Sultana tana tafiya Dikko yace zancen banza zance wofi yau duk wani mai tsohon laifi a wurina an famomin ciwon dana daÉ—e ina raino a cikin zuciyata saura waccan É—ayan É—an iska yau duk wanda ya hawoni saina lalata mishi rayuwa , yana faÉ—in haka ya shiga mota ya nufi gidansu ,

Yau duk wanda yaga Dikko lafewa yakeyi saboda tsoro , wurin mahaifiyar shi ya fara shiga itama da yanayin tsorata ta kalli Dikko tace kai lafiya kuma ? Banda lafiya kuma yau duk wanda yayi gigin shigomin rayuwa ko waye saina mishi babu daɗi ba ruwanki yau saina kashe Al ' Ameen a gidan nan kar wani yayi gigin taɓani ko zuwa kusa dani idan ba haka ba yau zan tara majiyyata da yawa a gidan nan , Dikko badai zaka barni na zauna lafiya ba ko ? Cikin hayani yace da ko wane daƙiƙi na rayuwata shi nake jira yau bana iya bacci saina kasheshi yana faɗin haka yayi waje.....

A tsorace Momy tabi bayan Dikko amma lokacin data fito ko sahun ƙafarshi babu tuni ya ɓace , tsayuwa tayi tana tunanin mafita taji gaba ɗaya gidan ya gauraye da hayani da sauri ta nufi inda take jiyo hananiyar tana zuwa Dikko ta gani shaƙe da wuyan Al ' Ameen ya riƙeshi duk wanda ya matso wurinshi halbi ɗaya yake mishi sai mutum yayi sama ya dawo ƙasa somamme...

Ƙatti majiya ƙarfi sunfi nawa amma sun zagaye Dikko an kasa samun wani da zai sake matsawa kusa dashi , cikin ɓacin rai Dikko yace har so nawa zan faɗa bana san wani ya sake zuwa kusa dani idan akwai mai sha'awar jinya ko mutuwa yazo..... Ya faɗi maganar a dai² lokacin daya ɗaga Al ' Ameen sama ya dakashi da ƙasa , Momy tace ku riƙe minshi mana , wani yabi ta bayanshi dan ya kamashi amma yana isa Dikko ya halbeshi ta baya shima saida yayi sama ya dawo some , cikin ɓacin rai yace har sau nawa zan faɗa bana so azo kusa dani kuci gaba da shigowa duk saina ƙarar daku a dai² lokacin da yayi wani irin tsalle ya dira akan ruwan cikin Al ' Ameen dako motsi bayayi yace zaka fita harkata ne ko zakaci gaba da shiga ? Kun hanani na zauna lafiya yayi maganar yana ɗaukar Al ' Ameen kamar ya ɗauki kaza yayi jifa dashi jikin wani ƙarfen fitila , yanayin jifa dashi gaba ɗaya suka rufa kanshi dan su riƙe shi , wani irin ihu yayi kai...... Wayyo wai...... Yaci gaba da dukansu babu ji babu gani duk wanda ya hawo saida Dikko ya kwantar dashi yau kam saida ya tsamama ma duk wanda ya hawo layin shi jiki ya kama gabanshi.....

Goruba road ya koma a daren yana neman wayarshi , kowa ce masa yake baya kyautawa abinda yake yi , baima kowa magana ba yace ina wayarshi , cikin girmamawa Ashiru yace gata mai gida , cikin ɓacin rai yace kiramin An mata , kallonshi Yazeed yayi yace "Yar matan daka wulaƙanta kake tunanin zaka kirata ta ɗauka , ai saboda wannan lalurar yasa na sakata a tarko , Yazeed yace dan kayi ta zalincin ta kana ɗaukar alhakinta ka ɓata rai kayi ta rashin mutunci warware hannun rigarshi yakeyi yana cewa dole sai tasan fushina kuma ta riƙa kiyayeshi na faɗa mata idan nayi fushi bani ne ba , ɓatamin rai tayi data kama hanya ta taho kuma nace bana so tana yawo ita sarkin soyayya dan nace mata mayya taji haushi tayimin zagin rashin mutinci.

Wani ne yace to kai me yasa kace mata mayyar ne ? Raina ne ya ɓaci a dai² lokacin da fushi ya hau kaina ita kuma taita kirana dana ɗauka na sauke fushin a kanta , tunda har zan zama mijinta dole ta koyi ansar laifin da ba nata ba , domin da zaran nayi fushi tofa ko kaina bana saurara.....

Tambayar shi suka sakeyi meya ɓata mishi rai haka da yawa har ya daki Sultana da yake iƙirarin ko wani ya taɓata saiya rama mata , cike da damuwa Dikko yace karuwai ne na gani ƙanan yara wanda shekarunsu bai dace da karuwanci ba "yan kuci²n yara wai su nan har sun giga sun tafasa har sun ƙone sun bushe fitilar idonsu wai sunsan daɗin maza , sun gagari iyayensu abin ne ya tadamin hankali , bansan masifar dake damun mutanen wannan zamani ba , wallahi wata "yar ƙaramar yarinya na gani sai kuma yayi shiru hawaye ya cika mishi ido a dai² lokancin da Ashiru ya miƙo mishi waya Sultana ta ɗauka , An mata miye kike kuka kina tunanin zan iya fushi dake ? Cikin kuka nace shine ka zageni kace min mayya kuma ka dakeni , haba An mata ki riƙa min uzuri don Allah ai kinsa bada gangan na faɗa ba fushi ne , tou nidai kazo in ganka , kallon agogo yayi yace dare yayi ki bari da safe zanzo , nidai kazo yanzu , cikin sansanyar muryarshi yace gani nan zuwa....

Gaba ɗaya kowa yace sai yaje yaga yadda za'a ƙare , yayin da wani yake cewa Allah yasa itama tasa ayi maka shegen duka , murmushi Dikko yayi a dai² lokacin da suka fito daga palon yace An mata bata iya fushi dani har abadan duniya domin wannan lalurar ne yasa na sanya mata maitata a zuciyarta , babban muradin ta a yanzu na aureta kaga idan na aureta ta zama tawa , idan har na auri An mata ba maganar yaji dan babu inda zata iya tafiya tabar Dikko muyi faɗa mu shirya danma tana da ƙananan shekaru har yanzu ta kasa kullema 20 , motoci suka shiga suka nufi gidansu Sultana...

11:52pm a gidan Kaka tayi ma su Dikko kuma duka ciki suka shigo da motocinsu , ba waya yayimin yazo ba kukan motarshi kawai naji nayo waje , saida na gaishe da duk abokanshi na shiga mota yana baya zaune ina shiga Ashiru ya fita , fashewa nayi da kuka na rungume Dikko cikin kuka nace shine kacemin mayya ? Yace ai mayyar ce ko ke ba mayyar Dikko bace ba , nima ai mayenki ne kuma ba kin rama ba , to ai har zagina kayi da turanci , murmushi Dikko yayi da gefen bakinshi yace ni wallahi ba zaginki nayi ba , iyakar mayya dana ce ban wani ɓoye da wani harshe na aibataki ba , gaki kin fara zama jajirtacciya soyayyata ta hana ki gano matsalata , haka zakiyi ta haƙuri dani An mata har Allah ya bani lafiya kinji , ya ƙarasa maganar cikin sigar lallashi. Nace to me kacemin da turanci ? Saida yayi dariya yace cewa nayi "yar ƙaramar yarinya kin hanani zaman lafiya , duk wannan doguwar maganar a "yar wannan kalmar ya tsaya ? Ajiyar zuciya ya sauke baiyi magana ba ,

Shashshekar kuka nayi tare da cewa tou me nayi maka haka da ciwo don Allah , riƙeni yayi da hannunshi na haggu har yanzu ina kwance a jikinshi shi kuma ya kwantar da fuskarshi a saman kaina ya fara magana cikin sanyinshi , yace An mata taron karuwai na gani abun ya gigitani wata "yar ƙaramar yarinya ba zata wuce shekarunki ba kinsan abinda na gani anayi da ita , shiru nayi ba tare dana bashi amsa ba , cikin kuka Dikko yace to maza ke layi akan yarinyar yadda kika san ana ɗaukar mutum a abun hawa a anshi kuɗi haka maza ke hawan yarinyar suna sauka suna bata kuɗi , ɗimuwar rayuwa ta sameni duk taron mutanen da aka tara An mata batajin kunya wai ta keɓe gefe ɗaya tayi ma maza masauki a jikinta , mata basu san illar namiji ba duk mayatar mace da masifar maitar namiji bata iya kashe namiji 2 a bariki , namiji kuwa sai ya kashe mace sama da goma yana nan zamzam , rayuwar mace taƙaitacciya ce amma rashin tunani ya hana su gane haka tunda na shiga anguwar da wanda ke gefe na da wanda ke gabana da duk wanda yake bayana zan iya baki labari , kallo ɗaya zanma abu na gama dashi yanayin mutum na kalla zan iya faɗa miki komai akanshi,

Ni mamaki ma nayi duk wa'an nan "yan iska ina ita wacce ta tarasu ta samo su ? Wai ke kinga taron ? Ya ubangiji ka tsare mana imaninmu ka shirya bayinka daga faɗawa tarkon zina , ina cikin jimami ke kuma kin dameni da kira a lokaci ni kuma ina so na samu natsuwa na kiraki ke kuma kin gagara daina kirana ne ina cikin tashi hankali bana so ban ɗauka kiranki ba kuma kiji babu daɗi ina magana dake raina ya ɓaci nayi ta faɗar maganganu babu daɗi , ita kuma wannan yarinya ta wani kama hanya ta biyoni bayan itama na ganta maza sai rumgumarta suke ,

Ai banma san na cire belt na zaneta ba ina cikin wani fushin ke kuma kika zo , ƙara riƙeni yayi sosai a jikinshi hawayenshi ya ɗigo a saman wuyana ya sassauta murya yace dan Allah An mata idan kika kirani ban ɗauka ba ki daina zuwa wurina kuma ki daina kiyi ta kirana idan kin kira sau ɗaya ban ɗauka ba kinji ko ? Nace tou haƙuri ya bani saida ya tabbatar na samu natsuwa ya gogemin hawayen fuskarta nima ya umarceni da in goge mishi nashi da hannushi yayi min nuni goge mishi nayi tare da shafa gemunshi najashi dan yana burgeni , murmushi yayi mai kyau tare da gogamin gemun a fuskata , a kasanlance na sake komawa jikinshi na kwanta , dariya yayi cewa jeki zanzo gobe insha Allah , dakel na iya fita daga cikin motar na wuce ciki kamar wacce bata da lakka a jikinta , cike da tausayin Sultana su Dikko suka bar gidan....

Bayan Dikko ya gama ci musu uwa motarshi ya hau yai tafiyarshi , haka akayi ta ibar mutane ana tafiya dasu asibiti , Momy bata faÉ—awa Dady ba amma dan sharrin mata aka samu wacce ta sulalewa Dady waya ta fesa mishi komai , shima daya tashi bai kira Momy ba ya kira Dikko bayan sun gaisa yace Babana duk abinda kakeyi ka barshi zuwa jibi ka sameni , wato kaga bana nan shine kake duk abinda kaga dama ko ? Na taho ganin likita ban dai tsira ba saidai ka kasheni hankalin ka zai kwanta ? To ka taho ka sameni zuwa jibi na baka yana faÉ—in haka ya kashe wayarshi.

Tunda na shigo É—akina nake tunanin wannan wace yarinya ce ? Bansan mutanen su Hafsa ba amma naji a raina inasan sanin yarinyar da Dikko yayi ma kuka saboda tausayin ta , kuma inasan nasan dalilinta na shiga karuwanci , Dikko yana da tausayi amma baida mutunci ko kaÉ—an da wannan tausayin nashi Allah ya kamamin zuciyarshi akan abinda yayi min a baya , tabbas ina san sanin ya rayuwarsu Amisty take yanzu , ina san sanin a wane hali Ummu Affan take matar auren da nayi silar zuwanta bariki , ina san sanin abinda yasa matar Baban Babana ta korasu daga gidan mahaifinsu , ina san sanin labarin Aunty Suwaiba , ina san karatu kuma ina san Dikko sannan ina san sanin abinda ya kashe matarshi ko da gaske tsafetan yayi ?.... Kuma gaba É—aya sai nayi babu wanda zan fasa a ciki !

Sai kuma rashin lafiyar Dikko da abinda yake sashi cusa ɓacin rai a cikin farin ciki wani , tabbas saiya faɗamin meya jawo mishi wannan lalurar da fushin wani yake shafar wani...

Asibiti mai kyau aka kai su Al ' Ameen duk wanda Dikko ya daka babu wanda baima rauni ba , ya gota wasu ya karya wasu Al ' Ameen duk yafi kowa shan wahala dan har safiyar yau bai dawo ba , amma likitoci suna ta bakin ƙoƙarinsu wurin ceto rayuwarshi...

Duk azabar dake damun Bello bata barshi ya zauna a asibiti ba guduwa yayi domin ya kudiri ganin bayan Sultana , dan haka yabar asibiti ya koma gida ,

Da sauri ya fito daga toilet yasha wanka a gaggauce ya saka kayanshi bayan ya shafa mai ya wanke jikinshi da ruwan turaruka dan yanzu yake so ya wuce akwai abinda zaiyi Abuja kafin yabar nigeria , cike da kissa ta shigo ɗauke da kofi ta haɗoma Dikko tea data barbaɗeshi da garin maganin da Al ' Ameen ya kawo mata , cike da kwarkwarewa tace my excellency kasha wannan kafin ka tafi , da sauri ya ansa ya ajiye a saman madubi yana ɗaura agogo bayan ya gama ya saka takalminshi wurin ɗaukar wayarshi kofin ya biyoshi ya faɗo ƙasa ya watse , cikin kyarmar jiki Jiddah ta dafa goshi tace bara in kawo maka wani , kallo ɗaya Dikko yayi mata yai murmushi yace haka nake ni da zaran gishiri yayi yawa abunsha ko abinci ɓarewa yakeyi haka rayuwata take tunda safe kina so ki ɗuramin masifa babu gaira babu dalili , yana faɗin haka yayi gaba ,

Ko wurin Sultana bai biya ba kuma bai kirata ba haka kuma baije gidansu ba danyi ma Momy sallama suka kama hanya daga shi sai Ashiru...

Bayan la'asar Yazeed yazo ciki muka shiga suka gaisa da Kaka aka kawo mishi ɗan abun taɓawa bai taɓa komai ba muka shiga firar duniya , ya daɗe sai gab magrib ya tafi bayan na faɗa mishi zanje daura gobe idan Allah ya kaimu yace zaizo ya akaini , yayi hauka da kuɗi wa duk wani ma'aikaci dake gidan itama Kaka ya bata kuɗi masu yawan gaske , ni kuma wasu irin jikkuna yasa aka shigo min dasu masu ɗauke da kaya iri daban ² kuma nima ya bani kuɗi gaba ɗaya ma'aikatan gidan maganar Yazeed sukeyi da irin kuɗin daya bada , tou wai me hakan yake nufi........?

20/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA...* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 60

Ɗan bubbuɗawa nayi na lalleƙa gaskiya Yazeed baida hankali wannan irin haukan duk me ya jawoshi ? Duk abinda ya shafi na sakawa a jiki babu abinda Yazeed bai sako ba , turaruka mayuka gyaluluwa takalmi jikkuna materials masu kyau da tsada lessess shaddoji masu tsada atamfofi ƙarshen iskanci hada breziya da fants ondy da sabuwar waya cikin kwalinta mai tambarin apple a bayanta , nima dai ya zubo kuɗi wanda saida suka bani tsoro ,

Salati nayi naja baya da sauri banma sake gigin ko kallon inda kayan suke ba bare na sake tunanin taɓasu , ɗakin Kaka na nufa na samu tana waya da Inna wuri na samu na zauna cike da mamaki , ina zama tace ga Maryam nan ta faɗi maganar tare da miƙomin wayar ,

Ansar wayar nayi tare da kallon Kaka ita tana san lulluɓi bata san ɗaura kallabi sai a wani fiddo kunne waje kome hakan yake nufi oho , Hajiya Inna haka na faɗa a dai² lokacin dana kara wayar a kunne na , ya kike ? Lafiya qalau wai yaushe zaki dawo ? Idan na dawo me zan miki ne ? Haba kema da Allah ki dawo Inna , zan dawo ai bai gama abinda yakeyi ba , waye ? Mijina mana , cikin in ina nace Inna miji......? Ey mana yanzu aure kikayi saboda Allah ? To kar inyi ? Wani irin kishin Babana naji ya kamani nace kawai sai kikayi aure haba Inna ke me zakiyi da aure da Allah ? Dariya tayi sosai naji tana cewa Sultana ce ,

Sultana zaku gaisa da Alhaji , nace ki gaishe shi sallah zanyi , ina faÉ—in haka na maida ma Kaka wayarta na shige toilet nayo alwallah sallah magrib bayan na fito É—akina nai tahowa ta , ina shigowa naji wayata na tsuwwa da sauri na isa wurin wayar , murmushi nayi tare da É—aukar wayar cikin farin ciki,

Na koma saman gado na kwanta cike da shaƙun so zuciyata nata tsumama da soyayyarshi nace hello , ke yarinya me kike nufi ne yau baki kirani ba ko kinyi fushi da nine ? Murmushi nayi tare da ɗan murginawa na lumshe idanuwa na gaskiya ina jin daɗin muryar Dikko tana sakani ciki wani irin yanayi dani kaina bana iya ganewa , nima irin abunda yakemin nayi cewa zanyi sallah idan na gama zan kiraka , tou kimin addu'a , nace me zan roƙar maka , ki roƙarmin Allah yasa miki soyayyarta wadda bata gogewa har abadan duniya , ubangiji yasa nine mijinki , duk wanda baya san aurenmu Allah ya sanyaya masa zuciyarshi shi da kanshi yace Dikko ka auri yarinyar nan kana santa tana sanka ,

Nace zan maka amma ni bazan aure ka ba , murmushi yayi yace ni ko zan aureki in Allah ya yadda kuma inaji a jikina lokaci yana kusa , ai nace bazan aure ka ba , Ey dama ai nine zan aureki bake ba , kinsan Allah ki daina min abinda bashi da kyau idan ba haka idan na aureki duk abinda kikai min saina rama , ka rama idan na aurenka mana...

Haka kika ce ? Nace Ey , aiko yarinya zaki ga ramuwa hada ta gayya kice zaki je gida in koma daga gefe in haɗe rai ince baza ki ba , kice dan Allah...... Wata magana yaso yayi amma ganin nayi masa "yar ƙarama kamar yadda yake faɗa saidai yayi dariya yace An mata Allah dai yasa ke rabona ce , a cikin zuciyata nace amin tare da tsinke kiran....

Wani irin ihun jin daɗi nayi na miƙe saman gado nayi rawa Allah yasa haka mutumina Allah yasa muyi aure , ina sanka ׳.............. Da tsalle na sauko daga saman gado ina rawar jin daɗi , rumgume hannuwana nayi nai juyi An mata.... Wai me yasa kake cemin An mata......? Banda mai bani ansar wannan tambayar....

Murmushi Dikko yayi tare da gyara kwanciyar shi yace An mata kenan kinga irin yarintar taki wai zakimin addu'ar amma baza ki aureni ba , hmm yarinya kenan kinaji da ƙuruciya sosai har yanzu kanki ɗanye ne amma zan dafa miki shi gaki ga Dikko ubangiji yasa nine mijinki am3n ,

Har yanzu Al ' Ameen bai dawo ba , likitoci suna ta bakin ƙoƙarinsu amma shiru kake ji kamar an aiki karuwa ɗakin kwarto , yauma abiyar zaman Momy ta kira Dady ta faɗa mishi har yanzu fa Al ' Ameen babu wani ci gaba sai ƙasa yake ƙarayi kuma Momy ko ganinshi bataje ba , kuma ta sani sarai ɗan ta yayi wannan iskancin tunda a gaban idonta ya doki Al ' Ameen bata ce komai ba tunda daga wurinta ya fito duk yadda akayi ma itace ta tiroshi sai Dikko ya zauna yaita iskanci amma ba'a iya ma yaro magana kamar ɗan ido ,

Tuni nace ka kaishi gidan mahaukata sai kace ɗanka lafiyarshi qalau yanzu mai hankali zaiyi abinda Dikko yayi ? Cikin ɓacin rai Dady yace ni ban haifi mahaukaci ba , lafiyar Babana qalau kuma Maryam babu yadda za'ayi tasa Babana ya daki wani tunda tasan abinda yake damunshi , duk dai abinda mutum yayi shida Allah kuma ba Maryam aka cuta ba ni aka zalinta duk mai sa hannu a lalurar Babana nakai ƙararshi wurin ubangiji kuma sai Allah yayi min hisabi dani dashi wallahi ban yafe ba kuma bazan taɓa yafewa ba , yana kaiwa nan ya tsinke kiran ya fara kiran Dikko.

