Trending Hausa Novels

Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 2.txt

Chapter 6 of 52

*_part 2_*
(littafi na biyu📕)

5⃣

Zama yayi kujerar dake kallonta, momy barka da dare.
Adak'ile tace barka.
Shiru babu Wanda yasake cewa uffan, hajia babba sai cika takeyi tana batsewa, Dan jitake tamkar karta amince da shawarar hajia khaltume, amma kuma wani 6angare Na zuciyarta Na nunamata hakan shine dai-dai.
Ta saci kallon khaleel d'in Wanda idonsa ke kan TV, amma azahirin gaskiya yana nazarin momyne.....
Ibraheem!!.
Na'am momy! Ya amsa yana maido kallonsa akanta.
Na amince da aurenka, amma da sharad'i.
Shiru yayi yana saurarenta, gakuma maganar tata ta dakesa, Dan baiyi tunanin yardarta da wuri hakaba.
Amma momy miyasa kika amice? Miye kuma sharad'in?.
Karka damu da dalilin amincewata, wannan sirri nane, sharad'in kuma shine nangaba zaka auri Aleeya itama.
Wani guntun murmushi yayi, Wanda yafi kuka ciwo, ya kauda kai daga kallonta yana cije le6ensa Na k'asa, babu damuwa momy ALLAH yaza6a mana abinda yafi alkairi.
Tsura masa idanu tayi cikeda mamakinsa, ko kad'an batayi zaton taurin kansa zai saka ya aminceba cikin sauk'i, anya kuwa bawani Abu yaronnan yake shiryawaba? Koda yake ance basu kama barau modibbo ba.
Yana kallon, kallon da momy kemasa da gefen idonsa, aransa yay k'aramar dariya, yana fad'in momy kenan, *'DAN HAKKIN DAKA RAINAFA....* shike tsone maka ido watarana.
Afili kuma yace momy kokinada damuwane?.
A'a Ibraheem babu komai, amma yanzu ina zaka zauna?.
Zan zauna inda gidana Na Asokoro.
A'a kazauna anan gidan, kaima indasu mujahedeen sukayi gini.
Miyasa momy? Kefa kikace bakiso Na zauna agidannan da matana idan nayi aure, miyasa kuma yanzu zaki canja?.
Haka kawai.
Ananma dariya yayi azuciyarsa, afili kuma yace shikenan momy duk yanda kikeso haka za'ayi to.
Farin cikine ya lullu6e kasan ranta, Dan ganin duk abinda tace baya mata musu.
Daga nan tasaki fuska sukad'an ta6a hira, cikin hikima irinnansu Na manya take sako masa tambayoyi akan aikinsa.
Amsa yake bata kai tsaye batareda tunanin miye manufartaba.
Itakam dad'i takeji yau tasami Ibraheem yanda takeso.

___________________________
Washe gari girkin mama, bayan tagama had'ama baffah breakfast agabansa tace Alhaji su Aysha zasu koma gida zuwa jibe idan ALLAH ya kaimu, Dan fadeelah zata koma d'akinta mijinta NATA waya.
d'ago idanunsa yayi yana kallon mama, baice komaiba yacigaba dacin abincinsa, saida ya mammala tsaf sannan ya fuskanceta sosai, fad'ima fadila ce kawai zata koma, amma Aysha tazo kenan, Dan bilyamin yabani, ita kanta fadeelah badan aure takeba da babu inda zataje, akoda yaushe inaso ki gane sud'in y'ay'a nane koda banine mahaifinsuba, inajinsu azuciyata tamkar su Mu'azzam wlhy.
Yanzu haka zancennan danake miki angama komai akan bautar k'asar Aysha (NYSCE) insha ALLAH k'arshen watannan zata fara, anan kusadamu. Dan munyi sa'a abin yazo daidai daza'a d'auki sababbi.
Hawayene suka cika idonmama saikuma taji kunyar abinda tayi, cikin hikima tabama baffah hak'uri.
Murmushi yayi tareda jawota jikinsa ya rungume yana fad'in babu komai first love d'ina, Dan bakisan irin matsayin dakike dashiba azuciyar Abdallah bane shiyyasa kike Raba d'aya biyu, amma namiki uzuri, daga yau karki sake.
Dad'ine ya lullu6e mama, Dan itama tana k'aunar mijin NATA, tak'ara k'ank'ameshi da k'yau kamar mai gudun kar'a kwace matashi.

