Maradams Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: MARADAMS book 2 by Aysha A Bagudo.txt
Chapter 14 of 14
Page 30
Granny zaune akan kujera mai zaman mutun biyu rike da qaurin qafafuwanta tana mammatsawa tana runtse idanunta alamun tana jin ciwo sosai muryarta a sanyaye tace “ wayyo allah qaurin qafata, wallahi qaurin qafar nan yana damuna da ciwo sosai umma dake zaune tare da aunty hasana najin haka ta tashi daga inda take zaune ta shiga d’akinta aunty hassana ta dubeta kana tace “sannu hajiya “yauwa hassana na gode, amman mai yasa bazaki dinga kunsa lalle ba yana maganin ciwon qafa sosai “ina yi amman wani lokacin idan ya tashi dole sai na had’a da man zafi .”bata kai ga rufe bakinta ba sai ga umma ta fito daga d’akinta ahankali ta qaraso inda granny take zaune hannunta rike da man zafi “sannu hajiya bari na shafa miki man zafi nan zaki d’an ji saukin zugin da suke miki, kinsan abu idan ya had’e maka da girma sai a hankali “ai kuwa na gode allah yayi albarka daman yanzu nake son tambayrki aboniki dan nasan bakya rasawa umma na qoqarin tsugunnawa sai ga maryama ta shigo bakinta d’auke da sallama .”tana ganinsu tayi murmushi ta qaraso da sauri ta tsaya kusa da umma tana cewa “umma mai ya samu granny naga kamar bata da lafiya ?”wallahi maryama qafafuwanta ke mata ciwo shine zan shafa mata man zafi “.“ayya sannu kinji granny Allah ya baki lafiya umma kawo man na shafa ma yar tsohuwar nan dan nasan ke ahankali zaki yi mata ni kuwa da iya karfina zanyi mata amfani dashi na durza sosai man zafin ya shiga ko….”
“sannu muguwa! “Inji cewar Aunty hasana “maryama ta kalleta a natse batare da tace mata komai ba “nace sannu muguwa ko karya nayi da kike kallona a wulakance ?”daman babu abinda kika iya sai tsiya da mugunta muniyar banza kawai kin wani kafeni da wasu gwala gwalan idanuwa ko zaki cinyeni? still maryam bata ce mata komai ba idan da sabo ta rigada ta saba da halinta sai dai abinda take mata ita da mahaifiyarta yana matukar damunta koma tace ya fara isarta amman tasan duk runtse duk wuya baza ta’ba iya maida mata magana ba yadda batayi magana ba haka umma da granny basu ce ci kanki ba ,maryama ta cigaba da abinda take tana bawa granny labarai masu dadi da kwantar da hankali granny ta lumshe idanunta tana cewa “yauwa diyar albarka ya isa haka ma na gode sosai Allah yayi miki albarka allah ta jikan mahaifinki Allah ya rabaki da mahaifiyarki lafiya walalhi har naji saukin zugin da yake min allah yayi miki albarka allah yasa ki gama lafiya .”maryama ta amsa da “Ameen”. fuskarta da bayyanan ne murmushin na farinciki dan idan akwai abinda ke sakata jin farinciki da natsuwa bai wuce taji kana mata fatan alkhairi ba .”
ATA tsaye acikin office dinsa sanye da wasu hadaddun suit wondo da riga ash colour haka ma takalman dake sanye a qafafunsa ash colour ne masu kyau da tsada yayinda jikinsa ke fitar da wani sanyayyen kamshi turare mai sanyi da kwantar da hankali .muryarsa a dake ya kira sunan sectary dinsa “Some !da sauri ta amsa masa da “ yes sir!” tana mai dubanshi cike da girmamawa da tsananin tsoro bai ce mata komai ba ya cigaba da aiki a system dinsa . yayinda itama ta cigaba da tsayuwa tana kallonsa da bayyanan ne tsoro a saman fuskarta ,fuskarsa babu walwala ya sauke kwayar idanunshi akanta tare da mika mata system dinsa “gashi ki duba sakonin masu neman aiki ne yau tsawon sati d’aya kenan ban samu dama dubawa ba yanzu haka ina son na d’an huta kad’an . “okay sir angama yanzu zanyi komai na gama ,ya dawo kan kujera ya zauna yana lumshe idanunshi yayinda some ta soma abinda ya sakata tana kallonsa ya mike a kan doguwar kujera da yake zaune ya kwanta tare da yin pillow da duka hannuwansa yana kallon saman office dinsa .”
Bayan kamar mintuna talatin ya mike ya shiga bayi ya d’auro alwala ya shiga d’akin dake cikin office dinsa domin gabatar da sallama bai fito ba sai around 2 :30 yana fitowa ya kirata da wayar office ,ta shigo da sauri still rike da system din dan sauran kad’an ta gama duba wad’an da suka cancata tace ” sir gani ! “ya ake ciki ? ta d’ago da sauri tana
dubansa sakamakon ganin sunan maryama cikin jerin masu neman aiki “sir !! na duba duka sakonin amman wannna sakon na qarshe akwai ….” kinga kiyi abinda ya dace kawai hanyar fita yayi daga office din “but sir!” kinga akwai abinda zanyi yayi saurin katseta ta hanyar fad’ar haka ya qarasa ficewa ”
D’aya bayan d’aya take bin number masu neman aiki har ta kawo Kan number maryama, ta kira number ya kusan sai uku ba’a daga ba a karo na hud’u ne ta d’auka tare da cewa “hello!daga can bangaren aka amsa mata da” hello ko muna magana da maryam hussein ne ? “Yes of course itace muna kiranki ne daga nan AGC company bisa sakon neman aiki da kika tura mana mun duba takardunki da safur din zanenki duk babu wata matsala yanzu dai sai mun ganki domin yin interview ta qarasa maganar a lokacin da ATA ya dawo office din ya zauna ya janyo system dinsa yana dubawa ”nan take maryama ta rud’e ta shiga kallon umma a rikice “aiki kuma ?”ai ni ban tura wani sakon ai …”umma ta matso kusa daita da sauri ta dafa kafad’anta “ki ce kinji ni na tura masu sako neman aiki .”
