Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Kida A Ruwa Part 4 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 7 of 28
{%}%{%}%{%}
Da yammaci su Dadah ne ke shan iskar ni'imar dake mamaye da tekunn.. Suna zaune ne daga waje dan haka suke jin armashin iskar da sanyin ruwan. Dadah ne a zaune Nimrah na daga kwance sai dai kanta na'a cinyarsa ne. Labari take bashi yana faman murmurshi. Dan labarin nata ba ƙaramin nishaɗi yake bashi ba.
Ita kanta ta fahimci hakan dan haka taji bata jin gajiya. Wayarsa dake gefe ta motsa, koda ya ɗauka ya duba saƙon Imran ne ke sanar masa mutumin fa ya sauka yanzun nan. Komai Dadah baice ba ya maida wayar ha ajiye. Hankalinsa ya sake maidawa ga Nimrah....
^^^^^^^^^
Anan kam anayin magriba Mole ya baro gidan su Mammah. Dan saƙo ya samu daga Dagger cewar ya same shi a hotel ɗin da yake. Saboda wannan karon ba hayar gida ya kama ba a hotel Dagger ya kama masa ɗaki saboda shirin su.
Ya iso hotel ɗin ana sallar isha'i. Dan ya samu jinkirin isowa saboda hold up daya ɗan riƙe shi a hanya. Kwance ya samu Dagger a gadon sa. Ya kawar da kai yana jin wani haushinsa. Sai dai a zahiri bazaka taɓa gane hakan ba. Sai ma cikin girmamawa ya fara gaishe shi da faɗin,
“Sannu da zuwa Oga”.
Zaune Dagger ya tashi, yana amsa masa da, “Kaima sannun ka. Ai harna fara tunanin ko baka ma taho bane”.
“Ka bari kawai go slow ne ya riƙe ni.”
“Okay, faka-faka zauna muyi magana dan akwai inda zanje. Ya ake ciki inata neman layinka baya shiga?”.
“Network ne kawai. Amma nima fa nata nemanka tun a jiya bai je ba. Sai na haƙura saboda nayi niyyar yau naje can dama”.
“Ai ba sai kazo ba, saboda ina son aikin nan ya tafi yanda ya kamata. Yanzu dai yaya?”.
“An samu matsala, domin basa ƙasar ma.”
“What!”.
“Kwantar da hankalinka Oga. Kasan dai babu abinda zai faru. Dan malami na yasan aikinsa. Yanda ya tafi da ita haka zai dawo min da abata. Yanzu abinda nake gani mu tafi shiri na gaba kawai”.
“Ba shirin bane damuwata, karfa aje a samu matsala. Dan wlhy ya taɓa min Mata naman jikinsa ma sai an tattara da cokali kafin a bizne. Kai ma kuma bazan ƙyaleka ba”.
“Babu ma abinda zai faru.”
“Zanfi kowa son haka. Maganar shiri na gaba ina ganin muɗan jinkirta shima. Abinda nake son ka bincika mana ranar da zasu dawo. Sai muyi amfani da wannan damar ku aiwatar. Ni kuma ina da sabon shirin da zai jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya.”
“Amma Oga......”
“Kayi kawai yanda dace”.
“Shike nan ba damuwa.”
Mole ya faɗa yana danne ɓacin ransa. Shi kuma Dagger ya miƙe batare da ko sallama ba ya fice a ɗakin. Dan akwai aikin da zai yi. Kuma su Mr Specter ne suka saka shi.
Da harara Mole ya bishi. Cikin zuciya yace (Matsiyaci, ALLAH ya kaimu. Ba kaine zaka jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ba nine zan jefa. Dan daga ranar zaka rasata. Rasawa na har abadan. Bawai ita kawai ba, hatta ni daga ranar zan ɓace maka. Dan yanzu kam nafi ƙarfin zama a ƙarƙashin ka. Nima gashin kaina zan fara ci sannan lokacin cika burina a kanka yayi) murmushi mai yalwa da faɗi ya suɓuce masa. Ya cije leɓuna yana miƙewa, dan dole shima ya fara sabon shiri kenan.....
