Complete Hausa Novels

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yarima_Abdulmaleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 5 of 8

*Page 5

Bashir daya karaso ganin abinda daya faru yasashi juyawa a 360 ya koma gurin Bilki hankali tashe yana shiga Bilki ta mike tsaye tana cewa "ina take"? Bashir dake haki kamar ransa zai fita dakyar yace "wani mai mota ne ya bigeta kuma ya dauke ta sun tafini yanzu ya zanyi"? Cikin harara Bilki tace "ya zakai kuwa banda hakuri"wani irin kallo ya mata daya sata kusan sakin fitsari yace "me kike nufi dan kinga ina shaye shaye sai akace miki bansan ciwon kaina ba kome"? Shiru Bilki tai ta zuba masa ido yaci gaba da cewa to bazai yuwu ba cikin biyu ki zabi daya ko ki biyani kudina ko ki bani hindu a madadin Zainab".

Mikewa Bilki tai kan ubancan tabdijan amma wallahi baka da hankali hindun 'yar riko zan dauka na baka me zancewa iyayenta to waima kana dan kwaya ubanwa zai dau 'yarsa ya baka tun wuri kasan inda dare ya maka Hindu ba sa'arka bace tafi karfin kazami dan jagaliya irinka kudin ka kuma da kake mgn na cinye bazan biya ba ka dau mataki idan ka isa".

Tunda ta fara magana Bashir ke kallon ta har takai aya jin zata raina masa hankali yace "haka kika ce "? Itama cikin fushi take kallonsa tace "eh ko akwai abinda zaka iya ne "? Kai ya jinjina kafin ya daga hannunsa dauketa da mari a firgice ta dago zatai mgn ya kuma wanka mata wani cikin bacin rai yahau dukanta kamar Allah ne ya aiko shi Hindu dake sauraronsu tun dazu ganin zai kashe Bilkin da duka ta mike a guje ta dauko itace tazo zata buga masa ya hankade ta ta fadi kasa kafin ya cilla Bilki daki ya jawo kofa ya rufe yana cewa Hindu "a kanki zan fanshi kudi na "wani ihu Hindu tai amma ba maceci.

Bilki dake daki ta leko ta window tana cewa "wallahi Bashir idan ka taba yarinyar nan kotu ce zata raba mu"ko kallo inda take baiyi ba yaja Hindun dayan daki ya rufo kofa.

Hmmm indai zaka gina rabin mugunta kayi dai dai kai don it may be kaine zaka fada.

Bilki kuka take tana buga kofa kamar zatai hauka musamman yadda taji muryar Hindu na fita kamar wanda take gargarar mutuwa fitowa Bashir yai yana bude Bilki yace "nidin ba mahaukaci bane kamar yadda kike dauka ta nasan me nake kuma bangama fashe kudina ba in anjima zan dawo" yana kaiwa nan yai waje hannu Bilki ta dora a ka tana cewa Allah ya isa mugu tsinanne baza ka gama da duniya lafiya ba azzalumi.

Hhhh wai yau Bilki ce me kiran wani azzalumi.

Musty ne ya fito yana mika cikin mmk yake kallon Yarima don jiya haryai bacci bai dawo ba zama yai kusa dashi yana cewa "wai jiya ina kaje ne tun yamma na rasaka nayi tunanin ma ko gida ka tafi dan nasan ba karamin aikin ka bane"shiru ya masa zuwa can yace "yarinyar na bige jiya a mota shiyasa ban dawo da wuri ba yanzu ma inaso zan koma asibitin ne"kallonsa Musty yai yace "ok Allah ya rufa asiri bari na shirya sai muje tare"kai Yarima ya girgiza "no need "da mmk Musty yace "me kake nufi "? Mikewa yai batare daya bashi amsa ba yace "let me go i don't want be late"? Ko tsayawa yaji me Musty zaice baiyi ba ya wuce domin a yanzu ma yasa an zo daga Abuja an dauke ta domin a kara duba lafiyarta shima zuwa jimawa zai tafi.

Sai dare ya isa gida ba wanda yasan ya dawo ko hutawa baiyi ba jakarta dake kusa dashi ya dauko yana budewa ganin takardu ne yasa ya mayar sai wani photo daya sashi kusan kwaruwa da ganinsa cikin mamaki ya zubawa photon ido idan ba mafarki yake yi ba kuma ba idonsa ne ke nuna masa hakanba tabbas wannan matar ta jikin photon tana matukar kama da mamansa dan farko ma yai zaton itace sai daya kalla dakyau sannan ya gane ba ita bace shiru yai ciki mmk to wacece wannan yarinyar daya buge wacece wannan matar dake kama da mahaifiyarsa shiru yai ba amsa dan haka dole ya hakura ya kwanta bacci wanda kusan rabi da rabine.
Asuba nayi dayai sallah yabar masarautar bai yarda an ganshi ba dan baya bukatar hakan.

