Best / Popular Hausa Novels

Maradams Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: MARADAMS book 2 by Aysha A Bagudo.txt

Chapter 3 of 14

Page 5

...Kusan minti biyar maryam na tsaye a bakin kofar shiga babban parlour'n gidan gabanta na wani irin bugawa da karfi, sai da aunty shahida ta sake maimaita magana sannan ta d'aga kafarta ta dama da kyar bata sauketa a koina ba sai acikin had'ad'den parlour'n ."
yadda gabad'aya penting jikin gidan yake fari sol haka zalika cikin gidan yake ,gidan ba wani babban gida bane akan sauran gidajensa domin kuwa duplex ne sama da kasa ,sama d'akuna uku ne sai d'aki d'aya wanda aka waresa domin baki , babu abinda babu acikin wannan d'akin, idan baki suka shiga cikinsa bazasu fito domin yin ibada ba dan anyi masa tsari na musamman tare da kujerar kwaya d'aya a d'akin wanda ake kira da (L)."

yayinda kasan gidan babban parlour ne mai d'auke da d'aki d'aya da bayi , sai makeken kitchen da dining area sai kujera three seter manya manya guda biyu da one one seater guda biyu na alfarma ga makeken tv bango 80 inches ,iya had'uwa wannna gidan ya had'u domin kuwa an zuba duk wani kayan qawa na more rayuwar duniya ,kai tsaye sama suka nufa da maryam rike da hannunta har d'akinta suka zaunar daita a bakin gado sannan aunty shahida ta shiga kallon d'akin komai kamfani ta tsarashi da kyau dan bata samu damar zuwa ba lokacin da zaa kawo kayan maryam "

Numfashi aunty shahida ta sauke kana ta soma magana "maryam yau dai allah yayi ikonsa gashi kin tare a gidan mijinki kuma danuwanki kiyi hakuri da duk wani abinda zaki gani marriage is sweet and sometimes is not sweet , so idan kikaga dadi kiyi farinciki ki gara godewa allah ,idan kika ga sa’banin haka Kiyi hakuri wanda daman hakuri kowacce mace ke yi a gidan aurenta ,matakin nasara a gidan aure ba komai bane sai addua juriya da kuma hakuri dan haka ki qara hakuri akan wanda kike dashi ko ba adamcy kika aura ba dole zakiyi hakuri bare kuma kinga irin mijin da allah ya baki mai matukar wuyar shaani ,amman da sannu idan kina masa abinda yake so zai canza miki daga adamcy da kika sani zuwa sanyin idaniyanki kiyi duk abinda mijinki yace abinda yace baya só ki barshi."

muryarta na rawa tace"naji kuma na gode aunty in sha allahu zan kiyayye sai da suka d'auki wa d'aya da wasu mintuna sannan suka fara qoqarin wucewa durkushewa maryam tayi a gabansu aunty shahida tasa masu kuka mai ta'ba zuciya, tausayinta ya kama su, dan sun san kukanta yana da nasaba da irin rayuwa da zatayi acikin gidan mai tattare da rashin 'yanci ,da kyar suka rarrasheta tare da bata kwarin gwiwa kafin sukai mata sallama suka kama gabansu ."

Bayan tafiyarsu ta tsaida kukanta tare da sa hannu ta goge hawayenta tayi shiru acikin makeken d'akin da babu abinda babu na jin dadin rayuwar duniya komai na d'akin blue ne da kujera sofa kwaya daya ta hade hannuwanta waje daya tana jin mummunar fad’uwar gaba "ko wani irin rayuwa zanyi acikin gidan nan ?ta yiwa kanta tambayar kafin a hankali ta yunkura daga zaunen da take ta qarasa jikin window d'akin ta tsaya tare da kai hannu ta d’an zuge labule tana kallon haraban gidan ahankali take kallon get din gidan tana jin fad'a uwar gaba mai tsanani ."

Shi kuwa ata daga inda yake a tsaye a haraban gidansu tunanin yadda zai yi da maryam yake bayan yasan kisan kai haramun ne a addini tabbas daya zuba mata shinkafar bera cikin abinci taci ta mutu ya huta ,wani naunayen numfashi ya sauke adaidai lokacin da wayar hisham ta soma ringing ya ciro wayar daga gaban aljihunsa ya duba ganin mai kiran ya saki fuska tare da d’agawa "hello my nuzlah!okay ina haraban gidan ma yanzu ,no karki damu anything for you my love a natse ya cigaba da motsa lip's dinsa “karki manta kece rayuwata kece wacce zuciya da gangan jikina suka yarda kuma suka amince da qaunarta “ya qarasa maganar yana washe hakora .”

kallon kasan ido ata yayi masa yana mai jin tashin hankali mara misaltuwa."Kai dan allah manta daita ai kece the best kece first lady ai yana magana yana murmushi mai tattare da farinciki "wani irin bakinciki ya mamaye gangar jiki ata yayinda zuciyarsa ta dinga tuttukin bakinciki bai tsaya cigaba da jin wulakanci da hisham yake yi masa ba ya juya cikin tsananin fushi yana jan tsaki ,kai tsaye inda motocinsa suke pake ya nufa."
Ya tsaya kawai cikin zafin zuciya yana ciza lip's dinsa na kasa da karfi ma'aikatan dss da wasu daga cikin masu tsaronsa suka zagayesa yayinda wasu na qoqarin bude masa mota ."cike da zafin zuciya ya shiga gidan baya ya zauna yana cigaba da ciza lip's dinsa yana girgiza kafarsa daya."

hisham yayi murmushi bayan wucewar ata sannan ya cigaba da wayarsa "hisham abinda kayi bai dace ba cin fuska ne ga ata "shi ya'ya mutane da yakewa fa ?ai gara shima a dinga masa yaji ko da dadi ,ka duba kaga yadda ya bari aka wuce da maryam ita kadai babu wata kulawarsa sannan kaji irin maganar daya fad'a maka sam sam maganarsa babu da'a acikinta, baya respting din mace , ka sani na sani kowa hakuri yake da abinda yazo hannunsa ,shi mai yasa bazai yi hakuri ba ? bana son nana hauwa'u nuzlah nake so amman hk na hakura daita nuzla dake sauronsa ta sauke numfashi aranta tace "sai ma ka rabu daita yadda danuwanta ya nuna rashin qauna gareni itama sai na bari ta d’and’ani qiyayya mai zafi daga gareka dan babu abinda zai hanani shiga gidan "kaga mu bar maganar mayi daga baya ."inji cewar salim.”

Direbansa cike da girmamawa ya tambayesa inda suka nufa "muryarsa can kasan makoshi yace "mb ! dan haka kira motar da zata fara yin gaba yayi ya sheidawa direban sannan suka sa kai motoci biyu ne a gabansu sannan motar da ata yake ciki sai mota biyu abayansu,cikin kankanin lokaci suka qaraso kan titin oduduwa road inda anan gidan mb yake ." bayan motocinsa sun shigo cikin haraban gidan sukai parking ,sai dai shiru ata ya cigaba da zama yaki fitowa sai daya d’auki mintuna shabiyar sannan ya fito a natse yana shan kamshi.”

