Complete Hausa Novels

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 9 of 22

page 25 - 26

Dagota muhammad yay yana murmushi yace." sweetie wayasan to bakyason auren,ay bamusan kinada wanda kikesoba saboda bakiyi mana bayaniba ashe bakyason zabin da daddy yamiki"
Hawayene yakuma ciccikuwa a idanunta saboda yousep dinta datake tunawa,cikin sanyin jiki tariko hannunsa tana cewa

" Bazan taba kin zabin da daddy yay minba saboda nasan baze taba zabamin abinda ze cuceniba don haka zabinshi nima nawane babu abinda zancewa daddy sedai Allah ya saka masa da gidan Aljannah" sarkewa muryanta yasomayi zata cigaba da kuka tunowa da cewar daddy ba mahaifinta bane
" Ya muhammad ina ganin wannan abin kamar a film wai daddy bashi yahaifeni bah haryanzu zuciyata takasa aminta wlh, gaskiya nayi asarar rayuwa dana kasance 'ya ga azzalumi kuma butulu, ashe shinema wanda ummi tabamu labarinsa, Allah sarki auntie har abada bazanga bakinki bah ashe ba ita bace ta haifeni shiyasa tafi kaunar yaya akaina, but dukda haka ina alfahari da ita kosau daya bata taba goran taminba wan nan ma abin ajin jina matane!"

Cikin kuka ta karashe maganar tata harda shasheka domin kuwa abin yana matukar taba mata zuciya,tamatukar bashi tausayi haryama rasa dawani kalami ze rarrsheta dole daman yasan zatayi kuka, to koba komai daga karshe auntie taga matsayinki a yanzu da irin gatanki a rayuwa,
Seda tayi kuka har kanta yasara mata ta lafe a jikinsa tadena shasheka sedai hawaye,

"Sweetie zakison wanda daddy ya aura miki kuwa?"

Tambayar tazo mata bashiri don haka kawai ta daga masa kanta alamun eh, sannan ta dago cikin tausayawa tana kallonsa da jajayen idanunta tace.

"Ya muhammad kaga daddy yaywa kowa aure amma banda kai kayi hakuri kajee sekace bwya sonka yawa ya mujaheed amma yakyaleka,kada kadamu kajee ni inada wadda nazaba maka saboda kauna da shakuwar dake tsakanin mu da kai,kuma nasan bakada budurwa koh?"

daga mata kai muhammad yayi yana kunshe dariyar da take cinsa,

"Cikin jin dadi meenal tace to ya muhammad kasan fah wadda take kaunarka sosai kuma kasan (is so beautiful) halayenta ma masu kyaune, meze hana ka aureta"

Muhammad nunawa yayi begane wadda take nufibah sam dakyar yake iya danne dariyar da take cinsa,

"Yaya mardiyya fah kasan tana kaunarka over ni inason ka aureta"

Muhammad yay murmushi ya jinjina mata kai yace. "Tom shikenan na nima kinsan bazanki zabinki bah sweetie tunda kin yaba da halayenta yayi in muka koma gida semu cigaba da magana koh,"

Cikin jin dadi takara rikeshi tana masa godiya a time din dazata kalli fuskansa da tagano a kwai wata a kasa saboda dariyar dayakeyi amma silent, sosai yake janye ta da hira da surutu har tasaki jikinta ma, dama kaka meenal da surutu, tadage tanata bashi labari irin yadda take rayuwa a gidan yanata zuba mata dariya yana kallonta cikin shaukin kaunarta da tagama kashe masa jiki, mikewa tayi tana gwada masa yadda takeyi idan sunfita,

"Ya muhammad idan mukaje unguwa naga bodyguards din nan suna take mana baya, habawa
zan fara wani konbo ina basarwa ina wani taku inagaya ma,fulatanci ne dama suna yimimshi zan zama kurma!"
Takarashe maganar suna dariya.

"Haba no wonder dole sweetie ki manta dani abinki"
Saurin dawowa tayi tazauna kusada shi tana cewa

" Ya muhammad bazan taba mantawa dakai a rayuwata bah, rana bata taba fitowa tafadi bah batare da natuno ka a zuciya taba,kai na dabanne a cikinta kullum cikin kewarka nakeyi matuka"
wani irin farin cikine yama maye muhammad wanda yasashi sakin lallausan murmushi batare daya shiryaba.