Gaisawa sukayi bayan ya ɗauka Dady yace Babana har yanzu me kakeyi ne ? Dady ni ina Abuja , tou duk abinda kake ka kasance tare dani idan Allah ya kaimu gobe na faɗa maka , insha Allah , me ya haɗaka da Al ' Ameen kayi mishi duka haka ? Wai bana hanaka wannan doke²n ba ? Badai zaka zauna da rayuwarka lafiya ba ko ? Sai kayi ta abu ana dan ganaka da zararre ,

Cikin kwantar da murya yace Dady kasan bana iya sarrafawa , tsohon laifi ne na daɗe ina ba zuciyata haƙuri jiya ne taji bata iyawa shi yasa haka ya faru , Allah ya kyauta ya baka lafiya , ubangiji ya yaye maka abinda yake damunka , da am3n ya ansa saida Dady yayi mishi nasiha sosai sannan yace kuma karya zo da kowa yazo shi ɗaya yace insha Allah , cike da soyayyar Dikko Dady ya ajiye waya yana mai tausayin ɗanshi da lalurar dake damunshi , gashi cikakken mutum mai cikar zati da ƙwarjini amma saboda haukan kishi na mata an birkita mishi kwalwar ɗa , matsalar dai kawai yayi fushi idan har yayi fushi tofa nan ake samun matsala danma ana ta roƙon Allah , kuma roƙon Allah gaskiya ne baya faɗuwa ƙasa dan ubangiji maji roƙon bayinsa ne....

Dikko yana da mutunci kuma yana da kirki Allah yasa mishi tausayi amma yafi tausayin mata a rayuwarshi , kuma tun kafin matsalar nan ta sameshi bai ɗaukar raini kuma da an taɓoshi sai anji babu daɗi bai iya zuciya ba haka kuma sai laifin wani ya shafe wanda baisan anyi mishi ba , dariyar mugunta dama haka Allah ya halicceshi tun fil'azal baya dariya kuma shi bai cika murmushi ba ,

Koda Dady bai samu namiji ba ya tashi hankali sosai kuma duk matanshi kowa addu'a take Allah yasa itace zata haifo , shi kuma a tunaninshi duk wacce ta haifa duk ɗaya tunda suma "ya "yanshi mata baice baya sansu ba kuma kowa tana da , amma tunda aka haifi Dikko sai wutar kishi taita ruruwa sai jefe² har suke ganin kauda Dikko daga duniya shine kawai kwanciyar hankalinsu , tun yana ƙarami suke asirinsu kuma basu gaji ba daga ƙarshe aka tura mishi aljannu su shanye jininshi ya mutu , yasha wahala sosai babu wanda yayi tunanin zai sake rayuwa amma ubangiji yayi alƙawarin rayayye ne ,

Ganin ba'a samu nasarar hakan ba yasa akayi amfani da fushinshi wurin saka wani fushin idan har yayi zuciya sai ya fita hayyacinshi yayi ta hauka bayaji baya gani ya riƙa kiran saiya kashe sai yabi takan mutum da mota , tou kalmar kisan itace ba'aso yana faɗa idan yana fushi dan idan yace zaiyi kawai sai yayi yake samun natsuwa , to idan yace saina kashe ka daga nan yake tafi sai ya ɗauke wuta ya faɗi , tanan ake neman sa'ar sa ake farautar numfashin shi a haka aljannu ke so suyi nasarar raba gangar jikinshi da ruhinshi su shanye mishi jini ya mutu.... Shi yasa ya faɗawa Sultana idan yayi fushi bashi bane ba ta kiyayi fushin shi saboda baya da kyau , tayi ta haƙuri dashi har Allah ya bashi lafiya !

Ana ta neman taimako dai , wannan magungunan da ake mishi amfani dashi na cikin baki dana shaƙawa abokin Dady ne ya nemosu dan ya tausayawa Dady akan lalurar Dikko saboda Dikko ke ciwon amma Dady ke jinyar bawai jinya ta kula ba , jinyar kar Dikko ya mutu shi yasa duk abokanan shi suka miƙe suka tayashi neman taimako , kuma har yanzu ba'ar nema ba , yanzu haka ma idan Dikko ya samu Dady a inda yake idan ya gama ganin likita zai wuce saudiyya suyi umara tare sai ya dawo dashi inda wani amininshi yace mai maganin yace sai an kawo mishi Dikkon , dan da Dady ya bari saiya dawo amma haukan da yayi jiya yasa Dady yace ya sameshi.

Dikko ganin Sultana bata da niyar kiranshi yasa shi ya kirata , har na fara bacci kiran wayar shi ne ya tashe ni , cikin gigin bacci na ɗauki wayar na gaishe shi da muryar wanda bacci yafi ƙarfin shi , cikin murya mai nuna da fushi yace har yanzu baki gama sallar ba ? Bacci ya riga yafi ƙarfina kawai na kashe wayar banma san na kashe ba , ƙara kira yayi har yanzu bacci bai sakeni ba , dakel na ɗauki wayar na ɗorata a saman kunne nace inajinkan , ni zaki kashe ma waya har kin isa in kiraki ki kashemin waya An mata......?

Da sauri na buɗe idona dan namayi tunani ko a mafarki nake wayar wallahi , yi haƙuri don Allah wallahi na fara bacci ne tsoki yayi tare da kashe wayarshi gaba ɗaya , da sauri nabi bayan kiranshi amma har ya kashe wayarshi akace a kashe take....

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un haba ina amfani halin Dikko dan Allah anyi mutum rayuwarshi babu uziri , kwata² bayamin adalci bayan yasan da kaina ina kiranshi , shi so nawa na kirashi bama ya ɗauka tou idan ka kira kai baka cika Dikko ba , kuma nima har abadan duniya bazan sake kiranka ba da Allah can tsamiyar biri dakai mtsww....

Komawa nayi nai kwanciyata cikin ɓacin rai , shi wannan Dikko baida haƙuri ko kaɗan sai zafin kai shi ɗan zafin zuciya ko an faɗa maka bana iya rabuwa dakai , ko zan ragu ne idan na ɓata dakai duk abokanka ma sunfi ka kirki masu haƙuri kaiko komai fushi duk namiji shi ke sarrafa fushin mace amma kai ƙato dakai saini zanyi ta haƙuri dakai ? To bazanyi haƙurin ba kuma an ɓata babu ranar shiryawa.....

Wuri ɗaya ya ƙurawa ido yana kallo , ajiyar zuciya ya sauke mai tattare da ɓacin rai , murmushin ƙarfin hali yayi a bayyane yace wai Allahna , wai..... Wayyo ya ƙarasa yana mai kwanciya dakel cikin yanayi mai nuni da wahaltuwa ,
lumshe idanuwanshi yayi ya ƙara cewa wai........ Wai Allahna , kukan Sultana ya riƙaji a zuciyarshi idonshi ya cika da hawaye yayin daya tuno yadda yayi da ita a safiyar daya anshi budurcinta ta ƙarfi da yaji ya ɓata mata , gangarowa hawayen yayi daga cikin idonshi saida ya sake wai..... Wayyo har yanzu idonshi a rufe a zuciyarshi yace Allah na tuba ׳ , Allah ka ƙaddara aure na da "yar yarinyar nan ya ubangiji kasa An mata rabona ce duk abinda zanma yarinyar nan nidai nafi so kawai na aureta ta samu natsuwa dani , ya Allah kaji ƙaina ka tabbatar da auren mu , zan nunawa An mata tsantsar soyayya mai tsafta zan gatanta ta kuma zata samu natsuwa daga gareni mai sa natsuwa ,

Ashiru ya kwalawa kira bayan ya samu natsuwa , da sauri ya shigo cikin girmamawa yace mai gida , ran Dikko a haÉ—e yace wani tunani nayi me kake tunani game da Yazeed da yace zaije zance.....? Cikin girmamawa Ashiru yace mai gida kila wasa yakeyi ,

Murmushi Dikko yayi tare dayin shiru yana nazari , bayan wani lokaci yace tabbas sai yaje wallahi sai yaje wurin An mata , nasan halin Yazeed ciki da waje , yanzu nayi wani tunani idan ka fahimci rayuwarshi ya cika leƙe² aiko idan har ya leƙo An mata saina tada katsina da bala'e ,

Tun bansan meye iskanci ba nakejin kalmar iskanci a bakin Yazeed , idan kayi tunani goruba ba majalissar shi bace tunda yaga An mata ranar dana daketa ya dawo da zama gidan nan , jinjina kai Dikko yayi yaci gaba da cewa lallai akwai abinda zai faru , miƙewa yayi tsaye yace zafa a samu matsala ya ƙarasa maganar yana ma Ashiru wani irin kallo , da sauri yaja da baya yana cewa mai gida haka bazai faru ba ,

Dikko yace abun yakemin yawo a zuciya yace An mata ta cika zama É—aki kamar mai jego , yawan zama da hijabi kamar mai takaba , ya gajiyan hawa doki ko zaki hau na bankwana , kyautar zobe a maimakon kuÉ—i kamar yadda sauran sukayi mata , duk haka yana nufin wasa ne.....? Me yasa su sauran basuce haka ba ? Mahaifiyar An mata bata nan tayi tafiya zuwa Dubai ita da mijinta da mukayi waya da ita nace sai ta dawo zan dawo da An mata , abinda yasa na mayar da ita shine ,

Washe garin ranar dana bata kashi su Yazeed su suke riƙeni lokacin dana bigawa An mata kai da bango , tayi ƙara sau ɗaya mai tsananin tayar da hankali , ihunta shine ya jawosu suka shigo ciki da gudu a lokacin ita kuma ta suma....

Gaba ɗayansu sun riƙeni , ni kuma ina zabura cewa saina kasheta , kowa haƙuri yake bani hankalin kowa yana kaina amma idon Yazeed yana saman An mata , abinda tayi min suka fara tambaya ina cikin wani yanayi saina ce na hanata fita shine ta fita maza suka daketa to da wani ya daketa gara ni da hannuna in kasheta , ko ina cikin yanayin fushi duk abinda akeyi ina sane kuma kar nake bana mantuwa , tabbas naji Yazeed yace wannan tafassar fa.......?

A dai² lokacin na kwace na fita daga gidan , ranar a gidan ya yini har 1:21am yana nan a tunaninshi zan tafi baisan tunda na dawo da An mata goruba na daina kwana gidana nake kwana tare da ita , ita kanta bata san gidan nake kwana ba saidai kawai ta ganni da safe , Yazeed yace min DK yaushe zaka wuce ne ? Nace masa aini bana fita sai kowa yabar gidan nake fita , sai yacemin tare zamu fita , nace masa bana zuwa da kowa kuma bana fita da kowa , yace zai bini a haka dai saida nayi mishi gatso² ya tafi , misalin 2:09am ya kirani na ɗauka yace wai na wuce ko ina goruba ne ? Nace masa ya akayi ne ? Murmushi Dikko yayi tare da cewa waini za'a ɗauka sakarai bayan har "yan cikin Yazeed ina kallo.

Kallon Ashiru yayi sosai tare da buɗe duk girman idonuwan shi masu ba mutane tsoro yace , kawai Yazeed cewa yayi wai "yar yarinyar nan nake tausayi an barta ko yata ƙara jin jikinta ne ? Sakaran banza sai na rubza shi a rami mayen kuma saiya faɗa , { bai faɗi maganar da yayi da Yazeed ba haka kawai yacewa Ashiru } Dikko yaci gaba da cewa ,

Da safe sai An mata ta fito palo ta sameni tana kuka , bata yafe ba duk wanda yaji mata ciwo a gefen fuskarta , na kirata tazo kusa dani na bata haƙuri kuma na lallasheta ta saki ranta mun fara magana Yazeed ya shigo , ni kaɗai nasan fassarar kallon da yayi mata , ta tashi na zaunar da ita saman kujera , kallon da yake mata yasa nace ta ɗauki makullin mota ta ɗauko mana abinci , tana fita ya matsamin muka fita , bayan takai miya ta kwanta yasa na fiddota , nayi niyar zuwa da ita wani wani taron da zamuyi a ranar daka maida ita gida bayan shine ya matsamin naje , na yadda yace inje da An mata nace masa bazani da ita ba , hmmm waini zaima wayau sai ya zuƙe da matarshi kaza ² ya kawo wani makirci ya raɓa , da naga zai maidani wani ruwan tsakar dare kawai na maida An mata gida wurin kakarta bayan na faɗawa mahaifiyarta , yaga gidan shine yace zaizo zance , kawai na ɗauka yana wasa ne amma naji a jikina kamar yaje , ko zaije Allah ya tsallake shi a tarko fitinata ,

Ashiru yace mai gida anya zaiyi haka duk halakcin da kayi mishi , Dikko yace manta da wannan matsayin dana ajiyeshi daban kuma idan ya kuskura yace zai shiga rayuwar An mata zanci ubanshi ne kawai kuma dan naci mutunci shi bazaisa na rabashi daga inda na ajiyeshi ba jeka kawai , fita Ashiru yayi Dikko kuma toilet ya shiga dan yayi wanka.....

Ashiru kuma tunani yake akan maganganun Dikko idan ko har Yazeed ya shiga rayuwar Sultana za'a samu matsala , kuma yayi ƙaton butulci dan Dikko ya suturashi ya farfaɗoshi daga masifar talauci ya kwato mishi "yan cinshi a cikin abokansu , yana zalincin Dikko amma dake shi abun duniya bai rufe mishi ido ba bayajin komai , domin Yazeed yana wulaƙanta dukiyar Dikko da ƙeta an faɗawa Dikko sai yace ai idan Allah ya baka arziƙi tou ba naka bane ba kai ɗaya , yace kuɗinshi na kowa da kowa ne duk yadda Yazeed ke facaka da kuɗin Dikko baya mishi magana kuma ko abokansu da sukayi ma Dikko magana ya kori Yazeed daga dukiyarshi karya talautashi kamar yadda ya lalata arziƙin mahaifishi Dikko cewa yayi ko haka ya tsaya ya daina neman kuɗi nan da shakaru dubu baya talauci....

Ajiyar zuciya Ashiru yayi tare da cewa gaskiya mai gida yana da haƙuri addu'a yayi Allah ya tsare arziƙin Dikko domin shi bangone ga duk wanda ya raɓeshi dan Allah yayi ma Dikko kyauta kuma kyauta mai ɗauke lumfashi hannunshi buɗe yake shi yasa Dady ke cewa yasan koya mutu Dikko zai zama uba ga "yan uwanshi , gaskiya Dikko yana da kirki sosai saidai matsalarshi fushi sai mugunta da ƙeta...

Yazeed abokin Dikko ne , kuma shima Yazeed ɗin babanshi cikakken attajiri ne sai Allah ya kawo mishi karayar arziƙi kuma duk Yazeed shine silar lalacewar komai na ubanshi dan shima yana harkar wasan danbe ya daɗe sosai a cikin harkar , da abokai suka ga bashi da wani kuɗi a hannunshi sai suka cireshi daga cikinsu shi kuma lokacin Dikko baya nan.....

Bayan ya dawo daga tafiya yaga baya ganin Yazeed daya tambaya sai sukace gaskiya DK mun cire Yazeed a cikinmu , bashi da ko sisi zai zama mana damuwa , Dikko yace ba'a rayuwa haka kar a barshi rashin kuÉ—i yasa ya shiga wani hali na daban gaskiya a ceto rayuwarshi dan duk wanda ya saba mu'amula da kuÉ—i idan ya rasa yana samun damuwa , a tausayawa duk wanda ya samu ya rasa....

Sai sukace sudai basa zama dashi gaskiya zai rage musu matsayi ne kuma ana ganin girmansu a gari duk wani matashi addu'a yakeyi ya zama kamarsu sai kuma su fara rage zafi gaskiya basa iyawa , amma sai kuma suka ɓoyewa Dikko Yazeed yana wasan danbe.....

Shine Dikko ya farfaɗo da rayuwar Yazeed ya bashi manager a wani companyn shi , yaga kuɗin banza ya shiga daddagar musu uwa , mutane yadda suka ga Yazeed lokaci guda ya zama mutum yana wulaƙanci da kuɗi sai sannan suka cewa Dikko ai yana wasan danbe Dikko yace ai basu faɗa ba shi kuma ya wuce wurin dan idan ya tafi baya dawowa , duk wulaƙancin da yakeyi da kuɗin Dikko shidai Dikkon bai taɓa nuna mishi komai ba , koda ya fara mai gida Dikko yace baya so ya kirashi kamar yadda ya saba tun farko ,

Sai ki haɗa mace 20 zakiji duk sunce su "yan matan Yazeed ne , ɗan neman matane na bala'e , duk macen daya gani saiya lasa ta , tunda yaga Sultana tsutsar masifar jarabarshi ya tashi kuma ya ɗana mata tarko itama so yake ya lashe ya wuce , idan har mace ta kuskura ta faɗa tarkon Yazeed nata ya ƙare......

Cikin farin ciki na wayi gari , a murnace nake ta huɗɗoni na sai shiri nake na tafiya Daura , tun ina wanka ake cemin nayi baƙo a waje , dan gaskiya rayuwar gidansu Inna babu takura zan fita duk lokacin da nake so in dawo babu wani tsanani , idan zan fita Kaka tana nan zatace min Allah ya tsare kuma idan na dawo taga dawowa na zatamin sannu !

Ina fitowa daga wanka hijabi na saka nayi waje , a harabar gidanmu naga motar Dikko , da farin ciki nayi wurin motar ina zuwa Ashiru ya sauke gilashi ya gaisheni , ansawa nayi cikin halin ko in kula , yace ranki ya daÉ—e mai gida yace inzo in zauna dake harsai ya dawo kuma duk inda zakije nine zan kaiki ,

Cike da masifa nace kamar ya ka zauna dani ? Ko ance neman wanda zai tayani zama nakeyi ni bana san kilbibi kawai ka kama gabanka , Ashiru yace babu inda zanje ko a napep zaki fita yace kawai in riƙa bin bayanki shine abinda yace , to me yake nufi da abi bayana , Ashiru yace nima haka yacemin , aiko sai inga wanda ya isa yabi bayana , Ashiru yace mai gida ya isa kuma sai nabi bayanki saidai ki fasa fita amma ina nan daga nan har Allah ya dawo dashi lafiya ,

Cike da masifa na nuna Ashiru da ɗan yatsa nace kasan sharrina kuwa ? Banza yayi ya ƙyaleni , nace tou bakai ba ko ubangidan naka bai isa ya sakawa rayuwata ido ba dani dakai mu zuba , nayi wanka yanzu zanje daura ka biyoni idan ka isa kuma ta gabanka zanbi in wuce lusari kawai dakai , ina faɗin haka nayi ciki ,

Murmushi Ashiru yayi tare dabin bayan Sultana da kallo , tunanin Dikko yayi da yace masa , An mata tana wayau sosai kuma haɗarinta yawa gareshi tana anfani da wani abu take sa mutane bacci dashi sai ka kula , mai gida ya akayi ka sani , wurin "yan daban da take amfani dasu domin saida nasa aka tattaromin su akan wani binke daya shafeni ka kula tafiyata ta zama dole saboda Dady yana jirana Yazeed sharrinshi yana da ƙarfi na baka amanar An mata Ashiru idan har wani abu ya faru da ita bazanyi kuka da kowa ba sai kai , Ashiru yace mai gida bana tunanin zata fita ta tsorata dakai , Dikko yace batajin tsoro na irin An mata duka baya mata amma zata tsorata dani da zaran na aureta dan irin su An mata hukunci ɗaya ne maganin su kuma dashi zan horata kowa zaiyi mamakin natsuwarta dan yadda nasan zan mutu haka nasan sai An mata ta fita ,

Ashiru yace lallai kuwa gata ita daura zata tafi ma , zanga ta gidan ubanda zaki bi ki fita , fitowa yayi daga cikin mota ya fara duba saman katangar gidan da aka zagayeta da wayoyi masu raba mutum gida biyu su tsisstige masa hanji , zagaya gidan ya farayi ko zai samu wani wuri daya buÉ—a inda zai ba mutum damar fita ,

Dariya nayi nace ga É—an boko wanda ya zaga duniya ga jahila wacce ba ilimin boko kuma babu inda taje tana rayuwarta ne a cikin birninsu yau zanga yadda zamuyi wannan wasan dakai malam Ashiru dan wallahi ko min bala'e sai naje daura kuma sai naje na dawo kana nan banza kwance a mota kana baccin asara............

