Complete Hausa Novels

Sulthana Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sulthana Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 43

*Page 6 to 10*

Lokaci lokaci takan share hawayen dake gangaro mata a fuska. Saida ta wanke kwanukan tas sannan ta share tsakar gidan tareda daura abin kari. Bayin gidan ta wanke ta Fito tadau Tsintsiya ta nufi dak'insu Hafsatu. A Kwance ta sameta tana barci gefenta kuma ameena ce zaune kan sallaya tana karatun alkur'ani, dan Rusunawa tai
"Ina kwana yaya Ameena"
Saida ta kamalla sannan ta juyo ta k'alleta da murmushi akan fuskanta
"Lapia lau Amal, kin Tashi Lapia"
Kanta na K'asa ta amsa da Lapia Lau.

Shiru ne ya biyo baya na wasu mintina, dakyar amal ta bude baki tace
"Dan Allah Yaya Amina ki tayani tashin yaya hafsatu inaso nai shara"
Batare da tace komai bah ta shiga tashin hafsatu, dakyar ta tashi suka bata waje ta gyara musu dak'in tsaf. Bata gama ayukanta bah sai wuraren karfe bakwai da rabi na safe, baffa ko sai masifa yak'e tak'i ta gama abin karyawa ga yara naso suje makaranta. Koko ta dama ta dafa musu dankalin Hausa, saida ta zubama kowa ta kaimai Sannan ta dau nata ta nufi zaure dashi.

Hafsatu da Amina suk'a leko dak'insu baffa bayan sun gama karyawa
"Mama, Baffa mun tafi"
Da Fara'a yak'e kallansu Tareda sa hannu cikin Aljihunshi, kudi ya Ciro naira Dari biyu
"Gashi ku raba"
Amsa sukai tareda mai godiya Suka wuce. Mama ta Kalleshi Fuskanta bah Walwala
"Mallan Idan nace inajin Dadin Abinda Kakeyi nayi K'arya"
Kallanta yayi da Mamaki
"Meh kuma nayi?"

Shiru tai dan Tasan Halin baffa Yanzu ya zazzage ta dah Masifa
"Keh nake sauraro"
Ta maza tai ta Kalleshi
"Haba Mallan, Baka gudun surutun mutane?? Koda yake surutu ni nake shanta bah Kai bah"
Kallanta yayi da Alamar mamaki
"Ki fito fili kiyi magana bah kwana kwana bah"
Akan Maganan Sulthana mana Mallan, Yarinyan nan batakai shekarunda zata Rink'a wadan nan Aikin bah, Sannan kuma ka hanata zuwa makaranta. Haba Mallan sai kace bakai ka haifeta bah"

Dogon tsaki yaja tareda mik'ewa
"Ina K'ara gaya miki ki fita Akan harkan Yarinyan nan Bah ruwanki"
Itama Mik'ewan tai tana kallanshi da damuwa
"Haba mallan wanne irin bah ruwana, yarinyan nan fah y'arka ce, jininka ce duk inda na zaga kallona ake ana nunani ana zagina akan ina cizgunama yarinyan nan, kowa laifina yake gani"

Gidon tsaki yaja yabar dakin a fusace, a tsakar gida yayi kicibus da Sulthana shigowanta kenan cikin gidan tana tattara kwanukan da aka ci abinci. Dasauri tabar wajan dan k'aramin aikinshi ne ya duketa batamai komai bah. Kwafa yayi ya fita daga cikin gidan a fusace..

Wanene Baffa?

Dan Asalin jahar kano ne a kauyen karaye. Cikakken Sunanshi Mallan Jamilu dan Mallan, mahaifinshi Mallami neh mai tara Almajirai. Shi kadai mahaifinshi ya haifa, bayan rasuwan mahaifinshi ya cigaba da kula da Almajiran mahaifinshi kasancewar shima yanada Ilimi sosai. Ya gaji gado mai tarin yawa wanda idan ana lissafin masu kudin kauyen zai zo saahu na biyu ko na uku.
A Haka Allah ya hadashi da Rabiatu yarinyar wani buzu da sukazo Cirani nigeria, Shida Rabi sunyi auren soyaiya da Kaunar juna. Sun shafe shekaru masu tarin Yawa har Mallan Jamilu ya sak'e Aure inda ya auri saratu, aurenta da shekara daya ta haifo Amina, bayan Shekara biyu ta K'ara Haifo Hafsatu. Rabiatu da Saratu sunyi zaman lapia sosai wanda ba wanda kejin Kansu duk da kuwa bah Gida daya suke zaune bah. Hafsatu nada Shekara biyar Rabiatu ta Samu Ciki, Cikin Ikon Allah ta Haifi Yarta Ranar Suna Ita da Kanta tasa mata suna Sulthana wato (Sarauniya)

Sam Mallan baiyi Farinciki da Haihuwan nan bah, Tun a Sannan Rabiatu ta fara Fuskantan Wulakanci da Cin Mutumci gurin Mallan, Sulthana nada shekara Sha Biyu mahaifiyarta Allah ya mata Rasuwa ta sanadin Ciwon zuciya wanda Mallan Yak'i kula da ita har Allah ya dauki rayuwarta. Bayan Rasuwan mahaifiyarta Mallan ya dawo da ita gidan d'ayar matarshi Saratu, inda Ya hana sauran yayanshi kowane aiki sai Sulthana, mama wato Saratu na matukar tausayama halinda take ciki itada Aminatu. Mallan Ya cireta a makaranta wanda dama ummanta ce ta sata, ya hanata Hulda da kawayenta, Gashi yan uwan mahaifiyarta bah a kasan suk'e bah..
Wannan knan.....

*Ummy Abduol✍🏻*
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: 💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
*SULTHANA*
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐

By *Ummy Abduol*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.