Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yarima_Abdulmaleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 8
Page 2
Da gudu Bilki ta fito ganin abinda daya faru yasa tace kan ubancan amma Zainab anyi muguwar yarinya sbd bakin hali saida kika karasa min bokiti to wallahi baki isa ba saikin biyani mayya kawai mitsiyaciya ta karasa maganar tana janta ciki hakuri Zainab ke bata amma wani irin gigitaccen Mari ta sauke mata saida ta durkusa har kasa bisa kafafunta saboda azaba wanda hakan yai daidai da shigowar Inna da sauri ta karaso tana dago Zainab din dake kuka fuskarta tayi ja wani irin kallo taima Bilki mai nuna cewa wata rana zaki nadama tace amma wallah Bilki baki da da'a sau nawa zan fada miki ki daina dora hannunki akan yarinyar nan rashin iyaye fa ba hauka bane kinsan irin bala'in da kike kwasarma kanki kinsan hukuncin mai zaluntar maraya me yasa baki da tunani ko kadan ina tsorace miki ranar da zaki kuka da idanunki Zainab ba yarinyar da za'a wulakanta bace duk abinda ya sameki ki kuka da kanki na fada miki.
Kallon sama da kasa Bilki ke mata tunda ta fara magana sannan tace ahayye nanaye kaji mace da kwarton munafirci meye ruwanki a ciki amma ba laifinki bane da alama yunwa kike ji ga dusa can idan kin gama ci kije ki sha ruwa munafikar tsohuwa kawai tana kaiwa nan ta wuce ta koma ciki.
Da kallon suka bita inda sabo kuma Inna ta saba da wulakancin Bilki ba tun yauba hannun Zainab ta rike tace muje dakina Zainaba ki huta kinji ki ta hakuri komai mai wucewa ne Allah ya jikan Umar da Khadija ameen Zainab ta furta cikin damuwa amma ko babu komai tana samun sauki idan Inna ta wuni a gida.
Yau Yarima ke shirin zuwa kano gurin kakarsa zaune suke a palor mama ta kalleshi tace gaskiya babyna kana da kyau kamar balarabe "harka shirya kenan"? Da kai ya bata amsa taci gaba da cewa Allah ya kare min kai baby inaji a jikina kamar zuwanka gurin ammi alkairi ne tamkar zaka hadu da wani abu dazai saka farin ciki kuma ya zamo maka garkuwa a rayuwarka.
Ido ya zuba mata bayan ya gama jin jawabinta yai murmushi har dimple dinsa na lotsawa amma baiyi magana ba mikewa mama
tai tana kire hannunsa suka fita har mota tai masa rakiya kafin ta koma.
Lokacin daya dayai perking da mota a harabar gidan da mamaki Mustapha dake tsaye kafar shiga palor yake kallon motar da tunanin waye a ciki bai kare mamaki ba Yarima ya fito yana gyara agogon hannunshi domin shi kadai ya bata shi mutum ne wanda baya bukatar takurar wasu fadawa ko bayi duk inda zaije shi kadai yake zuwa ko driver baya bukata.
Dagowa yai sukai ido biyu da Mustapha wani ihu yai yana rungumeshi cikin nuna tsantsar murna yace abokina kaine dama zan ganka kwana kusa gaskiya nayi kewarka yaushe raban da mu hadu kusan shekara biyu fa murmushi Yarima yai yana kallon shi yace sorry ba gani yau nazo muje ciki na gaji inason na huta shiga sukai wata farar mace ta dago tana kallonsu tace dama saida tunani na ya bani tunda naji Mustapha na ihu yana cewa abokina nace nasan kaine ba wanda zaizo yayi wannan haukan sai kai ta karasa maganar da murmushi.
Rungumeta Yarima yai a rayuwarsa yana matukar son ammi Mustapha ne ya fara dariya yana cewa wato Abdul-malik har yanzu baka janye wannan dabi'ar taka ba yanzu runguma ce gaisuwa dagowa yarima yai yana kallon ammi alamar ta tanka Musty yace malam bafa zakazo ka sanya tsohuwata magana ba ka baro taka acan tana hutawa zaka wani takura min tawa harararsa Yarima yai kafin ya mike yana cewa muje na gaji inason na huta bani da lokacin ka wucewa sukai yana cewa ammi bari ya dan huta.
Zainab ce zaune a tsakar gida tana hada kunun aya Bilki ta fito a daki tana cewa Zainab me kikeyi anan? dagowa ta tana kallonta tace kunun aya nake hadawa
[11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: Innalillahi dan Allah amin afuwa ban gama typing ba nayi sanding.
*👑Yarima Abdul-malik 👑*
#Yusrah m Abubakar
Yusrahmusa65@gmail.com
*💫ANNURI WRITES ASSOCIATION💫*