Complete Hausa Novels

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yarima_Abdulmaleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 8

*Page 6

Mikewa mama tai bayan ficewar Yarima ta shiga part din da Zainab take a bakin gado ta same ta ganin mama yasa ta sunkuyar da kai murmushi mama tai tana zama ta rike hannunta ta soma mgn "dota kinji abinda ya faru ba sai na sake yi miki bayani ba shin kin amincewa babyna zaki aure shi eh ko a'a? kada ki ji kunyata fada min gaskiyar abinda ke ranki idan baki amince ba babu mai yi miki dole kara sunkuyar da kai Zainab tai ta kasa mgn gabanta na faduwa ganin tai shiru mama dake kallonta tace "haka yana nufin baki amincewa baby ba baki sonshi"? Cikin sauri ta girgiza kai muryan ta na rawa tace "amince zan aureshi halaccin dayai min bansan dame zan saka masa ba daya wuce nai abinda ya nema yanzun zanyi masa biyayya bazan saba masa ba zai sameni mai ladabi a gareshi"rungumeta mama tai cikin jin dadi tana sa mata albarka.

Ba yadda mama batai da Yarima ba akan yaje ya samu mai martaba amma yai kirmishishi yaki zuwa ganin idan ta biye mai wankin hula zai kaisu dare yasa ita da dady sukaje gurin mai martaba ba wani boye boye suka fada masa komai mai martaba da shima haushin angama mgn da iyayen Hajara yasa yace "to meyasa tun wuri baizo ya fada min ba gashi yanzu an karba masa auren wata to saidai ya hada su duka biyun ya aura ya tafi dasu sbd bazai yiwu mu mayar musu da magana ba "amincewa sukai duk da mama bata ji dadin hakan ba to amma ba yadda zasuyi suna nan zaune ya shigo fuskarnan a matukar murtuke dan ya kasa boye damuwarsa mai martaba dake kallon shi yace "Muhammad kayi hakuri nasan zakaji babu dadi amma kasan mu idan munyi alkawari bama canjawa ina so ka cire damuwar komai a ranka in Allah ya yarda zakaga riba da nasara a gabanka"numfashi ya sauke ba tare dayai mgn ba har kuwa suka bar gurin mai martaba ba wanda yaji muryar sa suna shiga palor mama ta kalleshi tana cewa "baby me yasa bakaje gurin mai martaba kayi masa bayani ba gashi yanzu ka jawa kanka auren mata biyu dan me kaki zuwa tun ranar da abin ya faru"? Shiru yai babu amsa dan shi kadai yasan abinda zuciyarsa ta shirya masa.

Yau saura kwana goma Yarima ya bar kasar mai martaba kuma yace bai amince ba ya gaji da ganinsa ba aure sai dai ayi bikin cikin kwana goman din daya rage ya tafi dasu sbd idan ya tafi ba'a san ranar dawowarsa ba Yarima ya firgita lokacin daya ji wannan mgn amma sai ya dake bai cewa kowa komai ba har saida ya basu mmk musamman daya nuna rashin damuwarsa akan mata biyun dazai aura Yaha kan dataji labarin wai Yarima zai auri Zainab yar karamar hauka tai dan gani take bazatai nasara ba Zainab tamkar barazana ce a rayuwar ta musamman dataji ance iya na Zainab din za'a daura ita Hajara saiya dawo tunda karatu take babu kunya taje gaban mai martaba da kukan ta tace a daura harda Hajara karatu baifi aure ba duk sanda suka dawo taci gaba mai martaba yayi mmk ganin irin kukan da take amma sai yace mata shikenan za'a daura farin ciki kamar ta mike tayi rawa a gaban sa.

Yarima baiso mai martaba ya amincewa Yaha ba amma sai yai burus da zancen.

musamman mama ta dauko mai gyaran jiki ake kula da Zainab tayi kyau tai fresh abinta har mmk take idan taje gaban mirror kamar ba ita ba.

