Trending Hausa Novels

Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 2.txt

Chapter 48 of 52

*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_

_d'ingimemiyar gaisuwa ta iso agareku_
*_pherty xarah (ALLAH yakaimu ranar aurenki muzo sokoto musha shagali my kakus💃🏻🤸🏻‍♀) & Ummu Aysha (ALLAH ya kaimu ranar auren Aysha muyi rawar shaku-shaku😂🤸🏻‍♀)_*.

_ALLAH yak'aro muku haske a rubutunku kuma, ALLAH katsare k'ungiyar Haske dadukkan writers d'in dake cikinta 🤚🏻✋🏻, wannan shafin nakune gwarazan marubuta👍🏻👍🏻👍🏻_

4⃣8⃣

'Dakin taron tsit yake, da alama khaleel ake jira kawai, Dan kowa ya hallara, kayan hannunsa ya ajiye tareda had'e hannayensa waje d'aya alamar ban hak'uri da Lattin dayayi🙏🏻.
Duk manyansa ne awajen, shikad'aine k'aramima, kwazonsa da jajircewarsa akan aikice tasakasu shigo dashi cikin meeting d'in, Dan abinda za'a tattauna akai shine jigonsa.
Bayan bud'e taro da addu'oi suka fara abinda ya tarasu kai tsaye.
Jawabai sosai akayi, mafi yawa tashafi k'ungiyar su momyne kuma.
Khaleel aka bama damar tashi yayi jawabi akan nasarorin dasuka samu, dakuma abubuwan da aka kama k'ungiyar dasu.

Bayan khaleel yayi gaisuwar ban girma agaresu, yayi add'u'oi, sannan yafara jawabi cikin nutsuwa a harshen nasara ingilishi.

_"munkama mutane 57 dake cikin wannan k'ungiya, tareda bindugu 16, sai hodar ibilis (cocaine) datakai nauyin cg 1800,0 dawani abu, sannan akwai kwayoyi masu had'arin gaske suma masu yawa, saikuma yara 'yammata damuka ku6tar awani gida su 84, wasu acikinsu anyimusu viza za'abar k'asar dasu, akwai kuma 21 damuka samo a wasu k'asashe guda biyu"._
_har yanzun muna farautar kusan mutane 109 dake k'ashe daban-daban tareda yara kusan kimanin 800 da aka fitadasu tawasu hanyoyi daban-daban ak'asarnan. Akwai uku cikin wad'anda suke hannunmu suna kwance babu lfy acikin asibitinmu, saikuma 26 da suka mutu tawasu dalilai, wasu aciki mune muka harbesu, wasukuma sunmutune kawai, akwai mutum d'aya da aka bashi guba yamutu, Wanda munan muna bincike akan hakan, insha ALLAH kad'an garage mukawo sunayen masu hannu acikin kisan nashi."_
Saikuma mutun kusan 78 dawasu k'asashe suka samu kamawa 'yan Nigeria, wad'anda aka tabbatar sunada alak'a da k'ungiyar, suma munata k'ok'ari wajen ganin mun kar6osu, andawo dasu nan gida Nigeria ammusu hukunci dai-dai dalaifinsu. Da akwai mutane 13 ahannunmu dasuka fito daga k'ashen k'etare suma, wasu k'ashen suna buk'atar mubasu 'yan k'asarsu domin sumusu hukunci a k'ashensu, to badai muce musu komaiba har yanzu, munanan muna tattaunawa akan batun dai.
Saikuma jami'an tsaro dasuka fito a fannoni daban-daban guda 11 damuka samu cikin wad'an nan criminals, bincikenmu kuma ya tabbatar akwaima wad'ansu dabasu halarci wannan taronba aranar da'a kamasu, kuma gaskiya acikin manyane, dole saida had'inkan Ku za'a samu Damar kamasun, dukda akwai shirin damukeyi ta k'ark'ashin k'asa akansu.
Wannan shine bayanan da k'ungiyar tashafa, saikuma wad'anda basuda alak'a da k'ungiyar, muna shirin mik'a wasu kotu.
Suma d'in zamu shirya kaisu kotu acikin next week insha ALLAH.
AKWAI mutane uku dake hannun hukuma sss, d'aya d'an k'ungiyarne, biyu kuma laifinsu daban, munason suma subamusu danmu saka d'ayan cikin 'yan uwansa.
Yak'ame tareda salute Nasu Baki d'aya, sannan yadawo wajen zamansa ya zauna.

