Complete Hausa Novels

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 22

page 19 - 20

Cikin zubar hawaye bassam yace.
"wlh mamy kin cuceni bazan iya yafe miki cutar dakikayi minba se allah yasakamin da wannan torancin da kikajamin"
Cikin kuka itama asiya tasoma cewa.
"kayi hakuri bassam nima bayin kaina bane mahaifiyatace nima tasakani itace ta cucemu"
Alokacin kuma mahaifin bassam yataso yasoma dannawa asiya Allah ya isa, dagashi se Alhj.Sulaiman shima yataso yasoma tsinewa halin balaraba,
" wlh balaraba kinyi asarar hali aduniya mara mutumci mugun iri gara da Allah yatoni asirinki yanzu me bakar zuciya" yana maganar yanajin kamar yashaketa a gurin ta mutu, cikin kuka gwaggo ta mike ta iso garesu tana takarkarawa dakyar tasoma magana cikin yarensu na fillo cewa.

Sulaimanu kaine kaja mana duk wannan abun yafaru kaje ka auro mana mugun iri cikin zuri'armu gashi yanzu bakin halinta yanata bimin jikoki Allah ya isanmu balaraba kuma yau Allah yakawo karshenki a gidan nan, kado! kado! kaji tsoron halinsu bakowa yasan hallaciba"

Tana magana tana sharar kwalla,to Abbansu mimi dai mamaki ya hanashi magana da jimami kallon bassam kawai yake mutumin daya dau yardar duniya yabashi ashe shine maka shinsa besaniba,ummi in banda hamdala babu abinda takeyi da Allah yasa bassam berigada ya aurar mata 'ya ba asirinsa ya tonu,
Sosai kukan mimi ya tsananta saboda komai daya shiga dawo mata cikin kai, a ranar dazasu fita hana hasana yayi tafisu koda sukaje gurin siyan icecream hanata fitowa yayi daga mota yatafi shikadai kafin yadawo anyi gaba da ita ashe da abinda ya taka,haka sunata koke koke aka tarkatasu aka tafi dasu gida yakara hautsinewa koke koke yayi yawa

Tome karatu lamarin auntie se du'ah ei, haryanzu tanacan kwance kamar matatta nana ce a tare da ita tana kula da ita sosai take tausayin mahaifiyar tata don tabbas kuwa takawo kanta gidan dafa kanta.