maryama tayi shiru tana duban umma tana jin wani irin bugun zuciya” ki natsu kiyi magana dasu da girmamawa” nan take maryama ta ‘bata rai amman babu yadda ta iya dan bazata iyawa umma mutsu akan komai ba ,numfashi ta sauke da karfi tace “shikenan yaushe Zanzo domin interview din ?On 28 march tana gama jin haka ta katse kiran tana duban umma “why umma wani aiki kuma nifa wallahi babu wani tsarin aiki arayuwata tunda yusira tana samo min zan dinga yi a gida “.murmushi umma tayi tana cewa “a’a maryama Kiyi shiru kiyiwa kanki fatan alkhairi karki ja da ikon allah “bazan yi jayayya da ikon allah ba amman ni wallahi umma …” kar ma ki rantse idan kika ga bakiyi aikin nan ba mutuwa nayi amman muddin ina raye sai kin ci amfanin karatunki “maryama ta shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace”zanje ne kawai saboda son da nake miki babu yadda zaayi kice nayi abu nakiyi “nima ina sonki maryama shiyasa ma na tura miki neman aiki domin nasan shine cikar burinki wani dalili ne dabam yasa kika ce bazakiyi aiki ba ta qarasa maganar tana riko hannun maryama cikin nata tana jin wani irin a zuciyarta yayinda idanunta suka cika da ruwan hawaye sadam dinta ta tuna .”
ahankali maryama ta zare hannunta cikin na umma ta shige dakinta da umma ta barma ta fad’a kan gado ranta duk babu dadi tunanin rayuwarta ta shig yi sannu ahankali har bacci ‘barawo yayi awon gaba daita .”
“sir ina son nace wani abu shiru yayi bai amsa mata ba sai qarar daddana system dinsa kawai akeji sai data maimaita maganarta sannan yace “okay ina jinki na gama duk abinda kasani na kira wad’an da suka cancata “nasan zasuyi matukar murna dan babu wanda zai samu kiran daga kamfanin AGC bai ji dadi ba “sai wacan banzar yarinyar ba .” ya fad’a aciki ransa amman a zahiri cewa yayi “okay !sectary dai tayi shiru taso ya bata dama tun kafin ta kira number maryama amman yaki ,alamarin mai gidan nasu ne sai hakuri shi kawai zaiyi abinda yake so kuma alokacin da ya ga dama amman wani bai isa ba .”parlour’n mami dauke yake da manyan baki domin kuwa baba qarami ne tare da uncle jay da mami da aunty shahida har ma da aunty abida tare da sultana ,table din gabansu cike yake da kayan motsa baki wanda mami tasa aka kawo masu hira tayi dadi sosai inda aunty abida ta sako batun aikin sultana nan take baba qarami yace “ kai diyata karki damu ta shirya kawai ta fara zuwa aiki bama ita ba idan kina da masu bukatar son aiki akarkashinmu ki kawo muna maraba dasu “.
“wani irin murna tayi tana mai jin dadin maganarsa ita dai mami bata ce uffan ba aka cigaba da hira har sanda ATA ya shigo mami na ganin shigowarsa ta mike zuwa kusa dashi dan tasan baya son azo acika masu gida da hayaniya kuma baqaramin aikinsa bane yayi abinda zai korasu gabadaya “abinda ya bawa mami mamaki bai wuce yadda sultana ta mike tazo ta tsaya gabansa ba tana wani irin rausaya da lumshe masa ido “thank you so much for giving me the job ,gsky naji dadi sosai zanyi aiki a qarqashin AGC company “what ?ya fad’a a matukar tsawace yana kallonta kafin ahankali ya motsa lip’s dinsa “ina ganin kamar kin fara shaye shaye wa ya baki aiki a company “?baba qarami !”tayi mgnr tana duban inda baba qarami yake zaune”ni na bata kuma zatayi aiki alokacin dataso saboda itama uwarta nada ‘yanci acikin AGC “gsky baba qarami kana da matukar kirki amman shi wannan d’an naka ya fiyye jin kai ya manta cewar ni dashi asalin mu d’aya “to ai shi Adam bai da wannan kirki kuma duk cikin zuriarmu babu mara mutunci kamarsa amman wannan karon ko yana so ko bai so yarinya dole kiyi aiki a kamfani kwana nan ma zan dawo na cigaba da kula da kamfani dan nasan kan kamfani fiyye da wannan gatalallen yaron mara kunya idan ma naga dama zan iya dakatar dashi dan dama bai iya tafiyar da kasuwanci ba hauka da shirme kawai yasa a gaba saboda rashin sanin kan kasuwanci komai cikin zafin rai da fushi yake.”
ATA yayi shiru yana dubansa a kaskance har ya soma taku zai isa inda baba qarami yake aunty shahida tayi sauri ta mike tare da rike masa hannunsa gam cikin nata tana masa alamar kar yace komai “amman da kin bari nace wani abu saboda yarinyar sam bata dace da aiki a company dinmu ba dan babu abinda ta iya sai hauka “koma dai menene kayi shiru ka barsu qanin mahaifi ne kuma tmkr mahaifi ne abinda kasan baza kayi wa dad yana raye ba karka yi masa albarkasa albarka dad ne ,dan haka ka tafi d’akinka ka huta” mami tace ko akawo maka coffe “no !ya bata amsa a fusace tamkar itace ta ‘bata masa rai, me zakaci ko sai zuwa anjima ?”bana bukatar cin komai ni kawai ku bani dama nayi magana da wancan mutumin” ina mai baka umarni adamcy karka ce masa komai dan Allah kaje d’akinka kuma a yanzu idan kace masa wani abu ban yafe maka ba .”
