Maradams Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: MARADAMS book 2 by Aysha A Bagudo.txt
Chapter 12 of 14
Page 22
Kwanaki hamsin kenan da ATA yasa anemo masa kwararrun masu zane wanda yayi daidai da sauran sati uku daurin auren maryama da yaya sadam acikin lokacin nan babu abinda maryama take sai zariyar zuwa AGC domin gabatar da zanenta, haka zalika ta saki jikinta sosai da yaya sadam domin ta fara cire rashin son da bata masa tana ta qoqarin dasa soyayyarsa mai karfi acikin zuciyarta ,shima kuma bangarensa yana qoqarin kyautata mata shiyasa a yanzu damuwarta ad’auketa aiki akar ka shin AGC ne .” idan kaga maryama da yaya sadam a yanzu zaka d’auka tun asali masoya ne wadan da suka d’auki tsawon lokaci suna son juna, abu d’aya ne kawai dai har yanzu yake damun zuciyar maryama shine yawon shiru da shiga tunani mai zurfi da yaya sadam din yake ko suna tare ko yana shi kad’ai ko ayita kiransa a waya baya d’auka agabanta wanda ita hakan na damunta, kuma haka nan take ji ajikinta kamar akwai wani abu dake damunsa wanda yake boye mata , tayi iyakar qoqarinta tasan meye damuwarsa amman abun ya cutura domin dai abu d’aya ne kullum yake fad’a mata babu komai al’amuran aiki ne .”
mami na zaune a had’ad’den parlour’nta na farko idanunta na kallon tv yayinda hannunta Ke rike da casbaha tana ja ahankali kira ya shigo wayarta, tasa hannu ta d’auki wayarta tana dubawa sunan d’anuwanta data gani yana yawo a screen din wayar ne yasa tayi saurin kara wayar a kunneta bakinta d’auke da sallama “wani irin mikewa mami tayi jikinta na rawa tare da furta kalma “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ,ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagisu aslili shaani kulluhu wala takilni ila nafsin d’urfata’ai “kace yau kwana biyu kenan da faruwar sakin ?ta tambayesa cikin tsananin damuwa da shiga tashin hankali “yayinda cikin tsananin fushi d’an uwanta ya cigaba da sheida mata abinda ya faru .”“wallahi Abdul ban san komai akan sakin nan ba”
ta fad’a jikinta na wani irin ‘bari haka ma zuciyarta
bayan ya katse kiran kuka mami tasa tare da jin wani kullin bakinciki ya tsaya mata a qirji yaki gaba yaki baya wayarta ta lalubo ta soma neman layukansa amman shiru bata shiga dan haka ta kira Amar nan ta samu labarin tafiya yayi zuwa hollond abun yayi mata ciwo fiyye da tunanin mai karatu ammar din ma yana tambayarta ko tana son wani abu amman tuni ta katse kiran .”
batayi sanya a gwiwa ba ta kira ya’yanta a waya ai kuwa washegari gabdayansu suka hallara a gidan cikin tsananin tashin hankali aiko mami tasa masu kuka tana kiran “adamcy zai kasheni shikenan ya zama sila shiga tsakanina da d’anuwana muna zamanmu gwanin sha’awa, kana ganinmu kasan akwai shakuwa da soyayya a tskaninmu, muna ta qoqarin had’a kanmu dana ahlimu, mun rungume juna babu kyarma muna tsananin son juna amman yau sanadiyar adamcy ran d’anuwana ya sosu yayi min abinda bai ta’ba min ba .Abdul ra’uf bai ta’ba min magana cikin fushi ko ‘bacin rai ba sai a jiya “ni zulai na shiga uku nah me yasa na had’a auren nan ?”wallahi dana san abinda zai biyo baya kenan da ban had’a ba dana bar adamcy ya cigaba da rayuwarsa haka babu aure dan duk abinda zai lalata zumuncina da yan’uwana bana qaunarsa”.”
“kiyi hakuri mami ki daina kuka haka Allah ya qaddara kowani bawa da kalar qaddararsa wannna rabon dake tsakaninsu fa idan baa yi auren ba ta ina zaa samu ?inji cewar aunty shahida ,”kuka fa ya zamammin dole abdul’rauf na min biyayya duk abinda nace shi yake yi bai ta’ba sa’bawa umarnina ba "wai mami zaginki yayi ne ko me ?zabiba ta tambayeta “ko d’aya zabiba abdul bazai ta’ba zagina ba amman yayi min magana cikin fushi abinda bai ta’ba min ba sai jiya” nifa na kasa gane abubuwan nan na yaya adam mutun kamar babu tausayi a cikin zuciyarsa gsky mami yakamata ki san yadda za'ayi da yaya ga ciki ga saki dame sister zataji wallahi ni tausayi take ba ya dawo daita kawai .”nana hauwa’u ta qarasa mgnr tana sheshekan kuka aunty shahida ta numfasa kana tace “karki d’aga hankalinki auta kinga kema bake kad’ai bace za'a haukatar dashi bari ya dawo daga hollond lafiya amman dan dolensa ya maidaita ta haihu a gidansa idan ba haka ba wallahi wannan karon zai had’u da tashin hankali da bai ta’ba gani ba “ku dai bi komai a hankali domin dai acikinku babu wanda bai san waye yaya adam ba kusan yafi buqatar rarrashi da lalama muddin da tashin hankali zakuje masa wallahi bazai maku abinda kuke so ba .”
“da mamaki aunty khadija ta kalleta “abinda muke so kuma ke banda ke ?”gsky banda ni abinda kuke so am sorry to say dani yanzu bazan sake goyawa zaman aurensu baya ba ,ya kamata zuwa yanzu abarsu haka kada a takura masa ku kyalesa ya huta idan yayi ra’ayin maidaita da kanshi zai yi idan kuma iyakar zamansu kenan Allah yasa ya zama alkhairi ,sun d’auki lokaci suna tautaunawa a tsakaninsu sai dai zabiba ta tsaya akan raayinta wanda bai yi masu ba har mami .”
