Trending Hausa Novels

Kwarata Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Kwarata Complete.txt

Chapter 4 of 7

Ci gaba sukayi da caccar Babana suna gulmarshi suka tado da tarihin auren Inna ai saboda baƙar kafiyarta taje ta aureshi ta zaɓi namiji tabar iyayenta gashi yanzu taje ta haifo ɗiya ɗaya kwantilkwal ta rasa ubanda zai aure ta , ai tasan a zuri'armu auren zuminci kowa keyi jakkar banza taje ta rasa namijin da zata aura sai ɗan caca , shima ɗayan marar zuciyar dake sakarai ne aka sakota har ya dawo ya aureta , wato mijin da Inna take aure yanzu ko ?

Kaka tace to ina za'a kai rabon Maryam ? Cikin ɗaga murya tace rabon wahala ? Hajiya ku hausawa wani abune daku wai sai kuzo kuyi abu idan ya samu damuwa wai sai ku riƙa dangana shi da rabo ne sai kaji mutum na cewa wai rabo ko na abincine sai kaje kaci ka dawo babu wani maganar rabo tsabar kafiyace saboda haka ai itama ɗiyarta ta tana da ahalin Babanta taje can suyi auren zumincisu su haifo masu bakin hali "yan caca karuwan banza.

Ikon Allah wai waye ma yace musu auren "ya "yan nasu zanyi ? Aikin banza anba makaho kyautar ido yace banso wari yake dan yasan baya samu ne nima bana san "ya "yanku kuje can kuji dasu nayi maganar a dai² lokacin dana sauko daga saman gado ina tunanin wato ita Inna auren Babana tayi "yan uwanta basa so ? Toilet na shiga dakel ina cewa mune karuwan banza karuwan wofi.....?

Ku fiddomin shi Dady ne yake magana a fito mishi da Bello , bayan an fiddoshi Dady yace ina Sultana.....? Bello yace ban san inda take ba , Dady yace wai kunji har yanzu bai tuna inda take ba , tou ku sake markaÉ—ashi muji , saida Bello yasha juyin alalar gero akace ka gano ko tana ina ? A wahalce yace tana tare Dikko ,

Dady yace wane Dikko ? Cikin nishi yace Dikko U DK , Dady yace kai kana da hankali kuwa ? Idan har ka bari DK yaji ma kana danganta shi da wannan yarinya tou ka sani saiya yanke maka harshe wallahi , ko kana tunani DK zai saurare ta ne ? Bello yace wallahi yana tare da ita , kuma tana zaune a gidanshi na goruba road ,

Duƙawa Dady yayi kusa da Bello yace ya akayi kasan yana tare da ita bayan shi kowa yasan baya harkar mata , murmushi Bello yayi ya fara cewa.

Bincike na ya nunamin cewa tana zaune a gidanshi bayan dogon lokaci dana ɗauka ina nemanta , duk inda naje bata nan nasa an kirata da wayoyi da dama daga mutane daban² amma duk wanda ya kirata saita banbanta inda take ,

Da naga rainin wayan nata yayi yawa saina duƙufa wurin ganin na samota ko ta halin ya ya ! Nayi binke a wurin ƙanin mahaifinta bayan nayi masa ƙarya cewa zan haɗa kan "ya "yan Binna ne a wuri ɗaya shine yacemin baisan inda suke gaba ɗayansu ba , Sultana dai da tana nan amma wasu ke memanta saita bar wurinshi ,

Bayan an kwana biyu na sake komawa na tambaye shi ko masu neman nata sun sake dawowa ? Sai yacemin kullum sai sunzo yauma zasu zo ? Ban daɗe da zama ba muna fira da ƙarami sai gasu sun sake dawowa , drivern DK ne a da amma a halin yanzu sun rabu kuma bansan abinda ya rabasu ba ,

Bayan sun gama bincike² n su naje muka gaisa dashi Al ' Ameen nace masa lafiya kake neman Sultana ? Kai tsaye yace matar Dikko tasa a ɗauko ta kuma a halin yanzu sun gano tana zuwa erudite idan ta tashi tana zuwa islamiyya daga nan sai a nemeta a rasa ,

Tunda naji tana zuwa Erudite na É—anawa wurin tarkon , tun safe nake zuwa ina zama a wurin bana ganinta washe gari dana koma sai naga DK ya kawota da kanshi a mota , daya sauketa ya tafi sainabi bayanshi naga ya koma goruba road mai gadin gidanshi shi ya tabbatar min da Sultana tana zama a gidan.

Tashin hankali shine abinda Dady ya faɗa tare sa cewa wallahi bata taɓuwa a bayyane dole wurin boka zamu koma shine kaɗai ya isa ya kashe mana ita , domin barin yarinyar nan a raye barazane ga dukiyata domun ita kaɗai tasan sirrin komai idan har yarinyar nan bata mutu ba tabbas miliyan 45 na kuɗin gado zasu fito kuma daga cikin dukiyata zasu fito , manyan gonakai dake funtuwa da wanda suke a cikin gari gidajen zama da duk sauran ƙaddarori kai haka bama zai yuwu ba ,

Da kanshi ya ɗauko kayan Bello yace saka ka tashi mu tafi idan har ba haka ba dani dakai ƙaryarmu ya ƙare , zuciyar Bello cike da kudurirrika akan Dady domin dukan da yasa akayi mishi ya saka kayanshi suka fita daga cikin station suka nufi wurin boka...

Bayan nayi wanka nayi sallah na kira Inna muka gaisa nace Inna yaushe zaki dawo ? Tacemin sai bayan wata biyu , tambayarta nayi cewa ina so nasan ya akayi kika auri Babana ? Basar da maganar tayi cewa Dikko ma ya kirani ɗazu da safe kashe wayar nayi na ƙyaleta ni bata bani ansar tambayata amma ita tana so tayi min nata maganar daya shafata !

Ina tsinke kiran Inna na kira wayar Dikko , yana zaune a palon mahaifiyar shi tana ta zageshi ɗaiɗaya akan wai bayayi ma Jiddah adalci baya cin abincin ta yace zai riƙa ci , kuma tayi maganar Mardiyya , yace taje ta riƙa kwana , wato ana sasanci dai tana ta farfaɗo matsaloli kuma akan Dikko , Dikko dai sai haƙuri yake bawa Momy ya ƙagara ya tashi yaje wurin An mata gashi harta fara kiranshi , hankalin shi yana kan wayarshi yaji Jiddah na faɗawa Momy wai tayi ma Dikko magana baya barinta baccin dare ita yana shiga haƙƙinta da yawa maganganun dai babu daɗin ji , kunya ma ta hana Dikko ya iya ɗago kai gaba ɗaya wutarshi ta ɗauke zufa yaji tana tsiraro mishi cikin jikinshi lallai yau ya saki da lamarin Jiddah miƙewa yayi zai fita itama Momy kamar saukar aradu haka taji maganar cikin karyewar murya tace Dikko jirata ku tafi , Momy ba gida zanje ba yana faɗin haka ya fice daga palon ,

A kunyance ya shiga mota kamar wani yana kallonshi a zuciyarshi yake cewa tashin kallabi amma kullu yaci amanar koko yanzu idan har Jiddah ta sameni da wannan matsalar ai zamuyi maslaha basai ta tonamin asiri ba , dakel ya ɗauki wayar Sultana cikin damuwa yace An mata da Allah yi haƙuri ganinan ina zuwa wurinki yanzu in Allah ya yadda,

Karka zo gidanmu , me yasa ? Sunyi baƙi sosai kuma banajin daɗi ? Me ya sameki ne ? Inayin rashin lafiya , sannu bara dai inzo , a , a , nidai karka zo , wani abu ya faru ? Babu , gidan ne bana so kazo , ni kuma ina so in ganki bari inzo in ɗaukeki mu tafi goruba ? Nace tou , riƙe wayarshi yayi a hannu yana tuƙi a ranshi addu'a yakeyi Allah yasa An mata ita dai bata da wannan jakancin ,

Dikko yana fita Jiddah tace ni gaskiya Momy kin barshi ya tafi baki mishi magana ba , basarwa Momy tayi kamar bataji ba tace yanzu dai tunda nayi mishi faÉ—a saiki tattara Al ' Ameen ya maidaki.

A hankali na fito daga É—aki na shigo palo kuma har yanzu basu daina zagin Babana ba , shi kuma wanda suka zo su tara har yanzu bai iso ba , cikin sakin fuska na gaishe su babu wanda ya ansa inda Kaka take zaune na kalla tare da cewa zanje in dawo , Allah ya tsare hanya tayimin na fita dan Dikko yamin waya yazo.

A ƙofar gida na sameshi tunda na fito yake kallona cikin yanayin damuwa har na shiga motar , zuciyoyin kowa na ɗauke da damuwa ni ina tunanin yadda zanyi in faɗawa Dikko abinda akayi min akan zagin Babana da aibatashi da akayi , shi kuma yana jinjina yadda zai faɗamin tashi damuwar ,

Saida muka tafi yace An mata babu gaisuwa ? Yayi maganar yana miƙomin hannunshi , kamar jira nake yayi magana na fashe da kuka , murmushin ƙarfin hali yayi cewa Allah ya baki haƙuri danshi a tunaninshi maganar da yayimin yasa nake kuka , ni kuma abun duniya ya dameni ,

Har mukaje goruba kuka nakeyi kuma Dikko bai bani haƙuri ba saida nayi kuka na gaji nayi shiru dan dama da yayi parking bamu fita a mota ba , saida na gama kukan yace An mata meke damunki....? Dakel nace masa damuwa ji nake dama in mutu kawai in huta , ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa kiyi haƙuri dukkan tsanani yana tare da sauƙi , ina tare dake kuma in Allah ya yadda damuwa ya ƙare , kuma kiyi haƙuri dan idan ina damuwa ko kinayin taki zan faɗa miki nawa ki koyi riƙe damuwa biyu a cikin zuciya ɗaya , kuma ki koyi farantamin koda kina cikin damuwarki kiyi ƙoƙari ni ki bani farin ciki.

Yau idan zan faɗa miki abinda yake damuna ke kanki sai kin tayani jin babu daɗi , juyowa yayi sosai yana kallona yace An mata dan girman Allah ki daina tsokana na muna ɓatawa , ina da lalura ƙatuwa ki tausayimin ki riƙa kwantarmin da hankalina , ki kiyaye ɓatamin rai dan Allah , ki koyi riƙe damuwata kuma ki zama mai yayemin duk wani baƙin ciki idan kika ganin a yanayi mara daɗi , ni a rayuwata gaskiya ina san mace "yar gayu wayayya mai aji , wadda ta iya tarairayar namiji mace mai sirrinta sirrin ta da ɓoyemin nawa sirrin , macen da zata anshi buƙata ta kuma yi haƙuri ta biyamin ita cikin soyayya da kulawa ba tare data gajiya dani ba , ina san mace ma'aboci ƙamshi da tsabta danni gaskiya ban haɗa mace da komai ba ki zama mai kula da tsaftar jikinki domin ko wane lokaci zan iya buƙatarki kuma ina so duk lokacin dana zo ya zama na sameki a shirye dan natsuwa bata samu babu tsafta ba ƙamshi.

Har yanzu ke yarinya ce kuma kina magana irin ta yara maganarki tanamin daɗi a haka amma yanayin kallon da kikemin baya ɗaukar hankalina kallon da kikema kowa bada irin kallon nake so ki riƙa kallona ba , dole sai kin zama jajirtacciya ki zama gogaggiya wurin iya sarrafawa da kuma ɗaukemin hankalina ga tunanin kowa saike ,

Kwantar da kujerar mota yayi ya kwanta saitin zuciyarshi ya taɓa yace kinga ni ba mahaukaci bane ba amma ke kina ganin inayin ɗabi'u irin na mahaukata , murmushi yayi yace ina da lalurar aljannu basu a jikina amma suna tare dani suna shafar jikina yayin da na shiga yanayin fushi , shi yasa idan raina ya ɓaci nakeyi abu kamar mahaukaci yadda kika faɗa , amma ana ta addu'a kuma nima inayi kema ki tayani kinji "Yar matana ? Nace to , ba tare daya kalleni ba yace bara inyi waya a kawo mana abinci muci kisha magani sai in madaiki gida...

Wata irin ashariya boka ya babbaka tare dayin wani irin mazurai yana kallon su Bello......

27/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA...*💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 66

Daga Bello har Dady duk tsoro ya kamasu kowa a ƙagare yake yaji abinda boka zai faɗa bayan sun kora masa bayani cewa sudai duk yadda za'ayi ya kashe Sultana har yanzu basu samu yarinyar ba , kuma a halin yanzu babu wanda yasan inda take ,

Dariya boka yayi sosai sannan yace nace bazan iya kasheta ba , Dady yace me yasa ? Boka yace aljannun da nake tsafi dasu basa san mutum mai cika kamsus salawat dole sai yarinyar nan ta daina salloli biyar a rana kaɗai zasu iya kasheta , ba kuma zasu kasheta ba tana cikin jinin al'ada ba dole² sai ta daina sallah sannan kaɗai su iya kasheta.

