Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 1 of 22
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: π€ππ€π
RABON KWADO....
BOOK 3
πππππ
NA NANA BMB.
ππππ
BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM.
π€β€οΈπ€β€οΈ
page 1 -2
Shirune yakasance a parlour din domin kowa dahalinda yashiga cikin yanayi me tsanani mummy tace shin yaya menene wannan dalili dazesa kahana mujaheed auren meenal?
Shiru be tankataba,
Muhammad cikin wani yanayi yataso shima yazauna gefen mujaheed wanda yakejinshi kamar ba aduniyaba saboda tsananin tashin hankalinda yashiga,murya a raunane muhammad yace daddy kayi hakuri katallafawa farin cikinsu kada kayi musu haka suna kaunar juna daddy tunda yafara maganar daddy yake zuba masa wata muguwan harara.
Ganin daddy bazeyi magana bane yasashi kama hannuwansa yana cewa ina rokonka daddy kada kayi haka na tabbatar mujaheed zebata farin ciki har karshen rayuwarta,
Cikin tsawa daddy yace, MUHAMMAD KAENE MIJIN MEENAL!karigada kazamo miji agareta mijibincinta arayuwa!
To me karatu kowa poster yay a cikin parlour dinnan nepa din kowa seda tadauki, shikuwa mujaheed hannu biyu yasa yadafe kirjinsa saitin heart dinsa yana kallon daddy cikin firgita,
Galala da baki muhammad yace daddy kamar yaya? banganeba kamanta ni yayan meenal ne?
No muhammad yau komae zezo karshe tunda haka tafaru kacire wannan aranka daga yau domin kae mijine agareta,
Wata irin mikewa auntie tayi cikin firgici tace " WHAT" daddyn muhammad kasan mekakeson aikatawa kuwa? daddy beko kalletaba, Inna tafara salati tana sallallami yanzu dannan saboda danka zaka hana mujaheed yarinyar nan wani irin haline wannan kuma kake shirin daukarwa kanka?
Mikewa yayi yacewa da inna ina zuwa yanzu,
Koda yahaura sama befi yan mintinaba yasauko daukeda wani dan box me kyau yazo yazauna zuciyan auntie jitake kamar zata faso waje saboda tsananin bugun datakeyi mata,
Yar akwatun yabude yaciri wato farar takadda aciki yabudeta koda zefara karantawa seda yadago yakalli kowa yaga yadda suka maidashi TV kae tsaye yasoma cewa..
SHEKARA TA DUBU BIYU DA SHA UKU GA WATAN BAKWAI RANAR JUMA AH DUNMIN AL UMMAH SUKA SHAIDA DAURIN AUREN MUHAMMAD DA AMINA BISA SADAKI DUBU HAMSIN A BABBAN MASALLACIN JUMA AH, LIMAMIN MASALLACIN MALAM SHEHU IBRAHIM SHINE YAJAGORANCI WANNAN AUREN, ALLAH UBANGIJI YASANYA ALBARKA ARAYUWAR AURENSU.
Jisukae yaraf mimi tayanke jiki tafadi asume itakuwa auntie tundaga zsaye tayi zaman dabaro saboda tashin hankali mummy ce tayi gun mimi tana salati itada innah itakuwa nana saboda rudu batabi takan mimin bah ta isa gaban daddy tana cewa yanzu daddy duk wannan shekarun meenal tanada aure kenan?
Daddy be kulataba sema ruwa daya dauka ya guntsa abakinsa yaje yasoma fesawa mimi ahankali kuwa taja wani dogon numfashi tasoma bude idanunta tana wani marayan kuka mikar da ita daddy yayi yakamata yaje yazaunar da ita gefen muhammad wanda shida mujaheed dukansu sunyi suman zaune, kudi yaciri cikin akwatun yadanka mata yace meenal ga sadakinki nan daga rana irin ta yau muhammad mijine agareki wanda badon komae nahada auren nan nakuba sedan nawanke zargin da wasu mutane sukemin akanki.
jada baya mujaheed yafara yana girgiza kae yana karanto duk addu ah datazo bakinsa ba abinda yake tunawa se abinda ya aikatawa mimi a garden din gidansu, mimi na kuka tace daddy taya aure ze hallata tsakanina da yayana meyake shirin faruwane? kafin tarufe baki shima mujaheed yasome ya mimmike akayi kanshi shima se ruwa ake antaya masa amma ba alamun motsi atare dashi daddy yace sukamashi atafi hospital muhammad dukda jikinshi yana rawa haka yatemaka akasa mujaheed a mota mummy tanata kuka haka mimi a sukwane muhammad yaja motan suka tafi,
auntie tana zaune takasa ko motsi se nanace takula da halinda take ciki ta isa gareta tariketa tana girgizata auntie menene yasameki sam bata fahimtar me nana kematama,
Kallonsh mimi kawae take gaba daya al amarinnan ya cukwi kwiye mata kwanya hawayene keta ambaliya a idanunta tabbas tana cikin tsaka me wuya gaskiya takusa yin halinta cikin zuciyanta tana cemewa meenal kina cikin wani hali kina kaunar yousep sedae ayanzu kedashi sedae kallo daga nesa, koda muhammad yafado mata arae kukanta yakara kwacewa cikin zuci tana cewa nashiga ukuna ni mimi yazanyi da wannan bawan allah wata zuciyan tana cemata kawae ki gudu gidanku kome ze faru yafaru....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: π€ππ€π
RABON KWADO....
BOOK 3
πππππ
NA NANA BMB.
π€β€οΈπ€β€οΈ
page 3-4
Suna zuwa hospital aka soma bawa mujaheed temakon gaggawa seda awanni biyu suka shide tukunna yafarka yasoma kuka kamar karamin yaro muhammad yana gefenshi yarike masa hannu nujaheed cewa yake meyasa allah ze jarabceni da aikata laifi ya ubangiji kaga zuciyata kagafarceni, muhammad kayi hakuri kayafemin dumin matarka dana faraji kayi hakuri kallonshi kawae muhammad yake yarasa gane inda magan ganun mujaheed suka dosa dob basosae yake iya ganewa ahalinda yake ciki yanzu, hawaye yasoma share masa yana cewa babu laefinda da ka aikata my sweet broda kadena kuka ka kwntar da hankalinka indae masoyiyar kace zaka sameta saurin girgisaamasa kae yayi yace no muhammad kada ka kuma farta wannan maganar ko bayanraena kasaki meenak ban yafe makaba abinda daddy yayi yay daedae kuma ina goyon bayanshi,
Shiru muhammad yay masa akan maganar yanata rarrashinsa shikuwa inya tuna da abinda ya aikatawa mini a garden seya rintse ido zuciyanshi tana masa zafi yanzu matar muhammad ya lalube gaskiya kam yay asara,
Se aka sallameshi suma tafi gida mummy koda taga lokaci daya yadda dan nata yakoma inaga nan gaba tasoma zubar hawaye tana matukar tausayin dan nata, dama yau bamagar dinner kowa takae takae seda aka dawo sallar ishah ne baba yace kowa ya hallara a parlour zeyi magana, auntie taci kukanta takoshi tana ganin kuma takama ranar tonin asirintace sam bata taba tsammanin daddy zeyi mata hakaba arayuwa, seda kowa ya hallara a parlour baba yay gyaran murya yadora dacewa...