Mb na zaune yana kallon tashar labarai yaji sautin muryar ata yana sallama aciki ,fuskar mb cike da farinciki ya mike tsaye daga zaune da yake ya tarosa ya rungumesa ajikinsa yana cewa "kai mutumina daga ina haka ?sai daya sauke numfashi sannan yace "daga gida ! ya bashi amsa atakaice sannan ya samu waje ya zauna yana fesar da numfashi tare da runtse idanunshi ,amira dake kitchen ta fito hannunta rike da tray ta gaishesa fuskarta a sake "ango kasha kamshi ina yini ? " ta fada idanuta na kan tray din dake hannunta tana zuba hadin salad.”

fuakarsa a hade tmkr wanda aka fadawa sakon mutuwa ya amsa "lafiya lau madam ya gida da yaran ?"lafiya lau muke” tace masa atakaice dan ta qagu ta kammala abinda take ta bar gun taje ta shirya kanta ."tana sauka daga stares din dining area din mijinta ya cigaba tambayarsa amaryarsa ."
"Manta da wata amarya na dai baro su aunty sun wuce daita amman zan basu mamaki "kamar ya zaka basu mamaki ?.”

"bazan ta’ba kwana a gidan ba, aure ne nayi ,tariya ce na basu damar sukaita ,rayuwa daita kuma bai zame min dole ba haka zata qare rayuwarta batare dani ba " haba abokina karka yi haka mana ka tausayawa yarinyar nan mana ,”kaga ni ba abinda ya kawoni kenan ba “ mb ya gyara zamansa yana dubansa a tsanake tare da cewa “me ya kawoka?“nazo ne akan hisham ".

”hisham kuma ?mai faru dashi ?yayi masa tambayar a jere cikin tsananin tashin hankali ya sauke numfashi kana ya motsa lips dinsa kadan "hisham yana son mu samu matsala dashi “a natse ya cigaba da magana ya zayyano masa komai mb ya numfasa kana yace "gsky bai kyauta ba zan masa magana amman kai kuma ai bai kamata kaji ciwon abinda yayi ba tunda kaima halinka ne koma nace a wajenka ya koya,kaga yanzu lokaci yayi da zaka canza” ata ya d’an d’ago kanshi ya tsura masa tsumammun idanunshi “

”wallahi ka canza halinka kaga yadda yaruwarka baza taji dadin aure a gidanta ba kana cin zarafin ya’yan wasu da kanen wasu amman kai baka son ayiwa naka ai kai ma kasan hakan ba abu ne mai sauki ba ,kasani duk abinda kayi sai anyi maka “wannan ba gasky bane yayi maganar yana lasar lip’s dinsa “duk dai abinda mutun yayi akanshi zai qare ba akan wani ba mb ya bud’e baki zai sake magana ata yayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa “dan allah na gama da wannan maganar shi kuma hisham ka nemeshi kaja masa kunne, kuma zan kira auta matukar tana facing din matsala a gidansa sai kunji tsoron abinda zai biyo baya dan wallahi sai na kashe auren gabad’aya.”

“idan kuma tana son mijinta fa ? shiru ata yayi batare da ya ce komai ba yana nazarin maganar mb “ka tsaya ka natsu kayi tunani mai kyau domin kashe auren ba shine mafuta ba , ka barta tayi zaman aurenta lafiya , babu ruwanka da matsalar gidanta idan da wata matsala nayi imani nana hauwa’u zata kawo karshensa ,ina baka shawara ka cire hannunka karka zo kayi abinda zaa zo ana kuka da kai “ shiru ata yayi ya kasa cewa komai yana nazarin maganarsa har sanda amira ta sake fitowa ta cika masu table din gabansu da kayan abinci iri iri ta juya zuwa d’akinta ."

"Abokina ..!"rin wannan liyafa haka,gsky ina da rabo acikin abincin gidanka yau shyasa haushina ya kawo ni gidanka kasan bayan mun shigo haraban gidan nan naji kamar bazan shigo ba"yanzu dai kanka ake ji sarkin kwad'ayi,ga abinci nan kayi sarving din kanka ata yace " no bari amira ta fito "ta fito tai maka me ?”yayi masa tmbyr yana hararasa “hankali kwance ata yace “ta zuba min mana “ai kuwa baka isa ba sai dai idan bazaka ci ba ,amman matata ni kad'ai zata sarving ,idan kuma lallai ka matsu da cin abinci kaje ga matarka .”

"uhm !ata ya furta daga kasan makoshinsa sannan yace "banson iskanci fa mb matarka ko matarmu ? mb yayi murmushi yana dubansa adaidai lokacin da amira ta sake fitowa yace "darling zubawa wannan gogaggen dan iskan abinci yaci ba dan halinsa ba “ murmushi tayi ta zuba masu tare ."sai da ya gama shan qamshinsa kafin ya soma cin abinci."mb ya gyara zama yace “gsky abokina karka cuci kanka wallahi kaje
wajen matarka ko babu komai ai ka rage mara “ata najinsa amman yayi masa banza yayi tmkr ba dashi yake mgn ba ya cigaba da kai abinci bakinsa .”

mb ya ajiye spoon din hanunsa ya zuba masa ido yana kallonsa “ wallahi ata ka canza rayuwa “me ya faru da rayuwata da zan canza ?abubuwa daya kuwa sun faru da rayuwarka taya da ranka da lafiyarka ga lafiyayyar mata allah ya baka amman ka tsaya cutar kanka .”kowa da yadda yake rayuwarsa ni yadda nake rayuwata empty yayi min .” ata ya fad’a batare daya jallesa ba shiru mb yayi yana cigaba da kallonsa kafin daga bisani yace “kai ko baka da lafiya ne? ata ya d’ago a natse yana dubansa mgnrsa ta bashi dariya sai dai yaki yi dan ba aladarsa bace yin dariya .”

“Ka tsareni da ido ko kuma maganar mami ce ta tabbata yarinyar mafarkinka aljana ce ?”uhm mb kenan “babu wani mb kenan ka fito ka fad’a min gsky gabanka na tashi ko kuwa zero ne kai ?ata ya dauke kanshi yana cewa “babban tashi ma kuwa dan a halin da nake ciki sannan na samu irin kalar yarinyar da nake so to wallahi sai ahankali dan zataji jiki “mb ya kwashe da wata dariya yana buga hannunwansa “ kasan wani abu abokina ?ata ya kai abinci bakinsa yana dan kallonsa alamun yana jinsa "daman irin ku ne idan suka shiga hannun mace sai allah ,sai yadda akayi daku ba soyayya ba hatta gaban mace sai ku lashe baku sani ba” abincin bakinsa ya tofar da sauri bayan ya dalla masa katuwar harara kamar zai cinye shi ".

