Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 2.txt
Chapter 13 of 52
*_part 2_*
(littafi na biyu📕)
1⃣2⃣
Yana fita Aysha tasauke ajiyar zuciya, hijjabin jikinta tacire tayi simple kwalliya, tasaka siket da riga Na atanfa, kayan sunmata k'yau sosai, amma ita kokad'an bawani tadamu da sawar baneba, saboda gargad'in da mama tamatane kawai take kiyayewa.
d'akinta tagyara tsaf, tasaka turare sannan tanufi falo shimadai gyaran kad'an tamasa tasaka turaren, tayi mamakin rashin ganin kayan abincin jiya, aranta tace, "k'ila ya khaleel ne yad'auke".
Harta nufi hanyar kicin taji ana Knock d'in k'ofa, tajuyo dabaya danufin dubawa ya khaleel yashigo da sallama, Aysha ta amsa kanta ak'asa.
d'an nesa da ita yatsaya, idonsa kyam akanta, saidai fuskar haryanzu babu walwala. yace, "tarenake da bak'i, kinzo kin tsayamin akai, kije kisaka hijjab zasu shigo".
Haushine ya kama Aysha, batasan ta murgud'a masa bakibama, tawuce tana k'unk'uni batareda yaji mitake cewaba, ransane yad'an sosu, amma saiya danne yayimusu iso zuwa ciki, Dama suna bakin k'ofane tsaye.
Masifa natacin Aysha a zuciya tana d'akko hijjab a wardrob tana tsogumin yanda halayen ya khaleel yake, shidai bazai ta6a kuyi magana mai dad'iba dashi, to yaushema yasakema mutane fuska, itafa gaskiya bazata iya wannan rayuwarba.....
Tajiyo bayan tad'akko hijjab d'in danufin rufe wardrobe d'in taji tabuge Abu, ad'an figice tawaigo dansan ganin minene?. Bak'aramar fad'uwa gabanta yayiba ganin ya khaleel tsaye abayanta, kokad'an bataji alamar shigowarsaba.
"Zan.....zan wu wuce".
Tayi maganar cikin in ina da rawar baki, jikinta sai tsuma yakeyi.
Bai motsaba, kuma bai tanka mataba, fuskarnan babu alamar sauk'i.
Hakan yak'ara saka Aysha cikin tsoro, tatura murfin wardrobe d'in tareda jingina ajiki, idanunta Na kallon k'asa tana k'arema yatsun k'afafunsa kallo. Yayinda shikuma itad'in yake k'arema kallo, baita6a damuwa da kallon ya Aysha takeba a can baya, amma ayanzu saiya samu kansa dabin halittar jikinta da kallo daki-daki.
Kad'an tad'ago ido ta kalleshi, ganin kallon k'urillar dayake matane tayi saurin saka hijjab d'inta.
Yalumshe manyan idanunsa yana kauda kansa, Aysha tara6a ta gefensa zata wuce cikin d'ari-d'ari.
Da sauri yaruk'o hannunta, cikin Aysha yabada k'ululu!..
"dawo magana zamuyi".
Jiki a sanyaye tadawo baya, kafin yace wani Abu wayarsa tafara ring.
Cirota yayi yaduba, taheer ne, batareda yad'agaba yasaki hannun Aysha yanufi k'ofa, saida yabud'e sannan yace, "kizo Ku gaisa, zasu tafine, sannan kitanaji bayanin dazaki Kare kanki akan murgud'amin Baki dakikayi". 'Baijira cewartaba yafice abinsa'.
Bak'aramin rud'u Aysha tashigaba, itama tasan hakan ba daidai baneba, amma wlhy rantane bayason dizgin dayake mata.
Jiki a sanyaye tabi bayansa, gudun karta k'ara wani laifin.
Sannu da zuwa tamusu tanufi kichin, sukuma suna tsokanar ya khaleel d'in, wai daga kira yayi bulum ad'aki, miyakeyi?.
Tsaki yayi yana hararsu, yaxauna a kujera yana ''fad'in duk abinda zuciyarku tabaku shi Ibraheem khaleel yakeyi".
