Trending Hausa Novels

Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 2.txt

Chapter 18 of 52

*_part 2_*
(littafi na biyu📕)

1⃣7⃣

Ammah Na kacire saman kujera doguwa ta kurama TV data kunna idanu, kaikace tanajin yaren da'akeyi, tanason canzawa amma tarasa yanda zatayi, kunnan tvn dai ta iya.
Daga momy har Anty zuwairah babu Wanda yalura da Ammah, itakam tun shigowarsu idanunta Na Kansu, k'iyarsata yanda zataci mutuncin momy azuciyarta kawai takeyi.
Momy daketa harare-harare da hura hanci tafara kwalama ya khaleel kira. "Ibrahim! Ibrahim!! Kobaka jinane?".
"yaza'ayi yajiki? Bayan yanacikin halin ciwo Laure!".
Afirgice suka juyo suduka suna kallon Ammah, Anty shukurah dake k'ofar d'aki tsaye tayi murmushin jin dad'in ganin Ammah, shiru momy tayi takauda kanta daga kallon Ammah, zuciyarta sai suya da zugi takeyi.
Anty zuwaitah ce tasamu k'arfin halin Jan k'aramin tsaki, tana ta6e fuska.
Ammah tace, "kinyiwa Abdillahi da Laure, mara mutunci fitsararriya, mai girman kwabo kawai, 'Yar banza magajiyar uwarta".
"nidai badai uwataba ehe".
Tassssss!! Kakeji afuskar Anty zuwairah, gaba d'ayansu suka waigo dansan ganin Wanda yay marin, bakowa baneba face baffah da Anty shukurah takira awaya tasanar masa gasu momy can suntafi 6angaren khaleel.
Dafe kunci Anty zuwairah tayi, tunda ta girma tayi hankali baffah baita6a ko dungurintaba, amma yau harda mari? Da girmanta, ga zagada-zagadan 'ya'ya.
Momy kam baki bud'e take kallon baffah, tama rasa abin fad'a.
Ammah tataso tana tafa hannaye, ''kayimin dai-dai, kuma tabbas nahaifi d'an halak, kekuma kince badai uwarkiba?, to saitawa kenan?".
Cikin zubda hawaye Anty zuwairah tace, "nidai aii ban fad'aba ko".
Ammah zata sake magana baffah yace, ''kiyi hak'uri Ammah Dan girman ALLAH, basai kincigaba da 6ata rankiba akan rashin tarbiyya irin ta wannan mara mutuncin da uwarta ba, namuku biyayya Na auri Laure badan inason halayentaba, ayanzukam ina rok'on alfarma agareki, abisa madadin baba zan saki Laure yanzunnan, saboda halayenta sun isheni, banajin dad'inta, banajin dad'in 'ya'yanta sai shukurah da mu'azzam kawai, dan ALLAH Ammah kibari nasaketa kawai".
" humm bazaka saketaba Abdullahi, saboda wasu dalilaina, munhad'a aurenka da ita saboda darajar zumincin dake tsakanina da jummai mahaifiyarta, sannan kuma akwai 'ya'ya tsakaninku yanzu, to taci darajar y'ay'an dakuka haifa, d'ayan sirrin kuma nabarma zuciyata, dan haka kabarta duniyace zata koyar da ita hankali kwanannan".
Wani irin kallon momy take bin Ammah dashi, maid'aukeda abubuwa da dama, tsoro, tsana, k'iyayya, k'yama, hasala, bak'inciki, wai agaban 'ya'yanta wannan tsohuwar take cin zarafinta itada d'anta, lokaci yayi dazata d'auki mataki akan baffah da uwarsa, batareda tace komaiba tajuya afusace tabar falon.
Anty zuwairah ma baya ta take mata.
Baffah ya dakatar da ita, "kije yanzun ki tattara kayan 'ya'yanki da naki kibarmin gida Dan ubanki, kuma wlhy karna sake ganin k'afarki agidannan Harnan da shekaru biyu, inkuwa bahakaba saina sa6a miki kamanni Mara mutunci kawai, karna fito Na iskeki cikin gidana wlhy kinji Na fad'a miki shashasha".
Wannan hukuncin yamin dai-dai, Dan in ba hakaba wannan makirar saita kashema iro aurensa, Dan itace ke zuga uwarsu, Na tabbata ko wannan ciwon k'aryar da Laure taitayi harda bakin 'yar banzar can".
Anty shukurah tamatso jiki a sanyaye tana Bama baffah da Ammah hak'uri.
Albarka sukaita saka mata, sannan Ammah Tamusu bayanin ya khaleel d'inma bashida lfy.