shiru yayi kafin daga baya ya nufi hanyar d’akinsa har yayi taku uku yaji sautin muryar abida ta kira sunansa da isa ,da kamar bazai tsaya ba sai yayi wani tunani ya tsaya bata tsaya akoina ba sai a gabansa ido cikin ido take kallonsa tana masa murmushin gefen baki mai nuna alamun sunyi nasara daman da biyu suka shirya zuwa dan su aiwatar da nufinsu uncle jay ne kawai tafiyarsa dabam “ya kaji umarni da baba qarami ya zarta nasan baka ji dadin haka ba ko? amman dai aikin gama ya rigama ya gama ko kana so ko baka so kamar yadda ya fad’a sultana sai tayi aiki kuma a duk inda take so koda kuwa acikin office dinka ne baka isa ka tsaidaita ba, tunda ka kasa bata aiki wanda yake da iko akanka da kuma kamfani ya bata dama yanzu sai kayi duk abinda zaka..”ai bata kai ga qarasa maganarta ba taji saukar wasu lafiyayyun mari ji kake tass tass !! har guda biyu ajere akan kuncinta “enough..!ya fad’a a matukar tsawace gbdy mutanen da ke zaune a parlour’n babu wanda hankalinsa bai tashi ba cikin tsananin tsoro da tashin hankali aunty abida ta tsaya cak dafe da kuncinta tana dubansa fuskarta da bayyanan ne mamaki “Adam ka mareni ? “kad’an kika gani muddin bazaki daina shiga rayuwata ba “
ya fad’a a matukar tsawace .”
Hankalin aunty shahida a tashe ta qaraso inda yake tsaye jikinsa na wani irin tsuma ta dafa kafad’ansa
tare da fad’in “kana da hankali kuwa ?”ka kusan wacce ka mara ?matar aure ce kuma matar shakikinka tana magana tana nuna masa aunty abida da hannunta “.iskar bakinsa ya fesar yace “nasan ko wacece kuma nasan matsayinta kuma itama tasan ko waye ni bana cikin irin wadan mutanen da zuciyarsu Ke jurar raini wallahi idan bata daina enter dinta ba wata rana dukan mutuwa zan mata zaro ido aunty shahida tayi jikinta na wani rawa kamar yadda na mami ke rawa kana hauka ne adamcy ?”I don’t know but I fell like na haukace “wai meke damunka ne da kake abubuwa haka ?”dan Allah shahida ki barni kin cika min kunne abinda ya kamata kiyi ki ja mata kunne ta fita hanyata ta daina shiga lamarina that’s all yana gama fad’ar haka ya haye sama da sauri sauri yake taka step .”
gabad’ayansu da kwayar idanu suka bisa dashi har suka daina ganinsa .”aunty shahida ta soma taku zata bisa mami tayi saurin riko mata tana girgiza mata kai”karki bisa shahida kinsan halinsa “an san halinsa mami amman shikenan sai a zuba masa ido ya dinga abinda yaga dama .”?ai daman ita ke daure masa gindin yin iskanci da wulakanci da taka duk wanda yaso dadin abun itama bai barta ba shegen yaro mara tarbiya kawai “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun abinda aunty shahida ta furta kenan alokacin da taji abinda baba qarami ya fad’a tayi data sanin yin maganarta, da kuma tasan kalmar da zai fad’a kenan da wallahi bazatace komai ba jiki a sanyaye mami ta nufi hanyar bangarenta aunty shahida ta juyo ta kalli baba qarami dake qoqarin mikewa tsaye zuciyarta na wani irin tafasa taso kwarai ta furta koda kalma daya ce akan kalmar shegen daya furta ga adamcy amman sai zuciyarta ta gargadeta domin a yanzu ma kuskurenta ne ya janyo ya fad’a abinda ya fad’a bazata so ta sake aikata wani kuskuren ba ranta a ‘bace ta juya tabi bayan mami .”
Zaune ta isketa mami a baki gadonta tayi shiru idanunta na kallon sama d’akinta ta samu waje kusa da qafafunta ta zauna cike da girmamawa ta kira sunanta “mami ! mami ta sauke idanunta tana kallon aunty shahida fuskarta da alamun damuwa aunty shahida tayi kasa da kanta kana ta soma magana cike da biyayya “dan allah mami kiyi hakuri bisa kuskurena sam ban ji dadin abinda baba qarami ya fad’a ba domin idan mutun yace wa d’anka bashi da tarbiya to kai yake son ya zaga ya fake da zagin d’anka “numfashi mami ta sauke tana cewa “karki damu shahida idan da sabo na rigada na saba da halinsa kuma hausawa sukance dan kuka mai jawa uwarsa jifa duk wa ja min koda zagina yayi ?ni dai fatana allah ya canza adamcy allah kuma ya tsaresa daga sharrinsu Allah yasa kafin mutuwa naga canzawarsu aunty shahida ta share hawayen daya zubo mata “menene kuma abun zubar da hawaye ?wallahi mami kalmar tayi min zafi bansan me yasa yanzu baba qarami yake nunawa adamcy kiyayya haka ba ,ji nayi kamar na tanka masa “gara da baki tanka masa ba ai sai ya tabbatar da rashin tarbiyar da yace allah dai ya sawaka kawai zamu ce ahankali suka dinga tautaunawa wanda kusan duk akan adamcy ne .”
