Zumah Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zumah Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 9 of 10
Page 17&18
"Suka ɗaga segarin Jigawa, suna sauka airport wasu sojoji ne sukazo tarbarsu, daga nan suka harba kan kwalta suka nufi garin shuwarim...jadda kuwa bayan ta gama sallar asuba tazo ta duba Khalifa sedai a yadda taganshi hankalinta yayi mugun tashi, cikin tsoro tace "hamisu yazanyi dakai yau ni hauwa kulu inaganin lukutar masifa, wannan yaro haka kajigata? Innalillahi wani Inna ilaihi rajiun, bara nakirasu Sambo suzo sukaimin kai bayi na gyara maka jikinka kajiko. Cikin sauri yariƙe hannunta yana faɗar "aa jadda karki kira kowa please. "Yau nashiga aljanna da izinin uban giji to idan bankirasuba yazanyi hamisu? Tunda nidai bazan iya ɗaukarka ba, kuma bazan barka acikin wannan ƙazantarba. "No jadda karki damu nirakira babban yaya na tabbata yanzu ƴan uwana suna hanya, idan sukazo koma minene zasumin karki damu, yafaɗa da ƙyar, suna haka kuluwa tafito tagansu sarai amma tayi kamar bata gansuba tafice daga gidan.
Fitar ta keda wuya sega dirar motoci jadda taji aƙofar gida kamar zasu tada garin, yara kuwa duk sun kewayesu, harma da manya domin abokanan aikinsu da suka ɗaukosu a airport duk kayan sojoji ne aikinsu, sune kawai ke sanye da kayan gida, Umar ƙananun kaya riga da wando, hakama yaseer, faruk da Yusuf sune kesanye da jallabiya kasan cewar daga masallaci suka fito... Gaba ɗaya mutanen gari sun tsorata da ganin wannan sojojin kamar waƴanda sukazo yaƙi, amma su ko ajikinsu. Cikin kuzari da sassarfa suka nufi cikin gidan, kai tsaye, suna shiga jadda na fitowa, cikin farin cikin ganinsu tace "lale marhabin da mazajen mafa wlh kunzo a dede yusufa ga ƙanenku can cikin halin jinya kuma yaƙi yadda na nemo kowa ate makamin ingyarashi, yace lallai se ƴan uwansa sunzo to tun da ko iso kuzo kuga yadda yakoma mana. Kallonta Yusuf keyi cikin sanyin halinshi yace "karki damu jadda tunda munzo ai komi zezo da sauƙi. Shima yaseer riƙo hannunta yayi yana faɗar "jadda duk kin ruɗe tunda miji ba lafiya ko? "Badoleba yaro yazo lafiya lafiya amma kwatsam abu yasameshi ai doline hankalina yatashi. Tana maganar suna shiga cikin ɗakin da Khalifa yake, domin dai Umar da faruk dukkansu ba wanda yace komai. "Subahanallah little datti hakan abin yayi tsanani domin hakan suke kiranshi wani lokacin basa cewa Khalifa musamman canal Yusuf. "Umar ɗagashi muje toilet cewar canal yusuf yana riƙo Khalifa, suka dagashi su biyu suka nufi toilet dashi, yaseer yazuba musu ruwa yakai musu, shikuwa faruk ya shiga gyara ɗakin batare da wani ƙyanƙyamiba. Acan toilet kuwa, yaseer na kai musu ruwa, canal Yusuf yayiwa khalifa wanka Umar ya wanke kayan da suka cire mishi, seda suka wankeshi tass, kana suka ɗaukoshi, anan dakinshi suka dawo domin faruk ya gyara komai kamar ba abinda ya faru aciki. Wasu kayan canal Yusuf yasaka mishi, kana sukacewa jadda zasu kashi asibiti ne.
Acan waje kuwa ƙofar megari cike take maƙil da ɗan mutun, sabida ankawo me gari ƙorafi akan kuluwa, duk abinda tayi aranar dasu ilu suka biyota anzayyanawa me gari ta haddasa tashin hankali cikin gari kowa ya ɗauka ƴan bindiga ashe itace, gakuma waƴanda suka ƙone da talge sanadin wannan abin sunacan suna jinya, kana gasu ilu akwance rai a hannun Allah domin da ƙyar aka samu suka farfaɗo nan ne suke bada labarin aljanun kuluwa ne suka musu haka, to wasu sun yadda wasu kuma basu yadda ba, sunce bawasu aljanu shaƙiyancinta ne kawai. Gaba ɗaya kowa da abinda yake faɗa akanta da irin ta asar datayi masa, sosai me Gari ya ɗauki zafi hakan yasa yace aje azo nada da ita gabansa har ita har jadda.
