Complete Hausa Novels

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 6 of 22

page 17 - 18

Cikin zubar hawaye meenal takarasa ga mujaheed,tace.
"Shin ya mujaheed meyasa zakayiwa 'yar uwata haka?menene laifinta anan ko kana jah da kudira ta ubangiji ne?mimi fah alheri ce a garemu, itace sanadin dana gano ko wacece ni, saboda tana kaunarka shine zakayi mata haka,kasani gatace a gareka domin idan da nika furtawa SO sam bazan amin taba, saboda inada wanda nakeso"

Kallon muhammad mujaheed yay dajin furucin meenal cewar tanada wanda takeso,sauke ajiyan zuciya yayi sannan yace.
"Meenal kidena wannan maganar mana sam batada amfani saura kwana uku fa adaura mata aure,"

Zuwa lokacin muhammad yagama hassala da iskanci irinna mujaheed,yakaraso cikin takaici yace.

"Wai meyasa bakada hankali ne mujaheed? meyasa kakeson karyata zuciyanka karya kake kace bakason mimi karma ka yaudari zuciyanka don zakayi nadama babba"
"Banasonta! wai anaso dolane? kukyaleni mana"
Mujaheed yafada cikin daga murya dajin haushi, harara muhammad ya antaya masa yace.

"Zoka kalli kwayar idanunta kace bakasonta idan ka isa, asan nan zamu tabbatar da hakan"
Mujaheed batare daya kalleshiba yasa kai yay gaba yasoma sauka daga steps din cikin sauri, shima muhammad yarufa masa baya yanata ruwan bala i,
Mimi najikin mummy inbanda kuka babu abinda takeyi sosai take tausaya wa rayuwar ta haka hasana mah jikinta yayi sanyi matuka haka taja twins suka nufi ban garensu

Bassam yana zaune shikadai a garden yanata kuka tamkar karamin yaro,yana surutai meyasa mimi zatayi masa wan nan sakayyar meyay mata arayuwa haka dabata kaunarsa ko kadan,yana cikin wannan halin ne yaji an dafashi,koda yadago idanunshi dana hasana suka sarke nadan sakanni, kana ta matso tazauna gefenshi dukda irin tsanar data masa yau a yanayin data sameshi seda yabata tausayi,cikin muryan tausayawa tace.
"kayi hakuri ya bassam"
Share hawayen fuskansa yayi yana fitar da huce daga bakinsa mezafi yajuyo yakalleta yace.
"Hakurin mezanyi hasana? kinason nahakura nafasa auren yayarki,ta auri wanda baya sonta bayason ganinta,wai meyasa yayarki zatayimin haka? taso wanda besan darajartaba"
"Bayin kanta bane ya bassam" hasana tayi maganar idonta tafda kwallah, murmushin takaici yayi yace.
"Banyi mamakin jin furucinki ba hasana, saboda nasan yadda bakya kaunar na rabi yayarki, kina yimin kallon dan iska koh"
Sam kasa magana tayi illah idanu data zuba masa,
"Niba Dan iska bane hasana sam koda wasa bantaba kusan tar zinaba ,amma zeyi wuya kifahimceni koki yarda dani,"
Cikin zubar hawaye tace.
"Nayarda dakai ya bassam"
Da mamaki yadago yazuba mata manyan eyes dinsa dasukayi jah saboda kuka,hakanne yasata sunkuyar dakanta tana kallon zara zaran yatsun hannayen ta tace.
"Dama Abban mune yake nemanka, yace gobe insha Allah za ah fadi wanda sukeda sa hannu akan sace yayar mu da akayi"
Wani irin kara cikin bassam yabayar,wanda seda hasana ta dago ta kallesa, hakanne yasashi saita nutsuwarshi yace mata taje tanasanr yana zuwa, tamike kuwa tashige ciki tabarsa anan yadauki wayansa yayi kiranda seda yakwashi time sosai sannan yagama wayan,yamike yashiga ciki shima

WASHE GARI

Karfe 9 kowa ya hallara a gurin meeting anata cece kuce kowa da abinda yake furtawa akan suwa za ah kama yanzu,sam bassam baya cikin nutsuwarsa hatta abban su hasana yafuskan ci haka,isowar su (DPO) dinne yakara hautsina gurin saboda ko isowarsu bassam aka fara arrest dinsa akasa masa anchor,san nan aka kira sunan mahaifiyar sama wato asiya haka ta taso tana gun sheken kuka koda tafito itama sukace ina mahaifiyarta? zuwa lokacin bakajin komi se sallallami namutanen su kaji fulatanci kaji hausa harda turanci, hajiya balaraba tana zaune tayi sharkaf da gumi kunyar duniya ta isheta tsamo tsamo ta taso kuwa bakunya ba tsoron Allah kiri kirk aka daureta itama,se a lokacin (DPO) yayi magana yana kallon Abban su hasana, wanda mamaki da al ajabi sun hanasa koda kwakwaran motsi,

"Alhj,wadan nan damuka kama sune sukeda saka hannu akan sace yarinyarka,hajiya ba laraba tana taya yayanta abokin takarar ka kishi ne akanka mukamin ka dakukayi takara tare kayi nasara bashiba, wannan dalilin ne yasa sukaso suci zarafinka akan yarinyarka,bisa rantsuwar dakayi akan bazaka bar wanda yasace maka yarinyaba yasa nan da dan lokaci za ah fara shari ah dasu domin su fuskanci hukunci....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣️ RABON KWADO....!!

BOOK 3

NA NANA BMB.

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.