Dady yace zan baka miliyan É—aya , girgiza kai boka yayi cewa bata ansuwa kuma bata ciwuwa kuje kawai kusan yadda zakuyi ku dakatar da ita daga sallolin dana faÉ—a idan ta daina ni kuma zansa aje a tsige mata wuya , cikin hayani ya ida maganar cewa ku tashi ku bani wuri......

Daga Dady har Bello da sauri² suka fito daga wurin boka bayan sun fito ne Dady ya kalli Bello yace duk yadda za'ayi ka samo mana yarinyar nan mu kasheta da kanmu idan har ka samota zan baka zunzurutun kuɗi har naira miliyan 20 , murmushi Bello yayi ya kalli Dady a ranshi yace haba ai kafin Sultana ta mutu kaine mutum na farko da zan fara kashewa , yadda ka wulaƙantani a ofishin "yan sanda kana tunanin ka wulaƙanta banza.....?

Amma a fili sai yace zan iya Alhaji amma ba zanyi aiki bashi ba , Dady yace dama ka taɓamin aiki a bashi ne ? Bello yace har yanzu ina binka cikon kuɗin shiga rayuwar Binna da nayi tun muna matasa , ina binka kuɗin asirin da nayi masa ya shiga caca ya shiga harkar mata sannan kuma har yanzu kuɗin lalata rayuwar Sultana sisi ma baka bani ba ,

Dady yace to wannan zan baka dai , Bello yace tou idan ka haɗo kan kuɗaɗen saika kawomin ni kuma a ranar zan shafe lissafin sunan ta a cikin jerin sunayen masu lumfashi a duniya , Dady yace karka damu zuwa ƙarshen satin nan zan baka , haka dai suka shiga mota suna tattaunawa....

Auntyna ga wasu kayan mata na kawo miki suna da kyau sosai kuma zakiji daÉ—in amfani dasu masu kyau ne jarababbu ne , Mardiyya ce a gaban Jiddah take korata mata bayani akan kayan matan data haÉ—o take mata bayani cewa kinga wannan sunansa babu sauran kallo , wannan kuma rantse baki da kishiya , Jiddah tace ya rantse baki da kishiya.....?

Murmushi Mardiyya tayi cikin kwantar dakai mai nuni da salon yaudara tace ai Aunty idan kikaje sayen maganin sai kinyi rantsuwa baki da kishiya ma sannan a siyar miki dashi , dan idan har kina da kishiya ba'a baki shi dan Yaya DK bazai sake zuwa wurin ta kullum yana tare dake manne kamar hanta da jini , dariya Jiddah tayi ta É—auki maganin tace Mardiyya ina kika samominshi ne ?

Mardiyya tace ni na samo miki shi a BanbaÉ—awa kuma Aunty da tsada na siyo shi fa , shi kuma babu sauran kallo Yaya baya sake kallon ko wace mace saike domin kece sarauniyar zuciyarshi , dariyar jin daÉ—i Jiddah tayi cewa kuma kamar kinsan aure zaiyi , wata irin faÉ—uwar gaba Mardiyya taji lokaci guda taji wutar ganinta ya É—auke , Jiddah taci gaba da cewa ance ma Momy yana aiki gidanshi na goruba road wai acan zai ajiye matar , gidaje biyar ya siya ya haÉ—e yana tayi ma amarya gyara , amma Momy tace masa ko waye ya tsaya masa bazaiyi aure ba sai yace mata dama ai ba aure zaiyi ba , kuma da tace masa ance mata yana gyaran gida idan ba aure zaiyi ba me yasa yakeyi ? Shine yace mata masu gidajen ne kawai zasu siyar shine sukace da Allah ya siya shine fa ya siya.......!

Amma ni wallahi inaji a jikina Yaya aure zaiyi , gyara zama Mardiyya tayi tare da cewa Aunty taya zaiyi aure bayan ya faÉ—awa Momy bazaiyi ba ? Murmushi mai ciwo Jiddah tayi sannan tace idan har Yaya yace zaiyi abu to wallahi duk duniya babu wanda ya isa ya dakatar dashi sai yayi , idan kuma yayi rantsuwa akan abu shima ko za'a mutu sai yayi , kaifi É—aya ne shi kafin ya furta yake da wahala amma da zaran ya furta tofa ko kanshi baya saurara ,

Mardiyya tace amma me yasa baki faÉ—awa Momy auren nasa da gaske ne ba ? Jiddah tace Dady tayi ma magana akan ya dakatar da Dikko maganar aure ba zata yadda ayimin kishiya ba , sai Dady yace mata Babana zaiyi aure shine bai faÉ—amin ba yayi faÉ—a sosai sai Momy tace itama hasashe ne takeyi , sai Dady yace shirme kenan yama É—auka gaske ne da yace me yayi ma Babansa aure haka babu shawara ?

Cikin kwantar da murya da ladabin munafirci Mardiyya tace to aike ma Aunty ance ki samo sparm inshi kin gagara , Jiddah tace tunda bai bani ba wai ya zanyi ne ? Tayi maganar cikin hayani , ganin haka yasa Mardiyya ta sake kwantar da kanta tace akwai wani magani da zan samo miki a tea zaki zuba mishi ko a lemu amfanin maganin nan shine yana sa sha'awa na masifa kin gane ki bashi shi da safe zaiyi ta nemanki ya kwanta dake saiki ƙi yadda kiyi ta ja masa rai , zai kasa fita ke kuma kinayin abubuwa irin wanda zasu na tayar mishi da hankali kuma ba zaki kwanta dashi ba , zaiyi ta roƙonki idan kikaji nacin nasa yayi yawa sai kice zakiyi amma da sharaɗin zai baki.....? Zai ansa kai tsaye dan yana bisa matakin da bazai iya miki gaddama ba , haka dai sukaci gaba da tattaunawa taron wawayen...

Ko da aka kawo abincin a mota mukaci saboda gidan akwai taron ma'aikata sosai sun wasu ta ko ina kowa yana aikin daya shafeshi , bayan mun gama cin abinci ya fita yacemin yana zuwa , nima ta cikin madubi na leƙa na gani an ɗaukeshi a mota sun fita daga gidan , ina ganin ya fita kuma ga mota nima na koma mazaunin matuƙi na fice daga gidan na nufi sabon layi ,

Lokacin danaje sabon layi ban fita daga cikin mota ba saboda banajin daɗin jikina , ina zauna na kira wata mata nake tambayar matar nan ko ta dawo ? Tacemin ta dawo amma yanzu bata nan taje Qerau , ni da kaina na buƙaci tayi min kwatance ina taje a Ƙerau tacemin gidan Kaka , nace wacece Kaka ? Tacemin baki san Kaka ba ? Nace ban santa ba , tacemin aiko kowa yasan Kaka garin nan , wayarta ta buɗe ta miƙomin bayan ta nunomin hoton Amisty tana cewa wannan itace Kaka , murmushi nayi tare dayi mata godiya na maida mata wayarta bayan na bata kuɗi na tunkari Qerau kai tsaye....

Ina tafiya ina tunanin Amisty har ta zama Kaka bama uwar karuwai ba Kakarsu fa ? Lallai Amity tana da sa'ar rayuwa , babu wani nisa tsakanin sabon layi da Qerau cikin ƙanƙanin lokaci na isa ƙofar gidan Amisty , taron karuwai da "yan daudu duk wata tsinana da bakin iyaye ya kama gata nan tana wurin karuwai burjik , hada wasu daga cikin "yan gidanmu suma dai duk anyi musu sign in karuwanci , Hamida na gani naga Fa'iza naga Farida naga Zainab ni da yake dai ban san sunansu ba amma duk fuskokin "yan gidanmu na gansu sunkai su goma sha wani abu ashsha...

Inayin parking na sauke glass Hamida ta fara gani na ta rugo wurina cikin farin ciki tana Sultana kece ? Murmushi nayi kaɗan tare da cewa ya gda ? Lafiya qalau me kukeyi anan naga an taraku ? Kallon taron mutanen tayi sannan ta kalleni tace ƙuru'a akeyi , wace irin ƙuru'a ne ? Gasa za'a tafi ta wasan danbe ? Idona naji ya cika da hawaye na kalli Hamida sosai nace kema hada ke a zuwa gasar ne ? Dariya tayi mai nuni da nama raina ta , murmushin ƙarfin hali nayi cewa uhum ? Tace ai nima ina jagorantar team guda ne bayan anyi ƙuru'a idan mutum yaci sai ayi masa interview idan yaci sai ayi training.

Ina ne zakuje gasar ? Na tambayeta , tacemin a gabi za'a gabatar da gasar , bin taron matan nayi da kallo na hango Safiyya yarinyar Baba Ƙarmi itama ta samu isowa Maman Affan da Maman Sadiq kallon Hamida nayi na tambayeta suma wa'ancan hadasu za'aje ne ? Tace suma suna da yaransu , amma ba matan aure bane ba ? Murmushi Hamida tayi cewa ai matan aure ma sunyi kowa yawa a ciki , to me yasa suka shiga harkar danbe bayan suna da mazajen su ? Hamida tace kowa da matsalar data kawoshi kedai bar kowa yayi rayuwarshi , jinjina kaina nayi a lokacin dana hango matar da nake nema dan haka nacema Hamida ta kiramin ita.

Tafiya tayi dan kiramin ita yayin da ni kuma nabi taron dandazon mutanen ina kallo , hankalin duk wanda yake wurin akan motar da nake yake amma tunanin kowa dai Dikko ne shi yasa babu wanda yazo , turomin matar tayi ita bata dawo ba , bayan mun gaisa nace mata kin kuwa gane ni ? Murmushi tayi cewa ya kuwa za'ayi na manta Binna ? Nace yawwa , tou wai ya akayi ranar muna tsaye sai kawai kika ɓace abunki ? Cikin damuwa tacemin wallahi yaran Dikko ne suka ɗaukeni sukaje dani sukamin tambayoyi akan abinda na sani game da Binna da rayuwar ahalinshi , abinda yasa ya shiga harkar caca da kuma bincike akan mutuwarshi , yana da wasu abokan hamayya wanda suke takon saƙa nace musu babu , sundai bincike sosai kamar an bajewa uwar san banza dilar gwanjo.

Kallonta nayi sosai sannan nace to me yasa baki dawo ba ? Riƙeni sukayi a wurinsu har sai da DK yazo da kanshi , da yazo , shi me yace miki ne ? Shima dai tambayoyi yaimin , a tambayar me ya tambayeki ? Hankalinta yana wurin taron su dan haka tacemin ki bari kawai zamuyi magana daga baya , nace a , a ki saurareni mana , dan Allah kiyi haƙuri ko kuma ki bani number wayarki idan na gama abinda nakeyi zan kiraki , wayata na miƙa mata tare da cewa kisa taki a ciki sai ki kira dan kiga nawa , haka tayi bayan ta gama ta miƙomin ta wuce ,

Fita nima nayi daga cikin motar ina tunani kafin Dikko ya gama yin bincikenshi insha Allah ni na gama da matsalata , domin ni nasan abokan takon saƙar Babana, babu wanda ya sani saini ɗaya kuma saina kwatarwa kaf ahalina kuɗin gadonsu sannan kuma da hannuna zan ɗauki fansar mutuwarshi , nayi maganar ina kallon tafukan hannaye na ,

Fitowata daga mota yasa wurin ya ɗauki ihu mutane sukayo wurina suna ta runguma ta , yayin da wasu ke tambayata inda na shige , Amisty Hafsa da duk wanda na sani babu wanda bai rumgumeni ba haka nayi ta gaisawa da mutane cikin riƙe aji da kamewa sosai yayin da wasu kuma suke tambayata inda nake zama , babu wanda naba ansa saidai nayi murmushi kaɗan ,

A wayance Amisty ta fara gabatarmin da sabbin karuwai da irin jajircewar su a harkar bariki , saidai in jinjina kai , su Nana da A ` i Karima da Saude har Asma'u babu wanda babu a wurin domin naga suma sun ƙwace da yawa , Amisty ta zama gogagga sosai a bariki ta anshi takaddun gaba da degree a wurin karuwanci taci bilicin an saka haƙorin makka ƙasa da sama , anyi hujen hanci duk dai inda kake neman karuwar data ansa sunanta a harkar karuwanci kana ganin Amisty ka tsaya , domin kallonta kanshi shima abin burgewa ne , tadai zama Kakar da gaske.

