Trending Hausa Novels

Kwarata Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Kwarata Complete.txt

Chapter 6 of 7

*_Shafin nan gaba ɗayanshi sadaukar wane ga masoyan DIKKO a duk in da kuke a faɗin duniya , DIKKO na gaishe ku , ni kuma JAMILA MUSA nake muku fatan alkairi ku kasance a farin ciki , ina gaisuwa gareku domin ni kune maudu'una , farin cikina , gishirin rayuwar littafin KWARATA..._* 🤝🏻

*_na kuma miƙo gaisuwa gareku_* 👇🏻

*AMINA UMAR* _{ Ummieter }_
*HANEEY* _{ MRS KB }_
*HAWWA MUSA*
*RABI MUSA*
*AUNTY MUSA*
*HAFSAT NASEER*
*FADEELA LAMIÆŠO*
*HAJIYA A' I QERAU*
*SAFINA ALIYU KAROFI*
*ASIYA ILU BARDE* { MMN SUDAIS }
&
*ZALIHA GAMBO RAÆŠÆŠA...*

A rayuwarka babu abinda ka sani sai zafin kai , doke² , ɗaure fuska gaka mahaukaci ga aljannu kamar iccen tsamiya ni taurin kai , kai kuma zuciya talauci da arziƙi basa zama wuri ɗaya dole idan ɗaya yazo to ɗaya zai tafi , hawaye ne ya gangaro daga cikin idon Dikko bayan ya tuno maganganun da An mata ta jefeshi dasu , murmushi mai yagar zuciya yayi tare da kallon kanshi a madubi yana mai sakeyin murmushi wanda har saida kyawawan haƙoransa suka bayyana.

Wai nine mahaukaci ? Duk dana faɗa miki lalurata amma shine kikemin gori wai aljannu kamar iccen tsamiya kwantar da fuskarshi yayi saman sitiyarin mota a bayyane yace bani ne na ɗorawa kaina ba ƙaddara ne kuma haka yazo rubuce a cikin ƙaddarar rayuwata , ɗago kanshi yayi yaci gaba da kallon gabanshi dan tuƙi yake kuma har yanzu baije inda zaije ba , yaci gaba da addu'a ya ubangiji ka bani lafiya ka yaye min wannan lalurar ka bani haƙurin rashin An mata , goge hawayen daya zobo mishi yayi yana ci gaba da cewa wai duk girmana ni nake kuka wa mace , macen ma An mata ashe dama bata so na , wani irin duka ya kaima sitiyari a hayaniyance yace ni kika yaudara ? Nidai kika yaudara bazan taɓa yafe miki ba An mata kuma Allah bazai barki ba saiya min sakkayya ya ƙarasa maganar hawaye na rigangato wurin fitowa daga cikin kwarin idanuwan shi.

Har ya isa goruba ranshi a ɓace addu'arshi ɗaya Allah yasa kada wani ya hawoshi a dai² wannan lokacin da yake cikin ɓacin rai dan duk wanda yazo yana cikin wannan yanayi zafa a samu matsala , aljannu kamar iccen tsamiya ya maimaita a dai² lokacin da yayi parking , yanayin parking Yazeed ya fara gani ,

Fita yayi daga motar cikin tsananin ɓacin rai fuskar nan a haɗe , Yazeed yana ganin Dikko ya taso cikin girmamawa ya miƙawa Dikko hannu , bai anshi hannu ba yace ya akayi ? Cikin rawar murya Yazeed yace DK don Allah wani abokina ne aka kama wata ƙawarshi ta gayyaceshi zuwa gidanta sai mijin ya dawo ya ritsatsu dan Allah kayi magana yana sabon gari police station ,

Wani irin munafikin kallo Dikko yayi ma Yazeed , a hanzar ce Yazeed yaja baya yana kallon Dikko , tsoki Dikkon yayi ya fara tafiya Yazeed yabi bayanshi Dikko kuma yana magana cewe , baku da aiki kullum an kamaku wurin neman mata , nima yau an kamani na kasa fitowa , banyi maganin damuwa na bare inyi ma wani nashi , ina cikin ɓacin rai ka kama gabanka tun kafin in fara ƙwallo dakai....

