Kwarata Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Kwarata Complete.txt
Chapter 7 of 7
Ci gaba yayi da cewa mu ɗau haƙuri mu sanya haka ɗin jarabtace , kuma kowa akwai nashi a rubuce , babu wanda ya isa ya musulta ita ƙaddara idan ka rasa karka manta da Allah , ubangiji keda iko mu bayi "yan kallo ne ! Idan kinyi imani da Allah kuma kin yadda akwai samu akwai rashi , kuma idan har kinyi imani ubangiji yake bayarwa kuma shine yake karɓewa yadda da ƙaddara ki tuna wannan shi ake kira da imani , zumuncin mu yana nan insha Allah kije kuma ki ba Mama haƙuri idan har kinyi imani da Allah ki karɓi auren Sultan kuma ki zama mai biyayya wurin mijinki , kije Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarki na barki lafiya , yana faɗin haka ya sulala da motarshi a hankali ya fita , bin bayanshi nayi yana fita daga gidan ya tafi da tuƙin shi mai burgeni......
Kai tsaye g r a ya nufa dan ya samu ya sauke damuwarshi , yayin da hotunan abinda ya faru tsakaninshi da An mata ya fara wuce masa ta gaban idonshi , a ranshi kuwa kukan Sultana yaji a ranar da yayi mata babbar kajin ƙauri , tana roƙarshi cewa { kaji tsoron Allah karka ɓatamin rayuwa ka rufamin asiri dan girman Allah , } goge hawayen idonshi yayi tare dayin magana a bayyane amma dake banaji shine banyi haƙuri ba saida nayi kaicon ka Dikko me kaji ? Da nayi haƙuri na barta duk haka bai faru ba nima kaina da ina nan zamana lafiya haƙuri yana da matuƙar kyau a rayuwa kuma yana da wahala babu wanda zaiyi haƙuri yayi nadamar yinshi , amma idan kaƙi haƙuri kayi abinda zuciyarka tace tabbas sai kayi nadama da zaran ka gama aikatawa , wani irin wawan burki ya taka tare da juya kan sitiyari ya nufi inda su Bello suke yau saiya kashe Bello daya kawo mishi An mata wurinshi ! Saiya faɗa masa dalilin daya sa saishi aka zaɓa ya ɓatawa An mata rayuwa ƙalu bale gareka Bello.....
Inna kiyi haƙuri don Allah zan auri Sultan , ko kiyi haƙuri ko kar kiyi babu gudu babu ja da baya aurenki da Sultan babu fashi wallahi , to Inna in Allah ya yadda , amma dan Allah Inna me kikace ma Dikko ? Ai na ɗauka da kika bishi ya faɗa miki na tsani Dikko sakarar banza ballagaza dake dama Sultan yacemin ko a asibiti tare kuke kwana idan har kika bari Sultan yace ya fasa aurenki ƙaryarki ta ƙare asirinki ya tonu.
Haka ya kasance dani ɗan uwana ya fito yayi hidima da rayuwata munyi soyayya mai tsabta auren zuminci shine al'adar familynmu amma tunda ake haɗa aure ba'a taɓa samun maso san junansu ba sai mu domin mu ba haɗamu akayi ba mune muka haɗa kanmu , biki ko suna komai da kika sani duk inda zanje muna tare , munayi ma juna soyayyar da ta zama abin sha'awa ga duk wani wanda ke ahalinmu dan wannan soyayyar ta kafa tarihi mai girma , amma lokaci ɗaya Binna ya shigo rayuwata yayi min karatun yaudara zama ɗaya na ɗauka kuma na kifa kaina ƙasa nace na fasa auren Umar , duka zagi anyi amma na kafe sai Aliyu....
Abun ya zama abun tashin hankali da jimami a ahalinmu , yayin da wani ɓangaren ake kallon abun kamar anyi wani babban rashi , duk wani ɗan uwana ko "yar uwata suka juyamin baya wannan bai dameni ba tunda dai Aliyu yana tare dani , Umar yayi kuka kamar ranshi zai fita wasu kuma suna cewa ko na fasa a aura masani dole , amma nace idan har aka ɗauramin aure dashi wallahi saina daɓa mishi wuƙa ya mutu , kaf ahalina suka juyamin baya bayan an ɗaura min aure da Aliyu kinga dai yadda rayuwar gidan Babanki take kuma nayi haƙuri duk nayi ta tsotse dafin wahalar gidanshi amma kinga daga baya saiya sakeni waishi baya zuwa bikon mace , dakel aka anshe ni a gidan nan Umar kuma baiyi zuciya ba ya dawo yayi aure amma ba auren zuminci ba.
Mazan basu da tabbas ko kace kana sansu daga ƙarshe sai sunyi maka tultular ruwan tsohon tulu suyi maka gori abu kaɗan kayi musu sai suce ka gagari iyayenka ka zaɓesu ka bar iyayenka , wanda ya gagari iyayenshi abun mamaki ne ya gagari mijinshi ? Ko a kuskure kayi abu sai sun goranta maka auno girma da rashin mutuncin Dikko Sultana , bani na faɗa ba duk garin nan kowa yasan halin Dikko ya gwane wurin rashin mutunci baya ganin ƙima ko darajar kowa koya aureki bazai riƙeki da amana ba , gashi yanzu ya faɗa cewa mahaifiyarshi bata sanki nima bana sansa , haka zakije ki fuskanci wulaƙanci da hantara a cikin zuri'arsu , kuma nayi imani wata rana saiya goranta miki yace miki karuwa kuma zai miki gori kinbar uwa kin zaɓi namiji , tazara mai nisa tako ina Dikko yayi miki asalinki da nashi ba iri ɗaya ba , tun ba'asan meye suna ba tunin duniya tasansu , mutane masu arziƙi da cikar asali sunyi kuɗi na tashin hankalin da kwalwarki bata ɗauka , sun nemi kuɗi kuma sun samu sun tarasu tun mutane na bacci , Dikko yafi ƙarfinki kuma yayi miki zarrar da baki kamoshi ki shafawa kanki ruwa ayi miki aski ,
Ke kina wasa da lamarin Dikko ko ? Hmmm dan girman Allah wata rana kije inda yake zama ki kalli mata masu siga da nagarta kamar ba mutane ba tsabar kyawunsu , Sultana har Dikko yana kallon dakakkin mata "yan gayun bala'e masu ilimi wanda suka goge masu aji zai saurareki ? Dan Allah kije wata rana kiga yadda mata kebinshi , ko yace zai aureki ƙarya yakeyi yaudararki kawai yakeyi dan nayi imani Dikko baya aurenki yafi ƙarfinki wallahi , kiyi haƙuri kiyi ma kanki karatun ta natsu ke ba ajinsa bace ƙarya yake ba sanki yake ba kaiki zaiyi kawai ya baroki , tunda dai abinda yake nema ya samu kuma tunda ya more kiyi haƙuri ki auri dai² ke shine zaman lafiyarki.....
Inna wallahi Dikko yana so na , ke yarinya ce Sultana baki san Dikko ba baki da labarin halinshi ne ganinshi kikeyi filinshi kika sani baki san ɓoyenshi ba , duk yadda za'a faɗa miki iskanci Dikko ya wuce inda bakya tunani , hausawa na cewa idan ruwanka baya iskarka wanka sai kayi alwallah ka tashi.....
Amma Inna Dikko baya neman mata kuma na zauna gidanshi har na gama zamana banga wata mace tazo ba , murmushi Inna tayi cewa ai kinji yarintar in banda abinki tunda kina nan taya zai bar wata macen tazo ? Ko an faɗa miki gidan da kika zauna nan ne kaɗai gidanshi ? Ai wayau sukeyi saboda siyasa basa neman mata a gida saidai su haura sauran jahohi su ƙwanƙwaɗi iskancinsu su dawo , shiko Dikko karuwanshi duk ba "yan nan bane ba zuwa sukeyi daga wasu ƙasashe kuma yana gama biyan buƙatarshi zai basu kuɗi su juya abunsu ba tare da wani yaji ko ya gani ba , kinga waye ya ganshi da mace anan bare yace shima manemin mata ne ? hmmm ke yarinya na kiyayeki da Dikko domin haɗarinshi yana girma.
Nidai haƙuri nayi ta bawa Inna kuma na haƙura har a zuciyata na yadda da auren Sultan kuma na bawa Inna haƙuri sosai ta kuma gode tare da sanyamin albarka sannan tabar ɗakina , tana fita na rufe ƙofa na kwanta ni bansan me yasa ba idan har zanga Dikko ko naji muryarshi sai in nemi hankalina da tunanina duk na rasa ina ya tafi amma insha Allah koya kirani bana sake ɗauka na haƙura dashi Allah ya bani dangana.....
Wata irin shaƙara Dikko yayi ma Bello cikin sanyinshi yace me nayi maka don Allah ? Me yasa ka haɗani da yarinyar da kukeyi rikicinku bayan ni bai shafeni ba ? Shiru Bello yayi baice komai ba , Dikko yace faɗamin ina saurarenka kadai lura ina cikin fushi ko ? Jinjina kanshi yayi cewa tou faɗamin kafin in ɓare maka biyu in kashe ka kuma na kashe banza sai ka zaɓa ga mutu ga kuma rayuwa......
Da sauri Bello ya dafa hannun Dikko , sakinshi yayi tare da cewa ina saurarenka , cikin kuka Bello ya faɗawa Dikko saboda yayi fyaɗe wa wata yarinya da suke gidan shine shima Binna ya rama akan matarshi , wannan dalili yasa ya kudiri shima saiya gurɓatawa Sultana rayuwa kasancewarta bugun zuciyar Binna , soyayyar da Binna yake mata yasa duk inda zata tafi yana tare da ita saboda baya so ta shiga cikin wata damuwa ko halaka , Binna baida tsoro kuma bashi da mutunci akan duk wanda ya taɓo masa Uwar masu gida saboda yana jinta kamar wata rayuwarshi , ni kuma ina nan haƙe dashi ina neman sa'a yadda zanyi na taɓo wannan rayuwarshi tashi dan huce raɗaɗin ciwon abinda yayi min , ƙwatsam sai Binna yazo min da labari cewa yau Uwar masu gida taso ta jawo masa fitina da kanta ta zagi ɗan gwamna yaro mara mutunci daya raina mutane dakel aka bashi haƙuri ya haƙura saina lura Binna yanayin maganarshi ya nuna yanajin tsoronka bayan shi kuma bayajin tsoro kowa.
Ganin haka sai nayi amfani da wasu mutane daya ci bashinsu nace musu Binna yace bazai basu kuɗin nan ba yace ya cinyesu idan suna da wani isashshe yazo ya karɓar musu a hannunshi , nine na tunzurasu sukayi ƙararshi aka kamashi kuma ni dakaina na bada kuɗi wa "yan sanda sukayi mishi lullusar fitar hayyaci , kuma nine naje na biya kuɗi nayi belin shi , saina bashi shawara za'ayi caca yazo yayi ya shiga tunda yana da sa'ar caca bai taɓa faɗuwa a caca ba idan yaci kuɗin saiya biya bashin , nasan baida kuɗin da zai saka kafin alƙalamin caca shine nace masa kawai ya saka Sultana , da farko bai yadda ba duk da saida nayi masa asiri kuma bokana ya tabbatarmin da zai sakata a cacar ya kuma bani maganin da zan zuba mishi a abun sha wanda zaisa yayi wasi² , haka kuwa akayi bayan dai Binna ya yadda ya saka Sultana a wurin caca na zuba mishi maganin wanda yasa yayi wasi² ya faɗi a wasa.
Ba wani abu kayi min ba na kawo ta wurinka ba saboda na lura Binna yanajin tsoronka kuma na tabbata ko tsafi yake kai kafi ƙarfinshi saboda kai ka zama dodon duniya kuma kai jan gwarzon maza ne dan kowa yasan ka gaji nagarta , duk wani ɗan ƙaramin tsafin shi bazai kamaka ba dan kai nari ne ko an jefe ka haka nan jifar zataje ta dawo kuma idan taƙamarshi yayi shari'a dakai kune gwamnati bai isa yaja dakai ,
Gwamnatin ubanka Dikko ya faɗa tare dakai mishi wani irin kyakkyawan halbi a baki saida yaci uban Bello da kyau ya kuma sake ɓare mishi haƙora sannan ya kashe Dady da mari yayi haukanshi sosai babu wanda ya bashi haƙuri dan babu mai riƙeshi sunci ubansu kuma suma yau sun ƙara saki da lamarin Dikko saida ya tabbatar sun tashi aiki ya nufi gidanshi cikin ɓacin rai !
Cikin farin ciki kowa ya wayi gari duk wanda ka gani a gidanan yau yanayin farin ciki , kowa sai hidimar gabanshi yakeyi yayin da ni kuma nasha wanka na tsuke cikin wani ƙaton leshi kalar launi mai kyau , nima dai duk da banajin daɗi hakan bai hanani nuna farin ciki ba amma na ciki yana ciki , Inna ma tana cikin farin ciki tana ta hidima da mutanen arziƙinta kai Inna gaskiya wayayyace "yar gayu kisan farko ga kyau ga hutu wallahi baka gajiya da kallonta.
Misalin ƙarfe 2:00pm aka ɗaura auren da taron dubun mutane suka halatta , ina ɗaki kwance ina ta kuka na rasa abinda yakemin daɗi Inna ta shigo ɗakin cikin tsananin ɓacin rai tasha kuka har ta gode Allah , kayana ta fara tattarawa tana kuka idan ta zuba a akwati sai ƙawayenta su ɗauka sukai waje cikin mota su dawo , duk abinda ya shafeni saida Inna ta tattarashi kaf ta ware lefen da aka kawo jiya ta ajiyeshi a gefe wayata ta ɗauka tare da jawo hannuna tana fizgata cikin ɓacin rai haka muka keto cikin taron mutane kowa yana kallonmu , Kaka ta biyo Inna tana cewa Fatima wai kedai ban isa in faɗa miki ba ? Bata bata ansa ba har yanzu kuka Inna keyi , haka Kaka ta biyomu har harabar gidan amma sam Inna bata saurara mata ba ta buɗe bayan mota ta jefani ta kulle da kanta taja motar kamar zatabi ta kan Kawu ta wuce ta fita daga gidan , sauran mutanen da suka zo mata biki suka biyo bayanta.
Har muka zo gidan Inna dake barhim estate Inna kuka takeyi , ƙaton gida ne da akayi mishi ginin zamani gidan "yan gayu an ƙawata shi da filawowi wanda suka ƙara martaba darajar gidan , tanayin parking ta fita nima fita nayi daga motar nabi bayanta ina kuka palo ta zauna tana goge hawayen idonta da tissue a haka taron ƙawayenta suka shigo suna ta bata haƙuri dukansu da turanci suke magana ni dai bansan abinda suke cewa ba saidai inaji lokaci² tana kamo sunan Dikko , haƙuri dai suke ta bata har wanda nake tunanin shine mijinta yazo kiranta yayi suka shiga ciki ƙawayenta suka ci gaba da tattaunawa akan abinda Yayar Inna tayi bata kyauta ba ,
Tayi ƙatuwar cin amana sukaci gaba da maganarsu da yaren da nake fahimta su kuma sun kasa gane saboda nine Inna take magana dasu da turanci tunda tasan ban iya ba , wai ashe ita Yayar Inna jiya itace ta faɗawa Sultan wai ni ina da cutar ƙanjamau lokacin da akayi min fyaɗe aka sakamin cutar shi yasa "yan gidanmu sukayi ta ƙyanƙyanmi na ko kofi na taɓa basa amfani dashi wannan dalilin yasa na shiga bariki kuma abinda yasa na amince da aurenshi wai ni nake faɗa zan yadda na aureshi ne dan na saka mishi cuta , kuma ni karuwar Dikko ce kuma kona aureshi wai ni na faɗa mata bazan daina bin maza ba , da Sultan ya faɗawa Kawu , Kawu yace ƙarya ne ka auri yarinyar nan zaka zauna lafiya amma sam mahaifiyar Sultan tace wallahi baya aurena , Kawu yayi faɗa cewa ya taro mutane daga wurare da dama zasu zo ɗaurin auren ɗansa saiya musu waya yace an fasa saboda wulaƙanci ? Shine Mami tace sai a ɗaura auren da ɗiyar ita Yayar Inna , yanzu da ita aka ɗaura auren duk Inna bata san wainar da ake toyawa ba saida aka ɗaura yau akayi ta mata habaici wai ta lulluɓo "yarta kura da fatar akuya taso ni na auri Sultan na goge masa cuta , sukayi ta faɗin maganganu marasa daɗi akaina shine Inna taji haushi kuma in banda munafirci jiya sune suka tunzurata ta nemo Dikko tayi mishi wulaƙanci , ashe su sunsan Dikkon shine Dikko ita kuma Inna bata sani ba tunda dai kawai shi wannan Dikkon ta ɗaukeshi matsayin ɗa yana girmamata ta gayyatoshi ne ya tayata tayi faɗawa wa Sultana sai kuma ya kira Dikkon gidan gwamna yayi masa concrete worning ya fita harkar Sultana , shine tayi rashin mutunci wa Dikko data gane shiɗin dai ne Dikkon da take nema tayi ma Dikko wulaƙanci a daren jiya sosai wanda kare baya ci ,
Ita ba rashin Dikko bazai auri Sultana ba dama tasan babu maganar Dikko ya auri Sultana gaskiya saboda ba irinshi bace ita , tanayin baƙin cikin zumincin data dagula tsakaninta dashi , sai kuma kukan abinda "yar uwarta ciki ɗaya tayi mata yanzu da bata raye haka rayuwar Sultana zatayi ta wurgegeniya babu mai taimakonta , ita kanta ta sani wato ta bada "yarta ita kuma Sultana ko oho ,.......
Sai dare kowa ya tafi daga gidan shima mijin Inna tafiya yayi ba'anan zai kwana ba , Inna tana cikin damuwa sosai É—akinta ta shige ta kulle , tou banda abin Inna ita kuma Kaka meya shafeta a cikin wannan matsalar ne ? Wata zuciyar tace baki sani ba kila itama tace wani abu , tou amma me yasa inna ta haÉ—a hada Kawu ? Oho zuciya tace sudai suka sani domin sunfi kusa......
Duk gargaɗin da Inna tayimin akan Dikko saida na kunna wayata na kirashi , kamar jira yake tana shiga ya ɗauka ya gaggaɓe da wata irin dariya yace amaryar Dikko ai nasan wallahi dudduniya babu maike saini , yaci gaba da dariya cikin dariya yake cewa abinda yasa bana aurenka baƙin rai baka dariya ba fara'a doke² gaka mahaukaci sai aljannu kamar iccen tsamiya hahahaha ashe rabon mahaukaci ce lallai zamuga wasan kura An mata matar Dikko , ke kafiya ni kuma aljannu kamar iccen tsamiya , hmmm inzo Barhim ɗin zaki fito wurina..............?
Dan Allah kuyi haƙuri wallahi ina fama da matsalar rashin caji ne kuyi haƙuri da wannan !
06/10/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA.....* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 72
Bazan fito ba na bashi amsa , dariya ya sakeyi kaɗan cewa he ƙarya ne fa gani nan zuwa , kasan gidan ne ? Ko na sani ko ban sani ba damuwa na ne ina zuwa kuma ki faɗawa Mama ina gaisheta kice mata nine zanzo dan na kirata waya bata ɗauka ba , da sauri na miƙe ina tunanin yadda zan shirya kafin yazo naji yana cewa bafa sai inyi wanka ba ina zuwa nan da mintuna biyar yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.
Ɗakin da Inna ta shiga na nufa ina taɓa ƙofar najita a rufe , zan juya naji tace Sultana miye ? Inna Dikko ne yace zaizo , wane Dikkon ? Wanda kika sani , tou yanzu ya akayi ne ? Shigowa zanyi inyi wanka , duk kin san zaizo sai yanzu zakiyi wanka ? Nifa bansan zaizo ba Inna yanzu ya faɗamin yana zuwa , tou ki tafi ɗakinki mana , nidai Inna buɗemin don Allah , tsoki tayi tare da tasowa tazo ta buɗe ɗakin ta koma saman gado ta kwanta , bayanta nabi na shiga ciki har yanzu bata daina kuka ba !
Ban mata magana ba na cire kayana na shiga wanka , kafin in fito har Dikko ya iso sai kiran wayata yakeyi , Inna sai faɗa takeyi banda wawanci sai mutum yace zaizo na sirki wanka , ki fito ko baki gama ba , shiru nayi naci gaba da huɗɗar data shafeni , ita kuma Innar fita tayi taima mai gadi magana wai akwai baƙo a waje ya buɗe mishi ya shigo.
Da mai gadi yayi ma Dikko magana cewa yayi ai nan ma yayi suna da yawa ne basai sun shigo ba , mai gadi ya koma ya faɗawa Inna bataji daɗin haka ba , shi kuma Dikko abinda ya hanashi shigowa kar Inna ta sake feƙa mishi rashin mutunci kuma An mata tana fitowa ɗaukar ta zaiyi su tafi idan sun gama ya dawo da ita kar Inna ta fito ta tona mishi asiri cikin bainan nasi.....
Ina fitowa wanka na ɗauki kayana dana cire Inna tace ki ajiyesu dan ubanki ko su zaki maida ne ? Haba nifa ba su zan maida ba , da kika ɗaukesu ina zaki dasu ne ? Zanje in ajiyesu ne , da Allah aje ki wuce ga kaya can ta nuna inda ta ajiyemin kallonta nayi tare da cewa sannu ki daina kuka haka nan kar kanki yayi ciwo , idan yayi ina ruwanki naki ko nawa ? Allah ya baki haƙuri na nufi jikin madubi ina shafa mai sai powder tagumi Inna tayi ta bini da kallo har na saka kaya na shafa tutare kaɗan na ɗauki hijibin da Inna ta ajiyemin na saka na fita ,
Sultana tana fita Inna tayi magana a bayyane cewa wai Dikkon nan nawa ne don Allah ? Nifa na shiga rubibi dan har yanzu wallahi na kasa fahimta shin wai Dikko U DK shine yake zuwa wurin Sultana ko kuwa akwai wani Dikkon bayan shi Dikkon gidan gwamna ne ? Gaskiya ba DK bane tou ita Sultana ina ta samo wannan shi kuma .......?
Cike da zumuÉ—i na fito na buÉ—e gaba zan shiga naga ya ajiye filet a saman kujerar da kabeji anyi mishi yanka mai kyau sai cokali mai yatsu babu mai ba magi komai babu a ciki kuma Dikkon waya yakeyi rufewa nayi na koma baya na shiga na zauna , ina zama ya tafi yau bada su Ashiru yazo ba abokanshi ne suke tare , yana gama wayar ya É—auke filet in yana cewa dawo nan An mata ,
Daga baya na tsallaka na isa gaba na rumgume Dikko sunbatar gefen fuskata yayi zan kwanta jikinshi motar ta fara lilo da sauri ya figi sitirayi dan kaucewa motar gabanshin daya kusa haye mata , zaunar dani yayi saman kujerar daya ɗauke filet in yana cewa zauna An mata karmu faɗi , ƙin zama nayi zan sake tasowa ya danne ni da hannun damarshi ya riƙe sitiyari da hannun haggunshi ya miƙa hankalinshi da natsuwarshi wurin tuƙi yana cewa da nace kar kiyi wanka saida kikayi badai zaki daina raini ba ko ?
Ni ? Waye yace maka nayi wanka ? Nayi wanka a ina ? Ko kana tunanin zanyi ne dan na burge ka ? Sauke hannunshi yayi daga riƙon da yayi min ya ɗauko filet in kabejin daga inda ya ajiyeshi ya ɗoro shi saman jikina yana gyara rigarshi yace ci , me zanci ne ? Koma miye idan kinci bakinki zai faɗa miki , wai kana nufin ni zanci kabeji kamar wata akuya ? Koma dai mece ce ke bai shafeni ba cewa nayi ki ci , haba Dikko ni gaskiya bana ci , cikin ɓacin rai ya kalleni yace ke..... Ɗauka kici , cikin sanyin murya nace haba kabeji ne fa har yanzu ni yake kallo yace kabejin ci ya ƙarasa maganar fuskarshi ba wasa.
Ina gunguni na ɗauki cokali na fara ci , a dai² lokacin da muka iso goruba , amma yau ba gidanshi yaje ba wata kyakkyawar santa suka yanka suka haɗa majalissar su a saman titi sun kashe hanyar ta yadda wani baya wucewa dan duk a saman titin suka ajiye motocinsu su ishashshi duk wani abokin Dikko da nasan yana majalissa a gidanshi na ganshi har dai Yazeed na gani kuma naga irin "yan matan da Inna ta bani labarinsu daren jiya , kallon Dikko nayi da hankalinshi yake kan wayarshi naci gaba dacin kabejin ina yunƙurin amai bai kalleni ba yace idan kikaimin amai a mota saina zaneki , to ai na ƙoshi babu daɗi , ai a ba daɗin zaki cinyeshi kisha ruwa gashi nan a gefenki ,
Salaf ne fa , salaf ɗin An mata cinye shi da sauri , maganin mi to ? Ra'ayi nane kawai na tareki da kabeji kuma ki rufemin bakinki na fara gajiya da magana , Allah ya isa na faɗa ƙasa² naci gaba daci saida na cinye kabejin nan duka , ansar filet in yayi ya duƙo kusa dani yace to me ne ne ? Ngode na bashi ansa to yayi kyau sha ruwa ina zuwa ya ƙarasa maganar yana fita daga motar da filet in yana fita wani ɗan cika sheda ya ansa , shi kuma aka ɗaukeshi a mota suka tafi..... Kuma na kirashi a waya bai ɗauka ba , raina ya ɓaci kuma na ƙufula da yawa.
Gaba ɗaya ɗakin yayi shiru kasancewar ƙarar saukar marin da Momy ta tsinkawa Dikko duk ƙannenshi dake wurin da gudu suka tashi , yayin da ita kuma Momy ke cewa saidai ka zaɓa ko yarinyar nan Dikko ko ni saboda ba so ɗaya ba biyu ba na rabaka da ita baka bari , kai da bala'e ma zaka rabu da ita dan duk duniyar nan idan zata taru bisa kaina bazaka auri karuwa ba sakaran banza da baka san inda duniya ta nufa ba yaushe ka koma sakarai ban sani ba ? Ina tantama anya ma kaine Dikkon dana haifa da ciki na ? Karuwa Dikko ? Me ka gani jikinta wanda harya gigita ka yasa kake neman ka zama wani zararre ?
Mom..... Ƙara yanka mishi mari tayi tace idan ka sake min magana saina shaƙeka ka mutu na huta da baƙin ciki tashi ka fita ka bani wuri kuma kaci gaba da yawo da ita a garin nan ana bani labari , duk ranar dana sake jin labarin ka ɗauki yarinyar nan a motarka saina je har gidansu naci uwar uwarta na faɗa maka sakaran banza marar kishin kanshi tashi ka fita ta faɗa a tsawace , jiki a sanyaye Dikko ya miƙe ya fito daga palon ,
A waje ya samu Nabeela tana ganinshi zata ruga yace ke zo nan , cike da fargaba tazo ta tsaya gabanshi ta fara kuka , kallonta yayi na wani lokaci sannan yace waye yace ya ganni da An mata ? Cikin kuka tace wallahi Yaya bansan waye ba ina toilet ina alwalla naji ta tana magana a waya tana faÉ—a , bayan na fito ne na sameta tana tura maka text ,
Amma a tunaninki waye ya kirata ? Yaya wallahi ban sani ba , na baki nan da mintuna 5 ya nuna da hannunshi yana ci gaba da cewa ki ganomin ko waye idan kuma ba haka ba zaki shiga3n ki.... Yana faÉ—in haka ya nufi wurin mota ya shiga abokinshi yaja suka bar gidan!
Lokacin da Dikko ya dawo har na fara bacci shigowarshi cikin mota ya farkar dani , ina tashi na ganshi nace sai in kiraka baza ka É—auki waya ba ? An mata da Allah bazan É—auka ba kiyi magani na mana , ai baka dai kyauta ba kuma haka rashin adalci ne ka barni a mota kamar sakara idan kuma na tafi kace na tafi saika shanyani ka kama huÉ—É—oÉ—in gaban ka ? Ke kalli idona , kallonshi nayi yace baki lura da yanayi ba ? Ai ni naga lura da yanayin yasa ka barni ni taya ma zan iya ganewa bayan duk yanayin iri É—aya ne ? Rufe idanuwa yayi dan haka na kame bakina nayi shiru ,
Shi kuma idonshi a rufe yace na shanyaki sai zakiyi ya ya dani ne ? Shiru nayi ban sake magana ba dan yadda ya ɗauki zafin nan yana iya tsintsinka min mari , tafiya ya farayi da motar yana faɗa cewa ni bansan irin iskancinki gaba ɗaya na lura so kike ki mayar dani wani sa'ar wasanki wai me yasa ke kike san cin moriyar rauni na ne ? Kici gaba da haye man ƙaramar yarinya dake. Nidai ban sake mishi magana ba ,
Har muka iso ƙofar gidan Inna Dikko faɗa yake min yana cewa idan kinajin taurin kan ki sake magana kiga yadda zanyi parking nan in lalata miki fata , banza nayi dashi bance masa umm׳ ba , yanayin parking na fice da sauri bayan nayi mishi godiya kamar yadda yake so , har na kusa shiga gida ya kirani , dawowa nayi amma ban shiga motar ba , An mata kin yafemin ? Ya tambaye ni , da Eh na bashi amsa , tou zagayo nan kiji wata magana , zagayawa nayi saitin inda yake na tsaya ina kallon ƙasa.....
Idan Allah ya kaimu gobe zanje kaduna , Allah ya tsare hanya na bashi ansa , to bazaki tambayeni me zanyi ba ? Da kamar ince masa ai bani na aike ka ba , amma sai nace ɗin me zakayo ? Murmushi yayi yace An mata baiwar Allah ba kai tsaye zaki riƙamin magana ba na faɗa miki ki riƙa lanƙwasa min harshe wai ke ni haka nake miki magana ba sanyi ? A shagwaɓe zakice zakaje kaduna ka abarni ne , shiru nayi na kasa magana , ina saurarenki , ni dan Allah bacci nakeji , ai kowa ma yanajin bacci sai kin faɗa zaki tafi idan kuwa ba haka ba zamu kwana a titi , sai kin faɗa da shagwaɓa sannan zaki tafi , nidai kunya ta hanani kallon Dikko bare na maimaita abinda yasa na faɗa , text ɗin da Nabeela ta turo mishi yake dubawa bayan ya ajiye wayar yace ina saurarenki.
Ganin zamu dawwa a haka yasa na rufe fuskata na faɗa kamar yadda yace , buɗe fuskar ki , sauke hannuna nayi , matso nan , matsawa nayi kwantar da kanshi yayi samman murfin mota ya ƙara cewa matso , matsawa nayi da hannunshi ya nunamin nima na kwantar da kaina kamar yadda yayi , ɗaura kaina nayi ina kallon idonshi , shima kallon nawa idon yayi yace tou faɗamin ko baki so inji daɗi ? Ina so , kina so ko ? Eh , yimin magana a shagwaɓe yadda nace ki faɗa , dakel na iya faɗa cikin jin kunya bayan na rufe idona , buɗe idonki ba'a furta zancen so yayin da ido yake rufe ki faɗa a yayin da muke kallon idanuwan junanmu dan martaba soyayya , kallon idon abun soyayyarka yayin furta masa wata kalma da zaiji shauƙi yakan ƙara tabbatar da son mai magana a zuciyarshi , faɗa min kina kallon cikin idanuwana , dakel dai na faɗa , murmushi yayi tare da cewa jeki zanzo kafin in tafi badai haka yaso yaji ba , saida safe na faɗa tare da wucewa gida , saida na shiga gida Dikko ya tafi da tunanin wai me yasa yawancin mata basu iya magana mai tafiya da tunanin namiji ? Ba kallo mai burgewa magana mai laushi babu dai wani salo na tafiya da tunani wai a haka ma ita kunya ta takeji lallai yarinya kina da aiki kima tattara wannan kunyar gefe ɗaya ki ajiyeta saboda Dikko baya ma mace kawaici.
Dakel Dady yaja jikinshi ya leƙo yana ma mai gadin dake faman tsaron su babu dare kuma ba rana magana cewa da Allah ɗan sammin aron wayarka , ba wani damuwa ko tunanin abinda zai faru ya miƙa mishi waya , lambar matarshi yasa ya kirata , saida ya tsinke ya sake kiranta ana biyun ta ɗauka , ko gaisawa basuyi ba yace mata ɗan ƙawarki yana nan yana cin mutunci mu akan wannan tsinanniyar yarinyar dana faɗa miki tana san ta anshi kuɗin gadon su dan haka ki faɗawa ƙawarki tasa Dikko ya sakemu dan wallahi idan na ƙara biyu awurin nan mutuwa zanyi , cike da damuwa tace Dikko bai sanka ba ? Ya sanni mana ɗan iskan saida yacemin ma albarkacinki naci cikin kuka Dady ya ida cewa amma duk aya sanni yake ta ganamin azaba ba dare ba rana !
Maman Hafsa tace amma dai Dikko baida mutunci , bara zan kira Maryam ɗin dan na tabbata duk iskancin da Dikko keyi garin nan bata da labari ɗan iska mara mutunci dako bakin duniya bai kamashi , Dady yace dama banda abinki ya za'ayi bakin duniya ya kama irinsu wanda basu fito ba saida suka shiryama duniyar , ki kirata an fara kashedi kuɗin zai ƙare ya tsinke wayar.
Ina shiga gida a saman idon Inna na shiga kuma ta zageni sosai sannan ta shatamin layi karna sake bin Dikko fira idan ba'a ƙofar gida ba cikin palonta idan bayayi nan tou ya kama gabanshi , nace to na canja maganar da cewa kin daina kukan ne ? Dan bana so azo inda zata zagi Dikko , bata bani ansa ba dan haka nahau saman gado na kwanta kusa da ita ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni da tunanin rigimar Dikko.
Misalin ƙarfe 7:45am Momyn Hafsa ta kira Momyn DK tana ɗauka Momyn Hafsa tace tuba nake dai na tasheki bacci da safiyar nan dan Allah ina tare da damuwa ne nake ta Allah² gari ya waye , Momy tace ba komai , Mom Hafsa tace Hajjaju Dikko ne da mai gidana , Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un nan kuma ya dawo ? Eh , meya haɗa Dikko da mijinki Mariya ? Wata karuwars..... Ah ah Momy ta faɗa dan dakatar da Maman Hafsa tace Dikko bashi da karuwa ni kuma ban haifi mazinaci ba Allah ya tsaremin ɗana baya huɗɗar mata , me kuwa zai haɗashi da karuwa da har zaiyi riƙici da wani akanta ? Allah ya baki haƙuri ba haka nake nufi ba , Momy tace duk ma yadda kike nufi ki bari zan kira Dikko yanzu....
Kiyi haƙuri ki fahimci maganar tawa , Momy tace nafa fahimta kawai dai banji daɗi ba kike cewa wai karuwarshi kamar ba ɗanki ba ? Haba Mariya , haƙuri dai Mariya ta ƙara bawa Maryam sannan suka ajiye waya Momy bata bar Mariya ta gama maganarta ba , tsoki Momy tayi bayan ta tsinke wayarta , taci gaba da faɗa ita dai Dikko yana so ya kasheta ya hana mata zaman lafiya , idan ta rabashi da nan sai kuma ya koma nan Dikko ba ƙaramin yaro ba amma ya hana mata kwanciyar hankali , yanzu banda iskanci kuma meya haɗashi da mijin Mariya Jabeer , wayar Dikko ta fara kira tana faɗa amma sai Jiddah ta ɗauka tace mata tunda ya fita masallaci har yanzu bai dawo ba ,
Tun tsakar dare Bello ya fara tanɗar harshe kamar kwarton da yaga wawan zama , yana dariya ma Dady cewa saina tona maka asiri ׳ harararshi Dady yayi tare da cewa to ka tonamin dan wutsiyar gyatimin ka , dariya Bello yayi ta irin ya saki layi yana ci gaba da cewa saina tona maka asiri , a haka Dikko ya sami Bello yana ta abu kamar dai yaɗan zare haka....
Yana ganin Dikko yace Baba wannan Baban ne , Dikko rai babu haƙuri yayi ma Bello wani irin kallo yace nine Baban naka .....? Umm ya faɗa tare da gaggaɓewa da dariya yace ba kaine ka kamoni ba kayi man duka , kallonshi Dikko yayi tare da cewa ko kana so na ƙara maka ne ? A , a Baba na bari , tou me kayimin na dake ka ? Dan abinda shi Dikko ya fahimta kila kamar Bello ya tsorata da yawa yasa ya ruɗe , shi kuma Bello cewa yayi in faɗa maka gaskiya ? Da ƙarya ka faɗamin ? Inji Dikko , Bello yace wallahi nine nake so ta zama karuwa ,
Kuma nine na kashe Binna sa'ar caca na yana tafiya da rayuwar cacarsa dama boka yace zai haɗa sa'a tane a ta Binna danshi mai sa'a ne yacemin kuma idan har Binna ya daina caca shine komai zai lalace min bazan sake samun sa'ar caca ba kuma rayuwata zata zama kamar walƙiya idan har Binna ya daina caca , shine Binna ya fita a caca komai nawa yaja baya ,
Dana koma na faɗawa boka cewa komai ya taɓarɓare min kuma mutane suna gudu na , shine boka yace idan Binna bai dawo caca ba rigar da zan saka komai na rayuwa saina nema na rasa , dana ce Binna ya dawo caca ya ƙiya , shine na sake komawa na faɗawa boka shine ya tura aljannu suna bawa Binna tsoro a bacci ko zai dawo amma ya ƙiya.
Mafita na ƙarshe shine boka yace mutuwar Binna itace tsira da kuma salama a rayuwata shine na kashe shi , Dikko yace ai bashi ka kashe ba kaine ka kashe kanka , labarin kwalba ya akayi yazo wurinka ?
Malami karuwa da mawaƙi duk basu da amana , yayin da suka kama wani a lokacin suke watsi da duk wani mutunci dake tsakaninku , malamin da suka ba kwalbar ni malami na ne kuma nine na haɗashi da Mamy , da kwalbar tazo hannunshi shine ya kirani mukayi ciniki ita Mamy ta bashi naira dubu hamsin akan ya warware matsalar shine ya faɗamin ni kuma nace zan bashi naira dubu ɗari biyar ya bani kwalbar , shine nakai na anso ,
Aljannu goma ne a saman kwalbar suna gadinta daga nan har illah masha Allah , wannan sammu makarinsa ɗaya ne inji boka , saukar alƙur'ani mai girma tsawon wata ɗaya kullum sai an sauke alƙur'ani sau goma duk rana ɗaya a yanka raguna goma bayan an buɗe kwalbar kuma ba fasata za'ayi ba domin kwalbar itace matsayin ƙwalwar ita Sultana shi yasa akayi cushe² a cikinta an tosheta ta yadda iska baya shiga , buɗe kwalbar za'ayi a barta a buɗe daga ranar da aka san za'a fara sauka , sau goma za'a sauke fa kuma har tsawon kwana 30 za'a yanka raguna goma duk rana a raba ɗanyen naman sadaka.....
Yanzu ina kwalbar take ne ? Tana ɓoye a wani wurin sirri nine kaɗai nasan wurin , na ɓoyeta tun bayan lokacin dana anso ta daga hannun malam , fita Dikko yayi ya nufi gidanshi , bayan yaje yace Ashiru yaje ya ɗauki Bello ya kaishi gidanshi ya ɗauko saƙo , Ashiru yace to , Dikko ya wuce ciki.
Da wani irin ciwon kai yau Inna ta tashi ko motsin kirki bata iyawa tun jiya take kwarara amai kafin gari ya waye tayi laushi ko magana bata iyawa , ina zaune kusa da ita sai sannu nake mata bata min magana tadai bini da ido tana min kallo mai nuni da tanajin tausayin rayuwata ,
Mai gadi naji yana ta sallama daga waje dan haka na tashi na fita , nayi baƙi a waje shine abinda ya faɗamin , kai tsaye na nufi ƙofar gida wani mutum ne zaune a saman machine kusa dashi naje muka gaisa bayan mun gaisa ya ciro takadda daga aljihunshi yace gashi , nace ta miye ne ? Yace ki ansa ki kiranta mana , kaida ka kawota kaine zaka buɗe ka karanta , kallona yayi sannan yace sammaci ne ƙanin Babanki yana tuhumarki da sa hannunki a lalacewar tarbiyar "yar sa sai kuma maganar kuɗin gadonsu daya ji labari kin ansa kin handamesu.......
Kallonshi nayi amma ban anshi takaddar ba nace ina zuwa , komawa nayi ciki na ɗauki wayata na kira Dikko , saida kiran ya kusa ƙarewa ya ɗauka , fita nayi waje babu ko gaisuwa na fara rattafa mishi damuwata , shima yana cikin damuwa domin bayan ya koma gida Jiddah ta faɗa mishi Momy tayi waya , bayan ya kira Momyn ne tace yaje tana kiranshi , da yaje tayi mishi zagin girgizar "ya "yan magarya tare da faɗa masa cewa kashedi na ƙarshe tayi masa akan Sultana idan ya kuskura ta sake kiranshi akan Sultana zata mishi wulaƙancin da katsina bazata iya ɗauka ba , yana cikin tashin hankalin zagi da tunanin taya zaiyi ya rabu da An mata ita kuma ta kirashi tana faɗa mishi tata matsalar kuma shine take so ya sama mata natsuwa , ashe shine ma ya kamata ya koyi aje damuwa 2 a zuciyarshi ba An mata ba , damuwar shi , damuwar An mata , ajiyar zuciya ya sauke sannan yace kina ina yanzu ?
Ina Barhim , ina shi mutumin yake ? Yana waje , tou ki taho dashi mu haɗu daku wurin government house yanzu zan fito , ciki na koma na ɗauki hijabi na ko Inna ban faɗa mawa ba saboda na gani tana cikin damuwa bai kamata na ƙara mata wata damuwar ba amma nasan dole zan mata laifi tunda tace na daina bin Dikko kuma gashi zan bishi , kuɗin napep na ɗauka na fita waje ,
Ina zuwa wurin mutumin nace masa tou muje , ai ba yau ake nemanki ba sai sati mai zuwa zakije , Ey wurin Babana zamuje ka bashi kaga bai kamata ni na anshi sammaci a hannuna ba , kuma kaga daka zo bani ya kamata ka nema ba , iyayena zaka nema idan kuma ina da aure mijina , ina Baban naki ne ? Muje ai wurinshi zamuje yanzu , tada mashin inshi yayi yace in hau nace masa mu fita waje dai na samu napep.
Ina gaba yana bayana saman machine har muka fito wajen estate in , na samu napep na shige ko a napep mune a gaba yana bin bayanmu da machine har muka isa daga nesa na hango motar Dikko dan haka na sauka a napep bayan na bashi kuÉ—inshi...
Dikko yana hangoni ya matso inda muke tsaye , ta wurina ya tsaya tare da sauke gilashi , matsawa nayi kusa da motar ina cewa mutumin tou taho , ƙin tahowa yayi , ni kuma na sake cewa kazo ka kawo mishi yana jiranka ,tada machine ɗin shi ya farayi Dikko yace ya akayi ne ? Ya nuna kamar baima san abinda ya faru ba , wai kotu ake ƙarata wai ana tuhumata da lalata tarbiyar wata kuɗin gado duk ni ɗaya , a dai² lokacin da mutumin ya tashi machine ɗin shi Dikko yace kai zo nan , kashe machine ɗin yayi ya sauko dan yasa ko ya tafi zai bishi ne kuma idan ya bishi da damuwa.
Daga ɗan can gefe ya tsaya ya gaishe da Dikko , bai ansa gaisuwar ba yace ya akayi ne ? E dama ranka ya daɗe wai ita ake nema a kotu dan ansa wasu "yan tambayoyi , wane irin "yan tambayoyi ? Wani ƙanin Babanta ne yake ƙararta , biro Dikko ya ɗauko gefenshi ya bani yace miƙa mishi ya goge sunanki yasa nawa , ai ranka ya daɗe ba kai ake nema ba , Dikko yace wanda ya kira uwa ya kira ɗanta ne , haka zalika duk wanda ya nemi mata mijinta ya nema rubuta suna na ,
Ƙin ansar biron yayi tare da cewa tuba nake ranka ya daɗe , miƙo hannu Dikko yayi cewa tou kawomin , miƙomin takaddar yayi Dikko yace kai zaka kawota da kanka , matsawa yayi ya miƙa mishi , duba takardar yayi bayan ya ansa yace to jeka zamu zo rana irin na yau ko ? Yace E ba damuwa kuɗi Dikko ya bashi masu yawa godiya yayi sannan ya tafi...
Taho mu tafi , zagayawa nayi na shiga muka tafi gida , a hanya nake faÉ—a masa Inna bata da lafiya kuma tana ta amai tun jiya kuma na faÉ—a mishi kuka tayi sosai shi yasa bata lafiya , addu'ar neman samun lafiya yayi mata daga haka bai sake magana ba saini dana isheshi da surutu har muka iso gida , bayan munzo ne yake cemin ya fasa tafiya saboda wani uziri daya taso mishi ,
Sannan kuma ya tambayeni wai zan iya zama da Jiddah ? Ina zan zauna da ita ? G R A kinga ban gama aiki goruba ba kuma ni inaso muyi muyi aure , kallon gefe nayi nace idan munyi auren ka riƙa bani kabeji ? Murmushi yayi yace ke wallahi wannan kabejin nine nakecin shi a yadda kika jishi , babu daɗi ne ? Umm ba daɗi , zaki zaune da Jiddah ? Idan nayi maka laifi saika dakeni a gabanta ? A , a sai mun shiga ɗaki zan zaneki a saman gado kina so ko ? Tsoki nayi zan fita motar ya riƙoni yace An matana yi haƙuri kar kiyi fushi wasa nake miki fa , tafiya zanyi kar Inna ta tashi bana nan , naji zaki tafi amma kalloni , kallonshi nayi yace kin gode ? Ey , idan munyi aure ma idan kika zanu zaki gode ya ƙarasa maganar yanamin kallon tsakiyar fage.....
Fizge hannuna nayi na fita , dariya Dikko yayi yana An mata zo , ban dawo ba yace ki gashemin Mama zan dawo anjima ki ajiyemin abun daɗi kinji ko......? Ban juyo ba kuma ban bashi ansa ba na shige gida , murmushi yayi ya rufe ƙofar da Sultana ta bari buɗe sannan ya wuce , yana tunanin anya bazai bari ya gama aikinshi ba ? Kamar idan ya haɗa An mata da Jiddah zata sha wahala kuma gashi shi ba mazauni ba , wata zuciyar tace kawai cakuɗesu tayi hankali ma........
Mutumin daya kawo ma Sultana sammaci gidan Baba ƙarami ya nufa ,
08/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA....* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 73
Zaune suke ƙofar gida a saman dakali yana korawa Baba Ƙarami bayani cewa Dikko ne ya anshi sammacin daya kaiwa Sultana , gyara zama Baba ƙarami yayi tare da cewa ko shi gwamnan ne da kanshi ya ansa bai shafeshi ba shidai Sultana yake ƙara kuma koshi gwamnan ai yasan gaskiya in banda yarinyar nan ta gaji iskanci har tasan ta yadda zata haɗa wani da wata yayi iskanci ? Duk wannan bai isheta ba gidan da ni kaina ban sanshi ba amma ita taje ta ganoshi ta tattara kaf kuɗaɗen gado kuma tayi ruf da ciki dasu !
Amma kai waye yace maka ta anshi kuɗin gadon naku ne ? Jikar gidanmu ana ce mata Hafsa itace suka zo da wata yarinya ana ce mata Amisty , a saman wannan dakalin suka sameni cewa idan naga Sultana dan girman Allah inyi mata magana tasa a sako mata Dadynta , dana tambayeta abinda ya haɗa Babanta da Sultana sai ta koramin bayani ta kuma ƙara da cewa kuma ta anshi kuɗin amma har yanzu ba'a sako Dadyn ba shin saini in zura mata ido ta cinye duk wa'annan yawan kuɗin a cikinta ?
Kuma iskancin Sultana bai tsaya nan ba saida tabi hanyar da aka lalatamin tarbiyar yarinya , ita kaɗai taji tana ra'ayin iskancinta taje tayi babu wanda ya hanata amma akan me zata gurɓatawa wata da bataji bata gani rayuwa ba ? Abokin firar nashi dai bai sake wata magana ba saidai sauƙi daya nema tare dayi ma Baba ƙarami sallama ya tashi , Baba ƙarami kuma yaci gaba da bunbunai shi ɗaya.
A kwance na samu Inna tana waya da zani ɗaurin ƙirji da alama wanka tayi , gefenta na zauna ina tunanin rayuwar da zanyi a gidan Dikko idan har Allah ya ƙaddara na zama matarshi , zama dani da Jiddah ? Matar data zo har ƙofar gidan ubana suka ɗaukeni sukaje dani sukaci zarafi na ? Mahaifiyar Dikko ta tsaneni babu gaira babu dalili ga Al ' Ameen kuma tunda har mahaifiyar Dikko bata so na tou kuwa taya su "yan uwanshi zasu so ni ne ? Wace irin rayuwa zan fuskata ? Ya za'ayi idan har Jiddah tamin wani abu shin na iya ramawa ? Idan kuma na rama ta faɗawa Dikko ya goyi bayan matarshi ni ina zan saka tawa rayuwar ne ? Tunda dai nayi imani bazai goyi bayan ni bare ba ya yage bayan "yar uwarshi da sukayi auren zuminchie da mahaifiyar Jidda data Dikko uwa ɗaya uba ɗaya shin ya zanyi ne............?
Maganar Inna naji tana cewa ina kikaje ? Nan baya na zagaya na bata amsa dan bana san ina tunanin Dikko ana min magana wallahi , Inna tace ai kin kyauta ni tashi akwai ƙullun koko a palo nima yanzun nan aka kawomin shi yau da maitar koko na tashi a rayuwata saida na samu ƙullun nan hankalina ya kwanta kije ki dama min shi.
Inna ina zan dama miki wani koko ? Nan gidan mana , kinga karmu tsaya ba shari'a wahala ni ban iya ba Allah ya sani kuma Dikko yace yana gaisheki na faÉ—a mishi baki lafiya yace zai dawo anjima kuma a ajiye mishi abun daÉ—i..... Ya zo ne ? Eh , shine nace ina kikaje kika cemin kin zagaya baya ? Tayi maganar tana murmushi , nima murmushin nayi mata amma banyi magana ba.
Tashi tayi ta saka kayanta aka É—an matsa turare aka kashe É—auri ta fita palo , tashi nayi nabi bayanta a saman kujera nasameta zaune tana waya da mijinta , bedroom in na koma na kwanta nasan dai kafin in tashi bacci tasan "yar dibarar da zatayi wanda zamu ci ma cikinmu !
Biye yake da bayan Bello saf da ƙafa har cikin tsakiyar filin tsakar gidanshi , dakel Bello yake tafiya kamar zai kife Ashiru na biye dashi har cikin ɗakinshi , gaban wani ƙato bedsite Bello ya durƙusa a gajiye sannan ya fara ƙoƙarin turashi gefe ɗaya , Ashiru yasa hannu ɗaya ya janyeshi gefe Ashiru na janyewa Bello ya ɗafe wani bargo sai ya janye wani katako wani zurmemen rami ya bayyana mai tsananin duhu da matsakaicin zurfi.
Kwanciya Bello yayi ya zura hannunshi a cikin ramin ya jawo kwalbar kallo ɗaya Ashiru yayiwa kwalbar ya fara kakarin amai saboda yadda zuciyarshi ke tashi da tsikar jikinshi , bayan ya ɗauko ya miƙowa Ashiru yace kai kaci uwaka riƙeta muje , rungume kwalbar Bello yayi suka fita daga gidan.....
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ta faɗa da wata irin ƙara mai tayar da hankali tare da tashi zaune saman tsakiyar gado tana sauke wani irin numfashin wahala , da gudu Inna ta shigo tana lafiya ? Wai , wai , wai tayi tare da goge zufar goshinta tana numfashi a wahalce , ke Sultana lafiya ? Har yanzu numfashin ta bai daidaita ba , Inna tace wai mene ne ? A tsora ce nace wani ne ya biyoni a bacci wai zai kasheni kuma idan inajin wasa idan na tashi naje Qerau yau zanga karuwa ɗaya ta mutu sanadin kwakwale mata idanuwa da yayi kamar yadda ya kwakwale idanuwan Mamy , cikin faɗa da ɗaga murya Inna tace ki koma baccin ki faɗa masa baki kasuwa kuma babu wanda ya isa ya kasheki , ta ƙarasa maganar tana kwantar dani ta lulluɓeni da bargo.
Wayyo Allah Inna da Allah bana so wallahi banayin bacci , cikin hayani tace duk abinda ya cimmiki nasara a bacci a zahiri sai yayi nasara a kanki babu wani maiyi sai Allah haka babu mai rayawa da kashewa idan bashi ba ki faɗa masa baki mutuwa sai kwananki ya ƙare..........................!
Saukowa nayi daga saman gadon jiki a sanyaye nace nidai banajin wani bacci , toilet na shiga na watso ruwa dan inɗanji ƙwarin jikina , ina fitowa ko mai ban shafa ba na zura kayana ina gama sakawa na wuce wurin Inna mukaci abinci tare...
Duk wani mahaluƙin dake anguwar Qerau yau kam yana cikin tashin hankali abu ba'a magana anguwar ta cika faful sakamakon alhinin safkar idanuwan wata matar aure duk inda ka leƙa gida ko bisa santa labarin akeyi bayan an cire idanuwanta aka zo aka yadda ita a saman santa....
Tun asuba aka tsinceta mutanen da suka fito domin zuwa masallaci sallar asuba sune suka fara ganinta dan haka a hankali labari ya fara zagawa cikin anguwa kafin wani lokaci kuma gaba É—aya gari ya É—auka ba'a kaiga kaita asibiti ba tace ga garinku nan ,
Wannan tashin hankali ya zama baƙon al'amari ga mutanen wannan anguwa anyi mutuwa maimakon addu'a ga mamaciyar sai zaƙule²n abinda ya kaita ga afkawa bariki akeyi , ita dai mamaciyar tana da aure da yaranta biyu kuma tana zaman lafiya da mijinta , bakin abinda Allah ya rufa mishi asiri yana riƙe da gidanshi bakin iya gwargwadon karfinshi.
Wannan matar aure dai ta samu damar antayawa a harkar bariki ne sakamakon gurɓatacciyar ƙawa data tsinta a saman yanar giza gizo , mamaciyar ta shiga harkar bariki ne a sakamakon ƙorafi wa ƙawar tata ta hanyar nuna gazawar mijinta a wurin riƙon gidanshi.
Bayan ta tsinci wannan ƙawa a saman iska sun ƙulla alaƙa mai girma ta yadda kowa baya iya ɓoyewa kowa sirrinsa , wani zamani ne wanda Allah ya kawomu wai sai kaga mace a duniyar nan duk abinda taci ko tasha saita ɗaukeshi hoto ta turawa wata , duk ƙawar da kike tare da ita ta fara miki wannan tsire²n na ɗaukar abinci ta turo miki shi ta waya wannan ba ƙawa bace ba maza kija mata layi ba abokiyar tarayya bace ba idan har tanajin ita mai kirkice to ta zobo abinci a kwano ta bada a kawo miki bawai ta turo miki ta waya ki gani ba , kina gani miyanki ya fara tsinkewa saidai ki kalla ki ƙara kallo kina aimu ansha damu mukam mata muka rako wasu sun more duniya muko dai gamu nan rayuwa har yanzu bata canja ba.
Abota ta ƙulle mai girma kowa yana ziyarta ɗan uwansa , yayin da suka shawartar junansu ta hanyar tura saƙo wa junansu ta whatsapp , ita dai mamaciyar tana tura ƙorafin mijinta ne idan yayi mata abu kaɗan , yake "yar uwata ki kwantar da hankalinki yatsun hannunki kawai kika kalla kinsan ba tsawonsu ɗaya ba wani yafi wani wani kuma bai kai wani ba , ita rayuwa bata yuwuwa ace kullum ke abinda kake so shi zaka samu dole , ita rayuwa juyawa takeyi wata rana asha zuma wata rana a lashi maɗaci haka rayuwar take tafiya duk wanda kika gani yana da tashi damuwar idan mai haƙuri ne ya ɓoye sirrin shi wa rayuwarshi da zuciyarshi ke kuma mai surutu jira kike a tara taron sabga biki ko suna duk inda kika zauna harshenki ake ji ke sarki matsalar gidan aure kullum an miki , kuɗin cefanenki bai kai ba , waya aikeki ? Waya sa ki ? Duk namijin da kika gani duniya babu namijin da yake so afi matarshi wanda duk baima iyalinshi ba baya da iko ne , idan ko maƙetacin namiji ne yana dashi ya ƙuntata miki barshi da Allah ja bakinki kiyi shiru ki lulluɓe aibin mijinki sai Allah ya lulluɓe miki naki....
Bayan ƙawance yayi girma ta waya sai aka fara ziyartar juna , mai mutuwa itace ta fara zuwa gidan rayayya tare da yaranta dan sada zuminci an tareta da shagali mai girma ta hanyar tara mata abubuwan motsa baki na zamani irin wanda bata taɓa ci ko sha a rayuwarta ba , an yini ana fira kowa yana faɗar irin rayuwar da yakeyi a gidan aure , yayin da ita wacce akaje gidanta take faɗo nata nasarorin rayuwar , mai mutuwa kuma ta hankaɗe zuciyarta taci gaba da tona asirin mijinta ta hanyar nuna gazawarshi wurin riƙon gida , bayan ta tashi tafiya ita wacce akaje gidanta ta shiga store ta ɗan tattaro mata kayan abinci ɗanye , irinsu shinkafa , taliya , makaroni , cuscus da dai sauransu ta haɗa mata da ɗan kuɗi bayan ta haɗa mata da kwancen kayan sawa....
Bayan an kwana biyu ƙawa tace itama zata zo , dan haka mai mutuwa ta hana ma kanta zaman lafiya ta faɗa maƙota neman rancen kuɗi wai ƙawarta zata zo bata so tazo ta raina mata , haka dai tayi ta faɗawa maƙota tana neman rance harta samo tazo itama ta haɗa irin tata ƙaryar , bayan ƙawa tazo ana fira ne tace mata amma yadda kike faɗar talaucin mijin naki kamar bai kai ba gashi komai na gani babu dai wata damuwa , hmmm "yar maular saita buɗe baki taci gaba da sana'ar nata tunda taga idan ta faɗi damuwarta kuɗi ake bata dan haka tace tou duk wannan da kika gani bashi na ciwo kuɗin a maƙota dan in fita kunyarki kindai san hausawa sunce abokin cin mushe ba'a nuna mishi wuƙa , taci gaba da ɗimi faɗi ba'a tambayeta ba , amma ni a gani na wasu matan sunayin "yar sana'a haka a gida dan su taimakawa mazajensu da abinda suka gagara yi musu.
Da ƙawa ta tashi tafiya taba mamaciya kuɗin da suka gigita mata lissafi tace ta biya bashin da ake binta ita kuma tayi ta zabga , haka dai akaci gaba da abota rayayya tana taimakon matacciya sosai , ganin ana yi mata hauka da kuɗi yasa ta gaji ta tambayeta kodai tana kasuwanci ne ? Tace bata kasuwanci bata siyar da fari ko baƙi tana da abokai ne dai masu taimakonta a waje , ta nemi ƙarin bayani aka bata sirrin abun dan haka babu wani tunani ko hangen abinda zaije ya dawo itama ta yanki kati ta faɗa harkar bariki yanzu yau wa gari ya waya.........?
Bello rungume yake da kwalba har suka iso inda aka ajiyesu ake basu horo , Ashiru kasa taɓa kwalbar yayi ya barta a hannun Bello yadai faɗawa mai gida sunje sun dawo , mai gida yace kawai yaje abunshi.....
Bayan sati É—aya
Dikko yazo gidanmu a ranar da yace zai dawo kuma ciki ya shiga Inna da kanta ta lallaɓa ta nema masa abun daɗi kamar yadda ya faɗamin kuma yaci naji daɗi , daya zo kuma ya tanbayeni akan yadda akayi na saka Safiyya karuwanci nace ni babu ruwana kawai dai naji haushi ne sunamin gori na zama karuwa ranar da na rabu dashi a hanyarmu ta komawa makaranta mukayi faɗa na dawo gida ranar da suka ganni shine sukayi ta tura yaransu gida wai ga karuwa nan karna ɓata musu tarbiyar yara abin yamin ciwo shine na faɗawa Aunty Mamy daga nan bansan yadda akayi ba ,
Dikko yamin faÉ—a sosai kamar zai dakeni dan harsai da Inna ta kirani a waya dan a palo muke tana bedroom , ta tambayeni abinda ya haÉ—amu ban faÉ—a mata ba dan har Dikko yazo ya tafi Inna bata fito ba ,
A ranar ya sauke hidima wa Inna yayi jib da kwano na kuɗin da wallahi saida Inna ta ruɗe data gansu danni dama kyauta ta da Dikko biyu ce daga kuɗin daya bani a makaranta sai wanda ya sakomin a mota nasha mai da Umar ya kawomin wacce Al ' ameen ya ansa aka bawa Jiddah ita take hawa , sai kuɗin daya bani a ƙofar gidanmu ban ansa ba , ranar kam saida ya gigita Inna yasa mata mantuwar dole da manya kuɗaɗe a palo ya ɓaresu saman kujera ni kuma yayi fushi dani yai tafiyarshi saboda na haɗa Safiyya anyi iskanci da ita da baban Mardiyya duk da nace bani bace yace ba abinda ya dameshi bashi naci zamu bayan aure.
A ɓangarensu Bello kuma bai saki Dady ba amma tunda Momy tayi magana yasa aka sassauta bala'en da ake musu , an canja musu wurin zama ana basu abinci mai kyau shi Dady kuɗi kawai zai bayar ya kama gabanshi amma yace yana jiran wasu kuɗaɗe ne suzo saiya bayar ,
Tun washe garin ranar da aka É—auko kwalba Dikko yasa aka tara manyan malamai yayi musu bayanin abinda yake so na za'ayi masa saukar al'qur'ani sau goma a rana har tsawon kwanaki talatin , tou an buÉ—e kwalba kamar yadda Bello yace malamai kuma suka ci gaba da sauka kuma ragunann nan goma duk ranar duniya idan akayi sauka haka ake yankesu ana raba naman sadaka.
Ranar da ya kama zuwa kotu banje ba lawyer Dikko ya tura bayan ya faɗa masa yadda kuɗi yake , idan kuma an gama shari'ar yana ƙarar baba ƙarami akan ƙazafin da yayi ma matarsa kuji wani neman rikici da rashin san zaman lafiya na Dikko kuma........!
Maganar Bello daya faɗa shine ya kashe Binna da kanshi nayi amfani da wata magana daya faɗamin a police station cewa , inji tsoron Allah in babu nan akwai ranar hisabi duk wanda yaci zalin wani dai² da ƙwayar zarra ubangiji bazai barshi ba , ki daina ganin kin samu dama ta taƙin lokaci yasa ki manta da rayuwar gaba , karki biyewa zuciya ki kafa abinda zaisa kiyi nadama wata rana , tunda har yayi imani da ranar hisabi bazan bar akashe Bello ba zamu haɗu ranar hisabin dani dashi da *BA BINNA* wannan shari'ar Allah kaɗai zaiyi ta.......
Hafsa kuwa tana tsaye wurin ganin ta gano inda kakar Ba Binna take kuma ta faɗawa Hajiya cewa idan harta ganosu saita faɗa musu itace silar mutuwar "yar su kuma tana roƙo Allah yasa masu zuciyane su kasheta kowa ya huta mai baƙin halin masifa kamar zuciyar fir'auna.
Tunda nayi mafarkin an kashe wata matar aure a Qerau ban sake ganin mutumin a bacci ba kuma ban faÉ—awa Dikko ba ,
Dikko ya riƙo wuta sosai ya matse lamba wa Dady a tura gidansu An mata , Dady yace tou kadai ga yadda Mom inka take hawa da rana ɗaya bata sauko ba abun nata kullum gaba yakeyi akan bata yadda ka auri yarinyar nan ba , Dikko yace Dady nayi nisa fa za'a samu matsala Dady yace yanzu ya kake so ayi ? Ka tura "yan uwanka kawai su an somin auren ta babu wanda yaji babu wanda ya gani ,
Idan kuma bayan anyi auren matsala ta shigo fa ? Babu damuwa Dady ni zanji da duk wata matsala , shiru Dady yayi yana nazari sannan yace daga neman aure idan abun ya warware ba'a É—aura ba fa ? Dikko yace babu maganar neman aure kawai É—aura aure za'ayi daga nan sai ayi duk wadda za'ayi , tou ina zaka ajiyeta Babana ? G R A tare da Jiddah , Babana yarinyar nan bata iya zama da Jiddah gaskiya , Dady nidai tare zasu zauna Allah ya bada sa'a kawai zakace , murmushi Dady yayi tare da cewa Allah ya tabbatar da alkairi Dikko ya ansa da amin tare da faÉ—a masa ranar juma'a ne , Dady yace Allah ya kaimu zai tafi da Momy ta rakashi ganin likita kafin su dawo anyi komai an gama...........
Dikko da kanshi yazo ya samu Inna sukayi magana yau duk laɓe²nta saida ya ganta kuma ya faɗa mata cewa ya tsaida ranar aurenshi da An mata ranar juma'a saura kwana 8 daga yau kenan , Inna tace ita gaskiya kwana 8 yayi mata kusa² tana da hidima sosai , Dikko yace shi baya buƙatar wuce wannan lokacin , kuma wane hidima gareta ta manta da yanzu An mata tayi aure da Sultan ? Ko sai nashi ne za'ace yazo da wuri ? Kodai har yanzu bata daina fushi dashi ba ? Shiru Inna tayi bata bashi ansa ba , saida ya ƙari maganarshi ya tashi yauma kuɗi ya safke mata na mamaki mai nuni da ko rashin kuɗi yasa kwana 8 yayi mata kusa² , baima saurareni ba kuma dana gaishi bai ansa ba.
Bayan tafiyar Dikko Inna ta shige ɗaki ta kira ƙawarta suka tattauna dan ita Inna kallon ɗan duniya take ma Dikko shi yasa ta fara neman hanyar da zata gyara "yarta gani take wannan hanyar itace mafita....
Da mijinta yazo ta rattafa mishi auren Sultana yau saura kwana 8 aurenta , waishi ba'a kyauta mishi ba ya za'ayi masa haka abu babu notice tace yayi haƙuri , kuma daya tambayeta wanda Sultana zata aura aure haka kwatsam , cewa tayi sunanshi Muhammadu , waye ubanshi kuma sun bincika halinsa har zata ɗauki Sultana ga baƙon fuska ta bayar tayi mata aure haka kamar ta gaji da ita ? Inna tace sanin ubanshi halinshi da komai nashi sa fuskanci juna idan anyi auren ,
Inna ranar jinta takeyi kamar ba ita ba , tana cikin farin ciki mara musultuwa cikin ƙanƙanin lokaci gidanta ya cika da taron ƙawayenta ƙasaitattun mata masuji da kansu a gidan aure tou wai ita Inna ina ma ta samu wa'anan ƙwanƙwasashin mata ? Suke ta huɗɗinsu Inna ta faɗa musu Sultana Dikko zata aura , amma bansan abinda yasa ta ɓoyewa mijinta ba ,
Bayan kwana biyu yadda Dikko yasa aka haukata gidanshi yasa Jiddah ta gane aure zaiyi dan haka ta fara ɓarin kaya tana ta hauka tana zage² gaba ɗaya ta tashi hankalin duk wani wanda yake da dalilin sanin Dikko zai aure , tou ai babu mai iya tunkarar Dikko da zancen dakatar da aure sai Momy kuma bata nan Dady yajata sunyi tafiya dan Dikko yayi hidimarshi ya gama saida tazo ta samu amarya ,
Jiddah bata gama tabbatar da Dikko zaiyi aure ba saida taga katin ɗaurin aure kuma Umar ne ya kawo mata shi , Dikko yana kwance yana bacci ta shigo ɗakin da gudu bayan Mardiyya ta tunzurota ta shigo tana ta ɓarke²n zagi tana aibata shi san ranta bai mata magana ba yayi kamar bacci yake dan yasan zafin da raɗaɗin da mata keji yayin da za'a musu abiyar zama , ya gani yadda Yayarshi tayi da akayi mata abiyar zama aurenta kamar zai rabu dan Momy ɗaure mata ƙugu tayi ta dawo gida , ba abinda zaice ma Jiddah tayi duk haukanta kila haka zaisa ta samu natsuwa idan kuma tayi ƙoƙarin keta iyaka zai nuna mata nashi haukan sai yayi mata dukan da har ya gama auren tana saman gadon asibiti saboda shi abu ƙalilin ke ƙufular dashi.......!
10/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA....* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 74
Yaye bargon da yake lulluɓe tayi taci gaba kuka tana ɓarke²n zagi tana ma Dikko gori wai yaji kunya ya rasa wacce zai aura sai karuwa ɗiyar ɗan caca jahila matalautan da suka kasa siyen gidan zama saidai gidan haya ai duk talaucin da yasa mutum ya rasa gidan zama wannan talaucin ya kai abun a duba matsiyatan banza da wofi ,
Me yake nema a wurin yarinyar nan ? Bayan ita tafi ta komai kuma su masu kuɗi gidansu Sultana fa ? Duk abinda ake nema ga mace Sultana basu da , duk abinda ya cancanta ka aureta saboda shi babu ko ɗaya da take dashi , jahila daƙiƙiya mace babu ilimi ai kwankwon ashana ce domin shi ilimi tushe ne mai nuna dogon zango , kaga tun nan abinda kake nema baka samu ba , halin kwarai jari ne , bata dashi , su kuma kuɗi jigone masu nuna isashshen iko a cikin abunda na lissafo wane take dashi ?
Ai ni ina da duk abinda kika lissafo ko ? Ai kaine kake dashi ba ita ba , to na bata ilimina na bata halina na bata duk komai nawa ke kinsan An mata kuwa ? Ki bari tun kafin raina ya ɓaci na fara maganganun da zakiji babu daɗi dan haka ki tattara mutuncinki ki barmin ɗakina !
Bana tafiya sai kayi maganganu akanta munafikin banza maci amana , murmushi Dikko yayi cewa nine munafiki Jiddah ? Maci amana ? Wace irin amana ne naci haka da har kikemin gori ? Ban sani ba baƙin munafiki , sauka yayi daga saman gado yana cewa Allah ya baki lafiya ya wuce toilet , ita kuma taci gaba da ɓaɓɓarka mishi zagi harya gama abinda yake ya fito Jiddah bata daina sokawa Dikko zagi ba.
Inda take tsaye yaje ya riƙota cikin rarrashi yace ni ne ? Kwantar da fuskarta tayi saman ƙirjinshi tana kuka cikin shashshekar kuka tace Yaya dan Allah bana san auren nan , tou muje saman gado saiki faɗamin kinsan ban cika jin magana daga tsaye ba , ni bazan hau gado ba , tou tunda bazaki hau ba fitarmin daga ɗaki idan ba haka ba zan hau dake dole kuma jikinki zai baki labari , da sauri ta sauka daga jikinshi tayi waje da gudu tana kuka , murmushi Dikko yayi yace matsoraciya.
Saman gado ta faɗa taci gaba da kuka a zuciyarta kuma jinjina irin muguntar Dikko takeyi macuci idan har yana jin haushin mace sai yayi mata ƙeta mamugunci nufinshi yashata basilla murmushin mugunta Jiddah tayi a zuciyarta tace badai Yaya bane ba ? Kije kin samu Sultana idan dai tsintuwar fatalwa riba ne.....
Inna da kanta taje ta faɗawa Kaka Sultana zatayi aure Kaka tayi murna sosai kuma tayi ma Inna da Sultana fatan alkairi , ta kuma ƙara da cewa amma me yasa saida aure ya rage kwana 6 zata faɗa mata ? Inna tace mijin ne ya zaɓi haka , Yayarta dage zaune tana saurarensu tace badai girin² ba tai mai , Inna ta gane ta maso habaici maso faɗa wanda ya tanka shi yafi tou bata da lokacinta ,
Tunda Dikko yazo ya tsayar da ranar aurenmu dani dashi bai sake dawowa gidanmu ba kuma kona kirashi waya ya daina ɗauka ma , Inna kuwa kullum bata da aiki sai kwaɓe²n kayan mata tana bankamin saidai tsareni tana zagina wani lokaci hada mari wai bana gane wannan gata ne sai naje gidan aure , tun ina sha ina amai har cikina ya haƙura ya riƙa riƙeminshi dan idan zansha so goma na amayar Inna bata gajiya zata sake kwaɓa masifa ta bani na kwankwaɗar wa cikina.
Labarin auren Dikko ya zaga kaf illahirin birnin garin katsina mutane sun fara canfashi ya cika aure² ya auri waccan ta mutu bai tsaya hutawa ba ya auro wannan duka yaushe yayi auren har yake tunanin sake auro wato ? Yayin da wasu kuma suke gani izzar kuɗi ce ke nuna ikonta shi yasa yana matashin shi zai aje mata biyu cikin shekara ɗaya....
Dikko kuwa babu abinda ya dameshi da labarin dake yawo a gari shidai zaiyi , tunda ya taho kuma yaga mai tareshi matsalar bai faÉ—a ba zaiyi amma da zaran ya yanke hukunci tou fa ko kanshi baya saurara ,
Duk "yan uwan Inna dasu ake hidima kuma hada yayarta kwansu da kwalkwata suna zuwa ba wanda aka rage tun bayan tsaida ranar auren da kwana biyu suka fara zuwa , kowa tambayar Inna yake tou ina maganar kayan É—aki ? Saidai tace komai za'ayi , a kwana biyar za'ayi ? Inna tace Eh ,
Tou basu sani ba kayan É—aki kansu da kayan kicin duk abinda iyaye kema "ya "yansu dan fitar dasu kunya Dikko yayi saboda tunda ya fara aikin gidanshi na goruba inda zai ajiyeni daga farko dama shine yake da burin zuba komai na gida tou kayan nan yasa aka sauke su a wani gidan mijin Inna sai idan za'aje jere Inna tasa aje a É—auka a can yadda za'ace itace tayi.
Komai dai na hidimar auren nan cikin munafurci akeyinshi , dan ko lefe Dikko ne ya kawoshi da kanshi da daddare misalin 2:54am dashi da yaranshi bansan sunzo ba haka kuma banji tafiyarsu ba , saida safe na tashi naga wasu irin lafiyayyin akwatina masu tsinannen tsada da kyau na tashin hankali , akwatina 24 da wasu irin ƙattin jikkuna biyar babu wanda ba'a takeshi da kaya ba , wannan shine faɗawa mai zuciya biki ba mai tarin dukiya ba tou Dikko komai ya haɗa , nidai ban buɗe ba amma da Inna da mijinta saida suka zindire lefen nan kaf suka ganshi gaskiya naira wurin lefen nan taci bugu harta gode Allah wallahi komai na cikin lefen abun burgewa ne babu abu na banza komai baka isa ka raina ba saidai hassada.
Ƙawayen Inna "yan duniya lokacin da suka zo suka ga lefe sunyi ɓarin maganganu na isashshin mata wai Dikko dai ɗan gaye ne wayayye tebirin farko wallahi magana ya gayamin a lefe turaruka kamar suce wayyo Allah masu tsada abinda dai Dikko ke nufi yana san ƙamshi , wuraren daya kamata nayi amfani da turare suke faɗa duk abinda suka ɗaga a lefen sai sun faɗa fita nayi na bar musu ɗakin dan abinda na lura basu da kunya.....
Washe garin da aka kawo lefe akaje ganin ɗaki Jiddah tayi wulaƙanci tayi hauka marar ɗaura zani tayi bala'en daya tada hankalin duk wanda yaje ganin ɗaki Jiddah tace babu wata mace data isa ta zauna mata gida , wallahi wannan gidan tane daga ita sai mijinta , Dikko nata ne ita ɗaya babu maishi sai ita gidanta ramin kura ne daga ita sai jama'arta sai kuma "ya "yanta babu wata banzar ɗiyar ɗan caca data isa ta zauna mata da mijinta amma idan har Sultana ta shirya mutuwa ta shigo gaba ɗaya ma auren mamarta akayi wallahi , amma idan har Caca ta shigo zata goga da ita a kishi tou tabbas tana musu albishir kwanaki bakwai cas ta bawa Caca a gidanta zata dawo babu jimawa idan tana da sauran shan ruwa gaba kenan idan kuma bata dashi su tarbata a rimin badawa , sunan wata maƙabarta ne...........
Ta bubbugi ƙofofi ta rufesu ta hana ganin ɗaki tayi maganganu masu tsauri kuma kalamanta suna da kaushi ta fa barbaɗa rashin mutunci iyakar ƙarfinta guyawu a sace "yan ganin ɗaki suka dawo ba tare da sun samu damar ganin ɗaki ba , Inna da taji bayani kuwa cewa tayi to saidai ya raba musu gida , Inna ta yaba da masifar Jiddah baza ta yadda a haɗe Sultana da Jiddah ba dan cutar mata ɗiya za'ayi idan kuwa Dikko bazai raba musu gida ba ta yadda saidai a fasa auren nan, da ƙawayenta suka bata haƙuri cewa tayi har Sultana ma nawa take ? Ta gama haɗiye wani dafin zata fara kwankwaɗar na kishiya ? Masifa nawa zatasha ? Bazata laminta ba gara tasan abinyi tun kafin tabar nigeria idan zai yuwuwu ayi idan bayayi a barshi kowa ya samu natsuwa babu wanda zaisa ma "yarta ciwon zuciya........