Kallon Hafsa nayi nace ke kuma kinje wurin Dikkon ne ? A sakace tace ni naje wurin daga nan bansan yadda akayi ba , nace kamar ya ? Wasu suka saceni suka kaini wani gida sukayi danbe dani , keda baki san yadda akayi ba ya akayi kika san anyi dambe dake ? Na faɗi maganar ina dafa kafaɗarta muka fara tafiya muna fita daga cikin mutane ina mata tambayoyi kamar haka , su waye suka kamaki ? Ni bansu ba kawai napep yana sauki ni a fesra suka cakumeni , me yasa bakiyi ihu ba ? Nayi ihu dan a kawomin ɗauki daga baya sai suka toshemin bakina , me yasa baki ƙwaci kanki da karfi ba ? Bana iyawa saboda suna da yawa , da suka ɗaukeki ina suka kaiki ne ? A mota suka sakani suka tafi dani wani gida , da sukaje dake ko kinji suna cewa wani abu ? Eh bana iya tunawa dai amma naji mutumin dai yana ta maganganu kuma sunanki yake kira kawai dai na manta abinda yake cewa ,

Kiyi tunani mai kyau idan har kika tuno ni da kaina zan ɗaukeki a mota na kaiki wurin Dikko kuma tsaya ki gani , wayata na fiddo na fara kiran wayar Dikko , ashe Dikko harya koma gida ya samu bana nan , ƙin ɗaukar wayar yayi na sake kiranshi tuni Dikko ya gune yana jira in dawo ya saukemin rashin mutunci.

Ganin Dikko bazai ɗauki wayar ba nace yawwa kin gane ki tuno idan har kikamin gamsashen bayani wallahi sai na kaiki wurin Dikko , murmushin jin daɗi Hafsa tayi cewa , bara in tuno muji , dafe kanta tayi tare da ƙurawa wuri ɗaya ido , tunda taji maganar zan haɗata da Dikko dole nasan zatace wani abu.

Bayan wani lokaci tace yawwa , ni kuma nace dana kiraki kince min kina Qerau , nayi maganar niƙaf da hijabi nace Dikko yana jiranki a fesra ki fara tunani tun daga lokacin da kika hau napep.

Hafsa tace bayan na sauka a napep na fiddo wayata na fara kiran wayar Dikko sai akacemin a kashe yake , ina tsaye a wurin ban tafi ba ina ta kiran wayar kawai naji an nannaɗeni ta baya , nace su waye haka ? Ina zakuje dani ? Sai wani ya mareni yace wurin ubanki zamu kaiki , na nemi a kawomin ɗauki sai suka shakeni da niƙaf suka sakani a mota ,

Sun kaini wani gida bansan ko ina ne ba , wani ne ya fara zuwa a kaina yana danbe dani , sunyi maganganu dai , tayi shiru , ƙara dafeta nayi sosai nace waccan motar kinsan ko ta waye ne ? Hafsa tace ta DK ce , nace tunda har nahau motarshi ai kinsan kusanci yakai ko ? Tacemin Eh tana kallona , nace tou duk cikar faɗin birnin katsina Dikko baida aminiyar daya wuce ni , idan nace yayi zaiyi idan nace ya daina zai daina ya yadda dani fiye da lissafinki , me kike so na roƙar miki a wurin Dikko ? Cike da zumuɗi tace ni ya aureni kawai , nace Dikko ya aureki ya gama idan har kika bani labarin komai baki ɓoyemin ba saina sadaki da Dikko faɗa ina saurarenki , saida ta sake tunani taci gaba da cewa !

Tabbas naji wani yace nine Bello aminin ubanki , kiji da kyau yadda kikamin video tsirara haka zanyi miki kema , ni na koyama ubanki iskanci amma É—an iskan ya lashemin mata a daren farko , yace na É—ana masa tarko amma É—an banzan ya tsallake , idan baki sani ba nine nayi asiri wa Babanki kuma nine na haÉ—ashi yake tarayya da ahalinshi ,

Kuma yace nine nayi asiri wa Babanki ya sakaki a wasan caca nine na mayar dake kidahumar ƙarfi da yaji na sakaki kika antaya a ruɗun duniya , bayan ya gama magana yace ni Bello zanyi iskanci da "yar ka idan ka isa ka dawo daga duniyar mutuwa ka ƙwaci "yar ka a hannuna ,

Ya kira Binna daga baya kuma yadai yi maganganu sosai kuma Dadyna yana wurin , kuma mai maganar yace yayi asiri ahali ɗaya sunyi gauragauraya suna iskanci badai zan iya ganewa ba domin ina cikin wani hali a dai² wannan lokacin.

Sakin Hafsa nayi tare da juyawa nace wane irin hali kike ciki ? Juyowa nayi na shaƙe wuyan Hafsa ina cewa wane irin hali kike ciki ? Wane irin haline wannan ? Me Dadyn naki yake faɗa......? Me yace ? Nayi maganar cikin hayani sosai tare da cewa na rantse da Allah idan dai harni ɗiyar Binna ce ɗaya daga cikinsu idan ya sakeyin rayuwa mai daɗi ni ba ɗiyar Babana bace , sakin Hafsa nayi tare da turata baya da ƙarfin bala'e ta kusa faɗuwa Amisty ta riƙeta tana lafiya Mother , idona cike da hawaye nace dake da Hafsa dani gaba ɗayanmu ahali ɗaya ne ,

Gaba ɗayansu babu wanda baiji faɗuwar gaba ba , cikin tashin hankali Amisty ta cire gilashin dake saman fuskarta tana kallona , saida na goge hawaye sannan nayi murmushi mai ciwo nace kunji wani iri ko ? To nima haka naji lokacin da aka faɗamin ku "yan uwana ne , nayi kuka kuma nayi baƙin ciki kasancewa ta a cikin gurɓataccen ahali , cikin ɗaga murya sosai nace tou ku sani ni ɗin ɗiyar Binna ce kuma nima jikar gidan su Hafsa ce dani da "yan uwana da kowa na nuna Hafsa cewa tou idan baki sani ba Kakarki itace silar roshe komai , duniya ya ruɗeta yasa ta kora "ya "yan kishiyarta saboda san duniya wanda basu ji basu gani ba , ni ɗaya tak nake a wurin uwata kuma soyayyata a zuciyar Babana ba ƙarama bace ba , fashewa nayi da kuka ina cewa amma shine suka kashe Babanan, me yayi musu ne ? Cikin musulmar murya na sake cewa me yayi muku ? Mu kuma me mukayi musu suka mayar damu marayun ƙarfi da yaji ?

Inda taron "yan gidanmu suke na kalla tare da nunasu nace su kuma wa'ancan me sukayi muku ne ? Me suka tsare muku ? Shine kukayi silar maida ahalina karuwai........? Cikin ɗaga murya na cire gyalena na wurga saman mota ina cewa na rantse da Allah , na daki kaina , dai² zuciyata nakai ma duka cewa na rantse da soyayyar mahaifina idan nabar ubanki da kakarki sun huta Hafsa kice ni ba MARYAM ALIYU MUHAMMAD BINNA nake ba , ni ba ɗiyar BINNA bace ba.

Cikin tashin hankali Hafsa ta rugo da gudu ta riƙeni tana cewa Uwar ɗaki me yayi zafi haka ? Ki goge ƙudirin ɗaukar fansa a zuciyarki , cikin hayagaga nace ke ji nan kije ki tambayi wannan ruɓaɓɓiyar tsohuwar meye dalilin da yasa ta kora Binna da ɗan uwanshi daga cikin gidan ubansu , murmushi nayi mai kyau ina kallon Hafsa cikin tsananin ɓacin rai nace to ki sani nice na shirya komai ta yadda aka saceki akaje akayi wasan danbe dake , nina shirya komai kaidina da sharrina yafi alkairi na yawa , idan har kina so na goge babanki daga siraɗin ɗaukar fansa na baki daga yanzu zuwa gobe da safe kije wurin kakarki ki tambayota dalilinta na kora iyayena daga cikisu kizo kuma ki faɗamin idan kuwa ba haka ba kema zaki zama marainiya kamar yadda mu "ya "yan Binna muka zama marayu , ina faɗin haka na wuce na shiga mota nabar wurin cikin ƙunar rai.....

Daga Hafsa har Amisty sun gagara gane abinda Sultana ke nufi saboda toshewar tunani , Amisty tace taya ma zamu zama ahalinta ne wai ? Hafsa kuma tace kinji wata sabuwar barazana wai itace tasa aka saceni akayi danbe dani bayan babu abinda ta sani nice fa na bata labari yanzu bata san komai ba , tana ganin dan na bata labari zatayi amfani da wannan damar ta tayar min da hankali , can ita ta sani da ita dasu wannan ba damuwa na bane ba ,

Ina fita bakin titi wuri na samu nayi parking a gefen titi na fara kiran wayar Dady da wayar da Dikko ya bani ba tashi wacce ya bani ba , babu ɓata lokaci ya ɗauka , cikin wata murya daban nace bawan Allah sannu Allah ya ƙetare "yar ka daga hannun azzalimai , ai dama nace duk yadda za'ayi saina samu number ka na faɗa maka gadar zaren da ake gina maka na ƙarasa maganar ina fashewa da kuka ,

Dady yace wace ce ke ? Cikin kuka nace masoyiyar ka ce , wata ce take neman ganin bayan ka shine ni kuma zan tona mata asiri , dani da ita duk a bariki muka haɗu ƙawata ce kuma itama karuwa ce ana ce mata Sultana ko ka santa ? Murmushi Dady yayi yana cewa tana ina ne ? Tana ɓoye a halin yanzu domin tana nan tana nemanka ta kashe ka shine na sace numberka daga cikin wayarta dan in faɗa maka cewa ka ankare dai dan yarinya bata sanka da yawa , cikin rashin lissafi kawai Dady yace ai har yanzu Binna baida ɗiyar da zata ga bayana ke wace ce ? Nace zan bayyana amma sai ƙura ya lafa kuma karka faɗawa kowa domin da wani abokinka ta haɗa kai suke san ganin bayanka , Dady yace waye abokin nawa ? Nace bansan sunanshi ba saina siffanta masa kamanin Bello na ɗora da cewa wata rana kayi ma Sultana waya zaku haɗu a fesra hotel ita kuma ta kirashi ta faɗa mishi shine shi kuma ya bugama "yarka waya yace su haɗu a wurin dan yana jin haushinka sosai shine yasa yakai "yar ka sukayi danbe da ita kuma kaima yaso sai kayi danbe kaga "yar kace , wata irin ashariya Dady ya dandanƙara cikin jin haushi yace ni Bello zai cuta ? Amanata zaici ? Tabbas biri yayi kama da mutum domin idan ban manta ba ita Sultana tace min wai na ɗan ɓoye mota ta daga ciki dan wani ne zai sauketa , wato tayi haka ne dan kar Hafsa tazo taga mota ta ne , amma a cikinsu waye ya gayyato Hafsa , tsakanin Sultana da Bello........?

Bello ne domin shine ya shirya komai yana jin haushinka fiye da yadda baka tunani , amma Alhaji ina ganin shawara ɗaya me zai hana kawai kasa a kashe Sultana kafin ita taga bayan ka , Dady yace haka muke ta ƙoƙari mun faɗawa bokanmu amma yace sai ta daina sallah kaɗai zata iya mutuwa , shin ko zaki iya dakatar mana ita daga sallah ? Wannan ba abu mai wahala bane kauda ita daga duniya ni kaina idan ka bani izini zan iya shafe maka labarinta daga duniya guba kawai zan zuba mata a abinci taci ta mutu amma sai ka farayin wani abu akan Bello , Dady yace bari in fita daga Office sai muyi magana , godiya nayi masa tare da kashe wayata , bayan na gama na cire layin da Dikko ya siyamin na ciro layin da Dady ya bani na saka a cikin wayar da Dikko ya bani na fara kiran wayar Bello da layin da Dady ya bani , wato number da ake kirana ana cewa za'a kasheni , dan ina so nayi recording ita wayar da Dady ya bani ƙarama ce.

Tana shiga ya ɗauka sai yayi shiru dan abinda na fuskanta number da yake kiran nawa kila daban yasai layin , nace ka gudu daga inda kake ni ina san tseratar maka da rayuwar ka ne , cikin muryar shi dana sanshi da ita yace wace ce ke ? Sanin ko wace ce ni ba shine ba ina san tseratar da rayuwarka ne domin a halin yanzu suna san ganin bayanka , su waye ? Kamanun Dady na faɗa nace shine yake san cin amanarka , kun haɗa kai akan zaku kashe wata yarinya amma shine naji yana cewa sai ya kashe ka , dariya Bello yayi ni kuma na dannan record bayan nayi shiru shima cikin rashin lissafi yace wannan shine ƙudirna da ko wane wata da ko wane sati ko wane yini da ko wace awa kowace daƙiƙa saƙo da lungu rana da dare neman sa'ar mutuwarsa nake , saina kashe shi.