DK ka duba lamarin nan don girman Allah kayi wani abu akai matsalar babbace , da sauri ya juyo yace kai........... Ka wuce fa , ganin idanuwan Dikko ba'a launin daya saba ganinsu ba yasashi juyowa da sauri ya dawo baya yana tunanin halin da abokinshi yake ciki.

Matsala ce ta neman duniya shi abokin nashi yana da wata buƙata akan wasu harkokin shi nayau da kullum shine malaminshi yace sai ya samo maniyin matar aure kuma saiya nemi matar a gidan aurenta a saman gadon da mijinta yake kwanciya da ita , a jikin hankicif kawai ake so a gogo sperm in shikenan zance ya ƙare , amma zai dawo zuwa anjima idan Dikko ya sauko , zuciyarshi tace a , a kawai kaje wurin Sultana a gabanka zatayi masa waya a wuce da damuwar nan , kai tsaye Yazeed gidansu Sultana ya nufo !

A halin yanzu zuciyata ta cika fal da Dikko , muradina shine naga na haɗu dashi maganar gaskiya so nake na kasance dashi domin inajin Dikko kamar wata runduna ta tsagin rayuwata idan har na bari Dikko ya tafi na shiga3 na tawa ta ƙare , fashewa nayi da wani irin kuka a toilet nace ina sanka ׳ mutumina.....

Sai ihu nakeyi a toilet babu mai jina saboda gidanmu cike yake da mutane "yan kawo lefe , kuma gashi gobe idan Allah ya kaimu É—aurin aurena wanda za'a É—aura 2:00pm idan Allah ya kaimu , saida nasha kukana har na gode Allah na fito daga toilet ko mai ban shafa ba na saka kayana , wayata na É—auka na fara kiran wayar Dikko ,

Ɗauka yayi amma baiyi magana ba , cikin kuka nace Dikko gobe ne fa ɗaurin aurena , Ey ai kin faɗamin jiya da daddare ko kin manta , a , a ban manta ba ƙara tuna maka nayi fa , ina sane ban manta ba , to baza kayi wani abu ba ? Wani abu kamar me ? Shiru nayi ina kuka na kasa magana , Dikko yace Allah yasa alkairi ya baku zaman lafiya ina tayaki murna sosai yana faɗin haka ya tsinke wayarshi....

Wani irin ihu nayi wanda ya jawo hankalin duk wanda ke cikin gidan sukayo ɗaki wurina kowa yana tambayata lafiya ? Kamar baƙuwar mutane haka naci gaba da kallon mutane ɗaya bayan ɗaya cewa ya akayi ne ? Munji kina kuka ne , murmushin ƙarfin hali nayi cewa ba komai ni ba kuka nake ba wani abu ne ya faɗamin a ido , kowa Allah ya sawaƙe yayimin sannan suka fita.

Hijabi na saka na fita wurin Sultan dana baro a mota yana zaman jirana , dakel na ƙaƙaro farin ciki na isa wurinshi amma yanzu ban shiga motar ba a waje na tsaya , ki shigo mana , a , a , haka yayimin , bawan Allah ko murmushi baya gajiya dashi yace kodai naje na barki ki huta ne ? Cike da zumuɗi nace Eh , tada motar yayi yana cewa zan anso miki kayanki kinsan jiya mukayi dasu , godiya nayi masa tare da mishi addu'a Allah ya tsare hanya dan na matsu ya tafi wurin Dikko nake so naje , ina tsaye a wuri harya fita daga gidan yana fita motar Yazeed yana shigowa .{{{}}}

Inda Sultan ya É—auke motarshi a wurin Yazeed ya ajiye nashi tare da sauke gilashin gefenshi An mata wurinki nazo , ai na sani tunda na ganka gidan nan dama nasan saboda nine kazo , to dan Allah ki shigo wani wuri zamuje muyi magana naga gidanku cike da mutane , babu wani jayayya ko tambayar ina zamuje na zagaya na buÉ—e mota na kame a gaba Yazeed yaja muka bar gidanmu!

Iyalin Dady suna cikin tashin hankali da damuwa dan tun jiya suke neman Dady babu shi ba labarinshi kuma wayayonshi duk a kashe suke , saƙo da lungu nemanshi ake amma babu wanda yaji ko ɓirɓishin inda yake , cikin kuka Momy tace saika tafi ka saƙe duk ka tashi hankalinmu ? Ka tafi babu bankwana shin wai kana ina ne ?

