Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 2.txt
Chapter 33 of 52
*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_
_bilyn Abdull bata manta dakuba 'yan *BBC HAUSA NOVELS* wlhy ina k'aunarku kamar yanda kuke k'aunata, ngd sosai da comments d'inku, ALLAH yabar zuminci, I love you wijiga-wijiga Alkur'an sisters._
😂❤❤❤❤❤❤🤸🏻♀.
3⃣3⃣
Su ya khaleel Na isa office aiki kawai yafarayi, yakwana biyu baizo office ba, saboda tafiyar dayayi, dukda dai akan aikine shima, amma baihana yatadda jibgin aikiba dake jiransa a office.
Zamansa dakusan mintuna 40 kiran Taaheer yashigo wayarsa, harta kusan tsinkewa yad'aga.
Bayan sun gaisa taheer ya tabbatar masa da wadda zasu kama tafito.
"A'a mikuke jira, Ku kamata mana, damani banaso akamata cikin gidanmune kawai ne".
"OK sir".
Duk suka yanke wayar suduka.
Aiki ya khaleel yakeyi amma zuciyarsa tarabu gida biyu, rabi akan Aysha rabi wajen matar dasu taheer zasu kama.
Yana tsaka da tunaninnan akayi knocking d'in k'ofar office d'in, umarnin shigowa yabada, youseef yashigo hannunsa d'aukeda takardu, saida yayi salute nashi, ya khaleel yanuna masa kujerar zama sannan yazauna, hannu yabashi sukayi musabaha.
Yauseef yace, "sir, gashi munsami mutum kusan 16 masu tambarin kunamarnan".
Da sauri ya khaleel yakar6i takardun yashigo dubawa.
Saida yagama tsaf sannan youseef yacigaba da maganarsa.
" tabbas barau modibbo yana ciki, sannan akwai yaron Alhaji bishasha Lazarus shima yanada ita, akwai yara da'aka kama agidanka suma duk sunada ita.
Cikin mamaki ya khaleel yake kallonsa, kallo irin Na tabbatarwa.
Youseef ya jinjina masa kai alamar gaskiyane.
Huci mai zafi ya khaleel yafurzo daga bakinsa, gaskiya wannan lamarin yafara d'aure kansa, shin miyasa hakan kuma?, kenan da gaske akwai mai alak'a da wannan k'ungiyar acikin gidansu?, (zuciyarsa tana karkata ga zargin Aysha ne, musamman idan yatuna da lokacin da'aka sanarma barau modibbo zuwansu, ya tabbatar Aysha ce kawai taji hakan, amma to mizai sakata tiromusu 'yan Daba kuma? Bayan harda ita zasu cutar?, tokuma ya'akayi tasan talatuwa mai aikin Hajia khaltum ce?, kenan tanada alak'a dasu?, musamman idan Yakuma tattara bayanan matashiyar budurwa sakeena.
Kai, bai yarda da zuciyarsaba, yabibiyi Aysha amma haryanzun bai kamata dawani Abu dayashafi wannan k'ungiyarba, yakamata gakuma sato masa Sakina, zaimata wasu tambayoyi.......
Youseef ne yad'an buga table yace, "sir!, lfy kuwa?."
Da Sauri ya khaleel yakawo numfashi, kuma furzar da hucin yayi sannan yace, "babu komaiba youseef, cigaba ina saurarenka".
Ajiyar zuciya youseef ya sauke shima, yacigaba dafad'in sannan akwai wasu 'yammata biyu damuka kama kusan 3years kenan da cocaine a airport d'in Lagos, suma sunada wannan tambarin kunamar."
Cikin jinjina kai ya khaleel yace, ''kunyi k'ok'ari youseef, kuma kucigaba da aikinku cikin kulawa, ina alfahari daku sosai".
Murmishin jin dad'in yabon da ogansu yayimusu youseef yayi, yace, "duk wani kwazonmu yanadaga cikin tarbiyarka Sir".
Murmushi kawai ya khaleel yayi, yace, "babu damuwa kaje, zuwa anjima zan nemeku kaidasu Joseph".
"Ok, thanks sir".
Ya khaleel ya jinjina Kansa yacigaba da aikinsa.