Yana faɗin haka na tsine kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya na nufi goruba road , zuciyar Dady tana ɗauke da gudirin ganin bayan Bello , danshi a ganinshi idan ya kashe Sultana sai ya kashe Bello sune damuwarshi kuma sune suka san komai , idan ya kashe su gaba ɗaya babu wata sauran barazana a dukiyarshi , yayin da Bello shima yake ƙudirin ganin bayan Dady zaisa Dady ya kawo kuɗin da zai kashe Sultana yana bashi kuɗin zai burma ma Dady wuƙa a ciki ya mutu shi kuma saiya ɗauki kuɗin yaje ya kashe Sultana shikenan ya rufe wannan matsala....

Tunda na shiga gidan wani irin kallo Dikko kemin fuskar nan a haÉ—e yana zaune saman bayan motar abokinshi , su Ashiru suna tsaye kusa dashi , jikina yana kyarma nayi parking na fito da sauri na nufi wurinshi , abokinshi na gaida sannan na matsa kusa dashi ina bashi makullin motar , bai ko kalli inda nake ba dan haka na ajiye makullin kusa dashi na koma gefe nima na tsaya kamar yadda naga kowa yayi ,

Hmmm yayi tare da ƙuramin idanuwa yana kallona cikin ɓacin rai , yakai kusan minti 3 yana kallona kuma ko ƙyabtawa bayayi dole na shiga taitayina jikina ya fara tsimama da ƙyarma tuni na sauke kaina ƙasa dan kallo ya firgitani , bayan wani lokaci na sake ɗagowa har yanzu ni yake kallo , da sauri na sake sauke kaina banma yi gigin sake kallon inda yake ba dan bana iya haɗa fuska dashi , tafiya na farayi dan komawa bayanshi ya daina ganina ta gabanshi saboda banajin daɗin kallon ,

Robar ruwa ya ɗauka a gefenshi da magani yace zo ki ansa , ban koma ta gabanshi ba na tsaya daga bayanshi na miƙa hannuna na ansa , robar ruwan ya bani maganin kuma ɓallomin yayi ya miƙamin , ansa nayi nasha bayan na gama na maida mishi robar da sauran ruwan dana rage , ansa yayi ya maida ita a inda ya ɗauka yace tafi Ashiru ya maidake gida , kwantar da kaina nayi saman motar nace ngode , baiyi magana ba Ashiru ya ɗauki makullin yace muje ,

Bin bayanshi nayi ya buɗemin gidan baya na zauna ya rufe ya zagaya ya shiga mazaunin matuƙi yaja muka fita daga gidan , tunda muka fita Ashiru kemin nasiha yana cewa wallahi yau Allah ya tsareki irin dukan da yaso yayi miki Allah kaɗai yayi iyaka dashi haƙuri mukayi ta bashi kafin ki dawo , dan Umar ya kirashi waya yace ya ganki Qerau , mai gida yace ya barki goruba saida ya turo mishi hotunanki sheda ya gani ya yadda kuma ya dawo bai sameki ba , lokacin da kike kiranshi waya tou lokacin ya hau muna ta ƙoƙoarin saukeshi , wai kema ranki ya daɗe dole sai kin fitar wai ? Murmushi nayi amma banyi magana ba , har muka iso gida nasiha Ashiru yakemin , fita nayi tare dayi masa godiya kawai na wuce ciki....

Wasu irin motoci ne parke a harabar gidanmu masu kyau da tsada , kila ɗan uwan Inna ne ya dawo , tunda na tunkaro hanyar da zai sadani da palon naji maganar shi yana cewa ƙaddara babu wanda ya gagara yahau , ni banga abin ƙin wannan yarinya ba , matar ɗazu take cewa wallahi nidai jinina idan dai ni na haifeshi bazai auri yarinyar nan ba , idan kuwa ba uwarshi bace ni tou yaje ya aureta nayi bare duniya dashi ko lahira kada Allah ya haɗani dashi , yarinya karuwa kowa yasan karuwace a garin nan gata ɓarauniya kuma daƙiƙiya kidahuma gata bata fito daga tsatso mai kyau ba , haba duk iyayen mutunci sun haɗa ɗiyansu aure da ita ?

Ɗan uwan Inna yace tunda duk kowa ya hana ɗanshi ya aureta ni zan bada ita , cikin hassada tace ai kasan ɗan tsiya bai gaji arziƙi ba kana tunanin ka haɗa ta da ko driver n ka ko mai gadinka ai ƙarshe watsa maka ƙasa zatayi a ido tace bata sansa kaga kuwa ai ba haka kaso ba , ni ba cikin su zan bata ba , Sultan ɗana zan haɗasu aure a cikin satin biyu masu zuwa , Sultan kowa ya faɗa ɗanka mai mutunci da daraja shi zaka aurawa karuwa ? Gaba ɗaya palon ya gaurare da hayani har bakajin abinda wani yake cewa ,

Hawaye naji ya ɗigomin daga cikin idanuwa na , wayyo Allahna , kila sunyi tunanin zai haɗani da mai gadinshi ko driver ko wani dai mara galihu , ɓarauniya , karuwa , daƙiƙiya , kidahuma ban fito a tsatso mai kyau ba , yace yaji kuma ya gani ɗanshi zai aureni , ya zanyi da Dikko ? Idan har kuma ban amince da maganar ɗan uwan Inna ba ance dama zan watsa mishi ƙasa a idanuwa saboda ban gaji arziƙi ba ni ɗiyar tsiya ce , jinjina soyayyar Dikko nayi a zuciyata gaskiya Dikko yana min soyayya mai girma , a bayyane nace tabbas haƙuri zanyi dakai kodan in nunawa ɗan uwar Inna na fito daga ahalin masu mutunci zanyi haƙuri da soyayyar Dikko in anshi Sultan ko baimin ba , tou tayama zan iya rabuwa da Dikkon wai ? Tun ma farko kenan wayyo Allahna......

Ji nayi gidan yana juyamin yayin da zuciyata kece cewa *DIKKO KO SULTAN...?* cikinsu wa zan zaɓa......?

30/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA...* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 67

Biyu zuciyata ta kasu yayin da wani sashe yake cewa Sultana kada soyayya yasa ki manta da irin halakcin da Kawu yayi muku , kuna banzace a gidan Baba babu cin yau babu na gobe bare na anjima kaf ahalin Inna sun watsar daku basa shiga sabgarku amma Kawu ya shigo rayuwarku yana taimaka muku , Sultana ya sakaki makarantar boko da islamiyya , yana tare daku yana tsotse duk wata damuwarku yau rana tsaka kwatsam sai ya nemi alfar wurinki kice a , a ? Yaga kina tangaririya rayuwa tana ta wurgel dake ance miki karuwa ɓarauniya kidahuma jahila baki fito tsatson mutunci ba amma yace yaji ya gani a hakan yana so ma ɗansa ke , ga "yar uwar Innarki sai tada jijiyon kai takeyi nata bazai auri na banza ba haba Sultana ki so sa don Allah ,

Ajiyar zuciya na sauke yayin da wani sashe na zuciyata ya fara haskomin rashin mutuncin Dikko kai tsaye yake gargaɗina da ke Sultana ina hankalinki yake so ya tafi ? Dikkon me ? Mutumin da bai san komai ba sai rashin mutunci duka zafin kai , babu dariya bare fara'a kullum fuska a haɗe yanayin fushi da farin ciki iri ɗaya , ga matsalar aljannu yanzu ƙarshe ki zaɓi Dikko wani abu ya haɗaku yayi miki tsinannen duka yace ki bar masa gidansa ina zakije a lokacin ?

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un sam Dikko bazaimin haka ba , taya ma wai zai fara korani ? Yama zauna dani babu aure kuma yayi haƙuri dani bai koreni ba sai da yake aurena zaice na tafi ? Zuciyata tace ai wancan zaman bana aure bane ba yasan zaki iya tafiya ko wane lokaci amma zaman aure daban ne haba Sultana yaufa da gobe ake magana , raba kanki da yau da gobe zama ne zakuyi daga nan har mutuwa , kifa tuno rashin mutuncin Dikko babu imani a rayuwarshi duk sissiye gidajenku da yayi har kin manta Sultana ? Babanki da kika fi so fiye da komai a duniya Dikko ya watse shi da ruwan dake kwance saman ƙasa , Babanki mai sanki ya mareki saboda Dikko ? Me ake da Dikko ...?

Zuciyata ta kasa bani mafita , alkairin Dikko ɗaya ta kasa haskowa rashin mutuncin Dikko kawai take gani yayin da take harzuƙa ni tana tambayata ina maganar ɗaukar fansar budurcinki daya kece miki ? Kin fasa ramawa a shekara biyun ne ? Abinda ya faru dani dashi a ranar daya ɓanɓare min budurci ta ƙarfi da yaji ya dawomin kamar yanzu ne yakeyin abun dani , da sauri na rufe idanuwana naci gaba da kuka zuciyata tana ci gaba da huramin wutar ƙiyayyar Dikko ,

Da sauri na goge hawayena na shiga cikin palon da sallama , gaba ɗaya na gaishe su nayi ma Kawu sannu da zuwa na wuce , Maryam yaki , kawu ya kirani , gabanshi naje na durƙusa a saman ƙafafuwana cikin ɗa'a da ladabi , Maryam ai kin sanni ko ? Murmushi nayi ba tare dana kalleshi ba nace na sanka mana sosai , idan na baki guba zaki iya ci ? Cike da ƙwarin guiwa nace me kuwa zai hana Kawu ? Ai ba guba da zanci a abinci ko abun sha ba wuta idan ka hura kace na shiga sai nayi maka godiya zan shiga cikinta cikin aminci da salama Kawu , kallona yayi sosai cewa shin wani irin soyayya kike ma "yan uwan mahaifiyarki ? Goge hawaye nayi tare da cewa ina musu soyayyar da bana iya fasalta irinshi domin su ahalin uwa jigo ne mai girma ko soyayyarsu daban yake a zuciyata , tun kafin na sansu na gansu kullum mafarkina na gansu ina alfahari dasu kuma dana kasance a cikinsu inayin farin ciki bana fatan rabuwa dasu har abada dan su ɗin mutane ne masu mutunci da nuna soyayya akaina...

Yayar Inna tace kunji makirci ko ? Tou mu bama sanki gidan uwar wa muka nuna miki so ? Ke nan "yar tatsiyar alhaki dake har kin iya makirci , bama sanki bakya sanmu amma tsabar ƙwarewa da bariki mu zaki ma bariki ? Tou uwarki ma kanta a gabana aka haifeta ki sani ni nasan kina nan kinaji kamar ki cakamin wuƙa na mutu ,

Murmushi nayi mai ciwo tare dayin magana a zuciyata nace tabbas hasashenki gaskiya ne , amma a fili nace haba Inna aiko da duniya tayi tirr da Allah wadai da dani , magana ce na faÉ—a mata ita da take cewa bata so na kuma a matsayinta na Yayar mahaifiyata....

Kallona Kawu yayi sosai tare da cewa shin zaki iya auren ɗaya daga cikin ahalin mahaifiyarki kuwa ? Kallonshi nayi tare da cewa me kuwa zai hana idan har ya ganni nayi masa...! Idan ya ganki kinyi masa shi kuma ke bai miki ba fa ? Karka damu Kawu nayi alƙawarin sadaukar maka da kaina duk abinda kake so zan aikata , duk uwa sunanta uwa yayar uwa da ƙannen uwa duk iyaye ne yunwa mai tsanani da kewar abinci ya kamani , tsananin yunwa bana iya tashi ko ƙwaƙwƙwaran motsi bana iyawa ina kwance ina jiran mutuwa tazo , sai ga "yar uwar mahaifiyata tazo da ƙwano riƙe a hannunta sai tace "yata na ganki kinajin yunwa sosai wannan ƙwanon yana ɗauke da abinci mai daɗi na taho dashi na baki sai kuma naji nima ina da buƙatarshi kiyi haƙuri ni naci ke kuma ki jira wani , ita tafi ni jin ƙwarin jiki tunda har tana iya tafiya ni kuma bana ko iya tashi tsaye saboda yunwa ga kuma ƙamshin abinci yana ta dakar min hanci amma sai ta hanani bayan taga ni nafita buƙata , ta san wannan abincin shine rayuwata idan ta hanani zan iya mutuwa a ko wane lokaci amma ina kallonta ta zauna ta cinye abincin nan kaf a gaban idona tayi min ƙwalele sai nayi haƙuri ,

Ina nan kwance na kusa mutuwa sai gata ta sake shigowa da wani kwanon abincin shima sai ƙamshi yake , sai ga ɗan uwa mahaifiyata shi kuma ya shigo da nashi abincin amma sai yace Sultana gashi kici amma kiyi haƙuri ya fara yami naji ance min kina nan yunwa zai kasheki shine naje na samo miki wannan kici dan ki rayuwa , saina ansa zanci sai wannan "yar uwar ta mahaifiyata ta ajiyemin nata kwanon tace kici wannan shine sabo bai lalace ba karki ci nashi zai lalata miki ciki , tou faɗamin wane zanci a ciki tsakanin mai kyau ko mai yami ? Wanda baiji tausayin karka mutu ba saiya tausaya maka saboda lalacewar ciki....?