Da daddare bayan kowa ya kama gabanshi Inna tayi ma Dikko waya tana san ganinshi , yace mata baya nan yaje kaduna amma yana shigowa katsina babu jimawa idan ya dawo zaizo insha Allah , fatan isowa lafiya tayi masa ta kashe wayarta , kallona tayi tace idan kin ga dama ki tashi kije kiyi wanka kin zauna bursunai² dake kamar an ƙwatoki bakin kura , ban kalleta ba nace ai ko ɗazu nayi wanka , dan ubanki yanzu ma sai kin ƙara wani , ai Dikko dai kike so ko ? Badai kin zaɓeshi ba ? Yanzu kika fara wanka tunda dai kina san Dikko kije kinsamu , Dikko da kike ganinshi ƙyalƙyal na rariya ne zamani ne da kanshi idan zaki iya ga fili ga mai doki , tun cikin mutunci nace ki rufawa kanki asiri ki auri Sultan kikaje kikayi ta hauka tun ina nida ke saida kika ɗaga murya aka jiyoki uwayen sharri suka kira ubanshi a waya suka faɗa mishi bakya san ɗansa sun nemi sharrin duniya sun ɗora miki hankalinsu bai kwanta ba saida suka ga an fasa auren nan , hmmm Dikko dai ko ? Bazan miki baki ba.
Da kin auri ɗan uwanki asiri a rufe babu wanda yaji ya gani amma dake ke sakarya ce baki san wanda yake sanki ba kin biyewa ƙuruciya da san zuciya ga yadda ta kaiki Caca ma take kiranki tsabar ta maidake jaka ta ƙarshen benci iskanci da rashin kunya kuma duk garin nan ba na gaba da Dikko , "yar uwarshi ce can zaki musu iskanci su haɗe miki kai suci ubanki nidai bazan fasa tafiya ba , india ba fashi wallahi saina bi mijina zan baki makullin gida idan bai miki daɗi ba kizo ki buɗe ki shiga ko ki tafi wurin ahalin ubanki gidan Hajiya dai yai miki tsururu cikin hayani tace ki tashi daga gabana in daina ganinki , da sauri na miƙe zan fita tace baza kije kiyi wanka ba ? Jiki a sanyaye na dawo na wuce ciki danyin wanka !
Cike da damuwa Inna ta miƙe taje ta nemi wasu magunguna ta damesu da madara tana damawa tana mita Dikko ɗan duniya idan ba'ayi shirin tashin bama²i ba ai za'aji babu daɗi , Inna a ganinta wannan shine mafita ta mayar da cikin Sultana kamar wata tsohuwar rijiya duk abinda ta kwaso a cikinta take juyewa saboda wannan garinka da take bankawa "yarta abinci ma kwata² ya daina ciwowa gareta , wata "yar duniyar ƙawar Inna kuwa ke dafo wata munafikar kaza wacce ba'acinta ma sai an kashe fitila kamar kazar tsafi , Sultana tabi ta rame ta ƙanƙance saboda masifar Inna da magunguna idan ma tace bata sha haka zata rufe ta da masifa sai tasha a karkaɗe kofi ,
Ina fitowa daga wanka na hango Inna zaune gefen gado da ƙofinta riƙe a hannu , gabanta kuma kaskon garwashi ne , a takure nake tahowa dan ida bayyana a cikin ɗaki a tsawace tace min kiyi tafiya kamar kina da rai garwashin nan zai siƙe kuma kin sani sarai dakel aka samomin shi tunda gabanki nake ta nemansa tun safe , Inna shi kuma wannan ɗin na mene ne ? Na ubanki ne , tayi maganar tana kunce haɓar zaninta ta ciro wata "yar farar leda ta kwance tana ki wuto kizo ki duƙa nan , matsawa nayi kusa da ita nayi yadda ta nunamin ita kuma ta zazzage abinda yake cikin ledar duƙa tana cewa da kinsan ko nawa na siya saikin yaba ma ƙoƙarina , ko inda take ban kalla ba haka kuma ban bata amsa ba har ta uwarce ni dana tashi , tashi nayi ta miƙomin kofin ansa nayi nasha ta zuba ruwa na girgije na haɗiye , ɗaukar kwaskon tayi da kofin ta fita ni kuma na ɗauki kayana na saka na kwanta dan bacci nakeji bana wasa ba.
Tana fita ɗakin mijinta ta wuce bayan ta ajiye kayan data fita dasu a kicin , ni kuma naci gaba da baccina , saida Dikko yayo mata waya yazo ta shigo dan taga ko na shirya ta ganni kwance ina bacci , cikin takaici ta tasheni bayan na tashi tace shine kinyi wanka ki iya ki shirya kika wani kwanta bacci ? Ƙara takurewa nayi da niyar komawa bacci tace ki tashi idan kin ga dama ki gyara jikinki kafin in gama magana dashi yana ƙofar gida , cike da farin ciki na sauko daga saman gado Inna kuma ta koma palo tana jiran shigowar Dikko....
Fuskata na wanke da bakina na fito , lokacin har Dikko ya shigo kuma Inna ta ratta mishi cewa saidai fa ya raba mana gida dan bazata yadda ba ɗiyarta tayi rayuwar takura , sundai yi maganarsu sun gama abinda dai naji Dikko yana bata haƙuri cewa shi babu macen data fi ƙarfinshi kuma gidanshi bai gagareshi yayi hukunci ba , inda yaso ya ajiye An mata bai gama aiki ba zaman na wani lokaci ne zasuyi kuma wani abu mara kyau bazai faru ba , Inna tace tou kai dole sai kayi auren ne yanzu ? Dikko yace ba dole bane ba lokaci ne yayi tunda ai ba yau naso muyi auren ba , Inna tace to gaskiya saidai ka bari idan ka gama aikin gidan sannan , mijinta ne yace ba'ayin haka idan bashi da ikon raba musu gidan ya zakiyi kenan ? Sai a fasa auren , ki daina haka ki musu fatan alkairi da addu'ar zaman lafiya , ba haka Inna taso ba dan na fahimci bata san gardama da mijinta , bayan sun gama ne suka shigo cikin bedroom in ita da mijinta , Inna tacemin kije ku gaisa farin ciki fal zuciyata na tun kari hanyar fita , zan fita daga cikin bedroom in naji mijin Inna yana cewa wai ba DK bane ba ? Inna tace waye kuma DK ? Bawan Allah cikin dai kokonto yace ba shi bane ba kamarsu dai tayi yawa wallahi shi wancan wanda nake magana bana tunanin ma zaizo nan , bata bashi ansa ba kuma sai suka rangaɗo suka biyo bayana suka fita daga ɗakin mijin Inna kuma yana ƙara kallon Dikko.
Cike da farin ciki na isa wurin Dikko na rumgumeshi rabon da in ganshi ko inji muryarshi harna manta nayi faraicin lallausan jikinshi mai kama da bayan zomo , maimakon yaji daɗi ko yayi fara'a sai yace ke kullum sai kin hawomin jiki kamar wata mage ina dai lissafi kuma da guda² duk saina rama , gyara kwanciyata nayi saman jikinshi saida naja gemunshi sannan nace yanzu ma ka rama mana nayi maganar ina kallon cikin idonshi , murmushi duniyanci yayi cewa a , a ni na isa inzo har gidanku in rama abinda kikai min ? Zaki isko ni har gida saurin me kike ne ? Murmushi nayi ba tare da na sake magana ba , shi kuma yace meya sameki naji kin rage nauhi , da nayi niyar faɗa mishi abinda Inna takeyi amma sai wata zuciyar ta haneni kuma gaskiya dai idan ba'ayi hankali ba saina faɗa mishi abinda akemin !
Shi kuma a ranshi tunani yakeyi kila fa itama An mata anayi mata irin abinda ake ma "yan gidansu idan za'ayi musu aure , jinjina kanshi yayi tare da cewa Allah ya sawaƙe idan kuwa anyi mata cutar yarinyar nan zaiyi da yawa , An mata kawo kunnenki in tambayeki , matsawa nayi tare da miƙa kunne ne saitin bakinshi cikin raɗa yace naji kin rage nauhi meya sameki ne ? Wata irin kasala naji ta lulluɓemin jiki na ƙara kwanciya sosai a lallausan jikinshi ban bashi ansa ba
Shi kuma yaci gaba da cewa Mama take baki wani abu ko ? Kaina na ɗaga mishi alamar Eh , ɗago fuskata yayi idanuwanmu suna kallon cikin idon juna yace ai na sani hada kaza ko ? Shiru nayi ban bashi ansa ba , yace ai mu na gidanmu ina kallonsu wallahi hada tattabaru ake basu mutum yazo ya kasa cin abinci nasan kema hada irinsu ake baki ai ni gaskiya wannan shigamin haƙƙin rayuwa akayi gaki an takura miki an ramar min dake babu gaira babu dalili saboda ɗaukar alhaki , ni babu wata kaza da nake ci , hmmm haba An mata aiko baki faɗa nasan komai miye baƙona a mata ? Ya fara lissafe²n kayan mata kamar wata tsohuwar karuwa bayan ya gama yace sune baƙin nawa duk abinda na faɗa nasan aikinshi idan baki sani ba , Allah dai ya sawaƙe ya kuma kyauta wahala saukar min daga jiki karki shanye daɗin ke ɗaya....
Murmushi nayi sannan na tashi na koma saman hannun kujerar da yake na zauna , mukaci gaba da firar duniya bana soyayya ba yana bani labarin abokin Yazeed da aka kama yace wallahi An mata fitinar zamanin nan yana bani al'ajabi saboda tsabar ƙazanta kina matar aure dan karnikanci kinabin mazan waje , ni na rantse da Allah da nine mijin idan nasa an kamashi Allah ya tsinemin , dariya yayi sannan yace dama ya sani yana riƙe banza yayi masa irin yadda akayi ma Saminu ya fashe idon dake ganin matan , nidai da nine ƙarya mishi wuya kawai zanyi ya mutu a rage annoba a ƙasa , dariya yayi yana kallona yace kiyi dariya mana , ƙinyin dariyar nayi kuma ban kalleshi ba , taɓoni yayi cewa An mata miye ? Ai kai dama baka iya komai ba daga duka sai kalmar kisa shikenan abinda ka iya faɗa , ke karfa ki raina min hankali , daga haka fira ya koma rigima wai wannan "yar maganar harya ɓatawa Dikko zuciya ni kuma bada wani manufa nayi maganar ba , tsoki yayi tare da miƙewa cikin ɓacin rai ya tunkari hanyar fita ,
Binshi nayi da ido harya fita daga palon , saida ya fita na tashi nabi bayanshi har ƙofar gida amma banyi mishi magana ba , ina fitowa duk su Ashiru suka gaisheni cikin girmamawa kaɗan na ansa gaisuwar nabi Dikko da aka buɗewa mota kafin a rufe na riƙe murfin motar nace kayi haƙuri idan kaji babu daɗi insha Allah bazan sake ba , ba tare daya kalleni ba yace na yafe miki , yawwa ngode na bashi ansa sannan na juyo da sauri na dawo cikin gida , murmushi Dikko yayi yace kura ta fara lafiya yau wace rana bata biye an tashi hankali ba , murmushi ya sakeyi tare da kwaikwayon maganar Sultana wai da haka zatace naje nace mahaukaci aljannu kamar iccen tsamiya ! Hmm jarumata kenan..... Ina komawa kwanciyata nayi naci gaba da baccina dan yau su Hajiya Inna ba'a ɗakin za'a kwana ba...
Inna da mijinta kuwa bayan sun fita daga palo mijinta ya tabbatar da Dikko ne dan haka yace ma Inna wane gigi ya kaita ? Shidai babu ruwanshi tunda dama tun farko ta ɓoye mishi wanda Sultana zata aura Dikko dai ba kanwar lasa bane ba , amma yana musu addu'ar zaman lafiya kuma bazaiyi binciken inda Sultana da Dikko suka haɗu ba tunda dama ba'a so ya sani.......
Duk iskancin da Jiddah ta zaƙula ma "yan ganin ɗaki bai isheta ba Mardiyya ta tirota tace idan ta saki ta tsaya sanya za'ayi babu ita ta tadawa Dikko hankali a daren nan ta hana mishi bacci , shi kuma a gajiye ya fito daga toilet ɗaure da rigar wanka a jikinshi dan baya buƙatar komai a halin yanzu sai bacci , da masifa Jiddah ta shigo ɗakin kallo ɗaya Dikko yayi mata ya ɗauke idonshi daga kanta ya matsa inda ya ajiye kayanshi na jersey ya ɗauka ya saka ,
Jikin socket ya matsa da niyar kashe fitila ta riƙe mishi hannu , kallon hannu yayi sannan ya kalli Jiddah na tsawon minti ɗaya yasa hannun haggunshi ya kashe fitilar ya koma saman gado ya kwanta , yana kwanciya ta kunna fitilar , jinjina kanshi yayi sannan ya sauko yazo ya kashe fitilar a karo na biyu , saida ta sake tabbatar daya kwanta ta sake kunna fitilar yanzu bai sauko ba yace kasheta , bazan kashe ba , ki kasheta nace , bazan kashe ba nace maka , rufe idanuwanshi yayi sannan yace ke........ Ki kashemin fitila nace , a ɗan tsorace Jidda tace bazan kashe ba , cikin wata irin murya Dikko yace na rantse da girman Allah idan har kika bari na sauko daga gadon nan wallahi saina takaita miki rayuwa zuwa ɗaya zan miki na tasheki aiki har abadan duniya , da sauri Jiddah ta kashe fitila tayi waje da gudu tana kuka....
Tsoki Dikko yayi tare da ɗaukar wayarshi ya fara kiran An mata , saida ya kirani so biyu ana 3n naji cikin faɗa yace wai ke An mata sai inta kiranki sai kin gama iskancinki zaki ɗauki waya , a sanyaye nace kayi haƙuri bacci nakeyi , nine baccin , kayi haƙuri bazanyi haƙurin ba duk kina nufin bakiji ina kiranki ba sai yanzu munafurci kawai , cikin ɓacin rai nace kai Dikko kaima munafurci , murmushi yayi sannan ya ɗaga idonshi dakel saboda baccin da yakeji yace nine munafurcin ko ? Haba kaima wallahi neman fitina gareka , tou yi haƙuri An matana raina ne ya ɓaci kuma bacci nakeji na fiso inyi bacci dake a raina kiyi haƙuri don Allah idan dake ne zanyi bacci idan bake bace wallahi bana iya bacci raina zaiyi ta ɓaci a banza kiyi haƙuri mu raba ɓacin ran kin yafemin ko ya ƙarasa maganar yana jan wani irin numfashi mai ɗauke tunani yace muyi bacci mai daɗi ki ga Dikko a baccinki jarumata ,
Shiru nayi banyi magana , a kasalance ya kira An mata cewa meye ? Dakel na haɗiye miyan bakina banyi magana ba har yanzu , An mata.... ? Na'am , Dikko ne ? Umm tou yi haƙuri kinji zanyi bacci na gaji saida safe ya kashe wayarshi , yana kashe wayarshi yaci gaba da baccinshi cikin natsuwa da kwanciyar hankali saɓanin Sultana da bacci ya gagari idonta ,
Dikko baida adalci gaskiya shi kanshi kawai ya sani , matarshi ta ɓata mishi rai akan me zai kira wata da bataji ta gani ba kuma bata san anyi ba ? Ita Jiddah me yasa bayacin ubanta yadda yake ma Sultana ? Danni nayi imani da Sultana ce ta kashe fitilar nan wallahi sai Dikko ya zaneta , amma ita Jiddah sai tayi kwance² ta ɗana iskancin ta amma Dikko baya zane mata jiki irin yadda yake ma Sultana me ne ne dalili ? Shin san Jiddah yafi ko kuwa .....?
Ranar da akaje jere ma Jiddah ta ɓara iskanci wanda yafi wanda tayi ranar ganin ɗaki , ta tara ƙawayenta ƙosashshin "yan iska kuɗin mota ta turama ko wace har naira dubu ɗari wai suzo su tayata tarar kishiya sun cika gidan ba masaka tsinke sai iskancin suke zazzagawa wallahi zaman jere bai yuwu wurin mata ba maza ne kaɗai suka tsaya dan kayan na ɗaurawa ne kunga kenan ba aikin mata bane na maza ne , ko iri ɗan tukuicin nan da ake badawa na jere duk Jiddah ta murjeshi ta hana , dama na ganin ɗaki ma bata basu ba , kai Jiddah riƙaƙƙar "yar iska ce mai tikiti lallai Dikko ya ɗauki alhakin Sultana da zai haɗata zama da Jiddah.......
Bayan tafiyar matan suka faɗa kicin ita da ƙawayenta wai wannan kulolin da duk wani abu da aka saka mata yafi ƙarfin sayen ɗan caca dan haka tasa suka kwashe duk abinda take so aka kai kicin inta , ita kuma Mardiyya an tsaida ita a kicin tana dafawa Dikko da baƙinshi abincin da zasu ci sai waya yakeyi a kawo , "yar kwalbarta ta jawo daga cikin breziya ta kakkaɓe maganin ta kaf a cikin abinci , hamdala tayi ga Allah bayan ta tabbatar ta gama zubawa.....
Banda faɗuwa babu abinda gaban Inna keyi ganin taron mata sun dawo suma kansu sunji tsoron Jiddah ina ita Sultana ? Ƙaramar yarinya wacce shekarunta bai kai na Jiddah ba gaskiya zalinci yasa Dikko zai haɗa mata "ya zama da Jiddah , da tsausayi ta kalli inda Sultana take tana shiri Dikko ya turo Ashiru ya ɗaukota ya kawota wurinshi bayan yace masa wai kar yayi tuƙin ganganci kuma karya biyewa kowa yayin daya hau titi ya ɗauka duk wanda ke saman titi mahaukaci ne shi kaɗai ne mai hankali , hijabi Inna ta bani na saka bayan na gama shirina , saida ta rakoni har bakin get ta koma ni kuma na fita na shige mota muka tafi....
Kallon kaina nakeyi a zahirance wai in banda abin Inna taya zata sadani da hijabi ? Wannan ma idan wani ya ganni ai sai a rainani umm to ya zanyi ? Haƙuri kawai zakiyi Maryama....
Tun daga ƙofar gida har cikin gidan motoci ne , sai dawakai da aka tara a wajen gidan da ciki ƙosashshi "yan gayun dawakai masu tsada wata irin haniniya sukeyi sun karaɗe kaf illahirin wurin da kuka , ciki Ashiru ya shiga ya samu wuri yayi parking sannan ya turawa mai gida saƙo isowarmu ,
Shima rubuto masa yayi wai mu shigo yana ciki bayajin daɗi cikinshi ke ciwo , da Ashiru ya faɗamin cewa nayi bazan shiga ba idan baya fitowa ya bari , a , a ranki ya daɗe kiyi haƙuri mu ki shiga , wallahi bana shiga idan bazai zo ba ya bari yasa an ɗaukoni tun daga gidanmu nan ɗinma bazai iya zuwa ba ? Idan yana zuwa yazo idan baya zuwa can shi ta matse mawa....
Tura masa yayi cewa bazan shigo ba , yace gashi nan yana zuwa , fita Ashiru yayi daga motar yana cemin ki jirashi yana zuwa , ya daÉ—e sosai sannan ya fito mutanen da basu gaisa ba suke gaisawa bayan ya gama ya taho wurin motar ,
Gaba ya buɗe kujerar mai zaman banza ya ziro ƙugunshi ya zauna a gajiye ƙafafuwanshi a waje bai rufe motar ba , kwantar da kanshi yayi jikin kujerar yace wallahi bansan abinda ya sameni ba cikina kemin wani irin ciwo kamar zan mutu , ai idan ka mutu ka huta , Eh na huta ke kuma taki ta ƙare juyowa yayi ya kalleni sannan yaci gaba da cewa ai nasan idan na mutu ɗan ƙaramin hauka zakiyi sai kin riƙa kwacewa ana riƙoki , tou ka mutum ka gani idan zanyi haukan , hmmm yarinya kenan kina wasa da lamarina An mata , nima kana wasa da nawa lamarin kedai kika sani , kaima ka sani dakel yayi "yar gajeriyar dariya tare da duƙar da kanshi ya riƙe cikinshi yace wai Allahna.....
Jikinshi yana wata irin kyarma ya kwantar da kujerar daya ke zaune kai yana cewa matsa daga nan ke , gefe na matsa yana cewa kin dai yafe ni ko ? Tou zan mutu in mutu ? Wata irin ƙara nayi cewa ban yafe ba Dikko dake duƙe ya riƙe ciki da sauri ya ɗago yace mene ne kuma ? Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi murmushi yayi cikin ƙarfin hali idonshi ɗauke da hawaye kaɗan yace ya akayi ne wai ? Fashewa nayi da kuka nace mafarki nayi zaka mutu yanzu , murmushi ya sakeyi cikin jarumta yace ina nan zaune kikayi baccin ? ya ƙarasa maganar yana min wani irin kallo , tou amma na ganka ka kwanta kace zaka mutu , Dikko yace anan ɗin na kwanta ? Eh , ba kin ganni gani nan zaune ba ? Idan ba kaine ba waye ? To ni An mata ya za'ayi in sani ? Wallahi na ganka , hannunshi ya miƙomin na riƙe yace ke... wai mene ne ? Ko yunwa kike ji ne ? A , a , banajin yunwa kalli idona in ganki , kallonshi nayi shima ni yake kallo bayan wani lokaci yace ya isa haka fita muje ya fita........
Ƙin fita nayi ina tunani to wai idan ba Dikko bane ba waye ? A dai² lokacin daya buɗe murfin motar ya fiddoni yana cewa yunwa nakeji amma banajin zan iya cin abincin can gaskiya.......
12/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 75
*_Ga saƙon godiya Ummiee Zaria Jikar Lerawa Sultana tace a gaishe ki tana miki fatan alkairi..._*
Nifa bazanje ba kaje kawai zan jiraka a mota , da Allah wuce mu tafi banasan yawan magana ji nake kamar zan faɗi , nidai kaje abinka dan Allah , zaki wuce muje ko saina baki kunya , ai kaima zakaji kunyar , ni banajin komai idan ban ɗaukeki ba kice ba Dikko nake ba kuma idan na ɗaukeki saina fita ƙofar gida a tsakiyar mutane zan ajiyeki in dawo ,
Kaɗan ne daga cikin aikinshi dan haka nace muje badan halinka ba , naji muje dan naki halinki kuma da bakije ba yau da kinga yadda ake saɓanin igiyar ruwa , tafiya nayi na barshi a baya biyo bayana yayi yana cewa "yar raini magana fa nake kuma nasan kinaji na...
Kai aini yanzu na girma banda lokacin yarinta , dariya yayi yace ai nine zan baki girman kinga kina ƙasana har yau har gobe kullum ma kina ƙasa ina samanki yarinya kin gane abinda nake nufi yayi maganar tare da wucewa yayi gaba da ɗan gudu nima da sauri nabishi ina ƙarema gidan kallo gaskiya wannan gida ya haɗu masu kuɗi basu da aike sai bautawa ƙasar da bata da tabbas duk wannan ginin a kwana a tashi sai an tafi an barshi kuma ƙasar ce zata hiɗiye bata gajiya...
Wata "yar munafikar ƙara yayi "yar ƙarama yace wayyo cikina kuma bai daina tafiya ba nima ban daina binshi ba , gangarewa yayi ƙasa da gudu nima da gudun na bishi muka sauka muna sauka naga mun fito waje irin na farkon gidan amma ba inda Ashiru yayi parking ba , tsayawa nayi ina kallon wurin da mamaki jin ban biyoshi ba yasa ya dawo da sauri kamar za'a kamashi ya jani ta baya ina kallon wurin shi kuma yana jana da sauri , jinjina kaina nayi tare da cewa "yan gayu , ai kune gayun An mata mu "ya "yanku ne.......
Taho jirana akeyi , juyawa nayi na kalli gabana nace ina zamuje ? Can zamuje ai , ni gaskiya bazan je ba , ke da Allah wuce muje yanzun nan kika gama cemin kin girma ashe har yanzu An matance , nidai gaskiya bazanje ba , mi yasa ne ? Nifa tsoro nakeji , tsoron mi ? Da Allah wuce muje ke komai sai kinyi yarinta , ƙwacewa nayi nayo hanyar da muka fito da gudu , shima da gudu ya biyoni harna fara hawa matakal ya riƙoni yace wai me yasa kikemin haka ne ? Cikin kuka nace nidai bazanje ba , jawoni yayi kusa dashi yace tou in rungumeki sai muje ? Nidai bana so , yace um ummm Dikko ne fa ya faɗa tare dayimin kallon ƙauna , zo jikina kiji natsuwa An matana , a gajiye na sauka jikinshi cikin mutuwar jiki , yace tou ya kikaji akwai daɗi ko ? Eyy tou sauka muje babu wani abu da zai faru wallahi.... Ka tabbata na tabbata miki ya ƙarasa maganar yana duƙuwo dai² bakina na sumbaci gefen fuskarshi yace yawwa jarumata muje....
Yanzu bai riƙeni ba mukaci gaba da tafiya ta wata ƙofar gidan da ba'a rusa ba amma an fasa ƙofa ya shigo cikin gidan muka shiga shine a gaba ina baya kamar yadda yace nazo jikinshi zanji natsuwa na samu natsuwar banajin tsoro cikin dakewa nake binshi har muka shiga ciki...
Wani irin yagegen palo ne kuma an ƙawatashi da wasu irin mahaukatan kujeru masu kyau palon yana da girma maisa kaji juwa ta kamaka anyi masa ado dai² da zamani , mutane ne cike a wurin maza da mata "yan gayu ibar farko sai ƙamshin gayu ke tashi , muna shiga Dikko yace tou ga An mata nan ku gaisa ina zuwa yana faɗin haka ya wuce , binshi nayi da ido harya shige ciki ,
Dawo da hankalina nayi wurin "yan cikin palo nace sannunku , yawwa ki zauna mana , a , a zan wuce ne kawai ina faɗin haka nabi Dikko inda naga ya shiga , suka ce kizo ki jirashi ya fito , ko saurarensu banyi ba na wuce ciki , a gefen gado na sameshi durƙushe rabin jikinshi a saman gado idonshi a rufe hawaye na zubowa daga cikin idonshi , da sauri na isa wurinshi nayi yadda naga yayi sannan nace masa Dikko wai miye ? Ba tare daya buɗe idonshi ba yace An mata cikina kamar zan mutu haka nakeji , kace kanajin yunwa kaci abinci to , bana iya cin abinci a yadda nakeji na , to kasha magani mana , zan sha jeki palo ki jirani kinji ko ? Cikin kuka na matsa kusa dashi nace nidai zan zauna nan , a , a karki zauna kinji jeki ina zuwa yanzu , nidai , cikin hayani yace da Allah malama fita ki bani wuri nace kije ki jirani ki tashi kusa dani bana san numfashinki yana sauka a jikina , matsawa nayi na zauna gefen gadon nace tou zan jiraka anan ,
Wani irin kallo yayi min tare dayin dariya , murmushi nayi nima nace meya baka dariya ne ? ÆŠaure fuska yayi sannan yace ba dariya bace fusata ce , da gudu na tashi nabar É—akin , tsoki Dikko yayi yace kin rufawa kanki asiri dana yi miki maganin kafiya , cire kayanshi yayi ya shiga wanka a daddafe....
A palo kuma sai caccakar abinci sukeyi yayin da wasu kuma ke tacin ɗamara cikin shiga irin ta mahaya doki sai naɗa rawani sukeyi , wuri na samu na zauna bana kallon kowa zuciyata ce ƙawar firana tana haskomin Dikko da ɗabi'unshi , murmushi nayi ƙasa² nayi magana nace mutumine kenan....
A hankali mutane suka fara ragewa dan har yanzu Dikko bai fito ba abinda dai na fuskanta ko wane yana tare da budurwarshi ne ko matarshi ne nidai shine ban gane ba dan banga sunyi kama da masu zaman "yan ci ba , ina wannan tunanin ne Ashiru ya shigo hannunshi riƙe da kofi inda nake zaune yazo ya bani da girmamawa yace wai mai gida yace in baki ki kai mishi , kai tsaye nace bazanje ba , murmushi Ashiru yayi tare da cewa yi haƙuri kije ki daina haka babu kyau kinfa san halinshi sarai haba ranki ya daɗe ki riƙa mishi uzuri , ni bazanyi uzirin ba a cikin ni dashi waye ya kamata yayi uziri wa wani ? Kiyi haƙuri duk wanda yayi haƙuri bai iske ba kaɗan yayi ki ƙara haƙuri wata rana zai zama tarihi , wane tarihi kullum abu ɗaya ni na gaji wallahi , yi haƙuri ki ansa kinga gashi yana kira , ƙin ansa nayi na gyara zamana , ɗaukar wayar yayi yace E mai gida , tou gashi nan zata kawo maka ya tsinke wayarshi , yace dan Allah ansa ki kai mishi , ansar kofin nayi na tafi ɗakin kai tsaye !
Bayan ƙofa ya laɓe ina shiga ya kulle ƙofar da makulli , a ɗan razane nace masa gashi cikin girmamawa , kalli can ya nuna min gado , kallo nayi sannan na kalli Dikko da yanayin tuhuma , yace haka kika ganshi ɗazu ? Girgiza kaina nayi alamar a , a yace ai kin rainani ko ? Tou yau so nake mu fidda raini dani dake , da sauri na kalli kofin na sake kallon gadon ya gyareshe tas , meye a kofin ne ? Ya tambayeni bansan ko miye ba , tou shanyeshi sai in buɗe miki ƙofa ki tafi idan ba haka ba kuma in ɗoraki saman gado kema in miki yadda kika ganshi , nidai ka ansa tafiya zanyi gida , ai ba wani gidan da zaki yau yayi maganar tare da matsawa jikin madubi yana kallon kanshi saida ya shafa gemunshi da bayan hannunshi na haggu sannan ya fara cewa one , bayan wani lokaci yace tow , three , four , five , da sauri nace me zanyi ? A harzuƙe ya kalleni yace shanyewa zakiyi sai kizo ki dafa ƙafata kice kin gode , idan kuma kika bari na irga goma saidai kiji Dikko a saman ruwan cikinki....
Six yaci gaba seven , eight , nine ..... Da sauri na ɗaga kofin na shanye na riƙe moƙoshi na tare dayin wata irin ƙara sannan na fashe da kuka na jefar da kofin kamar nasha guba har a zuciyata kamar an kwaremin ita ƙirjina zafi maƙoshina kamar an tsatstsargar minshi , dariya Dikko yayi yace services gobe ma ki sakemin kafiya zo ki gode , da sauri na isa gabanshi kaina yana juyawa na dafa ƙafarshi ina kyarma nace na gode , to jeki Ashiru ya maida ke gida sai mun haɗu a ɗakina gobe idan Allah ya kaimu , da sauri na miƙe yace kimin addu'ar saukowa doki lafiya , har yanzu wuyana kamar zai fita nace Allah ya tsare yasa ka sauko lafiya , daure fuskarshi yayi yace yawwa kije ngode , yayi maganar yana tillomin makullin ƙofar , da sauri na ɗauka na buɗe na fita ina kuka....
A inda nabar Ashiru a wurin na sameshi nayi gaba cikin ɓacin rai yace ta nan zamu bi , banza nayi dashi na wuce , maganar Dikko naji da tunda na fito ya biyo bayana naji yana cewa ina zakije nan bakiji ana miki magana bane zo nan , ba tare da nayi magana ba na dawo da hannu ya nunamin yace wuce ta nan kuje kuma karki daina kukan zanzo da daddare ,
Kallonshi nayi , cikin tsawa yace ki daina kallona ki wuce marece yanayi sai ina miki magana kita kikkifa ido kina kallona , bayan Ashiru nabi har yanzu ban daina kuka ba , komawa Dikko yayi yaci gaba da shirinshi wai zasu hau taka ango duk wani abokinshi na nesa dana kusa idan dai yana da rai da lafiya yazo , yasa an ɗauko An mata da ya ɗorata doki amma ta ɓata mishi , kayan daya ajiye mata ta saka ma badasu zaiyi tunda batajin magana...
Abokanshi sunso ayi shagali amma Dikko yace a , a , sun tambayeshi dalili yace shi yasan dalili kawai bazaiyi ba , shine suka tsiro hawan doki dan tayashi murna kuma shima zai hau dan yana bawa hawan doki mutunci na musamman ,
Tunda muka taho kuka nake ina jinjina irin cuta da zalinci na Dikko , har yanzu wuyana bai daina maƙaƙi ba zafi yake daga ƙirjina har abinda ya sauko zuwa ramin zuciyata , goge hawayen da suka sake taruwa a idona nayi sannan na fara tunanin ya akayi Dikko ya kasu gida biyu ? To waye ya kwanta yace in matsa gefe ? Da nayi kuka kuma ya akayi naga banga na kwance ba naga Dikko ya ɗago ? Mafarki ne zuciyata ta tabbatar min da haka dan haka na manta da wani da na gani yana kwanciya a mota....
A ƙofar gida Ashiru ya saukeni ya wuce da gudu ni kuma na shiga cikin gida , duk sallamar da nakeyi babu wanda ya jini bare nasa ran za'a ansamin Inna da matan Baba ƙarami suke ta faɗa wai ni na koyawa Safiyya iskanci kuma naje na anshi gadon su Babana na lashe duk wannan bai isheni ba saida nasa Dikko ya ɗaure mijinsu sunga yadda za'ayi a ɗauramin aure , Inna tace aure anyi an gama ba fashi ko ƙarami ya ɗaura aure ko karya ɗaura sai an ɗaura auren Sultana idan Allah ya kaimu lafiya gobe kuma ko ni sai in fita in ɗaura mata aure tunda ba shegiya bace ba , shaggu ma an ɗaura aurensu bare Sultana , dama waye yake nemar a fasa aure ai jiki magayi dan hausawa kuwa cewa sukayi ko wattuna bara baiji daɗin bana ba , ai hangen duniya ne yasa kike harin bashi ɗiya ke haɗamammiya , Inna tace haɗama sai wanda ya isa yakeyi wani yayi yaga idan zai samu cusa kai babu ƙwarjini , matan Baba ƙarami sukace murnar mutuwa dai murnar banza yadda yayi ma mijinsu itama zai mata haka nan , banji abinda Inna tace ba na shiga ciki raina ɓace na fara kiran wayar Dikko....
Takalmi zanoty ne a ƙafarshi wando kamun ƙafa jawha milihi "yar gabas , babbar riga girken nufe yasha rawani mai bakin fara sai wuƙar hawan doki dake rataye jikinshi a jirge yadda dai masu hawan doki keyi , yasha kyau harya gode ma Allah sai hotuna ake ɗaukarsu a ɗan yamutse yake dan bayajin daɗi sosai komai cikin ƙarfin hali yakeyi...
Bayan sun gama ɗaukar hotunan suka ɗunguma suka nufi inda aka ajiye dawakan duk wanda zai hau doki sunsha ado sosai , gaban dokinshi ya tsaya da yasha ado da sirdi tunbas ajikin sirdin anyi masa kwalliya da bishiri guda huɗu , kayan azurfa gaban fuskar doki ɗan wuya ɗan gaba , ƙasan sirdi aka sa labbati mai kyau ɗan gabas da sha hirji... Yana ƙoƙarin hawa tsadajjen dokin kiran Sultana ya shigo....
Ɗauka yayi ya kara a kunnenshi tare da cewa inajinki , wai kai da Allah Dikko mi yasa bakayin abu da lissafi ? Tafiya ya farayi dan komawa ciki saboda wurin yayi taron mutane da yawa Sultana kuma taci gaba da cewa in banda hauka ƙanin babana zakasa a ɗaure ? Ai kinsan ni mahaukacin ne kika faɗamin damuwarki me yasa ke mai hankali bakiyi maganin matsalarki ba sai kin sako mahaukaci a ciki to ? Dana faɗa maka cewa nayi kasa a kulleshi ? Wanda zai ɗauramin auren Dikko ? Tou ai sai a fito dashi ya ɗaura auren idan ya gama saiya koma , cikin hayani nace kai mahaukaci..... Kafin in faɗi maganar da zan faɗa yace ai kinsan inda kika barni kizo ki sameni in nuna miki girman haukata shi baya san ke ɗiyar ɗan uwanshi ce ba yayi ƙararki duk sansanci da aka kasayi a gida to inda ya kaiki a can zasu sasanta nine nakeyin shari'ar ne ? Ko nine nake ƙararshi ? Yarinya dake kuma kece mahaukaciya ni ina da hankalina dokin Dikko kawai dake in hau kuma inyi sukuwa......... Yana faɗin haka ya kashe wayarshi !
Cikin ɓacin rai ya fita ji yakeyi baima ɓatama An mata rai ba dama yace saiya zaneta iyakar raini duk girman duniyar nan baiga wanda ya rainashi ba kamar yadda An mata ta rainashi ba , ta kalli tsabar idonshi ta kirashi mahaukaci ta faffaɗa mishi duk maganar daya zo bakinta baida wata ƙima a idonta amma zataci ƙaniyarta , da ɓacin ran An mata ya hau saman doki ya zakuɗa yadda sukeyi idan zasu gyara , bayan ya gyara yayi ma dokin diddige kowa yahau nashi suka wuce cikin tsari da gogewa irin tasu ta mahaya doki ango a gaba abokanshi a baya suna taka ma ango wannan shine ake kira taka ango zasu ɗan zagane inda sukaga ya kamata abunsu dai na manya.....
Dikko yana kashe wayarshi Inna tana shigowa , wuri ta samu ta zauna take tambayata abinda ya haɗani da Ba ƙarami , duk abinda ya faru dani bayan bata nan saida na zayyane matashi kaf amma ban faɗa mata zance Dikko yamin fyaɗe ba amma duk abinda nayi bayan na Dikko ban ɓoyewa Inna komai ba , bayan na gama tace yanzu inashi Baban Hafsa ? Bansan inda yake ba , shifa Bello ? Shima bansan yana ina ba , Hmmm Inna tayi cikin takaici sannan tace to dan uban ƙarami ya manta ni kenan ? Amma ina cikin gidan nan har aka kawo miki sammaci saboda Dikko ya fini mutunci kika saƙe a jikinki har kikaje kika kai mishi ina nan kwance Sultana ? Inna ranar baki lafiya bana so na tayar miki hankali , jinjina kai Inna tayi sannan tace naso ace ahalin babanki suka ɗaura miki aure amma nasan haka baza ta samu ba dan bana tunanin ƙarami zai iya ɗaura auren ki saidai "yan uwana su ɗaura miki aure...........!
Ba tare dana kalli Inna ba nace ba naki ahalin ba na Babana , Baba ƙarami ne zai ɗaura aurena da kanshi gobe idan Allah ya kaimu a ƙofar marusa ƙofar gidan su Babana haka na faɗa ma Dikko kuma haka yasa aka rubuta a jikin i v kuma a gidan za'a ɗauki amarya Inna dangi uwa sunyi kuma suna nuna soyayya mai girma da fifiko wa nasu akan ahalin uba kowa dai da nashi wurin , amma su ahalin uba garkuwar rayuwa ne gaba ɗaya daga zaran baka dasu tou fa ka koma liƙe² , Inna tace a jikin i v masallacin G R A za'a ɗaura aure haka aka rubuta ana gama sallar juma'a , kuma ko ƙarami ya ɗaura ko bazai ɗaura ba mijina zai ɗaura aurenki idan mai kowa mai komai ya bamu aron rayuwa da lafiya anan gidan za'a ɗauki amarya duk wanda bazai zo ba yasha zamanshi a gida.... Tana kaiwa nan tace in fito za'amin ƙunshi mai ƙunshi tun ɗazu take jiranki , wai duk girman kwana takwas sai yau za'ayi ƙunshin biki idan Allah ya kaimu gobe naje saloon sai kace auren wasan yara danni ina kallon abun kamar a mafarki ne....
Daren yau duk inda ka shiga a gari maganar su Dikko akeyi labari ya barbazu duk inda ba'a tunani ya dangane , sunyi hawa mai kyau da burgewa abokanshi sunyi mishi kara sosai wasu ma basu taɓa zuwa katsina ba sai dalilin wannan aure , dan duk auren da yayi duka biyun ba'a a katsina akayi ba , sai yau mutane suka tabbatar suka kuma yadda da wannan aure , hotuna sai yawo suke a social media , duk abin nan sai yau Momy ta samu damar buɗe wayarta , shi kuma Dady ya kira Dikko yace ya rufe kaf wayoyinshi karya tsaya duk inda wani zai ganshi tunda yace shi damuwarshi a ɗaura auren idan an ɗaura zaiji da sauran matsalolin , Dikko yace E fatan alkairi Dady yayi masa sukayi sallama ,
Dikko yaso yaje wurin An mata bayan sun sauko daga hawa amma baya iya zuwa ga gajiyan doki ga kuma ciwon ciki dake neman hanashi ya miƙe tsaye koda suka dawo a daddafe yayi sallar magrib yayi isha'e sannan suka shiga gida a saman kafet ya kwanta a wahalce ya kifa fuskarshi saman pilow shi kaɗai yasan azabar da yakeji , abokanshi kuma sun daɗe suna fira bayan sunci abincin dare ne suka fara tafiya wasu zasu koma gidanjensu anan cikin gari , baƙi kuma suna tafiya masauki ,
Bayan kowa ya gama tafiya ne aka rage Dikko dashi dasu Ashiru , wayar wani ya ansa a yaranshi ya kira An mata amma duk kiran da yayi ba'a É—auka ba saboda tabar wayar a É—aki tana waje ana mata lalle , gajiya yayi da kira ba'a É—auka ba ya mayar mishi da wayarshi , yace ma Ashiru ya samo mishi fura yaji ko zata shiga , fura dai itace ya samu yasha abinci dai ya gagareshi yau , abincin saidai aka fitar dashi dan ya lalace....
Bayan ta saka layinta Jiddah ta fara kira ko "ya "yanta bata nema ba sai Jiddah ta fara taɓowa ɗiyar zumuncin Allah Jiddah da ƙawayenta suna zaune a palon Sultana dan neman magana saboda bayan an gama jere an rufe da makulli amma sai ta kira aka ɓalle mata ƙofar wai wannan kujerun sunfi ƙarfin siyen ahalin caca mijinta ne ya siya dan haka babu wanda zai mata iyaka da dukiyar mijinta , komai na ɗakin amfani sukeyi dashi kuma cikin ƙeta da mugunta shi Dikko baisan abinda Jiddah take ciki ba dan ko ranar da Inna tace saidai ya rabawa Sultana gida bata faɗa masa cewa Jiddah tayi iskanci ba tace masa dai kawai ya rabawa Sultana gida da matarshi dan ta fahimci kawai da damuwa , shine Dikkon yace gidanshi bai gagareshi ba kuma shi babu macen data fi ƙarfinshi....
Jiddah tana ganin number waje ta san Momy ce dan haka tana ɗauka ta ɓarke da wani irin kuka mai tada hankali , na shiga3 na lalace ƙaryata ta ƙare kece garkuwata da bakya nan na zama abin tausayi duka na safe daban na rana daban har tsakar dare bai barni na huta ba saboda kawai zaiyi aure , wane irin aure kuma ? Momy wai baki sani ba ? Aure zaiyi har anyi jere yau duk inda kika shiga a garin katsina maganar hawan taka angonsu akeyi yace yayi hawan barin tarihi a katsina tunda ya auro muradinshi ni matar sadaka ce shi yasa baiyi ba a aurena dashi , Momy tace wai waye zaiyi auren ne ?
Saida ta sake ɓarkewa da kuka cikin makirci irin ancucetan nan tace Yaya zaiyi aure har anyi jere gobe ɗaurin aure haka akazo jere jiya bakiji yadda sukemin habaici ba suna zazzagina nayi haƙuri na ƙyalesu Momy ina cikin matsala , wai wane Yayan zaiyi aure ? Inji Momy , Jiddah tace Ya DK , Momy tace wai Dikko nawa ? Ko wane Dikkon ? Jiddah tace shi , Dady dake zaune saman abin sallah yana lazimi ƙaddarawa yayi ma bata wurin , Momy tace wace ce zai aura ? Caca zai aura , Momy tace wace ce Caca ? Wannan karuwar , wata irin zufa ta ketowa Momy cikin tashin hankali tace Dikkon wai ? Jiddah tace Eh , kashe waya Momy tayi ta fara kiran wayar Dikko amma a kashe yake , Ashiru ta kira bayan ya ɗauka tace ya bata Dikko yasan da kwanan zance dan hakanyace mai gida yaje kaduna wurin wasan polo , haka Dikko yace duk wanda Momy ta kira a cikinsu baya nan yana kaduna tunda dama zaije polo saukar da akeyi ma Sultana shine ya hanashi zuwa , Momy tace shi da waye ya tafi kadunar ? Ashiru yace shida wani abokinshi , turomin number abokin nashi , har zata kashe waya taji bata iyawa tace ubanshi ne yahau doki yau zakacemin yaje kaduna ?
Ashiru yace nidai ban sani ba hajiya nasan dai mai gida baya nan bara na turo miki number abokin nashi , ina jiranka ta tsinke wayarta , gyara kwanciya Dikko yayi bayan Ashiru ya gama waya da Momy dakel ya fara karanta tsohon layin Sultana dake hannunshi , bayan ya gama faÉ—a Ashiru ya tura mata ,
Tana gama waya da Ashiru ta kalli Dady tace kaji wai Dikko zaiyi aure , Allah yasa alkairi , Dady ya faÉ—a , Momy tace wai har Dikko nawa yake zaiyi mata biyu ? Dady yace yo shi É—in na wasa ne ? Karuwa fa ? Karuwar aini daya faÉ—amin zaiyi auren nan da banyi tafiyar nan ba , kunga tun nan Dady ya zame kanshi , Momy tace kaima bai faÉ—a maka ba ? Dady yace um umm , haka Momy tayi ta gwada number da aka turo mata amma batayi , cikin daren ta kira "ya "yanta mata tace idan Allah ya kaimu gobe lafiya suje gidan Dikko daga amarya har danginta suyi musu terere .......!
Hmmm tou waye ma zaije ya tashi rashin kunya har gidan Dikko duk girman mutum Dikko ya sauke mishi rashin mutunci , baka zo gidanshi ba kayi masa yaje ya isko ka har mazaunin ka ya gwagwaÉ—a maka rashin mutunci ina kuma ga ka hawo layinshi a cikin gidanshi................ ?
Ranar É—aurin aure !
Tunda safe Inna da kanta ta ɗaukeni a mota ta kaini gidan Kaka hmmm wai ni za'ama nasihar zaman aure , murmushi saida ta ƙari karatunta Inna ta ansa itama tayi har miyan bakinta ya kusa ƙarewa sannan tayi shiru kuma duk maganarta akan Dikko ne , daga gidan Kaka ta ajiyeni wurin wankin kai tace zataje ta dawo ,
Har aka gama abinda za'amin Inna bata dawo ba , ina nan zaune ina zaman jiranta kiran Yazeed ya shigo wayata , ɗauka nayi bayan mun gaisa yacemin An mata kanki ɗaya ? Nace meya faru ne ? Ki rasa wanda zaki aura sai DK haba An mata me zakiyi da DK ? Wallahi ba baki nayi miki ba ko kinje sai kin dawo kinsan iskancin DK kuwa ? Kuma wallahi ba sanki yakeyi ba yaudara ce kawai bakiga auren naku duk a munafurce akeyinshi ba ? Duk auren da yayi babu wanda baiyi hidima da shagali na tashin hankali ba , duk matan daya aura wallahi lefe akwatina 200 yayi kinga banbanci biyu ya fito ko ? Ji naki babu wani shagali tun nan kisan baya maraba da auren saboda baya sabgar mata yake so ya moreki ya koraki bayan ya gama hora miki zuciyarki da soyayyarshi , banbanci na gaba lefe akwati 24 yayi miki , kuma zai haɗaki gida ɗaya da matarshi cewa yayi wai bazai iya ajiyeki goruba ba gidan yafi ƙarfinki kinji yadda yake aibata ki ? Hmmm uwa uba kuma ga duka kwata² baisan darajarki ba mahaifiyarshi bata sanki ga masifar DK gana matarshi "yan uwanshi da mahaifiyarshi ina zaki saka kanki ? Ya ganki "yar yarinya shi yasa ya liƙe miki yayi ta cin zalinki Dikko mugune na bugawa a jarida kiyi karatun ta natsu kuma ki cire number na a wayarki nasan zai sake miki sabon layi ne ki kirani da sabon layin zan baki shawara , jiki a sanyaye nace tou ,
Ina kashe wayata Dikko ya riƙa zuwamin a zuciyata , kyawun fuskarshi maganarshi da yakeyi cikin sanyi sai kuma tsadajjen murmushin shi mai ɗaukar hankali kallonshi mai tayar da tsikar jiki rigimarshi idan ya kafe yana faɗa dani da gaskiyarshi jina yake kamar wata sa'arshi , murmushi nayi a zuciyata nace mutumi na Allah ya baka lafiya , amma fa maganar gaskiya Dikko yana da cuta a rayuwarshi , horn in Inna ya dawo dani daga tunanin dana lula , jakata na ɗauka nayi musu sallama na wuce....
Lokacin da muka dawo gida gidan ya fara ɗaukar taron jama'a ƙawayen Inna wankakkin matan da suka san abinda sukeyi , kuma matan Baba ƙarami sunzo dan rashin kunya da "yan uwan Inna , ɗakin mijinta ta wuce dan itama gobe zasu bar nigeria , ko walima bata tsayawa ayi da ita shi yasa bata da wani ishashshen lokaci kula da mutane tana ta shirinta ,
Ɗakin Inna na shiga ƙawayenta suka sa ni nayi wanka ina fitowa suka rubdigarmin suna min shiri na musamman nidai sai yanzu jikina ya fara sanyi da lamarin Dikko tsoranshi naji ya kamani da maganar da yayi min jiya a goruba wai muje saman gado mu fidda raini , sai wayar da mukayi dashi wai nice dokinshi zaiyi sukawa akaina , sai maganar Yazeed da yace Dikko ya ganni "yar yarinya shi yasa ya liƙemin zaiyi ta cuta na ne , fashewa nayi da wani irin kuka mai tada hankali nace nidai wallahi bana sansa ,
Inna data shigo yanzu cikin shiga ta wayayyin mata tace wane ne bakya so ? Dikko , dariya ƙawayenta sukayi gaba ɗayansu cikin shaƙiyanci suka kalleni cikin yanayin wayyo muna tausaya miki , Inna tace kin manta daren ɗaurin aurenki da Sultan abinda kikace akan Dikko ? Aimu saidai muce Allah ya baku zaman lafiya...
Ƙara sheƙewa sukayi da dariya , kamar wata taɓaɓɓa haka nabisu da kallo ɗaya bayan ɗaya Inna tace ke da Allah ki rufe mana baki ko ki fita ki bamu wuri , wata ce tace a , a karta fita tazo nan ta zauna , saman gado na koma bayansu na zauna sukaci gaba da firarsu na tafiyar Inna...... !
Bayan sallah juma'a dubun mutane suka sheda ɗaurin auren *DIKKO U DK* da amaryarshi *MARYAM ALIYU MUHAMMAD BINNA...* akan sadaki naira dubu ɗari ɗaya lakadan ba ajalan ba , ɗaurin aure yayi albarka wanda manyan mutane da dama suka samu damar halakta daga jahohi da dama , Baba Ƙarami yaje amma yaƙi yadda ya ɗaura aure mijin Inna ya zama waliyin Sultana , ana gama ɗaurin aure Dikko ya buɗe wayoyinshi , yana buɗewa saƙon Momy ya shigo !
_Idan ka kuskura ka É—auko "yar duniya ka watsa kanka ka watsa gidanka , kuma tunda bansan yarinyar nan ko ka aureta saika saketa.....!_
Murmushi Dikko yayi tare daci gaba da duba saƙonni , hada Yayarshi itama ta zazzageshi tass murmushi ya sakeyi sannan yace aike a cikin kayan miya ko matsayin ruwa baki kai ba sharar bakin kwata dake , na ɗayar Yayarshi ya duba itama dai abun babu kyan gani da daɗin ji , kanku akeji , saƙon Dady ya gani shi kaɗai ke masa fatan alkairi , bayan ya gama dubawa Ashiru yaba wayoyin yana gaisawa da mutane.
Wallahi Uncle na zuba , Mardiyya ce tsaye a gaban Al ' Ameen yace haba Doughter da kin zuba maganin nan idan an ɗaura auren nan niba ɗan Babana bane , tayi masa rantsuwa cewa ta zuba saidai idan bashi ne yaci abincin ba ko kuma baici ba , dan abincin sa daban aka zuba mishi , jinjina kai Al ' Ameen yayi tare da cewa aiki ya kwana uban gayya ya mutu , muna fama da Jiddah Sultana ta shigo , dolensu kowa zata kama gabanta amma Jiddah ce farko sai Sultana tabi bayanta , Mardiyya tace Uncle tare zasu tafi gaskiya , Al ' Ameen yace tabbas ki faɗawa waccan jakar boka yace azo a anshi saƙo gobe , Mardiyya tace to ta wuce ciki , tana wucewa Al ' Ameen yace zaki bani motarki da manki da kuɗinki inje in biyawa kaina buƙata.......
A wahalce Dady ya kalli Bello saida yayi nishin wahala sannan yace ɗan iskan yaron nan ma inajin ma ya mata damu ! Bello yace kaidai mu fita lafiya , Dady yace nidai jibi idan Allah ya kaimu za'a kawomin kuɗin nan na bashi na huta da wahala Dikko ɗan iskan yaro ne , dariya Bello yayi ta taɓaɓɓi yace mai naɗawa manya kashi....
Umar dai baya gajiya da gulma da kanshi yaje har gidan Amisty ya faɗa musu mai gida ya auri Sultana , Hafsa ita bata nan tana abuja wurin wata shaƙaƙƙiyar mata ta hawan kwakwa mai ranar bacci , Amisty tanajin labarin auren Sultana ta haɗa dabar karuwanta hada su wane yaro tace kowa ya shirya su tara gidan amarya amma kar a faɗawa Hafsa dan gudowa zatayi ta dawo kuma tayi zubin kuɗinta dan bata ɗaukar asara ,
Momy kuwa tana daga can ta tattara kan yaranta ta turasu gidan Dikko tace idan suka ragawa Sultana da duk masu rakota sai taci ubansu , dan haka suma suka taho ko wace kanta É—ure da iskanci suka iso gidan ,
Mardiyya kuma ta É—ora Jiddah saida ta tabbatar tafi jirgin sama tashi hankalinta ya kwanta , kuma faÉ—a mata Uncle zaije zaria boka yayi kira , Jiddah tace zasu haÉ—u da daddare.
Yazeed kuwa sai ƙara kirana yake yana jaddadamin na cire numbershi karna manta ya sanni da mantuwa , raina ya ɓaci dan haka kallo biyu nayi ma numbobin suka zauna akaina gaba ɗayansu.....
13/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 76
Ina ƙoƙarin ajiye wayata kiran Dikko ya shigo , fashe wa nayi da kuka naƙi ɗaukar wayar harya tsinke wani kiran ya sake shigowa ban ɗauka ba sai kuka nake mai tada hankali , wayata na yada na tashi da gudu nabi Inna ɗakin mijinta dawowar shi kenan yana labarta mata yadda ɗaurin aure ya kasance , wai kuma ana gama la'asar za'a ɗauki amarya ! Ina zuwa na rungumeta tare da ƙara ɓarkewa da wani irin kuka mai kama zuciya , da tausayi ta ɗagoni daga jikinta itama hawayen ne kwance a idanuwanta amma bai zubo ba , da yanayin ko oho tace wai meye haka ? Bana san iskanci fa , shi kuma kukan na mene ne ?
Inna na kirata tare da kallonta ina shashshekar kuka na kasa magana , murmushin ƙarfin hali Inna tayi ta jani muka fita ɗakin muka koma ɗakin ta , wata ƙawarta ce ta miƙomin wayata tace ana kiranki kuma har yanzu Dikko bai daina kirana ba , ina ansar wayar na kasheta gaba ɗaya...........!
Inna da ƙawayenta kuwa nasiha sukemin wallahi hankalina baya wurinsu kwata² banajin su kuma bana iya tuna abinda suka faɗamin har suka ƙari surutunsu suka gama a , a ciki bana iya tunawa , bayan an gama nasiha na tashi nayi sallah la'asar kuma har nayi sallah na gama hawaye ke ratata daga cikin kwarin idanuwana , ina gama sallah aka fara shiryani dan kaini ɗakin mijina.
Babu wani daga ɓangaren ango daya zo bikon amarya , duk maganar Inna batayi tsegumi ba ita burinta kawai akaini ta huta dan a ganinta aurena shine natsuwa a gareta dan tasan idan ta tafi ta barni yawo zanci gaba dayi tunda Allah ya kawo mai kwasheni sauka lafiya....
Babu abokin ango ko É—aya duk motocin Dikko ne akayi amfani dasu wurin kai mutane gidan amarya , ni kuma a motar mijin Inna aka É—aukeni dashi da É—an uwan Inna sune suka kaini har gidan Dikko da kansu......
Da farin ciki masoyana suka shiga gidan tare da dabar su Amisty domin sun riga amarya isowa sai aka shiga a tare kowa dai da abinda yake faɗa irin dai abun nan namu na mata yadda mukeyi idan ankai amarya kun dai gane irin abun ai , Jiddah kuwa ta murza wani irin ƙaton wanka na tashin hankali kamar zata tashi duniya dan haɗuwa kai Jiddah "yar gayun bala'e ce kanta yana hayaƙin rashin kunya , wata irin guɗa ta rangaɗa ayyuri yuriiii........ Ƙawayenta suka ansa da barka da zuwa *CACA* ga caca ga tawagar karuwanta a baya fatan kunyo mana tsarabar kwalaben giya a cikin jikkunanku dan kunsan ba'a shiga kasuwa saida kuɗin siyayya amfani giya kenan sai ansha akejin muradin mace , giya mata caca sana'ar uban wata ƙawata ne , hehehe ram aka kashe kundai san iskancinmu na mata yadda yake.....
Yayyen Dikko dai turawa ne sun huta tunda banajin abinda suke cewa kunsan ajiboters basu iya faɗa ba haka kuma basu iya hayani ba daga zaune dai suke ta watso nasu kalaman cikin harshen turanci , kuma su ƙawayen Inna babu wanda yayi musu magana , Mardiyya ce naji tana cewa gashi nan Aunty zai shigo , cikin yayun Dikko ne naji wata ta turance abinda yasa na fahimta naji Mardiyya tace Dikko ne , kila ta tambayi Mardiyya waye ne tace shine , kowa dake palon yayi tsitt , murmushi nayi a zuciyata tare da cewa sannu da zuwa jarumina , ban ganshi ba amma na hasko yadda zai fito daga mota ,
Zaiyi parking cikin ɓacin rai , sai ya fito daga mota da yanayin shagwaɓa zai tunkaro palon cikin jarumta zaiyi mazurai da kyawawan idanuwanshi idan ya shigo , daddaɗar muryarsa zata bayyana yanzu , sallamarshi naji yayin da ake ƙoƙarin shiga dani hanyar da zata sadamu da inda aka bani mazauni da "yan uwanshi ya fara gaisawa sannan ya kira Jiddah suka wuce ciki.
Ƙarshen ɗaki aka kaini wato bedroom saman tsadajjen gadona aka ajiyeni a gefen gado , nasiha dai aka ƙara yimin an nunamin matsayin haƙuri biyayyar aure kauda ido akan ƙaramin abu danne zuciya yayin fushi , ba abun duniya baya duk girmanshi tsabta naga yadda abiyar zamana takeyi inyi ƙoƙari in wuceta a gayu , babu wanda ya zauna saboda yanayin hararar da ƙawayen Jiddah ke watsoma "yan kawo amarya abinda yasa ma basuyi yunƙurin yin wani abu ba dan Dikko yana nan , shima Umar ne ya faɗa masa za'a tashi bama²n masifa a gidanshi shi yasa ya taho , duk wani abu da za'ayi a wurin walima idan Allah ya kaimu gobe Inna ta ƙanƙare da dangin miji , tayi gara na fita kunya kuma duk Dikko ne yayi dan ya siyamin mutunci a wurin ahalinshi....
Amisty taso tayi magana dan na lura da bakinta amma ƙawayen Inna suka ce kowa yazo a tafi yanzu , amma tacemin akwai dawowa , inaji ina gani suka tafi suka barni , Oh saini ɗaya a ɗakina kamar mayya babu ƙawa ko ɗaya babu wasu "yan uwa da zasu kwana a gidana , jakata na jawo na fiddo wayata na kunna bayan ta gama kunnuwa na kira Inna , amma bata ɗauka ba ,
"Yan palo kuwa kowa cikinsa ɗure da iskanci a ƙagare suke Dikko ya fita su caccakeni san ransu amma yaƙi fita har aka kira magrib , suna tunanin zai tafi masallaci a gida yayi sallah , isha'e ma haka , Yayyen shi ganin bashi da niyar fita sukayi mishi sallama suka wuce , godiya yayi musu tare da cewa ku huta gajiya , amma sun ɗauki gudirin zasu dawo idan Dikko baya nan , Sultana ta samu ɗagin ƙafa na yau basa so suyi rashin mutunci Dikko yana nan idan ya birkice musu gano dai²nshi sai Allah.
Misalin 9pm ya kira Jiddah ɗakinshi ya faɗa mata cewa idan Allah ya kaimu gobe rai da lafiya duk wata ƙawarta data san tazo gidan nan to ta tattara ta kama gabanta har Mardiyya baisan ganin kowa idan kuwa ba haka ba za'a samu matsala , amma sai Jiddah tace ƙawaye na zasu tafi amma fa Mardiyya babu inda zataje wallahi tunda tuni Momy ta gama magana idan kuma dan kayi aure zaka tona min asiri saika haɗa hada ni ka koremu gaba ɗaya....
Cikin ɓacin rai Dikko yace Mardiyya ta tafi daga gidana Jiddah , wallahi babu gidan ubanda zataje , Mardiyya ta barmin gidana gobe kafin raina ya ɓaci , wallahi ba zataje ko ina ba idan saboda kayi amarya ne sai haɗa hadani ka sakeni kuma kake maganar ta bar maka gida ai bani nace ta zauna ba Momy tace saboda haka ka bari sai ta dawo , tana faɗin haka tayi gaba abunta , shima tashi yayi ya nufi ɗakin amarya Sultana...
Da ɓacin rai ya tunkari ɗakin Sultana yanajin tuƙuƙin maganar Jiddah da tace babu gidan ubanda Mardiyya zataje zaici uban yarinyar nan amma sai zuwa gaba dan yanzu duk idon jama'a akanshi yake yana iya mata wani abu ace daga yayi aure ya fara cusa mata damuwa , yana da cikin Jiddah duk ranar daya tashi haifeta zai wulaƙanta mata rayuwa yadda mai tunani baya zato, ina zaune a inda nayi sallah har yanzu ban tashi ba ina ta kiran wayar Inna ba'a ɗauka , babu ko sallama ya shigo ke An mata ni zakiƙi ɗaukar ma waya ne ? Dake kin ɗaukeni sakarai ma daga baya kika kashe wayar wai me kika maidani yana maganar yana shigowa cikin ɗakin , kai tsaye nace mahaukaci , kalmar hauka ya fita daga bakinki dan jiya ba yau bace doki , dokina ya ƙarasa maganar yana ɗaukata yaci gaba da cewa do ki , da iskanci yake faɗar do..... Sai yace ki , yana yin irin yadda akeyi idan an hau doki bari ki fara jin nauhi na sai ki fara kiyayata tun kafin mu fara wasan danbe ,
Dikko bana so , a , a ya maƙale ƙafaɗar shi irin yadda ƙananan yara keyin ƙiwya yayi maganar a shagwaɓe yana yin wani ɗan kukan shagwaɓa mai sa mutum yaji yana lilo tsakanin sama da ƙasa , cikina naji yana halbawa jikina yanamin wani yami² a dai² lokacin daya saukeni saman gado yana min wani irin munafiki kallo mai nuni da zakici gidanku sannan ya sake cewa do ki yayi min kyakkyawan murmushin shi mai fiddo mishi da ai nahin kyawun shi ƙuramin ido yayi sannan yace ai dokina ne ke ko An matana ? Rufe idona nayi cikin jin kunya nayi murmushi kaɗan!
Ina sanki , idona a rufe nace Dikko dan Allah kada kaimin komai , ke meye nace ? Cewa kayi kana so na , ke kuma meye kike faɗa ? Cewa fa nayi kawai ina sanki , to idan na faɗa nima bazakamin wani abu ba ? Naga alama dai idan banyi wani abu ba bazakiji daɗi ba dan na lura kina tsammani wani abu daga gareni , buɗe idona nayi tare da cewa , a , a , ido ɗaya ya kashe tare da ɗagamin gira yace sumbata ɗaya tak , ai nasan bazai tsaya a ɗayan bane , durƙusawa yayi a saman guyawunshi ya dafa hannuwanshi gefe da gefe ina tsakiya kallona yayi sannan yace kamar ya ? Cewa nayi nasan bazai tsaya a ɗayan bane ba , murmushi yayi tare da kwanciya saman jikina a gajiye buɗe bakinsa yayi kaɗan da ajiyar zuciya mara sauti sannan yace Oh to kenan kin yadda da sumbatar ashe ? To amma nasan bazaka tsaya a ɗayan ba , da hannunwanshi biyu ya riƙe kaina cikin kwantattar murya ya ɗora bakinsa a saman leɓuna na yace ɗaya tak ya faɗa da wata irin murya mai tayar da tsikar jiki , cikin mutuwar jiki nace amma dai karya wuce ɗaya , murmushi Dikko yayi tare dayin wata irin sukuwa a kaina cikin sigar mugunta kamar yadda yace sannan ya ɗagani yana cewa tausayinki nakeyi An mata nasan baki iya ɗaukar Dikko wahala zan baki "yar yarinya ta bara dai inzo muyi bacci kinji ko , yana faɗin haka ya fita da tafiyarshi ta sakakkin "ya "ya ,
Ajiyar zuciya na sauke tare da lumshe idanuwana ba haka naso wasan ya ƙare ba , me ma Dikko yake nufi yana nufin ido zai sakamin saboda nayi ƙarama kai kuji mugu fa , hmmm lallai Dikko ba baƙon mace bane ba , amma maƙetacin mace ne , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya kamar yana nan na rufe fuskata.
Shiru² Dikko zai dawo babu shi ba labarinshi , tsoki nayi tare da gyara kwanciyata , tun ina tunanin Dikko zai dawo harna fitar da rai yana wurin Jiddah a can ya sauke damuwarshi yayi baccinshi ya manta dani , haka na haƙura nayi bacci da tunanin Dikko...
Yauma nayi mafarki da mutumin nan kuma ya faɗamin ya ƙwaƙwale gobe saura ni tunda na shiga sahun ma'aurata , a firgice na farka tare da kwarara wani irin firgitaccen ihu wanda ya karaɗe kaf girman gidan gaba ɗaya duk mahaluƙin dake gidan babu wanda baiji ihuna ba , ina buɗe idona na nufo palo da gudu ban tsaya ko ina ba sai jikin firij na buɗe na ɗauka ruwa saboda wata irin ƙishirwa da nakeji kamar zan mutu , saida na shanye roba ɗaya ta ruwa , a wahalce na dawo da baya na zauna saman kujera ina goge zufa...
Jiddah ce ta fito sanye cikin wasu irin kafirawan kayan bacci idonta da yanayin bacci tace uban waye nan yake mana kuka ? Kallo ɗaya nayi mata daga nesa na fahimci fitina ne ya fiddota kuma uwarta zanci yadda nake haƙe da ita saboda kirana da tayi da caca , ubanki ne yake kuka na bata ansa a dai² lokacin da Dikko ya dafa ƙarfen bene daga sama sboda mu dukanmu a yanzu muna ƙasa kowa ta sauko , ni abinda yasa na fito palon ƙasa nasan bazan samu ruwa a palo na ba shi yasa na gangaro na ƙasa nasan zan samu , ita kuma Jiddah masifa ya fito da ita ni kuma yau zan sauke mata duk wata tsutsar iskancin dake cizar mata kwalwa , An mata ya akayi ne ? Dikko ya tambaya , ruwa nasha na bashi ansa ba tare dana kalli inda yake ba , Jiddah kuma tace Caca ni kike zagi ? Sai in takaita miki rayuwa na illahta banza ba abinda za'ayi , Dikko ne yace kinsha ruwan ne ? Ey nasha , tashi kije ki kwanta tou ,
Babu gardama na miƙe zan tafi Jiddah ta riƙoni ta baya ta fara zagina tana cewa ke "yar marasa tarbiya babana bazai zagu a bakinki ba danni Babana bai sakani a caca ba , shi Babana yasan darajar matansa yasan na "ya "yansa kaf zuri'armu bamu da "yan iska banza ahalin kwarata , Dikko ne yace An mata wuce kije ki kwanta kinji , tou na bashi ansa tare da ƙwacewa Jiddah ta sake riƙoni taci gaba da cewa...
Kuma ni babu wanda ya siye gidan hayarmu ya mayar da gidan kiwon dawakai karuwar banza karuwar wofi , murmushin takaici Dikko yayi tare da cewa An mata taho , ƙyale Jiddah nayi na tafi ita kuma taci gaba da cewa ƙaryar banza ƙaryar wofi ba ance ke wata shegiya bace ba da kin tsaya dana ciccire miki gashin kai , Dikko yace gashin kanta kike baƙin ciki dashi ? Dan a lokacin Sultana ta shiga ɗaki bata san wainar da suke toyawa ba , yaci gaba da cewa mace kenan An mata ta burgeta ina ga maza kuma kenan ? Wannan shine zaɓi na farko dana fara cankowa a rayuwata ƙatuwar banza da ƙanƙanuwar yarinya ta fiki tunani , yana faɗin haka yabi bayan Sultana....
Ai kaine ƙaton banza ko kunya bakaji kaje ka auro wannan "yar magen yarinyar idan ka isa kaje ka auromin min cikakkiyar mace wacce zata fito na fito itace kishiyata Dikko da zai shiga ɗakin Sultana yaba Jiddah ansa cewa wannan ma ta isheki yana faɗin haka ya shige , ita kuma taci gaba da cewa wannan yarinyar ni wallahi ba kishiyata bace ba "yar aiki ce ka kawomin kuma tayimin iskanci saina bata kashin bala'e , ƙawayenta suka fito suka jata suka koma ciki da ita suka ci gaba dayi mata huɗubar shaiɗan!
An mata kukan me kike a tsakar daren nan ? Ba komai na faɗa cikin ɓacin rai , kusa dani ya zauna ya riƙoni na kwace kaina tare da matsawa daga kusa dashi dan haushin sa nakeji baizo ya kwana dani ba , kuma ko "yar kazar da ake bawa amare ni bai kawomin ba , ƙara matsowa Dikko yayi zai taɓani nace da Allah ka ƙyaleni , tou na ƙyaleki amma kiyi haƙuri dan ma an sakaki a caca to miye ? Shi a tunaninshi inayin fushi ne saboda maganganun Jiddah tou inajin ciwonsu amma nafi jin haushin shi a yanzu ,
Gyara bakina nayi banyi magana ba , cire takalmin ƙafarshi yayi suba silifas ba kuma ba soso bane ba amma dai zubin slifas garesu , kwanciya yayi saman gadon yace tou taho ki faɗamin , yi nayi kamar banji ba , bai sake magana ba ya gyara kwanciyar shi yaci gaba da baccinshi hannunshi a saman cikinshi inajin har yanzu cikinsa bai daina ciwo ba , can nesa dashi na kwanta ina kallonshi ,
Haba Jiddah ina wayewarki ? Ina barikinki ? Ina feƙewarki ? Maza fa idan sukayi sabon auren kansu rawa yakeyi ya kasa tsayawa wuri ɗaya ki fita sha'aninshi da matarshi ba jibi zai tafi ya barku ba ? Jiddah tace Eh to ki bari idan baya nan ki riƙa ci mata uwa la'ada waje idan gaban idonshi ne saiki riƙa tattalinta kina nuna mata soyayya ko ƙararki takai masa zaice bata san zaman lafiya , kibi sannu ki zuge mata rayuwar uwa kamar iccen zogala karki sake ki barta ta huta idan azaba tayi mata yawa ita da kanta zata gudu , salon mugunta sanka² suka koyawa Jiddah....
Kiran sallah asuba ya tashi Dikko daga bacci ni har lokkacin banyi bacci ba saboda tsoro , da sauri na juya mishi baya na daina kallonshi , sauka yayi daga saman gadon ba tare da yayi magana ba ya fita daga É—akin....
Cike da tausayin Sultana ya koma ɗaki shidai yana tausayinta gata "yar ƙararrama shi tayi mishi yarinya ji yake idan yayi jijjiga akanta kamar zataji ciwo , domin shi dai buƙatarshi tana da girma An mata bata iyawa dashi wancan ma da yayi mata yana nadama kuma har yanzu bai daina ba , shidai kawai ya aureta ne dan ya natsar da ita wuri ɗaya tunda kullum yana tare da ita , na biyu kuma ya aureta ne dan girmanshi daya sake mata yasan duk lokacin data ganshi zata riƙa hango abunda ya shiga tsakaninsu , tou waishi tayama zai fara hayema An mata gata duk ta rame ta zama wata "yar ƙarama shidai an cuceshi wallahi wannan ai ɗaukar alhaki ne , ɗan gajeren tsoki yayi sannan yace in taɓota kuma ta taramin mutane ma a gidan nan dana fita kowa yasan abinda nayi , ummm abundai ba wani sirri....
Dikko na fita masallaci Jiddah da zugar ƙawayenta suka shigo ɗakina hada Mardiyya , a saman abin sallah suka sameni tsaye zan kabbara sallah , Jiddah ce ta kama hijabina daga wuya ta yageta har ƙasa ta wurgar da tsumman ta cire kallabin kaina tana taɓa gashina , bayan ta tabbatar ban jiƙashi ba tace Allah ya rufa miki asiri da na rantse da girman Allah yau saina safke miki gashin kai banza ɗiyar ɗan caca tayi baya , Mardiyya ta matso tace ni nan da kika ganni nafi haɗarin jirgin sama kyan gani , ni haɗarina girma ne dashi domin idan nabi ta rayuwar mutum na fita tou fa lallai ya gama rayuwa har abadan duniya , na shigo gidan nan da niyar tarwatsawa ai kin tuna labarin dana baki a mota ko ? Daga haka bata sake cewa komai ba , ƙawayen Jiddah suka ci gaba da zuwa gabana ɗaya bayan ɗaya wasu su shafa fuskata wasu kuma su shafa gashin kaina , wata ma cewa tayi wannan ƙugun duk ke ɗaya ? "Yar yarinya dake da wannan babbar halitta ina kuma ga ni'imar aure ta tsargaki lallai Jiddah sai kinyi da gaske idan kuwa ba haka ba saidai tashin zance , haka dai sukayi ta daƙuna ni yayin da wasu suka riƙe ƙuguna suna jinjinawa , wasu kuma suna kallon gaban rigata dole Dikko ke birkicewa koni na samu wannan ai na gama da ko wace irin mace , dariya sukayi gaba ɗayansu banda Jiddah da Mardiyya ,
A ƙawayen Jiddah mutum 3 ya rungumeni ta ƙarshen itace ta warware gashin kaina ta rungumeni ta baya ta umarci wata cewa tayi mana hoto , ɗaukar hoton akayi da ƙarfi ta juyo dani ta sake rungumeni tace a ɗauka , sake ɗauka sukayi ana gama hoton tace ina sanki , murmushi nayi tare da kallonta nace ai tun baki faɗa ba na sani , gaba ɗayanku zan iya fitar da fetir zan kuma iya fitar da kalanzir a cikinku ,
Ku baƙin mata ne kuma baƙine a harkar lesbian ƙananan "yan iska , ke Mardiyya ke zaki basu labarin Sultana duk wacce tasan ta rungumeni a cikinku saina ɗauko mata hoton uwarta tsirara , ita Mardiyya furtawa kawai tayi ni na cika mata kalmarta ta hanyar ɗauko ubanta a cikin yanayi mafi muni a rayuwa , ke Jiddah kike ko wace ce ? Ni nan da kika ganni iskanci ne ɗore a cikin cikina da zaran kin latso wurin ƙaryarki ya ƙare ki kiyayi haɗuwarki dani , me kike tunani ne ? Tou idan baki sani ba a daren jiya Dikko maimaicin dahuwar dambu yayi min ko an faɗa miki ni ƙazamiyar mace ce mai kwana da janaba a jikinta ? Anyi an kuma an ƙara an ƙara ƙarawa kuje waje ku jirani kafiran banza da bakwa kallon alƙibla , tsoki nayi tare da naɗe gashin kaina na nufi hanyar toilet ,
Dariya Jiddah tayi tare da cewa burgar banza yo me yayi dake a daren jiya bayan tare ya kwana dani ? Ihun ki yasa ya fito banza duk abinda ya shiga tsakaninta da Dikko a jiya da magiyar da yayi mata dan da farko bata yadda ba haka tayi ta tonawa Dikko asari abindai bai kamata ba , jin kukan motarshi yasa suka fita daga É—akina Jiddah naci gaba da basu labari suna dariya ,
Jakunan banza duk saina ci uwarsu in Allah ya yadda wallahi naji ciwon yadda Jiddah ta buÉ—e sirrin Dikko abun baimin daÉ—i ba amma zai dawo ya sameni saiya faÉ—amin abinda yasa ya aureni , wayata naje na É—auka na kira Inna yanzu ma bata É—auka ba ,
Wannan tafiyar ma dubu ɗari biyar Jiddah ta bawa Al ' Ameen bayan ta cika masa mota taf da mai ya nufi zaria , zuciyarshi na saƙa ƙeta iri² , su kuma ƙawayen Jiddah shatar mota sukayi bayan sun tabbatar wa Jiddah zasu dawo sati na gaba...!
