Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 7 of 22
page 27 - 28
WASHE GARI
Daddy ne da Daddyn mujaheed da Abbansu mimi da manyan su, se general an hadu ana tattauna wa akan shagul gulan bikin daza ayi bisa tsari,gidan fulani sune zasu fara nasu shagul gulan sannan a rankaya ai kano, acanne za ayi taro na karshe amika amare dakinsu na aure.
Yau general ze wuce kano da iyalansa, mom juyin duniya tayi tayi da yousep yaje gurin matarsa su gana amma fir yaki haka ta hakura ta kyaleshi, yaran zamani kam se ahankali,nadiya se matsar kwalla take don sam batason tafiyar tabarsu meenal haka tadaure zuciyanta badadi nana se yage musu baki takeyi harta bawa mom tausayi ganin ko inuwarta yousep yaki kallah tamkar besan da ita a gunba haka suka tafi.
Su Daddy kwana daya suka kara yau kuma zasu tafi,sunata shirye shirye, ummi takule a daki kuka kawai takeyi saboda Abbansu mimi yahana ta zuwa inda auntie take ko Daddy tace sam bazata yadda safiyya ta rasuba su sukasan inda suka kai mata 'yar uwarta sam ya hanata zuwa inda suke abin duniya yamata zafi,su meenal ma sunacan suna nasu koke koken ita dasu hasana saboda shakuwa,
auntie kuwa seyau daza ah tafi tafito daga dakin datake taname addu ar kada Allah yahada ta da ummi harta bar wan nan gidan jitake kamar zatabar cikin kaya,mimi taki yarda sam su hadu da mujaheed seyau dazasu tafi saboda kunyar data addabeta takasa kallonsa ko kadan, shikuwa murmushi yayi abinsa gamida tabe baki yashige mota,
Meenal se rawar jiki takeyi Allah Allah take takoma gida taga waye wanda aka aura mata sannan tayiwa mardiyya albishir cewar ya nuhammad ze aureta,
muhammad ya kula da rawar jikinda takeyi amma seya kyaleta badai gidan zasu koma bah,kobi takan auntie meenal batayi wanda hakanne yakara sawa jikin auntie yin sanyi,
Tafiya tayi tafiya wanda basu suka kai gidaba se bayan ishah saboda suna tsayawa yin sallah dacin abinci koda suka kai gidan bawanda yatsaya wani hira kowa yanemi makwanci abinsa.
WASHE GARI
Meenal tariga kowa tashi a gidan saboda dokin gidan datakeyi gaba daya taga gidan yacanza mata shirunda taji ne yasata tabbatar wa da bawanda yatashi a gidan seda tagama zagayenta ta wuce garden tazauna harda harde kafafuwa,sosai tashiga tunanin rayuwar ta ashe ita abar tausayice bata saniba mahaifiyarta bata raye ga mahaifinta sam ba mutumin kirki bane wani irin tsanar shice take mata yawo a jiki hawaye masu zafi suka soma bimata fuska gashi anyi mata aure batare da tasan kowaye mijin nata bama, sosai take ganin an tauye mata hakkinta,idanunta a lumshe taji ana share mata hawaye,kamshin turarensa datajine yasata sanin kowoye,zama yayi gefenta cikin damuwa yariko mata hannu yace.
" Sweetie banason wan nan kukan naki kada kifara sawa kanki damuwa kowani tunani koda yaushe kikasance me kai kukanta ga Allah so kidena kuka banaso kinji koh"
" Ya muhammad kana ganin wanda daddy ya auramin yana sona "
Kallonta yake da mamaki don beyi tsammanin tambayar tataba yanzu,murmushi yayi gamida sauke ajiyan zuciya yace.
" Yana sonki mana so me wuyar fassarawa,sonda yakeyi mikine ma yasa ya mallaka miki zuciyansa gaba daya ke kadaice a cikinta,tun kina zanin goyo kaunarki tazama jinin jikinsa so kinga wan nan shine masoyinki na gaskiya ba yousep bah,kuma iname tabbatar miki soyayyar sa zata mantar dake wani yousep fargabar dayakeyi a yanzu shine idan yazo gareki zaki kaunaceshi ko kuwa bazakiyiba"
Kallonsa meenal kawai takeyi da mamaki dauke a fuskanta.
" Sweetie kiyi min al kawari aduk sanda kika kasance tare da mijinki zaki gaya masa gaskiyar abinda ke zuciyanki kada kice zakiji kunyar sanar masa,idan kinajin sonsa ki gaya masa haka idan baka sonsa ki gaya masa"
Hannunsa takara rikewa tace." pls ya muhammad ka gayamin wanene shi daya dade yana sona haka"
murmushi yayi yace." ay bakiyimin al kawarin bah tukunnah"
" To nayi maka al kawari, haba! ya muhammad sekace baka sanni bah inbana sonsa kobe tambayaba sena gaya masa but innaji ina ra ayinsa zan nuna masa,amma kagaya min wanene shi?"
muhammad yay murmushi yace." shedar auren tana nan zanbaki da sadakinki sekiga kowaye a ciki"
" Shedar aure kuma! ya muhammad tun yaushe akayi auren ne?"
Yamike yakama hannunta suka koma ciki seda suka shiga parlour yasaki hannunta yace, "kije kiyi wanka bayan breakfast kizo inbaki"
Ya haye sama abinsa yabarta nan tsaye da sakak ken baki,
Tunkan yashiga bedroom din yake jiyo masifar mujaheed seda yashiga yaga ashe waya yakeyi,yashiga masa murmushin mugunta seda yagama wayar yajuyo yana antaya masa harara,hakanne yasa muhammad fashewa da dariyar mugunta, be ankara bah kuwa yaji mujaheed ya cimimiyo masa riga yana cewa.
" Bakin mara mutumci komai kaine kahada shi ay banjiba banganiba kowa yakwaso masifar sa seya kirani kuma kazo kana min dariyar mugunta"
Cikin dariya muhammad ya kwaci rigarsa yana cewa "meyay zafi Allah yabaka hakuri kowaye zemaka mita kabashi hakuri abinda yanzu zamu fara indai shagul gulan bikine, mutum harseya gaji dazuwa"
Yana shafar cikinsa yana cewa
"be cool angon mimi maida wukar"
duka mujaheed yakai masa yay saurin shigewa bathroom yana dariya....
TAKU A KULLUM NANA BMB
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣️RABON KWADO....!!
BOOK 3
NA NANA BMB
GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da al kalami domin fadakar da al'ummah }
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.