🏃‍♀a 100 nafito, Dan lamarin yafi k'arfina, wannan fagen Na manyane😂 irinsu baffah😉.

_____________
Akwana atashi babu wuya wajen ubangiji, rayuwa tanata tafiya, yau kusan watanni uku kenan da saka bikin ya khaleel da Aysha.
Saidai babu mai shiga harkar wani shida Aysha, ita bautar k'asar datakeyi ya d'aukema hankalinta gaba d'aya.
Shikam yawon k'asashensa yahanashi zama waje d'ayama.
Yanzu haka yana Mexico kusan kwanaki 13 kenan, daga nanma France zai sauka a gaba d'aya headquarters d'insu dake Lyon city, sosai aiki ya d'auke hankalinsa a y'an kwankinnan, shiyyasama yakan manta dawata aba Aysha, dama ko number d'inta bashida ita, koyayi waya dasu mama kuma baita6a cewa abataba.
Ya gyara kwanciyarsa yana mai tunanin yanda rayuwar aure zata d'ore babu soyayyar juna.
K'aramin tsaki yayi, lokacin daya tuno rashin kunyar yarinyar, yatuna bakinnan nata maikama Dana tsuntsu dake masa murgud'e, kwafa yayi tareda fad'in zan kama kine aii afili.

Araina nace batama San kanayiba😂.

Aysha kam soyayyar ya khaleel Na nan mak'ale aranta, amma tana danne abinta, tareda nuna halin ko inkula akansa, ga cin kashin da y'ay'an hajia babba kemata da habaici akan auren, ita kanta hajia babba ba d'aga mata k'afa takeyiba.
Hakan baya damunta Dan aganinta kad'an yarage tayi maganin uwarsuma ba suba.
Anty zuwairah ma tazo ta tata tsiya agidan dantaga baffah bayanan, babu cin mutunci dabatayima mama da Aysha ba, saida Ammah tamata tas sannan tabar gidan, tabi jirgi zuwa Lagos Dan tasan gidan bazai kwanu agaretaba, saboda ranar Baffah zai dawo daga Turkey.
Sauran yaran kuwa kowa murna yakeyi ya khaleel zaiyi aure, zaikuma auri wacce suka Sani, amma ak'asan ran Zunnurain da musleem sunji babu dad'i, dansun k'yasa Aysha gaskiya😉.