Har yanzu ban daina kiran wayar Inna ba daga ƙarshe ma kashe wayarta tayi , tashi nayi na koma saman gado na kwanta ina kwanciya wayar Amisty tana shigowa , ɗauka nayi bayan mun gaisa take cemin Nana ta rasu , Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Amisty wace Nanar na tambaya idona cike hawaye , Amisty tace Nana wacce kika sani ? Me ya sameta ne ? Wallahi lafiyarta qalau tayi mana bankwana da dare ta fita asubar nan aka tsince gawarta an yadar da ita a bakin bola bayan an kwakwale mata idanuwa kuma an cire wasu sassa na jikinta babu nisa da wata maƙociyarmu itama haka aka cire idonta aka yadar da ita a saman bola bamu san abinda yake jawo hakan ba , wani irin ihu na kwarara tare da yada wayata ƙasa ina cewa na shiga 3 shi kenan sai ni yau zan mutu wayyo na bani na lalace shikenan ashe bazanyi tsawon kwana ba ,
A wannan yanayin Dikko ya shigo ya sameni , tambayana yayi abinda yake faruwa , kai tsaye na kwashe kaf na faÉ—a masa amma sai yacemin wai sheÉ—an ne yake zuwamin a bacci , haka ya lallasheni bayan ya faÉ—amin cewa shima da haka yakeyin irin nawa ko rashin lafiya ko wani zaiji damuwa duk abinda zai faru da wani a gidansu ko waye zai gani a bacci idan kuma ya tashi abin zai zama da gaske , wannan karki wani damu sheÉ—anu ne kuma zai daina , kallonshi nayi sosai sannan nace sheÉ—anu wane iri ? Aljannu mana , cikin tashin hankali nace wane irin aljannu kuma nayi maganar cikin mutuwar jiki na tsorata , cikin hayagaga yace ke da Allah ban sani ba ,
Nima cikin hayaniyar nace kar Allah yasa ka sani kuma ya toshe ilimin sanin naka , murmushi yayi tare da cewa tayi bakan damiyar nata saina kaiki goruba anjima naci ƙaniyarki "yar rashin kunya , sai kaje goruba zakaci me yasa anan baza kaci ba , anan ? A , a , ni bana taɓa ki a gidan nan ki ɓarewa mutane baki kiyi ta musu ihu saina kaiki can zan rufe ƙofa in baki wahala sannan na dawo dake , idan ka tashi karka dawo dani da raina ka kashe ni , babu wanda ya taɓa mutuwa kuma a kanki baza a fara ba amma zaki ci gidanku ƙaramar yarinya mai bakin tsiwa , badai kinci kaza ba ? Hmmm saina kulle bakin rashin kunya...
Sai kazo ka kulle , hmmm bakina waye ya isa ya rufemin tunda ba mutum ya bani abuna ba , juyawa Dikko yayi ya fita daga ɗakin bai sake magana ba , wayata dana faɗar ƙasa na ɗauka tare da cewa Allah ya jiƙanki Nana ke kuma taki ƙarshen haka yazo Allah na roƙeka ka taimakemu muyi kyakkyawan ƙarshe , da yanayin mamaki nace tou shi Dikko da yaga nashi sheɗanun ko ance za'a kashe shi ? Wayata na ɗauka na fara kiranshi , ƙin ɗauka yayi a bayyane nace kai ta dama , yana ramawa ne dan ya kirani jiya ban ɗauka ba , tou saina kira so adadin yadda ya kira bai ɗauka ba sannan zai anshi kiran nawa...
Da zullumin mutuwa a raina na koma bacci , wanda baiyi shawara dani zaizo ba , Dikko wanka yayi ya fice danshi Allah bai masa baccin safe ba , cikin bacci naji ni ina lilo saman ruwa da sauri na buɗe idona Jiddah na gani tsaye rungume da bokita a hamatar ta kaɗa kai tayi tare da nunamin inda agogo yake sannan tace an samu gado an wani mimmiƙe sauka kije kiyi aiki ko kina nufin nice zan girka miki abinda zaki ci ,
Kallon Jiddah nayi sannan na kalli inda ta jiƙa gadon sauran ruwan bai gama shiga cikin katifar ba nace ke zan dafa ma ko wa ? Ɗan ya tsina fuska tayi tare dayin wasa da bokitin hannunta cewa me kika iya wanda zaki girka ki bani naci ? Ai gidan ɗan caca babu cima , ƙanzo gari sai kuwa kwaɗon tuwo idan an samu kinga baki da ilimin dafamin abinda zanci , to me yasa kika tashe ni ne ina bacci ? Saboda baki isa kiyi bacci ba tashi zakiyi ki girkawa masu aiki abinci , saukowa nayi daga saman gadon nace aiko ubanda ya aifeki zanci , caca ubana yafi ƙarfinki mijina ma ya gagareki bare Babana ,ai saidai kici abinci ki miƙe a saman gado kafin Momy ta dawo taci uwarki ki koma inda kika fito , ni bana faɗa da kishiya saidai na kwace mijin ciwon zuciya ya kasheta , taya ma zan fara haɗa jiki dake in kwashi talauci ?
Ai an daina faɗan kishi saidai ayi a ɗakin miji , ido fa yana kallo wallahi saidai ki gani ki haɗe yawu lafiyayyen namiji mai kuzari wanda babu irinshi a bariki , jarumi ɗaya mai naɗawa mata duka naushin shi da daɗin kalamansa wurin yabo nada daɗin saurare Yaya yafi ƙarfinki , mamayata aurenki yayi tunda kin shigo saidai kici abinci kisha ruwa amma Dikko yafi ƙarfinki , daren farko na a america nayi shi , naci kaza nasha lemu keko ko ruwan faro ba'a baki ba , mijina ya kwaremin kayan jikina idonshi yana kallon nawa cikin soyayya ya lallaɓeni yayin daya kwanta dani , Allah yayi miki albarka Jiddah shine abinda ya furta lokacin daya jini sabuwar mota ce kin kawo min budurcinki ya faɗa cikin jin daɗi , gyara riƙon bokitin tayi taci gaba da cewa , a jiya kuma riƙeni yayi a jikinshi saida yayi min kirari uwar gida sarautar mata farar mace alkebbar amarya ni waccan jakar ban ɗauketa mace ba shi yasa na baro ta nazo gareki ki bani maganin damuwata tou ina soyayyar ? Ai dama a saman gado ake nunata ɗakinshi yafi ƙarfinki bare har kisa ran hawa saman gadonshi wannan ni'imar Jiddah kaɗai zataji ƙwalelenki Caca ,
Ngode sosai da saƙon ta'aziyyarku a gareni , Alllah ya bada lada ubangiji muma ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo am3n ,
Kuyi haƙuri idan har kunga banyi typing ba wallahi ina da ƙaton dalilin daya hanani kuyi haƙuri ni bana mantawa daku kuna raina kamar yadda An mata take a ran Dikko ,
*RABI MUSA* katsina zance ko kaduna ? Mrs Usman Abdullahi yau nayi typing sai a sakarmin mara inyi fitsari , mu duk muna miki fatan alkairi ubangiji ya ƙara zaman lafiya da kwanciyar hankali "yar uwata ,
17/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA ce....*💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 77
Murmushi nayi tare da shiga toilet na ciko boket da ruwa nazo na sheƙawa Jiddah bala'e Caca ni kika jiƙa ta fara anbaliyar aman zagi na "yan tasha ban bi takanta ba na koma toilet na sake cikowa nazo na zuba a gado sannan na mayar da bokitin na fito har yanzu bata daina zagi ba , bayan na fito na matsa gabanta nace sa idonki a nawa wace ce ke ? Waye Dikko ? Anshe goruba a hannun kuturu ba wuya yake ba , makaranta guda gareni da na tara taron mata nake basu ilimin zaman gidan aure nice malamar , ke har kin isa Dikko a nawa yake ? Bare kuma ke da baki da lissafi balbaɗaɗɗa mai tona asirin mijinta , ni bana kuri haka kuma bana cika baki a zahirance nake bayyanar da saƙona , maganar Dikko da ɗakinshi rashin cin kaza ko ya kwana a ɗakinki ba damuwa na ne ba , amma zan nuna miki yadda ɗakin miji ke zai gagareki shiga sakarar banza , kuma daga yau idan kika sake cemin Caca saina caccake miki idon uwa.
Wani irin duka takaimin a fuska a wahalance na riƙe hannunta tare da cewa bani zaki daka ba ki koma wurin wacce ta faɗa miki saiki faɗa mata abinda nace idan ta baki ansar magana na kya dawo , kokowa ta kamani dashi ga sulbin tiyels da aka jiƙa kuma ai Jiddah tafi ƙarfina tunda shekarunmu ba ɗaya ba , bamu wani daɗe muna cakusawa ba Dikko ya shigo cikin ɓacin rai gaba ɗayanmu saida ya zazzabga mana mari sannan yace meya haɗamu ?
Cikin fushi na juya mishi baya ina kuka ƙasa² , itama Jiddah kuka takeyi kunsan "yan gayu basa san wahala tasha mari ni kuma dama na saba , ni kuma yunwa ce ta saremin guyawuna da kuzarin jikina , cikin kuka take faɗawa Dikko abinda nayi mata da turanci , raina a ɓace nace idan ba munafurci ba a faɗa da yaran dana sani mana , Dikko yace ma Jiddah ta tafi , juyowa nayi tare da cewa ina zatace ? Ai babu inda zataje kayi gulma kace taje kuma ? Allah dai ya haɗani da munafikin miji.,
Nine munafiki An mata ? Eh idan ba munafurci ba kaje kacewa Jiddah ka ƙagara Mom inka ta dawo ta wulaƙantani baka so na ni jakace shi yasa baka siyomin kaza ba , ita kuma a daren farkon ta taci kaza tasha lemu ni ko ruwan faro baka bani ba , itace farar mace alkebbar amarya , bazanje ɗakinka na kwana ba shi yasa ta jiƙamin jikina da gadona wai a gidanmu ba'a hawan gado zan kwanta a ƙasa sanyi ya kamani ɗakin miji yafi ƙarfina bare na fara tunanin hawan saman gadonka , kuma jiya a ɗakinta ka kwana kana mata magiya , Dikko yace nine na kwana a ɗakinki ? Yayi maganar yana kallonta ? Yaci gaba da cewa nine nace miki ina jiran Momy ta dawo taci mutuncinta ? Ni nazo ɗakinki ???
Fuuu Jiddah ta fita daga É—akin , kallona Dikko yayi sannan yace kebaki gane sharrin mata ? Na rantse da girma Allah bayan na fita daga É—akin nan naje zanyi wanka in dawo kuma kema haka nace miki ina dawowa , toilet ina na samu Jiddah tanayin waya , nazo zan shiga toilet sai.... Tsoki Dikko yayi tare da cewa bama zan faÉ—a miki ba ni nasan abinda yasa ban dawo ba kiyi magani na , kawai kadaiji kunya an tirka ka.
Kuma ni bazanyi maganin ka ba saidai ayita ta ƙare kawai ka bani tikitin saki nayi gaba abuna , danni bana iya zaman takura haka kuma bazanyi haƙuri da wulaƙancin dangin miji ba , wai ke ni zaki maida ƙaramin yaro , ina faɗa kina faɗa ni zaki maida kamar mace kina sakani a shirmenku nine aka turke? Tou ki buɗe kunnen ki da kyau ki saurareni idan har nasan zan sakeki a rayuwata da bazan ɓatawa kaina lokaci na auroki ba , da bana sanki ko kuma nasan zan auroki dan naci zarafinki dana barki a tare dani kawai na zamar dake karuwata , idan zanyi kawai zanyi ne idan banayi banayi kamar iska haka nake yayin dana taho babu wanda ya isa ya tareni sai nakai , ni bana lallashi kuma ban iya ba saidai idan kinmin yarinta zan zaneki ba abinda ya dameni ki dawo da hankalinki jikinki kuma kisan inda yake miki ciwo ,
Bawai zan zauna nayi ta kare miki faɗa ba dan idan yau ina nan gobe bana nan , ki koyi haɗiye damuwa da ba abun duniya baya dan ba komai kake nema ka samu ba a rayuwa , kuma bawai kullum zakiji daɗi ba abinda kike so bashi zaki samu ba , domin rayuwa juyawa takeyi kuma tana tafe da darussa da dama wata rana uwa zaki zama dole sai kin zama jaruma a gidan aurenki domin ta haka kaɗai zaki fuskanci rayuwa , idonki zaki buɗe sosai ki gano abinda yake tafiya a gidan nan kiyi maganin damuwa tun kafin ta dameki kiyi ƙoƙarin gusar da abin harin rayuwarki tun kafin ya gama farautar abun harinsa ya fara farautar taki rayuwa , duk wanda kika gani a gidan mijinshi yana da tashi matsalar , wata uwar miji , wata dangin miji , wata abiyar zama wata mijin ne gaba ɗaya , keda kina nufin kinzo zaki kwanta idan abin ya dameki ki ɗaga waya ki kira Dikko ya tare miki faɗa ? Ki gyara tunanin dan wallahi ko a gabana Jiddah ta faɗar dake sannu bazance miki ba , bana san zama faɗa da zage² tayar da fitina yana lalata arziƙin namiji kiyi haƙuri duk abinda tayi miki wata rana zai zama labari , baki yunwa baki ƙishirwa ba rashin sutura ko damuwar wurin zama , idan zaki kwantar da hankalinki ki zauna lafiya tou idan kuma kincemin yarinta ina da maganinki ,
Ita kuma Jiddah bata da lissafi tana tare da makashinta bata sani ba , nasan halinki sarai idan har na faɗa miki maganar nan kikayi gori wallahi idan naji saina zaneki da bulalar dukan doki , ni nace Mardiyya ta tafi Jiddah tace baza ta tafi ba , zagina fa tayi wai babu gidan ubanda zataje , tou idan baki sani ba Mardiyya ta turomin text , wai ga Aunty Jiddah can bata san zaman lafiya taje tana matsawa Aunty amarya , Aunty Jiddah bata san zaman lafiya ta cika tsatstsaga , amma zan faɗawa Jiddah dan tasan matsayin Mardiyya a wurinta dan ita tana ma Mardiyya kallon mai santa hmmm zata kaita ta barota domin duk ranar da haƙurina ya mutu zanyi ɓarna a gidan nan....
Ki fita harkar kowa kiyi rayuwarki tun kafin fushina ya shafeki , yanzu a ina zan kwana , cikin hayani yace ban sani ba , goge hawaye na nayi tare da matsawa can daga nesa shikenan kuma bazan ci kazar ba ? Fita yayi daga É—akin bai sake magana ba , cire kayan jikina nayi na shiga wanka ina tunanin Mardiyya , tabbas a maganarta akwai lauje cikin naÉ—i , tana da wata manufa nata na daban , miye tsakaninta dani da har zata faÉ—awa Dikko ? Kuma har take goyon baya na ?
Ba kece damuwarta ba zuciyata ta bani amsa , yayin da maganganun Mardiyya suka fara dawomin a cikin kaina , Ni nan da kika ganni nafi haÉ—arin jirgin sama kyan gani , ni haÉ—arina girma ne dashi domin idan nabi ta rayuwar mutum na fita tou fa lallai ya gama rayuwa har abadan duniya , na shigo gidan nan da niyar tarwatsawa ai kin tuna labarin dana baki a mota ko ?
Lallai wani abu zai faru ko kuma yana faruwa , shi kuma Dikko yacemin idona zan buɗe sosai na gano abinda yake tafiya a gidan nan kiyi maganin damuwa tun kafin ta dameki kiyi ƙoƙarin gusar da abin harin rayuwarki tun kafin ya gama da abun harinsa ya fara farautar taki rayuwar , duk wanda kika gani a gidan mijinshi yana da tashi matsalar , ki gyara tunaninki dan wallahi ko a gabana Jiddah ta faɗar dake bazan miki sannu ba , wanka na naci gaba dayi ina tunanin duk amincin dake tsakanin Mardiyya da Jiddah shine take mata zagon ƙasa.......?
Jiddah ki farka idan bacci kikeyi Mardiyya bata sanki dan zata kaiki ta baroki , zata kaini ta baronin kai takai ta baro ne ? Tunda an ƙunsa ka a ɗaki an faɗa maka ƙarya da munafurci ai dole zakace bata so na , um umm ita ta faɗamin kuna faɗa da An mata wayarshi ya miƙa mata cewa duba ki gani , ansa tayi ta gani Dikko ganin ranta ya ɓaci yasa yace kindai gani ko ? Tou ki dakatar da ita domin da zaran na yanke hukunci tou fa ko kaina bana saurara....... Cikin ɓacin rai ta fita daga ɗaki ,
Daren jiya
An mata nasan baki iya É—aukar Dikko wahala zan baki "yar yarinya ta bara dai inzo muyi bacci kinji ko ? Yana faÉ—in haka ya fita da tafiyarshi ta sakakkin " ya "ya.
Wayoyinshi ya ɗauka daga palo ya shiga bedroom , a gefen gado ya ajiye ya tunkari ƙofar toilet kai tsaye , magana yaji ƙasa² a dai² lokacin daya dafa handle in da niyar murɗewa ya shiga muryar Jiddah yaji tana cewa Al ' Ameen Mardiyya tace kana kirana shiru , bayan wani lokaci tace taya zan fito bayan gidan yana cike da mutane idan an ganmu tare mutane zasu ɗauka wani abu a tsakaninmu tunda bakwa shiri yanzu , shiru , wane maganin ? Na zuba ai , ɗakinta , a , a idan ya gano da damuwa nan zai birkice kuma kaga damuwa za'a samu , ba komai mu haɗu ta ƙofar baya misalin 3:15 sai in baka , ba damuwa , idan kaje ka haɗani dashi zamuyi magana , yawwa sai anjima , fitowa tayi taga Dikko a tsaye a wayance yace ranki ya daɗe kema kinyi wankan ne ? A , a , ta bashi ansa , murmushi yayi tare da rumgumarta suka koma toilet in tare da tunanin me aka zuba a ina aka zuba ? Kardai itama An mata kamar na Sadiyya zai faru da ita ?, an zuba , kuma an kira ɗakin ta shine bai gane ba , bayan sun fito wanka ne ya kulle ƙofa yace ma Jiddah tare zasu kwana ,
A damuwance yaja ta zuwa saman gado bayan ya gama shirin kwanciya bacci , Sadiyya tazo mishi a zuciya ta tsaya mishi wayayya "yar gayu tanayin abu irin yanayin na An mata itama ma'aboci hawan jikinshi ce kafin suyi aure ,
A asibiti.
Ranta ne ke ta kai kawo tsakanin maÆ™oshi da zuciyarta , hawaye yana zuba daga idonta tace ka yafemin kuma karka riÆ™eni a zuciyarka ka manta da abinda nazo maka dashi a daren da yafi ko wane dare farin ciki , amma sai ya zamar maka dare mafi muni a wurinka , na kasa sarrafawa bana iya danne sha'awata ka yafemin don girman Allah ta haÉ—a hannayenta biyu ðŸ™ðŸ»tana kallon Dikko ,
Riƙe hannayen nata yayi tare da cewa na yafe miki nifa dama ban wani riƙe ba na faɗa miki na yafe miki² na yafe miki Sadiyya ya ƙarasa maganar yana kwantar da kanshi a gefen allon kafaɗarta yana ci gaba da cewa wai miye matsalar kukan nan ne haba Sadiyyata ki daina saka damuwa a ranki har abadan duniya wallahi na manta da wannan damuwar a raina , kayi min alƙawari ko bayan bana nan bazaka faɗawa kowa ba , nayi alƙawari bare ma kina nan bazaki je ko ina ba muna tare insha Allah , faɗamin meye ne ? Ya ƙarasa maganar yana ɗagowa ya ƙureta da kallo.
Fashewa Sadiyya ta sakeyi da kuka Dikko ya riƙeta da riƙo mai nuni daya martabata yace bana san kuka fa nidai sauri ƙufula gareni faɗamin meye raina ya fara ɓaci zanyi fushi cikin mintuna biyu , cikin ɓacin rai yace me ne ? Murmushi Sadiyya tayi tare da cewa Allah zai baka lafiyar damuwarka idan na ganshi bana iya ganeshi amma idan naji muryarshi a yaranka zan gane maganar shi saboda bana ganinshi waya mukeyi yana bada saƙo ana kawomin kuma da sa hannunshi a lalurarka ya haɗa kai da matan Babanka an gurgunta maka rayuwa akan naira miliyan biyu , yayi amfani dakai ya kai min rayuwata ƙarshe bashi da imani duniyar kawai yake so shi akan kuɗin zai iya koma miye....
Waye ? Dikko ya tambayeta , sunan sa da sanin waye shi ban sani ba , ke me yayi miki ne ? Sama lumfashin Sadiyya ya ƙarayi cike da soyayya ta kalli Dikko sannan taci gaba da cewa.
Na taso cikin soyayya da kulawa ta iyaye , iyayena shahararrin "yan boko ne suna da cikar arziƙi yahudawa ne sosai wanda basu damu da rayuwar yaransu ba , gani na a sake yasa nakeyin rayuwar data tari gabana bawai rayuwar iskanci ba rashin ji lanƙwasa gandar aiki bana aikuwa idan na shige ɗaki sai zanje makaranta nake fitowa , ɗakina babu mai zuwamin daga ni sai rayuwata sai kuma wanda naba izinin shiga.
Rayuwata ta samu matsala ne a makarantar kwana { boarding }, bayan nayi jss3 a makarantar jeka ka dawo wato day aka kaini makarantar kwana , ni bana san boarding saboda wahalarta , amma fur Hajiya tace sai naje , na shiga damuwa Yayuna maza sukace dama da makarantar kwana na dace haka sukayi ta zugawa tun Dadynmu bashi da ra'ayin haka harya amince na tafi boarding.
Ina shan wahalar makaranta yadda ya kamata domin dai ina bacci kamar a gida ina fita sch amakare kulle sai prefect sun zaneni , ni ban saba da wahala ba , kullum haka ake cimin uwa amma kullum saina makara kuma basa gajiya sai sun zaneni.
Yauma gani durƙushe a gabansu S P inmu ce tace karku daketa ke zo nan , tashi nayi naje gabanta na durƙusa wasa tayi da bulala a jikina sannan tace me yasa bakyajin magana ke jakace kullum ayita dukanki bakyajin zafi ne ? Kiyi haƙuri bazan ƙara ba , kullum haka kike faɗa kin raina nasu ko ? A , a , hijabina ta cire ta zaneni saida ta tabbatar ta farfasamin jikina sannan ta wurgomin hijabin tace tashi kije.
Yinin ranar kuka na yini yi , tun daga wannan ranar ta sakamin ido ko hostel bata bari na zauna lafiya nine ibo mata ruwa wankinta tsefe mata kai gyaran ɗakinta komai dai nice nakeyi mata banda lokacin kaina sai nata , wahala yasa na rame nayi baƙiƙƙirin ,
Tsugunne nake a ƙofar ɗakinta ina jiran fitowarta daga kwanar wata ƙawarta da gudu ta safko daga saman gado tana dariya tace ke ɗaukomun ruwan wanka nan , ɗauka nayi nabi bayanta har toilet , ajiye ruwan nayi zan fita ta riƙoni tare da cewa kwancemin towel ina , cikin jin kunya nace yi haƙuri Aunty , bazanyi ba kunce shi kafin ince ke zakimin wanka nan cire kar na sake miki magana , kiyi haƙuri don Allah , idan kika sake bani haƙuri saina ja miki sharri na hanaki zaman lafiya a makarantar nan kuma zan sakawa rayuwarki ido kuma saina miki fyaɗe zan lalata ki ne ba abinda ya dameni , zaro idanuwa nayi nace fyaɗe kuma ? Dama mace tana ma mace fyaɗa ? Dan Allah kiyi haƙuri , idan kika bari na sake magana zanci ubanki , rufe idona nayi tare da kai hannuna saitin da nake tunanin tana nan ashe baya taja , buɗe idona nayi dan ganin ko banyi saiti ba , daga can ciki na ganta ta sake wuri tana cewa ke nake jira ,
Cikin toilet in na shiga dan daga waje nake , shigo ki rufe ƙofa , dan girman Allah kiyi haƙuri, bana san haƙurin nan daga bakinki kullemin ƙofa nace , shiga nayi tare da cewa ai zan kunce basai na rufe ba , murmushi tayi tare da matsowa ta rufe ƙofa ta cire towel in jikinta babu kunyar Allah bare ni , ciremin hijabina tayi ta ɗora a saman inda ta ajiye towel inta tace kina so in daina dukanki ? Shiru nayi idona a rufe , bakyaji ina magana buɗe idonki mu fahimci juna , ƙin buɗewa nayi kuma banyi magana ba ,
Dariya tayi tare da ƙoƙarin fara ciremin rigata , riƙe jikina nayi da karfi ta yadda bazata iya cirewa ba , murya a sanyaye tace Sadiyya buɗe idonki mana , ƙin buɗewa nayi danni gaba ɗaya kunya ya kamani wannan ƙatuwar zata cire kayanta jikinta a gabana , hannuna ta kamo ta ɗora a saman ƙirjinta kamar wacce aka watsa ma ruwan zafi na janye hannuna , cikin rarrashi tace buɗe idonki mana bazan sake dukanki daga yau ba , kuma nayi miki alƙawarin wahala ya ƙare zanyi ta baki kulawa har na bar makarantar nan , zaki dawo ɗakina da zama zakiyi bacci kuma nice zan riƙa miki wanki komai da kike min ni zan miki natsuwa kawai zaki bani yanzu zan nuna miki yadda zakiyimin saki jikinki zan cire miki rigarki ,
Feƙaƙƙiyar "yar maɗigo ce tasan hannunta a harkar lesbian , tunda ta sameni ta tattara sabgar ko wace mace ta zubar saini , ta dawo dani zama ɗakinta bana wahalar komai kullum ina kwance tana nunamin soyayya fiye da yadda miji yake kula da matarshi ta iya tattalin mace kuma tana da karuwanta a met insu amma tunda ta sameni kawai ta zama mijina na zama matarta ko wanka bata bari na nayi da kaina kafin wani lokaci nima na goge a harka dan Yusra mayya ce akan mace ,
Karuwanta ganin ta zubar dasu hankalinta yana kaina yasa suka taso ma rayuwata ido , dan ta ɓata da kowa saini , duk inda zataje dani take tafiya a hostel lokaci guda nima na faso na zama gogaggiyar "yar lesbian ta ƙarshe , Yusra kishi gareta na tashin hankali wannan dalilin yasa take yawo dani lokaci guda suna na ya fara zagawa a makaranta dan Yusra azzalimar shugaba ce , taga dama yarinyar tayi mata laifi kafin ta sanni tace ta sameta ɗakinta da daddare yarinyar ta biya mata buƙatar ta korata , tunda ta sameni sai Allah ya fitar mata da san ko wace irin mace a duniya saini.
Karuwanta kuwa neman sa'a na suke suci ubana , wasa² nima na fara halbawa neman mata , idan mace ta taho haka zan tsareta da ido ina kallon ƙirjinta ƙugunta yanayin zubinta da dirinta abun yana neman ya zamar min kamar wani bakin iyaye dan ko a sch na tuno da yadda muke rayuwa da Yusra idan ban ganta ta rumgemeni ta ɗan jagulani banajin daɗi , maganar karatu kuma na daina bana ganin kowa bana gane kowa sai Yusra , ko kora ta fita kafin ta dawo na fara kuka banda natsuwa sai tana nan , tun abun yana burgeta harna fara tada mata hankali domin yanzu na fita jaraba , wani lokaci sai munyi faɗa zan riƙeta a yunwance dana gaji nace mata nidai tunda kin gaji dani ki sakeni kawai zanje na sake wata tunda kin gaji dani , haƙuri ta bani wai ita bata gajiya dani kawai dai in fahimta bawai kullum akeyin abun ba sai an huta taya ƙarfinta bai gama dawowa ba zata iya bani wata natsuwar , ko abinci ne ka kwakwafe ma ɗaya saiya fitar maka a rai , haka nayi ta roƙon Yusra tou ta fitar min da lokaci na ni ɗaya idan ba haka ba gaskiya zan barta nayi gaba ,
Na rabu da Yusra ne a lokacin da asirinmu ya tonu , abokan harkarta suka sameni a ɗaki da safe ita kuma lokacin ta fita dan dubo yara dake shara , sukayi min duka har suka sumar dani , da Yusra ta dawo ta sameni hankalinta ya tashi bayan na dawo dani daga suma ta tambayeni abinda ya faru na faɗa mata , duk wanda ya dakeni saida Yusra ta buɗe masa kai da sukundireba , wannan ɗanyen aiki da tayi shine yaja mana zuwa wurin shugabar makaranta , anyi case mai girma domin kowa babanta attajiri ne kuma saida aka tattaro iyayenmu tonan asirin dai babu daɗi , haka aka zane Yusra bugun bala'e akayi mata bayan an ƙwace kallabinta aka koremu dukanmu daga makarantar ,
Nidai a gidanmu Yayuna maza sukamin bugun leƙa lahira ki dawo , bayan komai ya kwaranye e aka maidani makarantar jeka ka dawo , haka nayi ta farauto yara ina kawosu ɗakina in basu kuɗi , ganin ban fita harkar mata ba yasa aka cireni daga makaranta kwata² gashi bansan garin da Yusra take ba banda number wayarta na shiga tashin hankali harna rasa ina zan shiga , haka nan na haƙura na koma neman abokan Yayuna bana wani jin daɗinsu nidai Yusra ita kawai nake so ,
Ana cikin wannan badaƙalar ne Allah ya kawoka rayuwata , tunda na ganka natsuwa tazo min na fara mantawa da Yusra saboda tunanin ka nidai ban taɓa ganin namijin daya shigomin rayuwa ya tsareta ba kamar kai , ina sanka kuma naso na zama rayayya domin kai namijin duniya ne ina ma macen data samu gwarzon namiji kamar ka murna , duk kuwa wacce ta sameka a matsayin miji damuwa ya ƙare mata kuma ta zama abin a yaba mata ,
Bayan kazo gidanmu zuwan farko ka tafi aka fara kirana da wata number mai kiran nawa yana da wayau kuma bai shigo rayuwata ba saida ya gama bincike ni kaf , yasan matsalata neman mata da neman maza na , kiran farko yacemin shi wani almajiri ne dana bashi sadaka nace ni bana bada wata sadaka bana ma fita , sai yacemin ka bada ka tuna ai sai matsiyata ka bada ka manta wannan shine cikar arziƙi , ko kin tuna ko kin manta nidai zan taimakeki , a ina ka samu number na ne ? Musulmin aljani daga saudiyya ya turomin yace na taimaki Halimatus Sadiyya zaki tafi gidan miji bayan kin gama lalata mutuncinki a titi na baki taimako saboda halinki na ƙwarai , idan har kikayi aure namiji ya sameki ba a yadda yayi tunani ba da damuwa , zai wulaƙanta ki haka yay ta faɗomin rayuwata kamar yana karatun littafi , banyi tunanin haka zamuje ba , a dai² wannan lokacin ne Momyn Hafsa ta shigo.
Sadiyya taci gaba da cewa shine ya aikomin da wasu layu yace nayi ƙoƙarin sakasu a ƙasan katifa kafin ka kusanceni , idan ka kwanta dani kaji ni a yadda kaji inyi kuka ince ka rufamin asiri , hmmm ya cuceni ashe ba'ayin kuka wanda ya bashi tsibbun yace idan har nayi kuka tou zanyi ta kuka har ranar da za'ayi kukan rashi na , bayan ya tabbatar da hakan shine ya sake kirana ya faɗamin zan mutu kuma a ranar aka cire layina daga wayata kwata² bansan waye ya cire ba , saida ta goge hawaye tace kuma yace zan tafi tafiyar da babu dawowa duk macen da tayi yunƙurin shigar Dikko haka zaiyi ta aikasu ƙiyama babu sassauci , kuma shine yake da sa hannu a damuwarka da taimakon matar uba , shiru Sadiyya tayi daga nan maganar ta ya ƙare , jijjigata Dikko yayi amma shiru domin yana da tarin tambayoyi da zaiyi mata , wannan dalilin ne yasa Hafsa tace yayi kuka kamar rashin zai fita , a cikin ku waye ne ...? Karku kashe An matana , tou ko kune take gani a bacci...... ?
Wannan dalili ya hana Dikko komawa ɗakin Sultana yaji an anbaci magani kuma ance ɗakinta tun a daren bai bacci ba har lokacin da Sultana tayi kuka a dai² lokacin da Jiddah ke dawowa daga wurin Al ' Ameen kuma ya fita ta kicin amma basuyi magana ba kuɗi kawai ta bashi ta dawo , shi yasa bai fito da sauri yaje wurin Sultana ba , ita tana hawowa ta ƙasa shi kuma daga sama yake saurarensu saitin ƙofar baya kamar yadda tace , haka yasa su biyun suka kasance a ƙasa shi a sama Jiddah da Sultana a ƙasa , kuma idonshi biyu Al ' Ameen ya kira wayarta kamar dai² lokacin da tace su haɗu , ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa yarana , to waye a cikin ku ? waye kai me kake so ne da rayuwata ?
Al ' Ameen ne gurfane a gaban bokanshi yace shi Jiddah ba damuwarshi bace ba yanzu Sultana itace matsalarshi boka yayi waje road da ita Mardiyya zataji da Jiddah.
Da kokowa Jiddah ta kama Mardiyya tana dan ubanki ni zaki ma munafurci yau sai kin bar gidan nan tunda ba gidan babanki bane ba , ni zaki kashewa aure Allah ya tona miki asiri kaza² , Mardiyya tace Aunty wai me akayi ne ? Kinje kin turawa Yaya text kince muna faɗa ke baƙar munafuka , cikin kwantar da murya Mardiyya tace Allah sarki Aunty ina tsaye ina tayaki kishi na ƙwaƙwafe a wurin ganin na ƙwatar miki "yan cinki amma bazaki gode ba , iyayena sai cewa suke na dawo gida amma ban tafi ba saboda ina so naga bayan Sultana daga gidan nan ta ƙarasa maganar tana fashewa da kukan makirci , tou a haka zakiyi ? Me yasa zaki tura text wa Yaya ?
Cike da ladabi tace Aunty dan ya yadda dani ya haɗani da kula da rayuwar Sultana ta haka zan shiga jikinta nasan sirrinta kafin ta ankara mai gamawa ta gama , amma kiyi haƙuri bansan abun zai miki babu daɗi ba , jakar bata gane komai ba sai tace tou kiyi haƙuri Mardiyya ai bansan haka kike nufi ba , wuri ta samu ta zauna Mardiyya taci gaba da kaita tana dawowa.
Lokacin dana fito wanka har an canja sabuwar katifa an goge ɗakin tas an sa masa turaren ƙamshi mai daɗi a gefe kuma wasu irin ƙatunan food flarks ne masu kyau a ajiye , wurin naje na buɗe dariya nayi tare da lashe bakina nace kajin ne ko me ne ne ? Koma dai miye zanci shagalina na gama na kwanta yarinya ta sake dawomin ɗakin ko tacemin caca saina kware mata fatar fuska.
Dikko kuwa daga wurin Jiddah wurin su Bello ya nufa , gaba ɗayansu sun zama abun tsoro sun saɓa kamannunsu abun dai sai Allah ya basu lafiya , Dady yaji uwar bari yasa an kawo kuɗi da takardun gonaye filaye da gidajen daya haɗa yayi handama da babakere , saida ya ƙara cin ubansu ya diddira musu yace ko a mafarki An mata ta sake ganin wani a cikinsu wallahi saiya takashi da mota yaja da'ira ya raba kowa da ita mai ƙararren kwana yazo , sunci uwasu har babansu sannan aka sakesu sai sun haɗu a wurin rabon gado , suka wuce shi kuma yayo gida.
Qerau cike take taf da mutane an zubar da gawar Nana a ƙofar gida ta zama abun kallo masu wayoyi sai ɗauka hoto sukeyi , abunda babu kyan gani mijinta kuwa mutuwarta ko jikinshi amma su Amisty sunji ta sosai , Hafsa kuma har yanzu bata dawo ba , yau zaman makoki da jimami a Qerau kuka da baƙin ciki yana wurin dangin gawa.
Saida naci na ƙoshi zuciyata ta fara tashi duk abinda naci dan na kwantar da tanzomar tashin zuciyar baya tsayawa kamar zanyi amai amma baya zuwa , toilet na shiga na wanke bakina na jawo amai amma yaƙi zuwa kam aiko sai kazo wallahi dan duk abinda naci ya tashi zuciyata fitarshi daga jikina shine natsuwa , saida na sheƙa amai hankalina ya kwanta , ina gamawa na gyara wurin na fita , hijabina na saka na fita dan samun abinda zanci dan gaskiya yunwa nakeji na tashin hankali.
Cikin yanayin gajiya na sauko na shigo palon da farin ciki , sai yanzu naji hayani , Aunty Suwaiba na gani zaune a saman keken guragunta a ɓangare ɗaya kuma ana riƙe Dikko yana saiya kasheta , yau kwata² baya riƙuwa duk wanda yaje kusa da Suwaiba dan ɗauketa sai Dikko yace kaima saina kashe ka , sai raba ido takeyi kamar karuwa ta tsare uztaz a ɗaki , ta sharara wani irin fitsari yafi liter goma ta ruwa , kallonta nayi sannan na kalli inda ake riƙe Dikko suna ta ƙoƙarin kaishi ƙasa amma yau sun kasa kwantar dashi , to me ya haɗa Dikko da Suwaiba kuma ? Kai.......... duk saina kashe ku...... dukanku...... yayi wata irin girgirza tare da zazzage su Ashiru ya ɓarar dasu ƙasa , ya nufi wurin Suwaiba idan har yaje mata a yanayin nan zai maida ita kamar damejin milcose , Ashiru ne ya riƙe ƙafar shi daga kwance wani irin ihu Dikko yayi mai tada hankali yace kai zan kashe kaina.............. Zan mutu saina kashe kaina.....................
18/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 78
Duk wanda ke gidan nan ihu Dikko ya tada mishi hankali wata irin zabura yakeyi Ashiru ya riƙe ƙafarshi dakel haka yaba sauran dake ƙasa kwance damar tashi suka nufo Dikko suna kamashi , duka ya farayi duka ɗaya tak yakeyi mutum ya tafi baccin wahala , cike da tausayi nabi Dikko da kallo to wai miye matsalar ne ? Cikin wata irin murya yace wai bana ce bana so ana riƙeni ba , saina mutu...
Jan keken da Suwaiba take zaune suka farayi dan fita daga palon , kai............. Wai , wai Allahna wayyo......... Kai....... Idan ta tafi saina kashe kowa a gidan nan duk saina kashe ku...... Riƙe keken nayi nace babu inda zakuje da ita sai Dikko ya bada izinin fitarta wallahi , Mardiyya tace gaskiya ki bari a fita da ita gudun matsala.
Kallon Mardiyya nayi sannan nace nabi matsalar da gudu , babu gidan ubanda zakuje da ita baƙaƙen munafukai duk sai Allah ya tona muku asiri ɗaya bayan ɗaya , Suwaiba hankalinta baya wurina kwata² jikinta ko sai kyarma yake idonta kuwa ya zubar da hawayen firgita bata san adadi ba , a dai² wannan lokacin aka kai Dikko ƙasa dakel bawan Allah har yanzu bai daina kuka ba idonshi yana ratata da hawaye hannunshi ya ɗago yana kallon inda Suwaiba take zaune aka zuba mishi magani ya ɗauke.
Ɗakinshi suka kaishi a ƙasa suka kwantar dashi saman kafet , bayan sun fito Ashiru ne yaja Suwaiba zai fita nace idan har ka bari aka gudu da ita wallahi saina faɗa masa , cikin damuwa ya kalleni ba tare da yayi magana ba ya fita da ita sai Dikko ya dawo daga hutun taƙin lokaci za'a zazzage sauran tashin hankali , yau wata zataci gidansu mudai ba ruwanmu , nidai kicin na wuce nayi abinda ya shafeni , ina tausayin kaina amma gaskiya ina tausayin rayuwar Dikko.
Kafin wani lokaci gidan ya anshi taron "yan uwanshi wanda suke uwa É—aya uba É—aya duk wacce tazo É—akinshi take wucewa fuskokinsu babu daÉ—i , ina gama abinda nake É—akina na wuce banbi takan kowa ba.
Da sauri na shiga bedroom dan kukan wayana da nake jiyowa , Yazeed na faÉ—a a bayyane tare da ansa kiran da sallama , gaisawa mukayi bayan gaisuwa yace bai canja miki layi ba har yanzu ? Eh zan kiraki anjima , ba damuwa na tsinke wayar.
Har yanzu Jiddah bata daina doke²n waya ba har Momy saida ta faɗawa ta tashi hankalinsu dan haka zasu tattara suma su dawo a cikin kwana biyu masu zuwa.
Al ' Ameen bai haɗa Jiddah da boka sunyi waya ba , yadai tattaro bala'enshi ya nufo katsina cikin ƙwarin guiwa ,
Tunda Dikko ya tafi wurin 2 na rana sai gab da magrib ya dawo kuma har yanzu "yan uwanshi suna nan basu tafi ba suna ta tattalinshi , kallo yabi su dashi bayan ya buɗe idonshi da salati , murmushi yayi wanda bai fito a saman fuskarshi ba , ƙanwarshi yasa ta miƙo mishi wayoyin shi , saida wayoyin suka zo hannunshi sannan ya tashi zaune ya jingina da gado ajiye wayoyin yayi a gefenshi ya tsare babbar ɗakinsu da ido.
Sannu tayi mishi , gyara bakinshi yayi cikin damuwa ya ɗan shafa gemunshi tare da dafe kanshi cikin ɓacin rai , gaba ɗayansu kowa sannu yake masa amma har yanzu ɓacin rai ya hanashi yayi magana , miƙewa yayi ya nufi toilet su kuma suka koma palo gaba ɗayansu , wanka yayi tare da ɗauro alwalla ya fito , yana fitowa ya ɗauki wayarshi ya kira Sultana , babu daɗewa ta ɗauka.
Ke ban lafiya kinfi ƙarfin kizo ko ? Magana tayi yace kizo ina kiranki , bayan tayi magana yace babu komai kiyi haƙuri , tou ya kashe wayarshi , Nabeela ya kira ƙanwarshi , ta ansa da na'am jeki kizo da An mata , yana faɗin haka ya saka kayanshi ya fara gabatar da sallar la'asar data wuceshi.
Itace da Jiddah suka ɗaukoni har gidanmu , kallo ɗaya nayi mata na ɗauke kaina , banda suke tsoron Dikko nasan da babu abinda zai hanata ɗuɗɗura ma uwata zagi dan yanayin fuskarta ya nuna tanajin haushi na kamar ta dakeni , shegiya ni kawai akace ta kira amma saida taje ta fara tura Jiddah sannan tazo ta kirani , banyi mata magana ba nabi bayanta har ƙaton palon da nake tunanin nan ne na Dikko.
Sallama nayi amma gaba ɗayansu babu wanda ya ansamin sallamar kowa ranshi a haɗe kamar yace kinci uwarki , ban sake magana ba nayi murmushi tare da murza ƙuguna na wuce inda nake tunanin nan ne hanyar da zata sadani da bedroom in na wuce ina musu tafiya mai nuni naci uwarku nasha ruwan kanwa maganin kwarnafin ciki.
Tsaye na sameshi a gefen gado yana ɗora hula saman kanshi ɗayan hannunshi wayoyinshi ya matsa jikin madubi yana kallon kanshi , da ɗan gudu na isa wurinshi na rumgumeshi , murmushi yayi amma bai taɓani ba yayi magana da fulantaci cewa , { dusudu kairu woni sudu ya nuna da hannunshi yaci gaba da cewa leso an min minwoni Dikko kuma inmin ɓilatama edow misudduma e guda miwaddanma fijo danbe ayidi koh ? Ya tamabayeni , } abinda yace wannan shine ɗakina nunawa yayi da hannunshi yana cewa gadona ni nine Dikko kuma nine zan ɗoraki a sama in lulluɓeki da bargo in miki wasan dambe ai kina so ko ? Rufe fuskata nayi a ƙirjinshi , murmushi yayi tare da ajiye wayoyin a saman madubi yace anshi.
Ɗagowa nayi na kalleshi , kallona yayi da salo mai tsuma zuciya wasa yayi da harshenshi tare da cewa bisimillah yana duƙowa dai² yadda zai kawoshi wurin bakina , riƙe wuyanshi tare buɗe bakina ya saka nashi a ciki , da hannu ɗaya ya riƙemin ƙuguna yana wasa da harshenshi a bakina , kyarma jikina ya farayi tunda uwar data kawoni duniya idan ba Alhaji mai gidan "yanci ba babu wanda ya taɓa shiga bakina sai Dikko , nashi kuma ba irin na Dikko bane ba dan salon na Dikko daban ne , me ye kike kyarma ? Ba tare daya cire bakinshi ba ya tambayeni ? Kaina na girgiza alamar babu , dafo kaina yayi ina kallon idonshi cewa bakya so ne ? Ina so na bashi ansa , cire bakinshi yayi tare da rumguneni saida ya ajiye ajiyar zuciya yace ba kin rainani ba , ni mahaukaci ko ? Zaki ga haukana a saman gado yarinya ,
Hmmm zan ɗoraki gadona badai kina so ki hau ba ? Shiru nayi ba magana , yaci gaba da cewa zaki hau yarinya kuma zakiji abinda kowa yakeji daga gareni , sakina yayi daga jikinshi yace ɗauko wancan makullin ki sanyo hijabi ki sameni waje , inda ya nuna makullin na ɗauka a lokacin harya fita palo yana gaisawa da "yan uwanshi , cikin farin ciki na fita ina mai jin daɗin yadda Dikko ya haɗamin bakinshi da nawa , hakan soyayya ne mai girma , wata munafukar ƙara nayi da murna na shiga ɗakina nima na zama mace naje ɗakin Dikko kuma ya rumgumeni da kanshi kuma ya sumbaci bakina wannan ranace mai daraja a gareni , saida nayi "yar rawa nace godiya nake mutumina.......
Bayan sun gama gaisawa yace ma Jiddah taje , Yayarshi tace ka ƙyaleta mana , miƙewa yayi tare da cewa ku gaida gida na gode sosai , yana faɗin haka ya fice abunshi , shi yana so yayi magana dasu dake su bahohi ne basa gane karatun kurma tou ya bar muku ita ku zauna tare ku dangi na kusa.
Dikko na fita suka fara zagin Sultana wai waccan "yar ɓeranyar yarinyar su take ma yanga ita mai ɗakin miji zataci ubanta , kan Jiddah suka juya haya² suke bata shawarar korar Sultana daga gidan Dikko , wai banda karuwanci kamar Sultana har ta iya yanga dan zata shiga ɗakin miji , Jiddah tace karuwa fa , Yayar Dikko ta ƙara ɗora Jiddah akan ta zage ɗamtse karta kuskusara tabar yarinyar nan ta huta har ta gaji ta bar gidan babu shiri , jakarta dake gefenta ta zage ta fito da wani magani na mata ta bawa Jiddah tace ki gwada wannan daga chaina nazo dashi bana ce miki komai ba labari sai naji ki a waya , haka suka ɗan ci gaba da ba Jiddah haske ga kuma ƙannensu da basu yi aure ba zaune suna ta sakin maganganu su haka suke tou ko Dikko yana nan haka zasuyi firarsu yana jinsu idan anyi abun dariya yaji yana iyawa yayi idan baya iyawa ya girgiza kai , ko kuma yace mata bakwajin magana....
Cike da zumuɗi na fita waje inajin farin ciki a zuciyata , rai a haɗe ya fito fuskar nan babu wasa , saida yazo inda nake tsaye yace muje yayi gaba nabi bayanshi ina rawar kai , kallona yayi tare dayin murmushin mugunta , yace shiga muje ya buɗe gefe ya shiga ni kuma na shiga mazaunin tuƙi naja motar da ƙwarin guiwa na fita daga gidan.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kwantar da kanshi jikin kujera a sakace yace goruba ya ƙarasa maganar yana lumshe idanuwan shi , cikin jin daɗi nace tou mai gida nayi yadda su Ashiru keyi , murmushi yayi tare da buɗe idonshi yayi min kallon gefen ido , murmushi nayi tare da ɗaga mishi gira , dariya yayi a ranshi cewa zaki natsu...
Saida na ibi hanya ya gyara zamanshi yace An mata na rasa abinda yakemin daɗi duniyar nan kamar zan mutu haka nakeji an dawomin da zuciya a bakin maƙoshi ya nuna saitin wuyanshi yana ci gaba da cewa an hanani na zauna lafiya kowa sai jifata yake kamar wani wanda yayi ridda , duk wanda ya raɓoni yasu² ma asiri suke ma junansu kowa so yake ya yafi ɗayan uwanshi a wurina , abun ya tashi ya koma jefe² mutane suna cewa wai duk wanda zai zauna dani sai yayi ɗamara da neman taimako idan ba haka ba yanzu akai mutum ƙiyama a dawo , ashe ma ba iya su suka tsaya ba nima ɗin so suke su kashe ni gaba ɗaya na zama kamar wani sakarai na zama wani ɓawon ayaba kamar bani ba haka nakeji na wallahi da raina ya ɓaci sai in zama wani zararre meke damuwana ? Dafa kanshi yayi yana hawaye yace ni kaina sai yanzu nake ganewa na zama mahaukaci na gaban feji wai wannan wane irin masifa ne ? Na rasa ina zansa rayuwata naji natsuwa , shiru nayi banyi magana ba , dan na lura yana cikin ɓacin rai na barshi ya sauke damuwarshi ko zaiji salama a zuciyarshi , ci gaba yayi da cewa abun bai tsaya a ni ba yana neman ƙetara iyaka , nafa gaji na gaji................. An mata wai meke damuwa na don Allah ,
Horn nayi aka buɗe get na shiga jikina a sanyaye , jiki a sanyaye ya jawoni jikinshi bayan nayi parking ya fashe da kuka yana riƙe kanshi da hannun haggunshi yace { surbajo waikowanna tayan gin Allah , a andi yaw an dunda in an huddi anduki min minajado , idume² gadaimi dun najabe gin Allah , ahn............ade'iti , to mirugga hugondube le ahan daga kuwanaibeyan e direba'en Ashiru en bedillai komoi rakkilayan mihoshsheta midillida emada midalai katsina misomi e masifa } abinda yake cewa An mata wai mike damuna don Allah , kinsan ciwo na tunda kece kika fara gane ni mahaukaci ne dame² nake yi na mahaukata don Allah ke.......... Kinyi shiru , tou zan kori duk wani wanda yake tare dani daga masu aiki direbobi su Ashiru kowa zai tafi ya bani wuri zan ɗaukeki nidai zan bar katsina gaskiya na gaji da masifa....
A tausaye na kalleshi nace kayi haƙuri Dikko ba'a kora maƙiyi kuma a cikinsu baka san waye yakeyi ba karka kora kuma karkayi nisa dasu , nasan wannan saboda Bello da Babana ka san mutane suke koya maka darasin rayuwa , ko maƙiyi ya tafi dawowa akeyi dashi karka bari maƙiyi yayi nisa da rayuwarka barshi kusa dakai kana karatunshi ta haka ne kaɗai zaka iya ganinsa sannan kuma kasan inda ya dosa , taya zan karantashi tunda na zama mahaukaci kuma ai kece kika ce ni mahaukaci ne , kayi haƙuri bazan sake ba insha Allah , meya haɗaka da Suwaiba ?
Da yanayin damuwa Dikko yace fita ki shiga ciki ina dawowa bai bani amsar tambayar da nayi masa ba , fita nayi , daga inda yake zaune ya koma kujerar dana sauka yaja motar kamar walƙiya ya ɓace daga gidan , ajiyar zuciya na sauke tare da juyawa na shiga ciki , ta inda yabi dani daren ɗaurin aure nabi na wuce har na isa ɗakin daya kulleni yasa nasha wani abu a kofi daya kira shi da service , a gefen gado na zauna nayi tagumi Dikko da fulatanci kuma shi naga Mamanshi buzuwa ce dan bata da hausa mai kyau shi yasa yakeyin wata irin magana shima hausar dai duk bata riƙe musu baki ba , Babanshi shine irin yarenmu amma baƙaƙen fulani ne sune na daji kenan amma bana tunani ya iya yare gaskiya tou a ina Dikko ya iyo yarenmu.............???
Zuwan Suwaiba....
Da gudu ya shigo gidanshi a dai² lokacin da aka fito da Suwaiba daga mota aka zaunar da ita saman keken guragunta , ita taji labarin auren Sultana ance mata ta auri wani matashi mai "ya "yan banki ta taho cin arziƙi bata san Dikko take aure ba , tou ita dai zata faɗa abinda ya kawota , bayan yayi parking ya fita da sauri dan hankalinshi baya wurinsu ciki zai shiga da ƙarfinshi saboda yasa abi mishi Al ' Ameen amma wanda yabi Al ' Ameen in yayi haɗari shine aka kira Dikko dan number Dikko ya bayar ,
Yana gaf shiga Suwaiba tace wayyo Allah na shiga3 ku maidani mota da sauri karku bari ya ganni kashe ni zaiyi , Dikko daya shiga da É—an gudu ya dawo baya da sauri jin muryar ta , bayan idanuwanshi sun tabbatar mishi itace ya juya gaba É—ayanshi yace saina kashe ki.............
Kalmar kisa daya anbata tasa su Ashiru fitowa da gudu , dan baya faɗar kisan da wasa cikin yanayi mai tada hankali dasa tsoro yake furta kalmar , da gudu ya nufi wurinta yana saina kashe ki , wallahi saina kasheki...... Yau bazaki sake guduwarmin ba , kafin yaje wurinta suka riƙeshi kuma shi baya so suna riƙeshi yana fassara riƙon da an maidashi wani sakarai tou da an riƙeshi shine yake ida firgicewa yayi ta fizge² yana zabura yana faɗar saina kashe.....
Ina yake.......... Zaki faɗamin ko saina kashe ki , riƙe suke dashi sosai irin riƙon da sukayi mishi ya bashi damar yin tsalle daga jikinsu ya kai mata wani irin ɗimautaccen halbi tun a wurin tayi fitsari na farko , ƙara riƙeshi sukayi ya birkice , palo aka taho da ita , shi yasa da Sultana tace idan ka bari ta gudu saina faɗa masa , tou shi Ashiru shine ya kawota palon dan ayita ta ƙare....
G R A ya koma yana jiran isowar Al ' Ameen , amma har 12 na dare babu Al ' Ameen ba labarinshi domin Mardiyya ta mishi waya cewa Suwaiba tazo gidan karya dawo , kuma itace ta fita taje ta anso saƙo ta dawo shi kuma ya ɓace cikin gari abunshi da motar Jiddah , Dikko ganin Al ' Ameen bazai dawo ba yasa ya haƙura ya bar gidan kuma gashi zaiyi tafi idan Allah ya kaimu gobe amma idan harya kama Al ' Ameen na lahira saiya fishi jin daɗi , ita kuma Suwaiba a gabanta ya faɗa cewa idan har ta ƙi faɗar sunan mutumin nan injishi a ƙware mata fatar jikinta babu sauƙi , shi kuma yaron shi da yayi haɗari a wurin rijiya mai suminti an dawo dashi katsina yana asibiti , kuma Dikko yaje ya duba shi , saida ya gama abinda zaiyi a cikin gari ya nufi goruba.......
Da ɓacin rai sosai ya dawo goruba , tuni Sultana ta manta da tayi bacci , ajiye ledojin daya shigo dasu yayi sannan ya cire kayan jikinshi daga shi sai short nicker ya matsa ya fara tashin Sultana daga bacci , baccinta yayi nisa dan haka ta sake gyara kwanciya ta rufe idonta , jawota yayi bakin gado , buɗe idona nayi cikin yanayin bacci , Dikko na gani tsaye daga shi sai gajeren wando , da sauri na rufe idona na sake buɗewa , ɗan buɗe bakinshi yayi kaɗan yaja iska da wani irin yanayi yace tashi na dawo yayi maganar cikin raɗa.
Tare da matsawa wurin wayarshi da ake kiranshi , kai amma Dikko baida kunya in banda iskanci basai ya ɗaura zani ba sai kawai yazo ya tsaya haka ƙarere a gabana ko kunya bayaji , tsoki nayi tare da kauda kaina gefe ina kallonshi da wutsiyar idona , kunga bashi da ƙiba ko amma daya hunce yana da ƙirar ƙarfi irin nasu na masu ɗaga abun ƙarfi wanda suke motsa jikinsu , juyowa yayi ya zauna saman dressing mirrow inda ake jera kayan shafa yaci gaba da waya da turanci yana min wani irin kallo.
Ta saman idona na kalleshi shima yaci gaba da kallona da yanayin ido zai raina fata , yanayin kallon da yayi min yasa naji zuciyata ta karaya tsoro ya kamani lokaci guda jikina ya fara kyarma da sauri na sauko daga saman gado a tsorace nazo kusa dashi nace na bari , riƙoni yayi da ɗayan hannushi wanda baya waya dashi ya nunamin irin kofin ranar nan da idonshi , kallonshi nayi yayi min irin murmushin da nayi mishi a mota shima ya ɗagamin gira kamar yadda nayi masa ,
Zanyi magana ya rufemin baki da hannushi yaci gaba da magana a waya da idonshi ya nuna karkimin kuka , cire hannunshi nayi na koma saman gado na kwanta , har na samu damar komawa bacci bai gama wayar ba , bayan ya gama wayar ya kashe wayoyinshi gaba É—aya ya nufi inda take kwance ya sake tashinta yana cewa ai yau bacci bai ganki ba , bake mara kunya ba , an turke ka mahaukaci munafikin miji sai kuma wata kalma data daÉ—e tana zugar min zuciya da kika faÉ—a ma Umar wai ni Dikko nine zaki gauraya dani ?
Tou ki tashi mu gauraya dani dake duk wanda ya raga ma wani shi ba ɗan Babanshi bane ba , badai kin rainani ba , tou na auroki mun zama ɗaya bana so ki tausayin min kuma idan kin ragamin baki haɗu ba ƙaramar yarinya dake tashi ga kazar nan ga komai nan na kawo miki ki anshi daren farko da ƙoshi a wurina ,
Abinda ya wuce bai kamata ana dawowa dashi baya ba , ni nawa ɗabi'ar kenan dawo da anjima yanzu inajin farin ciki yayin dana ke zalintar wanda nafi ƙarfi nakanyi murmushi ko dariya yayin da wani yakeyin kuka ko yake cikin halin tashin hankali , nidai nasan aka share miki fili dani nafi ƙarfinki a saman gadon ma nine oga hannunshi ya kawo yana ƙoƙarin cire min kayan jikina yaci gaba da cewa ki tashi ki gyara gadon nan kamar yadda kika ga nayi a daren aurenmu idan kin gyara kuma kije ki rufe ƙofa zanyi wanka na shirya nahau saman gado na jiraki kizo ɗaukar fansar shekaru biyun da kike jiran zuwansu yau ga abun ɗaukar fansar a gabanki ba tare da shekarun sunzo ba , kinga kin rufe ɗaki babu wanda zaiji kuka na ba bare in saka ran mai kwaceni a hannunki sai kinji tausayina kin kyaleni.
Ai ni na yafe maka , maƙale kafaɗarshi yayi cikin shagwaɓa yace ni ban yafe ba saifa an fitar da rainin nan yau hankalina zan kwanta zanyi tafiya ne shi yasa nake so ko a waya naji muryar gabana zai faɗi , kinga idan bana nan duk inda nake idan kika cemin Dikko kar kayi zan kiyaye saboda karki sake kulle ƙofa , a dai² lokacin daya buɗe ziff in rigata ya cireta daga jikina tare da saukoni daga saman gadon , na ƙwace da gudu na koma ina kuka , ke.......... Bana san wani kukan munafurci ba kinsan zaki gauraya dani ba kece ai kika faɗa da bakinki ba nine na matse bakin kika fada ba , nidai dan Allah bana san haka , cikin ɓacin rai yace sauko , Dikko dan girman Allah kayi haƙuri , na rantse da girman Allah bazanyi haƙuri ba yau sai kin gauraya dani , da nayi niyar ƙyaleki amma ɗazu da kikacemin munafukin miji shi yasa zakici kaza ki bada tukuici idan ba haka ba ni zan gauraya dake , ƙara fashewa nayi da kuka wurgomin makullin ɗakin yayi yace sauka ki kullo ƙofar , cikin kuka na sauka tare da ɗaukar hijabina , ki cireta tun kafin in sa ki sauke duk kayan jikinki , ajiyewa nayi zanja zani na sama yace ke........ Karfa ki bari na ɓaci.
Juyawa nayi na kalleshi ya ɗauke kanshi gefe yana murmushi hannunshi a saman kofin , kulle ƙofar naje nayi na kawo mishi makullin yace kije ki ɓoye abunki inda bana iya ɗaukowa kar inji wahala in gudu , banyi magana ba na ajiye a gefenshi na gyara gadon , bayan na gama yace zo ki sha , cikin ɓacin rai naje na ɗauka na shanye yau ma kamar na ranar ne cikin kuka na riƙe Dikko nace ngode , cikin iskanci yace a , a yau ba'a nan zaki gode ba bari sai kinji yadda nake a wasan danbe.
Juyani yayi na bashi baya ya kwantar da haɓarshi a saman kafaɗata yana sauke wani irin numfashi mai saukar da kasala ganin yadda na riƙe jikina yasa yayi wasa da gashin gemunshi a wuyana lokaci guda tsikar jikina ta mimmiƙe jikina yaci gaba da kyarma , cikin wata irin marainiyar murya yace ke kuma kazar auren naki da kuka zaki ci ? Banyi magana ba dan ina cikin yanayin damuwa ganin Dikko nake kamar bashi ba wallahi , ni duk abun a baƙunce yazo min ina hasko baya data wuce shi yasa nake kallon daren yau kamar a mafarki , duk ya zaneni da bulala mari halbi kuma yau zai kwanta dani.
Shima bai sake magana ba ya jani zuwa toilet , tare mukayi wanka kuma har akayi wanka aka gama idona a rufe yake dan Dikko bashi da kunya ko na misali , saida yayi alwallah ya fita ya barni a toilet in nima nayi na fito,
Nima dai kamar yadda yayi a daren farkon Sadiyya da Jiddah haka yayi a nawa , bayan mun gama ya miƙe tare da zare jallabiyar daya saka ya matsa jikin gadon yana cewa zoki nunamin yadda kike so na kasance , bara na baki satar ansa , mu ƙaddara wannan shine filin danbe an saka kuɗi masu yawa , dani dake mune "yan wasan kuma kowa yana jiran kowa sai aka haɗamu a wasa , da farko kafin ki shiga filin ki nemi albarka gado , sai ki hawo da ƙwarin guiwar ki , yadda ake wasan zaki riƙe kaina goshinki hanci zasuyi dai² da nawa , zakiyi magana da salon yarinta sai ki kalleni kallo ɗaya zakimin saiki rufe idonki ki fara tunano duk irin muguntar da kika iya ta yadda zakiyi nasara a kan abokin wasan naki , karki yadda ki faɗi idan kika bari na buga miki game over ta wannan hanyar zan riƙa horaki duk lokacin da kikayimin laifi , banza nayi banyi masa magana ba , yaci gaba da cewa daga lokacin na tashi daga Dikko zan koma ubangidanki a fagen jarumta , harararshi nayi cikin kuka ban masa magana ba har yanzu.
Murmushi yayi cewa ba damuwa , ƙudi yayi kaɗan mu ƙaddara abun da kowa yana jiran kowa ni dake , nine nayi miki irin raini da kikayi min aka haɗamu a wasan wane irin duka zakimin idan kika kamani , har yanzu banyi magana ba kuka nakeyi cike da soyayya ya kalleni yace karki damu nine ɗan wasan ai , ba damuwa bara in sakoki a filin Allah yaba mai rabo sa'a ya ƙarasa maganar yana dawowa inda ya barni ya ɗaukeni ya ɗorani a saman filin wasa........
20/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA....* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 79
Kifa kaina nayi saman katifa bayan ya saukeni a gado saboda kunya a raina kuwa ina jinjina girma da rashin kunyar Dikko , maganganun Yazeed ya fara dawomin sai kuma Inna da tace Dikko tantiri ne tunda kina so kin sama ga fili ga mai doki , wannan shine filin ni nice dokin kenan , zuciyata tace Allah sarki Sultana wallahi Dikko mugu ne.....!
Birkitoni yayi yana kallona yace yau zakiji idan ni Dikkon banza ne , kece zaki ba kanki labari idan niɗin na wofi ne ? Kuma yau zaki sheda niɗin ɗan Babana ne domin da bakinki zaki sa musu albarka da suka haifoni suka baki ni kyauta yau zaki tabbatar da na haifu kuma ni ɗin ɗane hada gyara , ya ƙarasa maganar yanamin kallon da bana so........
Kayi haÆ™uri , albarkoki wallahi "yar mata , dan Allah ðŸ™ðŸ», sai inyi haÆ™uri in zama munafukin miji ? Umm ummm wallahi sai an fitar da raini kowa yasan matsayinshi , kayi haÆ™uri fa , wai in Æ™yaleki ? Nama zama sakarai kenan , duk haÉ—ashi da Allahn da nayi fur Dikko yace bayajin yaren da nake magana dashi , cikin É“acin rai nace tou kar Allah ya baka haÆ™uri kayi duk zalincin dan na baka haÆ™uri sai kake ganin kamar inajin tsoron ka ne ? Dariya yayi tare da cewa ai nasan wannan bakin tsiwar bazaiyi shiru ba , tsorona kuma daga yanzu zai fara ziyartar zuciyarki ko a waya kikaji muryata sai kinyi ladabi bare kuma ki ganni kamar haka , ya Æ™arasa maganar yana tuÉ“e zanin dake jikina , da sauri na dafe Æ™irkijina na matse cinyoyina , yanzu baya ko murmushi yayi min wani irin kallo tare da cewa taso ,
Cikin ɓacin rai na tashi tare da rufe idona na matsa inda yake durƙushe , riƙe fuskata yayi yace buɗe idonki , fashewa nayi da kuka nace Dikko na bari don Allah , rungumeni yayi a jikinshi cikin wahalalliyar murya yace ba abinda kikayi min An mata da farko dai ina baki haƙuri kiyi ƙoƙarin ɗaukata kinji jarumata , ina da masifa jarabata bansan irinta ba , ni ban haɗa mace da komai ba bana neman mata kuma bana sabgarsu ban taɓa zina ba saida ƙaddara ya ratsa min a kanki hankalina bai kwanta ba saida na auroki na samu natsuwa , kiyi haƙuri akanki nasan daɗin mace dake na fara kuma akanki na iya , ni bana kallon iskance² amma duk wani logo na mata a tafin hannuna yake bana da sauƙi , mace kuma ni kaina tausayi take bani idan na riƙeta a gado bana ma mace kawaici haka kuma bana lallaɓata zanyi ƙoƙari na murje shekaruna kafin su sauka dan wata rana inaji ina kallon mace bana iya mata komai , yanzu ko inajin ƙuruciyata ina da lafiya babu inda yakemin ciwo a jikina jini babu inda baya halbawa yaudai ina miki sannu da jiki ɗaukar fansa ko soyayya ? Shiru nayi naci gaba da kuka , bana san kuka bana san yagushi sannan bana san magiya duk idan kikayi zan ida warwarewa gaba ɗayana , kalli agogo , ƙin kalla nayi naci gaba da kuka , yace tou yanzu 1 saura kwata kinga dare ne karkiyi kuka da ƙarfi kindai san kin kulle ƙofa da makulli ya ƙarasa maganar yana latse gefe da gefen kumatuna da yatsunshi na buɗe bakina da sauri saboda zafi.
Dariya yayi tare da yin irin maganata yace Dikko mugu ya ƙarasa maganar yana haɗe bakina da nashi daga durƙushen ya fara hawa jikina yana sakin ƙarfinshi , a hankali nake tafiya ina sauka yana ƙara sakin nauhinshi har na kwanta saman gadon ya kwanta saman jikina sosai yana fitar da wani irin numfashi daga hancinshi mai sa jiki ya zama matacce , bakinshi a nawa yace ke buɗe idonki idan bana kalloki taya zan samu natsuwa ,
Buɗe idona nayi ganin Dikko a wani irin yanayi yasa na firgice , murmushi yayi tare da cewa idan kika sake rufe idon nan ke zaki nemeni wallahi kinji dai na rantse ya ƙarasa maganar yana ɗaure fuska yaci gaba da cewa ki kalleni da kyau kema ki koya , ƙara tura bakinshi yayi sosai a bakina yadda ko maƙoshina bana iya haɗawa nunfashina ya fara sama , ɗagamin gira yayi tare da dafe kaina cikin wani irin salo yaci gaba da sumbatata yana lumshe idanuwa , duk inda yasan idan ya shafo a jikina zai firgitani saida ya bashi haƙƙinshi cikin salo mai wahalar gogewa a zuciya motsin kirki na kasayi nakai matakin da nake buƙatar a fara buga wasan , haka Dikko yaita ranfa dani kamar mage ta kamo ɓeran daya bata wahala , kunsan sai ta gama wasa dashi ta bashi wahala ya suma ya dawo sannan take cinye abunta....
Saida ya gama ɗimautani sosai ya murgina ƙasa na koma samanshi yana sauke wani irin numfashi kamar wanda yasha gudu ya gaji , hannu na ya kamo nasan inda zai kaishi dan haka da sauri na rufeshi , dakel yayi dariya kaɗan yace misali idan nace bazanyi danbe ba a wannan yanayi ya zakiji ne ? Gabana naji ya faɗi a zuciyata nace daka ɗauki alhakina , jijjigani yayi ke bakiji na ne ? Idan kina so nayi sai kince don Allah kayi idan bakayi danbe ba zan mutu a shagwaɓe nake so da irin wannan kallon ya nunamin , idan ba haka ba yanzun nan zan saukeki daga saman gadon nan inyi bacci , yana faɗin haka ya juyamin baya ya lulluɓe da bargo tare da rufe idanuwan shi,
Fashewa nayi da kuka nace Dikko wai miye haka don Allah , ba tare daya juyo ba yace ba kuka zakiyi ba sai kin faɗa zanyi idan ba haka ba yau saida kiyi kwanan haƙuri dan na gaji ya ƙarasa maganar yana yaye bargon ya ajiye a gefe ɗaya yace kallarni fa , da sauri na kauda kaina gefe ɗaya ni kaɗai nasan abinda na gani , to kin huta yayi maganar tare da sake jan bargon zai rufe jikinshi , riƙe bargon nayi kallon raini hankali yayi min yace kina so ne ? A kunyance na ɗaga kaina , to zo ki rumgumeni sai ki faɗamin , kwanciya nayi a saman jikinshi jikina yana kyarma na nace don kayi haƙuri idan bakayi danbe ba zan mutu na faɗa a shagwaɓe kamar yadda ya nunamin da irin kallon daya gwadamin nayi mishi , riƙeni yayi a jikinshi yace fa'idar neman miji mutunci ne , ke kina ƙarawa kanki daraja da martaba a zuciyarshi , babu girman kai ko nuna kafi wani yayin da kake kwance da iyalinka , kuɗi mulki ko saurata duk basa aiki a dai² irin wannan lokacin kar kiyi tunanin nine zan riƙa nemanki daga yau kinajina ko ? Eh , kuma kullum idan ina nan banaso ki ragwantamin ko alwallah nayi ki bada himma ki warwareta naji zan canja wata , ina sanki ne so adadin yadda bazaki iya ganewa ba bana so wata mace ta fiki martaba a zuciyata ta fanni iya karemin haƙƙina a nan ida har tafi ki nan tasha dake , ki riƙe akalata sosai idan kuma kika kasa zan ƙara aure ne kawai tunda na lura duk lusaran mata natattara a gdan , ke ɗinma da nake tunani gara ke tun ban taɓaki ba kin ɓare baki kina mani kuka da wata ƙyarmar banza , tsoki yayi tare da nunamin yadda zanyi masa nidai baƙuwar maza ce iskanci nawa a baki yake , har yanzu jikina bai daina kyarma ba gaba ɗaya kunya ta dameni na ƙagara aje filin yaƙi dan inji irin tashi jarumtar.
Ya gane abunda nake nufi sarai amma dake ɗan iska ne sai ya basar yaci gaba da wani luguidani , kai wallahi Dikko kwallon ɗan iska ne , lokaci² yakanyi murmushi sai kuma ya ɗaure fuska yayi min kallonshi mai tsayawa a rai , can ya gaji yace tunda a haka za'a tsaya sauka ki ɗaukomin kayana , girgiza kaina nayi alamar a , a , tou ai naga karatun yaƙi gaba An mata , a , a ɗagoni yayi daga gefenshi da nake kwance sama ya ɗagani daga kwance har saitin cikinshi , da ƙafa ɗaya ya buɗe ƙafa ɗaya tawa bayan yayi addu'a ya sakoni a saman alƙalaminshi da ƙarfi ya shigar dani , wani irin ihu nayi shi komai nasa sai yayi cuta , jifa yadda ya shigar dani da ƙarfin tsiya babu imani ba zaibi sannu ba kuma yanaji ana dakatar dashi , ke rufemin baki ba kece kikace inyi miki ba muje , cikin kuka nace wai miye haka ? Ni bance miye ba saike dan baki da kunya ci gaba da nushi lokacin ki ya fara....
Ƙasa motsi nayi sai kuka nakeyi dan azaba ji nake kamar zan mutu wallahi , idonshi yana kan agogo ni kuma ina kwance a ƙirjinshi ina kuka , shafa bayana yayi yace karfa ki manta a filin wasa ake yayi maganar yana ƙoƙarin ɗagani na ƙara komawa na kwanta kamar wata doluwa , da hannunshi yasa dan ɗagani na ƙara komawa na kwanta yace munafukin miji fa , iyakar turkewar kenan ? Murmushi yayi tare da cewa lokacin ka ya fara Dikko.
Birkicewa yayi tare da jawo ƙafafuwana ya ɗora saman kafaɗarshi yayi min runfa da ƙirjinshi hannunwan shi ya ajiye gefe da gefe na sannan ya kalleni yace , nasan zakiyi ji mamaki ina magana da yarenki ko ? Tou ni bana sauƙaƙawa gaba duk ƙarantar ta haka kuma bana san raini duk wanda ya rainani saina sa ya raina kansa ,
Tun ranar da kika faɗamin zaki ɗauki fansa shekaru biyu hankalina bai kwanta ba saida na tabbatar duk wani logo na fulani na kamo tasharshi , ba'a fini iya mugunta ba amma ina da yafiya , nakan manta da ɓacin rai na fuskanci rayuwar gaba kuma haka na faɗa miki a ke a dole shekara biyu zaki ɗauki fansa ga abin ɗaukar fansar kin gagara ramawa , kinyi maganganu akaina marasa daɗi amma kamar yadda kikace abinda ya wuce bashi da kyau dawo dashi baya na barshi amma sai nayi hukunci hada marin da kikayi min wallahi.
Daga haka yaci gaba dakai nushi kaɗan² , har yanzu ban dainajin azabar saukar dani da yayi a alƙalamin da ƙeta ba , cikin kuka nace Dikko da zafi fa , Ey amma ai nushin yana da daɗi ki ɓoye hawayenki kila zasuyi miki amfani anjima yanzu sharar bage aka fara gyara kwanciya ki anshi hukunci , a wannan rana na raina kaina nayi ihu nayi kuka har muryata ta shaƙe nayi yagi Allah ya isa ban yafe ba na faɗa bansan adadi ba , a zuciyata kuwa ina tunani Alhaji mai gidan "yan ci baimin irin wannan muguntar ba , Dikko yace duk Allah ya isa ɗaya saina ƙara mata muntuna 20 akan duk awa ɗayar da zanyi , kuma idan kika sake yagushina saina rama baki fini haƙora ba bara ki sake cizo na kiga yadda zanyi dake saboda ba'a cizo ba'a yagushi a danbe ki bada himma kiyi nasara lokaci yana tafiya miki idan nayi nasara akan ki ƙaryarki ta ƙare....
Dole na haƙura na ƙyaleshi , a hankali yake tafiya yana ƙara murza totir lokaci yana tafiya yana ƙara yawan gudunshi a haka har ya warware gaba ɗayanshi , ya manta da ƙarantar da yake tausayi ya neman hanyar da zai sama ma kanshi natsuwa ya ƙanƙameni , wani irin kukan kissa yakeyi Dikko mai daɗin sauti da ratsa zuciya mai wahalar mantuwa a rayuwa , a hankali yake fitar da sautin kukan cikin sagwaɓa Dikko baijin magana wallahi jarumin namiji ne a fagen daga da iya jan linzamin mace a filin wasan danbe , lumshe idona nayi cikin wahala a raina nace tabbas babu mai irin jarumtarshi a mazan bariki Jiddah , ɗaya kawai na ɗana nasu wato Alhaji bansan yadda suke ba amma sai sun haɗa da "yan dabaru , duk namijin da baya iya sauke haƙƙin iyalinshi ya zama lusarin miji a wurin mace kuma ta samu kafar rainashi idan ba'ayi dan mai gona ba anyi da mai gayya , idan bata raga maka ta wani wurin ba tabbas zata martabaka da ƙoƙarin kare martabarta da kayi a fannin kare haƙƙin aure , ɓanɓare Dikko na farayi yi dan na kusa ɗaukewa , da sauri ya ƙara riƙeni a shagwaɓe yace wayyo ya faɗa tare da ƙarayi min kyakkyawan riƙo wai , wai Allahna a , a An matana ƙyaleni , ki ƙyaleni.......