Gaba ɗayansu shiru sukayi suna kallona babu wanda ya bani amsa , kallon Kaka nayi nace Kaka wane zan ɗauka inci a ciki ? Cikin muryar tsufa tace ai wannan lalataccen shi kawai ya kamata kici , murmushi nayi na kalli Kawu nace abun mamaki shi ɗan uwan mahaifiyata yace abincin yayi yami amma ina dubawa sai naga ya fara tsutsa shin Kaka naci kona fasa ? Kaka tace ci kuwa , Kaka sai ita Yayar uwa ta buɗemin nata kwanon sai naga farfesun kaji ne da zafi ga ƙamshi tana kici wannan ki bar wancan ? Kaka tace kajin nan kuwa basa ciwuwa a gareki , dariya nayi na kalli Kawu nace ina fara cin abincin nan kawai sai ya koma min daddaɗa ina san duk wanda zaka bani ina san sa , ina sanka ina alfahari da kaf ahalin mamana fatan alkairi a gareku iyaye na gari , 🙏🏻 ina kaiwa nan na miƙe nabar palon.

Ina shigewa Yayar Inna tace tou na gane wato habaici tayimin yarinyar can ? Nice na cinye abincin dan ki mutu tunda nace ɗana bazai aureki ba , shegiyar yarinyar makira munafika wannan idan ta auri ɗanka aisai ta rabaka dashi har abadan duniya , Kawu yace babu gudu babu ca da baya sati biyu masu zuwa zan ɗaura musu aure , ƙarshe dai saida rayuka ya ɓaci kowa ya tafi Kawu yana cewa zai turo Sultan idan Allah ya kaimu su gaisa.....

Sai ƙarfe 2:19am na buɗe wayoyina kuma a dai² wannan lokacin nahau online na cire hoton Dikko dake a d p ina na saka hoton fulawa , layin Dady na kira yana shiga ya ɗauka yace baiwar Allah tun ɗazu nake kiranki wayarki a kashe , nace bari kaidai wurin yi maka record in maganar abokinka suka kusa kasheni shida Sultana shi yasa na rufe wayar na gudu dan tsira da rayuwata yanzu na samu wuri na tsaya haka nan na gwada sa'a har ina tunanin idan na kiraka a tsakar dare kamar nayi hauka ma ,

Dady yace ai ni tuni nayi bankwana da bacci matsaloli suna neman kunnomin kai , na yadda da Bello 100% tun yana matashi nake tare dashi amma yau rana tsaka zai tattara wannan mutuntakar ya zubar , Hmmm ai danma bakaji abinda yace maka ba , kuma ya buɗe kaff wasu ɓoyayyin surruka yana faɗawa ita Sultana , Dady yace wai me yake cewa ? Ina zuwa na faɗa tare da tsinke wayar , canja layikan nayi layin Dikko zuwa cikin wayar da Dady ya bani , layin Dady zuwa cikin wayar da Dikko ya bani , bayan na gama na kirashi ya ɗauka.

Da babbar wayata na kunno mishi maganar Bello , yaji Bello yana cewa wannan shine ƙudirina da kowa wace daƙiƙa saƙo da lungu rana da dare neman sa'ar mutuwarsa nake saina kashe shi.....

Dariya Dady yayi tare da cewa shirmen banza shirmen wofi akan kaina dukiyata da iyalina zan iya shafe labarin duk wani banza daga sahun masu lumfashi a duniya , speaker na saka wayar na kara babbar wayata na fara ɗauka , Dady yaci gaba da cewa ganin bayan Bello ba wani abu mai wahala bane a wurina na barshi ne ya rayu na wani lokaci dan kauda min rayuwar yarinyar dake adawa da dukiyata idan ya aika ta zuwa duniya matacci nima saina turashi zuwa can ni kuma inci gaba da rayuwata babu maƙiya sa ido da wata baraza akan komai dana mallaka a duniya domin na kauda matsala a rayuwata....

Ajiye recording in nayi a wayata sannan nace Alhaji Bello yana da hatsarin gaske bana tunanin zaka iya kauda matsala biyu a cikin kwana biyu na mutuwarka daya ibar maka , dariya Dady yayi tare da cewa ki bani zuwa jibi zakiji labari yasha banban yayin da za'a faÉ—a a gari cewa wani É—an cacan ya sake , sai kuma yayi shiru ya canja maganar da cewa ngode zan kiraki zuwa safe idan Allah ya kaimu lafiya...! Godiya nayi masa mukayi sallama na tsinke kiranshi na kira Bello.

Cikin maye ya ɗauka kuma daga jin yanayin wurin tabbas yana gidan caca , cikin muryar maye yace ke kika kirani ɗazu ? Ey nice na kiraka , na kiraki wayarki a rufe , Ey na bashi ansa , wai nine ma ɗan ƙaramin ƙwaron nan zai kashe ko ? Nace haka ya faɗa kuma haka yake shiryawa yace gobe²n nan iyalinka zasuyi kukan mutuwarka , amma wai me yasa yakejin zafinka haka da yawa ? Me kayi masa yake san ganin bayan ka ? Saurara kaji abinda yace maka.

Kunno mishi record in nayi yaji Dady yana cewa , ganin bayan Bello ba wani abu bane mai wahala a wurina , na barshi ne ya rayu na wani lokaci dan kauda min rayuwar yarinyar dake adawa da dukiyata idan ya aika ta zuwa duniyar matacci nima saina turashi zuwa can ni kuma inci gaba da rayuwata babu maƙiya sa ido da duk wata baraza akan komai dana mallaka a duniya domin na kauda matsala a rayuwata.

Cikin maye Bello yay dariya yace ni kuma a cikin daren nan zan sakashi a tarko naci gaba da farautar rayuwarshi zuwa ƙarfe 10 dai² na safiyar gobe zan kasheshi na kuma kashe Sultana saina kashe su wallahi , yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.

Wai me kike nufi ne ? Ni zakima gwala² ne ? Dikko ne kwance a saman gado yana jawo Jiddah jikinshi tana zuƙewa tanaja baya tasha wando jeans ta haɗa da belt , Mardiyya ta bata shawara ta daina bawa Dikko haƙƙinshi dan tana sakin jiki yana murjeta sosai shi yasa ya rainata ta kame abunta ta rufe a wando , saida ta bari wasa yayi nisa taga ya fara sakin layi ta ƙwace kanta , Dikko yace meye haka ne wai ? Cikin kwarkwasa da salo mai ɗaukar hankali tana yauƙi tace ai mantawa nayi da zakayi aure saboda ni bankai mace ba shi yasa zakayi min kishiya ? Tou kaje wurin waccen zaka aura sai ta baka maganin damuwar ka , murmushi Dikko yayi tare da ƙurawa Jiddah ido yace yanzu me kike so ne ? Saida ta sake girgizawa tace idan kana so ka kwanta dani sai ka sauka ƙasa ka bani haƙuri , ba tare da Dikko ya kalleta ba yace ai gara in mutu da in baki haƙuri danni mace bata ɗagamin hankali wannan abu fa duk taimakon kai da kaine , sauka yayi daga saman gadon yana cewa idan kinji kina muradi sai ki nema na baki danni bana hora mace da tauye mata haƙƙinta ,

Juyowa yayi ya kalli Jiddah yace duk macen data san kanta tasan mutuncin kanta bata tauye haƙƙin mijinta saboda wani tunanin banza nata , ni da mace neni na rantse da Allah duk mijin daya aureni sai yaga bariki na tashin hankali , ko inuwarshi na gani saina ɗage mishi zani na bashi natsuwa , amma ke har kinma samu an nemeki zaki rainawa mutane hankali waye yace miki horon hana namiji haƙƙinshi shine ke nemawa mace mutunci da martaba wurin namiji ? Idan har baki sani ba wannan abun babu abinda ya kaishi zubar da mutum mace wurin namiji , ƙimarki da darajarki sonki yana ƙara samun nakusa a zuciyata duk macen da tayi ma namiji horon hana haƙƙi taci baya a zuciyarshi.

Misali kece kikayi tafiya a cikin tsananin rana ƙishirwa ya kamaki sosai kamar zaki mutu yayin da kikejin wannan ƙishirwar bakya tarar ruwan da zaki sha wurin kashe miki wannan ƙishirwa , kwatsam sai gashi kinga ruwa a gabanki jikinki yana kyarma kika duƙa da niyar sha sai wani ya hanaki shan wannan ruwan ya tareki , idan kina iyawa a dai² wannan lokacin me zakiyi ma wannan mutumin daya dakatar dake daga biyama kanki buƙatar ki.......?

Jiddah tace sai inyi kokowa dashi in karɓa insha , girgiza kai Dikko yayi cewa ni bana iya gudu ina shan ruwa domin nasan baya kashe min kishirwata , haka kuma bana ci idan bana cikin natsuwa domin idan har naci abu ba'a natsuwa ba tabbas zaisa min tashin zuciya ko kuma inyi amai , ni bana danne mace da ƙarfi na kwanta da ita idan har na kwanta da mace ba'a cikin natsuwa ba bana samun natsuwar da nake so , ni a wahalce ita a wahalce me kayi kenan ? Abinda nake so ban samu ba , ni ba sakaran namiji bane da zaki tsuke da jeans da belt in kamaki da ƙarfi in cire miki na afka kanki kamar wani dabba ƙarshe inji miki ciwo kinga kaina nayi ma tunda gobe idan nazo na laɓe bayanki ina buƙata ya zanyi ? Ya ƙarasa maganar yanayi mata kallon ukku saura kwata , yaci gaba da cewa amma shawara ɗaya zan baki shine ki sake masu baki shawara su koya miki yadda ake tattalin miji wannan wacce ta koya miki haka ba ƙawa bace ba tunda har ta koya miki yadda zaki nakasa rayuwar mijinki , mai maimakon ta koya miki yadda ake tattalashi....

Tun asubar farko Mardiyya ce tsaye a cikin kicin ɗin Jiddah tasha wanka tasha jagira ta ranbaɗa powder da kwalli sai zuba ƙamshi takeyi kamar amaryar sarki , ta haɗu a cikin wani dakeken tsadajjen leshi baƙi tasha atacch ta zubo shi har tsakiyar bayanta , tayi kyau sosai , gaba ɗaya gidan ya karaɗe da ƙamshin girkin da takeyi Jiddah nacan kwance saman gado kamar asara dan Dikko tunda ya fita masallaci bai dawo ba gidansu ya wuce saboda takaicin Jiddah , Jiddah tana kwance Mardiyya ta dafo abinda zasu yi kalaci ta barbaɗe da asiri ta kawo mata , jakar ta sauko ta lashe , bayan Jiddah ta gama tace ta ajiye na Yaya a saman tebirin cin abinci bayan shima na Dikko an barbaɗe da magunguna...

Misalin ƙarfe 11:40am ya fito daga wanka yana fitowa wayar shi ya ɗauka ya fara kiran An mata , lokacin da wayar shi ya shigo ina tsaye a jikin madubi dan fitowa na daga wanka kenan ina shiryawa Sultan zaizo misalin 12:20pm kamar yadda Kawu ya kira ya faɗawa Kaka ta sanar dani , a daddafe nakeyin komai dan har yanzu banajin daɗi jikina yadda ya kamata ,

Wayar yana shigowa na tsinke kiran , sake kira yayi na ƙara kashewa , kallon number yayi yana cewa haba An mata me kuma ya faru ? Bayan jiya ban dakeki ba ranar dana dokeki ma ai bakiyi fushi dani ba yi haƙuri ki ɗauki waya An matan Dikko ya ƙarasa maganar yana sake kiran wayar , wayar yana sake shigowa na ɗauka cikin ɓacin rai nace wai me ye ne......?

Ke.... wa kike ma hayani ? Dakai nake , me yayi zafi ne to ? Haba An matana , yayi maganar cikin sanyin murya , natsuwa tazo jikina na nemi haushin Dikko na rasa kamar an tambayeni nace aure zanyi da ɗan Yaya mamana a cikin sati biyu mai zuwa , yanzu ma na fitowa wanka zaizo wurina mu gaisa , wane irin aure haka da rana tsakiya ? Ko dama kun jima kuna soyayya ne ? Cikin kuka nace a , a , ni banma taɓa ganinshi ba sunansa ma ban taɓaji ba sai jiya sunanshi Sultan , murmushin takaici Dikko yayi tare da cije leɓonshi na ƙasa yace to nima gani nan zanzo , a , a ka bari yazo ya tafi sai kazo , Dikko yace idan har nace zanyi babu wanda ya isa ya dakatar dani saina zo gani nan zuwa........ Yana faɗin haka ya kashe wayarshi.