Ita rayuwa dum ayadda tazowa mumini hakuri yake ya ansheta duk wannan abun daya faru makkadarine daga allah shekara kusan shidda kenan da auren muhammad da amina zuwa bakwai dalilin yin wannan aure kuwa shine, zariginda mutane sukeyi masa akan amina wasu suna ganin amina 'yarsace tacikinsa shiyasa ya yanke wannan hukunci cikin masu zarginsa kuwa harda matarsa maryam mun boye batun aurenne smse muhammad yakara mallakar hankalin kanshi ya isa rike iyalanshi tukunna kuma ALHAMDULILLAH, Yanzu anyi abu akan gaba komae yau yazo karshe,dubanshi yakae kan mimi yace amina nasan zuciyanki ciki take da rudani to amma kiyi hakuri ki fawwalawa allah duka lamarinki maganar gaskiya marainiyaceke abubakar rikonki yayi kuma kigodewa allah daya hadaki da marika nagari kicire komae azuciyanki kiringumi mijinki kibisi sauda kafa, allah ne kadae yasan nufinshi yasaka kaunarki azuciyan mujaheed, inaso kaima mujaheed kayi hakuri karumgumi kaddara dadage da addua ah allah ya saukaka maka abinda kakeji azuciyanka sannan ga kanwar kanan nana indae zuciyanka ta aminta da ita munkaba ita sedae bazamuyi maka auren doleba, wata zabura mimi tayi zata mike caraf suka hada ido da muhammad yana mata wani irin kallo dole tagyara zamanta dama yana facing dinta sabida haka taki dagowa seyanzu hawaye kawae ke bimata fuska yanzu tanaji tanagani ua ah rabata da mujaheed abin kaunarta wanda saboda shine taki furta gaskiya akan kowacece ita,
Itama nana a kidime tamike jin furucin kakan nasu datayi daddy kuwa yadaga mata hannu takoma tazauna tana hawayen takaeci mujaheed kansa a sunkuye tunda suka zauna yace duk hukuncinda kuka yanke akaena daedaene banida zabi ayanzun baba yay murmushi yace yayi kyau allah yazaba maka mafi alkhairi arayuwarka suduma sukace ameen,nasihohi yashiga yiwa mimi da muhammad mussamman shi kan cewar yarike marainiyar allah tsakaninshi da allah kada yabasu kunya yakuma amince, tambaysrsu yay inda wanda yakeda abin cewa se a lokacin mummy tabawa daddy hakuri akan haushinsa data faraji ayanzu kuma tafahimceshi,shima mujaheed haka yabashi hakuri yace abinda yay daedae ne yana goyon bayan hakan kuma yaywa muhammad addu ah zaman lpy shida matarsa, sosae daddy yaji dadin hakan da mujaheed ye fuskanceshi ,
Hka taron yawatse kowa yanufi makwanci yana sake sake azuciyansa kotakan auntie daddy bebiba yaje yasama kofansa key don karma tashigo tamasa shirme,
Mujaheed yakasa bacci haka muhammad kowa da abinda kemasa ciwo a zuci to bangarensu mimi hakan take kowacce tana matsar kwalla taya zasuga samu suka rashi koma meze faru mimi taci alwashin bazata bari a rabata da mujaheed bah, to wannan kenan
WASHE GARI
Duka gidan babu wanda yatashi dawuri da alamu daren jiya babu wanda yadamu ishasshen bacci,.
Koda karfe 1 taharba su mummy sungama shirinsu tsaf natafiya bauchi mimi taki fitowa tace batada lpy harsu ka tafi bata saukoba muhammad bekuma bi takantaba yacigaba da sabgarshi da la asar shima yakae daddy airport don yaune zewuce dubae shima, jiki na tsuma nana takira mardiyya tasanar mata duk abinda yake faruwa tasoma rabka salati tasa kuka daga tsaye tasaki wayan saboda dimuwa ta tawarwatse,nana wayan meenal tasoma bincike acikinta daedar nan kuma mimi tafito awanka nana tae saurin aje wayan takwanta da ido mimi kawae tabita,
Da daddare mimi tana kwance abin duniya ya isheta nana tace yanzu meenal yazakiyi da yousep kenan? mimi bata ko kalletaba bare ta tankata zuwa yanzu tasoma sabawa ma da wannan iskancin na mimi seda takuma tambayarta anan tace mata nabar mikishi,nana tai shiru batae tsammanin jin haka daga bakintaba basarwa tayi tace to wae ayaushene kuka fara soyayya da ya mujaheed bamu saniba?mimi tagaji da tambayoyin nan na nana ga halinda take ciki cikin jinhaushi tace nafara sonsane asanda nagono kina son ya yousep cikin cikin jin haushi nana tace to ubanwayace miki ni inasonshine?dukda halinda mimike ciki behana tayin murmushi ba tace am sorry yaya namanta ay kincewa su daddy kinada wanda kikeso shikenan shizan zaba masa mata wadda ta dace,
Nana tayi murmushin bakin ciki tace to matar ya muhammad yazakiyi da mardiyya masoyiyarsa natabbatar yanzu tana hospital bayadda banyi dakeba kidena biyewa mardy komae nashi kina gaya mata ashe sirrin mijinkine kike barbada mata kinyi kunnen uwasshegu da abinda nake gaya miki aihmga irin tanan harda cemin kinyi alkawarin seya aureta inzuba ido insha kallo ido yanzu nasoma zubawa ma, sam mimi taki tankata don takasa gane inda maganarta tata ta dosama, wayar nana ce tayi ringin koda taga mekiran nata kuwa tasaki dariyar mugunta tana dagawa yace turomin yarinyar nan tasameni a garden kit ya yanke wayanshi, nana tace sabon salo yaukuma sweetien ce tadawo yarinya kallon mimi tayi tana dariya tace to ke gareki mijinki yace kisameshi a garden cikin kidima mimi tamike tasaki kukan tausayi tace narokeki yaya kice masa nayi bacci,
Nana takuma bushewa da dariya tace narasa yaushe ya muhammad yazama dodonki dabaki kaunar zuwa inda yake mimi takuma cewa narokeki yaya mikewa itama nana tayi tace wlh bazan gaya masaba kinsan yanzu zeshigo yakama zazzaga masifa kitashi kawae kitafi abinki yarinya garama kiriki mijinki shene mafi a ala agareki,mimi jitake kamar taringa falla mata mari suna cikin jayay yakuma kiran wayan tana dagawa yace bata wayan, takuwa saka mata akunne don tasan bazata amsaba cikin hassala yace shin zaki zone ko kuwa inzo in sameki dakaena? koda taji hakan bata jira komaeba tasuri hijab tafice,.
