Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 16 of 28
   (★)★(★)★(★)
  A yau da kwanaki bakwai ke cika da fara case ɗin Jush rikici ya ɓarke tsakanin jami'an ƙasar sa dama ƙasar Dubai. Dan sun ce basu yarda ba da haɗin kan ƙasar budurwar tasa tai komai, dan aikin baiyi kama dana mutumin ɗaya ba musamman yanda suka kasa gane kan gubar da aka zuba masa. A gefe ga ƙyamariro tako ina a gidan amma ace basu naɗi komai daya faru ba. Wannan yafi ƙarfin yarinyar ita kaɗai.
   Tofa babbar magana, dan wannan rikici shine ya fiddo maganar kisan Jush ɗin kai tsaye ma duniya. Saɓanin farko da kawai ana nuna batun kisan batare da sunan wanda aka kashe ba. Sai a yau ne sunan ya bayyana ɓaro-ɓaro tare da hotonsa. Kafin kace mi manyan gidajen yaɗa labarai na duniya sun shiga haskawa da kace nace. Hukumomin Dubai sukai zaman farko a teburin tattaunawa...
   Wannan fa shi ake kira da sunan babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja. Labari da ɗumi-ɗumi mai kekketa zuciya da sanyata bugun fanfalaƙe ya riski kunnuwar ƴan ƙungiyar duhu. Koma muce sun gani da idanunsu, duk da a ranar farko sunga labarin. Kasancewar ba suna ba hoton wanda akai mawa ɗin yasa basu maida hankali ba balle ma abin ya dame su.
   Sannan kaf ɗinsu babu wanda ya taɓa sanin ma Oga Jush ɗin nada gidan sirri a Dubai balle budurwar. A matuƙar gigice kiran wayoyi ya fara kai-kawo a tsakaninsu. Hatta wanda basa ƙasar suka fara haɗo kayan dawowa. Dan wannan al'amari ne daya wuce misalin tunaninsu.
   Tuni waɗanda ke cikin ƙasa kam sun haɗa gangamin meeting na gaggawa. Duk da a babu shiri ne sai ga kusan mutum goma sun hallara. Duk da ma a hakan zaman iya na manya ne. Sauran ƙananun Members na can an barsu da ruɗani da tashin hankalin zuciya. To Oga ya mutu su ina suka kama?.
  ....★“Mike faruwa ne? Mi yake shirin faruwa?!!!â€.
   Mr Specter ya faɗa cikin ƙaraji da gigitar ruɗani jikinsa na karkarwa.
  “Akwai abinda ya kamata mu sani Æ™warai da gaske. Dan duk da anyi kisan a inda ba Æ™asarmu ba, bama yankin mu ba bazamu sakankance da tunanin babu saka hannun maÆ™iyanmu ba. Ashe shiyyasa muketa neman Oga kwana da kwanaki babu labarinsa. Wannan wane irin al'amari ne mai ruÉ—ar da kai?â€.
     “Wannan ya wuce ruÉ—ar da kai, harda ruÉ—anin zuciya. Ni gaba É—aya ma ji nake tamkar hawan jini na na sama.â€.
   “Ni ko ina ganin ba ruÉ—ar da kanmu ya kama muyi ba. A wannan gaÉ“ar nutsuwa mukafi buÆ™ata. Sannan a samar da sabon shugaba. A kuma jira su Viper su iso a sake sabon zama. Sannan fa ba lallai ace abinda ya faru ya farun ne daga É“angaren mu ba. Dan Oga na harÆ™alloli daban-daban a kasashe da ban da ban. Ku duba fa mu dukanmu yau ne muka fara ganin wannan gidan nashi na Dubai. Ita kanta wannan yarinyar gashi masana sunce bincike ya nuna ta jima tare da shi tun tana da Æ™arancin shekaru a duniya. Amma mu bamu taÉ“a sanin ta balle labarinta. Hakan na nufin akwai abubuwa da yawan gaske da suka shafi oga da bamu taÉ“a sani ba. Ba kuma dama ya zama lallai mu sani É—in ba tunda yana aikinsa yanda ya kamata matsayin shugaba akan abinda ya shafe muâ€.