”allah ya isa tsakaninmu da kai mb wannan ai cin fuska ne,ko zan so mace sai na kama wani lashe gabanta gabanta fa? ni adamcy ,i think ka fara hauka ,kai allah ma ya isa tsakanina da kai ya sake maimaitawa yana ajiye spoon din hannunsa tare da ture plet din abinci , alokacin da sugura ta fito da mugun gudu daga d’akinsu mansor na biye daita tana ganin ata ta nufo wajensa ta fad'a jikinsa tana kiran "uncle !"kaga yaya mansor ko ."
Ya rungume tsam ajikinsa yana kallon mansor dake haki "

”haba yaya mansor mai baby nah ta maka ?textbook din assignment dina ta yaga” ya fad’a Kmr zai yi kuka ata ya kalleta "baby da gaske kin aikata haka ?tayi shiru tana sake lafewa ajikinsa "ai tunda kaji tayi shiru ta aikata ne dan barna a cikin yarinyar nan baa magana babu abinda zata gani bata 'bata ba “inji cewar mb tare da kai hannu zai zuba mata rankwashi aka ata ya tare hannunsa "yana cewa “haba meye haka kuma ?wannnan hannun naka koni ka zubawa shi ai sai na tashi aiki bare ita ,mb yayi murmushi kawai ata ya kalli mansoor yace “kayi hakuri je ka dauko textbook din na gani ya juya da sauri ya shiga daki ."

ATA ya cigaba da shafa bayan sugura "a duk lokacin dana kalli baby sugura sai naga kamar princess dina tana yarinya "ko itace? Mb ya fad'a yana murmushi ata ya had'e rai sannan yace" banason iskanci yau fa naga wasu abubuwa kake min "babu wasu abubuwa idan itace shikenan sai ka cigaba da jira zan baka aurenta ."ATA bai qara cewa komai ba ya cigaba da shafa bayanta dan ya fahimci yau iskanci abokinsa yake ji ."

Bangaren maryam kuwa tana can zaune cikin tsananin tashin hankali gefe guda kuma jifa jifa tana duba agogo awani suka dinga zuwa suna wucewa ahankali ta mike ta shiga bathroom din dake manne acikin dakin tayi alwala ta fito tayi sallah magrib ,haka da ishai tayi ta sake mikewa tayi sallah duk abinda take gabanta banda faduwa babu abinda yake .”

"nan da wasu 'yan shekaru zamu fara ajiye surukai ,ya dai kamata kasan ciwon kanka Ata ka rungume aurenka , ko bazaka yi dan kowa ba kayi dan kanka dan rayuwar nan babu tabbas " karka mutu baka ajiye kowa ba “ muryarsa a matukar sanyaye ya motsa labbansa “wallahi ina matukar son haihuwa amman bada wannan yaron ba ,bana sonta mb “kayi hakuri ata ka daina fad’ar haka dan Allah kayi addua kawai “shikenan zan fad'awa sweetheart tayi min addu tunda addaur iyaye babu shamaki idan alkhairi ce arayuwarta allah yasa min sonta ko kad'an ne a zuciyata amman wallahi mb I don't know why ban ta'ba jin son yarinyar nan ba , kullum na ganta kamar na kasheta haka nake ji , suna tautaunawa mansor ya dawo hannunsa rike da textbook ya mikowa ata."

Ya kar’ba yace “mansor ai yagewar ba wani mai yawa bane kayi hakuri kaji yarona” kaiwa mamanku zata gyara maka yaron ya juya zuwa dakin amira sun jima suna tautaunawa har karfe shabiyu sauran sannan ata ya bar gidan zuwa gidansa dake lekki ." Ita kuwa maryam tana nan zaune har karfe goma sha daya ta wuce babu ango babu labarinsa ga tsananin bacci tana ji amman ta kasa ko kifta idanunta saboda tsananin tsoro jiki a sanyaye ta dauki wayarta ta kira mami "maryam ya akayi ya bakunta? adamcy ya shigowa kuwa ?"a matukar razane maryam ta dago ta kallon dakin ,sai kuma ta maida kanta qasa kamar tana gaban mami yayinda idanunta suka qara canza kala sakamakon qwallar data soma dan taruwa mata."

cikin faduwar gaba mami tace "me ya faru maryam ko bai shigo bane ? "mami bai shigo ba gashi tsoro nake ji mai matukar azabar
Idan bai shigo ba bazan iya bacci acikin gidan ni kadai raina ba " ajiyar zuciya mami ta saki"oh my god adamcy ,Allah yasa kar ya kasheni ,kawai dan anyi maka auren da baka so shine zai zama matsala ka dinga wulakanta mutane haka?maryam Kiyi hakuri nasan dole zaki ji babu dadi ko bama dan tsoro ba ki qara hakuri kamar yadda na fad'a miki bazaki taba bakinciki da auren nan ba ki barni dashi nasan yana sane zan sashi yasan aikinsa dan haka ki manta da adamcy kinji kiyi zamanki babu abinda zai sameki ga masu gadi nan bazasu ta'ba yarda wani ya shigo ba ,kinyi haquri ina tabbatar miki adamcy zai shigo komai dare ."

Cike da girmamawa tace "to! mami na gode sosai allah yasa kifi haka allah kuma ya bar min Ke mami ina sonki "nima haka maryam bye take care."yana zaune a parlour’n gidansa dake lekki phase 1 anjus avenue yana zukar sigari wayarsa ta soma ringing ya kai hannu inda ya ajiye wayoyinsa ya lalubo yana dubawa sunan sweetheart ya gani yana yawo a screen din wayar shiru yayi ya cigaba da kallon wayar yana zukar sigari gbdy yaji gabansa ya shiga faduwa dan bai san me zata fad'a masa ba idan ya dauka dan haka kiran na katsewa ya kashe wayoyinsa gabdaya ya kwanta rigingine yana kallon saman parlour'n yana cigaba da zukar sigari sai daya tashi da kwali daya sannan ahankali bacci yayi awon gaba dashi ."

Bangaren maryam kam karfe uku na dare bata runtsa ba har garin allah ya waye bata ko kifta idanunta ba balle tayi bacci yadda taga rana haka taga dare tausayin kanta ya kamata shi kuwa ata ko tunaninta bai yi ba dan babu digon tausayinta acikin zuciyarsa karfe shida daidai ya tashi ya shige bedroom dinsa ya shiga bathroom yayi wanka yayi alwala yazo ya gabatar da sallah bayan ya idar ya koma saman gado ya kwanta idanunshi na kallon saman d’akinsa cikin kankanin lokaci bacci ya daukesa ."