Yaha ce zaune a palor kamar a mafarki taga Yarima ya shigo ba tare daya kulata ba yai hanyar dakin Hajara da sauri Yaha ta mike tana cewa "malam me zakayo anan kayi ajiya ne"? Batare daya juyo ba yace "niko nai ajiye tunda gurin mata ta nazo bai shafe kiba idan kuma so kike ki ganewa idon ki abinda yafi karfinki saiki shigo"yana fadin haka ya bude kofa ya shiga takaicine ya kama Yaha to uban me zaiyiwa Hajaran da har zata shiga ta tuno abinda daya fada mata tajuya zuwa palo tana jiran fitowar sa, Hajara dake kwance cikin mmk ta mike zaune tana zaro ido waje tace "lafiya "? Harde hannu yai yana kallonta yace "lfy nazo Duba lafiyar mata nane ko tana cikin farin ciki "da sabon mmk ta kuma zuba masa ido cikin jin dadi anya kuwa ba mafarki take ba Abdul-malik ne yazo duba ko tana lfy katse shirun yai da cewa bani number abbanki zan kira shi mu gaisa a matsayinsa na suruki na baban mata ta kuma uwar 'ya'ya na ya kare maganar da dage mata gira alamar ita yake jira jiki na rawa ta dauko waya tana cewa "gashi dauki"hade rai yai "fado min "fada masa tai sannan yace "tnk my wife take care good night "bai saurari wani abu daga gare ta ba yai waje dan bukatar sa ta biya ko kafin Hajara ta fito har ya fice Yaha ce ta tare ta "ke lfy ina zakije "? Ihu Hajara tai tana rungumeta tace "umma ki tayani murna Abdul-malik da kansa yanzu ya kira ni da matarsa wallahi umma ya fara sona"cikin mmk Yaha ke kallon ta amma batai mgn ba dan ita hankalinta bai kwanta da zuwansa ba gani take kamar wani abu yake shiryawa.

Ranar alhamis masarauta ta cika tab da baki na sauran wasu masarautun Yaha tayi mamakin rashin ganin dangin su na masarautar maidiguri amma data kira abban Hajara sai yace mata duk gobe zasu zo kafin ayi daurin aure sai sannan hankalinta ya kwanta.

Yaha na zaune taga wata budurwa ta shigo tana karewa part din kallo kamar mai duban tsafta mikewa tai tana kallonta tace "wace ke me kike nema anan ko kinyi batan kai ne idan ma makancewa kikai to maza ki saitawa kanki hanya ba nan ne part din da ake bikin ba har kike wa mutane kallon banza daga ina kika fito"? Dan murmushi tai tana duban yaha tace "ni bakuwa ce munzo biki daga masarautar Bauchi sunana Salmah part din Ibrahim Abban Mahmud nake nema"cikin faduwar gaba Yaha ta kuma bude ido a kanta tace "nan ne lfy"? Kai Salmah ta girgiza ba tare datai mgn ba ta juya ta fice a part din kasa zama Yaha tai tana tunanin ita kuma wannan ubanwa ya aiko ta amma tafi zargin Amina ce (mama) tana cikin zagaya palo Abba ya shigo tararsa tai da cewa "Ibrahim wacce yarinyar daka turo tazo ta min wulakanci"? Ko kallon ta Abba baiyi ba ya wuce da gudu tasha gabansa tana huci tace "me kake boyemin wacce ita "? Kallo mai ma'ana da yawa Abba yai mata kafin yace "i think ta fada miki sunanta Salmah daga masarautar Bauchi right nine na turo ta domin baki zo da part din daga masarautar kuba kuma kada ki sake ki rufe kofa dan anan tace min zasu kwana "wata ashar ta saki batare data shirya ba tahau masifar me yake nufi da haka amma ko ta kanta baibi ba ya fice abinsa haka ta karaci kumfan baki ita kadai tai shiru.

Yarima yana zaune Musty ya kira shi cikin tashin hankali ya soma mgn "Abdul-malik me nake gani wacce wannan yarinyar da zaka aura dazu ina zaune Aunty ta turo min photon wedding dinku kamar Zainab nake gani wai dama tana gunka amma sbd rashin mutunci kaki ka sanar dani ka barni ina ta shan wahalar nemanta please ka bani amsa"? Murmushi Yarima yai yana cewa "amma alamu sun nuna kanka baya ja wannan zaka kalla kace wata zee dinka ko ka fara makancewa ne kalli sunanta mana ba Malika Ibrahim ka gani ba suna nawa Zainab din taka take amfani dashi"? Kara kure photon Musty yai da kallo wallahi abinda kawai wannan zata fi Zainab haske da kiba sai yanayin hutu, sake kallon Yarima yai cikin marairaicewa yace "please Abdul-malik na roke ka idan itace ka fada min na daina shan wuyar nemanta"wata harara ya samu maimakon amsa sannan yace masa "zakasan ba ita bace sai ranar da kuka hadu, malam ina da baki please zan koma gurinsu good night"bai bari Musty yace komai ba ya kashe camerar da yake video call ne suke Musty kan ji yake tamkar yai tsuntsuwa ya dawo Nigeria kodan ya gani da idonsa cewa ba Zainab bace dan ya kasa yarda gashi ko ranar tahowa bai saka ba haka nan dole ya hakura.