Gaba d'aya aka d'auki tafi, jikake raff raff raff!!!.

Lallai dolene hukumar police Interpol tamik'a gagarumin jinjina dayabo akan wannan gwarzon ma'aikaci nata, wannan hukuma da Nigeria harma da duniya baki d'aya bazasu ta6a mantawa da Ibraheem Abdallah ba, j! gwarzon ma'aikacine dayakamata ayi koyi dashi akowanne fanin d'ammara Na kaki, yakawomana nasarori masu yawan gaske, Wanda bamu kad'aibama duniya gaba d'aya dolene tayi alfahari dashi, yaje k'asashen duniya daban-daban yagudanar da aikinsa cikin nasarori, sannan wasu k'asashen sun gayyacesa domin taimakonsu duk Dan kwazonsane kuma, wannan k'ungiya damuke magana akanta ankai kusan shekaru 16 ana bincike akanta, amma bamu samu wani bakin zareba saida aikin yakoma hannun j!, jinjina agareka Ibraheem Abdallah, ALLAH yacigaba da haskaka rayuwarka kaji, ALLAH yasa ka d'ore ahaka kar watarana ka canja.
Gaba d'aya aka amsa da ameen.
Yacigaba da fad'in akwai ganawa da shugaban k'asa daza'ayi gobe a fadarsa, kowanne hukuma taza6i mutane uku dazasu wakilceta, sannan annad'a Wanda zaizama kwamitin shugabancin wannan zama baki d'aya.
Mudai anan J! Yana ciki, sannan kuma shine shugaban wannan kwamiti gaba d'aya dazai jagoranci wannan zama har fadar shugaban k'asa.

Nanma aka d'auki tafi gaba d'aya, kowa yayi na'am da hakan, saidai fuskar mutum biyu babu alamar sun amshi zancen, kuma koda khaleel yake bayani babu alamun jindad'in bayanan nasa, babu Wanda yakula da hakan sai khaleel da hankalinsa ke akan kowa, tunda dama yana zargin wasu manyansu acikin k'ungiyar, akwai guns kusan 6 acikin wad'anda suka kar6a duk Na jami'an tsarone, sannan ankama wasu acikinsu masu kaki.

Haka sukaita tattaunawa, kowa yana kawo albarkacin bakinsa, da hanyoyin dazasubi domin dak'ile ta addacin da'akeyi acikin gida da k'asashen k'etare ana zubarma da Nigeria mutuncinta.
Har 1:30pm suka kai ad'akin taron sannan aka tashi, amma khaleel yariga kowa fitowa, bama arufe taron dashiba yanemi excuse saboda time d'in sallah yayi, wad'anda suke musilmai awajen sai kunya Takamasu, dansu ko alamar tunawa da za'a shiga time d'in ibadarsu basu nunaba, saima k'ara 6ararrajewa suke suna sakin bayanai.
Shi dai khaleel yamusu sallam yafito, akan idan basu kammalaba har aka idar da sallah to zai dawo, idankuma sun tashi shikenan.

🙂👍🏻irinku mukeso khaleel masu girmama addininsu samada uzurorinsu Na duniya, wad'anda basa shakkar gudanar da ibadar aduk Inda suka tsinci kansu, masu kishin bautar ALLAH.

(Bawai ta addanci bane addini, Adinin musilinci ba addinin 'yan ta'adda baneba kamar yanda duniya take fad'a ahalin yanzun, duk Wanda kagani musilmi d'an ta adda to tabbas baya cikinmu, yana amfani dahakanne kawai domin kansa, sannan shid'in ru6a66en musulmine, mukuma maba d'aukarsa d'aya daga cikinmu, addininmu zaman lafiya da adalcin k'yautatawa junanmu yakoyar damu, yanunamana muhimmancin adalci gawad'anda bama addinimu d'ayaba, addinin musilinci adalin addinine, dake koyar damu k'yawawan ayyuka, sannan addinine mai sauk'i, danhaka duk wani d'an ta'adda dazai kira kansa musilmi munce k'aryane, shiba mabiyin addininmu baneba, ISLAM IS THE BEST RELIGION💪😭.