*******
On 28 cikin sauri sauri maryama tayi abinda zatayi ta shirya cikin riga da siket blue da ratsin yellow ta dauko after dres ta daura akan kaya tayi rolling din kanta da mayafin after dress din ta rufe koina ajikinta ga kyau ga qarancin shekaru wanda yasa tayi looking very attractive ta fito zuwa parlour’n sai dai duk ranta babu dadi , da granny ta soma cin karo ta durkusa har kasa ta gaisheta “barka da safiya granny “barka maryama fatan kin tashi ?”Lfy ina umma? bata rufe baki ba umma ta fito daga dakinta ta qaraso ta tsaya kusa da maryama ta dafa kafadanta “har kin shirya masoyiya ? maryama tayi murmushin jin dadin sunan da umma ta kirata dashi tace “na shirya umma barka da safiya “kin tashi lafiya ?ta gyada mata kai tana cewa “ alhamdulillah gamu zamu yakin karshe grany ta matso sosai kusa daita “maryama ki bi komai a hankali ki kiyaye banda shiga abinda bai shafeki ba allah ya baki saa a dukkanin abinda kike sa gaba .murmushi maryama tayi tana “cewa Ameen angama kakata ta kaina zan kula da duk abinda kikace, ta juya bangaren umma tana kallonta “sai ku tayani da addua, in sha allahu zakiyi nasara amman kamar kinso kiyi late ?” Aa banyi latti ba zamuyi daidai sai na dawo umma “ai baki karya ba ta fad’a tare da mikewa ta janyo hannuta bata tsaya koina daita ba sai inda ta ajiye mata plet din abincin data zuba mata ta zaunar daita ta soma bata abinci a baki tana ci tana duba mata lokaci har ta koshi ta sha ruwa ta mike tsaye tare da jiran adduarta “fatan alkhairi diyata karki sawa zuciyar karaya ki karfafa zuciyarki kisa aranki matsalarki tazo karshe da yarda allah ki kula da kanki please “in sha allahu ta kalli inda Aunty Hasana take zaune akan kujera wacce ko kallon inda take batayi ba a tun sanda ta fito daga daki sai man karanta wani littafi take .”
jiki a sanyaye kamar kartace mata komai tunda tasan ba fatan alkhairi take mata ba amman dai ta barwa allah komai kuma ko babu komai kanwar mahaifinta ce sai datai adduar samun nasara akanta sannan ta bude bakinta da kyar tace “aunty hasana ni zan tafi interview” fuskatar ta babu yabo babu fallasa ta dago tana cewa “in sha allahu bazaki samu aikin nan ba yadda kika fita da murna in sha allahu da bakinciki zaki dawo gidan nan kinyi sanadin kashe mana d’a amman Ke har kin manta kin fara neman aikinyi jikin maryama yayi sanyi hawaye ya cika kwarnin idanunta “hasana bai kamata ki dingawa diyar danuwanki haka ba “to mama ni meye nayi mata bayan gsky na fad’a aiki ne a gabanta ko zama tayi tunanin abinda Ke damun rayuwarta muddin kina son zaman lafiyarki damu ki kiyaye takurawa yarinyar nan kinji na fad’a miki “ai daman nasan duk kun tsananeni akan wannan yar iskar yarinya irin tsiya irin jaraba kawai masu mugun jini taja tsaki ta dauke kanta akansu .”
Shiru maryama tayi tsaye ta kasa kwakkwaran motsi tana duban Aunty hasana cike da sarewa gbdy sai taji zuwa interview din ma ya fita ranta domin tana ji ajiknta kotaje bazatai nasara ba granny ta janyota zuwa jikinta “maryam ki maida hankali lokaci na tafiya fa karki damu da maganar wannan mayar in sha allahu zaki samu aiki “okay granny na gode sosai “abinda granny ta fada in sha allahu haka ne zai kasance karki manta cewar hasana ba itace takawoki duniya ba dan haka babu abinda bakinta zai miki inji cewar umma idanun maryama suka kawo kwalla muryarta a raunane tace “ni dai ku bata hakuri idan wani laifi nayi mata ta yafe min dan banason tana fadar mummunar kalamai akaina umma idan kin sani bayan babu ran iyayenka addaur yanuwansu tamkar adduar iyayenka ne “.
“haka ne amman ita mummunar adduarta bazatai tasiri akanki ba saboda baki mata laifin komai ba ai baza ta’bawa yiwa diyar cikinta mummunar addua ba “Aunty ki daina hada diyar cikina da wannan yarinyar ita din ba diyata bace ya kamata ki fahimta “allah dai ya ganar dake gsky dan ni banga amfani kiyayyar nan ba , idan uwarta tana da laifi dan ta auri danuwanki ai danuwanki ma yana da laifi daya nace sai daya aureta .”inji cewar granny “Ni wallahi umma da nayi zamana dan ina ji ….”bazaki zauna ba kuma babu abinda kike ji sai alkhairi maza kama hanya ki wuce fatan alkhairi allah yayi miki albarka “Ameen ta juya cike da sanyin jiki take daga kafafunta .”
Ganin haka yasa umma ta mike ta biyota tana cewa “ki shiga wajen Auty ku gaisa kafin ki wuce amman kiyi sauri karki yi latti kinji masoyiya maryama tace” to umma na wuce sai na dawo “to sai kin dawo allah ya tsare “fatan alkhairi maryama allah ya bada saa ta fito bangaren mahaifiyarta ta shiga bayan ta gaisheta tayi mata sallama itama fatan alkhairi tayi mata “aunty ina after dad?yana ciki yana bacci “okay ki fad’a masa na tafi interview ku tayani da adduar samun nasara tana qoqarin fita daga part din aunty ta kira sunanta “princess ! ta tsaya cak tare da juyowa ta fuskanci mahaifiyarta tana mai gyara zaman Jakarta a kafadarta“kinyi breakfast kuwa da kike kokarin fita ta qaraso gabanta hannunta rike da cup din tea mai kauri tare da bread bata tsaya jiran mai za tace ba ta kai cup din tea bakinta “bude bakinki ki sha ko kadan ne bana son kina fita batare da kin sakawa cikinki komai ba .”ahankali ta bude bakinta tace “naci abinci daga hannun umma kuma na koshi amman bari naci daga hannunki ta soma kurban tea ba wani mai yawa ta sha ba tace “ya isa haka na gode sosai ta rungumeta tare da yi mata sallama tana fitowa daga part dinsu ta rufe fuskarta da qara min nikaf .”
