Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yarima_Abdulmaleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 8
Part din mama ya nufa dai dai zai shiga yaji Zainab na waya dan dakatawa yai jin tace "ina jinka nufin ka wai kazo gidanmu, tab a'a gaskiya zan dai fada maka amma ba yanzu ba saina tambayi mamana da dadyna
idan sun amince zan sanar dakai sai kaz______jitai an zare wayar afirgice ta dago ganin wanda batai zato ba yasata rudewa ga wani abu da take hangowa cikin idanunsa da batasan me zata kira shi ba tsawa ya daka mata cewa da ubanwa take mgn shiru tai mama dake bedroom batasan meyake faruwa ba jin karar Zainab yasa ta fito da gudu da mmk take kallon Zainab datai kneel down a gaban Yarima tana kuka shi kuma yana tsaye ya zuba mata ido karasowa mama tai tana daga zainab din cikin mamaki tace "baby lafiya? meya faru? Idansa nakan Zainab din yace "yaushe wannan yarinyar ta fara hira da samari cikin wayarki a ina ta sansu?"? Da sabon mmk mama tace "Zainab din"? Bai sake magana ba ya juya ya fita a part lallashinta mama tai sannan ta kama hannunta suka shiga ciki.
Washe gari suna zaune ana firar yaushe gamo su Abba sun dawo mai martaba ya kalli Yarima yana cewa "Muhammad ya kamata ace yanzun kayi aure kana da iyali kaima ko ba haka ba, kaga aure shine darajar kowanne mutum ya kamata kayi"sunkuyar dakai Yarima yai baiyi mgn ba alamar bai shirya ba mmk ne ya kama mai martaba amma sai yace "to shikenan Muhammad tashi kaje"mikewa yai yana fita Yaha tai gyaran murya tace "ranka ya dade ai wannan mai sauki ne Hajara ta dade tana sonshi saboda shi ta dawo nan da zama ta jona karatunta ta dade tana cemin na fada nace mata a'a".
Shiru palon ya dauka zuwa can mai martaba yace "kai Yusuf ya kake gani domin danka ne kaine mahaifinsa"? Cikin ladabi dady yace "a'a duk hukuncin dakayanke dai dai ne kai da kaya ai duk mallakar wuya ne"zuciyar mama tafasa take tun lokacin da Yaha ta fara mgn tasan akwai wani abu data kulla a cikin wannan abin Abba kam cewa yai "a'a a bari tukuna aji ta bakinsa idan ya amince shikenan "karaf Yaha tace "to shiyai kansa duk umarnin da aka bashi dole zaibi"mama so take tayi magana ta kasa mai martaba yace "shikenan zamuje medigurin in sha Allahu" Abba kan bai amince ba ya kuma cewa "gaskiya ya kamata a fara tambayar_____ tarar numfashinsa Yaha tai "ya kake jada maganar mai martaba ai ya gama yanke hukunci" tana fadin haka ta tashi ta fice a palon tana shiga part dinta ta sheke da dariya tana cewa "lokacin ki ya fara Yaha wallahi Abdul-malik sai na mayar dakai gawa.
Mama na shiga palon ta taga Yarima a zaune alamar yayi nisa cikin tunani dafa shi tai ya dago ganin mama ce yashi rungumeta jin zuciyarsa kamar zata fito waje cikin kwantar masa da hankali mama tace "baby kayi hakuri in Allah ya yarda abu mara kyau bazai taba samun ka ba kaga yanzu fitowa ta daga palon Mai martaba yace zasuje maidiguri a nema maka auren Hajara ni kuma wallahi harga Allah yarinyar nan batai min ba ko kadan".
Zabura Yarima yai jin abinda maman tace wai shi za'a aurawa waccan mahaukaciyar yarinyar to ba gara ya mutu baiyi aure ba wayar dake hannunsa yai wurgi da ita cikin sakan ya burkicewa mama shigowar dady kenan ganin abinda yake faruwa da sauri ya karaso yana tambayar lfy maimakon ya bashi amsa sai yai baya luuuuu zai fadi cikin sauri dady ya tare shi har ya suma cikin gaggawa mama ta debo ruwa suka hau shafa masa Zainab na gefe tana kallo sauke ajiyan zuciya yai yana bude idonsa sai kuma ya sake rufewa girgiza shi dady yai amma ya kara suma dan haka yaci gaba da shafa masa ruwan har ya samu ya farfado kalmar farko daya ambata shine "Zainab ke nake so ba wata ba kada ki bari wani ya shiga tsakanin mu"shiru sukai jin abinda yake fada Zainab kan da sauri tabar gurin cikin faduwar gaba kallon dady mama tai sai kawai sukai murmushi a tare dady yace "tunda haka ne da kansa zaije ya fadawa mai martaba ga wacce yake so ba yazo yana suma ba "dariya sukai dai dai lokacin daya bude idonsa ya tashi zaune ganin duk jikinsa ruwa yasa yace "lafiya "? Mama tace "kai zamu tambaya lafiya kazo harda suma"cikin mmk ya kalleta "suma dai "? Dady dake masa dariya tun dazu yace "babana karka tsaya bata lokaci kaje ka samu mai martaba da kanka kace ga wacce kake so zai fahimceka tunda abokin kane "shiru Yarima yai bayan ya gama tuna abida ya faru yace "nifa bance inason wata ba"wani kallo dady ya masa yana cewa "naga alama tashi kaje tunda baka ce kana son wata ba muma ai bakaji munce kana son wata ba "mama data bishi da kallo tace baby Allah ya shirye ka bata fuska yai ya fita a palon ko takalmi bai dauka ba haka ya tafi part dinshi.
Hhhhh wasa ne
Gaisuwa dai maman khaleepha Allah ya kara zumunci.
INDO ina godiya sosai Allah ya barmu tare.
ABLA'S ke ta daban ce.
RABI'AHH kina raina har bansan yadda zance ba.
MRS TSARI wannan sai Naja'atu Musa Abubakar.
#
##
###
####
#####
#YUSRAHMS ABUBAKAR #
Mrs Al'ameen Ahmed ce.
[11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: (*() *) (*()*) 📲Typing
👑YARIMA ABDUL-MALIK 👑
💫ANNURI WRITING ASSOCIATION💫
Dedicated to
Safiyya Aliyu
&
Zarah Musa
#YUSRAHMS ABUBAKAR
Moral lesson
If people care for you, you also show care for them.
MANZON ALLAH (S*A*W)
You are unique, the first and the last, no success without you, you are the mirror of life, you are everything, you are the answer to every question, you have no limit YA RASULULLAH.