Ayanayinda tahango muhammad ne yakara sawa zuciyanta ta karaya tajuma a tsaye sannan yace zamanne bazaki iyabane?haka dae tasamu tadan dosana agefenshi kasa yay da voice dinsa yace kinason mujaheed? tayi saurin daga masa kae tace ina sonsa inna rasa shi bansan ya rayuwata zata kasanceba,muhamammad yay murmushi yace good zakuwa kisameshi amma idan kika fadamin gaskiya kifadamin abinda yake faruwa shin wacece kene kuma ina matata take kiyimin bayani harta daddy yasoma tantama akanki cikin zubar hawaye tace yanzu nan yaya baka yarda dani harseda ka gayawa daddy,shiru tayi tana tunanin gidansu tabbas tasan yanzu bikinsu yakusa itada bassam muddin tayadda takoma kodame take yawo se abbansu ya daura arennan kuma abind babazata iya juraba kenan bazata yadda takoma gidaba tana fada masa gaskiya tofa gidansu za ah tafi ita yazatayi yanzu katseta muhammad yakuma yi da tambayarta, cikin wani irin yanayi tace meyasa wae ka kasa aminta danine muhammad yay murmushin mugunta yace sorry my wife nadena miki wani tunani dama ina cikin yanayine nakirakine domin kisani cikin shauki yanzunan idanunta kamar zasu zazzago tadago tana kallonsa ido cikin zubar hawaye tace nibansan mezanyi makaba kayi hakuri, seda yagama nazartatta tukunna yace kiss me! saurin barin gurin tayi tamike tsaye tana girgiza masa kae hannu yasa zedawo da ita inda take takara jada baya cikin daure fuska kuwa ya fisgota taizaman dabaro harseda taji zafi tarintse idanunta, i said kiss me yakara gaya mata mimi tasaki kuka tace wlh yaya bazan iyaba meyasa zakayi min haka,
muhammad yajinjina kae yace ok naji bazaji iyaba namiki uzuri yanzu nasan kinajin kunyata amma gaba zakiyi nasan tashi kitafi ciki abinki,tamike jiki nabari kuwa tai cikin gidan yakuma kiranta kamarta kurma ihu ta juyo yace shiga bedroom dina ki daukomin wayata yanzu ina jiranki kada kuma kibatamin time sanyi mimi taji azuciyanta tashiga ciki harda gudunta muhammad yasaki murmushin kyeta yace yarinya kenan yau zakiyi bayani don wlh yau sekin fadamin gaskiya zan kyaleki donnaga kinada taurin kan masifa mikewa yay yarufa mata bayashimaπ...
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: π€ππ€π
RABON KWADO....
BOOK 3
πππππ
NA NANA BMB.
π€β€οΈπ€β€οΈ
page 7-8
Auntie tana cikin waya taga nana ta fado mata daki a firgice da mamaki ta kashe wayan tana kallon nana tace lafiyanki kuwa? cikin kuri kuri da ido tanata haki tace wlh auntie meenal aljanune suka shigeta nifa tun wannan tafiyar datayi gaba daya meenal tasauyamin gayamikene kawae banba kullum cikin baccinta inajin tana wani yare to wlh yanzu harshen natama yajuye se hauka take ita kadae nidae bazan iya kwana a dakinba wlh wae seta auri ya mujaheed tanata hauka, cikin tsananin farin ciki auntie tamike tasoma babbaka dariya harda tafawa sannan tace zokiyi kwanciyarki anan nana aljanun su haukata ta itakadae ninasan abinyi yikwanciyarki kinjee nana jiki a sanyaye tahau kan makeken bed din na auntie takwanta tae tsumu mamakin mimi gaba daya yahanata sakat,
WASHE GARI
Nana dakyar ta iya tunkarar dakin nasu tana tsoron kada mimi ta danketa shahada tayi ta tura kofan ahankali tashiga dae dae lokacin kuma mimi tafito daga wanka idanunta sunyi luhu luhu saboda kuka ko inda nana take bata kallaba tazauna gaban dressing mirror tana mutsika mae duk abinda nana take tana ankare da ita sedae taki kallon inda takema, wankan nana tashige itama abinda haka zalika koda sukazo breakfast su hudu a dining nana se kallon mimi take takasa cin nata abincin haka itama mimi yanayin datake ciki yasa takasacin komae, gyara zama muhammad yay yana murmushi yakalli mimi yace my wife kici abincin mana haba kinsan banason damuwan nan naki ina tare dakefa akowani lokaci so kada kikara sama kanki damuwa kinji kodae dakaena kikeso in baki? daga mimi har nana baki sake suke kallonsa saboda yadda yay maganar shagawaba, harda kanne mata ido daya,wani dogon tsaki auntie taja tana antaya musu harara,lura da hakan da yayine yasashi gyara zama yace yawwa inaso natambayeki dama shekararki nawane yanzu?cikin sanyinta mimi da mamaki kuma tace 18 years WOW kinga kingirme 6ter dinki ita tana 17 yanzu mimi tayi murnushi jin yadda muhammad yake mata magana ashe haka yake shine jiya harda sharara mata mariπ
π
cikin jin dadi tace kundace kaeda matarka inayaku da murna yabaku zaman lpy gashi bantaba ganinta ba,muhammad yaji dadin addu ar tata yace ameen ya allah kada kidamu indae 6ter dinkice zaki ganta cikin kwana biyunnan, nan danan idanun mimi suka kawo ruwa tana kallonsa tana girgiza masa kae zatayi magana yadaga mata hannu yace no dolane ne fah kisa aranki wannan tafiya anyishi angama tayama zan kyale banason kukan nan naki babu abunda ze faru ki kwantar da hankalinki, kukan nana ne yasa su suka juya suduka suna kallonta ta rukumkume auntie tana cewa wlh maganata gaskiyace ashe ba meenal bace aljanune ashe ya muhammad ma yasani jiya inajinta tana sumbatu muhammad yasaki murmushi bekae karsheba dariya ta kufce masa haka mimi tana darawa tana kallon ikon allah gurin nana, dukda magan ganun nasu sunsa auntie aduhu hakan behanata dakewa ba cikin tsawa tace banason hauka nana meyake damunkine?
