Complete Hausa Novels

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yarima_Abdulmaleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 8

*Page 4

Yaha ce zaune a palor tana waya cikin fada tace "yanzu yaya kamar ni da girmana na daga waya na kira Hajara amma yarinyar nan tamin rashin kunya tana nufin ban isa da ita ba kome yanzu idan na kira ta a waya bata dagawa dan kawai ina son ta zo shine sai ta bata min rai dan Allah yaya ka turo min ita tazo".
Sai daya gama sauraronta ta gama sannan yace "ita Hajaran ce bata daga wayanki amma shikenan zan same ta saidai a yanzu bata da lokacin zuwa gurin ki domin jarrabawa suke taya kuwa zata zo miki saidai ki bari sai su gama".
Dan shiru Yaha tai zuwa can tace "shikenan yaya amma dan Allah tana gamawa ka turo min ita tazo ni zan sai mata makaranta anan inyaso sai taci gaba da karatunta". Mamaki ne ya kama yaya yasan Yaha dasan kudi lallai abinda Hajaran zatai mata babba ne dan haka zai bibiyi koma menene Yahan take shiryawa daga haka ya mata sallama.

Tsawon wata guda kenan Yaha na zuba ido amma babu Hajara babu alamarta yauma zaune suke tace "ka gani ko Mahmud yar iskar yarinyar nan tana so ta bata mana shirin mu" tabe baki Mahmud yai yana cewa amma dai Umma ai kinsan taurin kan yarinyar nan ko tunda yanzun Abdulmalik din bayanan ki bari mugani kafin ya dawo ko za ta zo". Jinjina kai "tayi kuma haka nefa to bari mu gani zuwa dawowar tasa idan ma bata zoba da kaina zanje har maidugurin in taho da ita".

Yau da wuri su Zainab suka shiga jarabawa amma basu fito da wuri ba, a hanyarsu ta dawowa gida tafe suke da Fati Zainab tace "kai wallahi jarabawar yau tai wuya mun dauki dogon lokaci dariya Fati tai tana cewa to dama karatun likata wasa kema lokaci zaizo da zaki fara operation zaki ga ribar wuyar da kika sha". Duka Zainab takai mata inji ubanwa niko allura bazan iyaba balle operation". Har lokacin dariya Fati ke mata zatai magana Zainab ta katseta da fadin "kinga ni dan Allah muyi sauri karki jamin jarabar umma dan nasan tanacan tana jira na".

Bayan kwana goma yau Yarima zai dawo amma babu wanda ya sani suna zaune a palon mai martaba kamar daga sama suka ganshi ya shiga palon cikin kasaitacciyar sallamarsa da wani irin murmushi a fuskarsa Abba ne ya kalleshi yana cewa "babana yaushe ka dawo"?har lokacin murmushinsa na nan yace "sorry Abba nayi shigowan dare ne". Ya fada yana kallon mama datai masa alamar jinjina da hannu.
Mai martaba da farin cikinsa ya kasa boyuwa yace "matso kusa dani mana Muhammad yaushe rabona dakai" mikewa Yarima yai yana karasawa rungumeshi yai cikin so yace "Allah ya maka albarka Abdul-malik" "amin" duka suka amsa banda Yaha data Mike ta fice a palon tana zuwa part dinta ta kira Hajara tana dagawa cikin 'kunar rai Yaha tace ''waike wacce irin yarinya ce nace kizo kinki ko zan fita a hanyarki fa cikin tabe baki Hajara tace "towai dan Allah umma idan na zo me zanyi miki"? Cikin fada Yaha tace uwarki zaki min kizo mana ai zaki gan___dif taji an kashe wata uwar ashar ta saki tana jifa da wayan.

Hhhh! mai son waya jama'a saidai taci screen ๐Ÿ˜‚.

Zainab kan angama jarrabawa kuma sakamakonsu ya fito ansamu abinda ake so dan haka tacewa Fati ta rakata zataiwa uncle Mustapha godiya Fati tace "nima daga can na ganoshi"dariya Zainab ke mata har suka shiga napep.

Don Allah ayi hakuri bani da caji in sha Allahu zuwa jimawa zan karasa muku page din.

Ana tare ๐Ÿ˜๐Ÿ’‹
[11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: Hhhhhhhh gani na biyu ku fito ku kashe kwarkwatar idonku๐Ÿ˜† Yarima ya tafi kano ko me zai faru muje zuwa.