Kwanan Zainab biyu a asibiti kuma alhmdllh babu abida daya sameta saidan kurjewa mamaki ne ya isheta ganin inda take tasan dai asibiti ne to kenan mai motar daya bige tane ya kawo ta tana cikin wannan tunanin likita ya shigo yana cewa "to alhmdllh yau muka baki sallama wanda ya kawoki yanzu zaizo ku tafi "kai Zainab ta daga tace "nagode "fita likitan yai da kamar minti goma taji anyi sallama da wata irin murya data sata dagowa da sauri ganin waye shima idonsa a kanta cikin wani irin mmk da yake neman sheke masa tunaninsa bai zauna ba ya tsaya a bakin gadon yana harde hannuwansa a kirji kawai ya kasa mgn.

Dan sauke nufashi yai yana kallon ta yace "amma kina matsayin mace kike irin wannan gudun a layi ina zakije"? Umh daga haduwa sai tambaya maimakon ace ya jiki sunkuyar da kai tai cikin sanyi tace "wani ya biyo ni"wani? "Me kika masa"? Cikin kuka tace kishiyar ummi nace tamin sharri kuma ta koreni shine tace ya biyo ni wai ya fanshi kudinsa da taci"tambayar ta ya kuma yi cewa "yanzu idan na mayar dake kano zaki koma gurinta"? Kai ta girgiza tace "idan naje ma bazata barni na shiga gidan ba ni kuma bansan inda zanje ba a matsayina na mace ina tsoron a keta min mutunci na idan kasan wani gidan marayu na rokeka ka kaini can na zauna".

Shiru yai ya zuba mata ido yana tunani a zuciyarsa yace "to ni yanzu ya zanyi da ita"? cikin sanyin nazari yace "to
ko masarauta zan kaita kila zasu samu mafita"jin zuciyarsa ta amince da hakan yace "ok taso juyawa yai ya fita ta mike tana bin bayanshi har jikin mota suka karasa ya shiga yana ce mata ta shiga daya site din sannan ya kama hanya wani dankareran gida ya kaita amma akwai tsaro har cikin bedroom ya karasar da ita yana ce mata ga toilet nan idan tana bukatar wanka ta zauna yana dawowa mmk ne ya kamata ita da tace ya kaita gidan marayu sai ya kawota wannan kyakkyawan gidan zama tai bakin gado tana kara kallon dakin da kyau.

Kwananta biyu a gidan amma bata kara ganinsa ba saidai komai ta bukata zata samu.

Shigarsa gurin mai martaba kenan yaga yadda mai martaba ke kallon shi abin ya bashi mmk amma sai ya dake ya mike zai tafi yaji muryar mai martaba yace "Muhammad wacce yarinyar ka ajiye a gidanka"? labari yazo min cewa kana ajiye mata a gidanka saidai ban gamsu ba don ba halin ka bane, mene gaskiyar al'amari "? Cikin mmk Yarima ya kalli mai martaba kafin ya juyar da kallonsa saitin Yaha wani irin shu'umin murmushi yaci karo dashi a furkarta nan take ya harbo jirgin ya kalli mai martaba yana cewa "ni kaina bani da labari akan hakan kakana kila so kawai ake a hada ni dakai kasan ba halina bane"kai mai martaba ya jinjina cikin gamsuwa yace "Muhammad nikaina ban yarda ba nasan sharri ne akai ma tashi kaje Allah yama albarka"murmushi Yarima yai yana kallon Yaha ya mata alama da tasa batasan lokacin da tace "kuturun ubacan ni kakewa haka"? Cikin haushi Abba yace "ke kuma da uban wa "? Shiru tai cikin takaicin ganin yadda Yariman ya nuna kamar badashi take ba hakan na nufin yamai da ita mahaukaciya a cikin mutane
Mikewa yai har lokacin da murmushin sa ya fita a palon ya bar Yaha kamar ta dora hannu aka tai kurma ihun takaicin sa.