Cikin ruɗewa naci gaba da shiri kar Sultana yazo ya haɗu da Dikko tunda tun jiya Babanshi ya faɗa zaizo idan kuma ya koma yace Babansa yazo ya samu nayi baƙo ai abun babu daɗi ,

Yarinya Dikko zaki tonawa asiri ? Ni zaki faÉ—a ma aurenki nan da sati biyu ? Duk duniya naga mai aurenki idan ba ni ba , lallai An mata baki da hankali inma banda wawanci da rashin lissafi kai tsaye sai ace za'ayi miki aure da wani kawai kinma yadda kin hankaÉ—eni gefe É—aya , naga jakin Sultan É—in ina fama da matsalar Yazeedu zaki sake tattago wata , yana gama sa kaya kiran Inna ya shigo wayarshi...

A zuƙuwa ya ɗauka , bayan sun gaisa Inna take faɗa masa mutuniyarshi ta faɗa mishi zatayi aure ? Cikin farin cikinta da jin daɗi take bawa Dikko labari cewa ai auren zuminchie ne dake a familynsu auren haɗi akeyi , cikin yanayin farin ciki Dikko yace to kun tambayi ita yarinya tana san yaron ne ? Duk abinda ya faru jiya kamar ansa Inna ta kwashe kaf ta rattabawa Dikko , dan ita bata san Dikko da Sultana soyayya akeyi ba kuma bata san waye Dikkon ba kawai dai tanayin waya dashi dan yayi tsayuwar arfa wurin ganota ya sadata da "yar ta shi yasa ta bashi wani matsayi na musamman a rayuwarta gashi kuma yana ƙoƙarin kiranta a waya yana gaisheta lokaci².

Inna ta ƙara da cewa aiko bata sansa su babu ruwansu haka suke haɗawa a can gidan aure ake fahimtar junan , cikin ƙarfin hali Dikko yace Allah yasa alkairi Inna ta ansa da amin tace itama zata dawo kafin bikin , Dikko ya ansa da a dawo lafiya yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.

Ajiye wayar yayi yana cewa An mata da gaske bari zakiyi a rabaki dani ? Haba yarinya Dikko Yazeed Sultan gaba ɗayansu nine zakaran rukuminsu gani nan zuwa a dai² lokacin daya rataya kayan da zai saka a jikin wani ƙarfe ya rungume turare yana bugawa , wani irin turare ne na "yan gayu mai masifar ƙamshi da tsada wanda ni da naji kuɗinsa naji dama kuɗin ya bani na siyawa "yan gidanmu gidan zama , shi turaren ba kaya yana a jikinki kake shafawa ba , sargafe kayan akeyi saman wani abu sai a riƙe ta inda turaren ke fita cikin hannun haggu ana zungurashi da hannun dama turaren yana fitowa , tou idan wani yana wurin akayi feshin shi kanshi turaren saiya bi kayanshi da jikinshi , idan kuma aka sakashi a jikin kaya ko an wanke ƙamshin baya fita kuma haka ƙamshin zai kama jikin wanda ya saka kayan.

Alhaji idan kuɗin nan sun haɗu ka kawomin dan zanba yaran da zasu tayani aiki wani abu a ciki yau nake so na kashe yarinyar nan gata nan na kamota , Bello ne kwance saman kujera ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya yana magana da Dady a waya ,

Dady yace kuÉ—i sun haÉ—u kana ina ne kaida yarinyar ? Bello yace ina sabon gidan bayan sabon gidan sarki ai ka gane gidana da nake gini ban gama ba ko ? Dady yace Eh Bello yace to ya taho da kuÉ—i ka É—auki gawar Sultana , Dady yace gani nan zuwa ya tsinke wayarshi.

Bello kallon yaranshi yayi yace yana zuwa sai ku rufeshi da duka harsai ya mutu mu kuma mu É—auki kuÉ—in saimu gudu ,

Shi kuma Dady yana gama waya da Bello ya kira "yan sanda cewa a bashi jami'ai cikin kayan gida su biyoshi dan zuwa inda wani ya kashe wata yarinya , bayan ya gama waya da polisawa yace haba Bello tunda dai burinka ganin bayana nine nan zan ga bayanka a banza a wofi dani kake zance ko ka manta waye ni ? Muke da gwamnati mu'ahhukuma hannunka dumu² a kisan Sultana "yan sanda na kama sai su kashe ka , Sultana ta mutu Bello ya mutu damuwa ya ƙare.....

Kukan motocin Dikko na jiyo suna shigowa wani irin kuka sukeyi suuuuuu ba ƙara sukeyi ba cikin laushi suke kuka suuuu ina lissafi a zuciyata saida mota biyar ta shigo , wani irin farin ciki naji a zuciyata a bayyane kuma nace barka da zuwa mutumina , a ƙagare na saka hijabi nayi waje cikin jin daɗi.

A harabar gida su Ashiru sun wasu kuma sun hana shiga ko fita harsai mai gidansu ya gama abinda yakeyi ya tafi ikon mallaka kenan , wani ne ya buɗe min mota na shiga inda Dikko ke zaune yana ta soɓaro baki cikin sakata , ina shiga ya rufe murfin motar , kallon Dikko nayi cikin jin daɗi tattare da shauƙin so , ɗan kauda kanshi yayi gefe yayi kyau sosai a cikin ƙananan kaya amma idonshi ya faɗa ma'ana yaɗanyi rama ,

Murmushi nayi tare da cewa kayi kyau Dikko , ba tare daya kalleni ba yace ngode An matana ya ƙarasa maganar yana murmushi tare da ɗaga girarashin duka amma bai kalleni ba , sai yayi shiru , ni kuma na sake cewa baka da lafiya ne ? Lafiyana qalau yayi maganar yana duba wayarshi , to kayi shiru ina magana kana kallon waya ,

Ey amma kuma kallon wayana bai hana naji abinda kike cewa , Dikko na faɗa maka , kin faɗamin zakiyi aure kin cire hotona a d pn ki , na sani ai , kayi haƙuri haka Allah ya tsara , ajiye wayar yayi tsakanin ni dashi ya juyo yana kallona yace ku mata kullum tunanin ku ɗaya ne , daga aure sai ku haihu bakwa gina rayuwar zaman auren da soyayyar junanku , bata yuwu kawai magini ya fara gino katanga daga sama baza ta zauna ba saboda a saman iska yake ta ɗora buloluwanshi , ni kuma ta ƙasa na fara nawa nayi foundation mai kyau bayan na zuba masa siminti tsaƙƙuwa da yashi na bi a hankali na ɗora buloluwa na da ko wace daƙiƙa cikin salon iya gini , na bashi ruwa katanga ya zauna dai² da dai² cif da cif faɗamin taya wannan katangar za'a iya ɗauketa a sake mata wurin zama ne ? Sai a sauke bololuwan ai , bulo dubu ne Dikko ya jera taya zasu sauko duka ba tare da wani ya roshe ba ? Kallon shi nayi cewa aiko wasu sun roshe dole a samu rayayyu , bulo dubu ne aka cire kuma ana so a sakeyin irin katangar da ake so a sake ma wurin zama shin gini zai kai kamar waccan da wurin cire bulo wasu suka rushe ?

Sai ayi dashi da fasassun , taya zasu zauna bayan babu dashi a cikin wacce aka rushe , sai a siyo sabo a ɗora , taya za'a haɗa sabon bulo da tsoho ? Ai gini dai ake buƙata abinda tsohon ya bada sabo zai bada irinshi , bolo ina 9incis ne sai akaje siye sai suka ce babu 9 sai 6 , sai insa su bugamin wani inci 9 idan aka samun banbancin siminti fa , wancan yaji suminti sabon kuma yashi yayi yawa...........? Sai ayi filester , ai bana buƙatar filester An mata wato kina tunanin zaki iya rusa soyayya ta ki gina ta Sultan akan tawa ko ?

Ai idan kayi tunani da babu kai zuwa kayi , tabbas babu ni zuwa nayi kuma nazo kenan bana tafiya , Sultan zaizo yayi ta gininshi a saman iska ne domin nasan zuciyarki ta gama ginuwa da soyayyar Dikko rabaki dani a halin yanzu tamkar raba bawa da mutuwa ne , kinkuwa ga abinda baya yuwuwa ne duk wanda yazo saiya koma idan har kina ganin baki mutuwa to na yadda soyayyana zai goge a zuciyarki yarinyar kirki kawai kin shigemin zuciya yayi maganar yana sauke gilashin gefenshi saboda Ashiru yana magana ,

Mai gida wai wani daga ciki akace zai shigo yana ƙofar gida , Dikko yace a , a ya bawa Ashiru ansa yana ɗage glass in , nace kaji mulkin mallaka gidan ubanshi ne fa , ai ni kuma katsinar gaba ɗayanta a hannunmu take ko ina namu ne , banda nan dai ke yarinya shima nan ɗin nawa ne idan kuma kince a , a yanzu in nuna miki ki gani ,

Shiru nayi shi kuma yaci gaba da rattafo kalamai masu girma zuwa zuciyata kaina kwalwata da tunani na , yaci gaba da ginawa kamar yadda yace , karatunshi mai wahar gogewa ne , kalamanshi na da daɗi , soyayyarshi tana da girma , yaci uwar awa biyu yana ɗorani a inda bana iya saukowa , saida ya tabbatar na hawo sosai yace inje zaizo anjima idan Sultan ya tafi , saida na rungumeshi na fita , shidai baya san yana taɓani kona rungumshi zai ƙyaleni saina sauka a jikinshi da kaina , ɗan gayun namiji kenan ga kyau ga tsafta ga wanka ga ƙamshi saboda yawan wankanshi idan ka taɓa jikinshi sai kaji wani irin laushi kamar ka taɓa bayan zomo , ina nan tsaye har suka fita jikina sai ƙamshin shi yakeyi gaskiya Dikko na daban ne.

Saida motocinsu suka ɓace daga wurin ko ɓushi²n ƙurarsu babu sannan motar Sultan ta shigo......

31/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA...* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 68

Wuri ya samu yayi parking ya fito a nutse yana murmushi , hannu ya fara bawa mutane suna gaisawa duk wani ma'aikaci dake wurin saida Sultan ya miƙa mishi hannu suka gaisa cikin sakin fuska , shima dai wankakken matashi ne wanda shekarun shi bazai wuce kamar na Dikko ba ,

Wurina ya nufo yana murmushi , nima murmushin nayi masa cewa takwarana barka da zuwa , da yawwa ya ansa yayi gaba nabi bayanshi muka shiga ciki , a palo muka samu Kaka gaba É—ayanmu wuri muka samu muka zauna , bayan mun zaune Sultan ya gaishe ta , ta ansa cikin sakin fuska da É—an barkwancin hakan nan dai.

Fira sukaci gaba dayi da Kaka ni kuma na miƙe nayi ɗakina , ina zuwa alwallah nayi na gabatar da sallah azahar bayan na gama naci gaba sabgogin gabana a cikin ɗakina , kayan da Yazeed ya kawomin na buɗe ina gani , wanda sukafi burgeni suka tafi da tunani na fara zamewa gefe ɗaya zan kai ɗinki.

Ina ta ciccire kayan ne Sultan ya shigo , kamar ya saba dani ya duƙa wurin kaya shima yana fiddowa yake tambayana me za'ayi dasu ne ? Ina murmushi nace ɗinki zankai na taɓa wanda zankai ɗinki da hannuna , ɗan murmushi yayi kaɗan ya fara ciro wasu daga cikin wanda na fitar zankai ɗinki yana cewa gaskiya wannan bama sanshi , tou wai har an kawo lefen ne ni ban sani ba .....?

Dariya nayi nace bafa lefe bane ba , dani dashi gaba É—ayanmu kallon juna mukayi lokaci É—aya , kyakkyawan murmushi yayi min yana cewa waye ya baki ? Wani ne ya kawomin , wayyo mun kuwa gode ya faÉ—i maganar yana komawa gefen gado ya zauna.

Sultana ya kira suna na , ba tare dana juyo ba nace na'am , Abba yace nazo na ganki na kuma gaisheki ni Abubakar Sadiq nake suna kirana Sultan ne sunan Baban Mami na ne , ina da mata É—aya yarana biyu , auren zumunci shine al'adar wannan ahali , amma ni aurena na farko banyi auren zumunchie ba saboda babu wacce zan aura a lokacin yaran duk basu girma ba ni kuma na tashi aure Abba yace inyi kawai daga baya idan yaran sun girma sai in kulle ta biyu da auren zumunchie , kin ganni na ganki ni kinmin a haka Allah yasa nayi miki.....?