Bayan kwana uku ahankali oga ATA yake saukowa daga cikin jirki tare da yaransa mutu biyu kai tsaye in da driver da masu tsaronsa ke jiranshi suka nufa, ya qara kyau aciki kwanaki uku kacal farinsa ya sake fitowa ga cigaba da ya samu da nasarori akan business ,yana sanye da royal blue three piece suit daya daga cikin yarasa na sak'ale da bak'ar jakarsa daka ganshi kaga wayayye wanda yasan duniya ko nace duniya ke damawa dashi, yayinda idan ka kalleshi zaka d'auka d'an shekara talatin da biyar ne amma gaskiyar lamari shekararsa arba'in da wani abu yake, da sauri aka bude masa gidan baya ya shiga ya kame yana shan kamshi daya daga cikin wayoyin ne ta soma ringin ya dauka ya soma magana a natse yana ciccin magani har suka qaraso unguwarsu waya yake bai ji komai ajikinsa ba sai da suka shiga cikin haraban estate dinsu yaji gabanshi ya fad'i sakamakon bai san abinda zai tarar ba amman a kudurtawa ransa komai zai faru sai dai ya faru amman har abada bazai qara zama da mrym ba".
ahankali ya fito daga cikin motar ya nufi babban falon cikin isa da iza ga kamshin daddan turarensa Reed na tashi ,yasa hannu ya tura kofar glass din parlour’n ya shiga ya iske mami zaune kamar koda yaushe yayi sallama aciki fuskarsa a had’e tamkar zaki , itama aciki ta amsa masa ya ta’be baki yadda ta amsa masa yaso ya bashi dry amman sai ya maze ya d’age girarsa duka tare da dakewa ya gaisheta “sweetheart barka da rana “wannan karon kam shiru tayi bata masa ba bai qara cewa komai ba kai tsaye samansa ya nufa mami ta karkace tabi bayansa da kallo yana taku d’ay d’ay batare da wata damuwa ko tashin hankali ba sai ma wani kyau da kwanciyar hankali daya samu matsuguni ajikinsa su kuma ya bar zuciyarsu da tashin hankali.duk wani tarba da rawar jiki da mami take akanshi idan ta gansa yau kam babu dan kana kallon fuskarta zaka fahimci akwai damuwa .”yadda mami bata masa maganar wata maryam ba shima bai yi mata maganar ba abun ma yayi masa dadi ya cigaba da tsabgogin gabansa da mulkinsa daya saba dan babu abinda ya canja har kawo yanzu dan ji yayi kamar an raba zuciyarsa da matsala ne dan da kullum zuciyarsa cikin tuttukin bakinciki da kunci take idan ya tuna zai koma gida ya ga fuskarta kuma amatsayin matarsa .”
mami dai bata gaji ba ta sake tara ya’yanta “har yanzu shiru adamcy bai ce min komai ba ga mrym da ciki har wata uku akace dame zataji saboda Allah ga ciki ga kuma gurb'ata mata raywua da yayi, gashi ya dawo yayi wa mutane shiru kamar bashi yayi sakin ba , ni na gaji wallahi nayi waya daita mrym din ta fad’a min abinda ya faru akayi sakin taki sai kuka take min ,shi kuma ya dawo ya min dif wallahi na kasa komai gashi bana son lokaci ya tafi batare data koma dakinta ba dan da zarar mrym ta haihu a gidansu shikenan abu ya sake dawowa baya bazai ta’ba maidaita ba mami ta fad'a tana kallon ya’yanta d’aya byn d’aya da suke zaune.aunty khadija tace "kwantar da hankalin ki mami zamu san abun yi bubuwa daya ne kawai ya tabbata a aurensu samun cikin mrym in sha allahu sauran ma zasu tabbata ne"Yaushe? Kusan shekaru ana abu d'aya ace har yanzu an kasa cimma komai babu wanda adam yake shaka daga mami har mu na gaba dashi kowa shakkarsa yake gsky zuwa yanzu dai ya kamata mu tashi tsaye .”inji cewar aunty shahida .”
kallonsu kawai mami take zuciyar na karye wa “zaku cimma daman amman dole sai kunyi hak'uri sannan ku bisa ahankali dan karku dinga mgn kuna manta waye shi b'angaren zafin kai da zuciya dole sai kun sha wahala kafin ku samu ku ya sauko ya saurareku ni wallahi dan tani da an bar kome nan kowa ya huta “wai meye haka zabiba?” sai ki dimga magana kina cire kanki acikinmu idan Kinsan bazaki goya wa mami baya ba me yasa kika zo ?Inji cewar aunty Khadijat “to yanzu me nayi kuma ?ai bazan ki zuwan kiran mahaifiyata ba haka zalika bazan goyi da bayan a sake tursasa wa yaya ba “haba Auty zabiba ya kike magana kamar babu tausayi a zuciyarki ?karki manta kema fa mace ce inji cewar nana hauwa’u “hk ne nima mace ce amman da zaku fahimceni ma gata nayi mata dan banga amfani aure da wulakanci ba shi yace bayayi ita tace tana yi ita Ke aure ko shi ?“dan allah yasa isa karki sake saka baki tashi ma ki wuce an sallameki nan da nan parlour’n ya hargitse sai da mami ta tsawatar masu sannan sukai shiru suna cika suna batsewa “wannan wani iri bala’i ne adamcy duk ya dagula min lissafi ya hadani da dan’uwana yanzu kuma zai raba min kan ya’ya .” a zuciyar zabiba tace “babu ruwan yaya duk kece kika dagula lissafin komai .”