Muyi wasan.....

21/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA....*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 61

Ina saka kayana ina mita cewa naga yanda za'ayi wani ƙaton banza ya hanamin nayi rayuwana yadda na tsara abuna , zanje daura dole saina san dalilin da yasa aka yankewa Aunty Suwaiba ƙafa , a madubi na kalli kaina kamar ina ma wani kashedi na nuna da ɗan yatsa duk wanda ya shigo da takura a rayuwata , abuna da nake fesawa na bacci na ɗauko dan yana cikin jakar makaranta na tuni nake neman sa'a akan Dady dan ina da ƙudiri akan shi sosai a zuciyata , ta cikin madubi na fesashi fesss dariya nayi tare da cewa haka zan feshe ka kamar na watsawa sauro magani maimakon kai ka mutu sai kawai ka tafi duniya bacci.....

Ina gama saka kayana na yafa gyalena na ɗauka jakana dan a lokacin har Yazeed yazo wayata na ɗauka da kwalbar abuna na fice daga cikin ɗakina dan ko Kaka ban faɗawa Daura zanje ba kuma ban leƙa mata ban kwana ba !

A harabar gidan na samu hayaniya ya gauraye tsakanin Ashiru da Yazeed kowa sai ɗaga murya yakeyi kamar zasu buga , wurin Yazeed na nufa nace masa ya akayi ne ? Cikin ɓacin rai yace wannan jakin ne zai ɓatamin rai , wai me yace ne ? Nayi tambayar ina kallon Ashiru amma Yazeed na tambaya ,

Yazeed yace cemin yayi ni ɗan iska ne ina leƙe² nazo zan leƙaki , ɗauke idona nayi daga kan Ashiru nace ma Yazeed miye leƙe² ? Duk shiru sukayi , murmushi nayi a raina na kalli Ashiru nace Dikko yace idan ka bari na fita zaka bini ko ? Yace Eh , nace idan Yazeed zai ɗaukeni fa ? Shima sai naje , kallon Ashiru nayi sosai ƙosashshen ƙato ne mai sigar "yan restyling ya ƙoshi sosai Dikko yayi mishi horon ƙarfi ko ina ya cika kamar anbi jikinshi an tsatstsaga mishi dutsina saboda cikarshi ,

Ajiyar zuciya na sauke na kalli Yazeed nace wai miye leƙe² ? Kowa shiru yayi , to tunda baza kuyi magana ba kai Yazeed muje kafin rana yayi , juyawa Yazeed yayi da niyan tafiya Ashiru ya shaƙoshi ta baya , murmushi nayi a bayyane tare da cewa kai yaro sakar mishi wuyan riga kafin inci uwarka , na ƙarasa maganar ina nuna mishi da kaina ,

Ni zaki ci ma uwa ? Ya tambayeni , nace ba kai kaɗai ba hada Dikko naci uwarka naci uwar wanda ya turoka ka zauna dani , gyara tsayuwata nayi sosai tare da nuna Ashiru da ɗan yatsa nace ai saboda so duk za'a sakawa rayuwata ido ko ? Shiru Ashiru yayi yana kallona a nutse baiyi magana ba , naci gaba da cewa ni dama inda na gode Allah ban taɓa cewa ina san Dikko ba , tou wai waye ma zai so mahaukaci ?

Yanzu mutum anjima aljani , a haukan nashi yake tunanin zan iya aurenshi ? Bashi da aiki sai zafin kai da doke² idan har baka fita harkata ba saina tona maka asiri , ke ni zaki tona ma asiri.....? Tabbas nasan ahalinka kaf kuma nasan abinda ya raboka daga gidanku ka dawo rayuwa ƙarƙashin mahaukaci , { kuma ƙarya nakeyi bansan komai game da rayuwarshi ba , }

Ashiru yace ke yarinya bamu da sata bamu da maita kuma bamu gaji iskanci ba duk duniya wannan abu 3n dana faÉ—a É—aya daga ciki mutum zai samu kanshi yaji takaici kuma shi ubana baya taushewa....

Nima ban gaji iskanci ba hayenshi nayi kamar yadda kaima baka gaji kwaraka ba kake rayuwa a ƙarƙashin wani , kuma idan ubana ya taushe kaima ai naka ya taushe saboda kunne ya girmi kaka yaro idan baka san asalinka ba yanki fili ka shiga siyasa , Sultana bata siyasa amma rayuwar kowa da labarin gidan kowa yana a tafin hannuna saboda ɓacin rana , kasan duk wanda baisan kanshi ba daya shiga siyasa duniya zata faɗa mishi koshi ɗin waye , nima siyasa ce duk wanda ya shigoni zan warware mishi dan nidai ubana bai taɓa murƙushe surikarshi da ɗiyar maƙocinshi ba , { kuma haka nan kawai na faɗa dan in ɓata mishi rai bansan komai game da rayuwarshi ba , } cikin ɗaga murya Ashiru yace ke...... Ki gyara kalamanki akaina tun kafin in ƙera miki rayuwa , a sanyaye nace malam Ashiru ai yanzu muka fara , zama fa tare dani zakayi anshi wannan kafin in dawo , kafin ya ankara na feshe banza ya ƙame a wurin ,

Da taimakon masu aiki da kuma Yazeed aka sakashi a mota bayan na faɗa musu ciwon farfaɗiya yake , haka ciwon yake taso mishi lokaci² , ina ƙoƙarin rufe motar naji wayar Ashiru tana kuka a aljihunshi , Yazeed nasa ya cirota nace waye yake kira ? Yace mai gida , saida nayi dogon nazari sannan nacewa Yazeed ya maida mushi wayarshi a jikinshi muje ,

Maida wayar yayi jikin Ashiru mu kuma muka shige mota mukai tafiyarmu , tunda muka kama hanya bana tunanin komai sai tunanin irin halin Dikko , ga zuciya kamar kumburƙuma , mema Dikko yayi min na rayuwa wanda ya kamata ace na so shi ? Bashi da aiki sai doke² so biyu yana dukana na farko saida na suma , na biyu dakel aka riƙeshi umm gaskiya bana san namiji da zuciya gashi bashi bada uziri ko kaɗan na rayuwa jiya daga ya kirani na fara bacci kawai ya hauni da masifa , na sake kiranshi ya kashe wayarshi gaba ɗaya..

Dai² saitin zuciyata na dafa a bayyane nace kiyi haƙuri dan Allah dan annabi kiyi haƙuri ki goge wannan mutumin daga cikinki , a sirrance na sake cewa me ma Dikko yayi miki na rayuwa ? Mota ce kawai ya baki sai miliyan ɗayan kuma dan ƙaranta daci baya mahaifiyar shi ta ansa , gashi bata so na , kallon Yazeed nayi da wutsiyar idona , zuciyata tace kalli Yazeed shima dai lafiyayyen matashi ne jini yana motsawa ko ina ajikinshi , yana da ƙirar burge mace kuma shima dai ɗan kwalisa ne , me ake nema na rayuwa ? Idan dai namiji yana da "yan canjinshi kuma ya iya soyayya ai shikenan , kawai ki watsar da Dikko duk da dai badai wata makusa shima dai kyakkyawa ne gashi ɗan gayu uwa uba ya iya magana mai daɗi amma yanayin Dikko yafi na Yazeed nuna gogewa a wurin iya ɗagawa mace hankali ƙwayar idonshi ya nuna haka giraren shi kawai ka kalla kasan zaiyi jarabar masifa duk macen da Dikko ya damƙa zataji a jikinta bare kuma ni da yakeji ma haushi nayi imani da Allah irinsu Dikko sune masu horar da mace da azaba a wurin kwanciya matsawar tayi musu laifi , mace taita ƙarewa a rasa abinda ke damunta , ai dama yama taɓa faɗa min da bakinshi cewa idan harya aureni sai nasan shi ba abokin wasana bane ba bare ga Dikko da ƙeta , umm manta da Dikko kawai ki auri Yazeed na tabbata zakiyi rayuwa mai inganci dan shima jajirtaccen namiji ne tunda har baiji tsoron Dikko ba ya shiga soyayya dake wannan namiji yakai jarumi...

Ajiyar zuciya na sauke na sake kallon Yazeed da wutsiyar idona , kallon siffarshi nayi sosai domin Allah Dikko yafi shi zarrar cika cikakken namiji nesa ba kusa ba , duk baƙar hassadar ka babu yadda ka isa ka kushe Dikko wallahi , domin cikakken namijine jajirtacce yana da zarrar da duk macen data ganshi mai lafiya da sanin duk wasu qualitative na namiji tasan Dikko yakai kuma wallahi babu yadda za'ayi yaba kanshi kunya wurin mace a gado , mutum ɗan tara ne bai cika goma ba , ni gaskiya na haƙura da Dikko dan bansan ranar da zai samu lafiya , idona ya cika da hawaye gaskiya ina san Dikko sosai wallahi idan har nace bana sansa nayi ƙarya , domin duk yadda zan faɗa muku Dikko gani nake baza ku gane ba ,

Da wata irin ƙara ya farfaɗo wayyo Allahna mai gida karka kasheni kayi haƙuri na bari , wayyo Allah ku taimakamin zai kashe ni wayyo............. Wani irin ihu ya sakeyi wanda ya jawo duk hankalin wanda ke cikin asibitin yana cewa gashi nan ku riƙeshi wayyo kakkafawa Al ' Ameen ya sakeyi yana fizge² idonshi a rufe saboda tsabar tsoro , dole tasa akayi mishi allurar bacci dan ya cikawa mutane asibiti da ihu kuma ga marasa lafiya sosai masu buƙatar natsuwa.

Me wannan yaron yake nufi zanyi ta kiranshi baya ɗaukarmin waya ne ? Ƙaton banza kila ma yaje ya miƙa mata fuskar tayi mishi feshi , shi uzirinshi idan ya kiraka so ɗaya baka ɗauki waya ba zai maka uziri har zuwa lokacin dakai zaka nemeshi da kanka , akan Sultana kaɗai yake maimaita kira dan idan ya kirata bata ɗauka ba duk bayan mintuna saiya sake kira yaji ko zata ɗauka , hardai ya samu sa'ar barin nigeria Ashiru bai kira ba bare yasan a ina aka kwana....!

Duk wani shiri daya kamata tayi , tayi ta tattara duk wani abu da tasan idan taje tayi zata tafi da imanin Dikko , duk wani tsafe² saida ta haɗo kanshi , turarenta da man shafawarta da powder har kwallin da zata shafa a idonta duk anbisu an barbaɗesu da asiri , kaya masu azabar² ɗauka hankali ta ɗauka , wai ita zataje jinyar ƙanin mahaifiyarta wato Al ' Ameen , shiri tayo mai kyau da makaman yaƙinta tayo garin katsina bata san sunyi hannun riga da Dikko ba.....

Ni yanzu ina zansa kaina komai ya fara warwaremin kayi wani abu haka nan mana ai bana tunanin akwai abinda ya gagareka , ya ina neman mafita kuma ɗan gwamna zai shigo rayuwarta , yaron nan ɗan iska ne ya raina mutane duk garin nan babu wanda baisan halinshi ba baida mutunci kuma ya raina mutane dan baya ganin girman kowa a garin nan , dan gaskiya idan aka aike ka neman tantirin ɗan iska daka ga Dikko ka tsaya ka samu saboda wannan dalilin ne yasa nasa kayimin aiki akan ya lalatawa ɗiyar Binna rayuwa dan nasan idan har Binna yace zaiyi wani abu Dikko kawai zai iya bi ta kanshi da mota ya wuce , dan na tabbata daba Dikko ne ya farke yarinyar nan ba da har yanzu zaune bai ƙare ba.

Bello ne zaune a gaban bokanshi duk ya koro wannan sharfin tare da fashe mishi da kuka cewa tuni kasa ni nabar sallah azahar da asuba da isha'e amma ka kasa wani abu ? Wata irin dariya bokan yayi cewa akwai sauran mafita É—aya , jikinshi na kyarma yace wace mafita ce ? Saura la'asar da magrib zaka dakatar , Bello yace na ajiye 3 biyun kake tunanin zai gagareni ne ? Na daina sallah dama ai ba kullum nakeyi ba ni koma miye zanyi amma duk yadda za'ayi nidai a raba yarinyar nan da Dikko ko kuma in aureta kawai kaga sai in ida cika burina tana gidana , hahahahaha bokanshi yayi dariya tare da cewa idan dai kana san ganin burinka ya cika na auren yarinyar nan yanzu sai ka auri mahaifiyar , zaro idanuwa Bello yayi tare da cewa kamar ya in auri mahaifiyata kuma boka ?

Wata irin dariya yayi mai ansa kuwwa gaba ɗaya dajin ya karaɗe da ƙarar dariyarshi bayan ya samu natsuwa yace yarinyar tana da ibada tana sallah akan lokaci kuma tana da karatun littafin Allah babu dare ba rana , kuma kasan munyi² mu rabata da sallah abun ya gagara idan har zaka iya auren uwarka duk daren duniya zaka kwanta da ita ne ka riƙa samun natsuwa daga gareta shikenan Sultana zata aure ka kuma duk duniya babu wanda ya isa ya hana auren , saboda sai mahaifiyar taka tayi bacci zaka kwanta da ita , tou yadda ka sadu da ita tana bacci bataji bata gani ba haka za'ayi aurenka da Sultana mutane bazasu ankara ba bare ayi ta surutu....

Shiru Bello yayi bayan wani lokaci yace wannan kauce hanya tayi yawa da wane idon zan tsaya a gaban Allah uwata fa.......? An zan samu rahama ranar gobe ƙiyama ? Boka yace wanda yayi kisa me ya rage mishi daga rahamar Allah a duniya da lahira ? Bello ga kisan kai ga zinace ² ga caca kawai kayi sai ka tuba idan ka kusa mutuwa tunda kana san rahamar , Bello yace to a rabata da Dikko basai na aureta ba , Boka yace ko ka aureta ko a rabata da Dikko saika auri uwarka , idan haka baiyi ba tou kisanta shine mafita kawai.... Bello yace shikenan zanyi shawara....

Har muka isa Daura ni banyi magana da Yazeed ba sai shi daya kunna wata waƙa ta "yan siyasa yakebi , wannan ta shiga ta fita , nidai hankalina da zuciyata ya tafi yayin da nake jinjina auren Yazeed sai kuma tunanin yadda zanyi ma in cire Dikko daga raina tun farko ma kenan. Haka nan naji gabana ya yanke ya faɗi ina tunano lokacin da Dikko ya sumbaceni a ƙofar gidanmu ranar dazai rabu dani , tashi tsikar jikina tayi yayin dana tuno yadda na kasance a jikinshi da maganarshi da yake cewa zamuyi aure bada daɗewa ba ,

Haukanshi na tuno yadda yake fizge² yana zabura kamar anba doki ƙwaya idan an riƙeshi , kai gaskiya ina san Dikko amma idan har na aureshi ranar da nayi mishi lafiya waye zai riƙeshi idan zai dakeni....? Murmushin Dikko na tuno a ranar da mukayi faɗa dashi hanyar tafiya bakori lokacin da muka tafi da Mardiyya maganar da yayi na tuno ,

Haba yarinya Dikko ne fa ! Kin manta nine na koya miki ? Nine nayi kuma nine na fara baki idan daɗi kikaji ko zafi duk nine dai , ruwa idan da rabon ka a ciki ko ka zubashi a kwando bai maka yoyo , ni ba abin farautarki bane zaki duk jarumtatai yana ganin ƙimar mafarauci a wancan karon suma kikayi wannan karon ma haka zata sake faruwa dake ba suma ba har jinya sai kinyi idan kika dawo ɗaukar fansa zaki gane Dikko ba sa'arki wasanki bane domin saina baki azabar da sai kinyi fitsarin wahala , bayan kin dawo daga duniyar suma tsorona zai shigeki a duk lokacin da kika kasance dani a shimfiɗa ɗaya ,

Wallahi jarumi ɗaya akeyi a ƙarni nine jarumin wannan lokaci , Dikko jarumin maza ne kuma keda kanki zaki faɗa kije ki dawo ina nan ina jiranki , murmushi nayi a bayyane nace wannan gaskiya ne mutumina Allah ya baka lafiya.....

Fita nayi daga cikin motar ina fita da Yayar Aunty Suwaiba na fara haɗuwa muka gaisa da ita take cemin yanzu nan aka tafi da Suwaiba Zaria wai sunje zasuyo wasu aune² , cikin rashin jin daɗi nace yaushe zasu dawo ne ? Tace insha Allah barasu wuce kwana biyu ba , nace tou dan Allah akwai wata waya a hannunta wacce aka bata a asbiti shin ko zan samu wayar ne da Allah ko kuma ta tafi da ita.....?

Shiru tayi irin na masu nazari tace me zakiyi da wayar ne , murmushi nayi ba tare dana bata ansa ba na buɗe jakata na ɗauko kuɗi na bata tare da cewa bani wayar ke kuma ki riƙe wannan , cike da farin ciki ta anshi kuɗi tare da cewa ina zuwa , mota na koma ita kuma ta shiga gidan Aunty , bata wani daɗe ba ta dawo da wayar ta bani , godiya nayi mata sosai tare da cewa zan sake dawowa godiya tayimin sosai har muka tafi tana godiya tare da ɗaga mana hannu har saida muka ɓace...

Har yanzu banyi magana da Yazeed ba amma na fahimci wasu É—abi'u nashi , ina wani tunanin ne wayar da Dady ya bani ta fara kuka da sauri na fiddo wayar daga jakata na É—auka tare da cewa Dady barka da wannan lokacin , na nunawa Yazeed yayi parking , yana yin parking na fice daga mota...

Barka dai kin wani manta dani ko ? Haka kin kyauta kenan ? Haba taya zan manta dakai bayan kullum kana raina kamar kuɗin haya kayi haƙuri ban manta dakai ba kullum tunanin ka nake yanzu haka ma tunaninka nake kawai sai ka kirani , dariya yayi cewa tou yanzu kina ina ? Kallon titi nayi tare da cewa ina gida , ina ne gidan naku wai ? Zaka zo ne ? Saidai ke kizo , kana ina ne ? Ina nan Ambasada kinsan wurin ne ? Nace Eh hanyar Shinkafi ko ? Yace Eh kizo to , gani nan zuwa amma zanzo sanye da niƙaf da hijabi wurin ina kake ne ? Kinsan Fesra hotel ? Eh na san wurin tou ina a wajen da Allah karki ɓatamin lokaci , baka da damuwa ina faɗin haka na katse kiran !

Kwanan wata na kalla a wayata nai murmushi cewa hawan ruwan ciki na fa sai mutum ya shirya baka da zarrar da zan miƙa maka linzamina rayuwata , wahalar banza zansha bayan ka haɗamin da "yan dabaru kayan maza , tsoki nayi tare da cewa anya ma muradin kake nema ? Ko kuwa dai......?

Kiran dana ansa a baya da baƙuwar number da akace za'a kashe ni na fara kira a kaina nake cewa zan gane yanayin iskan inda ake magana dani dan ranar dasu Al ' Ameen suka bini da gudu har muka haɗu da Bello naga motar Dady a ƙofar get in makarantarmu , kila Dady ya ganni Bello yana bina daga baya zasu haɗu sai yace meya haɗaka da wannan yarinyar da kake binta ? Kawai zaice ai ɗiyar *BINNA ce...* , ko kuma sunyi magana na shi yasa na ansa wayoyi daga mutane daban² kowa yana so yasan inda nake , tou idan wani abu bai faru ba taya akayi Bello ya kasance a wurin bayan Dady kaɗai yasan zanzo makaranta tunda shine kaɗai na faɗawa ina katsina ? Kuma wurin baiyi hanya ɗaya da majalissar su ba kwata² gidan Bello ba'a hanyar yake ba ? Murmushi nayi tare da cewa haba tsofaffi na gano makircinku amma idan ma nemana kukeyi yanzu zan gane ta hanya mafi sauƙi , a dai² lokacin da aka ɗauki wayar , ba mai maganar nake saurare ba yanayin iskan wurin nake so na fahimci ko a inda Dady yayi waya dani ne yake magana.....? Shi kuma cewa yakeyi ,

Zaki mutu mutuwa irin ta karnuwa wallahi saina kashe , dariya nayi tare da cewa baka iyawa , yace zaki mutu fa , nace ƙarya ne , sai na kasheki wallahi , wallahi kana iya kasheni ? Na tambaye shi , yace Eyyy , nace tou idan ka isa kai jarumin ne a harkar kisa ka kashe ni a Ambasada zanzo wurin Fesra hotel yanzu sanye da niƙa da hijabi bana kasuwa fa , sai kin mutu kuma kafin mu kasheshi sai kowa ya zagaya ki , gani nan ka kasheni in gani , ina faɗin haka na katse kiran na fara kiran wayar Hafsa...