#YUSRAHMS#

Zaune Zainab take a kofar daki Bashir ya shigo Bilki dake kitchen ta fito da sauri tana karbar ledar hannunsa ta dauko masa kujerar roba ya zauna yana dauko kudi a aljihunsa yace "ga kudin sadakin na samo ranar juma'ar nan nake so a daura mana aure na samu gurin zama a wani bariki"cike da rudewa Zainab ta dago tana kallon Bilki hawaye na zuba a idonta ๐Ÿ˜ขkallon kudin Bilki tai tace "nawa ne "? Bashir dake kallon Zainab yana murmushi yace "dubu biyar ne"hade rai Bilki tai "gaskiya ni bazan karbi dubu biyar ba kaje ka kawo min dubu ishirin indai kana so a daura"Bashir yace "to wannan dinma kinsan da yadda na samu akuya na sata sannan nasiyar ta na kawo miki"harararsa Bilki tai lallai ashe baka son auren shiyasa kake jada ni malam kaje ka cikato kudi ka kawo idan ba haka ba sai dai a fasa"kada kai Bashir yai yace "shikenan zan ciko to rike wannan din"mikewa Bilki tai batare data karba ba tace "a'a jeka da abinka a jumlace nake son kudin"mikewa yai yana fita a gidan Bilki dake cin kifin daya kawo ta kalli Zainab "ga irin kayan mijin naki idan zaki ci"takaicine ya kama Zainab sai kawai ta fashe da kuka baki sake Bilki ke kallonta tace "munafika ba gata zanyi miki ba".

Zaune suke a palon ammi Mustapha yace "wai ni Abdul-malik na tambaye ka mana yaushe zakai aure"? Wata uwar harara ya samu daga Yariman amma bai samu amsa ba cikin tsokana Musty yace "ya ina tambayar ka zaka wani rabu dani"kallo mai nuna ina ruwanka dani ya kuma yimasa dariya Musty yai yana cewa "da ruwana man ina matsayin baban ango don Allah Abdul-malik yaushe zakai aure"? Mikewa Yarima yai yana cewa "ranar da ka zaba min dan sa ido kawai banason takurawa malam ka rabu dani na huta" yana fadin haka yai waje dariya Musty yai yana daga murya yace "oho dai komai daren dadewa zamu ga gwanar taka ai".

Koda safe da kamar zai cewa Musty bazai rakashi ba sai kuma wannan yarinyar ta fado masa a rai don haka yace suje a hanya Musty ke ce masa "i have found a girl i want marry amma sai ta kara girma"ta tafar sauke Yarima baice ba har suka karasa makarantar.

Zainab ce ta fito daga wanka cikin sauri ta gama shiri ta fita a gidan don tana son taiwa uncle Mustapha godiyar nauyin karatunta daya dauka Yarima dake tsaye jikin mota jin ya gaji yasa yai niyar shiga office din Musty yadan huta yana cikin tafiya ba zato yaji yayi gware da abu da sauri ya dago yaga wanne banzanne yake tafiya kansa a sama ๐Ÿ˜œidonsa ne ya kalli fuskar Zainab datai baya zata fadi cikin sauri ya riko hannunta yana jawo ta donkar taje kasa cikin tsoro tai saurin rike masa riga tana kife kanta a kirjinshi jiki na rawa tai shiru zuwa wani lokaci da nutsuwarta ta dawo jinta jikin mutum yasa da sauri taja baya tana zaro ido ๐Ÿ™Štace "dan Allah kayi hakuri ban kula bane"idan dutsi zaiyi magana shima yayi ganin yadda take a tsorace yasa ya tabe baki ya juya yana wucewa ajiyan xuciya ta sauke daidai Musty ya iso yace "a'a Zainab Umar tsohuwar daliba ziyara kika kawo mana ne"?.

Cikin ladabi Zainab ta gaida shi sannan tana "uncle dama nazo nai maka godiya ne"katseta yai daga haka yace ba komai Zainab aiyiwa kaine ina kika baro kawarki Fatima Sulaiman"? Da sauri ta kalleshi cikin mamaki tace "tana gida ai basan na taho ba "ok yayi idan kin koma kice ina gaishe ta, fitowa sukai suna dan hira anan yake ce mata yana son Fati zaizo ta rakashi gidansu wai murna gurin Zainab kamar itace ta samu masoyi har jikin mota ta rakoshi Yarima na ciki yana kallon su da mamakin dama Musty ya santa a yadda yake gani kamar shakuwace mai karfi a tsakaninsu sallama sukai ta wuce shi kuma ya shiga mota suka kama hanyar gida suna cikin tafiya Yarima yace "na tambaye ka dan Allah"? Da mamaki Musty yace "Allah yasa nasani na baka amsa"kai Yarima ya jinjina yace "wancan yarinyar da kuke magana wacece ita"? Cikin zolaya Musty yace itace yarinyar da nake ce maka ina sonta"Yarima dake duba waya baisan lokacin da yace "WHAT"ba wanda yasa Musty binsa da kallon mamaki yace "menene"? "Batai bane"? Kai Yarima ya girgiza baiyi magana ba zuwa can ya kasa hakuri yace "to amma tasan kana sonta"? A yadda yai maganar saida yabama Musty dariya yace "kaifa da wasa nake maka kawarta dai dai nake so ita wannan idan kaji labarinta sai ka tausaya mata"kallonsa Yarima keyi cikin mamaki ya gaji da magana amma yana so yasan labarin nata dan haka yacewa Musty to amma banga wata alama data nuna min 'yar talaka bace"? Dariya Musty yai "kai waya fada maka ba maganar fariya ba ni na dau nauyin karatunta hatta kayan sawarta a wuya na yake tunda muka hadu da ita sunanta Zainab Umar____tsaf ya fada masa iya duk abinda ya sani game da ita shiru Yarima yai har saida Musty ya dafa shi amma bai dago ba kuma har suka je gida hakan nan ya rasa sukuni gani yake yanzu ma kila Bilki na mata abinda Musty ya fada masa.