Muhammad mikewa yayi yace wify muje garden mukarasa tattaunawa tunda naga tunyanzu anfara tsorata haka inaga nan gaba kuma?cikin bakin ciki auntie tace to don allah daga garden din ku bulla ta China kada kudawo mana nan karamin mara kunya kaega me mata koh!
Shidae muhammad ficewa yayi yana dariya mimi tabi bayansa sebayan sun zaunane yake cemata mimi inason kigayamin gaskiya shin kece mujaheed yatabawa jikinta ko meenal ce?wata irin kunya kuwa takama mimi kanta aduke tace nice ba meenal bace, muhammad besan sanda yasaki ajiyan zuciyaba yana godewa allah a zuciyansa tanason magana takasa, seda yabudi baki zeyi maganar ne ta tareshi da cewa dama abisa tsautsayi abin yafaru yatabani badon yana...Sekuma tayi shiru,
Muhammad yasaki shu umin murmushi yana cije lips dinsa azuciyansa yana cewa shegennan bakada dama wlh ayzamu hadu, sunjima suna tattaunawa a garden din wanda hakan yakara samusu fahimtar juna yafahimci so silent ce ita amma yana mamakin yanda kowa yaki fahimta duk karadi irinna meenal.
Yau talata takama ranar tafiya adamawa duka an hallara su inna da baba mummy da daddyn mujaheed dashi din kansa harda kanwar mahaifiyar muhammad hafsa,mimi kwallace tacika mata idanu ganin mujaheed yadda yakoma a 'yan kwanaki yawani rame se 'yar fuska, daddy tinda yadawo yake kallon mimi yana kara gasgata maganar dannasa dasukayi awaya, tunda garin allah yawaye auntie taketa faman sababi da masifa da tujara akan me za ah kirkirar musu tafiya adamawa kuma aki fadan abinda za aje yowa shidae daddy ta tafasa bece mataba yamayi kamar besan tanae bah anata shirin tafiya donkosu baba da inna basusan neza ahje yowa canba,
Mujaheed suna bedroom suna shiryawa yakalli muhammad yace waekae waca irin tafiyace wannan muhammad ka kaga mana anki kuma sanar mana abinda zamuje yowa,muhammad yay murmushi yace to maida wuyar aure zamuje nema maka wani irin kallo mujaheed yamasa yace kamarya? banganeba!manta kawae to inmunje can ka gane,
Wae kuwa majaheed dakukaje bikin sameer babu abinda yafaru da meenal,mujaheed yay shiru yana tunano abinda yafaru,cikin rashin fahimta yace kamarya ba abinda sameta?muhammad yay murmushi yace ina nufin bata tafi wani gurin kunnemeta kunrasaba?mujaheed cikeda mamaki yake kallon muhammad taya akayi yasan hakan kodae meenal tagaya masa komaene kallonshi yayi yace eh bamu nemeta munrasaba ya akayi kake tambaya, muhammad yace babu komae tasowa mujaheed yay yana cewa wlh karya kake da akwae wata akasa,
Muhammad yana murmushi yace to shikenan kabar komae semunje can zaka fahimci komae basena yimaka bayani bama pls kayi kashirya kasan da tafiya agabanmu, cikin jin haushi mujaheed yace a ah tafiyace a bayanmu ba agabanmuba! muhammd yakuwa bushe da dariya mujaheed yakyaleshi yacigaba da saka kayansa,muhammad kuwa turaruka yake fesawa kala kala zuciyanshi taf da farin ciki yau zega sweetienshi shigan dayayi tamatukar yimasa kyau yasha shaddi brown light tanata zuba uban kyalli haka hukansama daya dora shikansa daya kalla kansa a mirror seda ya kanne ido daya, shikuwa mujaheed boyel ne yasaka me tsadar gaske peach color kalarda mimi take matukar kaunar soh sosae yahadu inkace zaka tsaya tantance wanda yafi wani kyau acikinsu bata time ne ma, suka fito a tare abin sha awa, mimi koda tahango sahibinta batasan dmsanda tai gunsaba tarikeshi tana murna tace ya mujaheed baka taba yimin kyau irin na yauba pls katsaya muyi selfie,zuciyan mujaheed kamar zata fado dama yaya karfin hali kawae yake koda camera tahaskasu kasa fara ah yayi seda tasaki nata murmushinne tukunna besanda sanda yay nashi smile dinva shima tabbas yabada kala wadannan couple din abinda sha awa, mota biyu sukayi abinsu ta tafiya sunbata lokaci sosae gurinyin hotuna kafin akadauki hanya kuma dodar muhammad baki yaki rufuwa....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: π€ππ€π
RABON KWADO....
BOOK 3
NA NANA BMB.