Ba ɓata lokaci ta ɗauka muka gaisa da ita , nace Hafsa kina ina ne yanzu ? Cikin muryarta ta sakarkari tace ina Qerau gidan Amisty , nace kina da hijabi da niƙaf ? Me za'ayi dasu ne ? Nace Dikko ne naji yana maganarki yanzu yace baiji daɗin abinda yayi miki ba da zai ganki da zai baki haƙuri amma sai ya ganki cikin niƙaf da hijabi dan ranar nan ma abinda yasa ya dakeki wai saboda kinzo ko gyale babu shi yasa kika ɓata mishi rai dan kishinki yakeyi sosai ,

Hafsa tace muna da niƙaf mana wanda muke amfani dashi idan zamu shiga wurin da bama so asan mune , nace to ki saka niƙaf da ƙatuwar hijabi ki shiga napep karki tafi da wani ya rakaki kinsan su "yan siyasa basa san surutu shi yasa sukeyin komai nasu cikin sirri , kicewa mai napep ya kaiki Fesra hotel dake hanyar shinkafi idan kinzo wurin ki kira wayar Dikko kinji ko ? Tace to , nace yawwa kiyi sauri kinsan baya san jira , tace yanzu fa , tana faɗin haka na kashe wayata na sake kiran Dady ,

Bayan ya ɗauka nace ya kamata kaɗan sirrinta motarka a cikin hotel in dan wani ne zai ajiyeni a mota ban sani ba ko ya sanka , Dady yace ai dama ba'a mota nake ba ina zaune a ƙarƙashin wata bishiya ne ba da mota ta nazo ba , kashe kiran nayi tare da cewa lallai ka shiryamin zagon ƙasa da yawa ,

Wayar mai cewa saiya kasheni na sake kira bayan ya ɗauka nace wallahi ku dukanku baza ku iyamin fyaɗe ba , na rantse da Allah duk yawanmu sai munyi wasan danbe dake wallahi ׳ sannan mu kashe ki , idan kuma kinyi sa'a kin mutu kafin mu gama kin huta , dariya nayi tare da cewa aiko rijiya ta ƙafe da zaran anyi yasa wasu ruwan ne zasu sake ɓulɓulowa ƙananan kwartaye daku nice uwarku gani nan zuwa...

Kashe wayar nayi na koma cikin mota inda Yazeed keta jirana , ina shiga yaja muka nufo cikin babban birnin garin katsina ta Dikko É—akin kara , kunya gareku badai tsoro ba ,

A motar Yazeed na saka cajin wayar dana anso a wurin Yayar Aunty dan wayar a kashe take ba caji , bayan na saka naci gaba da sauraren waƙar da Yazeed kebi ta mai girma gwamna ,

A zahiri nake sauraren waƙar amma a baɗinance ina tunanin yadda zan ƙare da masifar da nake san haɗawa dariya nayi a bayyane a zuciyata nace ai basu iyawa dan basu da shedar da zasuyi shara'a dani harkar karuwanci dai kowa yasan anayi ko sunkai ni ƙara kawai zancewa alƙali ni karuwa ce kuma kawaliya ce , inayin karuwanci ne saishi Dady ya kirani yace inzo , sai ince ya mai girma mai shari'a da ya kirani to dama wayata ta kwana biyu kashe babu caji , shine ina buɗewa kiranshi Dady ya shigo bayan na gama waya dashi akan yana da muradi munyi ciniki nace na sallama , bayan na gama waya dashi sai na fara bin kiran miss calls in da aka ajiyemin a wayata bayan ya ɗauka shima dai muradin ne sai naji shi wannan zai bani kuɗi da yawa to kaga tunda ina kawalci kawai saina tura Hafsa taje wurin Dady nace mu raba ƙafa taje can ni inje wurin masu yawan dan danbe zasuyi tunda ni nafita kuzari da kuma daɗewa ana ɓarin wuta a gado ,

Sai Dady yace ya mai girma mai shari'a ai Hafsa ɗiyata ce , sai Alƙali yace ke Sultana me yasa kika haɗa uba da ɗiya sai ince ai ranka ya daɗe ni badashi na haɗa ta ba a tambayeta Dikko nace mata , wata zufa naji ta ketomin duk da a c dake cikin motar , yayin dana hasko har an kirawo Dikko ya fara wannan ihun nashi ana riƙeshi yana wannan zaburar yana saiya kashe kowa... Wayyo Allah ba Dikko ba kai ba ,

Ajiyar zuciya na sauke tare da sake tunanin Alƙali zaice kince Dikko to ya akayi kikace bashi ba kuma ? Shikenan sai inyi shiru inta mazurai banda mafita dan idan an tambayi Hafsa zatace ai cewa tayi Dikko yace in sameshi a Fesra hotel , na shiga 3 , ina cikin wannan jimamin sai Alƙali yace to ya akayi kika samu miss call na wasu kwanaki , sai in nuna mishi miss call in wanda aka taramin ranar da akace za'a kasheni , bayan alƙali ya gani sai kuma yaga nabi kiran babu daɗewa , da sauri na goge wancan tsohon kiran , sai Alƙali yace ya akayi duk kwanakin baki bi kiran ba sai yau ? Kuma kinga miss call , sai ince yamai girma mai shari'a ai nazo zan ɗauki wayar ta mutu saboda rashin caji , idan alƙali ya irga kwanaki sai yace har kwana kaza bakiyi caji wa wayarki ba ? Shafa kaina nayi tare da cewa ai cewa sukayi zasu kashe ni.....? Meye shedar ki kin shigo da wani zance a wani , kai aiko ubana zanci.

A , a bazanci ba tsautsayi sai yasa suce ai ranka ya daɗe ta kirani bayan na kirata , dama ina da record in kiran sai in faɗawa alƙali sai yace in kunno aji , zufa nagoge lokacin dana kunno amma ba m card a wayar an cireshi wani irin ihu nayi tare da cewa Dikko me yasa ka ciremin abuna ? Wallahi Dikko ya cireshi da sauri na zura ƙafata na taka burki tare da kaɗa kan sitiyarin motar kamar sakarai haka Yazeed ya sakar min motar dan mun shigo cikin gari kallo Yazeed yabini dashi tuni na juya kan sitiyari na tun kari goruba road Yazeed ya zuƙe gefe ɗaya dan rabi na a saman jikinshi nake shi tuni ya ɗauke kamar an ɗora kura saman kare , banma san yanayi ba , ina tuƙin nake tunani anya ma Dikko yana garin nan gaskiya baya nan dan daya nan bazai turo min Ashiru ba ,

Ai banma tsaya ba dana isa goruba yadda naga duk an watse gidan ana rusashi aiki ake mishi kuma baya zama , cikin hayaniya nace Yazeed ina Dikko yake zama banda nan ? Banza yayi dani dan baya iya magana , kai tsaye gidanmu na nufa a wurin Ashiru zan samu wannan ansar ,.....

Ilimi ake nema baiwa kuma samunta dace ne.

23/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA.....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 62

Tunda na shigo anguwar na danna horn biyyyyi , ina isowa bakin get in gidanmu tuni an buÉ—e min get na shige ko parking in kirki banyi ba na fito , ina fitowa Ashiru na gani tsaye jikin mota , kallon agogon dake É—aure a tsintsiyar hannuna nayi da mamaki ya akayi ya tashi tun yanzu ? Kamar yasan abinda nace yayi dariya yace shi kuma wannan wasan ya kika ganshi ne "Yar mata ?

Ashiru ba wannan ba ina Dikko yake ? Murmushi Ashiru yayi yace mahaukaci bari kiga saƙon daya bari a baki idan kin dawo , wayarshi ya ciro daga cikin aljihu yana cewa bani ɗaya bane nake tare dake irina da yawa mai gida ya watsa kina tunanin kin barni ina bacci tunda kika fita a gidan nan akazo aka dawo dani daga duniyar baccin da kika turani , saboda anga fitar motar Yazeed amma ba'a ga fitowa ta ba wannan dalilin yasa aka zo dubawa ko lafiya , amma abun kunya wai kin mameni na tafi doguwar suma , hmmm

Yadda sukayi tunani kuwa haka ne ina kwance a mota ina bacci kamar wani kolon namiji , irin abinda nake amfani dashi ya ɗauko a mota tare da wurgomin na riƙe yace mai gida yace a ƙara miki dan yasan naki ya ƙare daga yanzu , kinga wannan ya nunamin wani abu a baƙar leda yace dashi aka maidoni hayyaci na , ya kika ga wannan hotunan ya nunamin lokacin dana fita daga cikin motar Yazeed da lokacin dana koma cikin mota , har kuɗin dana bawa Yayar Aunty zuwana goruba , dariya Ashiru sosai tare da cewa kina ja da mahaukaci ne yarinya , tou bari kiji abinda majnun yace......{ mahaukaci }

Record ya kunno na maganar Dikko , "Yar yarinyana barka da hanya fatan kin dawo lafiya ? Ya gajiya ? Allah ya huta gajiya , am An mata nine mahaukaci dai ko ? To wai sai yanzu kika gane mahaukaci ne ni ? Aini tunda nake ban taɓa hankali ba kullum cikin hauka nake kuma wallahi ׳ zan nuna miki ni cikakken mahaukaci ne ina nan dawowa babu jimawa idan na dawo zan nuna miki babban haukana , duk fita ɗaya da kikayi ki sani ko wace da irin azabar dana tanadar miki wallahi saina zane miki jiki tass idan na dawo kinji nayi na rantse kuma wallahi saina rufeki a ɗaki zanga wanda ya isa ya kwaceki a hannun mahaukaci , kinyi ɗaya Allah ya baki sa'a kuma kada Allah ya sanyaya miki zuciyarki ubangiji ya ƙaro miki taurin kai da kangara ni kuma yabarni da fitina na dani dake wanda ya fasa shi ba ɗan baban shi bane , wato maganar dana taɓa faɗa mishi lokacin dana kashe mishi doki ,

Juyawa naji cikina yayi ƙuww maida wayarshi yayi a aljihu yace tou ni zan tafi dan mai gida yace in tafi in barshi dake tunda ke yarinya ce shi da izininshi bai yadda in fitar dake ba , yace kawai inje abuna inyi huɗɗoɗi gabana , har ya shiga mota ya fito ya sake cewa kalli wannan dan ki koyi yadda zakiy faɗa da mai gida ,

Dukan da yayi ma Al ' Ameen ne a wayar Ashiru , abiyar zaman mahaifiyar shi tayi video dan sharri ta turawa Dady , shine Dady ya turowa Dikkon shima dan ya gani Dady yace ina anfanin wannan ? Kaga irin abinda kakeyi Babana miye haka dan Allah ? Ta ɗauka dan tayi ta yaɗashi a duniya ta ɓata maka siyasarka , tou ka kiyaye wannan doke²n , amma nace mata wallahi idanma tasan ta tura ma wani vidio nan tasan yadda zatayi dasu su gogeshi idan har na naji labari ko ganshi yana yawo a duniya tasan abinda zai faru da ita ,

Dakel na haɗi wayun bakin na zufa ta ketomin , Ashiru yace ai finafinan yawa garesu wannan talla ce idan kika kalli cikakken film in fitsari zakiyi tsiii a wandonki , cike da ɓacin rai nace ya akayi banyi ba ? Ashiru yace sauri kike ? Ki fara lissafi daga yanzu duk ranar da mai gida ya riƙeki a hannun shi idan kikayi ni zaki fara tunowa kice ashe Ashiru da gaske yake , dariyar mugunta yayi tare da cewa an kunna wasan mudai Allah ya taimakemu mun fita lafiya , 1 ya faɗa tare da nunawa da ɗan yatsanshi yace ki daure ki fita ko so ishirin ne yarinya kiga yadda zai miki lullusar fitar hayyaci saiya maida ke gari muna gefe muna kallo , na barki lafiya yana faɗin ya shiga motarshi yayo wurin Yazeed ,

Saida ya kalleshi sosai yace kai kuma ni da kaina zanci uwar data haifeka idona idon ka saina baka kashin bala'e saidai in ka daina yawo a cikin garin katsina , murmushi Yazeed yayi tare da cewa nima idan har ka ganni ka gudu ka ɓoye dan sanyi da ruwa bazai hanaa inci uwarka ba , Ashiru yace mu zuba sakaran banza anyi maka rana kana nema kayiwa mutane dare gara ka tuba tun kafin kayi biyu , ko da yake ni nasan yadda nasan mutuwar da zata ɗaukeni mai gida bazai koreka ba danshi ba matsiyaci bane irinka amma nasan saiya ci ubanka cikin farashi mai tsada , sakaran banza butulu kawai mutum mai manta alkairi da akayi mishi a baya jaki ne , ka tabbata jaki , jakinma mai ɗan guntun bindi , kuma wallahi saika bar comparny tunda ba filin tsakar gidan ubanka bane ba , ko mai gida bai koreka ba wallahi da kaina zan kora maka uwa....... Yana faɗin haka ya fice da gudun tashin hankali ,

Wurin Yazeed na nufa nace da Allah ƙyalesu mahaukatan banza daga shi har Dikkon , murmushin ƙarfin hali Yazeed yayi lallai Sultana yarinya ce wato tana ganin wannan abun a rabu dashi ne , idan har yaran Dikko sukaji wannan wallahi sai sun ciccirashi idan har aka bajeshi a saman faranti akace su cinyeshi wallahi wani ma bazai samu inda zaici ba , dan Dikko yana da kirki yana musu hauka da kuɗi kuma shike cidasu sun tirku kamar karnukan turawa kuma an basu horo mai kyau na faɗa , idan har Ashiru ya faɗa musu halin da ake ciki ya tabbatar fita ya gagareshi har gida ma suna iya zuwa su ɗaukoshi kuma basujin yi haƙuri bare ku bari Dikko kaɗai ya isa ya dakatar dasu , Dady ya samo su dan su kula da tilon ɗanshi kuma Dikko baya fita sai tare dasu rabon dai Allah ya haɗashi da Sultana yake fita shi ɗaya zuwa wurin dawakai , kuma ranar daya fara zuwa shi ɗaya Allah yasa ya watsawa su Sultana ruwan dake kwance saman ƙasa ta bishi tana zaginshi zagin da tayi mishi yasa yayi mata mark tun daga wannan ranar bata sake ɓace mishi ba , kuma ai ita Sultana tasan irin yaran Dikko tunda shi Dikkon ya taɓa zuwa da ɗaya anguwarsu lokacin daya taka mata mage , dan Dikko ya tafi dashi yaci uwar Sultana amma yadda tayi magana cikin sanyi cewa da Allah cikinku waye yake tuƙar motar nan ? Ya takamin magena , sai Dikko yaji ta bashi tausayi kuma "yar ƙarama da ita amma ta cika taurin ido shi yasa yace mata itama gobe idan ta tsaya a hanya haka zaibi ta kanta da mota ya wuce , sai ya hana a daki Sultana dan gani yake duka ɗaya zai mata a shafe tarihinta a duniya...

Ajiyar zuciya Yazeed ya sauke wallahi baisan zai haɗu da Ashiru ba a dai² wannan lokacin da bai shigo ba , da yanayin gajiya ya kalleni yace bara in ɗanje in huta zan dawo anjima , sai ka dawo na faɗa tare da cewa ngode.....🙏🏻 , saida ya tafi na wuce cikin gida a tsorace.

Napep na sauketa ta fiddo wayarta ta fara kiran wayar Dikko wannan layi da ake kira a kashe yake , shine ansar da ake bawa Hafsa , tana tsaye tana ta kiran waya taji an nanɗeta ta baya , kai su waye haka ina zaku tafi dani wayyo Allahna , wani irin mari Bello yanka mata tare da cewa wurin ubanki zamu kaiki , kai ku sakeni mana a , a wai miye kukeyi haka ne ? Wayyo Allah bana so jama'a ku taimakeni masu satar yara , ku buɗemin fuskana kun shaƙeni da niƙaf numfashina zai ɗauke ,

Mota suka danna Hafsa da ƙarfin masifa , tana ihu suka daɗe dai² saitin bakinta dole tayi shiru dan sautin ihunta baya fita , basu dawo cikin garin katsina ba suka kama hanyar kaita da ita ,

Wayyo Allahna me zan gani haka ? Uncle waye zai kashe ka na shiga 3 ƙaryana zai ƙare karka mutu ka tashi don Allah , kallon rainin wayau Jiddah tayi mata cewa ke kuma wacece ? Cikin kuka Mardiyya tace Mardy beb mai dogon zamani , Jiddah tace ke kuma ya kike da majiyancin ne ? Mardiyya tace Uncle ...... Saida tayi shashshekar kuka tace Ubana ne Uwa na ne shine komai nawa , ke kuma wace ce ? Nice Jiddah , Mardiyya tace wace ce Jiddah ? Jiddah tace ni Jiddah Matar Dikko....

Cike da makirci Mardiyya ta rungume Jiddah tana cewa mun shiga 3 Aunty namu ya ƙare Allah yaba Uncle lafiya , Jiddah tace am3n , Aunty Yaya DK yasan Uncle baida lafiya kuwa ? Cikin ɓacin rai Jiddah tace ai shine ya dakeshi , Mardiyya fa tasan Dikko yayi dukan saboda Umar da kanshi ya bugawa mahaifiyar Mardiyya waya cewa Al ' Ameen baida lafiya kuma mai gida ya bashin kashin bala'e , danshi Umar komai da ruwanka ne haka "yan gidan gwamnati suke kiranshi shi yasa ko abu akeyi da an ganshi sai a bari idan kuma magana akeyi da an ganshi sai ayi shiru inba haka ba yanzu zai ɗauketa yayi gaba da ita , ita kuma Mardiyya tanayin magana da Jiddah dan su samu kusanci saboda so take ta zauna gidan Jiddah.

Sai wani shishshige ma Jiddah take , bayan sun gama jimamin Al ' Ameen cikin kuka Mardiyya tace Aunty Uncle yana sanki sosai kuma yana bakin ƙoƙari wurin ganin yayi maganin "yar iskar yarinyar nan dan kinsan ni dashi bama ɓoye ma juna komai , yana ƙoƙarin yadda zaiyi ya raba Sultana da Yaya DK yarinyar tsinanniya ce kuma karuwar ijece ita , karuwa ce mai zaman kanta amma tanayin karuwancin nata da tako ne domin ijin wuta takewa mutane sai ta akisu ta barosu , ƙara fashewa da kuka Mardiya tayi cikin kuka tace harfa girman Dad ina tasa wata matatta ta ɗauko mata ta turomin , kuma duk yadda akayi itace tura Yaya DK yayi ma Uncle dukan nan ,

Cikin rashin fahimta Jiddah tace harda matattu take huÉ—É—oÉ—inta kenan ? Ita kuma abinda Mardiyya ke nufi kafin Mamy ta mutu shi yasa tace wata matatta , a fahimtar Jiddah ita kuma wanda suka mutu dasu Sultana ke huÉ—É—oÉ—inta dasu , bata gane ba kuma bata tambayi Mardiyya tayi mata bayani ba , sukaci gaba da neman mafita yadda zasuyi maganin Sultana yayin da ita Mardiyya ke tunanin anshe goruba hannun kuturu ba wuya take ba , ita kuma Jiddah ta saki baki taci gaba da rattafawa Mardiyya bayani , ta kasa yadda zata samo sperm in mijinta , Mardiyya taci gaba dai da warware mata tunani tana É—orata a hanyar halaka....

