Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 2.txt
Chapter 12 of 52
*_part 2_*
(littafi na biyu📕)
1⃣1⃣
A tsakkiyar falon yatsaya, yanamai binsa da kallo daki-daki, komai ya birgesa da k'ayatar dashi, gawani sassanyan k'amshi Na tashi, Wanda akasan duk gidan amarya dashi, yadire ledojin hannunsa Wanda shima baisan miye acikinsuba, Dan youseef ne yabashi.
Rasa d'akin dazai dosa yayi, baisan ainahin d'akin da matar tasa takeba, yay shiru yana nazarin d'akuna ukku dake cikin corridor d'in, zuciyarsace tafi karkata dana k'arshe, cigaba yayi datakawa ahankali, kaikace yana tsoron Isa ga d'akinne. Harya k'arasa jikin k'ofar.
Zuciyarsa tashiga harbawa da sauri-da sauri, shikam ba jarumi baneba awannan ga6ar, zai iya rantsuwa baita6a kasancewa dawata mace daba muharramar saba Na tsawon minti talatin, dagashi sai ita, saidai abokan aiki, suma basukad'aiba gaskiya, dolene kasamu akwai wani taredasu.
Cikin rinmtse ido yamurd'a handle d'in k'ofar yashiga, bashida za6in daya wuce hakan, musamman idan yatuna da lectures d'in malamai data gudana a wajen waleemar auren nasa.
Sallama yayi amma babu amsa.
Jikin Aysha ne yafara rawa, danjin muryar Wanda batayi zaton ganiba a wannan lokacin, takuma cusa kanta acikin filillukan da aka k'awata kwalliyar gadon dasu, gaba d'aya jitai yau soyayyar datake masa tagudu, sai d'unbin tsoro da firgici dasuka maye gurbinsa.
Cikin takun nutsuwarsa da jarumtar data zame masa halittar jininsa yak'araso gaban gadon. suduka zuciyoyinsune suka k'ara karfin gudun harbawa, saboda kusanci dasuka samu dajuna.
Ya d'an lumshe idanunsa, tareda kauda kai daga kallonta, yama rasa ta'ina zai fara?.
Jinsa tsaye akanta yakuma karyar da jarumtarsa, rauni da d'unbin fargabane kawai keta gudu da bugawar zuciyarta, tsoronta yakuma hauhawar farashi lokacin dataji ya khaleel yazauna abakin gadon, kusa gab da k'afafunta, da'ace zata motsama dolene koyaya ta ta6ashi.
Wata jarumtace tazo masa alokacin daya tuna da wadda yake tare. Cikin muryarnan tasa, maikad'a hanjin marajjin magana yace, "k! tashi mana".
Shiru Aysha batako motsaba.
Yakuma fad'in "bak'ya jinane!!".
Yanda yay maganar ad'an tsawace, amma cikin sanyin murya yasa Ayshan tashi zaune, idanunta nacigaba da zubar da hawaye, tagefen ido tasaci kallonsa, tsoro yasake kamata saboda cin karo da fuskarsa a d'inke, kamar yanda tasanta.
Shima satar kallon nata yakeyi, yabi zara-zaran yatsun hannunta da kallo, lallen yamata k'yau sosai, daga bak'in har jan, yanda take hawaye saita bashi dariya, yau kam babu bakin rashin kunya, tausayinta yad'anji aransa, dan masu iya magana kance *aure yak'in mata*, amma yasan halin kayarsa, zumace saida wuta.
Mik'ewa yayi tsaye yana fad'in tashi muje.
Saida yakai bakin k'ofar sannan Aysha tamik'e da k'yar, bata sameshi a falonba, saikawai tasamu kujera ta zauna, jitake gabad'aya auren yafita aranta.