Ya zalinceni iya zalinci ya cuceni ya nuna fin karfi yadda yayi min alƙawarin saiya sumar dani dan na kiyayeshi na gane shi ba sa'ar wasa na bane ya turani suma naje na dawo kuma tabbas tsoranshi ya shiga zuciyata kamar yadda yayi alƙawai , nayi kuka na bashi haƙuri amma saida ya tabbatar yayimin lullusar kece raini ya barni bayan yasa nayi masa godiya da addu'a Allah ya ƙara mishi lafiya a fagen filin wasa yayi ta nasara a wasan danbe ,
Yayi amfani da ƙarfinshi ya bani wahala ya zagaya a wasan farko kuma an faɗar dani , na biyu ma shine yayi nasara a na 3 akayimin game over 3/0 wasa ya ƙare kuma Dikko ya rainani daga yau kuma har zuwa wannan lokacin ban daina kuka ba dan ƙetar da yayi min , bai sake bi takaina ba yaci gaba sabgar gabanshi ko kallo na ba sakeyi ba , bayan ya tsarkake jikinshi ya saka jallabiyarshi ya ɗauki wayoyinshi da makullin mota ya tun kari hanyar fita ,
Ina zakaje ? Na tambayeshi , bai kalleni ba ya juya yace Al ' Ameen nake nema nasan yanzu ya gama iskancin guje²nshi ya dawo , nifa tsoro nakeji gaskiya , cikin masifa yace kije kiyi ta jin tsoron ke baki da kunya ma ni zaki faɗa ma tsoro ya ƙarasa maganar yana min wata irin harara gabana naji ya faɗi , da sauri na komar da kaina na kwanta , tsoki yayi tare da buɗe ɗakiya fice cikin ɓacin rai. Saida na tabbatar ya fita na sauka gado a gajiye ina gunguni cewa ɗan masifa tsakar daren ma ba'a hutawa da fitina Allah ya baka lafiya ,
Ina shiga toilet in na tunkari inda naga ya tara ruwa tare da tara hannuna ruwan zafi ne tsoki nayi tare da tsugunawa dan toilet in bashi da kwamin wanka kuma ba cikin ainahin gidanshi bane inda ya siya ne wurin ne kaɗai ba'a rusa ba gidan maƙota kenan.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya isa G R A ko tsoron dare bayayi tunda ya tafi ranshi yake ɓace harya isa da wani irin tuƙuƙin fushin ci ma Al ' Ameen mutunci ya isa har yanzu bashi gidan motar daya fita da ita itama bai dawo da ita ba , ɗakin Jiddah ya nufa gaba ɗayansu daga ita har Mardiyya suna bacci saida ya gama kallesu tsaf sannan ya kashe hasken fitilar yaja ƙofa ya nufi ɗakin Sultana...
Sauke katifar gadon yayi tare da buɗe plow bed in duk abinda yake san gani babu , tsoki yayi tare da maida katifar ya nufi wadrof duk saida ya zubar da kayan ciki akwatinan lefenta ma haka ya zazzagesu ƙasa yaita janye²n kaya babu wani damuwa , palo ya koma nan ma babu wani sheda duk kayan daya zubar bai maida ba , Allah ya sawaƙe wahala ya faɗa tare da fita daga ɗakin.
Koda na fito daga toilet a gaban gado na durƙusa rabin jikina a saman gado naci gaba da baccin wahala , bacci yana ɗaukata na ganshi a gabana yana saina kwakwale idonki , a tsora ce nace wai mene ne damuwar ? Ka fita hanyata meye nasaba na dakai kullum ka kwakwale , me Nana tayi maka ka kwakwale idonta ? Me Aunty Mamy tayi maka ka kwakwale ? Kuma me yasa daka cire ake mutuwa ? Ansa zan baki ko kina so na fita rayuwarki ? Eh ka fita hanyata , tou ina wayar da kikayi min record , Dikko ya cire m card , idan har Dikko ya baki record in nan nayi miki alƙawari zan nuna miki inda aka binne asirin da akayi mishi , wani mutum ne yazo ya kamashi da kokowa yace idan ka faɗa saina kashe ka , kai ku riƙota karku bari ta gudu , wayyo na kwarara ihu tare da miƙewa a firgice a dai² lokacin da Dikko ya shigo , dakamin tsawa yayi wai wannan koken banzar ni ya fara isata , wuce kije ki kwanta , zanyi magana yace ki wuce nace bana san iskanci da Allah , fashewa nayi da kuka , yace mizanate , wai zai zaneni , ƙyaleshi nayi naje na kwanta ban daɗe da kwanciya ba na tafi bacci dan duk jikina wani irin ciwo yakemin.
Dikko kuwa gefen gado ya zauna yana latse² a waya , bayan wani lokaci kuma ya juya ya tsare An mata da kallo tana sauke ajiyar zuciya lokaci² ta kuka , murmushi yayi kaɗan yace An mata rigima ubangiji ya zaunar damu lafiya ya kare mana fitina Allah ya ƙara ninka miki soyayya ta fiye da wadda nake miki kunji irin san kan nashi fa.
Yau ko bacci É—aya Dikko baiyi ba yana zaune duk abun duniya ya dameshe har lokacin sallah asuba yayi , da zai fita masallaci ya tashi Sultana ya wuce , ina gama sallah na kwanta a wurin na ci gaba da bacci ,
6:33am ya dawo kuma a lokacin muka bar goruba , a mota nake tambayarshi memory yace baisan ina yake ba , zan sake magana yace nayi masa shiru yanajin ɓacin rai , shiru nayi ban sake magana ba , shi kuma yaci gaba da lissafin tafiyarshi a zuciyarshi.
Zasuyi hannun riga da Momy zai fita katsina a daren yau su kuma zasu bayyana a gobe idan Allah ya kaimu har suka isa gida da abinda Dikko yake saƙawa kuma yake warwarewa , har ɗaki Dikko ya rakani kuma har yanzu Jiddah basu ma san gari ya waye ba amma gaba ɗaya duk wani ma'aikaci dake gidan maza da mata kowa ya tashi ya kama hidimar gabanshi , gidan cike kamar ana wata hidima saboda babu wanda ba'a gidan yake zama ba idan dai har a gidan yake aiki , ƙaton gida ne sosai saboda yafi gidan goruba girma bama a haɗawa kowa da ɗakinshi palo bedroom da toilet akwai masu dafa abinci a saman icce can bayan gidan a manya tukwane a cidasu kuma a basu albashi , ko ɗan uwa gareka ka kawoshi shidai Dikko babu abinda ya dameshi amma saboda fitinar Jiddah wai nice zan tashi nayi musu girki , suna fa cin daɗi domin abinci da nama baka isa ka raina ba gaskiya Dikko yana da cikar arziƙi ubangiji ya ƙara rufa asiri.
A harmitse na samu ɗakina kallo ɗaya nayi masa na nufi gado , Dikko yace a haka zaki kwanta kina ganin ɗaki a haukace , ban masa magana ba na haye gado saida na kwanta nace wanda ya ɓata zaizo ya gyara , da fushi ya nufoni na sauka gado da sauri kafin iso na nufi inda kayan suke na fara tattarawa ina kuka , dama kin bari na sameki a kwance.........
Yana faÉ—in haka ya fita yana faÉ—a , É—akinshi ya nufa danyin wanka , saida na gyara É—akin nan tas na shareshi na goge sannan na kwanta naci gaba da bacci.
Tunda ya fita sai bayan la'asar ya dawo tare da Nabeela , nima tuni nasha baccina na tashi nayi wanka na kame mutuncina cikin riga da zani na atamfa , yau Jiddah ita kuma fitina take ji tunda na fita take sunkuyawa iyayena zagi amma ban tanka mata ba sai Dikko baya nan zanci uwarta kafin ya dawo , tou ashe bani ɗaya ba har Dikko bata raga mishi kina jiyo hayaniyarta tana masa rashin kunya , ran Nabeela idan yayi dubu ya ɓaci kamar Yaya DK Jiddah kema rashin kunya wallahi ta sire mata kamar fitar tusar safe.
A palon ƙasa yabar Nabeela yazo ɗakina cikin sauri² yace zo ki gani , tashi nayi naje wurinshi nima na ɗaure fuska kamar yadda naga yayi , murmushi yayi ba tare daya kalleni ba hankalinshi a kan takaddar yace yau an raba an fitar da haƙƙin kowa , an bawa shi mijin ƙawar Momy na ɗakinsu domin alƙalin haka yayi rabo ɗaki² , na ɗakin su Baba aka bada shi wa wannan mutumin da yayi ƙararki , nasa an rabasu aka fitar dana gidanku kuma za'a ciccira su a fitar da kowa kema An mata da Allah ki yafe musu kuɗin nan yayi maganar yana kallona da damuwa kalli kiga ya nuna takaddar yana gwadamin yadda rabon gadon ya kasance ,
An fitar dana Kakarsu Hafsa ita da tayi takaba aka sake kasawa aka fitar dana ɗakinsu Dady saina ɗakin su Baba , an raba aka fitar wa da Baba ƙarami nashi gidanku yara 61 da mata 3 ni tafiya zanyi idan sun gama kasanfinsu sa ajiye miki naki ya ƙarasa maganar yana jawoni jikinshi , riƙe kafaɗarshi nayi da hannun dama na tare da kwantar da kaina a jikinshi.
Ni zan tafi ga Nabeela nan na taho miki da ita ta tayaki zama kema ki samu mai ebe miki kewa , bana san faɗa karki kuskura ki biyewa Jiddah kuyi faɗa kinji ko ? Nace tou , zan baki makullin mota kuma bana san yawo mara amfani na yaddar miki da izinina ki fita duk lokacin da buƙatar fitar yazo , shiru nayi banyi magana ba , ɗagoni yayi daga jikinshi yace a wl'a a yetti , tou baki ce kin gode ba , cike da damuwa nace miyyetti.
Shima da yanayin damuwa yace , midillidai e maraicimada , tomi tunitake emada minanai beldun wala miwonda e mada miwadai katunanimada kullum , jemmare keya idewdi mahimmanci sosai to a han idan tunitida jemmare keyah e dume ittata kewamada ? Abinda yace wai zan tafi da maraicinki , idan na tunaki zanji babu daÉ—i bama tare zanyi ta tunaninki kullum , daren jiya yana da muhimmanci sosai a wurina idan kika tuna daren jiya da me zaki ibe kewa ? Fashe wa nayi da kuka tare da sake komawa jikinshi na kwanta ina hawaye , dariya yayi sosai tare da saukeni daga jikinshi yace inzo muje É—akinshi yayi gaba nabi bayanshi ina kuka.
Jiddah kuwa sai babbaka uwar ashariya takeyi bansan abinda akayi mata ba , Nabeela kuwa ɗakina tasa aka sauke mata kayanta bayan Dikko ya woner ta cewa idan ta kuskura An mata tace tayi mata wani abu ko taji wahalar zama da ita ko tayi baƙin ciki uwa uba tayi kuka zai kasheta ne ba ruwanshi , gabanta sai faɗuwa yakeyi ya wannan zaman zai kaya ne......... ?
Muna shiga ɗakin ya bani makulli wai in kulle ƙofa , zan ruga ya riƙoni cike da damuwa yace haba An mata , na Allah kiyaye fa zaki bani yi haƙuri don Allah yanayin maganar cikin nuna haɗama da zaƙuwa , zanyi magana yace yi haƙuri haba An matana Dikkonki fa cikin lallashi yakeyin maganar idonshi ya canja launi zuwa kalar jaraba , nidai don Allah ka ƙyaleni , cikin ɓacin rai yace bana san yawan magana zaki yi da arziƙi ko in danneki in kwata ta ƙarfi da yaji ne , a , a me yakai ta ƙarfi , to anshi , makullin ya bani yace rufe ƙofa cikin kuka naje na kulle ƙofar na dawo , bargo ya shimfaɗa a ƙasa yace jirani ina zuwa , wurin firij ya matsa ya fiddo wani ɗan madaidaicin galan ya zubo wani abu a kofi ya taho gabana ya durƙusa tare da zaunar dani yace tou sha , yana kai min kofin a bakina , wannan miye ? Da Allah sha malama kina ɓatamin lokaci , nidai kullum saina sha fa , Eyyy yauɗin ma zakisha idan ba haka ba zan ɗura mikishi ne ta hanci bata baki ba , one , two , three , tsaya zan sha , tou sha , ansar kofin nayi daga hannunshi nakai bakina miƙewa yayi ya fara kwance belt inshi.......
Shegiya butulu tsinanniya butulal cin amana kamar karuwar data zauna a garin legos aka zazzabga mata bulala , dariya Suwaiba tayi tare da cewa ko zaku kasheni bazan faɗa ba , ni har kun nunamin iskanci nida naci tsaye a gefen hanya nake miƙewa a bani tukuici ba'a katsina ba saida na tsalleke jahohi da dama naje iskanci daga ƙarshe na tare a ƙarƙashin gada can legos kaga kuwa rashin kunya ta tafi duk yadda kuke tunani , Ashiru yace ku barta mai gida zanje in ɗauko yanzu yana faɗin haka ya juya Suwaiba tace Ashiru kar muyi haka dakai zan faɗa ko saurarenta baiyi ba ya fice , Suwaiba ta darkaka wani irin ihu mai tada hankali tasan Dikko hankali wala.....
Daƙel na dawo ɗakina da bargon da Dikko ya kwanta dani a samanshi , ya bani makullin ɗakin goruba wai idan na samu lokaci inje in gyara ɗakin sai makullin mota da kuɗi , Nabeela na gani zaune a palona sallama nayi na wuce ciki ina kuka , tasowa tayi ta biyoni matar Yaya me akayi miki ne , banyi mata magana ba na hau saman gado na kwanta tare da tura fuskata a bargon naci gaba da kuka , gefena ta zauna wai inyi haƙuri idan naji babu daɗi kuma me akayi min nake kuka , maganar Dikko naji a palona dashi da Jiddah yana cewa bari in anso in baki ni An mata bazata biye miki ba , kuma idan tayi miki wani abu wanda bai miki daɗi ba ki faɗamin zan rama miki , ni nafi ƙarfin in faɗawa miji ya kare min faɗa saidai inci uwar yarinya , tou ni kuma kika taɓata zakiji da ɗaci.
A tare suka shigo yace An mata ina makullin motar dana baki , ba tare da nayi magana ba ko na ɗago na miƙa mishi , ansa yayi yace gashi na kashe fitina , ke An mata anshi na mota ta , wallahi bazata hau motarka ba saida ta anshi ta hannun Al ' Ameen dole , Dikko yace na rantse da girma Allah baza ta hau motar nan ba yadda tayi gwanjonta wa ke ta gama da ita har abadan duniya bata maimaici da mota tunda tana da ni , ai itace take hawan ta tun farko ka mayar mata kayarta , bazan mayar ba kuma yanzu bata hawanta , tou saidai ta fasa fita sai ta zauna harsai ka dawo , sai ta fasa uzirinta saboda bana nan ? Sai ta fita inda ranta yake so idan ke kike aurenta sai in gani , ba abinda ya dameni wata mota ce dai bata isa ta hau gidan nan ba saita hannun Al ' Ameen danma ta samu an bata motar a gidan ubanta ai a nepep take zuwa duk inda take zuwa , gidan mijinta ne yadda na saka sadaki na auroki haka na biya na aurota , nan ba gidan Babanta bane gidan Dikko ne kuma Dikko bazai bar matarshi tayi yawo a nepep ba wasu ma sunyi rawa bare ɗan makaɗi hannuna ya riƙe tare da cewa kiyi amfani da wannan motar kafin in dawo idan kuma kika bari ta anshi makullin ta baki motar Al ' Ameen zasu kaiki su baroki.
Yana faɗin haka ya fice , Nabeela da Jiddah suka bi bayanshi dan rakiya nidai banje ba , Jiddah bansan abinda ya firgita ta ba , saida suka dawo daga rakiya Nabeela ta wuto ɗakina , Jiddah kuma sai ɓaɓɓarka zagi takeyi saita kamu sunan Dikko ta luƙaƙa mishi zagi , wai gidan Dikko shine auren ƙaddara tana da saurayinta wanda yafi Dikko komai akaje aka cuci rayuwarta ana "yar murya da yanzu tana can ƙasar waje tana rayuwarta mai daɗi , sai ta kashe auren Dikko marar zuciya nace ya sakeni ɗan jaraba mayen mata yaƙi ya sakeni ,
Nabeela ta fita da gudu tace ke jaka har kin isa ki kira auren Yaya ƙaddara sakarar banza jaka dake , wace ce ke ? Ƙazamar banza bakisan halinshi ba ne amma idan kika sake zaginshi uwarki zanci ɗanyaɗanyarta bazan gasa ba , masifa ta cakuɗe tsakanin Nabeela da Jiddah sukayi ta masanyar kalamai nidai ban fita ba saboda sunfi kusa tunda da Maman Dikko da Maman Jiddah uwarsu ɗaya ubansu ɗaya ni ina ruwana ?
Duk wannan faɗan Mardiyya saida tayi musu video ta turawa Dikko , Nabeela ta dawo ɗaki tana ta zage² ni lokacin ma har na fito wanka ko inda take ban kalla ba dan abinda na lura yarinyar bata da kunya ko na misali , kayana na saka na fita dan sama ma cikina abinda zanci.
Bayan sati 3
Gaba É—aya yanzu Sultana ta kwanta ta samu wata irin natsuwa ta musamman ta rage rawar kai domin an kammala saukar da akayi mata dan warware sihirin da Bello yayi akanta , yanzu zuciyarta ta natsuwa ta daina bata umarni akan muguwar É—abi'a sai shakkun Dikko da takeji ko waya ya kirata a É—aÉ—É—are takeyin waya dashi bata sakin jiki kamar can baya duk bayajin daÉ—in hakan.
Momy ta dawo , a ranar data dawo ranar tazo gidanmu ta yalyaɗa ruwan rashin mutunci ta zageni tai mani gori ta mareni tai mani ƙwanya kuma tace tana nan tana jiran dawowar Dikko ko zai mutu saiya sakeni ai dan yasan zata dawo shi yasa yabar ƙasar , tafa zuba ruwan rashin mutunci na wuce misali haka Jiddah kuma tasa an ƙwace makullin motar Dikko an bani na wanda Al ' Ameen ke hawa , Umar kuma ya buga ya faɗa mishi ya kirani yace kar in sake in hau motar nan idan zanje wani wuri in faɗa masa zai turo akaini ,
A ɓangaren Inna har yanzu bata nemeni ba , kuma ni bansan number da take amfani dashi ba a can india , ƙawayenta dai sukan zagayoni lokaci² kuma suma wai basu da number Inna ,
Zama na da Nabeela banajin wata damuwa zata dai shata surutunta iya iyawarta banda lokacinta danni bana fira da yarinya gudun raini ta raina mutane "yar iska ce ta gaban jarida , bata da kunya yarinyar kwata² danni ko wuri ɗaya bana kwanciya da ita dan nasan tana zaune dani kuma tana karatun rayuwata ne shi yasa nake kiyayewa dan nasan banda haƙuri.
Yazeed ya kirani kuma yace min yana san gani na wai zamuyi magana mai muhimmanci duk abinda nake nayi ƙoƙari mu haɗu gobe , nace masa zan duba,
A ɓangaren Bello yana so yayi wani abu amma bashi da wadatacciyar lafiya dan tunda suka fita daga hannun Dikko gaba ɗayansu basajin daɗi ta lafiyarsu sukeyi a halin yanzu bana gabansu !
Hmmmm a daren yau ƙawayen Jiddah suka bayyana a gidan..... Dan sunso zuwa tuni Jiddah ta dakatar dasu wai sai Dikko baya nan , to sunji ya tafi sun zo kuma kowa ta ɗuro iskanci cike da kanta sun taho..........
22/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 80
*_TASHAR TSAKAR GIDA , AN GAISHE DA MADUGUN SHIRI UMAR MAI SANYI..._*
Wata irin shewa sukeyi tasu ta matan tasha , gaba É—aya sun haukata gidan da hayani suna ta nuna yadda sukayi maraicin junansu , bayan sun gama murnar haÉ—uwarsu kuma suka runguÉ—a sukayo kicin É—ina cike da gadara da nuna isa kamar irin gidan baban nan nasu.
Ina tsaye ina ɓare magi suka shigo dan na daina cin abincin gidan kwata² saboda duk idan na ci sai naji tashin zuciya sai nayi amai hankalina yake natsuwa shi yasa na zage nake girkawa da taimakon Nabeela.
Ko inda suke ban kallah ba naci gaba da abinda ya shafeni tunda nasan iskanci ne ya kawo su dan bama kicin ɗaya da Jiddah kowa da nashi , Nabeela tana zaune gefe saman kujera tana waya da ƙawarta suka faɗo tare da fara buɗe² , ke Mardiyya ƙara ruwa ki ƙara yawan magi ki zuba shinkafa bama cin kuskus naci uwar kuskus naci uwar mai dafa kuskus ɗin yarinya tayi magana in shaƙe mata wuyan uwa , duk inji Jiddah fa,
Hahaha suka gaggaɓe da dariya gaba ɗayansu tare da kashewa aka rangaɗa guda cikin iskanci , wacce tayi hoto dani tace yarinya kuma tace uhum taga yadda zamu naɗa mata shegen duka a gidan nan idan kin isa ki kalleni koda motsin kirki kiga yadda zamu ci uwar ɗiyar ɗan wasan caca , suka sake sheƙewa da dariya a dai² lokacin da Mardiyya zata zuba ruwa a tukunya ,
Jiddah kuma ta kwashe magin gabana tana cewa babu fa a gidan ubanta amma dan wani kilbibi hada wani zuba magi sai kace an saba ci a gida , wacce tayi hoto dani tace tsoho harya karci ƙasa baya gane testing in magi baya gane gishiri , Mardiyya tace taya kuwa zai gane bayan baki ya mutu da giya anzo nan za'a nuna mana ƙaryar rashin kunya dama ɗan talaka bai iya samun wuri ba , kashe waya Nabeela tayi tace ke ya zaki ƙara mana ruwa bayan kinga muna sauri shi yasa muke dafa abu mai sauƙi , kallona tayi sannan taci gaba da cewa matar Yaya ya kina kallonsu bazakiyi wani abu ba ? Kinfa san inajin yunwa a gabanki zaki bari a dawo mana aiki baya.....
Ke karki zuba ruwan nan , Jiddah tace zuba , Nabeela tace idan ko kika zuba su za'a samu matsala , ansar ruwan Jiddah tayi tare da zubawa tace ni na zuba "yar gadon rashin kunya marasa ragowa , ni bana neman suna haka kuma bana neman gindin zama tare da Dikko bare a kaÉ—amin ganye , masu so asan dasu kuma suke so su zauna su haÆ™uri ya duba dan gudun kar a korasu a koma cin Æ™anzo da garin kwali danni a gidan Babana ban rasa komai ba , hehehehe bafa garin kwali ba garin kwaki , Oh 🤦ðŸ»â€â™€kinsan abinda baka sani ba danni bansan da labarin gari ba saida na haÉ—u da Caca
Yarinya tayi iskanci ta koma gidansu aje can aci gaba da cin abinda aka fi wayau dashi , Mardiyya tace sai Aliyu ya sake sakata a caca , Jiddah tace ni kuma zan siye gidan in ajiye karnuka tunda shi dawakai ya ajiye , cikin ɓacin rai Nabeela ta taso daga inda take itama dai "yar babbar bala'e ce ni kuma fita nayi daga cikin kicin ɗin cikin ɓacin rai , wani irin mari Nabeela ta zabga ma Jiddah tare da ɓaro ruwan daga saman gas cikin masifa tace shin ba nace karki zuba mana ba ? To zan sake zuba wasu idan akwai wata "yar ƙaramar mara kunya ta sake taɓawa taga idan ban ƙona mata fuska ba banzaye ƙazaman banza duk kun cika mana wuri da tsamin dauɗa.
Jiddah tace ni kika mara ? Nabeela tace an mareki dan ita Nabeela ba Sultana ta shigar ma faɗa ba cikinta take ma yaƙi sake ɗora tukunyar tayi saman gas ta zuba wasu ruwan , itama Jiddah ta sake ebowa ta ƙara zubawa akan wanda Nabeela ta ɗora sannan ta yanka mata mari wai ta rama marinta , sake ɓare ruwan Nabeela tayi suka sake tashar magana zuwa harshen turanci kowa yana faɗawa ɗan uwanshi kalamai masu zafi daga baya kuma suka fara bige².
Kokowa ta rikice tsakanin Jiddah da Nabeela tun a kicin har suka fito waje , Jiddah na cewa ke har kin isa kice muna tsamin dauɗa , Nabeela tace nafa sanki tun baki san abinda kike ba duk ƙaryar shafa turaren da saka suturar waye ya koya miki in ba ni ba ? Wato yanzu kin waye iskancin ki zai sauka a kaina ko ? Mutuncin da duk wani feleƙe ma nice na siya miki rigar mutunci a gidan auren idan na zare hannuna daga kanki kashin ki ya bushe dusar gero dake...
Mardiyya kuwa komawa tayi daga gefe taci gaba da video , duk yadda akayi a raba faɗan ƙin rabuwa sukayi domin Nabeela tsatstsaga gareta itama kafiya kamar na Dikko kuma ƙarfi gareta dan duk ƙawayen Jiddah shigar mata sukayi , faɗa yayi nisa kuma Nabeela taƙi ta haƙura gashi sunyi mata taron dangi dole saida aka kira Babbar ɗakinsu Dikko wacce ke zaulayarshi tana cewa saida tayi aure aka haifeshi , itace tazo kuma ko ita Jiddah bata ragamawa ba saida ta zagate tasss ta uwa ta uba.
Da mamaki ta kalli Jiddah tace ni kike zagi ? Na zageki dangi masifa ahalin rashin mutunci , bana tsoron uban kowa a cikinku duk wacce tayimin sai inci uwarta , haƙuri taba Jiddah tare da cewa ita Nabeela tazo su tafi , Nabeela tace bazata ko ina ba tunda bata jin tsoron kowa kuma idan ta sake ganin yarinya a kicin ɗin sai ta kunna mata wuta , tayi tsoki ta nufi kicin tana gunguni ,
Ina kwance ɗaki ta shigo taita zagina wai nice munafuka nazo da asiri dan na firgita Jiddah na hanata zaman lafiya da mijinta , saida ta zageni tas itama tayimin mari da ƙwanya ta tsitstsinen min albarka tayimin gori sannan ta tafi.
Daga gidan Dikko G H ta wuce taje ta faɗawa Momy sai an miƙe tsaye da addu'a akan Jiddah yau taga aikin asiri dan tunda take da Jiddah tun kafin asan zata auri Dikko tana ganin mutuncinta kuma tana darata ta amma yau saboda aikin asiri ita Jiddah ta zaga wai mune dangi masifa ahalin rashin mutunci bata tsoron uban kowa a cikinmu duk wacce tayi mata sai taci uwar yarinya , Momy ki duba lamarin nan fa duk da dai niɗin ina da zaulaya ina shiga sabgar yara amma ko Dikko da nake masa hawan ƙawara ina masa abinda bayajin daɗi duk rashin mutunci sa yana ɗagamin ƙafa ni Jiddah ta zaga ?
Gaskiya Momy kija linzamin abun tun wuri idan har kika bari Dikko yasan halin da ake ciki zaije yayi abinda bai kamata ba idan ya dakar musu "ya ko ya saketa zuminchie zai lalace , ya saki wannan karuwar tun abun nan ana iya dakatar dashi kafin yakai fagen da bakya iya tsawatawa , Momy tace taje zatayi magana da Dikko kuma zatayi magana da Jiddah.
Mardiyya ta turama Dikko video n faÉ—a ya gani amma baiyi magana ba kuma bai kira Nabeela ba nima daya kirani ban É—auka ba , ya kira har ya gaji ya daina kira dan kanshi.
Mardiyya ita ta dafa abinci wa su Jiddah kuma haka ta barbaɗe shi tas da asiri takai ma kidahumar ta lashe , ni kam kafin Nabeela ta gama ta dawo har nayi bacci tsabar ɓacin rai......
Haka dai nake dogara rayuwar gidan Dikko babu daÉ—i tsakanina da "yan uwanshi sai kyara sai hantara ga gori basa so na ko kaÉ—an , Momy kuwa sai bawa Jiddah shawara takeyi tana É—orata a hanya yadda zata zauna lafiya amma tana nan shawarar ke amfani da zaran ta tafi Mardiyya zata warwareta kaf !
Ƙawayenta ma haka suke wulaƙanta ni san ransu yanzu kwata² ma na daina fita ko palo kullum ina ɗaki sai sun gama iskancinsu sun tashi nake fita da sauri naje nayi abinda zanyi na dawo ɗaki bawai dan ina tsoronsu ba saidai dan gudun rayuwar da zanyi dan a halin yanzu idan nabar gidan Dikko bansan ina zanje ba , gidan Kaka yafi ƙarfina saboda gidan ɗan uwan Inna ne kuma ban auri ɗansa Sultan ba an buɗa , gidan Baba ƙarami bazaije gareni ba Dikko yasa an ɗaureshi saboda ni , Inna bata nan kuma har yanzu ban samu wayarta ba kuma babu wanda yace min yana waya da ita , idan na tashi hankali nayi faɗa da Jidda tabbas Momy zata iya korata idan an koreni nikam ina zanje ? Dan haka zaman gidan Dikko shine mafita zanyi haƙuri idan ma na tayar da hankalina Dikko ya sakeni bansan ina zan nufa da rayuwata ba ,
Ga Bello ga Dady suma duk ni suke jira , shin rayuwar bariki zanje inyi ? Shin zan dawwa a harkar bariki kenan ? Haƙuri shine maslaha kuma na haƙura , ina tare da damuwa sosai na rasa wa zan faɗawa inji sanyi dan haka kawai zan faɗawa Yazeed , dan yace mu haɗu a washe garin waccan ranar banje ba amma ina jira idan ya sake kirana zan fita idan har ya yadda zai bani mafita kuma zai zamar min garkuwa kawai zan fita daga gidan Dikko inje in auri dai² ni sai in zauna lafiya....
Kwance nake a gado ina nazari yadda rayuwata zata kasance idan na fita daga wurin Dikko , tsikar jikina ta tashi a dai² lokacin dana tuno ranar da zai tafi , yadda lokacin ya kasance yazo a zuciyata ya tsayamin kukan da yakeyi nakeji a raina sautin kukanshi cikin shagwaɓa Dikko baijin magana dana tuna sai inji hankalina ya tashi tsigar jikina duk ta mimmiƙe bana tunanin komai sai san kasancewa dashi , Dikko jarumin namiji ne a fagen daga ya iya jan linzamin mace a filin wasan danbe cikakken namiji ne mai zanawa mace natsuwa mara gogewa a rayuwa taya zan iya rabuwa dakai ne.....................?
Muna waya da Yazeed kuma har yanzu nace masa zamu haɗu amma banje ba banma fita ba gaba ɗaya , har Dikko yayi wata 3 da sati3 da tafiya kuma har yanzu ƙawayen Jiddah suna nan kuma suna hantara sbd sun nemeni da les naƙi , sun nunamin duk wani karuwanci naƙi yadda , da sukaji haushi sai suke tira Jiddah ta riƙa jamin sharri a wurin Momy , haka zata turo "yan uwan Dikko su wulaƙantani wani lokaci su mammareni , kawayen Jiddah kuma sunyi alƙawarin zasu jamin sharri wanda bana iya fitar dakaina a wurin Dikko wai ya sakeni in koma inda nafi wayau lokacin nice zan nemesu idan na nemi na abinci da wurin zama na rasa , gashi banda lafiya ni bansan abinda yake damuna ba sam bana san hayani kuma bana san yawan magana , Mardiyya kuwa tuni ta cire hoton da ƙawayen Jiddah suka ɗaukeni a wayarsu wanda suka ɗaukeni washe garin da aka kawoni ta turama Dikko bansan iyakar sharrin data faɗa ba ko na kirashi waya baya ɗauka rabon da nayi waya dashi tun ranar data tura mishi hoton ya turamin kuma ya kirani yace shi bazai sakeni ba duk abinda naji ina iyawa inje inyi kaina nayi ma, ba bugu ba zagi amma idan na kasheshi na huta , gashi shi baya tsayawa ya fahimceke idan dai ya sauke nashi shikenan ,
Na rasa wanda zanyi shawara dashi , da na fara tunanin su Amisty sai zuciyata ta gargaÉ—eni da na fita hanyarsu gara dai na faÉ—awa Yazeed tunda tun farko shine ya faÉ—amin cewa idan ina da damuwa na faÉ—a masa zai bani shawara , wayata na É—auka na kirashi bayan mun gaisa nace yau zan fito ina zan sameka ne ? Wai yana jibiya , zanzo jibiyar wurin ina kake ne ? Ba'a kai jibiya ba kinsan me mujiya ? Ina ne haka ? Hirji matattara tantirai , yaushe zaka dawo ne ? Sai DK ya dawo , yaushe zai dawo ne ? Gobe idan Allah ya kaimu , zanzo hirjin , sai kinzo yana faÉ—in haka ya tsinke wayarshi.
Dakel nayi wanka na shirya cikin riga da siket na material cikin kayan da Yazeed ya kawomin wanda wurin kai ɗinkinsu ne Bello ya sossoka min wuƙa , kwalli kaɗai na shafa sai viseline dana shafama bakina kaɗa bayan na shafa mai da powder a fuskata , Nabeela tace nayi kyau kuma saida tayimin hoto , komawa nayi gefen gado na zauna bayan ta gama ɗaukana hoton ina neman sa'ar fita , wato inaji Dikko bai faɗa zai dawo ba kawai zaiyi mamaye ne dan da Jiddah tasan zai dawo ƙawayenta zasu bar gidan kuma dole zatayi gyara na musamman dan taci burin dawowarshi duk kuwa data kira aurenta dashi na ƙaddara ne.
Nabeela tana shiga toilet wanka na ɗauki jakata gyale na da makullin goruba na fice abuna , a bakin get na samu Umar muka gaisa yace Hajiya ina zakije ne ? Goruba na faɗa kai tsaye , yo ke baki san mai gida ya dawo ba ? Yana ina ne ? Yana abuja ai shi yasa ƙawayen hajiya zasu tafi nine na samo musu mota tasha baki ga har an fara fitowa da kayansu ba , waye ya faɗa musu ya dawo ne ? Ni na faɗa musu nima abinda yasa na sani Ashiru yacemin na gyara masa ɗakinshi kila shigowar dare zasuyi gobe idan Allah ya kaimu , daga cewa kayi shara sai kazo kayi ta surutu kai bakinka me yasa baya shiru ?
Dariya yayi tare da cewa tubani neke ranki ya daɗe , murmushi nayi cewa tou bani aron motarka na dawo , bani yayi na wuce na shiga naja nabar gidan cike da damuwa , naso ace Dikko ya samu ƙawayen Jiddah yaci ubansu , amma nasan ba saboda su yayi shiru da dawowarshi ba nasan dan Al ' Ameen ne , saida na fara zuwa goruba na gyara ɗakin na kama hanyar jibiya.
Wata irin zuba Al ' Ameen ya goge da boka ya kirashi a waya ya sanar dashi cewa Sultana tana da ciki , tashin hankali gashi Dikko zai dawo gobe kuma yanzu Zaria bata zuwa gareshi kuma boka ya tabbatar ma Al ' Ameen ita kanta Sultana bata san tana da cikin ba , idan kuma har Dikko ya dawo cikin bazai zubdu ba duk irin baƙin asiri da za'ayi shawara ɗaya yasan yadda za'ayi a zubar da cikin dan wallahi ɗa namiji ne zata aifa ,
Cike da tashin hankali Al ' Ameen ya kashe wayar ya kira Jiddah ya faɗa mata cewa idan har ta kuskura aka haifi cikin nan wallahi ƙaryarta ta ƙare duk yadda za'ayi a zuba mata abinda zata ci cikin ya zube , cikin rashin fahimta Jiddah tace wake da ciki ne ? Al' Ameen yace Sultana mana Jiddah tace yaushe ta samu cikin kuma waye yayi mata cikin ? Al ' Ameen yace mai aurenta mana , Jiddah tace ƙarya ne ai Yaya bai kwana da ita ba , Al ' Ameen yace tou tana dai da ciki kuma ɗa namiji zata haifa idan ko ta haifi ɗan nan na rantse da girman Allah ƙaryarki ta ƙare kisan yadda zakiyi da cikin nan ko maganin zubar da ciki ne ki bata a abinci ko abun shanta , saida Jiddah ta sunsunkuya zagi ta luƙaƙashi sannan tace ta daina cin duk abinci da ba itace ta dafa ba a gidan nan dan uban uwarta , shawara dai Al ' Ameen ya bata akan ta kira Yayyen mai gida ta sanar dasu ya faɗa mata abinda zata faɗa musu , godiya Jiddah tayi tare sa kashe wayarta tana neman mafita , kam ya zata yadda ita bata aihu ba sai wata data zo ɗazu da safen nan.........? Bazai yuwu ba koda duka sai sun fitar da cikin nan.
Da tambaya har na isa inda Yazeed yake tunda ni bansan wuri ba mutane ne sukayi ta É—orani a hanya har naje , bayan na isa na sanar da Yazeed nazo na faÉ—a masa inda nake yace yana zuwa , an daÉ—e sosai sannan yazo ta wata munafukar santa ya fito da mota , gaba yayi nabi bayanshi munyi tafiya mai nisan gaske wanda har na fara tunanin na kawo kaina , wato abun ba'a cikin inda za'a gansu sukeyi ba sunyi nisa da mutane , daga inda yace na sameshi zuwa inda ake wasan tafiya ce mai nisan gaske inajin su kaÉ—ai ne suka san wurin.
Muna isa na samu wuri nayi parking dandazon mata ne kamar ƙasa karuwai da suka ansa sunansu , murzajjin "yan iska da suka sha iskanci har sukayi gyatsa saboda lalacewa , wai ana gabatar da shirin wasan danbe babu jimawa , dan haka maganata Yazeed ya hana na faɗa wai in jira inga yadda ake wasan danbe sai muyi magana daga baya , haka mukayi ta ratsa mutane muna wucewa da yawa a wurin na sansu , Safiyya ɗiyar Baba ƙarami tana gani na ta taho da gudu tana zage² wai nice nasa aka kulle babansu , Yazeed ya dakatar da ita wai ta kiyayi kanta idan ba haka ba zai goge sunanta dama Kaka ta matsa masa yaa saka sunanta , laƙwas ta koma bata sake magana ba , gabana sai faɗuwa yakeyi nake bin bayan Yazeed , wato abinda na lura karuwan kila akwai manya akwai ƙanana domin an kasasu wuri daban² haka muka wuce har muka isa wani ƙaton wuri , tsakar fili ne na gida amma an zagaye wani wuri daban an ɗaga wurin da ciko yayi sama yadda duk inda kake zaka iya hange kamar dai yadda akeyin na restyling daga saman wurin kuma an ƙawatashi da wasu irin manyan katifai da pilaluwa an shinfiɗe da zanin gado ,
Wurin wasu lafiyayin maza ya kaini duk gajeren wando ne a jikinsu wai in gaisa dasu sune mazan da zasuyi wasa , murmushi nayi kaɗan na anshi karka rasa fuskata ɗauke da damuwa , bayan mun gaisa yace musu matar DK ce , DK 😳 suka zazzaro ido da mamaki sannan suka bini da kallo har naji babu daɗi , bayan sun gama kalleni tsaf sukace tou su babu ruwansu suka ci gaba da lissafin kuɗinsu , Yazeed yace taho nan ki kyalesu matsoratan banza ,
A , a , ni tafiya zanyi kawai mayi waya ai bansan haka wurin yake ba , Yazeed yace da Allah ki jira kiga danben dana baki labari kwanaki baki sani ba , a , a basai na kalla ba , wayarshi ya ciro a aljihu yana cewa tsaya ki gani mana kafin na ankara ya ɗaga wayarshi ya kwaso mu hoto solfie , zan masa magana akan me yasa ya ɗaukeni hoto Amisty ta shigo da gudu ta rungumeni cikin farin ciki da sauri na juya amma Yazeed ya ɓacemin , wata irin zuba ta ketomin yayin da zuciyata tace bakiyi zufa ba tukun ƙaryarki ta ƙare......
Amisty tace ai ana cemin kinzo kinji daɗin da naji , cikin tashin hankali na saki Amisty nabi hanyar da zan nemo Yazeed iya dubawa ta ban ganshi ba , tou me yake nufi ko ya ɗauka ne dan ya riƙa hansar kuɗaɗe a wurina kamar yadda na riƙayi a baya ? Kwawalwata tace ya ɗaukeni dan ya turawa Dikko idan ya gani zai sakeki shi kuma saiya ɗaukeki ya sakaki a danbe yana kasuwanci dake dan dama haka ya faɗa a baya.......
Dariya Yazeed yayi a dai² wannan lokacin cewa alhamdulillah nasara tazo haba ina zan bar DK da wannan babbar ƙaddarar ? Yarinya kyakkyawa mai kyan diri da siga mai ɗaukar hankalin duk wani lafiyayen namiji , kai ko mara lafiyar ya ganta dan ubanshi saita burgeshi munafiki ya samu "yar yarinya yana hutawa abunshi ai ba taka bace ba wannan nagartacciyar surar , tunda dai ban aura ba gara kowa ya rasa , ka tsere ma kaf abokanmu a naira riga mota matar ma sai kafi kowa ? Idan mun yadda kenan kai mana wayau , yadda nake ƙarƙashin ka gara na samu ko da macen na tsira , kai sarkin dabara kawai kaje ka ɗauko ɗanyen jini dan ka bamu wahala haka zamuje muna ganinta hankalinmu yana tashi to ni burina kawai ka saketa hankalina ya kwanta dan nan gaba yarinyar nan ta goge bata riƙuwa ga kuɗi ga hutu ga gayu dan yadda DK yake ɗan gaye dole komai nasa ya zama ɗan gayu , gara ni in kwasheta idan kuma bata aureni ba sai kawai in barta a wasan danbe nasan duk lokacin dana buƙace ta zan ɗan rage zafi uwa uba kuma zan linka arziƙi dan duk katsina banga irin mazan da zanba ita ba.
Na nemi Yazeed har na gaji ban ganshi ba , kuma na kirashi bai ɗauki waya ba , dan haka na haƙura na fito daga inda nake dubashi na sake dawowa wurin da ake taron danben a lokacin wurin ya cika taf tsit kake ji babu wata hayani ana kiran sunaye....
Hamida Aliyu Muhammed Binna , shine sunan da naji an kira tsagal² ta tashi ta shiga saman filin aka ɗauki ihu da tafi yayin da wasu ke busa usir , idan mutun ya shiga filin saiya tsaya ya kalli mutane sannan ya tuɓe kayanshi ya tafi da kwarkwasa ya hau saman katifa , sai a sake kiran wata itama haka zatayi duk sai an gama kiran sunayen matan sun hau katifa sai a kira mazajen da zasuyi wasan su jera layi sai aci gaba dakai naushi.
Banda lokacinsu domin ina tare da tashin hankalin daya fi wanda naga Hamida a ciki tunda ita tayi kuma kowa yasan tayi fita nayi daga wurin ina kuka , nifa ? Ina hotona zaije ? Kai nidai jakace.......
Aunty kusan abinyi fa dan Caca ciki gareta kuma wallahi ko ranar da aka kawota Yaya dani ya kwana a ɗakinshi kuma washe gari ya tafi amma tana da ciki , idan har ya dawo ya samu cikin nan zai yadda yace nasa ne saboda ta gama dashi za'a ɓata muku ahali shege ya fito a cikinku , idan kuma aka saketa ta fita da cikin nan shima idan ta haife cikin shima shine zaice nasa ne , gobe zai dawo meye mafita ? Zan shigo idan Allah ya kaimu suka ajiye waya , bata faɗawa Momy ba kawai ta yanke hukunci a kanta....
Sai bayan isha'e na dawo gida a gajiye a waje na bada makullin motar Umar a ajiye mishi idan ya dawo , Nabeela tana gani na tace ke kinji kunya kika shigo da cikin shege a gidan aurenki , kin É—irka dabkekiyar asara ai Yayan zai dawo zaki faÉ—a masa a gidan uban waye kikayi ciki...
Wata irin mummunar faÉ—uwar gaba naji na wuce ciki ban nuna damuwa ba , ikon Allah ashe ciki gareni ? Allahu akbar sai yanzu ma na tuna da yaushe rabon da inyi jinin al'ada , daÉ—i naji sosai a zuciyata addu'ata ta farko Allah yasa in haifi mai kama da Dikko komai da komai , tunani na biyu ya akayi suka san ina da ciki bayan ni ban gane ba ? Can su suka sani dai , kuma Dikko zaizo ya faÉ—a musu shine yayi cikin ba cikin shege bane ba , da farin ciki nayi bacci tare da tunanin Dikko.
Da asuba bayan nayi sallah bacci na koma , ban daɗe da kwanciya ba na tafi bacci yauma ya bayyana a mafarki na , kinga inda ya ajiye ne ko kuwa ? Ya tambaye ni , ban gani ba kuma na tambayeshi yace baya san surutu , tou albishiri na kwakwale amma yau ba'a mutu ba kina da ciki kuma zasu zubar da ciki kiyi ƙoƙari ki samoshi idan ba haka ba haɗuwa ta gaba tafiya ce babu fashi , waye zai zubar dashi , ta inda mutumin nan ya fito a ranar da nayi mafarki a goruba yauma ta wurin ya fito ya kamashi da kokowa , yana cewa waye yace ka faɗa ne ? Kokowa sukeyi sosai har mai cewa ya kwakwale ido ya samu damar cire abunda mutumin ya rufe fuskarshi , Al ' Ameen na faɗa lokacin da aka cire abun daya rufe fuskarshi a dai² wannan lokaci naji saukar bulali a jikina......
A firgice na farka daga bacci Jiddah da Yayar Dikko suke ta dukana babu ji babu gani , da sauri na sauko daga saman gado ina cewa me nayi muku ne ? Jiddah tace dole ki tambaya abinda kikayi tunda kinje kin samu an ɗuro miki ciki ke zakici dukiya tou Allah ya warware miki asiri tun ba'ayi nisa ba , riƙeni Yayarshi tayi Jiddah tayi ta kaimin duka a ciki da bokitin ƙarfe wani irin ihu nayi nunfashina ya tafi sama na kasa kwacewa , saida ta gaji sannan suka danneni ƙasa Yayar Dikko tayi min allura suka fita daga ɗakin bansan inda kaina yake ba.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Dikko ya faɗa tare da cewa Ashiru An mata wani abu ya sameta , Ashiru yace me kuwa zai sameta mai gida , Dikko yace tabbas wani abu ya faru wallahi dan naji a jikina wanda rabon da inji haka har na mata kiramin ita , duk kiran da akayi ma Sultana bata ɗauka ba , cikin tashin hankali yace kiramin Nabeela itama bata ɗauka ba , Jiddah yace a kira , itama bata ɗauka ba dan tabar wayarta a ɗaki tana ɗakin Dikko ita Mardiyya wai suna gyarawa , Mardiyya yasa aka kira tana ganin wayar Dikko ta fita daga wurin Jiddah sannan ta ɗauka , bayan ta gaishe da Ashiru yace mai gida yace kina gida ne ? Eh , tou meya faru a gidan ? Saida tayi dube² tace nidai naji ana cewa an zubar da cikin Aunty Amarya....
Kallon Dikko Ashiru yayi tare da cewa mai gida wai bata gida bayan ya kashe wayar , tsoki Dikko yayi cewa tafiya katsina ya kamani yanzu , Ashiru yace ka bari sai anjimar mana , umm umm muje yanzu , kallon agogo yayi yace la'asar tayimin a katsina.
Mardiyya kuma komawa tayi suka ci gaba da aikinsu , Nabeela kuwa bata nan bata san abinda akeyi ba dan tana makarata , su kuma hidimarsu sukaci gaba dayi mai kwalliya ta musamman Jiddah ta gayyato danni taci gayu yadda zata yaƙi zuciyar Dikko , Mardiyya ta tsareta da kallo mai tattare da maganganu.
Sai bayan la'asar Nabeela ta dawo har yanzu ina kwance a wurin da akamin allura na suma har na dawo da kaina na kasa ko motsin kirki wani irin ciwo cikina kammar raina zai fita , cike da fargaba Nabeela ta durƙusa gabana tace waye yace miki ana zubar da cikin shege a gida ? Daga na faɗa miki sai ki kashe kanki tou ni tafiya zanyi wallahi bakija min sharri , tana faɗin haka ta miƙe ta fara tattara kayanta , bata gama haɗawa ba Dikko ya bayyana a ɗakina misalin ƙarfe 4:29pm.
A tsorace Nabeela ta gaishe shi ta fita daga bedroom in , bai ansa gaisuwar ba ya nufo inda nake , hararata yayi cewa wani kuma sabon rashin mutunci ne kwanciya a ƙasa ? Yayi maganar yana ɗan tauna cingom bakinshi a rufe , kifa kaina nayi ƙasa dakel nace banda lafiya , me ya sameki ya tambaya cikin sigar lallashi....
Shiru nayi , da damuwa fa , banda lafiya ga naje wurin Yazeed kuma ban san laifin da nayi ma Dikko ya daina ɗaukar wayata ba , idan kuwa ya gano ni yau idan ya fara dukana waye zai ƙwaceni gashi ban iya tashi.........?
24/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA.....* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 81
Me ya sameki ne ? Ya sake tambaya a karo na biyu , nayi ɓari ne , kallon ɗakin yayi sannan ya dawo da kallonshi wurina yace wane ɓari ? Yayi tambayar a cikin rashin fahimta , ina da ciki ne shine ya lalace , ɓacin rai kwance a idonshi ya gyara zaman hular saman kanshi ya duƙo inda nake kwance sai yanzu ya lura da jinin dake kwance a wurin , shi bai gani ba amma Nabeela tun shigowarta ta fahimta , cikin tsananin ɓacin rai yace ban gane ba fa....
Ban sake magana ba daga haka dan maganar ta isheni kuma a wahalce nakeyinta , Nabeela........... Ya ƙwala mata kira da sanyayayyar muryarshi , da gudu ta shigo jikinta yana kyarma ta tsaya daga can gefe cewa Yaya gani , bai kalleta ba yace me ya faru ? Cikin rawar murya tace Yaya wallahi , tare ta yayi da cewa karki cemin wallahi² me ya sameta ?
Yaya ina makaranta , karki faÉ—amin kina makaranta me ya faru.............. ? Idan na sake magana zan kashe ki...... , cikin kuka tace matar Yaya ki faÉ—a masa abinda ya faru bayan bana nan , ke karki É—aukeni sakarai ai na ganta na kiraki , nunawa yayi da hannunshi ya fara one , two , three , four cikin rawar murya tace Jiddah........
Ba damuwa na Jiddah ba abinda ya sami An mata nake tambayarki , ƙara fashewa tayi da kuka ta sake kallona tana cewa matar Yaya kiyi magana , tashi yayi yaje gabanta ya yanka mata wani irin mari harsai da ta duƙe yace idan kika sake mata magana saina karya miki maƙoshi me ya faru........?
Yaya wallahi bana nan naje makaranta yanzu na dawo lokacin da zan tafi na barta tana bacci , a ina take baccin ne ? Saman gado , ya akayi ta sauko ƙasa to ? Kila ta tashi ne ta faɗi , jeki palo ki jirani zan fito idan kuma kika kuskura kika bar gidan nan na rantse da Allah saina baki wahala , cikin kuka tace tou sannan ta fita.
Dawowa yayi kusa dani , ya kalleni yanayin shi ya nuna yana nazari ne , bayan wani lokaci yace tashi , a tsorace na fara ƙoƙarin miƙewa amma na kasa , da Allah tashi bana san iskanci , tou na faɗa tare da tashi durƙushe dakel , tsugunawa yayi gabana yace ya akayi ciki ya lalace ? Yayi tambayar da harshe mai tada hankali , fashewa nayi da kuka nace Dikko , An mata ya akayi ciki ya lalace ya tsareni da idanuwanshi masu tada hankali idan yana fushi , kayi haƙuri na faɗa cikin rawar murya , bansan shi ba yaci gaba da cewa wato banda iskancin hotunan da kikayi har ma kike tunanin zan barki ciki ya zube ? Ba zubewar ciki ba yau ko naƙuda kikeyi saina zaneki , tashi kije ki gyara jikinki yana faɗin haka ya fita daga ɗakin.
Gaba É—aya ji nayi kamar an tsintsinkemin lakar jikina , idan kuma Dikko yasan naje wurin Yazeed wace matsalar zan fuskanta ? Ya zanyi ? Ni ba lalacewar cikin ne damuwana ba rayuwar da zan fuskanta idan ya gano cewa na fita naje wurin Yazeed , dakel na shiga toilet dan wanka ,
Cikin tsananin ɓacin rai yaje ɗakinshi , gefen gado ya zauna ya dafe kanshi , zuciyarshi tana mishi babu daɗi miƙewa yayi ya matsa jikin window ya zuge labile yana kallon yadda rayuwar gidanshi ke tafiya , kowa sabgar gabanshi yakeyi ɗora fuskar shi yayi jikin window ya dafa hannunshi a sama yana kallon waje , a zuciyarshi yake zance cewa An mata baki da lissafi ko kaɗan na rayuwa , ina baki dama ta rayuwa amma baki gane abinda nake nufi dake sai idan bana nan duniyar zaki san ni ɗin na gina miki rayuwa , baki da Baba mahaifiyarki ba take , take ba tana can ta kama sabgar gabanta tana gina sabuwar rayuwarta , baku da ahali mai kyau kwata² , Jiddah ce ta shigo ɗakin da sallama.
Ansawa yayi tare da juyowa ya kalleta so ɗaya ya koma yadda yake yaci gaba da zance zuci "yar rashin kunya da kinsan ina tausayinki iskancin da zaki zazzaga a gidan nan ba ɗan ƙarami bane ba mu zuba dani dake duk wanda ya fasa yaji kunya , tashi yayi a wurin ya nufi hanyar toilet yaga Jiddah zaune a gefen gado , ya akayi ne ? Ya tambayeta cikin kwarkwasa tace ba komai ta ƙarasa maganar tana kakkaɓa ido dan ibar mishi hankali , tou yayi jeki zanyi wanka , tashi tayi tana mummurza tafiya da salo mai ɗaukar hankali ta nufi wurinshi.
Murmushi yayi ya bita da kallo harta iso wurinshi ta shige jikinshi , ajiyar zuciya ya sauke tare da riƙeta sosai yana kallon fuskarta da tasha ado da kwalliya , ɗan shanye idon dama tayi tare da cewa nayi ne ? Sassauta ganinshi yayi tare da ɗauke idonshi baiyi magana ba , gyara tsayuwarta tayi ta fara rattafa bayani kamar yadda Mardiyya ta turota cewa.
Bayan Jiddah da Yayar Dikko sun gama dukan Sultana Jiddah ta kwakwkwaɗa mata bokitin ƙarfe a ciki suka danneta suka ɗura mata allura , suna gamawa suka fita a ɗakin , bata samu Mardiyya a ɗakinta ba data koma tana wurin Al ' Ameen , dan itama Mardiyyar tana gama ɗaukar video ganin zasu fito yasa ta fice da sauri ta ɓoye ƙasan bene , suna wucewa tayi wurin uncle.
Uncle gabana faɗuwa yakeyi fa , da Allah can matsoraciyar banza badai kinyi video ba ? Eh kwantar da hankali yau duk bala'e ni na faɗa miki gaba ɗaya gidan nan zai watse , tabbas idan mai gida yaji labarin ɓarewar ciki ranshi zai ɓaci , da zaran yayi fushi baya iya saita kanshi dan haka zai fara duka babu ji babu gani kuma bazai saurari kowa ba , abinda za'ayi yanzu ki faɗawa Jiddah idan mai gida ya dawo taje ta faɗa masa , murmushi yayi tare daci gaba da cewa zai sakesu gaba ɗaya , ita Sultana zai saketa saboda hoton nan , ita kuma Jiddah zai saketa ne idan ya daketa zatace bana auren duka sai ka sakeni dama mun rufeta da wannan asirin duk wanda yazo zatace bazata zauna ba sai an saketa tabbas saiya saketa , Yayarshi kuma bayanin hukuncinta yana wurin Jiddah dama itace ƙatuwar munafukar kinga sun rabu kawai sai kuyi aurenku ya faɗa yana murmushi , kina shiga sai ki haihu idan namiji ne sai mu kashe shi mu cinye dukiyarshi , idan mace ce sai a bari sai an ƙara , dariya sukayi tare da tafawa....
Bara inyi wanka in fito Dikko ya faÉ—a tare da fitar da Jiddah daga jikinshi , gefen gado ta koma ta zauna tana jiran fitowarshi shi kuma ya shiga toilet....
Lokacin dana fito daga wanka Nabeela ta gyara wurin dana ɓata tass kuma har yanzu bata daina kuka ba , ina fitowa toilet ta shiga da kanta ta wanke kayan dana cire ta wanke toilet in , bayan ta fito tace matar Yaya tsakaninki da Allah ni ina nan wani abu ya faru dake ? Ko inda take ban kalla ba na fara saka kayana.
Har Dikko ya fito daga wanka Jiddah tana nan , saida ya gama shiryawa yana saka kaya tace Yaya gaskiya abinda Aunty Rabiya takeyi bata kyautawa , Yayarshi kenan , ba tare daya kalleta ba yace me tayi miki ne ? A dai² lokacin da yake ɗaura belt a ƙugunshi , kaga dai ko ni kishirya Caca bana iya yimata irin abinda ita Aunty tayi , a dai² lokacin da yake saka riga , yace kiyi maganarki kai tsaye mana yana kallon kanshi a madubi tare da gyara zaman rigarshi , Caca ce take da ciki shine tace sai ta zubar dashi dan ita ƙawayenta sunce babu aihuwa a tsarin rayuwarsu , tsayawa cak Dikko yayi tare da daina ɓalle botiran rigarshi ya kalli Jiddah ta cikin madubi , data faɗamin zata zubar da cikinta dan ita zatayi gaba , shine na bata haƙuri tace bata yadda sai ta fitar ita ba zata zauna wani rainon ciki da "ya "ya ba taje ta tsufe ta lalata ƙuruciyarta , ni kuma sai nayi ma Aunty Rabiya waya a matsayinta na babba tazo tayi ma Caca magana dan karta zubar da cikin , shine tace ita ai bata so ka haihu dama shine fa tazo tayi mata allurar zubar da ciki....
Shiru Dikko yayi yana addu'a a zuciyarshi dan ya saita kanshi amma ya kasa sarrafawa , yayi ya riƙe yaƙi riƙuwa , a zuciye ya fita daga ɗakin zuciyarshi tana tafarfasa da wurin Momy zaije amma yana kawowa ƙofar ɗakin Sultana yaji baya iya wucewa , shiga yayi Nabeela tana ganinshi ta durƙushe irin gani na miƙo kaina , bai kalleta ba ya kalleni yace nidai ko An mata...... ? Dikko dai ko ? Ya tsareni da ido , kayi haƙuri , kamar jira yake inyi magana yace ke............. Saina kashe ki ya fara wani irin gurnani mai tada hankali , da gudu Nabeela ta fita tana neman ɗauki dan ita a tunaninta itace Dikko ya faɗa zai kashe , cikin sanyi nace ba komai kashe ni na faɗa hawaye na gangarowa daga cikin idona , dan bana iya tashi , nunani yayi cewa rufe min bakin munafuka jaka dake da bakisan inda duniya ta nufa ba na tsaneki....... Bana sanki haka kuma bana san ganin ki ya faɗa tare da kaimin wani irin halbi yana ci gaba da cewa ai baki burgeni ba da baki haɗa hada kanki kika mutu ba , bani kika cuta ba rayuwarki ce , zanje in dawo yau mai kwatarki a wurina sai Allah banza ƙazama.....
Fuuuu ya fita daga ɗakin , a palon ƙasa ya haɗu dasu Ashiru ko inda suke bai kalla ba ya wuce ya fita da sauri ji yayi G H tayi masa nisa wani irin ihu ya kurmama mai tsananin tada hankali ya durƙushe a wurin wai....... Wai , wai Allahna , wayyo , kai.........saina kashe kaina ya riƙe wuyanshi da ƙarfin bala'e , duk yadda akayi a ɓanɓare hannun Dikko daga wuyanshi yaƙi fita , kuma daga durƙushen an kasa kwantar dashi tashin hankalin ya girmi tunanin duk mai tunani , a ruɗe Nabeela ta fara kiran wayar Momy amma bata ɗauka ba , Yayarsu ta kira ta faɗa mata sannan ta turawa Dady text kuma har yanzu Dikko bai kwanta ba kuma bai cire hannunshi daga wuyashi ba har yaji ma kanshi ciwo jini yana fita daga wuyanshi.
A wannan halin Dady ya samu Dikko idan hankalinshi yayi dubu ya tashi , itama Yayarshi haka tazo ta sameshi duk wani mai san rayuwar Dikko haka suka zo suka sameshi har Momy kuma zuwa wannan lokacin ya daina lumfashi gaba É—ayanshi ya É—auke , Ashiru Dady ya kalla yace me yayi zafi haka ? Cike da damuwa Ashiru yace muna Abuja yacemin yaji gabanshi yana faÉ—uwa tabbas wani abu ya faru da Hajiya amarya shine yace in kirata dama sun kwana biyu basa waya ni bansan abinda ya haÉ—asu ba , Momy tace shegiya É—iyar matsiyata idan wani abu ya samu É—ana itama sai an ratayeta.
Hannu Dady ya É—aga mata ya dakatar da ita sannan yace ma Ashiru ina jin ka , sai na kirata bata É—auka ba , yace na kira Nabeela itama bata É—auka ba itama Hajiya Jiddah shine yace na kira Mardiyya bayan na kirata na tambayeta tana gida tace min Ey nace me ya faru a gidan ne ? Shine tacemin ita dai taji ana cewa an zubar da cikin Aunty amarya ne , bayan na gama wayar nace masa Mardiyya bata gida gudun karya shiga damuwa shine ya matsa muka taho katsina , ni daga haka bansan komai ba.
Dady yasa aka kira Mardiyya bayan tazo ya tambayeta abinda ya faru , tace Aunty Rabiya ce tazo tayi ma Aunty Amarya allurar zubar da ciki , Rabiya zatayi magana Dady yace ta rufe mishi baki , shiru tayi tana kallon Jiddah , Dady yasa aka ɗauki Dikko gaba ɗaya kowa da kowa aka nufi ɗakinshi dashi , a ƙasa Dady yasa aka kwantar dashi sannan ya umarci kowa ya fita har Momy , fita sukayi gaba ɗayansu , magani ya fiddo a cikin wata kwalba ya zuba mishi a kunne dan tun lokacin daya bi Dady ranar da gaya hotunan Sultana zata sha giya idan baku manta ba ai a ranar ya fara faɗa zai kashe kanshi , daga nan Dady yace zasuje saudiyya sai aje da Dikko wurin magani , salati yayi tare da buɗe idonshi , Dady yace Babana ka rufa man asiri ka barni na zauna lafiya.....
Kai......... Saina kashe Rabiya..... Riƙeshi Dady yayi idonshi ɗauke da hawaye yace yi haƙuri Babana , a , a , saina kasheta......... Kuma saina ɗaure mijinta daya barta take fita har tanayin iskanci a gidana birkicewa yayi daga hannun Dady yayo waje da gudu , Rabiya na ganinshi ta sauka ƙasa da sauri amma kafin ta ida gangarawa ya rigata sauka saboda shi ta sama ya sauko , yana ƙoƙarin riƙeta tace Jiddah ce...... Jiddah tana gani kowa yana rugawa amma sai ta tsaya , sokewa yayi saman guyawunshi zuwa ɗaya yayi mata ta faɗi ƙasa somammiya miƙewa yayi da gudu yabi Rabiya Dady yace ku riƙeshi mana , kai......... Karku taɓani idan kuka taɓani saina kashe kaina , daf da zata fita daga cikin palon yayi mata wani irin halbi ta fice somammiya , itama An mata saina kashe ta........... Dady yace wai bazaku kwantar dashi ba , wata irin zabura Dikko yayi bana kwanciya ya nufi hanyar ɗakin Sultana , da gudu su Ashiru suka bishi , kai...... Karku taɓani , wai har so nawa zan faɗa bana so ana riƙeni ne............. ? Ya juya tare da sauke ma Ashiru hannu a ciki ya koma baya ya faɗi ƙasa yana ihu , wurina ya nufo yana zabura cewa saina kashe ki......... Da sauri na jawo lokar bedsite na ɗauko abuna yana matsowa na feshe mishi fuska ya faɗo saman gado ruf da ciki saida ya kalleni sannan ya rufe idonshi a hankali ya tafi hutun taƙin lokaci , haka kawai zan zauna ne aljanu su lahanani ? Sun tsaya bayan fage suna ta iskanci an kasa maganinsu tou ni nice maganin su Allah dai ya bani lafiya.
Dady bai shigo É—akina ba Momy ce ta shigo saida ta zageni tas tace kuma Dikkon zai dawo daga duniyar suma zata faÉ—a masa nice na zubar da cikin zaici ubana kuma zai sakeni , a raina nace wane dare ne jemage bai gani ba ? Aini halin Dikko da duk haukarshi saidai in ba wani labari dan nayi imani nice mutum na farko dana fara ganowa shi mahaukaci ne ,
Dani da Rabiya da Jiddah aka tattara aka nufi asibiti damu umarnin Dady bayan an tafi dasu Sultana Dady yasa aka fiddo Dikko daga É—akin Sultana aka maidashi É—akinshi ,
Washe gari , duk wani taimako daya kamata anyi mana dukanmu nidai saida akayi min wankin ciki domin likita ya tabbatar da cikin ya lalace saboda allurar ta daɗe a jikina babu wani abu da zasu iyayi , Rabiya kuwa tunda ta dawo batayi ma kowa magana ba , Jiddah kuwa kuka take bata zama da Dikko saiya saketa tana ta ɓaɓɓarka zagi ita ba jaka bace ko a gidansu ba'a taɓa dukanta ba sai wani can ƙaton banza , gaba ɗayanmu dai sallamarmu akayi dukanmu kwananmu ɗaya a asibiti , Yayar Dikko mijinta ya ɗauketa Jiddah Al ' Ameen ni kuma Ashiru muka nufi gida , Jiddah kuma wurin Momy ta tafi sai an saketa.....
A ƙofar shiga ciki naci karo dashi , shi zai fita ni zan shiga ran nan nashi a haɗe yana waya ko inda nake bai kalla ba , gaishe shi nayi ƙaddarawa yayi baiji ba ya wuce , jiki a sanyaye na shiga ciki , Nabeela ta gyara ɗakin ta gogeshi ta sakar mishi ƙamshi mai daɗin shaƙa , sannu da jiki tayimin , kaɗan na ansa na wuce bedroom na kwanta.
Yana shiga mota kiran Yazeed ya shigo a wayarshi , kallo ɗaya yayi ma wayar ya ajiyeta a gefe yana ƙoƙarin tashin motar wani kiran ya sake shigowa , bai ɗauka ba ya fita daga gidan da tuƙin rashin sanin darajar rayuwarshi , ya kusa isa inda zaije text ya shigo , ɗauka yayi ya duba Yazeed ne mai turo saƙon , hannunshi ɗaya riƙe da sitiyari ɗayan riƙe da waya , dubawa yayi ,
_DK An mata ta fita hanyata , kaga dai har yanzu bata daina bibiyata ba sai bina takeyi ka duba a whatsapp na ajiye maka saƙo danni gaskiya bana san mayata...._
Da hannu ɗayan daya riƙe wayar ya tura masa.....
_Wace ce An mata kuma.....?_
_Matar ka.....!_
_Wace.....?_
_Sultana É—iyar É—an caca_
_Oh wai An matana......?_
_Eh_
_Me tayi maka ne ?_
_Tana biyoni duk inda naje..._
_Tou yi haƙuri ina driving , amma kana ina yanzu sai inzo in sameka muyi magana....._
Yazeed bai sake turo saƙo ba , ajiye wayar Dikko yayi yana cewa zakaci ubanka idan na riƙe ka , mtsww ko saƙon meye ya ajiye Koma dai miye saina gama zan duba , itama An mata saina sa ta rana kanta tunda bata da wayau bazan sake mata murmushi ba sai tayi nadamar sani na , banda Dady ya bashi haƙuri yace mishi babu mai laifin sai Rabiya tunda taje tayi abinda batayi shawara ba , dan yadda Mardiyya ta faɗa masa ya yadda da hakan shi yasa ya faɗawa Dikko aka ɗorawa Rabiya laifi gaba ɗaga banda haka da saiya tada Sultana aiki yadda ko bata tare dashi ta zama condem bata sake amfanin komai sakara ƙarar yarinya da ita.....
Bayan ya isa inda zaije yayi parking , bai fita a mota ba tunanin jiya ya farayi , duk abinda yayi ya dawo mishi a kanshi , Allah ka yayemin wahala , lallai An mata ni zata ma haka ko ? Wato ni zata feshe ma fuska ? Lallai yarinyar nan duk yadda akayi har yanzu tana da wani kuɗiri akaina , wata zuciyar tace ba haka bane ba , wani sashe na zuciyar shi yace kaima kawai ka yada ƙwallon mangwaro ka huta da ƙuda , murmushi yayi a bayyane yace An mata bata yaduwa kuma ita ba ƙwallon mangwaro bane ba idan na yadar da ita ina zataje ? Wane hali zata shiga ? Idan har na rabata dani banyi mata adalci ba gaskiya zama da ita dole saidai zan bata wahala a daren yau saina zane mata jikinta tasss , zan zauna lafiya na kwana biyu idan kuma zafin ya huce zan ƙara mata tunda ita ta zama doki sai an daketa zata tafi , bayan kwana biyu kuma zamu haɗu a saman bargo Allah ya baki lafiya jarumata.....
Fita yayi daga motar ya wuce ranshi a ɗan sauƙaƙen damuwa , kafin ya isa inda ya dosa su Ashiru har sun bayyana a wurin , a hankali mutane suka fara kawo hankalinsu wurin saboda zuwan su Ashiru , DK ya faɗa tare da riƙo hannun Dikko suka taɓa murmushi Dikko yayi kaɗan , abokin nashi ya cire hannunshi tare da nunawa da hannunshi ranka shi daɗe ya kake ya kyau ya zati ya ƙwarjini ya iko ? Murmushi Dikko ya sakeyi yace hali dai na nan Saminu me kazo yi nan ne.....? Ya tambaye shi yana wucewa abunshi ,
Bin bayan Dikko yayi yana cewa Allah ya kawoni kai ka fito ta can ni kuma na hudo ta nan kaga yauni lafiya lau kenan gani ga mai girma DK , Dikko bai sake magana ba ya wuce ciki saida ya gama dube²nshi yace da yaranshi dake binshi ku shiga ku dubomin shi , sun duba sosai basu ga Al ' Ameen ba , jinjina kanshi yayi yace ku wuce muje , yayi gaba suka rufa mishi baya , abokin nashi ne yace DK sallamarni mana nima in sheda , Dikko yace ni kuɗina basu zuwa wasan danbe , dan girman Allah ni yaushe rabona da danbe ai na bar ma su Yazeed , Dikko yace tunda aka fashe idon ka zakace ya faɗa yana dariya , nidai dan girman Allah DK bani , kai ba abinda zan baka , har wurin mota yabi Dikko yana haɗashi da Allah , Dikko kuwa mamakin yadda Saminu ya lalata ma kanshi rayuwa harya dawo ya fara maula abun bai mishi daɗi ba kuma baiso mishi haka ba , saida sukaje mota ya bashi kuɗin da babbban dumtsiya , cah.... Mutane suka rufo wurin suna maula.
Nidai Momy saiya sakeni , Momy tace ke sakarar banza karki kuskura Dikko ya sakeki ba dan ni na haifeshi ba Dikko miji ne ki riƙeshi wannan lalurar nashi zai zamar mishi tarihi Jiddah ki kwantar da hankalinki ki maido natsuwarki a jikin ki karki kuskura ki bari ya rubuta ko ya furta kalmar saki Dikko da kike ganinshi baida mutunci , haka kuma baida haƙuri kamar amai amma ida kikayi haƙuri komai zai zama dai² amma maganar saki ya fita harshenki ,
Nidai gaskiya bana sansa , cikin rarrashi Momy tace keda É—an uwanki idan baki so sa dan komai ba kiso sa dan zumunci mana haba Jiddah ina wayanki ina lissafinki ina tunaninki ? Karki ma kuskura kiyi wannan rashin wayan a gaban Dikko dan nayi imani da Allah ko da wasa kikayi masa maganar saki saiya sakeki duk kuwa yadda yake sanki ko zai mutu saiya rabu dake ,
Nifa gaskiya na gaji ko za'ayi tashin hankalin da ba'a ƙara maimaita kamarshi saiya sakeni , Momy tace ji Jiddah karki yi abinda zai baki damuwa daga baya fa , idan ya sakeni duk ranar dana zo nace kisa ya maidani ki tunomin wannan ranar , Momy tace ai bana fata ma yanzu tashi kije kiyi wanka kici abinci ki huta zuciyarki tayi sanyi , ni babu ranar da zuciyata zata huta sai ya sakeni , Momy tace yi haƙuri Jiddah idan kina gidan Dikko waye ya isa ya shiga ya katantane ? Bare idan "yan uwanshi sunje a watsar dasu a palo , idan kina gidan dake da duk wani ɗan dana haifa da "yan uwana gidan bazaku zama a raɓe ba , kuma idan ma dan wannan karuwar sakinta zaiyi kinga daga ke baza sake aure ba , nidai ko ya saketa bana zama , Jiddah kalmar saki ya fita daga bakinki bakisan hakin Dikko ba , tashi kije kiyi wanka kiyi bacci , tashi tayi tana ko za'ayi tashin hankali sai Dikko ya saketa.
Al ' Ameen dake rakuɓe yace Hajiya ki bari yayi mata ɗaya kila ta huce , Momy tace da Allah rufemin baki ɗan iska fita ka bani wuri , Allah ya taimakeki ya faɗa tare da fita , cikin farin ciki yace a gaban mai gida zata faɗa na gama da wannan wasan sauran Sultana..... Lokacin mu ya kusa farawa !
Suwaiba kalleni , Dikko ne zaune saman kujera ya kashe zamanshi da ƙafa ɗaya saman ɗaya , duƙar da kanta ƙasa tayi tana kuka , tunda nake faɗin kisa ban taɓa kashe wa ba amma zanyi rantsuwa kuma kinsan halina na faɗa ma na cika bare kuma na rantse idan har kika kuskura nayi rantsuwa zan kashe ki saina kashe ki , in kashe ki kuma na kashe banza dake da ɓeran gidana babu banbanci yadda zan kashe shi ba'a tuhumata abinda yasa na kashe shi haka zan ɓatar dake cikin mintuna biyar zan shafe labarinki a garin katsina ,
Waye....... ? Na rantse girman Allah ga sunanshi a zuciyata amma bana iya faɗa , Dikko yace duk halakacin da nayi miki dake za'a haɗa hannu na zama lusarin namiji ? Me nayi miki haka don Allah..... ? Ki faɗamin shi kawai sai insa a maida ke gidanki cikin mutunci da mutuntawa , wallahi ranka ya daɗe ga sunan shi a zuciyata amma bana iya faɗa , cikin ɓacin rai Dikko yace ku fiddomin zuciyar ta , ta ni idan na duba zan gane ko waye......
25/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA....* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 82
Suwaiba najin haka ta saki wani irin fitsari tare da jan jiki ta matsa kusa da Dikko tana ƙoƙarin riƙe ƙafarshi ya kai mata wani irin halbi saida ta koma baya suuuuuu , ke ni ba'a taɓani duk duniya abinda na tsana kenan wani ya riƙemin jiki shi yasa ko ina cikin yanayin fushi aka taɓani nake ƙara firgicewa , ku fiddomin zuciyarta nace................... !
Cikin kuka tace dan darajar Annabin rahma S. A. W kayi haƙuri ka ƙaramin zuwa gobe dan soyayyar da kake ma fiyayyen halitta idan har ban faɗa ba kayi min duk abinda kaga dama , sannan kuma ka tattaromin kaf yaranka duk wanda kasan ya taɓa zama ƙasanka lokacin da kayi rashin lafiya ko baya tare dakai to a nemoshi a taho dashi tunda na kasa faɗar sunansa idan naga fuska zan gane....
Miƙewa Dikko yayi baiyi magana ba ya fice daga wurin , Ashiru ya kalleta yace an daiji ɓitir shegiya munafuka Allah ya ƙara tona muku asiri gobe iwar haka lahira most go dan mai gida zai kashe ki....... Ya nuna yadda Dikko yake faɗa cewa zan kashe ki........
Sai bayan la'asar Dikko ya dawo , gidan yau shiru ba Jiddah ba Mardiyya Nabeela ma bata nan tunda ta fita bayan na dawo daga asibiti har yanzu bata dawo ba , da sallama ya shigo É—akina ko inda yake ban kalla ba na ansa naci gaba da kallon wayata da nake ta kiran layin Inna.
Kusa dani ya zauna ya riƙoni jikinshi yana wannan numfashin nashi mai tayar da hankali , kyarma jikina ya farayi nace sakeni , anƙi a sakekinki , cikin hayani nace da Allah ka ƙyaleni ke muguwa daɗi kikeji na taɓaki ga jikinki nan ya nuna , da hayani na ce sakar.... Mmmmmm na ƙarasa saboda haɗuwar bakunanmu wuri ɗaya.