Har d'akin ya khaleel baffah yashiga, khaleel Na kwance idonsa biyu, tun fara maganar Ammah dasu Anty zuwairah ya farka, komai akan kunnensa yafaru, bak'inciki da k'yamar halin mahaifiyarsa da 'Yar uwarsa yahanashi fitowa, dukda abin yahad'ama darashin jin k'arfin jikinsa.
Su Ammah na shigowa ya lumshe idanunsa, baya buk'atar Susan idonsa biyune, Anty shukurah tajawo stool d'in madubi ta ajiyema baffah gaban gadon, kusada ya khaleel, zama yayi yanamai tausayin d'an nasa, saboda halin mahaifiyarsa, yasan kokad'an khaleel bayajin dad'in mahaifiyarsa, hak'uri kawai yakeyi kasancewarsa mutum mai kawaici da had'iye damuwa, kokai waye Baka isa tantance damuwar khaleel ba, mutumneshi mai taka tsantsan da iya zaman duniya, komansa namasu nazari da dattakone, gashidai yaro amma akwai halayen manyan mutane tattare dashi, wannan baiwace da ALLAH yamasa tun yana k'araminsa.
Ahankali baffah yakai hannu yana shafa kan ya khaleel d'in, cikin taushin murya yace, "ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka, ALLAH yabaka lfy".
Ammah da Anty shukurah sukace ameen.
Ammah tace, " aii zazza6in ya sauka ko? Dan sanda yakirani yanajin jiki sosai, amma dayake iro jarumine baka gane hakan".
Murmushi baffah yayi, "Ammah da d'an sauran zafi kam ajikinsa, amma ba sosaiba".
"To Alhmdllh, aidayake likita ya dubasu".
Baffah ya jinjina kansa yana kuma fad'in " ALLAH dai yak'ara sauk'i, ina ita matar tasa?".
"Itama tana d'akinta babu lafiyar, Shukurah duba ita kiga tashi".
" to Ammah".
Addu'a ya khaleel yakeyi azuciyarsa ALLAH yasa kar Ammah tamasa 6arin makauniya a gaban baffah, kaidata gama kasheshi wlhy.......
Tunaninsa yakatse lokacin da Anty shukurah tadawo tana fad'a musu haryanzu Aysha barci takeyi.
d'akin Ayshama saida baffah yashiga, sun isketa tanata barcinta itakam hankalli kwance, itama baffah yamata addu'a sannan suka fito.
Suna fita Aysha tabud'e idonta, Ashe itama idonta biyu, duk badak'alar da akeyi acikin kunnenta, jin motsin tahowarsu yasakata rufe ido harda d'an munsharin k'arya.
Jitai wata k'aunar surikin nata kuma mijin mahaifiyarta na ratsata, tareda kakar mijinta, surukar mamarta, dakuma d'iyar mijin mamarta kuma yayar mijinta, ta share hawayen dasuke kwarara bisa kumatunta, zuciyarta Na mamakin hajia babba wace irin mutumce?, akoda yaushe tana mamakin taurin zuciya irinta hajia babba, ga maigadonta nan kuma sak tasamu Anty zuwairah.
Ta sauke ajiyar zuciya, yayinda tunaninta ya iso kan mijinta, shikuma halayensa sunyi mugun samun tazarar nisa tsakaninsa dana mahaifiyarsa, kokad'an ko alama babu kamanceceniya yanayin halitta ta halaye da jini da yakamanta hajia babba da ya khaleel, tomiyasa haka?, wannan ikone kuma Na ALLAH mad'aukakin Sarki, mai fidda rayayye daga jikin matacce, zuciyar Aysha tafad'a yayinda tunaninta ke k'ok'arin tasirantuwa da shakku, "hakane kuma" tafad'a tana gyara kwanciyar, tareda dawo da tunaninta akan mutanene jiya dasuka shigo musu gida.
Tabbas yakamata tayi tunani akan waya turosu? Shin ta 6angarenta sukazo? Kokuwa ta 6angaren mijinta?, tasan zuciyar su hajia babba a bushe take, bushewa kuma irinta kututturen marke daya mutu a shekarun tashen k'uruciyarsa, tacije le6enta Na k'asa da k'arfin masifa, kaikace zata hudashine da hakwaranta, lokacifa yayi dazatayi aiki ba saka lokaciba, inkuwa bahakaba lokaci zaita gudun zomo da tunaninta, zata kira Anty meerah dansu mik'e tsaye, wannan lokacin bana tsare-tsare baneba na gudanarwa ne da zartar da hukunci ga masu laifi irinsu hajia babba, zasu farane da k'ananun kwari irinsu glory domin dakushe kaifin su hajia babba, tasaki murmushin gamsuwa akan tunaninta.