π€β€οΈπ€β€οΈ
page 5-6
Sam mimi bata kawo komae azuciyantaba tana shiga tawuce bedroom dinsa kae tsaye tana shiga wani ni imtatceb kamshi yadoki hsncinta harseda ta lumshe idanunta, dube dube tasoma sedae bataga wayanba sema photon meenal dataci karo dashi amanne ajikin bango kamar zaka kirata ta amsa tayi dariya bakaramin kyawu tayiba a hotun tabbas ta tsaya gaban hoton aka kalleta anan za aga banbancinsu tana duniyar tunani taji huci a gefen face dinta ta dago a tsorace suka hada idanu yasakar mata murmushi kuwa, cikin tsaraka da idanu tasoma cewa yaya wlh bangantaba seda yakarewa hoton meenal kallo sannan yakalleta yace kema kinyi mamaki koh shiyasa kika tsaya kallonta, wani irin yawo tahadiye don tama rasa bakin magana, muhammad kallonta yake cike da mamaki shin wacece wannan haka datazo tarainawa kowa hankali haka kodae fuska tasakane irinta meenal dinshi, mimi kanta yana kasa sejin hannun muhammad tayi a face dinta kamar ze yage mata fuska tasaki kukan azaba zataja baya yakuma riketa sam bega wani alamuba cikin masifa yace tell me who are you?kuka mimi kawae take taki tankashi kara matsowa yayiyace ina saurarenki cikin kuka tace bansan mezance maka ba kuma kadena min haka banaso, rintse idanunsa muhammad yay saboda takaeci da bakin ciki cak kuwa tajee yadagata bedireta ako inaba se akan bed zuwa lokacin idanun mimi zazzagowane kawae basuyiba don firgici kallonta muhammad yake kuzata saduda haka tagaya masa gaskiya amma ina sema kokarin sauka datakeyi yakuwayi mata wata fisga takifa a bed din yay mata rumfa yasoma kokarin cire mata hijab din tarikeshi gam kuwa cikin shashhseka take cewa pls yaya narokeka kayimin rae kayi hakuri ka kyaleni banaso, cikin tsananin bacin rae idunshi yay jajir yace why dazan bari aiba haramun zan aikataba so kibarni na amshi hakkina tunda kin amshe kudin sadakinki yakarashe magana gamida fisge hijab din nata takarfi tasaki kara kuwa don jitae kamar ze tuge mata wuya koda yakae hannu kan rigarta tarikeshi jikinta yana karkarwa tace pls ka kyaleni haramunne abinda kake shirin aikatawa...Muhammad se a time din yadago yakalleta da rinannun idanunsa yace meyasa ze zama haramun mimi takasa cewa komae se kuka besanda sanda yadaga hannu ya sharara mata mariba yace cikin tsawa MEYASA ZE ZAMA HARAMUN? hannu biyu mimi ta dafe gefen fuskar tata cikin tsananin kuka tace saboda bani bace meenal, koda yaji haka yasaki rigan nata yasauka daga kan bed din yana furzarda iska mezafi daga bakinshi koda yajuyo yaga harta maida hijab dinta tasauko itama tanata kuka meban tausayi don taji azaba kam cikin bacin rae yace kin fiya taurin kan masifa tun a garden naso kiyimin wannan bayanin amma kika bari harta kaemu ga haka sannan kika fadi gaskiya kin batamin rae, kuma tambaya tafarko itace menene sunanki?
Cikin kuka mimi tace sunana safiyya amma ana kirana da mimi, DUM muhammad yaji kirjinshi yabuga safiyya yakuma nanata sunan yaname zuba mata idanu jin yadda yakuma nanata sunan ne yasata dagowa takalleshi fargaba takara dirar masa saboda koda tadago ayanzun fuskan auntie safiyyansa kawae yahango a tata fuskan cikin wani irin yanayi ya lumshe idanunsa nadan lokaci kana yasauke ajiyan guciya yanemi gu yazauna sannan yakalleta yace zoki zauna, sam mimi batae masa musuba tazo tazauna zuciyanta haryanzu tana mata dancing,
Murya a raunane yace mimi ina meenal take?kanta a sunkuye tace tana gidanmu baki bude muhammad yasoma kallonta cikin rashin fahimta yace banganeba, se a time din tagyara zamanta jiki a sanyaye tace insha allahu meenal tana gidanmu itama tana rayuwa amatsayina kamar yadda nakeyi anan allah ne kadae yasan nufinshi daya kaddara hakan takasance al amarinmu akwae ban mamaki seyau nakara tabbatar da hakan nakara ganin hotonta, muhammad yace mekikenufi kenan kikace insha allah baki tabbacin tana gidan naku kenan why dazaki yaudari iyayenmu haka tunda nafara dora idanuna akanki nasan bakye bace meenal dita wannan abun yadauremin kae meyasa hakan zata kasance taya kamanninki yazamo irin nata? mimi duka abinda yafaru da ita tasanar masa da irin mafarkin datakeyi da meenal da soyayyarsu da mujaheed, mamaki yahashi magana illah kallon ta dayakeyi, girgiza kae yay yace koda akasanar daddy bashi yahaifi meenalba sam baki shiga tashin hankali akan hakan bah wannan dalilinne yasa shima daddy fara tantama akanki, sesae daga rana irinta yau komae yazo karshe gayamin awanin garin kike inda meenal take rayuwa yanzu, mimi tace gombe! gombe ina? yola, tabashi amsa, yajin jina kae yace shin kece wadda mujaheed yafara furtawa so ku kuma sunfara soyayyane da meenal kafinke?mimi ta girgiza masa kae tace nice yafara furtawa so kuma na amshi soyayyar sane saboda nagani meenal tanada masoyinta shiyasa na amince masa tunda ina matukar kaunarsa nima, cikin daga hankali muhammad yace kina nufin meenal tanada masoyi yanzu haka?
Mimi takalleshi a takaece tace eh nagane hakanne saboda irin kalaman bakinsa da sunan datayi masa saving, cikin mamaki muhammad yace to wanene wannan nikuwa dabansaniba, broda din nadiyane aminiyarta shine suke soyayya, muhammad ya rintsu idanunshi yace kada nakuma jin kinfurta wannaa maganarma dole zuwa adamawa yataso mana,
Mimi cikin tashin hankali tayi bayi tana girgiza masa kae tace pls kada kumaidani gida yanzu batareda na auri ya mujaheed bah katemaki rayuwata,muhammad yace why?setayi shiru tana tunanin aurenta da bassam bashakka yanzu wannan auren yakusa, seda tahadiye yawo tace saboda mu bama auren bare sedae a family, da mamaki muhammad yace saboda me wani irin tsari gareku haka ko ince danku komadae meye kada kidamu ni nace namiki alkawari insha allah zaki auri mujaheed cikin tashin gamsuwa tace nidae katemakeni kada kamaidani gida batare da na aureshi zuwa yanzu seda yagama nazartatta tukun yace haryanzu da akwae abinda kike boyemin so kada kidamu sansan komae idan munje gidan naku kitashi kije kiyi bacci kikuma sawa ranki cikin kwanakinnan zaki koma gida, mimi tasaki kuka tadago zata kuma yimasa magana yadaga mata hannu, cikin daure fuska yace bazan kuma jin tabakinki bafa so jeki kwanta idanma karya kikayi duka zansan komae mimi cikin cikin bacin rae tafita daga dakin tana kuka,lumshe idanunsa yayi yana ganin wannan abun kamar a dramatic allah sarki auntie safiyya ga wani muhimmin abu yana shirin faruwa dake amma bakya nan allah yajikanki da rahama koda yabude idanunsa tafda kwallah yace kema mahaifiyata allah ya kyautata makwancinki yau gashi danki yayi aure barabon kiga jikokinki...
Koda mimi tashiga bedroom dinsu sam batabi takan kurarda tadebo nana bah tana gefe tanata charting fadawa kan bed tayi cikin kuka mimi tafara magana da fillanci gamida hausa harda turanci tana cewa meyasa zakayimin haka sam bakasan halin mahaifina bane dole nakoma seyamin aurennan nikuma banason ya bassam dinnan ya mujaheed nakeso kumashi zan aura ni kuka take me tsuma guciya, zuwa lokacin nana tagama firgicewa jin mimi na yarenda bata san ta iyashiba bakaramin tsorata tayiba tamike tayi wane da mugun gudu saboda ba makawa tasawa zuciyanta meenal aljanune suka shigetaππ ....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: π€ππ€π
RABON KWADO....