Shiru nayi tare da ƙara riƙeshi , girgiza kaina yayi da yanayin na kalleshi , jiki a mace na saka idona a nashi naci gaba da ansar saƙonshi , saida ya gama luguiguita ni ya cire bakinshi yana cewa me ya haɗaki da ƙawayen Jiddah ? An mata bakijin magana dai ko ? Kwanciya nayi a jikinshi da yanayin kasala nace Ey banajin maganar , ke yarinya zaneki zanyi ki gama ƙaryar rashin kunyar ina dawowa anjima ya ƙarasa maganar yana tashi bayan ya saukeni daga jikinshi , nima sauka nayi daga gadon nabi bayanshi har ɗakinshi.
Juyowa yayi ya kalleni tare da cewa zaki rufe ƙofa ne ? Girgiza kai nayi alamar a, a , tou me ne ne ? Ba komai na faɗa ina ƙoƙarin zama gefen gado , ke ׳ karki zauna koma can ya nunamin gefen madubi , babu wani damuwa na koma na zauna , kayanshi ya fara cirewa yana bani labari wai Suwaiba idan ta bari ya fara ranfa da ita saiya ɓoye halittar ta , wallahi An mata da tausayin matar nan nake amma yanzu na tsaneta ko ganin ta bana san yi shegiya ƙazama...
Zama yayi saman bedsite wai inzo in cire masa takalminshi in samu lada , kallonshi nayi ban tashi ba , taso mana shi yasa matan yare suka more ma matar malam bahaushe da ni mijin bayaraba ne ba'a bari na in cire riga dakai na , za'a ciremin da soyayya ana faɗamin kalamai masu daɗi ana kulawa dani harsai naji kaina ya min girma , ya ƙarasa maganar yana zame takalmin shi ya cire safarshi miƙewa nayi ganin yana kwance belt a tsorace , a , a koma ki zauna ai ba yanzu zan dakeki ba sai anjima , yi zamanki ni wanka zanyi.
Cikin kuka nace kayi haƙuri dan Allah , saida yazo kusa dani ya sumbaci gefen fuskata ya latsa cikina saida na zabura da irin maganata yace aradu bazan haƙura ba me kuka ci ne ? Ya ƙarasa maganar yana tambayata , ni abinci naci , ai nasan abinci kika ci idan akwai saura kawomin yunwa nakeji ,
Miƙewa nayi na fita , bayan Sultana Dikko yabi da kallo a ranshi yace Allah yasa "ya "yana suyi kama da An mata , amma kar suyi rashin jinta , ubangiji ka sake azurtamu da wani rabon mai albarka ka bawa An mata lafiya ni kuma ka bani haƙuri da dangana , ina can ina yawo ni banga irin abin nan da masu ciki keyi ba , ko me tayi ta kwaɗayi data samu cikin Oho , tou amma me yasa Jiddah tace wai An mata tace baza ta aihu dani ba ? Ya taɓa saitin zuciyarshi , murmushi yayi tare da faɗa a bayyane yace ƙarya ne "Yar mata tana san Dikko kuma dole zata so ta haihu dani kodan soyayyar da muke ma junanmu , rigima kenan naga Sultana da baby da farin ciki ya shiga toilet danyin wanka.
Ɗakinshi na dawo da abincin kuma har yanzu bai fito ba , ajiyewa nayi na fice a ɗakin , gaf zan shiga ɗakina ƙanwarshi mai bi mishi ta tareni tayo zugar ƙawayenta saida kowa ya zageni fes a cikinsu sannan ƙanwar tashi ta ansa tare da fara sokamin zagi waini har na isa saboda ni ɗin banza Yaya DK ya daki Aunty Rabiya waye ni bare ubana ɗan caca karuwa da aka saka a wasan caca su waye familynki ? Karuwan banza gaba ɗaya wace ce ke bare kuma ubanki duk cikar faɗin birnin katsina ? Waye ya tsaya miki ya ɗauremiki ƙugu kike iskanci , Dikko dake fitowa yace ni nine na tsaya mata dan hayaniyar su ta fiddoshi daga ɗakinshi jallabiya ce a jikinshi har yanzu jikinshi da sauran lema kuma itama kanta batayi tunanin zata sameshi gida ba , kuma Ashiru yaa fita da motarshi shi yasa ta ɗauka baya nan yaci gaba da cewa kuma itace tasa na daketa kuma kema saina baki kashin bala'e zaki fita gidan nan , ke har kin isa kizo har gidana kiyi ma matata takakkiya ? Kin taɓa ganinta taje cikinku ne ? Matata zaki zaga....... Dan baki da kunya ? Ashe nima zaki iya zagina idan kika samu dama ko ? Ya fara fita yanayinshi yana An mata zaki ga wanda ya tsaya mata ? Tou ni nine na tsaya mata ya nuna kanshi cewa to gani kin ganni ya akayi ne..... ?
Kyarma jikinta ya farayi tace Yaya ..... Daka mata tsawa yayi kafin ta faɗi maganarta yace zanci ubanki kika sake kiran suna na , kayi haƙuri , tou daga yau naji labari ko na sake ganinki gidana saina zaneki bata haƙuri , kallona tayi tare da cewa yi haƙuri cikin ladabi , kallon Dikko nayi ya ɗagamin gira , ba komai na bata ansa , hanya ya nuna musu tare da cewa kuje , da sauri suka gangare babu wanda ya sake magana ko waiwayenmu har suka fita , zo muje ya faɗa tare da wucewa gaba nabi bayanshi.
Har ya gama cin abincin baiyi magana ba bayan ya gama ya ɗauki wayarshi ya fara dube² tare da ɓalle botir in gaban rigarshi ya shafa kanshi da yanayin damuwa kallona yayi sannan ya sake kallon wayar yace da ina da ina kikaje da bana nan ? Dam׳ naji gabana ya faɗi kafin inyi magana harya ƙufule yace bakiji ina miki magana , daburcewa nayi nace naje goruba , daga nan sai ina ya faɗa yana tsareni da ido , ƙyarma muryata ta farayi nace sai ina naje tou ? Ina tambayarki kina tambayata ? Kayi haƙuri , miƙewa yayi yace inyi haƙuri.....? Tou kinma san abinda kika yi kike cewa inyi haƙuri kenan ? Nima miƙewa nayi na fara kuka , koma ki zauna idan kika fita ɗakin nan saina kasheki............
Karka kasheni Dikko , ke......... Rufemin baki wato saboda kin ɗaukeni mahaukaci shi yasa kikaje wurin Yazeed kai............ Saina kashe ki........... Da gudu na fita ya biyoni yana ihu ni zaki tona ma asiri saina kashe ki........ Na kusa shiga ɗakina naga kafin in shiga in rufe ya riƙeni da gudu na hau ƙarfen bene na sulala ƙasa suuuuuu kai............... Saina kashe ki......... Maimakon ta fita waje a taimaketa sai tayi tunanin a dole nan ciki zata sama ma kanta mafaka wata irin kururuwa yakeyi mai tada hankali yana maimaita saina kasheki.............. Yana wata irin zabura , da gudu ta sake komawa sama ya sake binta har yanzu bai kamata ba saina kashe ki........ Kawai yake faɗa , irin na ɗazu ta sakeyi amma sai sautsayi ya gitta......
Wani irin ihu Dikko yayi ke....... Karfa ki faɗa ki mutu , na fasa bazan kashe ki ba , An mata ya nufi inda take tafiya zuwa ƙasa dan riƙeta amma kafin ya riƙota takai ƙasa.......... Kai............... Saina kashe kaina zai faɗa ƙasa aka riƙeshi , riƙe kanshi yayi da duka hannayenshi biyu yace kai......... Wai , wai , wai Allahna wayyo................... Saina kashe kaina.......... Wasu suka riƙe Dikko dake wani irin ihu wasu suka tafi wurin Sultana da ko motsi batayi , An mata........................ Ya faɗa tare da faɗuwa ƙasa somamme.
Nabeela Mardiyya da Jiddah da suka shigo yanzu gaba ɗayansu wurin Dikko suka nufa suna kuka , ita kuma Sultana masu aiki mata ne akanta maza na tsaye kowa yana tunanin abinda yayi zafi har Dikko ya jefota daga saman bene ya kasheta , cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya cika da "yan uwansu Dikko wannan karon har wanda suke Baba ɗaya ba'a bari ba kowa yazo tunda sharri ne ya samu dan duk wanda aka faɗa mishi cewa akeyi Dikko ya jefo matarshi daga saman bene ta mutu , abiyar zaman Momy kuwa cewa takeyi tunda ya kashe shima sai an kashe shi hukuncin wanda ya kashe shima kisa ne , yaro ne yana iskanci ba'a iya hanashi ya zama ɗan ido kar akayi masa magana ya ragu , tou wallahi yadda ya kashe ɗiyar mutane shima sai an kashe shi Allah yasa mun gani da idonmu kuma saina tsaya ma iyayen yarinyar nan shari'a daga nan har a tashi duniya sai na tsaya akan kafafuwana an kashe Dikko tunda ɗa baifi ɗa ba.
"Ya " Yanta mata tace su É—auko Sultana , Momy ta kalli Rabiya tace karku bari ta fita da yarinyar can tunda babu wanda yake da tabbacin mutuwarta dan ko bata mutu ba zata iya kashe ta yadda ta shirya lafiyayen sharrinta , gaba É—aya wurin ya gauraye da hayani har bakajin maganar wani yayin da matar Dady ke cewa sai an tafi da Sultana , Rabiya tace ita a suwa ? Dan taga Dikko yana sume har ta samu bakin magana ai zai dawo , jin zance Rabiya yasa ta kira Dady ta faÉ—a masa Dikko ya jefo matarshi daga sama ta mutu ,
Salati Dady yayi cikin tashin hankali , babu daɗewa shima ya bayyana a gidan , ga Dikko kwance a dai² inda yaso ya riƙo Sultana aka riƙeshi ya suma , ga Sultana a ƙasa kwance kuma har yanzu ba'a taɓata ba daga yadda ta faɗa haka aka barta , Dady bai fara zuwa wurin Dikko ba wurin Sultana ya tsaya ya kalleta cikin tausayi sannan ya kalli "yan ɗayan ɗakin yace su ɗaukota su Ashiru kuma suka ɗauko Dikko suka fita daga palon aka bar Momy da " ya "yanta mata "yan rashin kunya masu irin baƙin haƙin halinta......
Fita Momy tayi tana cewa ina za'aje mata da ɗa ? Cikin ɓacin rai Dady yace ashe kina sansa ? Tio Babana ba ɗanki bane ba nawa ne , ga "ya "yanki nan na ɗauki nawa na bar miki naki wa'anda kike so ni ina sansa kuma bana san abinda zai sameshi insha Allah bazai mutu ya barni ba saina mutu na barshi duniya daga haka bai sake magana ba aka sakasu a mota suka fice daga gidan.....
Wannan ranar ta tuno ma Momy da zuwan Suwaiba gidansu , Dikko yana da rigima haka kawai yaje ya ɗauko musu wannan "yar iskar ya tausaya mata amma ita ta saka masa da sakayya mafi muni a rayuwa ta gudu ta barshi da masifa dake neman kaishi ƙiyama babu gaira babu dalili , ya taimaketa amma ta zama silar warwarewar rayuwashi gaba ɗaya kuma ta gudu ta barshi da hauka shi ba mahaukaci ba , jiki a sanyaye ta dawo palo wuri ta samu ta zauna ta zabgaga uban tagumi tana matse hawaye.
Suwaiba kuwa bayan tafiyar Dikko kuka tasha harta gode Allah , bakin gaskiyarta ta kasa faɗin sunan wanda Dikko yake so ta faɗa masa to ya akayi ta kasa faɗa shine tambayar da take ma kanta bayan a zuciyarta tasan sunan , tana wannan tunanin ne Al ' Ameen ya bayyana , tana ganinshi ta fara kaine kuma saina faɗa masa , dariya Al ' Ameen yayi tare da cewa haba "yar gurgus na kulle zuciyarki bakinki baya iya faɗar Al ' Ameen , kuma idan baki sani ba nine na harbeki kika zama gurguwa , abinda ya kawoni wurinki shine fatan sauka lafiya ayi rayuwar lahira lafiya ina nan saina ga bayan mai gida saina kashe shi na kwashe kaf dukiyarshi sai nayi rayuwar duniya mai daɗi nahau manyan motoci in ƙaro mata 3 masu zafi naje duk sauran ƙasashen da bai kaini ba ,
Waye yace maka ina nan ne ? Ni na sani da kaina dan nasan dama bazaki wuce nan ba , ya baki daga nan zuwa gobe mahaukacin banza yana can yana nema na a gari kamar wani lusari baisan ina tare dashi ba , daga wurin mahaifiyarshi nake na sauke zango na a wurinki , naira miliyan biyu aka bani naje na haɗo sammu nine na bashi a banci kuma a lokacin ni ɗaya nake tare dashi a ƙasar London , kuma nine na kashe matarshi har lahira , ni nayi komai kuma nine zan kulle bakin furta zan kashe ki................... Zan kashe ka.................. Saina kashe ku............... Saina kashe kaina............ Haba mai gida kayi haƙuri zaka mutu saurin me kake ? Mutuwar fa yana gaf da kai da zaran na haɗa auren nan aka samu haihuwa sai mu kashe ka kaga mun hutar da kai faɗar zaka kashe kanka Al ' Ameen zai aika ka zuwa duniyar mutuwa , Hajiya Suwaiba na wuce sauka lafiya zuwa lahira , murmushi yayi tare da ci gaba da cewa zai dawo yana zuwa zaice saina kashe ki.......... Haka zai faɗa Al ' Ameen baya faɗuwa dan haka sai ya kashe ki kinga na ture wata matsalar aiki ya ragemin yana faɗin haka yayi tafiyarshi yana dariya.
Fashewa da kuka ta Æ™arayi cewa Allah zai tona maka asiri babu daÉ—ewa azzalimi maci amana , murmushi Al ' Ameen yayi bai juyo ba ya É—aga kafaÉ—unshi 🤷ðŸ»â€â™‚ ya fice da sauri , kifewa Suwaiba tayi a wurin kuma sunan Al ' Ameen yaÆ™i zuwa a bakinta ,
Tunanin irin halackin da Dikko yayi mata ya dawo kanta , wurin da take taji yana juyawa yayin da zuciyarta tace ta yanka kanta ta rubuta *AL ' AMEEN* a jikin bango idan Dikko yazo zai gani , wayyo Allahna , ta goge hawaye tare da komawa ta kwanta a wahalce ta fara tunanin rayuwar baya................ !!!
Kuyi haƙuri da wannan don Allah , na farko dai banda caji , na biyunsu kuma ina da hidima wanda ba lallai ne gobe zuwa jibi kuji ni ba , amma idan na samu yadda nake so zanyi ko kaɗanne fatan zaku gafarceni.......
27/11/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 83
Da farko dai Dikko mutumin kirki ne a wurinta , nagartaccen namiji mai zama , tsayayyen namiji mai lafiya da cikar zati da kwarjini , jarumin namiji ba lusari ba , idan akace mutum bashi da mutunci ko rashin ragowa idan dai baiyi maka ba tou kai mutumin kirki ne a wurinka , duk halin mutum na kirki dana banza idan dai bai nuna a kanka ba tou bazaka sheda mugayen halayenshi ba , Dikko yana da mutunci amma shi baya shiga sabgar kowa , ko a baya data sanshi da lafiyarshi tasan baida haƙuri haka kuma bai ɗaukar sakarci da shirme , kayi ta magana yana jinka saidai yayi kunnen uwar shegu dakai , yana da tausayi sosai amma yafi tausayin mata a rayuwarshi.
Baya dariya baya murmushi idan kuma ka cika shi da surutu zai tsare ka da dara²n idanuwanshi har sai kaji tsoro kai da kanka zaka lallaɓa ka tashi ka kama gabanka , baya sabgar mata baida budurwa ko ɗaya amma yana da dawakai masu lafiya da ƙoshi , babu hoton mace a wayarshi amma zaka iya samun hoton doki babu adaɗi a wayarshi , ya yadda da doki sosai kuma bayajin wahalar sayenshi baida magana sai ta doki dan ko yana zaune da abokanshi idan suna fira masu zancen "yan mata sukeyi , masu mata suka labarta nasu shi zaice dokinshi kaza² , sai zancen kayan doki maganar polo kalamanshi dai suna tsayawa akan doki ne kawai da abinda ya shafi dokin , idan ance masa shi baya budurwa zaice shi baya san raini dan yaji yadda su kansu suke magana akan matan , kuma yana ganin yadda matan gidansu ke ranfa da maza , gashi kuma suna faɗar irin halayen da matan ke musu , kanaji da girmanka da shekarunka ƙaramar yarinyar daka haifa tayi maka rashin kunya shi duk sabgar da zata zo da raini ko rashin kunya baya ciki shi yasa bai shiga sabgar kowa saita doki , dan doki idan ya sanka kaine kake cidashi kake shadashi akwai ragowa tsakaninka dashi amma idan ya tashi aure zai auri cikakkiyar mace data san kanta mai shekaru da yawa shi gaskiya bazai auri "yar ƙaramar yarinya ba dan idan ya auri yarinya shi kanshi saiya raina kanshi ƙaramar yarinya mai ƙananan shekaru bata dace da rayuwarshi ba...
Murmushin ƙarfin hali Suwaiba tayi tare da goge hawayen dake kwance a saman fuskarta , a bayyane tace ashe dai da rabon sai ka auri ƙaramar yarinya , yarinyar ma ta ƙasan² shekaru , yaushe kuka haɗu kukayi soyayya har aka kai matakin aure .....? Hmmm koma dai miye Suwaiba ba damuwarta bane ba ,
Marin birich a jahar Lagos , madakata ce ta mutanen da basajin magana ko kuma nace wanda suka gagara , madakata ce ta mutanen da suka fi ƙarfin gida ko suka aikata ɓarna saisu gudu daga jahohinsu sai suyi ma kansu masauki a wurin domin tsira da rayuwarsu , mazauna wurin gafurtacci ne kuma gagararri wanda suka ansa sunansu wurin rashin jin magana ko iskanci.
Duk irin matsalar da kaje da ita a wurin sai kaga wanda ya shafe taka ya burjeta murus , idan kuma zancen iskanci ne da duk wata ƙaramar rashin kunyarka tou fa daga wurin dai an rufe littafi , idan ko ke karuwa ce a iskanci har kika je Lagos kikayi rayuwa a ƙarƙashin gada tou lallai iskanci daga kanki an kashe boss , duk namijin da yaje wurin shima dai abin kwatance ne tou ina ga mace kuma....?
Matsalar iyaye itace ta kaini garin Lagos kuma nayi rayuwa a wurin dana faɗi sunanshi daga sama , auren soyayya nayi dani da mijina wanda ni dai Allah ya sani dama bawai wani cancan nake jinshi a raina ba , na aureshi ne saboda girman dukiyarshi wanda mu a zuri'armu attajiri ne sosai dan talaucin mu , ni bana sansa kwata² amma ina nuna masa soyayya saboda kuɗinshi shi yasa yayi tunanin ina sansa har a zuciyata ,
Tou mundaiyi auren na soyayya kamar yadda mutane suke kallo a zahirance amma a baɗinance ni a wurina kuɗinsa na aura , tunda aka ɗauramin aure dashi iyayena sukayi min huɗuba cewa nadai gansu a gidan haye suke zama tou inyi ƙoƙari na ƙulla musu mazauni kafin mijina ya sakeni dan masu kuɗi basu cika zama da aure ba nayi ƙoƙari na gina kaina kafin yayi min wurgin kashi a shara , a nawa ganin nidai ina kallon anyi ma masu kuɗi fahimta ce mara kyau domin auri saki hali ne , kamar jini haka yake gudana a cikin zuciyar mai irin ɗabi'ar danshi auri saki babu ruwanshi da mai kuɗi babu ruwanshi da matalauci haline ne kuma yana ƙarkashin zuciyar maishi.
Tunda aka kaini gidan mijina duk ƙarshen sati sai an aiko ƙanina daga gidanmu wai in bada kuɗin zubin adashe , akan me zance babu ? Dan ko shi ƙanin nawa idan yazo sai ankai ruwa rana nake haɗa masa kuɗin motar komawa dan mijin dana aura mannanu ne bashi da alkairi ko kaɗan dan ko kuɗin cefane ya bada idan ya dawo sai anyi lissafi saiya ƙwaƙwale canjin shi tass ya barni zero ɗina.
Mahaifiyata data ga kullum ƙanina yana zuwa yana dawowa babu kuɗi satin gaba yana zuwa ta tattaro ta taho da kanta , nasha zagi sosai tace ina nan na shige cikin a c na manta da ita , ina nan kullum sai naci nama nasha ruwan lemu , da safe naci shayi da burodi na barta a daura tana can kullum safiya tana karo da zazafen tuwo , taɓarya zata kasheta saboda daka da wahalar rayuwa , ina shafa ruwan sabulu mai ƙamshi idan zanyi wanka tanayin wanka da garin omo sai Allah ya tsenemin tunda na barta take shan wahalar rayuwar.
Na nuna mata cewa kuɗin bafa a hannuna yake ba nima a ƙarƙashin wani nake sai abinda aka bani , kuma bani nake da alhakin kula da ita ba taje tayi haƙuri taci abinda Allah ya hore mata tace bata yadda ba dole irin abinda naci irinshi zata ci , kuma saina shiga adashen nan duk abokan aure na babu wacce bata mallaki ƙaddarar dabbobi ba dan haka nayi ƙoƙari na samu.
Duk yadda naso na nusar da ita ƙin yadda tayi wai a dole saina samo idan ya shiga wanka in riƙa lalube masa aljihunsa dan wallahi ta aiko satin gaba bata samu kuɗin nan ba kashe wannan auren zatayi dan bata ga amfanin aure babu ci gaba ba , nace tou , data tashi tafiya saida ta tunbiji kayan abinci shinkafa taliya makaroni kuskus ta ɗauke sauran madararmu duk abinda ta gani gidan saida tayi gaba dashi buhu guda ta cika na shinkafa da abinda ta tattara daga gidana.
Bayan mijina ya dawo ya shiga store ya fara dube² dama wannan shine al'adarshi duk daren duniya idan ya dawo saiya duba kayan abinci , idan kuɗi ya bani saiya anshi canji , idan naman abinci ya kawo saiya irgashi , tun daga store ya fara faɗa wai yau yaga abinci yayi ƙasa bayan yabarshi da yawa kafin ya fita , ina na kai mishi abinci ? Nace ina kuwa za'a kai abinci inda ya wuce cikin ciki........?
Karfa na raina masa hankali haka yai ta zazzaga ruwan wulaƙanci karshen film in dai yace min dangi ɓarayi sata kamar ɓere zai maida abincin ɗakinshi duk safiya zai auno min gwangwani ɗaya tunda na zama ɓarauniya ba ruwanshi da baƙo kuma idan taliya ya bani ita zanci daga rana har dare , in shinkafa ne itama haka , ya kwasa rashin mutuncin shi daga baya ya kwashe komai zuwa ɗakinshi , binshi nayi ina bashi haƙuri ya basar ya shige toilet , yana shiga naci gaba da bashi haƙuri ina ɗaga kayan daya cire , kayi haƙuri don Allah , a dai² lokacin dana ƙwale² aljihunshi tas , bazan ƙara ba , a dai² lokacin dana ajiye wando na ɗauki rigarshi , na bari don Allah na kwashe kaf kuɗin masu yawan gaske na fita daga ɗakin , ban nufi ɗakina ba na nufi bayan gidan na tona rami na rufe su na maida busashshiyar ƙasa na rufe nayi ma wurin alama da tsinken tsintsiyar kwakwa.....
Ɗakina na koma naci gaba da kuka ban ƙarawa , a haka ya sameni yana ina kuma kika kaimin kuɗin na , rigima ya kaure tsakaninmu tashin hankali na kada Allah maimaita mana anyi shi , kuma tun daga wannan ranar ban ragawa aljihun mijina ba , ba aljihu kaɗai ba ko wanka ya shiga haka zan bincike kaf ma'adanar kuɗinshi , kafin wani lokaci na ƙware da wurin iya sata , kuɗi kuwa duk satin duniya sai anzo an ansa a gidanmu.
Mijina kuwa sai ya daina shigowa da kuɗi gida ya riƙa barinsu a mota , dana duba naga babu komin dare saina lallaɓa na cire makullin naje na buɗe na kwashe kaf kuɗinshi , koda ya kai ƙarata gidanmu iyayena cewa suke aljannu ne dansu "yar su ba ɓarasuwa suka haifa ba , suka ɗauremin ƙugu naci gaba da tsula tsiyata....
Daga dai ƙarshe mijina ya samu kwanciyar arziƙi dan haka mahaifiyata ta murje idonta tas ta kashe auren nan mijina yayi kuka ya shiga tashin hankalin rabuwa dani ni dama can bana wani sansa , bayan mutuwar aure na gama iddah na sake auren wani amma baikai mijin dana baro rufin asiri ba , shima haka na taso tattalin arziƙinshi saidai na ƙareshi kaf nayi gaba abuna , kuma har zuwa wannan lokaci iyayena basu sayi gida ba , aure na gaba mijin wayayye ne domin shi a banki yake ajiye kuɗinshi ban wani daɗe ba na kashe auren dan zuwa wannan lokacin nima na goge da idan babu malasa gaba nakeyi abuna , bayan wani lokaci na sake aure na auri wani manomi bagidaje ne dan haka shi amfanin gonar na riƙa siyarwa , shima ya gaji ya sakeni daga haka ban sake aure ba dan duk wanda yazo ce masa akeyi ni ɓarauniya ce , wannan dalili yasa ban sake auruwa ba ,
A gida zaman dai babu daɗi dan banda aure kuma banda inda zan samo kuɗi aka fara hantara ta a gidanmu , dan haka na fara sata da maƙota cikin ƙanƙanin lokaci na zama mashahuriyar ɓarauniya a cikin anguwarmu , ko shaguna naje sayayya danaga ba'a kallona sai inyi sata in gudu....
Duk wannan ƙoƙarin da nakeyi a haka banyi ma iyayena ba dan haka na haɗa dai da "yar bariki ta , ina karuwanci ina sata kuma har yanzu basu sayi gidan zama ba , ganin haka yasa idan na sato na daina basu naci gaba da sata ina ɓoye abuna , wulaƙanci a gidanmu kuwa na dare daban na safe daban , a wurin iskancina na haɗu da wani babban attajiri shine ya ɗauki hayata ya tafi dani Lagos , a ranar daya kwana dani a ranar na ɗauke jakar kuɗinshi na gudu ,
Ban bar Lagos ba na nemi matattarar "yan iska wanda suka gagara shine aka bani tayin marin birich ranar da naje da ƙarfin bala'e aka ƙwace kuɗina , naga iskanci da ƙaryar rashin kunya , naga dabar data girmi irin wacce nake gani a garin Daura , naga karuwancin daya girmi nawa naga salon sata wanda ya girmi tawa , wurin yamin nayi zamana da safe zan fita cikin gari nayo iskanci na dawo , wata na biyar a wurin mai hali baya barin halinshi nayi sata naci bugun rabani da yaro kuma sunce sai sun kasheni haka suka ɗaureni a jikin ƙarfe suka watsamin fetir suka cinnamin ashana dan sunfi ƙarfina ina ji ina gani zan mutu kuma gani ɗaure , a dai² wannan lokacin ne Allah ya kawo Dikko , dashi da abokinshi shima kuma kanshi baisan haka wurin yake ba yayi rakiye kawai ni bansan abinda yakai su shi abokin nashi ba.
Dikko yasha dariya sosai sannan ya ɗauki ruwan wani gahurtaccen ɗan daba daya zuba a bokiti zaiyi amfani ya sheƙamin a jiki wutar ta mutu , tun bai gama zuba ruwan ba ɗan daban yasa yaranshi suyi ma Dikko gunduwa² wanda ya kunna min wuta kuma yasa yaranshi su sake tashin wata wutar amma akan Dikko , saboda wurin gungu² ne na sansasanin "yan iska , kowa da zugarshi kuma kowa yana da yaranshi mutanen dai sun kasu kashi daban².
Wanda Dikko ya rako ya ruga da gudu ya duƙa gabansu yace su rufa mishi asiri Babanshi yake neman gwamna karsu kashe shi , ashe ma basu zama gwamnan ba ? To ko ɗan shugaban ƙasa ne sai sun kunna mishi wuta , su kuma dabar wanda aka ɗaukar ma ruwa suka ce ko gwamnan ne sai sun fyeɗeshi harya isa ya shigo da'irarsu ya haresu ? Shi kuma Dikko yana kwunce Suwaiba daga ɗaurin da akayi mata kuma har yanzu bai daina dariya ba.....
Kawai dai anyi tashin hankali mara kyau dakel aka samu aka fitar da Dikko daga wurin da taimakon wanda abokin Dikko yazo wurinshi , kuma duk tashin hankalin nan da Suwaiba ya tafi , tun a mota Dikko ke kuka wai yanajin tausayin sauran matan da aka baro shi wannan wane irin rayuwa ne ? Me yasa mata zasuyi iskanci wai.......? Ya bani shidai baya so yaga mace tanayin abu da bai kamata ba shi dai zai koma ko zai mutu saiya fitar da duk wata mace a wurin , abokinshi yace tou ka rufawa kanka asiri dan ka sake ka koma wurin nan saidai wani ba kai ba , Dikko da kafiya cewa yayi saiya koma su kashe shi , duk haƙurin da aka ba Dikko ya kafe kai cewa saiya koma a kashe shi.....
Nice na bashi haƙuri nace kar ya koma dan na fahimci shi ma'abocin tausayin mata ne amma yana da kafiya idan ya duƙe akan abu sai yayi , nace kayi ka haƙuri ka ƙyalesu duk wacce ka gani itace taje da kanta take zama , kuma idan ka koma zasu nemeni su kasheni , daga haka yayi shiru dai bai sake magana ba , ni bansan abinda abokinshi yaje yi ba , kuma bansan dalilin da yasa shi Dikko yayi rakiya ba , dalilina na bashi haƙuri nasan idan har tsautsayi ya maidashi sai sun kashe shi har lahira....
A cikin jirgi muka zo kano daga Lagos jikina yana ta raɗaɗin wutar data ci jikina sama² , a kano aka ɗaukemu a cikin wasu irin zafafan motoci har katsina , saida ya kaini asibiti aka dubani.
A gidansu Dikko kuwa mahaifiyarshi tayi tashin hankali akan bazan zauna ba , ta zage shi so babu adadi tunda yace kiyi haƙuri Momy zata zauna bai sake magana ba yaci gaba da sabgar gabanshi , ita irin mutanen nan ne masu ƙyanƙyamin mutane , ankai ruwa rana Dady yace tunda Babanshi yace saina zauna babu wanda ya isa ya hanani zama.
Tunda nake zaune a gidan banda wata damuwa domin Dikko yace duk abinda nake so na faɗa masa , shike ɗauke da duk wata ragama tawa duk abinda nake so zan rubuta a rubuce na bada akai mishi , baida hankali wurin kyautar kuɗi hannunsa a sake yake yana da alkairi sosai amma bashshi da mutunci idan aka taɓoshi duk gidan sai kowa yaji masifarshi yana iya sati yana masifa akan abu ɗaya bai gaji ba dan bai gajiya da fitina gashi da kafiyar bala'e idan ya duƙe kai akan abu babu gudu ba ja da baya....
Tabbas Dikko yamin gata yamin halakci fiye da tunanin yadda mai tunani zaiyi zato , ko tafiya yayi ya dawo haka zai jibgomin tsaraba ta sutura saboda duk yadda zan faɗi gayun shi bama zan iya musultawa ba , yanda yake ɗan gaye saida ya tabbatar ya maidani "yar gayu ta gaban jarida , kuma nayi masa koken rashin mazaunin iyayena shi ya tsayar dani akan ƙafafuwana lokaci guda nasha gaban duk wani mai tayarmin da ƙura ya kulleni da motar hawa ta abun kwatance a idon duniya.....
Amma sai na ƙulla aminci da abiyar zaman mahaifiyarshi , ita tana jawoni a jikinta saɓanin mahaifiyar Dikko dan haka aka shiga neman kai ƙarshen rayuwar Dikko dani , itace take aikena nemo mata asiri tana san ganin ƙarshen Dikko tace yadda itama bata da namiji babu wacce ta isa tayi namiji a gidan , tun da aka haifi Dikko take neman sa'arshi bata samu ba kuma baza ta daina ba haka kuma bazata gajiya ba har sai ranar da Dikko ya daina numfashi.
Ina cikin ƙulun bitar bin malamai da bokaye Al ' Ameen ya saƙo cikin aiki ta hanyar bina da yayi ban sani ba har inda zanje , bayan ya tabbatar da komai yazo ya zayyana min hankalina ya tashi kuma na firgita amma sai yacemin na haɗashi da matar Dady na faɗa mata cewa shima yana san ganin bayan mai gida ne kuma yana shirye akan zai bata taimako ko wane iri take so.
Tayi na'am da haka itace ta bada kuɗi Al ' Ameen yaje ya samo asiri aka haɗa manyan masifa aka binne a wani daji sai iskokai suke gadi ana biyansu da jini duk karshen sati , wanda kuma ake so yaci a abinci shine idan yaci zai riƙa haukacewa duk lokacin da yayi fushi yana maganar kisa , iskokai kuma sune zasu riƙa shafarshi , Al ' Ameen yace zai iya bashi , tou shine maganin daya bashi a London , dan rigimarshi shine suka juya abun da faɗanshi shi yasa duk lokacin da yayi fushi sai ya riƙa cewa saina kashe ka................ Farkon asirin rashin lafiya ya farayi kaɗan² Dady yasa aka dawo dashi nigeria baida lokacin tafiya ya tsaya yana ta siyasa , Dikko yayi ciwo na tashin hankali babu wanda ya bashi tashi a duniya , saida aka saka mishi robar hanci kowa ya haƙura dashi , shine Dady yaita rashin lafiya sakamakon ciwon Dikko har ya samu ciwon zuciya saboda tunani , aminin shi Dady shine ya gano ciwon Dikko asiri ne ya kuma faɗawa Dady ciwon Dikko bana asibiti bane ba dan wasu Allah ya basu lilimin gane sihiri , kuma ya miƙe tsaye ya gano cewa Dikko ana so ne ya mutu ta ko wane hali idan bai mutu da kanshi ba yayi kisa sai a yanke mishi hukuncin kisa kuma shi ya samo duk wannan magungun nan da ake mashi amfani dasu ,
Abinda yasa Dikko yasan ina da sa hannu a rashin lafiyarshi , mai aikin Momy taji muna magana da Al ' Ameen a palo ni kwata² bansan tana nan ba kuma bansan ta shigo ba , Al ' Ameen yana magana ƙasa² yake faɗamin boka yace abokin Dady ya miƙe tsaye akan saiya gano duk wani mai sa hannu a rashin lafiyan mai gida shine boka ya bada wasu layu yace aje a tsakiyar gidan nan a rufe ana rufesu an rufe zancen , zaici gaba da magana aka kirashi a waya ya fita bayanshi na bi muka bar ɗakin gaba ɗayanmu , tou itace taje ta faɗawa Dikko iyakar abinda taji amma bata san da waye nake maganar ba , shine yazo yace min ni bazaimin komai ba amma in faɗa masa ko waye yake da saka hannu kuma waye zai binne layu a cikin gidansu , kafin inyi magana shine ya nufi wurin Mom inshi wai tazo taji da kunnenta an haɗa kai da Suwaiba an cuci rayuwarshi sai idan yayi magana ace bashi da haƙuri ya cika masifa , sanin halin Dikko yasa kafin ya dawo na gudu dan nasan duk da yace bazaimin komai ba nasan sai yayi idan har ya riƙeni mai kwatata a hannunshi sai Allah shine na gudu Dikko baisan daga inda nazo ba kuma baisan ina zan koma ba tsintoni yayi kuma na gudu abuna , ashe Al ' Ameen shine yayi sanadin zamana gurguwa , ya bini ya kasheni gudun karna tona musu asiri , shine ya ɗiɗɗirka min alburusai a ƙafa , wanda na faɗi bansan ina kaina yake ba saidai na gannin da yankakkin ƙafafuwa.
Bansan Sultana ba ina jinya aka ajiyemin kwalba da waya , na kira Malamin na bashi shi kuma malamin ya kira Bello ya bashi bayan sunyi ciniki ya ƙara masa akan farashin da ita matar data bani ya maida ma Bello kwalba , bansan Sultana tana auren Dikko ba , abinda yasa kuwa na koreta daga wurin nace mata bana san matsala ta sake shigowa rayuwata dan bansan ita kuma abinda rayuwarta ta dosa ba..........
Lahaula wala kquwwata illah billahil 'aliyyul azeem Dikko ya furta suna fita daga cikin gidanshi ya dawo daga sumar da yayi , a ɗiymuwance yace ina ne nan ina kuma zamuje ? Kallon kanshi yayi sannan ya kalli inda aka kwantar da kujerar gaban mota Sultana kwance , laluba aljihunanshi yayi sannan yace ina wayoyina ? Ya tambayi Ashiru , ban ɗauko ba , to koma , da rubos Ashiru ya koma har ƙofar get in gidan , yana tsayawa Dikko ya fita da sauri yaje ya ɗauko wayoyin ya dawo , yana shiga mota ya kira waya , bayan an ɗauki waya yake sanar da M D in asibitin yana da maralafiya suna zuwa babu jimawa dan a shirya ma zuwan nasu , ya kuma faɗa masa abinda ya faru , na cikin wayar yayi magana shi kuma bai sake magana ba ya tsinke kiran , kallon Sultana yayi yaga tana ciccire² ko fizge² kawai dai { Convulsion } salati yayi tare da cewa kai bi tacan , da sauri Ashiru ya juya sitiyari yana cewa Dady yace mu haɗu dashi gida , Dikko yace ba gida ba takamin motar nan da gudu kayi ta can yana nuna mishi hanyar da zaibi da hannunshi idonshi yana kan Sultana , gudu Ashiru yake falfalawa amma Dikko cewa yakeyi kaje ׳................ Ƙannenshi "yan ɗayan ɗakin dake binsu suna ganin Ashiru ya canja hanya suma suka bi bayanshi da gudu kamar yadda suka ga Ashirun nayi.
Dikko yana tsinke kiran M D ya kira doctors team on call su tanaji É—aki a amenity DK yana zuwa da mara lafiya kuma su shirya ma zuwan mara lafiyar da zai kawo.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka iya asibitin ƙashi kuma har yanzu Sultana bata daina fiffizgewa ba , tuni an shirya ma zuwansu a saman ɗan gadon da ake ɗaukar marasa lafiya aka ɗorata aka shiga da ita cikin accident and emergency ,
Taimako na farko da aka fara bata allura akayi mata diazepam dan dakatar da wannan fiffizgewar da takeyi , cikin mintuna 3 gaba ɗayan jikinta ya saki ta daina ciccire² a mintuna biyu da suka sake bugawa ta ɗauke gaba ɗayanta wato ta tafi bacci.....
Daga A & E aka wuce da ita amenity nan aka bata ɗaki , cike da tausayi Dikko yabi Sultana dake kwance a saman gado da kallo mai nuna da yana tausayinta sannan ya juyo ya kalli Ashiru dake bashi waya Dady yana kiranshi , ansar wayar yayi sannan yace ma "yan uwanshi suje waje , tashi sukayi suka fita har Ashiru , magana yayi da mahaifinshi bayan ya gama ya zauna a gefen gado ya riƙo hannun Sultana yana shafa fuskarshi dashi , da hannunshi na haggu kuma yana shafa gefen fuskarta ya tsareta da kallo yana mai addu'a ubangiji ya taƙaita wahala yasa An mata karta samu damuwa , likitoci suma kuma suna jiran farkowarta su ɗauki BP { Blood Pressure } nata sai ansan abinyi........
A hankali ya mayar da hannun nata ya ajiye tare da cewa wannan fa shine wauta bugun mace da mangariba , wayarshi ya ɗauka yana ƙara kallon hoton da Yazeed ya turo mishi shida An mata , yayi rantsuwa kuma ya ɗauki alƙawari da zuciyarshi Al ' Ameen Yazeed da Suwaiba idan ya barsu sun huta bai yafewa kanshi ba , Allah dai ya bawa An mata lafiya............
01/12/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 84
Kiran Ashiru ne ya shigo a wayarshi saida ya sake shafo fuskar Sultana ya ɗauki wayar tare da cewa ku shigo na gama , shigowa sukayi tayi dan duk wani yaron Dikko ya samu damar isowa a asibitin ɗakin baya anshe su , kallon Sultana Dikko yayi sannan ya kallesu yana cewa ku ɗan rage ina fitowa babu jimawa ya ƙarasa maganar yana kallon ƙannenshi yace ku kuma ku tafi gida kunji ngode ,
Yaya ai zamu kwana a nan ne inji Dady munyi waya dashi , murmushi Dikko yayi kaɗan tare da tsareta da ido irin kallon nan na rage gulof yace Dadyn yace ku kwana ? Ah Yaya ta daburce , ɗaure fuska yayi tare da cewa ku wuce ku tafi zanzo gidan anjima kunji ya ƙarasa maganar cikin sanyi.
Tou Yaya kuzo mu tafi tana jan "yan uwanta cikin rashin jin daɗi , har zasu fita Dikko yaga kamar babu daɗi yace Ni'ima zo ita ya kira dan itace babba a cikinsu , dawowa tayi ta tsaya gabanshi tana cewa gani kanta yana kallon ƙasa , me ne ne ? Kinji kamar ban kyauta ba ko ? A , a , Yaya , kun tabbata ? Ya ƙarasa yana kallon inda sauran suke tsaye , gaba ɗayansu suka ansa mun tabbata Yaya , yawwa to ngode ku huta gajiya , yawwa suka faɗa suna Allah ya bata lafiya.....
Momy kuwa bayan Dikko ya É—auki wayoyinshi ya fita itama bin bayanshi tayi ita da zugar É—iyanta wai tunda har akan Dikko Dady ya faÉ—a mata magana ta bar mishi shi kuma kada wanda ya buga mishi waya ya jajanta mishi yayi rashin lafiya sai Dikko ya gane bashi da wayau su mata ne kuma suna da yawa su haÉ—e mishi kai idan har suka bari ya rinjayesu zasu sha wahalarshi karsu sake zuwa gidanshi kowa yaje yayi rayuwarshi , idan yaji ya takura zai kira Dady ya faÉ—a mishi a lokacin ita kuma zata faÉ—awa Dady magana ,
Yazeed kuwa tunda ya tura hoto bugun zuciyar yaci gaba da halbawa ga abokinshi da aka kama wanda yayi ma Dikko magana ya fito dashi zasu shiga kotu , kuma ya daÉ—e da tura hoto baya goguwa kuma Dikko kaÉ—ai ya isa ya tsaya mishi , matsala ta taho lallai haÉ—uwarshi da Dikko ba daÉ—i amma addu'arshi É—aya Allah yasa Dikko ya saki Sultana.....
Matar Dady kuwa ta shiga ta tsaya tsaff a cikin yinin ranar yau tasa Al ' Ameen ya samo mata lambar wayar Maman Sultana har gidan Kaka yaje ya samota da kanshi , bayan ya kawo mata ta rangaɗa mata kira babu daɗewa Inna ta ɗauka suka gaisa ta gabatar da kanta da cewa ita matar gwamnan katsina ce , Inna tace sai akayi ya kuma ? Dan ita a tunaninta Maman DK ce , ita kuma taci gaba da rattafa mata cewa Dikko ya jefo mata "ya daga saman benen kanta ya daki ƙasa saboda shi ya riga gangar jikinta zuwa ƙasa ta daku sosai idan ta yadda ta ɗauke "yarta kafin ya kashe ta dama tana ta shan wahalar dangin miji tsangwamar kishiya masifar miji ga duka ga zagi ga gori abundai ba kyan gani , bayan ta gama faɗar duk buƙatunta Inna tace tou ngode sosai amma ni bana tare ma Sultana faɗa a gidan aure kuma duk abinda mijinta zai mata ni bai shafeni ba ai ina sane da ita tunda nasan na haifeta , na barta ta gurzu da rayuwa dan dani da ita ba'a san gawar farko ba ta koyi rayuwa ta koyi riƙe damuwa haƙuri da rayuwa dan idan nice yau bani ce gobe ba dan nima kin ganni nan nima nabi mijina dan shine gatana kuma marufar asiri na , Sultana yanzu tabar ƙarƙashin iyayenta ta koma ƙarƙashin aure banda iko da ita kuma ita ba yarinya bace idan taji ta matsu tana da ƙafafuwa ta gudu , Allah ya bata lafiya....... Tana faɗin haka ta tsinke kiranta.... Hmmmm Inna kenan manyan duniya...
Bayan awanni biyu da wasu "yan mintuna Sultana ta dawo , kamar mahaukaciya haka ta riƙa kallo tana motsa kanta kaɗan² tana kallo wurare , Ashiru yace sannu Hajiya , binshi tayi da ido ta kwalalo su sosai , Dikko dake zaune saman abin sallah ya tashi yaje wurinta An mata sannu , shima kallo tabishi dashi duk kamar dai mutane baƙi ne a wurinta sai kace wata sakara ,
Murmushi Dikko yayi tare da duƙawa kusa da ita yace sannu An mata , bata iya magana kwata² ta riƙe wuri ɗaya da ido tana kallo , ke me ne ne ? Baki ganni ba ? Ashiru yace mai gida ai sai a hankali zata ganeka , ƙarya ne ta ganeni mana ke ba kin gane ni ba ? Yayi maganar yana juyo kanta ta yadda kallonta zai dawo wurinshi ,
Kallo ɗaya tayi ma Dikko ta juyar da kanta gefe hawaye yana fita daga idonta , murmushi Dikko ya sakeyi tare da cewa bana faɗa maka ta gane ni ba , ɗan taɓe baki yayi yana cewa haushi na akeji baiwar Allah An mata ai koni saina baki shawara kiji haushin Dikko nima kaina haushin kaina nakeji , Ashiru jeka waje , Allah ya taimaki mai gida ya faɗa tare da fita daga ɗakin ,
Gefen gadon ya zauna yace An mata kiyi haƙuri don Allah na bari bazan ƙaraba ki gafarceni na yadda ni mahaukaci ne ya ƙarasa maganar hawaye yana fita daga idonshi , girgiza kai tayi dan bata iya magana , kinyi haƙuri ko ? Da kanta ta nuna a , a , haba An matana nasan kinyi haƙuri kuma bakiji fushi ba ke mai yafiya ce a gareni ki ƙara yafemin kinji An matana..... Ya ƙarasa magannar cikin yanayin neman gafara....
A , a , ta sake nunawa , hannunshi yasa saman idonta ya shafa ta rufe idon yace haba ƙaramar yarinya yau kuma Dikkon ake ma haka ? Abokin faɗan naki ? Kinyi min adalci kenan An mata ? Kiyi haƙuri mana nayi miki alƙawari bazan sake ba dan Allah ya riƙo hannun ta ɗaya ya soka "yan yatsunshi a ciki ya juyar da bayan hannun nata ya ɗora dai² saitin zuciyarshi ya danne da ɗayan hannun nashi yace kinji yadda zuciyata ke halbawa itama haƙuri take baki kiyi haƙuri An mata badan halin Dikko ba dan Allah ki rufamin asiri ki yafemin , karki yadda wani ya gano kinajin haushi na a gaban idon mutane ki nuna babu wani damuwa na yadda idan mun koma gida duk abinda kika ga dama kiyimin na yadda amma dan girman Allah idan kinga mutane ki riƙa sakin ranki karki wani haɗe rai kinji ko........ ? Shiru tayi batayi magana , kalli ya nuna mata idonshi jifa Dikko yana kuka ke bakyajin ƙunya ina miki kuka "yar yarinya ya ƙarasa yana murmushin ƙarfin hali , kallonshi takeyi har yanzu ba magana , hannunta yasa ya shafa gemunshi tare da ɗaga mata gira yace na bari matar Dikko ya faɗa da wani irin yanayi , duba wayarshi yayi da saƙo ya shigo , ɗaure fuska yayi ya goge hawayen tare da kama kanshi wai likitoci zasu shigo inji Ashiru ya turo mishi a waya , shima ya maida da to....
Hada Ashiru suka shigo , gaisawa sukayi da Dikko suna mishi yamai jiki , alhamdulillah daga haka bai sake magana saidai idan sunyi magana Ashiru yayi magana , bayan sun gama ɗaukar BP { blood pressure } nomal kamar yadda sukace aka wuce da ita C T Scan { Computered Tumography }. Dikko dai baije ba sai Ashiru da sauran tawagar suka bi bayan a can sun gama abinda sukeyi suka buƙaci sa hannun Dikko ya sa ya tafi ansa kiran Dady bayan ya gama sa musu hannun zai dawo kafin su gama abinda sukeyi.
Dady yayi ma Dikko faɗa sosai akan me yasa ya jefo ɗiyar mutane daga sama ko yayi hauka ne ? Waye yace masa ana dukan mace ma tun farko kenan ? Shi me yasa yakeyin abu kamar ƙaramin yaro wai ? Haƙuri yaba Dady shi bafa shine ya jefota ba faɗa yayi mata kawai saita firgita , Dady yace tou waye yace ana firgita mace ? Me na faɗa maka akan mace tun auren ka da Sadiyya ? Tunda baka san ta ka sawaƙe mata ta kama gabanta kafin ka jawomin tashin hankali , Dady ba haka bane , tare shi Dady yayi cewa ka rufe min baki ya faɗa cikin faɗa yana ci gaba da cewa ka saki yarinyar nan , haba Da.... , cikin hayani Dady yace bana san maganarka ka bani takaddar sakinta har sai yaushe zan huta da halinka Babana.......? Hawaye ya zubo daga idon Dikko yace Dady ni banayin saki , sai kayishi Babana sai ka saki yarinyar nan bazan bari ka kashe yarinyar mutane ba , yanzu da , da tsautsayi shi kenan maganar nan bazai rufe ba yana can yana zagawa a gari ka kashe matarka , dama na Sadiyya har yanzu surutu bai tsaya ba akan ka tsafe yarinyar mutane banda hauka kuma zakaje da gangan ka jefo yarinyar mutane kai sarkin zuciya itama ta mutu ka zama matsafin kenan ko................?
Shiru Dikko yayi kanshi yana kallon ƙasa lokaci bayan lokaci yana buɗe bakinshi kaɗan yana jan iska cikin ɓacin rai , Dady kuma ganin Dikko yana kuka yasa ya sassauta maganarshi yana cewa ni ne kaɗai na isa na faɗa maka gaskiya komin rashin daɗinta bana san abinda kake yi kaji ? Ya ƙarasa maganar cikin sigar lallashi , kallon Dady Dikko yayi sannan yace kaima mahaukaci kake cemin ko Dady ? Baban naka ne mahaukaci ko ? Ya faɗa yana ɗora kanshi a kafaɗar Dady yana kuka , tunda kacemin mahaukaci kowa ma zaice ni mahauka ci ne.
Bakajin magana Babana nace bana san halin nan bazaka bari ba ya kake so inyi ? Kayi haƙuri Dady na bari bazan sake firgita ta ba , idan na sake ji kuma fa ? Sai kayi min faɗa ya ƙarasa yana kallon idon mahaifinshi cikin soyayya , murmushi Dady yayi shima Dikkon murmushi yayi tare da rumgume Dady yana dariya........ Aka daina zancen saki.
Daga wurin Dady wurin Momy ya wuce duk sallamar da yayi bata ansa ba daga ita har "yan uwanshi kuma babu wanda ya kalleshi , Rabiya sai haɗe rai takeyi tana hararar bango , cikin rashin jin daɗi Dikko yace Momy meya faru ? Fuuuu ta tashi tayi ciki suma suka tashi suka bi bayanta , cikin yanayin damuwa Dikko yabi bayanta tana zaune a gefen gado sai ɓata rai take , wurinta yaje ya duƙa gabanta ya riƙe hannunta cikin lallashi yace baki lafiya ? Cikin faɗa tace lafiyata qalau , tou me yayi zafi haka ? Ya faɗa yana tsareta da ido , ban sani ba tunda kaje ka haɗani da ubanka kai ɗan zinari , me nace masa Momy ? Kace masa ni bana sanka , Rabiya tace Momy ji har kin manta kina masa magana shi yasa yake iskancin daya ga dama , cikin ɓacin rai ya leƙa ta gefen Momy inda Rabiya take zaune yace ki fita hanyata kafin in kwantar dake , Momy tace kwantar da ita Iliya ɗan mai ƙarfi , ƙannenshi ya kalla tare da cewa da Allah ku fita kuba mutane wuri , tashi sukayi suka fita wurin ya rage daga Dikko sai Momy sai yayyenshi , Rabiya tace to ka kwantar dani mara kunya , bai kalleta ba yace Momy me nayi miki ? Dikkon ne mai laifi a wurinki ? Haba Mamana waye zai haɗani dake ? Cikin sansanyar murya tace Dadynku ne yayi min wulaƙanci a gaban kishiya abin baimin daɗi ba , Rabiya tace ki kyale shi Momy ai duk shine munafukin , dunƙule hannunshi yayi tare dakai zamiya taja baya da sauri yace zan...... Riƙeshi Momy tayi tace ya isa ta faɗa tare da miƙewa taja hannunshi suka fita waje ,
Wurin motarshi suka tsaya tana masa magana wai yanzu ya daina santa a gaban idonshi ake mata iskanci a gidan nan yana kallo bayayin komai , yace Momy tou yanzu kuma me akayi miki wanda nayi shiru ? Ɗan ɓata rai tayi cikin rashin san zaman lafiya tace yanzu ba a gabanshi Bilki taje take faffaɗa mata maganganu marasa daɗi ba shine yayi shiru { abiyar zamanta } Dikko yace Momy dan girman Allah kiyi haƙuri babu yadda za'ayi ta faɗa miki maganganu kedai ki bari a zauna lafiya , sai kice anyi miki laifi kullum inyi ta hauka har an fara cemin mahaukaci , tou Dikko ƙarya nakeyi ta juya zata koma ciki da ɓacin rai tana gunguni , da sauri yasha gabanta yace shikenan zan mata magana , dariya tayi irin ta ƙasaitaccin mata , duƙawa Dikko yayi ta dafa kanshi tana cewa Allah yayi maka albarka , amin ya faɗa ta koma cikin ɗaki ,
A gajiye ya koma mota ya kifa fuskarshi a saman sitiyari shidai baisan abinda yasa gidansu akeyin bahaggon zama ba , sai zafin kishi da nuna "yan ubanci "yan wancan ɗakin basa san "yan wancan ɗakin , kowa ɗan ɗakinsu ya sani kuma shi yake so , sai kuma wani babban shirme idan ana faɗan kishi sai kowa ya shigar ma mahaifiyarshi wai me yasa mata sukeyin haka ? Shifa a tunaninshi matar uba uwa ce , ita kuma "ya "yan mijinta kamar itace ta haifa , gaskiya gaba ɗaya babu kyautawa su kuma wanda iyayensu basa gidan an ɗauki masifar duniya an ɗora akansu ga masifar aiki ga aike² kamar ba "ya "yan Dady ba sunayin wata irin rayuwa kamar "yan aiki kuma a hanasu ganin Dady saidai shi idan yana nan yake musu jagoranci zuwa wurin Dadyn , kuma shima Dadyn ya kamata idan baya nan ya dawo yaga kowa suma ya nemesu tunda ai yasan ya haife su , haka ya siyama kowa sabuwar mota amma duk wanda babu uwarshi a gidan babu rabonta , dole shine ya siya musu motocin da suke hawa Momy kuwa tace ina wuta ta jefa Dikko tayi tashin hankali saida aka kai ruwa rana suke hawan motoci , su Momy basa tunanin idan Dady ya sakesu ko suka mutu suka bar nasu "ya "ya wace irin rayuwa zasuyi ? Ya kamata a riƙa adalci a rayuwar "ya "yan da basa tare da iyayensu a gidan miji dan babu wanda yasan abinda gobe zatayi haka kuma babu wanda yasan maci tuwo sai miya ta ƙare , shi kuma yayi bakin ƙoƙarinshi wurin ganin Momy ta jawo yaran jikinta tana basu kulawa tarbiyya da tsaro kamar yadda take ba nata "ya "yan amma tace sam bata ƙaunar ɗan kishiya , tsoki yayi a dai² lokacin da text in Umar ya shigo Al ' Ameen ya shiga gidan gwamnati yanzu , dan yadda yasa aka sakawa duk wani motsin Sultana ido a baya haka yasa a sakawa Al ' Ameen.....
Yana tashin mota wani text in ya shigo amma yanzu ba Umar bane Al ' Ameen ya shigo yana ɗakin Aunty , kai tsaye wurin Dikko ya nufa da gudun tashin hankali ɓacin rai yana hawa , tunda motarshi ta tsaya gaba ɗayansu sukayo waje hada Al ' Ameen da matar Dady ita tana cewa wannan wane irin iskancin tuƙi ne zaka zo ka tashi hankalin mutane , wani irin kallo Dikko yayi mata sannan ya kalli Al ' Ameen yace me kazo yi nan ne ? Shiru yayi baiyi magana ba , fitowa yayi daga cikin motar ya taka ƙafarshi ta baya ya dafa murfin motar da hannun damarshi na haggun kuma riƙe a ƙugunshi yace da kai nake me kazo yi nan ne ? Aike na tayi , zuwa ina ? A daburce yace ca ca can..... Ya nuna da hannunshi , har yaushe aka fara aiken ni ban sani ba ? Yanzu ne mai gida , tou ya akayi ka shiga ɗakinta ? Kai Dikko bana san iskanci ni zan aiki yaro kazo kana mishi tambayoyi , hannun daya dafa murfin mota ya ɗaga mata ba tare daya kalleta ba yace hajiya ba dake nake ba yanayin fushi yana gaf ki kama gabanki ko kimin shiru , sakin murfin yayi ya matsa kusa da ita ya riƙe ƙugu yace ai nima a cikin matan na tashi kuma duk wani makirci na iya kuma duk a wurinku na koya ki bari kafin in gigita miki tunani , wurin Al ' Ameen ya koma ya riƙe wuyanshi amma bai matse ba yace tunda kake ka taɓa ganin wani mai aikinta yaje ɗakin Momy ?
Kafin Al ' Ameen yayi magana ta ɗaga murya tana salati cikin kuka wai ita Dikko ya daka ? Ta shiga 3 ta lalace , Dikko yace tou tunda sharrin kike so bari ki tara man mutane idan Dady yazo zance Al ' Ameen na kama ɗakinki , ta ɗage baki bata ƙara ihun ba kuma bata rufe bakinta cikin tashin hankali ta kalli Dikko tace ummmmmm , murmushi Dikko da gefen bakinshi yace ummmm a dai² lokacin da yayi ma kan Al ' Ameen kyakkyawan riƙo da duka hannayenshi ya buga shi da bango yayi mishi fashin kwakwa , amma ba fashewa yayi biyu ba , take a wurin Al ' Ameen ya ɗauke , dariya Dikko yayi ya kalli matar Dady har yanzu bata rufe bakinta ba , but ya buɗe ya jefe Al ' Ameen ya rufe yaja motar da gudu ya barɓaɗeta da hayaƙi bata matsa ba tana tsaye wurin , Goruba yakai Al ' Ameen ya cire wayar jikinshi ya nufi asibiti dan dare yayi.
Satina 3 a asibiti bayan nasha doguwar wahala dan bayan an haska ƙwalwata likitoci sun tabbatar da jini ya shiga brain ina saida akayi min borrhole surgery kuma kullum Dikko ne yake jinyata komai shi yakeyi min yana bani haƙuri akan abinda ya faru bazai ƙara ba , amma na daka kaina ƙasa bazan komai zama dashi ba.
Inna kuwa Dikko ya kirata ya faɗa mata banda lafiya tace Allah ya sawaƙe itama tasha fama da rashin lafiyar wai tayi ɓarin ciki , da yace mata gani cewa tayi tana gaisheni itama zata dawo kwanan nan ,
Dikko kuwa ya ƙufule akan duk wanda baizo ganin Sultana ba shima saiya rama , zama dai cikin mata yasa shima ya iya tsegumi da irin halinsu ,
Bayan an gama kai magunguna a mota da dai abinda ya kamata yace muje , fashewa nayi da kuka ni bazan zauna ba , haba An mata wai meye kikeyi haka don Allah ? Nifa gaskiya bana sanka saika sakeni da , da ƙarar kwana dana mutu an fara kiran marigayi Sultana , yi haƙuri bazan ƙara ba , nidai bazan zauna dakai ba mahaukaci , ba komai idan ma kince mahaukacin ne ai banji wani damuwa ba na yadda ni mahaukaci ne kiyi haƙuri dan girman Allah An mata , nifa bana zama dakai saika sakeni , daka min tsawa yayi tare da cewa anƙi a sakekin kuma tunda ke yarinya ce ta tashi mu tafi bara ki sake magana kiga yadda zanyi dake dan kiga ina lallaɓaki kike tunanin na warke ? Tou ina nan yadda kika sanni tun farko ban canja ba sai abinda yayi gaba ya ƙarasa maganar yana min kallon da bana so.
Naji tsoro amma saina kalli ƙasa na sake cewa saika sakeni , zama yayi kusa dani yace An mata kalli ya nunamin cikin ƙwayar idonshi da kallonshi mai ɓatar da damuwa yace yanzu ko dan albarkacin wannan bazanci ba ? Haba ƙaramar yarinyar Dikko cikin sigar lallashi ya ƙarasa maganar yana murmushi tare da rungumoni jikinshi ,
A wahalce na sauke ajiyar zuciya cikin shashshekar kuka , dafe ƙeyata yayi da hannunshi yace ai na sani kiji natsuwa daga jikina An mata yayi maganar yana jawo numfashi daga cikin cikinshi saiya ɗan riƙeshi a ƙirjinshi kamar shashsheka haka da ɗan sauri² mai tayar da tsikar jiki cikin salo mai tada hankali , shiru nayi ban sake ko motsi ba na ƙara lafewa a jikinshi , murmushi yayi a zuciyarshi yace haba An mata ina zaki tafi kibar mahaukaci ? Ai muna tare harsai hauka ya ƙare.
Saida ya tabbatar ya ladabtar da jikina ya fara ƙoƙarin sakina , ƙara riƙeshi nayi ina kuka , me ne ne kuma ? Ba komai na bashi ansa , tou sakeni , anƙi a sakenka na faɗa da irin ansar daya bani aa farko ina ƙara lafewa a jikinshi kamar ƙadangare ya lafe jikin bango idan yaga mage , murmushi Dikko yayi cewa tou tashi muje gida sai ki rufe ƙofa ga makullinma tun yanzu ya bani a dai² lokacin daya ɗagoni yana kallona yace kinga sai muci karenmu ba babbaka ko......? Ya ƙarasa yana ɓata fuska a sakace , Murmushi nayi banyi magana ba ina kallonshi , yace yawwa jarumata muje ya ƙarasa maganar yana saukoni daga saman gadon....
Ashiru ne ya É—aukemu , dani da Dikko muna baya kuma tunda muka baro É—akin har yanzu bai sake magana ba sai haÉ—e rai yakeyi kamar bai sanni ba , ko magana nayi mishi saidai yayi min wani irin gittaccen kallo , ni na kasa gane inda ya dosa wani irin birkitaccen hali yake dashi yanzu mutum anjima ba mutum ba , tsoki nayi ban sake magana har muka isa goruba road , ajiyemu Ashiru yayi ya tafi da motar ledar magungunan ya bani wai inje ciki yana zuwa kuma inyi wanka....
Banyi magana ba na shige , na daɗe sosai har nayi wanka na fito bai shigo ba , jikin madubi na matsa ina duƙar da kaina inda akayi min aiki , taƙaitaccen murmushi nayi tare da komawa da baya na zauna saman gado ina kallon kaina a madubi nace ina Amisty ? Kizo kiga ranar da nake faɗa tazo ,
Nace miki naji a jikina zan rasa wani babban abu mai muhinmanci a rayuwata , ni kuma zan shiga wani babban tashin hankali wanda bansan ranar zuwanshi ba , ashe abinda zan rasa ba komai bane sai Babana , tashin hankali kuma ashe shine wannan na taɓa kaina yau itace ranar wayyo gani anyi min aiki cikin kai niba mahaukaciya , fashewa nayi da kuka gaskiya rayuwata ta cika tsalle² a dai² lokacin nan ya shigo yana cewa kin fara ko ? Kedai kika sani An mata kiyi duk abinda kikaji kina iyawa , da gudu na tashi naje na rungume Dikko cikin kuka nace wai me yasa rayuwa take tsanantawa ne ? Ba tare daya riƙeni ba yace An mata duk yadda rayuwa ta baki kawai ki ansa , ya ƙarasa maganar yana jana zuwa gaban gado ya zaunar dani , wayata ya ciro daga aljihunshi Hafsa ke kirana , shine ya ɗauki wayar yace ya akayi ne ? Bayan wani lokaci yace lafiya , kila gaisheshi tayi nadaiji yace lafiya , ........, tana bacci , ........ Wane wuri ne ? ........ Tou bata da lafiya idan ta samu sauƙi zan kaita yana faɗin haka ya tsinke kiran !
Ajiye wayar yayi da nashi ya ɗauki kofi zai fita , tun kafin ya fita cikin kuka nace bazan sha ba , baiyi magana ba ya dawo ya ajiye kofin a inda yake ya nufi toilet , kuka naci gaba da yi ina maimaita bana sha kuma bazan sake sha ba mugunta kawai , har ya fito wanka ban dai tsegumi ba , ko inda nake bai kalla ba yaci gaba da huɗɗar gabanshi , ganin zai saka kaya nace nayi wankan na faɗa a tsiwace , tou ina ruwana da wankanki , ai kaine kace nayi wanka , rigarshi yake ƙoƙarin sakawa yana cewa tou ki kwanta kiyi bacci idan kuma kina zuwa tashi mu tafi G R A zanje Jiddah bata da lafiya , banyi magana ba na tafi inda ya ajiye kofin na ɗauka nace zansha , ai babu ya ƙare ki saka kayanki kawai mu tafi , yi haƙuri , a , a , dan Allah Dikko ai nace babu ya ƙarasa maganar yana kallona , na bari , zaki sha ne ? Ey tou jeki ibo ya faɗa yana cire rigar daya saka tare da cewa dandai baki lafiya amma yau dasai nayi miki rowa ƙaramar yarinya dake , murmushi nayi tare da juyawa na murza ƙuguna cikin salon jan hankali da neman faɗa , murmushi yayi ya biyo bayana yace bakijin magana ko An mata ? Nima yadda naga yana ɗaga gira nayi nace kai ka koyamin rashin jin ai...
Ah ni ƙarya kikemin , tare dashi mukaje wurin firij ni na riƙe kofin ya zuba yana kallona yace An mata nan gaba kodai nine zan riƙa riƙe makulli , hmmm idan ya ƙare bana sake siyowa inba haka idan kika kamani a ɗaki saina ci ƙaniyata yayi maganar yana riƙoni jikinshi bayan ya maida "yar jarkar a firij , ɗaga hannuna nayi da niyar shafa gemunshi amma saina ɗorashi a goshinshi , dan shima haka yakeyi baya yadda mace ta gane abinda yake tada mishi hankali a jikinta kuma ko yana kwance da mace yana warwarewa yana saiti baya surutu shiru yakeyi sai wani munafikin kukan kissa mai tsayawa a rai da tada hankali idan ka tunoshi , kome nake abun yana yawan zuwamin a rai , idan na tuno abun sai hankalina ya tashi sai naji maganar Dikko ko na ganshi ko naji ni a jikinshi nake samun natsuwa , Hmmm Dikko duniya , amma ban sani ba ko ni ɗaya yake ma haka ......?
Saifa na taɓo dan haka na ɗan basar na taho da hannu ina kawowa saitin bakinshi ya sumbaci hannun muah yana sauke wani irin nishi , tsikar jikina ta tashi yarrrrr da sauri na shanye maganin nace ngode , murmushi yayi ya jani zuwa ɗaki..... An danbace cikin tsari da sabon salo ba irin wancan ba...
Sai bayan isha'e muka isa G R A kuma an sauke bene anyi ma palo gyara na bada mamaki idan baka san wurin ba zaka rantse bene bai taɓa zama a wurin ba a cikin sati 3 , binshi nayi har ɗakin Jiddah ina ƙara kallon palon , ɗakin cike yake da mutane da "yan uwan Jiddah da mahaifiyar Dikko da danginshi , sai wata mai kama da maman Dikkon kila itace maman Jiddah , wani irin kallon tsana Momy ta bini dashi har naji babu daɗi jikina ya fara ƙyarma , kusa da Dikko na zauna idona ya cika da hawaye kuma har yanzu jikina bai daina ƙyarma ba dan ni a halin yanzu bana so nayi wani abu da zaisa nayi nisa da Dikko wallahi bana iya rabuwa dashi , cikin rawar murya nace Momy ina yini ɗauke kanta tayi bata ansa ba , kallona Dikko yayi yace me ne ne kike kuka ? Dakel na haɗiye yawun bakina nace ba komai , kallon Momy yayi sannan ya sake kallona , tana ganin Dikko ya kalloni ta nunamin saita kasheni , da sauri na ɗauke idona na gaishe da Maman Jiddah , itama ɗayan mara wayan ɗauke kanta tayi in banda rashin wayau abiyar zaman ɗiyarta aida da wayau ko ba daɗi tayi ta "yan bariki tace lafiya lau Sultana badai wayau "yan mata sunma makaɗi tusa.....
Duk basar dani sukayi sukaci gaba da firarsu ita Maman Jiddah babu ɗan kawaicin nan irin na sarakuta da Dikko ta saki baki sai ɓarin maganganu takeyi na rashin lissafi a gaban Dikko abinda na fahimta wurinta Jiddah ta gado surutun tsiya kamar akku , ita kuma Maman Dikko bata da yawan magana kuma bata cika dariya ba tana da natsuwa sosai tanayin magana cikin aji da kamun kai amma bata da mutunci "yar masifa ce wato mafaɗaciya su kuma su Dikko a wurin uwarsu suka gaji rashin mutunci , suna da sakin layi idan mutum ya shiga jikinsu dole zai raina su dan basu da sirri ga Mardiyya amma sai sakin layi suke suna maganganu.......
Dikko kuwa bayan ya gaisa dasu Momy wurin Jiddah ya koma yana ta jera mata sannu haushi abin ya bani kuma na ƙufule har a wuya ji munafurci ɗazun nan yake nuna ba wata bayan ni amma yanzu yaga Jiddah harya manta da Sultanar banza , kallon Jiddah nayi sai wani kwarkwasa takeyi tana kashe mishi ido shi kuma yabita da kallo , komi ya sameta ? Oho ma banza , miƙewa nayi na fita dan abune nasu na "yan uwa ni kuma a cikinsu bare ce ba "yar uwa ba dan haka na tattaro mutunci na nabar ɗakin ,
Palo na dawo na zauna , shiru² ba Dikko ba inuwarshi har 9:13pm gajiya nayi na kirashi a waya , ya akayi ? Ya tambayeni bayan ya ɗauka , bacci nakeji , kashe wayar yayi ya fito saida yazo inda nake zaune yace ai na ɗauka kin tafi kin kwanta , jeki ki kwanta fita zanyi yayi maganar yana miƙomin wayoyinshi , cikin ɓacin rai nace ai dama dole zakace naje na kwanta tunda kaje ka kasa ka tsare kai tattabara sarkin aure , yarinya kenan idan kinga dama tashi muje , nifa bana kwana gidan nan a ina ma zan kwana tunda an rushe ɗakin na ? Bai bani ansa ba yace tou naji baki kwana tashi kije Ashiru ya maida ki goruba , ai ni tsoro nakeji saidai mu tafi tare idan nayi bacci kaje inda zaka je , duk in fasa abinda zanyi sai kinyi bacci kammar sakaran namiji ? Ke zaki koyamin yadda zanyi rayuwa ma kenan ko ? Idan kinga dama ki bishi ni kinga tafiyata kuma karki zubar min da wayoyi yayi gaba abunshi............
02/12/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 85
Da sauri nabi bayanshi har an buɗe mishi mota ya shiga , yana shiga nima na shiga kafin a rufe , kallona yayi baiyi magana ba sai tsoki tare da matsawa daga kusa dani yana hararata , murmushi nayi kamar sakarai ina yaƙe haƙora , yadda nayi abun na bashi dariya yace hmmm Yarinya , tafiya aka farayi da motar ni kuma na miƙa mishi wayoyinshi yace in riƙe mishi zasu ajiyeni gida shi Kano zaije , cikin rashin jin daɗi nace haba Dikko Kano kuma yanzu na ƙarasa maganar kamar zanyi kuka , yi haƙuri An mata zan dawo ai ba kwana zanyi ba yayi maganar yana jawoni jikinshi , kwace jikina nayi ina cewa ai saika kaje kayi ta tafiya , yi haƙuri , ban sake magana ba har muka iso gida ,
Anayin parking na fita cikin ɓacin rai , kirana yayi nai banza dashi kamar banji ba , cikin fushi yace kije kiyi ta zuciyar ƙaramar yarinya dake , ban juyo ba na shige ciki da gudu ina kuka nidai bana so ya tafi da daren nan shine zai tafi ya barni , har sun fita daga gidan Dikko yaji kamar babu daɗi suka dawo , palo ya sameni kwance saman kujera ina kuka , cikin rarrashi yace An mata zo nan , dan bai shigo ba daga bakin ƙofa ya tsaya , ina tashi nayi bedroom , da sauri ya biyoni na kusa shiga ya riƙeni cikin disashshiyar murya yace haba An matana meye na fushi tou ? Yi haƙuri bazan daɗe ba maganina zan anso kinsan banajin daɗin tafiya da rana kafin ma kiyi bacci zan dawo insha Allah kinji An matan DK ya ƙarasa maganar yana rungumeni , banyi magana ba , ina shashshekar kuka , kinyi haƙuri ko ?
Ey , hannunshi yasa a aljihunshi ya ciro cingom saida ya saka a bakinshi yace kallar ni , tashi nayi daga jikinshi ina kallonshi , murmushi yayi da kallo mai kwantar da hankali tauna cingom in yayi sannan yace idan miji zaiyi tafiya ba'a mishi haka kinji ko ? Tom , ba'a yin abinda zaisa ya tafi da fushi kinji ? Tom , idan miji zaiyi tafiya addu'a ake mishi sai a rabu cikin soyayya da nuna kowa zai shiga taitaiyin shi idan abokin rayuwarshi baya kusa ki nunamin girman yadda zakiyi maraicina idan bama tare , zan tafi da soyayyarki kuma zanyi kewayarki zan dawo gareki ina mai farin ciki darajar waccan kulawar , kinga na baki wayoyina nace kije Ashiru ya maidake gida ni zanje na dawo ko ba daÉ—i sai kimin fatan alkairi ,
Kalli idona ki gani , kallonshi nayi cikin yanayin jin kunya , da nace zanje in dawo sai ki kalleni da irin wannan kallon ya nunamin cikin wata irin murya da shagwaɓa ina zakaje haka ne ? Kin gane ? Zanji wani iri a zuciyata kinyi min magana da salon da dole saina kalla , sai ya saki muryarshi yadda yake magana yace sai ince hajiya kano zanje , sake shagwaɓewa yayi ya nuna yadda zanyi idan zan bashi ansa , amma sai kiyi ta abu da Allah na yarinta ba lallashi komai maganarki a tsaye baki lanƙwasamin harshe nace miki bana san yadda kikemin magana saiki tayi min kallon da bana so , daga nace zan tafi kano ba addu'a ba komai fuuuuu ke ƙaramar Yarinya , kinsan Allah idan kikayi wasa saina ƙara aure ,
Tou kaje ka ƙara mana na hanaka ? Kinji yarintar ko ? Ji abinda kikeyi kina magana da miji kina ɗaga mishi murya , ba abinda kika iya sai kwanciya jikina shine kaɗai aikinki saina raba wurin kwanciya dake tunda ke Yarinya ce , kaje ka raba , murmushi yayi yace nasan ciwonki , yadda nayi maganar ya nuna dole zakace naje na kwanta tunda kaje ka kasa ka tsare kai tattabara sarkin aure , murmushi yayi tare dayin wasa da idonshi yana ci gaba cewa yes haka kishi ne , kishi kuma so ne , da hannunshi ya rungume kanshi yace wayyo An mata na kishi na ci gaba sabo ,
Da wata irin tafiya mai taɓa zuciya ya fita yana cewa ko bakimin addu'a a gabana ba nasan zakiyi a zuciyarki kuma saina yo miki tsaraba tunda kikaji kishina a zuciyarki saina sa kinyi farin ciki mage zan samo miki , ya fice , murmushi nayi da farin ciki na shige ɗaki da gudu na hau gado ina tsalle Allah ya tsare hanya mutumina.
Bayan na kwanta na ɗauki wayata na kira Amisty , babu wani daɗewa ta ɗauka bayan gaisuwa nace Amisty don Allah rubuto min An mata ki turomin , kamar ya ? An mata haka zaki rubuto min , tou ta faɗa tare da ajiye waya , burum ta rubuto ta turomin , gyara kwanciya nayi na rubuta An mata , wayar Dikko ta buɗe , Allah sarki Dikko ashe da gaske yake da sunan da yake kirana ya kulle wayarshi , ba wani ruwana da saƙonni wayarshi dan bana ganewa , ma'adanar hotuna na shiga ina kallon Dikko da "yan uwanshi , haka dai nayi ta zaliƙe² a wayarshi har na shiga inda nakejin maganata da tashi duk wayar da nakeyi dashi yana record kenan , Allah sarki Dikko , saida nayi filla² da duk inda nake iya shiga a wayar amma banga hotuna na ba , tou ina suke ai yacemin wayarshi bata san kowa ba daga An mata sai Doki , tou naga dukuna babu iyaka a wayar amma ina An mata tou........ ?