Hhhhhhhh rana fa bata karya ina masoya ku fito mu kwashi shoki dan abin yazo inji mai fadar aurensa yace gobene fa.

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

#Yusrah Musa Abubakar

Ina INDO ku matso kusa yau zamuje Abuja diban gara ABLA'S hanzar ta lalala ina RABI'AHH ai tafiyar bazata yuwu ba idan babu ke, sai kunzo mukan mun dau katuwar gana masgon mu munyi gaba dan ba jira ๐Ÿƒโ€โ™€๏ธkar muje ayi ba mu ๐Ÿ˜œ.

Washe gari da yanayi mai kyau gidan sarauta ya tashi kowa murna yake musamman bangaren mai martaba dasu mama abin bana magana bane sai wanda ya gani dan nikan na gani amman bazan fada ba.

Saida akai sallar juma'a sannan aka fara hidimar daura auren daya samu halattar manyan mutane masu martaba saida komai ya kammala Yarima ya tashi daga cikin abokansa ya matsa gurin mai martaba cikin rada yace "kakana kabar dayan daurin auren munyi magana da babanta ya amince tunda wata hudu kawai zanyi idan na dawo sai ayi na 'yar sa inaga zaifi da ace tana matar aure kuma tana yawon zuwa makaranta ba'a gidan miji take ba, amma me kace kakana"? Kai mai martaba ya jinjina cikin gamsuwa yace "kwarai gaskiyar ka kayi tunani mai kyau haka shine dai dai Allah ya maka albarka"wani irin murmushi Yarima yai ganin yaci nasara ta ko'ina dady tun dazu yana hankalce dashi ganin bayan sun gama maganar sai murmushi yake yasa ya jashi gefe yana masa kallon tuhuma yace "kai me ka fadawa mai martaba? dan haka kawai naji ban yarda dakai ba"? Cikin yar shagwaba baya ko kunyar mutane ya wani narke a jikin dady yana cewa "nifa babu abinda nace masa kawai munyi magana ne "kallonsa dady yai "to daga min jiki karka karasa ni kasan na fara tsufa"yar dariya Yarima yai yana kallon sa bai kara mgn ba ya sake shi yana komawa gurin abokan shi suka dau hanyar gida.

Cikin tashin hankali Yaha ta shiga part din Yarima ganin sa a palor yasa cikin tsawa tace "kai Abdul-malik! "Da mamaki Yarima ya dago yana kallonta cikin bacin rai ta soma mgn "wannan wanne irin rashin mutunci ne kayi dan kawai ka bakanta min shine sai da kasan yadda kai aka fasa daura na Hajara dan mugunta harda wani saika dawo wallahi baka isa ba azzalumi kawai" ta karasa mgnr kamar zatai kuka har lokacin kallonta yake cikin natsuwar tsokana yace "haba umma ki rika shan ruwan sanyi zaki sawa kanki ciwon kai da wannan ihun da kike ga guri zauna muyi mgn mene abin daga hankali aiba cewa nai bazan aure ta ba"wani irin kallon takaici Yaha take binsa dashi jin abinda yake fada tace "nice nake ihun kenan ka mayar dani kare kome "? Dan murmushi yai yana cewa a'a ko daya wa? Ni na isa nace miki kare amma bari na gyara miki ba kare zakice ba sai dai kice karya tunda ke mace ce kin gane bazanyi abinda zai takura ni ba na rufe wannan layin kamar yadda kofa ta riga ta kulle kuma dakin da matukar duhu akwatin sirrin na tantame shi da igiya bamai ganin wani abu daga cikin sa har abada "tunda ya fara magana Yaha ke kallon sa da mmk dan bata taba ganin sa yayi doguwar mgn ba sai yau gashi ya caccaka mata mgn kuma ya fuske kamar bai fadi komai ba wani zazzafan numfashi take fitarwa mai cike da kuna dakyar tace "me kake nufi ban gane ma'anar wannan sakalkalen maganar da kake min ba wai kai me kadau kanka? har yaushe ka girma? waye kai? Kai tsaye Yarima yace mata "I'm if you know sannan i'm not if you doesn't know ina fatan yanzu kin gane to zaki iya fecewa "wata tsawa ta daka wanda tasa shi saurin toshe kunne yana mikewa ya rike hannunta ya fara tafiya da ita saida suka fito a part dinshi ta fara kokarin kwace hannunta dan juyawa yai yana kallonta yace "idan kikai haka a gaban bayinki kiyi fada da danki mutuncinki zai zube dan haka ki nutsu"ci gaba yai da tafiya da ita kamar wata yarinya.