Karfe takwas daidai a gidan maryam tayiwa mami direba bai gama daidaita parking ba ta fito tana addua" Allah na rokeka ka kawo min sauki acikin rayuwata ka kawo min karshen wannnan damuwar "ta qarasa fada tana dafe goshinta ta tsaya a bakin kofar parlour’n tana kiran sunan maryam "maryam !! mami ta shiga kwalla mata kira da sauri ta miqe a rude ta sauko ta bude mata kofar parlour'n mami ta tura qofar ta shiga,yanayin fuskarta kawai ta kalla ta tabbatar mata ta sha kuka har gaji "ina adamcy yake ?cikin mutuwar jiki ta bud'e baki "ammm uhm baa gida ya kwana ba yanzu Ke kadai kika kwana a gidan nan ?ta gyada mata kai idanunta na kawo ruwan hawaye "ina masu gadi ?"suma tun jiya da misalin karfe goma ban sake jin motsinsu ba.”

mami bata san sanda ta fashe da kuka mai tattare da tausayinta ba ,da sauri cikin rawar murya mrym tace"dan allah mami kiyi haquri ki daina masa kuka sai wani mummunar abu ya samesa maganarta ta katse mata kukanta saboda yadda taga tashiga tashin hankali ta zubawa fuskarta ido, kawar da kanta tayi gefe tana qoqarin boye damuwarta dan hankalin mami ya kwanta kusan minti biyar kafin mami ta soma neman layin ata
Karfe goma daidai ya tashi wanka ya sake yi ya shirya cikin kananan kaya ya kunna wayoyinsa yana gama kunnawa kiran mami ya shigo.”

jiki a sanyaye ya dauka yaji tace "ni kuwa uwar data kawoka duniya ce ?wani irin tsinanne yaro ne kai ? cike da tantamar ba mahaifiyarsa bace ta kira numbersa,amman dan ta tabbatarwa kanshi sai ya cire wayar a kunnensa ya duba yaga tabbas sunanta ne sannan ya kuma karawa a lokacin da muryarta Ke cigaba da fadin"wai ni kam sa'arka ce adamcy ? ‚lallai na sakar maka da yawa kaga gadon barcina,wallahi sai na dauki tsatstsauran mataki a kanka kamar yadda yayana suka bani shawara "jin sunan yayanta kawai data ambata yasa shi dauke wayar daga kunnensa yana kiran sunan Allah “yau shi sweetheart ta kira da kalmar tsinuwa wani irin tsinanen yaro ne kai ?”ya sake maimaitawa kanshi cikin tsananin tashin hankali."

” tabbas akwai wani mummunar bala'i na daban dake son kunno kai cikin rayuwarsa ."
Yana tsaye cikin wannan tashin hankali kiran mami ya sake shigowa jiki a sanyaye ya dauka "kazo ka same yanzu yanzu ina gidan ina jiranka, sha sha kawai da bai san ciwon kanshi ba ,iska kawai iya fesarwa daga bakinsa ya kwashi wayoyinsa ya fito masu tsaronsa na ganin fitowarsa duk suka mike ya shiga mota suka fice a guje tare da jiniya cike da mutuwar jiki ya shigo parlour'n batare daya kalli inda maryam take ba dan gaba daya idanunshi na Kan mami né wacce kallo daya yayi mata yasan tana cikin tsananin damuwa amman km zuciyarsa babu digon nadamar abinda ya aikata bare tausayin maryam sai ma tarin qiyayyarta data ninku acikin zuciyarsa ."

"sweetheart ta kasa ganewa tursasa zuciyarsa da take akan yarinyar Ke sake hura wutar qiyayyarta acikin zuciyarsa ,ahankali ya samu waje ya zauan kusa da mami yana cewa "ina kwana sweetheart!dakata adamcy bana bukatar wata gaisuwarka" shiru yayi kawai yana kallonta yayinda yaji kanshi yana masa wani irin sara ,"ni zaka wa haka ko "? bai ce mata komai ba illa ya kalli inda maryam take zaune ya daka mata tsawa " ke tashi ki bar nan". ta mike da tsaye da sauri jikinta na rawa zata juya mami tace "Ke koma ki zauna " maryam ta girgiza wa mami kai hankalinta a tashe ."

"ni nace ki koma ki zauan babu inda zaki , ai ya raina ne shiyasa tunda ina masa fad'a dole ya huce akanki "no sweetheart ni ba haka nake nufi ba but at least ai.. "na rantse da girman allah idan ka sake kwana a wani gida ba gidan nan inda matarka take ba babu ni babu kai har abada kuma ko mutuwa nayi karkazo Kan gawata zan sheidawa ya'yana kowa ya sani "haba sweetheart Kiyi hakuri mana "nace kayi min laifi ne bare ka bani wani hakurin banza ?

"Ina baki hakuri ne dan kin janye maganrki "to bazan janye ,ba dai ka raina ni ba to wallahi bazaka qara jin dadina ba haka kawai ka dinga gana min azaba kana ganawa yarinyar mutane azaba, laifi ne dan ta rufa maka asiri ta aureka? "wace azaba kuma sweetheart yarinyar da babu abinda ya taba hadani daita ya qarasa maganar yana kallon maryam"ke nace ki bar nan ko ?"ta tsaya tana kallon fuska mami ya sake mata alamar ta bar gun akaro na biyu a matukar fusace ya mike tsaye "Ke kina hauka ne ina mgn kina zaune ? ya buga mata tsawa "

"babu fa inda zata karki sake ki bar wajena matsawar bani nace ba "wai sweetheart me nene haka né ?ya fad'a yana sake kallon maryam dake qoqarin komawa ta zauna yace "wallahi kika cigaba da zama a wajen nan sai na canza miki kamani"maryam ta kalli mami cikin tsananin tashin hankali tace "mami dan girman allah kiyi hakuri ki barni na bar wajena" ai kafin mami ta sake cewa wani abu tuni maryam ta bace .”mami tayi shiru ta zuba tagumi tana dubansa kawai domin ta rasa me za tayi har kusan mintuna goma sannan yace "sweetheart kinyi shiru kina kallona "me zance tunda kafi karfina ka rainani ka nuna min ban isa da kai ba ,duk lokacin da nace ga abinda zakayi bazakayi ba ,”amman wallahi bazanyi kaffara ba muddin baka cigaba da kwana a cikin gidan nan ba na rantse da girman allah babu ni babu kai har abada kuma zan cireka acikin ya'yana sai dai ka nemi wata uwar amman bani zulai ba ."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 6

"Wai meye haka ne sweetheart ?"dan  Allah ki daina fad'ar wannan maganar, karki manta nine fa d'anki wannan yarinyar kuma diyar wasu ce "  me yasa zaki dinga fad'ar  wad'an kalaman akaina?me yasa zaki min wannan hukunci ?ya fad'a cikin tsananin 'bacin rai tunda wannan hukunci kika zartar akaina ai gara ki kasheni kawai ki huta nasan bani da gata da galihu just kill me sweetheart ko  kuma  ki janye wannan hukuncin naki ." yayi maganar Kmr zai yi kuka ."

