Maradams Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: MARADAMS book 2 by Aysha A Bagudo.txt
Chapter 11 of 14
Page 19
Sosai mami ta dinga rarrashin maryam tana masu addua “allah ya daidaita tsakaninku ,Allah ya saka tausayinki acikin zuciyar adamcy ,allah ya kawo zaman lafiya a tsakaninku har qarshen rayuwarku “ahankali maryam Ke amsawa da “Ameen mami ,sai abu na gaba maryam na fahimci kina sakaci da addua ,Ina son kinsan wani abu ba’a nasara sai an rike Allah,idan ka rike Allah,Allah ta’ala zai taimakeka ki jajurce da adduoi maryam “ki rage wasu abubuwa ki maida lamarinki zuwa ga Allah maryam ta gyad’a mata kai alamun taji ,tana nan kwance ajikin mami har ta fara gyangyad’i alamun bacci .ahankali mami ta d’an buga bayanta tana cewa “maryam kwanta kiyi bacci da sannu allah zai kawo mana saukin wannan tashin hankali sannan ya kawo fahimtar juna a tsakaninki da mijinki .“maryam ta tashi daga jikin mami tana shafa idanunta sannan ta zame ta kwanta zuciyarta cike da soyayyar mijinta mami ta mike itama ta samu gurin nan kusa da maryam ta kwanta sai dai ita sam bacci yaki d’aukarta, kwakwaluwarta ne ya shiga cajin tunani
dan dole tasan abun yi tun kafin adamcy ya kashe maryam da bakincikinsa dan zuwa yanzu hakurinta ya fara qarewa akanshi .”
Juyi kawai mami take akan katifa kafin ahankali ta taashi ta sauko daga saman katifa ta tsaya gaban maryam tana kallon fuskarta bacci take, sai dai kana kallonta zaka san a matuqar wahale take baccin dan kana kallon yadda take sauke numfashi da ajiyar zuciya da karfi .”d’auke kwayar idanunta mami tayi ta fara zagaye d’akin kafin ta fara zance zuci ita kad’ai “dan dole zulai kiyi wani abu akan zaman ya’yanki “ to mai zanyi ?mai zanyi ? ta tambayi kanta har sau biyu tana cure hannuwanta waje d’aya “Kiyi qoqari adamcy ya kusanci maryam ko Allah zai basu rabo wata killa sanadiyyar hakan ya sauko ya sausauta mata ya rungume aurensu. “tabbas haka zakiyi zuciyarta ta bata wannan shawarar “to ta yaya zan masa magana ya fahimci abinda nake nufi ?”ta sake jefawa kwakwaluwarta tambaya shiru tayi yayinda ta koma ta kwanta akan katifa tana sauke numfashi tana mai sake had’e hannuwanta guri d’aya kafin ahankali ta soma sakin wani irin murmushi sakamakon abinda zuciyarta ta shirya mata wanda zai kawo mata saukin al’amuran ta, alokaci d’aya ta sauke wani naunayen ajiyar zuciya “dole dai kina bukatar shawarar shahida kafin ki aikata komai .”
Washegari da misalin karfe tara na safe maryam tana zaune akan kujerar sofa tana danna waya yayinda mami ke zaune akan salayya tana lazimi ATA ya shigo bakinsa d’auke da sallama sallamarsa kawai maryam ta amsa batare da ta kallesa ba ta cigaba da daddanna wayarta shima ko kallonta bai yi ba ya cigaba da tsayuwa mami ta d’an kallesa yana sanye da jallabiya yayi mata kyau sosai sai dai bata jin dadin ganin yadda ko yaushe fuskar nan tashi take a had’e’ ,sannan bata jin dadin ganin shi da maryam haka zaman su sam babu sha’awa kana ganin yanayinsu kasan gabad’aya zukatansu basa cikin walwala da jin dadi most especially adamcy wanda zaka fahimci baya son ko bisa kuskure ya kasance a duk inda maryam take .yayinda ita kuma tafi qaunar su kasance tare akoda yaushe ya rungumeta babu kyama ,mami na kallonsa ya juya cikin takun isa ya fita daga d’akin ganin tana lazimi ,bayansa mrym tabi da kallo har ya fice gabad’aya tasa hannu d’aya ta dafe goshinta tana jin wani tuttukin bakinciki tana jin zafi da ciwon abinda yake mata na kyarma da rashin son kallonta inda take ,amman ita ta rasa dalilin da yasa zuciyarta kullum take sake macewa akanshi ,a kullum zata d’aura kwayar idanunta akanshi to wallahi son shi da qaunarsa ne Ke sake huda zuciyarta da gangar jikinta” zata so ta mallakesa kamar yadda mahaifiyarta take buri amman hakan taki samuwa kullum babu abinda take hangowa attare dashi sai zallar qiyayyarta sam komai nata baya burgesa ita kuwa kwarjininsa kesa bata iya d’aukarwa kanta mataki ,bata iya tunkurarsa da komai tana matuqar jin tsoronsa aranta “da sanyi jiki mami ta qaraso inda take zaune ta kai hannunta ta dafata, ta d’ago tana duban mami da idanunta dake cike da ruwan hawaye mami tasa gefen hijab dinta ta goge mata hawayen da suka zubo mata batare da saninta ba wani wahallen ajiyar zuciya ta sauke tana kawar da fuskarta gefe“
“maryam !”
Mami ta kira sunanta ahankali maryam ta waigo inda mami take ta sake zuba mata idanunta tana kallonta fuskarta da tsananin damuwa ahankali ta sauke idanunta “ki daina damun kanki akan adamcy idan ba haka ba zaki rasa lafiyarki idan hakan kuma ta kasance babu ruwansa hasalima bazai ta’ba zama damuwarsa ba sai dai ta zama damuwarmu “kiyi hakuri ki dinga kawar da damuwar nan aranki sannan ki dinga kaiwa allah kukanki ,nasani maryam kina hakurin zama da adamcy ne saboda Kina matuqar ganin girmana da mutuntani da kuma qaunar da Kike masa nima kuma haka ne acikin zuciyata maryam ina qaunarki ina qaunar ku kasance a inuwa d’aya dashi .”numfashi ta sauke da karfi tana kallon mami “eh shine ma dalilin da yasa bakya son na rabaku maryam .
Maryam ta tsurawa mami idanunta “ko karya ne bakya sonsa ?zazzafan numfashi maryam ta sauke ta kasa cewa komai dan tasan gsky mami ta fad’a “kina dai danne sonshi ne saboda rashin qaunar da yake nuna miki amman ni naji ajikina kina qaunar adamcy ,maryam taji dadin yadda mami ta fahimci hakan sai dai kuma zuciyarta tayi rauni wasu sabbin hawaye suka zubo mata mami ta sake share mata “kuka bayayi miki kyau maryam hakan ya sake karya wa maryam gwaiwa ta fashe da wani kuka sosai .“wallahi mami ban san lokacin da son shi ya shigeni ba “nice silarsa maryam kuma nayi danasani had’aku aure ,mami ta fad’a da matsanancin tausayinta ,duk yadda mami take jin qaunar adamcy ji take tafita qaunarsa maryam ta tsananta kuka tana tuna tun lokacin data fara jin qaunar yaya Adam din acikin ranta rungumeta mami tayi tsam tana rarrashi alokacin wayar maryam ta soma ringing mami ta zare jikinta tana kallon maryam itama d’agowa tayi ta kalli mami sannan ta kalli screen din wayarta bata dauka ba ta cigaba da goge hawayenta yayinda kiran ya cigaba da shigowa still maryam bata d’aga ba .”
mami ta d’an yi gyaran murya “wake kiranki ne tun d’azu ?ummah ce !ta bata amsa atakaice idanunta na cigaba da zubar da hawaye “me yasa bazaki d’auka ba kika sani ko kiran mai mahimanci ne ?shiru maryam tayi ta kasa cewa komai dan tasan kiran me take mata, ita kuma ta gaji da abubuwan mahaifi yarta ,kullum abu d’aya kuma babu wani biyan buqata “ki d’auki kiranta kar rashin d’aukar kiran yasa hankalinta ya tashi tayi tunanin ko wani abu ne“.ahankali maryam ta gyad’a mata kai tana “cewa mami bari naje na dafa miki ruwan zafi “to shikenan maryam amman ki hada min da abinci “bamu da komai fa mami ,karki damu ki dafa min abinda kuke dashi . Mrym ta mike tsaye ta fito tana qoqarin d’aukar kiran mahaifiyarta daya sake shigowa ta sauko kunnenta manne da waya “umma dan allah ki daina kirana na tura miki sako mami tana gidan nan bana son taji komai “ amman me yasa zaki fad’i haka ummah?” kema Kinsan mami tana matuqar qaunata “a’a umma nifa gsky na gaji kawai abarshi na hakura bazan iya ba dan duk abinda zaa zuba cikin abinci bazai ci ba tunda baya cin girkina ,shiru maryam tayi tana jin yadda mahaifiyarta ta balbaleta da bala’i ta inda take shiga bata nan take fita ba.”
“kiyi hakuri ummah ba wai bana ganin qoqarinki bane saboda mami idan ta fahimci akwai abinda muke shiryawa d’anta zata ji babu dadi to shikenan gara ma wannan zamu iya sake gwadawa ko za’a samu ya kwanta akai ,to shikenan amman dan allah ummah karki kirani kiyi chart dina muyi komai ta chart ta qarasa mgnr tare da shiga kitchen ta soma qoqarin d’aurawa mami abinda zatayi breakfast dashi cikin kankani lokaci ta gama dafa ruwan zafi ta zuba cikin flaks sannan ta dafa shinkafa da miya ta fito tana qoqarin qarasawa dining mami ta sauko tana cewa “sannu da aiki maryam ?murmushi ta saki tana cewa “kai mami wani aiki kuma byn shinkafa da miya ce kawai na dafa miki. murmushi mami tayi tana cewa “kawo min nan diyata ta qarasa inda kujeru suke ta zauna maryam ta biyo bayanta ta ajiye kular abinci akan center table maryam tace “nasan idan kowa yaci abincina yace babu dadi mamina bazatace babu dadi ba ?”ina sam bazan fad’a haka ba zuba min na matsu banji dandanon abincin my daughter ba “abincin dai mami sai dai kiyi hakuri babu komai aciki ta qarasa mgnr muryata a sanyaye “karki damu maryam fara had’a min shayi cike da kulawa maryam take hidima da mami yayinda mami ke nuna mata farincikinki a zahiri amman a bad’ani bakinciki ne cunkushe acikin zuciyarta suna zaune ata ya fito yana taku a natse akan step sanye da kananan kaya jikinsa sai fitar da sihirtaccen kamshin turarensa yake ,ya qaraso parlour’n qasa hannuwansa duka zube cikin aljihun wondonsa tun daga nesa ya hango mami zaune tana breakfast da ruwan tea zalla babu wani abun hadi danginsu soyayyen Kwai da bread ko arish da sauransu abinda yasan ba d’abiarta bace, abun yayi matuqar bashi mamaki dan haka kai tsaye store ya shiga adaidai lokacin maryam ta mike ta nufi hanyar sama d’auko chazar wayarta .”
yana shiga dube dube ya fara bai ga komai ba ya fito ya shig kitchen duk sai daya duba cabinet din kitchen din nan ma bai ga wani abun kirki da zaa had’awa mutun breakfast mai kyau dashi ba dan haka jiki a sanyaye ya fito yana kwallawa maryam kira yayinda mami tana nan zaune tana kallon tv tana cigaba da kora ruwan tea da sauri maryam ta sauko tana dubansa gabanta na wani irin bugawa da karfi muryarta a raunane tace “ yaya gani ?“meye haka ?me ya faru kuma ?itama tayi karfin halin tambayarsa har ya d’aga hannunsa ko me ya tuna ya sauke ya dafe goshinsa a fusace ya cire hannunsa ya d’an saci kallon mami ita kuma ta zuba masa idanu tana ji da ganin abinda zai faru maryam taja baya tana jin yadda zuciyarta ke rawa “meye wancan agaban mami ?ya sake wulla mata tmbya tayi shiru tana dubansa a tsorace ya zira hannunsa daya cikin aljihunsa yana sake yin magana a tsawace “meye haka ina magana kina jina ?abinci ne !”what ?!ya furta a tsawace .”
ta sake ja baya kar ya wanka mata mari dan a yanayin da yake kallonta babu sausauci “amman zaki iya bawa mahaifiyarki irin wannan breakfast din ? gabanta yayi wani irin mugun fad’uwa ya tsura mata ido hakan ya bala’i bata tsoro gbdy ya sake canza mata ya fara taku zuwa inda take tsaye tana yar kyarma tana baya baya yana biyota har sai data kurewa bango “wallahi ba da gangan nayi ba babu komai a store ne komai ya qare iya abinda muke dashi na bawa mami .” afusace ya d’aga hannu zai wanka mata mari cikin wani irin masifaffen tsawa yaji sautin muryar mami “wallahi idan ka ta’bata ban yafe maka ba .” cak ya tsaida hannunsa tamkar an dasashi zuciyarsa na tafasa cike da zafin zuciya ya sauke hannusa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya juyo ya soma taku cike da ‘bacin rai ya qaraso ya zauna kusa daita kamar mai neman gafara ya fara kame kame “umm umm ummm nace ba “kace me ?”shiru yayi yana kallon mami yayinda maryam tayi sauri ta haye sama tana wai wayensu “ina jinka adamcy ?”Kiyi hakuri sweetheart banji dadin yadda naga kina breakfast haka ba “ bana zama a gida bansan babu komai a gidan nan ba sannan wannan yarinyar bata fad’a min babu komai ba ya qarashe maganar kamar zai yi kuka.”
mami ta kallesa sosai ta gano halin damuwar daya shiga adalilin breakfast dinta, daman kuma tayi hakan ne dan ya gani numfashi ya sauke yana sosa keyarsa yana cigaba da kallon mami ahankali mami ta tabe baki “to ka bata damar da zata fuskanceka bare ta fad’a maka babu komai acikin gidan nan “?amman !”sai kuma yayi shiru yana runtse idanunshi .”amman me adamcy ?kai kanka kasan baka da wata kalmar da zaka fad’a min na yarda a matsayinka na magidanci baka bawa matarka wannan damar ba sam matarka bata da cikakken iko acikin gidan nan yadda kake nuna baka qaunar jamaa da yanuwanka haka kake nunawa matar aurenka ,kai kanka kawai kasani baka damu da damuwar kowa ba dan haka karka rainawa kanka hankali ka nemi daurawa yar mutane laifi “ta qarashe maganar cikin fad’a saboda halin adamcy baqaramin damunta yake ba ,shi mutun ne wanda babu ruwansa da damuwar jama’a sai dai kanshi da aikinsa ya kamo hannun mami ya soma rarrashinta “sweetheart Kiyi hakuri kema Kinsan yanayin aiki ne sai ahankali ,ni kaina bana samun time din kaina kamar yadda kika sani amman at least data fad’a min zan sa a kawo komai “ta bishi da wani mummunar kallo “wai yaushe ka bawa maryam wannan damar yarinyar nan haka take rayuwa cikin qunci acikin gidan nan ga rashin so ga yunwa dame zataji ?”allah sarki maryam baiwar allah allah dai ya qara miki hakuri amman na cuceki na hadaki da damuwa ,na hadaki da mutun mara kirki ,na hadaki da mutun mara zumunci wanda ko yan’uwansa baya so bare wata aba maryam wallahi adamcy baka da tausayi da amana nayi danasanin hada auren nan allah dai ya gyara maka wannan bakar zuciyar taka .”