********
Babban hall ne aka tanadar masu ,suna zaune gefenta yusura ce itama sanye cikin shiga ta kamala kowanne ka gani acikin hall din rike yake da takardunsa na makaranta wasu acikin jaka, wasu rungume dashi ,tun daga Kan matakin diploma har zuwa kan digree na biyu .bayan wani lokaci aka fara kiran suna daya bayan daya har aka kawo Kan maryama da addua ta shiga inda zaa mata interview tana shiga ta yaye nikaf din fuskarta kasancewar taga mace ce ,sectary ta sakar mata murmushin dan ita tun ranar data soma ganinta taji ta kwanta mata arai yarinyar tana da natsuwa gashi tana shiga ta mutunci ko yanzu duk masu neman aiki babu wanda yayi shigar mutunci kamarta “ga guri ki zauna “na gode” maryama ta fad’a a natse tare da zama tana ma kanta addaur samun nasara .” bayan awa daya aka gama daita tare da daukarta aiki “maryama hussein idan allah ya kaimu gobe zaki fara zuwa aiki amman wannna abun da kike rufe fuskarki dashi ba lalla sir ATA ya yarda dashi ba .”
shiru maryama tayi tana jin da kamar wuya ta iya fita babu shi a fuskarta domin ta rigada ta saba tsawon shekaru haka ta taso idan ma bata saka shi ba bata jin dadi” muryarta can kasa tace “zan dai gwada zuwa dashi idan ya bukaci na daina zuwa dashi zan kiyaye na gode sosai.” ta fad’a tana mikewa ta bar office din a wajen ma’akatan ta jira yusira itama cikin ikon allah ta samu suka nufo gida cike da murna yanayinta ya tabbatar ma yan gidansu ta samu aiki ta rungume umma cike da farinciki.”
“alhamdulillah umma mun dace “kai masha allah masoyiya gsky naji dadi sosai da kyakkyawan albishiri da kika min ,zuwanki aiki zai rage miki damuwa sosai allah yasa ki fara a saa” maryama ta qarasa ta rungume granny” na gode matuka da adduarku da bani kwarin gwiwa ta shafa kanta “babu komai maryama gabadaya parlour’n umma ya cika da murna aunty da habib ma murna fal anan yusura ta wuni currr suna murna sai yamma tayi masu sallama ta koma gida da zumar sai sun had’u gobe .”
Washegari da misalin karfe bakwai daidai a AGC company tayi masu babu ‘bata lokaci aka nuna kowace office din da zata dinga aiki tare da basu file file da zasu fara aiki akansa basu kasance guri daya da yusura ba ,tare da sultana suka kasance a office daya sosai maryama ta dukufa aka aikinta tana Kan aiki sectary ta shigo ta mika ma maryama wasu file “please ki cike yanzu ki kawo min office dina “okay ma”! ta fad’a tare da amsa ta ajiye aikin da take ta fara wanda aka bata .”sultana kam ko ta Kan aiki batabi ba wayarta ma take opereting can ta soma magana da alamun vioce note take yi “kinsan wani abu qawata gani zaune babu abinda nake takardun banza daakawo gasu agabana haka zasu karaci yininsu bazan cike komai ba kuma bazan zana komai ba dan ba abinda ya kawoni kenan ba.” ta tura tai shiru tana murmushi can sautinta ya sake karade office din “wa wannan mutumin ai bai yi ba wani office aka kaini dabam ba idan yake ba amman duk bata ‘baci ba komai zai tafinmin yadda nake so ai bari Ke dai qawa mutumin nan ya hadu fiyye da tunaninki sai ma kin gansa a zahiri sai kin kusan sumewa .”ta qarasa mgnr tana kam kamkame jikinta .”alamun tana jin shauki akansa .”
Maryama na ciki aiki sai ga subai ta shigo office din hannunta rike da wasu file yayinda wuyata ke makale da ID card mai dauke da cikakken sunanta da tambarin Z&A da sauri ta qaraso gurinta tana dafa kafadanta“wa nike gani haka kamar maryama ?maryama ta dago a natse tana dubanta “a’a subaia wallahi nice ya kike ya kwana biyu ? lafiya kar dai kina cikin sababbin ma’aikatan daaka diba?maryama tai murmushi tana gyada mata kai alamun “eh !”kai gaskiya naji dadi dana ganki a matsayin maaikaciya anan .” Maryama ta maida hankalinta ta cigaba da abinda take ai nasan daman allah bazai barki haka ba kullum ina sakaki cikin adduarta na gode sosai da taimakonki gareni “kai karki damu ai yiwa kai ne fatan alkhairi “thank you dear .”har subaia ta juya maryam ta mike tana kiran sunanta
ta tsaya “Yauwa subai’a ina ne office din madam some?muje na nuna miki suka fita tare tana sauke nikaf dinta suna qarasa fitowa ta nuna mata da dan yatsanta”gashi can sai mu sake haduwa nima wani aiki ne ya kawoni sukai sallama ta karya kwana “.
ita kuma maryama tayi kokari shiga office din data nuna mata ta tura kofar glass sannan ta sanya jikinta ciki adaidai lokacin da idanun ATA ke Kan cctv “wacece wannan data shigo yanzu “?ya tmby yana dauke idanunshi ya maida kan fara takardar dake gabansa ya juyo mata compute daake ganin shiga da fitar mutane .”
Some ta sauke idanunta akan computer maryama ta gani muryar some na rawa tace “maryama hussein!”
“wace ce haka ?”sabuwar maakaciya ce “baki fada mata baa zuwa mana da irin wannna shigar bane ? “na fada mata sir “!yayi shiru yana maimaita sunan acikin zuciyarsa maryama hussein sannan yana sake kallon cctv tabbas itace yarinyar “ wannna ba yarinyar da muka bukaci zanenta bane watanin baya ba ?“muryarta na rawa tace “ita itace sir .” what ! ya fad’a tsawace “nan take jikin sectary ya dauki rawa “dan allah kayi hakuri sir “ itace yarinyar da akayi interview akan kasuwanci daita , yarinyar da take da kwarewa sosai akan zane itace yarinyar da kace anemo ta watanin baya “ kenan the same person ce “? ya fad’a yana ciza lips dinsa da karfi “yes sir duk mutun daya ce itace take zane but sir yarinyar tasan kan aikinta duk a rud’e take masa wannan bayanin.”
shiru yayi yana jin wani irin mummunar faduwar gaba from no where sai dai bai dago ba ya cigaba da typing din da yake cikin zafin rai .”kana kallon yadda yake daddana keyboard din system din kasan baya cikin natsuwarsa “bana ce kar a Kuskura a dauketa aiki ba ?kuma kikayi son ranki har ma kina min dogon bayani akan yadda ta wulakantamu”sir !sir !!kayi hakuri nayi ta kokarin na fada maka saboda gudun faruwar haka amman kaki bani dama “.