BOOK 3
πππππ
NA NANA BMB.
π€β€οΈπ€β€οΈ
page 10-11
Sebayan 'yan mintuna dasuka shude tukunnah ummi tasauko fuskarta daukeda fara ah tunkan tazauna meenal ta cinmata tana cewa ummi meya faru ne don allah kigayamin,ummi tayi murmushi takalli bassam tace kaje kasanarwa da family you munada manyan baki a gidannan,shima haka yatashi cikeda mamaki yafice, meenal takara rike mata hannu tace suwaye zasuzo ummi?kigayamin,itadae kallonta kawae take tana zuba murmushi tace bakine zasuzo mana kuje ma kubada oder irin girkin daza a fara yanzun kibar komae se idan sunzo zaki ga komae, itadae meenal addu ah kawae take allah yasa tunaninta yazamo gaskiya,tashi tayi don cika umarnin na ummi,
Tafiya tayi tafiya su muhammad bakaramin gudu suka shararaba kafin su iso cikin garin yola,mimi itace take musu jagoran tafiya ayanzu har suka iso GIDAN FULANI,anan tunanin kowa yasoma zama abin mamaki da aljabi mimi dakanta tafito tayiwa securities magana sannan aka bude musu gate suka wuce, zuwa gate na biyu anan aka bincikesu tas sannan sannan suka wuce bakin kowa asake da mamaki suketabin gidan da kallo, har parking space takaesu suka aje motan nasu sedae kowa yakasa fitowa acikin motar se mimi kadae data fito cike da farin ciki dajin dadi ko ina takebi da ido kobakomae tayi missing gidansu matuka gaya, muhammad ne yafara fitowa yazo gurin mimi zeyi mata magana ashe mujaheed yafito shima cikin jin haushi yace waekae meyake faruwane wannan wani irin gidane ko ince gari donyafi karfin gida wannan mezamuyi anan? muhammad yay murmushi batareda ya tanka masaba haka mimi adae dae time din bassam yafito daga bangarensu nasu mimi yanata balbalin bala ei da alamu shida hasana ne, cikin tsatstsan farin ciki mimi takwala masa kira,YA BASSAM! koda bassam yaji wannan kiran seya tsaya cak kamar baze waigowaba sekuma yajuyo ahankali yadora idanunsa akansu yakasa tantance wadda yake gani saboda 'yar tazararsu hakanne yasashi tunkaraso itama mimi tanufeshi harda gudunta, tana karasawa tarike masa hannu da yakuwa rintse idanunsa yaname cewa Oh! allah my meems gizo kuma kika farayimin yanzu,cikin dariya mimi tace bagizo nake makaba nice mimice take maka magana kabude idanunka ka ganni dakyau,cikin firgici bassam kuwa yaware idanunsa akanta don bashakka wannan muryar ta kalbinshi ce ba tantama dafe zuciyansa yayi kawae yaja baya yaname kallonta cikeda da rashin fahimta ko zurfafa tunaninsa yakasa, tsoro sosae yashigesa tace ya bassam shin kundrna tarbar bakone yanzu agidannan cikin in ina bassam yace bari nakirasu jiki nabari yajuya yana waigen mimi don atunaninshi wannan anya ba aljana bace mekama da mimi saboda yanzu yagadae yabarsu agida yafito,
Ganin hakanne yasasu daddy fitowa daga cikin mota dasu auntie al ummar data soma fitowa daga cikin gidanne yakara daure musu kae tako ina mutanene suke bullowa,
Mimi asanda tayi arba da ummi ya ilahil alamin! cikin wani irin gudu mimi tanufeta taje ta daneta btasan tafara kukan farin ciki bama, I MISS U I MISS U I MISS U I MISS U!ummi ashe darabon nakara sakaki a idanuna ummi nayi kewanki sosae ummi,cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa ummi tayiwa mimi kyakkyawar runguma tana zubar da hawayen jin dadi tana zuba addu ah ga ubangini daya dawo mata da diyarta lpy,kowa TV yamaidasu agurin nan, adae dae lokacin hasana tafito da meenal bassam yariko hannun twins,zuwa lokacin mamakin bassam yagama karewa kallon meenal kawae yake,asanda mimi tadago kuwa suka hada ido da meenal jiki nabari tasaki ummi taikanta tarukumkumeta tana ya allah meenal ashe darabon zamu gana, wannan abun kamar a mafarki ya allah kaene kadae kasan nufinka dakayi haka, meenal kallonta take tanata yashe baki yaki rufuwa addu arta ta amsu shikenan tarabu da gallababben auren nan na mimi zata koma gida duka azuciyanta take wannan tunanin,cikin farin ciki tace Oh allah abin godiya shin kina ina kekuwa duk wannan lokacin?mimi tasaki murmushi tarike mata hannu suka nufi inda su muhammad suke tsaye sudukansu,wayyo ay meenal wata fincika tayiwa hanunta saura kadan tayarda mimi akasa cikin gudunta nabara tafellah, tana kwalawa yayan nata kira YA MUHAMMAD! muryanta kuwa gaba daya seda taratsa ilahirin jikin sa ya lumshe idanunsa yaushe rabon duniya da ayyare dayaji muryar sweetiansa, cikin tsananin farin ciki muhammad yasoma zubawa allah godiya seda takusa karasowa kuwa ya isa gareta cak yacafe abarsa sama yana juyata cikin nishadin dabesan yanayibama,(da alamu yamanta dasu daddy) meenal tana dariya ahankali yasauketa takarasa fadowa jikinshi yay mata kyakkyawan rumguma kuwa sosae taji yadda yake sauke ajiyan zuciya, idanun jama ah kamar ze fado kansu don sun burge kowa dake gurin,sunkuyawa yayi yasoma yimata rada akunne yana cewa sweetie haka kika koma masha allah!cikin jin kunya tace ya muhammd haka ka koma kaema gaba daya kasauyamin,yasaki 'yar karamar