Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yarima_Abdulmaleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 3 of 8
*Page 3
Tana kallota tace "kunun aya nake hadawa".
Kudi ta mika mata jeki sayo min kayan miya bari na rika dura miki to Zainab tace tana amsar kudin tasa hijab ta fita a gidan Aliya ce ta shigo tana cewa, a'a Bilki harda kunun aya kika koma yine? Um lallai liyafa taci gaba ta karasa maganar tana zama a kujerar da Zainab ta tashi sai a sannan Bilki tai magana "a'a ba nawa bane na Zainab ne makaranta zata tafi dashi jin haka yasa Aliya tabe baki tace wallahi shiyasa duk yarinyar nan tabi ta rainaki ashe guri ta samu kina mata bauta Bilki zatai mgn Zainab ta dawo dan haka tai shiru aje kayan miyan tai tana dauka jakanta ta fita a gidan haduwa sukai da hindu a karshen layin anguwar suna tsaye da wani bata ko kalli gurinsu ba ta tsaida napep ta shiga.
A shirye suka fito shida Musty zai rakashi makaranta dan lecturer ne ammi ce ta kalli Yarima cikin wasa tace me soja zaije yi makaranta karfa ka firgita dalibai dan murmushi yai yana kallonta yace, dama ana gane soja ne ko baisa kaya ba? Dariya Musty yai ana ganewa mana musamman rashin fara'arka.
Mikewa yai yace to naji muje tunda ban sako dakai ba fita sukai suna shiga mota basu zame ko'ina ba sai makaranta babu yadda Musty baiyi ba akan ya karasa office dinsa amma yaki yace ya barshi anan idan yana bukata zai biyoshi hade rai Musty yai zaiyi magana Yarima yace masa "sorry"cikin haushi yace a'a uban sorry dan iska kawai wucesa yai shi kuma ya tsaya jikin motar yana waya da mama kamar saida akazo saitin kunnensa aka kwalla kiran Zainab wallahi ki tsaya kibani abuna idan na kama ki zaki sani haka kawai xuciyarsa ta tunzura shi ya kalli inda ake maganar idonsa ne ya sauka akan Zainab dake tsaye tana dariya rike da fefa a hannunta tana kalla alamar karantawa take wani irin kallo ya bita dashi cikin mamakin da baisan yayi hakan ba.
Karasowa waccen din tayi zata kama ta sukayi wani lungu da gudu dan dafe kirjinshi yai tare da runtse ido Musty ne ya dafa shi bai dago ba cikin mamaki yace abokina yadai meke faruwa? Shiru yarima yai ba tare daya bashi amsa ba saima shiga mota dayai abin ne ya daurewa Musty kai dan haka shima shiga yai daidai zaiyiwa motar key ya kuma cewa Abdul-malik wai dan Allah meke damunka naga gabadaya ka canja ba haka muka taho ba kodai kayi gamo ne? Wata uwar harara Yarima ya sakar masa batare da yace kala ba rabuwa dashi Musty yai dan ba amsa zai samu ba.
Koda suka koma gida ma kasa samun nutsuwa yai daya rufe ido ita yake gani lokacin da take dariya gabadaya ko abinci bai samu yaci ba har dare.
Bayan kwana biyar yau weekend ne Zainab tana zaune a daki taji muryar bashir ya shigo yana cewa masoyiyata ina kike? Ga kayan marmari na kawo miki da gudu Bilki ta fito daga daki har tana tuntube ta karbe ledar hannunsa tana cewa kai wanne irin banza ne ai ba ita zaka kawowa ba ni zaka kawowa tunda nice uwar 'ya cikin muryar yan kwaya bashir yace gaskiya ni kullum sai karbe min kudi kike kuma kinki fada min yaushe ne auren zama Bilki tai tana bare ayaba tace kwantar da hankalinka an kusa kadai kaci gaba da kawo kudi aure da Zainab kamar anyi ne shigowar hindu kenan ta karasa maganar tana cewa kwarai kan zamu sha biki ankon yi shirunka maraya zamuyi😂 amarya kuma sai ta dinka azari lilo da takalmi silifa dariya gabadaya sukai Zainab dake sauraronsu ta girgiza kai tana neman tsari daga sharrinsu 😡.