Shima ya khaleel suna fita yacije le6ensa, zuciyarsa namasa zafi da k'una, musamman daya tuna da gardawan jiya, zai d'auki mataki kam sosai, shi tunaninsama baikawo Kansu hajia babba, azatonsa daga wajen aikine aka masa turre.
Cikin k'arfin zarrar jarumtakarsa yature wannan tunani danasu momy, bayason 6ata wannan ranar farincikin nasa da 6acinrai, danhaka yamaye gurbinsa da tuna farinciki da baiwar da ALLAH yamasa adaren jiya, daga tagomashin alkairi na matarsa Aysha.😘👍🏻

____________________________
Babu inda zakije, saidai mutafi kamar yanda yayniyya tun farko, aini banso munafukarcan tahanashi ya sakeninba, saimima danya sakeni, bajira nakeyi agurinsaba, idan dukiya yake tak'ama da ita wlhy ayanzu ni Laurah na ninninkashi, idan k'arfin iko yake tak'ama dashi nafishi, idan k'yaune yanzunkam babushi Dan tsufa yacinye masashi, to saime? nace saime? Saime kegareshi dayakeda zarrar wulak'antani? Wlhy Abdallah kayi k'arya ka kwana da yunwar wulak'anta laurah dagakai har uwarka, dolene nad'auki mataki, dolene kasan laurah tawuce dasaninku da tunaninku tuniii!!!".
Yanda tak'are maganar a tsawace saida yasaka Anty zuwairah zabura, saikuma ta sauke ajiyar zuciya ganin momy na hawaye, "nayi kuskure tun farko a rayuwata, tabbas danasan ALLAH zai d'aukakeni zuwa yanzun dababu abinda zaisakani aikata hakan, Abdallah abinda yasani auranka danshi yanzu nafika, nace nafika abinda kesakaka tak'amar dahar nawahalar dakaina dominshi abaya!!, Abdallah zan d'auki mataki akanka cikin ruwansanyi, matakin dazai ta6a zuciyarka da rayuwarka, matakin dabazaka ta6a mantawa da lauraba, abinda kafiso da tak'amar dashi zan salwantar, wlhy nad'auki alk'awarin salwantar da ruhinsa domin haddasa bak'inciki dawwamamme azuciyarka na har Abadan".
Tsoro da mamakin maganganun momy suka rikita Anty zuwairah, kallon momy takeyi cikin matuk'ar tashin hankali da tunanin kodai tazarene?.
Atsorace tace, " momy wai mikike fad'ane haka? Nagaza fassara wad'annan kalaman naki".
Idon momy jajur tajuyo tana kallon Anty zuwairah, tayi wani murmushin takaici, "zuwairah bazaki ta6a ganewaba, Dan banama buk'atar ki ganed'in, kishirya keda yaranki kutafi kamar yanda ya buk'ata, kuma karki sake waiwayar gidannan harsai adadin abinda ya yanke miki yacika, nikuma zuwa sannan inamai tabbatar miki alk'awarin Dana d'auka yacika ko yana gab da cika".
" Amma momy.........".
"Karkice komai zuwairah, kedai kiyi yanda nace".
Jinjina kai Anty zuwairah tayi tana had'iye yawu mai kaurin tsiya, itafa lamarin momy yafara bata tsoro, wlhy tun kwanaki tafara tsarguwa dawasu lamura nata, takuma dulmiya zuciyarta cikin tunani lokacin data saka gwaggo bintu zama awajenta, anya kuwa momy bata aikata wani 6oyayyen Abu kuwa a 6oyewa?, to amma miyasa zatayi hakan?, kai zato zunubine aii".
Haka Anty zuwairah taita tunani tana had'a musu kaya.
Aranar sukaje airport itada mufeeda suka nemi jirgi, sunsami maizuwa Lagos, zaitashi 6:15pm, saida suka gama komai sannan suka dawo gida dansu ida shiryawa.
Momy tace, " Anty shikurah ma tasanarma mijinta yashirya musu jirgi nanda kwanaki uku sutafi.
"Momy mufa munzone danmu dad'e, inagama ni bazan komaba, dan wlhy nagaji dazaman wata k'asa, nafison zama a k'asata".
" Baku isaba shukurah, dolene Ku koma, bana buk'atar zamanki a k'asarnan, danhaka kishirya".
Uffan Anty shukurah batacema momyba.