Kuka yaci karfin mami .”
jikin ATA yayi mugun sanyi babu abinda ya tsana kamar hawayen mahaifiyarsa da bai da kamarta jin kukanta yake har cikin zuciyarsa ya sake matsowa kusa daita yasa kanshi akan cinyarta yana jin yadda zuciyarsa yake tafasa yana jin kukanta yana ganin laifinsa amman yafi ganin laifinta domin kuwa itace sanadin da yasa ya kasa sauke nauyin da allah ya daura masa sannan ya kasa mata biyayya ta matsawa rayuwarsa dayawa akan maryam ,shi kanshi baya jin dadin abubuwan dake faruwa ,jin kukanta yake aransa yana jin kamar yayi kuka .“
ahankali yayi amfani da karfin zuciya irin tashi ya fara bata hakuri da rarrashinta “sweetheart Kiyi hakuri nasan bana miki yadda kike so Kiyi min addua wallahi a shirye nake da na canza in zama mai faranta miki ,kuma wallahi ina son yan’uwana sweetheart wani dadi ne ya ziyarci zuciyar mami dan abinda tafi bukata kenan ta dade tana adduar ya canja .”
ya qara gyara kanshi akan cinyar sweetheart dinsa “sweetheart ki yafe min ko zan samu sausaucin abinda nake ji araina kada zuciyata ta buga sweetheart ,damuwa tayi min yawa wallahi ni kadai nasan halin da zuciyata take ciki a haka kamar lafiyayyen mutun ne amman sam ba haka bane mutun ne mai dauke da mummunar ciwo a qirjinsa da zaki barni haka babu nauyin kowa akaina zanfi ji dadin rayuwata sai dai zuciyata taji da damuwa daya amman yanzu damuwa tayi min yawa na rasa ya zanyi da rayuwata wallahi zan gwamaci mutuwa sweetheart akan rayuwar da nake .”mami tayi saurin saka hannu ta rufe masa bakinsa bata son taji batun zai mutu idan ya mutu tayi yaya ai ita babban burinta ta mutu ta barshi a duniya, tana shafa kanshi tana jin sonshi har acikin bargon zuciyarta “ki yafe min sweetheart “adamcy baka min laifin komai ba ban ta’ba rikeka araina ba kullum addau nake maka d’ana sai dai abu daya nake só kamo. ina son ka sausautawa maryam ka zauan da mace mafi cancanta ,maryam ta cancanta kowani nmj idan ya sameta zaka ji dadin rayuwa daita mace ta gari ya dago kanshi yana kallonta ya saka hannu shi ya rike kunnuwansa bazan iya ba sweetheart “but I promise you in sha allahu zan kawo miki matar da zan aura in sha allahu zan faranta miki zakiyi farinciki da zabina amman batun wannan yarinyar fa gsky sweetheart sai dai kiyi hakuri .he ending the talk with a smile .”
mami tayi shiru tana dubansa sam adamcy baya ganin girmanta baya tausaya mata duk son da yake ikirarin yana mata abaki ne bai kai har zuciyarsa ba .”shiru kawai tayi tana jin babu dadi ko kadan acikin ranta tana son zubar da hawaye amman data tuna irin matsifar da hakan zai jefa rayuwarsa da alamuransa sai ta fasa sai dai yadda zuciyarta take tukuki ta tabbatarwa kanta tana cikin tsannain damuwa akanshi, idan batayi gaugauwan kawar da hakan aranta ba shima wani bala’i ne ga rayuwarsa runtse ido tayi zuciyarta na shirya mata yadda zata kawo qarshen komai “Sweetheart me kike tunani haka ?”muryar ATA ne ta katse mata tunani , harara ta maka masa tana cewa “ina ruwanka da abinda nake tunani ?wayarsa ya ciro ya kira daya daga cikin yaransa ya bashi umarnin a shigo da komai na kayan abinci enough .”
Cikin kankanin lokaci aka dinga shigo da kayan abinci sai daaka cika store tab da kayan abinci babu abinda babu na amafani haka ma fridge tun a ranar komai ya sauyawa maryam sunci mai kyau ita da mami su sha mai kyua, sai abinda suka ga dama suka girka kuma basuyi wa ATA tayi ba shima bai damu ba tsabgogin gabansa kawai yake yi sai da yamma ne ya dan saci kallon mami yace “sweetheart ko zan samu irin coffee da kike min ?zaka samu mana amman a wajen matarka ba “tun da yaji ta fadi haka bai sake cewa um ba bare um um, ya cigaba da danna wayarsa maryam najin haka ta matso kusa da mami tace “mami dan allah Kiyi masa mana “wani kallo mami tayi mata na rashin zuciya irin nata ,mutun bai damu da kai ba amman kai kabi ka damu kanka akanshi “please mami ai kema kin iya kije kiyi masa ta rage murya sosai tace “idan nayi bazai sha ba amman muje muyi masa tare zai sha mami ta tsura mata ido kawai tana kallonta cike da tausayawa tare suka shiga kitchen din sukayi sai dai koda ta fito parlour bata gansa ba a d’akinsa ta sameshi zaune akan kujera yana amsa kira taja qaramin table din glass din dake tsakar dakin ta dora tray din akai ta tsiyaya masa acikin a cup tace “gashi !”ba tare daya kalleta ba ya dauka ya fara sha dan a bukace yake .”
ta juya ta bar dakin tana rufo masa kofa kwanan mami uku a gidan wanda hakan ya haifar da sukuni da kwanciyar hankali ga maryam har mamakin kanta tayi yadda yanayin jikinta ya canza, domin mami nayi mata duk wani abinda zai kwantar mata da hankali tare da kawar mata da damuwarta da zarar taganta cikin damuwa sai tayi duk abinda zata kawar da damuwar sannan hankalinta zai kwanta sosai take kula da cin abincinta mussaman ta dinga had’a mata fruit masu gyara skin da qara ni’ima ajiki most especially yankakkiyar ayaba da soyayyiyar gyada da kankana da madarar ruwa a had’a waje daya wannan kam kullum sai mami ta had’a mata ta bata ,wannan had’in mai dadi yana aiki abu biyu ne ajikin nmj ko mace yana gyara skin sannan yana qara ni’ima ajikin mutun. zaman mami a gidan ya dan kawo sauyi domin duk abinda ATA zai yi na rashin mutunci tana taka masa burki da fushinta domin dai idan ba fushinta ya gani ba baya kin abinda yayi niyya kuma yanzu babu laifi yana cin abincin gidan .”
Da misalin karfe shida na yammacin ranar da mami ta cike kwana biyar a gidan ATA ya tashi da rashin lafiya na ciwon kai mai tsanani wanda har sai da doctor dinsa yazo ya dubasa inda yayi wa doctor bayanin yadda yake jin ciwon Kan kuma koya sha magani baya masa sauki yadda yake buqata, doctor yayi gwaje gwaje ,a inda yace akwai kwayoyoyin da yake sha wanda sune suke haddasa masa wannan ciwon, dan shiru yayi yana tunani dan shi a sanin da yayi wa kanshi baya shan wata kwaya dama sigari yace itama yanzu ba koda yaushe yake shanta ba amman kwaya kam baya sha “doctor bana shan kowani irin kwaya amman ko zaa iya duba wace irin kwaya ce ?”eh zaa iya dubawa kuma zaa gano kowani iri ne amman dole sai kaajiye ayyukanka na gobe kazo hospital .” ATA ya gyda kai alamun zai zo .”
tun zuwan doctor maryam ta fahimci bashi da lafiya ne dan duk sanda kagansa to rashin lafiya ne bayan doctor ya gama duba ATA maryam ta shigo dakinsa hannunta dauke da tray ta sameshi zaune akan doguwar kujera yana sanye da singlet da gajeran wando kallo d’aya tayi masa ta dauke idanunta sakamakon yanayin data tsinci kanta d’an kwantaccen sumar jikinsa kawai ya isa tadawa mutun shaawarsa ,taja dan karamin table din glass din dake tsakar dakin ta dora cooler din abinci a kai ta zuba mishi a cikin plet tasa spoon tace “ga abinci shiru bai ce uffan ba ta sauke numfashi ta sake bud’e bakinta akawo maka coffe ?ya girgiza mata kai kawai alamun baya bukata wani sanyayyen numfashi ta sauke a boye a raina tace “alhamdulillah yau dai da alamun mutane kirki ne a kusa babu rashin mutunci,kamar baka jin dadi ?sannu allah ya baka lafiya meke damunka “?ba tare da ya kalleta yace “ki kama kanki dan naga kina wani jin dadi dan kinga sweetheart atare damu kisani ba tabbata zatayi a gidan nan ba zata wuce idan ta wuce kuma kema Kinsan me zai faru ?tace babu abinda zai faru sai alkhairi allah dai ya baka lafiya baby nah tana rufe bakinta daya daga cikin wayoyinsa ta soma ringin zuciyarsa cike da mamakinta karo na biyu kenan da ta kirasa da wannan banzar sunan kamar ya tashi ya gaugaura mata mari amman jikinsa babu kwari shine ma yasa ya qasa tashi kuma yana jin yadda zai ce tabashi wayar maryam ta fahimci haka, dan haka cike da sanyi jiki ta qarasa inda wayar take akan katifarshi ta dauko ta duba fuskar wayar nan take gabana yayi wani mummunan faduwa sakamakon ganin hoton wata kyakkwar yarinya a fuskar wayar mijinta .”
yarinyar kyakkyawa ce duk da fuskarta kamar zane ce aranta tace”ko dai wannna ce yarinyar mafarkin sa?kwakwaluwarta bata kai ga bata amsa ba “tajiyo sautin muryarsa can qasan makoshi yace “bani wayata “jiki a matuqar sanyaye ta kai mishi sañan tace bari na wanke maka toilet shi dai bai ce mata uffan ba har ta shiga ta wanke ta fito yana cin abinci yace “bani abinsha a fridge da sauri ta bude demsino na gwangwani ta dauko masa ta hado masa da ruwa nestle ta ajiye tana jin zuciyarta babu dadi duk da yarinyar mafarki ce amman abun ya damu zuciyarta zata cigaba tsayuwa ad’akin yace “please leave! simi simi ta fito daga d’akinsa yaja tsaki tare da cewa nonsense mace sam babu class ,to wani aji zatayi wannan ?allah na tuba ai isasun mata né masu aji shi yaji ajikinsa muddin zai had’u da princesa dinsa tabbas zata fita dabam acikin mata ranar da wuri ya kwanta bacci sakamakon maganin bacci da alluran da doctor yayi masa .”waahegari kuwa karfe biyu a office din doctor tayi masa duk wani gwaje gwaje anyi masa, inda doctor yace zai zo gida ya kawo masa abinda suka gani daga nan kai tsaye gidan mb yace a wuce dashi sun jima tare,bashi ya dawo gidan ba sai bayan ishai.”
Da misalin karfe goma sha daya na dare maryam ta fito daga dakinta sanye da kayan bacci iya cinyarta sai dai ta daura zani a saman kayan baccin kai tsaye d’akinsa ta shiga bata gansa ba dan haka ta sauko qasa cikin tsananin tashin hankali har zanin jikinta ya fita bata sani ba “yaya Adam kazo mami bata iya numfashi sosai ,ai da wani irin mugun sauri ya zabura ya mike yayi wulli da remut din hannunsa bai san yaakayi ba sai ganinsa a dakin maryam yayi har tsakiyar gadonta ya daga kan mami ya daura bisa kafafunsa yana qoqarin tallabota ya sauko daita ta girgiza masa kai “dan girman allah sweetheart wallahi baki san yadda naji a zuciyata ba “ke tsayuwar me kikayi kije ki dauko min wayata” yayi mgnr a tsawa ce yayinda maryam ta juya da sauri ta fita “haba adamcy ka dinga sausautawa maryam mana .tayi maganar da kyar”
furzar da iska yayi yana kamo hannun mami cikin nashi “adamcy nah! mami ta kira sunansa”na’am sweetheart sannu gobe gobe nan zan bar kasar nan dake “duk inda zaka kai ni bazai hanani mutuwa ba ,dan haka ma gara ka barni kawai a kasata idan mutuwar ce allah ya bamu ikon cikawa da imani ta qarasa maganar da kyar tana sauke numfashi “kinji abinda naji kuwa sweetheart da kikayi zance mutuwa nan dan girman allah ki daina fad’a min haka “to adamcy mutuwa ai dole ce maryam ta shigo ta mika masa waya ta hawo har saman gadon ta riko hannun mami cikin nata suka sakata a tsakiyarsu mrym tana mata sannu yayinda ATA Ke qoqarin kiran layin Aunty shahida “karka kira shida ka daga mata hankali sannan kiranta bazai hanani mutuwa ba idan mutuwar ce.” saurin runtse idanunshi yayi .”
Bai kula maganar mami ba ya cigaba da kiran layin shahida sai dai kiran na shiga bata d’auka daga adamcy har maryam duk suka zubawa mami ido hankalinsu a matukar tashe “maryam adamcy ku yafe min had’aku aure da nayi “haba mami dan allah kiyi shiru numfashi ki har yanzu bai daidaita ba kuma aurenmu da kika hada baki mana laifin komai ba inji cewar mrym “idan Ke ban miki laifi ba ai nayiwa adamcy “ki kwantar da hankalinki mami shima baki masa laifi ba muddin muna raye zai faranta miki har ma bayan ranki “shi kam ATA gabad’aya ya nemi natsuwar ya rasa dan har layukan mijin aunty shahida ya kira bai zuwa haka ma layin likitan dake dubasa yana qoqarin durowa daga kan gadon mami ta riko hannunsa ya dawo ya zauna cikin tsananin tashin hankali “dan allah sweetheart karki bari sanadiyar careless dinki na rasaki,wallahi bazan iya daukar zafin jarabawar nan ba “yayi mgnr kamar zai yi kuka “ haka rayuwa ta gada adamcy kuma ita rayuwa cike take da qaddarori da jarabawa iri iri sai dai idan baka cikin duniyar nan, yau dadi ne gobe kuka dukkanin rayuwa rubutattacen lamari ne daga rabbi da d’an adam yana gane wannan da bazai tsaya batawa kansa lokaci ba kamar yadda ka kasa ganewa “tana gama fadar haka idanunta suka juye numfashinta ya soma qoqarin tsayawa .”
“sweetheart sweetheart!! Kawa yake iya kira yayinda maryam ma ta dinga kuka tana kiran sunanta atare suka nemi durowa daga kan gadon suka jiyo sautin muryarta can kasa “maryam bani ruwa kishi nake ji .” ya dawo da sauri yana cewa “shikenan sweetheart mutuwa zakiyi ki barni ,dan allah karki min haka sweetheart, dan girman allah karki min haka ya allah ka d’auki rayuwata ka bar ta mahaifiya ta” ya fad’a yana damke hannunta cikin nashi gam wasu hawaye masu zabi suka gangaro masa “adamcy Nah kuka kake yi ?ya sauke numfashi yana kai hannunta bakinsa inda hawayensa ke diga “kayi hakuri haka rayuwa ta gada ,kana cikin jin dadi sai allah ya jeho jarabawa cikin rayuwarka “ka rike yanuwanka adamcy saboda kai ne kamar babba agaresu ,ka kyautata masu ,ka tsaya masu a dukkanin lamarinsa “dan allah sweetheart ki daina fad’ar haka “dole fa zan mutu adamcy fatana allah yasa mu cika da kyau da imani .”
Tayi shiru can ta motsa bakinta “ka min wani alfarma adamcy ya d’ago ya tsura mata ido yana sake damke hannunta cikin nashi “me kike so sweetheart just tell me matsawar zakiyi farinciki ki dawo daidai “ka ta’ba kusantar maryam ne amatsayinta na matarka ?shiru yayi yana duban mami zuciyarsa na bugawa da karfi ganin haka yasa mami ta soma tari wanda da kyar tarin yake fita “sweetheart sannu ya furta yana kwallawa maryam kira” ki kawo ruwan mana ko dan ba uwarki bace kike westing time “cikin yanayi na ciwo mami ta cigaba da magana “na tambayeka baka bani amsa ba “a’a sweetheart babu abinda ya ta’ba shiga tsakaninmu “yanzu ka kyauta kenan adamcy ?wata shida kenan da aurenku amman ka kasa sauke wannan nauyin kana ganin allah zai barka haka né ?shiru yayi yana daura hannunsa a goshin mami “me maryam ta tsare maka adamcy ?ta fad’a tana wani irin numfashi mai zafi idan laifi ko haushi ne nawa zaka ji domin nice silar komai .”
“Kiyi hakuri sweetheart ya fad’a adaidai lokacin da maryam ta shigo hannunta rike da roban ruwa ya fixge da karfi “idan mutuwa ne tuni ta mutu kawai kije ki kawo ruwa kinje kinyi zamanki saboda ba mahaifiyarki bace cike da rawar jiki ya bude murfin roban yana mai tallabo kan mami ya kai goran ruwan bakinta ta sha sosai sannan ta kawar da bakinta tana cewa maryam koma d’akin adamcy zai zo ya sameki kinji allah yayi miki albarka, jiki a sanyaye ta juya ta bar dakin sai dai ta qasa shiga dakinsa ta tsaya corriedor ta jingina bayanta da bango tana zubar da hawaye.”yanzu idan mami ta mutu ya zan yi da rayuwarta “?tayiwa kanta tmbyr tana fashewa da kuka .”
“Kayi min wannan alfarmar adamcy baka sani ba ko iya alfarmar da zan nema kenan daga gareka ya matso da kunnensa daidai bakinta dan yaji alfamar da take so “sweetheart ki fad’a min abinda kike bukata in promise you zanyi “ina son ka fad’a min gsky kana da cikakkiyar lafiya kuwa kamar yadda sauran maza suke ?numfashi ya fesar yana mai dagowa ya tsura mata ido “yau ba ranar wasa bace bare ya kawo rainin hankalin da ya saba ,dan hk da sauri yace “lafiyata kalau sweetheart ,amman wannan tamvayar ba yau bane karo na farko da kika min ,idan bani da lafiya kece mutun ta farko da zan fadawa “to na yarda tunda kai ma ka tabbatar da lafiyarka kalau ina son kaje ka sauke nauyin da allah ya rataya akanka na aure da maryam “lumshe idanunshi yayi kana ya bud’e ahankali yana dubanta ko kifta idanu bayayi ko bata fito fili ba ya fahimceta sosai “idan kayi min haka ko na mutu ruhina zai samu salama adamcy ,lalla a illalla muhammadu rasulillahi sallahu alaihi salam,dan allah adamcy ka cika min wannan burin , kayi min wannan alfarma kuma a yanzu ta damke hannunsa gam cikin nashi jikinta na rawa kamar yadda jikinsa yake rawa yana furta inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ita kuma mami tana salati tana furta ya cika mata burinta .”