Tashi nayi zaune na ciji ɗan tsayana cikin yanayin mamaki to dama masu gemu sunayin ƙarya ? Tsoki nayi tare da ajiye wayar , ina ajiyewa kira ya shigo , kamar ansa ni na ɗauka tare da cewa waye ? Caca , Oh Jiddah ce kenan ko ? Zuciyata ta fara turani inyi abinda zan ɓata mata rai amma sai wani sashi na zuciyata yace bari suja miki sharri Dikko ya sakeki , da sauri na kama kaina nace yana wanka , uban waye yasa kika ɗaukar mishi waya tou ? Ina da ansar bata amma nidai bana so naje nayi abinda zai jawomin tashin hankali har Dikko yayi fushi dani , tsinke kiran nayi , haka kiran yaita shigowa amma ban ɗauka ba , tunda kiran Jiddah ya shigo kira yaci gaba da shigowa , ita kuma ɗayar wayar naga hoton jirgi daga sama ita kira baya shigowa kenan ?
Da naji kiran yayi yawa zasu hanani bacci kawai na kashe wayar , nayi kwanciyata naci gaba da bacci abuna....
Yau kwanan Al ' Ameen 22 babu wanda yasan inda yake , duk wanda yasan yana da haɗin guiwa da Al ' Ameen akan "yan tsirkulle² hankalinshi a tashe yake danjin Dikko ya tafi dashi tun daga ranar da Dikko ya tafi dashi har zuwa yau basu da nutsuwa , su basu san ba'a kan matsalarsu Dikko ya riƙe Al ' Ameen ba shi Dikkon ya ɗauki Al ' Ameen dan yasan abinda ke tsakaninshi da Jiddah ne , wanda har ba'a magana sai tsakar dare , shi bai wani san akwai wani abu tsakaninshi da matar Dady ba.....
Zaune take ta wani kame abunta a saman kujera ta ɗauke kanta gefe gudu ba kajin wani lafiyayyen motsi sai ƙarar cingom in ita ƙasa×ⴠ, kallonta Dady yayi yace wai meke damunki ne ? Duk kinbi kin tashin hankalinki akan wani dalili naki na daban , akan me fushin wani ni zai shafe ni ne ? Saida ta ƙara ƙaras² sannan tace haba mai girma gwamna ya za'ayi ace duk inda Dikko yake ajiye mutane ace an kasa samo Al ' Ameen ? Kafa san halin Dikko kila ma yaje ya kasheshi ya jefar dashi ruwa , tou ni gaskiya bazan daina fushi da tashin hankali ba sai an samomin Al ' Ameen a daren nan.....
Dady bai sake magana ba ya fara kiran wayar Dikko , gaba ɗaya wayoyin a kashe suke , Ashiru ya kira kuma ba tare dashi Dikko ya tafi ba saboda shine yace ya maida Sultana Goruba shi zaije ya dawo sai bata bi Ashiru ba tabi Dikko , cike da girmamawa Ashiru ya ɗauki wayar Dady ya gaishe shi , bayan gaisuwa Dady yace ina Babana ya kai Al ' Ameen ? Har ga Allah Ashiru bai tunanin komai ba yace yana Goruba road , Dady yace ka kawoshi yanzu² , Ashiru yace insha Allah suka ajiye waya ,
Bayan Dady ya gama waya da Ashiru ya kalli Bilki yace tou kinma ji yana Goruba Ashiru zaizo dashi yanzu , murmushin jin daÉ—i tayi ba tare data kalli Dady ba tayi godiya kusa da ita ya zauna................. !!! | cikin "yan mintuna da basu wuce 15 ba Ashiru yakai Al ' Ameen , kuma lafiyarshi garas dan Dikko bai dakeshi ba tunda ya buga mishi kai a bango ya suma bai sakeyi mishi wani abu yana mishi tambayoyi ne kafin ya gama yaci mutuncin shi ,
Momy kuwa tana can sake da baki tana bacci bata san wainar da ake toyawa ba , dan ita ba ma'abociya sa ido bace da sanin halin da wani yake ciki ba , barta dai da zafin kishi taƙalo fitinar da bata garai bata da dalili dan mafaɗaciya ce ta farkon shafi kuma bata san zaman lafiya ko kaɗan , ko shiru taji gidan kwana 2 ba'ayi faɗa ba haka nan zatace ta fita ana mata kallon hadarin kaji haka zata saka Dikko gaba tace anyi mata an matsa mata ita zata kashe auren nan tayi tafiyarta bata zama hawan jini ya kamata idan kuka bari na mutu kun shiga3 kaza² duk dan dai ayi hayaniya , haka zata haukatoshi ya fito yaita cancara ruwan rashin mutunci dan duk yafi kaf "yan uwanshi fitina bai gajiya da faɗa kuma baida haƙuri kamar amai idan ya fara babu kyau , tou bata tsayar da kanta wuri ɗaya ba bare ta gane inda duniya ta dosa.....
Da inda ya ajiye Al ' Ameen ya fara bayan ya dawo daga kano babu shi babu dalilinshi , agogon hannunshi ya kalla 2:15am jinjina kai yayi ya nufi ciki , wayoyinshi ya ɗauka duk ya fitar dasu a jirgi , kai tsaye Umar ya fara kira , cikin yanayin bacci ya ɗauka , bayan ya ɗauka Dikko yace ina Al ' Ameen ? Kallon Al ' Ameen dake kwance kusa dashi yana bacci yayi sannan yace har kin farka kenan ? Dikko yace kai nine ta farka gidan su wa ? Ai na gane ki ranki ya daɗe Baki daɗe da kwanciya ba a kusa dani kikayi mafarki ? Shiru Dikko yayi yana sauraren Umar daya maidashi mace , Umar kuma yaci gaba da cewa ....... A ina kika ga ɗakin ne ? ....... Tou Allah ya ƙarawa mai girma gwamna lafiya da nisan kwana muyi ta zarce muci gaba da zama a gidan gwamnati kuma kema zan kawoki har sai kin kwana kamar yadda nake kwance dani da mai gidana Al ' Ameen a ɗaki ɗaya yana bacci , kashe waya Dikko yayi tou waye ya tafi da Al ' Ameen wato yana can ma yana bacci yasan zan nemeshi shi yasa bai tafi G R A ba ya tafi wurin Umar , tashin Sultana ya farayi , da sauri na buɗe idona a firgice dan mafarki nakeyi da mutumin nan , An mata tashi na dawo lafiya kuma na samo miki magen kamoni yayi yana sauko dani yake cewa muje ki anso fita zanyi , banyi magana ba kafin in saka takalmina har ya fita daga ɗakin ina fitowa harya fice daga palon da sauri , kafin na gangare daga sama har ya sauka , cikin mota na sameshi kwalin da magen take ciki ya miƙomin tare da cewa jeki saina dawo , ajiye kwalin nayi ƙasa zan riƙeshi a kasalance yace yi haƙuri An mata idan kika taɓani yanzu zaki jawo rigima , nidai dan Allah , tou taho ya faɗa yana kamo hannuna ɗan jirgewa nayi na zauna a jikinshi na kwantar da kaina a ƙirjinshi baimin magana kuma bai taɓani ba shi kaɗai yasan ɓacin raan da yakeji a zuciyarshi saida na gaji na tashi da kaina ya ɗauki kwalin ya miƙamin na wuce ciki shi kuma ya fita......
Yau yazo da wani irin ɓacin ran da babu wanda ya taɓa ganinshi a yanayin , yayi ihu yayi hauka yace ana shiga mishi haƙƙi ya daki kanshi da saitin zuciyrashi yace shi ba mahaukaci bane ba , shi Dikko yasan abinda yakeyi ya rantse da girman Allah a tsautsayi wani ya kuskura yazo kusa dashi saiya kashe shi da gaske yake kisa zaiyi zai kashe ko waye ya kuskura yazo inda yake idan kuma mutum ya taɓashi to tabbas ko gawarshi bazatayi kyan gani ba saidai shima ya mutu ya yadda da wannan , idan da wanda ya gaji da rayuwar duniya yazo yau shine zai kashe ko waye idan baiyi kisa yau a gidan nan ba tou wallahi ya yadda shi ba ɗan Babanshi bane ba ina Al ' Ameen ina wanda yaje ya taho dashi waye yasa aka fito dashi ne............ Ya ƙarasa maganar yana buga kafarshi ƙasa da ƙarfi tare dayin wani irin ihu mai tada hankali da gigita , dake dare ne ihun Dikko da hayaniyarshi ya karaɗe kaf ilahirin girman gidan gwamnati ihunshi na yau yafi na kullum tashin hankali dasa ɗimuwa , duk mai imani saida ya tausaya ma Dikko kuma kowa yasan wannan abu badai mutum ba , kowa yayo waje inda yake tsaye yana hayaniya sun zagayeshi amma an rasa waye zai shiga wurinshi , sunan Al ' Ameen ya kira da wata irin murya yace ba duka ba zagi ba harara bare magana mara daɗi ka fito da kafafuwan ka kazo ka shiga mota kafin in irga 10 idan kuma ka bari na fito dakai da kaina saidai uwarka ta sake haifo wani ba kai ba dan zaka shiga 3n ka kuma zaka bani ka lalace , rufe idanuwa yayi cikin rashin mutunci ya fara kiran numbobi One , Two , Three , Four , Five , Six , Ser..... Da gudu Al ' Ameen yazo gabanshi , Momy tace me yayi maka ? Babu ruwanki kuma nayi rantsuwa duk wanda yazo kusa dani saina kashe shi..............
Waye yaje ya ɗauko ka ne ? Ashiru ne Al ' Ameen ya bashi ansa , bai sake magana ba yayi gaba Al ' Ameen yabi bayanshi wurin yayi tsit kamar babu kowa yana fara tafiya suka riƙa darewa suna buɗe hanya har ya wuce , saida Dikko ya fita da Al ' Ameen hayaniya taci gaba tashi kowa yana tausayin rayuwar da ta samu Dikko gashi mahaifiyarshi bata da ragowa bare a fahimtar da ita yadda lalurar ɗanta take bata ajiye komai ba sai girman kai wulaƙanci rashin mutunci da masifa dama marar mutunci haka ake masa ana ganin kuskure babu mai gyara masa saidai a barshi yaje can yaji da halinshi.....
Uwar Jiddah kuwa data biyo Momy cewa tayi Maryam ashe ɗanki mahaukaci ne shi yasa kika maƙale saiya auri Hauwa'u ? { Jiddah } da yanzu tana can ƙasar waje tana aure yanzu haka ma takarar gwamna zai tsaya Dikkon ma har nawa yake ? Aure babu wani ci gaba ita ba ciki ba sai haƙuri irin wannan haukan yayi ya riƙemin ɗiya yaita bugu ita ba ƙato ba ? Kai ׳ gaskiya abun baiyi tsari ba kila ma bugun da yayi mata ne yasa take rashin lafiya gaskiya an shiga haƙƙina kinci amanata wallahi saida Hauwa'u tacemin bata zama kwanaki daya bigeta tace saiya saketa kika shiga kika fita ta haƙura ta zauna ashe zalinta ake ci , Momy tace aini ban iya neman asiri ba ita tayi ma kanta karatun ta natsu ta koma nidai shawara na bata kuma ta ɗauka , Maman Jiddah tace tou wallahi bana lamunta ni ban yadda da auren bugu ba waye ma Dikkon ? Waye shi........ ? Murmushi Momy tayi mai ciwo a zuciyarta tace Dikko kuwa kowa ne dan ba sakarai bane ba yasan damarshi , bata sake magana ba ta kwanta , Maman Jiddah kuma wayarta ta ɗauka ta fara kiran Jiddah tana ci gaba da cewa aure babu wani ci gaba har yanzu ko ciki babu ina ma amfanin rayuwar Dikko ɗan iska kawai daya raina mutane.
Bayan Jiddah ta ɗauka tace Hauwa'u ashe Dikko hauka yake mara ɗaura zani ? Magana Jiddah tayi , mahaifiyarta taci gaba da cewa wallahi nasan ba komai bane sai hassadar ganin zaki ci gaba shi yasa Maryam tasa kika auri Dikko da yanzu kina can ƙasar waje kina huta .......... Eh da kema zaki zama matar gwamna ........ Wallahi hassada ce kawai tunda taga ita "ya "yanta basu auri gwamnoni ba shi yasa tayi zalinci ta haɗa aurenki da mahaukacin ɗanta , haka dai taita maganganu Momy kuma bata ce ummm ummmm ba......
Inda yakai Suwaiba yaje yakai Al ' Ameen , kuma wuri É—aya ya haÉ—asu babu abinda ya dameshi Suwaiba kuwa sai bacci takeyi kamar jakar data kwana tana wahala , saida Dikko yayi ma Al ' Ameen lullusar fitar hayyaci ya É—ora da cewa idan wani ya sake zuwa ya bishi yaga yadda zaibi ta kanshi da mota kuma ya kashe banza , a wahalce Al ' Ameen yace nasan idan ka kashe ni ko bayan bana raye zaka tuno da maganganu na....
3 ta wuce ya koma gida kuma bai sake tashin Sultana ba haka kuma baiyi bacci ba yana zaune a gefen gadon yana nazarin wasu maganganun da sukayi da Al ' Ameen ,
Al ' Ameen miya haɗaka da Jiddah ne ? Wallahi mai gida ba abinda ya haɗani da ita kawai dai tana aike na ne na samo mata asiri tana san ganin bayanka , kamar ya zata ga bayana ? Saboda makirci da sharri irin nashi saiya kawo mishi zanje can baya wanda shi Dikko daga shi sai Allah sai Jiddah suka san wannan sirri na zance sperm , ya akayi maganar yaje wajen Al ' Ameen da wasu zantuka na rayuwar shi da ita a fanni auratayya ? Me yasa Jiddah ta tona mishi asiri ? Me yasa ta faɗeshi a yanayin da duk duniya ko iyayenshi baya fatar su san yana shiga irin wannan yanayin me yasa ׳............... Kai wannan wace irin mace ce ........... ? Hayaniyar shi ta farkar dani daga bacci , takalmin ƙafarshi ya fara cirewa ranshi a matuƙar ɓace kanshi yaji ya yamutsa daya tuno har kwanciyar da yayi a jikin Jiddah da bai sauka ba sai bayan mintuna 20 duk hadashi ta faɗawa Al ' Ameen wani irin ihu Dikko yayi mai tada hankali , da gudu na sauka daga saman gado jikina yana kyarma dan na firgita kuma ban taɓajin irin ihun ba , fashewa nayi da kuka , ke zo ki kwanta mana , maganar shi ta ƙara gigitani dan haka da gudu na fita daga ɗakin ya biyoni yana cewa karki hau bene An mata ki rufamin asiri , tsayawa nayi nace tou me nayi maka ? Da hannunshi biyu yake nunawa na yanayin lallashi bake bace ba yi haƙuri taho ,
A tsoroce naje wurinshi na riƙe hannunshi ina kallon idonshi , murmushin ƙarfin hali yayi tare da cewa wuce muje ciki idan ina ihu ki daina fita da gudu kinji ? Ni bana san ihun tsoro nakeji , kiyi haƙuri na bari bazan ƙara ba An mata , tou ina kakai m card in nan ?
Cikin murya mai kwantar da hankali yace me zakiyi dashi ne ? Wata É—auka da nayi zan goge , dalili ? Nidai ka bani , ni wallahi bansan inda na ajiyeshi ba , wani abu ya faru ne ? Ey , tou meye ne ? Muje É—aki , hannu na yaja muka koma ciki gaba É—ayanmu toilet muka shiga ni na wanke fuskata da bakina na fito , duk daren nan saida Dikko yayi wanka shi bansan abinda yasa ya mada rayuwarshi ta dare ba yanayin abu da dare kamar rana , bayan ya fito ya saka kayan jersey ya É—auki wayarshi ya shiga duniya yace ina saurarenki.....
Gefen gado na zauna shi kuma yana zaune gefen madubi , da farko dai ina baka haƙuri akan maganar da zanyi , baimin magana ba hankalinshi yana kan wayarshi , naci gaba da cewa can² baya na haɗu da wani mutumi muka shiga har ƙallar rayuwa dashi amma babu wani abu daya shiga tsakani , yadda abun ya faru na faɗa masa kaf da zancen maganar recording da nayi masamasa ,
Ranar dana fara ganinshi a bacci da zancen ƙwaƙwale ido da yakeyi kuma yake faɗamin kuma ya zama gaske , ganin Al ' Ameen a baccina ranar dana ga Dikko ya rabu biyu daren ɗaurin aurenmu kenan , yace shine ya turomin tsafinsu a auna nauhin idona saboda naci kuɗin su ban biya da idanuwa na ba za'a ɗauramin aure gobe sai su cire idona , a tsarin tsafinsu basa cin idon wacce babu igiyar aure akanta zanyi aure sai aka zo dubani , shine nayi kuka kake tambayata abinda ya faru , ranar da aka kawoni gidanka a ranar nayi mafarki dashi yacemin ya cire ido saura nawa tunda nayi aure....
Abinda yasa har yanzu basu cire idona ba saboda wannan record in da nayi mashi yana so ya tabbatar babu wata sauran hujja a wurina suna so na basu su goge shi , shin idan na goge ko sun goge zasu fita harkata ko kuwa zasu kaini nima kamar yadda suka kai sauran matar aure ne ? Tsoki Dikko yayi ba tare da kalleni ba ya gyara zaman shi yana cewa ƙarya ne , wannan labari tatsuniya ne , a , a Dikko da gaske ne wallahi , An mata banda ƙaryar bacci to me ya kawo Al ' Ameen a mafarkinki ?
Yacemin Al ' Ameen ya munafurce shi kuma wallahi zai tona masa asiri Al ' Ameen shine jagorar matsalar rayuwarka , duk haukan da kakeyi shine , ni banasan wannan maganar karki sakemin irinta , Dikko wallahi har inda aka binne asirin ya nunamin , cikin hayaniya yace da Allah bana san iskanci in banda iskanci ya za'ayi Al ' Ameen ni yayi min wani abu ? Zan sake magana ya dakamin tsawa yana cewa kwanta kiyi bacci idan na sake jin surutunki saina zaneki , Dik..... Ki rufemin baki karki ɓatamin rai a daren nan............. Ya ƙarasa yana rufe idanuwanshi.
A hankali na koma na kwanta tare da fashewa da kuka nace na rantse da Allah da gaske ne , kuma a ido biyu zan iya gane wurin , ka tsaya na faÉ—a maka abinda yace Al ' Ameen É—in yayi masa mana , ke.................. Ki rufemin baki....... Idan kika sake magana saina kashe ki......
Shiru nayi ban sake ko tari ba nabi shi da kallo , dakamin tsawa yayi cewa daina kallona ki juya can ki kalli bango , banyi magana ba na juya naci gaba kallon bango kamar yadda yace , har aka kira sallah asuba ban sake magana ba kuma ban koma bacci ba saishi dake ta ansa kiran waya , ana kiran sallah asuba kuma ya maida wayar jirgi ya sauya kayan jikinshi zuwa jallabiya ya fita masallaci.
Abinda ya faru a baccina kamar yadda na saba mafarki dashi lokaci bayan lokaci , ina ganinsa a wasu kwanaki na baccina wanda bana iya ganewa ko tuna lokacin da yake zuwa a baccin saboda ba kullum yake zuwa ba kuma ranakun zuwan nashi daban ne ,
Ranar da naga sunayin kokowa da Al ' Ameen , wata ranar kuma da yazo a baccina kamar yadda ya saba yace mi yasa ban goge ba ? Nace masa Dikko bai bani ba , shine yacemin inyi alƙawari na samo mishi record Al ' Ameen yaci amanarshi ya yadda dashi amma ya zalinci rayuwarshi , ga yadda ya faɗamin dai , kuma yace abinda yasa zai tonawa Al ' Ameen asiri yana so Dikko ya ƙoreshi daga ƙasanshi shima saiya tagayyara kamar yadda shi mai ƙwaƙwale idon ya tagayyara.......
Dani da Al ' Ameen dukanmu iyayenmu ne sukayi aiki a gidansu Dikko , mahaifinshi Dikko mutumin kirki ne mutum mai mutunci da mutunta kowa kuma yana da alkairi da san kyautatawa wanda bashi da hali haka kuma bashi da ƙyanƙyamin talakawa , lokacin da iyayenmu suke aiki a gidansu shi mahaifin Dikko lokacin yana da mata 4 cas mahaifiyar Dikko itace babba amma yayi aure² dan samun ɗa namiji ,
Dan ya tashi hankalin rashin samun namiji tun kafin haihuwa tayi nisa , haihuwar Maryam 3 a wancan lokacin kullum mata take haihuwa dan haka kawai Dady yaci gaba da aure saida ya tara huɗu gaba ɗaya , ganin haka yasa ita kuma ta dakata da haihuwa kwata² saboda baƙin ciki da kishi , ta tashi hankalin miji ta hanashi zaman lafiya da kwanciyar hankali dan duk yadda zan kwatanta fitinarta ta zarce wurin , ga rashin san zaman lafiya ga wulaƙanci idan ta fara fitina babu wanda ya iya yasa tayi shiru , dan haka itace ta ɓata kaf gidan ya haukace aka shiga sahun kishi da jefe²n juna , a lokacin da take ita ɗaya bata san "yan uwan Dady dan ita Allah yayi mata tsantsani da ƙyanƙyami idan dai ku masu kuɗi ne ko "yan gayu tou kune abokan tafiyarta dan ita "yar gayu ce ajin farko da ƙarshe bata tarayya da mutumin data fi wayewa cewa takeyi zai kidahumar da ita , tasan hannunta kuma tasan abinda take dan duk matan da Dady ya auro babu kamar ta , ga kyau ga gayu ga aji idan ta raina ka ko ƙofar ɗakinta baka taka mata bata da mutunci yadda baki tunani , idan tana sanka kawai tana sanka idan bata sanka bata sanka........
Itace babba kuma itace ta ɓata gidan , ita bata iya neman asiri ba amma tasan logo da kissa na duƙunƙune kan namiji shi yasa Dady ya fifita ta akan kowa sai suke ganin kamar asiri take masa dan haka suka tisota gaba jifa , nan fa gasar haihu ya tashi dan haka akaci gaba da watso ma Dady "ya "ya mata , ganin buƙatarshi bata biya ba ya fara tarawa da ebewa , amma ita Maryam duk rashin kunyarta ba'a taɓa jaraba mata bulalar saki ba.
Ganin ana haihuwa yasa itama taci gaba da haihuwa , tana komawa haihuwa Allah ya bata Dikko , tunda ta haifi Dikko su kuma suka tasashi gaba yadda basu haifa ba babu wacce ta isa itama tayi namiji sun yadda su kashe shi a tashi a tutar babu...
A kanshi aka samu namiji kuma har yau ba'a sake samu ba , bayan Dikko ya girma kuma aka riƙa harin rayuwarshi a waje idan ya fita shine dalilin da yasa aka haɗashi dasu Ashiru , shi kuma Al ' Ameen da ƙarfin bala'e ya shiga ya fita yake tuƙa Dikko kuma bansan abinda ya rabasu ba a halin yanzu amma dai nasan basu tare ya koma tafiya da zugar yaranshi.
Abinda yayi min shine , dani dashi gaba ɗayanmu munyi aure wurin zama da duk hidimar da kika sani anayi a aure Dikko ne yayi mana gaba ɗayanmu , tunda nayi aure na fita daga ƙarƙashin shi domin a lokacin Al ' Ameen ya zuƙeni daga jikin mai gida , amma duk da haka na yadda da Al ' Ameen sosai ganin iyayena da nashi sun tashi wurin aiki ɗaya kuma gaba ɗayanmu a gidan muke zaune , na yadda da Al ' Ameen jinsa nake kamar a ciki ɗaya muka fita , ashe ni mugunta ta yakeyi mugune azzalimi ne ya yaudareni anan inda nake tsaye a nan aka binne sihirin da akayi ma mai gida , abinda yayi min shine zaici gaba da faɗamin ne Dikko ya tasheni yacemin wai in tashi ya dawo , tabbas zan gane wurin amma ta ina zanbi inje wurin ? Ina Dikko ya ajiye m card in nan wai ? Har ya dawo daga masallaci ban tashi ba a yadda ya barni ba , kuma banyi sallah ba , cire jallabiyar shi yayi ya maida kayan daya cire ya kwanta.
Shin wai wannan mafarkin da gaske ne ko kuwa tatsuniya ne kamar yadda Dikko yace , tashi nayi naje nayi alwallah nazo na kabbara sallah , shi kuma Dikko bayan ya kwanta yana tunanin maganar Sultana da zancen Sadiyya sai kuma maganar Suwaiba da tace masa ya tattaro kaf yaranshi duk wanda yasan ya taɓa zama a ƙasanshi ko basa tare yazo dashi , ita kuma Sadiyya tace masa a cikin yaranshi wanda ya kasheta yake , An mata kuma tace masa Al ' Ameen , shin wai me ye gaskiyar lamarin nan ,
Gaishe shi nayi bayan na gama sallah , bai ansa gaisuwar ba kuma bai kalleni ba , nima ban sake gaishe shi ba nayi kwanciyata a wurin , bayan wani lokaci yayi tsoki tare da saukowa daga saman gadon , canja kaya yayi ya É—auki makulin mota ya fita , tashi nayi na koma saman gadon ina cewa aikin banza adashen tusa.....
Kai tsaye wurin da ya ajiye Suwaiba da Al ' Ameen ya nufa.........
04/12/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 86
Ya za'ayi Al ' Ameen ni yayi min wani abu ? Tou me mutumin ya faɗa mata ? Ina yasan Al ' Ameen ? Me yasa ni kuma Al ' Ameen zai zama jagorar matsalata ne bayan dashi ake nemamin magani , mi yasa dole sa a mafarki zai bawa An mata labari ? Ƙarar wayarshi ya dakatar dashi daga tunanin daya tafi , Momy ya faɗa tare da ɗaukar wayar suka gaisa , Dikko kana ina ne ? Ina nan bisa titi , ina zakaje a safiyar nan ne ? Zanje gida , wane gidan ? G R A , daga ina kake ne ? Goruba , daina tambayar tayi cewa Dikko kazo ina neman ka yanzu²n nan , cike da damuwa yace me kuma akayi miki ne ? Dikko nidai tafiyata zanyi na gaji da zaman haƙuri , kuma fa bata iya tafiya ko ina ta bar Dady , Momy kiyi haƙuri dan Allah,
Ni bazanyi ba , tunda ka tafi da Al ' Ameen jiya Bilki ta hana gidan nan zaman lafiya ta turo "ya "yanta sai rashin kunya sukemin dan taga ba kowa cikin yara duk su Nabeela suna wurin Jiddah ko nice zan fita inyi faɗa da Yara ne ? Nidai nasan nafi ƙarfin Bilki daga ciki har waje wani iskanci saida tasa yara suyishi , cike da damuwa Dikko yace Momy dan girman Allah kiyi haƙuri , wallahi bazanyi ba saidai idan Bilki ta koma uwarka sai in ƙaleka dama kwanaki dana faɗa maka ta zageni kace zakayi mata magana bakayi mata ba sakaran banza mara kishin uwarshi tana faɗin haka ta tsinke kiran.
Innalillahi wa'inna ilahir raji'un ya faɗa tare da samun gefen titi yayi parking , wayar Ashiru ya fara kira , Ashiru kuwa yanaji yana gani yaƙi ɗauka dan Umar ya bashi labarin abinda mai gida yayi a jiya kuma dama yasan tunda ya ɗauko Al ' Ameen saiya fuskanci matsala tou shi ya za'ayi ma yace ma Dady baisan inda Al ' Ameen yake ba taya zaice kuma bazai ɗauko shi ba ?
Yana ajiye wayar zai tashi motar text in Ashiru ya shigo , kayi haƙuri mai gida Dady yasa na ɗaukoshi kuma na kira wayarka a kashe ka gafarceni nasan ban kyauta ba , tsoki Dikko yayi tare da ajiye wayar saida ya fara tafiya ya fara kiran wayar Dady.
Cike da fargaba ya ɗauki wayar yace Babana lafiya ? Dan shi a tunanin Dady ba lafiya shi yasa Dikko ya kirashi a safiyar nan , Dady wai me nayi maka ne ? Babana ba komai , tou me yasa za'a hanani na zauna lafiya ne ? Da sauri Dady ya tashi daga kwanciyar da yake yace me akayi maka ne ? Horn Dikko ya danne ɓiyyyyy , Dady yace a , a Babana , Dady kawai zan mutu na huta , yi haƙuri Babana² dan Allah tashi tsaye Dady yayi cikin tashin hankali yace wai ina damuwar take ne ? Me yasa kasa aka taho da Al ' Ameen ne ? Yadda sukayi da Bilki ya faɗa masa , kashe waya Dikko yayo bai sake magana ba ya ajiye a gefe , me ne ne tsakanin Al ' Ameen da matar uba wai ?
Ko dan yace zaice ya kama Al ' Ameen a ɗakinta ne ? Tou kodai ? Karka yi zargi zuciyarshi ta faɗa masa , to me ya shafeta da lamarin Al ' Ameen haka da yawa ? Dama kwanaki daya dokeshi itace tayi video ta turawa Dady , yanzu kuma shine tasa akaje aka taho dashi ko ? Maganar Sadiyya ta dawo mishi a zuciyarshi an haɗa kai dashi da matan uba an maidakai lusarin namiji , ni kuma yayi nasara akaina yakai min rayuwata ƙarshe , ka tattaro kaf yaranka har wanda suka daina maka aiki ka kawosu idan na ganshi zan ganeshi { Suwaiba } , wallahi mai gida ba abinda ya haɗani da ita kawai dai tana aike na ne na samo mata asiri tana san ganin bayanka , { Al ' Ameen } , a , a Dikko da gaske ne wallahi , { An mata } , banda ƙaryar bacci to me ya kawo Al ' Ameen a mafarkinki ? Dady kuwa sai kiran wayar Dikko yakeyi amma yaƙi ɗauka dan haka ya kira Momy yace mata yasan itace ta ɓatawa Babanshi rai har so nawa yace su daina saka "ya "ya a damuwarsu basa bari , me yasa suke san ɓata mishi gida ? Kullum yana ƙoƙarin haɗawa su kuma suna rusawa ? Wai me yasa sukeyin abu na rashin tunani haka ? Tou wallahi tayi kuka da kanta dan zai mata rashin mutunci idan wani abu ya sami Babanshi.
Da wani irin ihu ya shiga inda ƙannen shi suke kaf dan duk irin wannan lokacin basa bacci zasu zauna sai bayan 6:45 su tashi idan da makaranta kenan haka wannan tsarin yake ko bakya sallah duk idan akayi sallah kaf "yan gidan sai sun haɗu a wurin amma "ya "ya ƙananansu da manyansu idan dai ɗan da Dady ya haifa ne harshi Dikkon , kuma ko aure kikayi idan dai kika zo gida sai kinyi wannan zaman tunin duniya haka suke haɗuwa kuma ba addu'a akeyi ba , ba karatu akeyi ba zasu haɗu dai kawai su zauna a wurin suyi fira ne , idan kuma ranar da babu makaranta sai 7 suke tashi , saida ya zane kowa a cikinsu duka bana wasa ba amma ƙannenshi bai daki yayyenshi ba kuma babu wanda baiji ma ciwo a cikinsu ba ya ɗora da cewa daga yau idan wata ta sake shiga cikin faɗan iyaye saiyabi ta kanta da mota ya wuce "yan iska marasa kunya , dakel aka fito dashi daga wurin yana cewa suma su Nabeelar duk saiya ci mutuncinsu wallahi ba babba ba yaro duk wani ɗan daya sake shigar ma uwarshi faɗa a gidan nan shine zan kawo ƙarshen rayuwarshi............
Sai kuka sukeyi , shi kuma ƙwacewa yayi ya nufi ɗakinsu , a falo ya samu Momy ta kashe saman kujera ta murza wani irin ɗaurin kallabi mai burgewa dan fita zatayi zuwa wurin Dady parking in da Dikko yayi yasa ta koma ta zauna tana ta gunewa , kusa da ita ya zauna ya riƙe duka hannayenta yace Momy dan Allah ki daina damuwa , nuna kanshi yayi da hannu ɗaya ɗayan kuma yana riƙe da hannuwanta yaci gaba da cewa idan ina nunfashi babu wanda zai isa yasa miki damuwa kuma babu inda zakije mu muna tare dake nima ina tare dake Mamana Dady nawa ne shima yana tare da duk abinda nake so kiyi haƙuri baza a sake miki abinda zaisa kiji damuwa ba , cikin sanyin murya tace Dikko ya za'ayi yara su riƙamin rashin kunya idan nayi magana sai ace banda haƙuri , ba tun jiya na faɗawa Dadyn naku ba yace wai bana san zaman lafiya , yi haƙuri Momy fushi yasa ya faɗi haka , me yasa baiyi fushi ya faɗawa Bilki ba saini mareniyar wayanshi ɓacin rai yasa Momy taita maganganu Dikko dai tsareta yayi da ido bai sake magana ba , wato ita dai mace duk shekarunta idan tayi wani abun saidai ace Allah ya sawaƙe ,
A mota ya ɗauketa suka tafi wurin Dady , shima ranshi yayi mishi zafi sai faɗa yakeyi yana kuma ƙara ɗora laifin a wurin Momy itace ta fara koyawa yaranta rashin mutunci kuma ai itace ta fara nuna rashin san zaman lafiya a matsayinta na babba , murmushin ƙasaita tayi tace ma Dikko yaje ya jirata falonta tana zuwa , saida ya gaisa da ya fita , Dady kuwa yabi Dikko da kallon soyayya harya fita , ×××××××.
Tunda Dikko ya fita Hafsa ke kiran wayata naƙi ɗauka ta dameni sosai dan haka na ɗauka bayan mun gaisa tacemin wai na fasa zuwa ne ? Ina ne na fasa zuwa ? DK bai faɗa miki rasuwa ba ? Waye ya rasu ne ? Kakar Babanku duk "yan gidanku suna can yau ake addu'ar 3 muma yau zamuje , wace ce kuma Kakar Babanmu ? Wacce ta haifi Maman Babanku , ke ina kika santa ne ? Kaka Sahura ta faɗa man inda take ni naje na gano wurin nakai "yan gidanku , ranar da mukaje na dawo na barosu can a ranar ta rasu , dan lokacin da zamu tafi na kiraki DK ya ɗauka yace baki lafiya sai muka tafi data rasu kuma na kirashi yace idan kin samu sauƙi zai kawoki , tou Allah ya jiƙanta na faɗa a tsiwace , dan Allah kiyi ƙoƙari kuje yau kuma duk "yan uwa sun haɗu kiga dangi kema , shi yasan wurin ne ? Ey nayi masa kwatance ranar dana kirashi na faɗa masa rasuwar , { wato ranar da aka sallamoni daga asibiti kenan } tou me yasa bai faɗamin ba , zan gani ina faɗin haka na tsinke kiran ,
Gaskiya fa ya kamata naje ko dan nuna soyayya wa kabarin Babana , Allah ya jiƙanka Babana yasa ka huta nayi rashin ka a duniyar nan shi kenan ka tafi inda bazan sake ganinka ba har abadan duniya , ka tafi tafiyar da babu dawowa shikenan ka tafi ka barni........, dole naje wurin ahalinka ko dan jaddada soyayya a gareka Baba na gari , kai sarkin fushi zakaje ko bazaka ba ne ni naje ? A dai² lokacin dana fara kiranshi , saida ta tsinke bai ɗauka ba , sake kiranshi nayi itama saida ta kusa tsinkewa ya ɗauka da abinda bana so wai ya akayi ne ? Dikko koma ya akayi ai zakaji yanzu , dan yadda akayin ne yasa na kiraka , ke karki min rashin kunya kinji , ba wannan ba ni zakaje ko ka fasa zuwa ne ? Ina ? Ba Hafsa ta faɗa maka rasuwa ba shine sai kace saina samu sauƙi bayan ni lafiyata qalau , ni bazanje ba sai kin dawo , tou babu damuwa ngode , ina faɗin haka na tsinke kiran , wayar Inna na kira , cikin hukuncin ubangiji kuma ta shiga amma bata ɗauka ba , ci gaba nayi da kira taƙi ɗauka ,
Dikko na sake kira , bayan ya ɗauka yace ya akayi ne ? Dikko na kira Inna kuma ta shiga amma bata ɗauka ba , da kyau , daga haka bai sake cewa wani abu ba , kaji , naji , tou kace wani abu mana , ai shine nace nace hakan da kyau , nidai baka so na , baka damuwa da abinda yake damuna , ni bansan abinda yasa kake min haka ba na faɗa cikin hayaniya ina kuka , duk saida na safke mai isata sannan yace tou yi haƙuri An mata gani nan zuwa zan miki abinda kike so , tou me yasa ni kake min haka ko ka daina so na ne ? Ina sanki mana tayama zaki fara wannan tunanin ? Bana fata kuma bana tunanin akwai ranar da zanji sanki ya ragu a zuciyata , kiyi haƙuri ki bini da addu'a har ubangiji ya yaye min damuwata dana tuno da abinda yake damuna sai inji raina yana ɓaci shi yasa a ko wane lokaci nake miki magana hayaniya² , kana ina yanzu ? Ina nan inajiran Momy data sallameni zanzo wurinki ai haka yayi miki ko ? Ey , to baki ce kin gode ba , murmushi nayi tare da cewa godiya nake mutumina , yawwa jarumata ngode yana faɗin haka ya tsinke kiran , bin wayarshi yayi da kallo yace mata kenan , ita ba abinda ya dameta shin ina lafiya ? Ko ina cikin yanayin fushi me ya sameni bayan na fito babu ya hanya ba komai itadai burinta ayi mata dai² , zan faɗa mata ba'a kiran miji kai tsaye a faɗa masa damuwa sai an tabbatar da yana cikin natsuwa.
Momy ta daɗe bata dawo ba , har Ashiru ya iso gidan danshi zai maida Maman Jiddah tunda Al ' Ameen bashi nan kuma tsarin nan Momy ce ta tsarashi shi kwata² Ashiru baisan Dikko yana nan ba , ita kuma Maman Jiddah tana gama shirinta ta fito falo dan Momy tayi mata waya cewa wanda zai kaita ya iso itama tana zuwa yanzu , shine tayo parking ta bayyana a falon , cikin girmamawa da mutuntawa Dikko ya gaishe da surukarshi....
Ba yabo ba fallasa ta ansa tana ta riƙe fuska , ko inda take bai sake kallo ba , ita kuma taci gaba da cunkusawa cikinta abinda ta samu an ajiye mata dan karin safe tunda zata ibi hanya ko kunyar sarakuta babu , Dikko kuma fita yayi ya koma mota yana jiran Momy , yana zama yaga Ashiru yasha ta baya da gudu , tsoki yayi tare da kallon agogon jikin waya 8:39am kuma har yanzu Momy bata fito ba shawara ya yanke kawai ya fara ganin Jiddah kuma suma su Nabeela ya zanesu kamar yadda ya zane "yan uwansu zaije ya dawo kafin ta gama ta fito , tashin mota yayi ya nufi gidanshi....
Yana fita Momy ta iso taga babu Dikko kawai ya wani ɓace abunshi , Momy kuwa tana shiga wuri ta samu ta zauna tana ma "yar uwarta magana , amma ke dake gidanki idan kin tanka tou Maman Jiddah tayi magana sai wani cika take tana batsewa , Momy taji ba daɗi amma ta haƙura ta kanne dan abu na "yan uwan taka dole sai an haɗa da haƙuri da kuma kai zuciya nesa , data tashi tafiya duk abinda Momy ta bata cewa tayi ita ba baƙuwar arziƙi bace ba tafi ƙarfin ita ta bata wani abu ta ansa ta riƙe kila zasuyi mata amfani wurin nemawa Dikko rubutun danga na , Momy tace wane irin rubutun dangana kuma ? Maryam gaskiya ni na kashe wannan auren , cikin tashin hankali Momy tace Yaya don girman Allah kiyi haƙuri wai miye matsalar ne ? Kuɗi , banbancin kuɗi ne ke naki ɗan gwamna ne ni kuma gwamnan zata aura gaba ɗaya , zaɓe yana tunkarowa bana tunanin ku zaku sake zarcewa siyasa zata wurgar daku a can tsohon gidanku gidan gwamnati kuwa zai zama na masu rabo ,
Momy tace mu kenan masu rabo ni inaji a jikina munci kuma sai mun sake wannan zaman darajar manzan Allah S. A. W gidan gwamnati sai mun maimaitashi , maganar kuɗi kuma ba damuwar Dikko bane ba saboda shi basu ne gaban shi ba yana dasu yadda tunaninki da ƙwalwarki basu ɗaukar misali dan dayabi izzar kuɗi da mulki wallahi Jiddah bata kai mace ba a wurinshi , Maman Jiddah tace aiko ke kinsan Jiddah mace ce hada gyara gwamna da kanshi yake santa gwamna fa ? Shin ke kin raina gwamnati ko ? Ban raina gwamnati ba amma nima na san nawan tunda ya fara saiya taka matakin da bakya tunani , da haukan zai taka matakin da har ni bana tunani ? Momy tace ba mahaukaci kuma ba hauka Dikko duniya , zamani ɗaya tak a ƙarni matashi mai sa'ar rayuwa , yaro da kuɗi abokin tafiyar manya , mahaukaci da kuɗi kuma mai maihankali babu , gwamnan da kike tunanin kashe auren Jiddah saboda shi tun kafin na ganshi nasan waye shi na tabbata duk kuɗinshi shi 30 baya Dikko ɗaya , yadda baki tunani Dikko ya kafu shi kanshi ubanshi alfahari yakeyi dashi yace yasan ko bayan baya raye zai tallafi "yan uwanshi shi yasa ya dage saida ya tabbatar ya gina Dikko sosai , amma duk da haka shi kuɗi basu ne gabanshi ba shi yasa yake rabar dasu kamar hauka , abinda yasa na kafe sai Dikko ya auri Jiddah dan naga wasu sunci ma bare nawa bana san ya baku² shi yasa na haɗa auren Jiddah dashi , dan nasan Dikko bashi da mutunci idan nice yau gobe bana nan na gina ku ne ku "yan uwana ko bayan bana raye arziƙin Dikko bazai muku wahalar ci ba saboda akwai Jiddah , amma idan har kika kashe auren nan kuka bar bare kuka hana zuminci wallahi gidan Dikko raɓe zaku zama , kuna iya zuwa ma tace muku baya nan kuma yana nan ta hanaku ganinshi , kallon banza ko magana mara daɗi kukayi ma matarshi tabbas nasan saiya ya taka muku burki ko kuma ya ɗauki matakin hanaku zuwa gidanshi ba abu bane mai wahala a wurinshi , ni bana miki hassada kuma bana miki baƙin ciki dan "yarki zata zama matar gwamna shawara na baki dai dan kece ya kamata tun yanzu ki daina tunanin kashe auren , a sanyaye tace kuma kece zaki anshi kuɗin nan ki fara nemawa "yarki rubutun dangana tun yanzu , ɗa ɗaya tak ragamar mata idan dai harya kafa soyayyarshi a zuciyar Jiddah tou sorryn ku ina jajanta muku domin ni kaina bansan a ina Dikko ya gaji zuciya ba , da zaran ya yanke hukunci tou fa ko kanshi baya saurara , karki raba domin yadda mukayi zaman nan zamu sake maimaitashi idan har kika tafi da Jiddah wallahi kuma Dikko yasan dalili tou fa tabbas yadda kika ga kiyi sabon rubutu a saman allo bai bushe ba ki tsomashi ruwa ba tare da kin murza ba rubutun zai sauka to haka Jiddah zata wanke a cikin zuciyarshi ko matalwa batayi , shawara ya rage naki neman rubutun dangana da mafita yana wurinki.....
Tana faɗin haka ta wuce ciki abunta , Maman Jiddah kuwa fita tayi dan Ashiru ya fitar da duk wani abu nata , haka ta fita waje taita tata ruwan rashin mutunci wai Maryam tana mata hassada mai takarar gwamna yana san "yarta take jin zafi , kurar Momy ta riga tayi kuka shi yasa kowa yake ganin Momy bata kyauta ba abu har ga "yan uwanta ashe ba'a kishi ba har "yan uwanta bata raga musu ba , saida ta gaji da tonon sililinta tayi ta tona musu asiri dan wasu basu iya riƙe ɓacin rai ba idan suna fushi sai su manta da abinda gaba zaiyi su kulle idanuwa suyi ta wulaƙanci na rashin lissafi , ko a mota haka ta ci gaba wulaƙanci su "yan gadon rashin mutunci , duk yadda Ashiru yaso ya nuna mata waye Dikko idonta ya rufe ita mai takarar gwamna kawai kuma saita kashe auren , da ɓacin rai suka isa G R A lokacin Dikko harya zane su Nabeela suma ya farfasa musu jiki ya wuce wurinsu Al ' Ameen.
Haka ta tisa ƙeyar Jiddah hada Mardiyya suka kama hanyar Kaduna , Dikko baisan wainar da ake toyawa ba , Momy kuwa tayi kukan baƙin ciki bata nunanin idan bata raye wannan karuwar zata bar Dikko yayi zuminci da "yan uwanshi , dole a sake nema ma Dikko wani auren a cikin familyn Dadynshi......
Lokacin da Dikko ya isa Al ' Ameen ya dawo kuma ya shaƙe Suwaiba tana ta halbe²n mutuwa , halbi ɗaya Dikko yayi mishi a haƙarƙari ya sake somewa , dakel Suwaiba ta nuna Al ' Ameen tace shine , idan baka yadda ba kuma ka tambayi Mustapha zai maka bayanin komai , wane Mustapha ? Mustaphan daka sani kuma saida ya zalinceshi ya munafurce shi yaci zalinshi sos.... Daga haka ta ɗauke Dikko yasa aka tafi da ita asibiti kuma a tsareta , Al ' Ameen kuma bazai dakeshi ba saiya dawo.....
Saida ya sake komawa ta gidansu ya tafi da abinda zasuyi kalaci kuma baije wurin Momy ba , sai 10:15am ya isa gida , lokacin harna shirya , bafa inda zakije yarinya , haba ? Ummm , to me yasa ? Bai sake magana ya zauna a gefen gado sannan yace An mata wai me mutumin cikin bacci yake ce miki ne ? Nima bana san wannan tatsuniyar , to wane iri ne ? Na manta , ke.............. Bana san iskanci ni zaki faɗamin kin manta................. Cikin ɗaga murya da hayaniya ya faɗa , a tsorace nace kamarshi biyu ce duk na faɗa masa sifofinshi dana sani , tashi yayi tare da kwantar dani saman gado yace me yace miki Al ' Ameen yayi mishi ne ? Bai faɗamin ba ka tashe ni daga bacci , danne ni yayi ta ƙarfi yace koma bacci ki tambayoshi abinda Al ' Ameen yayi mishi.................. , kyarma jikina ya farayi cikin kuka nace ai bazaizo ba ranakun zuwanshi daban ne a sati sau biyu yake zuwamin kuma ni bansan wace rana da wace rana bace ba , ke............... Kiyi bacci ko in kashe ki........ Fashewa nayi da kuka nace Dikko ka ƙyaleni don Allah , zaro ido yayi cikin ɓacin rai yace bazan ƙyaleki ba aradu sai kinyi bacci.
Dikko dan Allah , An mata dan Allah , mintuna 30 na baki kiyi bacci kizomin da duk wannan ansoshin , me yasa baya zuwa sai a bacci ? Me yasa baizo wurina ba sai wurinki ? Me Al ' Ameen yayi mishi zai tona masa asiri ? Me yasa yake san ki goge recording ? Me yasa yake kwakwale ido ? Me yasa basu cire naki ba ya kuma nuna miki hanya ta yadda zaki gane zuwa inda kika ce sun binne tsafinsu , me ne ne tsakanin Al ' Ameen da Aunty a cikin mintuna 30 idan kuma kika tashi babu wani bayani zan kashe ki kema kin zama munafukata kenan gawarki zan jefar da ita a cikin ruwa kadojina su cinyeki banza kawai dake , kafin in irga 10 kinyi bacci kafin na irga 200 kin tashi kuma zaki bani ansar duk wannan tambayoyin dana aikeki a wurinshi ki samomin......
Fara kiran nombobi ya farayi tuni har na saki fitsari dan nasan wallahi bazai zo ba , wani irin firgitaccen mari ya yankamin har kin isa kiyimin fitsari a saman gado ? Ni zaki ɓatawa ɗaki ? Da duka hannayena na riƙe kumatuna na runtse idona dan bana san kallon Dikko a irin wannan yanayin , shaƙemin wuya yayi yace me yasa kikayi min fitsari a saman gado ? Saina kashe ki na gano ki kema munafuka ta ce ashe , dama kince min saikin ɗauki fansa akaina shine kika zubar da ciki dama ko ? Duk yana cikin ɗaukar fansa , zuwa wurin Yazeed shima ɗaukar fansa ne , yanzu kuma kin ɗaukeni mahaukaci dake za'a haɗa kai ayi min asiri shine zaki rainamin wayau wai a cikin bacci kike gani dan kin ɗaukeni kidahumi ko ? Tou saina kashe ki..............
Ihu na farayi amma ya riƙemin maƙoshi na fara kakari ina halbe² Dikko yana cewa saina kashe ki tunda kema munafuka ce na tsaneki Sultanar banza Sultanar wofi , faɗowa nayi daga saman gado ni na rigashi zuwa ƙasa daga saman gadon ya ziro hannunshi ya riƙeni Allah ya bani sa'a na tashi da gudu nayi waje ya biyoni yana ihu mai tada hankali , sulɓewa nayi a ƙofar fita falo , wata irin zamiya ya kawo ya riƙeni na tashi da gudu , wuƙa ya ɗauka a saman firij ya jefeni da ita saida ta caki bayana ta sauka ƙasa , hannuna na miƙa ta baya na riƙe wurin , da gudu na gangare falon ƙasa kamar biri ya sauko ta sama ya rigani bayyana a cikin palon , sai ihu yakeyi yana faɗin saina kashe ki........... Da gudu na koma sama ya sake biyoni yana cewa bana sanki na tsaneki kuma saina kashe ki , tunanin yadda zanyi na fita na rufeshi nakeyi dan idan harna fita waje haka zai bini yana ihu , tausayin Dikko ya kamani sosai kuma na rasa yadda zanyi na fita dan ta ko ina ya riƙe hanya , tsayawa nayi tare da durƙusawa na duƙar da kaina ƙasa na rufe idona cikin kuka nace tou gani na tsaya idan dai har mutuwata zaisa kayi farin ciki na baka fansar raina ka kashe ni ,
Wani irin halbi yakai min saida nayi baya suuuuuu nayi ƙundunbala ina birkitowa na tashi da gudu ashe dai da gasken kashe ni zaiyi , saman benen na koma nace zan faɗa in mutu , ai nine zan jefaki da kaina , da gudu na sauka nayi waje kafin yazo naja ƙofar kai............. Saina kashe kaina , nidai bansan yadda akayi ba daga haka........
Fashewa Sultana tayi da wani irin kuka mai tada hankali da gudu mahaifiyarta ta shigo tace kin fara ibadar taki ko ? Cikin kuka tace har abadan duniya bazan daina kukan rashin Dikko ba , ina sanshi ׳ ina ƙaunarka mutumina , saida tasha ihunta harta gode Allah sannan tace Dikko zamani mai zaman kanshi inji Inna , ɗan gayun namiji wayayye ajin farko , mai buɗewar ido da gogewar rayuwa , bazan gaji ba kuma baxan daina kukan rabuwa dakai ba har abadan duniya , saida ta samu natsuwa nace tou ina Jiddah take......... ? Ina Al ' Ameen ? Ina Bello ina Dady ina su Amisty ina labarin sahura , kinyi karatun boko ko kuwa a , a , kin haihu da Dikko ko ah ah ? Dan naji a labarin naki baki min zancen karatu da haihu ba , da kika gudu kika zo gidanku "yan gidan su Dikko sunzo ko kuwa........? Ina Suwaiba ? Ina matar da Mami ta haɗaki da ita wacce ta bawa Suwaiba kwalba ? Ina Mardiyya ? Ina Alajinki ? Ina mutumin dake ƙwaƙwale ido ? An cire asirin ko a , a , Goge hawaye Sultana tayi sannan taci gaba da cewa........
*JAMILA MUSA...*
Mai karatu ina fatan dai ka gane ? Domin farkon labarin zaku kamoshi idan kuka duba ai kunga labari ne bani ce nake faÉ—a muku ba Sultana ce take bada labarin rayuwatar da Dikko ne , Allah dai yasa kun gane.......
*SULTANA....*
Maman Jiddah suna isa Kaduna da asibiti suka fara saida aka wanke cikin Jiddah tas dan tana ɗauke da ƙaramin cikin Dikko wata3 , Maman Jiddah kuwa bayan ta tabbatar da ciki ya fita ta buga waya ta faɗawa Momy ta zubar da cikin dake jikin Jiddah , hankalin Momy idan yayi dubu ya tashi tayi kuka kamar zatayi hauka taso ace ko cikin ta bari dan idan ka haihu da namiji duk matsayin da yakai da matakin daya taka idan dai kuna da zuri'a ka more mishi , dan duk ranar da aka wayi gari idan Dikko ya ida kicimewa tace ta auri Dikko saima an bata kashin bala'e dan tace tanaji a jikinta Dikko wani babban sa'a ne kuma shi ɗin hatimin nasara ne , idan ta bar cikin ta haihu itace haihuwar zatayi ma rana ba Dikko ba , amma abinda ya faru ya riga da ya faru ,
Dikko kuwa data faÉ—a masa bai jahilci lamarin ba cewa yayi Allah yasa hakan da tayi shine alkairi a rayuwarshi , kuma ta faÉ—a masa Maman Jiddah ta tafi da ita akan zata kashe auren shi ta aura mata mai takarar gwamna yace ai wannan ba komai bane ba , idan ita rabonshi ce dasu sake zama idan kuma babu rabo shikenan kawai.
Bayan wani lokaci kuma Maman Jiddah tazo tayi wulaƙancin na ƙarshe saida ta zazzage auren Jiddah hankalinta ya kwanta , da Momy ta kira Dikko akan ya saki Jiddah cewa yayi ai itace ta auro Jiddah , sai kuma ya saketa tazo daga baya idan wani abu ya haɗota da "yan uwanta tace shine yaje ya saketa , ya yadda zai saki Jiddah amma rubutunta ya zama a sama zai saka hannunshi daga ƙasa....
Momy itace ta rubuta saki3 kai tsaye ba tare da tunanin komai ba , ta kuma ɗora da cewa saboda Maman Jiddah ta buƙaci sakin Jiddaah dan zata aura mata mai takarar gwamna , bayan ta gama ta miƙawa Dikko ya saka hannu tare da rubutawa.
_Ni Dikko Umar Dikko na saki matata Jiddah saki 3 , ina mata addu'a Allah ya bata miji na gari wanda yafi ni...._
Tunda Jiddah taga takaddar saki tayi kuka , kamar ranta zai fita dan ita kwata² bata san haka za'ayi ba , uwarta ke cin kuɗin mai takara kuma itace ta tabbatar mishi da zata kaso auren Jiddah ta bashi ita , ita dai Jiddah tasan tana sanshi a da amma tunda aka zo da zance Dikko ta jingineshi a site , bayan auren Jiddah da Dikko ita kuma Maman Jiddah taci gaba da cin kuɗinshi akan zata bashi auren Jiddah ta ci gaba da aske mishi aljihu ta kuma tabbatar mishi da saita kaso auren Jiddah ta bashi ita , shi kuma yaji baƙin cikin kasashi Jiddah da akayi dan haka ya buɗe bakin A T M ya riƙa yayyafa mata ruwan kuɗin , saida aka kaso auren yace baya aurenta shima idan ta ga wani haka zata kashe nashi ta bashi aurenta , kuma ya ƙara da cewa shi babu wata takarar gwamna daya fito yayi haka ne kawai saboda yaga ita mayyar duniya ce ,
Ita kuwa Jiddah haka tayi ta guduwa tana zuwa wurin Dikko kuma haka take tarashi a Abuja , shine ya taka mata burki yace ta daina binshi karta ja mishi sharri , taƙiji taci gaba da binshi yace tou duk ranar daya sake ganinta wurinshi zai kashe ta ne kawai kuma ya kashe banza......
Mardiyya kuwa tana tare da Jiddah amma ba'a gidansu ba itama ta koma gidansu da zama amma suna ƙulle dai tunda ana gari ɗaya , Mardiyya itace take raka Jiddah wurin boka ana ci gaba da neman asiri akan Dikko ya shiga tashin hankali yaji idan baiga Jiddah ba yaji kamar zai mutuwa , idan ta haɗo tsibbunta haka zata zo wurin Momy idan taji Dikko yana gari aita barbaɗe² , Momy kuwa bataji wani komai ba dan ita Allah yasa tana san "yan uwanta , Dikko kuwa ko a ƙwalar rigarshi , itama dai Mardiyya tana ta ƙara gyara nata ƙaimun , amma har yanzu kamar suna tura agwagwa ruwa ne dan Dikko bayajinsu wannan jagwalgwalon sihirin nasu bai zo ba ,
Banda labarin Al ' Ameen haka kuma banda labarin Suwaiba kowa banda labarinshi dan a gidanmu nayi haihuwar farko , na haifi namiji kuma "yan gidansu Dikko sunajin labarin haihuwa suka zo suka ƙwace ɗan wai bazaisha nonon karuwa ba , sunan Dady suka sa mishi { UMAR FARUK } suna kiranshi da Papi , haka Umar ya faɗamin , kuma shine ya bani labarin saukar da Dikko yasa akayimin , ina zuwa makaranta yanzu nayi JSCE kuma tunda naje ban ɗauki position sama da 5 ba , dake kafin na koma saida Inna tayi tsayuwar arfa wurin bani taimako da karatu na musamman a gida , ina js2 nayi jarabawa da "yan js3 , Inna ta siyamin mota nake zuwa makaranta da ita ,
Sahura ta rasu , kuma dani da Inna munje gaisuwa , kuma naje wurin ahalin Babana a can ƙauye dani da Inna , kuɗin gado basu bani ba sun haɗa gaba ɗaya sun cinye , Dady dai shima rayuwar sai a hankali , Bello kuwa yana can yana fama da rashin lafiya ni banje ba kuma bansan abinda yake damunshi ba ,
Tou yanzu ina Dikko ya mutu ko yana raye................?
Wani irin ihu Sultana ta darkaka daga haka ta É—auke ashe ba'a tambayarta Dikko ni kuma na tambayeta.......!!!
06/12/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 87
*_Wallahi idan kunji haushi na da gangan , inaji dai kun manta yadda labarin nan yake tun farko , masu cewa na gaji na yanke labari kuma dai matsalarku , kamar yadda na faɗa yadda ta tsara abunta dole haka zanyi idan ya miki a haka kibi idan bai miki ba ki barshi babu lallai fa ba dole dan anyi ciwo an warke ai ba'a ba mutuwa haushi ba , nabi tsakar dare nabi rana nayi safiya nayi marece , naji daɗi ko ba daɗi nabi dai ina muku dan kuyi farin ciki amma jiya kawai dan rashin adalci ni hada masu gayamin kalami mara daɗi hmmm aiko idan har kukaimin haka ni baku kyauta min ba kuma ƙullu yaci amanar koko...._*
Inna ce ta shigo cikin ɗakin da sauri inda Sultana take taje ta riƙeta tana shafa mata ruwa take min magana cewa Jamila da Allah kiyi haƙuri da labarin nan haka nan ki tafi sai wani lokaci , Inna ki gafarceni don girman Allah ki barni takai min ƙarshe , Inna tace a , a kije kawai , zan sake magana ta dakatar dani ta hanyar ɗagamin hannu , jiki a sanyaye na fara ƙoƙarin sauka daga saman gadon a dai² lokacin da Sultana ta buɗe idonta dan dawowa daga sumar da tayi wanda ta dawo ta dalilin ruwan da Inna ta shafa mata , cikin kuka tace Inna barta na faɗa mata , Inna tace to karki sakemin wani koke² na faɗa miki , insha Allah Inna , fita Innar tayi ni kuma na koma na zauna ita kuma taci gaba......
Dikko bai mutu ba kuma bai sakeni ba , da na barshi rufe a palo ni bansan abinda ya faru dashi ba tunda ni banyi waya dashi ba kuma ban ganshi ido² ba.
Dikko na kira Inna kuma ta shiga amma bata ɗauka ba , da kyau , daga haka bai sake cewa wani abu ba , kaji , naji , tou kace wani abu mana , ai shine nace hakan da kyau , nidai baka so na , baka damuwa da abinda yake damuna , ni bansan abinda yasa kake min haka ba na faɗa cikin hayaniya ina kuka , duk saida na safke mai isata sannan yace tou yi haƙuri An mata gani nan zuwa zan miki abinda kike so ,
Abinda na fahimta ni a nawa tunanin shine , tunda yana da matsalar fushi da saurin hasala , idan yana fushi kuma baya iya murza kanshi , ban sani ba tunda bai faɗamin dalilinshi naƙin saurere na ba , kila shi zuciyarshi ta tabbatar mishi da cewa lallai ni munafukarshi ce kamar yadda ya faɗa , dole da mamaki ya za'ayi ace sai a mafarki zanga Mustapha , me yasa tunda yasan Dikko baije wurinshi kai tsaye ya faɗa masa damuwarshi ba sai yazo wurina kuma sai a yanayin bacci ? Miye nasabata ko alaƙa ta dashi ? Shi yasa ya warware gaba ɗayanshi ya kasa saita kanshi sai lalurarshi tayi mishi tasiri a dai² wannan lokaci ya alaƙanta abun akan ni dama na zubar da cikinshi dan ina so na ɗauki fansa , kuma na faɗa masa cewa zan ɗauki fansa komin daren daɗewa zansa masa baƙin ciki da damuwa mara gogewa , saiya kira zuwa na wurinYazeed shima yana cikin ɗaukar fansa wato kuma sai yake gani da ni aka haɗa kai akayi masa asiri tunda har nasan Mustapha kenan har yanzu ƙudirin fansa bai goge min daga rai ba , maganar gaskiya ne kenan tunda itama Suwaiba ta kira Mustapha kuma Sultana tasanshi amma sabon rainin hankali wai a mafarki , a ganinshi ina tare da Al ' Ameen bayan shi kuma ya rabu dashi ne saboda ni dan yakai gulmata a wurin Dadynsu Dikko tun lokacin dana zauna gidan Dikko na farko , shine dalilin daya haɗashi da Al ' Ameen ya rabu dashi ya dawo da Ashiru , wanda lokacin da zan koma makaranta a karo na biyu mukayi faɗa da Mardiyya a motar Dikko na dawo katsina su kuma suka wuce Abuja.
Zan faɗa in mutu , ai nine zan jefaki da kaina , da gudu na sauka nayi waje kafin yazo naja ƙofar , kai.............. Saina kashe kaina , da gudu na fita daga gidan jikina yana ƙyarma kuma har yanzu ban daina fitsari ba , gaba ɗaya na ruɗe na rasa abinda yake min daɗi , ina gudu ina waiwaye ko ya biyo ni ne ? Nabar wayata a gida kuma ban riƙe number Inna ba amma tunda har nake kiran wayar a da bana samu yau kuma na kira na samu tabbas zan samu Inna hakan ya tabbatarmin tana nan , kuma lokacin ban lafiya ai ta faɗawa Dikko itama zata dawo babu jimawa , ta dawo kenan shi yasa na samu kiran ya shiga , napep na tare na nufi barhim estate....
Kamar yadda nayi tunani kuwa haka ya tabbata , a buɗe na samu gidan na faɗa da gudu nabar mai napep a ƙofar gida , bedroom na samu Inna kwance tana baccin gajiya da gudu na hau saman gadon na riƙeta ina waiwayen bayana , a firgice ta farka tace ke lafiya ? Me ya faru ne ? Gaba ɗaya bana iya magana dan na firgice yadda tunani baya tunani , bayana na buɗe mata inda ya jefeni da wuƙa sai kuma wasu wurare danaji ciwo wurin guje² , sai gefen kafaɗa ta dake min ciwo saboda halbin da yayi min nayi ƙundunbala , mai napep kuwa mai gadi ya sallameshi ya kama gabanshi.
Meya faru dake ne ? Inna take tambayata , bana iya magana sai kuka , dan haka ta sauka ta ɗauki wayarta ta fara kiran wayar Dikko , amma duk kiran da tayi masa bai ɗauka ba , itace ta taimakamin nayi wanka ta bani kaya na saka , fita tayi ta samamin abinda zanci kamar baƙuwar abinci haka naci gaba da cin abincin a zalamance ina tsare Inna da kallo , kuma har zuwa wannan lokacin kiran Dikko takeyi , ina gama cin abinci na kwanta naci gaba da bacci wahlala.
Inna kuwa kiran Dikko da tayi bai ɗauka ba shine yasa ta fusata ta fara wallahi׳ wannan auren saina kashe shi ni har ya isa in kirashi bazai ɗaukamin waya ba , shiɗin banza shin ɗin wofi me akayi² shi ne ? Ɗan iskan yaro mara kunya daya raina mutane , nan fa ta fara kiraye²n ƙawayenta Dikko ya daki Sultana ya caccaka mata wuƙa yaji mata ciwo , yarinyarta ta lalace kunga yadda Sultana ta koma ? Aure sai kace auren bauta ? Waye Dikko ? Saboda tsabar ma shi ɗan iska ne ya zanemin ɗiya kuma nake kiranshi baya ɗaukar waya , to ni nafi shi kangara da taurin rai naga yadda za'ayi ta koma.
Bayan ta gama kiraye²n waya ta tasheni a bacci ina tashi na ganta da wata irin zuƙeƙiyar wuƙa , cikin magana mai kama da raɗa tacemin idan wani yace miki kina san Dikko dan ubanki kika ce kina sansa saina kashe ki idan mutane suka tafi , idona cike da hawaye na ɗaga mata kai , idan kuma kika kira Dikko ko ya kiraki ni kika ɗauka saina kasheki dan ubanki babu wanda yaji babu wanda ya gani , kaina na girgiza alamar to , sakarar banza Dikko baya sanki ya raina uwarki na kirashi ma bai ɗauki wayata ba , dama matar Babanshi ta faɗamin kullum dukanki yakeyi ga tsangwama ga gori ga masifar kishiya ki zubar da ɗan iska kwandon shara ki fuskanci sabuwar rayuwa , sake kaɗa mata kai nayi , Inna tace sai kin samu wanda yafi shi tunda ubangiji ya halicceki nagartacciyar mace , hawaye ne ya gangaromin daga cikin idanuwa nidai nasan wallahi ƙarya ne babu wani inda zan samu wanda yakai Dikko bare kuma wanda yafi shi.....
Inna kuma taci gaba da cewa idan kuma kika kuskura kika sake zaɓarshi kika koma zama dashi wulaƙancin da yayi miki a baya sai yafi wannan kina komawa gidanshi na cire hannuna a lamarinki , kuma duk ranar daya sake dukanki idan kika je wurin "yan uwana ko ahalin Babanki ko nan gidan da wannan wuƙar zan kashe ki in huta , yanzu ma da kai na bata ansa , saida ta ƙare duk mai isarta sannan ta ɗaukeni a mota muka tafi asibiti.
Tunda muka fita duk idan naga ɓakar mota ta wuce da gudu sai inji kamar Dikko ne a cikinta , tunanin Dikko kawai nakeyi ko yana a wane hali ? Ko ya zaiji idan ya tashi bana nan ? Me yasa nazo gida dama na tsaya a wurinshi gashi yanzu Inna ta ɗauka da zafi harta fara cewa wai ya sossokamin wuƙa , sossakawa fa , jifana yayi fa kawai , yanzu ya zanyi idan na tuna dashi a halin da nake yawan tunaninshi ina gidanshi , wace irin rayuwa zan fuskanta , dandai babu kyau zunubi mai girma ne tsallake maganar Iyaye da kawai saina koma amma ina iya komawa matsallar data fi wannan ta taso ina zanje a lokacin kuma.......? Waye zai ƙwaceni ? Allah sarki mutumina ko kana a wane hali , kana raye ko kuwa ka kashe kan naka kamar yadda ka faɗa......... ?
Har mukaje asibiti muka dawo tunanin Dikko nake , ya wani zo ya tsayamin a rai , ji nakeyi dama kawai zan buɗe idona naga mafarki nakeyi ina buɗe idona sai in ganni a gaban Dikko da nayi farin ciki , koda muka dawo gida bedroom na shiga naci gaba da tunanin da bashi da gaira bare dalili , shashshekar kukan Dikko nakeji a zuciyata yadda yakeyi idan yana kwance dani , yadda yakeyin wata ƙyarma yana wannan kukan nashi , bawai ɓare baki yakeyi yana ihu ba , a , a wani iri dai yakeyi mai riƙe zuciya dasa mutum tunaninshi a ko wane lokaci , nashi daban ne dan Alhaji mai gidan "yanci ba irin na Dikko yakeyi ba , kai na Dikko daban ne salon nashi ma yasha banban , uwa uba ya iya sumbatar mace cikin salon da bashi tafiya har abadan duniya , ko ina kike ko ina kikaje sai kinyi tunaninshi dole ,
Haka nake zaune a gidan Inna tunanin Dikko yasa gaba ɗaya na fita hayyaci na , na ƙara ramewa haske na ya rage ga rashin lafiya ta kunno min kai sai jarabar shan kankana idan na riƙe ƙwallo saina cinyeshi dukanshi , da safe ina tashi dashi zan fara , da rana haka idan zan kwanta bacci , Inna kuma dan na rage yawan tunani yasa ta samanin malami mai bani karatu na musamman a gidan , ina dai tunani sosai amma hakan bai hanani gane abinda ake koyamin ba , itace ta sakani a makaranta kuma ta siyamin motar da nake hawa , ina cikin wannan hali na shigar ƙaramin ciki Inna tabi mijinta sukayi tafiyarsu ta barni a gida dani da wata tsohuwa dan ina tunanin kila mijinta ya sake matarshi dan tafiya da Inna yayi yawa duk lokacin da zaje da Inna yake tafiya ,
A makarantar da nake zuwa a nan na haɗu da Umar bansan abinda yakai shi ba , naji daɗin ganinshi sosai wallahi sai naga kamar zanga Dikko ko zaicemin gashi mai gida zaiyi waya dani , bayan mun gaisa nace masa ko yana koyarwa ne anan ? Yace min a , a wurin wani yazo , ina taso yayi min maganar Dikko ya ƙiya , nace tou ko yanzu ka daina zama Qerau ne ? Nayi haka nidai dan inji an kamo tashar Dikko amma ya ƙiya , tou ina mai gidan naku ne ? Abinda kin guji mai gida sai kuma kice wani ina mai gida? Kamar ya na guje shi ? Ey ai haka kikayi ma Momy rashin kunya dan tazo tafiya dake , Dady yace aje a taho dake kije kiyi jinyar mijinki shine kika ce bakya san mahaukaci sai an sake ki , ai kinsan da rashin lafiyar nashi kika gudu kika barshi , tou haka akayi ? Na faɗa a zuciyata , Umar kuma yaci gaba da cewa mai gida yasha wahala kema Hajiya baki kyauta ba da kika faɗawa mahaifiyarshi baki san mahaukaci , yanzu yana ina ne ? Waye ma yasan a ina yake ? Yana can Dady ya tafi dashi itama kanta uwarshi bata san inda yake ba , a nan yake faɗamin mai gida Dikko yamin halakci da bai kamata koma miye na baɗa masa ƙasa a ido , shine ya faɗamin Dikko yasa anmin sauka da ragunan da aka yayyanka ya ƙara da cewa wallahi da nasan matsayina da yadda mai gida yake so na yake ƙoƙarin kyautatamin da ban saka mishi da muguwar sakayya ba , nasan mutum nawa Dikko ya rabu dashi saboda kawai nayi farin ciki ? Me yasa na tsananta ? Me yayi zafi haka ? Miye dalilin saka sharri akan alkairi , naji dai babu daɗi amma koma dai miye nasan Dikko zai dawo kuma tabbas zaizo , nice na faɗawa Umar inda nake na kuma yi masa kwatancen gidanmu....
Mai ƙwaƙwale ido kuwa na sake mafarki dashi , abinda Al ' Ameen yayi min ni na yadda dashi 100% shi yasa a gidana banyi mishi shamaki dashi ba , ko ina nan ko bana nan zai shiga gidana kamar gidanshi , tunda na fara neman matar da zan aura na faɗa mata cewa Al ' Ameen Yayana ne , tana ganin girmanshi kuma tana girmamashi a matsayin shi na Yayana , idan bana gari ko wani abu matata ke so Al ' Ameen nake turawa yaje yayi mata ,
Hmmm , da Al ' Ameen ya samu sake nidai banda wani ƙarfi kuma iyayena basu dashi tunda na faɗa miki daga ni har iyayena duk a ƙasan baban Dikko muka tashi , Al ' Ameen kuma a wancan lokacin shi yayi ƙutu² ya fitar damu a gidan yaje ya haɗo bala'en dashi kaɗai yasan iyakar irin makircin daya shirya akayi mana rashin mutunci a lokacin Dikko baya nan ya raka Dady ganin likita , amma a cikin rashin mutunci babu Momy a ciki dan ita bata cika surutu ba kawai dai idan tana sanka tana sanka idan batayinka ko sabgar ka bata shiga , matan Dady sune sukayi wulaƙancinsu suka koramu kafin dawowar Dady kinga bamu san abinda mukayi ba kuma Al ' Ameen bai nuna mana komai ba duk dashi muka sha jimamin abun har kuka yayi tare da cewa shima zai bar aikin gidan , Babana ne ya bashi haƙuri yace kada abinda akayi mana ya shafeshi a taƙaice dai ya bawa Al ' Ameen baki akan zai haƙura yaci gaba da aiki.
Fitarmu a gidan yasa muka fuskanci sabuwar rayuwar babu , talauci ya tiso ƙeyarmu gaba , na kira wayar Dikko bayayi danni a lokacin bansan akwai number ƙasar waje ba , kawai na ɗauka duk ɗaya ce , na kira Dikko har na gode Allah wayarshi bata tafiya dan nayi imani da Allah ko kisan kai nayi idan na zaunar dashi nayi mishi kuka zaiji tausayi kuma ko za'a mutu idan yace mu zauna gidan wallahi koshi Dadyn bazai koremu ba dan idan har Dikko yace masa kaza za'ayi tou sai anyi shi , idan Dikko baya san abu Dady duk yadda yake sanshi saiya fita sabgarshi , Dady yana ma Dikko soyayyar da tunda nake ni ban taɓa ganin irin soyayyar ba , amma saboda sharri da makircin Al ' Ameen saida yasa Dady yayi ma Dikko faɗa karon farko a rayuwarshi zuwanki a rayuwarshi kenan.....
Ba'a zagin Dikko ba'a daka mishi tsawa ba'a mishi kallon banza , amma yadda duk baki tunani Dikko yana da tarbiyya dan duk wannan soyayyar baisa ya zama sakaran namiji ba yasa abinda yake kuma Dikko ba ɗan iska bane yana da tausayi amma bashi da mutinci duk yadda baki tunani dan shima ya gaji baƙin hali wurin uwarshi kaifi ɗaya ne idan zaiyi² kawai , idan bayayi babu gudu babu ja da baya bazaiyi ba , yana da halin ko oho kuma yana da mantawa da duk abinda zai ɓata mishi lokaci yana da kafiya ko zai mutu saidai ya mutu ya yadda wani irin hali dai shi kaɗai yasan irin abunshi.
Ban wani ɓoyewa mata ta halin da muke ciki ba , ta tausaya min sosai , Al ' Ameen kuwa shine ya samamin uban gida aka bani mota na riƙa aikin mota ina ɗaukar fasinja zuwa jahohi daban² , da nace bana so yacemin na riƙe motar kafin mai gida Dikko ya dawo sai asan abunyi , haka na haƙura na anshi motar idan na tafi sai inyi wata ɗaya bana nan , idan iyalita tana san wani abu zan aiko direbobi masu yo wa katsina sai a bawa Al ' Ameen yakai ma matata.....
Ina can su suna nan bansan wane irin ɗan wanke suke jefawa ba , matata mace ce mai mutunci mai biyayya mai kawaici da kauda ido akan abun duniya , amma kinsan yawancin mata suna "yar ciwa²r nan tasu ta idan aka baka kuɗin cefane ka ɗan maƙale wani abu , tou haka matata take idan na aiko mata da kuɗi zata ɓoye batayin abinda ya kamata kuma bata cin abinci mai mahimmanci saita maƙale haka kuma ko ruwan da zatayi amfani dashi bata siya saidai idan an dawo da fanfo taje tabi layin ruwa acan ƙofar gidan wani tsohon attajiri da yake fito da tiyo waje mata suke ibar ruwa.
Al ' Ameen kuwa gani yakeyi kamar nine kasashshe wurin kula da iyalita , saiya fara wanketa da ruwan naira dan idan dai kana tare da Dikko tabbas kaima zaka samu bakin gwargwado kayi hidima da rayuwarka cikin rufin asiri kamar dai kaima mai halin ne , haka yake cikamin gida da abokanshi ni ban sani ba yakai cefane yakai abinda za'a dafa tayi girki suci a zauna min a gida har dare ana fira da matata , idan zan dawo gari ya sani dan ina faɗa masa bana ɓoye masa komai , matata kuma bata taɓa faɗamin Al ' Ameen yana zuwa shida abokanshi ba tunda dai na faɗa mata Yayana ne ta yadda a hakan kawai.