Wani irin gumji Dady keyi bayan an ɓanɓare Dikko dakel daga jikinshi yace baza ku faɗamin gaskiya ba ko ? Bello da wahala tasashi ya koma wata siffa daban tsakanin ranar daya yayyanki Sultana da wuƙa zuwa yau yace ranka ya daɗe wallahi shine yasa ni , yayin da shi kuma Dadyn yake cewa ƙarya Bello ke masa shine Dikko ranshi ya ɓaci yacicci ubansu yana cewa bazasu faɗa masa gaskiya ba suna masa wasa daa hankali ko ? Ya ƙarasa maganar yana ƙara kaiwa Bello halbi a baki.

Cikin kuka Bello yace wallahi bani bane shine , Dady yace wallahi ƙarya yakemin shine tunda shi ka kama da wuƙa kuma shi idonka ya gani ya yayyaka mata a jiki ni misali idan ma har zanyi kisa zan faɗawa wani ne ? Koshi sakaraine baisan shari'a ba ? Me yasa da nace yaje ya kashe ta baije ya faɗawa hukuma ba ? Ko zan hura wuta nace masa ya shiga yaje ya faɗa ? Idan har ka duba wannan abun kasan duk ƙarya ne sharri kawai yake nemana dashi bansan abinda nayi masa ba !

Bello ganin Dikko yaɗan so karɓar uzirin Dady yasa yace to ranka ya daɗe tunda naga kanshi ya sani baisan nawa ba kuma naga yana ƙoƙarin fita ni ya barni a ruwa bara na buɗe maka gaskiyar abun yadda shike....

Labari tiryan² Bello ya zayyanawa Dikko kuma ya ƙara da cewa kuma kwalbar da ita matar taje ta ɗauko yanzu haka tana hannun shi , wani irin ihu Dikko yayi yace saina kashe ku.............. Wayyo , wai...... Wai , wai Allahna , kai........... Wai , saina kashe ku wallahi kaine ka mayar min da matata daƙiƙiya ko ? Zai fara duka su Ashiru suka danneshi ƙasa dakel saboda ai har yanzu akwai munafirci a maganarsu abinda su suka fahimta kenan , ya akayi kwalbar ta dawo hannun Bello bayan shi yace wata tazo ta ɗauki kwalbar kuma an bada ita wa wani malami ? Shi malamin ya akayi yasan Bello kuma ya bashi kwalba ? Dole bazasu bar akashe su Bello ba Sultana ya kamata a nemo kuma a nemo inda matar data ɗauko kwalba take , bayan ankai Dikko ƙasa Ashiru ya koma mota da gudu ya ɗauko magani har yanzu Dikko zubar da yaranshi yake duk girmansu duk ƙarfinsu tuni tsoro yasa Dady suma shiko Bello yayi fitsari baisan adadi ba , sunga bala'e da masifar daya girmi nasu , dakel aka sake kai Dikko ƙasa aka zuba mishi magani dole tasa ya ɗauke....

Fiddoshi sukayi suka kaishi mota aka sake kulle su Bello sai mai gida ya dawo , Bello kuma maimaita kalmar matata kawai yakeyi , har yaushe Dikko ya auri uwar masu gida ? Lallai akwai bala'e É—iyar Binna zata zama matar É—an gwamna ? Surukar gwamna ? Sam wallahi abinda bazai yuwu ba kenan an É—aura auren ko kuwa ? Wannan ansar ita ya kamata na fara sani farko kenan ,

Kwance zariyar wandon shi yayi ya matsa kusa Dady yayi masa fitsari a fuska , nan take ya farko , ɗaure wando yayi yana cewa zaune fa bata ƙare ba matarka ba ƙawar matar gwamna bace ba ? Cikin jin haushi Dady ya tashi ya kama Bello da kokowa yana cewa ni zaka zubawa fitsari ? Bello yace kai da Allah dan ka farfarɗo akwai sauran rina a kaba fa , saida suka caku suka rabu da kansu , cikin wahaltuwa Bello yace kaji wani aikin kuma ko ? Tou idan baka sani ba ɗiyar Binna ta zama matar ɗan gwamna ,