Wani irin ihu Hafsa keyi yayin da aka fara gabatar da wasan danbe a saman ruwan cikinta , wani gidane suka kaita a can cikin garin kaita yayin da Bello ke cewa ba kince ke jar wuya bace ba , ai zaki iya damu ko ? Ba kince ke rijiya bace ba ko kin ƙafe da an yasa wasu ruwan zasu sake ɓulɓulowa ? Ai kince mana mu ƙananan kwartaye ne ba ? Yau zamu nuna miki mun manyan *KWARATA...* ne , a dai² lokacin da wani ya sauka wani ya taka saman Hafsa Bello yana cewa nine Bello aminin ubanki kiji da kyau yadda kikamin video tsirara haka zanyi miki kema , ni na koyama ubanki iskanci amma dan iskan ya lashe min matata a daren farkon dana shigo ina murna zan buɗe ta a leda amma ɗan iskan ya yage min mata ya gudu saboda kawai nayiwa yarinyar gidan da suke zama fyaɗe ba dangi uwa bana uba , amma banza ina gama dafuwata ya cinye kafin inci yasha ruwa ya kama gabanshi ,

Na saka banzan a tarko na amma ranar dana ɗana masa ɗan banzan ya tsalleke , idan baki sani ba nine nayi asiri wa Babanki kuma na haɗashi yake tarayya da ɗiyar Yayanshi wanda suke uba ɗaya , kuma nine nayi asiri na haɗashi yake iskanci da ɗiyar Yayanshi wanda da Babanshi da Baban yarinyar suke uwa ɗaya uba ɗaya , kuma nine nayi asiri ya sakaki a wasan caca nine na maidake kidahumar ƙarfi da yaji nasa kika antaya a ruɗun rayuwa ,

Wani irin ihu yayi tare da cewa naji baƙin ciki yau da ubanki bai duniya naso ya gani yadda zanyi zazzagar da yayi a saman matata yau zanyi akan "yarshi amma nasan soyayyar da yake miki duk da yana cikin ƙasa yanaji yana kallo yau ni Bello zan cinyye yadda ka kayimin nima zan rama idan zaka iya fitowa daga duniyar mutuwa kazo ka ƙwaci "yarka a hannuna ,

Dady dake gefe tsaye ya kasa gane inda maganganun Bello suka nufa , kamar ya yake nufi yayi asiri ya haɗa ahali ɗaya sunyi wannan gauragaurayar haka ? Yana tunani yaji Bello yace masa kaima Alhaji Binna yabi naka ya lashe baka da burin daya wuce ka lullusa akan wannan tsinanniyar yarinya a dai² lokacin da Bello ya afka magunguna a bakinshi ya kora da ruwa akaci gaba da video shi kuma yaci gaba da sharar fage yana ihu yau shine yake lalata "yar Binna ashe dai muradina zai cika ? Dady yace nifa duk ban gane abinda kake nufi ba , Hafsa jin maganar mahaifinta yasa tayi magana cikin wahala cewa Dady zasu kasheni , Dady jin muryar Hafsa yasa yayi wurin ya yaye niƙaf in bawai yana dan yana tunanin Hafsa bace ta kasance a wurin ba hasashe ne , yana yaye niƙaf in Hafsa ya gani tasha azaba sai zaro ido takeyi kamar ɓera yaci guba tasha kuka harta gode Allah saboda azaba , cikin hayani yace ma Bello dan ubanka ɗiyata ce sauka yana ɓanɓaro Bello amma Bello ya dafe Hafsa sosai yana cewa ba'a buga ƙaraurawa ba ,

Dady yace ƙaraurawar ubanka ince maka ɗiyata kana min maganar ƙaraurawa , Bello yace ai nasan ɗiyarka ce ka koma gefe kaima za'a buga naka zaizo , da ƙarfin bala'e Dady ya fizgo shi amma Bello ya ƙadaddabe Hafsa yana cewa ba so kike kisan su waye *KWARATA* ba ? Tou buɗe kunnenki da kyau , Bello kwarto ne , ubanki Binna shima kwarto ne , Yayan ubanki gashi nan tsaye a gefe yana so na sauka ya hau to shima kwarto ne , kowa kwarto kwarto kema kwartuwa dani dake dasu da kowa *KWARATA...* ne ,

Bello yace ku janyemin mutumin nan kumin baya dashi ni kuma inyi gaba da ita mu ci gaba da fafatawa , kama Dady sukayi suka riƙe suna cewa Alhaji ba haka akeyin wasan danbe ba kaima idan ka hau babu mai saukoka sai ka gaji da kanka ka sauka , Dady yace ba Sultana bace Hafsa ɗiyata ce dana haifa da kaina itace ya akayi kuka kawomin ɗiyata bayan munyi daku ɗiyar Binna shine kuma kuka cuceni kukaci amanata wallahi duk saina tsine muku albarka , cikin kuka Dady yace Allah ma bazai barku ba kuma nima bazan barku ba , da sauri Bello yakai dubanshi ga Sultana amma maimakon Sultana sai yaga Hafsa da tuni suma , shima cikin tashin hankali yace ina Sultana take ne.........?

Misalin ƙarfe 3:12am ƙaran wayata ya farkar dani daga ƙatoton baccin daya daɗe yana morar gangar jikina da idanuwana , dakel na lalubo wayar ba tare dana duba ba na ɗauka na ɗora a saman kunne na , nace hello , Dikko ne ya faɗa kai tsaye , cikin faɗuwar gaba na buɗe idona da sauri na tashi zaune nace ina kwana , lafiya lau ya kike ya rashin ji da taurin kai ? Kayi haƙuri don Allah , ai nayi haƙuri shi yasa na kiraki wannan kiran bana rarrashi bane ko yasa ki nemi afuwa ra'ayi nane yasa na kiraki kuma kiran nan bazai hana na zaneki ba wallahi saina zane miki jiki tass idan na dawo kuma bazanyi kaffara ba , kuma ban kiraki dan ince ki daina fita ba duk ba wannan ya shafeni ba yanzu soyayya ne , haka nake laifinki bazai shafi soyayyarmu ba , na faɗa miki ko munyi aure kikaimin taurin kai saina baki azaba kuma mu koma gado nanma in nuna miki girma na , kinsan mahaukaci baida zuciya...

Tou ya kike ? Fatan kinajin daɗin bacci , faɗamin kinyi missing ina ne ko ya ? Dan Allah kayi haƙuri , cikin muryar shagaɓa yace ke kina san mahaukaci ko ? Nidai dan girman Allah kayi haƙuri wallahi bazan sake ba , ah lallai abu ya girma An mata hada mafarkina ? Nidai ba haka nace ba cewa nayi kayi haƙuri , Ey wallahi ai haka nake so kullum nayi ta zuwa miki a baccinki , a , a ba haka ba cewa nayi kayi haƙuri , duk maganar dana faɗa sai yayi wata magana daban , tsoki nayi shi kuma yace ke karfa ki sunbaci ni yayi maganar yana yin wata irin dariya mai kama zuciya , naja miki gemuna An mata tunda baki gaishe shi ba , ki duba a whatsapp inki zaki ga Dikko yana gaishe ki , ni ina ruwana da gemunka , kai wannan gemu ya tsare miki zuciya Allah dai ya nunamin ina da rabon gani ranar da zaki ritsa uztaz a ɗaki kija gemu , yaƙi ya ida maganar yace bara dai in barki karki kasa komawa bacci , cikin wata irin murya mai saukar da kasala yace ina san ki...... Murya mai kama da raɗa ya maida maganar shi cewa mahaukaci ya barki lafiya , saida yayi muah da yanayi mai shiga zuciya ya kashe wayarshi ya barni da tunaninshi...

Buɗe data ta nayi saƙonni suka shigo , na Dikko na buɗe ina duba hotunshi , duk yayi su a cikin yanayin farin ciki hada Dadynshi ya rumgeshi cikin soyayya duk su dukansu suna cikin farin ciki , murmushi nayi tare da cewa an gaishe da mai kyau , idan yayi murmushi yanayin kyau an sharce gemu yayi kalar ɗaukar hankali , voice note yayomin to ya kikaga mutumin naki ne ?

Nima voice note nayi masa cewa wai kai shakarunka nawa ? Na tura , cikin magana mai haɗe da dariya ya maidomin cewa ke yarinya yo ai da kaɗan kika girme ni , bayan naji na tura mishi nine ma na girme ka ? Ey mana baki ganni ɗan yaro ba , ko gemuna ne yake buɗe miki ido ? Amma ai cewa kake kai babban mutum ne , haba An mata nima fa ɗan saurayi ne ko nayi miki tsufa kike tunani ? Karki ja da baya duk abinda kike tunani a wurin marar gemu a wurina zaki samu yarinya , to daga nan muka koma faɗa saida Dikko ya tabbatar nima ya ɓatamin rai akayi rabuwar baran² yace kuma naja ma kaina bazai sake kirana tunda banda wayau ,

Cike da sanyi jiki na koma na kwanta , nidai ina san halin Dikko ina sanshi matsalarshi saurin fushi , hotunanshi naita kallo kamar banda aikinyi , idan na kalli hotonshi sai in hararo siffar Yazeedu kai gaskiya jirgi yafi mota ko a tafiya ma akwai banbanci , murmushi nayi cikin yanayin ɓacin rai nace mutumina kenan ko harsai zuwa yaushe zaka dawo.....?

Murmushi yayi cikin yanayin jin daɗi yace An mata kenan na hayaƙaki ko ? Saina dawo zakiga yadda zanyi dake saina ɓata miki rai gaba ɗaya , hmm yarinya kin rainani da yawa wallahi , amma duk saina sauke miki duk wata rashin kunyarki dake ɗauwaniya da rayuwarki dole sai kinsan nine gaba dake , idan ba'a share masallaci ba za'ashare kasuwa ko wattuba dan wuya ba lada , kuma saina sake kiranki anjima ki gama fushinki saina hana ma zuciyarki zaman lafiya da tunanina.....!

Mardiyya gidan Jiddah ta kwana suna ta tattauna yadda zasu shawo kan wannan matsalar , yayin da Jiddah ta buɗe baki taita tonawa Dikko asiri duk yadda yake kwanciya da ita take bawa Mardiyya labari wai dole take ɗan haɗawa da kayan mata Dikko fitina gareshi kafin safiya tayi sai ya buƙace sau3 , wai ko wucewa tayi tana ɗan murzawa sai yace wai a likitance idan mace tana irin wannan tafiya tana buƙatar namiji ne , kai wasu matan dai wawaye ne wallahi mijinki ya kulle ƙofa dake yayi sirri ki fito duniya kina barbaɗawa , wacce kike ba labarin duk lokacin data ga mijin naki sai wannan maganar naki yazo ya tsaya mata tana kallonshi da wannan maganar da kika faɗa haka babu kyau kuma zunubi ne mai girma ,

Idan kuma kikayi sa'a da "yan iskan mata idan suka gano logon mijinki suka san yanayin sha'awarshi idan ɗan iska ne can zasu zagaye su riƙe miki wuyan miji suyi ta lalata dashi , ke kuma abarki ki zama hoto sunje sun riƙeshi sun zazzage miki shi ya dawo ya kasayi miki komai ke kuma daga nan zaki fara tashin hankali bayan ya riga ya gama horaki da irin yadda yake kwanciya dake , aikinki surutu daga nan saiki ce ai mijinki yanzu baya gamsar dake , dama sunajin haushin kin samu namijin dasu basu samu irinshi ba , naki ya iya gamsar da mace nakine yasan sirrin kwanciya da mace sunajin baƙin ciki basu samu kamar naki ba sai su koya miki bin mazan waje , daga ƙarshe kuma ya ganoki saiya sakeki kije kiyi auren kuma wanda kika aura yazo ya kasa miki irin wanda mijin da kuka rabu yake miki , kila mijinki ya saba kwanciya dake sau 2 ko 3 yadai danganta da yanayin ƙarfin sha'awarshi sai ya nemiki sau adadin lambobin dana faɗa kafin gari ya waye wasu kuma sai suyi 4 kofin haka kafin safe , kuma zai baki su lafiyayyu masu daɗewa suna miki yawo a zuciya , tou shi sabon mijin sai ya kasa baki ɗaya ƙwaƙƙwara daga nan kiji baki iyawa ki ɓallo , kina dai cin abinci mai kyau kici ki ƙoshi jini yana zagayawa ko ina a jikinki ƙarya kike kice baki buƙatar namiji saidai yanayin sha'awa kowa da irin nashi , haka zaki koma kiyi tabin maza kina ganin ina zaki samo kamar wanda kuka rabu , sai Allah yasa ki kasa samo kamar tsohon mijin naki ,

Itafa mace kamar tanda haka take horar da ita ake horon da namiji yayi mata tun tana toya waina jagwalgwalalla zata fara fiddo mai kyau , dan Allah mata mu riƙe ɓoye sirrin mazajenmu wallahi kanmu muke zubarwa da mutunci , Allah yasa mu dace.....

Jiddah taci gaba da cewa gashi kuma idan nasha magunguna ya sani duk lokacin danasha maganin mata ya kwanta dani zai faɗa , idan kukawa kikaji yana faɗin sunan kaya zakisha mamaki kodan ya tashi cikin mata ne ? Wai shi shine ɗan mai ganye idan ina so wai zai haɗamin wasu sirrika masu kyau inyi amfani dasu kuma duk haɗamata bazan iya ƙureshi ba , a yadda yakemin ma tausayi na yake fa , yana da rauni akan mace sosai , yace ita mace abun tausayi ce kuma abun daratawa ce shi yasa ko da yahaniya baya ma mace magana karta firgita , { amma saida Sultana ta ƙure Dikko harya ke dukanta....} tasha dai rashin wayanta ta ƙoshi Mardiyya kuma ta nannaɗe a haɓar zani ta shirya tayi asibiti dan yau Dikko yace ma Jiddah karta fita yawonta yayi yawa...

Wallahi gaba É—ayanku saina sa an É—aureku......

24/10/2019👇🏻

*JAMILA MUSA....*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 63

Bello yace kamar ya a ɗauremu ? Dady yace saboda ka lalacemin "ya a gaban idona har ina tsaye inabin layi a doka ƙaraurawa in hau saman ruwan ciki ɗiyar dana haifa , taya kake tunanin bazan sa a ɗaureka ba ? Bello yace gafara can itama ai wacce kake tunanin taka ruwan cikin nata itama "yar taka ce sakaran banza ka lalatamin duk wani tsari nawa ai duk cikar garin katsina da batsewar ta babu ubanda ya isa yasa a ɗaureni , bana ɗauruwu a wurinka kaidai sakaran banza mayen mace , to idan baka sani ba ka sani idan kuma ka sani ka ƙara sani Sultana ɗiyar Binna ce , wani irin juyi Dady yaji duniyar tayi mishi kanshi ya sara , cike da tashin hankali yace wane Binnan ? Bello yace Binna nawa ka sani ɗan uwanka da kuke Baba ɗaya dashi ƙaninka....

Saida Dady ya sakejin duniya tayi mishi ƙundubale yace Hajiyata ɗiyar Binna ce .....? Bello yace tabbas , wani irin haushi Dady yayi hafhaf kamar kare yace shikenan na kashe kaina shegiyar yarinyar nan tazo har majalissa ta sameni wai tana so taga bayan Binna dan wawanci da kidahumanci irin nawa ni idona ya rufe akan mace nace mata ai wani ya rigaki dan tuni an daɗe da tura Binna zuwa duniyar mutuwa , girgiza kai Dady yayi tare da cewa amma shu'umar yarinyar nan tacemin wane mai zarrar ne wanda yafi mace zafin nama....? Tabbas mutuwar ki ta zama dole abun kunya na rungumi ɗiyar ƙanina na farfaɗa mata maganganu masu girma na lashi bakinta na tura hannuna a cikin rigar nononta , na kamo hannunta nakai a girma na kai , idan har duniya taji wannan abun kunya sai tsinuwar mutane tahau kaina........

Wato a wancan lokacin taso na faɗa mata wani abu , tabbas nace mata ni Yayan Binna ne , tana tare da wani ƙuduri a ranta tuni tasan wani abu ko kuma wani abu ya faru ya akayi ta shigo rayuwata ..? Wannan shine abinda ya kamata na sani farko kenan kafin inyi mata hukuncin daya dace da rayuwarta , shiru yayi yana nazari zuwa wani lokaci yace an kira Sultana nan ya akayi Hafsa ta bayyana wurin a maimakon Sultana ? Sultana tace zata zo sanye da niƙaf ya akayi Hafsa ta sako niƙaf tazo....? Mu kai Hafsa asibiti saita dawo dole duk zamu samu ansar wannan tambayoyin namu.

Cikin ɓacin rai Dady ya kalli Bello yace tun can baya boka yayi magana akan Sultana me yace wanda yasa muka toshe kwalwarta a kwalba....? Cikin tashin hankali Bello yace bayan Binna yazo yana farin ciki a gidana an haifar masa yarinya mace yace nasarar rayuwa yazo mishi , na tayashi murna sosai yayin da yake cewa ya samu mai share mishi hawayenshi tabbas nasara ce tazo , sai yace kuma yanaji a jikinshi ko baya raye "yan uwanshi zasuyi alfahari da jaririyar da zai sakawa sunan mahaifiyarshi.

Na taya Binna murna sosai bayan ya tafi daga gidana nazo na sameka na faɗa maka duk yadda akayi , a wancan lokacin sai kace muje a faɗawa boka yayi bincike akan ita yarinyar , abinda boka yace mana bayan yayi bincike shine kawai a toshe kwalwar yarinya shine mafita , Bello yace da muka tambayi dalili boka yace idan yarinyar ta girma zatayi ilimi tunda Binna yana da ƙudirin haka akan ta , yarinya tana kishin mahaifinta idan ta tashi ta ganshi a harkar caca zatayi faraucin fitar dashi a caca ku kukace ya dawwama a caca da zinace² idan yana yinsu ya gama lalacewa a mantar dashi tunanin mahaifinshi bare yayi tunanin dukiyar da aka bar muku na gado...

Dady yace ya akayi tasan Hafsa É—iyata ce ? Ya akayi tasan cewa nine baban Hafsa ya akayi ? Ya akayi Bello tasan ina tare dakai ? Bello yace bata san muna tare ba gaskiya nidai nine nayi mata waya cewa saina kasheta , shine tacemin idan na isa zan iya kasheta in kasheta a wurin fesra hotel ,
yayin da zata sauko daga napep sanye da niƙaf , muna zuwa sai muka ganka a wurin sai muka tsaya muna gaisawa saiga napep ya sauke mai niƙaf bayan dama wacce muke nema tace mana zata zo sanye da niƙaf bamu tsaya bincike ba muna ganin mai niƙaf muka rufa mata tunda dai ta sauka a inda Sultana tace zata sauka , ka tambaya lafiya ? Sai nace maka Sultana ce , kace wace Sultana sai kawai nace maka ruwana ne , kace kana sha ba tare da sanin ko wace ce ba , ni kuma naga abokin cin mushe ba'a nuna mishi sai nace maka ni kasheta zanyi bayan mun gama morewa kai kuma kace muje bayan ka kira wacce kake jira bata ɗauki wayarka ba , sai muka haɗu gaba ɗaya muka taho nan dan bamu da isashshen lokacin da zamu tsaya muyi magana mun barshi akan sai mun gama zamuyi magana , Dady yace to bana tunanin Hafsa tasan Sultana muje asibitin munyi magana daga baya...

A wahalce yace mai gida... Hawaye ya gangaro mishi daga cikin ramin kwarin idanuwan shi yace na bari kayi haƙuri insha Allah bazan sake ba , tashi Mardiyya tayi ta matsa kusa da Al ' Ameen ta kama hannunshi ta riƙe tana kuka , cikin muryar kuka tace Uncle wallahi tunda har ya dake akan Sultana wallahi kafin in bar katsina saina korata zuwa duniyar mutuwa , dakel Al ' Ameen ya haɗiye yawun bakinshi cewa karki kuskura ki fara tunkarar yarinyar nan dan wallahi idan har mai gida ya sani naki ya ƙare farko ma kenan , gara ki koyi yadda zaki kyautatawa Sultana idan har mai gida yaga kina santa wallahi sai yaso ki har cikin ransa saboda yana ma yarinyar nan soyayyar dashi kanshi baya san kanshi , yana san Sultana fiye da yadda yake san rayuwarshi , ko wane awa ko wane minti ko wane daƙiƙa wutar santa sake ruruwa take a zuciyarshi ,

Batajin magana karuwa ce mai lasi da take karuwancinta cikin tako da ƙwarewa , duk inda bakya tunani sansanin yanki garin nan tayi suna amma a ɓoye take huɗɗoɗinta , tunda ta samu ta dafe mai gida ta watsar da ko wane namiji ta koma zama gidanshi tana kwantalarshi , mafita ɗaya shine mu nemi inda Sultana take sai ki shiga rayuwarta sosai a fili ki nuna mata soyayya , a ɓoye kuma sai muci gaba da ɗirkaka mata asiri har mu samu muga mun shafe babinta daga duniyar masu rayuwa , Mardiyya tace haka zamuyi Uncle Allah ya baka lafiya ya ansa da am3n suka ci gaba da tattaunawa.