Wlhy iyaye Ku kula sosai akan films da 'ya'yanmu suke kallo, musamman wad'anda ake nuna Muslim's amatsayin 'yan ta'adda, yaranmu kwakwalwarsu k'aramace, komai suka gani zasu iya d'auka hakane dai-dai, ALLAH yasa mugane.🤚🏻✋🏻😭

_____________

Koda aka fito sallah yaga sunfito saiya wuce office, zamansa babu dad'ewa youseef yay knocking d'in k'ofar, izinin shigowa yabashi.
Ya k'ame tareda yin salute Na ya khaleel.
Kansa ya jinjina masa sannan yamasa alamar ya zauna, bayan ya zauna khaleel yamik'o masa hannu sukayi musabaha🤝🏻.
Takardun dake hannunsa yamik'a masa, sir! ga wad'annan bayanan, mun tattarasu duka, insha ALLAH komai zaka samu. Maganar Munner kuma munata bibiyarsa ta number d'insa, haryanzu kuma yana cikin abujarnan. Saidai yayi wata waya damukayi recording ". 'Yay maganar yana mik'a masa k'aramar wayarsa.'
Kar6a khaleel yayi yakunna record d'in yana saurara. bayan yagama saurare yamik'ama youseef wayar yana furzar da isaka.
" naji youseef, shima zaibi jirgin 6:30pm ne zuwa Kano, kiramin Adams".
''OK sir".
Babu dad'ewa saiga Adams, cikin girmamawa yace, "gani sir".
''Ok, uhm dama inason naji katanadar mana jirginne?".
" yes sir!".

"Uhm Na k'arfe nawa?".
" 6:30pm".
"OK, bama saimunje kanoba, zamu kamashi a airport kawai. youseef kiramin Joseph, kace yayi shiri kune zakuje kama Munner, zuwa 6pm kaidashi Ku tabbatar kunzagaye airport, kaga insha ALLAH kafin akira sallar magriba kun gama da matsalar".
" babu damuwa sir, barama naje nasamu Joseph d'in a office, amma sir danazone please akan hajia, kadaure muje ka ganta, kullum saita ambaci sunank.........
Kasa k'arasawa youseef yayi, saboda wani mugun kallo da khaleel ya watsa masa.
🙏🏻" ALLAH ya huci zuciyarka sir".
Khaleel baice komaiba ya kauda kansa daga kallon youseef d'in.
Jiki a sanyaye youseef yamik'e, yay salute nashi sannan yafice.
Adams natsaye baice komaiba dai, amma shima yanason yarok'eshi akan yaje d'in, saidai yana shakka.
d'ago ido khaleel yay ya kalleshi, "akwai damuwane". 'Ya tambayi Adams yana maida idonsa a kan computer dayake latsawa'.
" a'a sir!, amma........
......Amman mi? Indai akantane karkacemin komai".
Yak'atseshi da Sauri.
Wani yawu Adams ya had'iye tareda girgiza kansa, shima saiyayi salute nashi yafice.

Binsa da kallo khaleel yayi, ya sauke numfashi tareda dafe kansa, ahankali yafurta momy kingama da rayuwata, ALLAH ne kawai kerik'e da zuciyata, amma datuni ta tarwatse☹✊🏻.

Agurguje inji Perty😉

********
Alhmdlh aranar su Youseef sunsami nasarar cafke Munner, kuma cikin sauk'i da nasarori.

****

Kusan 8pm khaleel yakoma gida, saida yafara shiga cikin gidan, Dan yanaso su gaisa dasu Anty Mamie, yau yafita da wuri basu gaisaba.
K'annensa suna falon, harsu Hasnah, fira suketayi, su Affan naganin khaleel suka taso da gudu sukamasa oyoyo, rungumesu yayi shima yana farincikin ganinsu, d'ai-d'ai yabisu ya sumbaci kumatunsu, shima duk haka suka sumbaceshi.
Manyan kuma suka gaidashi. Da 'Yar sakin fuska ya amsa, yabisu da kallo d'ai-d'ai amma babu Aysha.
"Su mamafa?". 'Yay maganar idonsa akansu'.