“me kke nufi ni ban fad’a miki ba karta samu aiki har karshen rayuwarta ba bama a wannan company din ba har other companies?Ke ma kinsani bana bawa kowani irin mutun second chance dan haka kije ki sallameta bana son ganinta acikin company din nan “oya go out ! ya nuna mata hanyar fita jikinta na rawa ta fito .”tana fita ya zabura ya mike tsaye ya daura hannunsa daya akan hannun kujerar daya tashi gabansa na wani irin mummunar faduwa zuciyarsa na tuttukin zafin kamar ya dakatar da some amman bakinsa ya kasa furta komai .
ya bar wajen ya koma jikin window yana kallon haraban maakatan yaso kwarai ya samu nasara sake ganawa daita amman ina bazai iya daukar iskancinta ba har kamar shi ya sauke girmansa ya kirata amman taki daukar wayarsa har ma da kashe masa waya ga mummunar sako data fadawa james bayan haka ya nemi ganawa daita a ogun shima batayi masa abinda ya bukata ba sai ma qara masa damuwa datayi jin abun yayi kamar alokacin ya faru babu wani sausauci da zai mata wanda ya wuce ya koreta daga karkashinsa .”
da sauri sectary ta fito zuwa office dinsu tana shiga ta isketa zaune da farar takadar agabanta tana zana mutun sanye da suit da wondo har ma da takalmi acikin mintuna da basu wuce ashirin ba ta tsaya tana sauke numfashi, ganin ita kadai ce a office ta qaraso sosai ta tsaya akanta tana tunanin yadda zatai mata magana dan sam babu dadi ka samu aiki ranar da ka fara zuwa ace an koreka tsayuwarta batasa maryama ta dago ba dan bata ma ji alamun shigowarta ba kokari take ta kammala aikin da ta fara dashi amatsayin aikin farko .”muryar some a sanyaye ta kira sunanta “maryam hussein ! maryama ta dago da sauri tana cewa “yes ma ,akwai wani aikin da zan miki “?”No you’re fared cak numfashin maryama ya nemi ya dauke sakamakon jin mummunar labarin datayi nan take dakin ya dinga jujjuya mata wani irin tashi hankali tashig mara misali kafin a hankali ta janyo numfashinta dake kokarin barinta ta dawo dashi gangar jikinta ta fuskanci sectary sosai hankalinta na qara tashi “wannan hukuncin MR ATA né “.
“Hukuncin Mr ATA”. ?ta furta da karfi tô kaifin me nayi masa nida yau na fara aiki anan ?tayi mgnr Kmr zatai kuka cike da tausayawa sectary ta dafata sai dai ta kasa cewa komai “ko zan iya magana dashi dan haka kawai bazaa dakatar da mutun batare da wani laifi ba ?tayi mgnr a fusace .”no no !! ba sai kingansa ba ,dan ni kaina a halin yanzu ina cikin matsala dan allah ki bar nan yanzu kafin ya shigo “ba maganar na bar nan bane ko kina cikin matsala ina son nasan dalilin da zai sa akoreni tunda nasan sai da dalili akewa mutun irin wannan korar lallai sai nasan meye matsalar kafin na bar maakatan nan ,”ki natsu please maryam sir bazai ganki ba a yanzu .”
“Kema kiyi hakuri kiyi min iso Ke bari ma naje da kaina .”fuuuuu ta nufi kofar fita da sauri some ta biyo bayanta tana kiran sunanta “maryama ki tsaya karki sake yin wani kuskure ta riko hannunta cikin zafin rai “bazai yuwa ma ki shiga inda yake ba wannan ya sabawa doka .”
“Doka wani doka kuma ?wallahi kusani kun tafka babban kuskure na korata ,bari ma kiji bani nayi applied din aiki a kamfaninku ba yi min akayi dan haka yanzu ma ban damu ba kije ki fad’a masa ko bansamu aikin a anan ba zan samu aiki adalilin baiwar da allah yayi min kuma bare ma zan samu aiki da takarduna” dan allah kiyi hakuri nima ba laifina bane .”shiru maryama tayi kafin ahankali tace”madam some ko zansa exactly laifin me kika min da kike bani hakuri ?ai nice yafi dacewa na baku hakuri ku da ake nema a wurinku ,amman ku kuwa wani irin tsarin ne da maakatarku hk ?a dauki mutun aiki rana daya da fara aikinsa a koresa ?kiyi hakuri maryam ki wuce kawai karma kisa rai ko a wani guri ma zaki samu aiki domin sir nada karfin iko a koina “to ni laifin me nayi masa haka ?ki tmbyr min shi laifi me nayi masa haka ?tai mgnr tana kuka “ai ban isa najewa sir da wad’an nan tamvayoyin naki ba “to shikenan amman wallahi kisani bazanje koina ba har sai naji dalilin dayasa ya koreni muddin bai fad’a min laifin da nayi masa ba anan zan qarar da rayuwata ..” ta samu guri ta zauna tana kuka mai matukar cin rai “.
“okay maryam bari na gwada saata ko allah zai sa ya saurareni ta juya da sauri ta fice yayinda maryama take zubar da hawaye masu zafi bata san sanda ta zamo kasa bisa gwiwowinta ba ta hade tafukan hannunta guri daya “ya allah meke shirin faruwa dani kuma ?wani irin tashin hankali ne wannan ?daga zarar na fita cikin wata maseefar sai wata ta bullo ya allah ka taimakeni .”a can gida ma hankalin aunty da umma har da granny duk a tashe yake umma ta qaraso da magani da ruwa a hannunta hajiya yau baki sha maganinki ba ga lokaci na wucewa “ni gbdy na ma manta da wani batun shan magani dan bana da natsuwa ban san halin da maryama take ciki ba wallahi hakan nan nake jin damuwa ya allah ka taimake yarinyar nan kasa karshen wahalarta ne yazo “karki damu in sha allahu alkhairi ne zai biyo ba tunda an dauketa aiki ai sai fatan albashi su fara shigowa to allah yasa alkhairi ne zai biyo baya .”ameen ta karbi magani ta kai bakinta .”