Gabad’aya ATA ya gigice ya fita haiyacinsa ganin halin da mahaifiyarsa take ciki ya juya da sauri ya fita daga cikin dakin a corriedoor yaga maryam tsaye ta daura hannuwanta duka a saman kanta tana rusa kuka ya tsura mata ido cikin tsnanin tashin hankali bashi da wani lokacin ‘batawa gara yayi abinda zai yi ya faranta ran mahaifiyarsa ko bayan ta mutu din ruhinta zai samu salama kamar yadda ta fad’a masa hannuta ya riko da karfi yajata zuwa d’akinsa nan fa gabanta ya shiga faduwa suna shiga dakin ya nuna mata Kan bed dinsa ,gabanta yayi wani irin mummunar faduwa ta tsura masa ido tana kallonsa cike da matsanancin mamaki yayinda idanunshi sukai balain canzawa suka koma ja ,ta taki hawa Kan gadon kamar yadda ya umarceta dan batasan me hakan yake nufi ba ya kalleta da fuskasa dake murtuk “ke bakiji abinda nace bane ?me kace yaya wallahi banji kayi magana ba,” ki hau gado .”
still maryam taki hawa sai ma qoqarin fita daga dakin take aiko cikin zafin nama ya fixgota da karfi ya maka ta akan gado da karfi ta zabura zata tashi ya buga mata wata muguwar tsawa ganin tana son ‘bata masa lokaci “Ke ki tsaya nayi abinda aka sani idan kuma kika nemi ‘bata min rai har Mahaifiyata ta mutu ban mata wannan alfarma ba zakiyi nadama har qarshen rayuwarki “ jin haka yasa maryam sauke wani wahallen numfashi tana mai jin sanyi aranta amman a zahiri fuskarta da jikinta babu komai sai tashin hankali.” ya kai hannu ya kashe wutar d’akin dan bazai iya kallon fuskarta ba ,ya hau saman gadon batare daya cire kayan jikinsa ba yayi mata runfa da fad’a den qirjinsa wani sanyi dadi ya mamaye zuciyar maryam hakika mami ta taimaki rayuwarta ,allah dai yaja da kwana mami domin duk ranar daakace babu ita a rayuwarsu akwai babban tashin hankali.”
wata irin matsa yayi mata kafin ya shigarta tayi shiru kwalla na gangarowa akan kuncinta dan bai tura dan sakon a tsakaninsu ba kamar yadda sharia muslinci yace hakan yasa taji zafi sosai taji gara ma ace baya cikin haiyacinsa ne ya kusanceta bangaren ATA kam bakinciki ne cunkushe acikin zuciyarsa jin kofarta a bude ,a ranshi yaja tsaki cike da bakinciki ya cigaba da abinda yake sai dai baya jin dadin komai ganin kawai zai yita batawa kanshi lokaci ne ya kawo tunanin princess aransa yadda yake zuwan masa a mafarki da yadda yake sarrafashi nan da nan yaji wani abu ya tsarga masa da tunanin princess ya samu yayi abinda zai yi ,ya mike ya kunna wutan dakin ya tsura mata ido cike da bakinciki baasi yake son ji amman ya kasa sarrafa harshensa illa tsaki yaja , ita kuwa maryam da sauri ta sauka daga Kan gadon ta fito ta nufi d’akinta inda mami take kwance tana numfarfashi .”
Bayan fitarta shima ya fito kai tsaye dakin maryam ya shiga inda ya iske mami kwanace tana fidda numfashi sam sama “sannu sweetheart ya kike jin jikinki “alhamdulillah ta fad’a tana yafitosa da hannunta ya matso sosai kusa daita “kayi abinda nasaka adamcy ?”nayi mami ! yauwa dan albarka allah yayi maka albarka ka gama cika min burina ko yanzu na mutu burina ya cika adamcy “kiyi shiru mami ki samu natsuwa barin naje nazo da shahida “to adamcy amman daka bari zuwa gobe da safi “girgiza mata kanshi yayi ya fice da sauri ya shiga dakinsa ya sanya jallabiya ya dauki wayarsa ya fito da sauri yana duba agogon wayarsa karfe daya saura .” masu tsaronsa ya kira tun kafin ya qarasa fitowa haraban gida har sun juya Kan motacici guda biyu gaban motar ya shiga suka bar gidan ya gyara zamansa sosai ya rungume hannuwansa duka a kirjinsa yana tunanin halin da zai shiga idan ya rasa mami .”
“duk iskancinsa yana matuqar shiga tashin hankali idan ya tuna zata mutu ta barshi kuma duk baccin da yake da zarra ya tuna zata mutu sai baccin ya dauke masa bazai manta ba lokacin yana da shekara ashirin da takwas duniya cikin baccinsa wai aka fad’a masa sweetheart dinsa ta rasu da mugun sauri ya farka ya shiga dakinta tana kwance abunta tana bacci ya Kai hannunsa daidai hancinta nan yaji tana numfashi wani naunayen ajiyar zuciya ya sauke gudu motar yake amman sam ATA gani yake kamar motar ba gudu take ba dan gabdaya ya rasa natsuwarsa daga jajayen idanunshi yayi ya sauke akan wayarsa daya har da wasu mintuna tsaki yayi yana jin zuciyarsa kamar zata buga sam baya ganin gudun motocin nasu yaji kamar ya karbi tukin watakila nashi zai fi nasu, tsaki yaketa yi yana qarawa kamar bazasu kai ba haka yake gani duk jikinsa tsuma yake kwakwa luwarsa ta hargitse kamar wanda sabon hauka ya kama a haka suka qaraso bakin get din gidan Aunty shahida tun baa gama daidaita tsayuwar mota ba ya fito da sauri ya shiga buga get din gidan da iyakacin karfinsa domin kana ganinsa zaka fahimci hankalinsa a matukar tashe yake tunda yayi bugun farko kowa dake cikin gidan ya farka a matukar tsorace ,mai gadi ma yayi takansa sai dayaji ya ambaci sunan aunty shahida sannan ya fito ya bude qaramin hujin get din nan take ya ganensa duk da cikin duhu ne .”
ya bude masa get da sauri ya shiga haraban gidan yana kwalla mata kira” shahida shahida !!”wani irin bacci ne haka?” meye amfanin wayoyinsku da karfi ya dinga buga kofar shiga falo masu aiki suka bude masa yaranta da masu aiki ya gani tsaye cirko cirko ya shiga yana cewa “ina shahida taje ?””mumy na sama inji cewar hamdiya second born din aunty shahida ,zuciyarsa duk a jagule ya diga kiran sunanta sai gata ta sauko da sauri “lafiya Adam ?lafiya zaki gani by this time ?” shima ya wulla mata tmby yana mata wani kallo “dan allah meye amfani wayarki data mijinki ?”zatai magana yace yanzu dai dauko kayan aikinki ran sweetheart a hannun Allah zan iya rasata akowani lokaci “ka kwantar da hankalinka zuwa da safe zan zo “ what “?ya fad’a yana mata wani irin mugun kallo sannna yace “dan allah idan wasa mike ki dawo hankalinki ki dauko kayan aiki muje ya riko hannunta .”
“bari na dauko kayan aikina “okay Kiyi sauri please cikin kankani lokaci ta daura hijab akan kayan baccinta ta sauko tare da mijinta yana rike da kayan aikinta yana ma ATA magana “a she mami ce babu lafiya “tsaki ATA yaja Tare kwace qaramin alkwartin kayan aikin aunty shahida dake hannunsa ya ja hannunta suka fice yana cewa “idan kukayi aure shikenan damuwar iyayenku ma bakwa damuwa daita sai ta mazajenku “karka sake ka fad’a min magana “an fad’a miki idan ma akwai abinda yafi haka zan fad’a miki ,nazo miki da matsala sai wani jan jiki kike yi kamar ba mahaifiyarki nace ranta a hannun allah yake ba har da wani jerawa da miji nonsense kawai “kai ne nonsense ai gara ne tun daga farko rayuwata har zuwa yanzu akan mata biyayya nake kai fa a matsayinka na nmj wanda hakinsa ne yayi biyayya ko dole ne ,kuma hatta aljannarka tana qarqashin tafin kafarta amman ka fad’a min meye kake wa mami na farantawa bare yanzu ka d’aga hankalinka akan rashin lafiyarta ?wallahi ko yanzu mami ta rasu alhamdulillah mun gama daita lafiya kai fa ?
“Wallahi sai kafi kowa shiga damuwa da tashin hankali “gori zaki min?” ya tambayeta cikin tsananin damuwa “eh anyi maka idan kayi zuciya ka canza rayuwa kayiwa mahaifiyarka biyayya ,kaso duk wani abinda take so “tana gama fad’ar hk ta shige bayan mota, shima kuma ya shiga gaban mota ya zauna maganarta na ci masa rai “abun har ya kai ayi masa gori ?uwarsu daya ubansu daya ma tayi masa gori inaga mutanen waje ?”allah ne kadai yasan abinda jama’a suke fad’a akansa” ya salam ya furta yana dafe goshinsa ahaka suka kawo gidan da sauri ya fito yana bud’e mata mota kallo d’aya zaka masa ka fahimci yana cikin damuwa da tashin hankali hannunta ya riko cikin nashi suka nufi kofar shiga parlour’n gidan .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 20
Tunda ATA ya bar gidan hankalin mami a matuqar tashe yake ganin maryam rasa babu wata alamun an kusanceta domin ta lura kamar babu wani abu daya sauya atattare daita "kar dai qarya adamcy ya girba mata bai aikata abinda tayi masa umarni ba?" hakan yasa taji wani sabon tashin hankali ya shigeta . bangaren ATA kuwa tafiya yake hannunsa rike dana aunty shahida har suka shigo parlour'n gidan, sauri sauri yake janta suna taka step, kallonsa kawai aunty shahida take zuciyarta cike da matsanancin bakinciki da tausayinsa ,bakincikinta saboda yadda yake janta, tausayinsa kuma saboda yanayin da yake ciki dan yanayinsa kawai zai tabbatar maka da baya ciki natsuwa da kwanciyar hankalinsa . kai tsaye d'akin maryam suka nufa inda suka iske maryam zaune rike da hannun mami tana zubar da hawaye nan da nan hankalin ATA yayi matuqar tashi , jikinsa har rawa yake ganin yadda maryam take hawaye ,ba iya jikinsa ba hatta zuciyarsa rawa take .jin motsin shigowa d'akin ne yasa da sauri maryam ta d'ago tana duban kofa idanunta ya sauka akansu ta share hawayenta da sauri ckin muryar kuka tace "aunty shahida ina kika ajiye wayarki ?"
“mami tana cikin wani hali har ta fita haiyacinta numfashinta baya sauka da kyau please aunty shahida ki taimaka banason wani abu ya samu mami ."ta qarasa maganar tana wani irin kuka ."
Jin ba mutuwa mami tayi ba yasa ATA yayi mata wani mugun kallo tare da yi mata alama da ido ta fita ta basu wuri ."babu musu maryam ta mike ta sauko daga kan gadon cikin mutuwar jiki ta biyo ta ra'ba ta gefensa ta fita tana kuka .bayan fitar maryam jingina bayanta tayi da bango corriedor tare da sake fashewa da wani kuka mai ta'ba zuciyata "mami bana son na rasaki ,domin kuwa ke din babbar jigo ce ga rayuwata da kuma rayuwar aurenta allah ya baki lafiya allah ya tashi kafad'arki".cikin taku mai tattare da damuwa da tashin hankali ATA ya matso inda mami take kwance numfashin ta na fita ahankali ,kafin ya bawa aunty shahida umarni ya tsurawa mami idanunshi tare da zama a gefenta yana qare mata kallo yana jin kamar ya fashe da kuka ya d'auki zazzafar qaddara rasa mahaifinsa na tsawon shekaru yanzu kuma idan ya rasa mahaifiyarsa a halin da yake ciki na tarin damuwa da matsalolin rayuwa ya zai yi ?"yaja zazzafan numfashi tare da sa tafin hannunsa ya share hawayen daya d'an cika gefen idanunshi . duk yadda mami take jin idanunshi akanta batayi kuskuren bud'e idanunta ba tana jira daga garesu ,lallausar tafin hannunsa ya kai saitin wuyan mami yana jin saukar numfashinta yana jin d'umin jikinta ahankali mami ta bud'e idanunta tana cewa "adamcy nah har ka dawo ?ina shahidar take ".
kai ya gyad'a mata tare da kallon inda aunty shahida ke tsaye yace "ya kika tsaya dan allah ki fara aikinki mana "ya fad'a kamar zai fashe mata da kuka alokacin ya d'auke hannunsa akan wuyan mami ganin bata da alamun qarasowa yace "wai meye haka dan allah naje na taho dake da kyar yanzu kuma kinzo kin ja kin tsaya kin zuba mana ido kodan kinsan idan wani abu ya sameta ni ne zan fi kowa shiga damuwa yasa kike min haka ?.yayi mata tamabyar a rud'e yana zufa "wai ..."mami tayi saurin katse shi ta hanyar cewa "adamcy nah zan sha tea "da sauri ya mike tsaye ya fita cikin tashin hankali yana fita maryam tayi wuf ta fad'o d'akin ,sai dai abun mamaki mami ta gani ta dawo haiyacinta ba kamar sanda ta barota ba tana kallon aunty shahida, bata gama mamakin ta ba taji fitowar muryar mami rasa. "zo nan maryam" ta yafitota da hannunta ta nuna mata kusa daita tana cewa "shahida sai kuma kika ga wannan rigimemen yarona yazo d'aukarki ?.
“wallahi kuwa mami ,da yake nasan shirinki shiyasa nayi masa wulakanci, yana fad'a ina fad'a har muka baro gidan mami tayi murmushi kawai"amman fa ya bani tausayi sosai ,da fatan dai komai ya tafi yadda muka shirya ? tô ya dai ce min ya aikata amman bansani ba ko karya yayi min duk da nasan karya ba d'abiarsa bace idan bai yi ba ,zai ce bai yi ba " mutuwar zaune maryam tayi agurin tana dubansu a matuqar gigice saboda tsananin tsoro "kenan ciwon mamai shiri né dan yaya adam ya kusanceta ? “Ita kuwa wani irin só mami take mata haka ?kwakwaluwarta bata kai ga bata amsar tambayoyin ba taji sautin muryar aunty shahida tana cewa "ke maryam !"maryam tayi saurin d'agowa ta kalli aunty shahida a gigice "wani abu ya shiga tsakaninki da adam né ?maryam tayi shiru alamun kunya "kinga karki 'bata mana lokaci idan kinsan babu abinda ya shiga tsakaninku a canza wani shiri ?"ahankalai ta gyd'a mata kai kawai "ki bud'e baki mana ki min magana ita kam bazata iya amsa wanan tambayar agaban mami ba fahimtar haka yasa aunty shahida tace "zan yi magna idan wani abu ya shiga tsakninku ki gyada min kai idan bai shiga ba kuma ki girgiza min kai.”
mami kam maganar aunty shahida kusan dariya yaso bata ,dan haka ta kawar da kanta gefe tana murmushi "wani abu ya shiga tsaknain ku ?maryam ta gyad'a mata alamun "eh "alhamdulillah ! ta furta a fili tare da cewa yanzu kuma sai muyi fatan allah yasa ya zame mana alkhairi " in sha allahu zai zama alkhairi fara dubani kafin ya shigo ya gane shiri ne kinsan halinsa da shegen ganiyar tsiya ". Inji cewar mami batare da 'bata lokaci ba aunty shahida ta bud'e qaramin jakar kayan aikinta ta soma duba jikin mami suna magana qasa qasa."otsin shigowa d'akin maryam taji hakan yasa tayi saurin waiwayo
wa ATA ta gani yana qoqarin shigowa hannunsa rike da cup din tea ganin ana duba mami ya ajiye cup din akan bedside ya tsaya idanunshi kyam akansu ko kifta idanu baya yi ,burinsa kawai mahaifiyarsa ta samu sauki . yayinda maryam take kallonsa kawai ta rasa abun yi saboda jin ciwon mami duk shiri ".
wani irin numfashi mai zafi ya fesar kamar ance ya kalli inda maryam take zaune yaga shi take kallo wani mugun kallo ya bita dashi mai tattare da tsana taga irin kallon tsanar da yake mata amman tayi kamar bata fahimta ba ta cigaba da kallon faukarsa har alokacin tana cikin yanayi na damuwa da tashin hankali ,mami kuwa hankalinta na kansu addaua take masa acikin zuciyarta "allah yasa qarshen wahalarsu ne yazo, allah ka dubeni ka shirya min adam ka fidda shi acikin halin da yake ciki ka dauke masa tunanin mafarkinsa ka mantar dashi komai akanta ka daidai tsakaninsa da matarsa ."kamar wanda aka tsinkara haka yayi kanta yana cewa "kallon iskanci me kike min ?".wani irin tari mai karfi mami tayi tana kiran sunansa da yafitosa da hannunta dole tasa ya dawo da sauri ya rike yatsun hannunta gam yana mata sannu amman idanunshi na Kan aunawa maryam mugun kallo da harara ."