Da sauri Dady yasa hannunwan shi biyu ya goge fuskarshi tare da yarfarwa , yace aure ? Ta auri Dikko ? Yayi maganar yana fiddo duk girman idanuwanshi , Bello yace ba kana can ka suma ba yace matata kuka mayar min daƙiƙiya yace duk saiya kashe mu , Dady yace sam ba'ayi aure ba , Bello yace idan ba'ayi ba kenan ai zaice budurwarshi , tunda kuma anyi sai yace matata , Dady yace idan anyi auren nan saina rabashi idan kuma ba'a ɗaurashi ba babu ubanda ya isa ya daurashi duk cikar faɗin birnin garin katsina....

An mata kin fito da wayarki ? Yazeed ne yake tambayar Sultana ko wayarta yana hannunta bayan ya samu ƙofar wani gida yayi parking , E na fito da wayata na bashi amsa , An mata dan Allah ki kira DK kice masa yayi waya a sakar min abokina , daga ina za'a sakeshi ne ? Yana sabon gari police station kamashi akayi , laifin me yayi aka kamashi ? Gonar wani ya aura kuma ya samu damar tattare kaf amfanin gona , to ya akayi harya tsaya aka kamashi ? Yankin ya shiga ba ita matar tazo nashi yankin , kaima Yazeed wannan ai ganganci ne , Eh An mata amma dan Allah kiyi ma DK magana yasa a sakeshi , murmushi nayi mai ciwo nace Yazeed zanyi masa amma me yasa wai suke san fasiƙanci da matan aure ne ?

Mafi yawancin matan auren sune suke miƙa kansu wa mazajen waje ta hanyar ɓoye kawunansu su masu aure ne , kowa da irin matsalar dake shigar da ita bariki da aurenta , wasu rashi ne na talaucin abinda zasu ci ko sha , wasu kuma rashin basa samun gamsuwa ne wurin mazajensu , wata kuma tana da komai babu abinda ta nema ta rasa kawai ra'ayi ne ,

Tou su mazan me yake sa suna neman matan waje bayan ga nasu matayen a gida , gyara zama Yazeed yayi cewa mafi yawan mazan waje masu neman matan aure suna nemansu ne saboda matsalolin matansu na gida , wasu kuma suna neman matan aure ne saboda neman wani abu na samun duniya , me yasa dole sai a matan aure ake san samu ne ? Duba girman aure kuma ki tuno daraja wacce Allah yayi masa duk wanda ya ɓata matsayi da darajar aure ya halaka , nidai kira DK a fiddoshi , kayi haƙuri Yazeed gaskiya ni halin yanzu bana tare da Dikko , me yasa ? Haka nan na fita daga rayuwarshi ne dan ina so nima ya fita tawa rayuwar , wai miye tsakaninku ne ? Murmushi nayi a zuciyata nace anzo wurin , kallon Yazeed nayi cewa to kai a naka tunanin meye tsakaninmu ?

Wata "yar munafikar dariya yayi yana cewa muje kawai na maida ke gida yanzu banda lokacin magana dan hankalina baya kwance amma zamuyi magana daga baya , yayi maganar yana taka motar muka tafi , saida muka isa gida sannan mukayi magana dukanmu , Yazeed yace zai kawomin wata ƙawarshi matar aure ce amma tana wasan danbe , kinsan miye danbe ? Ya tambayeni ? Nace masa a , a , Yazeed yace aiko yadda kike hakan nan kika shiga harkar danbe abin zai miki daɗi zaki taka matakai masu girma zaki fito duniya zata sanki kuma sai kinfi ƙarfi DK wallahi ,

Murmushi nayi tare da cewa in banda abinka taya zan iya raba fili inyi wasan danbe da ƙatti majiya ƙarfi ne ? Murmushi Yazeed yayi cewa ba irin waccan danben ba , kawai kidai kije zan turota tayi miki bayanin yadda danben yake , fita nayi daga motar ina cewa Allah yasa tazo lafiya , da amin ya ansa ya fita gidan da gudu lallai yana tare da damuwa , bin bayan motar Yazeed nayi da kallo nace ɗan raini kenan kamar yadda nake kallon kaina a madubi haka nake kallon inda ka nufa , murmushi nayi tare da tinkarar hanyar shiga cikin gida da sauri.