Mai gida ina ganin yarinyar nan sai an haɗa mata da roƙon Allah ko zata samu natsuwa sai inga kamar ba ita ɗaya bace ba , Ashiru ne yake magana da Dikko a waya , Dikko yace ita ɗaya ce tsabar iskanci ne kawai da raina mutane ka barta kaga yadda zan dawwarata idan na dawo , Ashiru yace to ai duk dai firgicin da nayi mata jiya wallahi yauma ta fita , Dikko yace ai dama nasan saita fita An mata halinta sai ita amma wallahi nine maganin rashin kunyarta , yau kuma ina taje , Ashiru yace wallahi mai gida tunda duhun asuba yarinyar nan ta tafi sabon layi can wurin one way layi ne na tsofaffin karuwai maza da mata , idan kana neman duk wani feƙaƙƙen ɗan iska daya ansa sunansa a harkar iskanci kaje wurin saika sameshi indai ya cika karuwa mai "yanci , tsofaffin karuwai ne da sukayi karuwanci shekaru da yawa da suka wuce sune suke rainon wasu ƙananan masu tasowa ,

Salati Dikko yayi tare da cewa innalillahi wa'inna ailaihir raji'un , wallahi saina zane An mata idan na dawo , wallahi ko zata mutu saina daketa saina dira kanta , cikin ɓacin rai Dikko yake magana shin mema tajeyi ne a wurin ? Ashiru yace mai gida wallahi ban sani ba , Dikko yace kenan tana nuna itafa duk duniya babu wanda ya isa ya dakatar da ita akan duk abinda tasa kanta, wallahi ׳ nine na isa na dakatar da ita duk duniya baki da mai maganinki iskancin ki saini , kashe waya Dikko yayi bayan yacema Ashiru bara zan kiraka.

Da sauri na kwanta saman gado tare da jan bargo na lulluɓe gyara muryata nayi na maida ita yanayin muryar bacci na ɗauki wayata dake tsuwwa saboda kiran Dikko dake shigowa , ina ɗauka nace kai mai zuciya ya akayi ka sake kirana bayan kace baza ka sake kirana ba tunda banda wayau ,

Murmushin ƙarfin hali Dikko yayi tare da cewa key kina tunanin zan iya fushi dake ne dama ? Wai kamar ya kakejin girman soyayyata ne a zuciyarka , An mata yanzu ba lokacin maganar so bane ina kika je ? Ni ? Na faɗa tare da dafe ƙirjina nace kaji sharri ni kuwa ina zanje bayan saman gadona , ke ina kikaje ? Dikko ina kuwa zanje bayan bacci ma nakeyi kiranka ne ya tasheni , An mata ina kikaje nace , cikin kuka nace wai wannan wane irin masifa ne bayan ɗazu wurin 3 da wani abu na dare ka kirani kuma ka tabbatar ina gida , ke ji nan na rufe idanuwana yanayin fushi ya fara hawa saman kaina kafin in faɗa miki magana mai muni ina kikaje yayi maganar cikin murya mai tada hankali , saida naji wani fitsari²n tsoro ya kamani cikin rawar murya nace ƙofar gida kawai na leƙa na dawo ,

Waye yace ki leƙa ? An mata baki so dai ki zauna lafiya ko ? Dole dai sai kin ɓatamin rai ? Nidai ko An mata ? Dikkon naki ? Haba An matana faɗamin wai meke damunki ne don Allah , duk cikin lallashi yayi maganar , shiru nayi na kasa magana ina shashshekar kuka , cikin murya maisa natsuwa yace dole dai saina dakeki zaki natsu ? Ya tambayeni , cikin kuka nace kayi haƙuri don Allah , wallahi An mata bazanyi haƙuri ba saina zaneki faɗamin ina kikaje ? Sabon layi naje , tou waya aikeki ? Babu , badai zaki kiyaye fushin mahaukaci ba ko ? Idan har kika sabar wa da kanki "yan doke²n nan ko aure mukayi hankalin baya kwanciya sai na dakeki banda kyau ne idan ina yanayin fushi kuma na faɗa miki idan na ɓaci ba nine ba , me yasa kin raini da Allah ?

Ban raina ka ba , wallahi kin raina ni har kin faɗawa duniya kowa yasan kin raina Dikko , kayi haƙuri , hmmm banyi ba kuma wallahi bazanyi ba idan dai taƙamarki taurin kai da kafiya nace miki nine kangara idan har bazaki gaji ba nima bana gajiya tunda kema so kike ki zama kamar doki ko anhauki sai an dakeki ina nan dawowa babu daɗewa...... Yana faɗin haka ya tsinke kiran.

Ajiyar zuciya na sauke tare da goge "yar guntuwar zufar data tsattsafomin a goshina bayan Dikko ya kashe wayarshi , lallai wato duk safko na su a wajen suka kwana , kaje ka dakenin wallahi bazan daina fita ba , kai ƙarewar fitar ma ai barin ƙasar kayi baki ɗaya ko kai nace karka fita ne ko karkaje ? Ɗan rainin hankali kawai ,

Abinda ya kaini sabon layi neman wanda yasan Mamy nakeyi , kuma na samu wanda suka santa , kuma na tambayesu ko akwai wanda yasan wata babbar aminiyarta amma ta ɓace kuma ni bansan sunanta ba amma nasan shaƙiƙiyar Mamy ce sosai shin ko akwai wanda yasan aminanta , lissafi akamin nace to sun san wacece aka kwana biyu bata nan ? Sai sukacemin *Raga* ce , nace tun yaushe basu ganta ba ? Lokacin da suka faɗa yayi dai² da lokacin dana san tamin waya cewa inyi sauri na samu Binna za'a kashe shi.

Ina ne iyayenta suke ne ? Na tambaye su amma sai sukacemin gaskiya Raga babu wanda yasan daga inda tazo , wata tace amma naji ance bata lafiya tana asibiti , dana tambayi asibitin cewa sukayi gaskiya basu san asibitin ba , nace to waye yace musu tana jinya a asibiti ne ? Sai sukacemin gaskiya jinyar sirri takeyi , na nemi sanin asibiti sai sukacemin wani karuwanta ne kaÉ—ai yasan inda take , wato kamar wanda suke iskanci dai , sai anjima zaizo nima kuma anjimar zan koma , matar data tunkari mutuwarta saboda ceto rayuwata saina ganta kuma sai naje babu wanda ya isa ya hanani fita ,

Dikko daga kan Sultana wurin Jiddah wayarshi ta sauka me yasa wata ta kwana gidanshi bada izininshi ba ? Ko an faɗa mata gidanshi gidan gwamnati ne ? Ita har ta isa ta daki ƙirji tayi iskancin data ga dama ba tare da saninshi ba ? Shike aurenta ko itace take aurenshi ne ? Daga yau idan Mardiyya ta sake kwanar mishi a gida sai yaci ubanta sakarar banza wacce ƙwalwata ke ƙallon gusin.....

Jiddah tace Yaya ni kwalwata ke kallon gusin ? Dikko yace to akwai wacce nake magana da ita bayan ke ? Aike inama tantama anya kina da ƙwalwa a kanki ? Sakarar banza saboda wannan surutun banzar naki sai kin wahalar da rayuwarki , cikin kuka tace Yaya baki zakaimin ? Ba baki zanyi miki ba Jiddah surutunki yayi yawa gaki baki da sirri ko kaɗan , tou wani abu akace maka nayi ? Wallahi babu abinda akace kinyi sanin hali ne yafi sanin kama surutunki na sani zama ɗaya sai kin warwarewa mutum komai na rayuwarki anyi mutum babu sirri ina ma amfanin halinki da Allah ,

Wannan Mardiyya da kike gani sai tayi cinikin ki a gaban idonki ta sayar dake , Yaya wani abu tace wai ? Babu abinda tace nasan ke ba'a sakaki a kwana ba kinyi surutu kamar kamun hauka bare ita kuma mai wayau ta sakaki a lungu taita dukan cikinki kina bata labari , tunda Umar yacemin a gidan ta kwana nasan yau kin kwana É—imi { surutu } wai anyi mace babu aji haba Jiddah wasu matan kamar ka biya kuÉ—i ka siya magana a wurinsu ni gaskiya bana san mace ba aji ki kama kanki tun kafin inyo miki abiyar zama....

Kishiya zakamin ? Tabbas wallahi aure zanyi kuma dana dawo zanyi shi in Allah ya yadda , kam bala'en nan ni zaka ma kishi ? Dikko yace tabbas kuma babu gudu babu ja da baya aure fa babu fashi ko a yadda ko kar a yadda idan dai har banyi auren nan ba tou ki tabbata mutuwa nayi......... Yana faÉ—in haka ya kashe wayarshi.

Dikko yana kashe waya Jiddah ta kira Momy ta fashe da kuka , cikin tashin hankali Momy tace me akayi miki ne ? Momy wai Yaya aure zai ƙara , Momy tace ƙarya yakeyi babu auren da zaiyi , cikin kuka Jiddah tace wallahi da gaske yake duk abinda yayi rantsuwa akanshi ba wasa yake ba Momy tabbas aure zaiyi , Momy tace wace ce zai aura ? Jiddah tace Momy ban sani ba kuma yace min wai kar Mardiyya ta sake kwanar mishi a gida bakiji zagin da yayi min ba har cemin yayi ƙwalta tana kallon gusin , Momy tace gidan banza gidan wofi gareshi har kema baki sake kwana ki tattaro kayanki ki taho , Jiddah tace Momy cewa zaiyi nayi yaji kuma kinsan bazai ce in dawo ba , Momy tace ki barshi dan ubanshi zai dawo ya sami ki taho , kamar dai Jiddah bata yadda ba amma ƙarshe dai ta haƙura Momy ta turo driver ya ɗauketa su Jiddah an sauka a gidan gwamnati.

Misalin ƙarfe 12:30pm na fito harabar gidanmu zanyi aike , Ashiru na gani shida wasu irin tiƙa²n mutane harda waɗanda suka zauna dani a goruba lokacin da Dikko ya saceni a wurin bikin birthday ina , shima ɗayan na sansa Dikko yaje dashi anguwarmu ranar daya takamin mage wanda nace jikinshi har wani mai² yake saboda girmanshi kamar an shafa mishi mai , ashe Ashiru ɗan ƙarami ne ma akansu , nafa firgita da ganinsu amma saina basar na kira mai ba filawowi ruwa na aikeshi , zan juya naji suna cewa aiko mun kamashi ba'a nan zamu dakeshi ba tafiya zamuyi da ɗan iska , ji nai cikina ya juya ƙulululu irin kukan nan da yakeyi idan yaji tashin hankali , da sauri na fara tafiya saboda wallahi basu da kyan gani naji wani yana cewa kun gane karmu daki Yazeed muyi masa kashedi idan mukayi saurin dukanshi mai gida zaice mun daki abokinshi kawai dai mu fara worner shi idan baiji ba sai muci uwarshi kawai.

Da gudu na shiga cikin palo har ina faɗuwa da sauri na miƙe nayi cikin ɗakina a tsorace , Kaka ma kanta da take zaune tamin magana bana jinta , ina shiga ɗaki wayata na ɗauka na fara kiran Yazeed babu ɓata lokaci ya ɗauka babu ko gaisuwa nace masa su Ashiru suna nemanka zasu dakeka fa , murmushi Yazeed yayi tare da cewa ki kira DK ki faɗa masa cewa yaranshi su fita hanyarki dake dani idan ba haka ba zaku samu matsala keda shi , nace ai nima yace zai dakeni ne idan ya dawo , Yazeed yace ba komai faɗa masa haka kawai , ba tare da tunanin komai ba na katse kiran Yazeed na kira Dikko.

Shima babu wani ɓata lokaci ya ɗauka nace Dikko ya ansa da na'am yaja na'am in a cikin murya irin ta sakakkin "ya "ya nace kaga yaranka su fita hanyar ni da Yazeed idan ba haka ba dani dakai zamu samu matsala , murmushi Dikko yayi yace wannan ba tunaninki bane yarinya ashe har yanzu kina wasa da mahaukaci to ki sani da abinda zakiyi da kanki da wanda aka sakaki kiyi komai naki na sani kuma ni halinki da rayuwarki sai in rubuta littafi akanki ,

Cikin ɗaga murya nace to me yasa suke binshi me yayi musu ne ? Murmushi mai sauti Dikko yayi tare da cewa bana cikin yanayin faɗa yanzu amma ki bari idan ina fushi saiki taɓoni ko kuma ki bari idan na riƙeki ina baki wahala ki tambayeni anan ne zan baki ansar tambayar da kikemin zararra kawai dake , kaine zararre , ai ni dama tuni na zare , Dikko yanzu me Yazeed yayi ma yaranka ne ? Duk abar maganar zare².

An mata yarana kenan wanda nakan ɓata musu a ko wane lokaci kuma sukeyin haƙuri dani , na saka baƙin ciki a zukantasu yayin da su sukeyin farin ciki , kuma suyi haƙuri basa zuciya dani , kinga su kansu suna kishina tun kafin ni inyi kishin kaina , suna jin baƙin ciki tun kafin ni inji baƙin ciki , suna tayani kishinki tun kafin ni nayi kishin naki , sunji baƙin ciki na samun kishiya a soyayyarki tun kafin ni mai san naki nayi kishin rabamin zuciyarki da kikayi gida biyu , ni ɗaya nake ko a gidanmu kuma duk zuciyar macen dana shiga bana gogewa har abadan duniya amma ke har kina tunanin jinjina soyayya ta data wani Yazeed , ni zaki ma soyayyata kishiya ko ? Hmmm idan har na barki kin huta dai² da saƙon ɗaya da tunanina kice ba Dikko nake ba. Yana faɗin haka ya ajiye wayarshi.

Cikin tashin hankali na sake kiran Yazeed bayan ya ɗauka na faɗa masa Dikko yace bazaiyi haƙuri ba , Yazeed yace sake kiranshi kice masa yayi haƙuri yaranshi su fita hanyar Yazeed , nace tou , wayar Dikko na sake kira amma sai bai ɗauka ba , nan fa na samu aikinyi ,

Har aka kawomin saƙon dana aika a siyomin ban daina kiran Dikko ba , ganin bazai ɗauka ba yasa na kunna data ta yana online kuwa kenan yaga kirana ɗauka ne bazaiyi ba , voice note nayi masa cewa Dikko kana ganin kirana bazaka ɗauka ba , ya gani kuma na tabbata yaji amma bai bani ansa ba ,

Whatsapp video call na kirashi ya ɗauka yana kwance saman gado yana cin cingom cikin salo mai ɗaukar hankali , murmushi nayi dana ga fuskar Dikko a kusa dani nace mutumina kaine a kwance haka ? Wani irin kallo yayi min amma baiyi magana ba , cikin sakin layi nace Dikko kai kana da kyau sosai wallahi kana burgeni matuƙa , har yanzu idonshi akaina yake amma baiyi magana ba yana kallona cikin wani irin yanayi , Dikko kayi haƙuri don Allah tsoki yayi tare da cewa ai kina so dai yarana su fita harkar Yazeed ko ? Nayi shiru , tunda kina san Yazeed na bar miki shi kuma insha Allah duk wani wanda ke ƙasana bazasu sake rabaki da Yazeed ba , na haƙura dake An mata na fita harkarki kuma ki goge number na a wayarki nima zan goge naki kowa yaje yayi sabuwar rayuwa ,

Dan kinga ina sanki zakiyi tamin wasa da rayuwa to na daina sanki ko diamond ce ke na haƙura dake bana so aje akaima Yazeed , yana faɗin haka ya kashe , wani irin tashin hankali naji kamar an tsinkemin jijiyoyin lumfashina , musulta irin tashin hankalin da naji akan kalaman Dikko bana iyawa , cikin kuka na sake kiran wayar Dikko amma yaƙi ɗauka wayyo Allahna kardai mutumina da gaske yake ?

Murmushi Dikko yayi da yaga Sultana tana ta kiranshi yace haba An mata ai tuni kin faɗa tarkona na , tuni na dana saka miki maitata a zuciyarki , murmushin mugunta yayi cewa bari in barki saina gasaki dayi miki rowar muryata nima yanzu zan ɗana irin iskancin da kikemin idan kikaji azaba dana dawo ke da kanki zakiy ta haɗani da Allah muyi aure , "Yar yarinya kawai dake kin maidani abokin wasanki , da girmana kin maidani kamar ƙaramin yaro in biye miki inta sakin layi ko girmana baki gani haba An matana so hauka ne .....?

Tun wurin 12 da wani abu nake kiran Dikko bai ɗauka ba har zuwa yanzu wurin 3 na kasa daina kiranshi kuma ko tausayina Dikko bayaji yaƙi ya ɗauka wayana ni kuma na kasa haƙura ,

Saida aka kira la'asar na ajiye wayar naje nayi wanka nayi sallah na shirya na fita daga gidan na nufi sabon layi.....

25/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA...*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 64

Lokacin dana isa sabon layi ban samu ganin matar da tacemin na dawo anjima ba , dana tambayi wacce ke bani ansar inda matar taje cemin tayi wai sun tafi wurin taron siyasa , kuɗi na fiddo a jakata saida na shaƙa mata su dai² hancinta na maidasu a jakata nace zan tafi ni suna na Sultana , kuma ni ɗiyar Binna ce ai kin san Binna ba.....? Zaro ido tayi tare da cewa Binna....? Murmushi nayi da gefen bakina tare da shanye idona na dama nace Eh nice na gajeshi masu iya magana nacewa kyan ɗa ya gaji ubanshi na gaji Binna ban gaji uwata ba na ƙarasa maganar ina yatsina fuska , jinjina kai tayi tare da sake kallona ƙasa da sama tace Binna ? Nace tabbas.

Dariya matar tayi ta zira hannunta cikin breziya ta fiddo sigari ta bata wuta , saida taja ta sosai ta miƙomin , ansa nayi ina murmushi na riƙeta a hannuna , ita kuma taci gaba da cewa lallai ai Binna namu ne , bara a kawo miki kofinshi kiyi mishi nayau tana faɗin haka tayi gaba , babu jimawa ta dawo riƙe da ƙofi a hannunta ta miƙomin cewa wannan da kike gani duk daren duniya Binna goma yake sha , kuma yabar wasiyya cewa duk daren duniya saboda san da yake ma giya koya mutu a zubar da kofin giya goma a saman ƙasa , ansar kofin nayi na riƙe a hannuna na ƙura mishi ido , hawaye naji ya cikamin ido bansan lokacin da suka fara gangarowa ba , ɗaga kofin nayi na kai bakina amma kafin in samu damar shanshi an ɓareshi , da sauri na ɗago kaina dan inga waye amma babu kowa kuma babu matar data bani kofin ,

Da sauri na kalli hannuna saboda sigarin hannuna ta cinye wutar har ta taɓomin hannu , yadawa nayi na duba mutanen dake zaune suna wasan lido nace ina matar dake tsaye a gabana da Allah , wasu ne suka ɗauketa a mota , wannan shine ansar da suka bani kawai , da sauri na rufe idona na girgiza kaina gefe da gefe na kalla ba kowa dan haka na juya na tare napep saboda wurin bisa titi ne na nufi gidan cikin ɗimuwa wato har yanzu akwai sauran masu bibiyar min rayuwata ina da sauran lale.

Kai...............Wayyo Allahna saina kasheta , shine kalmar da Dikko ke faɗa yayin da yaga hotunan "Yar matanshi ta riƙe sigari , watsi ya farayi da kaya yau sai ya koma nigeria , da sauri Dady ya dafe dai² zuciyar shi ya umarci a riƙe Dikko amma duk wanda yazo sai Dikko ya duƙe ya naɗa mishi hannu so ɗaya saiya koma da baya ya kwanta , wani irin gurnani yayi tare dayi ma Dady wani irin kallo kamar zaki ya ritsa mutum a dokar daji , cike da fargaba Dady yace ku kamamin shi , wani irin ihu Dikko yayi tare da halbin wanda yazo gaba shima ya kwanta , idon Dady cike da hawaye yace ku kwantar dashi mana gaba ɗayanku kuje , kai......... Saina kashe ku ya fara wannan zabure²n nashi taron mutane da yawa Dikko ya haukace gaba ɗaya yana saina kasheta....