Bai zauna a masarautar ba can gidansa ya koma dan bai kamata ya barta ita daya ba, bayan sallar isha yana zaune a palor yaji an bude get din gidan ko kafin yai wani yunkuri yaga su mai martaba sun shigo dukkansu zama sukai ba wanda yai mgn mai martaba yasa wadanda yazo dasu su goma su shiga gidan su bincike masa ko'ina wani irin faduwa gaban yarima yai amma ko kadan bai nuna ba sun jima suna binkice suka fito cikin girmamawa suka ce basuga kowa ba hamdala kowa yake a gun banda Yaha dan itace ta kara hura wutar ya kamata a zo a bincika gidan cikin jin dadi mai martaba yace "madalla da yaro na gari yanzu kan zargin mu akanka ya wanke Allah ya kara shirya mana kai", fatan baka shiga damuwar ganinmu dakai ba shiri ba"? Murmushi Yarima yai "kakana komai kukai ai kun isane kuma kuna sona shiyasa hankalinku yaki kwaciya sai da kuka tabbatar"mikewa mai martaba yai yace cewa su tashi su tafi har jikin mota ya raka su kafin ya dawo gidan direct dakin Zainab din ya shiga a jikin window ya ganta tsaye cikin mamaki yake kallon ta da alamar tambaya dan zama ta tace "naji abinda ake fada a palon shine na shiga toilet su kuma da suka zo iya budawa sukai ganin ba kowa suka rufe ni kuma ina bayan murfin toilet din"ajiyar zuciya ya sauke "shikenan good night "yana fadin haka ya fita a dakin ita kuma ta kwanta.

Gari na wayewa yace ta shirya zasu wani guri saida ta gama komai ta fito ta sameshi a mota mintina kalilan suka iso inda zasu cikin mamaki Zainab ke kallon masarautar a ranta tace kodai dan sarki ne, to amma me zasuyi anan? ganin ya wuce ta yasa tabi bayansa tana kalle kalle kamar 'beran kauye yaje birni bai zame ko'ina ba sai asalin babban palon mai martaba kuma yau gabadaya ahlin suna can bai tsaya ko'ina ba sai gaban mai martaba ya durkusa ya kwashi gaisuwa cikin mmk mai martaba yake kallon Zainab yace "Muhammad daga ina ka samo wannan"? Cikin ladabi ya fara fada musu komai har kuwa zaman datai a gidansa shiru palon ya dauka kowa na kallon Zainab cikin tausayawa banda Yaha da haka kawai taji tsanarta lokaci guda ta diram mata arai.

Mai martaba ne ya kalli Zainab yana cewa "ke yarinya daga ina kika fito? mene gaskiyar labarinki,? kada kiyi mana karya ke 'yar waye? Zainab da kanta ke sunkuye tun dazu muryata na rawa ta fara basu labari kowa ji yake tsumin jikinsa na tashi dajin labarin yayin da ita kuma take kukan tuna mahifanta.

Lallai kam taga rayuwa ace bakasan dangin ka ba ko daya wanne irin hali zaka shiga.

Mai martaba daya gama tunani yace "to yanzu mene shawararku akan wannan al'amarin domin abune mai girma"? Abban Mahmud ne yace ai inaga ba abinda zamuyi daya wuce mu rike ta anan tamkar 'yar da muka haifa idan shawara ta tayi, "amma ranka ya dade me kace"? Mai martaba yace "haka shine dai dai Ibrahim nima abinda nake tunani kenan idan ma mun barta ta tafi babu inda zataje, to amma a cikin ku waye zai riketa kai ko Yusuf "? Abba yace "a'a nizan riketa sai ta zauna a gurin Yahanasu duk abinda take so zata samu".

Gyara zama Yaha tai tana cewa "gaskiya nidai bazan riketa ba tunda Hajara ta kusa zuwa taya zan rikesu har su biyu kawai bansan yarinya ba daga ta fada muku karyarta ko da sharri tazo wa yasani sai a nemi a likamin ita ni dai bazanyi rikon wannan tsintacciyar magen ba"tana fadin haka ta mike ta fice a palon.

Da mmk mai martaba yace "Ibrahim dama matarka bata da kirki a gabana take iya fadar bakaken mgn haka"? Cikin ladabi Abba yace "ayi hakuri ranka ya dade amin afuwa"dadyn Yarima mai martaba ya kalla yace "Yusuf kai na baka ita daga yau kaine mahaifinta duk wani nauyin ta akanka yake"cikin girmamawa yace "to ranka ya dade godiya nake "kallon mama yai yana mata alama dan murmushi tai tana jinjina kai kafin ta mike tana cewa "yata tashi muje"mikewa Zainab tai tana goge hawayen maganar da Yaha ta fada akanta suka fita Yarima ma sallama ya musu yana fita domin shi kasar ma zai bari.