"Okay haka ma zaka fad'a ko ?ta daka masa tsawa yana qoqarin sake bude baki mami ta zuba masa lafiyayyen mari  tana cewa "kaji magana kawai sannan  kayi abinda nace kuma bazan janye kudirina ba wannan umarni ne na baka wallahi idan ka kuskura ka sa'bawa umarnina zaka ji abinda yafi haka daga bakina."

Maryam dake tsaye akan step a tun sanda ta bar wajensu   jin saukar mari  yasa da  sauri ta dafe qirjinta saboda  tashin hankalin data tsinci kanta ciki ,ta qara taku biyu idanunta ya sauka akan mami da ata dake  huci  tmkr zakuna ,wani hawaye ne masu zafi suka shiga turereniyar zubo mata ,kuka take sosai  tana datasanin kiran mami datai a daren jiya ,dan tasan da bata kirata ba da hankalinta bai tsaidu akanta ba har tayi musu diran makiya da sassafe ba ."

" wayyo allah nah ni maryam na shiga uku nah wannan duk laifina ne”. ta fad'a tana toshe bakinta da hannunwanta duka dan kar sautin kukanta ya bayyana ." cikin tsananin fushi ata yace "okay  sweetheart bazan bi umarninki akan wannan banzar yarinyar ba   "ya fad'a  atakaice yana furza da iska mai zafi daga bakinsa ."

"Naji bazaka bi umarnina ba amman kasani daga yau  babu ni babu kai  ka cigaba da rayuwarka kai kad'ai  har duniya ta nade " tana gama fad'ar  haka ta nufi hanyar step tana  kwallawa maryam  kira da karfi "maryam !!! mrym  ta qarasa saukowa da sauri  ta tsaya  cike da fad'uwar gaba  tana duban mami "d'auko  mayafinki muje "ina kuma mami ?tayi mata tambayar a matukar firgice ."

"gida mana dan bazan tafi na barki acikin  wannan gidan ba "kallon mami take cike da matsanamcin mamaki sannan ta waiga ta kalli ata dake tsaye  taga yadda yake  fidda numfashi har qirjinsa na sama da kasa wanda yake nuna tsananin tashin hankali".
cike da tashin hankali ta shiga girgiza ma mami kai  sannan ta soma magana "mami dan girman allah kiyi hakuri ki barni kiyi tafiyarki ni zan  yi  hakurin zama dashi haka ta fad'a voice dinta na rawa ".

"dan ubanki zaman me zaki cigaba dayi dashi yana  wulakantaki ?maryam tayi narai narai da idanunta tana damke hannuwanta cikin juna ,kin kuwa san babu wulakanci daya kai  miji  yaki kwana a gidan amaryarsa a daren farkonta zafi da ciwo ?"nasani mami dan ni kad'ai nasan halin damuwar dana kwana ciki jiya , tayi mgnr acikin zuciyarta tana qoqarin daidaita natsuwarta ."

"Ya wulakantanki ya tozartaki ya qunsa miki bakincikin da bazaki iya mantawa dashi ba har abada amman ki tsaya kina 'bata min lokacin" mrym ta girgiza mata kai tana mai share hawayenta "amman bake ya wulakanta ya tozarta ba ni yayiwa kuma na gode masa amman kisani bazan tafi na barki cikin wannan halin ba  dan haka ki hau sama yanzu ki d'auko mayafinki muje an gama wannan auren". mami ta fad'a cikin tsanani 'bacin rai.”

"kiyi hakuri mami duk laifina ne dana kiraki na d'aga miki hankali me yasa ma zan kiraki ? sannan me yasa zaki hukuntashi ? da  kin barshi ni ki hukuntani  mami akan abinda na aikata kina zaman zamanki na d'aga miki hankali " maryam ta fad'a hawaye na zubo mata ."you're very stupid so you're the one caused all this problems ? amman dan munafurci  kizo kinawa mutane  kukan munafurci ."

" ina zaman lafiya da mahaifiyata aurenki ya shiga tsakanina daita sannan dan kin cika mahaukaciya ballagaza kika kirata kikace ban kwana gida ba ,dan ubanki idan na kwana a gidan uban me zan miki ? "ya fad'a a fusace ".?a matukar rikice tace "please am sorry I never know she wil act like this "ta fad'a hawaye na sake zubo mata, wani irin mugun kallo ya watsa mata sannan yay qoqarin qarasowa inda take mami  na ganin haka tayi saurin  taresa da hannunta dan ta lura baya cikin  haiyacinsa "karka soma ta'ba min lafiyar yarinya mami ta fad'a muryarta na rawa bata ta'ba ganin yanayinsa haka ba ".

"Yau sai na kashe yarinyar nan da uban daya haifeta ya fad'a cikin cigaba da takowa cikin isa da 'bacin rai jin abinda ya fad'a yasa maryam rungume mami ta baya tana wani irin kuka tmkr qaramar yarinya "mami ki taimakeni dan girman allah "weetheart ki bani hanya naci ubanta na ganar daita kuskurenta wanda har abada bazata sake aikawata wani ba bare ni "ka shiga hankalinka “ita dai tashiga hankalinta “
“ adamcy banason abinda kake min dan babu laifinta ko d'aya idan hukunci ne ni dana mareka zaka hukunta."

"please sweetheart ki matsa dan babu abinda zai hanani ban hukunta wannan yarinyar ba akanta fa sweetheart kika mareni “yana qoqarin kamo  hannun maryam mami ta sake sauke masa wasu marukan ji  kake tas tass !! har biyu ajere ."wannan karon kam ata daskarewa yayi awaje d'aya yana kallon mami cike da tsananin mamaki  abun yayi mugun girgiza shi  "yau sweetheart dinsa ce tay masa mari har uku kuma duk akan wannan banzar yarinyar ".?

maryam kam fashewa tayi da wani sabon kuka ganin abinda  mami ta sake aikatawa " matsawar ka ta'ba maryam ban yafe maka ba tana gama fad'ar haka ta juya rike da hannun maryam sai dai abun mamaki mrym din taki biyota ta turje jikinta na kyamarrr , dole tasa mami ta tsaya ta juyo tare da zuba mata ido tana neman qarin bayani, amman mrym tayi shiru sai hawaye dake sauka akan kuncinta"kina ganin irin wulakanci da yayi min amman da yake ke baki da zuciya zaki ki biyoni wato ke gaki mai ..."

kafin mami ta qarasa maganrta mrym  ta zube kasa gabanta tana kuka tana bata hakuri .""Kiyi hakuri mami wallahi ba haka bane, ba kuma abinda kike nufi bane ,nayi nadama dan allah mami kiyi hakuri ki yafe masa ki daina fad'a masa kalamai haka marasa dadi ,kuma ni babu inda zan biki zan zauna a gidan mijina,da  dad'i da babu zanyi hakuri dashi "tana gama fad'ar haka ta sunkuyar da kanta kasa ganin irin kallon da mami take mata mami tayi shiru kawai tana kallonta gbdy taji kwarin gwaiwarta yayi kasa ."