Fitowarsace takatse mata tunaninta, saiyanzu tama kwalliyar tasa kallon tsaf, kayan d'azunne ajikinsa, amma yanzu yaje yacire babbar rigar, sai wando da riga y'ar ciki wadda dakad'an tawuce d'uwawunsa, yakuma cire hularma, sai kwantaccen gashinsa, Wanda baicika yawaba saboda askewa dayakeyi, hakama sajensa kwance yake luf, da'alama yad'an kwana biyu bai aske sajen nashiba, yasha gyaran fuska, wadda tafito da ainahin chocolate color d'insa, ya khaleel k'yak'yk'yawane, amma bazaka cedashi k'yawu ajin k'arsheba, komai nasa yana tsaka tsaki, idonsanefa dai ALLAH yabashi masha ALLAH, Dan manyane tubarkallah, ko mace sai haka wajen k'yawun idanu da girma, gasu farare tas, idan ransa ya6acine kawai zakaga sunyi jaa da k'ara fitowa, yanada k'yawun mai k'ayatarwa, Wanda zamu iya cewa kwarjininsane ya kuma fiddo taswurar k'yawun haibar tasa.
Batasan yak'araso falonba, saimaganarsa taji yana fad'in "k tashi ki d'auka min filet da cup".
Jikin Aysha amace tamik'e, saidai batasan inane kichin d'inba, amma tayi tsaye takasa tanbamayarsa.
Tsaf yalura da nufinta, amma saiya shareta yad'auki remote yana k'ok'arin kunna TV.
‘‘ya khaleel inane kichin d'in?”.
Shiru yamata, saida yamula Dan kansa sannan yanuna mata da hannu.
Kichin d'in yayima Aysha k'yau sosai, komai atsare gwanin sha'awa, kala biyune kawai a kichin d'in, jaa dakuma Fari, kamar yanda falonta yake, ta d'auki filet da cup tad'ora bisa wani madaidaicin tire tafita.
Yana zaune inda tabarsa, gabansa taje ta ajiye, ya nuna mata ledojin batareda yayi maganaba.
Itama bata tankaba tasakko, harzata fara bud'e ledojin yasaka hannu yazare gyalen dake lulu6e da jikinta, saboda kid'ima saida Aysha tajuyo ta kallesa, harara ya sakar mata, tayi azamar janye idanunta da kwallah suka fara taruwa aciki.
Ta d'auka tabud'e, ledar farko kayan fruit ne aciki, d'ayar kuma gasassun kaji guda hud'u, saikuma d'ayar ledar fresh milk ne aciki.
Kaza d'aya tasaka a filet d'in tanata tashin k'amshi, tabud'e fresh milk tazuba a cup d'in.
Tad'ago ido ta kalleshi, ganin idonshi akanta, ta janye nata, tanaso tacemasa tazuba amma takasa magana.
“Shin waike kinzama kurmane yau?”.
Kanta ta girgiza masa. Yace, "dabakinki nakeson ki amsa mini, dama Ashe ked'in mara kunyar k'aryace?".
Itadai bata kulashiba tace, " nazuba maka".
“kin zuba mana dai, ko kina nufin wad'annan kwala-kwalan idanun naki ba yunwa baceba?”.
Shiru tayi bata tanka masaba, aranta tace, “dayakema talle bazatama Audi goriba, kaima kanada kwala-kwalan idanun, komawa tayi jikin kujera tayi shiru.
Shima baisake cewa komaiba yasakko k'asan yazauna kusada ita, yunwa yakeji, rabonsa da abinci tun breakfast dayayi a Kano, fresh milk yad'auka yafarasha da bismillah.
Saida yasha kusan rabin kofin sannan yacire tareda d'ora kofin kan bakin Aysha, d'ago idanu tayi suka had'a ido, takuma marairaice fuska ALLAH ya khaleel nak'oshi.
Eh nasan kin k'oshi, nima aibance baki k'oshinba, ina jaddada sunnar manzon ALLAH ne (SAW), Dan haka bismillah.
Akunyace Aysha tabud'e baki ta kar6a, baicire kofinba daga baki ta saida yaga ta shanye.