>>>>>>%<<<<<<
“Dadah wai ina zaka je?”.
Nimrah ta faɗa hawaye na ciko mata ido. Jacket ɗin da ya ɗauka ya ƙarasa sakawa. Juyowa yay yana kallonta. Cike da lallashi ya furta, “Zo kiji na faɗa miki wani abu”.
Kafaɗa ta maƙe masa. Hawayen da take riƙewar suka silalo. Hannu ya kai ya ɗan murza goshinsa. Sai kuma ya ɗanyi hanzarin riƙota saboda yanda ta juya fuuuu zata fita. A jikinsa ya sakata, ita kuma ta shiga mutsu-mutsun son ƙwacewa.
“Ni dai ba ruwana da kai. Ka ƙyale ni. Kuma sai na faɗama Mammah kullum-kullum yawo kake tafiya ka barni ni kaɗai.”
Murmurshi yayi mara ƙarfi yana shafa bayanta.
“Idan kika ce babu ruwanki dani ai ƙura ta tashi kenan. Ke ce fa mai kwantar da rikicin nan da babu mai iya tunkara. Kiyi haƙuri kinji Babyn Babien ta. Bazan daɗe ba, abu ne mai muhimmanci shiyyasa zanje. Dan yana cikin dalilin zuwan mu nan. Faɗa min mi kike so na sayo miki”.
“Ni tsoro nake ji”.
Ta faɗa murya na rawa.
Fuskarta ya ɗago. Ya share mata hawayen dake zirara. “Haba Little Tiger ɗina, nasan fa ke ba matsoraciya bace. Kuma zan bar miki wayana aro ba sai ki kira su Mammah kuyi hira ba. Idan kuma cikin ma'aikatan can ɗaya tazo ku zauna to?”.
“Naji to ka bani wayar”.
Murmurshi yayi kaɗan, tare da rankwafowa ya sumbaci bakin da take tura masa. Idanunsa na cikin nata da raɗa ya ce, “Kin tabbatar kin haƙura ba zakiyi kukan ba idan na tafi?”.
Kanta ta jinjina masa.
“Good girl”.
Ya faɗa yana manne lips ɗinsu. Wani kalar nutsatstsiyar sumbata ya shiga mata. Sai da yaji jikinsa na neman rikicewa ya barta. Da sauri ta juya masa baya saboda kunya. Ya lumshe idanunsa da suka canja launi ya sake buɗewa a kanta. Sai kuma ya matsa ya sake rungumeta ta baya. Hannunta ya riƙe cikin nashi.
“Thank you AMANAR HAYSAM. Nayo miki tsarabar?”.
Kanta ta jinjina masa. Ya sake faɗin, “Mi kike so?”.
“Chocolate”.
“Lips ɗin nan ne Chocolate ɗin ai.”
Ya faɗa yana shafa su da yatsunsa biyu. Baki ta buɗe kamar zata cije shi. Ya janye su yana murmurshi.
“Kin zama kura ko? Sai me kuma za'a ƙaro miki?”.
“Ice-creeam”.
“A'a banda shi. Dan akwai sanyi anan. Canja da wani abun dai”.
“Komai ma to ka sayo”.
Wuyanta ya sake sumbata, sai kuma ya saka mata wayarsa a cikin hannu ya sake ta.
“Bye bye”.
Ya faɗa yana ficewa batare da ya kalleta ba, dan yasan zata iya saka masa kuka. Aiko kamar ya sani, tana hawayen ta matsa jikin window tana leƙen sa. A gaban idonta ya hau mashin ɗin ruwa aka buɗe masa jirgin ya fice da wani irin gudu na ƙwarewa...........✍️
Mubi su Dadah muga wa za'a cafko? Ko mu tsaya wajen Nimraty?.🤭🏃🏼♀️
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*
*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.