Ina shiga palo Inna na fara gani ta kame saman kujera an wani waye an goge ta fito cikakkiyar hajiya ga haƙorin makka tasha kuma wallahi yayi mata kyau sosai , da gudu na ruga na rungumeta na fashe da kuka , cikin jin kunya take ƙoƙarin rabani da jikinta tana kallon idanuwan mutane ita a dole sai tayi alkunya irin tasu ta fulani , ke saukar min a jiki cikin kuka na sauka ina kamo hannunta cewa Inna zo kiji , da yanayin tausayi ta kalleni ta taso kuma ta biyoni , ɗakina muka shiga muna shiga na rufe ƙofa na sake ɓarkewa da kuka nace Inna nidai tsakani da Allah bana san auren nan.....

Cikin tashin hankali ta kalleni tace Sultana ki rufamin asiri wannan maganar ma ki barta tun farko , ni gaskiya bazan barta kawai kice wani abu na rantse da Allah bana aurenshi nidai bana sansa kawai biyayya nayi ma Kawu nayi tunanin zaicemin ko ina da wani da nakeso amma sai bai tambayeni ba , Inna tace aiko dai ko zaki mutu wallahi auren nan babu fashi ni zaki tona ma asiri dan ubanki , kinsan bakya sansa uban wa yace tun farko kika amsa musu , bakisan halin mutanen ba kina wasa da sha'aninsu ko ?

Cikin hayani nace nima kina wasa da nawa sha'anin bari in fita na faɗa musu bana san Sultan , Sultan in banza Sultan in wofi , wani irin wawan mari Inna tayimin , kamar zan hau bori nace wallahi bana auren Sultan saidai ki kasheni , to na yadda saidai ko ki mutun , aiko bana mutuwa zanje na faɗa musu bana san Sultan tunda ni ba tsoronsu nakeji ba na tunkari hanyar fita zan buɗe ƙofar ɗakin , fizgoni tayi ta maidani saman gado ita kuma cikin damuwa ta buɗe ɗakin ta fita ta kulle da makulli ta waje , da gudu na sauka daga gado naje jikin ƙofar naci gaba duka ina cewa bana so ׳ wallahi ,

Inna kuwa palo ta koma ta ɗauki wayarta ta kira Dikko , yana ɗauka ta fita waje bayan sun gaisa tace da Allah na dawo kazo ina san ganinka idan baka komai , lafiya dai Mama ? Ya tambayeta , gaskiya ba lafiya Sultana tana so ta sake tado min wata fitina da "yan uwana , bayan an tsayar da ranar aurenta duk kwanakin da suka wuce batace ta fasa ba saboda Allah saida taga gobe²n nan ɗaurin aurenta Dikko tace ta fasa ? Na rasa ya zanyi duniya Allah yayi ma Sultana taurin kai , murmushi Dikko yayi tare da cewa me ne ne matsalar ? Nidai kazo yanzu²n , zanzo idan anyi isha'e , a , a Dikko yanzu dai , gani nan zuwa........

Cikin ƙanƙanin lokaci Dikko ya iso Inna tayi masa jagora har ɗakina , Dikko yana da raini tsabar rainin shi duk mutanen dake palon ko ɗaya babu wadda Dikko ya gaishe da , haka ya wuto su yana musu kallon ƙyankyanmi fuskar nan haɗe kamar hadarin tsakar dare har ɗakina , ina kwance saman gado ina ta kuka dan na gaji da bugun ƙofa har na koma na kwanta.

Bayan sun shigo ne naji Inna tace ina zuwa ta fita , shi kuma ya shigo cikin ɗakin har bakin gadona kuma bai cire takalmin ƙafarshi , kallo ɗaya nayi masa na juya mishi baya naci gaba da kuka , jawoni yayi daga saman gadon na fizge na koma na kwanta , cikin rarrashi yace zo inji waye ya taɓamin An matana ? Taho ya miƙo hannunshi , saukowa nayi daga saman gado naje kusa dashi na tsaya , kallona yayi sosai sannan ya kamo hannuna na dama ya ɗora saman kafaɗarshi ya riƙe tsakiyar bayana yace kallarni yayi maganar yana murmushi , kallonshi nayi ina kuka , wai me ne ne ? Dikko ya tambayeni , kwanciya nayi saman ƙirjinshi nace bana sansa , ke yar raini bana so kinaji na ? Kinga zaki tayar da hankalin Mama kiyi haƙuri kinji jaruma ta ?