Tab Yaha kam ko gabanta bata gani sbd bacin rai har gaban mai martaba ya kaita sannan ya sakar mata hannu da mmk kowa ke kallon su mai martaba ne ya fara magana "Muhammad daga ina haka ina fatan lfy"? Kai Yarima ya jinjina lfy kakana dama umma ce taje min tayani murna taimin addu'ar dana ji dadinta shine nace nima bari na kaita gurin babban abokina ta karbi tata addu'ar "murmushi mai martaba yai "hake Muhammad naji dadi kuwa Allah ya miki albarka Yahanasu"sbd bakin ciki Yaha durkusawa tai a gun tana fashewa da kuka dan ta kasa rike shi da mmk mai martaba yace "a'a lafiya kuma"? Yarima dake murmushi yace "ai kakana farin cikin addu'ar da kai mata ne yasa ta kuka tasan albarka zatai mata zobe a jikinta murnarta ta kasa rikewa gaskiya umma ta nuna jin dadinta akan auren nan kakana a kara bata wata albarkar ko tasamu tadan tsatso naga duk ta rame sai kace itace amaryar"dakuwa hajiya tai masa tana cewa "gidan ku ba ummarka bace ka maida ita kakar ka "bai sake mgn ba ya juya yabar palon yana murmushi ko ba komai gaba zata kiyayi rike girman ta dan hausawa sunyi karin magana cewa "any old man that don't fear to ride on donkey, donkey will not fear to throw the old man to the ground".

Yana komawa part din sa ko zama baiyi ba Musty ya kira shi kin dagawa yai saida ta katse sannan yabi kiran nasa Musty na dagawa cikin tsokana Yarima yace "malam wai meye ka dame ni ko yaudin ma kira na kai akan na fito maka da Zainab dinka sbd ka mayar dani dan yankan kai ko"?nidai shawara zan baka ka daina wahalar da kanka ba samun ta zakai ba dan kila ita ta shafe babinka a rayuwa kuma bari kaji idan ka sake kira na kana tuhuma ta akan batan Zainab zansa a kulle min kai aita dimar ka saika fadi inda na kaita"cikin haushi Musty yace prince, prince kasan Allah ka kiyaye ni ubawa zakasa ya kulle ni kasan yadda nake jin yarinyar nan a raina kuwa? kasan irin matsayin dana dauke ta da zakace haka"? Gyara zama yarima yai "na sani mana zai wuce malami da dalibarsa, kuma naji ka dage sai prince kake kira fatan ba dani kake ba? dan ni bashi bane"Musty yace "inji ubanwa kai bashi bane "yarima dake duba wasu kaya yace "ok to fada min mene ma'anar prince "? Musty ya ci gaba da cewa "a boy of royal birth, the son of a king like you "tabe baki Yarima yai "malam ba shi bane just kira ni Abdul-malik Yusuf dina shine sunana, kuma nidai ina sake tabbatar maka da cewa kai da Zainab kunyi hannun riga ba lallai ka sake ganin ta ba "yana kaiwa nan ya datse kiran tsaki Musty yai "wallahi Abdul-malik anyi dan iskan mutum in kaga na hakura da neman Zainab to saidai in bana numfashi.

Zaune duka familyn suke a gaban mai martaba yana musu nasiha da addu'ar fatan alkairi sannan yace idan Hajara ta gama karatu lokacin ya dawo a daura, Yaha kan ta cika tayi dam so take tayi mgn ta kasa sai juya hannu take ta matsu taga Yarima baya duniya gashi yazo ya auri mara asali yar tsuntuwa cikin dakewa tace "ranka ya dade Yarima dan dangi ne iyaye da kakanu me zamu cewa 'yayan su nan gaba idan suka taso akace musu uwarsu bata da dangi yar tsuntuwa c_____bata karasa ba Abba ya daka mata tsawa tai shiru wanda shi kanshi mai martaba yaji haushin mgnr data fada amma sai yai burus da ita ya kalli sauran yan palon yace "Yahanasu kinyi mgn mai kyau wacce za'ai duba a cikin ta amma ina so ki sani ko nan gaba idan aka tambaye ki waye mahaifin Zainab kice Yusuf ne mahaifiyar ta kuma kice Amina ce idan yayun ta ake nema kice Abdul-malik da Mahmud idan kanin mahaifinta akazo nema ga Ibrahim kakanu kuma da kike mgn akai mune ni da Aisha idan kuma gaba daya danginta ake nema kice mune ina fatan yanzu kan kin fahimta"shiru Yaha tai kanta ne kawai yadau caji ta rasa wanne irin so sukewa Zainab a gidan nan babu wanda ya sake mgn Abba ya rufe taro da addu'a sannan kowa ya mike ya fita da sauri Hajiya ta biyo Yarima tana cewa "kai naji ana cewa ranar monday zaku tafi ka tabbata ka bar mana saidar kimar matar ka idan kuma ba haka ba Wallahi sai ranar da kayi da kubar masarautar nan kaji na fada maka "juyawa yai yana kallonta yace "kinsan Allah ki fita idona ba ruwanki da wannan shafin ganin dama tane "harararsa tai sannu baba Yakubu baka isa ba to sai kayi ko ka hakura da tafiyar, idan kuma kaine baka da lafiya fada min inji sai a nemo maka magani"? "tafiya ya farayi yana cewa "eh bani da lafiya"Hajiya dake dariya tace "karya kake ".