ATA na tsaye har lokacin ya kasa zama sectary dinsa ta shigo “sir na fad’a mata hukuncinka amman tace baza tafi koina ba har sai ta gana da kai “no way !” ya fad’a yana jin wani irin faduwar gaba mai tsanani ”I won’t meet her ki koma ki fad’a mata haka” sir na fad’a mata taki tafiya ne wai sai an fad’a mata laifin da tayi daaka koreta aiki daga farawarta yau “kije ki fad’a mata ta bar kanfanin nan dan bazan ganta ba kema da kika dawo min da banzar maganarta idan kika sake zuwar min da mgnrta zaki samu matsala dan kinfi kowa sanin laifin datai ko ba da kanta taki amsar aikin da muka bata a tun farko ba ?”sannan na bukaci zanenta shima taki yarda ta ganni sau nawa ina kiran wayarta taki daga wa ta saurareni sannan nayi qoqarin tayi min aiki a ogun shima babu wani biyan bukata,yanzu kuma ta kwaso jiki tazo neman aiki kamfanina ?kema kinsan bazai yuwu ba ya fad’a a matukar a tsawace .”
Nan take sectary ta kame jikinta na rawa dan duk lokacin da yake mgn cikin fushi itama fita haiyacinta take ya sauke numfashi kana ya dunkule hannunsa ya naushi iska “aikin har yana arha haka ka kisa alokacin da kaso sannan ka samu alokacin da kaso “idan ma baki fad’a mata laifinta ba ungo nan ya zaro wata farar takarda ya mika mata kije ki bata amman ganina ko magana dani abu ne da zai mata wahala acikin wannan kafanin ke qarshen rayuwarta bazata sake ganina ido da ido ba “okay sir tasa hannu ta karba ta juya ta soma tafiya “idan aka sake halittarta a duniya aka bata aiki bazata ki karba ba nonsense girl kawai ya fad’a yana furzar da iska .”
Da sauri sectary ta shiga office din da maryama take tana mai kiran sunanta ta mike da sauri ta qaraso gareta tana cewa”laifin me yace nayi masa.” mika mata takarda tayi tana qara mata da bayani abinda tayi hawaye ne suka zubo mata” wayyo allah wallahi bana ki amsar aikin bane a wancan ranar dan yin kaina wata kawata ce tafi ni bukatar aiki shine na bar mata amman badan banason aikin bane” wanna shine dalilin da yasa mr ATA ya koreki kema abinda kikayi bai kamata ba bayan shi ma akan zane shima haka kika masa wulakanci bayan saboda abinda ya faru aranar da kikazo kawo zanensa yaji babu dadi aransa shine ma yasa James yayita kiranki akarshe shima ya kiraki baki dauka ba ,da kuma kika dauaka me kika ce ?”maryama tayi shiru tana dubanta “kikace bazakiyi ba !” Muryarta a sanyaye tace “am sorry !” Babu wani maganar sorry zaki iya tafiya dan bazaki samu wata dama ba “is okay na gode Kwarai da gaske tunda da farko nice naki amsar aiki sannan nakiyin aiki daku yanzu kuma na dawo kuka kini bani da yadda zanyi tunda ku kuke da kamfaninku tana gama magana ta juya da niyyar barin office din idanunta ya sauka akan kawarta subaia “kin rasa aikinki akaro na biyu maryama akaina ?”
“karki damu subai ba akanki bane haka allah ya qaddaromin Kiyi min fatan alkhairi.““ dan allah kiyi hakuri nasan duk laifina ne “nace karki damu ko na karba da farko haka zasu min dan da gani mai kanfani har wadan da suke aiki karkashinsa duk mahaukata ne na ma gode da ban samu aiki akarkashinsa ba suna cikin wannan halin sai ga yusura ta fito daga office din daakaita ,kusa da maryama taje ta tsaya tana tmbyarta “aikinta ta rasa adalilina aikinta da bar min “wata uwar harara yusura ta maka mata “ai gsky ne adalilinki ta rasa wancan aikin yanzu ma ta rasa wanna kenan ?subai’a ta gyada mata kai “a wani dalili ?”Ke !me ma ya kawoki ma tunda ai baa nan kike aiki ba ?karki manta da mai wannan kamfanin da A&Z duk mutun daya ne wani mahiman aiki ne ya kawoni “karku tsya bata lokaci please zaku iya wucewa kuje kasa ku cigaba da magana inji cewar some“maryama bari na dauko jakata mu tafi tare kawai zaman me zanyi ?no yusura karki damu kiyi zamanki bazan zama sanadin rugujewa farincikinki ba ,ina miki fatan alkhairi all the best to both of you tana gama fadar haka ta juya ta soma taku ,da kyar take iya d’aga wafafuwanta saboda nauyin da suka mata ,wani matashin mutun ta gani tsaye bata bi ta kansa ba ta raba ta gefensa ta wuce shi tana sauke nikaf din fuskarta shi kam kamewa yayi ya kasa kwakkwaran motsi shin mafarki yake ko kuwa zahiri yake gani ?.”