Bayan kwana biyu wanda ya kasance weekend tun karfe tara suka hallara da niyyar ayita ta qare ahankali yake saukowa daga saman mattakala jikinsa sanye da farin yadi inda kafafunsa ke sanye da farin silifas , agogon rolex ke daure da tsintsiyar hannunsa ,idanunshi na manne da wani hadadden farin glass ,a hankali ya cigaba da takowa cikin isa da izza shi din wani ne a fadin nigeria ,yana saukowa sanyayen kamshin turarensa REED ya soma tashi kamshin turarensa ne ya kaiwa hancinsu sakon fitowarsa . gabad’ayasu suka dago idanuwansu a natse suka tsura masa suna kallonsa tamkar ranar suka soma ganinsa shi kuwa ko kallo su bai yi ba hasalima yi yayi kamar bai ga wasu halitta a wajen ba .kai tsaye dinning área ya nufa yana shan kamshi , har ya samu guri ya tsaya tare da soke hannunsa daya cikin aljihun wondonsa ,basu dauke kwayar idanunsu akanshi ba ,gabdayansu an rasa wanda zai fara masa magana shi ya kamata yayi gaisuwa amman yaki “aunty khadija ta zunguri aunty shahida ta kalleta “gashi ya fito ya kenan ?
“Da alamun abinci zai ci bari ya gama ya samu waje ya zauna ya had’a coffee ya fara sha yana lumshe idanu su kuwa sai faman satar kallonsa suke ba qaramin kyau yayi musu ba cikin shigar da yayi ko dan bai fiyye saka kayan hausa bane yasa yayi masa kyau haka yunwa yake ji sosai amman ya kasa zuba ma kanshi abinci dan haka ya ja dogon tsaki mami ta fito sanye da doguwar rigar atamfa itama tayi kyau sosai ga tsufa ga tarin damuwa amman dake jikinta mai kyau ne wallahi bazakace tana da diya mai shekara 49 a duniya ba dauke kallonsa tayi ta girgiza kai kawai sannan ta zauna acikin ya’yanta .
zabiba ce ta fahimci abinda yake buqata dan haka ta mike a natse ta qarasa inda yake “ina kwana yaya ?lafiya !ya fad’a aciki batare da bata lokaci ba tayi serving dinsa ta ajiye masa plet din abinci gabansa. a hankali ya dauki cup ya kai bakinsa ya kurbi tea yana lumshe sexy eyes dinsa yana sosa keyarsa .”
Ahankali aunty shahida da aunty khadija suka mike suka nufi inda yake hajiya zualai tabi su da kallo gabanta na wani irin faduwa nana hauwa’u ta riko tafin hannunta “mami ki kwantar da hankalinki kiyi addua cike da sanyin jiki take duban kyakkya wan fuskarsa ya hade fuskarsa sosai ta yadda idan ba jarumta kayi ba bazaka iya fuskantar sa ba “karki damu mami everything will be fine “Allah yasa auta allah ya sanyaya zuciyarsa dan mrym na bani tausayi ina jin duk nice silar shigarta cikin damuwar nan nana hauwa’u ta damke hanunta sosai cikin nata tana danne kukanta dan itama mrym na bata tausayi tun shekaranjiya da sukai waya bata qara daukar wayarta ba saboda qara mata damuwa take .”a tare suka zauna suna fuskantar shi tun daya gansu ya fahimci abinda Ke tafe dasu kusan minti shabiyar suna zaune yaki daina cin abinci yasa ahankali aunty shahida ta soma magana “adamcy me yasa ka saki maryam ?”laifin me tayi maka ka saketa alhalin ga mami a raye baka sanar daita ba ka yanke hukunci kai tsaye ?”.
“bani ya kamata ki tmya ba ita da tace an saketa me tayi ?kuje ku tmbyeta abinda tayi aka saketa “nan da nan ran aunty khadija ya baci “wannan wace irin maganar banza ce ?”ta fad’a a fusace “ai mun san daita muka zo tmbyrka mara mutunci kawai so kake ka kashe mana uwa ka barmu da asara dan tuni mun kula baka da buri sai na ganin kasa mahaifiyar mu cikin bakinciki,to wallahi kasani zamanka da marym dole ne dan shi kadai zai sanyaya ran kowa acikin gidannan ,wallahi sam baka ma mami adalci ba kai kadai gareta amman kullum cikin sakata hawaye kake, kamata yayi ka dinga share mata hawaye amman tun baka kai haka ba kake sakata cikin damuwa.jin haka yasa mami ta share hawayenta . ta inda take shiga bata nan take fita ba sai zazzaga masa ruwan bala’i take shi kansa yayi mamaki maganganunta amman yayi shiru yana sauroronta yana tsakurar abincin gabansa batare da ya furta komai ba “.
“To kasani idan ka saki maryam dan ka yar da kwallon mangaro ka huta da kuda kasani kayi aikin banza dan ciki ne daita na wata uku kaga kayi aikin banza duk kinka daita kun zama abu daya “What ?” ya furta da mugun karfi yana sakin spoon din hannunsa “eh !yanzu haka jininka na can a jininta yana yawo idanunshi ya tsura mata yana nazari kafin ahankali ya mike tsaye yana girgiza mata kai
dukkansu kallonsa sukeyi yadda jikinsa ke rawa kamar anjona masa shocking , nan da nan idansa yayi wani irin canzawa " impossible! waitt,hw can dis even b possible ?tana dauke da cikina na wata uku alhalin ni duka wata guda kenan da sati biyu dana kusanceta”to kaga dole dai cikin dake jikinta naka ne, a ina aka tabayin haka? ya fad’a a fusace taya za'ayi cikin jikinta ya zama nawa “?gbdy hankalinsu ya tashi har mami wacce batasan sanda ta qaraso inda suke ba tana dubansa “bamu gane nufinka ba ?ko dai ka sha wani abu ne ?babu abinda na sha garas nike amman wallahi cikin jikinta ba nawa bane cikin wani kato ne a jikinta kuje ku tambayeta uban da yayi mata ciki wata uku .”