Jin mami tayi shiru hankalin mrym yayi mugun tashi rawar da jikinta yake ya qaru ta d'ago kanta ahankali taga ita din mami take kallo har lokacin muryarta a sanyaye tace "kiyi hakuri mami kece fa kike bani hakuri da kwarin gwiwar da har muka kawo matakin maaurata ,to me yasa akwana d'aya kawai da nayi  a gidansa zaki d'auki zafi akansa alhalin kin fi kowa sanin waye shi ."?

nan kuma jikin mami yayi sanyi ta tsaya kawai tana cigaba kallon mrym , shi kuwa ata zuba masu ido kawai yayi yana jin zallar 'bacin rai na ratsashi  yaji tsanar mrym ya sake qaruwa da mamaye duk wani sansar jikinsa "wallahi  bancin mami dake tsakaninsu da shi kad'ai yasan irin azabar da zai gana mata amman duk da haka bata tsira ba zai ganar daita Kuskurenta ,runtse idanushi yayi yana cizan lip's dinsa  na kasa da karfi yayinda hawaye ke bin kuncin maryam , tsaki yaja sannan ya juya a fusace ya haye sama cikin tsananin fushi yake taka step ."

Yana shiga d'akin daya zamo nashi ne ya soma zariya aciki he's thinking of if someone else did what his mother did to him today da wallahi allah ne kadai zai rabasu amman sweetheart rayuwarsa ce yana matuqar qaunarta, yana son duk  wani abinda take so wajen had’in aurensa da wannan bazar yarinyar ne  kawai raayinsu ya sha bam bam tsaki yayita ja tare dafe goshinsa dan wani irin sara kanshi ya cigaba da yi ."

"Maryam ta kamo hannun mami ta zaunar daita akan kujera sannan ta durkusa kasa gabanta "kiyi hakuri mami kema fa kinsan halinsa Kmr yadda kike cewa zai canza nima haka nasa araina wata rana idan allah ya taimakemu sai kiga ya canza, nayi miki alkwarin zan zauna dashi har tsawon rayuwata sannan kiyi  min alkwarin bazaki sake kai hannunki fuskarsa ba sannan ki daina fad'ar kalamai marasa dadi akanshi nima kona kiraki karki saurareni akan kowacce matsala ki bani hakuri kamar yadda kike bawa sauran ya’yanki."

Mami ta qirgiza mata kai alamun bazata iya ba “please mami do the same thing to me “bafa zan zuba ido ba maryam ,dole nayi mgn idan ma baki fad’a min ba dole zan san komai “please!..”bafa zan zuba idanu yayi miki wulakanci daya ga dama ba domin Ke din amana ce a wajena kuma duk abinda yayi miki dole ne ya dameni ko bakya adamcy ya aura ba dole ne nasa ido a gidansa idan naga zai cutar da ‘yar mutane bare ke da kika kasance jinina "duk da haka dai mami Kiyi min alkawarin bazaki sake damun rayuwarsa akaina ba mrym ta fad'a tana sakar mata murmushin dole wanda kana kallo had'e yake da tarin damuwa.”

"Shikenan bazan sake ba “mami ta fad'a tana kukan tausayinta dana tilon d’anta data san haka auren zai kasance wallahi data hakura tun farko daya nuna baya so  ."ahankali maryam ta kai hannunta tana goge mata hawaye tana cewa "mami ki bar kuka .
zubar da hawayenki akanshi maseefa ne a gareshi "ta d'aga mata kai  kawai dan batasan me zata ce ba dan kukan ne ya fiyye mata sauki akan mgnr da zatai " daga nan mrym ta cigaba da kwantar wa mami da  hankali ."zuciyar mami tayi sanyi ta sake amanna maryam itace mace d'aya da zata kular mata da rayuwar tilon d'anta."

murya a sanyaye mami tace "tashi kije ki kirashi yazo ya bani hakuri "maryam ta zaro ido tana kallon mami a matukar firgice "wallahi mami bazan iya ba he wil beat me to the exetended sai kin koka min kina kallo fa if bancin kina nan da yanzu ba wannan labarin ake fad'a ba  ."allah bazan ta'ba iya tunkarar sa ba kawai Kiyi hakuri ki yafe masa "mami  am so much in love with your lovely son amman bani  da wannan kwarin gwiwa ." ta fad'a aranta hawaye na gangaro mata ."

hankali ta dora kanta akan cinyar mami tana zubar da hawaye ."tana matuqar sonshi and  she don't want to loose him at all, she don't know what's happening to her brain, dan tana jin idan ya saketa ko idan mami ta raba auren zata iya mutuwa for real  mami tace "kiyi hakuri mrym ki daina kuka  nasan adamcy baya sonki shiyasa kikaga  bana tuna duk wani halin da zai shiga nake yanke hukunci akanshi ta fad'a tana shafa kanta ."

"Ni kuma kinga bana son abinda kike masa " mrym ta fad'a a fili tana sheshekan kuka "baki so ?"mami ta tmbyeta ahankali tace "eh mami  bana só ina jin ciwo a zuciyata sosai  kinga sakamakon abinda kika yi yau ya qara d'aukar zafi dani tsanata ya sake qaruwa a zuciyarsa , mami ta sauke numfashi ,gbdy ta gama karantar maryam tana mugu mugun son adamcy ,ta kuma san muddin ya gano hk zaa qara samun matsala ne ."

"Nima baa son raina bane dan burina bai wuce na ganku tare cikin koshin lafiya da farinciki ba amman shi adamcy din ne zuma ne  sai ancisa da wuta "haka zamuyi hakuri dashi muyita masa addua allah ya sausauta zuciyarsa ta fad'a tana sake kwantar da kanta a cinyar mami shiru parlour'n yayi baa jin motsin komai sai na saukar numfashinsu dana ac dake aiki sai  kusan shabiyu mami   ta mike tana jaddada mata tayi qoqarin ta shawo kansa yazo anjima bata hakuri ."ta qarasa mgnr tana dariyar tsokana ."

"Dan allah mami ki rufa min asiri ina ni ina tarar aradu wannan ai sai ke "mami tayi murmushi tare da yi mata sallama ta shiga mota suka baro gidan, mami kam da direbanta ya d'aukota bai  wuce koina daita ba sai hanyar gida tana zaune abayan mota tana tunani abubuwa dayawa abinda yafi komai daga mata hankali soyayyar adamcy din data ga ya samu kyakkyawan mazauni a zuciyar maryam da kuma qiyayyar adamcy gareta tasan baqaramin wahala da qalubali zata sha   a hannunsa ba dole tana bukatar taimakonta ,dan dole kuma tasa ido arayuwar gidansu idan ba haka ba maryam bazataji dadin rayuwar aurenta ba ."