🤣nace boss yamusu wawaso😜

*_2weeks ago_*

Misalin 5pm Aysha tafe a hanya, sanye take cikin wando da riga Na Nysce, bak'armin k'yau kayan sukai mataba, tasak'a k'aramin jijjab fari daya k'awata k'yawun haibarta, ta d'aure rigar saman kayan a k'ugunta, tafe take cikin nutsuwarta bayanta rataye da schoolbag, dolene ka kalleta kasake kallo, dukda yanayinta ya nuna a tsorace take.
Kad'an kad'an takan kalli sararin samaniyar dayay murutuk alamun hadari ya had'u bana wasaba, kuma ruwa zai iya sauka akowane lokaci, kullum driver ke kawota, idan lokacin tashinsu yayi takirasa ya d'auketa, amma yau takirasa wayarsa arufe, itakuma batason yin dare awaje Dan baffah bayaso, wannan dalilin yasakata hawan napep, saidai sunkusa shigiwa layinsu napep d'in yasamu matsala, ganin zata 6ata lokaci tace bara ta k'arasa kawai ak'afa Dan babu nisa, tama d'an tada jininta.
Tafiya tafara dad'an sassarfa saboda iska tafara kad'awa alamun hadarin yafara tasowa, kuka da Neman taimako tafaraji ad'an nesa da ita kad'an, tafara waige-waige damson ganin mai Neman taimakon?.
Saitin inda takejin kukan sosai matso, garadan samari biyu tagani suna k'ok'arin tura wata budurwa a mota.
Inadanu tazaro waje, tuni wata jarumta tazo mata Dan ganin harsun gama turata mota, d'aya nashirin cire wando, da alama ma amotar suke shirin keta mata haddi, Aysha ta waiga ko ina babu alamar mutum, kowa yashige gida, Dana birnin Abuja dawuya kaga mutane nayawo ak'afa hakanan, ga anguwar dama babu yawan gidaje sai kamfanonu, zuwa yanzu kuma antashi aiki, wani k'arfe ta d'auka a gefen titin, cikin sand'a tak'arasa wajen motar, mai cire wando dahar ya danne d'iyar mutane yana shirin afka mata ta kwalama k'arfen a k'afarsa data fito waje.
Azabace tasakashi sakin gigitacciyar k'ara, adaidai nan kuma ruwa ya sakko.
d'an daya toshe bakin yarinyar Dan hanata ihu yay saurin sakinta yana fad'in Arfan miya farune? Da sauri yazagayo garesa, ganin Aysha da k'arfe a hannu tana k'ok'arin jawo yarinyar dazasuma fyad'en yace kutumelesi, mikika masa? Wlhy yau sainayi kaca-kaca dake, yay maganar yana damk'e hannun Aysha.
Ihu Aysha tafarayi, Wanda takwalama k'arfen shima yataso yana d'ingishi, aii wlhy yau yarinya sai munmiki abinda bazaki sake moruwaba aduniya, ki yankemin jin dad'i sannan ki kwalamin Abu, aii saina fanshe ajikinki Dan ubanki.
Suka fara k'ok'arin cire hijjab d'in Aysha.
Hankalin budurwarnan yatashi, ganin Aysha ta taimaketa kuma abin ya juya kanta, rasa mizatayi musu tayi, sai kawai takwasa aguje babbar hanya tana kuka dafad'in a taimaketa....
Emanuel! Kamar yarinya nake hange agabanmu tana kuka?....
Eh sir, ammafa Baka tunanin ko wasune suka d'ana mama tarko....
Ya khaleel dake zaune abaya yanata danna lap-top nashi yace mike faruwane Adams?.
Babu komai sir, dama wata yarinyace gatacan mund'an wuceta take kuka, shine nace koza'a taimaketa, Emanuel yakecewa k'ila tarkon mak'iyane.
Da Sauri ya khaleel yajuya yana kallon bayansu, hango yarinyar yayi tana kuka da gudu tana tsaida motoci, amma babu mai k'ok'arin tsayawa.
Emanuel!!! Mujiya, ya khaleel yay maganar cikin matuk'ar tsawa.
Aii babu shiru Ema yajuya kan motarsa, sauran motocin suka biyo bayansa.
Agabanta suka taka birki, tana ganin haka tabud'e k'ofar baya dasauri tana fad'in Ku taimaka zasu keta mutuncinta, please yayana kataimakeni karsu cutar da ita.
Ya khaleel yatsura mata idanu yanason gano ainahin gaskiyarta, ganin yanda take yasakashi gaskatata, da Sauri yafito amotar batareda ya kula umbrella d'in da Adams yasaka masaba saboda ruwan yafara k'arfi.