Mama ce zaune Zainab na gaban ta tasha kwalliya da kayan ado iri daban daban hadi take mata tana sha kuma tana mata nasiha da hakuri domin tunda Yaha tace bata da dangi take kuka ta rasa wacce kalar rayuwa ta tsinci kanta a ciki ace duka bangare biyun bakasan ko daya ba suna nan jakadiya tai sallama tana cewa "ranki ya dade inji Hajiya lokaci yayi"wani irin faduwa gaban Zainab yai wanda dama kukanta a kusa yake sai kawai taci gaba dayin abinta mikar ta mama tai tana rike hannunta tace "kiyi hakuri dota muje dama nayi alkawari ko ba baby kika aura ba nice zan raka ki har dakin mijin ki "tafe suke da masu take musu baya har part din yarima ta kai ta kuma yi mata nasiha sannan ta mata sai da safe ta fita tana murmushi.

Shiru Zainab ta zauna tana tunanin ta inda zata fara neman dangin ta kodan gorin da ake mata zata tsaya tsayin daka ta samo su ko ta samu salama a rayuwar ta.

Jin karar bude kofa yasa ta dago da sauri Yarima ne ya fito daga wanka dauke kanta tai jikin ta na daukar tsuma ba tare daya kalleta ba yace "u'r welcome"shiru tai jikin ta na tsananta rawa batasan me yake ba domin kanta a sunkuye yake sai jitai an mikar da ita tsaye yana cire mata alkabbar jikinta aiko kuka ta saki harda shashsheka Yarima dake kallon ta yace "what "? Kasa mgn tai sai kokarin tsayar da kukan da take gira ya dage yana mata wani irin kallo dake mugun firgita ta cikin wani irin yanayi yace "kar ki damu da mgnr Hajiya indai kika biye ma wannan tsohuwar ba zaki abin arziki ba ki kwantar da hankalinki babu wanda zaiga first night din mu sai munbar kasar jeki dauro alwala zamuyi nafila"sakin ta yai yana fita daga dakin cikin sauri ta shiga toilet din har tayo alwalar ta fito bai dawo ba .

Zama tai cikin minti biyu ya dawo tare da wata tsararriyar abayat mai kyau da gyalen ta ya bata ta saka yaja musu sallah cikin nutsuwa da kyakkyawar addu'a mai shiga rai kafin ya mike yana cewa "kizo ga gado ki kwanta good night" ya haye abinsa yana jan bargo duk da haka kin tashi tai saida ta dade sannan ta mike tana cire abayar ta hau gadon kwanciya tai a bayan sa tana kallon gashin dake kwance jikin sa dan shi mutum ne mai ni'imar gashi dan taba kwanceccen gashin kansa tai ganin yadan motsa da sauri ta janye hannunta cikin fargaba
juyowa yai yana murmushi yace "yada tashi kuma madam ina cikin bacci na "dan hade rai tai batai mgn ba shima hade nasa ran yai yana cewa "ni da kika tsokana ban hade miki rai ba saike to bari kiga wani abu"wutar dakin ya kashe yana matso da ita kusa dashi.

Abin yayi kyau yaukan na gama typing see you next time.

Taku har kullum

*Mrs Al'ameen Ahmed *
[11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: ๐Ÿ‘‘Yarima Abdul-malik ๐Ÿ‘‘

๐Ÿ’ซANNURI WRITING ASSOCIATION ๐Ÿ’ซ

Dedicated to
Zarah Musa
Safiyya Aliyu

#YUSRAHMS ABUBAKAR

ANNURI WRITING ASSOCIATION i know everything about you is so good but one things is wrong that you are not mind wannan haka yake ana matukar tare.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.