Tana cikin wannan tunanin wayarta  ya fara ringing it was nana hauwa'u  sai data sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta dauka tana cewa "auta ya kike ya gida da fatan kuna lafiya ? to ya zaman naku yake ? "To shikenan ayita hakuri wata rana sai labari okay zan kirata in sha allahu ,yanzu ma ina Kan hanyar komawa gida ne daga wajen marym nike "eh to lafiya dai ba lafiya  ba "mami ta fad'i haka cike da  raunin murya baangaren nana hauwa'u tace "lafiya mami me ya faru daga tarewa jiya jiya km ?.”

"Kinsan halin yayanki ai "me yayi mami? "wai akai masa amarya yaki kwana a gidan wallahi jiya kwana nayi cikin damuwa da tashin hankali amman nima yau nayi masa hauka dan na nuna masa ba tsoronsa nike ji ba mari uku nayi masa masu kyau  ,wallahi kuwa nasan da zarar ya sauko zai shiga hankalinsa ya dawo ban hakuri ,ku barni dashi duk zan sauke masa abinda Ke damunsa in sha allahu bazan bar duniya ba sai ya canza rayuwa ai ko da mutane suke ganin Kmr yafi karfina, ba karfina yafi ba zan haifi d’a ne nazo ina jin tsoronsa? kawai dai ina lallabashi ne sbd bana son takurawa rayuwarsa mota na tafiya suna hira da auta har ta kawo gida."

Wayarsa  ce ta fara ringing sai data katse bayan ya gama shan kamshinta ya ciro yana dubawa Hannunsa daya yasa ya rike qugunsa dashi yana takawa zuwa bakin window din dakin ya bude yana kallon haraban gidan inda masu tsaronsa ke safa da marwa magana yayi  wanda bai wuce ta minti uku ba ya katse ya soma cire kayan jikinsa ya fad'a bayi dan wani irin zafi jikinsa ya d'auka ga sarar da kanshi yake masa zama yayi acikin bathtub ruwa na sauka a sansar jikinsa "

ita kuwa maryam ta shiga d'akinta cike da faduwar gaba ta zauna abakin gadonta tana tunani ta dauki lokaci zaune tana tunani hali irin na mijinta har sai data duba taga lokacin sallar azahar tayi ta mike ahankali ta shig bathroom ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallah bayan ta kammala ta koma ta zauna a inda ta tashi ta tsurawa  tv dakin ido sai dai sam batayi shaawar kunnawa ba bare ta debe mata kewa tayi shiru tana tunanin ya kama taci wani abu dan tun abinci jiya ne  acikinta dan haka ta fara tunanin fitowa ta samawar cikin wani abu ."

Ahankali ata yake saukowa  sanye da wasu kaya , jikinsa na fidda kamshi mai sanyi dadi ya ajiye wayarsa  akan center table  ya samu waje ya zauna ya d'auki remut ya kunna tv ya qara karfin ac ya daura kafafunsa  akan table yana duban tv ,ahankali maryam ta fito daga dakinta cikin sanda kamshin turarensa ya bugi hancinta sam batayi tunanin yana parlour'n ba tafi tunanin ko yana dakin yana shirin fita  ya bar gidan ne, dan haka ta cigaba da saukowa tana saukowa tana sake jin kusancinta da kamshin turarensa mai sanyi da bugar da zuciya ta lumshe idanunta tana cigaba da daura kafafunta akan step ai tana gama saukowa kawai taga mutun zaune tmkr wanda aka dasa ."

Tsananin tsoron data tsinci kanta ciki sauran kad'an ta saki fitsari a inda take tsaye ,nunayen ajiyar zuciya da numfashi ta sauke alokacin daya ta sanyawa jikinta jarumta kana ta soma tafiya cikin sanyin jiki zata shiga kitchen, a natse ya d'ago idanunshi ya zuba mata oly eye's dinsa masu firgitar da mutun dole taja ta tsaya sakamakon idanunshi da taji suna yawo a gbdy ilahirin jikinta ta hade yatsun hannunta waje daya ta dago kanta zuwa Kan kujerar da yake zaune taga yayi mugun hade fuska tmkr zaki yana kallonta a kaskance ."

" zata iya cewa tunda tasanshi arayuwarta bata ta'ba ganin yanayinsa haka ba alama yayi mata da ido ta koma amman ta dauke kanta tayi kmr bata fahimcesa ba har tayi taku biyu taji Kmr ya mike ai da mugun gudu tayi Kan step, bata tsaya akoina ba sai a dakinta har da  rufe kofar ta tsaya tana haki da maida numfashi "bayan ta samu natsuwa kwalla ta zubo mata "bata san tana tsananin tsoronsa ba sai yanzu yaya adam baya sona gashi ni kuma ina sonshi ta fad'a a fili cike da sanyin jiki ta zauna jugun tare da dafe kuncinta ."

kusan awa daya taji motsin fitar motocinsa ta sauko da sauri sai dai  hawaye ne ya  zubo daga idanunta
Sakamakon ganin ya rufe kitchen din duk inda ta kalla acikin parlour'n babu wani abu da zata iya sakawa cikinta dole taja jikinta ta dawo daki bayi ta shiga ta dauro alwala ta gabatar da sallar laasar ta kwanta lamo a saman abun sallah yunwa na nukur kusanta sai tayi kamar ta kira mami akawo mata abinci sai tayiwa kanta fad'a ta maida wayar ta ajiye ."

wasa wasa awanni suka dinga wucewa duhu ya fara sako  kai lokacin magariba yayi a daddafe ta tashi tayi sallahr magariba ta dawo ta kwanta a haka ishai tayi wanda zuwa wannan lokacin ta fara raina kanta tuni hawaye ya fara fareti akan kuncinta tasan mugunta da kuma hukuntata yasa yayi haka tana daga kwance amman jiri take gani saboda tsananin yunwa tuni idanunta suka canza kala saboda kukan yunwa  da take bata san yunwa bata da hakuri ba sai yau hatta test din miyon bakinta ya canza ."