har tsawon mintuna talatin aunty shahida tana Kan aikinta sannan ta samu numfashin mami ya dawo daidai ta mata allurar bacci sannna taja baya kad'an ta tsaya tana yiwa mami sannu ."yauwa shahida allah yayi maku albarka gabad'ayaku da ya'yanku allah yasa ina da rabon ganin ya'yan adamcy da auta "in sha allahu mami zaki gani allah dai ya baki lafiya "wani mugun kallo ATA ya watsa mata yana jan tsaki "da fatan dai baku sheidawa kowa halin da nake ciki ba ko ?nasan babu wanda d'an naki ya sheidawa dan nasan daya sheida masu da yanzu sunzo ko sunyita kira a waya amamn yanzu zan kira khadija , zabiba da auta na sheida masu halin da'ake ciki sai su zo gobe su duba jikikin zazzafan numfashi ya sauke dan kuwa babu wnada ya sheidawa cewar mami ta kusan mutuwa ya kai hannu ya d’an d’ago mami yasa mata pillow ya jingina bayanta ya d'auki cup din tea din daya shigo dashi ya kai bakinta yana bata tana kur'ba ahankali rud'ewarsa bai bawa mami mamaki ba dan tasan halinsa akan ya rasata zai iya aikata fiyye da haka dan duk iskancinsa idan zai ga 'bacin ranta ko rashin lafiyarta yanzu né hankalinsa zai tashi ,bai son ya rasata gashi kuma mutuwa tana Kan kowani bawa dole watan wata rana zaa wayi gari a sheida masa ta mutu ko ta mutu a hannunsa allah dai ya bata ikon cikawa da imani shine fatanta ".
bayan ta gama sha tea ya gyara mata kwanciya yana mata sannu tare da lullu'be mata jiki ya zauna a gefenta hannunsa na rike cikin nata yana jin qaunar mahaifiyarsa fiyye da komai, ahaka bacci ya d'auke mami ,ya tsura mata ido "ya allah ka bani karfin zuciyar yiwa mahaifiyata biyayya ba komai ya hanashi son abinda mahaifiyarsa ke so ba illa soyayyar princess daya ma zuciyarsa mummunar kamu ."hannun maryam aunty shahida ta kamo suka fito daga cikin d'akin,ahankali suke takowa zuwa parlour'n qasa "maryam ina tayaki murna allah yasa ku samu rabo a wannan had'uwar farkon da kukayi da adamcy." cikin yanayi na tashin hankali maryam ta sauke numfashi tana jin sabon tashin hankali na shigarta "abinda basu sani ba ai wannna had'uwar itace kusan ta biyar a tsakninsu dashi har bakin mota ta raka aunty shahida tana karfafa mata gwiwa ta bud'e mata gidan baya ta shiga ta zauna "allah ya tsare min aunty nah zaki shigo gobe né ?sosai kuwa zan zo gobe ai idan ban zo ba wannan muskililin zai iya kiran likitansa kuma zai iya gano komai allah ya kai mu gobe aunty shahida ta wuce gida ta barsu duk da taso tayi magana da adam amman ganin yanayinsa akwai tsananin damuwa koma tace haushinta yake ji .
Acan d'akin kuwa a hankali ATA ya runtse idanunshi tare da motsa labbansa "princess you want to kill me ba ?kina son sonki ya kasheni ba ?duk tsananin soyayyarki ne ya hanani yiwa mahaifiyata biyayya why kika kasa bayyana min kanki a zahiri gashi komai zanyi sai da tunaninki ".ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya da numfashi atare ya tuna lokacin da yake saduwa da maryam karfin tunaninta ne yayi tasiri a zuciyarsa har mazakun tarsa ta mike if not da bazai iya aikata komai daita ba "nima ina sonka sosai zuciyata da gangar jikina kai kad'ai suke jira saboda zuciyata da gangar jikina mallakinka ne har abada ,yaji sautin muryarta acikin dodon kunnensa suna masa kuwa ahankali ya bud'e idanunshi yana kallon d'akin .wani naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana furta "why princess ?ina son na ji sautin muryarki a zahiri kullum sai dai naji a bad'ini ya fad'a da wata irin murya kamar tana tare dashi ya dade zaune har goshin asuba sannan ya zare hannunsa cikin na mami ya fito ya nufi d'akinsa kamar ya d'an kwanta ya huta dan wani irin sara kanshi ke masa amman yasan ko ya kwanta bazai ta'ba iya runtsawa ba saboda halin da mahaifiyarsa take ciki ."
kai tsaye hanyar bathroom ya nufa ya tura kofar ahankali ya shiga domin tsarkake jikinsa bayan ya zare jallabiyarsa wanka tsarki ya soma alokacin da ruwa ya fara sauka ajikinsa zuciyarsa ta fara hasko masa komai daya faru a awanin da suka gabata "sweet heart kinga irin matar da kika za'bawa rayuwata ko ?" Kin aura min mazinaciya ,kin aura min macen data gama zubar da mutuncinta a waje “Ko adadin maza nawa ne suka kusanceta ?yayiwa kanshi tamabayr yana furta kalmar subhallah acikin zuciyarsa "a gaskiya sweetheart baki kyauta min ba ,shiyasa raina yaki amsarta zuciyata taki sonta, babu shakka wannan dabi'ar ce yasa zuciyata ta qasa amsarta amatsayin mamata "nan da nan zuciyarsa ta fara tafarfasa yana jin tuttukin bakinciki sakama kon yadda yaji maryam akan gado "sweetheart kin sadaukar da rayuwarki akan mazinaciya batare da kinsani ba wani zazzafan numfashin ya fesar kana ya cigaba da wanka da wannan tunanin yayi wankan tsarki Ya gama ya d'auro alwala ya fito ya sauya wani jallabiaya mamadin ya kwanta ko ya zauna sai kawai ya tsinci zuciyarsa da són gabatar da nafila "gara ya koma zuwa ga ubanginsa ko zai fita daga cikin maseefun da yake ciki na tsawon shekaru ."
Cike da tashin hankali maryam ta shiga d'akinta ta samu waje ta zauna tana duban mami "wani irin soyayya mami take mata haka ?ta furta a saman lip's dinta tasan mami na matuqar qaunarta amman bata ta'ba tunanin zata aikata haka akanta ba ,kanta ta kifa a daidai hannun mami hawayenta na zuba "allah sarki mami kina sóna da yawa ,kina son cigabana ta kowani hanya kina nan kina shirya min yadda zanji dadi a gidan d'anki ni kuma mahaifiyata tana nan tana shirya yadda zan cutar da d'anki domin kuwa da magungunan da sukai masa sunyi tasiri sai abinda tace masa zai yi amman duk runtse duk wuya bazata ta'ba barin yaya adam ya juya wa mami baya ba idan sukai nasara akanshi sake kwantar da kanta tayi tana tunanin irin kallon da ATA yake mata wanda ke d'auke da tambayoyi kuma tasan duk akan yadda ya sameta ne ."hakika maryam kinyi gaugau wa arayuwarki "ko a wani matsayi yaya adam zai dauketa fatanta allah yasa yau né cikin zai shiga dan kuwa idan ya shiga kafin yau akwai kutirin bala'i a gidan ."
sosai tayi zurfi cikin tunani qarar wayarta ce ya dawo da ita daga tunanin da take ta yunkura ta mike da kyar ta d'aga tana duba screen din wayarta sunan mahaifiyarta ce ta kalli agogon wayarta tana mamaki kiran me take mata adaidai wannna lokacin ? kamar bazata d'auka ba sai kuma ta kara wayar a kunneta ta shige bayinta tana magana qasa qasa ."ummah lafiya ?okay to shikenan amman karki aiko da komai sãi mami ta wuce “bayan ata ya idar da nafila ya zauna yana addua tare da neman zabin allah arayuwarsa ,wannan shine karo na farko da yayi wannna tunanin da kuma addua wa mahafiyarsa yana zaune har aka kira sallah asuba ya mike yayi alwala ya fita zuwa masallaci ya gabatar da sallah sannan ya dawo bai shiga d'akinsa ba ,ya shiga d'akin maryam domin duba mami wanda alokacin itama mrym tayi sallah tana kwnace abayan mami tsaki yaja tare da jan qafarta d'aya ."
firgigib ta bud'e idanunta ta mike zaune tana shafa idanunta bai tsaya wata wata ba yaja hannunta hanyar waje yayi daita ,maryam wanda keta rokonsa ya barta a kusa da mami amman bai kulata ba yana kaiwa waje yayi fillinging daita ta zube qasa tana dubansa "yayinda shi kuma yake jifanta da wani mummunar kallo,"bai ce mata komai ba dan idan ma ya nuna mata yaji ciwon rashin samunta a cikakkiyar budurwa zata iya cewa kishinta yake wanda shi kuma har ga allah ba kishinta yake ba, kawai yadda ta munafurci mahaifiyarsa ta nuna mata cewar ita din mutuniyar kirkice yafi damunsa "kiji abinda zan fad'a miki kar na sake ganinki a kusa da mahaifiyata domin ita din mutun ce mai tsarki "hannuwanta duka ta d'aura bisa kanta tana kiran "wayyo allah na shiga uku dan ko bai fito fili yayi mata dalla dalla ba ta fahimcesa fiyye da haka "shiiiiii ! karki kuskura ki tasa min uwa daga bacci idan ba haka ba wallahi kinji na ranste sai na d'agawa uwarki da ubanki hankali kin dai san halina, Kinsan abinda zan iya yi dan haka stay a way from my mum ."yana gama fad'ar haka ya juya ya koma d'akin ya zauna kusa da mami yana kallon yadda take sauke numfashi normal ba kmar d'azu ba ."
Maryam kam komawa tayi Kan step ta zauna ta raku'be jikinta waje d'aya tana tunani yadda zatayi "wani hanya zanbi ni maryam ya fahimci shine mutum na farko da ya fara sanina ya mace ?"babu wata hanya tunda rashin hakurinki ya janyo kika mallaka masa kanki baya cikin haiyacinsa zuciyarta ta bata amsa da haka “amman kuma ai kina da sheida ?tabbas kina dashi sister itace sheidata ta d’an ji natsuwa kad’an amman duk da hk hankalinta ba’a kwance yake ba .a hankali ta mike tsaye ta fara tafiya kamar mara laka ajiki jikinta ba qaramin sanyi yayi ba ganin irin kallon zargin da yake mata duk yadda taso taji haushinsa ko kuma taga laifinsa zuciyarta ta kasa kar'bansa amatsayin mai laifi ko wanda zataji haushi sai ma taga kamar ya fita gaskiya kuma kowaye dole irin kallon da zai mata kenan . idanunta taga suna ganin duhu akan kujera mai zaman mutun uku ta zube ta kwanta tana runtse idanunta ."
Karfe takwas saura maryam ta farka ta sauke idanunta akan agogo bata sake yunkurin komawa bacci ba ta tsaya ta gyara ko'ina tare da shiga kitchen da yin abincin da zasu yi breakfast dashi sai dai har lokacin zuciyarta cikin dar dar take ta kasa jin sukuni dan hango katoton matsala wa rayuwarta take . Karfe goma gabdayansu ya'yan mami suka harllara a gidan kuma a dakin maryam .maryam din ce kad'ai bata cikinsu tana parlour’n qasa cikin jimami yayinda ATA ke gabana mami yana magana cikin tsananin damuwa "dan allah sweetheart ki bari na fitar dake zuwa kasar Índia a duba min lafiyarki murmushi iya baki mami tayi tana cewa "adamcy kenan baka son na mutu ko ?mami tayi masa tambayar idanunta na kanshi "wallahi banaso sweetheart!"Yayi maganar kamar zai yi kuka kallonsa kawai mami take without saying a word to him sai dai wani irin tausayinsa ne ya mamayeta da sauran yanuwansa tabbas ta yarda kuma ta amince d'anta na mutuqar qaunarta damuwar dake yawo cikin rayuwarsa ne ya hanashi yi mata biyayya runtse idanunta tayi sai ga hawaye sharr yana sauka akan quncinta ".
hannunta ya riko gam cikin nashi yana cewa "why sweetheart?me yasa zaki zubar da hawayenki "ki daina kuka please idan wani abu kike so ki fad'a min am ready do anything for you sweetheart idan kuma tafiyar ne bazakiyi ba wallahi na hakura bazan takura miki ba amman dai bana son na rasaki, dan a yanzu idan kika mutu ba iya yan'uwana ba hatta mutane gari ma sai sun min gori akan rayuwata aunty shahida ta kallesa tasan sarai daita yake maganarsa ."an waye gari wai yar'uwata ce da kanta tamin gori sweetheart a karon farko naji na tsani kaina duk da nasan tayi min né akan abinda nake miki ,nasan na sakaki cikin damuwa sweetheart ki yafe min lafifukan da nayi miki abaya da wanda zanyi a gaba nasan kina sona da wannna yarinyar ne yasa kema kike takura min amman dan allah ki yafe min tsanar da nake fad'a miki inawa yarinyar a gabanki nasan tana sakaki cikin tsananin damuwa "wallahi sweetheart na sha fad'a miki Kiyi min addua ko allah zai saka min soyayyarta acikin zuciyata amman har yanzu shiru babu wata alama ta qaunarta "ya qarashe maganar muryarsa na rawa mami ta kallesa idanunta cike da ruwan hawaye tace "tabbas yawon fadar tsanar da kakewa maryam tana bata min rai amamn adamcy na yafe maka duniya da lahira burina allah ya had’a hankulanku waje d'aya ."
d’aya bayan daya yan'uwansa suka baro d’’akin zuwa parlour suka had'u gabadayansu suna hira har da maryam nan aunty shahida take basu labarin abinda ya faru "kai auntynmu dan allah da gaske ?wallahi ga maryam ku tambayeta "gaskiya auntynmu kin gama da yayanmu "inji cewar zabiba maryam ta mike tana mai jin tsananin farinciki yadda yan'
uwanta kuma dangin mijinta suke matuqar qaunarta aunty khadija tace "ai gara da,aka gama dashi baki ga yayi laushi ba duk ya canza kala kamar bashi ba ,yaro sai shegen taurin kai da fadin ran tsiya ai ni wallahi mami tayi min daidai ai da mun san d'an wannan shirin film din zai dawo dashi haiyacinsa da tunin an dade da wuce gurin aunty khadija ta qarasa maganar tana miqawa zabiba hannu suka tafa ."
“Allah dai yasa buqata ta biya." nana hauwa'u tayi murmushi tare da mikewa tana cewa “in sha allahu ta biya sai fatan alkhairi ta shiga kitchen inda maryam take qoqarin gama tuwon shinkafa da
miyar agushi .”
tun daga falo kamshin miyar ke shiga hancin nana hauwa'u har sai da yasa yawunta tsinkewa "matar yaya wannan kamshi haka kamar zaa tafi gasar abinci "kai sister yau kuma tsiya zaki min "?”ke mu bar wannan maganar yaya had’uwarku da yaya ta kasance daren jiya ?"nan da nan yanayin maryam ya sauya idanunta suka canza kala alamun zatai kuka "babu wani jin dadi sister yayanki wani kallo yake min wanda bazan iya fitowa na bayyana shi ba .nana hauwa'u ta dafa kafad’anta "karki wani daga hankalinki ko sarewa "me yasa zaki fad'i hka wallahi sister a matukar tsorace nake "ba gani ba meye abun tsoro ?nana hauwa ta fad'a cike da kulawa maryam bata san sanda ta rungumeta ajikinta ba tana share hawayenta ."shadaya da rabi daidai ata ya sauko ya fita daga gidan kuma alokacin maryam ta gama komai har da miya suna tsaye suna hira da nana hauwa’u inda nana hauwa’u take fad’a mata ciki gareta wani ihu mrym tayi ta rungumeta “gsky sister am very happy for you Allah ya hada miki komai da komai “kema sister kiyi ahankali fa dan baki sani ba ko ciki gareki mrym ta zaro ido waje “sister ina jin tsoron abinda zai biyo baya “ina nufin an samu a daren jiya “allah yasa ai da ni kad’ai nasan irin farinciki da zanyi dan ko baya so zan rike abina bare ma da gudu zai kwace suka dariya basu gama rufe bakinsu ba kawai suka jiyo sautin muryar ATA cikin hargagi da tashin hankali .”