" mama sunfita itada baffah, ummi Amarya kuma kanta ke ciwo ta kwanta, Anty Mamie tana d'aki itama."
Batareda yace komaiba yanufi d'akin Anty Mamie, saida yay knocking tabashi izinin Shiga sannan yatura k'ofar yashiga da sallama.
Da Aysha yafara cin karo zaune kusada Anty Mamie tana bata dambu abaki.
Suduka idonsu nakansa, duk suka masa sannu da zuwa.
A sanyaye ya amsa yanamaijin k'aunar mahaifiyarsa har cikin ransa. K'arasowa yayi ya zauna d'ayan gefen Anty Mamie shima.
"Babana andawo?".
Kansa ya jinjina mata, ya d'ora kan nasa agefen kafad'arta yana kallon Aysha, yace, " Mamie kidaina shagwa6a yarinyarnan, jiyafa ta6ara taitamin iri-iri."
Aysha tad'an murgud'a masa baki, tana fad'in "jealousy kawai".
Anty Mamie kam 'Yar dariya tayi, " babana aidolene Na shagwa6ata, bakaga ba ita kad'ai baceba, yanzu hakama abinci taci tayi amansa, shine matar zunnurain tayi dambu takawo mata, inad'an lalla6atane tanaci".
Rankwashi khaleel yamata agefen kanta, takuwa kware baki ta zabga k'ara tareda dafe kanta.
Da sauri Anty Mamie ta rungumota jikinta, shima tamasa rankwashi biyu akansa.
Dafe wajen yayi yana fad'in "uchhhh, dazafi wlhy Mamie".
" oooh kasan dazafin amma kama yarinyata? duk wata mugunta ka iyata babana salo-salo ko?".
"ALLAH Anty Mamie yarinyarnan batada kunya, kigafa murgud'en takemin harda gwalo? kibarni kawai Na caskalata".
Cikin 'Yar dariya Anty Mamie tamik'e daga tsakkiyarsu, ''kunga kutashi kuje 6angarenku, bazan iyaba dawannan rikicin, kuje wajan Ammah Tamuku shari'a".
" uhm tab, lallai Anty Mamie, yanzu naje wajan jar wuya aii bakina saiyaje gate, dama haushina takeji nak'i saya mata mota.
"Hhh kunfi kusa aii".
Jakkarsa Aysha tad'auka tafita tana dariya, tabarsu dansud'an gana.
Binta khaleel yayi da kallo yana murmuahi da jinjina hankali irin nata, yamaido kallonsa ga mahaifiyar tasa, wadda itama ayshan tabi da kallo murmushi d'aukeda fuskarta.
Khaleel yamatso kusada Anty Mamie, hannunta Na dama yakama ya sumbata, sannan yad'auki hannun yad'ora bisa kanta, murya amarairaice yace, " Mamie Na kisamin albarka, a office an za6eni cikin wad'anda zasu gana da shigaban k'asa gobe idan ALLAH ya kaimu, kuma nine shugaban dazai jagoranci kwamitin ma, wlhy duk fargaba tacikani, tunda safe naketa tattara bayanan dazanyi agaban shugaban k'asa ina kwancewa, narasa wanne zan d'auka, gashi inason kai kukana akan manyanmu danake zargi da hannu a k'ungiyar su momy."
Murmuahi Mamie tayi, tashafa fuskarsa da d'ayan hannunta, murya a sanyaye tace, ''karkakji tsoro babana, nasan kaid'in jarumine kuma jajurtacce, kasaka aranka CIKI DA GASKIYA, WUK'A BATA HUDASHI, shugaban k'asa mutumne kamar kowa shima kuma yanada sauk'in kai, danhaka karkaji tsoro ko shakkar ganawa dashi, katuna bayaune kafara ganawa da shugabannin k'asashen duniyaba."
"Duk inda kake addu'ata nabiye dakai, ALLAH ya albarkaci rayuwarku, yatsareminku aduk inda kuka tsinci kanku, kaje kayi wanka kahuta danka samu isashshen lokacin kanka".
" idonsa cikeda kwallah yace amin Mamana, farincikina, haske mai haska rayuwata, ALLAH yak'ara tsawon rai mai amfani da ingattacciyar lafiya", 'yak'are maganar da sumbatar hannunta'.
Jiki a sanyaye yamata sallama yafice.
Hawayenta tashare, tana murmushi, ahankali tace, "ALLAH Na gode maka".

6angarensu yanufa, dan baiga Aysha ananba, yasan tawuce.