Bangaren yousep kuwa tunda aka daura aure ya kule a daki bekuma fitowa bah, seyanzun da mom dinsu tazo tasameshi a kwance don tagaji da kiranshi yana kin dagawa, a kwance tasamesa ya kurawa guri daya idanu kamar baya numfashi cikin saurinta ta karaso ta dafashi, kallonta dayayi ne yasata sakin ajiyan zuciya, tazauna gefenshi,

"My son am sorry kajee nasan auren nan bada son ranka akayi maka shiba, to amma kasani shi Allah haka yake lamarinsa kayita Addu ah Allah yasa,nana fatiman itace alheri a gareka"
Yousep cika kawai yake yana batsewa kamar ze fashe jiyake kamar ya kwala ihu,

"Mom why da dad zemin haka? sam bana kaunar banzar yarinyar can sam halayenta ba masu kyau bane makirace ko ganinta bana kaunar inyi a rayuwata mayya kawai"

Cikin sanyinta tace."kayi hakuri mana son! banason in karajin kana zaginta yau da gobe se Allah wata rana zaka sota zata zamto taura ruwarka"
"No mom wlh bazan taba son waccar abar bah koda wasa kuwa"

Tayi murmushi tace, "Son kenan, katuna fah lokacin da dad dinku ya aureni kalmar so bata taba shiga tsakaninmu bah,kuma yanzu kaga yadda muke nunawa junanmu soda kauna da kulawa, har Allah ya azurtamu daku, don haka kadena wasu magan ganuma don bakasan me Allah zeyi gaba bah"

"Mom kufa na mussam manne yaza ayi ki hada kanku da waccar mara class din ma don Allah kidena maganar ma yanzu donni bazan taba kaunartaba wlh"

"Kace wlh son rantsuwa fah kayi"

"Eh Allah mom bazan iya son kowace maceba tunda aka rabani da farin cikina"

"Son Allah yayi itace farin cikinka dama tunda Allah ya musanya maka da ita kaga zuwanka Adamawa abin alfaharine a gareka daga zuwa anbaka 'ya sukutun"

"Mom nayi dana sanin zuwa garin nan tabbas bazantaba mantawa da zuwansa bah ashe tsautsayine yakawoni cikinsa ashe iftila ei ne ze fadamin,"
Mikewa mom din tayi tana cewa," lallai son kayi nisa to ni bazan biye makaba haryanzu yarinta na ibarka,Allah yaganar dakai gaskiya" tayi ficewarta abinta tabarshi zaune yanata kun kuni.

Mimi tafiya take cikin sanda harta isa cikin bedroom din dasuke kwana,sauke ajiyan zuciya tayi dataga duk sunyi bacci tayi hamdala don kuwa tasan suka ganta ahaka bakaramar kunya zatajiba ita kanta tasan a birkice ta dawo sauri tayi tashige wanka tayi maza tafito tashirya ta daure gashin kanta data gama busar dashi yanzu, a kasa tayi shimfida tayi kwanciyar ta saboda yadda boobs dinta ke mata zafi bazata iya hawa bed bah su fama matasu, rigingine tayi a kwance idanunta nata tsiyayar hawaye sosai takejin haushin mujaheed yanzu komai daya faru tsakaninsu yake dawo mata gani take komai dayayi mata da mugunta yaringa hadawa abin nashi.

To shima mujaheed koda yashiga makwan cinnasu yata rar da muhammad zaune kan sallaya, koda shigarsa yasau baki galala yana masa kallon mamaki, hakanne yasa mujaheed cewa.

" To CCTV camera! wani munafin cinne yahanaka bacci?"

"Mujaheed kada kacemin seyanzu kadawo daga garden" muhammad yay maganar cikeda mamakin mujaheed da tuni yashige wanka abinshi,

Koda yafito a zaune yasamu muhammad kan bed yana rike da haba yana kare masa kallo yace.
"Babbar magana abin harya kaiga wanka,waishin mujaheed ina auren dole akayi maka harda zaka soma nunawa yarinya rashinta ido,baiwar Allah zatayi fama da jaraba a gurin nan kwazzababbe kawai"

Dariyace taso kwacewa mujaheed amma seya basar don yasan jira yake ya tofa kala ya hayayya ko masa, yanaji yakaraci babatunsa ya kwansa.

To asuba tagari mutan gidan fulani.

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO....!!

BOOK 3

NA NANA BMB

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah }

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.