Ata kuwa tunda ya   fita yana wajen wani abokin kasuwancinsa  daya sauka a kasar yau din nan  sun jima suna tautaunawa akan kasuwanci shi kanshi banda coffee babu abinda yasanyawa cikinsa karfe bakwai daidai a haraban family house dinsu tayi masa, yana qoqarin fitowa daga mota yaga direban mami na fitowa daga gidanta hannuwansa duka rike da wasu hadaddun kuloli “ aransa yace “shegiyar yarinya sarkin rashi hakuri har ta kira akawo mata abincin ,ai da baki kira ba yau haka zaki kwana da yunwa nonsense girl kawai .”

massalaci dake cikin esate din ya shiga yayi sallah bai fito ba har sai daaka idar da sallah ishai ya zauna yana azkar yana nadamar abinda ya fadawa mahaifiyarsa wanda yayi haka ne cikin zafin zuciya gashi yanzu yana dayasani ."ahankali ya dinga jin rashin kyautatawar da yayi mata , nan da nan kyakkyawar zuciyarsa ta dinga umartanshi da yaje ya bawa mahaifiyarsa hakuri ya nemi tafiyarta yayinda bakar zuciyarsa ke gargadinsa har ma da bashi karfin zuciyar nisanta kanshi daita .”

wayarsa dake ringing ya katse masa tunanin da yake ya ciro yana duba wayar sunan ammar ya gani ya dauka yana cewa  "yaakayi ammar ?eh mun gama magana dashi yanzu haka ina family hausa ,ok  bani minti biyar yanzu zaka ganin a gaugauce ya fito ."
Kai tsaye  rufar da yake zama da bakinsa ya nufa inda ya iske ammar yana ganinsa ya washe baki yana cewa ango !ango !! angaishe da ango kasha kamshi"
"A ina kenan na sha ? A wajen ama... "kaga dan Allah malam ka barni naji da abinda ke damuna dan ni babu wani kamshi dana sha kuma bana saka rai zan sha shi har abada ".

“kai dai anyi mai cutar kanshi kai muguntar ma har da kanka zakayi wa ?"har kuwa karshen rayuwata zan cigaba da zama haka ban sha wannan kamshin ba ya fad'a yana zama acikin daya daga cikin kujerun dake ajiye agurin ."ai ni an gama da rayuwata an cuceni wallahi amman   I think kawai zan samu wata  in aura dan bazan iya  rayuwar aure da wannan  yarinyar  ba dan sam sam attitude dinta  is something else..." ya fadawa ammar yana jan dogon tsaki .”

"hmmm amman da kayi hakuri ka d'an sake daita kad'an  kagani  ko tafiyarku zatai daidai  "no it can be possible ammar "okay  idan haka ne  na hadaka da wata sabuwar mai bautar qasa dake karkashin kamfaninmu yarinyar tana da kirki sosai , koni bancin bani da wata matsala da salima dana  shiga sawun masu nemar aurenta  dan yarinyar akwai natsuwa  da kirki ga kamun kai .”

shuru ata yayi without saying a word."Ko baka  sonta ?.."ammar  ya tambayesa, ahankali yace
" ammar I don't really know tunda banganta ba  amman bani da zabi tunda na rasa princess zan iya manage da wata "ya qarasa  mgnr yana duban fuskar ammar" to kayi hakuri da mrym din kawai madadin ka qara da wata tunda itama wacce zaka aura din ba sonta zakayi ba manage ne ai kaga gara kawai ka dinga rage zafi da mrym kawai zai fi ga tarin ladan aure gana biyayyar mahaifiya" over my dead body ni fa I can't let the woman  I hate touch my fingers balle hannuna har azo ga jikina gaskiya ammar bazan ta'ba Iyawa ba ."

“Bama zan barta ta ta’ba ni ba bare ni na kai kaina dan rage zafi tayi zamanta haka nima nayi rayuwata haka amman batun rage zafi ma duk bai taso ba “
ATA sai hakuri fa kuma wallahi irin wannan auren ma ya fi dadi gashi da alamun mrym din ma tana sonka zakayi   yadda kakeso  daita har Allah yasa ka fara sonta  “ammar  ya fada yana dariya, da sauri ATA ya daga Kai yana cewa "me yasa kace tana sona ?ai mace idan bata son mutun da wahala ta yarda a daura aure ka duba nuzla misali ce guduwa tayi har sai byn daaka daura auren hisham da nana hauwa'u ".

“wannan ba gskiya bane , nana hauwa'u ta auri hisham ne ba dan tana son shi ba hakazalika nima na auri yarinyar nan ba dan ina sonta ba "anya kuwa wata killa fa nana hauwa’u tana son shi ta boye ne kawai dan bata damar samunsa a wannan lokacin dan hk kawai ka rike marym dinka kamar yadda hisham ya hakura da nana hauwa’u ."I can't" ya fada atakaice, dariya ammar  yayi yana cewa "Ka  bani dariya,irin ku né da anyi mistake kun kusanci matan da baku so sai ciki."duk fa zaka gama cika bakin  kiyayyar  ne ka gama zaka zo ka nemi hakinka ".

“Allah ya tsareni da ganin wannan bakar ranar "kai  dai sai idan babu rabo a tsananinka  daita  amma wallahi in da rabo komin kiyayyar dake tsakaninku sai kun jone anyi ciki "  ammar  ya fada masa hk cike da zolaya ."yanzu ya batun yarinyar da nayi maka maganarta yanzu zaka aureta na hadaku dan gsky idan dai da gaske aure zaka qara gara wannan yarinyar ?” wallahi kawai sweetheart nake tunani nasan ma da wahala ta barni “bayan  ta matsa maka ka auri zabinta sai kuma ta hanakali qarawa gsky ta barka ka qara tunda kana so .”

“Kai dai bari kawai ammar abinda nasani ko banyi acikin lokacin nan ba zanyi a gaba ko nan da  shekara goma ne sai na qara  aure "Gsky abun naka na gaske ne "kai dai ka tayani addua Allah ya bani wata  mai kyau kamar irin mace da nike so “da gudu ma kuwa zaka sameta dan wannna yarinyar da nake maka mgn akanta ta had’u sosai” ata ya girgiza kai "da wahala haduwarta ta burgeni nifa ina da test "okay kenan ya kamata ka hakura ka rungume matarka amman kuma wallahi maryama ta had’u matar manya irinku ce ".

"Maryama !"?ya furta sunan a tsanake yana duban ammar yana jin sunan na ta'ba ranshi wanda bai kamata yaji hkn akan kowa ba sai akan princess dinsa ,muryarsa a kasalance yace "sunansu daya da wannnan dolen dolalon yarinyar "wacce kuma haka ? wannan yarinyar daaka aura min mana“yayi mgnr yana jan tsaki ammar yayi murmushi yace” eh sunansu daya ko bazaka aureta bane sbd sunansu daya ?kai ban son iskanci ya kake wani tursasa ni kamar dole to bazaa aureta ba muyi abinda ya kawoka nan da nan yayi qoqarin canza mgn zuwa ta business dinsu.”

Ammar kuwa sai faman dariya yake “wallahi ata kabani dariya ” wai dolen dolalo kai ata wallahi baka da kirki nifa ina jiye maka tsoron ruftawa karkazo kana rokonmu muje maka rarrashin dolen dolalo tace sam bata san da wannan ba “wani tsaki yaja yana maka masa harara .”bai sake cewa komai ba ya mike tsaye yana cewa “ina ganin baka shiryawa kasuwanci ba “ko kafin ammar yayi magana tuni ata ya soma taku “ata tsaya mana dan allah ka dawo muyi mgn tsaki yaja ya shiga bayan mota dan tuni masu tsaranshi sun bude masa gidan baya .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.