Dikko nidai bana sansa don Allah nayi maganar cikin kuka sosai ina mai ɗagowa na kalleshi , ƙarya kikeyi da bakinki kika faɗamin kina sansa kuma na tambayeki yayi miki kika ce min yayi sai yanzu kice kin fasa ? Baya yuwuwa wallahi duk wanda ya tsaya miki sai an ɗaura auren nan kuma babu gudu babu ja da baya , wallahi ko na tafi kika sake cewa bakiyin auren nan zanzo in tafi dake goruba jawoni yayi a jikinshi sosai sannan ya shafa bayana da lallausar hannushi yana cewa zakiji a jikinki , da sauri ya ɗagani jikinshi jin ana shigowa.

A dai² lokacin da Inna ta shigo tana ta faɗa cewa ai dama nasan duk yadda akayi Sultana tana da maziga ashe wai wani tsinan yaro ne ɗan mara mutunci take tare dashi , kusa dani ta matso ta yayyanka min mari tana cewa meya haɗaki da Dikko ɗan iska yaron da baya ganin kowa da mutunci garin nan , ke banda kike jaka marar tunani duk wulaƙanci da tozarcin da Dikko yayi muku kin manta ? Tou idan kin manta ki tuna saida Dikko ya haramta muku mazaunin gida , gararin rayuwa wane ne bakuyi ba sanadin shi ? Ki rasa abokin tarayya sai mutumin da silarshi kika yanki tikitin shiga karuwanci , sassauta murya tayi cewa ban san Dikko na tsaneshi matsashi mai ɗagawa da baisan darajar kowa ba , yau da zanga Dikko dasai na ɗauki wuƙa na soka mishi a ciki ya mutu tsabar wutar ƙiyayyar shi dake ci a cikin zuciyata ,

Kin samu za'a rufa miki asiri wawiyar banza a aureki amma da yake ke jakace har kike tunanin zaki ce kin fasa idan banda ma Allah yasa Sultan ɗin mai imani ne an faɗa miki zai iya aurenki ne ? Tou Allah ya rufa miki asiri ma yaso ki a haka da duk katsina kin rasa mijin aure , wayata taje ta ɗauko ta kawo ma Dikko tace ka duba cikin wayar ka ganomin lambar ɗan gwamnan ka kirashi yanzu²n nan ka rabashi da Sultana...

Daga ni har Dikko kallan kallo muke ma juna , cikin jarumta Dikko yace Mama ke baki san Dikko ba ? Ina fa zanso sanin lalataccen yaron nan , to amma waye yace miki yana tare da ya nuna ni , Sultan yake faÉ—amin yanzu yace ko rashin lafiyar da tayi Dikko shine yake kwana da ita kirawoshi....

Kallona Dikko yayi sannan ya kalli Inna yace ai ba buƙatar kiran shi , me yasa ne ? Inji Inna , saboda Dikko tuni yazo , yana ina ne ? Nine *DIKKO* kuma nine *DIKKOn* da kike nema........... Gani nazo!

04/10/2019 👇🏻

*JAMILA MUSA...* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 71

*_Don Allah nidai ina roƙon alfarma wa mutanen da suke ɗaukar tsohon page ina suna saka mishi sabuwar number , abinda nake nufi misali sai a ɗauki page 1 a saka masa page 2 bayan ba labarin bane ba tou na roƙeki maimin haka dan darajar fiyayyen halitta S. A. W ki daina bana san haka idan Annabin ya isa dake ba danni ba._*