__________________________
Cikin nasarar aiki su Taheer suka sami damar cafke kubrah, a babban filin jirgin sauka da tashi Na Abuja, ankamatane tana k'ok'arin tafiya Lagos. mamaki yayi matuk'ar kama Taheer, Dan yasan kubrah sosai, tadad'e tana kamun k'afa dashi akan yashawo mata kan khaleel yasota. Yamzu har yarinyarnan zata iya ta'addanci haka?. Kai yanzukam ya gama yadda ba'a shedar mutum.
Kallon-kallo kubrah da Taheer sukayi, sai gumi takeyi da rawar jiki. pretending tafara musu, akan mitayi daza'a kamata?, tanayin hakanne kuma saboda taga Taheer, atunaninta zata samu sassauci daga gareshi. Amma abin mamaki saiya nuna halin ko inkula da ita, saima ka rantse baisantaba.
Cikin yaran taheer wani yadaka mata tsawa da zabga mata lafiyayyen maruka, tuni tadafe kunci tana hawaye, bakinta kuma yayi gum, danta gane rijiya bawajen wasan makaho baneba. kad'an daga aikin masu bak'ar fuskarnan su suburbud'a mata alburushi atsakkiya kwalwarta yanzunan.
Hankalinta baigama tashiba gaba d'aya, ta tabbata inhar ya khaleel nawajen zai kubtar da ita, tunda baita6a kamata dawata 6arnaba, koma hajia babba tasaka ya fiddota aii.
Nidai nace hummm.
********
Ya khaleel Na tsaka da aiki su Taheer suka dawo, ko d'agowama baiyi ya kalli taheer ba, yadai amsa gaisuwar da Taheer d'in kemasa tareda jinjina masa kai.
"Sir! Munsami yarinyarnanfa, amma abun mamaki da d'aure kai kubrah ce fa".
Babu shiri ya khaleel yad'ago kansa, yace, " kubrah kuma? Wace kubrah?. "
"Kubrah dai daka sani, mai zuwa gidanku, Dan haryanzun bansan dangar takar zumincinkuba".
Azabure ya khaleel yamik'e, lokaci d'aya kansa ya sara masa, yay saurin dafe kansa, yama rasa wane tunani zaiyi. Miyasa zuciyarsa ke alak'anta mutanan nan da matarsane?. ranar dinner d'insuce tafad'o masa arai, tabbas aranar hankalin Aysha da meerah yatashi saboda ganin kubrah dawasu mata biyu, idanma bai mantaba meerah barin wajen tayi baki d'aya, kuma Aysha batada wata aminiya sama da meerah. Sannan washe garin ranar lokacin su Sameer sunje musu sallama kubrah da wata mata sunshigo yima Aysha sallama, harya basu damar shiga inda take a bedroom, kuma yashiga d'akin kiranta saboda tazo suyi sallama dasu Nawaff, saiya taddasu cirko-cirko, tabbas akwai alamar tambaya akan matarsa.
To amma idan yace haka kuma, miye alak'ar Momy da kubrah, sannan hajia khaltum kuma?.
''Ya salam!! yafad'a da k'arfi yana dafe kai".
Da sauri Taheer yamatso kusadashi, "j! Miyake faruwane haka?".
Kansa ya girgizama Taheer, cikin k'unar zuciya yace, " Taheer ina zargin wasu abubuwa biyu, kuma akan mutum biyu, amma bana fatan hakan ta kasance, domin duksun shafi katanguna, ya ALLAH!".
kamashi yayi ya zaunar, yaringa kwantar masa da hankali, saida yaga yad'an nutsu sannan ya idamasa bayanin yafice.
Gaba d'aya yau ya khaleel yakasa ta6ukama kansa komai, tunani yafaracin k'arfinsa, yanaso yakira gida yaji yajikin Momy da Aysha amma haushinsu yahanashi, kuma yayi alk'awarin inhar suka kasance cikin abinda yake zarginsu wlhy billahi bazai d'aga musu k'afaba, saiya hukuntasu, kuma da hannunsa zai kamasu.
Wannan alk'awarine, bazai ta6a barin mai laifi a k'ark'ashin inuwarsaba.
Idonsa yayi jajur saboda 6acinrai, zuwa can maganar yarannan tadawo masa arai itama, lokacin dayake tambayarsu waye ya turosu, (sunce matar babansa hajia Bilkeesu) kai jama'a miyasa zuciyarsa take karkata dukkan zarginsa akan wad'anda ya yadda dasu? Mafiya kusancu agareshi kuma?, zai sakama dukkan wani dake gidansu ido kawai, Dan yanzu ba Aysha kad'aice abin zarginsaba, harda Momy da Anty Mamie.🤥
____________________
Yauma dai haka Aysha tayini duk babu dad'i, komai taci kamar jira saita amayar dashi, zogalene kawai dataci ya zauna, haka 'yan Kano suka tafi suna tausaya mata.