Mama na rike da hannunta har part dinta ta rakata wani bangare daban tace ta zauna tana zuwa ba'a jima ba ta dawo tare wata budurwa zamatai tana kallon Zainab tace "ranki ya dade dama Yarima Abdul-malik nada kanwa wallahi suna kama"? Murmushi mama lokacin zata fita tace "kedai yi mata lalle kawai ina dawowa yanzu"lalle ta fara zana mata mai kyau saida aka gama sannan aka fara yimata kitso tab masha Allah sai wanda ya ganta bayan angama komai tai wanka mama ta kawo mata kaya tasa ta fita palo.

Dagowa mama tai tana murmushi tace "dota zo ki zauna ga abinci nan zama Zainab tai tana sunkuyar da kanta tace "nagode mama Allah ya saka da alkairi" har lokacin murmushi mama keyi Yarima ya shigo cikin shirinsa alamar lokacin tafiyarsa yayi mikewa mama tai tana riko hannunsa tace baby harka shirya,? yaushe kuma zaka dawo"? Zama yai yana lankwasar da kai yace "bazan wuce wata biyu ba kawai"zaro ido mama tai "baby wai watan nan jinta kake kamar sati naga alama dadi kake ji idan ka tafi ka barni amma yanzu tunda muna da wata babyn shikenan kaje kai shekara ma"cikin shagwaba yace "haba mama kar muyi haka dake am first and last"cikin zolaya mama tace "tab waya fada ma"? Gara ka sake shiri dan kaidin yanzu babban yayane"yunkurawa yai zai tashi ta rike shi tana dariya tace "baby tsaya kaci abinci" dan bata fuska yai ganin ta dauko cikin lallami tace "ci ko spoon biyar ne sai ka tafi kaji babyna" tana fada masa magana mai dadi ta samu yaci abinci kafin ya tafi Zainab kan dataga irin lallabashin da mama keyi kamar yariri yasa ta zaro ido aranta tace "tabdijan shagwababbe".

Sati uku da tafiyar Yarima Hajara ta zo murna gurin Yaha kamar ta maida ita ciki duk abinda tace yanzu za'ai mata shi.

Abinda aka samai rana me karewa ne yau gida kacame yake da murna yarima zai dawo dan Hajara ma gabadaya ta kasa nutsuwa sai kaiwa da komowa take abinci kala Kala tasa aka mata na saukarsa a palon Yaha ta ajiye tana cewa bari taje tai wanka Yaha batai mata magana ba domin abinda ke damunta daban Abba da Dady sun tafi masarautar Bauchi mai martaba ya aikesu kawai ji take hankalinta bai kwanta da hakan ba da tafiyar da sukai.

Da yamma Yarima iso gida murna abin ba mgn kamar yadda aka saba tararsa koda yaushe yauma haka saida ya gaisa da mai martaba sannan ya shiga part dinsa don hutawa yana palo Hajara ta shigo da wadanda suke dauke da abincin suna ajiyewa sukai waje sai daya gama daura agogon hannunshi ya nufi hanyar fita shan gabansa tai tace "haba Abdul-malik mene haka"? Da mamaki yake kallon ta ita kuma wannan lfy uban me tazoyi nan cikin danjin haushi yace "ban guri idan kika kara shigowa part din nan saikin gane kurenki"cikin nuna isa Hajara tace "malam bafa zaiyuwu ka wulakanta niba dan kawai ina sonka bashi yake nufin kana da ikon da zakai min kowanne cin fuska ba"kallon ta yake cike da tsana danshi wannan me kama da tabaryar ba abinda zaiyi da ita zagaye mata yai zai fice ta jawo hannunsa tana cewa "wallahi fa baka isa ka fita a palon nan ba sai ka saurare ni ko anfada maka nidin sa'ar____bata karasa ba tai shiru jin wani lafiyayyen mari ya sauka a kumatunta ba arziki ta sake shi ko karasa kallonta baiyi ba ya fice yana jan tsuka kuka Hajara ta fice dashi tana komawa guri Yaha harda birgima a kasa wai marinta yai hankali tashe Yaha tace "ya mareki"? Amma wannan yaro anyi mara tarbiyya kinga daina kukan aure ke dashi kamar an daura ne"share hawaye tai "wallahi umma ko baya sona dole ya aureni "Yaha tace af kwantar da hankalinki nace miki nasan abinda zanyi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.