ya kai second goma yana kallon bayanta har ta kusan ‘bacewa ganinsa sannan ya juyo ya dubi some “ kinga wata doguwar yarinyar ta wuce yanzu ? “ yes sir ! da sauri yace “ mutun ce ko fataluwa ce ?mutunce sir sunanta maryam hussein “.maryam hussein !? ya furta a dan razane adaidai lokacin da yusura ta fito ta tabi bayan maryama da sauri tana kiran sunanta hankalin salim a matukar tashe yace “Adam ya ganta kuwa ?No sir aiki tazo nema har an dauketa yace akoreta” da sauri yace “kai bari naje na sake tabbatarwa itace ko kuwa dai kama ce ya bi bayanta da sauri ya sauka har kasan kamfanin yana nemanta bai ganta ba tsaki yaja yana cewa “ amman Adam ya cika hauka me yasa bai tsaya yaga yarinyar nan ba yana tsaye sai gasu ita da yusura maryama tana magana muryata da alamun tayi kuka sosai “karki damu yusura ki tsaya Kiyi aikinki karki yi Kuskure irin wanda nayi ,kin dai ga yadda abun alkhairi ya zame min ko? to ki tsaya kiyi aikinki ina miki fatan alkhairi “ta fad’a tana tsaida yusura tare da rike hannunta cikin nata .”Ahankali salim ya kara taku ya matso kusa dasu “shikenan maryama naji kuma na gode da shawarki allah yasa haka shine mafi alkhairi arayuwarki sai mun hadu a gida dan allah karki saka damuwa aranki komai yana da lokaci kuma in sha allahu zai zama alkhairi .”
numfashi ta sauke sannnan ta saki hannun yusura dake cikin nata ta juya itama ta juya ta soma tafiya da sauri kawai taga mutun agabanta yana sauke numfashi bai tsaya wata wata ba kawai ya daga nikaf din fuskata tare tsura mata ido byn Kmr second biyu ya saki wani irin murmushi wanda bashi da maraba dana farinciki muryarsa cike da in.. ina.. ya soma mgn”itace wallahi tabbas itace wallahi itace wacce danuwana ya dade yana nema yayi maganar yana riko tsintsiyar hannunta “dan Allah kiyi hakuri mu koma ciki akwai wanda zan nuna wa ke .”bai gama rufe bakinsa ba ta fixge hannunta tare da daukeshi da wani gigitaccen mari tana cewa “itace wa ?”
“Akan wani dalili zaka kai hannunka jikina ?”ammm but da kin ..”“kar kace min komai bana bukatar jin komai dan baka zo da siffar da zan saurareka ba daga ganin mutun sai ka wani kai hannunka jikinsa kasani koni matar aurece ta fad’a a fusace tana sake juyawa ya sake shan gabanta”wallahi babu inda zaki sai na kai ki gurin ..”“wallahi ka sake kuskure tabani sai na maka wulakanci da har ka matu bazaka manta dani ba ,matsa ka bani hanya na qara gaba da rayuwata “.
“to to ki bani numberki ko address dinki “i cant! ta fad’a tana bin gefensa zata wuce shi sam sam marin da tai masa bai damesa ba kamar tafiyar da zatai Adam bai ganta ba da sauri ya sake shan gabanta “kinsan allah bazaki bar nan ba batare da danuwana ya ganki ba wuce mu koma sama maryama ta dafe goshinta cikin tsananin tashin hankali “wannan shine karo na biyu da ta fuskanci irin wannan matsalar “ kafin ta ankare taji ya rike tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita cikin sauri sauri gudu gudu ya dinga tafiya, tana ya sakar mata hannu amman yaki da kyar da bala’i ya shigar daita lifter ya fad’a office din ATA daita a tsaye ya gansa rike da kugu ya juyawa kofa baya yayinda cup din coffee ke rike a hannunsa yana kurban coffe a hankali bai juyowa ba har sai da yaji salim ya soma mgn “ATA…”ya kira sunansa cikin wata irin muryar mai cike da tashin hankali ATA ya juyo a natse yana fuskatarshi alokacin da salim ya cire nikaf din fuskarta maryama yana rike a hannunsa wani irin bugu qirjinsa da zuciyarsa yayi alokaci daya bai san sanda cup din hannunsa ya subuce kasa ba. take ya tarwatse zuciyarsa ta tsaya cak ta daina aiki na wuncin gadi ,duk yadda ATA ya kai ga son motsa sassan jikinsa bun ya faskara,tamkar wanda bai da numfashi a ganganr jikinsa haka ya dawo saka makon wani yanayi mai sarkakiya da wuyar faasarawa ya ziyarci zuciya dama gangar jikin ATA abangaren maryama ma wani irin mummunar bugu zuciyarta keyi da mugu mugu sauri “la haula wala kuwata illa billa” babu tsumi babu dabara sai na Allah haka ATA yake ta faman ambata acikin zuciyarsa dake karkarwa yayinda maryama wacce bata san dalilin dayasa mutumin dake tsaye a gefenta ya shigo daita ba sai dai ganin fuskar mutumin dake tsaye a gabanta yasa ta nemi natsuwarta ta rasa .”
hakan nan damuwar dake cunkushe cikin ranta ta ninku yayinda soyayya da kaunarta ya dinga bin dukkan sassa na jikinshi ji yake kamar acikin mafarikinsa ya Allah kasa a zahiri nake ganin komai ba mafarkin dana sabayi daita bane ,wani irin so mai zafi ya dinga huda zuciyarsa yana bin jinin jikinsa wanda ma'abota so da shauki kadai ne suka san zakinta,yana son yarinyar kamar ranshi shikanshi yana mamakin zazzafar soyayyr da yake mata mai tafiya da dukkan wani motsi na bugun numfashinsa “adam kayi maza ka dawo haiyacinka karka biyewa soyayya dake kutimemeniya da rayuwarka gizo ce ba zahiri ba “to Salim dake tare daita fa ?shima gizo ne ko me “? tsaki taja tana duban fuskar salim a wulakance cike da tarin bakinciki mara misaltuwa muryarta cike da sheshekar kuka tace “Allah ya isa tsakanina da kai bazan ta’ba yafe maka ba “.sautin muryarta ce ta dawo da mr ATA cikin haiyacinsa tun bai kai ga bawa kanshi amsa ba ya ware idanusnhi sosai ya zuba mata kwayar idanunshi yana kallonta tamkar zai cinyeta “.
Alhamdulillah
Anan zan dakata sai mun had’u a littafi na uku wanda zai zama na qarshe ina maku fatan alkhairi
Mmn suka
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.