Ba tare dana juyo ba nace Ey mana kamin ina sanka , amma fa ni karuwa ce shin zaka aura karuwa ? Yi yayi kamar baiji abinda nace ba yaci gaba da cewa Mami ta bada shawara a ɗaura aure sati mai zuwa sati na gaba kuma sai ayi shagalin biki , nace tou Allah yasa alkairi ya bamu zaman lafiya fita da sharrin dake ciki ubangiji ya kauda shi ya tsinkule idanuwan maƙiya , am3n Sultan ya ansa tare da miƙewa idan kin gama haɗa kayan ki sameni a waje sai in kaiki , na ansa da tou shi kuma ya fice...

Yana fita naci gaba da fiddawa bayan na gama haɗawa na zuba a lader na ɗauka na fita , a mota na samu Sultan na buɗe na shiga saida na zauna na rufe yace ina zamuje ne ? Nace masa goruba road , murmushi yayi tare da kallona yace kice dai amaryar tawa mai kuɗi ce goruba kike kai ɗinki ? Murmushi nayi ba tare da nayi magana ba , jinjina kai yayi bai sake magana ba ya taka mota muka fita daga gidan , muna fita wayarshi ta fara ringing ɗauka yayi banji abinda abokin wayar yace ba shidai yace zanje goruba ne , a , a kayi haƙuri don Allah jirani yanzu zan ajiyeta nazo don Allah , babu damuwa bara na fara zuwa tou yana faɗin haka ya ajiye waya , yana cewa yi haƙuri da Allah na anshi saƙo , babu damuwa na bashi ansa.

Hajiya wai bayan su Dad inmu shi Malam kafin ya mutu yana da wasu "ya "yane don Allah ? Hafsa ce zaune a gaban Kakarta take tambayarta shin ko Dad inta yana da wasu "yan uwane bayan wanda ita ta aifa da cikinta ? Hajiya dake kwance tana gab da ramin mutuwarta tace Hassatu me yasa kikai min wannan tambayar ne ?

Gyara zama Hafsa tayi cewa ba komai kawai dai ina so na sani ne , cikin yanayin wahaltuwa ta majiyyacci Hajiya tace yana da yara biyu amma basa tare damu a halin yanzu ? Hajiya suna ina ne haka ? Fashewa da kuka Hajiya tayi cikin kuka take cewa haƙiƙa ita rayuwa taƙaitacciya ce kuma ƙarewa takeyi ba tare da tayi shawara dakai ba , duniya da komai zaka ajiye kaje ga Allah , babu wanda yazo da arziƙi kuma babu wanda zai koma dashi , ruɗin duniya da shaiɗan yasa na tabka kuren da bashi da gyara kuma rayuwa ta riga ta ƙuremin , cikin kuka sosai taci gaba da cewa yau da zanga Aliyu da ɗan uwanshi dana roƙi gafararsu su yafemin , ni nake kwance ina ciwo amma duk lokacin dana kwanta da sunan bacci sai nayi mafarkin ina faɗawa cikin wani irin tsukakken rami kuma wuta yake ci a cikin sa ,

Hassatu duk arziƙin ka baka isa kayi ma wani arziƙi ba , haka kuma idan ubangiji ya arzurtaka kai bawa baka isa ka talauta wanda ubangiji ya azurta ba , kowa tsirara yazo babu wanda aka haifa da wando ko riga kowa haka ya faɗo kuma kowa haka zai koma daga shi sai likafanin shi , duk abinda kazo duniya ka tara kanaji kana kallo kana sanshi zaka tafi ka barshi magada suci gadonshi , ka bar musu dukiya sunajin daɗin duniya kwana kaɗan sun manta dakai sunci gaba da sharholiyar duniya sai ɗaiɗaiku a "ya "yan naka zasu riƙa tunawa dakai har ka samu suyi maka addu'a.

Haka take ga mace , idan mijinta ya kwanta ya mutu kuka na wani lokaci zatayi daga inda aka raba gado aka bata shikenan ta mance da shafinka a rayuwarta , ga dukiya ka mutu ka bar mata gidanka taci gadonshi tanajin giyar kuɗi yana motsa ta taci abinda ranta yake so tasha wanda take so idan za'a nemi shawararta a misali za'a ce mata Hajiya ko a dawo da Alhaji daga duniyar mutuwa cewa zatayi a , a , a ƙara kwaɓa ƙasa a zuba a saitin kanshi , bayan wasu watanni tayi takaba ta gama tuni ta manta dakai namiji zata samu ta aura kana lahira wani yana kwana a gidanka...

Idan kana da "ya "ya da ita kila idan tana da sauran imani ta kallesu ta tuna dakai , dan ba duka aka taru aka zama ɗaya ba , to ni ba auren nayi ba Hassatu dukiyar nake mawa wannan dalili yasa na fasa gidan na kora "ya "yan malam biyu suka shiga duniya yayin dana kashe uwarsu saboda san duniya kuma duk saboda "ya "yana nayi haka dan ina so suji daɗi kuma sufi na kowa , amma kaico duk wannan yaƙin da nayi Hassatu ubanki sai yayi ruf da ciki akan kaf wannan dukiya shi ya cinyeta duka ya hana "yan uwanshi komai nima mai yaƙin sisi bai bani ba duk abinda nace masa ina so , ko ya kawo abu ya ƙare sai yayi masifa sosai sannan ya ɗauko ya bani kamar zai dokeni. Ki gayamin ɗan da bai ma idonka ba bayan idonka zaiyi ne ? Hafsa tace a , a , murmushi mai ciwo Hajiya tayi sannan tace...

Ina da abiyar zama kuma tana girmamani sosai a matsayina na Yayarta a wurin miji , tana bani girma na yadda ya kamata ko aiki taga zanyi bata barina nayi idan har kika ga ina aiki tou lallai Maryam bata lafiya ne , kuma ko tana ciwo saita daure cikin ƙarfin hali tazo ta kamanin dan dai ta bani girmana da mutuntuwa na ina gaba da ita a gidan aure.

Tunda nake ban taɓa ganin ɓacin rain Maryam ba domin mace ce mai haƙuri kunya kawaici da kara , duk "ya "yana dana haifa bana musu wanka ko tsarkin kashi ko goyo duk Maryam take musu idan har kika ga ɗana a hannuna to wallahi nono yake sha kuma yana gamawa Maryam zata ɗaukeshi ta goye , wankina dana yarana duk itace take haɗawa tayi ,

Duk lokacin da Maryam ta samu ciki sai nayi yadda na lalata cikin nan ya zube nayi ta neman asiri karta aihu amma dake ubangiji yayi alƙawarin biyu sai sunzo duniya Allah ya bata Aliyu da Muhammadu , bana san yaran kwata² ina ta neman hanyar da zanyi na sabauta musu rayuwa dan bana san ace "ya "yana suna da "yan uba ba hangen wata irin ƙatuwar gona da Malam yake da ita tun a wancan lokacin an taya gonar naira dubu ɗari 3 da hamsin bana so ace an raba wannan kuɗi idan Malam ya mutu wasu su samu sai nawa kawai.

Wannan gona duk duniya itace kaɗai Malam ya mallaka bayan ita bashi da komai a duniya kuma gonar itama ba gadonta yayi ba , domin talauci ne ya isheshi shine ta fara harkar tsibbunci kuma Allah ya dafa mishi kasuwa ya buɗe yayi ma wani attajiri aiki da buƙata ya biya shine ya baya da gonar yace ya riƙa noma dan ya cida iyalinshi.

Haka Malam yaci gaba da aiki a ƙauye har manyan "yan siyasa suka ganoshi duk buƙatar da mutum yazo dashi insha Allah Malam yanayin aiki an dace , abinda ya maidomu garin Katsina wata yayi ma aiki tayi mishi kyautar gida muka tattaro muka dawo birni.

Muna dawowa liƙafa yaci gaba sosai a taƙaice dai Malam ya tara manyan kuɗi da ƙaddarori manyan gonaye a garin funtuwa gidaje a cikin gari , ganin kullum Malam yana ƙara ginuwa shine na nemi hanyar da zan kora Maryam , bayan nayi shawara da wata aminiyata itace ta bani shawara mutuwar Maryam shine kawai mafita , idan ba mutuwa tayi ba ko sun rabu da Malam itama zata saka ran zataci wani abu a dukiyar gadon fitina za'ayi sosai shafeta daga duniya shine kawai abinda ya kamata muyi , to itace ta rakani wurin wani boka yayi asiri ya haɗa Maryam da aljannu aka tura mata yace idan ta firgita tayi ƙara aljannin zaiyi tsalle yahau saman harshenta take a wurin zai zuƙe jininta shikenan an rufe littafinta , idan kuma ta kira sunan Allah aljanni bazai iya zuwa wurinta ba , haka kuwa akayi Maryam dai ta tafi.

Bayan mutuwar Maryam kuma nayi makircin da nasa Malam ya korasu Aliyu daga gidan nan , nayi tunanin idan suka tafi za'a sacesu dan nayi zaton kawai zasu halaka a duniya ne , da naji labarin basu ɓace ba shine nayi asirin da zasu manta da gida kwata² , kwatsam sai naji labari wani gida sun ɗaukesu suna zama dasu shine na faɗawa mahaifinki nace yasan yadda zaiyi da yaran nan dan a lokacin Malam ya rasu nace idan har hankin yaran nan ya dawo gida zasu buƙaci a basu gadonsu ,

Wannan dalili yasa Dady ya tura Bello ya shiga rayuwar Binna , saboda Bello baijin magana ko kaɗan iyayenshi ma kansu ji sukeyi dama basu haifi banzan ba , kuɗi Dady yake biyanshi kuma shine yace yana so Bello ya gurɓatawa Binna rayuwa yadda ko ya girma ya zama mara gulihu dan karya nemi kuɗi kuma yanaso Binna yayi wulaƙantacciyar rayuwa karya zama na gari dan baya so kwata² ya tuno da labarin gida , Bello da Dady sukayi ciniki Dady ya bashi rabin kuɗin aiki , shine Bello yayi asiri ya saka Binna ya fara caca shan giya neman mata da sauransu , wannan aikin duk na Dady ne Bello kuma ya biya mishi buƙatarshi , aikin Bello kuma shine ɗaukar fansa akan abinda Binna yayi mishi na ansar budurcin matarsa , Binna ya gudu shine Dady yace ba'a barin maƙiyi ya tafi ka dawo dashi wurinka yadda yayi maka kaima ka rama , shikenan Bello yaci gaba da jifar "ya "yan Binna da asiri...

Duk nice na kawo wannan shawarar amma Ubanki ba "yan uwanshi ba ni kaina sisi ya hana a kuɗin gadon nan , girgiza kai Hafsa tayi tare da cewa har nawa ne kuɗin gadon ? Hajiya tace zunzurutun kuɗi Malam yabar naira miliyan 45 gonaye da kuma gidaje , miƙewa Hafsa tayi tana shafa wayarta tace tou ƙalu bale ga rayuwarku domin ɗiyar Binna ta tiso ƙeyarku gaba dake da Dady ƙaryarku ta ƙare ba abinda ya shafeni kinga tafiya.......tana kaiwa nan ta fice daga gidan.

Da gudu Hafsa ta fita tana kuka innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu Baba Binna ƙanin Dady ne shine yayi iskanci dani......? Wani irin ihu tayi cewa na bani na lalace ni Hafsa ubana ya kwanta dani ya buɗemin jikinshi na gani , da sauri ta rufe idanuwanta ta dafe kanta , yauni na shiga 3 ni Hassatu na lalace Baba Binna Allah ya rufa maka asiri da baka raye yau da wane irin baƙin ciki zakaji idan har kasan ni ɗiyar ɗan uwanka ce ? Wayyo Allahna ƙanin ubana yayi iskanci dani kaico da wannan tsohuwa , tirr da halinki duk kece silar rushewar komai ni naga tsiraicin ƙanin ubana yaga na "yar sa Sultana kuma taga na Dady , itama ita da Dady kenan sunyi ? Tabbas sunyi shi yasa har ta ɗauko videon girmanshi ta turomin , kai mun shiga 3 mun lalace wani irin ihu ta kurmama tare da faɗuwa ƙasa somamiya.....