"ku yanzu daku zaa had'a baki ayi min haka "? a she yadda nake qaunarku ku ba haka kuke qaunata ba ?"daman na dade dasanin haka ,na gode allah ya saka da alkhairi ku tashi ku bar min gidana gabandayanku bana son ganin fuskokinku” ya qarasa maganar adaidai lokacin da su maryam suka fito rike da hannun juna a bakin kitchen suka ja suka tsaya jikin maryam banda rawa babu abinda yake ".dan kwata kwata bata son ganinsa cikin tashin hankali
“Ya kalli inda maryam suke tsaye ya nunata da yatsan hannunsa “kema bazan qara zama dake ba ki tattara duk abinda kikasan naki ne acikin gidan nan ki bar min gidana na sake ki saki u…”cike da tashin hankali aunty shahida tayi wani Irin qarasowa inda yake ta rufe masa baki tana girgiza masa kai tare da nuna masa yatsanta d’aya alamun d’aya zai furta maryam kuwa tun kafin ta gama ji ta d’aura hannuwanta duka bisa kanta tare da shiga wani sabon tashi hankali"wani laifi suka masa haka ?ta jefawa wankakkiyar kwakwaluwarta tambayar ."
inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda nana hauwa'u ta shiga furtawa tana maimatawa wanda yasa maryam ta kama tana yi bakinta na rawa wannan wace irin maseefa ce inji cewar aunty khadija dan gabadayansu babu wanda jikinsa bai d’auki rawa ba maryam kuwa tashin hankalin da take ciki ya hanata kwakwaran motsi a inda take tsaye magana take son yi koda kalmar hakuri ce garesa amman ta qasa furta komai numfashi kawai take ja ta bakinta tana fitarwa dashi da kyar .”
alamarin ATA ya girmi tunanin yan'uwansa suna kallonsa ya buga ma aunty shahida razananniyar tsawa bayan ya cire hannunta “cikin tsananin tashin hankali da fad’uwar gaba take rokonsa "Adam ba’a saki cikin fushi idan kuma ya zama dole sai kayi kayi d’aya wani mugun kallo yayi mata yana mai janye jikinsa daga nata ya sake maida kallonsa ga maryam “tsayuwar me kike yiwa mutane maza ki fara qoqarin bar min gidana ,kuma haka banason ganin kowacce acikinku wallahi na tsaneku sannan na cire kaina acikinku aunty khadija ma tayi karfin halin qarasowa inda yake yayi saurin ja baya "bana son jin komai kawai kuje tunda kunfi son farincikin yarinyar nan akaina shekara nawa ina fama da zazzafar qaddara amman acikinku ko sau d'aya babu wacce ta zaunar dani ta fahimceni amman dan rashin Imani irin naku daku aka had'a baki na kusanci wannan guntuwar yarinyar wallahi kun cuceni .””ai tun daga zuwa d’auko shahida ya kamata ace na fahimci akwai wani abu a qasa amman babu komai kuje na gode .”
mamaki da matsanancin tsoro suka kama maryam “daman akan ya kusanceta ne ya zartar da wannan hukuncin akanta? ganin maryam bata da niyyar bar masa gidansa ya qarasa inda take ya kamo hannunta yana ja bata iya ce masa komai ba sai ma binsa da take har ya kai bakin kofa ya bud'e tare da hanka d’ata waje ya maida kofar ya rufe da karfi wasu hawaye masu zafi da ciwo suka zubo mata tasa bayan hannunta tana gogewa wasu na sake biyowa kuncinta ."ATA na gama juyo idanunshi ya sauka akan mami tsaye ,cikin tsannain tashin hanakali take kallonsa muryata na rawa tace "me ka aikata haka adamcy ?yanzu sweetheart har za’a had’a baki dake a cutar da rayuwata ?ban shirya yin rayuwata da wannan yarinyar ba saboda me zaa min karya da ciwonki ?numfashi mami ta sauke tana kallonsa "dan haka na saketa saki uku dan bazan qara zama daita ba gabad’aya babu wanda bai furta kalmar “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ba har mami dan kam sai data dafe qirjinta dan wani luguden bugu yayi .”
nana hauwa'u ta qaraso inda yake cikin rud’ewa da rawar jiki ta riko hannunsa ya fixge "har ke ban cireki acikinsu ba kuyi rayuwarku nayi tawa tunda bakwa sona nima na hakura daku har abada zabiba ta bud'e baki ta soma magana cike da in ina "ni ..ni dai yaya wallahi banda ni dan ba dani aka shirya komai ba hasalima yau din nan nasan komai aunty kahdija ta ta'bata alamun tayi shiru amman ta zame jikinta "dan allah yaya karka mana haka wallahi muna tsananin sonka muna qaunarka ta durkushe kasa tana jan gwiwowinta zuwa garesa ya tsaidaita ya juya ya haye sama a matukar fusace yake taka step ."wani irin naunayen ajiyar zuciya suka sauke atare "mami ta kallesu daya bayan tace "garin yaya kuka yi wannan kuskuren ?yaakayi kuka bari yasan komai ? tayi masu tambayar ajere cikin tsananin tashin hankali,gbdynsu sukai shiru dan basu da bakin magana ta sake sauke ajiyar zuciya "ina maryam take ? tana waje ! nana hauwa’u ta bata amsa cikin kuka kai tsaye kofar mami ta nufa ta bude inda taci karo da maryam durkushe tana zubar da hawayen mami ta kai hannunta ta d'ago ta ta rungumeta ajikinta tana shafa bayanta .”
jinta ajikin mami yasa ta sake fashe da wani sabon kuka mai ta’ba zuciya " dan allah mami ki fad’awa yaya bani da masaniya akan komai ,kuma allah danasan shiri ne ciwonki da bazan ta'ba amincewa ba gara na cigaba da rayuwata haka dashi "kukan ya isa haka abinda ya faru ya wuce ba kuma zai gogu ba ta zareta ajikinta suka koma parlour'n ta zaunar daita akan kujera sannna ta zauna a gefenta tana rarrashinta "yanzu mami ya zaayi kenan ? "ku da kuka tona asirin komai sai kusan yadda zakuyi dan babu ruwana ,ban da son jawa mutane tashin hankali meye abun baje hira a gidansa alhalin kusan halinsa? Kiyi hakuri mami ki yafe mana inji cewar aunty shahida "mami dan allah kije ki shawo kansa ya janye sakin ya maidashi d’aya Ke kadai ce zaki iya shawo Kan yaya nana hauwa’u ta fad'a tana share hawayenta "da sauri maryam ta kalli inda take zaune “sister saki ukun yayi min kenan ?nana hauwa’u ta gyad’a mata kai alamun “eh!ahankali ta runtse idanunta gam tana jin wani irin rad’ad’i da ciwo acikin zuciyarta wallahi tayi wa kanta alkawari muddin ba ita ce acikin gidansa ba babu wacce zata zauna cikinsa cikin jin dadi, duk inda ake zuwa dan biyan buqata zata domin ta hanashi jin dadin rayuwa kuma duk runtsi sai ta dawo gidan zaman lafiyarsa ya janye sakin kamar yadda sister ta bada shawara bata gama fita daga wannan tashin hankalin ba taji muryar aunty zabiba ta karad’e parlour’n “.
“gsky mami ya kamata mu ajiye son rai a tsaya a duba lamarin yaya shima tunda ya nuna baya son aurenta kar a wani maidashi a hakura kawai allah ya hada kowa da abinda yafi zama alkhairi .” da sauri maryam ta bud’e idanunta ta kalli inda take zaune qirjinta na wani irin bugawa "bayan ya gama maidaita qaramar bazawara zaki fad'i haka ? aunty khadija ta fad'a a fusace "to meye amfanin wannna auren tun kafin ayisa yace bai so ?tunda akayi auren nan ku fad'a min rana daya wanda muke da kwanciyar hankali ?”kullum zuciyarmu cikin fargaba take, yin aure halal ne haka barinsa halal ne idan ma zai gare rayuwarsa haka abarshi mana matsawar bazai dinga biye biyan mata ba ,”tunda suka fara magana a tsakaninsu mami bata ce uffan ba har Qarfe uku ATA bai sauko ba gabdaya cikin damuwa da tashin hankali suke most especially maryam wacce har wani rama tayi nana hauwa’u dake kusa da maryam ta dinga kwantar mata da hankali “sister karki d’aga hankalinki yaya zai janye sakin da yayi miki yanzu fa kin rigada kin zama jinin jikinsa jininsa gauraye yake da naki wata killa ma akwai ajiyarsa ajikinki shiru kawai tayi dan bakinta bazai iya furta komai ba dan hatta miyon bakinta ya qafe idan tayi qoqarin had’iye wa jinsa take tmkr mad’aci ."
Da misalin karfe biyar ne mami ta mike ta haura sama ta shiga dakin ATA ta iske shi zaune akan kujera kwaya d'aya dake dakin yayi baya da kujerar yana kallon saman d’akin ganin shigowarta ya runtse idanunshi gam .da sanyin jiki mami take qarasowa inda yake stood ta janyo ta zauna gabansa ta zuba masa ido tana kallonsa tana nazarinsa dakin yayi shiru tamkar babu kowa aciki har tsawon minti goma mami na zaune agabansa yadda batayi magana ba haka bai bud’e idanunshi ba ta kira sunansa "adamcy nah! shiru ne ya sake biyowa baya ta kai hannunta ta kamo hannunsa ta kai bakinta tana sheshekan kuka saukar hawayenta yaji a hannunsa ya d’an bud'e idanunshi akanta tabbas hawaye ya gani yana sharara akan kuncin mahaifiyarsa abinda ya tsani gani kenan naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske sannan ya kai dayan hannunsa yana d’auke mata hawayen fuskarta dake kwarara sannan ya motsa lips dinsa da kyar "why sweetheart?Bata ce masa komai ba illa cigaba da zubar da hawaye "da fatan ba Adam bane yayi sanadiyar zubar hawayen nan ?ahankali ta gyada masa kanta alamun shine.”
numfashi ya sauke yana son sanin dalilin kukanta "adamcy kana son saka sweetheart dinka kuka,baka jin damuwa yadda kake saka sarauiyar dad dinka kuka ?mami ta furta tana dago da idanuwanta ta zuba masa da matuqar damuwa "ina cikin damuwa adamcy !"nima acikin damuwar nake” jin sautin muryarsa cikin tsanani bacin rai ya qara d’aga mata hankali ya zame hannunsa ya mike ya qarasa qarahen dakin ya tsaya rike da kugunsa yana jin zafi da ciwon abinda mahaifiyarsa da yan'uwansa suka masa "."Adamcy na !ta sake kiran sunansa a karo na biyu yana jinta yaki juyawa mami ta cigaba da magana "ka sake min wani alfarma a karo na biyu adamcy .” ya d’an juyo a natse ya kalleta "kayi hakuri ka janye sakin da kawa maryam ka maidashi d’aya sannan ka maida maryam d’akinta saboda allah da girman mahaifinka da darajan haihuwarka da nayi "ya bud'e baki yi zai magana "karka ce aa adamcy ta katse shi ta hanyar fad’ar haka “kayi dan allah da mahaifinka da kuma ni da nayi silar zuwanka duniya domin muddin ka rabu da maryam zata shiga damuwa mai tattare da tashin hankali idan ta kasance cikin damuwa nima zan shiga domin nice silar komai .”
ya juyo sosai ya fuskanci mami "abu na farko tana rayuwarta batare da kai ba na shigo daita cikin rayuwarka, abu na biyu yanzu kun zama abu daya wayasani ma ko rabo ya shiga tsakaninku "gaksy ni sweetheart bana son abinda kike min akan yarinyar nan ban gama fita cikin matsala ba zaki sake shigo min da wata damuwa "ba zancen shigo da damuwa bane adamcy naji hakan ajikina akwai rabo a tsakaninka da maryam .”yayi shiru kawai yana mamakinta a ransa yace “ai kuwa badani ba dan bazan sake gigin kusantarta ba kuma ni bana jin haka ajikina domin spam din daya fitar ba d’a bane dan duk spam din da zai zama d’a fitarsa nada matuqar wahala daga jikin d’an adam mami ta d'an yi gyaran murya "ni mahaifiyarka ce zan iya sakaka kayi min abu dole koda kuwa ranka bai so amman a wannan karon banason na maka dole alfarma nake sake neman da baka hakuri saboda dalilai masu yawa dan allah ka janye ka kuma maida maryam iska ya fesar mai zafi daga bakinsa sannan yace "shikenan naji na janye na maida ita ."iyakar abinda ya fad'a kenan ya fice daga dakin domin idan ya cigaba da tsayuwa zata nemawar yanuwnasa afuwa abinda bazai so ba kenan shi dasu har abada .”
“Alhamdulillah! mami ta dinga furtawa tana nemammansa afuwa da sauki a wajen Allah suna zaune jugun jugun ya sauko ya nufi kofa "zabiba ta zabura ta mike zata bishi aunty shahida ta dakatar daita tana cewa "da alamun kin fara manta waye adam arayuwarki wallahi zamanki matar aure da ya’ya bazai hanashi yi miki mugun bugu ba mu barshi har ya sauko da kanshi "ni dai zan wuce gida dan bazan bari wannan fuskar ta sake shigowa muyi ido hudu ba inji aunty khadija gabdaya suka kwashe da dariya ban da maryam wacce idanunta sukayi jajur tsabar kuka” nima tashi zanyi na wuce nasan mami zata shawo kansa suna shirin mikewa mami ta sauko "mami ni zan wuce gida inji cewar aunty khadija itama zabiba ta gyara zaman mayafinta nima zan gudu dan yau sai wani ikon allah ,allah yasa dai ya sauko "kun gama hadasa mana tashin hankali shine zaku gudu daya bayan daya ?"dan allah mami Kiyi hakuri bamu san zai dawo ba tunainmu fitarsa yayi nisa "ai shikenan tunda ya janye sakin .""
Wani irin ihu nana hauwa ta saka tare da zuwa inda maryam take ta rungumeta "sister yaya ya maidake ai na fad'a miki yanzu kin zama wani bangare na rayuwarsa "kunga kuzo ku wuce sai qarshen wata kenan "in sha allahu mami suka hada baki gabdayansu sukai mata sallama gidan ya saura daga mami sai maryam nasiha da kwnatar da hankali mami tayi tawa maryam muryata a dashe tace “mami na gode “har karfe goma suna zaune a parlour'n sallah ne kawai Ke tashinsu amman babu ATA babu alamunsa har shabiyu ta buga suka rufe kofar parlour'n batare da sun murd’a key ba koda zai shigo suka hau sama daga maryam har mami babu wanda ya runtsa sai faman juyi suke bayan sunyi sallar asuba ne suka kwanta inda wani naunayen bacci ya d’aukesu sai karfe shadaya suka tashi da sanyi jiki maryam ta sauko domin samawar mami abinda zata ci kawai ta gansa kwance akan kujera ya daura tafin hannunsa d’aya a daidai mararsa yayinda d’ayan hannunsa ke saman goshinsa idonsa biyu sai dai tunaninsa yayi nisa domin likitansa bai dade da wucewa ba abinda sakamakonsa ya nuna ne yake yawo acikin brain dinsa “wai anyi masa amafani da wasu kwayoyin jima’i ne wanda shine ya haddasa masa azababben ciwon kai da bai jin magani “ how come ?ya tambayi kanshi Idanunta na kanshi ta shige kitchen ta fara aikinta .”
Kwana bakwai kenan da ATA ya maida maryam
sai dai bbu wani saukin al'amura dan babu abinda ya canja daga yanayin zamansu duk da mami dake tsakaninsu dan bai kallon duk inda mrym take idan yana gida hatta mami baya wani hira daita harkar gabansa kawai yake .addu'a dai mami take qara yi kan Allah ya canza masa rayuwa ya kuma daidaita tsakaninsu yasa zaman lfy ya shigo cikin rayuwar aurensu .yau tunda safe maryam ta tashi da aikace aikace gyaran cikin gidan, aiki kawai take kmr wacce tasha kwaya domin koina yayi kura dan ta kwana biyu bata kakkabe gidan ba tun kafin zuwan mami duk mami na zaune tana kallonta shirun da mami tayi ne yasata kallon inda mami take mami tace “anya kuwa mrym bazaa kawo miki masu aiki ba dan naga aiki yayi miki yawa kuma ko babu komai zasu dinga d’auke miki kewa idan na wuce .?tayi murmushi kawai batare da tace komai ba “ki bar aikin nan haka mrym ki huta gobe zansa a kawo miki masu aiki sai suyi ,yanzu zanyiwa cristi magana tasa akawo mutun biyu nasan sun isheki ?”