da wani uban murya mami tace" kalleni adamcy ka san da wacce kake magana ka kuma dinga tauna min mgn kafinka sakosu, niba tsohohuwar banza bace, kai har ka isa kace cikin wani kato ne a jikin maryam dan ubanka ai kaine katon kenan tunda kai kamata cikin dan iska yaron kawai “.mami ta fad’a tana hawaye domin karo na farko kenan da ta furta masa wannan kalmar garesa. hakan yasa ta fashe da wani sabon kuka jin kalamn da ida wani ne ya jifesa dashi Allah kawai zai rabata dashi amman gashi itace da kanta ta furta masa haka gbdyn suka rikice sai suka dawo bawa mami hakuri ,ya isa haka mami don Allah karki sake zaginsa suka fada suna wani irin kuka mai tsuma rai “ku daina bani hakuri shi zaku bawa hakuri abinda mami take fad’a kenan "yanzu bayan ya sake nayi shiru yanzu har da cikin jikinta zai yi rejecting yanzu adamcy ka kyautawa
danka ?d’a daya tak tilo, daza fara samu a duniya zakayi wa haka .da wanne mrym zata ji da sakin daka mata ga sharri”. sweetheart trust ur son wIhh wannan cikin ba nawa bane ni ban mata ciki ba, nana hauwa’u ta goge hawayenta “Kace bakai kayi mata ciki ba “? Ki lissafa sweetheart ranar da kika bani umarni zuwa wajenta yau kwanaki nawa ne ?mami tayi shiru tana lissafi byn Kmr second biyu ta d’ago tana dubansa tabbas baayi wata uku ba to meke faruwa ?”
“Sweetheart idan kin gama lissafi ku san yadda zakuyi daita domin mazinaciya kika aura min baki sani ba yana gama fad’ar haka ya juya da nufin fita daga parlour’n da sauri nana hauwa’u ta tareshi tana kallonsa fuskarta da tsananin damuwa karara ya dago yana kallon idanunta itama shi take kallo eyes to eyes muryarta cike da kuka tace “wallahi yaya mrym ba mazinaciya bace cikin jikinta naka ne jininka ne acikinta “ni babu wani jinina dake yawo ajikinta dan ban mata ciki ba and wIh wlh idan kuna yi dan na maidaita ne bazan maida auren nan ba na gama zama daita kenan “naji yaya amman ka yarda ni cikinka ne hannunsa ya d’aga zai sauke mata mari yaji an rike hannunsa ta baya .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 23
A matuqar fusace ya juya bayansa yaya hisham ya gani tsaye cikin kananan kaya fuskarsa dauke da murmushi ,a natse ya sakar masa hannu yana cewa "ranka shi dade babban yaya laifin me auta tayi haka ?" maganarsa cikin sanyi rai yayi wanda yasa nana hauwa'u ta fashe da wani rikitaccen kuka, ina ma yayanta zai kasance kamar mijinta mai sanyi hali da tausayi tare da shagwaba mace da kyautata wa ?bata san tayi sa'ar samun miji ba sai da komai ya daidaita a tsakninsu tasan wa take aure ,kuka take sosai tana kiran "wallahi yaya cikin jikin maryam naka ne, ni sheida ce tana gama fad'ar
haka durkushe a gabansa tana zayyane masa komai daya faru tun daga farko. a matuqar tsorace yake kallonta "take kwakwaluwarsa ta shiga caji na tunani babu abinda yazo zuciyarsa sai maganar doctor nasir akan ciwon kan da yake fama dashi wanda yayi tunanin duniya ya rasa a inda ya sha maganin da yayi masa illa "shi kam wasu irin yan'uwa allah ya bashi masu son kansu dayawa ?"laifin me yayi masu ?duk wani bala'i da yan' uwana ake had'a baki."yadda taga yanayinsa ya canza har tana iya hango yadda jijiyon kanshi sukai rud'u rud'u yasa ta zabura ta mike tsaye gabanta na wani irin fad'u wa da matsanancin karfin gaske ."
ya tsura mata ido ya balain canza mata daga yanayin farko ganin ya fara taku zuwa inda take ta fara yin baya yana biyota kafin ya qarasa inda take yaya hisham ya shiga tsakaninsu yasa hannuwansa duka ya qare matarsa yana bashi hakuri ,yaya hisham bai san ya'akyi ba sai gani yayi ATA ya fixgota da karfi zai buga bayanta da bango a matuqar agigice ya rungume matarsa yana cewa "kayi hakuri tayi laifi amman dan girman allah ka yafe mata ,idan ba cikin jikinta ba wallahi zan barka ka yi mata duk irin hukuncin da kake so amamn kayi hakuri ciki ne ajikinta ."sai lokacin idanunshi ya kai ga cikin jikinta wanda har ya fara nuna alama ,saurin sakar mata hannu yayi yana dungule hannunsa yannayin bugun zuciyarsa bai saisaita ba, yannayin tsoratarsa kuwa sai ya baka mamaki gabad'aya tsigar jikinsa suka mike "ciki hisham yayi mata ?ya tamabyi kansa yana mai furzar da iska mai zafi jiki a sanyaye ya yake dubanta cike da tsananin fushi yana sauke numfashi da karfi dan bancin zuwan hisham wallahi da wata killa ba wannna zance ake yi ba."
ahankali take cigaba da rera kuka Kiyi shirunki baby yayanmu zai miki afuwa ."cikin kaukausar murya ATA ya soma tashi acikin parlour'n "ba ciki ba idan duniyar nan gbdy zata haifa min ku saka aranku ni adam tariq abdullah bana só ba kuma na bukata gabadayansu suka kallesa cikin tsananin tashin hankali aunty shahida zatai magana ya d'aga mata hannu "wlhh yadda bana só auren nan ba zai yiwu na karbi komai daga gareta ba, sai abu na gaba kafin na saketa nayi tunanin qarasa rayuqata daita amman na kamata da abu mafi muni wanda nasan bazata ta'ba sheida maku laifin da tayi ba abinda yasa na saketa kamata nayi dumu dumu da tukunyar tsafi zata saka min akarkashin gadona "hakika Mahaifiyata bata cutar dani ba kamar yadda auta ta cutar dani domin cikin nan an samesa kafin umarnin mami if not haka zamu rabu daita zero amman koma menene ni dai banaso sai dai idan ku ku zama ubansa amamn bani ba idan kuma akace zaa tursasa ni na rantse da girman Allah ran kowa zai yi mummunar baci yadda mami ke kallonsa a tsorace haka sauran yan'uwansa ke binsa da kallo zukatansu na rawa dan bakinsu ya mutu da girman laifin mrym yana gama fada ya haye sama ya barsu cikin jimami da tashin hankali ."