Namanma koda yaci saiya kai baki ta, danma karta masa gardama saiya kuma had'e fuska, duk kunya ta dabaibaye Aysha, amma babu yanda zatayi, dole taita kar6a, ganin zaisata amai tace wlhy nak'oshi ya khaleel.
Daina bata yayi yana fad'in gulmammiya, dama kinaso kiketa wani dojewa, amare natsoron cin kazar amarci amma ke kincinye guda d'aya sukutum, ammadai kinji kunya gaskiya.
Aysha batasan sanda murmushi ya su6uce mataba, can k'asan ranta kuma tanajin nishad'i, ya khaleel ya ciyar da ita da hannunsa, batayi zaton samunsa da sauk'i hakaba, ganin halin ko'in kula dayake nuna mata kafin auren Nasu, azatonta kafin auren zata had'a watama bata ganshiba wlhy.
Wringing d'in wayarsane takatse tunanin Aysha, shima cikin matuk'ar mamaki yace, "wanene a darennan haka? Yay maganar yana ciro wayar daga aljihun rigarsa, Momy kuma? to ALLAH yasa dai lafiya? Ya kalli agogon dake tsintsiyar hannunsa sannan yad'aga wayar.
Maimakon muryar Momy saiyaji ta Anty Zuwairah.
‘Khaleel kana gida kuwa?’ tafad'a akid'ime.
“eh ina gida, amma lfy a darennan?”.
Babu lafiya khaleel, momyce keta murkususu harda suma cikinta Na ciwo.......
Da sauri yamik'e yana fad'in, "subahanallah, ganina zuwa", baijira amsartaba ya yanke wayar. Amma zuciyarsa Na mamaki, ganin babu dad'ewa da dawowarau wajen dinner. koda yake ba'a mamaki da ikon ALLAH, saima ta iya mutuwa, wannan kad'an daga ikonsane.
Aysha tace, “lafiya kuwa?”.
“momyce babu lafiya, bara nadubo jikin Nata ”.
To kawai Aysha tace, tareda fad'in, “ALLAH yabata lafiya”.
Yana tafiya yana amsawa.
Kokad'an batun baikama hankalin Ayshaba, tabbas tasan makircine, saidai tana tsoron kullin nasu.
Da sauri tamik'e tashiga bedroom d'inta, wayarta tad'auka takira Anty meerah.
"Lil sholy lfy kuwa da daddarennan? Ina kikabar mijin naki?".
Yafita wajen Momy.
Kamarya sholy?.
Aysha ta zayyane mata komai tana hawaye, tak'are maganar da fad'in Anty meerah wlhy inajin tsoro".
'Dolene Aysha, Dan tabbas akwai abinda suka shirya, su Anty glo shaid'anune, nasan sun sanarma surukarki komai, yanzu ki kulle ko ina, kuma ki ajiye waya a hannunki, dakinji abinda bai gamshekiba ki kira ya khaleel ki sanar masa'.
" Anty meerah banida number sa".
'Babu damuwa, bara nad'auka a wayar dadyn Raudat Na turo miki, ALLAH yasa da ita yake aiki, dannaga waya d'ayace a hannunsa k'aramar Nokia'.
To amin, baradai Na turo miki.
Babu dad'ewa Anty meerah taturo mata number ya khaleel, gaba d'aya a tsorace take, duk motsin dataji saita k'ara k'ank'ame jikinta tana addu'ar daduk tazo bakinta, tun tana saran shigowarsa harta fara fidda rai, har karfe hud'un asuba tayi, iskar asuba datake busowa ta taimaka barci 6arawo ya sace Aysha batareda ta shiryaba.
Ya khaleel kam tunda yafita da sassarfe ya isa 6angaren hajia babba, cikin halin ciwo sosai ya isketa, yazauna abakin gadon kusada Anty Shukurah, suna d'akin itada Anty zuwairah da Anty glo da kubrah.