Kai anshi ka irga kuɗin , Bello yakeyin magana bayan yasa wani matashi ya anso jaka daga hannun Dady , buɗe jakar sukayi amma da mamaki sai suka ga wayam , ce ma Bello sukayi ai babu komai a ciki , ɗago kai yayi da niyar yima Dady magana Dady ya gaggaɓe da dariya yace kana wasa dani kenan ko ? Ai kace idan na kawo kuɗi saika sokamin wuƙa na mutu Bello ka cika tsarabarka da yaji ƙaryarka tasha ƙarya yau nine ajalinka hukuma zata kashe ka da hannunta bayan ta kamaka da hannu dumu² a kisan Sultana ,

Bello yace ai hukuma bazata kashe ni ba ta dalilin kisan Sultana saida ta kamani ta dalilin kisan ka , idan baka sani ba bara na faÉ—a ma tun daga ranar da kasa akayimin duka a ofishin "yan sanda duk wani abinda ya faru tsakanin ni dakai tun daga ranar dana fara zuwa wurin Binna ya É—aga wasu takaddu yace to ka sani yana rubuce anan ciki.....

Wannan gurzajjin ne amma na gaskiyar ya tafi zuwa hannunshi , duk halakkacin da nayi maka lokaci ɗaya kasa ƙafa ka shure saboda kai kanaji kana da hukuma a hannunka kai ɗan siyasa tou ka sani nawa siyasar yafi naka , dani dakai yarinyar da muka haifa tayi wasa da hankullanmu lokaci guda wurin ganin ta haɗa mana fitina ta yadda zamu fara muna farautar junanmu ,

Na ganota ne domin kirana da tayi da layin da ita kaɗai na kirata dashi cewa saina kasheta , na yadda da hakan da tayimin maganar ka ta kuma yimin maganar Sultana , tana tsaye ne a saman ƙafafuwanta wurin ganin taga bayanmu dukanmu gaba ɗaya daga ni har kai ,

Shi yasa tayi amfani da wasu sirrika data sani wanda kwalwarta da tunaninta ya bata , sai tayi amfani da wannan sirrinka wurin kirana tace kace kaza² kaima saita kiraka wanda haka yasa yanzu kazo min da jaka babu kuɗi.

Saboda ka yadda da cewa zan kashe ka ne yayin daka bani kuÉ—i domin tafiya da gawar Sultana , banzo da ita ba kuma ban kamota ba amma ina tare da duk wani motsi nata , ta fita daga gida bayan sallah azahar misalin 2:31 , wani ne ya É—auketa a mota bayan Dikko yaje gidansu ya fita kuma yasa an tare hanyar fita da shiga harsai ya gama magana da ita ya tafi ,

Mota mai lambar kaduna ta daɗe a ƙofar gidan sakamon hanata shiga da akayi cikin gidan , bayan kimanin awowi biyu da wasu mintuna Dikko ya fita daga gidan mota mai lambar kaduna ta shiga , ta daɗe motar sosai sannan ta fito daga cikin gidan bayan mai tuƙa motar ya fito ɗauke da Sultana ,

Yaje kasuwa central market ya anshi saƙo , daga nan ya wuce goruba road , yanzu haka tana goruba road j ta fita daga cikin mota ta shiga shagon ɗinki a halin yanzu tana cikin farin ciki shin zaka bayar da kuɗi na basu damar kasheta ko kuwa.....?

Dady yace takaddun da kake magana ka tura zuwa gareshi waye shi ? Bello yace Dikko ne nayi haka ne domin kuɓutar da tawa rayuwar shin zaka bada kuɗi nace su dawo dasu karsu isa wurinshi ? Har yanzu kana da sauran dama mutuwar Sultana ko kuma taka wace ce ka zaɓa.....?

Dady yace amma me yasa ka tura shedar takkadu wa Dikko ? Saboda shine mijinta kuma ya zama dole yasan duk wasu sirrika da yake ta faman bincike babu dare ba rana , na yanke kawai na rubuta komai na tura mishi ta hanyar ɓoye sunana amma na bayyana naka , abinda yasa kuwa nayi haka dan kayi min kuri da hukuma shi yasa na miƙa kaina ga hukumar gaba ɗaya ,

Kai.... Dady ya faɗa tare da nufa wurin Bello ta haɗashi da bango yace kana da hankali ne ko kayi hauka ne ? Dariya Bello yayi tare da cewa lafiyata garass amma ka sani matar da Mami ta turo ta ɗauki kwalbarnan munyi dukawa matar sosai ta samu ta kubce bayan mun bita bamu samu ganinta ta ɓace mana a cikin asibiti , taje ta ɓoye tayi jinyar sirri a wani wuri daban bayan ta samu sauƙi ta dawo ta duƙufa neman Sultana bata samu ganinta ba amma a bincikenta ta gano Sultana tana tare da DK shi yasa ta tafi wurinshi domin buɗe mishi duk wani ɓoyayyen sirri kenan kaga faɗan yazo ƙarshe , na kashe ko a kashe ni wannan shine muradina domin ni nasan ƙaryana yazo karshe kuma banda sauran dubara ko mafita tunda case ya koma hannun Dikko.........

Ka saki wuyana kawai kaje ka fara neman shedar da zaka kare kanka , 45miliyans sai aje ayi ÷ ÷ ɗinsu in to su Sultana........ Kowawa sukaci gaba dayi tsakanin Bello da Dady , dariya Bello keyi domin shi ƙarya yake ma Dady babu wani abinda ya rubuta akaima Dikko amma karuwarshi yaji labarin tana ta zuwa neman Dikko ba'a barinta ta ganshi , kuma yana ta farautar ta har yanzu basu haɗu ba , dan ƙawarta wacce ta bawa Sultana numberta tace zata kirata itace ta bata labarin yaran Dikko sun kamata sunyi mata tambayoyi kuma ɗiyar Binna tana nemanta , tace ta anshi number Sultana amma ta manta bata ajiyeta a wayarta ba , data tambayeta inda Sultana ke zama shine tace tana zaune wurin DK a goruba road...

Shi kuma Bello ya girgiza Dady ne dan ya anshi kuÉ—i a hannunshi amma kamar yadda yace duk wani motsin Sultana yana hannunshi tabbas yana tare dashi...

Saida suka gama cakuwa kowa ya saki kowa cikin wahala , saida Bello yayi nishin wahala yace kuma nine na tura yarinyar ka ta zama karuwar Binna , wani irin gumji Dady yayi da niyar riƙo Bello amma ya ruga da gudu ya hau mota ya nufi goruba road domin ganin bayan Sultana dan lokacin da boka ya ibar masa wa'adinsa ya cika , danshi baya iya auren uwarshi gara kawai ya kashe Sultana magana ce ta shari'a kawai ai tayi ana Sign daga ƙarshe ƙotu tacezaiyi gidan yari , Dady cikin ɓaci rai yace ma "yan sanda da yazo dasu suje zai sake nemansu ,

Hafsa kuwa mutane suka É—auketa suka mayar da ita cikin gidan Hajiya , aka yayyafawa banza ruwa ta dawo , tana dawowa taci gaba da ihu tana na bani na lalace... Gaskiya Hajiya ke sheÉ—aniya ce ta bada labari a jarida ina ahalin mahaifiyar shi Ba Binna......? Wato mahafiyar ita Maryam kakar ba Binna kenan wacce ta haifi mahaifiyarshi ina suke...............? Ta tambayi Hajiya yayin data sake tafiya zuwa duniyar suma.

Ina zaune a saman kujera shagon É—inki ana nunamin style Sultan yacemin bari yaje ya dawo kafin in gama zaiga wani abokinshi a road na gaba , fatan dawowa lafiya nayi mishi ya tafi ni kuma naci gaba da dubawa saboda tun farko nace nidai suymin basai na duba ba amma suka tursasani wai indai duba...

Bayan na gama zaɓa na miƙe ana auna ni juyowar da zanyi naji kaina ya sara sakamakon Bello dana gani tsaye ya raɓa ƙofa biyu yana kallona , wata irin mummunar faɗuwar gaba naji a dai² lokacin daya fara kwaikwayon muryata cewa kun haɗa kai akan zaku kashe wata yarinya amma shine naji yana cewa sai ya kashe ka , shigowa yayi cikin shagon yana cewa idan baki mata ba da kikayi wannan maganar ai dariya nayi miki , na baki ansa cewa ko wace daƙiƙa saƙo da lungu rana da dare neman sa'ar mutuwarsa nake saina kashe shi.

Hihihihihihi yayi dariyarshi ta raini wayau yace zakiyi tunanin banda lissafi shi yasa nayi wannan maganar ? Tou saboda kece kaɗai na siya layin nan , nine nan na kiraki nace saina kashe ki , yasa anata gadinki ya hanaki fita saboda baya so ki mutu shin yanzu yana ina ? Ko ya isa ya tseratar dake daga mutuwa ? Kin taɓajin labarin zafi da radaɗin azabar fita rai ? Hihihihihi ya sake dariya yace ai na manta yarinyar malama ce ba mamaki an baki labari a islamiya yayi maganar dai cikin yanayi na jahilci.

Saida ya sake dariya tare da tafa hannayenshi ya ɗora hannunshi a saman kunnenshi kamar yana waya da irin maganata zanzo fesra hotel sanye cikin hijabi da niƙaf napep zai saukeni idan ka isa ka kamani ka kasheni a wurin hihihihihihihihi ya ƙarasa maganar yanayin dariyarshi mai tada hankali sai kuma ya ɗaure lokaci guda yace a maimakon kizo sai kikayi wa Hafsa waya ke mai wayau kika rufzata a rami sai tazo saida ya sakeyin dariya ya fara matsowa inayin baya yaran shago kuwa rugawa sukayi suka fita daga cikin shagon lokacin da suka ga Bello ya fiddo wata irin shareriyar wuƙa daga cikin rigarshi yana cewa rana dubu na ɓarawo rana ɗaya cif shine na me kaya yau gani gaki bankwana da duniya , ya ɗaga wuƙarshi ya nufo dai² saitin zuciyata dashi...........

Yana cewa ba kin kirani cikin dare ba ni kuma na faɗa miki cewa zan kashe shi misalin 10 dai² na safiyar yau , kina tunanin ina cikin maye ko ? Tou kwalba biyar na shanye a daren amma kaina baya manta komai , idan kin isa barzahu lafiya kicewa Binna zanzo na yayyafawa kabarinshi giya kwalba biyu ta tayashi murnar isowar uwar masu gida wurinshi....

01/11/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 69

Hihihihihihi yayi wannan munafikar dariya da bana so , saitin wuyana ya ɗora wuƙar dai² maƙoshina lokaci guda na ɗauke numfashina zufa ta ketomin hawaye suka ci gaba da gangarowa nabi Bello da kallo , dariyar ya sakeyi tare da jan majina , yace kin tuna kika tuɓeni kika ɗaukeni video ? Ka turo da dubu ɗari biyar idan ba haka ba zan watsa su a yanar giza gizo , yayi irin magana na , dakel na haɗi yawun bakina cikin tsoro nace wai me kake so da rayuwata ne ?

Bana buƙatar komai a halin yanzu sai mutuwarki , bara in faɗa miki abinda kika kasa sani nine nan na kashe Binna da hannuna , kuma nine na toshe miki kwalwa na maidake kidahumar ƙarfi da yaji nine na haɗa Binna da Hafsa da Amisty suka zama karuwanshi , haka yake jerasu a layi ya hau akan ɗaya ya sauka ya hau ɗaya , nine nan na shirya komai ta yadda ya faɗa wasan caca shine kawai zai fita a caca nayi na mayar dashi ya ƙiya saboda kawai yayi miki alƙawari ya daina yaso ya lalatamin tsarina ne ni kuma kawai na kashe banza , to me Babana yayi maka haka da zafi ? Ke matar da nake so ya maida ita zawara a ranar da nake farin ciki zan shiga daga ciki , da farko na barshi ta tafi Yayan Babanki ya zugani na dawo dashi ni kuma na hura wutar ɗaukar fansa a zuciya , zan gama da matsalar Binna dake na koma wurin ɗayan ɗan iskan saina ƙare kaf ahalinku dan bana buƙatar ganin jinin Binna a saman doron ƙasa , kauda kaina nayi gefe ɗaya ina wani irin gumji nace kaine ka kashemin min Babana......? Nine na kashe shi ko in nuna miki irin zamiyar da kikayi a jikin gawarshi ne ? Yadda nayi ya nunamin kina cewa wayyo Babana karka ka tafi ka barni tashi Babana baza ka mutu ba gani nazo , buɗe idonka kar kayi bacci uwar masu gida wayyo Babana yi murmushi hihihihihi yasha majina jeki....... Ya faɗa tare da so kamin wuƙa a kafaɗata wanda ba haka yaso ba zuciyata ya saita kuma a samanta yaso wuƙar ya shiga...

Wani irin ihu nayi tare da haɗa hannayena wuri ɗaya 🙏🏻idona yana tsiyayyar da hawaye nace na roƙeka karka kasheni , wata "yar iskar rawa yayi da ƙugunshi yace ke kina tunanin zan barki ki rayu bayan nace miki nine na kashe Binna ? Cikin kuka nace ai banji ba , hihihihi yaja majina ƙazamin banza yace sai kin mutu......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.