Wani irin naunayen ajiyar zuciya suka sauke kafin ahankali yaya hisham ya zaunar da nana hauwa'u akan kujera ya zauna kusa daita yana rarrashinta d'aya bayan d'aya suka samu waje suka zauna duk jikinsu a sanyaye yayinda zuciayarsu ke cike da mamaki mami kam kasa cewa komai tayi domin daman ita ta d'an yi zargin wani abu akan haka sai dai taki yarda zuciyarta ta amince da hakan "mai yasa marym ?"me yasa zaki min haka ?duk qoqarina baki gani ?ta furta acikin zuciyarta "yaya hisham dake rike da yatsun hannun nana hauwa'u ya sakar mata hannu yana gaishe da mami numfashi ta sauke tana amsawa "mami karki d'aga hankalinki dan kin rigada kinsan halinsa ,kubishi ahankali har zuwa sanda zai sauko zai amsa ai mutun bazai ki jininsa ba "hisham ina jin tsoron zuciyar adamcy idan yace bai son abu to kamai zai faru sai dai ya faru ni yanzu ba sakin yafi damuna ba kmar yadda yace bai son cikin jikin maryam" ko yaso ko kar yaso jininsa ne abinda Ke cikin kuma dole ya amsa sunansa addua kawai zaa cigaba da yi masa Allah ya sanyaya masa zuciyarsa yana gama fad'ar ya tashi yana ma nana hauwa'u magana kasa kasa ."
Bayan fitar yaya hisham "ya'yan mami suka sakata a tsakiya "yanzu mami ya zaayi ?ya kuwa zaayi banda hakuri kowa ya kawo ido ya saka masa Allah ya kawo masa sauki ,zan kira Abdul rauf nayi masa bayani "allah yasa ya fahimceki " inji cewar aunty shahida to "ameen zai fahimceni in sha allahu "basu wani zauna ba kowace ta d'auki gyalenta da jakarta ta yafa atare sukai wa mami sallama suka fito kowacce ta shige motarta nana hauwa'u ce kawia ta saura tsaye tana kiran layin mijinta tana tsaye yayi parking tare da fitowa ya karbo jakar hannunta ya bud'e mata gaban mota ta shiga ta zauna tare da cewa "na gode zumana !"ya maida murfin mota ya rufe ya zagaya ya shiga mazaunin direba suka kama hanya gida ."yana tuki ya dan kalleta "baby me yasa kuka aikatawa ATA haka ?tayi shiru "kisani kunyi kuskuren aikata amman dai Allah ya kawo saukin wannna tashin hankali numfashi ta sauke tare cewa "amen ! ta kamo hannunta d'aya cikin nata tana massaging tun nan ya fara jin wani iri ajikinsa wanda ita ba wai tayi da wata manufa bane .
suna isa gidan d'akita suka shiga ya cire rigarsa ya ajiye sannan ya janyota ta fad'o jikinsa tare da ciremata mayafi sannan yace "habibty na yau dai baza'a hanani na shoshale ba koh" nok'e kanta tai cikin k'irjinsa sannan ta fara magana cikin shagwab'arta wacca take k'ara birgeshi take kuma k'ara sakashi ya rikice tace "kai yayana gaskiya ni yanzu agajiye nike kuma kasan fa kayiwa doctor alkawarin zaka dinga d'aga min kafa na kwana biyu biyu har cikin nan yayi kwari sosai "ai da kin daku yau a wajen wannan yayan naki da kin gane agajiye kike "tasa dariya tana sake makalewa ajikinsa tare da d'an cizon qirjinsa da" ai tunda naganka nasan bazan daku ba " tak'arasa maganar tana matsa kan nipples dinshi, "aaashhh....!!!" yai y'ar k'ara sannan
ya kalleta da sexy eye's nashi da ya dan fara canzawa
yace baby ni dana taimaki zaki ciza zaki " dariya tai sannan tace "ai kai naka yafi zafi sosai wannan ai ba zafi" wani kallo ya mata "ok ba zafi koh toh bara na maki kiji idan ba zafi" nan ya juyata ya maidata k'asa sannan ya fara kiciniyar rabata da rigar dake jikinta ganin da gaske yake kuma tasan halinsa ta fara kuka tana neman tuba bai saurara mata ba sai daya sucking brest dinta son ranshi sannan ya barta.”
Batun sakin maryam ya bazu acikin abdullahi estate masu murna nayi ,masu bakinciki nayi aunty abida kam tafi kowa murna faruwar wannna sakin dan lokacin da taji har wani tsalle da rawa tayi a bangarenta batare da kid’a ba tana cewa “shikenan nan sultana zaki dawo a saa, kece zaki maye gurbin kowace mace a wajen adamcy ,inganga inganga !!rawa tayi sosai tamkr wata zararriya a qarshe ta suri wayarta ta shiga neman layin mahaifiyarta sun d’auki mintuna talatin suna waya sannna sukai sallama ta kira sultana tana d’auka tace “wai zaman me kike yi ne har yanzu ?” Kiyi qoqari ki dawo dama biyu ta samemu ya saki matarsa ga kuma neman masu kwararrun zane da yake nasan yana ganin zanen Kanwata zai rud’e daga nan kuma shinkenan “okay to shikenan dan girman allah ki ajiye komai ki dawo kar murasa damarmu okay bye ta katse kiran tana cigaba da rawa yesmin ta fito daga dakinta tana kallonta murmushi ta sakar mata tana cewa “yesmin kin kusan zama cikakkiyar ‘ya a wajen babanki AD “‘ya kuma mum ?yes auntynki sultana zai aura ta qarasa maganar tana rungumeta“.tsabar murna washegari aunty abinda ta shirya walima gabdaya estate din babu wanda bata aikawa da snks da drink ba duk wanda ya kalleta zai fahimci tana cikin murna .”