Dariya sosai suka Sanya masa da shak'iyanci irinnan abokai. Ayaha tafito daga kichin d'aukeda babban tire dake cikeda drinks, ta ajiye a tsakkiyar falon takoma, babu dad'ewa tadawo da snacks, ta ajiye takoma tad'akko glass cups, duk suka mata sannu.
Cikin kunya take amsawa, anutse tagaishesu, duk sun yaba da ayshan, harsuna taya abokinsu burna azukatansu, sunta tsokanarta irinnan abokan miji, bata iya cewa komai saidai murmushi.
Ya khaleel kam saima karantse baya falon, waya yaketa dannawa batareda saka bakinsa a zancensuba.
Aysha tamik'e tabar musu falon dansu d'an ci abinda ta ajiye musu.
Shigarta d'akinta da y'an mintuna saiga anty glo...da kubrah, saida suka gaisa dasu ya khaleel afalo sannan suka shigo, bisa umarnin ya khaleel d'in.
Zumbur Aysha tamik'e daga bakin gadon, Dan batayi zaton ganinsuba.
Anty glo tashek'e da dariya tana "fad'in sholy amarsun ango, Ashe dama tsoron john Na k'aryane kikeyi, koda yake naga kinzama y'ammata, ina Antyan taki meerah?".
Amamakinsu sai sukaga Aysha tayi murmushi, takoma bakin gadon ta zauna tana musu wani kallon rainin hankali, "mtsowww! Wlhy ku kama kanku, kenaga kanki rawa yakeyi glory!, inaga dai k'awar taki bata sanar dake wanene mijin nawaba ko? Karfa wajen tone tonen kaza, tatono wuk'ar yanka kanta".
Kubra tabud'e baki zatayi magana kenan ya khaleel yaturo k'ofar ya shigo, kallo yabisu dashi su duka, glory da kubrah sund'anji shock da shigowar tasa, Aysha kam ko'a kwalar rigarta, Dan zuwa yanzu batak'i komai ya 6aciba.
Ko kallo su kubra basu isheshiba, yace, ''taso kuyi sallama zasu tafi".
Aysha tamik'e itama batareda ta kalli su kubra d'inba tanufi k'ofa.
Ganin haka suma dole sukabi bayanta, bak'aramin Sosa ransu lamarin yayiba, suna mamkin yaushe Ayshan tawaye har haka? Lallai hajia laura kallon baibai takema Aysha, kuma dolene sud'auki mataki akan Aysha da meerah, Dan zasu 6allo musu ruwane.
Bayan tafiyarsu glory da abokan ya khaleel, mutanen Kano sukazo mata sallama, kowa dai yak'ara mata nasiha, gayyar ciki da gaskiya fans ma sunzo sallama, cikin mutunci Aysha ta kar6esu, ko'ina sun zagaya a gidanna Aysha, sannan suka mata sallama suka tafi, harda 'yan kwallanta kuwa, acikin fans d'in ciki da gaskiya kuwa wasu basuso tafiyaba😂🤧😜.
Amma na tusa k'eyarsu gudun samun matsala,🤣, karsu ragema ya khaleel jin dad'i💺😏🤧kundai gane😉.
To Alhmdllh bak'i sunyi halin ruwa, gida yayi tsit, saisu Anty zuwairah da y'ay'ansu kawai.
______________________________
Har 4 ya khaleel bai shigoba, Aysha tad'an damu, ko breakfast baiyiba, Na ranama da Anty Mamie ta aiko itakad'ai taci.
Yanzu haka saboda bak'in daketa kara kaina shiyyasa yak'i shigowa.
Bayan tayi sallar la'asar takuma gyara ko ina da'aka 6ata, gidan yad'auki k'amshi, babu wuta gakuma babu Wanda yashigo, ta zauna shiru tana tunanin ina ya khaleel yashiga? Tundaga rakkiyar 6ak'ifa.
Jitayi ana Knocking d'in k'ofa, tamik'e a d'arare taje tabud'e, su Tasleem ne d'aukeda abinci, rungume juna sukayi Dan duk yau bata gansuba.
Suka shiga tsokanarta matar yaya matar Yaya.