Bansan yadda akayi ba ya ɓatamin mata ba idan ina nan nine miji idan kuma bana nan Al ' Ameen shine mai gida , haka maƙota sukayi ta bugomin waya suna faɗamin abokina fa yana zagayawa idan bana nan , da farko ban yadda ba sai naga tou idan sharri ne me yasa mutane da yawa zasu faɗa ? Ashe neman da yake mata akwai gejin da zai kai yana amfani da ita an bashi kuɗi ana neman idon matar aure amma sai anyi fasiƙanci da ita so adadin kwanakin da suka faɗa mishi sai a zuba mata maganin a idonta ana zubawa shi kuma tsafin zai cire idonta , ni kuma ranar da zan dawo katsina sai ban faɗawa kowa zan dawo ba , da farin ciki na shiga cikin gidana amma saina samu matata ba ido tana ta kakarin mutuwa , dana tambayeta sai tacemin Yayana ne yake nemanta shine ya cire idonta , daga haka ta mutu.
Nasan banda wani Yaya wanda ya wuce Al ' Ameen kai tsaye nayi ƙararshi amma sai ya samu ɗaurin ƙugu wurin manyan da yayi musu aiki sukaje suka baza kuɗi aka kori shari'ar kuma har lokacin Dikko bai dawo ba , haka na ƙara ɗage ƙara duk inda mukaje kuɗi ne suke magana , maimakon inyi haƙuri saina biye sharrin zuciya nima na nemi hanyar tsafi dan nayi alƙawari sainayi kuɗi da gasken gaske , zuciya ta ingizani nima na faɗa sana'ar ƙwaƙwale idanuwa , wanda Al ' Ameen ya haɗani dashi ya bani mota shine aka kaiwa idon matata , dan haka na koma wurinshi nima na shiga ƙungiya kuma da idon nashi matar na fara , na lashi takobin duk matar auren da ta zama makwaɗaiciya saina ƙwaƙwale idonta kamar yadda aka ƙwaƙwale na matata ,
Ƙungiyar ashe tana da wani tsari wanda ni ban sani ba , su zasu baka magani kayi amfani dashi ido kawai zai fita kai zaka zuba magani su kuma zasu turo tsafunsu ya zama maciji kana zuba maganin a idon mace macijin zai tsotse idon ya kuma shanye jinin jikin mace , idan yasha jinin saiya zuba wani a cikin ƙwarin idon daya cire kafin tsafin ya gama tsafinshi shine jini zai riƙa ɗiga a idon mutum da zaran an gama shikenan mutum ya tafi kai kuma sai a baka kuɗinka , tsarinsu shine shekara 3 sai kaima su tafi dakai ,
Mu mune ƙanana su kuma sune manya , mu zasu tura muje mu nemo musu matan aure muyi iskanci dasu sai mu zuba magani , kashe duk yaransu sukeyi bayan shekaru 3 sai suyi sabbin zubi , bansan da wannan tsari ba na faɗa ƙungiya kai tsaye saboda wani muradi nawa , ba wurin gudu babu wurin tsira mutuwa tazo min kuma shima Al ' Ameen zai mutu idan dai kayi musu aiki saika tafi saidai a wayi gari ba'asan abinda ya kashe ka ba , to me yasa sai matan aure suke so ne ?
Wannan tsarin tsafinsu ne shi ya faɗa musu irin wanda yake so bashi ya basu kuɗi , wasu zasu ce "yan mata , wasu matan aure , wasu zawarawa wasu mahaukata wasu jarirai wani tsafin kuma zaice mace mai ciki yake so , wasu makafi wasu guragu ko "yan maɗigo ko mazina ci , mai wasa da sallah ko wacce ta raina iyayenta , tou su nasu wacce ta raina aure suke buƙata , kinga ke ni ban kwanta dake ba amma kinci kuɗi dana tabbatar ke ba matar aure bace ba suka sa na koraki , amma sun matsa akan mutuwarki dan record in da kikayi sun takura sosai akan ki mutu , amma basu samu galaba dake tsafi yace kinyi kusanci da sallah yawan karatun al ƙur'ani da addu'a lokacin kwanciya bacci , cire hular saman kanshi yayi ya duƙar da kanshi gabana yace kin gani bani da sumar kai bansan ranar da aka cireta ba sun bugamin lamba , shima kuma tabbas nayi imani sun bugawa Al ' Ameen irinta gaba ɗayanmu zakiji labarin mutuwarmu.
Tou ta ina ne zanbi nazo inda aka binne tsafin da akayi ma Dikko ne ? Labarin tsafinshi ya goge idan ya dawo zai baki labarin komai banda sauran lokaci wanda aka bani ya ƙare , hankalina kuma ya kwanta tunda shima Al ' Ameen zai mutu , yana faɗin haka ya zama maciji suuuuuu ya gudu da wuce , da tashin hankali na farka kuma tun daga wannan ranar ban sake ganinshi a bacci na ba har yau ,
Inna ta daɗe a tafiya lokacin data dawo cikina ya shiga wata 7 bata sake komawa ba har na haihu , dana aihu ni na faɗawa Umar na haihu ita kuma Momy tazo har asibitin da muke ta anshe jariri wai ba zaisha nonon karuwa ba yazo shima ya zama karuwi , ta tata rashin mutunci dai² iyawarta tayi gori tace kuma tunda bata san zamana da Dikko duk wanda ya tsayamin a garin nan zata ga wanda ya isa yasa na sake zama da Dikko , zai dawo saki 3 zai bani babu sauƙi , idan kuma ina tunani Dadynsu zai tsayamin kamar na aurenmu da Dikko yaƙiji ya aureni Dady ya goya mishi baya yanzu haka bazai goyu ba , shi da kanshi zaisa Dikko ya sakeni , ban santa ba labarinta na keji , nayi kuka nasha hauka bansan iyaka ba , kuma da suka tafi da jaririn Umar yazo ya faɗamin wai Momy tace ma Dady nice nayi waya wai azo a ɗauki jaririn nan yadda bana san Dikko haka bana san jaririn kuma duk jinin da Dikko ya haɗo dashi bana sanshi , idan basuje sun ɗauki yaron nan ba komai zai iya faruwa tunda tun cikin naso na zubar bai fita ba zan kashe yaron , ta dai haɗa da ɗan makircita.
Abinda yasa nake kuka har na tafi shine , Umar yacemin Dady yake faÉ—a da yana tausayina kuma yana so na tunda Babanshi yana so na , ashe bani da mutunci har na danganta mishi É—a da mahaukaci kuma nice zan kashe mishi jika daga wurin Babanshi dama na zubar da ciki a farko tunda nice nasa Rabiya tayimin allura , Allah yaba Babanshi lafiya ya dawo saiya sakeni.........
Dana tuna zan rabu da Dikko sai inji dama mutuwa nayi kawai na huta da baƙin cikin rayuwa..............!!! Ga Dikko yace baya zuwa bikon mace , iyayenshi sun ɗauki zafi , nima Inna ta gune akan rashin ɗaukar wayar da Dikko baiyi ba kuma har yanzu bai kirata ba , kuma tace idan har na koma gidan Dikko babu ita babu ni har abadan duniya saidai idan Dikko zai zama uwata , tasa kullum ina kiran wayar Dikko akan ya bani takaddar sakina naje nayi aure , wayoyinshi gaba ɗaya basa zuwa , shin yana ina ? Yana nigeria ? Ko yana ina ?
Me Dikko zaice idan ya dawo ? Wane hukunci zai ɗauka ? Ya zaiji idan iyayenshi suka ce nice na maida musu ɗanshi nace bana riƙewa saboda bana sanhi , shin zai sakeni ko kuwa zai zauna dani ? Ya zanyi ׳.................. ??? Yadda zanyi da mafita da rabuwa , gaba ɗaya na tattara lamarina wurin ubangiji duk abinda ya zartar a kaina dama haka yazo a rubuce kuma bawa bai isa ya goge ƙaddara shi ba ,
07/12/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA....* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 88
*_Godiya mara iyaka zuwa gareku ,_* 👇ðŸ»
*_HADIZA MATAWALLE..._*
*_RUKY " " " " " "_*
*_FATY " " " " " "_*
*_ZEE " " " " "_*
Ngode sosai ku huta gajiya Allah ya daÉ—a zuminchie...
*_Gaisuwa marar iyaka zuwa gareki ZAINAB AHMAD KADUNA { Sheke } ina miki fatan alkairi tare da NA'IMA ABU KANKIYA..._*
Tabbas wannan zance haka yake , Allah ya bawa Dikko lafiya ya ƙara soyayya a tsakaninku ya kuma ƙaro irinsu Papi hada Junior Dikko muzo musha suna , murmushi Sultana tayi amma batayi magana ba , saukowa nayi daga saman gadon ina ɗan gyarawa cewa ni zan wuce zan tara ƙarshen labarin a takardar labarin rayuwarki , godiya tayi min sosai mukayi sallama cikin mutunci da mutuntawa , itama Inna munyi sallama cikin mutuntawa na barsu lafiya nima zan tara muga ƙarshen labarin tare daku masoyan Sultana & Dikko ,
Bayan Jamila ta tafi wanka na farayi tare da ɗoro alwallah dan magrib ya gabato , ina fitowa kayana na saka na shafa mai sama² da powder naci gaba da tattara kayan da Inna keyin parking zatayi tafiya zuwa Abuja ita da mijinta.
Inna ce ta shigo ɗakin tana cewa wai ga wani Abbakar can yana miki sallama a waje , ba tare dana kalleta ba nace wane Abbakar kuma ? Abokin ɗan iskan yaron nan mana , murmushin jin daɗi nayi a zuciyata a fili kuma na ɗan basar cewa Hajiya Inna kenan waye ɗan iskan yaro kuma ? Dikko , Inna wai me yasa kikejin zafin Dikko da yawa ? Bana san yaron ne kwata² gaba ɗaya ya siremin kamar tusar safe....
Saura kaÉ—an na fita na zageshi dan dai kar ace na haukace , ai bana nan ma dan ni bazanje ba , aiko sai kinje kodan ya ganki baki lalace ba ci gaba aka samu ba ci baya ba yaje ya bawa Dikko labari , nidai Inna gaskiya bazan wani je ba , aiko sai kinje kuma kin barbaÉ—a masa rashin mutunci yadda Dikko da uwarshi suka tozartaki kema sai kin tozartasu kuma sai ya baki sakinki tunda basu da mutunci....
Inna kenan na faɗa a raina , a zahiri kuma na bita da kallo , kin wani tasani kina kallo kamar niɗin baƙuwarki ce ki wuce kije ki dawo , banyi magana ba na ɗauki hijabi na fice , a harabar gidan naga wata irin lutsetsiyar mota ɓaka sai sheƙin sabinta take tunda na taho nake ganin kaina a jikinta bana iya ganin na cikin motar shima a gilashin kaina nake gani saboda yana da duhu , jikina ya bani ba Dikko bane a ciki amma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba duk inda wannan motar ta fito tashi ce kuma ban taɓa ganinta a cikin motocinshi ba ,
A jikin motar na tsaya na ciki ya sauke gilashin motar tare da cewa sannu , yawwa na faɗa rai a ɗan haɗe , ya gida ? Lfy , kin gane ni ? Ey a Bakori daka kawo katifa a motar ka ko ? Murmushi yayi tare da cewa ashe baki da mantuwa , ya akayi ne ? Gefenshi ya kalla ya ɗauko wata "yar leda bansan ko miye a ciki ba ya miƙomin ba tare dana ansa ba nace meye a ciki ne ? Ki ansa koma miye zaki gani , hannuna ɗaya a ƙugu ɗayan nake nunashi amma bada ɗan yasa ba kawai ka faɗa danni bazan karɓa ba , ki ansa An mata , ban sake magana ba na juya na wuce dan kar in ɓata lokaci Inna ta biyoni ta yabamin , sallah na samu Inna tanayi nima abin sallah na shimfiɗa na kabbara sallah.
Kai Ashiru ɗauki yaron nan ka maidashi gida fita zanyi , riƙe Dikko yaron yayi yana kuka cikin gwaranci yace bajan je ba tare da maƙale ƙafaɗarshi , Ashiru yace mai gida bazai zo ba , kai da Allah ɗaukarshi basai zaije ba ku tafi zanzo nima , ƙara riƙe Dikko Papi yayi yana kuka , kafin Dikko ya sake magana Abbakar ya shigo inda Dikko yake tsaye yayi parking tare da sauke glass yace DK bata ansa ba , ko tace maka wani abu ne ? Yadda sukayi da Sultana ya faɗa masa , babu damuwa An mata tana da matsala , ni bansa abinda ya faru ba tunda bana nan bazan iya ƙarda komai ba , kawai anje an kwaɓa abu duk sun jagwalgwale min komai , taya kai tsaye zan tunkari inda take bayan Momy taje ta ɗauko yaro ta taho dashi dole kowa zaiji babu daɗi , Momy Dady duk su ba'ayi musu dai² ba , itama Mamar kanta yayi zafi , kallon Ashiru yayi tare da cewa kiramin Umar yazo yanzu²n nan ya ƙarasa maganar yana kallon Papi daya duƙunƙune shi , isowarshi kenan su Nabeela suka zo dashi yi ma Dikko sannu da hanya da kuma dubashi da jiki , shi kuma sai wani bin Dikko yakeyi kamar yasanshi dan ko su Nabeela gajiya sukayi suka tafi suka barshi yaƙi binsu , iyakarshi gidanshi baije gidansu ba ,
Kai ka sanni ne ? Ya tambayi Papi fuska a haɗe , yadda yayi abun yasa Papi yayi dariya danshi a tunaninshi Dikko wasa yakeyi mishi , kai kasanni ne nace ? Ƙara ƙyalƙyalewa da dariya yayi yana kallon Dikko , tsoki yayi tare da buɗe mota ya sakashi a baya ya rufe yace ma Ashiru idan Umar yazo kace masa nace yaje wurin An mata haka kawai zakace masa , Ashiru yace to , zagayawa yayi ya shiga gaba suka fita da Abbakar ,
A palon Momy ya samu Jiddah tasha wanka na ɗaukar hankali da firgita tunani , Dikko ne a gaba Abbakar yana ɗauke da Papi da yayi bacci , suna shiga Momy ta ansheshi tana cewa Nabeela taje ta kwantar dashi , ansar shi tayi ta shiga ciki dashi su kuma suka samu wuri suka zauna , Yaya DK sannu da zuwa ya ƙarfin jiki ? Ko inda take bai kalla ba bare ta sa ran zaice yawwa , gaishe da Abbakar tayi shidai ya ansa saida ta rufe bakinta sannan Dikko ya gaishe da Momy , ta ansa cikin jin daɗi tana nuna yanayin farin ciki ɗanta ya dawo lafiya kana kallonta dai kasan tanajin daɗi ne a daren nan , labari marar ma'ana taita bashi akan Papi shidai shiru yayi baiyi magana ba kuma ko murmushi baiyi ba hankalinshi da kaf tunaninshi yana can wurin tunanin yadda zai taro matsalar da suka haifa da kansu , amma An mata ta bashi mamaki yayi tunanin ko bashi ne da ita suka haifi Papi ba zata iya riƙe mishi ɗanshi ko bayan baya nunfashi amma shine ta bada yaro da baiji bai gani ba da yana da ƙarar kwana daya mutu shikenan ya sake tashi a zero.....
Momy ce ta dawo dashi daga tunanin da yakeyi taci gaba da fanfo da ƙaga abinda bai faru ba kuma ba'ayi ba akan Sultana tayi mata rashin kunya ita da uwarta , yadda ta faɗawa Dady haka ta faɗawa Dikko ta kuma ƙara da cewa tuntuni suke aiken rashin mutunci akan ka sakar mata "yar ta , hankalin Dikko akan waya yace wa suka aiko ? Wata maƙociyarsu ce can Barhim , sai kuma kai tsaye aka barta ta shigo saboda an aikota daga gidansu An mata ? Ya ƙarasa maganar yana tsare Momy da ido , tou ƙarya nake Dikko , ah yi haƙuri ba nufi na kenan ba , daga haka bai sake magana ba sai ita taci gaba da farfaɗo maganganu marasa daɗi da ɓatanci , a ranshi kuma yace da na saki yarinyar nan gara na dawo da ita muci gaba da cakuɗawa daga inda aka tsaya har tayi hankali danshi kullum kallon Yarinya yake ma Sultana bai san ta ƙara girma ba , saida Momy ta tsiyaye mai isar ta tana faɗa tana kunnuwa ta tata rashin mutunci iyakar iyawarta , har tayi ta gama Dikko bai sake magana ba , ita ta gaji da kanta tace ya tashi ya bata wuri sakaran da baisan inda duniya ta nufa ba , miƙewa yayi ya fice Abbakar ya biyo bayanshi amma Jiddah Momy tana fara faɗa ta tashi....
Bai fita ba saida ya haÉ—u da sauran "yan uwanshi suka gaisa suna mishi sannu da addu'ar Allah ya tsare gaba ya bashi lafiya mai É—orewa , suma dai sunyi mishi labarin Papi wai ya tambayi Papi ina Mamanshi yaji me yake cewa , murmushi kaÉ—an Dikko yayi wanda iyakarshi kawai a saman fuskarshi ya tsaya baizo baki ba , bai wani daÉ—e ba ya wuce saboda Dady baya nan ,
Abinda yasa ya tura Abbakar wurin Sultana waya ce ya bada yakai mata zasuyi magana dan tabar wayarta a goruba road ta gudu tou yaso ta ansa wayar suyi magana yaji ita kuma Mama ko tayi fushi ? Wai me yasa wasu iyayen miji suke tsanantawa akan matan "ya "yansu ne ? Suke nuna ƙiyayya tsana da kuma hantara ne ?
Matar ɗa abun so ce kuma itama ɗiyarki ce inda mutunci , abin tausayi ce ta wuce wulaƙanci , baki san yadda take zaune da ɗanki ba , tanajin daɗin sa ne ? Ko kuwa wahalarshi take sha ? Idan kinsan ɗanki yana da kyawawan hali kila ita matarshi munana yake mata , idan ke yana da haƙuri a wurinki kila ita rashin haƙuri yake mata Koma dai wane irin baƙin hali ɗanki yake da tadai yi haƙuri ta zauna dashi , waye yasan ni ina dukan An mata ne ? Duk wanda ya ganta idan dai mai hankali ne da ilimin karantar rayuwar ɗan adam yasan An mata bata da kwanciyar hankali , na doketa na zageta mari rashin haƙuri akanta gashi kuma sam² baya mata uzuri akan komai ƙanƙantar laifi idan tayi mishi , gaskiya iyayen miji ku daina tsanantawa wa matan "ya "yanku a gidan aure dan baku san yadda su matan suke haƙuri da "ya "yan naku ba ,
An mata tayi haƙuri da halinshi tuni ba tun yau ba kuma a hakan dai tana sonshi bata daina ba , ko a yaddar mishi ko kar a yaddar mishi , ko aji daɗi ko kishirya hakan shidai ba yaro bane yasan abinda yake shine yake auren matarshi dalilin wani bazaisa ya sake aurenshi ba , dan haka babu wani abinda ya dameshi dasai an yadda ya dawo da ita kawai zaije ya taho da matarshi ,
Umar ne zaune a palon Inna yaci abinci yasha lemu ya wani mimmiƙe yana kallo , dan ita Inna bata san Umar ko daga ta ina ya fito ba kawai dai tana gani na dashi data tambayeni waye shi nace mata a can gidan Babana lokacin bata nan ne yake min mutunci tou shine take cewa ya shigo idan yazo ,
A zahiri kallo yakeyi amma a baÉ—inance wallahi rahotanni kawai yake iba , danshi Allah yasa mishi bakinshi bashi da saiti akan magana duk abinda ya gani ko yaji kamar mai aljanun surutu saiya faÉ—a , ya daÉ—e sosai daya tashi tafiya Inna ta bashi kuÉ—i wai yasha mai ,
Ƙarfe 8:21pm yabar gidanmu misalin 8:41pm Dikko ya bayyana a gidan , kuma kai tsaye ya shigo har palo ba tare daya bari an bashi izinin ya shigo ba , da sallama ya shigo daga ni har Inna muna ciki ina tayata tattara kayanta , jin muryar Dikko yasa na sauko daga saman gado da gudu Inna tana cewa ina zakije ne ? Banyi mata magana ba na bayyana a cikin palon a dai² lokacin da itama Inna ta fito , gefe na koma ina maida numfashi Inna da Dikko suna fuskantar juna kan Dikko a ƙasa ni kuma duk su nake kallo saina kalli wannan na kalli wancan ,
Mama barka da yi..... Fizgoni Inna tayi muka koma ciki gefen gado ta zaunar dani ta durƙusa gabana ta riƙe hannayena , cikin lallashi tace karki manta da yadda kikayi kuka Dikko ya turo aka ɓanɓare miki yaro daga aihuwarshi yace a anso mishi ɗanshi baya so yasha nonon karuwa , kinaji kina kallo suka anshe ɗan suka tafi dashi , a gaban idonki nayi ta kiranshi a waya yaƙi ya ɗauka daga baya ma ya rufe wayoyinshi gaba ɗaya kuma har zuwa yau bai kirani ba , wannan shine ya dace ya zama siriki na ? Mijin da bashi mutunta mahaifiyarki ? Mijin da baya so ɗan sa yasha nononki yace miki karuwa ? Kar ɗansa yasha nononki shima ya zama karuwi ? Wannan shine mijin daya dace ya zama siriki a gareni ? A , a , tou sakinki zai baki maza nawa kika sani suna jiranki ? Me zakiyi da Dikko daya fara tsofewa ? Nan zai tsofe ya barki ki shiga tararrabin rayuwa , sakinki kawai nake so ki anso zakiga mijin da zaki aura yafi Dikko duk abinda kike tunani kiyi ƙoƙari ki more rayuwarki tun kafin duniyarki ta ƙare.
Inna waye zan aura ? Wayarta ta ɗauko ta nunomin hoton wasu matasa har 4 wai idan bana san wannan ga wannan kuma duk shekarunsu kamar na Dikko ne , bayan na gama gani nace umm umm suma dai duk sun tsofen tunda naga zasu kai shekarun Dikko , amma aisu basu ciccika fuska da gashi ba , gemu take nufi da ƙasimba , taci gaba da cewa ya sakeki ki auri zaɓina ko kuma dani dake kowa yaja tashi da'irar danni gaskiya bana san Dikko a matsayin siriki , me yasa Inna ? Saboda yaron baida kunya ko kaɗan , to me yasa kika yaddarmin na aure shi tun farin fari ne ? Wancan karon ra'ayi ne yanzu kuma muradi ne shin Dikko kika ɗauka ko ni.............???
Haba harma sai an tambaya ? Ai ke na zaɓa Inna , idan ni kika zaɓa ta faɗa tana bani biro da takarda a hannuna anan ciki zaki dawomin da ansar , ansa nayi na fito jiki a sanyaye ban samu Dikko a palo ba , dan haka na fito harabar gidan , a mota na sameshi zaune yana waya , tsayuwa nayi ina jira ya gama , buɗe murfin motar yayi ya fito da duka ƙafafuwanshi waje sannan ya kirani da hannunshi ɗaya wanda bai riƙe waya dashi ba , matsawa nayi ya riƙeni jikinshi ni kuma na dafa kafaɗarshi ina wasa da gemunshi da ɗayan hannuna , murmushi yayi ya kalleni amma bai daina magana a waya ba ni kuma baiyi min magana ba yadai tsareni da ido yana kallona.
Ɗauke idona nayi gefe ɗaya na janye hannuna daga gemunshi , kamo hannun yayi ya maidashi a dai² lokacin daya ajiye waya , riƙo ƙuguna yayi da duka hannayenshi ya jinjina shi tare da ɗan girgiza jikina sannan ya ansa biron hannuna da takaddar ya ajiye a gefe , jawoni yayi jikinshi yace me ne ne zakiyi da ? Ya nuna inda ya ajiye , Inna tace ka sakeni , wane irin saki haka babu daɗin ji ? Shiru nayi banyi magana ba , yana nan dai da halinshi na faɗa , yace ina miki magana kinmin shiru kuma kinaji , yanzun ma banyi magana ba , turani yayi baya daga jikinshi yana cewa wuce ki bani wuri , da sauri na sake komawa , dakamin tsawa yayi karki sake ki taɓani ya ƙarasa maganar yana gyara zamanshi zai rufe mota ,
Ƙara matsawa nayi da sauri na riƙe murfin motar cikin rawar murya nace yi haƙuri na bari , cikin fushi yace ni duk abinda kika min banji fushi a kanki ba saike mai Mama zaki wani cemin wai tace miki na sakeki ? Me nayi miki ? Ƙiyayyar harya kai fagen saki ? To me yayi zafi haka ne ? Ke ko kunya ma bakij.... Nima irin abinda ya taɓayi min can² baya nayi mishi nima na kulle bakunan mu wuri ɗaya , da sauri ya sauke ajiyar zuciya ya riƙeni jikinshi sosai yanayin lunfashi da yanayin gajiya , riƙe fuskarshi nayi da duka hannayena gefe da gefen fuskarshi na lumshe idanuwa na nima inayin irin yadda yakeyi idan yana kwance dani , murmushi yayi mai sauti amma bai raba bakunanmu ba kuma ba magana yayi ba yana dai ci gaba da fitar da numfashin kamar wanda yakeyin mura , miƙa yayi a kasalance da niyar ƙara jawoni jikinshi najiyo muryar Inna tana ta kwararamin kira cikin ɓacin rai , ƙoƙarin raba jikina da nashi na farayi amma ya wani riƙeni sosai , ƙyarma jikina ya farayi har yanzu bai saki bakina ba , nace Dikko Inna ke kirana kar tayi faɗa fa , fita yayi daga bakina yace shigo , Inna kuma ƙara kira takeyi Sultana........
Ƙoƙarin kwace hannuna na farayi daga riƙon da yayi min dan tafiya wurin Inna , shi kuma yacemin shigo , Inna fa ke kirana , Innar , shigo nace , ah ni gaskiya bazan shiga ba , shigo nace , haba Dikko wai meye haka ne ? Nima bansan koma miye ba , Sultana.......... Na rantse da Allah idan nazo wurin nan saina zaneki , Inna ta ƙara² faɗa , cikin kwantacciyar murya yace karki tafi ki barni , ko kina so inyi rashin lafiya ne ? Ya ƙarasa maganar yana yimin yaudararren kallonshi fuskarshi ɗauke da kyakkyawan murmushin shi mai ɗaukar hankali , girgiza kaina nayi alamar a , a , tou zo muje kinji jarumata yayi maganar cikin sigar lallashi , ita kuma Inna zuwa wannan lokacin ta ƙufule ta daina kirana , ni kuma Dikko ya ɗaukeni a mota muka bar gidan....... Shin Inna laɓewa tayi ta gani abinda mukeyi ? Me yasa ta kirani , Allah kaɗai ya sani.
Saida muka fita daga barhim na matsa na riƙe Dikko , murmushi yayi cikin izza sannan ya riƙeni da ɗayan hannunshi ɗayan kuma ya riƙe sitiyari amma baiyi magana ba , kwantar da kaina nayi a jikinshi fuskata tana kallon kyakkyawar fuskarshi saida naja gemunshi nace ina kaje ne ? Ba da fuskarshi ya kalleni ba da idonshi ya kalloni kaɗan sannan yace nima bansan ina naje ba , ba kin gudu kin barni ba ? Baki san ɗana ko An mata ? Hmmm ba komai ni ina sanki a haka ,
Sauka nayi daga jikinshi cikin hayaniya nace bana san² , ai basai kin faɗa da yanayin fushi ba nasan yadda abun yake , ai nima na sani , karki min rashin kunya ƙaramar yarinya , Dikko nayi , ai baki da lissafi mai gotacciyar kwalwa dake kuma saina ƙara aure tunda har yanzu baki da lissafi , kaje ka ƙara mana ba kaji abinda Inna tace ba , shiru yayi bai sake magana ba saini nayi ta rattafa ɗimi kamar wacce ta lashi wuta , kafin muje G R A harna ratto mishi yadda Momy tazo ta ƙwacemin ɗa , har yanzu bai sake magana ba , bayan yayi parking bai fita ba kashe motar yayi ya ɗauki wayarshi yana latse² , ni kuma har zuwa wannan lokacin abin faɗawa Dikko bai ƙare a wurina ba , saida na gaji na ɗauke da kaina , cire makullin motar yayi tare da cewa muje yayi maganar ne a dai² lokacin daya fita daga motar , nima fita nayi nabi bayanshi ina cewa kuma ai ni banajin tsoron kishiyar ko an faɗa maka ni ɗin lusarar mace ce mai ma auren miji kuka , jinjina kai yayi cikin ɓacin rai , saida muka raba palon 2 ya juyo yace nidai kika raina ko ? Yadda yayi maganar cikin ɗaure fuska yasa na koma baya ina kallonshi , jinjina kai yayi cewa muje yayi gaba nabi bayanshi har ɗakinshi....
Yau da kanshi ya rufe ƙofa , kuma bai wani bani wannan maganin nashi da yake bani idan zai kwanta dani ba , na yau wani iri ne daban saida nasha akaje wasa , kamar dai na daren farkonmu yauma saida ya tabbatar ya gama gigitani yace tunda na raina shi saida in tashi in tafi gida , kamar sakara haka naita kuka ina bashi haƙuri amma sam Dikko ya kifa kanshi wai bayajin yaren da nake mishi magana dashi , nayi kuka kamar raina zai fita ina cewa bana san hakan wai kai me yasa mugu ne da Allah ? Ba kin rainani ba ? Tou yi haƙuri , cewa zakiyi kin bari bazaki ƙara ba , na bari bazan ƙara ba , ɗan gajeren tsoki yayi cewa kawai kije idan kinyi hankali sai kizo inyi wasan danbe , riƙeshi nayi ina kuka yace min na fita jikinshi karya kasheni , ƙin fita nayi naci gaba da kuka ina kallonshi , dariyar mugunta yayi min sosai yana min video , kuma ban daina mishi magiya ba , haka yaita gwalgwala ni , yana dariya wai saina faɗa yadda ake cewa wasan danbe da indianci idan ba haka ba shi bayaji da hausa , cikin ɓacin rai nace ban iya ba buɗemin ƙofar na tafi , anƙi a buɗe ba makullin a hannuna yake ba ? Idan kece kika kulle ai sai kinga dama kike buɗewa , sai kin faɗa , kuma ko kin faɗa sai Dikko yaga dama zai danbace ƙaramar yarinya ya ƙarasa yanamin gwalo , da nazo nayi shiru sai inji bana iyawa , kamar wata zararra haka ya haukatani a ɗaki naita hauka yana min dariya , saida ya gaji da ranfa ni sannan ya kwanta dani da wani irin baƙon salo , daga farko naji daɗin yadda yayi min daga ƙarshe saida yayi ɗabi'ar tashi dan idan baiyi mugunta ba ji yake bai haɗu ba , da naji azaba nayi magana sai ya nunamin vidion yace kefa kika roƙa , saida ya tabbatar ya wahalar dani sosai sannan yace gobe ma ki sake raina ni kindai ga amfani na...
Tare mukayi wanka , kuma kayan da nazo dasu sune na maida , saida na gode masa kamar yadda ya koyamin , shine da kanshi ya maidani gida , bayan yayi parking yace kin yafemin ? Saida nayi shashshekar kuka nace na yafe maka , rumgumeni yayi a jikinshi yace Allah yayi miki albarka , nace amin , kuma wasa nakeyi miki bazanyi wani aure ba , ai babu mai iya haƙuri da halina saike , ina sanki sosai "yar matana Allah ya ƙara miki haƙuri da halina , banyi magana ba ina kallonshi dai , murmushi yayi tare da sumbatar saman bakina , yace yi haƙuri don Allah , banyi magana ba har yanzu , da , da ne nake masa wannan kallon daya zazzaromin ido yace daina kallo , kinyi haƙuri ko ? Ey , tou jeki , kuma ki huta gajiya ngode , yawwa nima ngode na faɗa a dai² lokacin dana fita na rufe ƙofar bam ,
Ajiyar zuciya ya sauke bayan Sultana ta shige , vidion da yayi mata ya kalla sannan ya ƙyalƙyale da dariya yace baiwar Allah An mata , cike da tausayin Sultana da soyayyarta mai girma ya ɗaga mota yabar gidan.
Har yanzu Inna batayi bacci ba , a palo na sameta zaune tayi takurarren zama , Inna har yanzu bakiyi bacci ba ? Na tambayeta , ummmm ta bani amsa ba tare data kalleni ba , kuma cikin yanayin jin kunya dai ta bani ansar , zan wuce ciki ta kirani har yanzu bani take kallo ba ta kasa haɗa ido dani kwata² , ɗazu bakiji ina kiranki ba ? Yi haƙuri Inna banji ba , dama taya zakiji tunda kina so kibi Dikko , shiru nayi ban sake magana ba , tou tsaya kiji ina tsaye wurin ganin na nemo miki mutuncin ki da martabarki harni zan kiraki kiyi kunnen uwar shegu dani kibi namiji a gaban idona ke mara kunya ko ? Yanzun ma shiru nayi mata , idan wani abu ya faru ke kin isa kice Dikko ne ? Munafikin Allah ya saɗaɗo ya biyo dare ya ɗaukeki to ina kukaje ? Kaina na kallon ƙasa nace kiyi haƙuri don Allah ,
Wallahi bazanyi haƙuri ba saidai ki tattara kayanki ki koma wurin Dikko danni babu mai jamin dogon zance da karkata kai ina wallahi² , tunda kina san Dikko kawai kije ki koma amma ki sani idan har shi yayi miki wani abu ko "yan uwanshi karma ki sake kizo min gida na faɗa miki , tunda kika zaɓi Dikko wallahi na bar mishi ke duka , dama ai nace miki idan kika zaɓi Dikko a kaina saidai dani dake kowa yaja tashi da'irar , kin bishi kuma kin dawomin babu takaddar sakin ki , zanyi magana ta dakatar dani ta hanyar dakamin tsawa tana ci gaba da cewa jaka ya ɗaukeki sakarar banza da baki da kyakkyawan tunani , tunda kin bari ya rainaki ya ɗauke matattara sauke buƙatunshi , yazo yayi miki daɗin baki kin kwashi jiki kin bishi amfaninki kawai ya samu natsuwa dake ya samu kuma ya maidoki hoto kawai dake , to sai kije idan wahala ta kasheki kece kika huta idan sun barki kin zauna ɗangin nashi kiyi ta haihuwa suna ɓanɓare "ya "yan ta ƙarfi da yaji , shi kenan kin zama jaka saidai kullum kisha wahalar ɗaukan ciki ki haihu a barki da shan ruwan zafi , In , ki rufemin baki ko inci mutuncinki a daren nan , kuma sai kin barmin gida tunda kin zaɓi Dikko akaina , I , ki rufemin baki wallahi kika sake kamo suna na saina wulaƙantaki , simi² na wuce ciki ita kuma tana cewa ki tattara kayanki yazo ya tafi dake , tunda kinƙi ya sakeki ki aure wanda nake so a cikin maza 4n dana nuna miki.........
Da safe Inna haka ta barbaɗomin kayana a tsakar gida ta rufe ɗakunanta , duk haƙurin dana bata² saurareni ba bayan ta cemin kar na sake naje inda duk wani ɗan uwanta yake , duk saboda ta kirani Dikko yace nazo muje akan me zan bishi ? Kuma itama ai tasan kiran wanda yake gaba tsakanin miji da uwa , kawai dai tana so ta kashe min aure ta auranmin wanda ranta yake so , a cikin mazan da tace na zaɓa su tana da tabbacin daga su har iyayen nasu dashi kanshi wanda zan aurar bazasu wulaƙantani ba ?
Dikko baice baya so na ba , bai wulaƙanta ni ba , tou wai me ma yayi min ne ? Ko sai in kashe auren nawa inzo in zama na Jiddah nima in tashi biyu babu , idan kuma nabi irin nata ra'ayin ita Inna kenan itama ba wannan mijin aka ce ta aura tun farkon farko taƙi aurensa taje ta auri Babana , saini zance Dikko ya sakeni inje inma kashe auren Allah ya jarabeni da fitinar duniya , zawarci ai shima ɗaure yake da ƙugunshi ,
Saida nayi musu rakiya har wurin mota duk addu'ar sauka lafiya da nayi mijinta kaÉ—ai ya ansa ita kuma ko kallona batayi ba , addu'a ta dai su sauka lafiya kuma su dawo lafiya.
Haka na yini a filin gidan Inna har kicin inta ta rufe abinta , ina zaune a ƙofar ɗakinta data rufe kamar asara duk abinda zanyi a bayin tsakar gida nake huɗɗoɗina amma har dare babu abinda naci saboda banda ko si² a hannuna. A ranar yau Dikko bai zo ba , kuma a maƙotan gidan Inna na kwana ganin zan kwana da mai gadi , a gidan ne suka bani abinci naci ,
Washe garin tafiyar Inna ma Dikko baizo ba , kuma ranar ma a maƙota na kwana , saida akayi sati biyu da tafiyar Inna Dikko yazo , ina maƙota mai gadin gidan Inna ya kirani , yauma babu driver ba ɗan rakiya a mota na sameshi zaune daga shi sai wani ɗan kyakkyawan yaro anci mishi gayu cikin wata irin zuƙeƙiyar shadda { getzner } hutu ya zauna a jikinshi sosai , kallo ɗaya zakayi ma yaron kasan gidan kuɗi ya fito daga shiyar manyan mata gogaggi wanda suka san darajar wanka da gayu sai kuka yakeyi , Yaya mu cafi jida ya cire hular da aka ɗora mishi a kai ya riƙe a hannu sam ya hana Dikko yayi min magana ,
Kai ni bazan tafi ba waye yace ka biyoni ? Ni a nan zan kwana , ƙara fashewa yayi da kuka yana ta maimaita suje jida , kashe motar yayi yana cewa muje ciki , taya zan iya faɗa masa Inna ta kulle ko ina ne ? Ah kawai mu zauna a mota shi kuma harya fito da yaron daya zo dashi yasa na ɗaukeshi sai yagushin fuskata yakeyi yana kuka baya co , ƙafarshi ɗaya a waje ɗayar a ciki yake miƙomin wayoyinshi da hular da yaron ya jefar , daka mishi tsawa Dikko yayi yana cewa kai bana san iskanci kaji , shiru yayi yana kallon Dikko yana kuka kaɗan² , saukeshi ya tafi da ƙafafuwanshi , da sauri na sauke shi nima ina kallon Dikko kamar yadda yaron keyi tare da cewa wurin fa a rufe yake....
Tou kije ki buÉ—e yayi maganar hankalinshi nakan wata leda da yake dubawa , shiru nayi na rasa abin cewa , da faÉ—a ya juyo kunzo kunmin tsaye nace kuje ciki zanzo , babu makulli a hannuna , sai a hannuna nake da ? A , a ina nufin bana nan Inna ta fita bata dawo ba , daga Abujar ? Kai tsaye nace masa Ey , da É—an yanayin damuwa yace shikenan ku shigo mu tafi ba tare daya kalleni ba yayi maganar yana gyara zamanshi ya rufe ,
Zagayawa nayi zan shiga motar yaron nan ya fara kuka bana shiga musu mota , Dikko yace kai zan zaneka wallahi , fashewa yayi da kuka yana turani baya , juyawa Dikko yayi bayanshi ya ɗauko dorina yace masa gafara daga nan , cikin kuka yace bata ciga ya matsa baya ya riƙemin hijabi wai basu zuwa dani , da bulalar ya kawo duka yaron ya matsa yana kuka bai sameshi ba sai cewa yakeyi bacu zuwa dani , Dikko yace An mata shigo muje mu barshi a nan , ɗaukarshi nayi na sakashi ciki nima na shiga na rufe , tunda muka ibi hanya Dikko yake faɗamin Mama ta kirashi ta tozartashi iyakar iyawarta , abun bai mishi daɗi ba dan saida tasashi ya sameta har Abuja ta wulaƙantashi hmmmm , cika idonshi yayi da hawaye yace ta faɗi maganganu masu muni a kaina marasa daɗin ji , nayi mata uzirin ɓacin rai nasan duk fushin abinda ya faru ne ta tattara ta sauke a kaina da bansan abinda ya faru ba , ina can ina jinya banma san ina nake ba , ina nan zan barki kizo ki zauna gida har banzo ba ? Da nasan inda kaina yake ko a waya ai zan kiraki tunda gashi ranar dana dawo ai ranar nazo wurinki , kuma ita Mamar da tace ta kirani ban ɗauka ba idan naga kiranta zan basar ne ? Haka nan ma nake kiranta na gaisheta babu ranar da bana kiranta na gaisheta tunda na aureki , tou idan baki saki ba ranar da kika kulleni a ɗaki kika gudu kinsan yadda na kasance a wannan ranar ?
Ba abinda ya dameni da yadda ka kasance har ni kake cema kayi ma Inna uziri idan bakayi uzirin ba me zakayi ? Ko itama haukar zakayi mata ne ? Cikin ɓacin rai yace aike yarinya ce uzirin ne hauka ? Ni nasan darajar duk wanda ya haifi ɗiya ya bani , bawai rashin kunya ko rashin ɗa'a yasa nace nayi mata uziri ba , ina nufin nasan taji fushi da ɓacin rai akan abinda akayi miki na ɗauke Papi ya nuna yaron yana ci gaba da cewa shi yasa kirkina dubu wannan dalilin ya gogeshi na dawo mara mutunci a idonta , to kici gaba da kiran hauka zamu haɗu anjima , shiru nayi ban sake magana ba har muka iso G R A , haka na taho ba abinda na ɗauko daga gidan Inna , kuma bansa yadda sukayi ita da Dikko ba amma tabbas nasan zai faɗamin yadda sukayi da ita har yaje ya taho dani , da yadda ya kasance bayan na kulleshi na gudu , da yadda suka ƙare da Yazeed da Aunty Suwaiba Al ' Ameen da kuma labarin Mardiyya.
Saida Parpy yayi bacci Dikko yasa Ashiru ya maidashi , kuma yau da ya bani maganinshi ban ma yadda nasha ba dan abinda na fahimta ta cikin maganin nan yake haukatamin lissafi , yayi lallashi nace bafa zansha ba , haba An matana dan Allah kisha , Allah bazan sha ba , kar Allah yasa kisha "yar rainin hankali , oho maka dai......
A ranar wasan ba magani akayi shi , kuma ran Dikko ya ɓaci , tunda naƙishan maganin banzarshi , har gari ya waye bai min magana ba sai fushi yakeyi , daya tashi fita ma nayi masa a dawo lafiya bai ansa ba , daya dawo ma sannu da zuwa na ma bai karɓa ba.
Haka dai mukaci gaba da dafa rayuwar , Momy tayi ruwan wulaƙanci da taji labarin na dawo kuma tazo ta zabgaga rashin mutuncin ta iya ƙarfinta , kuma Dikko yaji babu daɗi sosai ya bani haƙuri kuma nayi , Dady kuwa Dikko ya zauna ya warware masa komai kuma Dady yayi ma Momy faɗa yace bataji dai daɗin halinta ba , ɗiyar ɗanta da girmanta ta zauna tana mata ƙarya bata kyauta ba , kuma ya ƙara maimaita mata batayi hali mai kyau ba data raba uwa da ɗanta ta guji ranar da sakayya ta waiwayota , shi dama bai wani ɗauki zafi da Sultana ba Momy ce takaishi ta baroshi kuma yanzu ya gane gaskiya dan haka ya dawo daga rakiyarta.
Gaba ɗaya Dikko ya tsameni daga sabgar "yan uwanshi , biki suna jaje ko mutuwa bana zuwa , yace tunda basa so na kawai inyi rayuwata na manta da sabgar duk wanda baya sabga na , hankalina kwance banda wata damuwa dan Dikko ya hana duk wannan gayyar "yan gidansu zuwa gidanshi , kuma makaranta ɗaya muke da sauran ƙannenshi amma ba wanda suke ɗaki ɗaya ba , ban koma SS a tsohuwar makarantar da Inna ta kaini ba , Ashiru ke kaini yana ɗaukoni , idan kuma Dikko yana gari shine yake kaini yana dawo dani ,
Muna cikin haka ne babbar ɗiyar Rabiya ta kwanta ta mutu , kuma banje gaisuwa ba , mutuwar ta tashi rankatakaf hankalin ahalinsu Dikko , saboda babu wata jinya da tayi lafiyarta lumi tana cin abinci maka'ikan mutuwa ya zare ranta , koda akaje asibiti likitoci sunce tuni ta mutu saima a wurin wankan gawa aka kwakwale sauran abincin daya maƙale a bakinta.
Rashin shigata cikinsu yana musu ciwo Dikko kuwa ya zuƙeni daga cikinsu kwata² , tou rashin zuwa gaisuwar ne ya ƙara basu mamaki , abin ya damesu , koda Momy tace ma Dikko meya hana matar ka zuwa gidan gaisuwa ? Cewa yayi shine ya hanani , dalili Momy ta tambaya.........
Kuyi haƙuri wallahi wayar lumshewa takeyi bata doguwar tafiya yau dasai na ƙarƙare labarin nan amma ku bari mu ƙara ko feji biyu ne ,
18/12/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 89
*_YAHANASU YUSUF A Y RAƊƊA , {{ Mrs TANIMU MUSA QERAU }} yau gaisuwar taki ce ke ɗaya matar Yayana , ina miƙo saƙon dubun gaisuwa ta zuwa gareki tare da addu'ar fatan alkairi , kiyi farin ciki , cikin farin ciki kuma kyakkyawa..._*
Shiru Dikko yayi ya gagara cewa ummm ummm idonshi yana kallon ƙasa ya kwantar da gefen kanshi a gefen kujera kusa da inda Momy take zaune , ita tana sama kenan shi yana zaune a ƙasa , cikin sigar lallashi tace Dikko mace ta fini mutunci a idon ka ko ? Yanzun ma shiru yayi babu amsa , idona biyu ban mutu ba kenan , idan kuma na mutu ka gama da "yan uwanka har abadan duniya haka kayimin adalci kenan ? Yanzun ma a ɗauke yake baiyi magana ba , me yasa daga kai har matarka bakuje wurin zaman ta'aziyya ba...... ???
Ba tare daya ɗago ba yace ai ni naje , sau ɗaya tak kaje fa , ko kana tunanin ban sani ba ko bana ganewa iye..... ? Duk yaran gidan nan tunda akayi rasuwar nan suna gidan Rabiya suna tayata jimamin rashin ɗiyarta , duk wacce ke aure kuma mazansu duk dasu ake zaman ta'aziyya , sai kai zaka kawomin wata sabuwar aƙida a cikin zuri'ata ka warwaremin zaman lafiya ka jefa ƙiyayya a cikin kai da kuma "yan uwanka ? In banda kake ɗan iska yarinyarta ta kwanta ta mutu ba ciwon kai bare na jiki , kuma ba yarinya ba budurwa Dikko kace kaine ka hana matarka zuwa gidan ta'aziyya kuna cikin "yan uban suna nan suna kallonku kuma suna karantarku idan har kuka kuskusara suka ga wata ɓaraka ta fita a cikinku sai sun hanaku zaman lafiya ,
Zaiyi magana ta daka mishi tsawa tace rufemin baki mara kunya , baka san dama ƙufule nake dakai ba ? Ni bana san "yar iskar yarinyar nan bana santa ׳ ko zan mutu bazan so yarinyar nan ba , ƙaton banza ƙaramar yarinya ta maida kai susutancen namiji , har nawa take da zata juyaka sakaran banza marar tunani , tou ita ɗin da kake gani kana iya rabuwa damu saboda ita muɗin dai daka ɗauka ba'a bakin komai ba mune na gaskiyar , ita kana iya rabuwa da ita kuma wata zaka auro , mace ana canja ita amma ni da "yan uwanka baka iya canja mu har abadan duniya , ka saki gaibu ka kama zahiri idan ba haka ba sai kayi dana sani wata rana , da sauri ya ɗago ya kalli Momy cikin damuwa yace kar kiyi min baki Momy , ba baki nayi maka ba , gaskiya na faɗa maka , bani na faɗa ba kaima ka sani kuma kowa ya sani , karuwa har amana ne da ita ?
Karuwa bata zaman aure , sai ka gama gina rayuwarta zata zazzage ka tayi gaba abunta , badai yarinya ka auro ba ? Yarinyar ma karuwa , karuwar ma da bata fito daga tsatson mutunci ba ko ? Hmm addu'a ɗaya ma zakayi karta kashe ka , dan wannan yarinya daga ganin idonta babu Allah a lamarinta kana can ana barbaɗa maka kana tanɗewa , Allah kaɗai yasan iya ƙazantar da take baka kake ci a abinci , layu kuma baka san ta ina kake takasu ba , ka kwanta akansu ka tashi akansu gaba ɗaya ta ɗimauta ka , ka dawo wani sakarai , banajin daɗin ganin wannan ranar Dikko ka cuci rayuwata daka auri karuwa , ka rusa gidanka ka rusa rayuwarka da bayanka , dama mutuwa nayi banga zuwan wannan ranar ba , ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka.
Parpy dake tsaye bayan Momy saman kujera yana wasa da makullin motar Dikko yace , Culcana , shi Dikko ba wai duka yaren Papi yake ganewa ba dan hausarshi bata fita yana tsamin baki , Momy taci gaba da cewa , ina gudar maka irin abinda ya faru da mijin Safiya Ya'u ne , haka mijinta yaje ya auro karuwa , Papi ya juyo ya anshi labarin yana zaro ido cikin tsoro cine Culcana ta yankaci , ya ƙarasa maganar duk idonshi a waje yana nuna yankawa da hannunshi dai² wuyanshi , maimakon Momy tayi ma Papi faɗa tunda ita tana gane abinda yake cewa sai tace Ey mana haka zata yanke Yaya ya mutu shima , dariya Papi yayi yana kallon Dikko , ita kuma taci gaba da cewa hankalinta da natsuwarta bazata zauna lafiya ba harsai taga ya saki yarinyar nan , zata natsu.
Jiddah ce ta shigo palon da sallama gaba ɗaya palon ya disashe duk wani ƙamshin turare da wani turaren wuta gaba ɗaya turarenta ne kaɗai ke tasiri , tafa wanku yadda hankali baya iya hasasowa dan Jiddah "yar gayu ce sosai , murmushi tayi tare da taɓo Perpy tana cewa dan Yaya yazo baza kamin Oyoyo ba ? Da sauri yayi baya yana goge inda ta taɓa mishi fuska , Momy ji abinda Perpy yakemin , Momy tace ai kun saba , Perpy kuma cewa yayi kuma baciyi cau ba , Jiddah tace kam lallai ma yaron nan aiko na haɗu kuma nayi kyau ka tambayi Yaya kaji , daga bayan Momy ya leƙo Dikko yace Yaya aije batayi cau ba , shiru Dikko yayi bai kalli Perpy ba kuma bai ɗago daga yadda yayi zamanshin tun farko ba , a yangance Jiddah tace Yaya barka da yini , yawwa ya faɗa tare da fiddo wayarshi daga aljihu yace Momy zan tafi , da sauri Papi ya sauko yayi gaba kar Dikko ya tafi ya barshi , Jiddah kuma ciki ta wuce tana wata irin tafiya mai ɗaukar hankali , da wutsiyar ido Dikko yabi bayanta da kallo , a ranshi yace hmm mata kenan..........
Momy kuwa taci gaba da cewa , ashe karuwar nan badan Allah ta auri mijin Safiya ba kuɗi aka bata akan ta kaso shi , shi yasa gabana yake faɗuwa kar haka ta kasance dakai , shima kamar kaine dai , da iyayenshi sun hanashi aurenta amma yayi kunnen uwar shegu dasu yaje ya aurota , ashe bai sani ba ajalinshi ya ɗauko , daya aureta dangi suka taso ta gaba saiya tsameta daga cikinsu dama tunda taje gidan bata ma wani yadda tayi ciki ba tunda tasan aiki ne ya kaita , Dikko ni nake faɗa maka wannan labarin dare tabi ta yankeshi ya mutu har lahira , da wuƙa nake faɗa maka , Allah ya jiƙanshi , saida Momy ta ƙara zage Dikko sosai tana farfaɗa mishi manyan illoli game da auren karuwa da kuma haɗarinta , sannan tace ya tashi ya bata wuri sakaran banza da mace ta gama dashi ,
Jiki a sanyaye tattare da damuwa Dikko ya fito daga palon , makullinshi ya ansa a hannun Papi ya faffalla mishi mari yace ya wuce ya bashi wuri idan ya sake biyoshi saiya ci ubanshi , riƙe Dikko yayi ya fashe da wani irin kuka mai tada hankali , danshi Dikko idan dai ranshi ya ɓaci tou saiya rarrabashi kowa ya samu , cikin hayaniya yace sakeni yayi maganar yana zazzaro mishi ido , kallon Dikko yakeyi kuma bai daina kukan ba yaƙi sakinshi , jin ihun Papi ne yasa Momy fitowa tace me yayi maka ne ? Ni babu inda zanje dashi , Momy tace sai kaje dashi , cikin ɓacin rai yace haka zan ɗauki yaro inta yawo dashi a gari kamar wani sakarai , ai sakaranne , shima ya san kai sakarai ne shi yasa yake ganin ka kamar wani abokinshi.
Ni gaskiya babu inda zanje dashi , Momy tace wallahi sai ka tafi dashi , Papi kallon Momy yayi yana shashshekar kuka bai saki Dikko ba , Momy tace sai yaje dakai daina kuka kaji ko.....? Har yanzu ita yake kallo sai kuma ya kalli Dikko bayan wani lokaci , Dikko baiyi magana ba ya buÉ—e mota ya shigar dashi suka tafi....
Momy kuwa palo ta koma cike da ɓacin rai , irin wannan ranar ce take gudun zuwanta kuma gata nan tazo , wannan dalilin yasa taso Yaya tayi haƙuri karta kashe auren Jiddah , gashi tun ba'ayi nisa ba Dikko ya hana kowa zuwa mishi gida , ya tsame matarshi tsam daga cikinsu bare in tazo su riƙa muzanta mata , gaba ɗaya Dikko ya canja hali kuma ya rage masifa ya zama wani ruwan sanyi saboda mace , ita dai Allah ya sani bata san Sultana kuma idan dai tana rayuwa saita raba Dikko da yarinyar nan , dan ta faɗawa wata ƙawarta abinda yake faruwa kuma tana nema ma Dikko auren "yarta amma tace matarshi ta katantane ko ina ta hana wata shiga , ɗiyar Yayarta ma da yake aure itace tayi mata asiri ta tashi hankali saida dai akayi saki Jiddah ta samu natsuwa , kuma saki 3 ne babu damar a koma , ita bata iya wannan ɓatar ba ta neman asiri amma idan zata iya ta fitsare ƙafafuwanta ta fitar da Sultana ita kuma zata sa Dikko ya auri ɗiyarta.
Da ɓacin rai ya dawo gidan , tunda naga yanayinshi banma shiga sabgar shi ba daga sannu da zuwa ban sake mishi magana ba , kuma bai ansa ba , tunda ya shiga ɗaki bai sake fitowa ba , da Papi yayi bacci text ya turomin inje in ɗaukoshi daga ɗakinshi , ko da naje ɗaukarshi faɗa yayi tamin wanda shi kanshi baisan dalilin faɗan ba , waishi yafi ƙarfin mace ta raina shi , haka kuma babu wata banzar macen da zata iya juyashi ko wacece ita , nidai ban masa magana ba na ɗauki Papi zan fita yace idan naje na kaishi inzo , a ɗan tsorace nace ina zan kaishi ne ? Saman kaina zaki kaishi ,
Allah ya baka haƙuri , na ɗauka zan kaishi wurin Ashiru ne ya maidashi , duk yadda kike so haka zakiyi , yadda dai kake so Dikko , to da kinsan wurin Ashirun zaki kaishi zaki tsaya kina tambayata saboda raini......? Tou ki sani jiya ba yau bane ba idan kuma kika ce zaki min yarinta yanzu zakiga yadda zan ruɗa miki rayuwa.
Ajiye mishi ɗanshi nayi zan fita , An mata zo nan , yi nayi kamar banajin shi , wallahi idan kika fita saina zaneki , zo nace , tsayawa nayi ban dawo ba , karki bari na sake miki magana , ɗaure fuska nayi na koma wurin shi , cikin ɓacin rai yace ke har kin isa ni zaki ma baƙin rai ? Wace ce ke ? Ɗaukarshi , ban sake magana ba na ɗauke shi na fita ,
Ina kaishi na dawo , ci gaba yayi da faɗa yana rufe idanuwanshi cikin rashin mutunci , waishi ya gaji da cin zarafin da ake masa akaina , ko aure kanshi farau saidai insan inda zanje danshi ya gaji , da wane rayuwa zaiji da Allah , gani nima mara kunya na raina shi harna faɗa masa , tou ya gaji wallahi saidai in tafi gidanmu , ƙyarma jikina ya farayi gaban ya faɗi , a raina nace na shiga3 Inna ta koreni kaima ka koreni ? Abinda Inna tace tunda na zaɓi Dikko ko zai kasheni karna zo mata gida ta yafe mishi ni duniya da lahaira , cikin rawar murya nace Dikko me kuma nayi maka yanzu....... ? Ba abinda ya dameni ki barmin gidana ni na gaji bana iyawa , kayi haƙuri idan nayi maka wani abu insha Allah bazan sake ba , cikin ɓacin rai ya juyo tare da nunani yace ke............ Ki barmin gida nace ,
Fashewa nayi da kuka nace kayi haƙuri don Allah , bazanyi ba.......... Sai kin tafi daga gidan nan , yau akanki zagi nawa Momy tayi min ? Tacemin sakarai har take cemin Perpy ma yasan ni sakarai ne , ance kin shanyeni tou yau sai kin barmin gidana dan kowa yasan ni ba shanyeyyen namiji bane ba , ya ƙarasa maganar yana ciro bero daga gaban aljihun rigarshi....
Cikin kuka nace haba Dikko me kakeyi haka don Allah ? Ke ni ba mahaukaci bane ba nasan abinda nakeyi ya nuna saman ƙoƙon kanshi , ita Mamar taki kinsan me tacemin akanki ? Ta muzantani ta tozartani me nayi mata ne ? Kayi haƙuri Dikko , naƙi inyi haƙuri tunda kika shigo rayuwata farin ciki yayi bankwana da zuciyata , matsalar yau daban ta gobe daban in fita waje a ɓatamin rai in dawo gida dan na samu natsuwa kimin rashin kunya , ba tattalin miji kwata² baki san darajata ba , kina ƙasa na amma kina nuna ke wata isashshiya ce , wace ce ke ? Wanda kinsan ko a gado nine a samanki duk ta inda aka juya , na bari , hararata yayi cikin fushi yaci gaba da cewa , wane fi'ili zakimin duk wani feleƙenki a tafin hannu a yake , me ma kika iya ? Me kika sani akan namijin....... ?
Shiru nayi ina kallon ƙasa , yaci gaba , kullum ɗaurin zanin ki iri ɗaya ne , tafiyar ma tun wacce na sani , kullum kina nan dunkume ba ranar da zaki buɗe idonki kisan wace irin rayuwa akeyi , babu ilimin zama da miji sai rashin kunya shi kaɗai kika iya mutum ya taɓaki ki ɓare baki kiyi ta wani kukan munafinci , { idan yana kwanciya dani } me kika nema kika rasa ne ? Ni wallahi bana san kidahumar mace , bana san jakar mace bana san ƙazamar mace , idan na faɗa miki yadda nake so kiyi rayuwa dani sai kicemin ina miki cin fuska , me Jiddah tafi ki ne ? Babu abinda takai ki a cikin mata dubu baki kasuwa ba'a fini mata ba amma an fiki sanin zamani , cikin ɓacin rai nace niba kidahuma bace ba , kuma kai kanka kasan ni ba ƙazamiya bace ba , dan kaga ina baka haƙuri kake ganin kamar inajin tsoron rabuwa dakai ne ? Banda ilimin zaman mijin kuma bazan koya ba , idan ka rabani da kanka zan mutu ne ?
Ai saika rubutu abinda zaka rubuta ga biron nan a hannunka , ni ba abinda zan rubuta da biro ajiyeta zanyi saidai in zaneki kikaimin rashin kunya , murus zan kasheki babu wanda yaji babu wanda ya gani , amma yau sai kin tafi gidanku na faÉ—a miki , bazan tafi gidanmun ba , wallahi babu inda zanje , cire kayanshi yayi ya nufi toilet yana cewa shi yasa duk namijin da yasan abinda yakeyi wallahi bai auren yarinya , kullum kaida mace faÉ—a cikin gida , ai kasan inda ake auro manyan mata kaje ka auro mana , shigewa yayi bai sake magana ba , ni kuma naci gaba , banyi shiru ba har yayi wanka ya fito.
Yana fitowa yaci gaba , ina ma amfanin mace ba soyayya , kije cikin matan gidanmu su koya miki yadda ake tattalin miji , ki koyo yadda ake rainon miji , a koya miki kissa su koya miki wanka da saka sutura tunda ni kin raina ni , Nabeela zata koya miki yadda ake tafiya a gaban miji je kiga yadda suka wayar da Jiddah suka buÉ—e mata ido baki ajiye komai ba sai girman kai , da raina miji , kin É—auki miji kamar wani sa'arki ina magana kina É—aga min murya sama sai kace kece kike aure na.
A daren yau saida ya tabbatar ya ɓatamin rai harsai da nayi kuka ya jagulamin lissafi tas , sannan yayi shirinshi yana gama shiryawa ya wurgamin kuɗi a saman gado shi ya tafi Abuja kuma kar in sake zuwa makaranta saiya dawo , binshi nayi ina kuka , kila tausayi na bashi ya tsaya ya rungumeni yace An mata bakijin magana wallahi , cikin kuka nace Dikko dan Allah na bari , na faɗa ina kallon idonshi , riƙeni yayi sosai a jikinshi , a hankali ya duƙo saitin fuskata cikin magana mai saukar da kasala yace yi shiru , ya ƙarasa maganar yana tsareni da kyawawan idanuwanshi , rufe bakina nayi ina kallonshi , buɗe bakinshi yayi , yayi wani iri da harshenshi kaɗan yana wasa dashi sannan ya kirani da harshen nashi ,
Saida na sauke ajiyar zuciya cikin shashshekar kuka na riƙe jikinshi tare da shiga bakinshi da nawa , kullum idan zaimin wani abu yakan canja min sabon salo ne , nayau daban , na gobe ma zaizo da baƙon salo , ya ɗauki wasu "yan ƙalilan mintuna sannan ya sakeni daga jikinshi , ƙara riƙeshi nayi ina kuka nace dan Allah karka tafi , ba tare daya kalleni ba yace ki bari sai kin iyo riƙe namiji a gida sai ki riƙeni in zauna , inaji ina gani yayi tafiyarshi....
Ɗakinshi na koma na faɗa saman gado ina kuka , nidai Allah ya sani banda wannan idon tsakiyar kai irin na gogaggin mata , ko a can baya dana riƙa iskancin nan ba'a hayaccina nayi ba , ina naje ina aka sanni ne ? Wa na gani waya ganni ? Ban taɓa haura Katsina ba daga Daura sai Katsina iyakata nan , kenan tunda akayi min sauka aka sauke duk wani sheɗanci dake saman kaina , tou me Jiddah tayi wanda yasa Dikko yake faɗamin ita a magana harso 2 ? Duk yadda akayi kila yaga Jiddah ta burgeshi ne , shidai Dikko yana san gogaggiyar mace , mai tafiya da zamani , wacce ta waye sosai idonta ya buɗe da duniyanci amma a gidan aure , ƙwanƙwasashshiyar mace a fagen tarairayar miji , "yar duniya da tasan logon maza , wacce ta shahara ta kuma ƙware a wurin iya wasan danbe ,
Tou ba Dikko kaɗai ba duk mazan zamani mata haka suke , gadai Jiddah an saketa amma tunda tasan yadda yake san mace ta kasance ta kasa sanya , kullum a riƙe take , irin su Jiddah ne matan da idan namiji ya sakesu zasu kashe shi da bariki shi kuma yaci gaba da zagayawa kina gida kwance kamar asara ana can ana hidimar duniya babu ke , yanzu zamanin nan duk inda kika nufa mazan sun zama iri ɗaya ko wane baya san afi matarshi kuma basasan baƙauya ko ƙazamiya , wallahi duk kyanki duk tsarinki duk iya haɗuwarki duk irin sigarki da nagarta da kike da , idan dai baki da gayu baki da wayewa baki iya girki ba tsafta da ilimin zaman aure ke hoto ce , hoton ma elajiment da zaran an liƙaki a bango an gama dake , tou haka macen da bata san damarta ba take wurin mazan zamani , baki da wani amfani saidai ki share gida kici abinci , idan kuma kikayi sa'a da ɗan duniyan namiji kina nan sake da baki kina ta rashin wayanki yana can shi kuma yana miƙa kuɗinshi ana sashi a ɗaki , duk hidimar da miji yake miki zata ragu tunda masu ci sun ƙaru , gaki ke matar gida ga matan bariki , yake "yar uwata me akafi ? Wane duhun kai kika tsaya ? Tou rayuwa ta canja , zamani ya juya keda mijinki kina ji kina kallo makwaɗaitan matan bariki zasu ɓanɓare miki miji ta ƙarfi da yaji ,
Dan wallahi wasu mazan basu iya ba koya musu akeyi , wasu kuma dama can jarabar a jininsu take , wasu abokai ne suke kaisu su barosu , wasu kuma matan nasu ne da kansu suke yanka musu tikitin shiga bariki, idan kikayi masa magana ya daina kwanciya dake in kinci sa'a ya faɗa miki illolinki idan kina da rabo saiki gyara , idan kuma kin samu namiji mai zafi ya buɗe miki ita tsaye yace ake ƙazamiya ce ba wanka ba gayu ba shafa turare haka zai dosoki kina ƙarnin hayaƙi ko zufa ko zarni fitsarin yara , ke kuma sai kiji haushi an faɗa miki gaskiya ki masa rashin kunya , idan akaci sa'a da irinsu Dikko su zaneki a barki da kunburaren jiki , ke kuma fuuu kinyi yaji daga nan matsala ta samu hanyar shigowa , mata mace ƙwalisa ce ita , fulawa ce bata rayuwa saida gyara , zamanin ga ya lalace idan kuma kika kwanta tou fa lallai kinji a salansa , bawai ina nufin ki tashi ki nemi asiri ba , a , a ki tashi ki gyara domin zamanin yazo da sabon salo.
Tunda Dikko suka ibi hanya saidai yayi tsoki , Sultana fa ga mace har mace komai yaji , ga kyau , ga siga , nagartacciyar mace gata tayi dai ko ta ina baka isa ka kusheta ba inba hassada ba , ga ƙugu An mata , ƙaramar yarinya da ita amma Allah yayi mata zubin bodi irin na manya mata , saidai ɗanyen kai ya hanata ta fuskanci damuwarshi , wace ce Jiddah ? Wace ce ita idan An mata tana nan ? Gaskiya An mata kyakkyawa ce , mace ce ta tsara , fitacciyar mace mai kyakkyawar halitta , bakinta mai kyau , tana da tsarin haƙora masu burgewa kuma tsaftatacci , tayi sosai gaskiya saidai matsalarta yarinta , zuciyarshi ce ta bashi haƙuri cewa shekarun Jiddah da Sultana ba ɗaya ba , inda Jiddah taje Sultana bata je ba , ƙawayen da Jiddah keda su ba irinsu An mata take da , ba wani , yaran ƙauye ai basu kai An mata ba ake musu aure kuma lumi suka riƙe miji babu mai ji , saishi ko kwanciya zaiyi da ita saida "yan dabaru , zuciyarshi dai haƙuri take ta bashi akan cewa idan Sultana ta goge wallahi shi kanshi saiya zama swry ya kwantar da hankalinshi da sannu za,azo wurin......
Wayarshi ya É—auka tare da tura mata text , taje makaranta , sai kuma adireshin { address } in gidan Rabiya taje mata ta'aziyya , sai izinin hawa mota da inda zata É—auki makullin saboda Ashiru bashi nan , hada lambar { number } Momy ta kirata tayi mata gaisuwa , kuma daga makaranta gidan Rabiya karta je ko ina......
Saida safe naga saƙon Dikko bayan nayi sallah asubahi zan koma bacci na gani dana ɗauki wayar , ban ce masa na gani ba kuma ban kirashi ba nima na basar da lamarinshi , da ya tafi saida yayi wata ɗaya da sati biyu kuma har yaje ya dawo banyi waya dashi ba , koya kirani ma bana ɗauka kuma banje gaisuwar ba , kuma kuɗinshi a inda ya wurgasu a gado ban taɓasu ba banma ko kalli inda suke ba , yadda yabar ɗakin haka ya dawo ya sameshi , ya cancara ruwan rashin mutunci a daren nan saida yasa ni na gyara ɗakin na goge ko ina da ina yace kuma tunda banda wayau kar in sake zuwa mishi ɗaki , ni kuma abinda ya ɓatamin rai dashi da yace wai me Jiddah tafi ni ne ? Ashe ma kallonta yakeyi , sai kuma abun ci baya waini zanje Nabeela ta koyamin yadda ake tafiya a gaban miji , inje inga yadda suka wayar da Jiddah suka buɗe mata ido , wato ni ban iya komai ba ? Shine abinda ya ƙonamin rai nake zuciya tunda ya tafi har ya dawo kuma ban huce ba.
Fita nayi daga É—akin ya biyoni yana cewa ko zaki mutu saina faÉ—a miki gaskiya duk duniya baki da wanda ya isa ya faÉ—a miki iskan nan mai kaÉ—awa saini , ko yayi miki daÉ—i ko yai miki zafi saina faÉ—a , ke ni har zaki nunamin fushi ? In banda iskanci ni zaki barma É—aki har inje in dawo yadda na barshi haka zanzo in sameshi , nace kije ma Rabiya gaisuwa shine baki je ba kuma bazaki ba inyi duk abinda zanyi , zama nayi a gefen gadona nidai na rasa abinda yakemin daÉ—in duk an jagulamin lissafi , wayata na É—auka ya fizge wayar ya bugata a bango duk ta tarwatse yace ina miki magana zaki latsa waya , nace kije ki koyo zamantakewar aure idan kinji fushi ki koyo saiki zauna lafiya.
Ke in kina da hankali ma har ni zakiyi gaba dani ? Nine nake aurenki ko kece ? Ni zan kiraki a waya ke a dole kinyi fushi , tou ƙarya na faɗa ne ? Ba komai cikin wannan sakaran kan sai wauta da yarinta , idan kinga dama ki shirya zamu fita , yana faɗin haka ya fita abunshi.
Goge hawaye nayi cikin ɓacin rai , duk duniya babu wanda ya cuceni sai Inna , ko waya na kirata ta daina ɗauka , gata a raye Dikko yake iƙirari shine kaɗai zai faɗamin gaskiya , tabbas shine zai faɗamin , zanji fushin na iya zamantakewar zama dashi dan mu zauna lafiyar.....
Ya daɗe sosai sannan ya dawo ɗakina , yasha gayu cikin sigarsu ta "yan gayu , nima nayi wanka na shirya amma daya shigo saida ya gyaramin diresin , yana cewa saura in munje ki saki baki kita surutu ko yawan murmushi , daga ina yini Allah ya jiƙanta kika sake ko kallon wani muka dawo zan kulleki a ɗaki.
Shine a gaba ni nake bayanshi bayan ya gyaramin tafiyata muka fita , 9:32pm a palon Rabiya tayi mana , kafin ta fito saida tasa aka fara tara mana "yan abubuwan taɓawa , Dikko ya nunamin ko ruwa nasha muka koma gida saiya ɓatamin rai , yana tsaye wurin ganin ya siyomin mutunci amma ni bahaguwar kwanya gareni ,
Bayan wani lokaci ta dosa , ƙarar takalminta kakeji a saman tayils ƙwas׳ , ƙamshi yayo gaba ta bayyana a palon sai isa takeyi mijinta na biye da ita , saman kujera mai zaman mutu 3 { 3sieter } suka zauna , mu kuma muna saman 2sieter , gaisawa aka farayi nima na gaisheta tare dayi mata ta'aziyya , ta amsa dai cikin sakin fuska , daga haka ban sake magana ba , sukaci gaba da firarsu , bamu wani daɗe ba muka tafi , kuma Rabiya tace ko ruwa musha Dikko yace an gode , tace tana zuwa kila wani abu zata bayar yace ai zamu dawo ,
A mota ne yake cewa kaje wuri ana marmarinka ka tafi kafin ka fita ran mutane , kin gani dai ko ? Dare ne muka je amma kallarta shirye , tsakanin palo da bedroom sai an saka takalmi masu kyau , kana doso miji yasan ka taho , amma ke duk babu wannan takalmin ma "yan maraÉ—i kike yawo dasu babu wani notice saidai kawai mutum ya ganki , har muka isa gidan gwamnati Dikko faÉ—a yakemin , kuma saura idan munje canma inyi surutu ko inci wani abu Jiddah tana nan idan ta barbaÉ—eni ba abinda ya dameshi ,
Daga gidan Rabiya har gidansu babu abinda na kalla kar yacemin na cika ƙauyanci , a kame nake dan nima ba sakara bace ba , amma a raina inajin daɗi , tunda Dikko yayi parking su Nabeela suka yo waje har Papi shima baiyi bacci , duk sannu sukayi mana , Papi kuma ya tafi wurin Dikko yana oyoyo , hannunshi ya kama sukayi gaba Papi yana bashi labari shidai baya gane yarenshi.
Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji lokacin da idona ya sauka akan Momy , kai uwar Dikko "yar gayu ce , ta haɗu ׳ , Allah yayi mata kyau sai kuma ya haɗu da hutu uwa uba kuma gayu , kamar yadda Dikko yayi nima a ƙasa na zauna jiki a sanyaye sai mulki Momy ke zubawa , kai Momy tayi wallahi ta haɗu "yar gaye ce first class kuma ko a ajin ma itace ta gaban benci , bayan sun gama gaisawa da Dikko nima na gaisheta , saida ta mula tasha iska bayan ta gama kalleni tas sannan tace lafiya qalau , ƙannenshi suka shigo wanda muke karatu dasu makaranta ɗaya , wai me yasa kwana biyu banje sch ba ? Saida na kalli Dikko sannan nace musu ba komai , su jina suke kamar wata ƙawarsu dan haka sukace inzo muje ɗakinsu suma ,
Momy tace bazata je ku koya mata kilbibi ba , Dikko yace Momy ki barta suje , kasan yaran gidan nan munafukai ne basu aje komai ba sai kilbibi da gulma idan suka ɓata maka mata da tsigudidi ka huta , Nabeela tace matar Yaya zo kiji , ta leƙo daga ciki tana kirana , kallon Dikko nayi , da girarshi ya nunamin inje wurin Nabeela , tare da sauran masu cewa naje ɗakinsu duk muka runguɗa ciki , muna shiga suka ciremin kallabi suna ganin gashina , Nabeela ta ɗauko abin taje kai ta fara tsigarmin kai , wai ince ma Yaya zan kwana , nidai banyi magana ba , sune sukayi ta surutu nima ina so ince wani abu amma Dikko ya hanani magana dole nayi shiru , Jiddah kuwa yanzu ta shigo ta fara masifa wai anzo ana ciccira musu datti a gado , ganin babu wanda yabi ta kanta ta koma palo ta faɗawa Momy amma sai Momy tace idan mun gama an gyara ,
Nan Dikko ya barni yace zaije ya dawo , Momy ma ciki ta dawo bayan fitar Dikko , kuma bata wani ji ƙanƙamina ba , ganin Dikko ya tafi yasa ta kora duk wanda ba itace ta haifesu ba , tana satar kallona lokaci² irin kallon nan na gefen ido , itace ma tayi ma Nabeela faɗa ta rufemin kaina saboda dare , shine Nabeelar tace muje ɗakinta , Momy tace bazanje ba ,
Har 11:46pm Dikko bai dawo ba , ni kuma na gaji ni bana san irin kallon da Momy kemin kila kuma karatu na takeyi , kallon Nabeela nayi tare da riƙe hannunta nace nidai muje ɗakinki , Momy tace muyi zamanmu , sai kuma take tambayata bayan gidan Rabiya sai ina Dikko ya kaini , nace sai nan , zai kaini gidan Yayarshi wacce yake bi itama inje in mata ta'aziyya nace to , wai kuma duk abinda akayi in riƙa zuwa idan ba haka ba babu wanda zai sanni nace tou ,
Sai 1 saura Dikko ya dawo kuma Nabeela tace masa in kwana yace a , a , itace ta anshi Papi ni kuma muka wuce gida , tun daga wannan ranar ina zuwa gidansu Dikko amma tare dashi , idan kuma anyi wani abu biki ko suna Nabeela take zuwa ta tafi dani ko Dikko baya gari , basa dai min wani gani² ko habaici , amma Jiddah idan muka haɗu sai tacemin ga irin asiri wai na mallake dangi miji , bana tanka mata tunda dai Dikko ya gargaɗeni da baya san inje in zama ɗaya dasu na riƙa kama kaina banda yawan surutu banda yawan dariya , ba ruwana da sabgar kowa , kuma kar in kuskura na riƙa shiga sabgar Jiddah.