Kulawa kuwa tunda ta fito taje gonar mlm audu ta tsinko mango da goriba, kana ta ɗauko hanyar dawowa gida, tana shigowa cikin gari tayi kiciɓis da mlm garba wanda ta yanke wa zakaru jiya tacinye, to yaran dasuganta sun gaya masa shine tafito wuri janjan yana nemanta zeje gidansu, to shinefa yanzu suka haɗu. "Ke kuluwa, tsaya anan dan ubanki waya sakaki kiyankamin zakaru eye? Kece kika yimin kiyonsu to wabillahil azim sekin biyani kinji nagaya Miki muguwar banza muguwar wofi, yafaɗa yana ƙoƙarin damƙota. Baya tayi da sauri tana kwaɗamai harara cikin tsiwa tace "eh ancinye zakarun kuma baza'abiyaba, da wayace kasakesu suje ɓarna da sata agidan mutane? Ai ina da hatsin sata kaciyar dasu, shiyasa nima barage maka nauyin haram ɗin da suke ɗauko ma nacinyesu, kaga na taƙaitama wanda zasu ɗauko ma agaba sekaji da wanda duka abaya, taƙarasa zancen tana murguɗa masa baki. "Ke dan ubanki nizakiyiwa rashin kunya? Agidan ubanwaye sukaci haramun ɗin? Shegiya fitinanniyar yarinya, yana maganar yana yowa cikinta da zimmar yadaketa, haba, ai tsalle ɗaya tayi ta kwasa aguje tana ihu, Shima binta yayi yana faɗar atare masa ita, aiko cikin sauri wasu samari suka taso zuwa kamata, tsallakesu tayi tabi ya tsakanin ƙafar ɗaya tafice aguje, tana ware ƴaƴan goribar data tsinko tana jifansu dashi tana ihun kiran akawo mata ɗauki karto yabiyota, "wayyoo Allah jama'a akawo ɗauki kwarto da rana tsaka, wayyoo zekasheni kwartoo jama'a, hakan take ihu tana kiran mutane kuma tana jifansu da ƴaƴan goriba dana mango, kafin kace me tuni tayi musu rauni domin ta fasawa kusan mutum huɗu kai da giribar ciki kuwa hadda mlm garba, amma hakan suke binta dafe da goshi yana zubar jini. Mutanen da take kira kuwa duk wanda yatinkaro yaga itace seyaja baya domin ba wanda besan wacece kuluwar jadda ba a shuwarim.
Canal Yusuf ne ya ɗauko Khalifa a kafaɗa, ƙanenshi da jadda na biye dashi abaya, yaseer yabuɗemai mota yasakashi, jadda se addu'a take masa, suna cikin hakan sega saƙom megari. Cikin ladabi suka ƙarasa gun jadda sabida ganin wannan zugar sojojin, kana sukace "jadda megari ne kesan ganinki keda kuluwa yanzu a fada. "Innalillahi mikuwa kuluwar tayi yanzu har megari kenemanmu? Ta tambaya a tsorace. "Idan muje zakiji jadda, cewar ɗaya saurayin. "Mike faruwa jadda? Cewar canal Yusuf. "Wai ƙanwarku ce megari kenema nasan kuma wata maganar ta ɗauko, to jekace kuluwa dai bata gida nikuwa kunganni anan jikokina ne sukazo ba inda zani domin jikanane bashida lafiya sabida haka yayi haƙuri sejikana yasamu lafiya zamuzo nida kuluwar, tafaɗa cikinjin haushin kiran domin duk abinda kuluwa keyi jadda bataso datti yasani. "Aa jadda baza'ayi hakaba, bara muje muji mike faruwa tunda Allah yasa munzo, Umar kuje asibiti kaida yaseer nida faruk kuma zamuje gun Kiran da megari keyiwa jidda...kafin ya rufe bakinshi sukajiyo hayaniya da sautin gudu, hakan muryarta tafara sauka akan dodon kunnensu tana kiran kwarto, kafin ta ɓullo kwanar tana gudu tana ihun kiran kwarto su mlm garba nabiye da ita, gakuma tururuwar yaran da suka biyosu, tana isowa inda suke ko kallo su batayiba tabige mercial Umar dake bakin ƙofar gidan tafaɗa ciki aguje.....!
Book ɗin ZUMAH paid book ne 1k kacal 👌zaki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 9112799371 moneypoint sha'awanatu kasim. Idan kuma a Niger kike zaki turawa anan 👉 +2347037092176 My Nita sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on WhatsApp 🙏
Ga kuma wadda ke buƙatar books ɗina biyu zata iya biyan 1500, idan kuma uku kikeso zaki iya biyan 2k 🙏
Autar alheri✍️
[15/05, 10:41 pm] Autar alheri: 🐝🐝 🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝 *ZUMAH*🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
ZUMAH
GAZAƘI GA HARBI
MAGANINKI🙄
(SEDA WUTA🔥)💃
Erotic love funny with sexy story 🥳🥳🥳
Writer by
Autar alheri✍️
🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝
Up'up'upp Dr Yasmeen 🥳💃
Oh'oh'ohhhh 💋🔥
This story bance komai ba 🤭 amma fa idan kinsan bakida miji akusa koda ke matar aurece please ki haƙura kawai zefi🤷
Bismillahirahamanirrahim
Book 1