nan da nan zance ya kai kunnen mami babu abinda tace face “allah ya shiryeta domin duk mace mai hankali bazatayi murna dan an saki yaruwarta mace ba ita yanzu bazata sake matsawa adamcy ba amman kullum cikin yi masa addua take idan da rabo allah ya daidaita su. .allah sarki maryam ta dad'e kwance akan gado tana sak'e-sak'e a ranta, dan ta ji zafin abinda aunty abida tayi ,tsaki taja tare da mik'ewa tsaye tana d'an zagaya d'akin "dole ne na nuna ma
abida kuskurenta,zan nuna mata baa kishi da irin mu yaran zamani, tunda na lura shiru baya mata sosai abinda aunty abida tayi ya 6ata ma maryam rai, zan nuna mata iskancinta wasa ne wannan karon a bayyane tayi maganar tana wani shu'umin murmishi.”
*********
Zaune yaya sadam yake a haraban gidansu akan daya daga cikin kujerun dashi ne ya ajiyesu saboda abokansa domin zama yana sanye cikin farin yadi idanunshi manne da farin glass idanunshi kar akan wayarsa yana karanta sakon Nadia a natse ta fito zuwa garesa ahankali ya soma ganin tahowarwata ta kasan idanu shi cikin tafiya ta Kamala sanye cikin doguwar riga yellow ya dago kanshi ya tsura mata ido tana kyau sosai dan maza zai had’ata da nadia ba har ta gama qarasowa garesa fuskarta dauke da murmushin farincikin ganinsa tace "sannu yaya dan allah kayi hakuri na barka zaune ka kadai“
murmushi ya sakar mata tare da lumshe mata idanunshi "karki damu ko zan kwana ina jiranki bazan gaji ba sauraniyar kyawawan mata duniya kuma zabin umma nan ki zauna ya nuna mata kusa dashi ta zauna a natse tana kallonsa cike da jin kunyarsa "ina yini ya aiki da fatan komai Lfy ?tayi masa tmbyr a jere tana sunkuyar da kanta kasa tare da kamo yatsun hannunta tana wasa dashi "maryama duk Alhamdulillah mun godewa allah ya mumcy take ?ta gyda masa kai kawai alamun lafiya a hankali ya soma janta da hira sai dai bata wani mgn daga uhm sai uhm take cewa "maryama ! Ya kira sunanta ta dago a natse ta kallesa na second daya ta sake maida kanta ta sunkuyar "ga dukkanin alamun kamar agajeye kike ? Tai murmushi batare data dago ba "nan da sati uku zaki kasance a gidana a yanzu nake jin na matsu naga kin kasance a gidana” ajiyar zuciya mai karfi ta sauke tana dago kanta ta tsura masa idanunta "ta so ya kurewar tamvayarta aikin da take fita nema kullum amman sai ya wani kawo mata maganar aure .”
ta fahimcesa sosai shi mutun ne da bai da caring me taci ko me tayi ko a wani hali take duk ba damuwarsa bace idan ma yazo gurinta ba wani hirar soyayya yake mata ba wanda zai dauki hankalinta zai kama gabansa shiyasa duk tsawon lokacin da mahaifiyarsa ta hadasu bata ta'ba jin komai akansa ba sai dai tana danne komai saboda mahaifiyarta da mahaifiyarsa .”yana ganin girman mahaifiyarta sosai yana kula dasu sosai tun kafin a had’asu aure "kinyi shiru kina kallona kice wani abu mana ?shiru ne dai Ya sake biyosa baya har sanda wayarsa ta dauki qara sauti Ya dauki wayarsa dake ajiye a gefensa ya duba sunan nadia ya gani yana yawo a screen din wayar cike da firgic ya dubi inda maryama take sannan ya sake maida idanunshi akan wayar da kyar ya sauke naunayen ajiyar zuciya yayi disconnecting din kiran ya cigaba da magana " a she dai ni ne wanda zanyi wuf da wannna kyakkyawar yarinyar magana yake amman zuciyar maryama ta kasa samun natsuwar allah sarki yusif ashe Ke din ba rabonsa bace ?naunayen ajiyar zuciya ta sauke “kina da kyau sosai na godewa ummah datayi tunanin hadani dake na gaji da ganinmu haka ina son na killaceki a gidana "kana son ka killaceni agidan cike da rashin yanci ba ?tayi masa tmbyr a zuciyarta .”
“maganar da nake miki yanzu haka komai da zan saka agidanmu ya kammala zamu yi rayuwa mai dadi ko kina son na ajiyeki a wajen umma ne saboda yanayin aikina.”? yana gama fadar haka Ya mike sakamakon wayarsa data sake daukar qara "excuse me! ya kamata ace kana duba yanayina yaya sadam har yanzu ban ji amincewarka akan aikina ba zaka yarda na cigaba da yiwa kafanunka zane ko kuwa ?.”“bana son sai bayan munyi aure kace bakasan da zance ba wannan aikin rayuwata ce kuma ina son ya kai ni matakin da ya zarta yadda nake a yanzu babban burina bai wuce na samu aiki kafanin AGC ba .taí shiru tana jiran taji mai zai ce amman yayi mata shiru saboda raayinsa amman dole yanzu kam ya amince dan yasan idan yaki amincewa zai ta’ba zuciyar ummansa ya tsura mata ido yana nazarinta a yanayinta zata iya komai akan aikinta ." ta mike a natse tana dubansa "kayi shiru yaya sadam kace wani abu mu kawo qarshen maganarmu banason muyi aure daga baya muzo muna samun matsala akan aikina "ka amince zaka aureni da aikina sannan zaka min hanya naga mai kafanin AGC ? ta fad’a hk sbd tasan su yusif nada hanya da karfin iko shiru yayi yaki cewa komai yana sauke numfashi da kyar, domin kuwa abu biyu né suka hade masa guri daya ga tambayar maryama ga kiran da nadia ta damesa dashi wanda baya jin zai iya duka abu biyu din ."