Hajia babba tarik'e hannun ya khaleel tana fad'in zan mutu Ibraheem.
"Ba zaki mutuba Momy". 'Anty zuwairah why not asanarma Dady mutafi asibiti'.
'A'a Ibraheem karku sanar masa, yana tareda bak'i'. Hajiya babbace mai maganar tana murk'ususn ciwo.
Badan yasoba ya hak'ura, haka sukaita zama jigum-jigum, da barci yad'an figeta, sunfara yunk'urin tashi saita farka tana ihu.
Glory da kubrah saisu kalli juna a sace suna y'ar dariya. haka suka kwana zubur batareda sun runtsaba.
Saida sanyin asuba yafara busawa, ALLAH yaymusu maganinta barcin gaskiya ya saceta.
Daga Anty Zuwairah har Anty shukurah sun galabaita da barci, glory da kubrah kam dake sunsaka kansune basu damuba, ya khaleel madai da sauk'in damuwar, Dan yarigaya yasaba, tunda wani lokacin aikin dare yakan kamasu.
Ganin barci ya d'auketa yazare hannunsa dake rik'eda nashi ahankali, kuje kud'an kwanta tunda barci yad'auketa, zuwa Safiya idan ALLAH ya kaimu saimu tafi asibiti.
anty zuwairah tace, “to khaleel sannu da k'ok'ari, anbar Aysha dai ita kad'ai”.
“ALLAH yasa bata kwanta cikin tsorob”. ‘cewar anty shikurah’.
"Yazatayi Anty Shukurah,? Inma tanajin tsoron aii dolene ta dainashi, tunda nid'in ba mazauni baneba”.
Hakane
"Amma Dukda hakadai akwai tausayi, amarya guda adaren farko babu ango". Kubrace da wannan maganar.
Batareda ya tanka mataba yafice abinsa.
Anty zuwairah ta ta6e Baki, yayinda kubrah taraka bayansa da harara tana maganar k'asa-k'asa, (wadda nima banajinta).
Koda tashiga saiya fara cin karo da kayan dasukaci abinci.
Tattaresu yayi da sauran naman duk ya kaisu kichin, ya ajiye komai Inda yadace, sannan yad'auki gyalenta yanufi d'akinta dashi. Akan gado ya hangota k'udundune da bargo, dagani kasan tayi barcin cikin tsorone, girgiza kansa kawai yayi yafice bayan ya ajiye gyalenta kan sofa..
d'akinsa yashiga komai tsaf, sai babbar rigarsa da hula d'aya cire ya ajiye bakin gadon, jin Anfara kiraye-kirayen sallar farko yacire kayansa yashiga wanka yad'auro har alwala, koda yafito jallabiyya kawai yazira bayan ya tsane ruwan jikinsa, ya shinfid'a sallaya ya kabbara sallah, raka'atainul fijir yayi, sannan yafita masallaci.
Saida yafara shiga d'akin Aysha, tana nan yanda yabarta kwance, tunanin yanda zai tada ita yatsaya yi, ganin lokacin sallah zai kwace masa yad'an duk'o Kansa saitin Inda take kwance ya yaye bargo data lullu6a, yanda Kasan idonta biyu, tamik'e azabure tareda kwallah k'ara!!.
Da sauri ya ruk'ota, "k Aee'sha nutsu mana nine, yay maganar tareda rungumeta ajikinsa".
Jin muryarsa yasakata sakin kuka tana sauke ajiyar zuciya.
Baice komaiba, saidai buga bayanta dayakeyi ahankali alamar lallashi.
Aikam sai sabuwar shagwa6a tatashi ga Aysha, tacigaba da raira masa kukan, jin ana shirin Shiga masallaci ya janyeta daga jikinsa, kinga bara natafi masallaci, kema kitashi kiyi sallah, da hanzari yafice batareda ya kalli fuskartaba.