Kwana biyu da fara shari ar su bassam sega ganeral shida 'ya'yan sa yousep da nadiya,se matarsa a gidan fulani abin kamar a al mara, domin tafe suke da Abbansu mimi,yadda yousep ya rame inka ganshi seya baka tausayi saboda duk abinda yake faruwa nana tasanarwa nadiya hatta da zuwansu nan, ita kuwa nadiya farin ciki ya isheta zasu hadu da meenal aminiyar ta mom dinsu kuwa 'yar kauye ta koma tasau baki tanata bin gidan da ido tun farkon zaman aurenta da ganeral a nan yola takejin labarin gidan fulani harzuwa sanda suka koma kano dazama bata tama sanin yadda yakeba seyau, direct part dinsa yawuce dasu nan danan aka cikasu da kayen ciye ciye, babu kowa a gidan se ummi kadai wanda zuwan nasu dama ya hanata binsu hasana suje gurin su meenal,seda sukaci suka koshi sannan Abbansu mimi da ganeral suka fara yiwa ummi bayanin abinda yake tafe dasu,
Batune a kan bassam sam bashida laifi yaudarar shi mahaifiyarsa tayi sam besan cutarda mimi za ayiba sedaga baya,wan nan dalilin ne yasa yakira ganeral yasanar masa da duk abinda yake faruwa dakuma gurinda suka boye mimi,badon shiba kam da tabbas mimi bazata dawo da raiba ko ince meenal,
Allah sarki ummi tausayin bassam ne yakamata matuka saboda tasan beyi dacen uwaba ne yasa irin haka yake faruwa dashi,
auntie bata juma da farkawaba nana takira su daddy tana shaida musu auntie tafarka kamar zautatta saboda ta tubure setabar wanan gida sam bazata iya zamansa ba,a parlour su daddy sukaci karo da ita tana shirin yowa waje su mummy nariketa don masifa irin nata tana tafe tana tangadi amma taki saduda, muhammad yadda yaga auntie tagama firgicewa da rudewa yasa dariya takamashi daurewa kawae yakeyi duk yasan saboda ummi take wannan haukan da borin kunya,
Hannun ta daddy kawai yarike suka koma cikin bedroom, sosai yake daurewa don shima dariyar yake sonyi daurewa yayi yabata fuska yasoma cewa
"Haba maryam menene haka kikeyi ne? kinson tonawa kanki asiri dakanki,yanzu idan sukaga kina wannan borin kunyar naki ba tuhumarki za ah cigaba dayiba gaba daya kinfice a hayyacinki kamar bakida hankali sam ba safiyya bace kika gani yakamata kinutsu haka, 'yar uwartace ba ita bace bah, nan ne asalin safiyya yakamata kisan mekikeyi fah! kikama kanki,yawwa kinga yanzu ina amfanin mugun hali idan da abun azziki kikayiwa safiyya bazaki shiga wannan halinba a yanzu,kullum ina nusar dake ina fahimtar dake kikayi watsi da maganata, yanzu ga sakamako kinso magani kinga asalin safiyya koh, tafiki asali idan kudin kike takama kingani dai tafiki azziki tafiki matsayi babu abinda zaki nuna mata, sedai dake zuciyanki tayi nisa idanunki sun rufe, kisani kusan saboda ke na aurawa muhammad meenal,saboda zarginda kikeyi na meenal 'ya tace, zuwa yanzu kuma nasan duk wani zargi dake zuciyanki yafita koh sekuma kiyi shirin girbar abinda kika shuka"
Duk maganar dayakeyi auntie kuka takeyi meban tausayi tana jimama wannan lamarin kaico duniya kaico! ganin abin take kamar a tatsuniya wai yau itace a cikin family din safiyya haka,
To fitowan daddy kenan sega su yousep sunshigo shida nadiya suna gaba,se mom dinsu da ummi abaya, Ya Allah! meenal koda tayi arba da abin kaunarta mancewa tayi da komai tamike cikin tsananin farin ciki tanufesu, zuciyan muhammad tamkar zata fado saboda harbawan data somayi,

"Ya yousep!" tazo zata rumgumeshi saboda murna da farin ciki, cikin mamaki matuka yayi baya yana kallonta, harda rike baki yace.
"Ke meye haka zakiyi kinmanta kinada aure ko yaya"

"Nashiga uku!"

Meenal tafada tana dafe girjinta da hannu biyu saboda tsananin firgicin data shiga,tace.

"Wani makaryacinne yagaya maka? wlh kowaye karya yakeyi"
Nadiya batasan sanda dariya ta kwace mataba tarike mata hannu tace.
Yanzu meenal kina nufin baki saniba? ko kuwa a tunaninki bazamu jiba,duk wan nan gyaran dakika sha kinata kyalli ga kunshi kinsha amma yatashi a banza"tuni kwalla tacikawa meenal ido jiki a sanyaye tace. "wlh bestie ba bikina za ayiba na sister nane kune baku saniba"
Yousep kallon inda su muhammad suke zaune yayi yana son sanin cikin shida mujaheed waye mijin na meenal, to drama din datake faruwane yasa mujaheed darawa sosai yakewa muhammad dariya jin furucinda meenal takeyi,dukda yana cikin damuwa hakan behanashi darawaba,mimi kuwa ganin hakanne yasata sakin ajiyan zuciya tana hamdala ganin sahibin nata yasoma saukowa, rabonta daganin fara arshi tun a kano lokacinda sukayi selfie, cukurkude fuska da muhammad yayine yasa yousep tunanin shine mijin nata,
Kallon nadiya yayi yace. "Sister shige muje tunda bata saniba to ko baza aji mutuwar sarki a bakina bah"
Cikin rashin fahimta meenal taje gurin daddy tazauna gefensa cikin wani irin yanayi tace.