“Ina duba yanayi na zaman takewar aurene yaya sadam domin kuwa kai kana cikin mutanen da suka san koni wacce irin rayuwar gidanmu mahaifiyata da mahaifina taí mgnr tmkr zatai zubar da hawaye dan gbdy idanunta har sun canza kala daga fari zuwa yellow "ya kamata mu tsara komai yaya sadam domin kuwa banason damuwa arayuwar aurena ta qarasa mgnr tare da kai yatsun hannunta biyu ta dauke hawayen dake kokarin saukowa kuncinta ".
numfashi ya sauke da karfi sannan yace "shikenan zakiyi aikinki “bari naje ana nema zamuyi waya ya fada yana kokarin barinta tsaye tare da manna waya a kunnensa ya nufi kofar fita taí shiru tsaye tana duban bayansa "yanzu irin wannan mijin zata aura tai rayuwar aure dashi ?anya kuwa idan ta auresa zata ji dadin rayuwar aure kuwa yadda yake da rashin nuna caring ?” yanzu a halin da take ciki kowa Ya ganta yasan tana cikin damuwa dan gbdy komai nata Ya canza amman kalli yadda ya bar gabanta batare da Ya tsaya ya fahimci matsalarta ba bare ya kawo mata mafuta oh allah karkasa nayi Kuskuren aure irin wanda Mahaifiyata tayi ya allah ka taimakeni kasa ya canza duk da banason shi saboda rashin caring dinsa dan kusan matan duniya shine matsalarsu a gidajen mazajensu a yanzu, cike da sanyin jiki har ya bacewa ganinta tana tsaye a wurin rungume da hannunwanta a kirji jiki a sanyaye ta nufi kofar part dinsu ."
*******
motarsa na shigowa haraban ma'aikatan yaji gabansa yayi wani mummunar faduwa da karfin gaske shiru yaki fitowa daga cikin motar yana tunanin abinda yasa yaji hk byn tun a gida bai tsinci kansa cikin wannan yanayi ba sai daya shigo ma'aikatan iskar ya furzar ya daga kafadunsa alamun babu komai a hankali ya zuro kafafunsa dan tuni an bude masa kofar mota ya fito yana gyara zaman suit din jikinsa sannan ya soma taku a hankali qirjinsa na cigaba da luguden bugu yayi qoqarin kawar da yanayin da gangar jikinsa ya shiga ta hanyar tura hannusa daya cikin aljihun wondonsa." duk inda ya wulga maaikata ne Ke kokarin kawo gaisuwa sai dai kai kawai yake gyada wasu ,wasu kuma yayi masu banza har ya hau lift da zai kaisa sama na uku inda anan office dinsa yake yana sauka yaji wani sabon faduwar gaba wanda ya rasa dalili nan ya dan rage tafiyar da yake ya dawo yana daga kafafunsa da kyar saboda sanyin daya ziyarcesu alokacin daya tun daga nesa ya hango bayan wata yarinya suna magana da wasu daga cikin maaikata kamar ya tsaya sai kuma ya karya kwanan da zata kaisa office dinsa cak yaja ya tsaya sakamakon jiyo sautin muryar yarinyar shiru yayi yana cigaba da saurara maganarta tamkar dai mafarkin da daya saba yi “anya kuwa muryar tace ko dai mafarkin daya saba yi daita ne suna hira ?.
hannunsa ya kai yana shafa daidai satin zuciyarsa dake bugawa tmkr zata fasa qirjinsa tayo waje ya dinga jin tamkar yayi reves ya dawo ya shiga inda yake jiyo murayarta ya tabbatar ita din ce ko kuwa muryar ce kawai tazo daya amman sai zuciyarsa ta kwabesa wankakkiyar zuciyarsa ta sake yin magana dashi kaje ka duba ko itace wata zuciyar tace kai ba itace ba ,ba yarinyar mafarkinka bace, dan haka a natse ya daga kafarsa daya bai kai ga ajiyewa ba ya sake jiyo sautin muryarta"."ku ne fa kuka bukaci kwararrun masu irin aikinmu yau tsawon wata guda kenan ina zariya a ma'aikatan ban samu nasarar ma hawowa saman ba sai yau ,yau din tun karfe bakwai na safe nake cikin compaing dinku kafin ma ku yarda na hawo saman nan sai da kuka bata min lokaci na samu da kyar na hawo yanzu kuma kuna kawo min qabli da baadi kunsa irin wahalar dana sha kafin na kammala aikin nan kuwa ?"kunsa lokacin da yake daukar mutun kafin mutun ya kammala ,shikenan shikenan!! tunda bakwa bukata ku bari na wuce na kama gabana daman an fada min wahalar banza kawai zanyi byn hka bakwa girmama masu tallata kasuwancinsu tana gama fadar hk ta juya haka zalika fuskarta a rufe take "no madam bamuce bama bukata ba mutane dayawa sun kawo nasu zanen maganar da nake miki har yanzu mai gida bai duba ba bare ya tantance bazamu iya cewa komai ba a yanzu dole sai an agwadawa boss ".