Wani kukan Aysha tasaki, saida tayi mai isarta sannan tatashi ta d'auro alwala tayi sallah, tana idarwa takoma gado, Dan wani azababben barci takeji.
Shima koda yadawo masallacin saiya shige d'akinsa ya kwanta, babu dad'ewa barci ya kwasheshi, dama ga gajiyar biki Na nukurkusarsa.
___________________________.
Ya khaleel yariga Aysha tashi, saboda kiran da Taheer yamasa akan bak'ifa zasu tafi, yakamata yazo akawosu su gaisa da amarya amusu rakkiya.
A hanzarce yay wankan ya shirya cikin farin boyal mai shara-shara, Dan har best d'insa ana gani, babudai hula amma yayi k'yau, turare yafesa kad'an sannan yafito yana saka ma6allin link d'in hannun rigarsa.
d'akin Aysha yashigo da sallama, tana tsaye jikin madubi fitowarta kenan daga wanka, daga ita sai guntun towel.
Batayi zatoba taji dallamarsa kuma harya shigo, cikin rikita tafara neman abinda zata rufe jikinta.
Shima kallo d'aya yamata yakauda kansa tareda juya bayansa.
Bayan kamar Monti biyu yajuyo Dan yanada tabbacin ta kimtsa, hijjab d'in datayi sallah tasaka, yakaimata har k'asa, taduk'ar da kanta k'asa saboda kunyar ganinta dayayi ahaka.
Shima kanshi yaji wani iri, Dan hakan baita6a faruwa dashiba, ganin mace ahaka, bashiga d'akin k'annensa yakeba, bakumashi dalokacin kallace-kallecen films d'in banza, shi indai film baishafi bincike-bincikeba baya kallonsa.
"Ehhm, bara naje zamuzo dabak'i, dan zasu wuce yau".
Aysha tace, ''to, tana d'an satar kallonsa, kwalliyar tasa tamata k'yau, saidai fuskarsa babu walwala, itakam batasan randa zata fara ganin dariyarsaba".
Juyawa yayi zaifita, tace, " ALLAH ya tsare".
Ya amsa da amin ciki-ciki.
Harya kama k'ofar zai fita tace, "umh....".
Saikuma tayi shiru.
Juyowa yayi yana kallonta, alamun yana saurarenta, ganin tayi shiru yace, " kinsanfa ana jiranane".
Cikin jinjina kai tana had'iye yawu tace, "dama zancene bazaka karyaba?". 'murya a sanyaye tayi maganar'.
"Saina dawo zan karya", 'yayi maganar yana fita'.
A gaggauce yashiga ya duba Momy, amamkinsa saiya isketa ragal, tanata dannama cikinta breakfast.
" A lallai Momy sauk'i yasamu? harkinsamu kina cin abinci?".
d'an murmushi tayi tana gyara zamanta, "da sauki kam Ibraheem, jiki Alhmdllh, amma inazakaje haka kaci gayu?".
" Zanje nazo da abokainane zakuyi sallama, duk yau zasu wuce".
"To masha ALLAH, ya Aysha?".
"Lfy lau take, bara naje Momy. koma wajen baffah bazan shigaba saina dawo".
Sallama yamata yafita ad'an hanzarce.
Itakuma tasaka dariya tana fad'in Ibraheem kenan, inhar ina raye bazaka ta6a had'a shinfid'a da y'ar isakar yarinyarnanba, lafiyata k'alau, nasan bazaka ta6a biyuwa ta sauk'iba shiyyasa na 6ullo maka tahaka, damacan natsani uwarta bare ita...............✍
Nace hummm, hajia babba sai ku zuba migani keda Aysha.🤝🏻😂
Wlhy banajin dad'i, ALLAH yasama Na iya typing gobe idan ALLAH ya kaimu😥, INA buk'atar addu'arku🙏🏻.
💋💋💋💋💋💋💋💋💋😍😍😍
[9/12, 6:48 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.