Maryam ta girgiza kai alamun “a’a ! “mami karki wani damu da masu aiki dan ni bana ra’ayi masu aikin. bbu abinda na fi tsana a rayuwata sama dasu dan wallahi wasu masu aikin ba aiki yake kawo su ba , mami tayi murmushi dan ko bata fad’a mata ba ta fahimceta “ to ai shikennan Allah ya bada sa'a Amman dai yanzu ki bari ki dan hutu haka. naga ko karyawa bakiyi ba ,ai yanzu nan zankarasa nama kusan gamawa.mamaki ya cika zuciyar mami ganin irin aikin da take wanda bata yinsa a lokacin da take gidanta komai masu aiki suke yi mami ta gyara zamanta tare da kunna TV tana kallo daga nan inda take zaune suke hira da mrym din ,kafin wani lokaci mrym ta gama komai har abinci .”koda yamma tayi ma zagaye mami tayi ta shiga kitchen ta shirya masu lafiyayen abinci , farar shikafa ce da miyar pepesoup din kayan ciki ,sannan da miyar pepesoup din freshe fish dataji kayan hadi da ganye ugu aciki sai kamshin ke tashi .”sannan taje ta shirya komai tsaf tsaf a dinning ta bude kulolin abinci ta dinga d’aukar girkin hotuna da vedio byn ta gama ta rufe komai taje ta sheka wanka ta hade cikin daguwar rigar atamfa wacce ta sha stone work sai kalli take zubawa ga wani kamshi na musamman dake tashi ajikinta. karku manta mrym akwai son kwalliya da posting a social media tana gama kwaliyar ta fara zubawa kanta hotuna kala dabam dabam kamar yadda ta yiwa girkin sai datayi posting sannan ta soma qoqarin fitowa ”
ahankali take saukowa zuwa parlour kasa tayi maseefar kyau sai kyali take abu ga farar mace kusa da mami ta samu guri ta zauna sai dai idanunta na kallon tsaitin kofar shigowa mami ta kalleta tana murmushi tace “ kai Kai maryam kinyi kyau ,yau adamcy bazai ganeki ba “mrym ta saki wani murmushin jin dadi tana cewa “kai mami har wani kyau nayi . ?”wallahi kinyi kyau sosai kuma naji dadin ganin wannan kwaliyar daman inata son nayi miki magana akan kin rage kwalliya ba kamr sanda kike gida ba, marym ta sake yin murmushi “gsky kinyi fine sosai allah yasa adamcy yaga kyan kwaliyar nan “Ameen ta amsa a cikin ranta .”bayan kamar mintuna goma suka jiyo sallamarshi a ciki suka amsa alokacin da yake taku cikin parlour, kunnenshi makale da waya yana magana da saurinta ta mike ta tarbeshi zata karba briefcase din hannunsa ya hanata batare da ya kalleta ba ya nufi hanyar sama yana jan tsaki dan baqaramin jin haushin nacinta yake ba“.
jiki a sanyaye maryam ta shige kitchen ta zauna tana runtse idanunta yayinda zuciyarta ke mata wani irin zugi mami sarai ta fahimci damuwace tasa yin haka nan da nan itama taji damuwa zuciyarta ta sosu ta mike ta shiga kitchen din ta iske mrym zaune har lokacin idanunta a runtse suke ta kai hannunta ta riko hannunta ba tace daita komai ba suka fito kai tsaye dining area suka nufa ta zaunar daita itama ta zauna tana ta’ba qirjinta alamun ta kwantar da hankalinta .”byn kmr minti talatin ATA ya sauko jikinsa sanye da riga white t shirt da wando jeans three quater sai kamshin turarensa Red ne yake tashi ajikinsa , kai tsaye dinning area ya nufa inda ya hangi su mami zaune da alamun zaman jiran fitowarsa suke .'ahankali ya karaso gurin tare da samu guri ya zauna kusa da mami yana gaisheta “ai na d’auka bazaka gaisheni bane ?dan ka wani shigo ko kallon inda mutane suke bakayi ba ta fad’a cikin rashin sakin fuskar numfashi ya sauke yace “barka da dare sweetheart ?barka ya aikin ?alhamdulilllahi ya fad’a atakaice sannan ya ciro wayarsa yana operating .”
ahankali mami tayi wa mrym alamar ta koma kusa dashi ta tashi ta koma kusa dashi ji yayi kamar ya tashi ya canza guri amman ya share ya cigaba da dandana wayarsa “maryam bismillah kiyi serving dinmu wani irin mikewa tayi wanda yasa gabadaya santsar jikinta girgiza most especial qirjinta d’agowa yayi da niyar sauke mata ruwan bala'i idanunshi yaci karo da girjinta kallo daya yayiwa Rabin nonuwanta ta saman rigarta ya d’auke idanunshi amman duk da haka say da yanayinsa ya d’an canza nan da nan kwalkwaluwarsa ta shiga circulating ya dinga jin wani iri a sansar jikinsa abinda bai ta’ba ji akanta ba kenan sai yau .”cike da natsuwa tayi serving dinsa. bawani abinci kirki ya ci ba ,ya ture plate din gefe 'ahankali ya maida bayansa ya jingina da kujerar da yake zaune akai Tare da dan zamowa kadan yana duban mami itama mami shi take kallo tana tabe baki “ba dai har ka koshi ba ?”
ya dage mata girarsa daya alamun haka ne ,”yanzu duk yadda girkin nan yayi dadi ? ya yatsina face dinsa kawai batare da ya cewa mami komai ba dan bai ji wani dadin da yayi ba murya a sanyaye mrym tace” to ko na hado maka coffee ne?bai ce uhm ba bare um uhm parlour ya dauki shr har kusan tsawon minti goma batare da ko tari yayi ba , sai da mrym din ta km maimaitawa tmbyrta tukun muryarsa a dake yace “ please banason damuwa dan Allah“
“maryam je ki had’o masa zai sha tsabar jin kai ke damunsa jin haka yasa mrym din mikewa 'ahankali tana jujjuya mazaunanta har ta nufi kitchen mami tace “adamcy kalli can ya kai idanunshi inda ta muna masa bayan maryam ya hango ya waigo ya kalli mami”sweetheart me hakan yake nufi kuma ?me nayi ?na nuna maka ne kaga irin halitta dirin da allah yayi wa matarka ,mrym nada daidai nata kyau adamcy “takaicin da ya tsaya masa a makwashi ne ya samu ya hadiye da kyar yana hango tahowarta da yadda take motsa qirjinta saurin d’auke idanunshi yayi ya kamo lip's dinshi na kasa yana cizawa da karfi har ta karaso ta’aje masa coffee a gabansa bai dana cizan lip's dinshi ba,yana son shan coffe din amman yaki d’auka ya sha .”
Mami ta zuba masa ido tana kallonsa kafin ahankali ta d’auki cup din coffe ta mika masa babu musu ya kar’ba ya fara sha yana lumshe ido mami ta cigaba da kallon yadda yake shan coffe sak mahaifinsa kusan har ya so ya zarta tariq abdallah da komai ya d’an dubi mami yace “ ya’akayi sweetheart ?ta hararesa tana cewa “ban sani ba nan kafi kauri ga abinci ka zauna kaci yadda ya kamata aa sai ruwa “tsam ya mike tsaye ya soma taku rike da cup “sweetheart ni zanje na kwanta bacci nake ji tabi bayansa da kallo ,”to Allah ya tashemu lfy “daren ranar sam ATA kasa runtsawa yayi kwana yayi yana juyi yana watsa jikinsa ruwa hannuwanshi yasa duka ya dafe jijiyarsa dashi yana juyi da kyar ya samu ya runtsa sakamakon wani irin feeling da ya dinga tasoma masa sai wuraren asuba bacci mai nauyi yayi nasarar daukar shi.”washegari da sassafe ya bar gidan ya wuce office .”
zaune yake a office dinshi aiki yayi masa yayinda kanshi ke duke yana fama da aiki rubuce rubuce dake gabansa yaji Knocking din kofa , kansa na duke ya bada izinin shigowa batare daya dago kansa ba yaga ko waye ba ammar ne ya shigo cikin office din da sallamarsa ATA ya amsa batare da ya dago kansa ba ya cigaba da abinda yake" ganin haka Yasa ammar ya tsaya abakin window , yana kallon haraban ma’akatan wanda ma’aikata ke kai kawo dan yasan tunda ya iske ATA kan aiki bazai taba sauraransa ba matsawar bagamawa yayi ba dan sanin da yayi masa kenan na maida hankalinsa matuka akan aiki idan yana yi .Kusan minti shabiyar yayi tsaye , sannan ya soma takowa ahankali izuwa bakin makeken tablet din da ATA ke zaune ,yaja kujera daya ya zauna yana dubansa, Sai lokacin ATA ya d’ago tsumammun idanunsa ya dubeshi har ka gaji da tsayuwar kennan ?
“Ba dole nagaji ba dan naga alamun sai nakai ga zama tukun zakiyi lokacina ya fad’a hk yana mikowa ATA hannu suka gaisa ,yaushe ka dawo qasar ? Dariya ammar yayi yana cewa “shekaranjiya na dawo yau km nace nazo naganka ,ko bai yi bane ?
Wani irin farinciki ya lullube zuciyar ATA ya danyi murmushi har dimple dinsa ya lotsa tsantsar kyawunsa ya sake bayyana ,yana son a dinga nuna masa kulawa da soyayya ,ammar yace aboki lfy kuwa irin wannan farinciki haka ?”babu komai nima haka na tsinci kaina ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune yana jujjuyawa dashi , ammar yace “ya mami da dolen dolalo ?sai da ATA ya yamutsa fuska sannan yace “sweetheart tana lfy ita dayar ce dai gsky bansani ba ammar ya sake yin dariya kace zaka qara aure har yanzu shiru ko ka canza shawara né zaka cigaba da zama da dolen dolalo?
“Ammar kafa dawo kenan “ya fad’a yana jan tsaki “dan kaki bin shawarata ne wallahi da kaga maryama zata maka yarinyar abar tausayi ce ga maraici ga rashi “bana jin zan iya auran irinta koda zan yi aure ,kai ina ganin na hakura ma .ok zaka cigaba da zama da mrym din kenan ? ya gyada masa kai kawai ,amman to why not ko sau daya kaga maryama ni ina dalilina son ku had’u da juna “dan Allah ka rabani da wannan shirmen ai tunda sunansu ma yazo d’aya da yarinyar nan naji na tsani had’uwa daita ammar ya bud’e baki zai sake yin mgnr d’aya daga cikin wayoyinsa ya dauki kara 'ahankali Yasa hannunsa ya janyo wayar maganar second biyu yayi ya sauke wayar ammar na zaune yana kallonsa har yagama wayarsa , yana shawarar yadda zai bullo masa yafi son ya ganta yana son yaga rud’ewar da zai yi akanta ,hira suka cigaba dayi kafin daga bisani ammar yayi masa sallama ya wuce .”
Satin mami biyu ta soma tattara kayanta babu yadda maryam batayi ba akan tayi zamanta tace aa “dan allah mami ki zauna banason ki tafi “aa maryam shiyasa nace akawo miki masu aiki bakin kishinki ya hana tayi murmushi “kai mami wani kishi kuma ?aikin gidan bashi da wani yawa fa koma dai menen Ya rage naki ni dai tafiya zanyi gobe .
da daddare da ATA ya dawo ta sheida masa “ in sha allahu gobe zata koma gida “sweetheart kiyi zamanki mana “a’a bazan cigaba da zama ina ganin wulakacin ba dan banga abinda zamana yake tsinana maka a gidan ba hassalima qaro sabon wulakanci kayi lada ya isa haka idan ka ga dama ka duba allah kayi wa matarka adalci idan kuma kaki zakaje ka had’u da allah né sai abu na gaba idan zaka zo qarshen wata kazo min da maryam washgari ta kasance asabar da misalin karfe hud’u na yamma suka rako mami haraban gidan inda ATA ya bud’e mta bayan mota ta shiga ta zauna maryam ta zagaya dayan bangaren ta ajiye mta jakar kayanta mami ta dubi ATA “ka tabbatar kazo qarshen wata sannna kazo da maryam "in sha allahu ya fad’a tare da rufe mata murfin mota yana cewa direbanta ya jata Ahankali mami tayi warning din glass din mota tace “bani wayarka !babu mutsu ya mika mta number mrym tasa masa tayi saving number da sunanta “ga number mrym nan na saka maka ka dinga qoqarin sauke nauyin dake kanka .”
Itama maryam tace mata “nasan kina da numbersa ki dinga kiran mijinki koda kuwa bazai d’auka ba duk runtse ki sauke nauyin dake kanki allah ya had’a hankulanu tace “Ameen tana daga mata hannu suna tsaye har mota data shiga da masu tsoron motar suka bar gida sannan suka shiga ."bayan tafiyar mami da kamar awa d’aya ya sauko sanye da wasu kaya ya ajiye wayoyinsa akan center table ya samu waje ya zauna ya dauki remut ya kunna tv ya qara karfin ac ya daura kafafunsa akan center table yana duban tashar labarai ahankali maryam ta fito daga dakinta cikin sand’a take saukowa sakamakon yunwar da take ji dan tun abincin safe ne acikinta ko kallonta bai yi ba ta shiga kitchen ita kuwa tayi haka né dan tasan yanzu sai wani ikon allah tunda mai shiga tsakaninsu bata nan bata ki bin umarnin mami ba kullum tana iyakar qoqarinta na kiransa kmr yadda mami tace wani lokacin ya dauka ya danqara mata bakar magana wani lokacin kum bazai dauka ba ahaka har suka zo qarshen wata .”
******
Alhamdulillah DG m malik ya fara samun lafiya sai dai baya iya magana sosai idan baka matso da kunnenka kusa da bakinsa ba bazakaji abinda yake fad’a ba ,haka zalika sansar jikinsa ba koina yake iya sarrafawa ba yana kwance yayi wa matarsa alamar ta d’auko wayarsa ,byn ta dauko ta tsaya kusa dashi kamar yadda ta saba, ganin magana zai yi ta rankwafo daidai bakinsa anatse ya fara magana sunan wanda ya ambata da abinda yake son tayi masa ne yasa ta soma rubuta text message ta turawa ATA sakon ya samu ata alokacin da yake zaune a a gurin shakawata a gidansa tare da yaronsa V.O ahmed ya d'auki wayarsa ya soma karanta sako Kamar haka "Assalam, mai gida yaushe zaka shigo saboda ina da magana da kai . ATA ya ajiye wayar cikin jin haushi yana kallon Ahmed "M Malik na yi maka uzuri saboda tunaninka ya canza idan ba hk ba zakayi magana dani me yasa bazaka fad'a min ba ko ta hanyar text message ne tunda zaka iya rubutu ya qarasa mgnr tare da yin shiru "ranka ya dade wannan gsky ne DG m malik yana cikin wani hali sai dai addua kawai "to allah ya bashi lafiya amman ni ko zan shiga wannan kasar ba yanzu ba watakilla ma har su dawo qasar nan bazan samu damar shiga ba ya juya ya kalli Musa. "musa Kai !"musa ya qaraso da sauri ya iso gaban ATA cike da ladabi "dauki buhunhuna nan na Ahmed ka kai masa bayan motarsa "to yalla'bai!ya juya da sauri suka cigaba da tautaunawa ."
"Gaskiya kema maryam da laifinki, taya zaayi ace har wata shida cikin na bakwai da yin aure amma ki kasa shawo kan mijinki ku zauna lafiya bare har wani abu ya shiga tsakaninku maryam ta girgiza kai tana cewa “ya kusanceni sau d’aya bayan nan ne dai har yanzu shiru gashi nayi duk abinda zanyi dan mu zauna lafiya dashi amman yaki bani lokacinsa "ki bude masa aiki kawai ko zama ko rabuwa maryam tayi saurin zaro ido tana cewa "kai ni’ima bazan iya ba gskiya ai sai ma ya kasheni da duka ."ni’ima diyar yayar mahaifiyar maryam ce da suke ciki daya aikin soja né ya kawota lagos daga zuru “duka ?”Ke kuma sai ki tsaya ?”idan dai zai huce idan ya dakeni sai na tsaya mana "to dama fa an fada min bakya son laifin mijinki,kowa yaga wannan abun yasan mijinki baya sonki kuma bakya gabansa amman ke har wani side dinsa kikeyi maryam ta zauna a kujera a sanyaye ko da yake " illar wani auren zumuncin kenan “wallahi ni’ima ba side dinsa nake ba kawai soyayyarsa ce tayi min yawa shiyasa nake hakurin zama dashi dan ko na bar gidan nan gangar jikina ne ya bar gidansa amman ruhina yana gidan nan “.
“Ai kuwa kina da aiki ta yaya ma kike bashi kulawa muji idan akwai inda kuskure yake ki gyara ?babu abinda banayi masa na kyautatawa duk ta zayyane mata amma duk a banza ko kallona fa baya son yi “amman maryam kuma bakya tunanin ko wata ce take dauke masa hankali a waje ? maryam ta girgiza mata kai tana cewa “bana tunanin haka! dan miskilancinsa bazai bari ya kula mata ba abinda na fahimta kawai shine, yaya Adam yana son wata yarinyar mafarkinsa amman azahiri bai san meye so ba "ta yaya zaace mutum kamar wannan bai san meye so azahiri ba ?"To in ma dai ya sani banga hakan a zahiri ba sai a mafarkinsa ya sani , amma ina fatan wata rana ya dandani radadin so irin wanda nake dandana a zahiri ko hakan zai sa ya tausaya mini ya bani kulawar data dace. " ina zai dandana tunda kince bai san meye so a zahiri ba ?ni’ima ta fad'a sannan ta soma cin abincin da maryam ta kawo mata maryam tayi shiru dan itama bata san mai zata sake cewa ba .”
ATA V.O d Ahmed duk suna inda suke zaune Ahmed ya russuna cikin fara'a yace “nagode sosai sir ! Allah ya kara arziki yasa kafi haka.ATA bai ce uffan ba tunin musa ya soma daukar buhuhunan ya nufi bayan motar ahmed ,atare ahmed da ata suka mike suka biyo bayan musa ahmed ya shiga motarsa , masu gadi suka bude masa get ya fita.ATA ya kalli kofar fitowa daga falo a tunaninsa zai iske mrym a wajen tunda tasan fita zasuyi yau ya kalli agogon hannunsa ya d'an ja tsaki. “me wannan yarinyar ta tsaya yi ne tana bata min lokaci ? ya sake jan tsaki yasa hannu a ajihu ya ciro wayar sa ya soma kokarin kiran layinta ya saka a speaker ,wayar maryam dake ajiye a kujera ta soma ringing.ni'ima dake cin abinci da maryam wadda ke zaune a kujerar dake fuskantarta suka juyo suka kalli wayar ,maryam ta mike ta karasa ta dauki wayar ta duba sannan ta kalli ni'ima cikin alamun tsoro "mijinki ne ko? maryam ta gyada mata kai alamun"eh " Kar ki dauka, kyale shi ya karaci kira har ya gaji cikin tsoro maryam tace "saboda me?”wallahi Ina mugu mugun jin tsoron fad'ansa ke bai ma ta'ba kirana ba sai yau fa yau din ma nasan dan fitar da zamuyi ne “ tana rufe bakinta kiran ya katse cikin jin haushi tace"wai ke baki da 'yanci ne? bai ga kinyi bakuwa bane da zai dameki ? wallahi Ki rage jin tsoronsa haka ,idan ba haha ba bazaki ta'ba yin martaba a idanunsa ba "haba ni'ima ya kike irin wannan maganar bakiji nace miki fita zamuyi ba ? gidan mami zamu kuma Ko babu aure a tsakanina da yaya Adam, dan uwa nane fa!"To sai me...?ta fad'a adaidai lokacin da ATA ya shigo falon fuskar shi a daure yana kallon maryam a kaskance "bakya ji ina kiran wayar ki ne .”?
