Complete Hausa Novels

Sulthana Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sulthana Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 1 of 43

Compiled by Umar Dalha.

💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐
*SULTHANA*
💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐

By *Ummy Abduol*

*Page 1 to 5*

Yarinya ce da bazata wuce shekara sha uku bah rak'ube jikin katanga cikin duhun dare sai rawar sanyi take, bata ankara bah ruwa ya tsuge kamar da bak'in kwarya. Dasauri ta koma zauren gidan ta samu guri ta k'ara rakubewa dukda zauren yana zuban ruwa hakanan ta zauna tana matsar kwalla a hankali..

Ruwan sama ake tsugawa a garin kamar da bak'in kwarya, dakyar ta sulale k'asa ta kwanta tana Cigaba da rawar d'ari, Haka barci ya dauketa.
Kiraye Kirayen Sallan Asuba taji, a hankali ta gyara kwanciya saboda sai lokacin ta samu barci sosai, bata gama gyara kwanciyar bah taji tokari. Koba'a fada mata bah tasan Baffa neh, dasauri ta Mik'e zaune tana soshe soshe tana k'ara kallan Baffa dak'e tsaye ya hasketa da tochila.
"Dan Uwarki kinaji ana kiran Sallah bazaki tashi bah, waike Wacce irrin dabba ce zaki tashi koh saina mangareki"
Dasauri ta mik'e ta shige cikin gida tana cigaba da soshe soshenta.

Mama ta hango bak'in rijiya tana jan ruwa, ta k'arasa dasauri ta rik'e gugan
"Mama kawo naja mik'i"
D'an murmushi mama tai
"Aa Sulthana barshi, dauko butta na zuba mik'i kiyi Alwala"
Bah musu ta dauko buta ta k'araso bakin rijiyan, dai dai nan hafsatu ta fito daga dak'in barcinsu tana sosa kai dagowan dazatai taga hango mama na zubama Sulthana ruwa a buta
"Lallia ma Sulthana, dan tsabar iskanci mama ce baiwar ki?? Har tana jawo ruwa tana zuba mik'i a buta"

Nan da nan jikinta ya soma rawa dan tasan halin hafsatu sarai, yanzu ta kamata taimata dukan tsiya
"Haba Hafsatu, menene dan nazuba mata ruwa, yanzu tazo zata amsa na hanata"
Saurin K'arasowa wajan Hafsatu tai
"Haba mama ya k'ike irin wannan maganan, Baffa ya gaya mata duk aikin da zata rink'a yi a gidan nan ciki kuwa harda jan ruwan nan, Anma saboda iskanci tak'iyi saike zaki ja."
Hade rai mama tai tana cigaba da kallan hafsatu
"Banasan iskanci, ki wuce kije kiyi Alwala"
Zumburo bak'i tai ta juya ta kalli Sulthana dak'e tsaye kanta a kasa tayi kwaffa tabar wajan..

Mama ta maida dubanta ga Sulthana
"Ga ruwan maza jekiyi Alwala kamin Baffanku ya dawo"
Amsa tayi ta shiga bayi ta kama ruwa ta fito tai Alwalan, dai dai itama mama ta gama nata Alwalan
"Sulthana shigo dak'ina kiyi Sallan kafin Baffanku ya dawo maza ki hanzarta"

dasauri sauri ta sauya kayan jikinta zuwa wata kod'adiyar Atampha dogon riga, Hijabin mama ta sanya ta tada Sallah. Tana Cikin sallan taji sallaman Baffa, Hanjin Cikinta neh ya k'ada dakyar ta k'arasa idar da Sallan ko Addua bata tsaya yi bah ta fito daga dak'in. Hangoshi tai a Bukkan tumakin shi yana zuba musu Abinci, dagowan da zaiyi yaga ta fito daga dakinshi tana yan Rabe Rab'e kanta a k'asa..

"Sulthana! Daga wani dak'i naga kin fito yanzu"
Inda Inda ta soma yi chan sai mama ta fito sanye da hijabi da Alama Sallah ta idar
"Sallah nace tazo tayi"
Mugun kallo Baffa yabi mama dashi
"Sau nawa Saratu zan fada miki ki fita harkar Yarinyan nan anma Kink'i"
Sakin Bak'i mama tai da mamaki tana cigaba da k'allan Baffa
"Haba Mallan sai kace bakai ka haifeta bah, baka tsoron hakki. Yarinyan nan Amanace fah a Wurinka mai yasa Kake ha.."

"Dallah rufemin baki"
Maida Dubanshi yayi ga Sulthana dake tsaye har lokacin kanta a Kasa da Alama kuka take
"Keh kuma tsayuwa kikai kina Karemin Kallo bazakije kiyi aikinda Yakamata bah"
Dasauri tabar wajan ta Nufi kicin dinsu, kwanonin datti ta soma fitowa dasu tana kaiwa bak'in Rijiya tana Ajewa, lokaci lokacin takan share hawayen dak'e gangaro mata a fuska...

*Shin anya kuwa Baffa mahaifin Sulthana neh?"*
Ku biyoni dan jin Cigaban Labarin

*Ummy AbduAbduol✍🏻

💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐
*SULTHANA*
💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐

By *Ummy Abduol*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.