Yau Monday har Musty ya gama shiri Yarima na kwance yana kallonsa juyowa yai yana kallon sa yace wai malam lafiyarka kalau ko junnu suka shafeka gabadaya ka bi ka sauya to nidai tashi ka shirya ka rakani makaranta.
Mikewa Yarima yai yana daukar towel yace jeka bazani ba gida zan tafi zaro ido Musty yai kai da kace zakai saki uku daga daya kace wai tafiya zakai shiga toilet yai yana cewa eh idan kuma zaka hana to dariya Musty yai ni asuwa kare da gudun layya ka gaishe min da aunty na yana kaiwa nan ya fita.
Cikin minti goma ya gama shiri sama sama yai sallama da ammi ya kama hanyen Abuja lokacin daya isa gida tararsa harda mai martaba kamar zai mayar dashi ciki wani irin abune ya tsayawa Yaha a makoshi dakyar take hadiyar yawu ganin yadda kowa yake rawar kafa akansa barin gurin tai kamar zata tashi sama tana shiga part dinta tafara kaiwa da komowa ta ciji yatsanta yafi sau a kirga harsai da yatsan ya fidda jini bata sani ba saboda zafin da takeji a ranta daga waya tai tana kira bugu daya aka dauka cikin tsawa ta soma mgn hajara nace kizo kinki ko kinsan irin halin da nake ciki kuwa na baki nan da jibi ina son ganinki cikin Abuja bansan shashanci daga can dayan bangaren hajara tace wai umma meke damunki naga da ko nazo ko kar nazo baki damu ba gaskiya bani da lokaci a yanzu tana fadin haka ta katse kiran tsaki Yaha tai dai dai lokacin da Mahmud ya fito daga part dinsa yana mika alamar daga bacci ya tashi kallonsa tai cikin takaici tace sakaran banza ba dole kai bakin jini ba tunda bakasan ciwon kanka ba shashasha😁kallonta Mahmud keyi yace me kuma nayi daga tashina kefa abin laifi bayai miki kadan wata uwar harara ta sakar masa cikin san huce haushinta tace uwarka da ubanka kaimini dariya Mahmud yai yana cewa ke da Abba kenan shiru Yaha tai ta zuba masa ido cikin takaici bata sake magana ba.
Yarima kuwa sai daya huta gajiya ya tafi gurin mama fara'arta ce tamasa maraba rungumeta yai yana cewa fatan alkairi gareki momy na su ammi na gaishe ki da wannan yaron.
Wane yaro kuma badai Mustapha kake nufi ba dan wannan babanka ne tunda kanina ne shagwabe fuska yai to amma aina fishi "eh komai kayi ba finsa ba shidin uncle dinka ne"
Tab aikwa bazai samu ba, dan shiru yai zuwa can yace mamina zanyi tafiya gobe zan dawo nan da wata uku kallonsa tai tana cewa Allah ya tsare min kai babyna zamewa yai ya kwanta akan cinyarta yace ameen mom nagode da addu'arki.
Washe gari tun sha biyu ya gama shirinsa cikin kayan soja yaje sallama da mai martaba a gabansa ya durkusa yai kneel down yana cire hular kansa hannu mai martaba ya dora akan nasa yana jero addu'a ana amsawa saida ya gama masa ya mike yana rungumeshi cikin jin dadi kafin yaje ya rungume dadynshi albarka sosai ya samu kafin ya shiga motar da zatai masa rakiya zuwa airport.
Bilki ce ta fito daga daki tana kwalla kiran Zainab jin shuru yasa ta leka dakin ganin bata nan tace lallai yarinyar nan uwar raini ce bari zata dawo duk gidan uban wanda taje ma.