dariya yace bawani zaki wayance kinji nace kingirma koh kema irin ta yaya ta yaya kin girma kin fara....Toshe masa baki meenal tayi tana rintse idonta don kunya tana cewa pls kar ka fada wlh bangima bama ni,muhamma yashagala da kallonta ma baduka abinda tafada ba yaji yana mamakin ganin meenal dinshi yadda takoma,daddy ne yakaraso yace oh muhammad bazaka sakar min 'ya mugaisabane? cikin mamaki meenal tadago tana tana cewa lah daddy harda kae akazo tarike masa hannu atime din taga mujaheed yana tsaye kamar gunki,tasaki kara tai kansa tana cewa ya mujaheed harda kae dama ay ban gankabah, alokacin kuma nana takaraso don tagaji dashan mamakin haka cikin rudu tariko ta tana cewa meenal! habawa wani tsalle tayi ta dafe nana saura kadan su fadi tana cewa yaya haka kika dawo ya allah kowa ya sauyamin asannan tahango su mummy dasu inna tace oh allah farin ciki kasheni don murna daya bayan daya meenal taje tana rumgumesu saboda tsananin farin cikin datake ciki bata kula da yanayin da auntie tashigaba sakamakon mugun gamo datayi,haka muhammad suman tsaye yayi ganin wadda take tunkarosa, ummi ce fuskarta dauke da fara ah tamaraso gurin muhammad, tace ikon allah kenan kaene wanda meenal kullum take ambato a cikin baccinta,tabbas bakawa yanzu yatabbatar da wannan auntie safiyya ce cikin firgici yace auntie safiyya!dama kina raye? itama cikin kidama tarike masa hannu tace muhammmad menaji ka ambata yanzu? lips dinsa yana kar karwa idonsa tafda kwalla yace auntie safiyya dama kina raye? Ya allah jikin ummi yana bari tace wlh ba ita bace muhammad ba safiyya bace 'yar uwartace ni sosae tarikesa tasaki kuka tace na rokeka tana ina ina take safiyya 'yar uwatace,tunranda nafara ganin meenal nasan ba mimi bace nayishiru dabakinane saboda wannan tunanin danakeyi kuma gashi yazamo gaskiya tabbas bakawa itace tahaifi meenal tana ina dukda kullum ina kuka idan natuna da 'yata mimi bansan tana cikin wani haliba bansan waca irin rayuwa takeba haka na hakura sabod jikina yana bani nakusa ganin 'yar uwata safiyya!tana ina kagayamin tana maganar tana girgizashi shikuwa muhammd kamar dolo haka yasau baki yana kallonta,
A time din motocin abbansu yasawo kae cikin gidan kae tsaye yafito don yasan ba lafiyaba,ganin muhamma d bashida niyyar tanka mata yasata sakinsa tanufi gurin meenal, to me karatu lamarin Dr se addu ah gaba daya tanemi kuka tarasa tadafe zuciyanta cikin girgiza kae tace impossibls baze yiwuba cikin kidima takara maimata BAZE YIWUBA! taya hakan zata kasance sosae jikinta yake kar karwa tana fiddo maganaeππ su mummy dukse suka zuba mata idanu ganin tana shirin ficewa a hayyacinta,
Cikin kuka ummi tarike meenal tace meenal narokeki kigayamin ina mahaifiyarki take? cikin jin tausayi meenal tace ummi lpy kike kuka?girgiza mata kae tayi tace meenal ina mahaifiyaki take? hannunta meenal takama suka nufi inda auntie take tsaye....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: π€ππ€π
RABON KWADO....
BOOK 3
πππππ
NA NANA BMB.
π€β€οΈπ€β€οΈ
page 12- 13
Suna tun kararta tana jadabaya cikin firgici numfashinta yan shirin daukewa saboda tsoro tana girgiza kae tana cewa baze yiwuba impossible meyake shirin faruwane? dakkyar take iya fusgo numfashinta motan data cikaro da itane ta baya yasata tsayawa taname dafe zuciyanta,
Cikin tsananin mamaki meenal tariketa tana cewa auntie lpy meyake faruwa dake haka?Ummi batabi takan yanayin da auntie tashigaba saboda itama a kidime take hannunta zata rike aikuwa tafasa wata irin kara taja gefe, cikin zubar hawaye ummi tace mekikeyi haka ina mahaifiyarta take kugayamin don Allah,jiki asan yaye meenal tace Ummi, itace mahaifiyata fah! mekike tunani akanta meyake faruwa? naga auntie kamar bata cikin hayyacinta,
Da mamaki Ummi take kallon meenal,tace itace mahaifiyarki fah kikace!meenal tadaga mata kai cike da mamaki,sam Ummi batasan sanda ta cakumi auntie bah cikin kuru kuru da idanu tace, bazan yardaba karyane,wlh bagaskiya bane sekin fadamin inda 'yar uwata take bake kika haifetaba karya kikeyi sekun gayamin gaskiya yau, saboda meenal jini nace ita zancenku karyane cikin hargowa take magana da fitar hayyaci tuni auntie tadade da sumewa, tayi yaraf kan mota din amma dukda haka Ummi jijjigata take tana cewa karya kikeyi kitashi sekin gayamin gaskiya zan kyaleki,
Kuka meenal tafashe dashi jin wani batu daya daure mata kae, alokacin abbansu yakaraso, inda Ummi taketa faman yagulan auntie yasoma kokarin janyeta daga jikinta, sedae bakaramin riko tayiwa Dr bah πππ, cincin karfinsa yasa ya bambare hannunta ajikin auntie yana gama janyeta kuwa tafi jikinshi ba alamun numfashi atare da ita,
Gaba daya mutanen gurin nan mamaki da al ajabi ne suka hanasu koda motsi bare suyi yunkurin temakon auntie, seda abbansu yayi magana tukunna kowa yayi tamaza kuma, akazo aka tattaro auntie akayi cikin gida,
TOme karatu gidan fulani ya yamutse.