___________________________

Ammah fa yau gaba d'aya takoma 6angaren su ya khaleel, har break fast d'intama can aka kaimata, zuwa sannan kuma ciwon ya khaleel ya karad'e gidan, tuni k'annensa suka fara turuwar zuwa dubashi, wannane yasaka Aysha watstsekwar dole, dan batason asakata a lissafin masu rashin lfyar.
Shimadai yaji d'an dama-dama Dan harya fito falo, inda Amman da Aysha da k'annensa ke zaune.
Sannu suka shiga yimasa da tambayar jikinsa, amsa musu yaytayi cikin yanayin rashin jin dad'in jiki, tsakaninsa da Aysha kam sai 'Yar satar kallon juna, dukda shid'in yakan kalleta kai tsayene wani lokacin, Amma itadai takasa kallonsa.
Anty Mamie dakanta tabashi abinci abaki, yana matuk'ar k'aunar matar, musamman yanda take tattalinsa da nuna masa k'auna irinta mahaifiya, wadda mahaifiyar tasama tagaza nuna masa koda mafi k'ank'antane, sarai taji bashida lfy, Amman tagaza koda lek'oshi sau d'ayane, hakama k'annensa da Anty zuwairah, sai Anty shukurah kawaice keta zarya, Amman momy tun zuwan safennan datayi bata kuma lek'owaba barema kiran wayarsa tasamu tabbacin bashida lfyar.
Anty Mamie kam da Ammah tun d'azun suke tsaye akansa, harda matarsa da Ammah kebama kulawa cikin hikima, Dan bata bada k'ofar da kowa zai fahimci ainahin abinda ya haddasa ciwon na khaleel ba, hakan yamasa dad'i, dan kobabu komai Ammah Tarufe sirrin aurensa da matarsa.
Kiran sallah yasaka Ammah da Anty Mamie mik'ewa, sai Anty Ama..., sauran yarankam yawanci duksun fita wajen aiki da school, Ummunoor, Nuriddin, da 'yan uku suna Kano tareda mama, kasancewar yara suna hutun makaranta, su tasleem ne kawai agida da maleeka, kasancewar bana suka kammala secondary d'insu.
Anty Mamie takalli Aysha dake kwance cikin kujera 1seat, tayi shiru, ko baki bata sakawa a firar tasu Ammah, ''Aysha tashi ki had'ama mijinki ruwa maid'an zafi yayi wanka, danya kuma samun k'arfin jikinsa kinjiko".
''To Mamie", 'Aysha tafad'a cikin jin kunya'.
Bayan fitarsu Anty Mamie falon yay tsit, saisu biyu kad'ai, kan Aysha ak'asa tamik'e tanufi d'akinsa dan cika umarnin Anty Mamie, binta yayi da kallo kawai harta shige d'akin, ya lumshe manyan idanunsa yana fesar da huci ta bakinsa.
Kunsan mintuna uku da shigarta shima yabi bayanta, tana cikin toilet, kayansa yafara cirewa, ya d'aura towul, tana shirin fitowa shikuma yashiga, karo sukayi ak'ofa, Aysha tayi saurin jada baya tana fad'in "sorry, wlhy bansan katahoba".
Idonta ak'asa take wannan maganar, dan wata matsananciyar kunyarsa takeji sosai ayau, shikam hard'e hannayensa yayi ak'irji yakafeta da mayun idanunsa masu tsoratar da mara gaskiya, fuskardai ba'a d'aure takeba, sannan ba murmushi yakeyiba, tana asakedai yanda mutum bazai tsorata dashiba🙂.
Ganin yak'i bata hanya tawuce tace, " ga ruwan nahad'a".
Bakinsa yad'an ta6e sannan ya warware hannunsa yana cije le6ensa na k'asa, k'ara matsowa yayi gab da ita ya tsaya, yasaka hannun damarsa yad'ago fuskarta, lumshe idanunta tayi, yasaki guntun murmushi yana k'arema zara-zaran gashin idonta kallo, suna matuk'ar d'aukar hankalinsa dasakashi a shauk'i suda kwantaccen gashin dake goshinta.
Ahankali yashiga hura mata iskar bakinsa saman idonta, far-far tafarayi da ido, dole tabud'esu batareda ta shiryaba, amma suncika da kwallah, ruwan hawayen saiya k'ara musu wani k'yalli mai d'aukar hankali, daga ita harshi anrasa mai tankawa.
Sakin fuskar tata yayi yajawota ya manna da jikinsa, ajiyar zuciya suka saki atare, yasaka hannu agadon bayanta yazuge zip d'in rigarta doguwa.
Cikin sauri tayi k'ok'arin raba jikinta da nasa, amma saiya kuma k'ank'ameta, saida yakai k'arshen zip d'in sannan yacirota dakansa, hannu yasaka akafad'unta zai zame hannuwan rigar tayi saurin dafe hannayensa.
Muryarta na rawa, dan tuni hawayen sun fara zuba, tace, ''please sallah zanje nayi fa".
"Uhhhhmm!"
Kawai yafad'a ya ture hannunta ya ida zare rigar gaba d'ayama, Aysha ta matse idanunta, hawayen masu d'umi suka zubo, baibi takantaba yacira bra d'inma, sannan yad'auketa cak yadire a kwamin wanka, shima yashige.
Haka akayi wannan wanka idon Aysha arufe, shiyayi kid'ansa yay rawarsa, harya gama yanad'ota a towul bayan yasakata yin alwala.
Mai yashafama kansa, sannan yajuyo ga Aysha dake zaune kamar gunki ido arufe, dariya tabashi amma baiyiba, yamatso kusada ita bayan yasaka k'ananun kaya ajikinsa, man yafara shafa mata, tana kakkaucewa har aka gama.
Yabud'e wadrob nashi ya d'akko doguwar riga Arabian gown, ita mamakin wad'annan kaya dayake fiddowa d'ai-d'ai takeyi, dakansa yasaka mata, takuwa yimata azabar k'yau, ta haskaka farar fatarta, sannan tamata cif tamkar an gwadata, ita kanta Aysha rigar ta birgeta sosai.