Zainab ce zaune gaban wani tsoho kallonsa tai tace dan Allah kaka Abdullahi abbana bai taba fada maka labarin danginsa ba? Kai ya jinjina cikin tausayawa yace Zainab tunda nake da Umar bai taba fada min asalinsa ba saidai a yanayinsa idan yai wani abun zakiga tamkar shidin jinin sarauta ne amma bani da tabbaci akan hakan hakanan Khadija ma bansan asalinta ba tsintar ta nai kawai bata cikin hankalinta nai mata magani ta warke amma dana tambaye ta ko tasan danginta tace a'a ta mantasu har tabar duniya kuwa bata tuno suba. Kuka Zainab ke yi harda shashsheka sosai Abdullahi ke tausayin Zainab saidai ba yadda zasuyi nasiha ya mata kafin yace ta tashi ta tafi gida.
Bayan sati daya tafe suke daga farkon layinsu zasu tafi gida ba wanda ke magana Zainab ce ta kalli Fatima tace wai nikam lafiyanki kalau? Sauke ajiyar zuciya tai tana cewa inafa lafiya zuciya ta nason jefani a tsaka mai wuya wani take so dan murmushi Zainab tai tana cewa wakenan babu boye boye ta fada mata cewa uncle Mustapha take so sai dai tana tsoron kada ya gane ya kore ta danko lecture yake musu tana yawan hada ido dashi.
Yar dariya Zainab tai tace bawani korarki dazai tunda ni muna mutumci dashi idan zanje gurinsa zamuna tafiya tare sai ku saba dashi ko ya kikace murmushi Fati tai cikin jin dadi tace nagode Zainab dai dai sun karaso anguwar su kowa ya shige gida.
Da sallama ta shiga Hindu dake wanki tace gadontsiya andawo daga yawan tambadancin kenan gaban ta Zainab ta karasa tace idan harni tsiyace kema haka baki da bakin da zaki fada min magana ki kiyayeni na fada miki ki guji ranar da zaki kaini bango zakisha mamakin matakin dazan dauka a kanki dan wallahi saina dumama miki jiki da duka.
Mikewa hindu tai tana cin kwalarta tace ke nikike fada ma mgn haka kwarai yaushe kika samu wannan damar kan mage ya waye ko to wallahi zanci uwarki wani irin mari Zainab ta dauketa dashi sai da taga taurarin azaba ✨ cikin bacin rai tace kar ki kuskura wannan kazamin bakin naki ya kara zagarmin uwa dan akanta zaki ga anahin wace Zainab Umar zan iyayin abinda ba'ai zato ba tana fadin haka ta tureta tai gaba mamaki ne da tsoro suka bayyana a fuskar Hindu bata taba zato cewa Zainab nada baki haka ba shigowar Bilki kenan ganin yadda Hindu ta zubawa guri daya ido tace ke kuma lafiya? Kai Hindu ta girgiza cikin takaici tace bakomai ta koma gun wankinta kira Bilki ta kwalawa Zainab fitowa tai cikic fada tace ina kikaje yau? Da ladabi Zainab tace makaranta naje wata uwar harara ta mata bance ki zauna a gida shine dan ban isa ba kika fita wato na kasheki ko? Kai Zainab ta girgiza kiyi hakuri
Keda hakurin kunci gwafar ubanku tashi dora min miya ni kada lokaci ya kure mikewa tai ta shiga kitchen.
😍Ana tare in sha Allah yan group din ANNURI W A gaisuwa ta a gareku da bata da iyaka.
INDO KINA RAINA CAN CIKI BA WANDA ZAI TADDOKI.
ONE LOVE 💋❤
*Mrs Al'ameen Ahmed ce*
[11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: (*() *) 8:18Am typing 📲
👑YARIMA ABDUL-MALIK 👑
💫Annuri Writer's Association💫
Story and written
Yusrah Musa Abubakar
Always be watchful dont take risks don't try to get lost try to protect your life always.
Manzon Allah (s*a*w)
Ya mana nasiha cewa muso juna mu rike gaskiya da amana sannan mu raya zumunci hanya ce ta aljannah duk makiyin zumunci bazaya kusanci ceto ba.
Muna sonka fiye da rai da iyaye da dukiya.
#Y M ABUBAKAR#