      “Haka ne. Scythe yazo da magana ta hankali kuma wadda ya kamata mu duba. Mu kuma kalleta a matakin nutsuwa hakan zai sama mana kwanciyar hankali da yin nazari yanda ya kamata. Koba komai zamuyi abinda ya dace daga namu É“angaren. Dan ni dai zuciyata tana raya min akwai hannun maÆ™iyanmu a wannan al'amarin. Duk da na rasa ina zan kalla ko kamawa daga É“angarorin maÆ™iyan namu. Saboda wannan aikin duk inda ya fito ya fito ne daga masu Æ™arfin iko da É—aurin Æ™uguâ€.
     “A wannan gaÉ“ar ba'a raina maÆ™iyi. Dan duk maÆ™iyi sunansa dai maÆ™iyi. Dama É—aya yake jira ta halaka. Abu mafi damuna anan yanda komai na Æ™ungiya ya tsaya tsahon wata É—aya kenan. Gashi Oga ya rushe dukkan tsoffin tsarikanmu da shirin gina wasu. Da yanzu nan da kwanaki biyu zai iso domin Æ™addamar da su. Wannan nan babban Æ™alubalene a garemu. A gefe idan ma maÆ™iyanmu basu da hannu a wannan kisan, a yanzu sun samu lasisin farmakarmu. Dan tsohon Janar É—in nan shegen kansa ne. Balle ya tattara akalar mulkin ya danÆ™a a hannun tsinannen nan Zak-Shadow. Na rasa wane irin mutum ne mutumin nan. Munbi duk wata hanyar kauda shi amma kamar munayi a banza. Gubar nan ta Æ™arshe da muke da yaÆ™ini a kanta ma shiru kake ji gashi nan ma ya cigaba da harkokinsa kamar komai bai faru baâ€.
    Shiru ɗakin ya ɗauka. Zantukan da suka tattauna na ratsa su. Musamman ma na ƙarshen nan da suka fi komai shigar su. Dan tabbas da gaske akwai babban ƙalubale a gabansu a wannan gaɓar. Dole ne kuma ɗayan biyu ta kasance a kansu. Ko su miƙe da shirin sabon yaƙi. Ko ayi nasara a kansu ta hanyar da basuyi zato da tsammani ba......
    +++++++++++
   “Amma ke dai baki da zuciya wlhy. Yanzu kina nufin komawa zakiyi?. Ke ko kishin kanki baÆ™yayi da Dad. Duba fa tunda kika baro gidan uwarsu ta kira taji nan kika zo babu wanda ya sake kiran mu har itaâ€.
      “Ni dai babu ruwan ka. In ma bani da zuciyar ai tawa ce ko. Kai ko bance zan koma ba ai kace na koma. Jiba fa inda muke a É—akin hotel guda É—aya jal mu huÉ—u. Ni kaÉ—ai mace a cikinku. Duk da kuke Æ´an uwana idan son zuciya ya raya muku cutar da ni fa, tunda Dad ma ba kullum muke ganinsa ba.â€
    “Amma Hanoon baki da hankali. A cikinmu ubanwa ya taÉ“a yi miki wani abu mara Æ™yau?â€.
   “Idan bakuy min ba ai wataran zakuyi min. Ince kai randa nazo a bayi na sameka da yarinyar mai aikinmu ta da. Ka iya zama ka lallaÉ“eta ta kawo maka kanta shegiya ko sisi bata samu sai wahala. Ƙarshe ma itace ke baka kuÉ—in. Sannan gashi nan abinci ma sai mu yini bamu ci ba muna wahala. Ko É—akin Hotel É—in badan Dad ya jima da biyan maÆ™udan kuÉ—i ba a kansa mun isa mu zauna?. Ai har ku É—in dole ku koma can. Dan haka ni dai ba zan zauna ba. Gara na koma.â€
     “Humm munafuka, kedai kice zaki koma saboda wannan tsohon dattijon da girman jikinsa ke kwasar kiâ€.
     “In ma dan haka É—in ne ina ruwanka. Kaji da taka damuwarâ€.
   “To wa zai baki kuÉ—in jirgi?â€.
  “Ina ruwanka koma wazai bani tunda banzo nace kai ka bani baâ€.
Hanoon ta faÉ—a tana jan akwatinta ta fice ta bar su Afeef da Dayyan da kallon juna baki sake..........âœï¸
_Zaku sameshi a waÉ—an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.