Dakel aka kaishi ƙasa yana wai... Wai Allahna .... Wayyo idonshi yana zubar da hawaye yake kallon Dady duk wanda ke wurin saida Dikko ya bashi tausayi har a ƙasa harbe² yake yana An mata ni zaki tonawa asiri me yasa kike min haka saina mutu tunda baki san Dikko saina mutu wallahi , shaƙe wuyanshi ya farayi tunda bazan kasheta ba ni zan mutu kawai Dady mutuwa zanyi An matana take taɓa kofin... Sai kuma yayi ihu sosai tare da watse mutane dasu ka danne shi , Dady yace karku barshi ya miƙe danne Dikko akeyi amma abun yana nema ya gagara ,

Da ƙarfi ya miƙe ya watsar dasu ƙasa , Dady yace ku rufamin asiri ku maidashi ƙasa , ƙara kama Dikko akayi dakel aka sake kaishi ƙasa a karo na biyu cikin kuka yace idan har na mutu rayuwarki ta zama walawala duk wanda kike tunanin zaiso ki da gaske ƙarya ne nine nake sanki da gaskiya , nine kaɗai zan riƙeki da amana nine kaɗai bazan cuta rayuwarki ba haba "Yar matana karki kuskura ki bari Dikko ya fita a hannunki , birkicewa yayi yana kallon sama yace idan kina ganin munayin faɗa wannan tafiyar babu dawowa har abadan abada idan na tafi babu waiwaye ki natsu mana An mata gaki "yar yarinya ƙarama kina so ki ɓata rayuwarki wai meke damunki da Allah , surutunshi yayi yawa Dady yasa aka zuba mishi maganinshi a baki lokaci guda ya ɗauke ya tafi baccin wucin gadi...

Ganin har yanzu Hafsa bata dawo ba yasa Dady ya shaƙi wuyan Bello yace ka tabbata idan har ɗiyata ta mutu wallahi saina kashe ka har lahira ya ƙarasa maganar yana tura Bello baya , murmushi Bello yayi tare da matsowa shima ya shaƙi wuyan Dady yace ni kuma idan har wannan tsinaninyar yarinyar ta rayu sai na tona maka asiri kuma saina kasheta dan uban daya ci uwarka....

Kokowa ta rikice tsakanin Bello da Dady yayin da Dady ke cewa kai har ka isa kaci kwalar rigata kai waye ? Nan fa Dady ya ƙwance ya fara aman turanci yana zage mashayin giya ɗan wasan caca Bello ba'asan komai ba irin kan Sultana ne haka nan akai ta wanka ana zuwa makaranta , empty brain.

Rabasu akayi dakel Dady yana kiran stupid , Bello yace kai kaima stupid olowa ƙwaira dakai shima dan dai ace wani shege ne , Dady ya sake shaƙo wuyan Bello saida yayi mishi lullusar fitar hayyaci sannan yace ina Sultana take dan uwarka ? Dariya Bello yayi hihihihihi kamar mahaukaci da bakinshi daya fashe jini yana binshi yace nima nemanta nakeyi , wani irin mari Dady yayi masa tare da cewa ina Sultana take ne ? Bello yace ai kana da numberta ka kirata mana , ganin Bello zai raina masa hankali yasa yayi waya polisawa suka zo suka tafi da Bello yayin da Bello kema Dady kallon idan na fito sai naga bayanka...

Ana tafiya da Bello Dady ya fara kiran wayar Sultana , ni kuma a tsorace na shigo cikin gida gabana sai faɗuwa yakeyi kamar banda lafiya haka naji yanayin jikina suku² da sallama na shiga cikin palon gidan , Kaka tana zaune a palo tayi baƙi gaishesu nayi na wuce har zan shiga ciki Kaka tacemin "yan uwanki ne "ya "yan kawunki ne , murmushin ƙarfin hali nayi cewa sannunsu na wuce ciki da sauri.

Ina shiga na fara cire kayana bayan na gama nayi ɗaurin ƙirji dan har yanzu kiran wayar Dady bai daina shigowa ba , saida nayo alwalla na ɗauki wayar Dady cewa barka dai alawar zuciyata , murmushi yayi maicin rai tare da jinjina kanshi yace Hajiyata kina ta ina haka.....? Cike da iskanci nace ka ganni ina nan hotel tun shekaran jiya wani Alhaji ya tafi dani ana wasan danbe dani...

Shiru Dady yayi ni kuma naci gaba da cewa ko zaka zo ayi dakai ne kaga wata yazo ƙarshe , ciki² yace ummm nace tou kayi sauri ka sameni ina nan hanyar shinkafi a cikin fesra hotel ɗaki na 10 , gani nan zuwa , nace kai saurara ba zafin zuwa ba kazo da kuɗi ai zanzo dasu nace mintuna biyar na baka idan ka wuce babu kai a lissafi Dady yace to ina faɗin haka na katse kiranshi na fara kiran wayar Dikko , bai ɗauka ba kaima kayi fushi da yawa haka mutumina Allah ya sawaƙe , ina faɗin haka na ajiye wayar na kabra sallar magrib.

Mota Dady ya hau ya bata wuta ya ibi hanyar shinkafi gudu yakeyi sosai yanayi yana kallon agogo cikin ƙanƙanin lokaci ya isa dan bashi da nisa da wurin yana isa ya fara kirana a dai² lokacin dana sallame sallah na ɗauki wayar yace Hajiyata na iso , ina ka iso ? Fesra hotel ! Ina ne kuma Fesra ? Inda kika ce na sameki ? Ni ? Ni nace ka sameni a Fesra Dady ? Ashe manyan mutane ma suna ƙarya kai amma kaji kunya , da ciwo ya jinjina kanshi tare da cewa tou kina ina yanzu ? Ƙasa² da murya nayi cewa zaka ganni ne ko kaima zakayi wasan danben ne.....? Na ƙarasa maganar ina dariyar mugunta , Ey tou yi sauri ka sameni ina nan ƙofar ƙwaya mintuna shidda na baka ,

Mintuna 6 daga shinkafi zuwa ƙofar ƙwaya ? Idan ka shirya kawai ka taho idan kuma ka ƙoshi in kakkaɓe zani na in rufe abuna inyi gaba mabuƙata da yawa ai , kallon agogo yayi ya hasko tafiyar dake tsakanin shinkafi zuwa ƙofar ƙwaya yace kidai ƙara zuwa mintuna goma , bana jira , Dady yace aiko baki nemi mu haɗu ba Hajiyata , murmushi nayi tare da cewa tou shikenan indai tayin banza wulaƙanci ne albarka ma amsa ce , dariya Dady yayi mai ciwo cewa gani nan zuwa , yana faɗin haka na ajiye wayar banza na ɗauki wayata da nake kiran kowa da kowa da ita.

Yazeed na kira har ta shiga ta fito bai É—auka ba , wai meke faruwa ne haba da Allah , shi wannan sarkin zafin kan baya É—aukar wayana , Yazeedu kuma me ya faru dashi kardai su Ashiru sun dafe shi ? Aiko idan har sun kamashi ni wallahi basuyi min adalci ba.

Haka nan na zauna jigum ina tunanin duniya , gaskiya nima dai wasa² "yar iska ce mai lasisi , tabbas duk wanda ya ganni yasan karuwa ce ni amma har yanzu dai karuwanci bai huda jikina ba dan kunsan akwai karuwar da ka ganta kasan karuwa ce , akwai kuma wacce ko ance maka ita karuwa ce sai kace ƙarya ne nima dai yanayi na kawai zaka kalla farkon kallo zaka kirani karuwa amma sanin fili akayi min sirrin ɓoye kuma ni marowaciya ce ga mazan bariki , nayi danfara wa mazaje da dama na feshe na kwashe kuɗi na gudu , na ɗauki tsiraicin maza nayi amfani dashi wurin ansar kuɗaɗe a hannun su , naɗanyi dai suna kaɗan kasancewar shagon da muka so buɗewa na kafa ƙungiyar kwarata a halin yanzu Amisty ta fini suna a harkar bariki ni kuma nayi suna sanadin tarayyata da Dikko dan mutane gani sukeyi ni karuwarshi ce !

Hmmm nifa na buɗewa Amisty hanyar zaman "yanci , ta daina zaman karuwanci a gidansu ta dawo zama tare dani har tayi gidan kanta amma wai ni zatafi suna a harkar bariki , kiran wayar Dady ne ya dawo dani daga duniyar tunanin dana lula , ina ɗauka yace Hajiyata nazo ƙofar ƙwayar , tsoki nayi tare da cewa wai kai Dady wace irin kwalwa gare ka ne ? Ba tare dana jira ya bani ansa ba naci gaba da cewa me kuma ya kaika ƙofar ƙwaya kai da nace maka ka sameni ƙofar ƙaura ? Jinjina kai Dady yayi cikin tsananin ɓacin rai tare da danne zuciyarshi yace Hajiyata ai tsakanin nan da ƙofar ƙaura na kusa zuwa ma ,

Tou cewa nayi ka taho ? Ai nasan cewa zakiyi mu haÉ—u wurin shi yasa na taho yanzu haka na iso , Dady kenan nifa ina filin jirgi yanzu haka , me kikaje yi a filin jirgi ? Hoto naje É—auka yanzu mun gama kawai mu haÉ—u Qerau , ina faÉ—in haka na tsinke wayata nayi kwanciyata.

Saida yaje airport sannan ya nufi Qerau ɗan wahalar , duk inda ya duba bai ga Sultana ba , haka ya haƙura ya tafi station yasa akayi Bello jakin duka yace duk a ɓare mishi haƙoran bakin Bello na gaba idan dai har bai faɗa masa inda Sultana take ba , Bello yace shi wallahi baisan inda Sultana take ba , Dady yace suyi ta dukanshi harsai yaje maƙabarta ya dawo... Haka akai ta dukan Bello harsai daya suma kuma basu daina dukanshi ba har ya farfaɗowa , Dady yace ka tuno inda take ? Cikin kuka Bello yace a , a , Dady yace kuci gaba saiya koma ya ɗauko kwalwar inda ya ajiyeta , haka akayi ta ma Bello gwalagwala yana zuwa duniyar suma da duka kuma yana farfaɗowa saboda azabar duka...

Su Ashiru sune suka É—auki matar data bawa Sultana kofin giya , sune suka tafi da ita bayan sunci ubanta sosai suka É—auki bayanai a wurinta kamar yadda da suka faÉ—awa Dikko ya umarcesu , bayan sun gama kuma ba sakinta sukayi ba umarni daga Dikko aka ajiyeta a wurin daya basu umarni , bayan sun gama ne suka tura mishi hotunan da sukayi ma Sultana wanda shine yace duk inda suka ganta da abinda takeyi su É—auko mishi ita su tura mishi ,

Su Jiddah an samu abinda ake so ana wurin Momy kuma sai ƙara tunzura Momy takeyi yayin da ita kuma Momyn take ta daɗa hawa kamar kashin safe ,

Dady kuwa bayan ƙura ta lafa ya fara doke²n waya cewa a ƙara saka shi da addu'a lamarin Dikko fa gaba yakeyi , yanzu banda furunci zai kashe , shi da kanshi yake cewa zai kashe kanshi kuma yana shaƙe wuyanshi , itama Momy haka ya faɗa mata itama dai tasha kuka kamar zata mutu , kuma haka itama tayi ta doke²n waya tana faɗawa "ya "yanta mata Yayun Dikko su biyu ne wanda suke ma'auri tace su saka ɗan uwansu a addu'a.

Bayan Dady ya gama yake tambayar Dikko meya ɓata mishi rai ? Cikin kuka Dikko ya rungume Dady yace Dady nidai ka yafemin badan halina ba kayi haƙuri kabarni aure zanyi idan kana san farin ciki na da kwanciyar hankali na , Dady yace haba Babana kana ɗan yaronka zaka fara taretaren mata ? Nidai Dady a haka dan Allah , Dady yace Babana kayi haƙuri kar kayi aure yanzu lalurar mata biyu kanka baya ɗauka gaka baka da lafiya ka bari ka samu sauƙi mana ,

Ɗagowa yayi ya kalli Dady cewa amma ka manta fa lokacin Sadiyya kafin ta rasu aka fara maganar auren Jiddah nidai Dady gaskiya aure zanyi kuma saura wata ɗaya kawai na faɗa maka dan in fita haƙƙinka , Dady yace ba umarni na kake bi ba ? Kayi min addu'a dan Allah Dady kuma bana so ka faɗawa Momy tace saidai in mutu bazanyi kishiya wa Jiddah ba ,

Shiru Dady yayi yana kallon ɗanshi daya ɗauki soyayyar duniya ya tattara akanshi , kyakkyawan murmushi Dikko yayi ma Dady tare da ciro cingom a aljihun wandon shi ya cireshi a takardarshi ya rabashi gida biyu yasa rabi a bakinshi rabi a bakin Dady yana ma mahaifinshi kallo mai tattare da tsantsar ƙauna yace ai nasan ka yadda Dady shi yasa nake alfahari dake ya ƙarasa maganar yana ƙara rumgume shi , murmushi Dady yayi cikin yanayin damuwa ya fara tauna cingom in da Dikko yasa mishi a bakinshi yace ina bayanka Babana , tafawa Dikko yayi da duka hannayen shi biyu yace na gode Dady.

Shi kuma Dady shiru yayi amma bai tambayi Dikko dalilinshi na abinda yasa yake so ya ƙara aure ba , yadai ansa kuma har a zuciyarshi ya yadda amma dake bayahude ne Dadyn na bugawa a jarida babu abinda ya dameshi da wani auren Dikko kawai dai yana ganin wani ra'ayi ne nashi na daban tunda bai faɗa ba shima kuma bazai tambayeshi dalili ba , kuma bazai hana Dikkon yayi aure ba , dan sanin da yayi ma Dikko a baya babu abinda yake ɓoye mishi kamar aboki da aboki haka suke faɗawa juna damuwar junansu sakamakon Dikko yanzu daya fara zurfin ciki , ajiyar zuciya Dady ya sauke yabi Dikko da kallo shi baya gajiya da kallon Dikko saboda soyayyar da yake mishi ,

Bayan sati 4,

Abubuwa da dama sun faru , kuma duk cikin kwanakin nan babu ranar da bana fita kullum rana saina fita kuma kullum sai anyi hotuna an turawa Dikko , kuma ni ina kiranshi kullum baya É—aukar waya , nadaiji babu daÉ—i kuma inayi tunani sosai nakan tuno masu abubu sai inyi murmushi.

Inna har yanzu basu dawo ba , tana can ita da mijinta sunma bar Dubai sun ƙara gaba abunsu , kullum sai sunyi waya da kaka ni kuma sai lokaci² nake kiiranta mu gaisa dan idan ban kirata ba bata kira tana daiyin kara haka ta fulani saidai ta kira mahaifiyarta kuma idan ta kira bata cewa ina Sultana ,

Al ' Ameen ya samu sauƙi sosai an sallameshi daga asibiti ya dawo gidan gwamnati da ƙudurika da dama a zuciyarshi , kuma har yanzu Mardiyya tana nan bata tafi ba ,

Jiddah ma tana wurin Momy har yanzu bata koma gidanta ba , kuma tuni Umar ya biga waya ya faÉ—awa Dikko Jiddah tayo yaji tana nan gidan gwamnati ,

Hafsa ma ta samu sauƙi babu laifi an sallamota amma dake kanta irin na Sultana ne ta gagara gane yadda abun ya faru kwata² , Bello kuwa har yanzu yana can ana gana mishi azaba yanki² , Dady kuwa ido rufe neman Sultana yakeyi kuma har gidansu taje wurin mahaifiyar Dady wato kakarsu Hafsa ,

Yau tunda gari ya waye da faɗuwar gaba na tashi , idan abu na ɗauka saidai ya kubcemin ya faɗi ƙasa , ko magana akayi sai in firgita , da sauri na fito wanka zanje wurin Yazeed ne dan ya daina zuwa gidanmu saidai muyi waya kuma duk yawan kwanakin nan bamu haɗu ba dan shima yaje tafiya jiya ya dawo shine yau yayi min waya cewa na sameshi company ,

Saida nayi sallah isha'e na fara shiri , Yazeed sai kirana yakeyi kila na ɓata mishi lokaci , ɗauka nayi yacemin kin taho ne ? Nace a , a yace ni nabar company yanzu ina tafiya zuwa G R A mu haɗu dake a wurin , idan kin hau napep wurin wanki motoci na cikin G R A za'a ajiyeki , nace sai nazo ina faɗin haka na ajiye waya naci gaba da shiri ,

Ina gamawa na fice babu wanda ma yaga fita ta a gidan ina fitowa na samu napep na faÉ—a mishi inda zanje mukayi ciniki na faÉ—a yaja muka tafi ,

Da sauri ya sauko daga saman gado jin wayarshi tana ringing kuma ya ajiyeta nesa dashi , kafin ya isa inda wayar yake harta tsinke yana isa wurin a dai² lokacin da wani kiran ya sake shigowa , ɗauka yayi tare da kara wayar a kunnenshi mai gida tana nan cikin G R A , baiyi magana ba ya tsinke wayar , makulin mota ya ɗauka ya fita daga ɗakin cikin tsananin ɓacin rai....

Hajiya nifa na kasa gane inda zan ajiyeki wurin wanki motocin biyu ne ke baki san sunan companyn ba ne ? Kiran Yazeed nayi cewa nifa ban gane ba gashi ina tare da mai napep muna ta yawo , cewa yayi in ba mai napep in waya na bashi ya faÉ—a mishi inda zai kawoni ,

Baya muka koma muka sha wata kwana mai napep sai masifa yakemin wai tun farko ban iya kwatance ba , da tuni nace masa majalissar Yazeed ai da baisha wahala ba , banza nayi dashi dan bana cikin yanayin fitina yau gabana faÉ—uwa yakeyi har yanzu ,

Mai gida yanzu napep yayi parking da ita a majalisa , kashe waya yayi har yanzu baiyi magana ba , ya tafi wurin kai tsaye zuciyarshi tana ƙara ruruwa da zafin masifa ,

A gaban wani irin makeken wuri yayi parking an ƙayata wurin da wasu irin fitilu masu ɗan bara'un haske , anyi parking motoci masu zafin bala'e daga waje har cikin wurin da aka zagaye shi da wata irin waya mai kyau amma kana ganin wanda ke waje shima na waje yana ganin na ciki , wurin ya haɗu duk matasa ne zaune a saman fararen kujerun rober wasu da ƙananan ƙofinan nan irin wanda ake shan shayin nan na maza duk shekarunsu bazai wuce kamar su Yazeedu ba , duk wanda ubanshi ya tara wasu manyan kuɗi na tashin hankali gashi ya hallara a wurin.

Mai napep na sallama na tun kari wurin kai tsaye , wurin bashi da banbanci da rana kowa yana ganin kowa haka zaka iya gane duk wanda kuka sake haɗuwa a wani wurin daban , can gefe ɗaya kuma ga "yan mata zafafa suma an parkersu sai sheƙi sukeyi dan ubansu gayunsu irin ɗaya babu wacce tafi wata haɗu suma dai cikakkin "yan iska ne kowa tasha karuwanci ta ƙoshi duk "yan yara ² ne sunsha atach sunci bilicing har sunce wayyo Allah sai jin kansu sukeyi ,

Amma ina shigowa wurin wallahi duk macen dake wurin saida ta shiga taitayinta , gaba ɗaya wurin ya anshi ƙamshina ya fara yawo zuwa cikin ƙoƙofin hanci duk wanda ke wurin , ba mazan ba suma kansu matan na zama abun kallo a wurinsu , wurin Yazeed na nufa amma kafin in ida isa tuni ya shigo a haukace wurin da mota , motocinsu Ashiru a bayan tashi ,

Gaba ɗaya wurin ya karaɗe da hayani haba DK kowa DK yake faɗa yana magana da turanci , ɗan duniya uban Yazeed zaici amma sai yayi murmushi a dai² lokacin dasu Ashiru suka fito daga cikin motocinsu fuskar kowa babu imani ,

Da sauri na juya zan fita amma Dikko yace Ashiru riƙemin An mata karka barta ta fita wurin nan , da gudu na wuce Ashiru cikin hayani Dikko yace na rantse da girman Allah idan har ka barta ta fita zakaji ni da ɗaci , tsoro ya kamani a dai² lokacin da Dikko ya taɓa Yazeed amma ba dukanshi yayi ba yanayin dana ganshi na firgita matuƙa , ga Ashiru ya ɗaure fuska kamar bai sanni ba dole na kama kaina na tsaya nabi Dikko da kallo.