*_Attention , labari mara daɗi daya riskeni kusan kwana biyu da suka wuce bana san yawan ƙorafe² a jikin pages ina amma yau dole tasa ni sai nayi magana , cikakken suna na shine JAMILA MUSA , kuma ni haifaffiyar KATSINA ce iyayena da komai nawa yana katsina masoyana ku saurara kuji , yake "yar uwa me amfani da suna na kina maula to kiji tsoron Allah domin ko ba komai ƙarya haramunne inji manzan Allah S. A. W bazan ja miki Allah ya isa ba amma dai kituna zaki mutu kuma nima zan mutu dani dake duk zamu haɗu gaban Allah SW , bani bace nake waya daku cewa ku turomin kuɗi zan siya data zan yi kaza² ni JAMILA MUSA bani bace ba ƙarya ne kuma ƙarya take da suna na tana ansar kuɗaɗe a hannunku dan haka kuyi karatun tanatsu domin da kuɗin nake buƙata a hannunku bazan roƙeku ba sadai na siyar da littafin amma ba komai nasan ƙauna ne yasa yasa kuke bayarwa amma daga yanzu duk wacce tace muku itace JAMILA MUSA ƙarya takeyi 07016--78 shine farkon da kuma ƙarshen number na ngode sosai masoyana ina muku fatan alkairi...._*

Kaine Dikko ? Inna tayi maganar tana kallon idona ! Shima ni ya kalla yace ƙwarai nine Dikkon da kike magana , ai nasan kaima sunan ka Dikko bakai ba Dikkon gidan gwamna shi nake nufi , har yanzu idon Dikko a kaina yake ya ba Inna amsa cewa shine ai , kaine .....? Umm ya bata amsa , yanzu kaine ɗan iskan yaron nan daka raina mutane ? Murmushi Dikko yayi tare da cewa amma dai ai ke ban raina ki ba , wannan duk faɗar mutanen da basa so nane , na raina mutane bana ganin mutuncin kowa idan na taho bana kaucewa kaza² wannan duk labarin "yan uba ne Dikko ba haka yake ba kayane aka linke ta baibaya shi yasa ake ganin mununsu....

Kai da Allah rufe min baki ɗan iska mara mutunci na tsaneka duk duniya idan akwai wanda na tsana tou ka sani ba kowa bane kaine ...... , bana sanka yau ji nake kamar in yanke kunne na saboda ɓata lokacina da nayi ina waya dakai , har yanzu murmushi yake kuma bai daina kallona ba yace itama kamar yadda kikayi haka ta ɗauki zafi , nuna kanshi yayi cewa irin bakinmu ɗaya itama Momy wai bata san An mata kema baki san Dikko anyi anko kenan to amma ai dani da An mata kowa yana san kowa ke ko kin daina so nane ? Yayi maganar yana tambaya na da kanshi......

Nima murmushi nayi masa tare da bashi ansa ina sanka kuma saina aureka ko za'ayi ruwan bala'e da ƙanƙarar masifa a cikin familynsu wannan ni bai shafeni ba , duka zagi ko habaici baya gabana ko za'a mutu a dawo idan na kafe a hanya ɗaya tou wannan hanyar duk girman katsina babu wanda ya isa yasa na juya zuwa wata , nuna shi nayi sannan na nuna kaina Dikko ina sanka kuma saina aureka cikin amincin Allah da salama duk wanda baya maraba da auren nan tabbas canja maganar nayi cewa zai so ma...

Cikin ɓacin rai Inna tace fita....... Dikko fitar min daga nan , a , a Mama cikin hayani Inna ta fara turance Dikko shima da yaren da tayi magana yayi mata nidai na zama "yar kallo dan banajin abinda suke cewa kuma bansan yadda sukayi ba Dikko ya fita cikin damuwa , kafin na sauko daga saman gado Dikko ya fita daga ɗakin da gudu na fita lokacin harya shiga motarshi ya tada , cike da fargaba na isa wurinshi nace Dikko ka tsaya dan Allah , tsayawa yayi yana kallon can gefen cikin tsananin ɓacin rai.....

Kusa da motar na tsaya na dafa hannuna a saman glass ɗin daya rage bai ida saukewa duka ba , Dikko me Inna tace maka don Allah , dakel ya kalli gabanshi ya busar da iskar bakinshi a damuwance yace ba komai Sulthanah........ Dam׳ naji gabana ya faɗi sunan babu daɗi a bakin Dikko sai naji wani iri haka da ya kirani da Sultana tunda na haɗu da Dikko da rashin mutunci muka haɗu amma bai taɓa kamo tashar suna na ba sai yau lallai abun yaci tira karuwa ta tsira malam.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.