Adai cigaba da bibiya
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kuɗi ne mai buƙatar karantashi bayan na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number ɗin 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan Number 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntuɓii chaneel ɗina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 21
Shiru maryam tayi tamkar ba da ita yake magana ba, sai dai ta tsura masa idanunta yayinda acikin zuciyarta tsoro ne daskare muryarsa a tsarƙe ya cigaba da magana. “fito mu tafi karki ɓata min lokaci” jarumta ta aro ta sanyawa jikinta tana faɗin. “kayi haƙuri kafin nayi picking ne kiran ya katse kuma kaga ai nayi baƙuwa bai kamata na tafi in barta ba” ATA ya kalli Ni'ima dake zaune a wulaƙance sannan ya kalli maryam. “Ke ban son iskanci ni zaki faɗawa kinyi baƙuwa ?ina ruwana da ita?” yayi maganar a tsawace wanda yasa hantar cikinta kaɗawa nan da nan tsoro da matsanancin firgici ya bayyana a gbdy ilahirin jikinta. “darajan sweetheart kikaci if tace nazo mata dake kema Kinsan har abada bazan taɓa haɗa tafiyata dake ba” yana gama faɗar haka ya juya da sauri ya fita daga parlour'n . “maryam ta dubi Ni'ima cikin tsananin damuwa tace . “Kinga abinda nake gudu ko? gashi har yayi fushin nashi zuciyarsa iya wuya ne kamar jira yake ya hau zubama mutun faɗa” Ni'ima ta miƙe tsaye tanabin ƙofar daya fita da kallo sannan ta kalleta cikin fushi. “wallahi maryam wannan mijin naki bai ɗaukeki da daraja ba, hatta komai ma dake cikin gidan mai amfani da mara amfani ya fiki muhimmanci agurinsa” maryam tayi shuru kawai tana kallon Ni'ima da sauraronta “wannan auren zumuncin da akayi muku gsky ke aka cuta”
Maryam ta karkata kai tana cigaba da kallon Ni'ima “haka kike gani?ai kinfi kowa sani wannan maimaci ne nayi miki amman kinsan ke aka cuta” “nifa ba cuceni ba ni'ima dan ina son yaya adam tun asali in takaice miki tun kafin mahaifiyarsa tayi tunanin haɗamu dan gsky da ban samesa ba da haƙurina zai gaza domin kuwa ciwon zuciya ne zai kamani”
“ke da Allah rabani da maganar wata shegiyar soyayya uwarsa tasan duk wannan cin kashin
da yake miki?” “tasan komai kuma tana iyakacin ƙoƙarinta, bata son duk wani abinda zai ɗaga min hankali duk abinda yayi muddin zata gani ko taji labari sai inda ƙarfinta ya ƙare” “dai-dai kenan idan ya ɗaga miki hankali ki dinga kirata ki ɗaga mata hankali, idan kuma tsoronsa ya hanaki aikatawa sai ki zauna da baƙin ciki” Ni'ima ta soma yafa gyalenta tana kallonta “zo mu jera sai mu rabu a titi” maryam ta gyara zaman mayafinta ta ɗauki wayarta tare da sakala hand bag suka nufi kofar fita daga parlour'n .
Mai gadi ya buɗe tafkeken get ɗin gidan motocin ATA suka nufo kofar a hankali zasu fita a dai-dai lokacin maryam da Ni'ima suka fito daga parlour suka ga motocinsa. “lah Ni'ima kinga bai tafi bama ashe, bari in tsaida shi basai naja mota ba kema ki shiga mu rage miki hanya” ta nufi motar da sauri tana ɗaga masa hannu “yaya Adam! Yaya Adam..!!” yana kallonta amman bai bada umarnin a tsaya ba motocin a guje suka fice daga gidan ."maryam ta tsaya tana kallon Ni'ima mai gadi ya rufe get din Ni'ima ta iso gaban maryam cikin fushi tana kallonta. “haba maryam! akan me zakiyi irin wannan zaman rashin darajar kamar wata baiwa?wallahi in baki ƙwaci ƴancinki ba ciwon zuciya ne zai kasheki a banza da wofi” cike da damuwa Maryam tace.“To ni yanzu ya zanyi? babu abinda ban masa ba tun daga Kan tsafta biyayya duk nayi kamar yadda na fad’a miki hatta taimako umma tasha aiko min akansa amman duk a banza ko kallon arziki ban ishesa ba” “na baki shawara?” da sauri maryam ta gyaɗa mata kai. “Kawo kunneki” maryam ta matso kusa daita sosai tayi mata raɗa a kunne nan take maryam ta girgiza kai “ke kan wannan mutumin fa baya jin komai gara kawai na cigaba da zama haka idan da rabon zai canza ina fatan haka .”
Tare suka jero inda motar maryam take a parking space ni’ima na cewa “ki samu lokaci ki shiga Zuru da kanki yarinyar wallahi sai yadda kikayi dashi duk wannan taurin kan sai kin nema kin rasa “akwai wata tukunya da umma tace zaa aiko min daga can , “eh nasan dashi ai zuwa wani sati zaa aiko zan sa a hado miki da wasu abubuwa ma ,”ta fad’a adaidai lokacin da suka shiga mota suka bar gidan niima na cigaba da magana “ai ina fad’a miki muddin kikayi masa amfani dashi zakiyi mamakin yadda zai rikice ai wallahi sam ya’yan zuru basu cancaci wulakanci a gidan miji ba mu dake juya maza son ranmu amman ace ke kin bigi a wulakance a gidan mini “wallahi ni’ima ni kaina abun na damuna kamar na tattara na bar gidan amman bazan iya ba darajan mami da kuma karfin soyayyarsa “masu aikin mami ne a sunkuye a gaban dinning suna jere food flask.
Mami ta fito daga kitchen Riƙe da tray me ɗauke da lemuka a hannunta ta nufo dinnig dasu.tabawa mai aikinta ta iso gabanta da sauri ta karɓa taje ta ajiye mami ta ɗauki air-frshner ta soma feshe falon sannan ta ɗan tsaya alamun sauraro, ta juyo ta kalli tabawa mai aikinta tabawa ta juyo ta kalleta sanda take ƙara gyara zaman kujerun. “Tabawa!” “Na'am mami” “naji tsayuwar mota ina zaton adamcy ne suka iso , hanzarta ki bawa sauran masu aiki umarni su ƙarasa gyara wajen su bar nan tun kafin ya ƙaraso”
ATA ya shigo cikin parlour'n da sallama mami ta amsa da “Amin wa'alaikas salam” ATA ya iso gaban mami ya rusuna yana gaisheta “sweetheart barka da rana” cikin sakin fuska mami tace. “barka da zuwa adamcy Nah ɗan albarka ya gida ya kuma ƙarfin jikin?” “Alhamdulillah” Mami tace. “ka ganmu muna ta shirin tarbanku kamar wasu baƙi ko?” ya miƙe yana kallon ɓangaren dining sannan ya zauna.
Yana cewa. “sweetheart da kanki kikayi komai?” “Ƙwarai kuwa, ni da tabawa muka shirya muku abinci sai sauran masu aiki da suka taimaka ” ATA yayi shiru kawai suna cikin magana suka jiyo sallamar zabiba ta karaɗe falon mami ta ɗago ta kalleta tana cewa. “Zabiba har kin ƙaraso?” Zabiba tace. “Eh mami na ƙaraso suma suna hanya yanzu muka gama waya dasu ina yini?” “lafiya lau zabiba ya yaran suke?” “suna lafiya suna gida tare da babansu khaira ce ta maƙale wai lallai sai ta biyoni taga hajiya mami nace ban zuwa daita tazo takurawa rayuwata” “ai wannan takwarartawa sai ahankali last time da kuka zo ta dameni da aunty girl”. mami ta faɗa cike da farinciki tana murmushi .”
muryar zabiba cike da tsoro tace. “yaya ina yini?” bai ce mata komai ba dan tunda ta shigo ya maida fuskarsa wani ɓangare. Mami tace. “adamcy ana gaisheka” a taƙaice yace. “Lafiya” ahankali ta samu waje kusa dashi ta zauna “yaya Adam!” yana jinta yayi mata banza ahankali tace. “please yaya kayi hakuri ka yafe mana wallahi bazamu sake ba” tsaki yaja yace. “ai daman haka kukeyi idan kuka ɓatawa mutun rai kuyita nacin ban haƙuri kamar bazaku sake ba amman da zaran mutun ya haƙura ƙoƙarin aikata wani kuke yi dan haka gara ku riƙe haƙurinku dan ni tuni na cireku a rayuwata” nan da nan zabiba ta shiga aikin nan wato bashi hakuri da kuka amman ko ajikinsa girgiza kafarsa ɗaya kawai yake zabiba kuwa kuka take kamar ranta zai fita ahaka sauran ƴan'uwanta suka shigo suka isketa gabaɗayasu suka sakashi a tsakiyarsu suna masa magana amma ko motsa laɓɓansa bai yi ba. “ku rabu dashi Ke kuma zabiba ki daina asarar hawayenki kuna zaune zai huce” cewar Mami dogon numfashi ya sauke yana taɓe baki.aransa yace “ai kuwa zan baku mamaki .”
Nana hauwa'u tace. “mami ina auntynmu take?” nan da nan mami ta kallesa sai lokacin kanta ya kawo wuta “Ina Maryam ɗin da nace kazo min daita Ko tana cikin mota ne?” ATA ya ɗan sosa ƙeya “na barota a gida a cewarta tayi baƙuwa” da mamaki mami ta tsura masa ido “ka barota a gida adamcy acewarta tayi baƙuwa kuma?”eh !haka tace idan ta gama zata taho don bazan iya zaman jiranta ba, kuma wallahi sweetheart kiyi ma yarinyar congret warning dan kwanakin nan wasu ƴan iska qawayenta take tara min a gida alhalin ni gidana ba dan ƴan iska na ginashi ba” cikin fushi mami tace. “adamcy kasan me kake faɗa kuwa? Ƴar tawa da take aurenka zaka cewa Ƴar iska tana tara ƴan iska ?” “ai sweetheart wannan yarinyar ta wuce ƴar iska a gaban ita wanna Ƴar iska ƙawartata take ce min wa..” hannu mami ta ɗaga masa cikin fushi ta fara magana. “saurara! bana son jin komai daga bakinka, ka tashi yanzu ka koma gidan ka ɗaukota tun rai na bai gama ɓaci ba...” ATA ya gyara zamansa cikin damuwa yana kallonta kafin ahankali ya motsa laɓɓansa “haba sweetheart me yasa kike nuna mini wariyar launin fata a tsakanina da yarinyar nan ? Ni fa kika haifa ba ita ba” cikin fushi tace.“dan kana ɗan cikina sai in goyi bayan riƙon sakainar kashin da kake mata?” ATA yace. “To ai bata gama shiryawa bane tana hira da Ƴar iskar ƙawarta”
“Yanzu ka tashi ka koma gidan ka jirata har sai ta gama kimtsawa idan ma sai ta sallami ƙawarta ne ka jira sannan kuzo min tare yanda nace” mami bata kai ga rufe bakinta ba Ni'ima da maryam suka shigo cikin falon Ni'ima na riƙe da Maryam a kafaɗarta wanda goshinta yake a fashe yana ɗigar da jini, mayafinta da ɗankwalinta yana a hannun Ni'ima nana hauwa'u ce ta fara lura dasu ta soma salati tare da faɗin.“lnnalilahi wa'inna ilaihir raji'un!”jinj !
Nan mami da sauran ƴaƴanta suka juya da sauri suka kalli maryam “Subhanallahi!” mami ta furta a ruɗe tana kallon ATA “Adamcy kaga abinda ka janyo ko? don me ka barta a gida Kashe min ƴa zakayi?”Adamcy ya kalli mami a natse ya juya ya kalli inda maryam take gbɗy ya kasa magana juwa ne ya ɗibi maryam ta sulale ƙasa a sume, nana hauwa'u ta ƙarasa da gudu suka tallafo ta ita da Ni'ima
mami da ƴaƴanta suka nufi wajenta da sauri suna jijigata jikin mami na rawa tace. “ku kwantar da ita akan kujera shahida taimaka ki duba min ita” duk mami ta ruɗe shi kuwa gogan ko ajikinsa dan haka nan yaji ajikinsa suman ƙarya tayi.Mami banzo da kayan aiki na ba, a kira doctor nasir” da sauri mami tace. “Auta maza shiga ɗakina ki ɗauko min wayata” da sauri nana hauwa'u ta nufi ɗakin mami ta ɗauko wayar tana niman layinsa yayinda aunty shahida ke bata taimakon gaugauwa shi kuwa ATA mikewa tsaye yayi yana jan tsaki ya ra’ba ta gefensu ya fice yama bar gidan gbdy .”
Bayan awa uku
Maryam na zaune a kujera tana sauke numfashi ansa auduga da plasta an rufe raunin goshinta yayinda mami ke zaune a gefenta riƙe da hannunta Dr.Nasir Ya miƙe tsaye sanye da coat da farin gilashi hannunsa riƙe da first-aid box ya miƙawa mami Ƙaramar takardan magunguna “hajiya ga wannan takardar magungunan da zatayi amfani dashi ne insha Allah da zarar tasha a hankali ƙarfin jikinta zai dawo baboda naga Allah ya taƙaita babu wani babban rauni da zai sa muyi admitting ɗinta asibiti ko kuma yiwa cikin jikinta illa Wannan treating ɗin ma da nayi mata is okay for her” mami ta jinjina kai tana faɗaɗa fuska cikin farinciki tace. “doctor kace ciki gareta?” Doctor Nasir yace. “ƙwarai kuwa hajiya in sha allahu ranar monday akawota hospital domin yi mata scan dan mu san iya adadin kwanakinsa” “masha Allah Dr.Nasir nagode sosai ka min albishiri mai daɗi” na dade ba’a fada min maganar data saka zuciyata farinciki ba dr nasir ya kalli maryam da murmushi a fuskarsa “to hajiya Mar-Adam zance ko Mrs Adam? Allah ya bada lafiya” maryam tayi murmushin ƙarfin hali tana kallonsa zuciyarta na rawa dan tun daya fara maganar ciki ta shiga damuwa mai tsananin dan ita kanta tana zargin ciki gareta duba da watan ta na uku kenan bata ga period ɗinta ba. “Allah ya sauwaƙe ya bada lafiya” da “Amin” ta amsa cikin ƙarfin hali.
Dr.Nasir Ya juya ya fita daga gidan farinciki agurin mami da ƴaƴanta ba'a magana kowa ka kalli fuskarsa kwance yake da annurin farinciki gabaɗayansu murna suke har sun kasa ɓoye murnarsu mami ta riƙo hannun maryam cikin nata tana kallonta cike da kulawa tace “ke kuwa Maryam garin ya akayi kika samu rauni?” maraym tace. “walalhi mami muna qoqarin karya kwana ne akayi akasi wani me mashin ya kwaso a guje, ganin kamar zai yo kan motar ne sai ido na ya rufe daga hk ni dai bansan yadda akayi ba kaina ya bugu da stearing” mami tace. “yanzu banda Allah ya taƙaita ai da abun ya wuce haka ga ciki ajikinki” .nana hauwa'u tace. “Alhamdulillah da Allah ya taƙaita” cike da murna ta ƙarasa maganar. “ai duk adamcy ne ya janyo da yanzu wani abu ya samu cikin jikinta me za'ace?” nan da nan mami ta shiga zuba wa Adam faɗa da baya nan akan me yasa bai jira Maryam ta gama shiryawa sun fito tare ba? cikin raunin murya “daman ai duk shi yaja mana wannan matsalar, wallahi mami in kinga abubuwan da yayi mata agabana sai kin tausaya mata” cewar ni'ima “kamar wata baiwa ya ajiye a gidansa ba matarsa ba” mami ta tsurawa Ni'ima ido tana kallon fuskarta kar dai itace Ƴar iskar ƙawarta da yake faɗa? “ko abinci ta girka sai yaga dama yake ci, komai tayi bata masa gwaninta, sai yayi tayi mata tsawa yana hantarar ta wannan wani irin aure ne?” mrym tayi saurin take ƙafar Ni'ima “kinga malama ki bari ayi magana yanzu an daina auren wahala idan bazai iya ba ya sallame ki, ki kama gabanki idan kin haife abinda yake cikinki ki kawo masa ki dire ai namiji goma ba uba goma bane " Hjy zulai da mamaki take cigaba da kallon Ni'ima tana tunanin in da tasan fuskar “haba Ni'ima wai meye haka ne ?dan Allah kizo ki wuce gida dan Allah nace miki ina son rabuwa da mijina ne? koni na faɗa miki yana min duk abinda kika furta “au karesa zakiyi saboda baki da hankali ai duk abinda idanuna suka gane min kamar na faɗawa ummah na gama” tana gama faɗar haka ta juya cikin tsananin fushi.”