Nandai suka zauna sunata hirarsu, ananma suke bata labarin soyayyar tasleem da maheer, maleeka da shakur, sosai Aysha tayi farinciki.
Suna cikin hirar ya khaleel yashigo.
Kowa yay tsit, suka shiga gaisheshi da sannu da zuwa.
Bayabo babu fallasa ya amsa tareda nufar d'akinsa.
Su Tasleem suka mik'e, rok'onsu Aysha tashigayi akan su zauna, basu sauraretaba suka gudu.
Tarasa miya dace tayi?, tana nan zaune inda suka barta ya khaleel yafito, ya sauya kayansa zuwa jallabiya blue black, ya zauna afalon bisa 2sita, tareda ajiye system d'insa dake hannunsa da wayoyi.
Mik'ewa Aysha tayi tashiga kichin, yabita da kallo a munafunce.
Bata dad'eba tafito d'aukeda k'aramin tire, tad'oro ruwa da cup, sai drink.
Harya kunna system d'insa yafara aiki, da'alama aikin mai muhimmancine, kuma yazo masa a gaggaucene, ruwa Aysha tafara zuba masa, ya kar6a hankalinsa nakan aikinsa, saida yasha ya ajiye cup d'in sannan yad'an d'ago ido yakalli Ayshan, kallon dabaifi second4 ba yamata yajanye idonsa, "wazai gyaramin d'aki?", 'Yay maganar murya adake'.
Kunyace takama Aysha, Dan yakamata ace tunda safe tashiga ta gyara, to amma tsoron dizginsa takeyi, murya a sanyaye tace, ''kayi hak'uri, wlhy bak'ine sukamin yawa, amma zan gyara yanzu, sannan ga abinci, naga ko break fast bakayiba kafita".
Baice da ita uffanba, saima k'ok'arin amsa call yakeyi, "hello Joseph!, yawwa nagani, amma yakamata kunema mana bayanai akan Ak'ilu Abbas d'innan, Dan banyarda dashiba, idan kanutsu akan zancensa akwai kalamai masu kama da rashin gaskiya, ina Hutu amma tilas gobe idan ALLAH ya kaimu nafito aiiki, Dan zankama Lazarus da kainane".
"OK babu damuwa, kausar da fharuk sumin binciken asusun bankinsa, inason bayanai kuma akan hajiar data tura massege wa Barau modibbo, awaccan ranar".
Bayan ya sauke wayar yakalli Aysha dake tsaye tana saurarensa, yace, " waye barau modibbo? ".
maganarsa takusan sakata fitsari atsaye, tawaro idanu akansa batareda ta shiryaba, tace, "ya khaleel kamarya? Wanene barau modibbo?".
Kafeta yayi da mayun idanun nan nasa, masu hana Mara gaskiya zaman lfy, soyake yagano ainahin gaskiyarta, muryarsa adake yace, "idan ban mantaba, aranar na rutsaki kina waya a garden, sannanma kena aika kika d'akkomin guns ad'akina, kifad'amin gaskiya, kece kika turamasa massage akan yagudu?".
Innalillahi wa'inna ilairirraji'un, "wlhy ya khaleel bansan komai gameda hakanba".
Ahankali ya lumshe idanunsa sannan yabud'e akanta, "shikenan jeki kiyi aikinki".
Innalillahi kawai Aysha take ambata azuciyarta, tana mamakin miyasa tun awancan lokacin baimata maganarba sai yau?, tabbas bata shakku akan zarginta hajia babbace, Dan tata6ajin sunan barau modibbo abakin Anty kubra lokacin suna UK, ayanzune yakamata tayi aikin sirri da ya khaleel batareda yasaniba", tasaki murmushin mugunta.
d'akin nasa yabirgeta sosai, komai farine tamkar tsohon d'akinsa, cikin nishad'in samun bakin zaren tona asirin su hajia babba tafara aikinta.