"Daddy kaji abinda suke cewa kagaya musu gaskiya nibanida aure"
Murmushi kawai yayi yashafi kanta yace.
"Yata takaina kinada aure mana,nayi miki aure tuntuni, amma inason kibar maganar semun koma gida"
cikeda tsoro meenal take kallonsa dakuma jin kamar yana mata ta tsuniya, kura mata idanu kawai muhammad yayi yanason ganin yanayin dazata shiga, cikin muryar kuka meenal tace Daddy waka auramin?
Kallon takaitaccen lokaci yamata sannan yace. "Itama wannan maganar kibarta semun koma gida"
Kai kawai meenal ta iya jinjina masa tamike dakyar tabar parlour din batare da takuma kallon su nadiya bah,nana kuwa kana kallonta zakaga zallar farin cikin datake ciki tagode Allah yanzu tasamu 'yan cinda zata mallaki yousep,
Kuka meenal take meban tausayi ta kulle kanta adaki saboda zafinda zuciyarta keyi mata meyasa Daddy zeyi mata haka bayan ga wanda takeso ita,
Har dare bata fitoba saboda ankule su meenal bakuma wanda yaje inda take bare ya rarrashe ta har muhammad kuwa, duka an hadu a parlour anata hira cikin farin ciki dajin dadi banda ita banda auntie,
Se bayan ishah Abban su mimi da ganeral suka dawo gidan suna dakinsa nasaukar baki suna tattaunawa yakira yousep awaya yasanar masa yazo yasamesu,
Ana cikin hira yousep yamike yafita wanda kamar jira nana takeyi dama, takuwa mike tabishi itama ko kunya🤔,
Sarai yaga nana tabiyoshi wannan dalilinne yasa shi karawa tafiyan sa sauri, cikin tafiyarsa ta takama yay mata nisa hakanne yasata saka gudu, itama tacimmasa don harya kusa isa inda zashima, batareda shakkar komaiba nana tariko masa hannu, hakanne yasa yajuyo a fusace yana kallonta ganin bata da niyyar magana ne yasa yafisge hannunsa yace.
"Sakeni tunda bakida abin cewa ni inada abinyi"

Ya juya zecigaba da tafiyarsa nana takuma rikesa idanunta nata ambaliyan hawaye cikin maida numfashi tace.
"Narokeka katsaya ka fahimceni kada kayimin haka katema ki rayuwata kasoni koyaya,kaine kadai zuciyata take kauna a duniyar nan kada kayi min haka, Allah yayi nice rabonka ba meenal bah"

Tana maganar tana kara shigewa jikinshi kamar zatayi kuka, cikin takaici kuwa yousep ya fisgeta daga jikinshi haryana huci yanuna ta yace.
"Nana kada kiyaudari kankifa! don narasa meenal hakan bayana nufin nasoki bane kingane koh! saboda haka kikama kanki kisan mekikeyi nibazan taba sonkiba kada kikara tabani koda wasa nagaya miki"
Cikin shashekar kuka nana tace.
"Narokeka kada kajuyamin baya wlh bansan yadda rayuwata zata kasanceba kate makamin nizan maka abinda meenal btayi makaba ka yarda dani"
Tsaki kawae yousep yayi yajuya,caraf suka hada idanu da Dad dinshi, da Abban su mimi suna tsaye suna kallonsu,zuciyansa kuwa tasoma bugu yana addu an Allah yasa basuji abinda yafaruba....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣️RABON KWADO....!!

BOOK 3

NA NANA BMB

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al' ummah}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.