Cikin dan kankanin lokaci aka hada babban meeting kowa ya hallara, mujaheed kuwa dole yabaka tausayi idan kakalli fuskansa saboda halinda yashiga, meenal da mimi su akasaka agaba kowa yana furta albarkacin bakinshi akansu, Ummi tana jikin hajiya mahaifiyarsu inbanda kuka babu abinda takeyi kankameta,
Auntie kuwa koda Dr dinsu yadubata yace babu wani matsala tsananin firgitane datayi,amma zata iya farkawa akowani lokaci,
Cikin wani wani irin yanayi mimi ta tashi tazaiyano duka abinda yafaru, kowa se salati da sallallami ana zubawa meenal odanu, ita kuwa tayi sukui da ita azaune se aikin raba idanu,
Seda ta kammala tukunna, aka nemi jin tabakin mahaifin na meenal wato daddy,
Yakuwa mike yasoma zaiyanomusu abinda yasha kansu da mamaki zuwa haduwarshi da safiyya irin abinda take fiskanta gurin imam dasakin daya mata dakuma zaman datayi agidanshi harzuwa lokacinda allah yay mata rasuwa sedae bata taba fada masa inda danginta sukeba tace ita marainiyace wannan dalilinne yasa yarike meenal amatsayin 'yar cikinsa saboda kada tafuskanci halin rayuwa,
Sosae muhammad yakejin tsananin tausayin meenal azuciyansa saboda dole yasan zata shiga cikin mawuyacin hali dawannan bakon al amarin datakeji,
Sosae ta kankame mimi tana kuka metsuma zuciyan mumini tamkar numfashinta ze dauke tunowa da irin abubiwan da auntie keyi mata, nana ma hawaye kawae take sharewa saboda tausayinda meenal tabata,
Haka ummi tamkar zatayi bori tana cewa wlh safiyya bata rasuba bazan yardaba wlh data rasu datuni bana duniyar nan nima su sukasan inda suka kaita bazan yardaba ace tamutu,
Cikin wani irin yanayi yaya babba tamike tasoma ibar albarka,
Haba koda naji ashe wannan yarinyar ba jikatace bace bajinina vace dole tayimin ibar albarkar datayi awashegarin data dawo gidannan ashe 'yar gidan sallamammiyace dole zatayi abinda yafi haka, badole safiyya taga karshenta arayuwaba ay wlh dama bazata taba samun farin cikiba,
Jin hakanne yasa hajiya takama Ummi sukabar gurin su daddy kallon mamaki kawae suke wa yaya babba jin furucinda takeyi akan safiyya, seda gwaggo ta tasoma tasoma sauke mata ruwan bala ei tayi shiru,
To kowa da abinda yake furtawa agurin nan shikuwa mujaheed ko kalma daya takasa fitowa daga bakinsa saboda irin zafin dayakejin zuciyansa tanayi masa su meenal kawae yake kallo, abbansu meeanal cikin farin ciki ya rumgume daddy yana godiya ga ubangiji,
Seda aka kira sallan magrib taro yawatse domin yin sallah....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: π€ππ€π
RABON KWADO....
BOOK 3
πππππ
NA NANA BMB.
π€β€οΈπ€β€οΈ
page 9
GIDAN FULANI
Menalce kwance adakinta tana kan gado hawayene kawae yake bimata fuska dukta rame saboda ta tashi hankalinta sedae jikinta yayi suwae har kyalli yake da gashinta sunsha gyara fuskarnan tayi suwait tayi kyau sosae tana cikin wannan halinne aka buga mata kofa tanadaga kwancen tace "enter" hasana ta turo kofan tashigo tazauna gefenta taname cewa yayarmu banason kullum ina ganinki cikin wannan halin kinji yau saura 'yan kwanaki yakamata ki fawwalawa allah komae meenal bata tankataba don ita seyanzun take bakin cikin yin shiru datayi tunfarko datayi bayani komae dahaka bata faruba hankalinta gaba daya yana gidansu, tana daga kwancen tace hasana inason muyi magana nidaku baki daya harda abbanmu idan yadawo kije kihayawa ummi,hasana cikin fargaba tace wani magana yaya badae cewa zakiyi kinfasa aurenba cikin fushi meenal tace ina ruwanki da abinda zan fada kije kigaya mata, jiki a sabule hasana tace to ay itace ta turoni nakiraki masu kunshi suna jiranki tundazu tace kifito yanzu, kafin takarasa magana meenal tamike tanufi hanyar fita hasana tace pls yayarmu kigyara fuskarki kada kifito ahaka kinji, fita tayi tabata guri ita kuwa dama ta kudurce aranta komene zefaru sedae yafaru don tabbassa kafin a daura aurennan setabar gidannan,
Koda hasana zasanarwa ummi sakon meenal setayi murmmushi tace aydama nayi shirune inji ta ina gaskiya zatayi halinta dole nasan taga za ayi auren nan tafadi gaskiyar al amari irin wannna kudira ta ubangiji, cike da mamaki hasana tace bangane ummi kinsan abinda zata fadane meke faruwane wae, ummi takalleta tace anjima kibari zakiji komae ay dakanta zatayiwa kowa bayani,
Kunshi tsan tsararre ake yiwa meenal nagani nafada sedae sam hankalinta baya kansu, wayan ummi ce tashiga ruri wayar na hannun hasana tana daga kwance tace ummi ana kiranki da bakuwan number, waca number ce? hasana takaranto number din meenal koda taji number dinda hasana ta karanto zuciyanta tai wani irin harbawa jin an ambaci number irin tata hankalinta inyay dubu yatashi ummi harta share sekuma tace kawomin wayar koda ta amsa kiran ya tsinke se ta aje wayan abinta, allah allah meenal take acire mata kunshin ta dauki wayar umman nasu gashi sun tsaya mata fi ili turaruka kala kala akewa kunshin tana jikuwa kamar tashakesu π
bayan tafitone awanka tazauna gaban mirror tana kallon kanta ita har mamakin kanta take yadda takoma ayanzun ga girmann data kara seda karewa kanta kallo tashirya sboda sauri ko dankwali bata dauraba tarikoshi ahannu tafito, sam bata kulada bassam ba a parlour sejitae yace Wooow my meems narasa wani irin kyaune wannan kike karawa haka tubar kallah batareda tajuyoba tasoma tura baki tabude dankwalin nata tarufe kanta, kallonta kawae yake da mamaki shi yarasa meyasa meenal takeyi masa haka yanzu insuna cikin jama ah tayita zuba masa surutu amma idan sukadae suka kasance ko maganar 'yan mintuna bata bari suyi tunda tadawo,murmushi yayi azuciyansa yana cewa komadae meye kinkusa zama tawa komae yazo karshe ay,
{KOMAE YAZO KARSHE KUWA TUNDA GAME ITANAN ZUWA!}
tana shirin wucewa ne tajiyo rurin wayan ummin taso ashema ta nan parlour din dasauri kuwa tajuyo zuwa inda take alokacin kuma ummi tasauko itama, tace wake kirana? koda meenal taji haka jikinta a sabule tadauko wayan takawo mata ganin nunbern din nan dae tadazu yasata daga wayan tana me neman guri tazauna, tome karatu koda ummi taji me magana tacikin wayan tamike tsaye cikin bakon yanayi da al ajabi tace MIMI! juyowa ummi tayi takalli meenal dakyau kawae tahaye sama, jiki nabari meenal tamike zata biza bassam yace no mimi kada kiyi haka, damamaki takallesa jin yakirata da mimi abinda bata tabajin yayiba sedae yace meems, dole takoma tazauna jiki bakwari....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: π€ππ€π
RABON KWADO....
BOOK 3
πππππ
NA NANA BMB.
π€β€οΈπ€β€οΈ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.