Shigata cikin familynsu Dikko yasa na gane banbanci tsakanin "yan geto area da boti sayit , na gane matsayin wanka kuma na gane shima kanshi wankan iri² ne , na gane matsayin gayu kuma nasan nawa gayun an daina yayin irinshi , na zubar da gayun rayuwar baya dan na ɗauki sabon darasin wanka a wurin wayayyin mata , lokaci guda kaina ya fara hayaƙi nima na fara fizge² , idona ya fara wayewa , akwai banbanci tsakanin wayewar talauci arziƙi da kuma rayuwar lingu , ko a karuwanci ashe iri² ne nawa da nayi a baya wahalallen karuwanci ne , Nabeela tana taimako na tana shiga dani wuraren da tunda nake ma bansan akwai su a cikin garin Katsina ba sai su masu kuɗi , kai talaka ya rayuwar haƙuri ? Talaka bawa alere dangin jakki ka mutu gobe a sake sabo , da nasan zanzo irin wannan rayuwa da ban ɓatawa kaina lokaci ba wurin shirmen da nayi a baya , wanda bai haifa min komai ba sai ɓacin suna , karuwancin wahala ya bugamin tambari mara goguwa , kai kuɗi na inda suke gayu wayewa da buɗewar ido na gidan gwamnati , idan taƙamarki wanka sai kin gama wankuwa har kin gaji , idan kika tunkari ahalin Dikko sai kin raina kanki ,
Nidai ban sani ba , shin Dikko yayi magana da "yan gidansu dan su ɗago rayuwata ko kuwa sune suka ga ya kamata su wayar dani oho musu , nidai dama can gaskiya bawai wata kidahuma bace ba saidai kunsan wayewar kuɗi da talauci ba iri ɗaya bane ba , kawai dai ciwona rashin ganewa a boko shine ciwo na tou yanzu ina ganewa kuma na iya , rabon da muyi faɗa da Dikko harna manta , shidai burinshi ya samu natsuwa cikin kulawa da soyayya kuma kullum nazo masa da baƙon salo , na jiya ba irin na yau ba , na yanzu daban na anjima ma yazo a baƙo , kuma karna gajiya da sauri shine dalilin yasa yake bani magunguna dan na ɗauki buƙatarshi har ya samu gamsuwa ba tare dana gaji ba , na zama jajirtacciya mai juriya a fagen tsakiyar filin wasan danbe , sai kuma biyayya shi mutum ne mai san ka bashi girma , yana san girma sosai kuma yana so ka girmamashi , saboda san girmanshi yasa Rabiya ke zaulayarshi cewa saida tayi aure ma yazo duniya , kuma shi mutum ne mai san godiya , yana san godiya akan duk abinda yayi maka , sannu da zuwa idan ya dawo cikin soyayya rakiya idan zai fita da addu'ar Allah ya dafa mishi akan duk abinda yasa gaba na alkairi , yawan damuwa da rayuwarshi ta hanyar yi masa waya idan baya nan , sai kuma idan yana gari bana zuwa ko ina sai makaranta shikenan matsalarshi.
Inna kuwa har yanzu babu ruwanta dani , ko gidanta mukaje dani da Dikko haka zata watsar damu sai mun gaji da zama mu tafi , dan dama Dikko shi komai rayuwarshi na dare ne yakeyi kamar mara gaskiya , shi yasa ko gidan Innar sai dare muke zuwa.
Ita dai yanzu Momy bata da sauran ja tunda tayi karatu na kuma ta fahimci rayuwata , kawai dai tayi ma Dikko addu'ar mu zauna lafiya , ɗiyar ƙawarta kuma da taso ta aurawa Dikko ashe itace karuwar bata sani ba , can wata ƙawarta ta faɗa mata yarinyar nan da take nemawa Dikko fa batajin magana har ciki aka zubar mata kwanan nan , sai ta zauna tayi karatun ta natsu tare dayi ma Dikko addu'ar su zauna lafiya da Sultana , sai kuma tayi hangen idan Sultana ta tafi bata san wace surukar zatayi ba , shine suke lallaɓa Sultana a jone , a taƙaice dai kawai ta gane idan bata share masallaci ba aradu kasuwa zata share hada mofin ,
Amma duk da haka nan dai yana nunamin nesa² dai , danshi yasan "yan gidansu yanzu sukeyin ka anjima su sauke ka ƙasa , Dikko dai yana tsaye kullum yana ta kwatanci yana ɗorani hanya , idan yaga na lauye nan zai ɗagoni ba faɗa ba ɗaga murya , zaice wannan da kikayi ba haka akeyi ba , haka zakiyi , zama dai nayau da gobe idan kuma yayi min wani abu nayi fushi , zaicemin ba'ayin fushi da miji kuma ko nayi miki abu ya ɓata miki rai ki riƙa haƙuri ba komai ne zakiyi fushi akanshi ba , rayuwa juyawa takeyi ba kullum akeyin farin ciki ba , kuma shima kanshi ba kullum zan sameshi yanajin haƙuri ba idan na hawoshi yana ɓacin rai ba abinda ya dameshi kawai zai zaneni ne kuma inyi masa godiya idan ya gama , wannan shine ake cema yau da gobe...
Ina shiga ahalin Inna sosai , duk abinda akayi ina zuwa , idan Dikko yana nan Ashiru ke kaini , idan basa nan ni zanje da kaina , idan yana Katsina da abokinshi Abbakar suke fita ni kuma a barni da Ashiru , idan kuma zai bar gari tare suke tafiya gaba ɗayansu , masu gadi da sauran masu hidimar gida ake bari , dan yanzu Dikko baida lokacin kaini wani wuri kuma ko yana gari nima kaina wahalar gani yakemin suna can wurin siyasarsu zaɓe yazo sunƙi haƙura su fita wasu su shiga , itama Momy bata zama suna can basa nan basa can hada Jiddah ake zuwa , niko banma ga fuska ba bare ince ko so ɗaya naje naga yadda akeyi , hmmmm Dikko ? ׳ halinshi saishi.
Gidan Sultan ma duk abinda akayi ina zuwa , amma ni Dikko baya bari na zama wuri , mintuna 15 shine nawa idan na fita , idan yaji dani 25 ne , makaranta kaɗai nake zuwa na daɗe , nidai bansan dalilinshi na wannan tsarin ba , ko gidan Inna idan naje shima haka ne , ni idan tana gari ina zuwa dan wallahi shi yanzu ya daina zuwa gidan kwata² , haka zamuje yaita gaisheta tanaji tana kallonmu tai mana banza , shi kuma tsakani da Allah ya bita² harya gaji idan kuma zamu tafi taita zagin Dikko tana aibatashi , shi yasa ya daina zuwa , tun kana da mutunci a idon siriki yana jin nauhinka har kazo kayi abinda zaka fita ranshi haba ina ma amfani da Allah..............?
Sati biyu rabon da nasashi idona sai yau a asibiti , yazo ganin Kaka nima Ashiru ya kawoni muka haɗe , kuma shine ya iskeni , yana shigowa nasa takalmina nayi gaba ina jirashi waje , koda ya gama abinda yakeyi bansan ta ina aka ɗaukeshi ba kawai ya ɓacemin saida na ga an hau motoci babu shi , na koma ko an barshi ban ganshi ba , nima sallama nayi musu na wuce gida raina ɓace , kuma shi ba waya yakeyi ba saida ya turo text.
Duk yadda na kasa na tsare a ranar ban ganshi a gida ba , washe garin ranar ma baya nan , wata washe garin sai naji shi kawai ya halba Abuja bansan abinda yajeyi ba , kwanashi biyu ya dawo , ina makaranta ya dawo kafin in dawo harya bar gidan , naji babu daɗi dan haka na zauna na zuƙa mishi zuƙeƙen text nace kana can kana yawon kamfen ka manta da yankin iyalinka , waini waye ya faɗamin shi yawon kamfen yakeyi ? To nidai koma me kakeyi ina san ganinka , gani nan zuwa......... !
22/12/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 90
Bayan na gama dubawa ajiye wayar nayi na nufi madafar abinci dan samawa cikina abinda zan bashi , ko uniform ina ban cire ba yunwa nakeji sosai kamar zan faɗi , Dikko kuwa bai wani daɗe ba yazo , kicin ya sameni wai gashi yazo ta ina zai fara kamfen in a yankin iyalin tashi , yayi maganar yana murmushi , dariya nayi sannan nace kaima sai kawai ka kama kayi wani tafiyar ka abunka , gaba ɗaya ka wani manta dani na ƙarasa maganar ina shiga jikinshi ,
Dariya yayi cikin izza ya riƙe ƙuguna yace yi haƙuri An mata , naƙi inyi haƙurin , nine zahiri bakiyi ba tunda har kin faɗamin magana , wai na manta da yankin iyalina banyi kamfen ba , dariya kika bani nace tou ? 🤔 bari in rugo kar aƙi bani ƙuri'a ranar zaɓe , wannan "yar yarinya har tayi ƙorafi gaskiya Dikko bai kyauta ba. Ey mana inata jin babu daɗi na zama kamar wata marainiya dubeni da Allah duk na wani zama abin tausayi , na ƙarasa maganar a shagwaɓe ina kallon idonshi da yanayin kallon da yake so , murmushi yayi tare da lumshe idanuwanshi yace An mata......... Ya ƙarasa maganar yana sumbatar bakina.
Fita nayi daga jikinshi na juya da niyar tafiya inda na ɗora girki , riƙo ƙuguna yayi ta baya yana jawoni jikinshi , ai ƙarya kikeyi bayan nazo kamfen , da Allah ka ƙyaleni yunwa nakeji , taɓe baki yayi tare da ɗaga gira yace , tou ? Ya faɗa cikin yanayin mamaki sannan yace , idan nayi tafiyata karki sake kirana kice inzo kamfen , tou ka tafi mana sai me.... ? Juyawa yayi yaɗanyi tafiya , inajin ƙarar takalmin shi , na juyo a dabarance naga shin da gaske tafiyar zaiyi , ina juyowa muka haɗa ido , dariya yayi tare da cewa yes 💪🻠, da baki juyo ba dana tsaya amma kinga tafiyata , da za'aimin yanga a wani latsani sai Allah ya kamaki nima saina rama , yana faɗin haka ya fita daga kicin in da sauri , kashe gas in nayi na bishi nima da sauri , ɗakinshi ya wuce yana dariyar mugunta.
Lokacin dana shiga harya cire agogon hannunshi , da farin ciki ya rumgumeni wai oyoyo An mata , ya faɗa yana tsuke bakinshi tare da lumshe idanuwanshi yana ɗan kaɗa kanshi cikin yanayin shauƙin so , ya riƙeni sosai a jikinshi , murmushi yayi mai sauti ya sake maimaita wai kana can kana yawon kamfen ka manta da yankin iyalinka , kai An mata , tou ya akeyin kamfen a yankin iyali ya ƙarasa maganar yana haɗa idanuwanmu wuri ɗaya kowa yana kallon kowa , bayan wani lokaci yace caf aiko lallai nan ne ya kamata inyi kamfen muje a gama abincin inci nima in ƙara tsatsubo ƙarfina.
Bayan mun koma ya zauna a saman matakalar da zaka shiga kicin yana yanka albarsa , da yaji azabar yaji yace kai ban iyawa anshi harna yanke , kawo dai in miki wani abun wannan wahala ji naji ciwo yana nunamin inda ya yanke tare da goge idonshi yace wai wahala , nidai albasar zaka yankamin , ke ban iyawa kinji , nima ban iyawa saidai a dafa abincin ba albarsa , ai yama fi daÉ—i yi sauri ki gama.
Ciki ya shiga yana wanke hannunshi wayashi ta fara ringing , ni yasa na ciro mishi ita daga aljihu , dana faɗa masa Momy ce da sauri ya anshi wayar tare dayin sallama , bansan abinda Momy tace masa ba saidai yanayin idonshi ya canza zuwa launin ja , ya tsareni da kallo har naji tsoro ya kamani , gani nan zuwa ya faɗa tare da fita daga kicin in cikin tsananin ɓacin rai , ajiyar zuciya na sauke tare da cewa Allah ya tsare hanya , bai ansa ba ni kuma naci gaba da abinda ya shafeni.
Hankalin kaf "yan ɗakinsu Dikko idan yayi dubu ya tashi har Momy gaba ɗayansu sun hallara a bedroom inta sai koke² sukeyi , wai Jiddah ta bawa Perpy fiya² a lemu , Dikko yayi tashin hankali shi ba kanshi yakeji ba An mata yake tausayi , yasan zata shiga damuwa duk da tana nuna kawaici da kara akan yaron amma ai tana san ɗanta kodan bata fito ta faɗa ba ? Yarinya mai kunya da kawaici waye ma zaiyi irin haƙurin da An mata tayi ? Idan da wata mara kunya ce aka ɗauki ɗanta ba uwar miji ba ko uwar waye sai anyi tashin hankali , Allah kaɗai yasan ciwon da takeji akan rashin Papi baya kusa da ita , amma bata taɓa faɗa ba bata kuma taɓa nunawa ba , koshi bata taɓa nuna mishi ba daɗi ba akan rashin Papi , ta daiyi haƙuri tabar ma ranta , kuma babu wanda yasan ina ma Jiddahr tayi , Dikko kuwa cewa yayi shi baiga ma duk dalilin wannan fitinar da tashin hankalin da yasa aka ɗauko Papi ba , mema yasa tun farko aka ɗauko yaron daga wurin An mata , shi ina zaisa ranshi ? Wane hali rayuwar Sultana zata shiga ? Gaskiya fa ba'ayi ma rayuwarta adalci ba , me yasa ׳.............. ? Wallahi idan har Papi ya mutu saiya kashe Jiddah , sannan shima ya kashe kanshi dan wallahi yana jin kunyar An mata.
Shima Dady cikin tashin hankali ya iso , ganin Dikko yana kuka yasa Dady shiga wani irin mawuyanci hali , yace Babana yi haƙuri ka daina kuka , a shagwaɓe Dikko yace kuka Dady ? Ai yanzu ma na fara , yi haƙuri Babana zai samu sauƙi bazai mutu ba , ya faɗa yana kallon idon Dikko cikin yanayin shi Dikko ya tausaya mishi , Dikko yace haba Dady misali nine a irin wannan yanayi nayi imani kai da suma zakayi , yadda kakejin ni nine zuciyarka ya nuna kanshi , sannan yaci gaba da cewa nima uwarshi itace zuciyata , idan har yaron nan ya mutu , An mata ɗan ƙaramin hauka zatayi , wane irin hali kake tunanin zan shiga idan ta shiga wani hali ? Idan na shiga wani hali kaima shiga zakayi , kana shiga Momy ta shiga , Momy na shiga kaf "ya "yanta sun shiga , na rantse da girman Allah idan yaron nan ya mutu tou tabbas nima mutuwa zanyi dan bazan yadda inga tashin hankalin da An mata zata shiga ba , saina hau saman bene zanyo ƙundubala kuma nima saina sha fiya²n in faɗo matacce........ Yana faɗin haka ya fita yabar ɗakin.
Cikin damuwa Dady yake kiran Dikko , Babana² , amma Dikko yai tafiyarshi , hankalinshi kuma ya tafi wurin Sultana da tace masa yana can yana yawon kamfen ya manta da yankin iyalinshi , dole yaje ya bata natsuwa duk haƙurin ta saida ta cire kunyarta ta nemi haƙƙinta wurinshi , itama Jiddah sai yaci uwarta idan ya riƙeta babu wanda ya isa ya tashi hankalin An mata idan dai yana numfashi , ƙaramar yarinya mai haƙuri , ai haƙurin An mata yayi haƙuri ko sai an kasheta ne wai............?
Cikin wani irin ɓacin rai mai tsananin ɓaci ya dawo , ni bana san ganinshi a yanayin fushi tsoro yake bani wallahi , tunda na gama abincin banci ba naje nayi wanka ina zaune ina zaman jiran dawowarshi , sannu da zuwa nayi mishi bai amsa ba , saida yazo dai² inda nake zaune yaja hannu na har zuwa ɗakinshi kuma baiyi magana ba.
Dakel ya rufe ƙofa sannan yazo inda nake tsaye ya fara cire kayan jikina , kallonshi nayi cikin damuwa nace baka da lafiya ne ? Baimin magana ba yaci gaba , saida ya saukeni duka sannan ya jani zuwa bakin gado , da hannu ya turani na faɗa sama ina kallonshi , bargo na ɗauka na rufe jikina tare da saukowa ina matsawa inda kayana suke nace masa ka barshi kawai ngode , yaye bargon yayi tare da maidani saman gadon , ban sake saukowa ba , a damuwance shima ya hau gadon , har yayi abinda zaiyi ya gama baiyi magana ba kuma bai wani nuna yanajin shauƙi ko farin cikin kasancewa dani ba , kuma duk fushin da yakeyi bai hanashi maidai nushi ba , ya maida duka sosai , saida ya tabbatar na samu natsuwa kuma ya bani natsuwar da farin ciki da ƙoƙari ba wani lalaci , saida ya tabbatar nakai sosai sannan ya barni , ya rigani yin wanka , yana fitowa ya shirya , godiya nayi masa tare da masa addu'ar Allah ya ƙara mishi lafiya kuma ya bashi wata lafiyar a fagen wasan danbe , yayi nisan kwana mai albarka , baiyi magana ba ya shirya ya fita daga ɗakin amma duk wayoyinshi a nan ya barsu kila ba fita zaiyi ba.
Bayan ya fita nima na gyara jikina na fito , palon ɗakinshi na sameshi zaune saman kujera ya kwantar da kanshi saman hannun kujera , ina fitowa ya fara faɗa wai ba ya hanani wannan ƙazantar ba ? Kodai in rabo kayana ɗakinshi da nawa , yana nufin in ibo wasu in ajiye a ɗakinshi , ko kuma duk lokacin da zanzo in riƙa tahowa da wasu kayan , daga yau bazai sake min magana akan idan na cire kaya na daina maidasu ba saidai zai zanemin jiki tunda kunnen ƙashi nake da , murmushi nayi ba tare da nace masa komai ba , nasan kila wani ya ɓata mishi rai yana neman hanyar da zai dakeni ne danya huce shi yasa yake nemen ya tsakuloni faɗa tunda banda haƙuri in masa rashin kunya ya zaneni yai tafiyarshi , dole kimin dariya tunda kin raina ni , haba niɗin banza ? Ni na isa in raina ka tunda nasan amfaninka ina faɗin haka nayi waje.....
Cike da tausayi yabi bayan Sultana da kallo , wata zuciyar tace masa kodai ya faɗawa An mata abinda ya faru , yayin da wata zuciyar ta gargaɗeshi akan ya barta kawai tayi farin ciki , idan kuwa ba haka ba yau bata iya bacci kuka zatai tayi mishi kuma yace zai daketa , ya ƙyaleta Allah dai ya bawa Papi lafiya kawai ya ɗauko mata ɗanta , ashe shi yana ta hasashen Jiddah zata barbaɗe An mata ashe tunaninta ya karkata ne akan ɗanta , hmmm Allah ya kauda ɓacin rana , dan ya ɗaukar ma kanshi idan har Perpy ya mutu wallahi saiya kashe Jiddah ,
Dady kuwa ya kira Dikko baisan adadi ba amma Dikko yayi fushi bai ɗauki wayar ba , Momy ma ta kirashi itama har ta gode Allah amma sam Dikko yanaji kuma yana gani amma ya basar da kiransu , Dady kuwa yayi ma Momy fata² yace bata da lissafi kwata² in banda hauka da rashin tunani irin na mata , yace yarinyar da uwarta ta kashe auren "yarta da ɗanta akan wani dalili banza can nasu na mata , kuma "yar ta fita da ciki taje ta zubar da cikin kuma ta kirata ta faɗa mata dan taga iyakarta , duk abinda sukayi hakan baisa ta gane inda duniya ta nufa ba taje ta sake jajibo Jiddah ta kawo cikin zuri'arta , dama ita Momyn Jiddah ta zubawa fiya²r ta mutu kowa ya huta , ya ƙara da cewa kuma idan har Papi wani abu ya sameshi ba abinda ya dameshi da yadda zuminchin su yake saiya ɗaure Jiddah daga ita har uwarta. Momy zatayi magana Dady yace ta rufe mishi baki , ba abinda zata faɗa mishi , batayi ma Mom Papi adalci ba , ko albarkacin yadda Babanshi ya jefo yarinyar mutane daga sama kuma ta dawo daga duniyar ƙanwar mutuwa a hakan bata rabu da Babanshi ba ta haƙura ta zauna dashi , idan bata sani ba Babanshi dukan yarinyar nan yakeyi wahalarshi takesha kamar tashin hankali amma ahakan tayi haƙuri ta zauna dashi bata taɓa guduwa ta barshi ba ,
Cike da nadama Momy tace taya zai daketa ne ? Dady yace da kanshi ya faɗamin ko nasan sunyi ne ? Yaje ya ɗauko amanar yarinyar mutane yazo ya kulle yarinya a gida yana ta gana mata azaba , nayi imani da Jiddahr ce tuni saita faɗa kuma sai anyi tashin hankali , ita kuwa ya doketa ya zageta duk haukarshi idan ya tasoshi akanta yake sauke masifarshi , ko wani ya ɓata mishi rai saiya je ya juye akanta ko ita jakace ne ? Ita iyayenta basa santa ? Ko ita ba haifarta akayi ba ? Amma duk wannan baiyi ba da masifa saida sukaje suka fitar mata da ciki tun farko ya nuna Rabiya , yace duk da haka tayi haƙuri kullum tana liƙe dashi haba baki da adalci , da kece akayi ma wani daga cikin "ya "yan naki ko aka taɓoki a gidan nan haka zaki ƙurmusashi a ɗaki ki haukatoshi ya fita yaita hauka yana saiya kashe² , baƙin halinki yasa aka birkita miki tunanin ɗa , baya auren karuwa , ita karuwa ce ki kiyayi kanki da duniya , da hannunshi ya nuna yace duk sirrin dake rufe ki kiyayi buɗeshi idan kuwa ba haka ba wata rana sai kunya ya hanaki fita , mtswww ya fita daga ɗakin.....
Dikko nidai banajin daɗi , ba tare daya kalleni ba yace An mata me ya sameki ne ? Ya tambaya a sakatance , kallonshi nayi tare da cewa cikina ne ke ciwo na faɗa ina kwanciya jikinshi , yana burgeni idan yayi magana da shagwaɓe ko sakata irin nasu na "ya "yan "yan gayu , sannan yayi murmushi dakel yace to ko sai na ƙara kamfen in ne ? Yayi maganar yana riƙeni da riƙon da nake so , ƙara lafewa nayi sosai a jikinshi , gyara kwanciyarshi yayi tare da ɗagoni daga saman gadon ya ɗora rabin jikina a jikinshi yace ta ina kikejin ciwon ne ? Ya ƙarasa maganar yana laluba cikina da lallausan hannunshi , agogo ya kalla da sauri ya saukeni daga jikinshi yace Dady yayi maganar yana sauka daga saman gadon jikinshi yana ƙyarma , lafiya yazo gidan nan ? Yayi maganar cikin tashin hankali , a zuciyarshi yace na shiga3 kardai Papi ya mutu Dady ya taho , da sauri yasa talkaminshi ya fita ,
Sauka nayi daga saman gadon na fita palonshi ta jikin window na tsaya tare da yaye labulaye , a dai² lokacin da naga Dikko ya isa wurin Dady da gudu ya riƙeshi yana magana , wurin da nisa sosai banajin abinda yake ce masa , amma shi Dikko yanayin maganar da yanayin fushi yana nuna kanshi sai kuma ya nuno bayanshi , da hannu Dadyn ya nuna mishi yayi haƙuri yana shafa kanshi , girgije hannun Dady yayi daga saman kanshin da yake taɓawa ya juyo cikin fushi , riƙoshi Dady yayi ya rumgumeshi yana magana cikin yanayin lallashi , shima Dikkon riƙe Dady yayi ya rufe idanuwanshi yana ci gaba da magana , bansan yadda akayi ba naga Dikko da Dady sun shiga mota sun fita daga gidan , Ashiru da Abbakar kuma sun fita a motar Dikko sunbi bayansu , tsoki nayi tare da cewa wannan siyasar banza Allah ya raba Dikko da ita......
Yau bai kwana gida ba , kuma washe gari bai dawo ba sai 11:30 na dare , ko makaranta yau ni naje da kaina ba Ashiru ya kaini ba , kuma daya dawo gidan baifi mintuna 5 ba ya fita , dan naji shigowarshi amma kafin in fito harya fita ban samu haɗuwa dashi ba , saida yayi kwana biyar baya gida kuma yana Katsina , ranar daya dawo , dashi da Papi dasu Nabeela suka sauka gidan , palo na samesu su dukansu "yan uwanshi manyansu da yaransu , Papi sai kuka yakeyi yana kiran Momy , Dikko kuma yana kwance saman kujera 3siater da yanayin damuwa , Rabiya tana zaune saman hannun kujera sai cewa takeyi yayi haƙuri , kai gaskiya bazan gaji da faɗa ba , "yan uwan Dikko wayayyin matana ne , "yan gayun billahillazi , ibar ƙarshen ƙarni , gogaggi masu ilimi da buɗewar ido , duk iya gogewarki idan kika tun karesu wallahi sai kin kama kanki dakarun mata ne da zamani kebinsu , sannu nayi musu nima na samu wuri kusa da Nabeela na zauna ina kallon Dikko , kaɗan ya buɗe bakinshi yaja iska ta ciki da yanayin da idan muna cikin wani yanayi dani dashi , murmushi nayi tare da sauke kaina ƙasa , shima murmushin yayi tare da cewa An mata ga ɗakinki nan yana kiranki , da gudu Papi yayi wurin Rabiya yana ci gaba da kiran Momy ya maƙale ƙafaɗarshi ya riƙeta ya juyo yana kallona.
Jawoshi Dikko yayi gabanshi yace kai sa idonka nan , kallonshi Papi yayi yana kuka , nan ne gidanku ɗan ƙwaƙwar tsiya kana can kana ƙwaƙwa za'a kashe ka bari inji ka sakemin kuka kaga yadda zanci maka , dariya akayi gaba ɗaya , duk suna kallon Dikko da Papi , ƙara ɓata fuska da baki Papi yayi saida yayi ajiyar zuciya yace Momy , Dikko yace ga Momy can ya nunoni tare da cewa kai fashin iyaye kakeyi ne ? Ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na biyu yana kallon Dikko , murmushi Dikko yayi cewa zaka hau doki ? Ya ƙarasa tambayar da girarshi , kai ya ɗaga alamar zai hau , waya Dikko ya ɗauka ya fara kiran Umar , bayan ya ɗauka yace a kawo doki Papi ya dawo gida , yana faɗin haka ya tsinke kiran yace je ka wurin Momy itace zata ɗoraka a doki , wurina ya taho yana ajiyar zuciya , amma da yazo saiya tsaya wurin Nabeela yana kallona ,
Dikko yace kace mata ka daina kuka zaka hau doki , cikin shaƙaƙƙiyar murya ya faɗa yana kallon cikin idanuwana , dan kauda kaina nayi cikin yanayin jin kunya , dariya Dikko yayi tare da cewa Papi riƙeta idan baka riƙeta ba bazata ɗoraka ba tace , da sauri na tashi , dariya Dikko yayi sosai yace ku kalli fulani da kawaici , yau ni ga ɗan farko gaban An mata , kam aiko yau saina ɓanɓare miki kunya tashi yayi ya ɗauki Papi suka biyoni ɗaki ,
A kona ya sani ya sauke Papi ya riƙe hannunshi yana daga ta bayanshi , cikin kwantacciyar murya yace riƙeni ya faɗa yana min kallon ƙauna , riƙeshi nayi cike da soyayya , yace sumbaceni ya nunamin saman bakinshi da ɗan yatsa kuma bai daina kallona ba , matsawa nayi na sumbaci bakinshi , da hannun ya riƙo ƙeyata ya haɗe bakuna wuri ɗaya yana sauke ajiyar zuciya cikin ƙaramin sauti mai tada hankali , bakinshi a cikin bakina yace ke Papin ne baki ɗauka ? Ni bana san wannan kunyar gaskiya so kikeyi yazo bai saba dake ba kullum yana kiran Momy ? Haba An mata nidai bamu iya irin wannan abun ba kinji ? Kija ɗakin a jiki idan Umar yazo da doki ki ɗorashi da kanki , yana san doki sosai , kuma zan bar muku doki ɗaya anan zaki ga ya liƙema gidan nan bazai wani sake tunanin gidanmu ba , kiyi wasa da ɗanki kija shi jikinki idan kina wannan kunyar haka zasuyi ta ibe miki "ya "ya suna tafiya dasu su kuma zasu saba da can ke kuma ko oho , idan kika bar "ya "yanki sake haka za'ayita labbatarki ana kakkashe miki su , ki koya ma "ya "yanki tsoron mutane , banda Allah yasa Papi yana da sauran rayuwa yanzu da an kashe miki ɗa , kuma ai nasan zakiyi kuka ko ? Ya ƙarasa maganar yana ci gaba da tsotsar bakina cikin wani irin bahaggon yanayi , mutsurniya na fara ya girgaza kanshi alamar in bari , kuma in bashi harshe na , riƙe harshen yayi tare dayin murmushi mai sauti yana kallon idona cike da tsantsar ƙauna , gaba ɗaya jikina mutuwa yayi na kasa wani ƙwaƙwƙwaran motsi , da ɗayan hannunshi ya kamo hannuna ya ɗoramin inda yake so na riƙe mishi kanshi , nice na ajiye ɗayan da irin yadda yake so ya kasance , dan nima zuwa wannan lokacin na fara zama "yar hannu , ina riƙeshi kukan Papi ya fara fitowa , sakeni yayi tare da jana ya kwantar dani gefen gado dan yasan bazan iya tsayuwa ba , dan cewa yayi wai da an taɓani sai kawai in wani mutu murus , shi wannan abun yana mishi baƙin ciki ragguwa da ni , fita yayi daga ɗakin dashi da Papi.....
Har dare duk basu tafi ba , nima ban sake fita ba , koda Umar yazo da doki shine ya ɗora Papi , abinci ma Momy ce ta bada aka kawo musu , bayan abinci yazo Nabeela tazo ta kirani muci abinci , gaba ɗayansu sun hallara a saman tebirin cin abinci nima kujera naja na zauna , mai bin Rabiya take ba Dikko labarin yadda suka ƙare da mijinta da zaiyi aure , bansan farkon labarin ba , amma tunda naga Dikko yana gaggaɓa dariya nasan cuta akayi , jakarta ta buɗe ta fiddo irin maganin da Dikko ke bani , ƙara ƙyalƙalewa yayi dariya yace nafa yadda basai na gani ba , mata ? Mata ? Hmmm , Rabiya tace ai raina ta ma yayi ni tayama namiji zai fara hasashen ƙara aure bare ya fara tunkarar matan , dariya Dikko yayi tare da riƙe kanshi da hannun haggunshi yaci gaba da cin abinci kanshi yana kallon filet in da yake cin abinci , Nabeela tace ai wallahi ba wanda ya isa ya auramin tsoho tayi maganar tana fashewa da kuka , Rabiya tace banza karki ma kanki baƙin baki wannan jakar matar tashi ba a bakin komai take ba wurinshi , koma komai ce ke a wurinki mayinos ce , cikin kuka tace ni sai kace nice kaɗai ɗiya a gidan ? Dikko yace tou auren tsoho miye kuma ? Yayi maganar yana ɗaure fuska , yace ko dan anyi magana a gabanki zaki mana rashin kunya , cikin kuka tace Yaya amma waye aka haɗa da tsoho ? Saini ? Rabiya tace ai tsohon yafi saukin shigarwar lungu , ga matarshi wata tutar ƙasa ce , ke har akwai macen da zata tayar miki da hankali ? Dikko yace ƙyale sakara , Nabeela tace nifa banajin matarshi kawai dai yamin tsufa ne , Dikko yace to zani ne shi da zaki ce ya miki tsufa wurin ɗaurashi ? Ko zani ne shi ai abun iyawa ne ma , idan ya miki tsufa ai kinsan irin wanka ke da zaki ɗauka iya wankuwarki iya adadin yadda tsufan zai ɓoye a jikin tsuhuwar sitirar da kika saka , kinga tunda ya haɗu dake basai ki rage mishi tsufan ba ? Nuna Rabiya yayi tare da cewa ai kamar Hajjaju ce da atamfar data ɗaura tun ina rakiyar zance take da atamfar nan har yanzu kullum kyau take mata duk tsufarta , dariya akayi gaba ɗaya amma banda ni , Rabiya tace lallai Baban Dady amma wallahi ka rainani da yawa , kai lokacin da nayi zance ma ina kazo duniya ? Ɗaure fuska yayi , gaba ɗaya suka sake ɗaukar dariya , maibin Rabiya tace bar ɗan iska saboda yaga ya ajiye wannan gemun yake raina mutane sai munbi dare mu askeshi , dariya yayi tare da cewa da kuwa kun asko masifa , mai bin Nabeela ta canja firar da cewa mukam dai sai baba gomna muma muna bayan Dady , Nabeela tace idan ya faɗi zaɓen fa ? Kike wani kiran gwamna , mai bin Rabiya tace bama zai faɗi ba sai yaje insha Allah , ah munga su Nabeela as matar gwamna , kwarkwasa kenan ,
Dikko kuwa cewa yayi oh , An mata kin daiji ko ? Wai ita matar ta gidan itace tutar ƙasa , bata miƙe ba kenan tana kwance , jinjina kanshi yayi tare da cewa lallai matan ciki sai sun dage , ai ya kama ace idan mijinki zaiyi aure ita wacce zata shigo ya zamana gabanta na halbawa saboda shakkunki da tsoron kishi dake , amma sai ya zama ita mai shigowar wai itace zata halba zuciyar ta ciki , kina aikin me mace ? Haba mata ? Idan ke tutar ƙasarce kamar yadda kuka faɗar saita shigo gidan dake da mijinki da "ya "yanki tazo ta gigita miki miji , kina can kina haukar banza zakiji karatun yasha banban , idan kuma mara adalci ne saidai ya yarfeki tunda shi ya samu lallausar rayuwa , nidai idan zan ƙara aure nasan amaryar sai taji tsoron An mata , Rabiya tace ƙwarai kuwa ita bama zata yadda ta fara shigowa ba ko Sultana ? Tayi maganar tana kallona , Dikko kuwa cewa yayi ai zanyi auren da wuri ne ,
Gyara zamanshi yayi tare da cewa bara in baku labari , a london na haɗu da wata "yar tasha , tunda ta shigo jirgi kawai tayo wurina ta zauna kusa dani , ɗan yamutsa fuska yayi tare da nuna yadda mata keyi , da irin maganar mata , yaci gaba da cewa aka wani cemin sannu ko ? Ya nuna yadda tayi maganar da yadda ta zauna , yadda yayi abun ne ya ba kowa dariya gaba ɗaya harni saida nayi dariya ina kallon Dikko , wallahi Dikko baijin magana ko kaɗan , shi kuma baiyi dariya ba yaci gaba da cewa da wutsiyar idona na kalli sakarai a zuciyata nace suna can na baro gidanmu , nidai ban mata magana ba , riƙe take yarinya tana da aji sosai gaskiya "yar gayu ce kuma ta iya wanka tana fama da wani irin girman kai , amma duk girman kanta da tazo wurina saida ta saukeshi , nidai banyi mata magana ba kuma ban kalli inda take ba , can bayan wani lokaci sai ga Abbakar yazo , yana zuwa yace DK ya haka kuma ? Shima Abbakar ya kwaikwayi maganarshi , yaci gaba cewa keda ke Katsina idan kin gansu ko kinji maganarsu tou Dikko yasan suna nan daga ita har Abbakar in , Abbakar yace malama da Allah tashi , batayi ma Abbakar magana ba ta juyo wurina tace suna na Yusra , haka nan naji zuciyata ta tashi kamar zanyi amai wallahi , da sauri naci cingom ,
Abbakar kuwa yaci gaba da cewa bara ki tashi a wurin ba ? Wurin zamanta ta nuna mishi da hannu tare da cewa ni ba'amin magana a saman kai , danni maza basa burgeni , saboda hauka irin na Abbakar ƙiƙi² ya kamata da kokowa , yana bara ki tashi a wurin ba ? Naso in musu dariya amma sai nace ya barta , bayan ya saketa ni saina tashi nace shi ya zauna , ina tashi ta taso da yanga sai ƙwarƙwasa take tana yauƙi tafiya cikin tsari da ɗaukar hankali irin tafiyarki Hajjaju ya nuna Rabiya , yace cikin kissa tace haba Yayana ya nuna da salo mai burgewa yana ci gaba da cewa tace yi haƙuri idan na ɓata maka rai , tana maganar tana wani kakkafe ido , ya nuna yadda takeyi , gaba ɗaya aka sakeyin dariya amma yanzu banda ni , Dikko yayi wata irin dariya , yace kamar wani sakarai haka na kalleta , kallona yayi tare da cewa tafa burge , kunga kenan ya ɓadda labarin akan yadda ya ɗaukoshi , ai farkon labarin cewa yayi duk girman kanta da tazo wurinshi saida ta sauke , kuma yace data faɗi sunanta yaji zuciyarshi ta tashi , amma da yaga naji kishi saiya juya labarin kunga kenan ya fasa faɗar yadda labarin yake kenan , bai ci gaba da labarin ba , duk yadda akayi kila Yusra ƙawar Sadiyya matarshi data mutu , irin tafiyar Rabiya da ya faɗa kenan yana so ni na koya kenan.
Cikin fushi na tashi , amma kafin in miƙe ya zaunar dani da ƙarfarshi yana kallona , Rabiya kuma tace , tou ya kukayi ? An mata najin kishi mubar maganar , Rabiya tace haba Sultana ai laifin kine ma fuska kika bashi har yazo gabanki ya samu ikon maganar mace , Dikko yace ai ban shanyu ba shi yasa zanyi ma Perpy wata Momyn.
Canza labarinsu sukayi akan kishiryar Nabeela wai ƙazama ce ba gogewar rayuwa , bata iya komai ba saidai taci ta jibge a wurin , Dikko dai bai sake magana ba ni yake kallo , yanajin yadda ake ta aibata sakarkarin mata , sai ƙara yi ma Nabeela ɗamara ake ana ƙara ɗorata a hanya , bayan wani lokaci kuma sai suka koma labarin kayan mata , tashi Dikko yayi dan har yanzu Umar bai dawo da Papi ba ,
Nima tashi nayi na barsu , ina shiga ɗaki wanka na shiga , lokacin dana fito har sun tafi , sai Nabeela da Papi kaɗai , ina fitowa suka shiga danyi mishi wanka , kafin ta fito na ɗauki kayana nayi ɗakin Dikko , sannu da zuwa yayi min tare da ansar kayan cikin ladabi , yace Allah ya taimakeni kenan ? Ai ina nan nace tou kai Dikko me ya kaika ? Ila marin mace da mangariba , 🤔 ai na ɗauka yau dahuwar kan rago zakimin ? Nayi tunani kila a saman wuta zan kwana dan nayi wannan maganar , nace Dikko yau zakaci ubanka An mata tayi fushi kuma ga Nabeela , Allah dai ya rufamin asiri ashe ina da rabon zanyi farin ciki a daren nan yayi maganar yana zaunar dani gefen gado , yaci gaba da cewa ai ban sani ba "Yar matan nawa ta girma ba.
Kusa dani ya zauna ya rungumoni , sannan ya shiga rattaɓamin kaf abinda ya faru da Papi , naji babu daɗi sosai amma shi saina nuna mishi ai ba komai , yace munafuka ce Jiddar nan , yace lokacin da nayi rashin lafiya , wanda na tafi na barshi kenan , yace tazo ta zauna tayi ta haɗa masifa , kuma itace ta kai Momy ta barota suka ɗauko Papi kila tun lokacin take so ta kashe shi....
Bayan kin tafi kin barni...........
Kai.................... Saina kashe kaina , wallahi saina mutu tunda baki so na mutuwa zanyi , Yazeed kike so ko ? To ni zan mutu in bar mishi ke , buɗe ƙofa nayi na fito , na biyo bayanki amma ban ganki ba , komawa nayi ina ihu , na ɗauki wayar wuta da aka sauke ƙasa na koma ciki , ina shiga na hau sama ina ihu saina kashe kaina , mai gadi ya fara kiransu Ashiru , nasan na ɗaura waya a wuyana bayan na ɗaure ƙarshen a jikin ƙarfen bene nayo ƙasa ,
Daga haka ban sake sanin abinda ya faru ba , Ashiru yacemin da mai gadi yai mishi waya gaba ɗayansu suka zo , hankalin kowa ya tashi gani na zube a ƙasa , kila wayar bai ɗauru ba , ko kuma nayi ma ɗaurin nauhi shi yasa ban tsaya a saman iska na mutu ba , a haka suka sameni , da suka tambayi mai gadi abinda ya faru , yace bai sani ba amma ya ganki kin fita da gudu ni kuma ina kiran Yazeed , Dady suka kira kai tsaye suka sanar dashi cewa Mai gida ya mutu , Dady yana jin haka ya maƙale wurin ya daina aiki kwata² , sune suka sanar da kowa Dikko ya mutu , Dady kuwa daya dawo saidai yace Babana , haka yaita ɗaukewa kamar "yan nepa suna wasa da wuta , tafiyar ƙarshe ce da yayi saida aka kaini government house Dady ya dawo , yayi kuka wanda bana san ina faɗa , saida aka taru Dikko ya mutu , An mata da anyi gaggawa rufeni da an binneni da raina.
Bayan an tabbatar ban mutu ba wanda shima Dady ne ya kafe ban mutu ba , irin sabbatun nan na wanda zafin rashi ya ɗimauta , haka Dady yasa akaita kirayen² likitoci , a ido ni na mutu amma a baɗinance Dikko yana nan , murmushi yayi tare da cewa wai aljannu sun shanye numfashi na , haka aka fita dani waje akayi ta magani daban ciwo daban , jinyar nan da Dady akayita bawan Allah....
Abinda yasa dana samu sauƙi ban wani ji damuwa akanki ba , nasan ina da fushi sosai kuma haka nike da riƙo kuma ina da halin ko oho , duk abinda na bashi baya na gama dashi har abadan duniya wallahi , bansan abinda yasa ni bana iya fushi dake ba , ko nace zanyi zuciya dake bana iyawa , tunda nake a rayuwata ban taɓa gardama wa iyayena saida kika zo rayuwata ,
Labarin mafarkin da kikeyi kaf abinda kika faɗamin saida Mustapa ya faɗawa Ashiru , kuma shine yace wai anyi ma Al ' Ameen lamba su duba kanshi zasu ga aski da lambar mutuwarshi , ni bansan Al ' Ameen yana tsafi ba kwata² , tou tayama zan fara mishi wannan mummunan zaton bayan rayuwar kowa a rufe take , babu wanda yasan sirrin wani sai wanda ya faɗa , Mustapha yasa aka fitar da Al ' Ameen yace wallahi mutuwa zaiyi kuma idan ya mutu hannuna zan tabbata matsafin kamar yadda mutane duniya ke kallona.
Naso naga Al ' Ameen dan naso zanyi magana dashi amma hakan bai yuwu ba , shi Mustaphan yayi ma Ashiru jagoranci zuwa inda sukayi tsafe²nsu , komai Ashiru yayi saida suka gama komai lumfashi na ya dawo , tunda nake ban tabajin irin wannan tashin hankali ba wai an shanyemin nufashi kiji wani masifa , hmmmm , Yazeed kuwa Ashiru yaci ubanshi kuma shine ya maido Abbakar company duk bansan anyi ba ,
Waye shiɗin ? Kawai abokina ne amma abotar ba wani can² ba ya faɗa yana yatsina fuska , tou shi me yasa Ashiru ya ɗaukoshi ne ? Munyi maganar shi da Ashiru anyi ma wata "yar uwarshi fyaɗe harta mutu , da na shiga cikin lamarin Ashiru ya fitar dani , amma ni Mustapha yacemin wai matan Babanku dasa hannunsu a damuwarka , kwanciya yayi tare da kwanto dani jikinshi yace can damuwarsu duk abinda mutum yayi kanshi , idan nayi maganarta nayi imani Dady saiya saketa ni kuma bazanji daɗin haka ba , saboda duk Momy za'a ɗorawa laifi , familyn su Dady haushinta sukeji sosai danma suna shakkun su Rabiya ai da yanzu sunyi waje da ita , ya faɗa yana nunawa da hannunshi , yaci gaba da cewa "yan uwan Dady basujin magana yadda baki tunani amma zaki gani tunda zaki shiga cikinsu , suma dai wayayyi ne amma Momy ta raina ma wayewarsu shi yasa "ya "yanta suka fita daban , tsarinsu ya fita daban idan kun shiga zakiga yadda su Rabiya ke bada haske a taro , gasu da rainin wayau , idan su Rabiya suka raina miki ƙura tom hmmm ya jinjina kanshi , amma duk wani banzar wayewar familyn Dady idan "ya "yan Momy sunzo to kin zama "yar kallo da koyon gyara inda aka tsere miki a wanka , zamani yazo anan zaki gani ki koya ki kuma yi gyara , ni dama bana wani shiga sabgar kowa , tunda bana binsu biki ko suna , iyakata dasu gida , idan basa nan zanji babu daɗi gidan yamin ba daɗi kuma Momy bata da magana , ni kuma faɗan da mukeyi dasu ne nakejin kewarsu idan basa nan , ko wuri zasu zasuce munafiki yau idan muka tafi bazamu dawo da wuri ba , kuma kowa baya rayuwa da "yan wasu ɗakin sai "yan ɗakinsu , haka zan gaji da zama in fita cikin gida bana nan bana can kamar wani maraya tunda ni bana fita waje iyakata gida Dady baya bari naje wani wuri saidai in saci hanya idan baya nan , idan suka dawo zanyi farin ciki , kuma zasu bani labarin duk abinda ya faru idan sunje wuri sun dawo , ni ba abinda ya dameni da rayuwar wani tawa nakeyi , sai "yan uwana mata sune kaɗai abokaina muyi faɗa mu shirya , suma "yan uwan Dady ni babu wani ruwana dasu dan Momy ta koyamin tsoronsu tun ina ƙarami , su kuma suna so na saboda yadda Dady yake ƙaunata dan soyayyar Dady a kaina bai ɓoye ba , amma iyakata da mutum sannu daga nan kawai zan zama kurma , kenan bayaji bare ya bada amsa , idan kuma ba'aci sa'a ba ko kayimin magana sai in maka shiru bazan ma ce maka sannun ba sai in tsare ka da ido ya faɗa yana murmushi , yace sai kiga simi² mutum ya kama gabanshi , kuma ba ƙarya ya faɗa ba , ashe yana sane da duk iskancin da yakeyi , dan aradu idan Dikko ya riƙeka da ido sai kaji babu daɗi har ka kama kanka , tou gashi baida yawan murmushi kuma shi dariya ma sam² da bayayi sai yaji mugunta zakiji shi ƙa׳ yana dariya , kuma dariya ba ƙaramin kyau take mishi ba , Allah sarki mai uwa baya san laifinta , amma gaskiya Momy gaba ɗayanta batayi ba bata da mutunci ko kaɗan , gata da raini , rankatakaf ta ɓata "ya "yanta da baƙin hali basu san mutunci kowa ba saina mazajensu shi yasa mazan nasu kamar sun masu asiri biye mazajensu suke dasu , kuma ita bata iya neman asiri ba saidai bariki da duniyanci wurin iya nannaɗe zuciyar namiji , shi yasa Momy ta share kowa a wurin Dady dan yanaji da ita sosai , amma basa san ace Momynsu tana da miyagun halaye , kai , amma gaskiya "yan uwan Dikko da suke ɗaki ɗaya zamani ne su , makaranta ce mai zaman kanta , sunyi׳ , sun haɗu׳ wayayyi ajin farko , kuma sunfi "yan ko wane ɗaki yawa a gidan , ga kuma Mai gida DK nasu.....
Satin Papi 3 a wurina amma har yanzu bai daina kukan Momy ba , kuma Nabeela tana nan ta dawo gidan kwata² da zama , ga Dikko baya zama , ni kuma banda lafiya , dana ce masa ko akai Papi wurin Momy cewa yayi kar a sake akai mishi ɗa wani wuri yaje yaita kukan idan ya gaji zai daina , Nabeela kuwa ta faɗawa Momy Papi yana ta kuka shidai Momy , tazo da kanta itama dai tayi kewar Papi , cike da soyayya Papi ya riƙe Momy su tafi wurin Dady , har ranar da suka dawo dasu Rabiya saida yaba Momy labari amma wasu ya manta sai ya tambayi Nabeela , murmushi Momy tayi irin na ƙasaitaccin mata da irin yanayin kallon Dikko , dai² gani sukeyin kallon amma idan kasa ido sosai zakaga kallon nasu yanayin ƙasa kuma basa motsa idon , baka ganin lokacin da idon yake tafiya idan suna rageshi , idan kuma suka gyara kallon nasu sai kallon ya bada wani iri mai burgewa , da irin kallon ta tsare Papi tana cewa ni duk naga ka zama wani baƙauye ta faɗa tana murmushi da gefen bakinta tana ci gaba da cewa Nabeela anya zanyi auren nan ? Kafin Nabeela tayi magana Papi yace ni nayi cau ya faɗa yana harar Momy.
Dariya tayi tare da cewa ni bakaimin wani kyau ba , iyayenka basu iya raino ba kuma bazanje dakai ba , kuka ya farayi yace ina juwa , dama da yawo ta kama Papi , duk wankan da akayi Papi saida Momy tasa Nabeela ta sake wankeshi aka gayeshi tace Nabeela taje anjima ta dawo dashi , gaba É—ayanmu mukayi mata rakiya ta tafi.
Dikko kuwa ya kirani yayi faɗa sosai yace an ce masa wai anga Papi gidansu , meya faɗa min ne ? Zanyi magana yace in mishi shiru ni dama na raina mutane , ya ƙara da cewa ya rantse da Allah idan wani abu ya sameshi ni idan nayi mishi kuka saiya zaneni , itama Nabeela zai haɗu da ita shima Papin zaici ubanshi bari ya dawo , yana faɗin aka ya tsinke wayarshi.
Ashiru ya bashi haƙuri , Dikko yace shi bawai yana hana Papi zama wurin Momy ba , fiya² fa aka bashi sai kace wani ƙwaro , idan suka kashe mata ɗa ni ba abinda ya dameni kuka ne dai bata isa tayi min ba , gidan nan munafinki gida ne kuma na faɗa mata , mu kanmu "yan gidan ya muka ƙare bare kuma wani jika , kadai san halin Momy haka take zama ta tisa Papi taita habaice² , tana irin wannan maganganun nasu na mata. Haƙuri Ashiru yai ta bashi ƙarshe dai Dikko yayi shiru ya ƙyale Ashiru.
Nabeela kuwa kila shi ya kirata yaci mata mutunci , bansan yadda akayi ba taje ta taho da Papi , yana ta kuka , ta waya Dikko ya zageshi yace kuma bari yaji ance masa ya sake kiran Momy saiya turo Jiddah ta kashe shi aje can a jefar dashi , bazai sake ganin Momy ba kuma bazai sake cin abinci ba ,
Na faɗawa Inna banda lafiya , kuma na faɗa mata ciki nake da , na ɗauka zatayi farin ciki ta kirani tunda saƙo na tura mata , cewa tayi can ni ya dama , kuma bata faɗamin duk abinda ya shafeni da Dikko kar na sake faɗa mata ba ? Dole na haƙura naci gaba da rayuwata daga ni sai Dikko da "yan uwanshi mata.
Rabona da Inna kenan , saida ta kirani ta faÉ—amin rasuwar É—an uwanta baban Sultan , yayi haÉ—arin mota , a nan gidan Kaka ake zaman ta'aziyya , za'ayi jana'izarshi da bayan azahar , dani da Nabeela da Papi muka tafi , kuma kaf "yan uwan Dikko sunje min a ranar da akayi rasuwar suna nan akayi jana'iza bayan an dawo sukayi gaisuwa wa Inna Kaka da matan mamacin sukayi tafiyarsu , amma muna tare da Nabeela , Dikko kuwa bai zo ba dama baya gari , yadai turomin text in tafi gida haka nan bawai nan zanje in jibge ba harsai an raina ni ba , dana nuna masa ya bari zuwa anjima cemin yayi ya gama magana , dana faÉ—a ma Inna zan tafi taji damuwa tace in bari sai anjima nace mata shi yace in tafi , taji ba daÉ—i dan kowa da "ya "yanshi a kusa dashi haka na tafi tanaji kuma tana gani bataji daÉ—i ba , gashi ba dama ta kira Dikko.
Tun daga ranar ban sake zuwa ba sai ranar addu'ar 3 , Momy ma taje min a ranar kuma su Inna anji daɗi matar gwamna tazo , haka taita tattaro mutane tana cewa ga surukar Sultana suje tayi musu ta'aziyya Momy kuwa riƙenta take tana wannan rainin nata , da ta tashi tafiya ta bada kuɗi masu yawan gaske sadaka , shima Dikko ranar addu'ar 3 yazo , kuma yana zuwa yayi gaisuwa yai tafiyarshi bayan shima ya haukatasu da kuɗi sadaka , ranar mu kuma sai dare muka koma gida dani da Nabeela bayan nima na bada tawa sadakar dan nima yanzu inaji na dai² nake da duk wani mai jin shi yana da hatimin nasarar shi , dan duk wata damuwa ko takaici Dikko ya shanyemin shi , baya bari inyi tagumi shi yasa ya sakarmin ragamar girman kuɗi , buɗa min fili kawai yakeyi ina yadda naga dama da rayuwata....
Yana nan bazai sake tafiya ba sai an gama zaɓe , itama Nabeela bayan zaɓe za'asa ranar aurenta , addu'arta Allah ya maida Dady a mulki sai kuma wanda zata aura shima ya haye , shima Dikko addu'arshi kenan Dady ya koma mulki , nima ina mishi fatan komawa bana so su faɗi.......
24/12/2019 👇ðŸ»
*JAMILA MUSA...* 💅ðŸ»
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇ðŸ»
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 91
_Alhamdulillah_
_Alhamdulillah_
_Alhamdulillah_
*_Assalamu Alaikum masoyana , suna na Jamila Musa wacce kuka fi sani da Meelat Musa , ina muku fatan alkairi maudu'in rayuwata 😊 , zanyi matuÆ™ar kewarku sosai , inajin wani iri a raina , jiki yai sanyi , idona shima zaiyi kewarku , yana muku bankwana da hawaye 😠, gaskiya ina matuÆ™ar sanku yadda bazaku iya ganewa ba , hmmm , tou ina dai muku fatan alkairi a duk inda kuke a faÉ—in duniyar nan alfaharina , zan tafi׳ , sai kuma Allah ya sake haÉ—amu idan muna rabon sake haÉ—uwa a cikin sabon littafina mai taken ÆOYAYYAR SOYAYYA , KWARATA yazo , kuma zai tafi , Dikko da An mata suna muku fatan alkairi , ni kuma Jamila nake neman yafiyar duk wanda na mishi babu daÉ—i , wani ban ganshi ba , amma rubutu na yaje gareku , ina alfahari daku , kuma ina muku fatan alkairi , ina matuÆ™ar Æ™aunarku sosai da sosai , masoyana da mukeyin waya daku , wasu kuma cht da wanda Allah yasa na gansu ido² duk ta dalilin Dikko da An mata ina matuÆ™ar Æ™aunarku , Allah ya sadamu da alkairi gaba É—ayanmu , ngode ׳ da yadda kuka nunamin Æ™auna , na barku lafiya......_* ðŸ‘ðŸ»
Yaya janje , a , a , da gudu Papi yabi bayan Dikko yana kuka , kai nifa babu inda zanje dakai , ƙara faɗar janje yayi yana bin bayan Dikko da sauri dan taƙaita gudun saboda ya isko shi , a , a Dikko ya sake maimaitawa , bin bayan shi Papi yakeyi yana ci gaba da kuka , dariya Dikko yayi sosai yace tou zo muje , yayi maganar yana kama hannun shi , juyowa Papi yayi tare dayi ma Nabeela gwalo da tace Allah yasa kar a tafi dashi , murmushi Dikko yayi ba tare daya sake magana ba suka fita , yayi kyau sosai a cikin ƙananan kaya , riga jinin kare baƙin wando rufaffun takalmi suma baƙi sai baƙin agogo , Papi kuma manyan kaya ne jikinshi.....
Dariya nayi tare da kallon Nabeela nace zakisha mamaki , tunda yayi waccan dariya lallai sai yayi ma Papi wani abu na mugunta , kuma zaki sha al'ajabi bara su dawo , dariya Nabeela tayi tare da cewa kuma nima in rama gwalon da yayi min da zai fita.....
Gaban mota Dikko yasa Papi yana cewa ai dai zakaje ko ? Ya ƙara tambayar Papi , goge hawayen shi yayi tare da cewa Janje Yaya , yayi maganar yana kallon idon Dikko , tou zauna , zama yayi a dai² lokacin daya tashi mota ya fara tafiya , Ashiru dake tsaye daga gefe yace Mai gida ai ban san fita zakayi ba , ba tare da Dikko ya tsaya ba yace ai ba nisa zanyi ba , ya ƙarasa maganar yana ɗage gilashin gefenshi da ya sauke danyin magana da Ashiru ya fice daga gidan da gudu.....
Suna fita muma muka zagaya can bayan gida ina taya Nabeela aiki zatayi baƙi , gidan ne gaba ɗaya aka firgita , yasa ana ta rosheshi , nidai a ganina asara ce kawai dan wallahi gidan ya haɗu iyakar haɗewa , kuma banga abinda yayi ba , duk komai na gidan da aka fitar tsohon namu kenan , yaranshi ne suka kwashe su , ni ɗakinshi ma nafi tausayi dan Allah ya sani an daddaƙe ma kuɗi rai a ɗakin Dikko , anyi masa haɗuwa ta haɗaɗɗin haɗewar masu haɗuwa , can baya ma da akayi gidan anyi surutunshi sosai kuma har yanzu ba'a gama surutun ba , yanzu kuma wane irin gini za'ayi...... ? Aikin baizo wurinmu ba shi yasa bamu tashi ba , amma dai duk an fitar da komai na gidan su Ashiru sun kwashewa "yan uwansu , ba komai a gidan muma goruba road zamu tafi a daren yau sai an gama aiki zamu dawo , aikin da nake taya Nabeela baida wani yawa , amma kunsan yadda jiki yake , shi jiki sabo ne dashi , idan an horashi da wahala da ita zai horu kuma idan harma bakayi abun wahalar ba bakajin daɗi , idan ya saba da hutu tabbas baya iya ɗaukar wahala , shi yasa "yan gayu ashe muke ganinsu kamar sun raina mana hankali , to ba haka abun yake ba , saida na shiga fagen na gane haka , nima dai yanzu bana iya sakin jiki inyi aikin nan kamar jakkar ci rani , idan kuwa nayi aiki mai yawa sai nayi jinyar gajiya.....
Bare dama akwai masu aiki maza da mata , kuma duk wani ma'aikaci , daga direbobi , masu shara , masu girkin abincin da ma'aikatan gidan ke ci , masu gadi , masu ban ruwa wa fulawowi har masuyi musu aski su gyarasu idan sun zame daga tsarin da ake sansu , gaba ɗaya a gidan suke zaune , suna da wurinsu daban , kuma a gidan ake basu abinci kuma albashi ake basu duk ƙarshen wata , amma shi Dikko bayacin abincin gandu , namu mukeyi daban ina da mai aiki ta daban amma baya san abinci masu aiki sai ni zanyi idan yana gari , kuma masu aiki basa gyara masa ɗaki , ko yanzu da bana lafiya shi yake gyarawa ya goge komai fes kamar mace , ya iya gyaran gado idan har yayi miki gyaran gado zakisha mamaki , baya san ƙazanta ko kaɗan , da nace masa Nabeela cewa yayi a , a , dan iyakarta palonshi bata taɓa shiga bedroom inshi ba , nidai da nazo amma ban sani ba ko a zamanin Jiddah tana shiga ba , saida muka gama abinda mukeyi Nabeela tasa aka kwashe komai aka kai a motar ta , sannan muka taho dan komawa ciki.
Da gudu ya shigo gidan a dai² lokacin da mu kuma muka bayyana gaban fuskar gidan , tun kafin motar ta ida tsayawa cak ya kashe motar ya fito , tunda nake da Dikko ni ban taɓa jin waƙa a motarshi ba sai yau , ya wani ƙuro volume , buɗe hannuwan shi yayi ya nufo inda muke tahowa yana wata "yar munafukar rawa , daga ni har Nabeela dariya mukayi , rumgumeni yayi tare da ƙyalƙyalewa da dariya ya raɗamin wai Papi ya girma , cikin rashin fahimta na leƙa ta gefenshi naga Papi ya fito daga mota yana cewa ban nuna muku , dariya Dikko ya sakeyi sannan ya sakeni yana cewa yanzu zai cire wando ya fara kuka , ya faɗa yana nuna ma Papi yayi rawa , tsalle Papi ya farayi yanayin yadda Dikko keyi , murmushi Dikko yayi tare da kallon Papi ayyo ah² wayyo yana murmushi , sakin jiki Papi yayi yana ta rawa , saida Dikko yaga ya shagala yana rawa , ya koma mota yai tafiyarshi.
Nidai ban gane girman da Papi yayi ba , kuma ni kwata² raina bai kawomin kaciya Dikko yayo ma Papi ba , saida muka shiga ciki yaci gaba da cewa ban nuna muku abinda Yaya yayi min , ya faɗa yana rumgumer bango , duk babu wanda yayi ma Papi magana , bayan Nabeela ta fito wanka yace mata , yayinya joki in nuna miki , cire wando Papi yayi , Nabeela tana zuwa , yayi dariya tare da maida wandonshi yace baci gani ya faɗa yana mata gwalo , kowa fita harkarshi yayi muka ci gaba da abinda ya shafemu , shi kuma sai murna yakeyi , saida ya fara shan azaba ya cire wando , muma bamu sake shiga sabgar shi ba kuma bamu sake kallonshi ba , allura tana fita Papi ya fara ihu....
Yana taɓa kaciya , Nabeela ta fara dariya tana ɗaukarshi a waya , tana cewa da nace karka je ba sai da kaje ba ? Yanzun nan zan tura Momy ta gani , nima abun dariya ya bani sosai , iskancin Dikko saishi , kullum abunshi gaba yakeyi babu alamar sauƙi , Nabeela daina video tayi ganin Papi yana halbe² a ƙasa yana cewa nama ɓata da Yayan nan , rumgume Papi tayi suka ci gaba da kuka tare ,
Duk daɗewar da Dikko yayi waje harya dawo daga Papi har Nabeela basu daina kuka ba , da nace masa me yasa yayi haka baiga Papi ƙarami bane ba ? Kallon Papi yayi tare da cewa gobe ma idan ka biyoni ƙaro maka zanyi , cikin kuka Papi yace kuma na fata dakai , ai nine na ɓata dakai shi yasa naje na kaika akayi maka , miƙa hannunshi yayi tare da cewa zo muje , maƙale kafaɗa Papi yayi yana harararshi cewa kuma saiya faɗawa Dady , murmushi Dikko yayi tare da cewa tou jeka fa faɗa masa , yayi maganar yana fito da wayarshi yace bara kaji ma in kira Dadyn ya ƙarasa maganar yana kara wayar a kunnenshi.
Bayan wani lokaci ya fara magana a waya , Dady ga Papi zai kawo ƙarata yayi maganar yana ba Papi waya , cikin disashshiyar murya Papi yake faɗawa Dady abinda Dikko yayi mishi , bansan abinda Dadyn yace masa ba , ajiyar zuciya Papi ya sauke sannan yace to , shiru yayi , bayan wani lokaci Papi ya sake sauke ajiyar zuciya yace to , ajiyar zuciya ya ƙara saukewa ya faɗi Nabeela , ɓata fuska yayi ya taɓe baki yana ajiyar zuciya , bayan wani lokaci kuma yaba Nabeela waya , bayan ta gama tabani waya nima na gaishe shi , yamin sannu da mai jiki , bayan mun gama gaisawa nima nayi masa addu'a kamar yadda naji Nabeela tayi , sannan nabawa Dikko waya , fita yayi daga ɗakin yana magana a waya.
A gaggauce muka shirya muka bar gidan , saida muka biya ta wurin Momy , tayi faÉ—a sosai da abinda Dikko yakai Papi akayi mishi , ta kuma yi addu'a Allah yasa a fita lafiya , anjima zata aiko Ashiru wurin Papi , bamu wani daÉ—e ba muka wuce goruba mu dukanmu , shi gidan an gama aikinshi , kuma babu abinda ba'a saka ba , komai na gidan sabo ne katakal , har kicin ma anyi mishi tsari mai kyau babu abinda babu. Abundai , sai Allah sabunanni......
Satinmu biyu a goruba road , gaba ɗayanmu bamu da wata damuwa , rayuwar mukeyi cikin farin ciki , amma tunda wannan satin ya kama Nabeela da Papi basa tare dani saboda asabar ta gaba ake zaɓe suna can gidansu , mijin da zata aura kuma an tsayar da ranar aurensu ne idan yaci zaɓe za'a haɗa da murnar cin mulki da kuma shagalin ɗaurin aure , idan akayi rantsuwa kuma amarya zata tare a gidan gwamnati kenan......
Ni yanzu gaba ɗaya na daina gane kan Dikko , ya burke bansan abinda yake damunshi ba , saidai idan na buƙaci ganinshi zaizo ne ya bani haƙƙina da zaran kuma ya gama zai kama gabanshi , da nace masa wai ina yake zuwa yanzu sai yacemin shi bazai zauna gida ba tunda ba mace bane shi ,
Abun ya dameni sosai , dan haka na kira Rabiya na faɗa mata kai tsaye , haƙuri ta bani tare da cemin in bari idan aka gama zaɓe zata zo , Inna dana kirata nace mata shawara na kirata muyi cemin tayi idan dai ya shafi Dikko karma na fara faɗa mata.
Har akayi zaɓe aka gama ni bansa Dikko a ido ba , kuma Allah ya basu sa'a sun sake ɗagewa sama , wanda Nabeela zata aura shima yaci , duk shagalin da akayi banje ba Dikko ya hanani zuwa , Nabeela bataji daɗi ba kwata² , Momy ma taji babu daɗi da tace azo a taho dani cewa yayi idan dai shine yake aurena ya hanani zuwa idan kuma aurena ba a hannunshi yake ba tou inje , Momy da kanta ta haɗani da Dady a waya nayi mishi murna ,
Shagalin sake komawa a mulki banje ba , amma na ranar da aka ɗaura auren Nabeela naje , kuma tun safiyar ranar ina wurin Momy , kayan da zan saka Momy ce da kanta tayi minsu , duk abinda ya kamata itace tasa akayimin nima dai na fito kamar sahun "ya "yanta tunda ina da kyau na mai burgewa da baka gajiya da kallona , kuma banda irin wannan duhun kan na ƙauyanci , suna ta nunamin ƙauna da soyayya daga ni har Papi ,
Hmmmm , anyi wani irin shagali daya zo ma al'ummar jahar Katsina baƙo , ɗiyar gwamna ta auri gwamna , manyan mutane daga jahohi da dama sun samu damar halattar wannan gagurumin ɗaurin aure , wanda aka tara dubun² mutane , ni ina nan zaune a bedroom in Momy saman gado zaune kusa da Rabiya , abun duniya duk ya dameni , dan yanzu ko wayata Dikko ya daina ɗauka idan na kirashi saidai ya turo min text , wai idan wani abu nake so daga gareshi in mishi a rubuce basai na wani dameshi kira ba , kenan idan bani na buƙaceshi ba shi baya buƙatata ? Me hakan yake nufi tou......?
Lokacin da za'a tafi wurin shagalin party , yanzun ma Momy ce ta bani kayan da zan saka da mai kwalliya ta kuma tsaida Rabiya wurina dan ita tana fama da jama'a , idan dai mutum ya gitto wurin ya gani zaice masha Allah , wasu daga ahalinsu Dikko basu sanni ba , idan akace wacece Rabiya zatace matar Dikko ce , ko abokan wasa daa suka fara jana da wasa Rabiya cemin tayi kar in koya musu , basu da mutunci. Duk yadda dangin miji zasu soki idan dai baki da power wurin miji kin zama katin É—aurin aure ,
Jiddah tana cikin tawagar "yan gidansu , kuma hada Mardiyya Hafsa da Mom inta suna tare da Asma'u amma banga Amisty ba , nidai duk jina nake a takure , Papi kuwa yana liƙe da Nabeela tana fama da hidima amma yaƙi tafiya wurin kowa sai wurinta , duk yadda Momy taso su Ashiru su fita dashi Dikko cewa kar wanda ya ɗauko shi wai su barmin ɗa na can , nidai bansan abinda ya faru ba tsakanin ni da kuma Dikko , amma kuma na fahimci kamar Momy da Dikko akwai abinda yake faruwa.
*_Uhum baya da ƙura kenan_*
Anyi shagali na wuce ni na rubutashi , kowa ta ƙiyasta yadda hankalinta da tunaninta zai iya ɗauka , ɗiyar gwamna ta auri gwamna , ga gidansu amarya da kuɗi ko ba mulki su dama attajirai ne wanda kullum kuɗin nasu kamar aiko musu su akeyi , caf lallai , neman suna ba banza ba , ga wani ya tafi nema amma ya rasa ranshi bai samo ba , su Dikko tun ba a waye da sanin amfanin a sanka ba sukayi suna kuma aka sansu , sun nemi kuɗi kuma sun samu tun ba'asan amfanin kuɗi ba , rabon da naga Dikko harna manta sai yau a wurin party , yayi wani irin wanka na tashin hankali , yasa wata irin sheɗaniyar shadda akayi mata ɗinki "yar ciki wando da babbar riga , gemun nan yasha gyara sai ɗaukar hankali yake , yana tauna cingom a hankali cikin salo mai ɗaukar hankalin duk wanda ya kalleshi , yayi׳ , ya haɗu iya haɗewa , ya burge , yayi kyau harya gode Allah , wallahi an tara duk irin mutanen da baku tunani wurin shagalin nan , amma na rantse muku da girman Allah babu kamar Dikko a wurin , ya haɗu iya haɗuwa yaci taro , yaba maza azaba kuma yaƙi barinsu su huta , duk wani mai kucakin gayu a wurin ya kama kanshi , yana gaba su Ashiru na biye a bayanshi , yana tafe yana jin kanshi kamar zai tashi duniya.... Su Ashiru na biye dashi ɗauke da wasu irin ƙattin jakukkuna biyu , tunda ya doso wurin yake ɓata rai , mutane sukaci gaba da darewa suna buɗe mishi hanya yana wucewa , daya wuce sai abi bayanshi da kallo.
Rabiya dake tsaye kusa dani tajani muka tunkaro hanyar fitowa , wai dan kar in gani , hmmmm , hankalin kowa ya koma wurin Dikko tunda ya shiga inda ake rawa , ya kafe kanshi yaci gaba da ɓara mata kuɗi , makaɗa suka ruɗe , duk wani mawaƙi da aka tara wurin nan ya daina waƙa sunan Dikko kawai yake kira ana mishi kirari , da kuɗin hannunshi ya ƙare sai a miƙa mishi , DK kawai suke kira , dakel aka fiddoshi daga wurin dan bashi da hankali akan ɓarar da kuɗi , idan zai kwana a haka baya gaji kuma bazai daina ba , zaiyi ta zubawa ne baya gajiyawa , haka kuma idan zai bayar yake kyauta maisa ɗimuwa. Wace ce ita.....................???
Nace muku banda labarin Bello ko Dady ko ? Babu ruwansu dani , dan tunda Dikko ya gwagwaÉ—a musu layi akaina , yace musu ko ciwon kai nayi ko naji an kira sunansu bacci a bacci yayi musu rantsu kashe su zaiyi , tou wannan dalili yasa suka fita sabgata....
Mardiyya
Jiddah
Amisty
Hafsa
Saude
A ` e
Tawagar gidanmu , su tuni na siya musu gida kuma har yanzu basu daina harkar bariki ba , danbe da duk wata harkar iskanci.....
Ummu Affan , ita mijinta a saketa , Abbu Afsar wato { Alaji } wanda da Dikko ya tafi dani Babana ya ƙafe ? Wanda ya siya min rigar birthday ? Ya kula da Baba ? Tou har yau ni banda labarinshi , kuma ba abinda ya dameni da sanin halin da yake ciki.
Yazeed
Wace ce Dikko yayi ma liƙe a wurin party...... ?
Mu koma baya......
Gyara zamanshi yayi tare da cewa bara na baku labari , a london na haÉ—u da wata "yar tasha , tunda ta shigo jirgi kawai tayo wurina ta zauna......
Dikko yace ai ban shanyu ba shi yasa zanyi ma Perpy wata Momyn ,
Ashe ni ina tunanin Yusra ƙawar Sadiya matarshi data rasu ne , abinda yasa tace ita maza basa burgeta bata samu irin tsarin da take so ba , shi kuma yace kamar wani sakarai haka ya kalleta ,
Ya ɓoye labarin , haukata ya hana na barshi naji yadda labarin yake na tsaya wani kishin banza da wofi , duk yadda Dikko yake tsaye akaina ? Kuma "yar uwarshi ke tsaye kaina , soyayyar mu da Dikko zakuyi tunanin akwai wata bayan An mata........?
Wane sakaci nayi ne ? Me na rageshi dashi ? Meye yarinyar daya kakkaɓe idonshi ya mata liƙe take masa , Dikko baya zina ya akayi wata macen ke riƙeshi waje har yakai 3 dare bai dawomin gida ba ?
Jamila Musa gareki.......
Jama'a duk wanda ya kalli labarin nan yasan tuni na yankeshi , naso kuyi haƙuri kubi labarin yadda yazo min , ba labarin zamu kalla ba darasin ciki zamu ɗauka , amma sai kuka firgitani , idan kunyi nazari shi labarin rayuwarka yasha banban da labarin shaka tafi , ba ƙirƙira bane ba da zan rubuta muku yadda kuke so ba , kowa da yadda Allah ya rubuto mishi jarabtarshi , kuma babu wanda ya isa ya goge ƙaddar rayuwarshi a yadda tazo ,
Maganar lalurarshi , yace Ashiru yaji da komai , kuma duk Dady baisan anayi ba , bai faɗa masa ba saboda baya so Dady ya saki matarshi dan kar Momy tayi baƙin jini , meya faru bayan Mustapha yakai Ashiru wurin daya ce nan ne asirin yake ? Ya aka ƙare ne ? Ina Al ' Ameen ? Ya mutu ko yana raye ne ? An dai buga mishi lamba haka Dikko ya faɗa tunda bashi nan baisan abinda ya faru ba , Al ' Ameen daya fita daga inda Dikko ya tsareshi ina ya tafi ? Me yayi bayan ya fita ? Meya faru ? Koma dai miye idan ta amince zakuji ya warke ko yana tare da matsalar ne.............?
Duk mai imani yasan akwai jarabta , ni naso na rubuta muku yadda duk zamu ƙaru gaba ɗayanmu , naso kuji yadda Sultana tayi rayuwarta a gidan Dikko dole ta nan zamu warwaro matsalolinmu , mu fahimta inda muke da gyara kuma mu gyara , amma sai kuke cewa bana san Sultana ina bata wahala , bayan bani bace na ɗora mata ba , wasu kuma sai suke zagin Dikko , wasu Sultana , wasu kuma niɗin suke zagi babu gyara babu dalili , daga gyara kayanka ai bai zama sauke mu raba.....?
Nidai ina san insan yadda kissa da kisisina da kuma kwarkwasa take , tafiya magana kallo da dai sauransu , mi ke kawo yawan mace²n aure ? Tou idan mai labarin ta yadda zaku jini , salon labarin zai dawo muku da wannan tambarin..... 👇ðŸ»
*KWARATA RETURN...*
_{Ƙalu bale gareku matan aure....}_
*SAINA AURI DK*
Labarin zaizo muku a kyauta ne kamar dai yadda wannan yazo , bana siyarwa bane ba ,
Ga dai .
*JIDDAH*
*MARDIYYA*
*HAFSA*
*YUSRA*
Kowa a cikinsu saita auri Dikko , su suna waje An mata a cikin gida , gadai Yusra tana riƙe Dikko yana kai 3 na dare yana waje , shi baya zina tou dame take riƙeshi wanda har yake tafiya wurinta yabar matarshi ? Me ta iya wanda Sultana ta raga mishi ? Sultana zata yadda kuwa wata ta shigo ? Koma dai miye idan ta amince zaizo a cikin sabon labari mai taken.
*KWARATA RETURN*
Alhamdulillah jama'a , Jamila tana godiya sosai , sai Allah ya haÉ—amu a sabon littafina in Allah ya yadda 👇ðŸ»
*ÆOYAYYAR SOYAYYA...*
Gasuwa ta musamman gareka *IBRAHIM MUSA QERAU* { Alhajeje } ngode sosai da ƙoƙarin da kayi mana , muna godiya sosai daga kai har mutuminka Mai gida DK , ngode׳ sosai.
Godiya gareku "yan uwana , ngode sosai da irin taimakon da kukemin , wurin ganin kun tayani yaÉ—a wannan labari , ngode sosai da Æ™auna Allah ya daÉ—a zuminci. 👇ðŸ»
*SA'ADATU* {{ AUNTY MUSA }}
*HAWWA MUSA* {{ F JIDDAH }}
*RABI MUSA* {{ MRS USMAN }}}
BISSALAM.
MASOYANA 😊 na barku lafiya , ina matuƙar kewarku cike da maraicinku.......
*RUƘAYYA MATAWALLE* , ina godiya da kyautar rake...... 😘
26/12/2019 👇ðŸ»
Daga alƙalamin
*JAMILA MUSA QERAU...* ngode ׳ Allah ya sake haɗamu da alkairi.