Bak'in 6angaren Momy ma duksun wuce, inna jummai Ce kawai tarage.
Misalin 10 Na safe baffah yashiga duba hajia babba, bayan sun gaisa da inna jummai yashiga d'akin.
Duk 'ya'yanta suna zagaye da ita, har mufeedah dake raku6e gefe d'aya.
Ganin baffah suka fara yunk'urin fita amma saiya dakatar dasu, kujerar madubi husnah tabashi yazauna, Momy Na kwance dukta kuma janga6ewa saboda dagaske batada lafiyar, k'arfin haline kawai, da k'yarma tasha tea da magungunanta takwanta yanzu.
Sannu yamata cikin tausayawa, da tambayar k'arfin jikinta, tace, k'irjintane kemata ciwo yanzun, amma tasanarma doctor dasukazo yanzun shida sultan, yace zai kawo mata magani.
"To shikenan ALLAH yak'ara afuwa, sannan kuma ki kwantar da hankalinki, Dan kinsandai kinada hawanjini. Idankuma hankalinki ba'a kwanceba ciwon bazai barkiba".
Kanta ta jinjina masa, wasu siraran hawaye suka zirara a idonta na dama, suka gangara har cikin kunnenta, Anty shukurah ce ta goge mata.
Baffah ya maida kallonsa ga mufeeda, "k kuma kishirya kayanki, 6angaren Ammah zaki koma harki haihu, rashin ganinki zai sassautama mahaifiyarki rad'ad'in datakeji".
Mufeedah kuka tafashe dashi, Dan tasan inhar takoma 6angaren Ammah bata Isa zubar da cikinnanba, tasan jarabar Ammah da k'unatar tsiya.
Cikin daka tsawa yace, " kobak'ya jinane?".
Azabure tace, "to baffah".
Yayi tsaki yana maida kallonsa ga Momy dake yunk'urin tashi zaune, Anty zuwairah da Shukurah suka taimaka mata tatashi.
Muryarnan ta Momy duktayi low, tace, " Alhaji kana ganin ita Ammah baza'a takurataba?, nida canayi tabi inna Jigawa kawai, idan ta haihu saita dawo, koya kagani?".
"Eto kema kinzo da shawara mai k'yau, amma abani nanda kwana uku nagani".
Murmushin samun nasara Momy tayi, tacigaba dafad'in " to ALLAH ya kaimu, sannan sai kayanta, yakamata akwasosu aii".
"A'a baza'a kwasosuba, Dan zamu maida auren kan Nafisa d'iyar k'anen Bilkisu Hameesu, tunda ta isa aure, dadai tasleem ko maleeka zan bashi, tokuma duk sunada manema ashe, Dan haka baza'a kwaso kayanba, mungama magana da innah za'a d'aura auren k'arshen satinnan, shukurah keda Amatullah kuje Ku d'akko kayan sawar Mufeeda kawai, sannan karku d'akko akwatinan lefen, kubarshi can, sadakintama za'a maidashi Na Nafisane".
Tunda baffah yafara magana Momy take zabura, haryakai k'arshe, " Alhaji ban gane wannan zancen nakaba?, daga INA kuma wannan annamimancin yafito?, asaki 'yata agida, bayan kwana biyu rak da kaita gidan, sannan amaye gurbin gidan da jinin Bilkeesu, wlhy impossible, wannan wane irin rikitaccen tunanine?, ko ance muku idan mufeedah ta haihu bazata koma d'akinta baneba?".
Mik'ewa tsaye baffah yayi yana guntun murmushi, yace, "Laurah Baku Isa hanani abinda nayi niyyaba, Ammah datai sanadin kawoni duniyama ta amince, hakama d'an uwana ya amince, Ameenudden ya amince, ahakama iyayen yarinyar, banida abinda zan sakama Ameenudden dashi saboda zalincin da ballagar 'yarki tamasa, adalilin sakacinki, babu abinda zai saka aurennan fasuwa saidai mutuwa, idanma zaku kwantar da hankalinki Ku kwantar, idan bazaku kwantarba kune awahale, narigada Na zartar da hukunci babu mai canjashi, wlhy da'ace akwai budurwar danake da ita bayansu Tasleem saina aura masa, bazankuma aura masa Hasnah ko Husnah ba, saboda suma hankalina bai kwanta dasuba, ki kiyayeni kuma".