Cike da ɓacin rai nana hauwa'u tace. “sister wannan fa wacece ita? Jiki a sanyaye ” Maryam tace. “ɗiyar sister ɗin ummammu ce “kai shiyasa nake ta mata kallon sani kar dai ɗiyar umaima ce?” Maryam ta gyaɗa mata kai alamun eh. “shine zata dinga faɗar magana akan yaya? kuma ai kice kika bata wannan damar” “kamar ya sister?” maryam ta faɗa jikinta na ɗan rawa “idan baki faɗa mata komai akanshi ba ya'akayi tasan irin zaman da kuke yi?” aunty shahida ta faɗa ranta a ɓace “karfa kiga duk muna bayanki ki ɗauka bama son shi ne, adam rayuwarmu ne kema kuma kinsan da haka Maryam ta runtse idanunta sai ga hawaye masu zafi cike da tashin hankali take jin yadda numfashinta ke sauka da ƙarfi. shi kenan Ni'ima ta haɗa mata bala'i “duk muna bayanki sakamakon irin tsanar da yake nuna miki da kuma irin ƙaunar da mahaifiyarmu ke miki” “ dan Allah aunty shahida kuyi hakuri ba'a bakina taji komai ba ummace ta faɗa amman..” katseta aunty khadija tayi ta hanyar cewa. “ita umman taki meye amfanin faɗawa mutane? mun sani sarai adam bai kyautawa amman kuma meye abun faɗawa mutane anan? mufa mun sani sarai ummanki bata ƙaunar danuwanmu, amman mu dai-dai rana ɗaya mun taɓa sauke haushin haka akanki ? kullum yanda rayuwarki zata samu cigaba a gidansa muke" .
Maryam tasa kuka cikin tsananin damuwa .”
“dan Allah ya isa karku saka min yarinya gaba da bala'i dame zataji ?da maseefar ɗan'uwanku ko da naku sai kun harbe mata zuciya ta mutu kowa ya huta ? kuma ai bai barku ba bare ku shigar masa” kuma karya aka fada akanshi ?halinsa ne fa ?“koma dai menene mami bazamu lamunta ba kuma kar mu sake jin taje gidanki daman shima yace ayiwa ƴar iskar ƙawarki congrent warning karta sake shigar masa gida ilai kuwa ashe ƴar iskar ce ai duk abinda kika ji yaya yayi mgn akai mai mahimanci ne” cewar zabiba nana hauwa'u kam tun maganar farko bata sake cewa komai ba, atare suka miƙe aunty shahida aunty Khadija da zabiba sukai ma mami sallama tayi masu addu'a tare da yi masu fatan alkhairi nana hauwa'u bata sake cewa komai ba mami ta laluɓo wayarta daga gefenta ta ɗauka ta soma ƙoƙarin kiran ATA “Bari ina zuwa na kirasa dani yake zancen wato cin mutunci da tozarci har agaban mutane?" maraym tayi saurin riko hannun mami tana kuka tace. “dan Allah mami ki rufa min asiri kar kiyi masa magana yanzu idan ma son samu ne karki ce masa komai” mami ta ƙara wayar a kunnenta tana cewa. “rabu dani gara na faɗa masa halin da'ake ciki tun kafin baƙin cikinsa yasa a rasa cikin jikinki .”
alokacin da mami take neman layinsa yana zaune acikin wani ƙayataccen gida me ɗauke da komai na manyan masu kuɗi da manyan ƴan boko gidan kamar aljanar duniya tsabar haɗuwa wannan gidan bana kowa bane face gidan ammar ATA na zaune a gaban ammar suna tautaunawa akan kasuwanci kiran mami ya shigo ya ɗauki wayar ya manna a kunne “hello kana ina?“ina gidan ammar” abinda ya faɗa kenan yana lumshe ido “to in ka fito kazo gida da gaggawa ina son ganinka” katse ta yayi da faɗin. “lafiya sweetheart?” Mami tace. “ita ta kawo haka bazaka ma tambayi Jikin maryam ba kaji halin da take ciki? ka bar ƴar mutane cikin wani hali gashi..” tun kafin ta faɗi abinda take son faɗa taji ya katse wayar “Hello.. Hello... adamcy” tuni ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli screen ɗin sannan ya sauya kujerar sa yana dafe goshinsa da hannuwansa duka ammar ya dawo gabansa ya fuskancesa yan faɗin. “lafiya ?waya kiraka ?ya ɗaga maka hankali gashi bamu gama tattaunawarmu ba?” “sweetheart ce ni dai allah yasa karsu kashe ni akan ƴar iskar yarinyar nan..” “yanzu me ya faru kuma?” “ban sani ba ni dai na barsu wai ta suma” “wa kenan ta suma?” shiru yayi na second biyu sannan ya ɗago kanshi ya kalli ammar “Sweetheart ke son ganina amma zamu iya ƙarasa maganar Okay, Sai dai kuma ya kamata a ce ka ɗau tsanttsauran mataki akan sauran yaran daka faɗa min saboda har kullum shi kasuwanci tattalinsa ake. bana son kabar wata kofa da wasu zasu samu damar janyo mana asara dan bazan ɗauki asarar ganganci ba” “shikenan zan haɗa taron gaugauwa ranar monday zan yiwa P.A ɗina magana, zamu san abin yi kafin matsalar tayi nisa” ATA ya jinjina kai sannan ya buɗe wani file ya duba bayan ya gama dubawa ya miƙe “ni zan wuce” ammar ya jinjina masa kai a sanyaye atare suka fito .”
Can ɓangaren maryam kuwa kuka take sosai abun ya haɗe mata tana kallon nana hauwa'u ta miƙe ta yafa mayafinta tana yiwa Mami sallama “kema wucewa zakiyi ?” “eh Mami yaya hisham yana jirana” “to ai Shi kenan Allah ya tsare hanya” mami ta fada ranta a dagule saboda ganin ya’yanta sun hadewa mrym kai ,nana hauwa’u bata kalli in da maryam take ba ta nufi ƙofar fita, takun maryam taji abayanta tana magana cike da raunin maryam tace. “sister kema fushi zaki yi dani bayan kinsan kece ƙarfin gwaiwata” juyowa tayi ido cikin ido suke kallon juna “kiyi haƙuri sister nayi kuskure” nana hauwa'u tayi murmushi tana kallon cikin idanunta “shi kenan komai ya wuce Allah ya inganta mana babynmu” jiki a sanyaye sukai sallama tana jin kamar zata rasa rayuwarta ne dan gbɗy jin tana ɗauke da cikinsa bai saka zuciyarta samun natsuwar ɗari bisa ɗari ba ta dawo kusa da Mami ta zauna “ki rabu dasu karki wani ɗaga hankalinki akan ɗan wannna abun” Maryam tace. “allah Mami hankalina a tashe yake su aunty shahida sunyi fushi dani” “zan kirasu babu abinda zai faru ni dai fatana ki kwnatar da hanaklinki kar wani abu ya samu cikin jiknki”
Numfashi ta sauke sannna tace. “Mami dan allah karki faɗawa yaya batun cikin nan tukun Kinsan halinsa” Mani tace. “kai babu abinda zai yi sai farinciki aj wannna cikin sai ya kawo miki sauy arayuwarki Maryam tace. “ walalhi yadda yaya baya sona bana tunanin zai so abinda nake dauke dashi Shiru mami tayi tana sauraronta “ai kuwa da Adamcy bai kyauta mata ba idan yaki abinda mrym take dauke dashi “ko kuma za'a iya ƙin fad'a masa har ya gano da kanshi” kai kawai mami ta gyda mata ahankali mami ta dinga janta da hira sai dai jikin Maryam a mace yake kana kallonta zaka fahimci hakan.
A galabaice ya shigo parlour'n mami ya zauna tare da runtse idanunshi gam mami dake zaune ta tsura masa ido ruwan bala'i take son sauke masa amman yanayin yanda ya shigo yasa tayi tunanin kar ta masa faɗan sai tasa aka kawo masa abinci buɗe idanunshi yayi ahankali yace. “gani sweetheart ina son na wuce gida na kwanta na huta” mami tace. “kaci abincin da akawo maka tukun sai muyi magana” kaɗan yaci abincin sannan ya tsurawa mami ido yana son yaji kiran me take masa suna zaune sai ga maryam ta fito daga ɗakin mami jiki a sanyaye ta zauna kusa daita wani mugun ɓata rai yayi “Adamcy!” mami ta kira sunansa ya ɗan kalleta tare da faɗin. “ina jinki sweetheart” mami tace. “me yasa kaci zarafin Maryam a gaban ƴaru'warta?” baƙaramin fusata yayi ba shi kam bai san randa mahaifiyarsa zata barshi ya huta da maganar yarinyar nan ba “amma ajiye wannan maganar ma tukun, ka fita ka bar matarka cikin wani hali baka kira kaji a wani hali take ciki ba bare ka mata sannu da jiki” daga haka ya miƙe ya fice daga parlour'n dan bazai zauna ya cigaba da jin magana akanta ba “maza tashi ki bishi kuje zan zo wani sati sai na daukeki muje scan din “to mami na gode allah ya qara girma “Allah ya tsare da ɗan saurinta ta ɗauki mayafinta ta fito alokacin tuni ya shiga mota ta zagaya da sauri ta bude bangaren da yake ta shiga ta zauna suka wuce gida ."
Bayan kwana biyu da misalin ƙarfe goma kiran Ni'ima ya shigo wayarta tana kallo kiran na shigowa taƙi ɗauka sai a karo na biyar ne ta ɗaga tana ɗauka tace “lafiya Ni'ima kiran me kike min bayan kin kusan jefa rayuwata cikin uku bala'i ? babu ruwanki da duk halin da nake ciki zan gargaɗeki da babban murya karki sake zuwa mijina yace baya son ganinki a gidansa idan kuma kinyi taurin kai zaki gane ke ƙaramar mara mutunci ce” shiru tayi tana sauraron Ni'ima “ni dai nace karki shigo tunda kince saƙo ne daga umman zuru ki tsaya a wajen get idan kinzo zan fito na karɓa amman karki zo ” washegari kuwa da misalin karfe bakwai Ni'ima ta kirata ta fita cikin sanɗa kasamcewar ranar tun safe ATA na gida bai je koina ba wanda alamunsa Ke nuna tafiya zai yi taje ta karɓo saƙon umma zuru irin tukunyar farko da aka aiko mata dashi ne. cikin sauri ta shige ɗakinta dashi ta fito parlour'n ta zauna , tana zaune ATA ya shigo ya haye sama bayan Kamar mintuna talatin ya sauko yana fita, ta miƙe da sauri ta haye sama kamar a mafarki taga kofar ɗakinsa a buɗee wani kyakkyawan murmushi tayi da sauri ta faɗa ɗakinta ta ɗauko tukunyar ta dawo ɗakinsa ta tsaya tare da buɗe tukunyar tsafi ta soma ambatar sunanshi da abinda take son yayi mata kamar yadda aka fad’a mata bayan ta gama ta ajiye tukunyar ta ɗaga katifa ta ajiye a gefe, ta ɗauko tukunya zata saka taji taku tare da tafi daga bayanta ai da wani mugun sauri ta juyo ganinsa tsaye yasa ta saki tukunyar aiko nan take ta fashe sai ga wani mummunar hayaƙi ya shiga fitowa daga ciki .
Cikin zare ido yace “Meye wannan?” tambayar daya jefa mata kenan bakinta da jikinta ya kama rawa “kina son kashe ni saboda bana sonki ko?" Girgiza masa kai tayi tare da faɗi. “a'a ba kashe ka zanyi ba.." cikin daka tsawa yace. “shut up with your dirty mouth! you want kill me?” zatayi magana ya sake buga mata tsawa “shut up how dare you enter my room kuma riƙe da tukunyar tsafi?” nan da nan jikinta ya kama rawa “daman naji ajikina kina son kasheni” sake girgiza masa kai tayi jikinta na wani irin rawa “why you this girl ?me nayi miki da zaki kashe ni ? duk da bana sonki duk da yanda nake ji araina kamar na kashe ki na sha faɗa miki ni ne ajalinki amman na taɓa ƙoƙarin kashe ki?” jikinta na rawa ta girgiza masa kai “why you want to kill me ?” cikin rawan murya tace. “Wallahi ba kashe ka zanyi ba, ka fahimceni wallahi ba wata illa zan yiwa rayuwarka ba kawai dai..” sai kuma tayi shiru ta kasa ƙarasa maganarta “baki da abinda zaki iya kare kanki kije na sakeki saki ɗaya " .
mutuwar tsaye tayi cikin tsananin tashin hankali da matsanancin gigita jin furucinsa, yayinda hawayen idanunta ya ƙaru suka shiga kokuwa da juna gurin silalowa ga wani irin ƙyarma da jikinta ke yi, sai dai rawar da jikinta ke yi ya sanyata saurin durƙusawa a gabansa domin ƙafafunta sun tabbatar mata bazasu iya cigaba da ɗaukar gangar jikinta ba, baya ga haka ma ga wani iri jirin tashin hankali dake ɗawainiya da ita .Wani irin bugawa kanta ke yi tamkar zai rabe gida goma , cikin wani matsanancin rashin Hankali muryanta na rawa tace. “da gaske ka sakeni yaya adam? dan Allah ka janye sakin zan maka bayanin komai domin idan kana tunanin zan...” dakatar da ita yayi ta hanyar faɗin. “shiiii na sake ki kuma babu wanda ya isa ya sake takurani nayi rayuwa dake, dan haka ba abinda ya rage miki a gidana gari ya waye ki bar min gidans kuma bance kije gidan mahaifiyata ba, ki wuce gidanku gidan ubanki tunda ke ɗin ba shegiya bace” shiru kawai tayi tana dubansa cikin tsananin faɗuwar gaba domin dai a kallon da take masa ta rigada tasan bazai taɓa daina tsananta ba a cikin zuciyarsa” maganar sa ne ya katse mata tunaninta. “bazan taɓa daina tsanarki ba, abinda kika kasa ganewa shi so halitta ne..” cikin matsanancin kuka ta dakatar dashi da faɗin. “yanda yake halitta nima haka nake ji akanka me yasa zaka rabu da zuciyar da batasan sanda ta fara sonka ba ?sonka shine mafarin kasancewata a karkashin mahafi....” cikin daka tsawa yace. “bar ɗakin nan stupid! tun kafin nayi losing control , dan ina jin baƙin cikin kasancewata dake ahalin yanzu yayi maganar a zuciye cikin tsananin fushi da tashin hankali mara misaltuwa.”
bata bar ɗakin ba kamar yanda ya furta sai rarrafawa tayi ta koma gefen doguwar kujerar kushin ƙwaya ɗaya dake ɗakin ta rakuɓe , tana kallonsa ya miƙe ya shiga bayi batare daya cire kayan jikinsa ba saukar ruwa a bayin yasa ta fahimci wanka yake a hankali ta rike gefen kanta dake sara tana haɗeye wani ƙululun baƙin ciki tare da share hawayen dake tsiyoyo mata, ta tattara tukunyar tsafin ta kai dakinta ta ajiye ta dawo ɗakinsa ta zauna dan babu in da zata aurenta dashi mutu ka raba ya saketa amman bata saku ba dan tayi imani mami naji zata maidaita."Da mamaki ya fito ya isketa kallon mamaki da naci irin nata yake “zaman me kikewa mutane a d’aki ?” ya faɗa Yana kallonta “babu fa inda zani har sai ka maidani ” wani mugun kallo yayi mata sannan ya ɗauki jug din coffee da zafinsa wanda ta kawo masa bai sha ba ya dawo inda take ya juye mata tsab a jikinta wata razananniyar ƙara ta saka da sauri ta shiga kakkaɓe rigar dake jikinta , cikin faɗa wanda bai hana zazzaƙar muryarsa fitowa ba yace. “banace ki bar min ɗakina ba ?” Ya faɗa yana ware mata idanunsa dake cike da bala'i jikinta na rawa sosai ga kuma zafin coffee da yake ratsa illahirin fatar jikinta wanda har cikin naman jikinta take jin zafin, babu shiri ta bar masa ɗaki zuwa nata tana zubar da hawaye .”
ranar Maryam bata runtsa ba kuma tayi dauriya domin dai bata kira kowa acikin ahlinsa ba washe gari kuwa tun da asuba tabi mota zuwa abuja taso shiga jirgi amma saboda bata da kuɗin jirgi kamar ta tambayi mami kuɗin ticket amma tasan hakan zai sa ta gane akwai matsala shiyasa ta shiga motar haya
Tunda suka ɗau hanya kanta na kife ,rufe ido tayi sosai tana zubar da hawaye masu zafi sannan acikin ranta tana ƙissima yanda zata hana rayuwar adam samun kwanciyar hankali yadda bata ji dadi agidansa ba bazata bari Ya kawo wata yaji dadin rayuwarsa daita yadda gallazawa rayuwarta wallahi tayi alqawarin sai ya gallazawa duk wacce ta rabesa zatayi komai akan yanke masa duk wani jin dadin rayuwa .” ɓangaren ATA shima tana barin gidan ya bar ƙasar zuwa hollond .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.