Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 22
page 14
Tsegumi kuwa kowa da abinda yake furtawa akan su mimi, masauki na musamman aka bawa su daddy abinci da abinsha kala kala sewanda suka zaba ga wata lafiyayyar fura da nono nata zuba kamshin ayaba da kwakwa cikin kwarya an aje musu tanata nason sanyi,seda kowa ya kimtsa tukunna aka azauna aka soma maida magana kuma,muhammad yana sane da halinda mujaheed yashiga amma seya shareshi betanka masaba abincinma kasa ciyayi dayawa fuskarnan tamau da ita,
Hakima Dr kuwa har kawo i wannan lokaci taki farkawa tana room dinda aka shimfideta ita kadae
meenal tana jikin mummy takoma abar tausayi haryanzu kuka take idanunta duk sun kumbure don bakaramin girgiza tayiba wae daddy ba mahaifinta bane ganin abin take kamar a drama sunyi rarrashin harsun gaji takiyin shiru, su daddyn kuwa abbansu mimi ne da alhj aliyu mahaifinsu ummi, se kakan bassam sune sukaje suka samesu daddy suka fahimtar dasu tun silsila abinda yafaru da safiyya,
Daddy kuwa ya girgiza dajin labarin safiyya,azuciyansa yake magana.lallae seyanzu ya yarda da wannan kalmar ta bahaushe dayake cewa "RABON KWADO... Baya hawa sama" donkoyaje zefado yasameshi, tabbas imam kayi asarar rayuwarka dakayiwa safiyyar irin wannan sakayyar lallae kayi kuskure kuwa wanda ahalin yanzu nasan kana kan gani, Allah me iko kenan meyanda yaso dabayinsa,
Koda yakara gwada musu hoton safiyya anan suka kara gasgata al amarin sede jikinsu duk yay sanyi saboda safiyya bata raye, muhammad mamakine yahanashi furta komae yana tunanin to a ina daddy yasami hoton auntie safiyya? sosae kanshi yakulle akan wannan al amari,
Ummi tana kwance kusada hajiya abin duniya ya isheta inbanda aikin kuka babu abinda takeyi dakyar suhajiya suka rarrasheta domin ta dage setaje tasamu auntie ay ita tasan inda
'yar uwarta take, su hasana da twins suna gurinsu mummy da mimi wadda zuciyanta take cike da fargaba ganin yanayin gogan nata datayi babu annuri,
Sewajan 9 da wani abu su muhammad suka shiga inda aka sauki su mummy yanata zalkin ganin amaryarsa,sam barka kuwa yahangeta jikin mummy anata rarrashi, soyake kawae ya rarrashi abarsa amma babu hali tana gun mummy,seda suka zauna tukunna mummy tace muhammad gara dakuka shigo yanzun munkasa shawo kan meenal, kazo kaji da ita don Allah, muhammad yay murmushi yataso yazauna gefenta yana cewa haba sweetie meyasa zakiyita wahalar dasu mummy ki fawwalawa allah komae kinji duk yadda kikaga bawa haka allah yatsara masa, toke seki godewa allah kinji bakuka zakiyiba kada kuma ki kuskura kisawa zuciyanki maraeniyace ke ko kadan karki fara,
Zuwa lokacin kukan meenal ya tsananta yanzu dagaskendae wanda taji ana ambata shine mahaifinta meyasa aka boye mata kam,koda muhammad yadagota rintse idanunta tayi gam tana shahshsekar kuka, itadae mummy tasamu tamike tashiga toilet don mararta acike take, hakanne yabawa muhammad damar janye meenal daga room din, mimi tayi tsamo da ita don inda take mujaheed be kallaba hasana baki sake kuwa take kallon ikon rabbi, takasa dena kallon meenal yanzu dama bada yayarsu suke rayuwaba wannan wani irin abin mamakine haka?
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....
BOOK 3
💕💕💕💕💕
NA NANA BMB.
🤍❤️🤍❤️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.