Yajuya zai fice abinsa.........
Cikin k'araji hajia babba tace, kayan kicin aida kud'ina nasiya, Dan haka sai an kwasomin kayana, kuma zargin dakama sauran 'ya'yana ban yafeba, dama cin zarafina kazoyi gaban 'ya'yana ba dubaniba, dama aii tuni nagama sanin Bilkisu ta shanyeka, kayi nisa bakajin kira, ALLAH saiya mana hisabi tsakanina daku".
Juyowa baffah yayi yana kallonta. Yasaki guntun murmushi, kiyima kayan kichin d'in kud'i konawane zan biya, sauran maganarki kuma kisameni zan baki amsarsu, amma ba'a nanba, yanagama fad'a ya ficewarsa abinsa.
Kuka rurus momy takeyi, sai zage-zage da zabgama mufeedah ALLAH ya isa takeyi, wai itace taja ake cin zarafinta.
Inna jummai tashigo tana mata fad'a.
Dak'yar suka samu yayi shuru kuwa.
___________________
Har bayan isha'i ya khaleel bai dawo gidanba, Aysha Na kwance bisa doguwar kujerar ammah, lullu6e take cikin bargo saboda sanyi datakeji, ga zazza6i mai zafi ajikinta, tun d'azun tunanine da damuwa suka to she kwalwar kanta, duk yau bataga ya khaleel ba, dukda tana zargin yatafi aiikine, amma yakamata yakirata yaji yajikinta, ganin bai kira d'inba takirashi har kusan 4times amma bai d'agaba, hawaye masu zafi suka zubo akan kumatunta, tun d'azun take kukannan, saboda lullu6a datayi da bargo har fuskarta yasa ba'a ganin.
Ammah dabatasan abinda ke faruwaba, suna zaune da inna jummai suna hirarsu irinta zuminci, sai Tasleem da maleekah dake can gefe zaune kowacce suna chatting, inbakama saniba zaka zata suna falonba.
Sallamar ya khaleel tasakasu d'agowa suduka, amma da inna jummai suka masa sannu da zuwa, suma su Tasleem suka gaidashi.
Ya amsa awani yanayi, Ammah sai binsa da kallo takeyi, Dan taga Alamar yana tareda damuwa.
Inna jummai tamik'e tafita, waizata duba jikin Momy tadawo.
Ko kallo bata ishi ya khaleel ba, danshi bayason wanda bai sonsa, tana fitama k'amin tsaki yaja, ammah datajisa batace dashi komaiba, Dan tuni take fuskantar 'Yar tsamar dake tsakanin Khaleel da kakarsa tawajen uwa, kuma k'anwar kakarsa ciki d'aya.
Zama yayi saman hannun kujerar da Aysha ke kwance, wadda tunda taji sallamarsa tashare hawayenta.
Hannu yakai ya yaye bargon, hucin zafin zazza6in yasakashi fad'in ''ya salam, wannan zazza6in har yanzu bai saukabane Ammah?".
"Yana sauka yadawone iro, aii saidai hak'uri kuma, idan ba kwari yayiba haka za'aita fama".
" ALLAH ya k'ara lfy, yay maganar yana lek'a face d'in Aysha data lumshe ido, saika d'auka da gaske barci takeyi, ammashi tuni yagano idonta biyu.
K'aramin hannun rigarta ya janye, babu komai a damtsen hannunta, aransa yace k'ila d'ayan hannun tane kunamar take?, saikuma yace amma banta6a ganiba?".
Aysha dai batako motsaba, yamaida bargon ya lullu6eta yana mak'ewa, ammah bara nad'an watsa ruwa, shigowata kenan gidan.
".
A to yakamata aje a kimtsa, kazo ga abincinka Bilkeesu ta aiko dashi".
Kansa kawai ya iya jinjina mata yafice, Aysha tabishi da kallo asace, tabbas akwai abinda ke damun mijin nata gaskiya, to minene?".
Batada amsa, babu kuma mai bata, wannan yasakata tsuke bakinta tayi shiru. Tana binsa da addu'a a zuciyarta................✍🏿
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻🙏🏻🙏🏻😭
*_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*
*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of expert & perfect writer's)_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.