Washe gari Zainab ta tafi sayo kayan miya kenan Aliya ta shigo gidan da magana a bakinta ko gaisawa basuyi ba ta fara fadin "Bilki me kike kallo za'a haifa miki shege a gida ki gamu da surutun mutane"cikin rashin fahimta tace "kamar ya"? Aliya taci gaba da cewa jiya nadiya na dawowa daga makaranta tace min taga Zainab ta shiga motar wani saurayi sunbar anguwar nan dama nace kila baki sani ba a matsayina na kawarki nake fada miki kisan matsayin da zaki dauka dan zainab ta fara fin karfinki"salati Bilki keyi tun dazun tace yanzu Zainab keda ciki ban sani ba bari ta dawo saita fadamin a gidan uban wanda ta dauko"jin haka yasa Aliya tace "ki dau mataki kan ni natafi sauri nake"tana fadin haka tai waje.

Babu jimawa Zainab ta dawo mikewa Bilki "tai zonan Zainab dama bin maza kike"? Cikin mmk Zainab ke kallon ta tace "wallahi tallahi karya ake min umma"mari Bilki ta dauketa dashi tana dukanta ta ko'ina tace za'ai miki karyane annamimiya dama na dade ina zargin haka kuma wallahi yau sai kin bar gidan nan inyaso sai kiji dadin karuwancin"kuka Zainab keyi sosai gashi inna batanan taje gida dakinta Bilki ta shiga ta fara cillo mata kayanta waje waje cikin kuka Zainab tace "dan Allah umma kiyi hakuri idan kika koreni ina zan tafi "? ๐Ÿ˜ญBilki data gama watso komai waje tace duk gidan uban wanda zaki ma ni bai shafeni kafin na fito daga daki kibar gidan nan dan wallahi sainai miki dukan mutuwa"jakar takardun makarantar ta kawai ta dauka ta fita tana kuka a zauren gidan ta zauna tana ciki kuka Bashir ya shigo ganin ta haka yace "masoyiyata ke da waye ubanwa ya saki kuka"? Bata kullashi ciki ya wuce jin Bilki tace "dani ce nan"Korarta nai domin tana bin maza "Bashir dake kallonta yace kuma kudina fa da kika ci"? Cikin ko in kula tace kabita ka kamota sai kazo ga daki ka fanshi kudinka"jin haka yasa Bashir juyawa da gudu yai zaure ashe itama Zainab din tajiyo dan haka a guje ta bazama Bashir daya fito hangota dayai acan nesa yasa shi kara gudunsa kafin sakan har ya cimmata ganin ya kusa da ita ta kara gudunta amma sai dayai nasarar rike hijab dinta taci mugun tuntube ta fadi kasa wani uban ihu tai ta mike tsaye zai sake riketa ta hankada shi ya fadi kafin ya tashi ta kuma zubawa a guje ko gabanta bata gani harta iso bakin titi babu zato taji mota tai sama da ita wani razanannan ihu tai ta dawo kasa a sume
Cike da rudewa mai motar ya fito wa zan gani Yarima Abdul-malik ne cikin sauri ya ciccibeta yasa ta a mota dan ya kaita asibiti ya shiga yama motar key cikin gaggawa.

๐Ÿ˜‹ Um abin yazo sabuwar duniya sabuwar rayuwa sabin yan uwa da kuma sabon muhalli ๐Ÿ˜€ ๐Ÿ˜€

Ina sonki 'yar uwata Naja'atu Musa Abubakar

Zarah musa dan adam kina rai na

Maman khaleel bani da bakin godiya a gareki saidai kawai nace ina sonki โค

*YUSRAHMS ABUBAKAR *

Mrs Al'ameen Ahmed ce

๐Ÿ’‹Everything about you is so good but one things is wrong that you are not mind.

๐Ÿ’žINDO ke ta daban ce
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
Wallahi ana tare yan uwa
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
[11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: *๐Ÿ‘‘Yarima Abdul-malik ๐Ÿ‘‘*

#Yusrah m Abubakar #

*๐Ÿ’ซANNURI WRITES
ASSOCIATION๐Ÿ’ซ*

*Umh! The parrot that speakers *

*True love never end in the world ๐ŸŒ

Ina matukar godiya a gareku masoya Allah yabar zumunci *INDO ABLA'S DA RABI'AHH may Allah help and bless you anywhere you are.

*Mrs Al'ameen Ahmed *

Banda kamar ku.
Fatima musa Abubakar
Abubakar musa Abubakar.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.