Ya khaleel kam koda tabar wajen saiya bita da kallo, wasu al'amura Na yarinyar suna bashi mamaki, tundaga randa abinnan yafaru yad'ora zarginsa akanta, amma zuciyarsa tak'i amince masa, tana nuna masa hatsabibancin yarinyar baikai nanba, to amma wacece? Yasha bibiyar Ayshar amma baiga wani abun rashin gaskiya tattare da itaba, yafurzo zazzafar iska daga bakinsa, Kokuwa badaga 6angarensa mai tura massage d'in takeba?, yakamata yabinciki Joseph Taheer youseef, alokacin dazasuje kama barau modibbo awaccan ranar suna inane?.
Da wannan tunanin yacigaba da aikinsa.
Aysha tagama gyara komai tsaf tafito, dama babu wani datti.
A inda tabarsa anan ta iskesa, yakuma maida hankalimsa gaba d'aya akan aikinsa, itama saikawai tamaida hankalinta ga TV.
Lokaci-lokaci yakan d'ago ya kalleta, yamaida kansa, ahaka har aka kira sallar magriba, yarufe lap-top d'insa yamik'e danyin alwala yana "fad'in kidafamin shayi kafin nadawo".
Aysha ta amsa da ''to tana mik'ewa itama".
______________________________
Yauma abinda yafaru adaren jiya shiyya faru, bayan dawowar ya khaleel daga sallar isha'i kaitsaye d'akin Aysha yashiga, gama wayarta da Anty meerah kenan tafad'a mata komai akan zuwansu kubrah da tuhumar da ya khaleel yamata, sunk'ullah hanyar dazasuyi aikin sirri da ya khaleel batareda ya fahimci suneba.
Khamshin turarensane yasaka Aysha d'agowa, Dan ciki-ciki yay sallama, cikin hanzari tafara Neman hijjab d'inta ta sanya, Dan k'ananun kayane ajikinta, sunkuma kama jikinta sosai amma sunmata k'yau.
Jiyayi wani Abu yadaki zuciyarsa yay azamar kauda kai daga kallonta, itama cikin in ina take masa sannu da zuwa.
Kansa kawai ya gyad'a mata yajuya zai fita yana fad'in zoki bani tea.
Aysha batajin dad'in yanda yake mata wlhy, amma yazatayi, insha ALLAH zata canjashi kamar yanda Anty Mamie tasanar da ita, (mace takan canja namiji duk a yanayin datakeso, cikin hikima da ilimin da ALLAH ya bata irinna y'a mace mai daraja), ajiyar zuciya tasauke, afili tace hakane Anty Mamie, insha ALLAH nima zan gwada.
Saida ta zumbula hijjab sannan tafito, zaune ta iskeshi da remote ahannu yana Neman tasha, tabi tabayan kujerar dayake zaune tanufi kicin, babu dad'ewa tafito d'aukeda tire k'arami Wanda tad'ora k'aramin filas da mug, taja table gabansa ta d'ora, tana k'ok'arin fara zubawa yace, "cire wannan hijjabin".
Da sauri Aysha tad'ago ta kalleshi.
Ya harareta, ''miye kikawani tsareni da wannan kwala-kwalan idanun? karfa zuciyarki tafad'a miki shirme, danbakida abinda zan kallah ajikinki, mtsoww".
Maganarsa ta 6ata mata rai, ta janye idanunta daga kansa tana murgud'a baki.
Ganinta kawai tayi a cinyarsa, amma batasan tayaya ta hauba.........✍
Kuyi manage da wannan jikin babu kwari😟.
*_ina tayamu murnar shiga sabuwar shekarar musulinci, alkairin dake cikinsa ALLAH ya sadamu dashi, shirrinkuwa ALLAH ya nisantamu dashi, ALLAH ka gafartama mahaifanmu dadukkan y'an uwa musulmai baki d'aya, muma ALLAH ka gafarta mana, kacika zuciyarmu da tsoronka da soyayyar ANNABINMU (SAW), ameen._*🙏🏻
_ngd da addu'oinku gareni, masu kirana daturomin sak'o dukna gode, ALLAH yak'ara mana lfy baki d'aya ameen._🙏🏻🤝🏻💋💋
❤❤❤❤❤💋💋💋💋💋💋💋💋💋.
[9/13, 7:32 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.