Ita kanta batasan tarik'e hannunsaba tana jansa saboda kid'imewar datayi.
Sun k'araso lokacin da samarin ke kokawar cirema Aysha dogon wandonta, amma tarik'e kam tahana, d'ayan sai marinta yakeyi amma tak'i saki, mamakin taurin kanta sukeyi da k'arfi, farar fuskarnan tayi jajur saboda mari, garuwan sama ya jik'asu.
Bai tsaya bin ba'asiba yahau jibgarsu.
Aysha tamik'e da Sauri tana kuka, ganin ya khaleel yasakata zuwa da sauri Inda yake ta k'ank'amesa tana kuka da fad'in ka taimakeni ya khaleel zasu cutar dani, karka barsu, azzalumaine su.....
Gaba d'aya arikice take, sai yanzu ya khaleel yaga Aysha, hankalinsane Yakuma tashi, danhaka ya tureta daga jikinsa tareda damk'osu ya gwara kansu, dukansu yakeyi afusace, dak'yar securitys d'insa suka kwacesu, dansunga zaiyi kisankai.
Abirkice yajuyo kan Aysha dake gefe tana mak'yar k'yar sanyi, Dan ruwa aketa tsulawa kamar da bakin kwarya, mari ya falla mata, yana fad'in ubanmi yakawoki nan wajen?!!, nace miya kawoki?!!!!!!!.
Cikin matuk'ar tsawa yayi maganar, Dan harsu Adams saida suka zabura Dan tsoro.
Aysha tarik'e kumatunta tana matsawa baya saboda tsawar daya daka mata, wani Marin Yakuma kai mata Adams yatareshi yana fad'in please sir cool dawn.
Ya cije le6ensa tareda kuma kaimata duka saikuma yafasa ya rumtse hannun yana ciza la66ansa da k'arfi, jiyake tamkar ya had'iye zuciya awajen, ransa amatuk'ar 6ace yake, ya tura hannunsa d'aya a aljihun wandon oxblood d'in suit nasa, dasuka gama jik'ewa da ruwa, idanunsa sunyi jajur, ya watsama Aysha harara yana fad'in Adams kallafa kaga wajennan?, shin miya kawo yarinyarnan har suke shirin k'etaramin gonata? batareda ni Nayi koda gewayentaba?.
Yanzu dabamuzoba mikake tunanin zai farune? Mutuncinafa zasu Shiga saboda Mara hankalin yarinyarnan, Na mauje tama nahuta da ganinta.
Yay maganar yana ture Adams gefe tareda kaima Aysha wawura.
Yanzunma Adams kuma tareshi yayi, dukda bai fahimci zancen ogan nasaba, Dan baisan alak'arsama da yarinyarba.
Budurwannan ne tak'araso tana kuka dabama ya khaleel d'in hak'uri, tamasa bayani akan balaifin ayshar baneba, taimakonta tazoyi, itama a d'aya daga kamfanin take aiki, motartace tasamu matsala, daga Neman taimakonsu shine suke shirin mata fyad'e, Aysha ce ta taimaketa.
Zuciyarsa tad'anyi sanyi, amma bai huceba, Dan saiyaji ubanwa yasakata biyo hanyarnanma mai had'ari?, ina drivers d'in dake gidansu? Dahar ta taho ak'asa.
Ya watsa mata harara dayin kwafa, rigar suit d'insa yazare ya jefa mata, saboda farar rigarta ruwa yajik'ata dukta nuna jikinta, har kalar bra d'inta ana gani.
Jikin Aysha Na rawa tad'auka tasaka, dama Duk kunya tagama isarta.

Dariya nayi azuciyata, Dan hannun rigar yamata tsawo, gata tayi tsumu arigar kamar antsamo zomo aruwa🤣🤣.
Da kansa ya tattara kayanta, bag d'inta da hijjab, sai lemon green d'in rigarta data d'aure k'ugu, ijjab d'in yakuma jefa mata tasaka, dukda gyararren gashinta data d'aure a tsakkiya yagama jik'ewa jalab da ruwa bar d'iga yakeyi.
Yadaka mata tsawa, bazaki shige mujeba saina 6alla kasuuswanki anan......
Bata bari yak'arasa ta zuba dagudu, saida batasan motar dazata shigaba, dolene tajira ya k'araso.
Samuel karaka wannan yarinyar, kukuma Auwal ajeda yarannan kucimin ubansu dai-dai gwargwado, Adams kumuje.
Atare suka amsa,, aka kwashi samarinan dasuka gama fita hayyacinsu saboda duka.
Yana hararta yabud'e mata mota tashiga, sannan yazagaya Inda Adams yabud'e MASA shima yashiga shima.........✍🏿

💋💋💋💋💋
[9/6, 9:21 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_

*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.