Agurguje😎

___________________

Washe gari su khaleel suka samu damar ganawa da shugaban k'asa, sunsami tarba mai k'yau daga fadar shugaban k'asa, sunkuma tattauna muhimman abubuwa dazasu kawo cigaban k'asa, dakuma yanda za'a dak'ile ta'addancin dake faruwa ak'asarnan.
Sund'au tsawon awanni kusan 5 taredashi, tarema sukayi lunch da president da tawagarsa, yamusu jinjinar bangirma tareda k'yaututtuka masu k'yau, musamman ma khaleel saboda k'ok'arinsa, sannan suka gana da 'yan jaridu Na awa d'aya.
Sunyi sallama da shugaban k'asa suka tafi, bayan khaleel yabama wani makusancin shugaban k'asar short note domin yabashi.😎👍🏻

________________

Akwana atashi babu wahala wajen ubangiji, kwanaki Na Sauri sati Na gudu, watani tamkar sati ya koma.
Acikin wannan gudun fanfalak'e da suniya takeyi yau ga cikin Aysha yashiga watanni takwas.
Abubuwa masu yawan gaske sunfaru awannan tsakanin, ciki harda kammala bautar k'asa da Aysha tayi, (Nysc) Alhmdlh tagama cikin nasarori.
Rufaida da sadiya duksun haihu, Aysha kuma taje har Kano suna, kwannta 8 a can, saboda khaleel baya k'asar alokacin, amma da k'yar yabarta taje.
Matar youseef ma ta haihu baby boy itama, hakama bishirah, ta haihu, da k'yar khaleel ya yarda Aysha tabi gwaggo bintu sukaje suleja suka mata barka.

Mufeedah ma baiwar ALLAH, anata Jan ciki, ita harma tashiga watan haihuwarta.

Ansaka bikinsu hasnah, watanni hud'u kacal, harda musleem dasu maleekah ma, baffah yace gwamma ya aurar dasu kawai yahuta baki d'aya, yazauna da 'yan k'ananun 'ya'yansa su ummunoor.

*******
Momy dai ana nan anata shan jinya, amma jikin NATA da sauk'i, saboda tana samun kulawa, Idan tayi magana anaji yanzu, sannan tana motsa hannunta kad'an-kad'an.
da k'yar khaleel ya yarda yashiga ya ganta tana barcima lokacin, danhaka batasan yajeba, yafad'ama su baffah suma sunje sun ganta.
Babu wanda bai zubar mata da kwallaba ganin yanda duk ta lalace, ta canja kamanni kamar ba itaba, k'ibarnan dukta zube.
Hawaye taita zurarrwa saboda ganinsu, magana take amma basajin mitake fad'a, dole suka hak'ura.

Saida Baffah yayta lallashi daban magana sannan khaleel yayarda yasakko innah jummai, amma da yasaka anyi rammm da ita a station d'in su, yace anan zata k'are sauran rayuwarta.
Saida k'yar da lallashi yayarda yasakota.
Rasa inda zata nufa tayi kuwa, doledai tadawo gidan mak'iyar tata Ammah, suna zaune awani yammaci kawai saigata tamkar an jehota.

ALLAH Sarki d'an uwa mai dad'i, saiga Ammah takar6eta da hannu bibiyu, suka rungume juna suna kuka, daneman yafiyar juna.
Annan innah jummai tazauna sabodama batada isashshiyar lafiya, ciwon k'afa da hawan jini.😏

____________

Su khaleel duksun gama shirye-shiryen kai k'ungiyar su momy kotu, sunsami nasarar cafke sauran mutanen dasuke zargi, dakuma kar6o Na k'asashen k'etare, ciki harda manya-manyan mutane wad'andama bazaka ta6a tunanin akwai saka hannunsuba............✍🏻

🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀kumuje zuwa yanda zata kaya a kotu, dolene masu laifi su kar6i hukuncinsu ahannu😎🖐🏽.

🤕yanzu saboda buk yazo k'arshe, ankama muku hajia babba shine babu comments ko, aiko zan ajiye nak'i k'arasa typing d'in😎, rashin comments d'inkuma yasakani jin gandar typing d'in wlhy,☹.
Idan naga ruwan comments yau, kwaji yanda takaya gobe, idan naji shiru, nima nawuni barci abuna yafimin dad'i😏😏.

Yawan comments, yawan girman hukuncin su hajia babba😎😎😎👯‍♀

*_I love you all_*💋💋💋💋
[10/26, 4:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.