Nidai 'Yar rahotonku haushi yafara kamani😠, sai wani Abu sukeyi kamar kurame😏.

Sallar Azhur yajasu, bayan sun idar yajuyo yana kallonta, yajikinki? Yafad'a ahankali".
Cikin turo baki tace, "nidai lfyata lau, kainedai za'ace yajikinka?".
Baisan sanda yasaka guntun murmushi ba, yasa yatsansa ya d'alli bakinta data turo gaba.
Da sauri tasaka hannu tadafe bakin, saiga hawaye.
Jikinsa yajawota ya rungume, " kewai baki gajiya da shagwa6ane? Laififa kikayi na hukuntaki, to miye nakuma asarar hawayen? Ke kullum babu Abu mafi arha agareki irin hawaye?, waishi saunawa kikeyin kuka arana?".
Yay maganar yana d'ago fuskarta tareda zuba mata idanu.
Shiru tamasa tana kuma kwa6e fuska zatayi wani sabon kukan, "a'a nikarkimin kuka, tashi muje kibani abinci nasha magani, inga zuwa la'asar zan iya fita, inason naje office akan maganar yaran jiya dasuka shigo gidanan.
Kanta ta jinjina masa tana yunk'urin mik'ewa, da sauri yajawota tadawo saman cinyarsa, " magana zakimin dabaki, kinsan banason shariya".
Kallonsa tayi damamki, shi babu dad'i yakema mutane shariyar?, amma afili saitace to". 'Cikin sanyin murya'.
"Hummmm abin mamaki, waini yau kinzama ustaziyane?, kokuma wani salihancine yazo bayan biyan kaza?".
Kunyace takama Aysha, tacusa fuskarta a k'irjinsa tana dariya k'asa-k'asa.
Shima rungumeta yayi tsam yana sakin tattausan murmushi.
Daka gansu kasan suna matuk'ar farinciki da nishad'i na musamman................😂✍

*_inayinkufa wlhy🙋🏻‍, acigaba da gashi, suya sai anacin uban hajia babba♀😜_*

🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀babu ruwana karta kaini karuwanci turai, masoyan hajia babba amin afuwa😆🤭.

❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤💋💋💋💋
[9/18, 3:59 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_

*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.