Ta juyo ta fuskacensu sosai.” har zuwa wani lokaci kenan zaa gwada masa sannan zuwa yaushe zanji feed back ?zai iya daukar wata uku zuwa ..tsaki taja ta sake juyawa tana tafiya tana cewa "gashi nan na bar maku bana da bukata domin ko na koma dashi gida babu amfani da zai min ."snyayen Kamshin turarenta ya bugi hancinsa yayi saurin lumshe idanushi zuciyarsa na cigaba da mugun bugawa ta kusa dashi tazo ta wuce har tayi taku uku ta fahimci ba ta nan hayar fita take ba dan haka ta sake juyo wa ta nufi kofar da lift yake ahankali Ya juyo yabi bayanta da kallo yana kallon every step of her doguwa ce sosai kuma bakar mace ce yayinda tsayinta ya fito da ainin shape dinta na cocacola iya haka kawai ya iya fahimta domin hannunta da kafafunta abayyane suke haka hijab din dake sanye ajikinta qaramin ne hkn ne ya bashi damar dan fahimtar wani abu a tattare daita "
ATA yana tsaye tamkar gunki yana kallon tafiyar yarinyar da bai san ko wacece ba amman jin sautin muryarta da yanayin tafiyarta yasaka zuciyarsa jin wani irin tsoro mai tsanani da shiga tashin hankali shi gani yake ma babu tantama itace ba anya kuwa ba gizo tayi masa ba kamar yadda yake ganinta a mafarkinsa har yanzu kwayar idanunshi yana Kan hanyar databi ya kasa kwakwaran motsi wani irin ajiyar zuciya ya sauke tamkar ya dakatar daita ya daga black nikaf din dake manne da idanunta yaga fuskarta amman gangar jikinsa da komai nasa yayi rauni zuciyarsa kuwa sai bugawa take babu Kaukautawa ba shiri ya dafe daidai saitin zuciyarsa ya a manne jikinsa da bangon wurin dan yanayin da yaji akanta ya wuce misali hakan yasa kafafunsa suka kasa dauakarsa ."ya sake kurawa hanyar data bi ido har lokacin tafiya take mai hade da rasauya tamkar fure hankalinta kwance take taka kasa tana gyara zaman qaramin hijab dinta wanda akewa lakabi da haif sunnah, gyara tsayuwarsa yayi sosai tare da zura hannunwansa duka cikin aljihun wondonsa zuciyarsa na cigaba da bugawa da sauri sauri yayinda gabadaya ma'aikatan dake aiki a office din da maryama ta shiga suka fito domin binta da makeken hotonsa wanda ta zana ."
turus sukai gabadaya suna kallonsa kowannensu ya gyara tsayuwarsa yana kare masa kallon abinda basu ta'ba ganin ya faru ba, basu ta'ba ganin abinda ya dauki hankalin mai gidan nasu ba sai yau ya kusan miniti goma yana tsaye yana fama da zuciyarsa dake karkarwa" Wayyo allah ina ma zai iya da yasa an dakatar daita ko sau daya yaga fuskar ko mafarkinsa ce har ta shige lift bai motsa ba ,sautin gaisuwarsu ce ta dawo dashi hankalinsa a natse .kallo daya yayi masu ya juya batare daya amsa ba yana tafiya yana sauke numfashi a natse ya dinga daga kafafunsa tamkar mara laka a jiki jikinsa baqaramin sanyi yayi ba har ya shiga office dinsa ya wuce sectary dinsa zaune tana ganinsa ta mike da sauri cike da girmamawa ta biyosa office dinsa har sai data ga ya samu wuri ya zauna "good morning sir cewar sectary ya gyada mata kai ta wuce domin komawa bakin aikinta , a can waje kuwa tabe baki ma'aikatan sukai sannan suka koma office bakin aikinsu ."wanda yake rike da katon zanen adam Ya nufi inda aka ajiye sauran zanen da mutane suke kawo ."
, ATA ya zauan tare da kunna system dinsa sai dai zuciyarsa ta kasa samun kwanciyar hankali amman haka ya cigaba da aikinsa amman ya kasa samun natsuwar yin aiki ji yayi duk wani kuzari nasa yayi kasa wata irin soyayya princess dinsa ce ta dinga taso masa daga zuciya yana jin kansa muddin babu ita arayuwarsa tabbas nashi rayuwar bashi da wani amfani ya furzar da iska mai zafi yana ture system zuwa gefe ya dauki waya ya kira number sectary dinsa mgnr daya yayi ya katse ya sake janyo system gabansa ,byn kamar second uku ta bayyana a gabansa rike da wani file cike da girmamawa tace "sir !"yaake ciki game da masu zanen danace?sir ai kwararrun masu zane sun kawo irin zanensu "me yasa baki fad'a min ba ?sir ganin baka da time shiyasa ban maka magana ba "ni nace miki bani da time ?yayi mata tambayar a tsawace nan take jikinta ya kama rawa ta sake kankame file din hannunta "kayi hakuri sir nayi kuskure numfashi ya sauke yana cewa "get out ."
Ta rusuna masa sannan ta juya byn Kmr mintuna talatin ya fito yayi hanyar waje yana kiranta ta biyosa da sauri bai tsaya akoina ba sai bakin koridoor ya tsaya yana bata umarni " call ja....kafin ma ya qarasa ta nufi office dinsa ,basu wani jima ba suka dawo tare dashi "good morning sir “amm james muje naga creations din da'akawo "okay sir !
Da sauri yayi gaba ATA na biye dashi wanda da kyar yake iya daga kafafunsa yayinda sectary dinsa ke biye dashi har zuwa babban dakin daaka tanada domin ajiye duk wani creations din da'aka kawo yana gama shiga dakin ya já Ya tsaya batare daya basu umarni ba suka shiga bude masa duk wani creation da'aka kawo yayi shiru yana kallon creation daya bayan daya wasu zanen kaya sukai doguwar , wasu suit da riga wasu kuma zanen mutane haka yayita kallo duk babu wanda ya dauki hankalinsa dan haka yayita jan tsaki yana qarawa har ma ya soma gajiya da kallon creations din har ya juya James yace "sir kalli wannan ka gani juyowa yayi sosai yana kallon zanen da shine aka zana sak
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.