Yazeed har so nawa nace bana so kana tara mun mata a wurin nan ne wai ? Shima kanshi Yazeed zufa ke zobo mishi kanshi ƙasa ya kasa magana , murmushi Dikko yayi tare da cewa ba abinda zan maka idan har nayi faɗa dakai akan mace ni na zama sokon namiji , salon soyayyata a zuciyarta baya buƙatar dukan abokin takara wurin lashe zuciyarta , gani gaka ga An mata macece ita kuma zuciyarta tana da rauni na baka dama dani dakai kowa yaje yayi fira da ita ta bani lokaci naje kaima ta fitar maka da lokaci kaje na baka nan da wata ɗaya idan har ka samu ƙarɓuwa a zuciyarta na baka ita duniya da lahira amma karka sake fiddota waje , yana faɗin haka ya ciro hula daga saman kanshi irin tashi da kwakwar nan ya goge ma Yazeed zufar dake saman fuskarshi bayan ya goge mishi ya kamo hannunshi ya ɗora mishi hular a hannunshi , Yazeed yabi Dikko da kallo , duk saida yabi abokansu ya gaisa dasu sannan yaja hannuna ya sakani a mota yana cewa muje in baki tsaraba..

Ya faɗi tsaraba yana min kallo mai nuni da kasheki kaɗaine bazanyi ba , zagayawa yayi ya shigo cikin motar ni kuma na fashe da kuka , murmushi yayi tare da cewa baki farin ciki na dawo lafiya ? A dai² lokacin daya fara tafiya da mota , ni kuma naci gaba da kuka yace wallahi ki rufemin baki yayi maganar yana kallon madubi ko su Ashiru shi suka biyo , tsayawa yayi ya sauke gilashi yace Ashiru kuje kawai zamuyi waya , banji abinda Ashirun yace masa ba naji yace a , a barshi kawai amma dai goruba zanje yanzu ,

Yana faɗin haka ya ɗage gilashin yana cewa An mata kinsan bugun rabani da yaro ? Kuka nakeyi har yanzu banyi magana ba , Dikko yace wallahi yau mai ƙwaceki a hannun majnun { mahaukaci } sai Allah kawai miƙomin wayata inga waye yake kirana , ɗauka nayi na miƙa mishi , Jiddah ya faɗa tare da cewa lafiya ita kuma wannan ? Yayi maganar yana ɗaukar wayar yace inajinki , banji abinda tace ba yace Ey naje zance yana faɗin haka ya ajiye wayar yana cewa wallahi An mata yau na raina miki wayau , aini ko mace ce banga ranar da zanbi namiji ba ,

Namijin mi Allah na tuba ina mace ? Namiji ma ya biyoni yana so ai sai yaga yanga da kisisina , macen da aka santa da kwarkwasa da ƙwalisa aji da ɗauka kai ke kuma gaki nan sake dan wawanci kin taho kin biyo namiji sakarar banza dake da baki san namijin so ba , wallahi ni da macece ni dana ba maza azaba ko zance namiji yaje wurina dan ubanshi saina daɗe ban fito ba dan yasan yes wannan tasha banban da sauran mata a cikin mata dubu sai yasan ni ɗin ta daban ne , kuma in fito ina isa ina riƙe aji , namiji yayi magana goma ansa ɗaya zan bashi , nidai a tsarina ina mace ko driver bana yadda Yazeed yayi min bare dan ubanshi harya ɗaukar min jakata , ashe hakanan nake tun ƙaho "Yar mata tana da class nan ma ashe zero kin ban kunya kuma kinci baya , saboda Yazeedun banza da wofi kika hau napep ƙarshe ya wulaƙantaki yayi miki masauki inda suke ajiye karuwai nan yace ki sameshi ke kuma wawiyar kika kama hanya kika taho wallahi ji nake kamar in wurgaki waje in take ki da mota ki mutu in huta da takaici , mtsww haba inama amfanin mace ba aji ?

Gunguni nayi mishi yace me kika ce ne ? Shiru nayi ban sake magana ɗaure fuska yayi cewa bari haushinki nakeji da yawa wallahi , tsoki nayi cewa to ai sai ka kasheni nayi maganar ina miƙa mishi jikina wani irin mari yayi min wanda yasa na ɗauke lunfashina lokaci guda...

26/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 65

Jin nayi shiru yasa yace ki sake cewa wani abu mana marar kunya da kika raina mutane , ke "yar mitsitsiya dake nan har kin iya masifa da ƙure rai wanda idan nayi zuciya ina iya haɗiye ki ba tare da nasan naci komai a bakina ba wawiya "Yar matan Yazeed dake,

Tunda na taho daga inda naje wallahi bana tunanin kowa sai ke , na taho cikin farin ciki ina kyarma inzo in ganki amma kika lalata min lissafi , maimakon ki tareni da farin ciki sai kika tareni da hawaye.

Cikin kuka nace ba kawai dai kanajin zalinci kazo ka kamani kana ta dukana babu abinda nayi maka tsabar ƙwarewa da zalinci ai dama ba so na kake ba kullum baka da burin daya wuce kaga kana zalinci na.

Haba An mata ke harni zaki faɗa ma bana sanki ? Idan har bana sanki ke har kin isa ki kalli tsabar idona ki zageni ? Na baki tayin soyayya na maimakon kalami mai daɗi sai mummunan sakamako , kicemin mahaukaci kuma ƙarshen ki wulaƙanta ni ki faɗa a gaban yara dake ganin girma na , duk a bana sanki ne kika ɗaga hannu ki zabgagamin mari na gyaleki ? Na rantse da girman Allah da bake ce kika mareni ba idan basai nabi ta kan ko waye da mota na wuce ba Allah ya tsinemin albarka , tou wai taya ma mutum zai kalleni bare kuma har yayi tunanin faɗar mummuna akaina ? Ko bakya so na ko albarkacin darajar wannan bazanci ba ? Yayi maganar yana taɓo gemunshi yaci gaba da cewa ba'a zagin mutumin daya ajiye shi amma ke sam baki da lissafi.

Shashshekar kuka nayi ina cewa kana so na kake dukana ? Har so biyu ka dokeni , kaji min ciwo a gefen fuskata ka farfasa min jikina wannan duk soyayya ne ? Ai na faɗa miki kema so kike ki zama kamar doki ko an hauki sai an dokeki har so nawa na faɗa cewa bana san kina fita ai ke sai kin fita ki nunamin kunne ƙashi gareki ai dai yau jikinki zai baki labari...

Wayyo Allah dama nasan wallahi ba so na kake ba yauma dukan nawa zakiyi ? Duk duniya zuciyata da kwakwalwata ko Dikko basu sani ba sai An mata , haka wayata ma bata san wani Dikko ba itama kanta An mata ta sani amma Dikko ke amfani da ita , ki É—auki wayata password ina ki rubuta Dikko wallahi zata ce miki a , a amma kina rubuta An mata saita buÉ—e miki ,

Banda hoton komai a wayata sai doki amma zuwanki yasa na zama zararre ki duba ki gani babu hotunan kowa a wayata na mace sai naki , duk inda kika shiga a wayata An mata zaki gani amma wallahi yau mai ƙwaceki a hannuna sai Allah addu'a ɗaya zaki dage kiyi shine Allah yasa har in gama dukanki ina cikin hayyaci na...

A dai² lokacin daya shigo kwanar da zata sadashi da gidanshi tunda ya shigo santar ya kwace da gudu na tashin hankali kamar zai tashi sama motar har wani lilo take ya danne horn , gabana sai faɗuwa yakeyi cikina sai juyawa yakeyi hawaye kuma basu daina zubowa ba , koda muka iso har an buɗe get in hancin motarshi ya saka ya raba get in biyu ya sauke gilashin motar cewa kai Amadu zo nan...

Da gudu yazo Dikko yace kai buɗe nan baya ka ɗauki wata foodflarks na nan kaje ka samun murfinta , matsawa yayi ya buɗe ya ɗauka yace mai gida ai ba'a siyar da ware² a idan za'a siyar da murfin tou dole da uwar ake siyarwa ba'a rabasu , ta cikin madubi Dikko ya kalleshi yace ni ba abinda ya dameni murfi kawai nake so ka samomin irinshi.

A tsorace na kalli Dikko murmushi yayi min tare da ɗaga min gira yana min kallon rainin wayau ya taka motar muka shiga cikin gidan da gudu , gidan an ƙara mishi wani irin girma na tashin hankali an maidashi gidan "yan gayu anyi mishi bene hadaɗɗe gidan ya ginu sosai gwanin burgewa amma ba'a gama aikin ba , ko me yasa yake sha'awar sissiye maƙota yayi gini......?

Malam Amadu yace mai gida wallahi ba'a siyar da murfi , da sauri Dikko ya fita daga cikin motar bayan yayi parking ya koma wurin get , Amadu na ganin Dikko ya fito a hayaƙe ya wuce da sauri yabar gidan yana kallon rigima irinta Dikko ya za'ayi wai ya samo murfin wannan abun ne ? Ko a kasuwa ba'asiyar da ware² to kodai mai gida yana so yaɗan sha iska ne da macen daya zo da ita shi yasa ya korashi ? Saida ya kalli kular ya kallo gidan da Dikko ya rufe get in da kanshi !

Cikin tsananin ɓacin rai ya dawo da sauri na fito daga cikin motar faɗuwar gabana ya ƙara tsananta yayin da Dikko ya ɗage but ya ɗauko wata irin zureriyar dorina irin wacce ake bugun dokuna da ita yace wuce muje , cikin fargaba nayi gaba Dikko ya biyo bayana ina tafiya ina waiwayenshi , cikin hayani yace ki kalli gabanki ki daina kallo na ya ƙarasa maganar yana zazzaro min duk iya girman idanuwan shi.

Wata irin kyarma na farayi ta tsoro na shiga cikin palon na samu wuri na rakuɓe kamar asirin mayya ya tonu , shima wuri ya samu ya zauna a gajiye tare da cewa zo nan , ƙin tafiya nayi kamar banji shi ba , bakiji ina miki magana ne ? Basarwa nayi na nuna mishi ƙangara da yarinta , cikin hayani yace idan na sake cewa kizo baki zo ba saina tuɓe miki kayan jikinki zan zaneki ,

Kamar ina iyayin wani abu nace ai sai kazo ka tuɓemin dama tuɓeni kake so kayi shi yasa kazo dani ko ni zaka nuna ma hauka ? Kai kaɗai ne mahaukaci kowa mahaukaci ne ? Naci gaba da zagin Dikko yace dama nan nake so kizo , ajiye dorinar yayi ya cire belt yazo yaci gaba da zabgamin shi kamar yana dukan "yar shi yana dukana yana cewa zaki sake zagina ne ? Cikin kuka naci gaba da zaginshi ina Allah ya isa mugu munafiki azzalimi ,

Yanayin fushi ya fara zuwa ki daina zagina....? Ya ƙarasa maganar yana rufe idonshi daya rufe ido komai zai iya faruwa , cikin kuka na matsa daga wurin da sauri nace yi haƙuri don Allah kayi haƙuri 🙏🏻 kafin in rufe bakina ya fara zabura cewa saina kashe ki.......

Cikin ruɗewa na fara gudu zan fita waje amma kafin in fita har Dikko ya ɗauko wata wayar wuta da aka sauke ƙasa ya wurgota ta naɗoni ya fizgo da ƙarfi na faɗi ƙasa ya jawoni na dawo cikin palon , saina kashe ki tunda kin rainani , dorunar ya ɗauka yaci gaba da dukana zaki sake zagina ko bana nan ? Yaya dan Allah kayi haƙuri zaki sake fita idan nace bana san abu zaki sakeyi ko bana nan ? Wallahi na bari ƙarya kikeyi sai kin sake kawai kasheki zanyi inje in wurgaki a ruwa ,

Malam Amadu kuma ganin Dikko ya rufe gida ya lura kamar baya hayyacinshi sai yanzu ma ya gane Sultana ce bayan yayi dogon nazari , da sauri ya fiddo wayarshi ya fara kiran Ashiru , da farko Ashiru kamar bazai ɗauka ba dan yasan dama Amadu zai ce masa mai gida yana dukan Sultana ne shi kuma yana so Sultana taji yadda Dikko yake yarinyar bata da mutunci kwata² ga raini ga rashin kunya yauko zataci ubanta tunda ta raina mai gida , har wayar ta tsinke bai ɗauka ba Amadu ya sake kira saida ta kusa tsinkewa Ashiru ya ɗauka yace ya akayi ne ?

Amadu yace mai gida ya rufe gida kuma ya aikeni wai na nemo mishi murfin kula kuma kamar yana yanayin fushi yazo da Sultana , Ashiru yasan komai dan haka yace to ka sani ko soyayya sukeyi ne ? Amadu yace duk dai yanayin fushi da farin ciki irinsu ɗaya a wurinshi bana tunanin soyayya da Allah kuzo , Ashiru yace ai kaima namiji ne ka shiga ka bashi haƙuri dan yacemin yau sai saɓa mata kamannu ai ta raina mutane barta taci ƙaniyarta yana faɗin haka ya tsinke kiran...

Bayan Ashiru ya ajiye wayar yace kai gaskiya fa za'a iya samun matsala kunsan mai gida matsalarshi da yake duka yana buga mutum da wani abu , itafa ba namiji bace ba duk da bana tunanin zai bata wahala sosai kai ku tashi mu tafi kada rayuwar yarinyar nan ta samu matsala dai , gaba É—ayansu suka fito suka taho goruba cikin motocinsu ,

Zuwa wannan lokacin ni kuma Dikko tunda ya ɗaga ƙafa zai takamin wuya ya kare in mutu kamar yadda yace na riƙe kafarshi na kalli idonshi cikin kuka nace karka kasheni ina sanka don Allah , murmushi yayi tare da takani da ƙafarshi a hankali yace ƙarya kike , da gaske nake ina sanka wallahi , duƙawa yayi ya ɗagoni daga ƙasa ya rungumeni yace da gaske kina so na An mata ? Cikin kuka na ƙara rungume Dikko kaina kamar zai ɓare saboda ya buga min a bango yayi wasan kura dani ya bani wahala sosai duk jikina ciwo yakeyi kamar jirgin ƙasa yabi takaina ya wuce , kwantawa nayi jikinshi sosai ina kukan wahala.

A dai² wannan lokacin da aka fara dukan gida ni kuma daga nan ban sake sanin abinda ake ciki ba , cire Sultana ya farayi daga jikinshi amma ya kasa , An mata tsaya inje inga waye , ina Sultana ta tafi batajin Dikko dakel ya ciro wayarshi daga cikin aljihu saboda cakumar da Sultana tayi mishi Ashiru ya gani yana kiranshi , bai ɗauki wayar ba yace An mata sakarni in buɗo gida , tuni Sultana ta daina motsi dakel Dikko ya ɓanɓareta daga jikinshi ya kwantar da ita ƙasa har yanzu hawaye bai daina fita daga idonta ba amma gaba ɗaya ta tsaya ,

Fita yayi daga cikin palon yazo ya buɗe gidan , Ashiru ya gani tsaye yace ya akayi ne ? Ashiru yace naji shiru ne nace bara inzo inga lafiya ? Lafiya lau Dikko ya bashi ansa , Ashiru yace mai gida to ina Sultana take ne ? Tayi bacci , Ashiru yace bacci ? Umm ya bashi ansa da kanshi , ɗan gyarawa Ashiru yayi yace tou amma ai kayi haƙuri ko ? Na daketa amma kaɗan yayi maganar yana yatsina fuskarshi ,

Ashiru yace mai gida kuma duk da ka daketa sai tayi bacci ? Murmushi Dikko yayi tare da cewa ko ina cikin yanayin fushi nasan abinda nakeyi naso na bata gwalagwala amma sai tayi sauri tace tana so na , wannan kalmar ya ceceta daga azabata kuje kawai zanzo idan na maida ita gida , Ashiru yace bara dai mu jiraka daga ciki , ba tare da Dikko yayi magana ba ya dawo ciki ya bar musu gidan buÉ—e ,

Ɗaukar Sultana yayi ya fito rungume da ita a jikinshi ya kaita mota , idan mutum ya suma a wurin faɗa ko duka ba'a fesa mishi ruwa , idan mutum ya suma a ruwa ba'a zuba mishi ruwa saidai a buɗe bakinshi a busa mishi lumfashi idan kuma yasha ruwa sosai sai ake danna ƙirjinshi a hankali , idan kuma mutum ya suma a faɗa ko ana dukanshi firfita ake mishi , idan mutum ya suma haka nan babu gaira babu dalili shine ake yayyafa mishi ruwa.

A mota Dikko ya riƙe ruwa a bakinshi ya fesawa Sultana tunda ita dai ba lokacin daya doketa ta suma ba tana kwance a jikinshi ta ɗauke , ajiyar zuciya ta sauke ta sauke a wahalce , rufe motar yayi ya zagaya ya shigo ya rufe , ba tare da yayi magana ba ya tada motar muka fita a gidan.

A waje yaga Amadu tsaye da kular daya bashi ya samo mishi murfinta , yana ganin fitowar Dikko yayo wurin cewa mai gida ba'a samo ba , ba tare da Dikko ya kalleshi ba yace maidata inda ka É—aukota , buÉ—e bayan motar yayi ya ajiye ya rufe mukayi gaba su Ashiru suka rufo mana baya ,

Har muka isa gida babu wanda yayi ma wani magana , fita nayi daga cikin motar dakel banyi magana ba , har zan wuce yace An mata zo , dawowa nayi banyi magana ba na tsaya , baki gode ba ? Nayi shiru , shigo , komawa nayi cikin motar a wahalce na zauna , rashin godiya ba ɗabi'a mai kyau bane dana kawo ki gida ai sai kicemin kin gode waike baki iya irin ɗan makircin nan na mata ba ? Gaskiya aikin yawa zaimin in koya miki hankali kuma in koya miki zaman takewa na rayuwa ya zama dole ki koyi kissar zama dani danni bazanyi haƙuri dake ba ke ya zamar miki dole kiyi haƙuri tunda nine samanki fita ki ban wuri ,

Ƙoƙarin fita na farayi yace kuma tafiyar zakiyi da gaske ? Komawa nayi na zauna , kwantar da murya yayi sosai yace kin yafemin ? Da kaina na bashi ansa Eh , zaki aureni aiko ? Shiru nayi ina nazari , yaci gaba da cewa insha Allah ƙarshe watan nan zamuyi aure kuma idan munyi aure bazan miki ko kallon banza saidai ki anshi hukuncin ki a gado , wannan dukan insha Allah shine na ƙarshe bazan sake ba abinda yasa ma na dakeki nayi rantsuwa so adadin da bazan iya gane ko so nawa na rantse ba, ina sanki har abadan duniya bazan taɓa goge ki a zuciyata ba , kuma ai kema kina so na ko ? Yanzu ma da kaina na bashi ansa Eh , ngode zanzo da safe insha Allah kije , fita nayi ina masa godiya kamar yadda yace na wuce ,

Cike da tausayi Dikko yabi Sultana da kallo a bayyane yace duk wannan ɗa'ar wallahi ta banza ce bazata bar abinda take ba , motarshi yaja ya fita daga cikin gidan yana mai ƙarajin soyayyar An mata a zuciyarshi.

Tsaye nayi a gaban madubi bayan na fito daga wanka ina kallon yadda Dikko ya farfasamin jiki sahun bulala babu inda bai fito ba , a fuskata kuma har yanzu akwai sahun marin da yayi min , murmushin ƙarfin hali nayi tare da cewa saidai ka kasheni wallahi bazan daina fita ba idan har baza ka gaji ba nima bazan gaji ba.

Washe gari da wani irin masifar zazzaɓi na tashi ko sallah asuba kasawa nayi ina kwance a gado na rasa abinda yakemin daɗi har 11:15am , ga gidan namu yau cike yake baƙi "ya "ya da jikoki sai hayani sukeyi ɗan uwan Inna zai dawo daga tafiya shi yasa suka taho tararshi , dan abinda na fahimta shine gaba ɗayan ragamar su bana tunanin akwai wani mai kuɗi idan bashi ba ,

Murmushin ƙarfin hali nayi yayin da naji murya wata mata akan ita babu yadda za'ayi a cuci rayuwata a gauraya mata zuri'a da jinin Aliyu , sunan Inna ta faɗa tana ci gaba da cewa har sukayi aurensu suka gama ni ban taɓa zuwa ko anguwar daya zauna ba bare nayi tunanin taka ƙofar gidanshi , ɗan iska mashayin banza mashayin wofi duk ma wanda yasan kanshi taya za'ayi ya bari a gauraya mishi zuri'a da gurɓataccen ahali.

Maganar Kaka naji cikin rawar murya tana cewa ai hannunka dai baya ruɓewa ka cireshi ka yar ko kina tunanin asalin ɗanki yafi ita Maryam ne ? Cikin bala'e tace nidai babu wanda zai haɗamin ɗa aure da wannan yarinyar wallahi , yarinya "yar iska jahilar banza jahilar wofi , sai cin mutunci takeyi wa Babana , abun yamin ciwo amma banda yadda zanyi ,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.